sashe yayi muku kadan kenan ku suka raɓa ba ku kuka raɓa su ba"
Haihuwa-Da-Hanji-Complete Hausa Novel · about 230 min read
Hakane kuma gaskiya Gaje, kai Sabrina ta gyaÉ—a
"Zan san abin da zan yi akai, amma ko za ku dawo nan É—in ne?"
"Ta ya kenan 'yar albarka?"
Baba ya faÉ—a, ta saki murmushi
"Kar ku damu na san yadda zan yi saleem yayi musu korar kare a gidan nan"
Hira suka cigaba da yi wane sa'anninta ba iyayenta ba duk wani tuggu sun haɗa shi a ƙarshe
baban ke cewa
"Ai duk yadda za mu yi mu yagi rabon mu kan a je lahira za mu yi, ko a gaban Allah laifin mu
kadan ne ita ta ga dama ta bamu hanya zuwa cikin gidanta shekara nawa ina faÉ—i tashi akan ya
kula ki sai da na hakura na cire rai kwatsam ta dawo da zancen ashe muna da rabon dangwalar
arziki mu ma, bari mu je mu fara tattare"
Sallama suka mata suka bar gidan ransu kal...
****
"Saleem..."
Ya kira sunan yana zama gangar shi, buÉ—e rinannun idanunshi yayi ya zuba su kan Rayyan É—in
ba tare da ya ce komai ba, duk wannan É—in ba halin Saleem bane na Rayyan ne hakan ya sa
Rayyan É—in ya É—an damu.
Yana zaune kawai ya ga Shigowar saleem É—in office É—in kuma bai ce mishi komai ba bayan
sallama ya samu wuri ya kishingida.
"Menene? Me yake damunka?"
"Ni ma ban sani ba Rayyan, kawai ina jin ƙunci ne raina babu daaɗi zuciyata na mini zafi ba na
iya bacci"
"Saleem kana karatun Alqur'ani?"
Ya girgiza kai don ya fi 2weeks rabon da yayi karatu in ba a sallah ba.
"Alqur'ani wani dafa'i ne na yaye ƙuncin zuciya saleem, idan ka ga ba zaka iya bacci ba kayi ta
nafilfili kana karatun za ka ji sauƙi, ka fi kowa sani na har a yanzu bana bacci kaman na mutane
amma da na riƙe ibada ban zauce ba... Ka roƙi Allah ya yaye maka dukkanin damuwowinka"
Kai ya gyaÉ—a, Rayyan bai kara cewa komai ba ya tashi yayi playing karatu a office É—in ya je ya
É—auko ruwa ya kawo mishi ya É—an sha tare da kwanciya a three seater abin mamaki tun karatun
na shigar shi har bacci mai tsananin daaÉ—i da natsuwa ya É—auke shi ba tare ma da ya san yayin
ba.
Saleem ya yi baccin Awa biyu cip kan ya farka har lokacin Rayyan na office É—in yana wani aiki a
system ganin ya farka ne ya mishi sannu, kai ya gyaɗa ya miƙe ya shige toilet da ke ta tashin
kamshi wanke fuska yayi tare da alwala don ana ta kiran la'asar, bayan ya fito Rayyan ma ya
rufe duk abin da yake yi don baya tunanin daga masallaci zai dawo office É—in ya shiga bayin
yayi alwala ya fito yana gyara hannun lafiyayyar farar shirt É—in shi da ya É—ora akan navy blue
wandon jeans, rigar suite É—in ya dauka da briefcase É—inshi suka fice yana kulle office É—in. Sai da
ya zube abubuwan a mota suka isa masallaci suka yi sallah.
"Za ka iya driving É—in ko in mayar da kai"
"No zan iya"
Ya faÉ—a a hankali.
Da kallo ya bishi har ya shiga motar shi ya bar wurin, ƙasa natsuwa yayi da yanayin saleem ɗin
duk sai ya tsaya mishi, da wannan 'yar damuwar ya nufi gida horn yake dannawa a kofar gidan
da gudu aka wangale mishi gate ya cusa motar ciki, idanunshi ne suka faÉ—a kanta sanye take
da wani stylish crepe Adire ta haÉ—a shi da matching colour purple na Jersey, daga inda yake
yana hangar labbanta dake shekin man baki sossai tayi kyau amma shi ba kyaun yake gani ba.
Dr. Sulaiman dake tsaye yana mata magana ya ɗan zubawa idanu kan ya ƙarasa parking ɗin ya
sauƙa sai ya ɗauke kai kaman bai san akwai halittu wurin ba, tafiya yake kaman ba zai taka
ƙasa ba har ya ɗan gota su Dr. Sulaiman ya taso
"Assalamu Alaikum warahmatullah Dr. Rayyan"
Sai da ya É—an lumshe ido ya buÉ—e kan ya É—an waigo ya kalleshi ba don ya san muhimmancin
sallama ba babu abinda zai sa ya amsa, hannu ya miƙa mishi suka gaisa ya juya ya shige ciki
fuskar nan kaman an mishi mutuwa.
Sai da ya ɓace ta sauke numfashin da ta riƙe Dukda ko kallon inda take bai yi ba, kwarjinin shi
ya matuƙar cika ta ta tabbatar haka Sulaiman ma don babu wanda baya shan jinin jikinshi a duk
sadda Rayyan ya matuƙar tsumewa, ita dai ta san Rayyan ba ya rasa nasaba da sarauta.
"Afeefah me kika ce?"
Dr. Sulaiman ya faÉ—a
"Zan tambayi Mammi in shaa Allah in ta amince tunda gobe half day juma'a sai ka zo mu je in
na tashi school"
"Toh shikenan, ga wannan"
Ya miƙa mata leda kin karɓa tayi sai da ta ga ranshi ya ɓaci kan ta amsa don bata yadda ta iya.
Kai tsaye wurin Mammi tayi don ta bata ledar ba ma ta bukatar buÉ—ewa kan ta kai mata, da
kuwa ta san abinda zata tarar da bata shiga ba faÉ—a sossai Rayyan ke yi na shi baya son
tarukuce idan abinda zata yi kenan ta tattara ta bi samarin nata yaushe har ta tafasa da zata
ƙone? Haka ta ga Abeeha na yi? Toh shi ba irin tarbiyar da yake ba ƙannenshi ba kenan in
kuma tana gidan dole tayi abinda ta ga su Abeeha na yi.
Jikinta rawa ya ɗauka, Mammi ta riƙo hannunshi
"Duk faÉ—ar nan na Sulaiman ya zo ba tare da ka sani bane? Kayi hakuri ni ce na mata izinin fita
ba haka kawai tayi fitan gaba gadi ba kuma ko mintuna biyar bai kai ba idan nima na yi laifi sai
in ji..."
Shiru yayi bai ce komai ba.
Tana tsaye a gefe kaman yajin kosai kafafunta kaman za su kayar da ita saboda yadda suke
rawa don mugun kallon da ya aika mata, ledan hannunta ya kalla
"Ba kin ga kalar rainin da bana so ba Mammi? Mun ce ba mu dashi ne da zai kunso koma
menene a leda ya kawo mata? Ko ta tambayi abu ba'a yi mata ba?"
"Saraki...! Bana so! ka ga bana so don Allah, ka duba yadda ka firgita ta? In kuma hankalina
kake so ka É—aga ka cigaba"
Da É—an faÉ—a tayi maganan, haushin kanshi ya ji ina ma ruwan shi da zai damu da tarbiyar ta?
Shi ba wani tsiyar yake dubawa ba sai kar ta lalace da tara samari tun bata kai lokacin ba,
Miƙewa yayi ya nufi fita daga ɗakin ranshi a haɗe fuskar nan murtuk, wani irin chill abu ne ke
bin jikinta na tsoro, bata san me yasa shi baya wani damuwa da damuwarta ba a ranta take jin
kaman bai yi na'am da zamanta a gidan nasu ba, ita idan ba don mammi ba wlh ko inuwa ba
zata so haÉ—awa da shi ba bare har magana, gashi nan tana ta aikata laifin da zai ji haushinta.
Kamshinshi ne ya daketa a sadda ya wuce ba tare da ya ko kalleta ba ta lumshe ido sai da ta
tabbatar ya tafi ta sauke numfashi ta isa wurin Mammi tana jin hawaye na tsinke mata
"Mammi ki yi haƙuri ban san ba'a haka anan ba, na fita ne ba don wani abu ba sai don Roƙon
da Dr yayi ta min a kan ko ba zan É—auke shi Masoyi ba in É—auke shi wa da zan iya neman abu a
wurinshi yayi min, ya ce min Mamanshi ta damu tana so in je ta ganni ta ji lafiya ta don kaman
'ya itama ta ɗauke ni wlh ba ni na roƙe shi ba Mammi kin ga da kyar na karɓa har saida ranshi
ya ɓaci..."
Dafa ta Mammi tayi
"Natsu Afeefah! Ki natsu kar masifar Saraki ya dame ki, haka yake wlh kin ga su jidda basu isa
su kula saurayi ba sai ya fara zuwa ya ganshi yayi bincike ya amince mishi kan ya zo idan yayi
bincike bai mishi ba ko wayanshi suka sake É—auka mai karbar su a gidan nan sai ya shirya, na
sani a yanzu babu zancen aure tsakanin ki da Sulaiman shiyasa na bari kika fita, kuma ai ba'a
mayar da hannun kyauta baya... Goben ki shirya sai ku tafi da Abeeha in ta dawo school ku
gaishe da mahaifiyar tashi kinji?"
Tsoro ne ya sake rufe ta jin yana duka, itama kenan zai iya bugun ta in tayi ba daidai ba
"A'a Mammi ba sai na je ba, zan bashi uzuri..."
"Kar ki wani damu zan mishi magana"
Ledar ta ajiye don ji take ko abin ciki bata sha'awar gani, hankalinta ba'a kwance ba ta tashi tayi
É—akinta ko da ta shiga sai da ta sakawa kofar key don ji take kaman zai biyo ta ya cigaba da
faÉ—a.
🖤Gureenjoh🖤
HAIHUWA DA HANJI
(A True life story)
Fatima Muhammad Gurin
(Gureenjoh)
Wattpad-Gureenjo6763
Arewabooks-Gureenjoh
*FREE BOOK*
*FATIMA A MUHAMMAD Sirikata kuma namecyna ina so in yi amfani da wannan dama in miƙa
saƙon godiya da kuma jinjina bisa irin kokarin da kike yi a kan wannan littafi, haƙiƙa ba ni ma da
kalmar da zan nuna miki jin daaÉ—i na da kuma yabawa mai tarin yawa wannan shafin naki ne
kiyi yadda kika ga dama da shi... Jama'ar gidan haihuwa da hanji conversation room ina ganin
tarin comments naku sai dai lokaci baya bani dama a kullum na shiga a sha fira da ni amma ina
matukar jin daaÉ—i kuma ina yabawa ku sani muddin Aminiyar ango(Fatima A Muhammad) ta
amsa wallahi kaman ni ce nan na amsa. Ina kuma yi muku albishir gobe public holiday za mu
samu damar jero shafuka biyu in Allah ya yardar mana. Na gode sossai*
*27*
Washegari friday har ta je school ta dawo bata daina tuna irin faÉ—ar shi na jiya ba, ita kam ba
don mammi ta tabbatar mata da sai ta je ai shi zumunci yake so da ita ba tsiya ba, wanda yake
sonka da arziki kuwa ya gama maka komai da babu inda zata je ai zama lafiya ya fi zama É—an
sarki.
Ko da ta dawo da É—akin Mammin ta fara ta duba jikinta suka É—an yi hira kan ta wuce É—akinta aka
biyo ta da abinci, sai da ta ci kan ta shiga tayi wanka da alwala ta zo tayi sallah, a gaban mirror
ta zauna tana kallon kanta a yanzu ko ita ta san ta yi kyau, ta ɗan yi ƙiba skin ɗinta na wani irin
yalki don man da Abeeha take shafawa ita ma shi ta saya mata kuma skin tone É—in su É—aya, ta
sake cika tayi kumatu kaÉ—an sai ya mata kyau, kwalli ta zana a idanunta bata cika sakawa ba
amma ta san yana mata kyau kawai dai bata son sakawa ne don yana sa idanunta hawaye sai
wani ruwa ya kwanta ciki kaman mai, dama gasu da girma masha Allah, lip gloss ta shafa ta
miƙe ta tafi gaban wardrobe.
Abaya ta É—auko wani blue da adon fari egyptian ne ya amshe ta sossai ta saka farar hula don
farin gyale yake da shi sai ta yafa gyalen ta yi kyau sossai sai ta ji nishadi a ranta, wa zai ganta
ya ce Afeefar Dutsen-wai ce, Mayya kuma annoba? Wa zai ce tagayyara aka so tayi Allah ya
dube ta ya tallafi rayuwarta? Malamin islamiyyarta na makaranta na cewa Allah zai buÉ—e ma
bayinsa kokafofin rahama da sauƙi cikin ko wani tsanani muddin ka saka tsoronshi da tawakalli
cikin ranka, sannan zai buÉ—e maka kofofin arziki ta inda baka yi zato ko tsammani ba ko a
mafarki bata zaci ganinta cikin irin wannan gida tana rayuwa ba, tayi tunanin za ta tabbata a
bauta da wahala a kasakance amma da Allah ya ce ba hakan bane ga inda ya kawo ta a yanzu.
Da kyar ta bar gaban madubin wurin Mammi ta nufa.
"Masha Allah Daughter ta tayi kyau tabarakallah!"
Murmushi tayi tana zama gaban Mammin
"Mammi zolaya ta fa kike ina kyau anan? Ko fa powder ban shafa ba"
Mammi za ta yi magana kenan Abeeha ta shigo kaman ta jima da Dawowa don ba da kayan da
ta fita ta shigo ba.
"Afeefah Dr. Sulaiman ya kira yana harabar gidan nan"
Mammi tace
"Abeeha gobe dai tunda saturday ne ku je ki nema mata waya mai kyau"
Murmushi Afeefah tayi tana Miƙewa
"Sai kun dawo a gaishe su, sannan a kula. Abeeha kar ku jima kin san Yayanku"
Da Toh duk suka amsa suka fice daga parlorn.
Ta jima sossai tana tuna Afeefah a ranta kan ta sauke ajiyar zuciya tana Miƙewa da kyar cikin
yanayin rashin ƙarfi da cikakken lafiya ta shiga cikin ɗaki.
A harabar gidan kuwa suna fitowa Rayyan na parking, gaban Afeefah ne ya faÉ—i zuciyarta ya
shiga doka wa da ƙarfin gaske, a natse ya buɗe murfin motar ya sanyo jikinshi waje Farar
jallabiya ce da daga ganinta zaka san tana da tsada sai maiƙo take yi kirar Kasar dubai don
tana da wani ado mai yanayi da rubutun larabci daga gefen kirjinshi kaÉ—an har karshen hannun
hagunshi, hirami ne baƙi mai layi layi fari ya mishi wani ɗauri a kai yadda Larabawa suke yi ya
zauna mishi sossai yayi kyau, kafafunshi sanye da halfcover Milano baƙa, hannunshi na daure
da wata silver agogo yayinda zoben azurfan dake yatsar shi na kusa da ƙarshe ke ta daukar
idanu.
Kallon duk a seconds biyar ta yi mishi don fargaba da ta kan tsinci kanta a duk arean da yake,
baƙar shade na maƙale a idanunshi ba za ta san ya ko kalli iskar da ya kwaso su ba yau ko
Sulaiman dake zaune cikin mota bai kalli sashen da yake ba ya shige gidan kamshinshi na buso
musu, Abeeha ce ta iya yi mishi
"Sannu da dawowa"
Hannu kawai ya É—aga mata wai shine amsar ya shige abunshi.
Motar Sulaiman suka isa Afeefah ta shiga gaba Abeeha ta zauna baya suka fice daga gidan
suna sake gaisuwa.
Har suka isa shi ne yake hira da Abeeha ita kam tana zaune shiru, shi ya musu iso har cikin
gidan Baaba ta taso ta rungume Afeefah dake ta murmushi a ƙasa ta zube tana gaishe da
mahaifiyar shi Umma ta miƙa mata hannu ta je kuwa ta kama sai ta zaunar da ita gefenta tana
É—an rungumeta kaÉ—an
"Ina ta jin labarin É—iyata sai yau Allah yayi zan ganta! Barka da zuwa barka da zuwa"
Murmushi Afeefar ke ta yi hakika ta ji matukar daaÉ—in irin tarbar da ta samu, kayan kwadayi da
su drinks aka cike musu gaba da su ita dai kunyar Ummar take ji yadda take ta jansu da hira shi
Sulaiman ya fice Sashenshi da a cikin gidan yake.
Sun jima sossai har aka yi la'asar suka je suka gabatar suna dawowa parlorn Su Fauza suka
fito shirye don wucewa islamiyya suka yi sallama akan su ma za su zo musu suka fice, basu
jima da fita ba sai ga Sulaiman da matarshi sun shigo, kyakyawa ce kuma fara tasss bata da
wani girman jiki a shekaru kuma da kaÉ—an za ta iya fin Afeefar kila su yi sa'a da Abeeha, zama
tayi tana ce musu sannu.
Gaisawa suka yi kadaran hadaran, tunda ya ce mata da Afeefah yake ta zuba idon ganin
Afeefar da bata santa ba amma ta yi matuƙar haddace sunan saboda yawan Ambaton da
Sulaiman ke yi musamman in tayi wani abu, sai ta ga Afeefar ma ba wai kyau ta fita ko ado ba
haÉ—iye abin da take ji tayi ta yi musu sallama ta fice.
Baaba ce ta kawo zancen su kawu tana tambayar Afeefah me yasa suke kiranta annoba? Shiru
ta ɗan yi kan ta shiga basu labarinta daga farko har ƙarshe, Baaba da Umma sun sha kuka
umma ta sake rungumeta tana cewa
"Sannu Afeefah... Sannu! Allah ubangiji ya ƙara miki karfin zuciya da imani ya wanke miki duk
wannan wahalhalun"
Ta amsa da Ameen tana murmushi don a wannan karo bata yi kukan ba illa iyaka Adu'a da tayi
ta bin iyayenta da Aunty zee.
Sulaiman dai bai iya ya ce komai ba a ranshi yake ayyana Dole ta sha piya-piya don kashe
kanta, dole ta samu saukar jini don damuwar, ya so da ita ce a É—akin shi a yanzu matsayin
matarshi ya bata duk wata kulawar da ta dace amma gani yake lokaci ya riga ya ƙure, Dukda
haka zai zauna matsayin yayanta zai bata duk wani gudumawar da ya dace a rayuwarta daga
yanzu.
Karfe hudu ya maida su sun bar gidan da tsaraba niki niki daga Umma ta kuma roki Afeefar da
ta dinga zuwa mata, har cikin gida ya dawo dasu suka yi mishi godiya suka nufi ciki.
****
Karfe 3:40 ya fito ya wuce masallaci sai wuraren 4:20 ya koma cikin gidan kai tsaye sashen
Mammi ya nufa don ya duba ta, tana zaune kan sallaya sai dai kanta na kife ne a bakin gado,
da É—an hanzari ya isa gareta
"Mammi! Lafiya kike kuwa?"
Ta ɗago ta sakar mai murmushi ya runtse ido da ƙarfi, da gaske murmushi take sai dai a cikin
murmushin wani irin ciwo yake hanga da damuwa haÉ—e da gajiya, a idanunta wani abu mai
wuyar fassara yake karantowa, tausayi da rauni suka rufe shi wanda basu ɓuya ba sam don a
kan Mammi baya iya danne damuwarshi.
"Saraki..! Ina lafiya, ka zauna za mu yi magana"
A gabanta ya zauna kasancewar akwai turkish center carpet mai tsananin taushi da tsada dake
malale tsakar É—akin.
"Ina muka kwana da zancen mu? Saraki babu lafiyayyen namijin da zai iya dawwama ba tare
da mace ba, aure na sani ba dole ba ne amma babbar sunnah ce ta ma'aikinmu sannan akwai
wani hadisi da Manzon Allah yayi magana akan bayan mutuwar mutum komai nashi zai tsaya
chak sai abu guda uku, sadaka mai gudana, ilimin da ya samu ya kuma bayar da shi sai É—a
nagari mai mishi Adu'a ashe baka Fatan ka ajiye 'ya'yan da za su yi maka Adu'a bayan baka
nan? Bana so in sake ji ka ce min ba zaka taɓa aure ba wanchan kuskure aka samu da akasin
rashin sanin nagarta da kyaun halinka... Ba duka aka taru aka zama É—aya ba"
Kallonta kawai yake idanunshi duk sun sauya sun zama red har jijiyar kanshi na tashi, sam
baya so baya son jin zancen wani aure daga bakin Mammi, a baya dai ya so yi amma bai san
mummunar taɓonshi zai sa a hana shi aure ba, bai san za'a iya kallon cikin kwayar idanunshi a
faɗa mishi kalmar da har abada ba zai taɓa mantawa ba, baya so a maimaita baya so samm.
"Mammi..."
"RAYYAN...!"
A razane yake kallonta jin yadda ta katse shi, ta katse shi da asalin sunanshi da bata taɓa ƙira
ba... GabaÉ—aya sai hankalinshi ya sake tashi a raunane ta ce
"Rayyan kana so in mutu ban ga ka samu cikakkiyar natsuwa da kwanciyar hankali ba? Kana
so in tafi wurin ubangiji ina tunanin rayuwar ka zai iya taggara bayan babu ni? Kana so in tafi in
barka ban cika alkawarin da na É—auka wa rayuwarka ba?"
"Yaaa ilaihil alameen..."
Ya faɗa a rikice sai ya miƙe tsaye don wani irin tashin hankali yake ji, taku biyu yayi gaba ya
juya yayi biyu baya yana shafa kanshi zuwa fuskarshi ji yake kaman ya tsala ihu ko zai fahimtar
da Mammi abin da yake ji a cikin zuciyarshi.
Zama yayi ya kalleta
"Mammi saboda ke don ke kaÉ—ai zan amince da zancen aure! Amma ban san kuma ta yadda
zan je in cewa mace ina sonta ba, ban ma san menene son ba, ban san ta ina zan fara ba
kuma... Na bar miki, na bar miki wuka da nama duk abin da kika yanke ni mai karɓa ne"
Shiru tayi tana kallon shi, ya riƙo hannunayenta
"Mammi kin san yadda na ɗauki alƙawari, na miki alƙawari zan yi iya kokarina a duk abinda za
ki yanke a kaina, wanene ni da ba zan miki biyayya ba a duk abin da kike so? Ki kawo ko
wacece zan zauna da ita yadda kike so matuƙar hankakinki zai kwanta, matuƙar za ki daina yi
min zancen tafiya ki bar ni... Mammi kika ci gaba zuciyata za ta iya tarwatsewa"
Hawayenta ne suka zubo, ta gimtse hannunshi dake cikin nata tana murmushi a lokaci guda ko
babu komai zai tuna da ita ta zaɓar mishi mata, zai tuna da ita ya yi mata adu'ar alkhairi a duk
sadda zai ga wannan mata ya ji farin ciki, in shaa Allahu ba zata yi zaɓin nan da kanta ba za ta
bar wa Allah, za ta tsaya tsayin daka ta roƙi ubangiji yayi mishi zaɓi da kanshi ta san sai ya fi
dacewa duniya da lahira...
Anan suka bar maganan ya miƙe ya fice, ta bishi da kallo ta tabbatar yau bacci rabi da rabi zai
yi hannu ta É—aga sama tana cewa
"Allah ga bawanka nan Rayyan! Allah ka sassauta mishi Allah ka yaye mishi matsalarshi Allah
ka sada shi da duk wani farin cikin wannan duniya ka bashi dacewa a ƙiyama..."
Ta shafa.
Daga wannan rana Mammi ta dukufa adu'ar neman zaɓin Allah, ko sau daya bata yi tunanin
wata mace ba damuwarta kawai Allah ya zaɓa mishi mafi alkhairi cikin mata, ya zaɓa mishi
matar da za su tabbata har a aljannah wacce zai so ta, wacce idan ta tashi barin duniyar za ta
kular mata dashi ta yadda ba zai yi kukan rashin ta ba don har a yanzu jin Rayyan take kaman
yaro ƙarami da kan riƙe hannunta yayi kuka yayi kuka matuƙa idan an faɗa mishi abin da ya
taɓa zuciyarshi, har yanzu ganinshi take kaman wannan dakakken yaron mai tsananin juriya da
ƙarfin hali wanda duk wani abin da zaka mishi baya bari a ga rauninshi sai in yana gabanta.
Ta ɗauki tsawon sati biyu tana wannan roƙon Allahn a cikin uku bisa ɗayan dare lokacin da
Allah ya ce mu roƙe shi zai amsa mana, lokacin da ubangiji ke sama na ɗaya yana neman
bayinshi masu roƙon shi ya amsa musu babu hijabi, a yau daren Alhamis safiya juma'a bayan ta
gama nafilfilunta ta kwanta kaɗan saboda dan ciwo dake damunta a ciki, dole bacci ya lallaɓa
ya dauƙeta ana ƙiran farko na assalatu ta farka a ɗan firgice ta miƙe zaune, a hankali ta saki
murmushi mai kyau kan tayi Adu'a ta miƙe ta nufi bayi don gabatar da Alwala.
🖤Gureenjoh🖤
HAIHUWA DA HANJI
(A True life story)
Fatima Muhammad Gurin
(Gureenjoh)
Wattpad-Gureenjo6763
Arewabooks-Gureenjoh
*FREE BOOK*
*Comments É—in ku shi zai yi determining Page na dare%*
*28*
Tun ƙarfe goma sha ɗaya na safe Rayyan ya bar office don ya je da wuri yau din saboda wani
aiki da ya taso, gida straight ya koma yayi wankan juma'a don yana so ya fita da wuri yana so
ya fara biyawa wurin salim da ya rasa gane kanshi a kwanakin.
A shirye ya fito cikin shigan manyan kaya don fa shi yana son manyan kaya haka kawai bai cika
son sa kananun kaya ba kaman yadda yake saka manya É—in, governors yard ne da aka yi wa
dinkin zamani ya zauna mishi sossai da sossai, ko da ya fito É—akin Mammi ya fara yi ya sameta
zaune tana azkar É—inta da bata rabo da shi.
"Sannu da hutawa Mammi"
Ya faÉ—a yana zama gefenta
"Sannu Saraki ashe ka dawo har ka yi wanka"
Ya gyaÉ—a kai
"Ina so zan fita da wuri ne zan biya wurin Salim"
"kwana biyu kam bai shigo ba, ko da shike lafiya shi ke ɓuya ko?"
Murmushi kawai ya ɗan yi zai yi magana sai ga Afeefah ta shigo hannunta riƙe da tray mai
dauke da plate na abinci.
Bata san yana nan ba da bata shigo ba don fa ita duk abin da zai haÉ—a ta dashi kiyayewa take
saboda yadda bata samun natsuwa a area É—in da yake gashi abin laifi baya mishi kaÉ—an yanzu
ya hau faÉ—a da masifa, a gaban Mammi ta ajiye tray É—in ya bi trayn da kallo kan ya kalli Mammi
dake godiya ya ce
"Ba dai wannan abin za ki ci ba?"
Daga ita har Afeefah kallonshi suka yi abinci ne ya zama abu?
"Me yayi?"
Bai amsa Mammi ba sai Afeefah da ya kalla da idanunshin nan yace
"Kashe ta kike son yi?"
Wani irin faÉ—uwa gabanta yayi jin zancen kisa, hankalinta sai ya so tashi idanunta duk ta zaro
waje tana so tayi magana amma Muryar rawa yake, tana da trauma na batun kisa da ita kanta
bata sani ba, amma yadda ake jefanta da kalmar kisa yayi affecting mind É—inta ta yadda ko ya
aka ambaci kisa aka danganta ta da shi sai hankalinta ya tashi.
Tsawa ya daka mata cikin muryarshi da ke razana ta
"Na ce kashe ta kike son yi? Me yake damun ki da za ki dafa kowani shirme ki kawo mata?"
Ganin yadda ta sake firgita Mammi ta dafa shi.
"Saraki...! Wai me haka ne? Meyasa kake haka? Idan ka bi ta a hankali ai za ta fahimta ba sai
ka yi mata faÉ—a ba, kuma ni na saka ta dafa min ba gaban kanta tayi ba"
"Mammi ina Merry?"
Yayi tambayar ranshi a hasale, idan da bayanan sai Mammi ta ci abincin nan don ya tabbatar
ko don wahalar da wannan yarinyar tayi ta dafa zata iya ko loma kadan ne don yarinyar ta ji
daaÉ—i, Dukda Couscous ne amma akwai abubuwa masu yawa da bai kamata ta saka mata ba
ciki.
"Merry bata ji daaÉ—i ba jiki da jini, Abeeha na school shiyasa nace ta dafa É—in amma na tabbatar
bata gane bayanin da na mata bane ba da gangan tayi hakan ba"
Tsaki ya ja ya É—auki tray É—in ya fice.
A ƙasa ta zube tana sauƙe numfashin tsoro yadda yake zaro mata ido kawai take gani, Mammi
ta dafa ta
"Ki yi haƙuri Afeefah duk ya firgitaki"
"Mammi ban san akwai abubuwan da bai kamata ki ci ba ciki kiyi haƙuri laifina ne"
"ba wani laifin da kika yi na kirki Alaiyahu da kuma tomatoes da kika saka ciki duk are high
potassium veggies da bai kamata in ci ba su ne fa kawai sai zubin da yayi yawa kasancewar
Couscous É—in daga wheat ake samun shi, amma ai ina da ido kuma zan iya miki gyara shi dai
kawai zafin kanshi ne dayawa"
Dukda halin da take ciki sai da ta É—an murmusa kaÉ—an, yau public holiday shiyasa bata je
school ba itama Abeeha wani research take yi shiyasa ta tafi Merry wacce ke da karatu na
musamman akan nutrition É—in irin masu ciwon Mammin bata da lafiya shiyasa ta shiga kitchen
É—in ta girka ba wai don gwaninta ko nuna iyawa ba, jikinta ya yi sanyi bata ma zauna wurin
Mammin ba ta fice kar ya dawo ya sameta.
Shi kam kitchen É—in ya koma, a hankali masu aikin suka zame suka fice sanin kila da kanshi zai
yi girkin kaman kuwa sun sani, a take ya fara shirya abincin Mammin, idan ka ga yadda yake
aiki za ka zaci wani professional Cook ne cikin taka tsantsan da tsantsar tsafta da Allah yayi
mishi, wanke hannu kuwa ko me ya taɓa sai ya je ya wanke hannu da handwash ya dawo, ko
sau ɗaya kayanshi bai taɓa komai ba har ya gama ɗan small portion na chicken salad wanda da
breast ɗin kawai yayi amfani duk wani ƙashi babu ciki, babu gishiri ya gasa da herbs kawai da
lemon, ya haÉ—a salad din wanda lettuce ne sai cucumber da Bell peppers da albasa kaÉ—an, ba
mayonaise ko cream ya saka ciki ba sai ya zuba man zaitun pure one a cikin dan karamin bowl
ya saka 1 tsp na vineger ya kaÉ—a da 'yar habbatussauda kaÉ—an ya juye a cikin salad din ya
gauraya ya zuba a cikin wani bowl mai kyau. Shinkafa ce 'yar kaÉ—an ya dafa mata half cup ya
haÉ—a da ruwa don bata shan wani sugar ko juice ya É—auka ya nufi É—akinta.
Murmushi ta saki tana mishi godiya, ita bata yi mamaki ba don kafin yayi hiring merry da kanshi
yake yi mata duk abinda zata ci shi ya uzzurawa su Abeeha har suma suka iya duk cimar ta da
yanayin awon duk sun haddace, godiya ta mishi yace
"Mammi babu fa wannan tsakanin mu har Abada, abin da ya zama min dole ne nayi"
Daga nan ya mata sallama ya koma É—aki ya sake gyara jikinshi kan ya kara turare ya fice daga
gidan.
Kai tsaye gidan su Salim yayi, kasancewar yanzu ba kaman da ba ta babban parlor ya shiga da
sallama, Mommy da ke zaune ta zabga tagumi ta É—ago ta amsa a hankali, ya zamu wuri ya
zauna yana gaisheta
"Lafiya ƙalau Rayyan ka shigo?"
Samha dake kuka ya É—an kalla kan ya kalli mommyn
"Lafiya kam mommy?"
"Ba ƙalau ba Rayyan, ban san me zan ce ba ban kuma san ta ina zan fara ba amma tabbas
Salim baya cikin lafiya da natsuwar shi... Rayyan ko za ka bashi shawara? Ko zaka mishi faÉ—a?
Don saleem bai É—auke ni uwa ba kuma, saleem ya fi gane maganar matarshi akan nawa yanzu
ya bar nan bayan ya fasa bakin Samha don kawai ta roƙe shi kuɗin makaranta suna shirin
exams bata biya ba matarshi ta sa baki sai tace mata ba da ita take ba da É—an uwanta take
shikenan har ya kai abin duka kuma yace ba zai biya É—in ba rashin kunyarta ya biya mata?
Saleem dai ina mishi magana ya É—aukeni banza? Innalillahi wainna ilaihi rajiun..."
Wasu irin hawaye masu zafi take zubarwa bata taɓa zato ko tsammanin irin wannan butulcin
daga Sabrina ba, shi karan kanshi Rayyan yayi mamaki don kowa ya san saleem ya san yadda
ya ɗauki mahaifiyarshi da ƙannenshi, shi ɗin mai biyayya ne ko da ko baya so zai yi don ya
faranta ran mahaifiyarshi, ya san dai saleem ya chanza mishi amma bai zaci har mahaifiyarshi
da yan uwanshi ba, sai ya kira shi ba zai É—aga ba kuma ba zai kira shi back ba, sau biyu yana
zuwa headquarter baya samun shi shiyasa ma ya yanke ya zo gida ya same shi, Dukda shi
namiji ne kuma ba kaman sauran maza ba amma daga maganan mommy ya fahimci akwai ayar
tambaya mai girma akan saleem.
Bai gama tunanin ba aka fara sallama, sameerah dake zaune shiru gefe ta miƙe ta nufi kofar.
"Mun zo daga companyn gadaje da kujeru ne mun kawo order É—in da aka sanya wannan
address É—in..."
"Anya gidan nan ne? Ko zaka kira Layin da aka yi order É—in?"
"Toh bari na ƙira"
Kira yayi cikin mintuna biyu sai ga saleem da Sabrina sun sauƙo, ganin Rayyan ya sa ya je ya
bashi hannu suka gaisa
"Saleem kana lafiya?"
Yayi tambayar yana sake nazartar abokin nashi da ya ji wani irin tausayinshi ya tsarga mishi.
"Lafiya me ka gani?"
Girgiza kai kawai yayi ya ce
"Zauna za mu yi magana"
Babu musu saleem ya zauna Sabrina za tayi magana ya É—aga idanu ya zuba mata haka kawai
kwarjinin shi ya wani irin cika ta, duk yadda ta so tayi magana kasawa tayi sai ta nufi kofa ta fice
tana kwafa.
"Me ya sameka? Me ke damunka abin da baka yi ba tun kana ƙarami zaka yi shi yanzu da ka
mallaki hankalin kanka? Saleem uwa ba Abar wasa bace ba kowace uwa ba, ba irin
mahaifiyarka da tayi dedicating lafiyarta, karfinta da kuruciyarta don ganin ta gina rayuwarka
ba... Ta gina ka ne don ka girma ka tallafi kannenka, yau idan baka biyawa su Samha kudin
makaranta ba wa kake tunani zai biya musu? Me ya hau kanka haka saleem?"
A tausashe yake maganan, saleem bai ce komai ba ya zauna shiru duk yadda Rayyan ya buga
ya kaÉ—a akan ya faÉ—a mishi menene matsalar bai ce komai ba, daga karshe Rayyan ya ce
"Saleem ka ba Samha kudin makaranta yadda ka saba bata"
ÆŠago ido yayi ya kalleshi shima shi yake kallo zuciyarshi na rawa, tabbas akwai ayar tambaya
akan dabiun saleem sai dai ba zai yi saurin yanke hukunci ba, yana zaune nan sai da saleem
ya dauki tsawon mintuna biyar kan ya zaro wayanshi yayiwa Samha transfer É—in kudin yadda ya
saba bata, mommy ta duƙar da kai tana kuka mai ciwo. Da zafi abin da zafi kana gani a
sauyawa danka rayuwa daga yadda yake zuwa wani abu daban.
"Je ka shirya mu tafi masallaci"
Bai ce komai ba ya miƙe ya haura sama, Rayyan ya runtse ido a hankali sama da seconds
goma ya buɗe sun dan sauya, Miƙewa yayi ya fice bai kula godiyar da mommyn ke mishi ba, a
gaban motar shi ya tsaya yana kallon Sabrina da ke tsaye ana sauƙe wasu kwalaye cikin store
nazarin ta sossai yake yi chan ya ɗauke idanu ya sauƙe kan saleem da ya fito, yana kallo sai da
yaje wurinta suka yi magana ta É—aga ta kalleshi kan ta gyaÉ—a kai saleem ya wuce ya zo ya
shiga motar suka fice daga gidan.
"Saleem idan ka ga Afeefah a yanzu za ka iya aurenta?"
Shi karan kanshi bai san ya jefawa saleem É—in tambayar ba don ya jima yana mishi yawo a rai
kuma yana son tabbatar da zarginshi kan Sabrina. Sunan Afeefah ya sake maimaitawa a ranshi
don dai bai taɓa ambatar sunan a fili ba ma sai yau.
"Aure? Ai ina da aure"
Ya amsa shi muryarshi babu wannan karsashin idan yana maganar da ya shafi Afeefah, kaman
ma wata ce chan daban da bai wani sani ba.
Bai ja maganan ba ya yi shiru, dole su tashi tsaye akan Saleem da alama zautar da shi ake
shirin yi, amma yayi matukar mamaki irin mamakin nan da bai taba zaton hakan zai iya faruwa
da saleem daga aure ba, auren ma na dangi ba bare ba.
****
Zaune take gaban Mammi don sai da ta tabbatar ya fice kan ta dawo, abincin ta tsurawa idanu
yadda ya tsara shi kaman wani chef tana mamakin yadda ya iya girki haka, Mammi bata ce
komai ba ta shiga cin abincin sai da ta gama tsaf ta dubi Afeefah tace
"Afeefah akwai maganar da nake so mu yi da ke ko kuma in ce akwai alfarmar da nake so na
roƙe ki ban san ko za ki iya yi min ba, ba abu bane da ya saɓawa shari'ar musulunci abu ne da
muddin kika amince min Afeefah zan yi matuƙar farin ciki fiye da zaton ki"
Afeefah ta gyara zama jin maganar serious ne, kuma a yadda Mammi ta É—auke shi da
muhimmanci ya sa itama ta ji ta bashi muhimmanci itama
"Tashi ki dawo nan Afeefah"
Miƙewa tayi ta koma kusa da ita yadda ta roƙa hannayenta duk biyu ta riƙe
"Afeefah na dauke ki ne tamkar Abeeha, ba zan taɓa yin wani abu da zai cutar da rayuwarki ba
amma ban san yadda za ki É—auki maganar ba.."
"Mammi yanzu fa kika ce ni tamkar Abeeha ce a gareki nima kuma ba ni da uwar da ta wuce ki,
wlh duk abin da kike so matuƙar zai faranta miki kuma bai saɓawa shari'a ba ni mai amincewa
ne Mammi, faɗa kawai za ki yi in cika shi na san ba za ki taɓa cutar da ni ba."
Afeefah ta katse ta ganin kaman contemplating take na gaya mata abin da take so, ita kuma
tana da yakinin koma menene Mammin za ta roƙa ba sharri bane.
"Afeefah za ki iya auren Saraki??"
Afeefah ji tayi kaman kunnenta bai ji mata daidai ba, bata motsa ba don bata gama fahimta ba
jin Mammi ta yi shiru tana kallonta yasa tace
"Mammi ina sauraranki in shaa Allahu zan yi duk abin da kike so"
"Afeefah abin da nake so shine kafin na mutu in ga na haÉ—a aurenku ke da Saraki...! Shin za ki
iya auren shi? Za ki iya yi min wannan alfarmar?"
Wani irin shock ne ya ratsa Afeefah daga kanta har cikin tafukan sawayenta, a matuƙar razane
ta zare hannunta daga na Mammi ta miƙe tsaye zuciyarta na wani irin bugawa kaman zai ratso
kirjinta ya fito
"a..ure? Ni Mammi? Ni... Ni Afeefah da Wanchan mutumin...??"
Don ji tayi ba zata iya ƙiran sunanshi ba ma ko Rayyan ɗin ko Saraki idan tayi hakan kaman
wani zunubi ne da muddin ya ji ta sai ya sauya mata kammani, kallon kanta take yi daga sama
zuwa kasa ta É—ago ta kalli Mammi kaman wacce ta zauce...
🖤Gureenjoh🖤
https://chat.whatsapp.com/BuI7cmoy3ed3C3IimZKZA0
HAIHUWA DA HANJI
(A True life story)
Fatima Muhammad Gurin
(Gureenjoh)
Wattpad-Gureenjo6763
Arewabooks-Gureenjoh
*FREE BOOK*
*29*
Hasaso Rayyan É—in ta shiga yi a majigin kwakwalwarta, kallo É—aya tak za ka yi mishi ka san
cewa shi É—in soja ne a sojojin ma na daban, yana da lafiyayyar jiki murÉ—aÉ—É—e kuma a tsaye yake
fatarshi babu ɗigon baƙi ko guda ɗaya, Dukda ba zata ce ga yadda yake cikin khaki ba amma
ko daga maganar shi zai tabbatar maka jajirtacce ne kuma gwarzon namiji wanda ko daga
kallonshi za ka sha jinin jikinka.
Zaman shi, tafiyar shi da yanayin dabi'unshi kuwa za ka zaci wani babban sarkin ne na wani
yanki na daban, yana da wasu irin idanu kyawawa da ko tuna yanayinsu tayi sai ta ji tsikar
jikinta ya zuba kaman ba namiji ba, fasalta kyaun fuskarshi da sauran halittar da Allah yayi
mishi ma wani tulin bayani ne na daban, don Allah ina ita ina irin gawurtaccen nan? Ta ina ma
Mammi ta fara wannan tunanin?
Tazarar da ke tsakaninta da Rayyan kaman tazara ne da ke tsakanin sama da ƙasa ko ta
amincewa aurenshi ita ce zata wahala daga karshe saboda ba zai taɓa son irin ta ba, ba zai
taɓa kaunar mace kamar ta ba wacce ta fito daga kauye cikin tsantsar jahilai, wacce take da
tambarin Maita kuma annoba, wacce ko wucewa ta zo yi gidajen mutane sai an zuba tafarnuwa,
Ƙashin kifi da garin kukan miya a wuta don hayaƙin Mayu.... Ai ko da gami wane ita da Rayyan.
"Mammi kaman ban ji abin da kika faÉ—a ba"
Ta sake maimaitawa har yanzu a kidime.
Miƙewa tsaye Mammi tayi ta riƙo hannunta suka koma zaune.
"Ki natsu Afeefah kin ji? Ki ba ni hankalinki kar ki yi wani tunanin fin ƙarfi, namiji bai taɓa fin
karfin mace ba in har ta amsa sunanta mace, ke kyakyawace kar kyaun Rayyan ya ruÉ—e ki, ke
yarinya ce mai hankali, ladabi, natsuwa da kuma biyayya kina da zuciya mai kyau, you are the
purest soul i've ever met... Afeefah ba zan hada ki da Rayyan bane saboda wani ra'ayi nawa ko
buri eh ina da buri a kan ku duk biyu, sai dai burin ba na komai bane sai na son ganin
rayuwarku duk ya inganta kun tabbata cikin farin ciki"
"Mammi shi ya ce miki yana so na?"
Ta tambaya a sanyaye don ba fahimtar kalaman Mammin take ba don abu ne da take ji ba zai
taɓa yiwuwa ba.
"Ba shi ya ce ba, ni ce na ga cancantar kasancewarku inuwa É—aya kar ki damu da halinshi ko
yanayinshi na fushi da dacin rai Saraki na da wani tabo ne da ya mayar da shi hakan wanda
dole zan faÉ—a miki Afeefah... Ina so in fada miki ba don tonon asiri ba, sai don ya zama dole ki
sani kan ki yanke shawarar za ki aure shi ko ba za ki aure shi ba? Ba zan miki dole ba wlh
kuma ba na so ki dube ni a yayin yanke hukunci ki yanke duk abinda ke ranki ni me karɓa ce
don sai da na nemi zaɓin Allah kan na tunkareki"
Shiru Mammi tayi idanunta sun rine sossai har suka tara hawayen da ya fara bin ƙuncinta, ɗacin
maganan da zata faɗa take ji har kan harshen ta maganan da bata taɓa faɗa da Bakinta ba
bata taɓa ambata ba sai a yau da ya zame mata dole, idanunta na kallon gefe ta furta
"Rayyan ba É—a na bane!!!"
Wani irin bugawa zuciyar Afeefah yayi da har sautin shi na fitowa fili ta zaro idanu gabaÉ—aya
tana kallon Mammi dake ta zubar hawaye
"Eh Afeefah ba ni na haife shi ba, hasali ma babu abin da ya haÉ—a ni da shi na jini ko na kusa
ko na nesa... Ni sunana Khadija ni haifafffiyar wannan gari ce ta Kaduna, mahaifina Alhj Isma'il
mai rasuwa mutum ne mai tarin dukiya mai yawa a gaske kuma su biyu Allah ya ba wa
iyayensu É—an uwanshi ma na da nashi arzikin don gada suka yi, mahaifina mutum ne da dukiyar
shi bai taɓa rufe mai ido ba, yana da kyauta tsantsa haka yana da taimako don haka ko da na
zama ni kaÉ—ai 'yar shi yana da Æ´aÆ´a dayawa da suke karkashin shi don lakabinshi ma shine
Uban marayu da masu uba... Yaran da ya biyawa suka karatu basu kirguwa sai dai in baki zo
wurinshi da kuka ba sai ya share miki hawaye, wannan dalili ya sa nima na taso da irin
zuciyarshi Dukda rashin lafiyarmu don shi ma ciwon sugar ne ya kashe shi kaman yadda ya
kashe baban shi, ƙannunshi ma Uncle Musa haka yake don suna da nasaba mai kyau suna da
ilimi boko da arabi.
Akan irin rayuwar da na tashi kenan har na kamallah jami'a ta ina da shekaru ashirin da É—aya a
duniya, wata rana ina driving na zo daidai wurin ba da hannu sai na hangi wani kyakyawan yaro
da ba zai wuci shekaru shida ba yana da irin kyaun da in ka kalleshi sai ka sake da sauri ya zo
ya shiga gaban motana ya fara wanke mini glass don kaman sana'ar da yake yi kenan a wurin
ake bashi goma biyar na cin abinci, Dukda fuskarshi a matuƙar haɗe ko alamun dariya babu
kayan jikinshi kuma basu ji jiki chan chan ba amma sun dan yi duhu kaman ana yawan tsoma
su ruwa, bayan ya gama ya dawo gefena ya tsaya tsantsar tausayinshi ne ya rufar mini,
wannan yaro ƙarami da ke bukatar ingantacciyar rayuwa yaron da bai wuce a ce yana gaban
mamanshi a kwance ba shine ke wannan walagigi yana neman abin da zai sanyawa cikinshi,
sauƙe glass din nayi muka haɗa ido na sakar mishi murmushi
"Yaya sunanka?"
Na jefa mishi tambayar ga mamaki na ko ci kanki bai ce ba banda idanu da ya tsura min yana
kallo, ganin an ba da hannu sai na zari dubu biyu na miƙa mishi kaman ba zai karɓa ba sai ya
karɓa ya juya ya bar wurin bai ce min komai ba.
Har na dawo gida tunanin wannan yaro ne a raina bayan kwana biyu na kasa mantawa da shi
haka na É—auki mota na koma inda na fara haÉ—uwa da shi na ajiye mota na shiga yawon neman
shi da ƙafa, na yi nema sossai kan na same shi zaune gefen wani juji ya haɗa kai da gwiwa
Dukda uban ranar da ke dukanshi ko motsi bai yi ba, daga farin Fatan shi da yanayin sumanshi
na gane shi don ya fi yanayi da Fulanin usuli, gangar shi na je na duƙa na taɓa shi ya ɗago ya
kalleni da idanunshi da suke a matuƙar rine fuskarshi yayi jazir, dabiun yaron sai bai min yanayi
da na sauran yara ba don idanunshi na nuna wasu al'amari da na kasa fahimta, maganan
duniya na mishi bai ba ni amsa ba sai ido na miƙe na je wurin wani mai wankin mota a kusa da
wurin na nuna mishi yaron
"Malam Don Allah wanchan yaron baya magana ne?"
"Hajiya yadda kika ganshin nan haka mu ma muka ganshi kuma in za ka mishi maganar duniya
ba zai amsa ba amma kin ganshin nan idan ya kwana da kayan jikinshin nan da safe zai zo ya
ba ni goma in bashi ruwa da bokiti ya kwaba omo ya wanke zai zauna daga shi sai karamin
wando idan ya bushe zai saka ya cire wandon ma ya wanke ya mayar da kayan, kin ga inda
yake zaunen nan idan ba zai fita neman kudin abinda zai ci bane bai taɓa barin wurin ba sai
wanka ko wanki da ya kan zo nan"
Wani iri na ji har cikin raina, na mishi godiya na bar wurin na koma wurin mota na tafi na je na
sayo duk wani abin makulashe da na san yaro zai buƙata na dawo na bashi ya ƙi karɓa a
ƙarshe ajiye mishi nayi na tafi, Washegari na sake komawa don tausayi da kaunar shi ya riga ya
samu gurbi a zuciyata, a ranar takalmina na cire na yi irin zaman da yayi nima Dukda ina jin
zafin ranar minti minti sai ya É—an waigo ya kalleni ban ce komai ba shima kuma bai ce komai ba,
har dare ina tare dashi sallah kawai nake zuwa wani masallaci a wurin dake da ɓangaren mata
abin da ya bani mamaki kuma shima haka zai je Sallar ya dawo ban tafi ba ranar ma sai da na
sake cika mishi gaba da abubuwan cima kala kala, a takaice na jera kwana uku ina zuwa
wurinshi a na huÉ—u ne ina zaune kawai sai na kama kuka, yayi shiru sai ya juyo ya kalleni
kaman zai share chan dai na tsinci muryarshi kaman daga sama yana cewa
"Me ya same ki?"
Numfashi mai nauyi na sauƙe ashe ba kurma bane
"Ba ni da lafiya ne kuma bana son zaman rana"
Ga mamakina sai ya miƙe ya kama hannuna muka koma inuwa duk muka zauna bayan nan duk
yadda zan yi yayi magana ya ƙi na sake yin kwana biyu muna zama a inuwa kan ranar kawai ya
kalleni ya ce
"Me kike so?"
Ina mamakin yadda yake magana wane babba
"Kai nake so in taimaka kai nake so in É—auke daga wannan jujin in kaika gidan mu kayi rayuwa
mai kyau, za ka bi ni?"
Kallona kawai yake, ni kuwa ina hakan ne da zuciya ɗaya ba zan so rayuwar shi ya ƙare a kan
titi ba ba zan so ya tashi a haka ba zai iya shiga ko wani hali.
Kai ya gyaÉ—a min na yi farin ciki kwarai na kira babana ina mishi albishir don ya san labarin
yaron har ya yarda duk ranar da yaron ya tanka ni kuma ya amince ya biyo ni ina da kyautar
kujerar umura na yi farin ciki sossai da amincewarshi Dukda ba don kujerar ba saboda ko a
lokacin na je Makka so ba adadi, na dauke shi daga nan muka dawo gidan mu.
Ban barshi cikin ma'aikata ba na kaishi É—aki na musamman na fita na yi mishi sayayya kan na
dawo yayi wanka ya ci abinci na bashi kayan a hankali ya ce min
"Na gode"
Murmushi nayi a raina ina raya wannan yaro idan ya girma ba karamin mutum za'a yi ba don
bashi da rawar kai irin na yara masu shekarun shi.
"Ya sunanka?"
"Ban sani ba"
Abin da yace kenan na yi mamaki ƙwarai kuma kaman akwai abinda ya ɓoye min amma ban
bincika ba nace
"Zan saka maka suna amma sai na yi tunani sunana Khadija, mahaifiyata ta rasu ni kaÉ—ai ce sai
babana a gidan nan ka É—aukeni tamkar mahaifiyar ka duk wani abin da kake so ni kuma zan
cika maka shi ka ji?"
Ya kalleni nayi murmushi
"ban kai in haifeka bane? Shekarunka nawa?"
Ya É—aga min yatsu shida nace
"To ka ga, da na yi aure ina 15 da na haifeka irin auren kauyen nan da ma ba'a kai hakan"
Ya É—an yi murmushi daga nan na fahimci shi mai É—abi'ar miskilanci ne tsantsa babana na samu
da shawara shi ya ba da sunan Rayyan in saka mishi ni kuma nake ce mai Saraki don ko sarki
bana tunanin ya kai shi sarauta..
A lokacin gab aurena da baban su Jannah ne ko da ya zo shima farar daya son yaron ya shiga
ranshi yayi alkawari zamu rike shi kaman mu muka haife shi ko da zan kaishi makaranta tare
muka tafi da Mahaifin su Jannah shi yayi mishi komai aka ba da sunanshi Rayyan Mohd
Khamis, bayan aurena da baban su Jannah bai fi da shekara ba Allah yayiwa mahaifina rasuwa
ta hanyar ciwon sugar da ya sha fama da shi, na shiga tashin hankalin da Saraki ne kawai ke
iya saka ni cin abinci kan daga baya na zo na watsakke don dama wannan dole ne, ranar da na
haifi Jannah a ranar Saraki ya fara kirana da Mammi don tunda muke bai taɓa kirana ba ko zai
yi magana sai dai kawai yayi na ce ko Aunty ya ce min ya ƙi, Rayyan bashi da lafiya don yadda
yake ganin rana haka yake ganin dare idan yayi bacci kuwa haka zai yi ta wani irin juye juye
yana haɗa gumi daga karshe cikin wani mummunan yanayi zai farka tun yana ƙarami muka fara
ganin likitocin psychiatric su ma da kyar da pills ake samu yake dawowa daidai idan abin ya zo
mishi especially lokacin zafi kasancewar a tsakankanin ne muka hadu.
Baya so a mishi magana akan abin da ya kawo shi wurin ko iyayenshi tunda na fahimta ban
sake yi mishi ba ko da wasa, irin kiyayewa da kular da muke bashi shine sanadin da ya sa ya
samu ingantacciyar rayuwa yayi karatu mai zurfi har ya zama soja, bayan nan ne aka gano ina
da Ciwon ƙoda Rayyan yayi fadi tashi kwarai har ƙodar shi yayi offering mini Mahaifinsu Jannah
ya hana aka biya makudan kudi aka yi min dashe amma ba'a dace ba, a lokacin da nake jinyar
Baban su Jannah ma ya rasu ga rashin lafiya ga rashin miji na yi ciwo sossai duk Rayyan ne
yake tsaye tsayin daka a kaina ga ƙannenshi Jannah da Abeeha bai bari na tagayyara ba, yana
mini son da iyakaci kenan ko da ni ce na haife shi.
Saraki ya taso mai tsananin jarumta gashi dama magana ma bata dame shi ba don ko abokai
bashi da su, sannan yaro ne da idan yana abu dole ka kalleshi yana da jin ƙai ko magana yake
dole ka kalleshi, dalili na ya tafi short service a harkar lafiya don dama science ya karanta a
secondary school, ba'a fi shekara biyu ba na matsa mishi da zancen aure ya nuna akwai wacce
yake gani zai iya aure, magana ta fara nisa ranar ya je wurinta babanta ya zo ya same shi ya ce
mishi
"Ina so in ka koma ka tambayi asalinka sai a fara batun neman aure amma ba zan ba da auren
É—iyata wa marar cikakken asali ba"
Wannan magana ya dake shi sossai, wanda ni na ɗan lallaɓa shi na tura uncle Musa sai ce
mishi suka yi ba za su bada auren ba basu sani ba ko ba É—an sunna bane ko an same shi ta
gurbattacciyar hanya, magana ce mai girma a gareshi wanda ya tado ciwon baya da kyar muka
samu ya dawo daidai bayan tsawon wata shidda baya bacci kuma ya ki faÉ—a mini wani irin
mafarki yake ko wa Dr ɗinshi, gashi Rayyan baya taɓa zubar da hawaye, tunda ya girma rabon
da in ga hawayenshi kila da wani abu zai ragu a zuciyarshi, daga nan yayi alkawarin ba zai
sake neman aure ba don duk wanda ya sake kallonshi ya mishi gorin asali sai ya kashe mutum
har lahira.
Afeefah kin ji waye Rayyan, kin ji cewa bashi da cikakkiyar asali sai dai yana da tarin nagarta,
ilimi, natsuwa da sanin ya kamata ga ibada tsantsa, yana da ni matsayin uwa da na bashi duk
tarbiyar da uwa za ta iya ba yaro daga yarantarshi har girmanshi, ya samu gatan iyaye both
uwa da uba don baban su Jannah har ya rasu bai taɓa nuna ko da da second daya cewa ba
shine Uban Rayyan ba, kin ji cewa bashi da cikakkiyar lafiyar kwakwalwa ba na hauka ba sai na
tsantsar damuwa akan abinda ya shafi rayuwarshi da ciwo a zuciyarshi wanda ya mayar dashi
mai irin zafi da faɗan nan, tun yana yaro ba za ki taɓa ganin dariyar shi ba sai murmushi shima
sai ya kama, shin za ki iya auren Rayyan a haka? Afeefah za ki iya yi min wannan alfarmar??
🖤Gureenjoh🖤
HAIHUWA DA HANJI
(A True life story)
Fatima Muhammad Gurin
(Gureenjoh)
Wattpad-Gureenjo6763
Arewabooks-Gureenjoh
ADABI WRITERS ASSOCIATION
*FREE BOOK*
*30*
**Tana tunanin da kashe kai shi ne hukunci mafi sauƙi ga bawa a duk sadda ƙaddara ta ruro
wutarta za ta samu miliyoyin mutane a raye ne?"**
Da wani irin amo sautin muryarshi ke dawo mata a sadda yake faÉ—a farkawarta daga shan piya-
piya, ashe da biyu yake yi mata irin wannan faÉ—an? Ashe shima duniyar ba daaÉ—i tayi mishi ba?
Wasu irin ruwan hawaye ne ke bin fuskarta babu kakkautawa, sai taji har gwara ita ma da shi
kaman ƙaddarar ta ya fi nashi sauƙi tunda tana kwanciya tayi bacci lafiya ƙalau, kuka kawai take
yi duk yadda mammi ta so tayi shiru ta ƙi, sai da tayi ma'ishi Mammi ta bata ruwa ta sha kan ta
É—ago ta kalli Mammi bata ce komai ba.
"Za ki iya cewa Meyasa ban bashi Abeeha ko Jannah ba ko? Har raina na É—auki Saraki É—an da
na tsuguna na haifa ne shiyasa har abada na haramta mishi auren 'ya'yana, uba yake a gare su
a yanzu da basu da wani uba shi ya raine su bayan yana jinya na, shi ya basu tarbiya cikakkiya
da har in sun fita ana sha'awar su. Wannan dalili ya sa ko da wasa wannan tunani bai taɓa
darsar min ba don har in mutu bana fata ko sau É—aya Saraki yayi tunanin don ba ni na haife shi
ba zan iya ɓata mishi..."
A hankali Afeefah da idanunta suka sauya ainun ta riƙe hannun Mammi
"Ke mutumiyar kirki ce Mammi, kina daga cikin sahun 'yan aljanna in shaa Allah... Hakika kina
da zuciya mai kyau wanda Allah ne yayi miki kyautar shi don samun irinki sai an tona"
Murmushi kaÉ—an kawai Mammi tayi zata yi magana Afeefah tayi saurin cewa
"Mammi ki bar roƙo na kin yarda da ni ni kuma in shaa Allahu ba zan ba ki kunya ba, wlh har
raina na amince kuma zan yi iya kokarina in ga na ba da abinda ake so"
Rungumeta kawai Mammi tayi cikin farin cikin da yake ratsa zuciyarta.
****
Shi kam Rayyan daga masallaci ya mayar da Saleem gida bayan yayi ta mishi tuni akan
mahaifiyarshi da 'yan uwanshi irin muhimmancin su a rayuwarshi duk yana ji amma amsawar
wani iri, bai damu sossai ba don shima zai taya abokin nashi da Adu'a yana kuma da yakinin
duk abinda yayi farko yana da ƙarshe musamman abinda ba don Allah aka yi shi ba.
Daga nan gidan Jannah ya wuce, tana zaune kawai ta ji ana knocking ta tashi taje ta buÉ—e sai
ta ganshi tsaye, murmushi ta saki tana mishi sannu da zuwa ya amsa yadda ya saba musu ya
shiga ya samu wuri ya zauna, cikin mintuna kaÉ—an ta cika gabanshi da kalolin abubuwa su
snacks da su abinci kan ta dawo ta zauna
"Barka da juma'a Yaya"
"Barka dai ya gidan?"
Ta amsa da farin ciki
"Lafiya ƙalau ya su Mammi?"
"Alhamdulillah"
Ya faɗa yana shan zobo don yana matuƙar kaunar zobo bayan ya sauƙe cup ɗin ya kalleta
"ba ki da wani damuwa ko?"
Kai ta gyaÉ—a
"Babu komai Yaya"
Ya ce
"Masha Allah"
Miƙewa yayi ya zare kudi ya ajiye mata dukda tana aiki godiya tayi ta mishi ta raka shi har mota
ya tafi ta dawo tana murmushi ya kan yi hakan tun bayan aurenta, haka kawai sai ta ganshi zai
zo ya duba ta ya tabbatar tana lafiya ya ajiye mata kudi ya tafi.
Gida ya nufa kai tsaye, bai je Sashenshi ba don la'asar ya kusa yana so ya duba Mammi kan ya
fita yayi sallah sai ya dawo ya huta gabaÉ—aya, ko da ya shiga yanayin wurin ya É—an zubawa ido
Dukda ya fahimci Mammi ta yi hawaye sai dai idanunshi da suka shiga cikin nata ya É—an ji wani
yanayi da har bai ɓuya ba, seconds ya kwashe yana kallonta kan ya ɗauke kai sai ta miƙe ta zo
zata fita muryarta na cracking tace
"Sannu da dawowa"
Bata jira amsarshi ba ta wuce don ganinshi kaÉ—ai tausayi yake bata.
Ɗan shiru yayi kan ya taɓe baki yana ɗaga Kafada ya isa wurin Mammi
"Mammi why did you cry? Yarinyar chan ne ko?"
"Ni ce dai na sakata kuka ba ita ta saka ni ba, ka dawo?"
Bai ja zaren zancen ba yace
"Eh, hope baki ji yunwa ba?"
"No ban ji ba, na san ma Abeeha ta kusa shigowa ko na ji ma zata zo ta sama min wani abin
you should rest"
Kai ya gyaÉ—a ya É—an jingina da kujera yana lumshe ido
"Ni ko ina son yin wata magana da kai"
BuÉ—e idanun yayi yana kallonta
"Saraki ka tuna kai ka ce in zaɓa maka mata ko ma wacece za ka aureta in dai ni ce na zaɓa?"
ÆŠan shiru yayi kan chan dai ya gyaÉ—a kai.
"Toh mun samu Mata Saraki"
Bai wani nuna ya ji daaÉ—i ko zumudi ba sai ma runtse idanu da yayi ya É—an buÉ—e.
"Baka tambayi wace ba kuma a ina?"
"Mammi ke fa kika shirya wannan aure duk abubuwan nan ba lallai sai na ji ba ayi duk abinda
ya dace kawai"
"haka za ka aureta baku fahimci juna ba? Ai ba'a haka dole za ka nuna mata itama macece
kaman sauran mata ka bata darajar ta na neman soyayya da ma kyautatawa da kan shiga
tsakanin saurayi da budurwa"
Idanunshi kawai ya zubawa Mammi don jinta kawai yake baya tunanin zai iya yin ko abu guda
cikin wanda ta lissafo.
"Mammi kin fa san duk ba zan iya wannan ba"
"Toh na ji amma ka san wacece yarinyar? Ka dai san ba zan zaɓa maka wacce na san bata
dace da kai ba ko? Kuma ka yi min alkawarin ƙarbar ta yadda take ko?"
Ya ɗan matsa kaɗan ya riƙe hannunta
"Mammi duk zagaye-zagayen nan na menene? Kin fa san yadda na É—auki girman alkawari
wallahi zan amince, wacece?"
Yadda take ta zagayen ne yasa ma yaji yana son sanin wacece haka.
"Afeefah ce!"
ÆŠan shiru yayi yana tunani don sai ya ji kaman ma bai san sunan ba, amma duk inda ya zagaya
a kwakwalwarshi mace É—aya tak ya sani da wannan suna, mace É—aya da ya sani kuma
buduruwar abokinshi ce salim.
Da sauri ya kalli Mammin yana girgiza kai
"A'a Mammi ki samo wata ba wannan ba"
Da zuciya É—aya yayi maganan kuma kai tsaye.
"Ban gane in samo wata ba, Meyasa?"
"Mammi ni wannan ta yi min yarinya wlh ba na son hauka da raini, sannan Mammi buduruwar
saleem ce fa! Ta ya zan fara zaman aure da ita?"
Murmushi Mammi tayi a maganan nashi na farko
"Ina saleem É—in? Ina yana chan yayi aure yana zaune da matar shi? Ko ma bai yi aure ba ba
zan amincewa Afeefah ta auri saleem ba ba kuma don shi a karan kanshi ba sai don
mahaifiyarshi ba zan so ta koma inda zata sha wahala ba shiyasa na zaɓa mata kai ina da
yakinin za ka kula da ita har karshen numfashi"
Tayi maganan cikin tabbatarwa, duk ya É—an ruÉ—e mata kaman zai yi kuka ya fara magiyar ta
chanza wata shi dai wannan yarinya bata mishi ba.
"Ba fa zan fasa ba Saraki sai ka bani kwakwarar hujjar da zan gamsu ban da buduruwar
saleem, ban da kuma baka sonta itama bata son ka dukkanku za ku koyi son juna idan zama ya
haÉ—a ku, banda kuma tayi yarinya don kaima ka san ba yarinyar bace"
Hangota kawai yake a idanunshi yana son tuna menene kuma aibunta wannan idanu farare
manya da take zarowa duk sadda yayi magana yake hangowa kawai, da É—an sauri yace
"Mammi baƙa ce!"
Dariya Mammi ta fara tana girgiza kai ya kwaɓe fuska shi da gaske yake
"Yaushe kuma ka fara zaɓar kala? Kenan ni da babanku bai aureni ba kenan ko kuma da Su
Jannah ba za su auru ba"
"To ai ku daban ne ita daban Mammi"
"Ka san Allah idan ba legit hujja zaka kawo ba, maganan nan babu fashi ka fara shiri... Saboda
yanayin jiki na ba za mu É—auko wani hidima ba É—aura aure kawai za'a yi ayi walima kowa ya
shaida ta tare"
Duk yadda ya so ya zamewa Mammi ya kasa, don komai ya ce tana da amsa har aka kira
la'asar ya tashi ya tafi, ta bishi da kallo tana murmushi idan ta ga yana hira da ita haka hakan
na yi mata matukar daaÉ—i a rai, ta kan rasa Meyasa baya son Magana alhali ya iya ba bai iya
ba, kawai dai ya zauna shiru ya fi mishi ko mahaifin su Jannah da yana raye sai dai ya ji dariyar
ta ba zai ji maganan Sarakin nata ba yayi ta tsokanarsu kenan tana shigarwa Sarakin don shi
bayan ita wasa da sakin fuskanshi babu mai gani gwara ma saleem da suka shaku sossai
shima don salim É—in ya karanci halayenshi ne tsaff kuma ya iya zama dashi.
Tana fata ko ba yanzu ba ya so Afeefah ya sake mata fiye da yadda ita take ganin wannan side
ɗin nashi, hannu ta ɗaga tana roƙon Allah ya nuna mata wannan rana da zata miƙa shi ɗakin
matarshi.
Daga nan ta miƙe ta shige don alwalar la'asar, bata yi ƙasa a gwiwa ba da daren ta sa driver ya
kaita gidan ƙanin mahaifinta Uncle Musa dattijo ne sossai shima kuma natsatse mai tarin ilimin
boko da arabi yana da zuri'a kuma duk zaman lafiya suke da su Mammi, sossai ta mishi
bayanin Afeefah ta kuma roƙi da su je su nema mata aure a wurin dangin mahaifinta don a fita
hakkin su, bata so su bada komai amma tana son A karɓi auren Afeefah daga shakikanta. Ya
gamsu shima kuma yayi na'am da hakan sun yi hira sossai don tana kwana biyu bata je ba sbd
jikinta shi ne ma ya kan zo har gida ya duba ta haka yaranshi da wasu jikokinshi, bata bar gidan
ba sai da suka tsayar zai yi tattaki da kanshi da babban danshi su tafi Dutsen-wai su nemi a
basu ranar auren daga nan sai a fara shiri.
****
Mommy ce kwance a kan gado tsabar damuwa da tunani da ta sakawa kanta ne ya sa jininta
hawa sossai, su Samha ke zagaye da ita a yanzu É—in ma hawaye take zubarwa na tausayin
Saleem da damuwar halin da yake ciki wanda ta yarda laifin ta ne amma me yasa su Yaya za
su rama alkhairinta da mugunta? Me ta musu da zafi haka?
Bata gama tunanin ba Sabrina ta shigo É—akin ta samu wuri ta zauna
"Sannu Hajiya mommy ashe kuma jiki ya ƙi?"
Mommy ta danne tace
"Eh amma Alhamdulillah"
"Toh Allah ya kara sauƙi dama Saleem ne ya aiko ni"
Yadda ta kira sunan sai da suka daga kai duk suka kalleta.
"Wai cewa yayi ku koma wanchan tsohon gidan na gado ya riga ya tashi 'yan hayan yana son
yayi renovating nan, kin ga yanzu mun yi yawa ga iyali zai fara tarawa ga su Gaje gininsun ya
tsofe cikin ko wani minti zai iya rufta musu suma dai duk nan za su dawo"
Galala suke kallonta da kyar mommy ta iya cewa
"Saleem É—in ne yace haka?"
"Ai kin san ban san yan hayan ba bare in tashe su, shine yayi komai kuma ya tabbatar min kar
ku wuce yau don gobe masu aikin za su fara zuwa"
Wasu irin zafafan hawaye ne suka shiga sulmiyo wa mommy da su Samha, Sameera ce ta iya
daurewa ta miƙe tsaye ta fara hada kayan mommyn don ba zasu zauna ba, gwara su tafi ɗin
babban matsalar dukkansu babu mai aiki cikinsu karatu suke yi, mommyn sai kallonta take tana
jin tururin zafi a zuciyarta tuni Sabrina ta fice, mommy tashi tayi ta fito kai tsaye ta haura saman
su ta buga, su Samha duk suka bi bayanta jikinsu a matuƙar sanyaye sai da tayi mintuna biyu
kan aka bude saleem ta ƙura wa ido sama da seconds goma kan tace
"kai ka ba matarka saƙo ta ba mu?"
Kai ya gyaÉ—a
"Duk abinda tace haka ne!"
Jiri ne ya kwashe ta ya yunkura zai tare ta ta ture hannunshi ta juya da sauri ta sauƙa su Samha
ta cewa su hada kayansu duk suka hada suka fito a motar sadiqa suka zuba duk abubuwan
buƙatar su ta ja suka fice daga gidan dukkansu suna kuka, basu sake jin tashin hankali ba sai
da suka iso gidan duk 'yan haya sun lalata shi komai dai sai a hankali kuma dakuna biyu ne da
parlor sai kitchen duk jiki a sanyaye suka zauna a parlorn mommy na dafe da kanta har lokacin
kuka take yi.
"Mommy..!"
Sameera ta kira sunanta.
Sai ta É—ago ta kalleta
"Kina jin zafi a ranki ko? Kina jin ciwo da raɗaɗi ko? Kina jin baƙin ciki da tsantsar damuwa da
tashin hankali ko?"
Mommy tace
"Ba sai na faÉ—a ba Sameera abin da nake ji ba zai misaltu ba ni saleem ya É—aga daga gidan shi
zai dawo da surukanshi? Ni fah? Ko a mafarki ban taɓa zato ko tsammanin saleem zai iya juya
min baya a kan mace ba"
"Mommy in faÉ—a miki gaskiya? Laifin ki ne, dukkanmu muna da laifi a abin da ya faru... Mommy
kin yi tunanin inda Afeefah ta nufa da muka kore ta? Gwara mu muna da nan kuma ko ba komai
muna da junanmu amma ita kaÉ—ai ta fita bata da kowa bata da inda zata je, kin tuna irin
wulakancin da muka mata? Ashe alhakin da muka raina zai iya bibiyarmu, kin tsane ta ne
saboda saleem yana son ta kina ganin son nan da yake mata zai sa ya bijire miki kika zaɓa
mishi wacce kike ganin ke ce da riba sai kuma akasin hakan ya faru. har yanzu kina ganin laifin
Yaya da kika mishi dolen karbar wacce bai taba so ba? Kina ganin laifin Yaya da ƙarfi da yaji
yana kuka yana komai kika raba shi da Masoyiyar shi? Mommy ina jin zafi ina jin ciwo ina ji a
zuciyata cewa duk wannan abinda ya farun alhakin yarinyar nan ne, Allah ya jarabceni da
azabar so na ji yadda itama ta ji a sadda muka raba ta da nata savior É—in, na ji kwatar abinda
yaya ya ji a kanta amma muka hadu muka nufeta da sharri har da ƙagen lalata da samari wlh
idan ba mu neme ta mun nemi yafiyarta ba to kadan kenan muka fara gani"
Dukkansu maganganun sameeran sun shige su barin ma mommy da Samha dake ta kuka,
gaskiya Sameera ta faɗa bata kyauta ba kuma duk laifin ta ne da tun farko ta kwaɓe su ba zasu
yi ba amma bakin alƙalami ya riga ya bushe sai dai su tari gaba, tana tuna irin abubuwan da
suka mata tana tuna irin yadda taje ta haÉ—a ta da maza don tayi rayuwa saboda kawai an ce ne
ita Mayya ce sai ka ce jahilai waenda basu yi karatun islama ba sun ci zarafinta baiwar Allah,
sai gashi Allah ya nuna musu É—an Adam ko ya yake mai daraja ne a gareshi, ya nuna musu
ikon shi a kan bayinsa.
"A ina za mu sameta mu nemi yafiyarta a ina zan ganta Sameera?"
"Wannan sai Allah mommy, yanzu ina so ki daina yiwa yaya kuka mu dukufa Adu'a da sadaka
Allah ya karkato da hankalinshi mommy adu'ar ki karɓaɓɓiya ce a gareshi ke kika ɓata ke ya
kamata ki dukufa ki gyara"
Ta gamsu sossai kuma ta fahimci karatun duniyar, ta fahimci ayar da Allah ya nuna a kanta don
haka gwagwalanta ta cire ta ba sadiqa akan su je su sayar su musu sayayyan duk abinda za su
buƙata haka suka fice kasuwa suka bar su su biyu da Samha da har lokacin jikinta kaman an
zuba mata ƙanƙara.
🖤Gureenjoh🖤
HAIHUWA DA HANJI
(A True life story)
Fatima Muhammad Gurin
(Gureenjoh)
Wattpad-Gureenjo6763
Arewabooks-Gureenjoh
ADABI WRITERS ASSOCIATION
*FREE BOOK*
*31*
A hankali kwanaki ke ja har ranar da Uncle Musa ya yanke da za su tafi Dutsen-wai su samu
kawu, shi da yaranshi manya biyu sai Driver suka É—auki hanyar, tafiyan awanni kaÉ—an ya sada
su da kauyen, kusan abin da ya faru da 'yan uwan Sulaiman hakan ce ta faru amma dayake ya
riga ya sani suma kuma sun sani so basu wani damu ba.
A kofar gidan Labaran suka yi parking motar su biyu suka fito suka bar uncle É—in cikin mota,
gidan da rabin shi a zube a ƙasa suka ɗan zubawa idanu suna mamakin me ya kawo Rayyan
har nan neman aure? Daga ka ga gidan zaka san suna fama da masifar talauci, buhuhuna ne
da suka zama jajazir aka kare ɓangare guda na gidan dashi, ga yara nan dukunkun rabin su
tsirara suna ta wasa a kofar gidan, daga gefe wasu matasa ne suna shaye-shayensu ko a
jikinsu, É—ayan na shirin turawa a kira musu mai gidan sai ga kawu Labaran ya fito a zuburen shi
ganin mota ya sa ya taka birki
"Lafiya?"
"Ƙalau sai Alheri, Malam Labaran muke nema"
Kanshi ya nuna
"Ga ni"
Girgiza kai babban da sunanshi Mansur yayi wani abu sai bakauye Dukda wasu kauyukan
mutanen cikinshi akwai kara da girmama baƙo haka kuma mutane suna suka tara, amma babu
gaisuwa babu komai bare iso ko ruwa kawai a yi abinda ake so.
"Mun zo ne akan maganar 'yar wajenka Afeefah"
Uncle Sanusi ya faÉ—a, tun ma kafin ya gama kaiwa aya Kawu ya katse shi
"Wace Afeefah? Ai mu bamu da Afeefah a zuri'ar mu kap"
Uncle Mansur yace
"Afeefah 'yar wajen ƙaninka?"
"Ah Annoba zaka ce sai na fi ganewa, ai na jima da sallamar wa duniya ita ko a chan ne tayi
muku wani abin ba wurina za ku zo ba ita za ku kama babu ruwan Labaran Ah to"
"Malam ka natsu mana ka ji bayanin da muke tafe dashi"
Uncle Mansur ya faÉ—a da É—an zafi don yana da faÉ—a shi, BuÉ—e kofan da Mahaifinsu yayi ya fito
ne ya sa suka yi shiru, uncle Musa ya miƙa mishi hannu suka gaisa ya ce
"Ba wani abu bane ya kawo mu illa nemawa jikana, É—an wajen su auren 'yarka Afeefah, mun zo
ne da batun na gani ina so idan babu damuwa zaka iya ba mu rana sai mu zo a É—aura aure"
"aure??"
Ya faÉ—a yana sake kallonsu Dukda sun yi zubin masu hankali kuma kaman suna da kuÉ—i amma
wani gida ne zasu yadda dansu ya auri Afeefah? Kila dai basu san wace ita ba, zayyano musu
wace ita da mutanen da ta kashe ya shiga yi har abinda ya sa ta bar garin
"Duk mun san da hakan"
Uncle Sanusi ya faÉ—a.
"Kuma kuka yarda É—an ku ya aureta?"
"Eh a haka yake sonta, bama buƙatar komai daga gareka ita ɗin ma ba sai ta dawo nan ba
auren kawai muke so ka bamu da kanka kuma mutanen garin nan su shida zaman aure zata
cigaba da yi ba dadiro ba kaman yadda kuke ta faÉ—a"
Numfashi ya sauƙe ai tunda babu abinda suke so shikenan kila ma suma manyan mayun ne
don waenda basu ji tsoro ba bayan jin labarinta ai basu da maraba da mayun, kuÉ—i har dubu
hamsin suka bashi a cewar na gani ina so ne. Ya hangame baki yana kallon uban kuÉ—in kaman
faɗa ya karɓa yace tunda sune zasu zo su gaya mishi kawai randa suke so a daura, suna ta
mamaki shi ba ruwanshi da bincike ko wani abu tunda ya ga kudi kawai ya ruÉ—e, suka tsayar da
nan da wata guda a haka suka yi komai daga tsaye suka shiga mota suka juya suna mamakin
ƙarantar mutumin.
A chan wurin kawu kuwa kaman zai kifa ya shiga gidan
"Asabe, larai ku fito ku ji abin mamaki wai na kwance ya faÉ—i"
Duk waje suka yo larai ta kasa shiru
"Wannan uban kudin fa malam daga ina haka?"
"Nima duk kaina ya kulle, wasu ne suka zo yanzu a mota wai sun zo neman auren Afeefah
wannan kudin na gani ina so ne suka bayar"
"Afeefah dai???? A mota?? Wannan uban kudin kawai na na gani ina so ne? Kuma ka amince
musu??"
Duk a jere suka jero tambayoyin cike da tashin hankalin hassada.
"Toh ko ban basu ba ai zasu iya auren tunda ba gabanmu take ba tunda suka ba da wannan a
na gani ina so ki yi lissafin nawa zasu bayar sadaki?"
"Amma malam Afeefah annoba Mayyar taya zata yi aure ta bar yaranmu zaune? A dandi fa
take basu sani bane?"
"Sai da na basu labarinta tsaff kuma sun ce sun ji sun gani"
Wani irin abu ne ya taso ya tsayawa inna larai a makogoro Ah ba zai yiwu ba, sam Afeefah bata
chanchanci auren mai kuÉ—i ba dole ta san yadda zata yi zama bai ganta ba.
Ko ta kan bayanin da kawun ke tayi bata bi ba shi lissafin zuwan kuÉ—in shi yake don ya ce sai
ya bi Afeefar ya ga inda zata zauna in gidan kudi ne yayi ta zuwa ana bashi kasonshi ai ta
zauna gidanshi sama da shekaru goma yana ciyar da ita a banza.
Inna larai gyale ta saɓa ta fita afujajan ko auren ya lalace ko kuma ya dawo kan daya daga cikin
'ya'yanta ba zai yiwu tana ji tana gani Afeefah ta yi aure inda zata je ta huta ba su suna nan
suna cin wuya, har ita a wa? Daji sossai ta shiga sau ɗaya ta taɓa rako wata kawarta wurin
bokan don bata taɓa zuwa ba amma ganin aikinshi yayi a kan kawarta ya sa ta gamsu zai iya
wargaza auren Afeefah ya dawo dashi kan 'yarta, ɓacewa tayi tayi ta zagaye a garin neman
inda zata kulla sharrin ta maciji ya sare ta, wani irin ihu take da kururuwa tana neman taimako
Allah ya taimaketa akwai wasu mutane a gona suka zo suka fara taimakonta kan aka É—auko ta
mutu kwaikwai rai kwaikwai aka dawo da ita cikin dutsen wai, abu kaman wasa kafa ya fara
zama wani abu daban kaman ba macijin gaske ba don duk maganin da ake yi na macizai an yi
mata sai zabura take ga zazzabi tayi sharkar da gumi tana surutai...
****
Afeefah na zaune tana azkar na bayan Magrib Abeeha ta shigo tana shigowa ta rangada guda
"Ahayye matar babban yaya bi'izinillahi nan da wata guda za mu sha shagali"
Gaban Afeefah ne yayi wani irin faÉ—uwa, kenan wata daya suka saka auren? Jikinta yayi wani
irin sanyi ta fara jin hawaye na zuba mata dukda ta amince har ranta da auren sai dai tana jin
wani irin ciwo a ƙasan ranta na auren wanda baya sonta bai ma dauketa mace ba, kila ma ko
sunanta bai sani ba don bata taɓa ji ya ambata ba, Abeeha ce ta tsuguna tana tsokanarta har ta
fara kukan auren kenan? Da kyar tayi shiru.
Bayan isha Mammi ta aiko aka ƙirata bayani ta mata akan kwanakin da aka sa auren, bata ce
komai ba Mammi ta ce zata iya tafiya a Washegarin aka fara zuwa yi mata gyaran jiki don
mammi sossai ta tashi tsaye Dukda ciwo dake nukurkusarta amma auren É—an farinta babu
batun zama, shi dai kam ma a satin aka tura shi wani assignment Zamfara ya wuce kuma zai yi
akallah sati uku.
****
Ta ɓangaren su mommy fa rayuwar ya juye musu, a hankali suka fara fahimtar abin da rayuwa
ya kunsa barin ma da ta mayar da sunna Tv da kuma Africa tv3 abin sauraro, suna takure sai
dai basu rasa ci da sha ba kuma duka yaran suna zuwa makarantar su sai dai hankalinsu ba'a
kwance yake ba, ga ayyukan su da suka manta yadda ake su wanki, guga, shara wanke wanke
da girki duk su suke yi idan basa nan suna school haka mommyn ce ke yi dole, ko wani dare
karfe uku baccinta ya ƙare don ciwo ne sossai a ranta na abin da aka yi wa saleem, tana roƙon
mishi waraka kuma tana roƙon Allah kar ya kama shi da laifi don ba laifinshi bane nata ne.
Yau da ta ji tana matuƙar kewanshi ta tura Sameera da Samha gidan akan su duba shi, ko da
suka je kaman baƙi haka suka tsaya jikin kofan suna knocking kusan mintuna biyar tukuna Gaje
ta zo ta buÉ—e ganinsu ya sa tayi murmushi
"Ah ashe su Sameera ne sannunku da zuwa bismillah"
Sai suka ji wani iri a gidansu ne ake musu iso?
Shiga suka yi suka samu Yaya zaune cikin kujera relaxed irin gidan shin nan, zama suka yi
suka gaishe shi ya amsa kan Samha tace
"Wurin Yaya ne muka zo yana nan?"
"Eh yana nan bari na dubo Sabrina ta turo muku shi. Talatuwa..! Talatuwa...!! Kawo musu ruwa"
Su dai banda ikon Allah babu abinda suke gani wai in faÉ—a ya fi karfinka sai ka mayar da shi
wasa ba kuma baki sai kunne murmushin dole kawai suke yi har Talatuwa ta fito, da tausayi
take kallon su amma ya zata yi dole ta cigaba da aiki da mutanen da suke gidan in tana bukatar
abin rufa wa kai asiri, ruwan ta kawo musu ta gaishe su suka amsa a sanyaye.
Sun fi mintuna talatin kan ya fito ya zauna yana kallon su itama Sabrina ta zauna gefenshi don
su Gajen duk sun tashi sun yi wuraren da nan ne É—akunan Mommy da nasu suke a baya,
gaisheshi suka yi ya amsa
"Lafiya?"
Ya tambaya sai Samha ta fara zubar da hawaye, wai yaya saleem ne ya zama musu baƙo?
Yaya saleem dai da yake matuƙar kaunarsu ne wannan zaune?
"Rashin kunyar taku ne kuka zo har nan ku cigaba ko? Duk wanda kuka dinga yi mata a baya
bai ishe ku ba?"
Shiru suka yi don basu san me suka yi ba wani irin tsawa ya daka musu
"Ba Za ku gaishe ta ba??"
A É—an razane suka shiga gaisheta tayi murmushi tana amsawa har da tambayar su mommy na
lafiya? Suka amsa da lafiya lau.
"Me kuke so? Ba na ce zan neme ku ba?"
Ya faÉ—a har yanzu babu walwala a fuskarshi
"Dama mommy ce tace mu zo mu duba kana lafiya?"
"Jinjiri ne ni? Ko idan banda lafiya ku nake jira ku kaini asibiti?"
Shiru suka yi sai Sabrina ce tace
"My S ka daina fushi ai ba laifi bane don sun ji lafiyarka, ku je ku ce mata yana lafiya yana miƙa
saƙon gaisuwa kuma bai manta da ita ba zai zo idan ya shirya shikenan?"
Sameera ta miƙe ta kama hannun Samha
"Za ta ji, sai anjima"
Ta jata suka fice sai kuka samhar ke yi har suka shiga napep hannun Sameera ta rike
"Sameera har da laifina a mayar da yaya saleem haka, duk ni ce da ban kiraku É—akin Afeefah
ba da bamu san suna soyayya har mu raba su mommy ta aura mishi wannan fitsararriyar mai
ido a tsakar ka ba"
"Samha ki daina wannan kukan, komai ya wuce dukkanmu muna da laifi... Ki yi shiru bana so
mu je wurin Mommy kina cigaba da wannan kukan kar hankalinta ya sake tashi, Yaya Adu'a
yake bukata ba kuka ba"
Dukda itama hawaye take sharewa lallai ta yarda duk soyayyar Uwa ga É—a tana iya zama
mummunar kaddararshi ko da sanin ta ko akasin hakan, mommy ta zamewa salim mummunar
kaddara sai dai Allah ya bashi ikon hayewa ya bashi ƙwarin zuciyar ɗauka kar ya halaka a haka.
****
A sati uku da suka biyo baya idan ka ga Afeefah za ka rantse da Allah ba itan ba ce, Caramel
skin É—inta wani irin daukar ido da sheki yake, tayi wani irin kyau har ta gaji, ba gyaran jiki kaÉ—ai
ake yi mata ba sessions ne daban daban a satukan ga karatu, ana koya mata dressing irin na
wayyayyun matan aure, ana koya mata girke girke na zamani da bata kware ba ana kuma koyar
da ita rayuwar auren da ma auren karan kanshi haÉ—e da dabarun zama da miji, ta É—an rame
saboda stress amma ta wani irin cikowa tayi kyau masha Allah, ba kananun kudi Mammi ke
bararwa ba Dukda ba buki za su yi ba sam.
Ko da su Umman Sulaiman suka ji labari su ma ba'a bar su a baya ba, Baaba jummai ta kan zo
ta yini bata shawarari kuma tsaff take É—auka wasu dai sai dai tayi murmushi don ta san ba dai
Rayyan za ta yiwa ba don wani abin bata tunanin har abada ma zata yi amfani da shawarar,
mixed emotions take ji akan auren.
Wai ita ce Afeefah za ta yi aure? Ita da ta fara sallamar da zancen aure a rayuwarta saboda
mummunar Taɓonta, ko da a da ta yi tunanin auren tayi tunanin aure zai zo mata a kaskance
cikin rashin galihu da gata, auren da zata iya zuwa ta cigaba da shan wahala kaman yadda ta
faro a rayuwarta sai gashi ta samu gatan da bata taɓa tunani ba, gatan da ko iyayenta suna
raye karshen abin da za su yi mata kenan, ta kan raba dare tana kuka tana miƙa godiyar ta ga
Allah tana kuma roƙon shi da kar ya nuna mata ranar da za tayiwa waennan bayin Allahn
butulci.
Yau Asabar da wuri ta tashi don sun yi class da mai koya mata girki, gasashen kifi suka yi
talapia ya ji onion sauce sai irish da aka gasa aka yi ganishing a gefen kifin, a gefe wani hot
beef stir fry jollof Rice ne, a dining suka shirya don ita da Abeeha suna ci Mammi ce dai ba zata
ci ba, bayan sun gama taje tayi wanka yadda aka nuna mata sabon method na yi har da
dauraye jiki da ruwan turare ta fito tana zuba uban kamshi, gaban wardrobe ta tsaya tana
tunanin kayan da zata saka, a hankali ta zaro wani dogon riga mai yanayi da silk material ta
zura yayi mata kyau sossai don A line ne rigar bai kai ƙasa sosai ba kuma ƙasan ba a zagaye
ba ana iya ganin idanun sawunta, hula mai butterfly a gaban Goshi ta saka ta É—an tsaya gaban
madubi sai taga kaman kayan ya mata yawa bata fita classy ba, komawa tayi ta nemi belt ta
É—aura a daidai cikinta sai ya bata wani kyaun na musamman murmushi ta saki ta É—auki wayanta
ta fito, daidai Abeeha ma ta fito daga nata É—akin.
"Ku ne kyau amare"
Ta tsokani Afeefar da kullum aikinta kenan, murmushi Afeefah tayi don tun tana rigima har ta
gaji ta shiga kyale Abeehar.
"Wlh Afeefah kina da kyau, kaman fa wata model haka kika fita, duk kayan da zaki sa yanzu kin
san irin adon da zaki musu su fita daban"
Suna shiga cikin parlorn suke zancen, Afeefah na cewa
"Addah Abee ai ina ga zan saka fashion design cikin mafarkaina don gaskiya abin na burgeni
bana rabo da kallon fashion show"
"Toh ke madam komai ma kina so? Ke fa kika ce business woman kike son zama na inna naha
don kina son yin kuÉ—i"
Ta faÉ—a da dariya.
"Ai duk mace tana bukatar waennan a gani na fa, kin ga girki ya zama favorite thing É—ina
saboda wajibi ne a gidan aure, dressing ma wajibi ne in kana so ka burge masoyinka duk ba
laifi bane business kuma shine asalin abin da nake so, ina so nayi kuÉ—i na samu na kashewa
marayu da bayin Allah, ina so nayi kudi na tallafi rayuwar yaran da suke wahala a duk sadda
suka rasa iyaye, gidauniyoyi nake mafarkin buÉ—ewa na wayar da kan mata akan mecece
rayuwa da kuma yakar jahilci a yankunanmu"
Abeeha na dariya take cewa
"Su burge masoyi, a'a ka ga Masoyiyar Ya Ra..."
Katse wa maganar yayi suka tsaya chak idanunsu a kan Rayyan dake zaune dining yana
karyawa hankali kwance, kuma tsaf ya ji su don daskare wa da suka yi ya sa ya É—ago firgitattun
idanunshi ya zuba musu yana aika musu da kallo mai kama da gargaÉ—i....
🖤Gureenjoh🖤
HAIHUWA DA HANJI
(A True life story)
Fatima Muhammad Gurin
(Gureenjoh)
Wattpad-Gureenjo6763
Arewabooks-Gureenjoh
ADABI WRITERS ASSOCIATION
*FREE BOOK*
*32*
Idanun ya ɗan tsayar a kan Abeeha kan yayi baya da su kaman zai ɗauke sai ya sauƙe a kanta
ya É—an tsayar kan ya janye ya mayar kan abincin shi ya cigaba da ci in his majestic way.
Wani irin bugawa zuciyarta ke yi fiye da misali, ko da wasa bata ji Mammi na maganar zuwanshi
ba daga ita har Abeeha kasa gaba suka yi kuma sun kasa baya, ita dai Afeefah tsabar bugun
zuciya har idanunta sun tara kwallah kiris take jira ta sako su, a tare suka juya za su bar wurin
suka ji muryarshi ya ce
"Ku zo nan!"
Wani irin tsalle zuciyar dake bugawa yayi, ita dai bata san Meyasa bata iya controlling
heartbreat É—inta ba in dai akan magananshi ko kallonshi ne ta ajiye akan tsananin tsoron shi da
take ji ne ya janyo hakan, Dukda bai taɓa dukan ta ba amma ya sha yi mata faɗa, faɗan ma
babu kaman na ranar da ta fara É—ora idanunta a kanshi a rayuwarta.
Kaman waenda kwai ya fashe musu suka dawo, Abeeha da ta san halinshi ba lallai ma ya kara
magana ba ta ja kujera ta nunawa Afeefah kujeran da idanu, kaman ba zata zauna ba sai kuma
ta zauna Abeehar ma ta ja wani ta zauna ta É—auki plate a hankali ta yi serving É—insu Rice É—in
daban daban Allah ma ya sa shinkafar da tsokar nama suka yi da babu protein za su ci don shi
zallar kifi da irish É—in yake ci.
Abeeha ta fara ci a hankali kan ta buÉ—e baki tace
"Sannu da dawowa Yaya"
Kai ya É—an gyaÉ—a har lokacin bai É—ago ba, ita dai Afeefah ko spoon É—in bata É—auka ba gashi
tana tsoron magana, kuma kar bata yi ba ya zama laifi da kyar ta ce a rarrabe
"S..sannu da d..dawowa"
Yadda tayi maganan ya sa ya É—ago slowly ya kalleta kan ya mayar da kanshi yana kai fork na
karshe baki bayan ya haÉ—iye ya É—auki ruwa daga fari kal É—in glass cup dake gefenshi ya sha
kan ya miƙe ya bar wurin, a tare suka sauke ajiyar zuciya Afeefah tace
"Adda Abee Meyasa da ya dawo da mu kika sa muka zauna?"
Tayi murmushi tana cin shinkafar tace
"Har yanzu baki san Yaya Rayyan ba, ai ya tsani saboda shi ka ƙi yin abinda ke gaban ka
yanzu da za mu tafi bayan ya kiramu ya kuma san me za mu yi anan muddin muka tafi haka zai
titseyemu ya tsare gida ya ce sai mun faÉ—a mishi dodo ne shi da muke avoiding É—inshi..."
"Shi dai komai kayi baka burgeshi?"
"Aikam bana tunanin akwai abinda yake burgeshi muddin ba abinda ya shafi Mammi bane"
Ajiye hirar shi suka fi suka cigaba da cin abinci don hanyar lafiya a bita da shekara dazu sun
tsira gaba basu san me zai faru ba.
Bayan sun gama wurin Mammi suka yi suka samu ma tana waya ne da wata cousin É—inta akan
boxes da ake haÉ—a mata na auren, ita dai Afeefah a kunyace ta zauna don yanzu sai take jin
kunyar Mammin na rufeta, bayan Mammin ta gama waya ta dube ta
"Afeefah yaushe ne kuke gama exams ne? Bana so kina yawo cikin rana ana wannan gyaran
jikin"
"Mammi wednesday za mu ƙare"
Ta mayar mata da amsa.
"Da sauƙi, saturday ne ɗaurin auren Abeeha ya zancen telan?"
Sai da gaban Afeefah ya faÉ—i ita ta kasa sabo da zancen auren sam, ji take kaman ana
daddaureta ne in aka yi maganar sai ta ga kaman ba gaske ba ita ce zata yi aure, auren ma
Rayyan za ta aura? Ya subhallah wani chill take ji yana running over her spine.
"Mammi kin san telan Jannah ne zan ƙirata na ji ko ya gama haɗawa ko ni sai in je in karɓo"
Hira suka cigaba da yi akan bikin da za'a yi shi ne a yini guda, ɗaurin aure, yini, walima da miƙa
amarya É—aki in ji mutanen garinmu suka ce Jollof, ba ana yinshi bane saboda talauci ko wani
abin, ana yin hakan ne saboda sauƙaka zirga-zirga expecially a irin situation na Mammi da bata
bukatar stress ko kadan.
Ranar Juma'a ana yi mata lalle sai ga su Fa'iza da fauziyya har da Ummusalma matar Sulaiman
da ta sake da ita sossai a yanzu, ga Abeeha da Jannah sai suka zama kaman bridemaids suka
cike É—akin da hirarraki ana yi ana dariya, Mammi kuwa sai sawa take ana turo musu abubuwan
taɓawa sossai hakan yayiwa Afeefah daaɗi sai take jin nishadi a ranta na taruwansu ko ba
komai Allah ya haɗa ta da tarin mutanen kirki, wani irin kyau lallen nata yayi baƙi da ja ya karɓi
hannu da kafafunta duk suma 'yan matan sun yi. Mammi ma tayi ja a yatsun hannu.
Sai dare suka tafi har Jannah akan sai gobe da sassafe za su dawo.
Rana bata ƙarya sai dai uwar ɗiya ta ji kunya, yau aka wayi garin Asabar kuma a yau ne ake
shirin ƙulla wani babban al'amari mai tarin nauyi tsakanin Afeefah da Rayyan, da misalin karfe
takwas ya shigo É—akin Mammin don ta kalli kayan da ita ta bashi ya saka a ranar don rana ce ta
musamman a gareta da ma shi baki É—aya.
ÆŠan uban sun Men lace ne fari kal mai shegen tsada Æ´ar ciki da babban riga ya wani zauna
mishi sak kaman don shi aka halicci yadin, hula da takalminshi bakake ne haka agogo tsadadde
dake ɗaure tsintsiyar hannunshi zuwa azurfa mai baƙin dutse da ke ƴar yatsar shi, fasalta irin
fita a angon da yayi ma ɓata lokaci ne sai kamshi kam kaman an yi barin turare, fuskar Mammi
ya zubawa ido kawai don bai taɓa ganinta cikin nishadin da ya ganta a ranar ba sai ya ji wani
abu mai sanyi na sauƙa cikin zuciyarshi, matsowa tayi ta kama hannunshi tana murmushi tace
"Za ka tafi a saurayi ka dawo matsayin magidanci Saraki, ba zan ce komai ba illah Allah ubangiji
ya tsare muku hanya daga zuwanku har dawowanku"
Yayi murmushi ya juya zai fita tace
"Saraki...!"
Ya waigo ta É—auko turarenta ta sake fesa mishi ya fita ranshi fess Dukda wani abu da yake ta ji
na tsungulinshi akan auren.
Ga dumbin mamakin shi yana fita ya tarar da motoci sun fi sha biyar dauke da tarin ma'aikatan
asibiti da ma 'yan uwanshi sojoji, a hankali ya juya ya kalli Sulaiman da ke mishi murmushi sai
yaji wani abu na mishi yawo a jiki, bai taba zaton za'a mishi irin wannan karan ba duba da
gaisuwa ce kawai ke hada shi da kowa, wani iri yake ji a sadda ya shiga gaban motan Sulaiman
suka fara barin unguwar babu saleem, ya nemi saleem a waya har ya gaji baya samunshi ko da
ya dawo gidan ya je mai gadi ya tambaya ya tabbatar mishi sun yi tafiya da madam, ya tambayi
su mommy yace basa nan suma. Ko jiya sai da ya koma amma bai same shi ba akan basu
dawo ba bai ji daaÉ—i ba sam da hakan ta kasance.
Bai gama shan mamaki ba sai da ya kalli tarin dangin Mammi, iyalai da jikokin uncle É—inta
motoci kusan nawa har da abokanan arziki don a matsayin auren jikan Uncle É—in za'a yi, kan su
tafi Mammi ta roƙi uncle Musa akan duk runtsi a dawo da sadakin Afeefah wanda Saraki zai
bayar in ya so ko wani abu ne a bashi daban amma sadaki na Afeefah ne.
Mutanen Dutsen-wai suna zaune kawai suka fara ganin lafiyayyu kuma tsararrun motoci suna
shigowa one after the other, babban masallacin garin da bashi da wani girma sai haraba suka yi
wa tsinke tuni dama Uncle Mansur ya aiko da masu canopies an kafa dayawa a harabar don
masallacin ba zai É—auki mutanen ba, an shimfida carpets-carpets anan suka yi masauki, Kawu
an nemo na ƙasan akwati don maƙon shi ma bai barshi yayi sabon ɗinki cikin dubu hamsin din
chan ba bai tashi jin kunya ba sai da ya ga mutanen alfarmar da suka taru a wurin, kowa
mamaki yake yara sai leke suke wasu matan ma na maƙale saman katangu ana kallon ikon
Allah, kowa Allah Allah yake a ce wannan shine mijin Afeefah Annoba su kare mishi kallo...
Fara haramar É—aurin aure ake, a hankali Rayyan ya kalli Sulaiman
"Nawa ake bayarwa?"
Sulaiman ya É—an juya hannu alamar mene kenan?
"Sadakin?"
"Duk abinda kake dashi hawa hawa ne amma last da na duba a masallaci ƙarancin sadaki yana
dubu É—ari da tamanin da uku ne"
A lokacin aka fara ambatan sunayensu a hankali ya karkata ya zaro bandir É—in dubu-dubu guda
biyar ya miƙawa Uncle Sanusi aka miƙawa liman an ɗaura auren Afeefah Kamal da Rayyan
Moh'd Khamis akan sadaki naira Dubu É—ari biyar lakadan ba ajalan ba, wani irin yanayi ne yake
ratsa shi da ya kasa fahimta, idanunshi da suka sauya ya runtse yana ji ana ta rabon goro da
dabino da sweets.
Sai hannu ake bashi ana mishi murna da kyar yake iya kawo murmushi fuskarshi don yanayin
da yake ji baya misaltuwa mishi, kawu sai kallonshi yake baki galala yana ayyana lallai wannan
zai iya zama maye tunda gashinan irin mazan da yake kallone idan yara suna kallon India, a
fina-finan ma wannan ko ya aka yi kuÉ—inshi daban ne, limami ne yake rike da kuÉ—in sadakin
kawu yaje ya fara kokarin karɓa sai uncle Musa yayi interrupting ɗinsu
"Kun dai san sadaki hakkin mallakar matar ce ko?"
Limamin ya gyaÉ—a kai
"Toh zan tafi da wannan tunda ita yarinyar na gabana zan bata"
Yana kai nan ya nuna Mansur shi kuwa ya karɓi kudin gabaɗaya wani irin kullutun bakin ciki ne
ya tasowa kawun har wuya, uncle Musa ya murmusa ya fiddo dubu hamsin ya ba kawun Dukda
haka bai huce ba sai kumburi yake, anan aka yi reception 'yan kauyen sun ga abinci da kaji iya
gani, yana ta mamakin ya aka yi Mammi ta shirya waennan abubuwan with her condition, duk
kauyen babu gidan da ba'a ci shinkafa da kajin auren Afeefah ba don enough aka yi shi.
Karfe goma sha É—aya suka fara barin garin, kawu ya tafi zai shiga mota Uncle Musa ya janyo
shi
"Malam Labaran na ga kana kokarin shiga mota?"
"Eh wai dama in je ne in kalli inda 'yar tawa za ta zauna"
"Ah ai ba'a yi haka ba, ba yanzu ba zaka bari sai ta kwana biyu da kaina zan zo in kai ka yanzu
ka ga mutanen da ka tara dole ka tsaya ka ga sun tafi cikin salama"
Yana maganan ne yana tuna zancen Mammi da tace duk rintsi kar su dawo da kowa, tana so ta
dasa musu wani bakin ciki ne a rai gashi dai wacce suka kora sun haɗa ta da ƙaddarar ta
rabonta shine ya kawo ta har cikin Kaduna, sannan gashi sun gani kuma sun shaida a yanzu ta
shallake wa tunanin su kuma babu yadda za su yi babu abin da suka iya. Kwalelen biri da
hantar kura.
Shi dai bai gamsu ba amma haka uncle Mansur yayi ta mishi zaƙin baki har motocin suka watse
illa Sulaiman da Rayyan wanda yake jingine jikin mota ya harde hannayenshi a kirji yana
mamakin ikon Allah wai yau shi ne da aure. Ko sha'awar kallon kawun baya yi don ko da kawun
ya zo yana washe mishi baki tattare girarshi yayi ya haÉ—e fuskarshi ta koma ainihin shi mai tarin
kwarjini dole kawun ya kyale shi.
Su ne karshen barin garin sai masu canopies, sai cece kuce ake to Annobar ya saki Afeefah ne
ko an mata maganin mayun ne? Kap kauyen babu yarinyar da aka É—aura mata aure
kwatankwacin na Afeefah, sadakinta kaÉ—ai yayi sadakin mata ashirin a kauyen kaf... Inna Larai
na zaune da suntumemen kafa da kullum kara hauhawa yake tana jin komai tana hawayen
bakin ciki, inna Asabe ma sai uhmm uhmm take tayi abin duniya ya taru ya masu yawa barin
ma da aka aiko kulolin abinci wai na gidan kawun, ko da Afeefah ke mata abincin sayarwa
wannan yayi jarinsu sau goma don daga ganin shinkafar ka san ba na yara bane ga kaji baja
baja.
Suna gani Afeefah ta haye? Garin yaya duk basu sani ba. Ni kam na ce Allah take dashi.
Ko da suka iso Kaduna shi kadai ya nufi babban parlorn akwai mutane ciki sossai don yan uwa
Mammi duk suna nan ga su Umma duk sun zo yara ana ta ciye ciye ana wasa, kai tsaye
karamin parlorn Mammi ya leƙa sai ya ga wata cousin ɗinta tace mishi
"Tana sashen ka Rayyan"
Bai amsa ba don duk ana ta ango ango kanshi kasa da kyar yake dan murmusawa don kanshi
sara mishi yake.
A parlorn shi kuwa ya samu Mammin da wasu, tsayuwa yayi kawai yana kallonta ta ci wanka
cikin leshi blue doguwar riga ta É—ora gyalen da ya shiga da leshin a kanta da aka yi wa dauri
mai kyau, daga wuyanta kunnenta zuwa hannayenta da yan yatsunta gwalagwalai ne da suka
kawata adonta ta mishi kyau ainun har bai san ya fadada murmushin shi ba ya shigo ciki. Ta
tako a hankali ta kama hannunshi sai hawaye suka shiga zubo mata
"Alhamdulillah! Alhamdulillah!! Alhamdulillah!!! Allah na gode maka da ka nuna min wannan
rana, Allah na gode kwarai da ka ba ni lafiyar kasancewa da É—ana a rana mafi muhimmanci
cikin rayuwarshi, Allah ka dube su ka basu zaman lafiya Allah ka sanya musu tausayi, jin kai,
bege da kaunar junansu ka bashi ikon bata kariya da sauƙe duk wani hakki nashi na aure...
Rayyan..."
Sai ta kasa magana sai hawaye, kaman zai yi kukan shima yana jin adu'o'in nata har a cikin
zuciyarshi ya sa hannu yana dauke mata hawaye, jan shi tayi suka zauna ta zaro wayanta ta
kira Abeeha
"Ku zo da ita"
Daga haka ta kashe.
A gefen Mammin ya zauna yana gyara mata gyalenta nan masu hoto suka shiga aikinsu, sossai
suke yin kyau don shine yake ba ta kulawa bayan ya gama gyara mata gyalen ya sake share
mata fuska kan ya kalleta yana murmushi duk ana É—aukar su, suka kalli cameran suka
murmusa a tare ba karamin kyau suka yi ba, zai yi magana suka yi sallama suka shigo ganin
murmushin Mammi yayi yawa ya sa ya kai idanunshi inda take kallo.
Afeefah ce ke tahowa a hankali kaman wacce ke tafiya a kan ƙaya, tayi masifar kyau cikin wani
exlusive luxery lace da aka yi wa É—inki na amare, ko ina na jikinta a rufe ne ruf banda hannu da
fuskarta makeup da aka mata ya matuƙar amsarta ko don shine karo na farko a rayuwarta ne
bata sani ba, amma kam tayi kyau Tabarakallah.
Mammi ta miƙe ta tarbota
"Masha Allah, Tabarakallah É—iyata you made a beautiful bride"
Shi kam kallon seconds biyu yayi mata ya janye idanun har suka zo suka zauna Mammi tana
tsakiya Afeefah na gefenta na hagu yana zaune a gefenta na dama, idanunshi ya É—an tsayar
akan yatsun Afeefar da suka yi kyau ainun har yanzu mamaki yake, Mammi ce ta kama hannun
shi ta kamo na Afeefah ta haÉ—e a tare suka É—ago sai zuruf idanunsu suka faÉ—a cikin na juna,
idanunta da suka sake haske suka yi mai saboda kwallin da aka saka mata ya tsayar da kwayar
nashi a kai, ba zata iya jurar kallon ba sai ta duƙar da kanta daidai Mammi ta ɗora nata hannun
a kan nasu camera man yayi musu magana suka kalleshi aka shiga É—aukar hotuna.
Ko da za'a musu su biyu Mammi bata tafi ba don ta san in ta bar wurin shima sai ya bari, ta
miƙe ta mishi umarnin komawa mazauninta ya koma ɗin amma har lokacin da space tsakanin
shi da Afeefah mai hoton ya kalleta yace
"Amarya ki É—an matsa kadan sai ki sa kan ki akan kafadarshi"
Irin bugawar da zuciyarta ke yi tunani take kila saura kiris ya fashe ta mutu, kamshinshi
presence dinshi a kusa kusa da ita haka sai ya nemi ruda ta, yana so ya tashi don ya gaji hakan
ya sa ya É—an matsa kaÉ—an Jannah da duk tsoronta ta zo ta kama hannun su ta haÉ—e sai suka
kalli juna don duk sadda jikinsu ya haÉ—u su suka san abinda suke ji, kallon ya ba da wani
ma'ana na daban nan aka shiga daukar hotuna. Sossai yake a takure na tsaye aka ce shine last
Mammi dai bata yi magana ba amma idanunta ne ya hana shi barin wurin wallahi.
Bayanta ya koma, ya matso sossai har tana jin kirjinshi na taɓa bayan nata babu zato ta ji
hannunayenshi duk biyu ya zagaye cikinta, a É—an razane ta É—ora nata biyu a kan nashi
"Kin natsu ko sai na karyaki biyu? Baki san mutum ya gaji bane??"
Da É—an faÉ—a yayi maganan a kausashe amma wanda suke tare za su dauka wani abin arzikin
yake rada mata aka daddauka ya zame ya bar wurin su ma suka fice.
An yi yini an ci an sha an yi hidima har la'asar kan aka sake wanka aka fito harabar gidan
walima, amarya na sanye da wani tsadaddiyar Abaya da yanayinshi kaÉ—ai ya bayyana tsadar
shi canopies da kujeru aka shirya sossai aka yi walima aka ci aka sha kan mutane suka fara
watsewa don bayan isha aunties É—in su Jannah za su kaita part dinshi dake cikin gidan, Mammi
bata mishi maganan wani gida ba saboda ta sani ne ba zai taɓa tafiya ya kyaleta a gidan ba,
kuma parts dake gidan kenan don a tsare aka yi ginin Allah ma ya sa dakuna biyu ne a nashi
part É—in da kitchen da store sai parlor da dining section kaman flat ne mai zaman kanshi.
Aiko kan bayan isha mutane kadan ne a gidan masu aiki sai aikin tattare gidan suke, Afeefah
tayi sallah aka shirya ta again cikin atampha aka ɗora mata lafaya aka miƙa ta wurin Mammi,
sossai ta yi mata nasiha tana hawaye itama kuka take don bata da bakin godiya ga Mammi, ta
yi mata abubuwan da godiya sun yi kadan ta cika mata burinta na ganin ta auru, ta rungumeta
ta zame mata uwa da uba ta bata duk wani gata da take tunanin ta rasa to da me zata saka
mata in ba da zama lafiya da kuma zuciya É—aya jal da É—an ta mafi soyuwa a gareta ba? Sossai
take kuka tana tuna mamanta da Aunty zee ina ma Aunty zee na nan ta ga wai Afeefah ce a
É—akin miji? A haka aka kaita É—akinta da Adu'a a Bakinta.
Mammi waya ta É—aga ta kira shi, ba'a yi mintuna biyu ba ya shigo sanye da kananun kaya ash
har da hoodie don zazzabi yake ji tsabar hayaniyar da yake ji ya mishi yawa ya saukar mishi da
ciwon kai sossai.
"RAYYAN...."
🖤Gureenjoh🖤
HAIHUWA DA HANJI
(A True life story)
Fatima Muhammad Gurin
(Gureenjoh)
Wattpad-Gureenjo6763
Arewabooks-Gureenjoh
ADABI WRITERS ASSOCIATION
*FREE BOOK*
*33*
"Rayyan a yau Allah ya nufa ka sake samun wani nauyi a kanka bayan nawa da na ƙannenka,
na san ba wai ka ganta bane ka ji kana so har aka yi muku aure Allah SWT ka ba zaɓi shi kuma
ya zaɓa maka abinda ya fi dacewa da kai da kuma rayuwarka, idan har ka ci amanar ta ko ka
ha'inceta ba ita ka yi wa ba Allahn da ya baka shi ka yi wa, kar ka kalleta domin ni, kar ka so ta
domin ni, kar ka yi mata wani abu na alfarma domin ni duk abin da zaka yi mata ka yi saboda
Allah, idan ka so ta ka so ta saboda Allah don Allah ba don ni ba ka ba marar É—a kunya. Ka
zame mata gatan da ta rasa, ka zama uwa, uba kuma jigo a rayuwarta, ka zama majingina a
gareta ka tallafi rayuwarta daga cikin duhuwa zuwa haske madawwami"
A hankali ya ɗan ɗora kanshi a gefen kafaɗarta sai ta ji hucin zafin jikinshi na sauƙa Mata,
hannunta ya kama
"Mammi in shaa Allahu zan yi amfani da duk abin da kika ce"
Daga haka bai sake magana ba, ta san a takure yake ta kuma san akwai abinda ke cinshi a rai
a yanzu haka wanda bata tantama shi ya haddasa mishi zazzabi kuma muddin ya cigaba a
haka ba zai yi bacci ba amma sam ba zata tambaya ba, ba za ta matsa mishi ba.
"Ka tashi ka sha magani Saraki"
Ta faɗa, da kyar ya buɗe lumsassun idanunshi da suka rine ainun ya miƙe zaune, karbar pills
É—in yayi ya sha wanda ta haÉ—a da panadol a hankali ya kalli time karfe tara ne da wani abin,
Miƙewa yayi yana mayar da hannayenshi cikin aljihun hoodien jikinshi cike da dauriya yace
"Sai da safe"
"Allah ya baka lafiya"
Ya amsa da Amin kan ta mishi sai da safe ya fice da kallo ta bishi ta san sai a hankali zai saba
da wannan sabuwar rayuwar kuma, ta san sai Afeefah tayi haƙuri ta kara juriya kafin ta samu
yadda take so da shi matsalar kawai ya kasance ta shiga ranshi murmushi ta É—an saki kan ta
sha nata maganin itama ta shiga don kwanciya saboda kowa ya tafi baƙi kam duk babu kowa.
Wani iri yake ji a haka ya kutsa kanshi cikin parlorn bakinshi É—auke da sallamar da iya shi kaÉ—ai
ya san yayi kayanshi, taku biyar yayi ya samu kujera ya zauna yana dafe kanshi da kaman zai
rabe gida biyu, numfashi ne yake mishi wahalar fita kuma ya san yanayinshi ne da tunanin da
ya saka a ranshi, wani irin zafi yake ji kaman ana É—ora mishi wuta a kan zuciyarshi ina ma da
zai iya da kuka zai yi da ihu zai yi ta yi sai ya samu salamar abin da yake ji a ranshi, zamewa
yayi ƙasa kan carpet ya ɗora kanshi a kujeran yana rike zuciyarshi ya jima sossai cikin wannan
yanayi sai da ya ɗan samu relief ya miƙe ya nufi ɗakinshi kai tsaye, ruwa ya sha har gora uku
kan ya shiga zame kayan jikinshi daga wurin yana nufan bayi, ruwan sanyi ya sakarwa kanshi
yana yamutsa gashin kan nashi a lokaci É—aya yana dan buga glass É—in wurin wankan da
hannunshi.
Sai da yaji zai iya faÉ—uwa idan bai bar wurin ba ya fito É—aure da towel ya hau gadon ya kwanta
ko ruwan jikinshi bai tsaya tsantsanewa ba ya ja bargon ya rufe har kanshi ba wai don zai yi
baccin ba don ko ya rufe ido abin da ya tsana yake kallo.
Ita kam Afeefah dama ta san ba zuwa zai yi ba, bayan kowa ya tafi ta miƙe tana kallon ɗakin
har lokacin zuciyarta ke maimaita mata wai ita ce fa matar aure, yanzu ita ta tashi daga
buduruwa matar auren ma wai matar Rayyan, Allah buwayi gagara misali Allah mai yadda ya so
a lokacin da ya so, a hankali take bin É—akin da kallo ya ji kaya iya kaya yayi kyau fiye da misali
gashi wadatacce don za ta iya komai free ciki yana da girma, akwatunan da aka jera mata ta bi
da kallo guda goma sha biyu wai akwatunan aurenta ne, ita dake da kayan da basu wuci biyar
ba ita dake fama da allura da zare a kullum tana facin kaya ita dai Afeefah Annoba kuma
Mayya, sai hawaye suka fara sintiri a idanunta tana jin karin imani tana jin wani irin yarda da
ubangijinta.
A haka ta shiga bayin shima ta ƙare mishi kallo komai na 'yan gayu, bata yi wanka ba don sai
da tayi wanka ta saka kaya aka kawo ta karamin akwatin da Abeeha tace mata kayan bacci ne
ciki ta buÉ—e ta duba silk riga da wando cream Color yana da adon Black lace daga kirji da kuma
ƙasan kafafun wandon ta saka, kamshinta da kamshin ɗakin har ya so yayi mata yawa ga
sanyin Acn dake busawa kashe wutan tayi ta hau gado ta kwanta tana sake jin salama a ranta
sam bata wani sa damuwar rashin ganin Sarakin ba don ta riga ta sakawa kanta haƙuri da juriya
har Allah ya kawo karshen komai Dukda bata san yaushe ba bata san ko karshen zai zo ba
amma she have her trust in Allah zai mata komai ba sai ta damu kanta ba Adu'a ne babba
kuma zata cigaba.
Washegari da safe bayan tayi sallah ta ɗan koma bacci, ƙarfe tara ta farka ta sauƙa daga gadon
da kaman kar ta tashi tsabar daadinshi da take ji ta wuce bayi ta yi wanka ta fito ta fara neman
kaya cikin sababbin dinkunan da telan Jannah ya chanchada mata, wani atampha doguwar riga
A shape ta fitar ta shirya ciki tayi kyau sossai ta feshe jikinta da turarukanta sababbin waenda
kamshin suka yi mata ta kafa É—auri, bata sa kwalli ba sai ta saka lipstick kawai accesories da
tayi anfani na silver sai suka ƙara haskata tayi kyau ainun gidan ba baƙonta bane amma sai ta
fara tunanin ta saka gyale ne ko kar ta saka?
Tsoro take kar ta fita su haÉ—u don yanzu ba kaman da bane da ba lallai ma su hadu ba in ba
wurin Mammi ba, a hankali dai ta sa hannu ta buÉ—e kofan É—akin ta sanyo kai cikin parlorn, ko
taku biyu bata yi ba idanunta suka sauƙa kanshi a farko ta tsorata sai kuma ta fahimci kaman
bashi da lafiya ne don ga matar da take matsayin likitarshi zaune a kujeran dake fuskantar shi,
yayi relaxing sanye da wasu blue pjamas riga da wando complete, kafafunshi babu takalmi
suna lume cikin tattausan carpet É—in dake shimfide parlorn, fuskarshi yayi ja sossai haka gashin
kanshi a hautsine.
Wani iri taji a ranta sai taji tausayin shi na bin jikinta kaman ruwa, ta riga ta san dalilin da ka iya
kawo mishi ciwon a hankali ta shigo cikin parlorn Likitar na kallonta ta saki murmushi itama ta
mayar mata a hankali ta ɗan duƙa ta gaisheta ta amsa da kulawa tana tambayarta Ya Rayyan
da jiki? Ita dai ta amsa da da sauƙi amma bata ma san bashi da lafiyan ba sai yanzu.
A hankali ta kalleshi idanunshi na a lumshe har lokacin, matar ta miƙe
"Allah ya baka lafiya zan zo gobe da safe, please make sure ka ci abinci ka sha waennan pills
É—in"
Ta karashe tana ajiye mishi wasu pink pills a roba.
Sai a lokacin ya É—an buÉ—e ido
"Thank you"
Tayi murmushi ta yiwa Afeefah sallama ta fice.
Sai aka bar su su biyu a parlorn, yatsina fuska yake don kamshinta har kanshi yake ji ba tun
yanzu ya fara ji ba tun ranar da suka same shi a dining da Abeeha ya iya bambance nata
kamshin da na Abeeha, yanzu ma gashi ta zo ta tsaya mishi sai hawa kanshi yake tsaki ya É—an
ja ya buÉ—e ido sai karap suka hada idanu don kallonshi dama take tana tunanin ta inda zata fara
gaishe shi ganin ya kalleta sai tayi saurin cewa
"Ina..kwana!"
Ya yunkura ya miƙe zaune da kyau, bata yi zaton zai amsa ba sai jin deep and calm voice ɗin
shi da bai yi matcing da situation da yake ciki ba ya ce
"Good Morning!"
Daga haka ya miƙe ya wuce ta ya shige ɗakinshi, ta sauke numfashin tsoro tana nufan kofa
saboda knocking da ake, masu aiki ne rike da baskets na abinci kai tsaye suka jere mata su a
dining suna gaisawa don sun saba da juna dama, plates, cups da spoons taje ta É—auko ta zo ta
ƙarasa haɗa dining ɗin amma bata sani ba ta kirashi ne ko ta kyale shi, ta san ba zai so
shisshigi ba in ta dameshi ya iya karyata don ya sha ambata kalan ya zo ya faru ta shiga uku,
abincinta ta zuba ta ci har ta gama karyawa bai fito ba don haka tayi sashen Mammi don ta
duba ta.
A zaune ta sameta ta gama karyawa tana shan magani tana ganinta fuskarta ya washe da
fara'a
"ÆŠiyata ni da nace yau za ki huta sossai sai ga ki da sassafe? Sannu da zuwa"
Yadda take mata sai ya saka kunya kamata kaman wacce ta fito daga wani unguwar, a ƙasa ta
duƙa ta gaisheta tana mata ya jiki.
"Alhamdulillah dawo nan gefena Afeefah, ina shi Sarakin?"
Wani kunyar ne ya sake lullubeta ta kasa magana Mammi tayi dariya kawai ta janyo wayanta ta
kirashi
"Jiya ya tafi anan ban gamsu da yanayinshi ba, kun gaisa da safen nan?"
Kai ta gyaÉ—a
"Eh na fito na same su da likitan shi suna magana"
"kin ga ko, sai in rasa Meyasa yake ajiye damuwar da baya bayyanawa yanzu baya so in sani
ne ya ƙi zuwa nan tun sassafe na kira ban same shi ba je ki ce ya zo"
Gabanta ne ya faɗi rassss, ta ya zata fara kiranshi? A hankali ta miƙe ta fice zuciyarta na racing
har ta shiga parlorn inda Allah ya taimaketa ma ta samu yana parlor a zaune kan dining yana
karyawa wayanshi na a speaker alamu waya yake, a gefenshi ta ja ta tsaya sai ta ji Muryar
dake tashi kaman ta san Muryar kuka me Muryar take har tana shidewa a hankali take cewa
"Ya Rayyan bakin cikin Ya Saleem zai kashe mana Mommy, duk abubuwan da ya dinga yi a
baya mai sauƙi ne yanzu ya kore mu ya saka surakanshi a gidan, bai damu da mun ci ko bamu
ci ba, mun yi karatu ko ba mu yi ba muna lafiya ko babu tun muna zuba ido yanzu wata kenan
da ko mun je gidan ba'a bari mu shiga, ga mommy kwance a asibiti saboda damuwa da hawan
jini...!"
Dukda maganan da take yi É—in ya shige shi sossai, damuwa ya nuna a kan fuskarshi sai dai bai
tanka ba har ta gama ta cigaba da kukan.
"A wani asibiti take?"
Ya jefa maganan a hankali
"Tana 44 ne, anan muke da file"
Kai ya gyaÉ—a kan ya katse wayan, Afeefah dake tsaye jikinta ne yayi wani irin sanyi a hankali
zuciyarta ke motsawa da wani irin yanayin damuwa ba dai saleem da ta sani ake magana akai
ba? Amma ai wannan Muryar ta Sadiqa ce, saleem ne har ya kori mahaifiyarshi a gidanshi? Ko
jikinta duka kunnuwa ne ba zata yarda yana cikin hankalinshi yayi hakan ba, Wani irin tashin
hankali ne ya zo mata har ta kasa boyewa ta manta waye a gabanta tace
"Yaya Saleem ne cikin wannan hali? Shi ne ya kori mahaifiyarshi da kanshi? Su Samha ne ke
cikin irin wannan damu..."
HaÉ—a idanu da suka yi ya sa maganar ta katsewa idanunta har sun cika da kwalla suna shirin
zubowa, gani irin kallon da ya mata ya sa ta saukar da idanun ƙasa, ajiye spoon ɗin hannunshi
yayi ya zari wayan bai miƙe ba yana nuna ta da wayan ya ce
"Kika kuskura kika sake hawaye É—aya ya zubo miki a kan fuska za ki gane ba ki da wayo...!"
Mukut haka ta haÉ—iye kukan zuciyarta na cigaba da racing cikin mixed feeling ga idanun da ya
zuba mata yana jira ya ga zata yi kukan ne ko ba zata yi ba ga damuwar halin da ta ji wai
saleem na ciki.
"Mam..mi na ƙiran ka"
Ta faɗa a ɗan tsorace. Kwafa yayi ya miƙe ya fice daga wurin da sauri ta dafa dining ɗin tana
jan kujera ta zauna....
🖤Gureenjoh🖤
HAIHUWA DA HANJI
(A True life story)
Fatima Muhammad Gurin
(Gureenjoh)
Wattpad-Gureenjo6763
Arewabooks-Gureenjoh
ADABI WRITERS ASSOCIATION
*FREE BOOK*
*34*
*Don Allah readers ina É—an so ne in ja hankalinmu a kan wani abu da na fahimta, zan É—an yi
magana ne da miyaun marubuta. A duk sadda marubuci ke rubutu ba duba iya zallar
nishadantarwa yake ba ko da kuwa littafin akan nishadi ne, ba son rai ake dubawa ba saboda
ba shi ne ake son isarwa ba, duk sadda marubuci ya É—ora alkaminshi a kan Littafi tunanin farko
da zai fara shine me ya kamata na isar? Shin wani saƙo ne nake da shi a cikin labarin nan da
zan ba al'umma kuma su amfana da shi? Kar mu raja'a ga iya fannin nishaÉ—i ko soyayya don
rayuwa bai taɓa tafiya babu ƙalubale ba... Don haka don Girman Allah mu daure muna karatu ta
fuskar É—aukar darasi don akwai darusa masu yawa da marubuci kan jefa a cikin kowani labari
wanda ba sai an fito fili an ce yi kaza kar ka yi kaza ba mu dinga kokari muna fahimtar hakan
saboda mu marubuta mu samu ladar kuðŸ‘ðŸ™*
****
Da kyar ta iya danne kukan da ke taso mata, tsoron Allah na ƙara rufeta tana tuna irin iko da
isan mommy akan saleem ashe har za'a iya samu macen da za ta raba wannan iko da isar cikin
lokaci kankani haka?
Miƙewa tayi ta nufi sashen Mammi, ba za ta zuba ido rayuwar saleem ya cigaba da tafiya a
haka ba don salim ya cika mutum cikakke É—ari bisa É—ari ya taimaketa a sadda bata da mai
taimako bayan Allah, shi ne namiji na farko da ya fara nuna mata so tsakani da Allah ba tare da
kyama ko tsoron tabbatuwar zancen al'umma a kanta ba, ya hana hawayenta zuba ya kuma
ƙarfafa mata gwiwa akan jajircewa da haƙuri da rayuwa, ta san babu abin da zai saka saleem
saɓawa mahaifiyarshi don ya san darajar ta fiye da kowa face sharrin asiri. Abin da ya sake
bata mamaki ya É—aure mata kai shine ta yaya wacce mommyn ta yarda da ita har ta aura mata
saleem ba tare da yana so ba ta zama sanadiyar rabuwarta da É—anta? Sam bata kawo cewa ko
alhakinta bane saboda ta san ita É—in ba dolen su ba ce da su taimaketa da kar su taimaketa duk
wannan tsakaninsu da ubangiji ne yo waenda suka zama dolen nata ma basu mata ba sai bare
ne za su mata?
Ta saka a ranta son zuciyar mommy ne ya janyo mata wannan wahala da suke ciki, tayi
negleting duty É—inta a matsayin uwa tana ganin dabararta shi zai sa 'ya'yanta su cigaba da
zama ƙarƙashin ikon ta alhali 'ya'ya ba ababen iko da gadara bane ta manta Allah ne ke da
dukkan iko akan bayinsa kuma shi ne ya san abin da yake fili da na ɓoye.
Ko da ta isa wurin Mammi bata samu Rayyan ba, zama tayi cike da damuwa tace
"Mammi Yaya saleem na cikin masifa"
Ta ƙarasa idanunta na cika da kwallah, Mammin ma ta fahimce damuwar Afeefar don Saraki ya
sanar da ita komai kuma tausayin Saleem É—in duk ya rufeta itama.
"Yanzu Saraki ya gama sanar mini, nayi mamakin yadda aka dau lokaci bai zo ba har ma aka yi
auren Saraki saleem ba ya a kusa da shi ashe abin da ke faruwa kenan, laifin mahaifiyarshi ne
Allah ya sa wannan abu da ya faru ya zame mata Aya ya sa ta hankalta"
Kai Afeefah ta gyaÉ—a tana amsawa da
"Ameen ya rabbi, Mammi ina so in taimaki Saleem Dukda ban san me Ya Saraki zai yi ba
amma ina so in ba saleem gudummawa kaman yadda ya ba ni a sadda na rasa madafa don
Allah ki taimakeni akan hakan"
Ta ƙarasa a karye.
"Me kike tunani Afeefah?"
Mammi tayi tambayar cike da kulawa.
"Mammi ina so ki yi convincing Ya Saraki akan za ki dinga bashi magani yana saka saleem sha
ni kuma zan dinga haÉ—a zobo ko wani kalar drink da ayoyin da mafificin annabin mu annabi
Muhammad (SAW)
Yayi mana umarnin amfani da shi don karya sihiri, ko da kurba bibbiyu zai yi Allah zai ba mu
nasara kuma ina so zan yi wani abu na sadaka da tawassilin Allah ya dube shi ya dawo dashi
hayyacinshi kar mahaifiyarshi ta mutu da damuwarshi"
Sossai Mammi ta yabawa hankalin Afeefah ta kara jin kuma tabbas bata yi wa Rayyan zaɓen
tumun dare ba, ta gamsu kuma da shawarar don haka ta tabbatar mata zata bata duk wani
taimako da take so.
Afeefah ta ji daaÉ—i ta koma É—aki ta fara neman takardar ta da tayi rubutu akan hakan a sadda
malaminsu na islamiyyat ke koyar da su, ta kuwa samu bayan dogon bincike Adu'a kawai take a
ranta Allah ya taimaketa.
****
Rayyan na fita Asibitin ya wuce kai tsaye ya samu kuwa mommyn na jin jiki yaran sai kuka suke
yi, har ranshi tausayinsu yake ji kuma yana jin su ne tamkar su Abeeha, shi karan kanshi a
yanzu ya gamsu cewa asiri ne ke dawainiya da abokin shi in ba haka ba ko mahaukaci ai ya
san girma da darajar uwa.
"Kukan nan me zai yi mata? Ko ba ku san Adu'a shi ne makamin ko wani mumini ba? Ko kukan
lafiya zai bata?"
Da É—an faÉ—a yayi maganan don sun cika mishi kunne, duk shiru suka yi don sun san shi baya
É—aukan nonsense da likitan da ya duba ta yaje yayi magana don anan É—in ma yana da office
kuma yana aiki da nan É—in Dukda ya fi zama Capital.
Daga nan ya shiga ya duba ta tana bacci ya dawo ya kallesu yana so yayi magana da
hankalinsu zai kwanta bai iya ba sai cewa yayi
"Komai zai wuce in shaa Allah"
Daga haka ya zaro kuɗi mai yawa ya basu kana ya fice, yana shiga mota Mammi ta ƙira shi a
waya.
"Saraki idan ka samu Saleem ko da a waya ne kar ka yi mishi magana da tashin hankali, ka bi
shi da lalama kuma kar ka tsananta magana akan mahaifiyarshi da 'yan uwanshi ka nuna baka
damu ba don kar matar tashi tayi yunkurin shiga tsakaninku don akwai abinda nake so kullum
ka tabbatar kana bashi yana sha, shi ramin ƙarya a koyaushe ƙurarre ne zai wuce ne kaman
ba'a yi ba"
Ya gamsu kuma ya san Mammi wani abin zata sama mishi na karya sihiri ya ji daaÉ—i don bai
san ya zai yi ba, ya tabbatar saleem a gidan ba zasu barshi yayi komai na malamai ba bare
yace zai kaishi wurin wani malami. A kan ibada da azkar ne zai tsaya sossai ya ga saleem É—in
ya koma yi don tun da chan É—in shi saleem ba mai wasa da ibada bane kai duk iya ibadarka
idan Allah ya nufa kamun asiri na cikin jarabawarka dole sai ya kama ka sai dai ka samu
sassauci saboda ka riga ka yi tawasilli ubangiji shine mai yin komai.
Kai tsaye gidan Saleem ya je Allah ya bashi sa'a ya dawo don yana horn aka buÉ—e mai gate a
mota ya tsaya ya shiga kiran Layin saleem É—in ringing na karshe aka sada shi dashi, amsa
sallamar kawai yayi ya ce
"Ina waje"
Yana kai nan ya yanke wayan kusan mintuna uku sai ga saleem É—in ya fito, ido kawai Rayyan
ya kura mishi don kaman ba shi ba ya É—an yi duhu kuma ya tara gashi sannan fuskarshi babu
walwala haka ya iso ya buÉ—e gefen zaman banza ya shiga ya zauna.
"Ya kake?"
Saleem É—in ya tambayi Rayyan yana kallonshi.
"Lafiya ƙalau, ka yi wuyar gani."
Murmushi yayi wani dry smile da babu annuri ciki
"An tura ni Lagos ne wani aiki shine muka tafi da madame fa, inda nake kuma babu wani
service na kirki"
Kai Rayyan ya gyaÉ—a.
"No wonder, ya kowa da kowa?"
"Lafiya ƙalau"
"mu shiga mana in gaishe da mommy kwana biyu ban leƙa ta ba"
Saleem ya É—an yi shiru don wlh ya manta da ya tura su chan gidan.
"Mommy bata nan sun koma tsohon gidan mu"
"Amma me yasa? Ina haya kuka saka a chan?"
Ya É—an yi shiru
"Eh, nan É—in ya É—an takura mu ne ga iyayen Sabrina sun dawo shiyasa nace su koma chan"
Kai kawai Rayyan ya girgiza duk ranar da Allah ya bashi macen da zata raba shi da Mammi bai
san irin hukuncin da zai mata ba don idan bai kasheta har lahira ba sai ya nakasata yadda ba
zata taɓa amfani ba har abada.
"Ya Mammi da jiki?"
Saleem ya katse mishi tunanin da yake yi
"Tana ta faÉ—an kwana biyu baka shigo ba ai, ni kam saleem in tambayeka mana?"
Kai yaa gyaÉ—a mishi
"Ya tsakaninka da ubangijinka?"
Ya É—an yi shiru kan ya kalli Rayyan É—in
"ban gane tambayar ba, ina sallah biyar a rana yadda aka umurci kowani musulmi"
"na sani, ina magana ne akan nafilfili musamman na dare da na sanka da shi da azumin nafila,
yau ka ma yi azkar na safe?"
Numfashi saleem ya ɗan sauƙe kaman abin na damun shi
"A gaskiya na manta rabon da in yi wani azumi da Sallar nafila, azkar ne nake dan yi watarana
wani sa'in wani abu ya taso ko bacci ya hana ni amma zan yi kokarin ganin na gyara"
"Don Allah saleem ka gyara, da karatun alqur'ani kar ka manta ko da baka yi a fili ko baka nuna
kana yi ba idan ka ji ƙuncin zuciya ka dinga ambaton Allah zai yaye maka ka ji?"
Ya ƙarasa da tausayin abokin nashi, kai ya gyaɗa.
"Ka shiga ciki"
Rayyan ya faÉ—a don ganin Sabreenar na tsaye tana kallonsu, ba don tsoronta bane baya so ta
fahimci ya san matsalar saleem din kuma baya so ta tambayi saleem É—in abinda ya wakana
tsakaninsu don irin su akwai wayo idan baka iya kama ɓarawo ba aka ce sai ɓarawo ya kama
ka.
"Gobe zan zo in gaida Mammi"
Kai ya gyaÉ—a
"Sai ka zo"
Daga haka ya fice shi kuma ya ja motan ya bar gidan.
****
Afeefah yinin gabaÉ—aya bata zauna ba, musamman Mammi ta ba da aka yi mata sayyayar
kayan zobo don ta san saleem na son abin, ta dafa shi ta tace bayan ta gama yi mishi haÉ—i ta
zauna ta yadda idan tana karatun numfashinta zai dinga sauƙa ciki ta fara karanto Ayatushifa
Suratul tauba aya ta goma sha huÉ—u 14.
Suratul Yunus aya ta hamsin da bakwai 57.
Suratul Isra'i Aya ta tamanin da biyu 82.
Suratul nahl aya ta sittin da tara 69.
Suratul shu'ara aya ta saba'in da takwas har zuwa na tamanin da biyu 78-82.
Suratul fusilat aya ta arba'in da huÉ—u 44.
Ta Yi su ne kafa bakwai bakwai, ta yi su da tawassilin cewa Allah zai karɓa har cikin zuciyarta
babu kokonto don ba'a yi wa Allah kokonto ta yarda da cewa muddin ya yi amfani da wannan
ayoyin na tsawon kwana bakwai duk abin da ke jikinshi sai ya kau. Ba sai a zobo ba ko a cikin
ruwan miya ko a cikin ruwan tuwo kai duk abu da mutum zai iya ci muddin aka yi ayoyin nan
kafa uku uku ko kafa bakwai bakwai da yardar Allah ko niyyan sihirin ne aka yi maka ba zai
kama ka ba bare wanda ke cikin jikinka.
A gefe akwai ganyen magarya guda bakwai busassu ta cika farin bokiti surr da kyakyawar ruwa
shima ta zauna yi mishi nashi a yayin da Abeeha ke tayata dura zobon a goruna don a sa a
frigde. A cikin wannan bokiti mai dauke da magaryan ta shiga karata ayoyin kaman haka:
Suratul Fatiha.
Ayatul kursiyu.
Suratul A'araf aya ta É—ari da shida zuwa É—ari da ashirin da biyu 106-122.
Suratul Yunus aya ta saba'in da tara zuwa ta tamanin da biyu 79-82.
Suratul kafirun kafa É—aya.
Falak da Nas ƙafa uku uku.
Sai ta karanta wannan Adu'a:
'Allahumma rabannas azhabal ba'as washfi antas shafi la shifa'un illa shifa'uka shifa'un la
yugadiru saƙaman' kafa uku.
Sai ta rufe da
'Bismillahi Urkika min kulli shai'in yu'uzika wa min sharri kulli nafsin Allahu yashfika Bismillahi
urkika' shima kafa uku.
Hawaye ne ya sauƙo mata bayan ta gama tsaf, ta sa hannu ta share tana Miƙewa tsaye tayi
yakini akwai waraka cikin alqur'ani, ta yi yakinin saleem baya bukatar wani boka ko malami da
waennan kaÉ—ai Allah zai isar mishi.
Sossai Mammi ta jinjina mata don bata bar sashen Mammin ba sai bayan isha, zobon duk a
fridge na sashen suka shirya wanda ya kai gora hamsin ta ajiye ruwan ma lungun kujaran da
Mammi ke zama a rufe.
Sallama tayi wa Mammin zata fita Mammi tace
"Ki bi sai ki É—auka muku dinner É—in ku daga kitchen na san Saraki yana chan yana jira don tun
É—azu ya yi min sallama"
Da Toh ta amsa kan ta fice Mammi ta bita da kallo tana murmushi.
A basket yanzu ma ta samu an shirya musu komai da komai ta É—auka ta nufi sashen, ita dai
wannan yanayi da take shiga ta rasa shi don tana tura kofan kamshinshi da ya cika parlorn ya
sanar da ita yana ciki kaman kuwa ta chanka daidai don yana zaune kan kujeran dining
gefenshi energy drink ne da yake kurba a hankali yana dannan waya fuskan nan babu É—igon
fara'a.
Ajiye basket É—in tayi tana tsoron yin magana ta yi laifi sai ta fara cire kwanukan tana shirya su a
kan dining ɗin, ta tafi ta samo cutlaries da plates ta fito da su taje ta ƙaro ruwa da drinks ta kawo
ta fara kokarin ajiyewa a lokacin ya ajiye wayanshi ya É—aga ido ya kalleta sai ta nemi ruÉ—e wa
garin ajiye ruwan goran sai ya faÉ—i ya Buge cup É—inshi na energy drink da ta samu a wurin ya
ɓare kan wayanshi... Wani irin zaro ido tayi ta zari wayan ta fara gogewa da hijabin jikinta tana
furta
"Innalillahi..."
*Ban yi alkawarin na dare ba amma in har na samu dama za ku ji ni*
🖤Gureenjoh🖤
HAIHUWA DA HANJI
(A True life story)
Fatima Muhammad Gurin
(Gureenjoh)
Wattpad-Gureenjo6763
Arewabooks-Gureenjoh
ADABI WRITERS ASSOCIATION
*FREE BOOK*
*Ɗazu na ɗan leƙa online na ga yadda ake cigiyata har gabana ya faɗi na zaci laifi na aikata wai
sai na ga ashe Haihuwa da hanji ake nema ido rufe😅 Za ku dinga haƙuri da ni Weekdays
gaskiya don Sai yamma nake samun lokaci ko kuma dare, weekend da kuke samu raɓa raɓa
ma saboda babu inda nake zuwa ne kuma ba ni da aikin komai, and ban da saka tsammanin
pages biyu a weekdays ba zai haɗu ba, don Allah a rage ambaton Gureenjoh razana nake🤣🤣*
*35*
Baya baya yayi ya jingina da kujerar tare da relaxing, idanunshi har lokacin zube a kanta yana
aikin kallon yadda ta ruɗe sai haƙuri take bashi tana share wayan da hijab ɗinta, he is surprise a
lokaci daya kuma he's amuse bai taɓa ganin halittar dake tsoron shi irin ta ba, shi ba dogon
magana yake mata ba shi ba dukan ta ya taɓa yi ba amma yadda take yi akan wayan sai ya ga
kaman cewa yayi zai sa bindiga ya harbe ta.
A hankali ya miƙa tattausan hannunshi ya ɗora a kan nata da ke riƙe da wayan, abin da taji shi
ya sakata natsuwar dole ta É—ago ido ta kalleshi suka haÉ—a idanu, for some seconds ya janye
idanunshi ya zare wayan ba tare da ya ce komai ba.
Ita har ga Allah tana mamakin shegen miskilancinshi ayi mutum babu magana ai sai yayi ciwon
baki, ganin bai ce mata komai ba sai ma kokarin saka abincin yake tayi saurin É—aukan spoon ta
shiga serving É—in shi bayan ta tura mai ta juya za ta bar wurin ta ji ya ce
"Ina za ki je?"
Juyowa tayi ta kalleshi kaman ba shi yayi maganan ba hasali ma abincin shi yake ci hankali
kwance, ganin tsayuwar ba zai mata ba sai ta nufi kujeran dake nesa dashi ta zauna ta É—an
saka abincin kadan ta shiga ci a hankali. Bai fi mintuna ashirin ba ya miƙe ya bar dining ɗin ta bi
shi da kallo har ya shige É—akinshi.
Washegari kuwa da Mammi ta faÉ—a mata saleem zai zo har gidan ta shiga kitchen ta musu girki
ta sake yin tofin a ruwan abincin da ta shirya musu, a dining ta jera musu ta wuce É—akin Mammi
tana shiga bata zauna ba yana shigowa, a ƙasa ta zauna wurin kafafun Mammin shi kuma ya
zauna daga gefenta Mammi ta amsa gaisuwar da ya fara yi mata ta É—ora da
"Ya jiki?"
"Alhamdulillah Mammi, ya naki?"
Ta amsa cikin kulawa.
"Afeefah kawowa mijinki ruwa mana"
Wani irin dukanta kalmar yayi a hankali ta É—an kalleshi shima ita ya kalla jin wani mijinki da
Mammi ta faɗa ya janye ido, ta miƙe ta isa fridge ta ɗauko zobon nan da Cup ta kawo mishi
tana ajiyewa ya furta
"Thanks"
Yana É—an lumshe ido saboda kamshinta da ya shige shi, yana mamakin kalar turaren da take
amfani dashi ko yaya ta matso kusa dashi sai yayi perceiving smell din, tsiririn tsaki ya ja.
Ta juya zata fita Mammi ta tsayar da ita
"Ina kuma zaki je Afeefah ba kin zo taya ni hira bane?"
Dukkansu basu yi tsammani ba suka ji muryarshi yana cewa
"Dodonta ya shigo dole ta fita."
Calmly yayi maganan, ta É—an wara idanunta bata ce komai ba sai da Mammi ta É—an yi dariya ta
yi rau da fuska a É—an karye tace
"Mammi akwai abin da na manta ne ban yi ba a kitchen shiyasa zan fita fa"
Ya É—ago cup na zobon yana sha suka haÉ—a idanu da sauri ta fice, ya juya ya kalli Mammi
"wannan yarinyar ta cika tsoro da yin abu a zabure, ko ina haÉ—iye mutane ne?"
Shi dai da gaskiyar shi yayi maganan yana mamaki kuma.
Dariya sossai Mammi tayi
"Ka haÉ—iye mutane ai babu zaman lafiya kawai yadda kake É—aure fuskar ne yayi yawa Saraki,
ya kamata ka sakar mata tunda matarka ce"
Bai tanka ba chan ya É—aga cup na zobon
"Yayi daaÉ—i."
"matarka ce tayi!"
Ya kalli Mammi yana maimaita matarka a zuciyarshi Mammi har ta haddace kalmar, zai yi
magana ƙira ya shigo wayanshi saleem ne, Miƙewa kawai yayi ya fice.
Chan sai gasu sun shigo babban parlorn, Mammi ta fito suka gaisa tana ta mishi magana baya
shigowa yanzu ya dube ta yana murmushi mai nauyi yake furta
"In shaa Allah zan ke zuwa Mammi"
"yauwa gwara kam ka zo Saleem, idan ba damuwa ma ina so in roƙi alfarmarka"
A kunyace yace
"Mammi kun wuce alfarma ai a wurin mu sai dai umurni"
"Yauwa toh na gode da wannan matsayi, idan har ba zaka takura ba ina so in dinga ganinka
kullum for seven days akwai maganin kariya da Saraki ke sha ina so ku sha tare duk aikin naku
É—aya Fatan mu dai Allah ya kare mana ku ya sa ku gama lafiya"
Suka amsa da Ameen, cike da biyayya da yake da shi tun chan yace
"Na gode sossai Mammi kuma in shaa Allah zan ke shigowa har kwana bakwan"
"yauwa Allah ya muku albarka, ku isa ga abinci chan an shirya muku a dining"
Tana kai nan ta miƙe ta koma sashenta, hira suke ɗan yi kaɗan kaɗan a hankali ya ɗan lumshe
ido ya buɗe kan chak ya miƙe yana furta wa saleem
"Ina zuwa!"
Corridor da zai kai ka side É—inshi daga nan babban parlorn yayi aiko a gab wurin fitowa parlorn
suka yi karab da ita har tana Buge mishi ƙirji, baya baya tayi tana ɗagowa suka haɗa idanu
sanye take da wani riga da skirt na lace da bai wani kamata ba amma yayi masifar amsarta
kasancewar shi Red colour tayi É—aurin ture ka ga tsiya, É—an kunne ne kawai a kunnenta bata
saka sarƙa ba sai wuyan nata ya fita fresh yana ɗaukar idanu, ga mamakin ta mugun kallo ta ga
yana mata sai ta sake shan jinin jikinta.
"Ina kike tunanin zuwa?"
Tambayar sai ya sakata cikin duhu dama ina take zuwa a gidan da ya wuce wurin Mammi ko
Abeeha.
"Ina magana kin yi min banza? Na fara wasa dake ne?"
Da faÉ—a yayi maganan sai ta matsa baya idanunta na cika da kwallah tace
"wurin Mammi za ni"
"Daga yanzu har nan da kwanaki bakwai ko da wasa bayan gaisuwan safe da za ki je yi wa
Mammi ki bari mu yi ido huɗu dake a main parlor sai ranki yayi mummunan ɓaci, wuce ki bani
wuri"
Hawayen da take ta riƙe wa na tsoron ne ya zubo mata da sauri ta juya ta koma, bai bar wurin
ba sai da ya ga ta ɓace ya ja tsaki mai ƙarfi ya juya ya koma parlorn, inda ya tashi ya zauna
yana sake jan tsaki.
"Lafiya kam?"
"Ƙalau, mu je mu yi lunch azahar ya kusa"
Miƙewa saleem yayi suka isa dining ɗin Rayyan yayi serving ɗinsu suka zauna suna ci saleem
sai yabon girkin yake har suka gama suna É—an hira tsakaninsu daga nan suka shiga wurin
Mammi ta haÉ—a su da zobon Dukda sun sha a dining bayan ta basu maganin a cup masu kyau
duk su biyu suka sha saleem yayi mata sallama suka fito tsakar gidan.
Suna shirin fita masallaci Motar Abeeha ya shigo gidan tayi parking tana saukowa fuskarta a
É—an washe ta gaishe su, duk suka amsa saleem na tambayarta school ta amsa da
Alhamdulillah daga nan ta shigo ciki su kuma suka fice daga gidan, sai bayan sun yi sallah ya
zo ya É—auki motar shi ya wuce gida, shima Rayyan mota ya É—auka ya tafi duba Mommy ya
samu da sauƙi sossai ma akan idanunshi aka bata sallama shi ya biya duk bills ɗin kasancewar
akwai mota bai kaisu gida ba sai kwantar wa mommy hankali yayi suka tafi shima ya nufi gidan.
Ita kam Afeefah É—akinta ta koma ta zauna akan kujerar mirror tana kallon kanta, a hankali ta sa
hannu ta dafa saitin zuciyarta da har yanzu bai daina bugawa ba hawaye ne taji suna silalo
mata, bata san wani mataki zata ajiye kanta ba a wurin Rayyan tsanar ta yayi ko kuma haushin
kusancin ta da mahaifiyarshi yake ji bata sani ba, Meyasa zai saka mata boundry da shiga cikin
gidan? Me tayi? Da kyar ta kauda tunanin ta tashi ta fara kokarin shirya wardrobe É—inta tana
janye tunanin, a wayanta ta saka karatun qur'ani tana aikin har la'asar kan ta gama ta adana
akwatunan ta tafi tayi alwala ta zo tayi sallah, tana zaune taji ana mata knocking ta miƙe taje ta
buÉ—e sai ta ga Abeeha ce murmushi suka sakarwa juna ta shigo ciki.
"Cigiyarki na zo yi tun fa jiya rabon da mu haÉ—u matar bross"
Tana É—an murmushi tace
"Da kin taimakeni in kika daina dangantani da wannan Yayan naki, Mammi ma da take faÉ—a
bani da yadda zan yi ne"
"Toh Meyasa? Ke ba matar tashi bace?"
Abeeha ta faÉ—a tana zama kan couch na É—akin.
"Gabana faÉ—uwa yake a duk sadda aka dangantani da shi, ban sani ba tsabar yadda nake jin
shakkarshi ne ko yaya"
"ke fa ba mu bane Afeefah, ya kamata ki rage wannan tsoron nashi wlh ko mu bama mishi irin
tsoron da kike mishi ke matarshi ce sirrin shi, a ina kika taɓa ganin matar dake shakkar mijinta?
Lalalalala idan kika tafi a haka ke za ki cutu"
"Adda Abee ba za ki gane bane ke kam, ya saleem É—in ya shigo? Kin ganshi? Ya ci abincin?"
Kallonta Abeeha tayi
"Eh ya shigo, sun ci har ya tafi ma tun azahar"
Ajiyar zuciya ta ɗan sauƙe suka cigaba da hira da Abeehar, Abeehar na nuna mata tayi amfani
da trainings da aka yi mata kar kudin Mammi ya tafi a banza ita dai sai dariya take don ko
tsireta za'a yi ba za ta iya ba wlh, sai Magrib Abeeha ta tafi ita dai Afeefah bayan tayi isha ta fito
ta samu an kawo musu abinci kaÉ—an ta É—iba ta koma É—akin don ko haÉ—uwa bata so su yi.
Daga ranar kullum Saleem sai ya shigo kuma Mammi bata taɓa ƙasa a gwiwar basu tofin ba
yayinda bayan an gama abin kari Abeeha ke shiga kitchen da kanta ta musu girki tunda anan
yake cin abincin rana har kwana bakwan, kafin ta gama girkin take zuwa ta gaishe da Mammi
bayan ta gama ma ta kan leƙa ta kan ta wuce sashenta bata sake zuwa sai gobe tunda ya hana
gwara ta bi umurninshi ba tare da ta san dalili ba, a sashenta take zama tayi karatu tayi bacci ta
gaji gashi bata iya zaman parlorn don bata so su haÉ—u kuma kaman ka'ida tun daga ranar basu
sake haÉ—uwa da shi ba har kwana bakwan ya wuce don ko abincin dare ana kai musu zata je ta
diba ta shiga É—akinta ta rufe. Adu'ar ta kuma a koyaushe shine Allah ya dubi Saleem ya yaye
mishi wannan bala'in.
Ta ɓangaren saleem tun daga ranar da ya fara zuwa wurin Mammi yana shan tofin kuma yana
ci a abinci ya fara jin wannan nauyin na zuciyarshi na raguwa, kanshi da kaman an daddaure
baya wani tunani mai kyau ya ji kaman ana kwakwance jijiyoyin, bai dai nuna komai ba don tun
bayan kwana biyu da ya fara zuwa Sabreena ta saka shi gaba Meyasa yake zuwa gidan aboki
yake cin abincin rana bayan bata Gaza ba wurin cinshi? Meyasa ma yake zuwa gidan su
Rayyan É—in abin da baya yi da kaman ka'ida kullum sai ya je?
"Sabrina yaushe ya zamana in zan fita ko zan yi mu'amala da wani sai na bi ra'ayinki ne kam?
Meyasa za ki damu da abin da bai shafe ki ba? Yau na fara cin abinci a gidan aka ce miki? Toh
bana son damuwa da ciwon kai idan maganan da zaki cigaba da yi kenan ki tashi ki bani wuri"
Da wani irin tsantsar mamaki take kallonshi
Za Ta yi magana ya daka mata tsawa
"Ki fita nace!!"
Da sauri ta miƙe ta fita har tana haɗawa da sassarfa bata tsaya ko ina ba sai wurin Gaje don
babanta baya nan ya fita.
"Mun shiga uku! Gaje Ya Saleem yau ni yake yi wa tsawa! Me yake shirin faruwa?"
"Ke ki natsu dallah chan me zai faru kuwa? Ya wuci kin je kin dameshi ne yana so ya huta, ki fa
sani ko da mallakarshi da muka yi sai kina bin shi a hankali"
"Gaje bai fa taɓa ɗaga min murya ba tunda na shigo gidan nan ina tsoron kar wani abu ya faru
ne"
"Babu abin da ya faru daga ni har mahaifinki muna da yakini kan aikin da aka mana har abada
ba zai kwance ba, ki bashi lokaci sai ki koma"
Ko da ta bashi lokaci ta koma bai yi mata magana ba, sai ta yarda da cewa ita ce ta takura
mishi don haka bata kara magana akan zuwa gidan su Rayyan ba, yau ya shigo gidan sai ya
tsaya chak a parlorn yana bin sababbin kujerun da kallo, a hankali ya tsayar da idanunshi kan
kujerar da mommy ke yawan zama, tunanin mommyn ya fara sai yaji kanshi ya wani irin sara
gabanshi ya shiga faɗuwa zuciyarshi na bugawa da ƙarfi da ƙarfi daidai Sabrina ta fito ganinshi
dafe da kujera ya sa tayi hanzarin isa kanshi
"Ya Saleem lafiya? me ya sameka? Menene?"
"Ƙira min Mommy!"
Darammm ta ji zuciyarta ya buga...
****
Kawu Labaran ne riƙe da Ghana most go yana kallon Inna Larai dake ta juya kai tana fama da
suntumemen ƙafarta da kudaje ke ta sukuwa a kai yace
"Ki yi min adu'ar dacewa ai na ji unguwar da É—aya kawun nashi ya ambata chan zan je in
tabbatar da gidan da Afeefar take sai na dawo da ita ta kai ki asibiti don ni dai ba ni da wani
kudin asibitin birni! Kin ga dama ke ce uwar É—akinta..."
Inna Asabe ta katse shi
"Malam anya za ka yi hankali kuwa? Wani irin zance ne kake yi hakan? Taya Afeefah zata fara
taimakon mu bayan duk abubuwan da suka faru? ka manta ita da kake ikirarin itace uwar goyon
nata ko ɗakinta bata taɓa bari Afeefar ta taka ba?"
"Amma dai mun ciyar da ita kuma mun tufatar da ita, har É—aki sukutum muka ware mata tayi
rayuwa kaman 'ya'yan gidan nan ni ko hassada kike yi min ne ma kin ga zan je birni?"
"Allah ya kyauta in maka hassada, ina dai tunatar da kai ne ita Larai É—in me ya hana 'ya'yan ta
yi mata? Mugun alkaba'in da muka bi yarinyar nan dashi shi muke gani a wurin namu yaran
daga masu shaye shaye sai masu cikin shege ana ɓararwa a maimakon mu fara tunanin laifin
mu mu fara neman hanyar gyara ka sabi jaka don son zuciya zaka tafi neman kudi wurin wacce
ka yiwa korar kare a gidan nan..."
"Na rantse ko ki min shiru ko in saka sandata in Buge ki, ni zaki faÉ—awa maganar banza? Idan
wulakanta Afeefar ne duk wa ya more ta bayan ku? Ina ce anan kullum take dawo muku da
kudaden da take samo muku ni me na taɓa sakata sayar min? Ko ba kece kullum dare kike
hayaƙin tafarnuwa da kuka da Ƙashin kifi ba duk saboda Afeefar? Idan akwai waenda ba zata
yiwa abu ba sai dai ku, ni kam dolenta idan ma bakin ciki kike min sai na je... Ke kuma Larai ki
jirani in dawo"
Yana kai nan ya juya ya fice, inna Asabe ta bi shi da kallo kan ta mayar da kallonta kan Inna
Larai dake zaune varender É—inta a yanzu ko tafiya bata iya yi, komai sai an yi mata ga yaran
nata kan su yi mata sai ran kowa ya ɓaci sun yi ta mita da kananun maganganu kenan, abinci
wannan tunda kawun ba wani ciyar dasu yake ba sai in Asaben ne taji tausayinta ta bata daga
wanda ta dafa a 'yar sana'ar da take yi na cikin gida.
Wa'azi taji a redio ranan da ya sakata zurfafa tunanin akan sharrin dake bibiyar 'ya'yensu gashi
dai sun haifa amma a yanzu babu ɗaya da za'a cire na ƙwarai, sai yanzu wani abu ke shiganta
akan neman ilimi barin ma da taji neman ilimin addini farilla ne kan kowani musulmi kuma baka
da hujjar kare kanka da rashin sani a wurin ubangiji muddin baka nemi ilimi ba, tunda ta san
lokacin da ake sa wa'azuzzukan sai ya zama kullum da hantsi sai ta ji anan ta fara tunanin daga
ina ne rayuwarsu ya kuskure tun farko...?
Shi dai Kawu Labaran machine ya hau har ya fito kauyen gaba da su ya samu mota da ya kawo
shi farkon garin Kaduna ya dire, nan ya tsaya zare ido tunda yake bai taɓa shigowa cikin
Kaduna ba bari dai kauyuka yana zuwa sossai musamman na bayansu amma bai taba zuwa
babban birni haka ba, zare ido yake tayi yana kalle-kalle wani mota ya tsaya kusa dashi wasu
maza huÉ—u ne ciki
"Ya dai ina ka nufa?"
"Na zo wurin 'yata ne tana nan cikin gari"
"Wani unguwa?"
"Ni dai ban tabbatar ba amma kaman unguwar masu kuÉ—i ne wai G....A...R"
Da kyar ya fadi alpabets É—in suka tuntsure da dariya
"GRA kake son cewa?"
"Yauwa eh nan fa dai..."
"Shigo"
Shiga yayi yana washe haƙora yau dai Allah ya nufa gashi a birni basu yi nisa ba ya ga duk sun
saka facemask kan yayi magana sun ja window suka fesa mishi wani powder nan ya sulale ya
sume...
****
Tsaye yake gaban madubi, wanka ya fito daga shi sai towel jikinshi, ginannen jikinshi fari tasss
sai daukar ido yake saboda ruwan dake bin murdaddun damatsanshi zuwa parks da ya tara a
ciki, madubi ya kurawa idanu yana tunanin irin yanayin da ya shiga a daren jiya wanda rabon da
ya ji kwatankwacin hakan sama da shekaru ashirin da biyar, da ƙarfi ya runtse idanunshi da
suka yi wani irin jajazir yana fesar da huci daga bakinshi tsaki ya ja a karo na babu adadi ya
miƙa hannu zai ɗauki mai kenan aka turo kofan aka shigo da sauri ya ɗago sai idanunshi suka
sauƙa kan....!
🖤Gureenjoh🖤
HAIHUWA DA HANJI
(A True life story)
Fatima Muhammad Gurin
(Gureenjoh)
Wattpad-Gureenjo6763
Arewabooks-Gureenjoh
ADABI WRITERS ASSOCIATION
*FREE BOOK*
*Alhamdulillah na gode sossai da adu'o'inku gare ni jiki da sauƙi sossai ku lallaɓa da wannan
kafin gobe na sake samun ƙarfin jikin, Allah ya bar ƙauna masu kira duk na gode sossai*
*36*
Ƙoƙarin buɗe idanun da suka yi mishi wani irin nauyi ya fara yana jin yadda fatar jikinshi ya
É—auki raÉ—aÉ—i tamkar wanda aka É—ora saman tukubar tsire, kaman ruwa haka tunanin abin da ya
faru ya kwararo mishi cikin kwakwalwa har bai san ya buÉ—e idanun ba tare da yunkura wa ya
zauna yana zaro su waje.
Wasu garadan matasa ne tsaye kusan su huÉ—u cikin É—akin daga kawunansu har kafafunsu a
rufe
"Su...su su waye ku?"
Kalaman suka fito fitt ba tare da ya shirya ba, babu wanda ya amsa sai chan bayan ya gama
zare ido yana jin cikinshi na É—urar ruwa kan É—aya ya matso ya ja wani kujera ya zauna tare da
riƙe haɓar kawu Labaran cikin hannunshi
"kai kalle ni nan! Nan ba wurin wasan ka bane idan ka yi abin da muka umurceka lafiya lau zaka
fita amma idan ka yi akasin hakan hahahahaa"
Ya saki wani dariyar bosawa
"za ka yabawa Aya zaƙin ta don ungulu muke bama jewar banza"
Wani irin kuuuuuuuuu cikin kawu ya bada ƙara jiki shi ya shiga rawa kar kar kar
"Me ku..ke so"
A rarrabe yayi maganan harshen shi har yana sarƙewa.
"Ba ni lambar yarinyar taka dake GRA!"
Ya faÉ—a yana zaro waya.
"Ba ni da shi wlh bani da shi..!"
Kawu ya basu amsa har lokacin jikinshi bai daina rawa ba.
Kallon kar ka raina min hankali yayi mishi kafin yayi wani yunkuri mutumin ya sauke mishi wasu
zafafan maruka da ya sa ya daina ji da gani na mintuna, wani ƙaraa yake ji suuuuu a cikin
kunnenshi da kyar ya iya jiyo zancen mutumin cikin hargagi
"Ni za ka rainawa wayau?? Ka manta abin da na gama ce maka ko? Toh kan in sauya
kamanninka maza maza ba ni layinta"
Kuka kawu ya fashe dashi da karfi bayan dawowa hayyacinshi yana rantse rantse babu irin
azabar da ba su mishi ba amma shi ya san bashi da wani Layin Afeefah, da kyar suka kyale shi
"Ka yi maza ka fara tunanin Layin nan in ba haka ba sai na tabbatar na sauya maka kamanni
yadda babu mai iya gane ka! Kuma zan saka flyer in tsige faratunka É—aya bayan É—aya kan in
jefawa kungiyar mu kai su san yadda za su yi da jini da tsokar ka don na faÉ—a maka idan ma
kana kokarin ɓoye kudinka ne za ka ba da jiki da jininka...."
Kawu bai san yana fitsari ba don tsabar tashin hankali, bilhakki yake kuka yana neman afuwa
sai da suka gama azabtar dashi suka juya suka fice suka bar shi nan yashe.
Bai san adadin lokutan da ya dauka cikin azaba ba, chan ya ji ana kwarara mishi ruwan sanyi a
razane ya farka
"Wlh zan...zan ba da Layin... Zan ba da layi"
Numbern su Larai ya bayar aka ƙira aka saka shi yin shiru.
"Yanzu haka mijinki na hannun mu muna bukatar kuÉ—i kimanin Naira Miliyon goma ko kuma ku
da ganinshi har gaban Abada..."
Salati ta kwarma da ya ja hankalin Inna Asabe da sauran yaran suka taho.
"Ke! Natsu!!"
Ya sake daka mata tsawa tuni ta shiga taitayinta ya miƙawa kawun waya a rikice cikin tashin
hankali yake cewa
"Larai ku taimakeni... Akwai kudi a ɗakina ƙasan gado ina da 'yar rami a ciki akwai tulu na binne
za ku samu kuÉ—i...ku..ku haÉ—a har da gonan gado na ku sayar da gidan da muke ciki ku basu
duk abinda suka roka don Allah...zasu kashe ni ku taimakeni" da kuka sossai ya ƙarasa.
Inna Larai manta halin da suke ciki tayi
"Au dama kana da wannan uban kuɗin ka ƙi kaini asibiti? Lallai ka cika azzalumi..."
"Ke kina da hankali kuwa?"
Ya ƙare maganan yana sanyawa kawu bindiga a makoshi wani irin ihu ya kwarma yana cewa
su taimake shi kar su kashe shi
"kun ji abin da yace ai ko? Toh idan kuna son shi ku aikata ku kawo mana kuÉ—in idan kuma
akasin haka za ku tsinci wasu sassa na jikinshi a cikin Ghana most go...kuka sake kuka sanar
da 'yan sanda dukkanku sunayen ku gawarwaki..."
Yana kai nan ya katse wayan suka fice suka bar kawu cikin halin ha'ula'i sai kuka yake wane
karamin yaro don bai taɓa zaton haka tashin hankalin kidnapping yake ba.
A chan kuwa Dutsen-wai tunani suka fara na yadda za su nemi masu sayan gona da gidan da
suke ciki, inna Asabe ta tafi ta É—auko kudaÉ—en da yake magana duka duka basu fi dubu dari
biyar ba a hakan ma mamaki suke na yadda ya iya boye irin kudin suna cikin talauci da wahala,
nan yaran suka tashi akan ba za'a sayar da komai ba idan kwananshi ne ya ƙare Allah ya ji
kanshi amma ba zai mutu ya bar su basu da komai ba idan ya mutu su yi yaya? Zazzafar kace-
nace ne ya barƙe har suka manta ma Ubansu na chan hannun 'yan sari.
Kwanan kawu É—aya a wurin ruwa kawai suke bashi duk ya firgice ya jeme ga yana dakuwa don
lillahi in suka tashi jibgar shi kaman buhun hatsi suka samu, a rana na biyun ne suka sake
dawowa sai dai duk kiran da zasu yiwa su inna Larai sun ƙi picking.
"Banza marar Amfani iyalan naka ma ba kaunar ka suke ba..."
Ya faɗa yana ball dashi ihu ya kwarma yana basu haƙuri inaa suka saɓe shi suna zura mishi
wani bakin kyalle a kai sai wani É—akin na daban, ko da suka buÉ—e mutane uku ya gani a tare da
shi zaune duk a jeme kawunansu kwal-kwal, shima aski aka yi mishi tal aka bashi wani riga mai
kaman dogon riga ya saka a kausashe waenda suke gadin wurin alamu sun fi waenchan zafi
suka ce
"Jininka ya halalta a yau zaka bakunci lahira..."
Bai san wanchan tashin hankalin da ya shiga mai sauki bane a yanzu ba zai iya fasalta halin da
yake ciki ba barin ma da mutanen da ya samu suka ce mishi tunda har sun furta zai mutu yau
sai ya mutu basa magana biyu, yankashi zasu yi su ba dodo jinin shi naman kuma suyi romo su
cinye don matsafa ne wani irin zawo ya barƙe dashi tsabar kaɗuwa ya gigice sai haƙuri yake
basu kuka kam har ya rasa hawaye amma sun ƙi kula shi a gigice yake cewa
"Yanzu na san asalin tsafi...ashe Afeefah babu abin da kike yi? Na shiga uku wayyo Allah!
Afeefah baki isa yin irin wannan ba...wannan ya fi karfin tunaninki...Na shiga uku na lalace
wayyo Allah na..."
Kuka bilhakki yake yana kiran sunan Afeefah a gigice don dai gashi nan da layun kariya daga
mayun ya fito daga gida incase mijin ma maye ne kar su cinye shi sai gashi yana kallon asalin
maita, suna shirin cinye shi banzar layunshi sun kasa mishi anfani, bai san adadin kuka da
magiya da yayi tayi ba babu sunan wanda bai kira ba har aka zo aka sake fita dashi zuwa É—akin
tsafin nan ya ƙara firgita ganin wasu irin halittun dodanni ga wasu masu jajayen kaya da baƙake
marasa imani jibga-jibga sai muzurai suke suna ganinshi kaman sun ga nama ko kuma ya ce
naman ma suka gani, yana tirjewa yana tsandara karar a taimakeshi amma chadak suka É—aga
shi kaman kayan wanki har gaban shugabansu.
A tsaye yake amma suna haÉ—a idanu bai san ya zube ba.
"Ka taimakeni ka ji kaina wlh ni maraya ne, ba ni da kowa iyalina ma basu da kowa bayan ni kar
ku kashe ni, kar ku sha jinina na tuba...!"
Har a ranshi magiya yake yana kuka da majina dariya suka sheke dashi wata murya dake fita
bibbiyu ya daka mishi tsawa...
"Yi mana shiru!! Ka riga ka shigo nan babu fita ka sa a ranka za ka bakunci lahira a yau jininka
kuwa zai zama abin sha mafi gardi ga shugabanmu a wannan dare yayin da za mu kashe dare
cikin party da namarka..."
Suuuuu haka kawu ya sume sai dai duk yadda zai sume baya seconds zai farka da karfin tsafi...
A haka aka ɗauke shi zuwa gaban wani tukunya dake bararraka da baƙin abu aka zaro wata
shirgegiyar wuƙa dake sheƙi aka ɗora mishi a wuya, ya gigice! Ya ruɗe! Ya fice daga cikin
hayyacinshi! Zuciyarshi kiris ta rage ta fita daga madaukarta, kashi da fitsari kam bai san adadin
da yayi ba barin ma da ya ga da gaske mutuwar zai yi...
****
"Mommy...! Mommy...!!!"
Da ƙarfi yake kwala kiran sunan yana zagaye gidan don jinshi yake kaman zai yi hauka idan bai
sanya mahaifiyar tashi a idanu ba sai dai yana buÉ—e É—akin mommy gaje ya gani zaune tana ma
cin nama ne soyayye a plate.
"Ina mommy?"
Shiru tayi daidai Yaya ya fito shima daga É—akin da ya san dai na Sadiqa ne.
"Ina 'yan uwana? Ina mahaifiyata?"
Ya yi maganan da ƙarfin gaske da ya sa suka zabura suna dawowa hayyacinsu ganin yadda ya
zama lokaci guda Yaya ya dafa shi
"ka natsu mana Saleem, mu ma ai iyayenka ne tunda iyayen matarka ne ka manta kai ka fitar
da su mahaifiyar taka daga gidan nan ka ce mu dawo mu zauna tare?"
Wani irin riƙe kanshi yayi dake flashing mishi duk abubuwan da suka faru tun daga auren
Sabrina, ji yake kaman zai yi hauka da kyar ya fara ambaton
"Innalillahi wainna ilaihi rajiun! Hasbunallahu wani'imal wakeel...!"
Kai tsaye gaban Sabrina da jikinta ke rawa ya ƙarasa yayi mata wani irin mugun riƙo da tana
tunanin kila hannunta ya karye a tsawace yace
"Me kika min? Me kika aikata min!!"
Yadda yake zazzaro idanunshi da suka zama Red ya sa ta sake firgita.
"Saleem me za ta yi maka k...."
"Shuttt up!! Ku yi min shiru a yau na rantse da Allah sai kun faÉ—a min me kuka yi min? Me kuka
yi min da ya sa na zaɓe ku kan uwata da 'yan uwana??"
Sabrina zata yi magana yayi wurgi da ita har ta bugi kujera tana zubewa ƙasa, kofan parlorn
yaje ya rufe da key ya koma da hanzari ya rufe na baya ya zo ya haura É—akinshi kaman zararre
ya samo belt ya sauƙo da gudu ya rufeta da duka yana ihun tambayar me ta mishi me suka
mishi? Don ko jikinshi kunnuwa ne ba zai yarda da gangan yayi duk abin da yayi ba ta gigice
duk inda zata gudu ta ɓuya ta gudu amma sai ya fusgota yana dukan yana tuna irin dukan da
yayiwa Sadiqa, babanta da mamanta suka makure wuri guda suna kallon yadda yake jibgar 'yar
su idan tayi wurinsu da gudu suma sai su runtuma kar bulala ya same su da ta ga no go ta fara
ihun
"ba ni ce nayi ba wallahi su ne... Su gaje ne su suka yi komai su suke karɓo magani wurin
bokaye muka mallake ka wlh su ne...."
Dakatawa yayi yana kallonsu
"Me take cewa?"
Duk ya haukace tsoro ya rufe su, bindiga ya zaro
"Ko ku faÉ—a min me nayi muku da kuka zalunceni ko kuma dukkanku in kashe ku... Me na
muku???"
Da wani irin tsawa yayi maganan duk suna zube a ƙasa a gigice don yadda yaken nan tsaff sai
ya harbe su, a darare Yaya ya fara cewa
"Kayi haƙuri Don Allah ka yi haƙuri.."
Gini ya harba karar bindigar ya saka Yaya fitsari Sabrina da Gaje suka tafi a sume, ruwa ya
kwaso ya zo ya kwarara musu yana nuna gini
"Kun ga yadda ginin nan ya fashe ko? Toh billahi ko ku faÉ—a min ko in fashe kawunanku haka"
"ka saurareni ka yi hakuri zan faÉ—a wlh zan fada maka..! Mahaifiyarka da ni mun kasance 'yan
uba tun da muka tashi iyayenmu mata ke nuna mana ba É—aya muke ba, hakan yasa muka tashi
da wani irin ƙin juna a zuciya, sai kuma Allah ya daukaka Hussaina hakan ya ƙara mini hassada
da kyashinta barin ma da muka rasa iyaye bata daukeni dan uwa kuma abokin shawarar ta ba,
bata kula ni ko 'ya'yana sai in bukatarta ne ya kawo ta wurin mu, ta daukeni tamkar É—an gidanta
bata girmamani babu ruwanta da kyautata mini tana nuna min itama wahalar ta ya sama mata
in tashi in nema anan na ƙudiri aniyar mayar da dukiyar ta nawa, mun yi shige shige dayawa a
baya kasancewar kana yawan zuwa duk ruwan da za mu baka akwai wani asiri ciki sai dai duk
basa kama ka saboda kana neman kariya kuma kana Adu'a, har ma mun fitar da ran samunka
muke tura yarinyar mu nema mana kuÉ—i da surarta don muna so itama ta auri mai kuÉ—i mu
kerewa Hussaina(Mommy) sai kwatsam ta dawo da son zuciyarta garemu... Mun yi amfani da
hakan Allah kuma ya bamu dama saboda ba don Allah ta neme mu ba muka juye ka ka zama
sai abin da Sabrina ta ce..."
Hawaye ne ke sauka mishi a haukace yace
"Ni na zama kwallonku kenan?? Ni ne da nake tausaya muku nake taimakonku daidai
gwargwado kuka zaɓi salwantarwa da tura ni cikin fushin ubangiji??"
"Kayi hakuri don Allah! Ka yi hakuri..."
"Ku tashi ku fita a gidan nan har abada kar ku bari fuskata ta kalli naku... Duk ranar da hakan ta
kasance sai na sa bindigata na harbe ku ku fita nace!!!"
A gigice suka miƙe suna ji suna gani suka fita da kayan jikinsu kawai don ko cokali ya hana su
É—auka duk tatsarshi da suka dinga yi na kuÉ—i suna boyewa duk yana cikin gidan, ko takalmi
babu kafafunsu haka suka fita rike da Sabrina da ta sauya kamanni tana ta kuka barin ma da ya
furta ya sake ta saki biyu ta je ta ƙarata..
(Ƙarshen alewa ƙasa!)
Su mommy suna zaune suna kallon sunna Tv da ake hasko wa'azin likitan zuciya wato sheikh
tijjani Ahmad yusuf guruntum kawai suka ga an turo kofa an shigo, a razane suka miƙe tsaye
sai ganin Saleem suka yi yana tahowa yana haÉ—a hanya a rikice mommy ta nufe shi
"Saleem..! Saleem...!! Kai ne? Kai ne da gaske.."
Taro shi tayi ganin zai faÉ—i yana furta
"Mo..myy"
Sai ya sume musu..
🖤Gureenjoh🖤
HAIHUWA DA HANJI
(A True life story)
Fatima Muhammad Gurin
(Gureenjoh)
Wattpad-Gureenjo6763
Arewabooks-Gureenjoh
ADABI WRITERS ASSOCIATION
*FREE BOOK*
*37*
Bayan ta tashi daga baccin da ya dauƙeta tun bayan Sallar asuba wanka tayi ta shirya cikin
wata doguwar riga mai hannun roba purple da ya amsheta ta É—aura dankwalin a kanta sai ta
nufi sashen mammi don gaisheta, da sallama ta sanya kanta ciki ta ga mammin kwance a kan
sallayar da tayi sallah ta É—ora kanta saman pillow tasbihi take a hankali tana ta maimaita
"Allahumma inni As'aluka husnal khatima, Allahummar ruzuƙnee taubatan nasuha qablal maut,
Allahumma ya musalibbal quluub thabbit qalby ala dinika, ya musarrafar quluub sarraf
quluubina ala É—a'atik..!"
Abin da ta lura kusan kullum a kwanakin ya zama tasbihin Mammi kenan, a ganganta ta zauna
"Mammi...kina lafiya?"
Tayi tambayar hankalinta na kan mammin gabaÉ—aya ganin yanayinta kaman marar lafiya
lumshe idanu mammin tayi ta buÉ—e kan ta ce a hankali
"Afeefah je ki buÉ—e bedside za ki ga wani kwali ki É—auko"
Miƙewa tayi taje ta buɗe ta ɗauko ta dawo tana zama riƙe dashi
"Mammi gashinan!"
Mammin bata motsa daga kwancen ba don bata jin zata iya tashi tace a hankali
"Afeefah ki buÉ—e ki gani menene ciki?"
BuÉ—ewa tayi sai ta ga set ne na dankunne sarka da abin hannu da kuma zobe, daga gani ka
san ba ƙarami bane don ma bata san gold ba da sai ta ce wannan ɗin gold ne babba ma don
yadda yayi wani irin kyau ga É—aukar ido.
"Set na sarka ne Mammi"
"Masha Allah, sadakinki kenan da na yi amfani dashi na saya miki wannan kadarar, ki riƙe a
wurin ki naki ne halak malak ban baki tsabar kudin bane don na san ba zai ajiyu ba amma
wannan ko shekara nawa zai yi a zaune babu abin da zai yi sai ma darajar shi ya ninku"
Rasa bakin godiya Afeefah tayi sai hawaye ya shiga ziraro mata
"Mammi kin yi min komai a wannan duniyar ba ni da abin da zan saka miki face Adu'ar Allah
ubangiji ya baki lafiya, Allah ya yaye miki wannan ciwo ya kawo mana karshensa mu ga kema
kin warke kaman kowa, Allah ya sa kaffara kika yi"
"Ai lafiyar ta zo ma Afeefah"
Ta faÉ—a tana rufe idanu jin yadda take jin ciwo mai tsanani a ciki da ma jikinta gabaÉ—aya.
"Mammi...!"
Sai ta ga wani irin zufa na karyo mata numfashinta na fita da kyar da kyar har chasbin hannunta
na zamewa da kanshi, wani irin tashin hankali ne ya ziyarce ta da gudu ta miƙe ta fito sai tayi
side É—insu kaman za ta kifa haka ta tura kofan ta same shi tsaye gaban madubi, ba zata ce ga
yadda ta riske shi ba ita dai ta san ta isa gabanshi tare da riƙe hannunshi
"Mammi...! Mammi.."
"Me ya sameta?"
Ya faÉ—a hankalinshi na tashi lokaci É—aya, ganin duk ta ruÉ—e yace
"Je ina zuwa"
Fita tayi da sauri shi kuwa ya É—auki boxers kawai ya saka da jallabiya tare da zaran keyn mota
kafafunshi ma silifas ce ta wanka ya fice da hanzari, yanayin da ya sameta sai da ya ƙara ɗaga
masa hankali haka ya É—auketa Afeefah na ta kuka suka nufi Asibiti duk ma'aikatan hankalinsu
ya tashi da sauri aka karɓeta sai oxygen aka sanya mata sun yi iya kokarinsu har numfashinta
ya É—an daidaitu, Rayyan dai ya kasa aikata komai don ba karamin girgiza yayi ba duk tashin
ciwonta bai taɓa ganin kaman wannan ba, bai zaci za su iso asibitin da ranta ba jikinshi rawa
kawai yake yana tsaye daga gefe yana kallonsu a sadda zuciyarshi ke cigaba da bugawa
kaman zai fashe, idanunshi sun rine sai adu'a yake yana roƙon Allah akan ya bata sauƙi a
ranshi.
Ganin ta dawo daidai oxygen É—in na tafiya a hankali ba kaman daga farko ba da in ta ja kaman
ba zata sauƙe ba ya isa gangarta ya riƙe hannunta kawai ya zauna, a jikin gadon ya ɗaura
kanshi yana danne abinda yake ji na taso mishi, ina ma da zai iya kuka da yayi ko don samun
sassaucin abinda yake ji a ranshi da ma kwakwalwanshi!
Ba zai ce ga adadin lokutan da ya É—auka zaune a wurin cikin wannan yanayi ba chan dai ya ji
kaman ana shafa suman kanshi da É—an hanzari ya É—ago sai suka haÉ—a idanu tana ta kallonshi,
gyara zama yayi yana kirkiro murmushi mai nauyi ya ce
"Mammi na! Kin farka? Ya jikin?"
Ta sake yin murmushi a hankali ta nuna mishi oxygen na hancinta sai ya cire yana jin yadda
take sauke numfashi a kai akai
"Mammi ki yi saving energy É—inki kar ki yi magana kin ji?"
Ta sake yin murmushi
"Ina so na ji abin da ke bakin ka! Ka ba ni labari...tun jiya na lura kana son min magana amma
kana riƙe wa menene?"
Shiru ya É—an yi
"Speak up Saraki, yanzu ne kake da lokacin magana da ni anjima kaÉ—an kila sai dai matarka ko
'yan uwanka"
Da sauri ya ɗan kalleta tana ta murmushi, kanshi ya duƙar a hankali ya fara furta
"Mammi ki daina irin wannan maganan don Allah"
"Toh na daina Saraki!"
Ta faɗa tana lumshe ido, hannunshi dake cikin nata ne ya ƙara yin sanyi she can feel the
nervousness a cikin tafin hannunshi zata iya cewa yana cikin yanayi ne marar fasaltuwa sai dai
da yake namiji ne kuma jarumi yana iya shanye damuwarshi kaman babu komai.
Idan Mammi ta tafi ba tare da ya sanar da ita menene a ƙasan Ranshi ba tabbas zai yi nadama
mai girma, tunaninsa ya dinga rarrabuwa har yana jin kaman zai zauce idan ya cigaba da
zurfafa a cikin muguwar tafiyar rayuwarshi...iya tunanin kaÉ—ai kan karya duk wani guntun
karsashinsa.
*****
A hankali yake buÉ—e idanunshi har ya ware su akan Mommy da su Sadiqa dake zaune a É—akin
jugum jugum.
"Saleem! Ka farka? Sannu ko mu je asibiti ne?"
Girgiza kai yayi yana Miƙewa zaune jikin gadon ya kalli mommy da ita ma take kallonshi a
hankali yace
"Mommy na tuba! Mommy ki yafe min wallahi...."
"Shhhh Saleem na sani, na san ba da saninka ka aikata hakan ba na san baka cikin hankalinka
a lokacin da komai ke faruwa, laifina ne wlh laifina ne ka yafe min Saleem son zuciya ɓacinta,
hakika na yi amfani da son zuciyata wurin É—aiÉ—aita maka rayuwa don Allah ka gafarceni"
Ta roka yafiyarshi tana kuka su ma duk su sadika suka shiga bashi hakuri, anan ya zauna yana
jin yadda komai ya kasance... Hakika mommy ta yi kuskure Afeefah ce ta faÉ—o mishi a rai ko
tana cikin wani hali yanzu? Ko ya rayuwa yayi da ita? Allah masani
******
"Mammi..!"
Ya sake ƙira a karo na biyu ba tare da ta buɗe ido ba tace
"Uhmm"
"Zan faÉ—a miki ne, zan faÉ—a miki wanene ni..."
Da sauri ta buÉ—e ido ta kalleshi cikin yanayin jin jiki ta zura mishi idanun a hankali ya cigaba da
cewa
"Ban manta komai ba, na ƙi faɗa ne saboda wacce daraja da ƙimarta suka zama ƙololuwa a
gare ni ta yi fatali da hakan ta É—auke ni ta yasar tamkar tsumma a cikin al'ummar da ba ni da
masaniyar yaya suke bare ya rayuwarsu take, ya al'adarsu take ko ya imaninsu yake, ba tare
da ta damu da zan ci ko bazan ci ba, shin rayuwata za ta inganta ko za ta yi lalacewa marar
iyaka? kafin na haÉ—u da ke na zaci uwa masifa ce ga 'ya'yanta ta kan nesanta su da farin ciki ta
saya musu wahala, ta kan zama tamkar ginin ƙasa da muddin ɗa ya jingina da ita sai ya faɗi, a
maimakon ta kasance garkuwata sai ta zama ita ce a farkon cutar da rayuwata, na kasance a
koyaushe bana rufe idanu na buÉ—e ba tare da na ga sadda take cire hannayenta daga cikin
nawa ba tare da tura ni cikin dattin juji...ta tafi! Ta tafi da rayuwata da dukkan farin cikin da ya
taɓa wanzuwa cikinsa ta tafi da rai da ruhi na..."
Shiru yayi yana cije lip ɗin shi na ƙasa da har su ma rawa suke yi.
"Ke ce kika ba ni hope na rayuwa, a kan ki na yarda uwayen ma suna suka tara Mammi kin
zame min gata a sadda na kasance cikin wahala, kin ba ni duk wani kulawa da gata ba tare da
tsammanin lada ba kin bani kaunar da bata taɓa yankewa ba, kin zame min rayuwa, rahama da
kyautatawa da bata da iyaka. Mammi Sunana Sameer..."
Lumshe ido tayi a hankali hawaye na sauka mata ya sa hannu ya share mata.
A hankali ya cigaba da bata labarin da kafin ya gama jijiyoyin kanshi sun yi raÉ—a-raÉ—a, idanunshi
tamkar garwashi muryarshi har yankewa yake amma Dukda haka jarumtarshi ta ƙi barin ruwan
hawaye ko guda ya diga bisa fuskar shi ko zai samu salama cikin rai da ruhinshi, ba zata iya
Miƙewa ba da zata iya da ta rungumeshi ta rarrasheshi da ta nuna mishi komai na duniya mai
wucewa ne, da ta tuna mishi da irin girma da darajar da Allah ya ba uwa don kalamanshi sun yi
tsauri sossai a kanta, bata san dalilin ta na yin hakan ba amma ta san babu uwar da zata so
tagayyarar É—an ta, É—an ma mai tarin gata, daraja da martaba irin Rayyan.
"Ka zama mai haƙuri da rayuwa! Ka zama mai afuwa Saraki haƙiƙa an cuce ka an kuma ɗauki
alhakinka mai yawan gaske amma ina roƙon ka da ka bari komai ya wuce kaman ba'a yi ba, ka
yi uzuri ga mahaifiyarka ka waiwayi gida..."
Shiru tayi sai ta ɗan yunkura kaman zata tashi ta koma ta kwanta tana shaƙuwa.
"Ka min alƙawari Rayyan!"
Girgiza kai yayi yana É—ago rinannun idanunshi gareta sai ya ji tana ambaton Allah da salati
ɗauke a Bakinta a kan idanunshi, hannunta na a cikin nashi Mammi ta ja numfashinta na ƙarshe
da ya tafi da duk wani ƙwarin gwiwanshi, ya tafi da duk wani haske da yake tunanin da shi yake
amfani wurin haskaka tarin duhun dake mamaye da shi, gigice wa ya nemi yi sai ya manta da
cewa shi É—in ma likita ne, ya kasa yanke hukuncin cewa ta tafi ya kasa yardar wa kanshi cewa
da gaske ta tafi ta bar shi...
"Innalillahi wainna ilaihi rajiun..."
Shine kalaman da ya fito da kyar ya ratsa harshenshi har ya fita sarari.
Ya fi mintuna ashirin a zaune a haka baya iya ko da kifta idanun kirki, kila mafarki yake, kila
bacci tayi za ta buÉ—e idanu kila zai iya ganin kirjinta ya motsa ya cigaba da bugawa kila za ta ja
numfashi ta ce mishi wasa take... Shigowar wani likitan ne ya tabbatar mishi da cewa da gaske
ya rasa Mammi rasawa ta har abada haƙiƙa ɗaci da raɗaɗin mutuwa ba za su faɗu ba ba kuma
za su misaltu ba.
A chan reception kuwa Su jannah da Afeefah ne zaune cikin damuwa mai yawa don tunda suka
shigo Afeefah bata daina zubar da kwallah ba, ta san mutuwa kuma ta ga mutuwa daban daban
bata fata ya kasance a kan Mammi nan kusa Dukda ta san da cewa mutuwar dole ce ga dukkan
mai rai, su uncle Musa da iyalan shi da Abeeha ta ƙira ta sanar musu jikin Mammi babu daaɗi
duk suna cikin asibitin a lokacin da wannan likita ya fito ya sanar musu da rasuwar gigice wa
suka yi suka fice daga hayyacinsu, Jannah ce ta yanke jiki ta faÉ—i sai jini ya fara fita mata
Abeeha kam rasa ma ya zata yi tayi sai da uncle Sanusi ya riƙo ta yana ta maimaita salati ta
kankanmeshi ta fara kuka mai tsuma zuciya shikenan sun zama marayu babu uwa babu uba,
Mammi ta tafi lallai dukkan mai rai mamaci ne.
Afeefah kam ba zata ce ga yanayin da take ciki ba, Dukda ta kaÉ—u iya kaÉ—uwa sai dai ko motsi
ta kasa yi daga inda take hawayen idanunta ma kafewa suka yi, wata cousin É—in su Abeehar ce
ta riƙe mata hannu sai ta firgita tana kallonta idanunta duk a waje...
"Wai cewa suke Mammi ta rasu? Ko kunnuwana ne basu ji da kyau ba?"
"Sai haƙuri Afeefah, sai haƙuri..."
Wasu irin hawaye ne suka shiga zubo mata masu zafi da raÉ—aÉ—i, da kyar take iya maimaita
innalillahi wainna ilaihi rajiun....
A lokacin Rayyan ya fito hannunshi na tura gadon da mammin take kai a hankali yana tafiya ne
ba tare da ya san inda yake jefa kafafunshi ba, Uncle Sanusi ne da matarshi suka taho da sauri
suka saka mishi hannu don kaman zai kifa, idanunshi sun zama wani iri jikinshi na rawa
zuciyarshi a bushe haka suka fice yana gaban motar da Mammi ke ciki wacce amblance ce aka
dauko ta a baya har cikin gida, a É—akinta aka sanyata babu wani jinkiri Matar uncle Musa
dattijuwar malama da taimakon wasu malamai mata aka yi mata wanka aka yi mata sutura, kan
kace mene gidan ya dinke da mutane masu kuka na yi masu yabon kyaun halinta na yi, Jannah
dai tana asibiti don ɓari tayi ba tare da ta sani ba.
Abeeha da Afeefah banda kuka da du'a babu abinda suke yayinda Rayyan na a parlorn shi a
zaune wane mutum-mutumi tasbihi yake yi amma ba zai iya cewa ga abin da yake cewa a ciki
ba, Saleem ne ya shigo Dukda ba ƙarfin jiki ya samu ba sai dai labarin mutuwar ya dugunzuma
hankalinshi.
"Rayyan!"
Ya kira sunan.
Jajayen idanunshi ya buÉ—e ya zura mishi ba tare da yayi magana ba
"Sannu! Allah ya gafartawa Mammi Allah ya haskaka makwancinta ya sadata da annabin
rahama"
Da kyar ya iya furta
"Ameen"
Idanunshi na kan hawayen da Saleem É—in ke yi ina ma zai iya? Ina ma ya san ta yadda zai
nemo hawayen? Ina ma zai iya cire zuciyarshi ya yasar? Da yayi hakan ko zai huta raÉ—aÉ—in da
ke gasata wane wuta.
"An gama shirya ta ayi alwala a fita gabatar da sallah don samu a kaita makwancinta!"
Wannan kalma ta Uncle Mansur ya zama kaman zuban wuta a jikinshi, shikenan fa yanzu ko?
Shikenan zai rabu da Mammi rabuwa ta har abada? Saleem ne ya ja hannunshi har zuwa bayi
yayi alwala suka fito a tare zuwa É—akin Mammi aka É—ago makarar aka nufi fita da ita haraba
inda kuka ke tashi, kowa idanunshi na kan Rayyan ne da yake ta focusing akan hanyar da yake
takawa kar ya faɗi riƙe da gawar Mammi da yayi mata sallama na ƙarshe da qulhuwallahu ahad!
A tare da shi aka yi mata Sallah aka kaita makwancinta na gaskiya, shine ya ba da ghdumuwa
wurin sakata a rami kuma shi ne ya fara zuba mata ƙasa kan yayi baya baya zai faɗi aka tare
shi su Uncle Mansur ne da Saleem, É—agowa yayi yana kallonsu kila su basa jin abinda yake ji
tunda gashi suna hawaye! Har aka gama binne Mammi aka kamo Rayyan zuwa mota baya
gane fari ko baƙi don duk wanda zai ji mutuwar Mammi a bayan Rayyan ne.... Innalillahi wainna
ilaihi rajiun ðŸ˜
Allah ka sa mu yi kyakyawar karshe!
🖤Gureenjoh🖤
HAIHUWA DA HANJI
(A True life story)
Fatima Muhammad Gurin
(Gureenjoh)
Wattpad-Gureenjo6763
Arewabooks-Gureenjoh
ADABI WRITERS ASSOCIATION
*FREE BOOK*
*38*
"Dakata!!"
Wata murya mai amo tayi maganan.
Chakk suka tsaya daga ɗora wukan a maƙogoron kawun.
"Mecece alaƙarshi da ƙungiya?"
Yayi tambayar a kausashe.
"Babu mai girma shugaba"
"Ku kyaleshi jinin shi bai halalta mana ba"
Suman daaÉ—i ne ya tafi da kawu Dukda azabar da yake ciki, dunkule shi suka yi suka tura cikin
buhu aka saɓe shi kaman kayan wanki aka fitar sai haushi suke ji bai musu amfani ba tsabar
lalacewarshi, a booth na mota aka saka shi sai da suka yi tafiya mai uban nisa kan suka buÉ—e
booth ɗin suka cilla shi ƙasa suka yi tafiyarsu.
Ya fi awa nawa yana mutsu-mutsu ga zafin rana Allah ya kawo wani mai ruwa ya taimake shi ya
buÉ—e buhun sai ya fara tari da mayar da numfashi sama sama, da kyar yake ambatar
"Ruwa! Ruwa!!"
Mai ruwan ya bashi ruwa a gora ya sha sossai yana sauke numfashi kan ya fara kalle kallen
wurin da yake, wani kauye ne na daban
"Me ya saka ka cikin buhu bawan Allah?"
"Sace ni aka yi 'yan yankan kai ne suka sace ni Allah ya kubutar da ni"
Abin mamaki ya É—auke shi har gidan mai garin garin suna da karamci aka bashi wuri yayi wanka
ya wanke najasar jikinshi ya rama sallaolin da suka hau kanshi, har abinci ya ci aka ba shi kuÉ—in
mota ya nufi Dutsen-wai cikin zuciyarshi saƙe-saƙe ne mai yawan gaske ga bakin cikin abin da
su larai suka yi mishi ga yadda ya sha jinin jikinshi da abin da ya riska a kwanakin wanda har
abada ba zai taɓa mantawa ba, yana isa Dutsen-wai gidan mai gari ya nufa yana neman iso
aka mishi iso ya ce
"Toh dama na zo ne in sanar kuma in nemi a gargaÉ—i duk jama'ar garin nan cewa duk wanda ya
sake cewa ÆŠiyata Afeefah Mayya sai mun yi shari'a har kotun koli don Afeefah ba Mayya ba ce,
ita kuma ba Annoba ba ce"
"Toh fa da kanka Malam Labaran? Kana lafiya kuwa?"
"Lafiyata ƙalau kawai dai na san Afeefah ba Mayya ba ce kuma kar a sake ce mata haka don
abin da Mayu suke yi ko a mafarki ba zata iya ba wannan abu ne da ya shallake dukkan tunanin
mai tunani."
Ya ƙarasa cikin tabbatarwa da jimami.
"Dama tun farko tsantsar jahilci da son zuciya ya sa kuka lakaba mata abinda ba shine ba, ashe
kenan mutum ba zai taɓa mutuwa haka siddan ba? Har fa tambari kuka buga na cewar tun tana
ciki ta cinye É—an uwanka amma Alhamdulillah tunda ka gane gaskiya kuma kana shirin tsayawa
a kanta sai ka yi wa kanka faÉ—a ka nemi tsari da jahilci don wallahi mugun ciwo ne kuma shi ke
ɗawainiya da mafi yawanku cikin wannan ƙauye".
Malam liman ne ya jero wannan jawabin, kawu ya gamsu har ya ji jikinshi na É—an sanyi barin ma
da malam liman ya sake nusar dashi akan Allah shi ba ruwanshi, da ya turo mu duniya yayi
mana umarnin mu nemi sani a kanshi kafin mu bauta mishi, ba ka da hujjar kare kanka da
rashin sani a wurin Ubangiji matukar baka tashi ka nema ba.
kan ya dawo gida labarin dawowarshi ya riske su bai damu da zancen mutane ba da wasu ke
cewa kila ta cika shi da kuÉ—i ne wasu na zaton ko don ta auri mai kuÉ—i yanzu ai dole ya ja ta jiki.
Shi kuwa hankalinshi ya fi tafiya ga jan hankalin da liman yayi mishi na neman ilimi Dukda a
yanzu wani tataburzun ne gabanshi don saurin da yake zabgawa yana so ya tabbatar babu
kowa ne a gidanshi kafin faÉ—uwar rana.
Kaman daga sama suka ganshi ya faÉ—o Asabe murfin tukunya ce a hannunta sai da ya subuce
ya faɗi ƙasa ya tsaya kyamm yana kallonsu
"Toh ban mutu ba! Kuma dama an ce sai abu ya same ka kake sanin masu sonka ashe
dukkanku maƙiyana ne na tara? Ashe za ku iya bari na in mutu? Toh an gama wallahi gwara in
zauna ni kaÉ—ai na da in cigaba da zama da ku don haka kowaccenku ta tattara ya nata ya nata
ta bar min gida na sake ku saki É—aiÉ—ai..."
"Innalillahi wainna ilaihi rajiun Malam ka tsaya ka saura..."
Ya katse ta da masifa
"Babu abin da zan saurara Asabe! dole ku bar min gida a yau ba sai anjima ba kuma ku tattaro
yaranku kaf ku fice min daga gida a tabbatar kuma an dawo min da kudade na mugayen banza
mugayen wofi"
Sai masifa yake ko ya tsaya ya saurare su abin ya mishi zafi rigima fa sossai ya kachame don
suma sun ce in zasu tafi ba zasu tafi da yara ba tunda ba da su suka zo a kullin gararsu ba ko
hutawa bai yi ba aka sake komawa gaban manya ya rantse shi ya sake su su tafi kuma baya
bukatar ko wani É—a don za su iya saka wuyanshi gabas su yanka tunda suka iya watsar da
rayuwarshi alhali yana chan cikin tsaka mai wuya.
"Labaran!"
Malam liman ya kira shi ya amsa
"ka san ko ma menene suka yi laifinka ne?"
"Ta yaya? Ina fa chan gaban azzalumai mutanen nan don basu da imani suka ƙi daukar waya
alhali ga abin da nace su yi da kuÉ—ina ba nasu ba su kubutar da ni, ba don Allah na so na da
sauran numfashi ba da na jima da mutuwa yanzu zaman makoki ake"
"Labaran ka yarda kaso mai girma na abin da ya faru laifinka ne"
"shiyasa na ce ina so in ji ta yaya?"
*****
A ɓangaren Rayyan ba zai ce ga yadda yinin ya kasance mishi ba don baya gane komai, kawai
yana so ya ji an daina ko magana a gangarshi ya ji shiru na ratsawa don ya samu damar
gamsar da kanshi cewa da gaske ya rasa mace É—aya jal mafi muhimmanci a rayuwarshi, wacce
ta cire shi daga wahala ta bashi so da kauna ta raine shi fiye da yadda ta raini 'ya'yan da ta
haifa da cikinta, ko gaisuwa aka mishi sai dai ya gyaÉ—a kai don baya magana, idanunshi har
tsoro yake ba wa wasu idan ya buÉ—e, An yi an yi ya ci wani abu tun safen har dare ko ruwa bai
yarda ya sha ba don raÉ—aÉ—in da yake ji daga zuciyarshi har akan harshen shi baya tunanin zai
iya cin wani abin don cikin nashi ma jinshi yake a cushe, ganin yana shirin yi wa kanshi illa ya
sa Sulaiman yi mishi allurar bacci don daga ƙarshe numfashi wahalar fita ya fara mishi.
Su basa yarda da wani zaman makoki daga yinin da aka binnetan duk na waje suka watse,
Afeefah tsabar yadda ta kasa yarda cewa Mammi ta tafi a É—aki ta cigaba da zama hakan ya
mata hijabi da haduwa da mutane dayawa ciki har da su mommy da Saleem, don Saleem yayi
niyyan kwana a tare da Rayyan mommy ta sanar dashi yayi aure ai, ya shiga tsantsar mamaki
ya kuma ji babu daaÉ—i a lokaci guda, yana mamakin yadda Rayyan yayi aure cikin kankanin
lokaci alhali shi bai taɓa ji Rayyan ya furta sunan wata macen a matsayin buduruwa ba, ya
kuma ji ba daaÉ—i yadda bai kasance tare dashi a bikin ba amma ya mishi Fatan alkhairi ya É—auki
su mommy suka koma gida don har yanzu a tsohon gidansu suke har shi, ya ce ba zasu koma
chan inda ya zauna da Sabrina ba wani zai saya musu don bai san me suka binne ciki ba.
sai dare ta fito ta nufi É—akin Abeeha dake kwance rib da zazzabi, a gangarta ta zauna tare da
rike hannunta
"Afeefah da gaske Mammi ta tafi ko? Idan na je É—akinta ba zan ganta ba ko? Yanzu shikenan
ba mu da uwa ba mu da uba?"
Ta danne hawayen da ke shirin ziraro mata tace
"Haka Allah yake lamarinshi Adda Abeeha, dukkan mu da muke rayuwa a yanzu kwananmu ne
bai kare ba idan ya ƙare dole za mu tafi"
"ba za ki gane raÉ—adin da nake ji ba Afeefah"
Ta girgiza kai
"Duk wanda za ki ji Adda Abeeha na ji shi, kar ki manta ko da aka haifeni ba ni da uba, ban
kuma buÉ—i ido na tarar da mahaifiyata ba sai a hoto kin ga ko zafi da raÉ—aÉ—in maraici na fara
dandana, shi ne tun a cikin cikin mahaifiyata har zuwa zanin goyona. Adda Abeeha ku gode
Allah kun rayu da iyayenku har girman ku..."
Kuka ne ke shirin kwace mata amma ta dake ta danne.
"Don Allah ki daure ki daina yi wa Mammi kuka haka! Mu bita da Adu'a shi ta fi buƙata a halin
yanzu"
Matar uncle Sanusi dake É—akin tace
"maganar Afeefah gaskiya ce Mahaifiyarku Adu'a take buƙata Abeeha ba kuka ba ita ai tata ta
yi kyau! Allah ya sa jinyar da ta sha ya zama kankarar zunubanta ne"
Suka amsa da Ameen.
"Mommy ya Adda Jannah?"
Afeefah tayi tambayar a sanyaye.
Matar uncle sanusi tace
"Ta farka amma tana under kulawar likitoci don ɓarin ya zo ne bagatatan ga cikin ya fara girma,
ta dai ji jiki kam sai dai Allah ya kawo na moro suna chan tare da su mamanku"
Ta fahimci da su matar uncle Mansur take nufi don haka Adu'a suka mata na samun
ingantacciyar lafiya.
Abeeha ta dubi Afeefah
"Yaya fa?"
Shiru Afeefah tayi don bata san me zata ce ba, a lokacin mommyn ta fita daga É—akin
"Yana É—akinshi Adda Abeeha"
Miƙewa zaune Abeeha tayi ta riƙo hannunta.
"Afeefah na san zaman ku da yaya babu daaÉ—i, na kuma san kina tsoron shi da kuma tsoron
kasancewa inuwa ɗaya da shi amma wallahi a yanzu babu wanda Yaya zai fi buƙata kaman ke!
Mammi za ta yi farin ciki idan kika kular mata da shi at his worst moment irin wannan..."
"Ta yaya Adda Abeeha? Mutumin da bai taɓa min kallon matsayin abu mai muhimmanci ba,
wanda bai taɓa ɗaukata da kima ko daraja ta mace ba macen ma matarshi?"
Tayi maganan cikin sanyi, tun ɗazu yaƙi take da zuciyarta akan Rayyan, tana so ta je inda yake
amma tana tsoro ta san yana buƙatar wani amma bata san ta yadda za ta rarrashi mutum irin
shi mai dakakkiyar zuciyar da baya bayyana rauninshi a fili ba.
"Trust me Afeefah za ki iya, na san kema kin san me ya fi buƙata a yanzu tunda duk waennan
abu kin yi going through a rayuwarki... A lokacin da muka rasa Abbu akwai Mammi Dukda bata
da lafiya ta tsaya mana dukkanmu har saida muka zama daidai muka amshi ƙaddararmu amma
a yanzu bata nan ita da ta fi kowa sanin Ya Rayyan a duniya, na sani a kwanakin nan bacci sai
dai idan da allura ko magani hakanan zai yi ta ciwo amma ba zai nuna ba, ba zai yi magana ba
ba zai ci abinci ba don Allah ki taimakemu ki kula dashi matsayin ki na matarshi"
Kai Afeefah ta gyaÉ—a ganin Abeehar ta fara hawaye, tun dazu take so taje gareshi har cikin
zuciyarta amma bata san me zata yi ba in taje ɗin, Miƙewa tayi tana kallon Abeeha
"Ki yi bacci zan kula da komai in shaa Allah"
Godiya Abeeha zata yi mata amma tayi saurin ficewa Abeeha ta mayar da idanun ta rufe
hawayenta na gangara.
Afeefah na barin sashen tayi É—akin ta wanka tayi saboda yanayin zafi da ake dan yi tayi Sallar
isha ta jima tana yiwa Mammi Adu'a tana hawaye kan ta yi shafa'i da wutiri ta nemi riga da
wando na bacci jajaye ta saka ta ɗora hijab har ƙasa a kai sai ta fito ta nufi ɗakinshi, sai da tayi
knocking ta buÉ—e ta shiga hasken a kunne don haka ta hange shi kwance kan gadon É—akin
idanunshi a rufe ya É—an dukunkune kaman mai jin sanyi amma kuma bai rufa ba, kamshin shi
da ya kama É—akin na nan yadda yake ta nufi gaban gadon ta É—an tsaya a kanshi kaÉ—an tana
kallonshi.
Allah sarki mutuwa, in ba mutuwa ba mai ya isa ya jijjiga Rayyan har haka a yini guda har ya
rame, fuskarshi dake fari tass yayi wani irin ja musamman kan hancinshi, daga yanayin baccin
da yake zaka san ba na farin ciki bane don a baccin ma sai yamutsa fuska yake, a hankali ta ja
bargon ta lulluɓa mishi har kafada, sai ta isa wardrobe dinshi ta dubi wani bargo ta zo ta
shimfida a ƙasa ta zagaya ɗaya ɓangaren ta ɗauki pillow daya dake cike da kamshinshi
zuciyarta na bugawa sossai ta kwanta a ƙasan bayan ta kashe wutan ɗakin, ko motsi tayi sai taji
kaman yana nan a kusa da ita saboda yadda daga bargon har pillown ke fidda azabbaen
kamshin shi ga kasancewar ta under roof ɗaya da namiji abin da bata taɓa ba sai take jin ta
wani iri da kyar bacci ya É—auketa. Chan cikin dare sai ta fara jin kaman numfarfashi a É—an
tsorace ta farka ta miƙe zaune sai ta ji kaman daga kan gadon da yake kwance ne da sauri ta
miƙe tsaye ta tafi ta kunna hasken ɗakin ta nufi gangar shi.
Ya haÉ—a zufa yayi sharkaf sai juye juye yake kaman mai mummunan mafarki, numfashinshi na
seizing kaman mai ciwon asthma hankalinta ne ya tashi bata san ta riƙe hannunshi ba tana
jijjigawa
"Ya Saraki! Ya Saraki ka tashi..!"
Duk ta ruÉ—e saboda yadda yake yin kaman zai mutu, da karfin gaske ta jijjigashi hakan ya sa ya
buÉ—e rinannun idanunsa ya zuba mata yana sauke numfashi a hankali hankali, hawaye ne ke
bin idanunta suna diga a duk inda suka samu zarafi kama daga gaban hijabinta har kan
hannunshi dake cikin nata.
"Mummunan mafarki kake? Sannu ka ji? Bari na kawo maka ruwa"
Duk ta rikice tsabar yadda ta ganshin ya dameta, da sauri ta nufi frigde ta kawo mishi ruwa da
kyar ya miƙe zaune ya ɗan yi tapping wayanshi ya kalli time karfe biyu, lumshe ido yayi ya buɗe
a kanta tana miƙa mishi ruwan, bai san me yasa ya karɓa ba ya dai tsinci kanshi yana shan
ruwan yana jin wani abu dake tsaye mishi a makoshi na sauƙa a hankali, sai kuma ya ji cikinshi
na murdawa yana jin amai na taso mishi rabon shi da abinci tun jiya da daddare don ko
karyawa bai yi ba rashin lafiyar mami ya riskeshi, ruwan ya miƙa mata tana daga tsaye tana
kallonshi har lokacin idanunta na cike da kwalla.
Ƙoƙarin sauƙa yake daga gadon ba tare da ya ce uffan ba sai jiri ya kwashe shi ya tafi zai faɗi
da wani irin hanzari ta riƙe shi
"Ya Saraki baka da lafiya...! Jikinka zafi sossai me kake so in kawo maka?"
A karye take maganan, kaman ba zai yi magana ba yana tsaye tana dafe dashi Dukda ya
tabbatar in faɗuwar ne ɗan tiny body ɗintan nan bai isa riƙe shi ba a hankali yace
"Amai...!"
Kalma na farko da ya furta kenan tun bayan Ameen da yake ta cewa in an yiwa Mammi Adu'a.
"Amai za ka yi? Sannu mu je bayin ko in kawo maka abu ka yi daga nan?"
Shiru ya mata sai ya yunkura zai cigaba da tafiya nan ta gane bayin yake son zuwa da
taimakonta ana tafiya ana hutawa suka shiga bayin, sai da ya dafe jikin sink ya kalleta ya kalli
kofa.
"In fita? Za ka iya?"
In ba don halin da yake ciki ba za ta iya rantsewa ya Harare ta, bata ƙara magana ba ganin ya
zuba mata idon da suke sake firgitata da bata tsoro ta fice da sauri sai da ta rufe kofa ya lumshe
ido.
Kai tsaye kitchen nasu taje ta haÉ—o tea mai kauri ta dawo É—akin gadon da ya jajjanye bedsheets
É—in ta gyara ta tsaya daga gefe kaman security, ganin ya jima bai fito ba ta yunkura ta nufi bayin
tana shirin yin knocking yana buÉ—e kofan da sauri ta matsa baya, ya kalleta ya dauke kai ganin
bashi da ƙarfin jiki ta matso ta kama hannunshi bai hanata ba har suka isa kan couch ya zauna
yana jinguwa tare da riƙe kanshi da kaman zai fashe yana cewa
"Asshhhh!"
Kaman zata yi kuka take jera mishi sannu.
Tea din ta É—auko
"Ya... Saraki!"
Ta faÉ—a a rarrabe, ya É—an buÉ—e ido ya kalleta yana jin sunan na mishi wani iri har a cikin jikinshi
"ka sha tea ka ga cikin ka babu komai sai ka sha magani Don Allah..."
Ya lumshe ido kawai fuskar nan tamau, hawaye ne ya zuba mata ta É—an ja Shesheka sai ya
bude idanun yana kallonta ya zubawa hawayen idanu haushi yake ji, takaici yake ji Meyasa shi
ba zai yi kukan kaman kowa ba? Meyasa take da arhar hawaye a sadda shi yake nema?
Zuciyarshi zafi yake mishi raÉ—aÉ—i da kuna yake mishi.
Hannu ya miƙa mata don yana da buƙatar yin Sallar isha don bai yi ba kuma ba zai iya samun
karfi ba matukar ba abu bane ya shiga cikinshi, da sauri ta miƙa mishi ta koma gefe tana share
fuskanta wanda ta rasa me yasa hawayen nata suka ki tsayuwa muddin ta kalleshi sai ta ji suna
zubowa tsabar tausayinshi.
Kurba bai fi hudu yayi ba ya ajiye, ta dubo magungunanshi ta ajiye mishi ya kalleta tace
"Don Allah Ya Saraki ka sha ko zaka samu sassauci...!"
A karye tayi maganan yayi shiru
"Wanne ne zan cire maka?"
Ya sake yin shiru
"Ya Saraki...!"
"Get out of this room..!"
Yayi maganan a kausashe ta girgiza kai za tayi magana ya ce
"Nowww!"
Da ƙarfi yayi magana yana zaro mata idanu...
🖤Gureenjoh🖤
HAIHUWA DA HANJI
(A True life story)
Fatima Muhammad Gurin
(Gureenjoh)
Wattpad-Gureenjo6763
Arewabooks-Gureenjoh
ADABI WRITERS ASSOCIATION
*FREE BOOK*
*39*
Kuka ta sakar mishi mai sauti ya kawo idanu ya zuba mata yana mamaki a ƙasan ranshi, ganin
ta ƙi fita ya sa bai bi ta kanta ba ya ɗauki maganin ya hadiye ya tura mata taje ta ɗauka ta
mayar inda ta samu ta sake ja ta tsaya, Miƙewa yayi ya isa wurin Sallarshi ya tada sallah.
Bayinshi ta shiga itama tayi Alwala ko kan ta fito ya idar da isha nafilfili yake yi itama ta fara
nafilfilin sai uku da wani abu taji ta gaji shima yana zaune ne kanshi da yake jin kaman zai fashe
jingine da jikin gado, Miƙewa tayi taje ta kwanta a inda ta kwanta da farko nan ƙasa tana
kallonshi zuciyarta cike da tarin tsantsar tausayinshi tana kuma mamakin irin karfin halin da tayi
har bacci ya sureta bata sani ba.
Karfe biyar da rabi ya buɗe idanunshi ya miƙe yaje yayi alwala, har ya wuce ta kaman yayi
fitanshi ya kyaleta sai ya tuna irin kulawar da ta bashi a daren na jiya da irin yadda tayi ta zubar
da hawaye akan damuwarshi, ko da Abeeha ce ba zai barta ana sallah tana bacci ba,
tsugunawa yayi don bashi da wani ƙarfin magana ya sa hannu ya ɗan ja hijab ɗinta firgigit tayi
ta tashi tana kallonshi don baccin dama rabi da rabi ne inda bata saba ba, Miƙewa kawai yayi
ya fice bai ce komai ba.
Da sauri ta miƙe taje ta yi Alwala ta zo ta gabatar da sallah, bata tsaya doguwar Adu'a sossai
ba ta miƙe ta gyara ɗakin tsaf ta share ta saka turaren wuta kan ta fice zuwa babban kitchen,
duk abincin da aka ci jiya a wurin makoki order ne daga manyan restuarants yau kuma a gidan
za'a girka don haka tana bukatar ganin me zasu yi Dukda ba wasu mutane ne na waje ba
kadan da suka Kwana duk na gida ne.
Pepper soup ne na cowtail da bread sai tea da suke zubawa flasks flasks daga nan ta wuce
wurin Abeeha ta samu idanunta biyu suka gaisa take tambayarta jikinta ko da Abeeha ta
tambayi
"Ya Yaya Rayyan?"
Bata wani damu ba ta ce
"Ya fita masallaci"
Murmushi Abeehar tayi É—an kaÉ—an Allah sarki ta je ta kulan dashi kenan.
Shi kam daga masallaci mota ya É—auka ya fice asibiti su jannah sai ganinshi suka yi, da sauri ta
sauƙo ta zo ta riƙe shi zata fara kuka ya rabata da jikinshi ya ja hannunta zuwa bakin gadon ta
zauna.
"Menene na kukan? Uhmm? Lafiyar ki ya kamata ki yi focusing a kai mun riga mun yi rashi,
haƙuri kuma ya zame mana dole ki bar kukan nan"
Kai ta gyaÉ—a tana share hawayen dake silalo mata, bata jin tausayinsu kaman yadda take jin
nashi don yana maganan ne kana jin yadda É—aci dake shimfide bisa zuciyarshi ke hauro wa har
kan harshen shi.
Ya gaishe da matar uncle Mansur dake É—akin É—ayar cousin É—insu ya gaishe shi ya amsa suna
ƙara yi mishi gaisuwa.
Sai da yaje wurin bills aka tabbatar mishi mijinta ya biya komai ya dawo ya nemi da su zo su
koma gida tunda ta ji sauƙi, tattara wa suka yi ya ɗauko su har gida ya shiga ciki ya duba
Abeeha a lokacin Afeefah bata nan, ko da zasu fara kuka ganin juna faÉ—a ya hau su dashi dole
suka yi shiru ya gaisa da iyayen da suke ciki kan ya miƙe ya nufi sashensu har lokacin kuma
kanshi kaman zai rabe amma juriyarshi ya hana shi kwanciya.
A tsakiyar parlorn suka haÉ—u ta fito daga É—akinta sanye da doguwar riga mai faÉ—i sai karamin
hijab da ya shiga da kayan, ganin shi ya sa ta dake tare da danne tsoron ta ta furta
"Ina kwana Ya Saraki? Ya jikin?"
Da É—an hanzari tayi maganan ganin zai wuceta.
"Lafiya"
Ya amsa kan ya wuce ya shige É—aki, zama tayi don ta san kila yanzu wanka zai yi sai da ta
ɗauki awa kan ta miƙe ta nufi dining ta haɗa mishi tean ta ɗauki bowl ta dibi pepper soup ɗin ta
haɗa a karamin tray ta nufi ɗakin, ya yi wanka manyan kaya ne a jikinshi kaftan baƙar yadi mai
taushi da ya sake fito da ainihin hasken fatar shi sannan ramarshi ma ya bayyana, a kan couch
yake zaune yanzu ma yayi relaxing sossai idanunshi a rufe, waya ya gama yi da likitarshi bata
nan ta samu labarin rasuwa hankalinta ya tashi roƙon shi take akan ya samu ya zubar da
hawaye yayi leting damuwarshi fita ko kaÉ—an ne in ba haka zai iya samun matsala ya dai mata
shiru ne amma bai san ko zai iya ba yana son yin shima ko zai samu sassauci amma taurin
ranshi na dayawa, kuma hakan na da alaƙa da training da ya samu a farkon rayuwarshi.
Shigowar ta bai sa ya buÉ—e idanu ba har ta ja É—an table ta ajiye mishi tray É—in ta tsuguna
"Ya Saraki..!"
Har ranshi ya ji sunan, bai san Meyasa duk ta kirashi hakan sai ya ji kaman an kirashi ba kuma
dole zuciyarshi take motsawa ta wani ɓangaren kuma sai yaji kaman Mammi ce ta ƙira shi, dole
ta sa ya buɗe idanu ya kalleta ta sauƙe nata ƙasa don ba zata iya jurar kallon cikin idanunshi ba
ko a yana ƙalau ma bare yanzu da suke a birkice.
"Ga abin kari nan na kawo maka, Don Allah ka ci ka samu ka sha magani."
Idan dutse ya tanka to ya tanka, jin shirun yayi yawa ta É—aga ido ta kalleshi yana lumshe da
idanun abin shi.
"Don Allah dai ka ci Ya Saraki! Ko babu daaɗi ka lallaɓa ka ci ko kaɗan ne a yanzu ba mu da
wani majingina bayan kai, ko da ni bana buƙatarka su Adda Abeeha suna da buƙatarka bare ma
dukkanmu kaine bangon mu a yanzu ba za mu so ganin komai ya same ka ba a wannan gaɓar
da bamu warke raunin tafiyar Mammi daga rayuwar mu ba.."
Muryarta ya shiga rawa hawaye ya shiga silalo mata.
Sunan Allah yake ƙira a hankali
"Ya Allahu!"
Kalaman sun dirar mishi da wani rauni da baya tunanin ya taɓa jin irin raunin zuciyarshi na rawa
sossai, yadda ta furta cikin kuka ya sa yaji idanunshi kaman za su iya kawo ruwa muddin ta
cigaba da irin waennan kalaman cikin sanyin murya da Salon karya zuciya.
"Ki je zan ci!"
Ya faÉ—a a hankali, bazata taji kalaman kuma hakan ya sakata jin daaÉ—i tunda ya yarda zai ci ta
miƙe ta kawo mishi magungunan shi kusa kan ta fice sai da ta fita ya buɗe idanu ya zubawa
kofan da ta rufe sama da seconds goma kan ya É—auke ya mayar kan abincin, ya kuwa sha
pepper soup ɗin mai yawa ya sha tean tare da magani ya ajiye ya miƙe ya koma kan gado ya
kwanta don jiri yake gani a cikin maganin akwai na saka bacci ko da bai so ba dole baccin ya
É—auke shi dama ya saba ko da zai sha da daddare baya iya bacci amma in da rana ne yana yi
ba tare da mugun mafarkin shi ba.
****
"Malam Labaran Haƙƙin uba zuwa ga 'ya'yansa yana da matuƙar muhimmanci musamman a
musulunce, wannan haƙƙi yana tattare da nauyin kulawa, tarbiya da tabbatar da rayuwa ta gari
ga 'ya'ya ciki sun haÉ—a da:
Samar da halal É—in haihuwa wannan ba sai na yi dogon jawabi ba na san ka fahimta ya kasance
an samu wannan yaro ta hanyar aure kaman yadda addini ya tanadar.
Alhakin samarwa yaro suna mai kyau da ma'ana wadda bai sabawa Addini ba.
Ciyarwa da sutura uba na da nauyin ciyar da 'ya'yansa da matansa daidai gwargwadon iko,
hakanan da saya musu sutura da tufafi daidai gwargwado.
Ga babban wato ilimi da tarbiya, koyar dasu abubuwan ibada sallah, azumi da sauransu. Samar
musu da ilimin zamani da horo da zai sa su zama masu amfanar da kansu da al'umma.
Ka ga tarbiya a kan hali ba karamin alfanu yake da shi ga yaranmu ba dole ne akanka ka basu
horo a kan gaskiya, amana, girmama manya da kyakyawar mu'amala da mutane.
Suna da alhaki akanka na basu kariya da tsaro hakan ya haÉ—a da hana su mu'amala da
miyagun abokai ko dabi'u kaman su shaye-shaye, fasikanci da sauran su.
Malam Labaran uba kan zama abin koyi ga É—a wajen addini, hali da mu'amala ina so ka yi
nazari a iya tunanin ka matsayinka na uba kuma miji me ka sauƙe a cikin waennan?"
Inna Larai ta numfashi
"Wallahi malam liman ina ga bayan hakkin farko na samar da su ta hanyar aure babu abin da
Malam Labaran ya sauƙe ciki ko haihuwa aka yi mutumin nan baya ragon suna."
Inna Asabe da kanta ke ƙasa tace
"Mun samu tawaya sossai saboda rashin ilimi da rashin sani gashi mun lalata rayuwar
'ya'yanmu"
Malam Labaran yayi shiru jikinshi a sanyaye kenan shi fa Allah zai kama da laifi? A hankali yace
"Toh malam liman wani hanya za mu bi mu gyara abin da muka ɓata tun farko? Hakikanin
gaskiya ina samun abin da zan iya rufawa kaina asiri da gidana amma son zuciyata ya sa nake
kyashin sayowa in kawo, kowa ta kanshi yake kaman rayuwar bariki hatta sutura wannan na
manta rabon da in saya ma kowa a gidan, Dukda ina kallonsu da suturu da ma wasu ababen
ƙawa amma ban taɓa tambayar ina suka samu ba sai ma fata nake in ga nasu in kwace ko in
sace...kaico kaico da wannan rayuwar jahilcin"
Hawaye ne ya zubo mishi don sai a yanzu yake fahimtar irin illar da jahilci yake dashi, ga yaran
duk sun lalace ya tabbatar babu mai auren su a tunaninsu Afeefah ce ba zata auru ba saboda
yadda tayi tambari a garin sai gashi ta auri wanda kaf kauyen basu da kamarsa, haƙiƙa yayi
matukar nadamar abubuwan da yayi tayi a baya na tsantsar rashin ilimi.
"Hanya ɗaya ne jal kuna raye lokaci bai ƙure ba, ayi Adu'a a nemi yafiyar waenda aka zalunta
babban hanyar shine a nemi sani akan addini."
Nasiha ya cigaba da yi musu mai ratsa jiki sai gashi duk jikinsu yayi wani irin sanyi, inna Larai
dake fama da azabar kafa kawai ta kama kuka, lallai Allah mai girma ne kuma baya abu kan
kuskure hassada da bakin ciki akan rayuwar Afeefah ya ja ta jefa kanta da kanta ga halaka.
Anan aka saka kawu Labaran mayar dasu dakunansu, inda ya nemi zai dinga zuwa daukar
karatu masallacin da malam liman ke koyawa kowani bayan Magrib haka zai yi kokari ya ga ya
sauke duk wani hakkinshi amma bai san inda zai ga Afeefah ba.
"Za ta zo ne! Dole zata neme ku don ku ne dolenta"
Kanshi ya duƙar ba tare da ya yarda da zata zo ɗin ba don su kaɗai suka san irin cutarwan da
suka yi mata.
****
Samha ce zaune da Abeeha bayan Magrib tana É—an janta da hira yayinda jannah ke kwance
akan gado idanunta a lumshe Afeefah tayi sallama ta shigo É—akin.
Idanu suka hada da Samha, sai tayi kaman bata santa ba ta É—auke kai ta nufi wurin jannah
"Addah jannah sannu, ya jikin? Akwai abin da kike bukata ne?"
Ta girgiza kai
"Babu, bacci ma zan yi yanzu ki huta da zirga-zirgan nan haka please tun safe kece nan ke ce
chan baki huta ba"
Afeefah ta É—an murmusa kadan Dukda ta gajin iya gajiya rabon da tayi irin wannan wahalar ma
tun Dutsen-wai, ita ce kitchen ita ce kaiwa mutane abinci da sauran dai duk wani zirga-zirga da
za'a rike mutum a gida a yayin hidima ko ta aure ko ta mutuwa.
"Shikenan Addah jannah, Allah ya kara sauƙi... Adda Abee Allah ya bamu alkhairi wanka zan yi
na kwanta"
"A huta gajiya Afeefah sannu"
Tayi murmushi kawai ta juya ta fita.
Samha da ta zuba mata idanu tun shigowarta gabanta na wani irin faÉ—uwa tana sake kallon irin
sauyawar da tayi da kyaun da tayi ga kamshi kaman wacce ta tsumu ta tashi cikin arziki ta miƙe
tsaye tana kallon Abeeha
"A..Abeeha wanchan ba Afeefah ba?"
"Kin santa ne?"
Abeeha tayi tambayar kaman bata san labarin komai ba.
"Afeefah Afeefah...!"
Sai ta rasa wani kwatance zata yi da Abeeha zata gane
"Afeefah dai wacce ta fito daga wani kauye wai shi Dutsen-wai?"
Abeeha tace
"kila kama dai, wannan Afeefar kaman sister take a wurin mu kuma ita ce matar Yaya Rayyan"
Wani irin kallo Samha ke mata zuciyarta na bugawa da ƙarfi ko a mafarki ta ganta zata gane ta,
Afeefah ce ta koma haka? Wait Afeefah ce take auren Rayyan? Rayyan fa! Kwakwalwarta ya
kasa É—aukar wannan zance za ta yi magana Sameera ta shigo
"Samha mu tafi tun dazu Yaya Saleem ke faÉ—an mun ajiye shi"
Bata tsaya jiranta ba ta fice, Abeeha tace
"Ki je kar yayi faÉ—a, mun gode sossai fah sai da safe"
Ta ɗauki Jakarta ta fice zuciyarta fal mamaki da saƙe-sake to ko bata gane Afeefar bane? Kai
dole in sun zo gobe ta nunawa mommy da su Sameera ita ko ita ce bata gani da kyau ba haka
ta danne maganan ta kasa yi da kowa har suka bar gidan zuwa gidansu akan gobe ma zasu
shigo.
Ita kam Afeefah ko tsayawa tunaninsu bata yi ba dama damuwarta Saleem ne kuma fahimtar ya
dawo daidai hankalinta ya kwanta don haka bata da wani issue da su, wanka tayi ta nemi cotton
peach kayan bacci riga da wando dogo ta saka sai da tayi isha ta yi shafa'i da wutiri ta miƙe ta
kashe komai na É—akin ta É—auki wayanta ta fito gabanta na faÉ—uwa, rabon da su hadu tun safe da
ta bashi abin kari don da rana yana parlorn waje da su Saleem so a chan aka kai musu abinci
basu haÉ—u ba, bata san ma ko ya ci ko bai ci ba haka dai ta nufi É—akin tayi knocking tare da tura
kofa ta shiga, kallon wurin yayi sai suka haÉ—a idanu yana zaune akan gadon kafafunshi biyu na
cikin bargo bayanshi na jingine da pillow ramarshi ya sake fita ainun.
Ɗauke kai yayi chan ƙasan ranshi yana mamakin yadda a yanzu take shigo mishi ɗaki don
tsabar neman magana ya kore ta kuma ta mishi kuka bai sani ba ko tare aka gina musu É—akin
ne oho, abin da ke damunshi ya dameshi don haka bai kula ta ba har ta É—auko bargo ta
shimfida inda ta shimfida jiya taje ta É—auko pillow ta zo ta ajiye sai ta matsa kusa dashi
"Ya Saraki sannu! Ya jikin? Kana bukatar wani abu ne?"
Ya buÉ—e ido ya kalleta ta É—auke kai kaman ba zai amsa ba sai taji ya ce
"Da sauƙi"
Daga haka bai sake magana ba taje ta ɗauko ruwa ta zo ta ajiye a bedside ko zai buƙata,
wayanshi ta gani a kan couch taje ta É—auko tazo ta ajiye mishi gefen ruwan kan taje ta kashe
wutan ta zo ta kwanta ta bar shi da mamakin ƙarfin hali irin nata...
🖤Gureenjoh🖤
HAIHUWA DA HANJI
(A True life story)
Fatima Muhammad Gurin
(Gureenjoh)
Wattpad-Gureenjo6763
Arewabooks-Gureenjoh
ADABI WRITERS ASSOCIATION
*FREE BOOK*
*Ina Editing ashe ban gama ba bacci ya É—auke ni. Ku karya da wannan*
*40*
Ya jima zaune yana kallon figure É—inta cikin duhun É—akin kan ya zame ya kai kwance yana
sanya pillow a kirjinshi, idanunshi a lumshe sama da awannin da ba zai iya lissafawa ba har
bacci ya É—auke shi a haka É—in, chan cikin baccin shi ya fara jin abin da yake ji muddin ya rufe
idanu da sunan baccin dare ji yake kaman zai mutu, kaman an saka abu ne aka danne mishi
kirji numfashinshi ya toshe juye juye yake ya haÉ—a zufa sharkaf sai numfarfashi yake fitarwa
sama sama.
Cikin baccinta ta soma jinshi a hankali ta buÉ—e idanu sai dai jin yadda yake yin yasa bata san ta
miƙe ba taje ta kunna wuta gabanta na faɗuwa ganin kaman zai faɗo daga kan gadon ta ƙarasa
wurinshi da gudu tana jijjiga shi Muryarta na shaking take ƙiran sunanshi
"Ya...ya Saraki! Ya Saraki...!
Ka buÉ—e ido.. Ka tashi ya Saraki mafarki ne... Don Allah ka bude ido...innalillahi!"
Duk ta rikice ta ruÉ—e sai dai kaman bai san tana yi ba har lokacin idanunshi a rufe suke yana jan
numfashi da kyar, kuka ta saki tana janyo wayanshi ta shiga neman Layin likitarshi jikinta na
tsuma saboda tashin hankali, kiranta tayi Allah ya taimaka ya kusa yankewa ta É—aga
"Dr. Yaya Saraki ne... Ban san me zan mishi ba ya ƙi tashi sai juye juye yake kaman zai mutu ki
taimakeni..!"
Likitan da take sensing tashin hankali a Muryar Afeefah tausayinsu duk ya rufeta ta ce
"Ki natsu Afeefah natsu! FaÉ—a min me yake yi?"
Kaman za ta taya shi kokawa da numfashi ta shiga cewa
"juye juye yake yi, ya jiƙe sharkar da zufa, he's just gasping for air kaman baya iya isar da
numfashi inda ya kamata jikinshi rawa yake.."
"Ki ji Afeefah Rayyan na gab da shiga cikin mummunan yanayin matsalar kwakwalwa idan baki
taimakemu ba, ki taimaka ki san yadda zaki yi ki saka shi yayi kuka ya zub da hawaye in ba
haka ba akwai matsala..."
Wasu tips ta bata tare da yanke wayan akan dole gobe da safe su tafi asibiti he cannot continue
like that.
Jefar da wayan tayi a kan gadon ta tattare ƙarfinta gabaɗaya ta ɗago shi ta jijjigashi da karfin
gaske tana ambatar sunanshi sai ya ja numfashi mai tsawo yana buÉ—e idanu amma sai idanun
su tafi luuu kaman za su rufu idan ta sake ƙira sai su buɗu sun yi wani irin ja da sauri ta kafa
gwiwowinta akan gadon ta zare hijabinta ta jefar tare da ma kanshi ta mishi kyakyawar masauki
a kan kirjinta ta rungumeshi Tsam tana kuka sossai, yadda ta yi hugging nashi, yadda take
shafa kanshi da duk hannayenta biyu zuwa wuyanshi yadda take kara matse shi, sautin fitan
muryarta cikin kuka ya sa bai san sadda ya mayar da hannayenshi jikinta ba ya rungumeta
ƙamƙam... Cikin sautin kuka take furta
"Ya Saraki ka sassautawa zuciyarka don Allah, wannan wahalar yayi maka yawa don Allah ka
daure ka zub da hawaye ko kaÉ—an ne... Zan zama kurma daga jin sautin Muryar fitar
damuwarka! Zan zama makauniya daga kallon ruwan hawayenka! Kwakwalwana zai shiga
É—imuwa har lokacin nan ya zama tamkar mafarki ko dilusion a gareni just cry ka ji? Ka yi kuka
ba zan ji muryarka ba i promise...Muna mu...na son lafiyarka we will always be there for you...
Ka yi kuka just let your worries our this will be our Lil secret ka ji?"
Har lokacin bata daina shafa suman kanshi ba cikin wani irin kulawa, sake ƙamƙameta yayi
kaman zai ɓallata jikinshi na sake ɗaukar rawa zuciyarshi na wani irin tsitsinkewa Dukda irin
yadda take ji da zafi dake ratsa ta haka ta sake hugging nashi, she hugged him until his soul
melts into tears sai ji tayi yana sauke wani irin numfashi mai tafe da zafafan hawaye masu
rikitarwa.
Lips É—inta ta datse tana runtse ido a sadda sautin shi ke shiga cikin kunnuwanta a hankali yana
samun masauki a cikin zuciyarta, bata daina shafa shi ba shi kuma bai daina sake kankanmeta
ba ya fi mintuna talatin cikin wannan yanayi kan a hankali ya fara sassauta riƙon, gefe gefe tayi
ta kwanta yayinda ya bita har lokacin kanshi na kan chest É—inta dake beating so so fast tana
shafa shi da hannunta tana jin jikinshi na sauyawa daga zufa zuwa zafi dake shiga har cikin
jikinta, sai da suka kai kwance ta iya jin ruwan hawayen shi na sauka a kan silk maroon rigan
baccinta Yana taɓa fatarta ta runtse ido kawai. Basu san iya adadin lokutan da suka ɗauka a
hakan ba har bacci ya É—auke shi itama baccin tayi.
Ƙarfe biyu da wani abu ya sake farkawa, shiru yayi yana shakar fitinannen kamshinta yana jin
hannayenta a jikinshi, É—aya a cikin tattausan gashin kansa É—aya a bayan wuyanshi, a hankali ya
zame ya miƙe zaune wutan ɗakin a kunne har lokacin amma ba tarrr ba mai ɗan duhun yana
iya kallon fuskarta a haka, idanu ya zuba mata yana aikin kallo her caramel skin, dogin lashes
É—inta pointed nose É—inta zuwa thin beautiful lips É—inta he just felt lost a kallon nata moments
É—insu na É—azu na dawo mishi kaman yanzu, he can't believe that it happened.
It really happened! he cried in this little Girl's arms, the way she caresses him, pet him like a Lil
boy ya tsaya mishi sossai a rai. Sauƙa yayi daga gadon ya ja duvet ɗin ya rufeta zuwa kirji sai ta
É—an gyara kwanciya kaman dama a takure take ya shiga toilet yana jin wannan nauyin na cikin
zuciyarshi ya ragu, ruwa ya kunnawa kanshi ya jima a ciki har lokacin kuma duk motsinshi
kallon kanshi yake akan chest É—inta tana bashi utmost kulawa, wanka yayi ya fita ya zo ya nemi
jallabiya ya saka ya fara nafilfili har sai da ya ji zazzabi na neman fin karfinshi ya miƙe ya zare
jallabiyar ya saura daga shi sai guntun wando da karamar vest da ya bayyana duk wani
kakkarfar sura mai cike da zati da Allah ya mishi gadon ya hau ya ja bargon shima ya É—an rufa
tare da juyawa ya zubawa face É—inta idanu tana baccinta peacefully har bacci ya sake sace shi
a haka.
Ita ta fara farkawa da asuba ta sauke idanunta akan kyakyawar fuskarshi, ta É—an jima tana
kallonshi kwakwalwarta na tuna mata abin da ya faru a daren, nauyi da kunyarshi suka lallaɓo
suka rufeta amma ta kasa É—auke idanu daga kallonshi he's just handsome so so handsome da
bata san ya zata kwatanta shi ba, yana baccin kaman ba shi bane Saraki mai zuciya a kusa,
wannan masifaffen marar fara'a da son Magana murmushi ta tsinci kanta da yi Alhamdulillah
atleast ta samu riba a kanshi wani abin dole ta san ya ragu mishi hakan kaÉ—ai ya faranta mata,
sauƙa tayi daga gadon tare da ɗaukan hijabinta ta saka ta shiga toilet don yin alwala tana jin ko
me ta mishi bata ragu ta kowani fanni ba saboda he's her life savior ba don shi É—in ba da yanzu
tana cikin matattu matattun ma cikin sahun masu gingimemen laifi wa ubangijinta.
Tana rufe kofan bayin ya buÉ—e idanu sai dai bai motsa ba don zazzabi ne sossai a jikinshi har
numfashin da yake fesarwa na fitar da zafin hucin zazzabin, bayan tayi alwala ta taho gadon ta
taɓa goshinshi sai taji shi rau a hankali ta shiga kiran sunanshi
"Ya Saraki..! Ya Saraki...!!"
Ya rasa wani irin effect sunan ke dashi a zuciyarshi don wani irin tsalle zuciyar tashi tayi a
sadda ta ƙira sunan cikin tsiririyar muryarta
Idanu ya buÉ—e ya kalleta
"Sannu! Na ji jikinka zafi sossai za ka iya tashi ka yi sallah? Ko in idar in kawo maka ruwan
nan?"
Idanunta kawai yake kallo hakan ya sa ta kawar da idanun yace a hankali
"Zan iya"
Daga haka ta koma baya ta tada sallah kar ya ga kaman ta cika zaƙewa, shi kuwa ya ɗan jima a
haka kan ya yunkura ya miƙe zaune yana dafe kanshi, a hankali yake tafiya har ya isa bayi yayi
alwala ya dawo sai ya kasa Sallar a tsaye duk kafin halinshi a zaune ya gabatar bayan ya idar
ya miƙe ya koma gadon tare da lullubuwa, bayan ta idar ta miƙe ta ninke sallayar tana shirin fita
wayanshi ya ɗauki ƙara sai ta koma taje ta ɗauka ganin Likitarshi yasa ta ɗaga suka gaisa take
tambayarta ya ya kwana nan ta mata bayanin zazzabi ne a jikinshi sossai Dukda ya samu ya
zub da hawayen.
Hamdala tayi da farko kan tace za ta turo yanzu collegue É—inta zai zo ya saka mishi drip da
wasu allurai in shaa Allahu zuwa yamma zai samu lafiya don Allah ta kula dashi ta amsa tare da
godiya ta sauƙe wayan, ficewa tayi zuwa kitchen ta ga abinda suka fara a lokacin gari ma ya
fara haske taje ta watsa ruwa don duk yadda ta motsa kamshinshi kaman tayi wanka da
turarenshi kamshin na sakata jin kaman har lokacin yana kwance ne a jikinta rungume da ita
Dukda ba don soyayya ko wani romance suka yi ba taimako ne ta mishi amma hakan ya mugun
tsaya mata,bayan ta fito ta shirya cikin atampharta riga da siket da ya zauna mata chass ta
É—aura dankwali sai ta nemi gyale mai girma da kauri ta yafa ta fita parlor tana shirin shiga side
dinshi aka yi mata sallama.
"Mery ya dai?"
"Wai wani likita ne ya zo duba Oga Rayyan"
"oaky ki ce ya shigo"
Tana nan tsaye har ya shigo suka gaisa kan ta mishi jagora har ciki, har lokacin yana kwance
ba bacci kuma yake ba don zafin zazzabin bai barshi ba, tana daga chan gefe har likitan ya
haÉ—a drip ya mishi allura ciki ya saka mishi canular yayi wani a canular kan ya É—aura ruwan sai
ɓata fuska take kaman ita ake ɓula wa.
"Toh madam za ki iya samun ruwa masu ɗan dumi kaɗan da towel ƙarami a shafa mishi a kan
nan da Goshi zafin jikin zai ragu Dukda na mishi allurai amma hakan ma na da kyau don
temperature É—in shi is very very high"
"in shaa Allahu mun gode kwarai Dr"
"Mention not"
Daga haka ya fice, bayi ta tafi ta haɗa ruwan ta samo ƙaramin towel ta dawo bakin gadon ta
zauna ganganshi ta cire gyalen ta ajiye tare da matsa ruwan ta É—ora mishi a Goshi ya buÉ—e ido
ya kalleta saboda sanyin da ya ratsa shi yana sauƙe ajiyar zuciya mai nauyi, wani iri take ji da
kallon nashi amma ta dake ta cigaba da shafa mishi da kanshi ya gaji ya mayar da idanun ya
rufe sai ta sauke numfashin da ta riƙe tuntuni, idan ta zo daidai kwantaccen sajenshi sai ta tsinci
kanta da zame towel ta bar fatar hannunta na shafa lallausan gashin wurin a hankali.
Jin abin nata na so ya fi karfinshi ya ɗaga hannu ya ture hannunta, ta ɗan tura baki ta miƙe ta
nufi bayi tana mita
'Mutum bama shi da lafiya amma hali ba zai chanza ba!' Sarai ya ji ta a maimakon ya ji haushi
Sai É—an murmushi da yayi a cikin zuciyarshi wanda ko alama bai fito fili ba, bata ma fito ba bacci
ya É—auke shi don akwai allurar bacci ciki daga nan ta É—auki gyalenta ta yafa ta nufi cikin gidan,
É—akin su Abeeha ta shiga inda ta samu suna zaune sun yiyyi wanka Mommy da mama da suna
nan tun rasuwar basu tafi ba suma suna É—akin da alamu sun zo duba kwanansu ne.
Har ƙasa ta duƙa ta gaishe su suka amsa cikin kulawa kan ta dubi jannah ta gaisheta tare da
mata sannu da jiki suka gaisa da Abeeha a karshe, wata cousin É—insu Aaliyah ce tace
"Na ga likita yana shiga wurin ku da safen nan Allah dai ya sa ba wani abu bane?"
Kanta ƙasa tace
"Wlh Ya Saraki ne ya kwana da zazzabi amma Alhamdulillah an saka mishi drip yanzu haka
bacci yake"
Cike da jimami suke mishi Allah ya kara sauƙi ta ɗan jima anan har aka gama fito da kayan kari
ta karya anan suna hira kaman dama chan ita ma she's part of the family don basu ware ta ba
sam.
Sashensu ta koma ta leƙa ta samu har lokacin bacci yake ta koma parlor tana kallon time, a
chan kuwa fitan ta ba jimawa sai ga su mommy sun shigo babban parlor aka dawo da gaisuwar
makota dai kan shigo a yi gaisuwa da su Ƙawayen su Afeefah har ma da dangin mijin jannah ita
dai Samha sai baza ido take ta ga ta inda Afeefah za ta ɓullo amma bata ganta ba.
Ko da Saleem ya shigo suka gaisa Abeeha ya tambaya Rayyan fa don ya ta kiran wayanshi
ba'a picking nan ta faÉ—a mishi ai bashi da lafiya an ma saka mishi drip kila bai tashi ba har
lokacin, bai shiga ba don ya san akwai bambancin da da yanzu ba zai yiwu ya je har É—akin ba
sai fita yayi akan yana parlorn waje.
Sai karfe sha ɗaya da rabi da Afeefah ta leƙa ta samu baya kan gadon alamar ya shiga wanka,
gadon ta gyara tsaf kaman ba'a kwanta ba ta fice chan sai gata rike da tray mai dauke da
dafaffen dankali sai wani curry chicken soup da ta mishi da kifi gasashe a gefe sanin yana so
sai tea da ta haÉ—a mishi, ya gama shiryawa cikin riga da wando masu taushi don ba jeans bane
wandon cotton ne mai ɗan faɗi Brown, shirt ɗin burnt orange ya karɓe shi sossai ya sake zama
pale kana kallonshi zaka san yana ciwo.
A kan table na gaban couches na É—akin ta ajiye ta kalleshi shima ita ya kalla sai suka haÉ—a
idanu ta É—an rausayar da nata tace
"Ina kwana Ya Saraki? Ya jikin?"
Bata zaci zai wani amsa ba sai kuma taji ya ce
"Alhamdulillah da sauƙi"
Dukda a hankali yayi magana amma ta ji ta É—an murmusa
"ka karya sai ka sha magani"
Ya nufo inda take sai da ya É—an wuce taji ya ce
"Thank you!"
Zama yayi ya ja abincin ya shiga ci hakan ya faranta ranta sossai ta juya ta fice, a parlor ta
zauna tana kallo kusan mintuna talatin sai gashi ya fito ya fita waje.
Sai lokacin hankalinta ya kwanta ta miƙe itama ta nufi wurin su Jannah tana shiga babban
parlorn da sallama suka hada idanu da Mommy...
🖤Gureenjoh🖤
HAIHUWA DA HANJI
(A True life story)
Fatima Muhammad Gurin
(Gureenjoh)
Wattpad-Gureenjo6763
Arewabooks-Gureenjoh
ADABI WRITERS ASSOCIATION
*FREE BOOK*
*41*
"Sannunku"
Ta faÉ—a tana É—auke kanta daga cikin idanun mommyn da ta kusa daskarewa a wurin a zaune.
Bata ƙara firgita ba sai da taji matar uncle sanusi na cewa
"Sannu Afeefah, jigilar nan ba zai haifar miki da ciwon jiki ba? Kece nan ke ce chan ya kamata
kina hutawa fa"
Matar uncle Mansur tace
"Gaskiya kam ya kamata ki dinga ji da mijinki kawai su jannah duk ba ga mu nan ba, shima ba
don baudadden halinshi ba ai da duk sai mu kula da ku don kema na tabbatar raunin tafiyar
Mammi na nan É—anye a zuciyarki."
Murmushi ta ɗan saki tana zama za tayi magana Sameera ta miƙe tsaye don tun dazu duk su
huɗun kaman an kafa su ne idanunsu ƙurrr a kanta.
Nuna ta take hannunta na rawa
"Afee...fah?"
"Ita ce ko Ya Sameera? Ita ce ba gizo na gani jiya ba ashe!"
Samha tayi saurin faÉ—a kaman jira take wani ya fara magana cikinsu.
Mommy ta kasa ma magana tsabar yadda taji da ganin Afeefar ƙare mata kallo take yadda ta
wani sauya tayi mugun kyau ko atamphar jikinta ka gani ka san bata cikin wahala sai hawaye
suka fara zuba mata ta tuna ranar auren Saleem inda take ce mishi a lokacin Afeefah na chan
tana raba wa maza kanta tana samun na cin abinci idan zai mantata gyara ya mantata.
"Kun santa ne?"
Mama tayi tambayar da mamakin irin shock da ta gani a tare da su ga mommy ta fashe da
kuka.
Jannah ce da daman ta kasa sakewa dasu saboda har lokacin bakinsu take gani akan abinda
suka yi wa Afeefah tace
"Sun santa Mama, mommy kin ga ta sauya ko? Kun ga yadda Allah ke ikonshi ko? Ku kun ƙi ta
mu mun so ta mun karɓeta hannu bibbiyu, kun muzguna mata hakan bai hana ta muku taimako
mafi girma ba a rayuwarku... Ita ce ta taimaka da ayoyi da ruwan tofi ba ji ba gani har saida ta
tabbatar asirin da aka yiwa Ya Saleem ya karye, gata nan yanzu haka ana dawowa makaranta
exams na karshe zasu rubuta tana kan karatu. Nasara mafi girma da daraja shine tayi aure ta
auri namijin nunawa sa'a wanda ko cikin maza sai an tara dubu a samu tamkarsa É—aya. Afeefar
da kuka sani ce dai ita ce matar Ya Rayyan ta sunna a yanzu haka"
Afeefah ta mayar da kanta ƙasa hawaye na taruwa a idanunta sam bata san sun zo gangarta
ba sai jin mommy tayi ta riƙe hannunta tana sake ƙara fashewa da kuka mai tsuma rai, Abeeha
ma bata yi shiru ba ta kara da labarin irin yadda ta taimakesu akan Saleem.
"Don Allah ki yafe mana Afeefah, haƙiƙa ba mu da bakin neman yafiyarki saboda mun aikata
miki ba daidai ba, mun kasa duba kasantuwarki mace mun kasa yarda cewa Allah ke komai a
sadda ya so na bi dare na raba ki da Saleem karfi da yafi na aura mishi wacce nake ganin ta fi
cancanta ashe ban sani ba ƙabari na haƙa mana... Haƙiƙa na so na ganki ba tare da aure ba
nayi adu'ar Allah ya bayyana mini ke ko ta wani hali in nemi yafiyarki in kuma gyara kuskurena
ashe ke kam Allah ya dubeki ya Musanya miki da alkhairinki... Don Allah ki yafe mana ki yafe
mana Afeefah!"
Sossai duk suke kuka suna neman yafiyarta sai ta nemi rudewa Dukda tayi mamaki amma ta
sani duniya aka ce makaranta.
"Mommy ku daina neman yafiyata wlh tun kafin na bar gidan duk na yafe muku Yaya Saleem ya
wuce yadda kuke zato a wuri na. Ban riƙe ku a zuciyata ba ku daina wannan kukan don Allah".
Samha ta fi kowa bata haƙuri sai Mommy, duk ta nuna ita komai ya wuce a wurinta suka koma
gefe suna ta kallonta ko motsi tayi burgesu take, basu taɓa sanin haka take ba sai a yanzu yinin
da suka yi a ranar suka kara sanin wacece ita kunyar duniya duk ya rufesu na tunanin duk irin
wulakancin da suka yi mata, lallai da gaske ne da aka ce mai haƙuri shi yake dafa dutse har ma
ya sha romonta.
Mommy ta tabbatar Saleem bai san da wannan labarin ba, gab za su tafi ta kira shi a waya
akan ya zo ciki duk jama'ar sun watse a babban parlorn sai Afeefah dake zaune tana duba abu
a waya mommyn ta fito daga É—aki ganinta yasa tace
"Yauwa ashe kina nan dama ke zan je dubawa kitchen. Yanzu Saleem zai shigo ku gaisa..."
Gabanta ne ya faÉ—i rabon da su hadu kusan watanni bakwai zuwa takwas kenan, ya rabu da ita
cikin kuna da zafin zuciya tare da hawaye a yanzu zai haÉ—u da ita matsayin matar aure, matar
ma ta abokinshi me zata ce mishi? Ta san akwai laifin mahaifiyarshi a rabuwarsu amma ta san
dole zai ji zafin samun wannan labari, anya ma zai yi farin ciki da ganinta? Bata gama tunanin
ba ta ji sallamarshi gabanta ya sake faɗuwa ta miƙe tsaye sai suka haɗa idanu a lokacin da take
amsawa da iyaka lips É—inta.
"A...Afeefah? Ke..ke ce nake gani? Afeefah ba gizo idanuna suke min ba kece tsaye a gabana?
Ta yaya kika zo gidan nan? Ina kika shiga Afeefah? Ina kika shiga...?"
A ruÉ—e yake maganan idanunshi na cika da kwallah kaman yadda nata ya cika fal da hawayen
ganinshi.
"Ya Saleem...!"
Ta faÉ—a a sanyaye sai ta kama hawaye.
Sake matsowa yayi kaman zai taɓa ta tayi saurin matsawa baya sossai tana girgiza mishi kai.
"Ka gafarceni Ya Saleem yanzu da baya ba É—aya bane..."
"Afeefah na san akan mahaifiyata ne wlh yanzu duk sun yi nadamar abin da suka aikata miki,
na tabbatar za kuma su nemi yafiyarki don Kullum adu'arsu shine mu ganki mu nemi
yafiyarki...ko babu komai a yanzu za mu cika burinmu za mu cika alkawarinmu na mallakar
juna..."
Daidai lokacin Rayyan ya sanyo kai parlorn he just stood there fuskarshi kadaran-hadaran yana
kallonsu.
Hawaye take yi sossai
"Lokaci ya riga ya ƙure ya Saleem, kayi hakuri Allah bai nufa na zama rabonka ba. Ni din yanzu
matar aure ce."
Jikinshi yayi wani irin sanyi wani tashin hankali da damuwa na lallaɓo wa ya rufe shi murya na
shaking yake furta
"A..a..aure Afeefah? Aure kika yi? Da waye? Me..me yasa?"
Idanunta ne suka shiga cikin na Rayyan da sauri ta kawar heartbreat É—inta na kara gudu ganin
kallon da yake mata.
"Ka sa a ranka ƙaddara ce ta zo haka, amma ni matar aure ce don Allah ka ajiye zancen alaƙar
da ta riga ta wuce Ya Saleem"
Daga haka tayi saurin wucewa sashensu ta barshi kanshi a matukar kulle, idan bai ce ya
matuƙar kaɗuwa da wannan zance ba yayi ƙarya zuciyarshi raɗaɗi ya shiga mishi, saboda
rauninshi tuni hawaye suka shiga zubo mishi haƙiƙa ya so Afeefah kaman ranshi har gobe yana
ƙaunarta amma gashi ƙaddarar su ya zaɓar musu rabuwa aure tayi a sadda yana chan ya rasa
hankalinshi, me yasa bata yi haƙuri ba? Meyasa bata jira ba? Me yasa yayi jinkiri? Tun da ya
dawo hayyacinshi a neman ta yake ko Allah zai sa ya ganta ashe ita kam tana chan tare da
mijinta tana rayuwa mai kyau don ko skin É—inta ya bayyana hakan.
Mommy ce ta fito ganin yanayin da yake ciki ta kalli Rayyan dake tsaye har lokacin a bakin kofa
hannunshi harde a kirjinshi wanda da alama Saleem É—in bai kula da wanzuwar shi ba tayi saurin
kama Saleem ɗin ta zaunar taje ta kawo mishi ruwa bai karɓa ba sai ma maganganu da ya fara
"Mommy ta ya kika ga Afeefah? Me ya kawo ta gidan nan? Mommy wai da gaske Afeefah aure
tayi? Aure tayi? A yanzu haka Afeefah ta haramta mini?"
Mommy ta kalli Rayyan ta mayar da idanunta kan Saleem.
"Saleem Afeefah ta yi aure laifina ne duka, laifina ne ta subuce maka ka yafemin ciwon da nake
sakawa zuciyarka ka ɗauki dangana da haƙuri. A gidan nan muka samu Afeefah tana kuma
auren abokinka ne Rayyan..."
Da ƙarfin gaske ya miƙe har yana Buge ruwan hannunta ya faɗi ƙasa
"Rayyan?? Mommy all this while Rayyan na tare da Afeefah? Har ma ya aureta? Rayyan dai
Rayyan Moh'd Khamis??"
GabaÉ—aya wani duhu ne ya taso ya rufe mishi gani tsabar wani irin bacin rai da ya zo mishi
juyawa yayi zai fita yaje ya samu Rayyan É—in sai suka haÉ—a idanu nan ya nufe shi ya tsaya a
gabanshi.
"Rayyan da gaske Afeefah ka aura?"
Shi karan kanshi ya san yayi mugun ƙoƙari a sadda ya buɗi baki ya furta
"Saleem Afeefah matata ce idan har ka san darajar aure da kuma martabarsa za ka kiyaye irin
kalmanka a kan matata... Ƙaddara ta riga ta raba ku ta bani ita a lokacin da ban yi zato ko
tsammani ba don haka don't Look at me with those eyes dake nuna kaman I betrayed you or
something like that, you should questioned yourself nd your family not me..."
Yana kai nan ya wuce don har ga Allah bai san dalilin da yasa yake ji kaman zai kama da wuta
ba, mommy ya kalla har kaman zai wuce ya tsayar da idanunshi kanta ba zai iya yi mata
magana kai tsaye ba ba kuma don komai ba sai don uwa ce ya juyo ya kalli Saleem dake
kallonshi rai a tsananin ɓace yace in a respectful manner.
"Rasuwa aka yi mana ko ba rasuwa ba muna da darajar da ba za'a tako har nan a ci mana
mutunci ba Saleem, idan ba zaka taya mu baƙin ciki da jajen rasa wani sashe na bangonmu ba
za ka iya zama da kai da familyn ka a gida. Mun gode"
Daga haka ya nufi sashensu ya bar su nan tsaye calmly kaman ranshi ba suya yake ba.
Wani irin duka Saleem ya kaiwa bangon wurin yana yin baya tare da zuba yatsun shi cikin
gashin kanshi kaman zai fashe haka yake ji, su Samha ne duk suka fito a tare da Abeeha jin
salatin mommy.
Ganin yanayin da suke ciki suka shiga tambayar me ya faru? Menene?
Mommy tana zubar da hawaye tace
"Na sake wani kuskuren, da na san hakan zai kasance Saleem da ban nemi ku gaisa da
Afeefah ba! Na zaci zaka yi farin cikin ganinta idan ka ji kuma tana da aure zaka taya ta murna
da Adu'a ka karɓi kaddara amma me kayin nan? Abokinka ne fa Rayyan abokin da ya zama
É—an uwa ya kuma tsaya mana duka a sadda muke neman tagayyara. Rasuwa fa mahaifiyarshi
tayi ko lafiya bai samu ba me kake yin nan?"
"Rayyan ya ci amanata mommy, ashe ya san inda Afeefah take ya zaɓi ya ɓoye min? Ashe
aurenta yake shirin yi ko da na matsa ya nemo min ita a sadda ba ni da daman hakan saboda
kalamanki ya san inda take ya dinga zurma ni akan ya neme ta ya rasa? Meyasa tun farko bai
ce min sonta yake in sakawa zuciyata hakan ba? Idan ba da wata manufa yayi hakan ba
Meyasa ina zuwa gidan nan bai taɓa nuna min tana nan ko ya bari na ganta ba?"
Abeeha da ranta yayi mugun ɓaci tace
"Ya Saleem baka kyauta ba sam...! Ban zaci ko Ya Rayyan amanarka ya ci zaka iya aikata
hakan kuma ka jefe shi da irin kalaman nan ba. kar hankalinka ya gushe mana... Toh wallahi
Yaya Rayyan ya auri Afeefah ne bisa umurnin Mammi, ya karɓi auren cike da tunanin mai zaka
É—auki hakan a duk sadda ka dawo hayyacinka... Idan ma ya faÉ—a maka a lokacin kake nemanta
cewa coincidently sun haÉ—u a sadda ta taimaki Mammi Mammi ma ta taimaka mata ta kawo ta
gidan nan me zaka yi? Kar ka manta a sannan Allah ya isan mahaifiyarka ke kanka muddin ka
mata magana? Idan da yana da mugun nufi kanka da ba zai ba da gudummawar dinga kawo ka
gidan nan kana ci da sha daga ayoyin Allah ba har ka dawo cikin hayyacinka...idan da yana da
wata manufa ta daban da ba zai bari ku kasance tare da ita a zaman makonkin nan ba don
kaima ka san zai iya kaita ko ma inane... Wallahi ko ni bayan labarin da Afeefah ta bamu na ji
har abada ban bata goyon bayan aurenka ba, Mammi ta zaɓa mata miji kuma ta karɓa hannu
bibbiyu kuma take ibadar aure... Ko da Yaya Rayyan baya sonta a baya bai kyamaceta ba
Dukda ya san labarinta kaman yadda kaima baka kyamaceta ba bambancin kawai mu da
mahsifiyarmu muna sonta kuma muna so rayuwarta ta inganta ashe idan baka godewa Ya
Rayyan ba ba zaka ga baƙin shi ba. Ka je kayi nazarin kalamaina kan ka sake yanke kowani irin
hukunci ne"
Tana kai nan ta juya ta koma ciki cike da jin haushinsu dukkansu, tunanin ta ya tsaya akan ya
Rayyan da banzar zuciyarshi Allah ya sa kar ya sauke akan Afeefar.
Tana zaune bakin gado ta toshe bakinta da gyalen ta tana kuka kawai taji an turo kofan an
shigo, da sauri ta É—aga idanunta dake zub da hawaye sai suka shige cikin nashi da ya jirkice,
wani irin kallo ya mata da ya sa tayi saurin mayar da idanunta ƙasa tana Miƙewa tsaye.
"Kin raina ni ko? Ni za ki wulaƙanta??"
A hankali yayi maganan. Sai ta É—ago tana cewa
"Kayi haƙuri ban san zai shigo ba, ban san mahaifiyarshi ta kira shi ba da na nemi izini..."
"Shuttt up!! Just shut up Afeefahh"
Ya daka mata tsawa har saida ta tsorata tayi baya baya zata faÉ—i ta dafe jikin gado kirjinta na
sama da ƙasa. Yau ne karo na farko da taji sunanta a bakinshi Dukda kaɗuwar da tayi hakan
bai hana sunan sake amsa kuwwa cikin kunnuwanta ba da muryarshi.
Shiru yayi yana sauke numfashi idanunshi a tsaye a kanta ya ce a zafafe
"Ko babyn roba na aura, ko 'yar tsana ce ta amsa sunan matar Rayyan Moh'd Khamis wallahi
billahi na fi ƙarfin ta wulaƙanta min aure... A gabana kike cewa aurena dake ƙaddara ce??"
"Ka yi ha..kuri ba haka..."
Juyawa kawai yayi ya fice yana buga kofar da karfin gaske sai da ta sake razana.
"Na shiga uku!"
Ta ambata tana zama bakin gadon.
🖤Gureenjoh🖤
HAIHUWA DA HANJI
(A True life story)
Fatima Muhammad Gurin
(Gureenjoh)
Wattpad-Gureenjo6763
Arewabooks-Gureenjoh
ADABI WRITERS ASSOCIATION
*FREE BOOK*
*Yauwa. Ga Page É—in ku na yau, it's monday already! ba ni da tabbacin zama available through
out.*
*42*
Zaune kawai yake a kan couch bayanshi na jingine da jikin kujerar idanunshi a lumshe, tun da
ya dawo daga Sallar isha haka yake.
Wani iri yake ji lokaci lokaci ya kan buÉ—e idanu ya kalli kofan ko za ta shigo amma shiru babu ita
ba alamunta, sai wuraren sha biyu ya miƙe ya ɗan yi shirye-shiryen shi na bacci ya koma gado
ya kwanta sai ya tsinci kanshi da kallon wurin da take kwanciya a kwana biyun yadda inuwarta
ke yi, irin rikicewar da tayi ta rungumeshi a daren jiya hannayenta na yawo a cikin sumanshi da
bayan wuyanshi ya tabbatar da ana lafiya ne ba za ta taɓa iya hakan ba, sai yaji emptiness da
ya rasa na menene, da kyar yayi bacci bayan ya yi overdosing magungunanshi.
Ta ɓangaren ta tana so taje ɗakin amma tana tsoro, kila bai huce ba kar taje kuma ya hau ta da
faÉ—a ko ya make ta, haka ta shirya ta kwanta a kan gadonta sai ta dinga tunanin moment É—insu
na jiya sautin numfashinshi na dawo mata har heart É—inta na racing a haka bacci ya É—auketa.
Karfe goma na safen Washegari ta fito a shirye cikin half boubou da skirt na lace cream colour
da mix of dark pink yayi mata kyau sossai ta yafa pink gyale bayan dan kunne da wani zoben
gwal dake yatsanta bata wani saka acessories ba ta fito zuwa babban kitchen ta karbi abincin
su ta kai ta shirya a dining kan ta koma wurinsu jannah da Uncle ya kira mijinta ya zo ya
dauƙeta yau duk su mama ma yau za su koma gidajensu.
Shi kam tun da ya dawo Sallar asuba bacci bai É—auke shi ba yana zaune kan kujera inda kaman
nan ne wurin zamanshi a É—akin, as usual idanunshi a rufe ruf bai motsa ba har sai da Abeeha ta
kira shi a waya akan su Mama za su koma gidajensu ya miƙe ya fito suka sake mishi gaisuwa
da ban haƙuri kan suka tafi bayan sun raka su har waje, ya kalleta amma bai tsawalla kallon ba
don haushin ta har lokacin yake ji barin ma da ya kalli yadda idanunta suka zama saboda kukan
da tayi jiya Dukda ba kowa zai lura ba amma shi with a single gaze ya fahimci lids É—in are
swelled up a little.
Bai koma ciki ba motar Sulaiman ya shigo gidan sai suka isa kan kujerun da aka shirya don
hutawa a chan gefen gidan suka zauna.
"Ya dai? Na ga kaman ranka a ɓace sossai?"
Sulaiman yayi tambayar don a hankali Sulaiman É—in yayi mugun karantar shi har ma ya zama
kaman Saleem a wurinshi É—an zaman da suka yi daga aurenshi zuwa yanzu rasuwar Mammi.
"Hakane am just worried sick about one or two things."
Sulaiman ya gyara zama
"Toh fa, menene kuma?"
Nan ya bashi labarin duk abin da ya faru Sulaiman sai yayi murmushi
"Are you jealous?"
"Menene hakan?"
Yayi tambayar kaman bai san me ake nufi da kishi ba.
"Rayyan kana kishin Afeefah ne sossai kayi adu'ar sassaucin zafin kishi, anan dai zan baka laifi
Saleem ko da bai auri Afeefah ba kaman Yaya yake a wurinta sannan Saleem yana da fahimta
am very sure bai san reasons naka bane yasa ranshi ya ɓaci, shima fa mutum ne kaman kai
yana da zuciya a kirji, your words are harsh gaskiya kenan.."
Ya gyaÉ—a kai
"I know, tun jiyan i wanted to call him amma sai na bari ya huce tukuna. I just lost control tunda
ta furta wai aurena kaddara ne kalaman sun min zafi"
Dariya Sulaiman ya fara
"Kana wasa da So Surgeon General Ryan Khamis, kuma fa babu wani abin zafi a maganan nan
kishi ne kawai irin naka... Ai komai ma mukaddari ne daga Allah ta wani mawaki yace Nufin
Allah ne! HaÉ—in Allah ne ko da basa so su gani sai anyi! Ka ga kenan dole da kaddara a komai.
I'am advicing kaje ka samu Saleem ku yi resolving issue É—in nan"
"Kai! ka fa dameni da zancen kishin nan idan ma kishin ne ai ban yi laifi ba a gaban ka na cire
kuÉ—ina na biya sadaki!"
Yayi maganan da iyakan gaskiyarshi yana sake kame fuska Sulaiman yana ta dariya.
Basu jima ba ya wuce, shima ya shiga ya zari key bai ko bi ta kan abin kari ba ya fice daga
gidan kai tsaye gidan su Saleem É—in ya tafi, bai shiga ciki ba ya kirashi a waya akan yana waje
mintuna kaÉ—an sai ga Saleem É—in ya zo ya buÉ—e kofan motar ya shiga ya zauna ba tare da ya
ce komai ba.
"Ka tashi lafiya?"
Rayyan É—in ya faÉ—a, bai jira amsar Saleem ba ya É—ora da.
"Na zo ne in baka haƙuri akan abin da ya faru tsakaninmu we are not perfect in everything
sannan a zaman tare dole watarana a saɓa. A koyaushe kai ke haƙuri da ni I really respect and
appreciate you Saleem kuma ka fi karfin duk abinda kake zato a gareni! Saleem...Billahi ban
ɓoye maka wanzuwar Afeefah a gidanmu saboda son zuciya ko wata soyayya ba don har
yanzu ban sani ba shin ina sonta ko ba na sonta na dai san ban tsane ta ba"
Ya É—an yi shiru kadan kan ya cigaba
"A lokacin da muke waya da kai akan Mommy ta kore ta na ganta amma ban zaci saboda kora
ne take tsaye a kan titi ba, jin irin damuwar da ka shiga ya sa nayi deciding in koma in É—auko ta
kafin ka samu masalaha da mahaifiyarka, ko da na koma ban sameta ba a sannan aka kira ni
ba'a ga Mammi ba cikin damuwar rashin ganinta na tafi asibiti ka san halina farin sani damuwa
na ba komai bane illa kar a samu wasu su cuceta ko su zalunce ta sanin bata san gari ba. ko da
na isa asibitin sai na samu ashe ita ce ta taimaki Mammi, from there Mammi ta fara ƙaunarta
har ta mayar da ita gida ba tare da na ce musu komai akan labarinta ba Dukda na san Mammi
da su Abeeha amma ba zan so ta samu matsala a gidan yadda ta samu a naku ba, nayi tunanin
faÉ—a maka sau ba adadi ina tsoron saka ka cikin wani damuwar don na san in har ka san inda
take ba lallai ka cigaba da yiwa mahaifiyarka biyayya ba, zai iya zama ka saɓa umarnin ta
saboda mace ko kuma shaidan ya ja ka ga fushintan ta hanyar yarinyar, na bari akan daga
baya idan kayi settling komai sai na faÉ—a maka. Unfortunately abun nan ya zo ya faru
tsakaninka da ex wife É—in ka da i even called her name to your ears ka nuna baka santa ba
kana da mata..."
Daga nan ya bashi labarin duk yadda aka É—aura aurensu da Afeefah.
"Na karɓi auren ne saboda Mammi Dukda ta rokeni ya zama saboda Allah zan yi wa Afeefah
komai ko da bata nan zata samu peace of mind na cewa ta barta inda ba zata wulaƙanta ba, na
san Afeefah ce tayi adu'o'in duk da kake using na seven days a gidan mu ban damu ba saboda
na san ka cancanci fiye da hakan daga gareta, ko da ka samu lafiya kafin mu yi maganan Allah
ya kawo ajalin Mammi... Wallahi idan da za ta zaɓe ka Saleem ta tabbatar min za tayi farin ciki
a tare da kai zan iya sakinta ka aureta... Saboda burin Mammi shine ta samu farin ciki da
natsuwa a duk rayuwar da zata yi. I am terribly sorry da kalamaina na jiya i hope you forgive
and forget ban san me ya hau kaina ba."
Ya sauƙe numfashin wahala don ya gaji matuƙa da maganan, Saleem ya ɗauki ruwa dake
tsakiyar su ya buɗe mishi ya miƙa mishi sai ya karɓa ya kurba kaɗan ya mayar mishi sai suka
É—an murmusa.
"Kishi ne ya hau kanka ba komai ba"
"Ana kishi haka siddan ne? Dazu Sulaiman ya gama ranting about that!"
Saleem yayi dariya yace
"Lallai kai sabon shiga ne, ai ba'a kishi babu So irin nakan nan ma mai zafi ne ƙanwata ta ma
zuciyarnan dabaibayi ba zaka farga ba sai ka gama zurmawa saura mu saka ƙasa kawai mu
binne"
Murmushi mai sauti Ryan yayi bai ce komai ba. Saleem ya dube shi yana sauƙe numfashi
"A haƙiƙanin gaskiya nima a sadda na dawo na kwana da tunanin actions ɗina na jiya, kawai na
saka a raina cewa ban samu labarin bane ta yadda ya dace hakan ya haddasa saɓanin da
muka samu. Tun a jiyan tun da na fita daga gidanku na riga da na sakawa raina har Abada
Afeefah matsayin ta É—aya da su Samha a gareni, ban san wani irin rabo bane ya haÉ—a ku ban
san me Mammi ta hanga ba ta haÉ—a ku but i believe har karshen rayuwarku Afeefah ba zata yi
kuka da kai ba muddin ta iya tafiyar da kai! Menene burina dama?"
Ya É—an ja numfashi
"Burina ɗaya da Mammi shine ta samu rayuwa mai kyau and am very sure tunda ta karɓi auren
take zaune lafiya she accept it with all her heart and soul to na me zan damu? Abeeha... She's
so brave kalaman ta sun shigeni sossai da sossai am also sorry for what happened Ina yi muku
Fatan alkhairi i also hope and prays za ka bani daman zama É—an uwan da ba ta da shi a
rayuwarta"
Murmushi Ryan yayi ya É—ago ya kalleshi
"Anya zan amince? ai sai ku haÉ—e min kai Thats the role that Sulaiman is playing fah"
Saleem yayi dariya.
Kallon gidan Ryan yayi
"Why are you guys still here ba ku takura ba?"
Saleem ya É—an yi tsaki yana sake kallon gidan shima
"Mun takura fa kawai rasuwar nan shi yayi delaying É—ina da yanzu mun koma Nan gidannan
nawa na Malali already an gama komai maybe gobe we move out"
Kai ya gyaÉ—a suka sake hira kaÉ—an a kan aiki kan suka sallami juna Rayyan ya fice Saleem ya
koma ciki hankali kwance.
Ya dauki hanyar unguwar su kenan aka kira shi a waya ya duba ya ga uncle Musa ne, dagawa
yayi cikin ladabi suka gaisa
"Ina so dama na ganka ne Ryan idan ka samu dama ko yanzu ka zo."
"In shaa Allahu Baba gani nan zuwa"
Juya motar yayi ya nufi Unguwar sarki inda nan ne gidan uncle musan yake.
Yana zuwa ma ana kiran azahar yayi alwala suka shiga masallacin tare suka yi sallah kan suka
dawo ciki, an kawo mishi abincin rana don haka a tare suka ci kan uncle Musa ya dube shi
"Ryan ka san idan mamaci ya mutu ana so a yi gaggawar sauƙe mishi duk wani nauyi har gado,
Toh zaman dai ya kamata mu yi da Abeeha da jannah ne amma sanin kana gaba da su kuma
kai uba ne a gare su yasa na fara kiran ka, wannan takardu"
Ya miƙa mishi ya karɓa yana dubawa Dukda komai na Mammi ya sani, haka komai na su
Abeeha da jannah na wurin babansu dake hannunshi wanda Mammi ta sakar mishi yake kula
musu da shi duk ya sani.
"Mamanka ta ce in tabbatar maka ita ta baka halak malak har abada baya cikin abinda za'a
raba nata"
Da sauri ya kalli Uncle Musa.
"Rabin dukiyar ta ne fa anan"
"Eh, ta saka hannu zaka gani lawyer É—inta ya saka akwai kuma shaidu akan hakan. Ta mallaka
maka rabin abinda ta mallaka wanda gado ne daga wurin mahaifinta kyauta"
Dukda arziki baya gabanshi kyautar ya kaÉ—a shi sai yana jin sabuwar Soyayya da kuma
tsananin kewa na Mammin, idanunshi suka sauya sossai ya kalli uncle da ya sake cewa
"Wannan kuma sauran rabin abinda ta mallaka ne na su jannah shima ta ce ne in bari a
hannunka kai zaka zauna da su idan suna bukata ka basu idan sun bar maka ajiya ta tabbatar
za ka juya musu yadda ya kamata"
Karɓa yayi yana jin wani iri sossai da sossai. Da kyar ya haɗa natsuwar shi wuri guda yayi
godiya wa uncle É—in kan ya fice daga gidan ya nufo gida.
Yana parking wayanshi ya É—auki ringing ganin ogansu ne yasa yayi picking tare da saluting
maganan mintuna biyar suka yi ya sauke wayan tare da bude media group dinsu, news dake
yawo ya zubawa idanu sama da mintuna goma ba tare da ya sani ba kan yayi baya baya ya
jingina da kujera wani irin abu na tsaya mishi a tsakiyar zuciya, sossai news din ya jijjigashi
amma yana iya kokarinshi wurin ganin ya danne don in ka kula har jikinshi rawa yake sai
lumshe ido yake yana buɗewa lip dinshi na ƙasa a ɗan datse tsakankanin hakwaranshi.
Sai da ya gaji ya buÉ—e murfin motar ya fita ya nufi cikin gida, a babban parlor ya samu jannah
da Abeeha suna zaune shima ya zauna suka gaishe shi ya amsa da kulawa ya dubi jannah
"Yaushe kike shirin komawa ne kam?"
"Dama yau ne to kuma ya tafi Abuja É—azu yace in zauna kawai gobe zai dawo in ya dawo zai
biyo ya daukeni sai mu wuce gida"
Cikin girmamawa tayi magana. Ya gyaÉ—a kai
Nan ya musu bayanin gadon su tare da fitar da papers É—in ya ajiye.
Abeeha tace
"Ni dai Yaya bana bukatar rike komai a hannuna gaskiya, babu abinda ka rage mu dashi ko da
Mammi ke raye baka barta ta mana komai da kuɗinta ba don haka ka haɗa duka ka riƙe a
wurinka kawai."
Jannah ma tace
"Gaskiya nima dai babu abinda zan yi dashi a yanzu, kana min ko da nayi aure baka daina ba
shima kuma bai rageni da komai ba for now ka bar wannan a hannunka yaya"
Kai ya gyaÉ—a ya dubi Abeeha
"Gobe zan tafi wani aiki chan Gabas maso yammacin ƙasar nan ban san adadin kwanakin da
zan yi ba don haka ki duba ki rubutu duk abinda za ku bukata da safe zan kaiku shopping sai a
saya"
Godiya ta mishi da Adu'a. Ya miƙe ya nufi sashensu.
Afeefah na zaune shiru cike da tunaninshi, bai karya ba hakan ya dameta sossai har take jin
babu daaÉ—i sai tunani take ko ina ya je? Ko yana lafiya? Tsoronta ma ya sha magani? Kar
zazzabi ya dawo mishi yana ta yawo a rana duk ita kaÉ—ai dai ta yanke dole zata bashi hakuri ta
kuma fahimtar da shi ba da wani manufa ta aikata abinda ta aikata ba.
Ta miƙe zata fita wurin su Abeeha kenan shi kuma ya shigo, kallo ɗaya ya mata ya ɗan ɗauke
kai sai yayi sallama yadda zata ji ta amsa tare da cewa
"Sannu da dawowa Ya Saraki"
Ya É—an lumshe ido ya buÉ—e kan ya ce
"Yauwa"
Daga haka ya wuceta ya nufi É—akin shi bai bata daman magana ba kenan har yanzu fushi yake,
jiki a sanyaye ta fice wurin su Abeehar anan take jin labarin wai zai tafi wani Assignment gobe
ba lallai ya dawo kusa ba jikinta ya sake yin sanyi ƙwarai har bayan Magrib bata san me zata yi
ba, luckily ko da ta ajiye mishi abincin dare ya ci.
Bayan tayi isha ta gama shiryawa cikin cotton Light blue riga da wando dogo na kayan bacci ta
ɗora navy blue hijabinta har ƙasa ta nufi ɗakinshi don ta yanke zuwa kawai ta bashi hakuri kar
ya tafi yana fushi da ita.
🖤Gureenjoh🖤
HAIHUWA DA HANJI
(A True life story)
Fatima Muhammad Gurin
(Gureenjoh)
Wattpad-Gureenjo6763
Arewabooks-Gureenjoh
ADABI WRITERS ASSOCIATION
*FREE BOOK*
*Tsakani da Allah ba ni da abin da zan ce da masoya sai na gode, ina ganin irin ƙaunar ku
gareni. Na gode kwarai da gwalagwalan adu'o'inku. Ta Baba Makkah kin faranta min kwarai, sai
masoyinka na haƙiƙa ne zai tuna da kai a gaban ɗakin Allah har yayi maka Adu'a da Fatan
alkhairi don haka wannan Page É—in sadaukarwa ce gareki Allah ya bar zumunci har a aljannah,
Allah duk ya dube mu ya biya mana buƙatunmu na alkhairi.*
*43*
Ta ɗan jima tsaye jikin ƙofan tana tunanin ta shiga ne ko kar ta shiga? Da kyar ta tattaro
kuzarinta ta É—an yi knocking kan ta tura kofar ta shiga gabanta na tsananta faÉ—uwa.
Hasken É—akin ba shi da wani yawa don haka tsaf take kallonshi zaune tsakiyar gado jingine da
pillow gabanshi system ne yana kallo, idanu ya É—an zuba mata tana tahowa a hankali har ta isa
jikin gadon ta É—ayan side É—in inda shi kuma yana jingine ne da side É—in da ya saba kwanciya.
Muryarta na fita a hankali cikin tsoron faÉ—an shi ta shiga furta
"Na na..zo ne mu yi sallama na ji wai za kayi tafiya, kuma ina so ne in baka haƙuri wlh ban san
kalmar ba zata yi maka daaɗi ba. Don Allah kayi haƙuri."
Tun da ta shigo ya ɗauke kanshi daga kan system ɗin ya zuba mata ido sauƙar muryarta a
kunnuwanshi ya sa Ya ɗan lumshe idanun ya sake buɗewa a kanta. chan ƙasan muryarshi yace
"Zo nan."
Bai cigaba da kallonta ba sai ya mayar da idanunshi kan system dake aiki gabanshi wanda kallo
yake na wani horror movie, tun da yayi shirin kwanciya tunaninta ya so ya dameshi sam shi bai
ma san me yake damunshi ba daga dan kusancin da suka samu kwana biyu shikenan kuma sai
a ta shiga lokacin hutawarshi ta hana shi hutawa da tunaninta? System ya jawo ya fara kallon
dole sai kuma Allah ya jefo ta.
A hankali ta hau gadon kamshinta na dukan shi har yana jin bugun zuciyarshi na sauya wa.
Idanunshi ya kai ga kallonta ganin tana chan nesa ya ce
"Matso nan"
Ya taɓa gefenshi, a ɗan tsorace cikin bugun zuciya ta matsa tana dana sanin zuwanta ɗakin
don ji take kaman zuciyarta za ta fito daga madaukarta don tsabar bugu, inda hannunshi yake
ta matsa kaman an ce ta kalli fuskan computern aka nuno wani abin tsoro da ya firgigita don ta
tsani film mai abin tsoro za ta gudu ya riƙo tsintsiyar hannunta babu zato sai gata bisa kirjinshi
daga gefen kafadanshi ya mayar da hannunshi na wurin ta bayanta inda tayi saurin binne kanta
a kirjin nashi sihirtaccen kamshin shi na sake shiganta yana ƙara bugun zuciyarta, baya baya
yayi ya jingina da gadon yana sake kara kusantar da ita jikinshi.
Bai ce komai ba ya cigaba da kallon yayinda tayi shiru kawai tana sauraran bugun zuciyarshi,
sun kwashe sama da awa guda a haka ko da ya gama ya É—an É—ago ta zai yi magana kawai ya
ga tayi bacci, ya san kwanakin tana ƙoƙari kuma bata samun isashen bacci yadda baya yi itama
bata yi, gwara ma shi da safe ya kan taɓa amma ita ko da safen baya ganin tana yi sai zirga
zirga.
Hijabin ya zare mata ya jefar ya zubawa fuskarta idanu yana kallo, bai san me ya riƙe shi a
fuskar ba ya dai tabbatarwa kanshi da she's Drop-dead gorgous wanda bai taɓa fahimtar fuskar
ba irin yau, kallon natsuwa yake binta dashi da ya rasa dalili a hankali ya furta
"what's wrong with me?"
Ya kai hannunshi É—aya yana jin zuciyarshi na pounding har sound É—in na iya shiga
kunnuwanshi...
Yana so ya kwantar da ita akan pillow amma sai ya ji ba zai iya ba don haka ya gyara
kwanciyarshi ya gyara mata ta yadda rabin jikinta na a nashi ya lumshe idanu ga mamakinshi
tunaninta ya cigaba da yi Dukda gata jikinshi da kyar bacci ya É—auke shi.
Basu farka ba har aka shiga masallaci suratul Fatiha da ake karantawa shi ya farkar dasu duk
su biyu lokaci ɗaya ta yi saurin Miƙewa zaune tana ɗan matsawa kanta ƙasa, ya ɗan kalleta
kadan yadda tayi kaman wacce aka kama tana sata ya sa ya É—an yi murmushin da bai fito ba ya
sauka ya shige toilet, hijabinta ta ɗauka ta sauƙa ta gudu.
A bayi ta tsaya tana kallon kanta, bacci fa ta sake yi a jikinshi comfortably? Wayyoo Allah ta
ayyana a ranta tana dafa zuciyarta, gashinta da tayi parking cikin messy burn ribbon É—in ya fice
bata ma san ta baro a É—akin ba, da kyar ta haÉ—a tunaninta wuri guda tayi alwala tazo tayi sallah
ta kwanta a wurin, sai Eight ta fito a shirye cikin Abaya Grey da yayi mata kyau sossai hula ne a
kanta kai tsaye taje ta dubo abincin taga wanda zai iya ci ne ta kwaso ta kawo sashen nasu ta
shirya dining ta saka turaren wuta a parlorn don a gyare yake tsaff yana kyalli ta juya zata koma
ya buÉ—e kofa ya fito, kallonshi tayi yana sanye da wani Army Green riga tare Black wando da ya
amshe shi, rigan ya kama shi ya fitar da kirarshi sossai bai mishi ruwa ba sam sai taji wani
nauyin shi ya rufeta ta mayar da kanta ƙasa, ya kalleta ya ɗan shafa gashin kanshi kaman zai yi
magana kuma sai ya nufi dining kawai.
Binshi tayi sai da ya zauna tace
"Ina kwana?"
"Kin tashi lafiya?"
Ya bata amsa ko numfashi bai bari ta ƙarasa saukewa ba idanunshi na akan fuskarta sai kawar
da ido take daga kallonshi wanda hakan ma dariya ya bashi amma ko a fuska bai nuna alamu
ba, ta haÉ—a mishi abin kari da yau English breakfast suka yi a gidan ta tura mishi, bata so ta tafi
tayi laifi don haka ta É—auki omlet É—aya ta haÉ—a tea ta ja kujerar da take zama chan nesa dashi ta
zauna tana karyawa, bai ce mata komai ba itama bata ce ba.
Bayan ya gama ya miƙe ya koma ɗaki ta bishi da kallo tana ɗan taɓe baki mutum kaman
hawainiya, tattare wurin tayi tsaf kaman ba'a ci abinci yanzu ba ta wuce nata É—akin, monday za
ta fara waec don haka dole ta fara duba takarda kafin taje ta faÉ—i sai ta fara lalabo takardunsu
na makaranta ta É—auko wayanta ta fara bincike akan past questions da take son fara dubawa.
Shi kam kusan sai da ya gama haɗa duk abin da zai buƙata lokaci lokaci yana dan daakatawa
ya tafi nazari kaman wanda baya kaunar tafiyar kan ya É—auki keyn mota da wallet É—in shi ya fito
sanye da wata White sneakers da ta sake fito da shigar tashi idanunshi ya rufe da baƙar space
sai ya zama kaman wani model ya san kan wanka ba laifi, a babban parlor ya samu su Abeeha
suna ganinshi kuwa suka miƙe tsaye don dama sun shirya saboda sun sanshi yadda ya washi
jira sai dai a jira shi...
Har sun nufi kofa yace
"Ina take?"
Duk tsayuwa suka yi Abeeha na so ta tambayi ita wa amma fuskar shi da ba'a sake ba yasa
tace
"Afeefah ina ga bata san da ita za'a yi fitan ba bari na ƙirata"
Ta ƙarasa tana nufan sashensu a ranta tana adu'ar Allah ya sa ita yake nufi kafin ya fara mata
masifa, sai taga ya fice daga parlorn jannah ta bi bayanshi.
Zaune ta sameta hankalinta kwance
"Tashi maza É—auki gyalen ki muje"
"Ina za mu?"
"Shopping Ya Rayyan ya riga ya fita yi sauri kafin ya hasala"
"amma ni ba abinda nake bukata fa Adda Abee..."
"Ke wlh tunda ya neme ki sai kin je, gwara kin tashi"
Bata fuska tayi don wlh bata son zuwa ko ina, kai Abeeha ta gyaÉ—a
"Ki same mu a mota kuma ki yi sauri"
Miƙewa tayi ta chanza Abayar jikinta zuwa wani orange, ta saka farin takalmi tayi wrapping
kanta da farin Jersey veil ta É—auki wayanta ta nufi waje har lokacin fuskarta ba'a sake ba.
Tun da ta fito ya zuba mata idanu ta cikin glassses na idanunshi yana kallo, a fuskarta ya tsayar
da idanu yadda take dan ɓata ran ya bi jikinta da kallo Dukda ko ina a rufe yake sai da ya ɗan ji
wani iri, tafiyar ta kaman tana rausaya Dukda ita sauri take, bai ji haushi ba idan ma zai yi
judging wani gefen na zuciyar tashi akan gaskiya zai ce he enjoyed the walking ba tare da ya
san dalili ba, tuni su Abeeha suna baya dole ta buÉ—e gaba ta shiga ya É—an lumshe idanu saboda
kamshinta da ya shige shi ya buÉ—e tare da tada motar ya fice daga gidan.
Su Abeeha sun zaci ba zasu wuce shopping malls da suka saba zuwa ba na nan kusa kusa ko
market square ko barnawa shopping complex sai suka ga ya miƙa ma yayi chan unguwar rimi
bai tsaya ko ina ba sai Kaduna Galaxy Mall yayi parking suka sauƙa tana shirin sauƙa yace
"Ki ji!"
Ta É—an kalleshi tana dawowa ta zauna
"Na'am Ya Saraki?"
Ya zare glass É—in ya kalleta sai ta kawar da kanta, kaman zai mata gargadi akan wannan
sarakin da take faÉ—a take motsa mishi zuciya sai ya fasa.
"Kina ɓata rai babu abin da kike buƙata ne?"
Ta Yi mamakin yadda ya karance ta Dukda tunda suka fito babu wanda yayi magana a cikinsu.
"Kin min shiru ina magana?"
Ya faÉ—a ba da faÉ—a ba...
"A'a akwai, za mu fara waec monday akwai abubuwan da nake buƙata na makaranta sai da na
fito na tuna"
Bayan ta gama bayanin kuma sai ya mata shiru ta É—an sake haÉ—e fuska shi baya son shiru
amma ya ƙware a yi wa mutane banza, sauƙa tayi ranta ba daaɗi su Abeeha har sun shige ita
yanzu ina ta nufa ba zuwa ta taɓa yi ba ganin a kyau da tsarin shi ya bambanta da wanda suke
zuwa da Abeeha.
Wayanta ta duba don ta ƙira Abeehar ma ta ji inda suke su tafi da ita taga katin ta ya kare ta
É—an yi taku biyu tana furta
"Oh! ashe ba ni ma da katin, to yanzu ina zan yi??"
A karye tayi maganan tana sauƙe hannunta ƙasa, babu zato babu tsammani taji ya sanya
hannunshi na dama cikin nata na hagu ya gimtse, da sauri ta kalleshi kaman ba shi ba dole ta
fara Binshi sun zaga sossai har wurin kayan makaranta ta É—auki duk abinda take so suka dawo
wurin turaruka ya É—auki turarenshi ita bata bukatar komai don kayan aurenta duk babu abinda
ma ya dauki hanyar ƙarewa suna nan set set, a wurin biya suka ga su Abeeha.
Abeeha da ta hange su daga nesa ta taɓa jannah
"Addah Jannah kalli ki ga...!"
Jannah ta waiga tana kallonsu suna tahowa sun yi matuƙar kyau da dacewa fiye da yadda baki
zai fasalta, da sauri ta É—aga wayanta ta fara musu hoto tana murmushi ganin zai É—agota tayi
saurin sauƙe wayan tana cewa Abeeha
"haƙiƙa ba ƙaramin sa'a Afeefah ta taka ba, samun soyayyar namiji irin Ya Rayyan....Ya Allah i
just can't imagine.."
With so much excitment tayi maganan. Abeeha ma tace
"Wlh shima yayi dace Mata Kaman Afeefah are very rare sun dai dace kawai duk su biyun they
Look so breathtaking"
Gab da su ya saki hannunta ya zaro Atm ya biya aka hada musu komai nasu suka nufi mota,
bayan ya shiga ya kunna Ac ɗin sai yaji baya ba da iska kaman gas babu tsaki mai ƙarfi ya ja ya
kunna motar suka fice yana sauƙe glass a hankali.
Kwanciya tayi ta lumshe ido jikin kujera tana sauraron dukar da zuciyarta ke yi, hannunta da ya
riƙe throughout ta kaishi fuskarta ta shafa tana sake sniffing kamshin da ya bar mata har lokacin
tana jin softness na hannun cikin nata, bata san sun yi nisa ba sai da suka zo last danger na
É—aukar hanyar gidansu ta É—an buÉ—e idanu sai taga wasu maza a cikin napep suna kallonsu
kaman an ce ya kalli wurin ya sake jan tsaki ya miƙa hannu ya dage glass ɗin ɓangaren ta har
sama, ta É—an kalleshi bai ko kalli inda take ba ana sake su yayi kwana zuwa gida.
A yanzu bai ɓata lokaci ba don idan ya tsaya batawa zai iya makara gashi takeoff din nasu 12
ne dot. Wurinta ya fara shiga tana zaune kawai ta ganshi ta miƙe tsaye.
"Zan tafi."
Tayi mamaki kwarai don ita yana kasheta da mamaki a tsakankanin.
"Allah ya tsare ya ba da sa'a ya kuma dawo da ku lafiya."
Ya amsa da Ameen a kan lips É—in shi yana kallonta.
"Ina fata kina sane da jiya ba yau ba ne, bana son yadda kike fita school anyhow make sure kin
saka ko hijabi ko ma Abaya before going in ya so in kin isa ki cire, just focus on abin da ya kai
ki. Ki kula sossai don ina da matuƙar kishi akan abin da nake so."
Yana kai nan ya ajiye mata bundle na 1k guda biyu a kan gadon É—akin ya juya ya fita.
neman faÉ—uwa tayi ta samu wuri ta zauna tana jin kalaman nashi na dawo mata
"Kishi akan abin da yake so? Waye yake son?"
Da sauri taje gaban madubi tana kallon kanta sai ta girgiza kai ba dai ita ba kila bata ji da kyau
ba ko kuma kariyar nashi irin na ya da kanwa ne.
Jikin Window taje ta tsaya tana kallonshi yana magana da duka ma'aikatan gidan sama da
mintuna biyar kan ya shiga mota wanda ba ma dashi suka fita ba ya ja ya fice daga gidan,
saƙon Shigowar message taji ta janyo wayanta sai ta ga kati ne mai yawa aka saka mata ta
kama baki ta riƙe mamaki na so ya kasheta da ranta data ta kunna sai taga hoton da Jannah ta
É—auke su ne ta turo mata sossai hoton ya mata kyau har bata san ta saki kyakyawar murmushi
ba tana shafa fuskar wayan...
🖤Gureenjoh🖤
HAIHUWA DA HANJI
(A True life story)
Fatima Muhammad Gurin
(Gureenjoh)
Wattpad-Gureenjo6763
Arewabooks-Gureenjoh
ADABI WRITERS ASSOCIATION
*FREE BOOK*
*44*
*Laamu Fombina – Daular Gabas*
A yankin kudu maso gabashin ƙasar Arewa da bafulatani kai tsaye ke ƙira da Fombina bature
kuma ya ce Southland, an yi wata Daula mai kafaffen tarihi da kuma mulki wacce ta samo asali
tun daga jahadin ÆŠanfodiyo ta hannun É—alibinsa Muhammadu (Modibbo Adama) tsakanin
shekarar 1809-1847.
Mafi akasarin mutanen wannan yanki Fulɓe ne ko kuma a ce musu Fula suna daga cikin
manyan ƙabilun Africa musamman a yammacin nahiyar. Asalin su yana da matuƙar zurfi,
masana tarihi sun taɓa jayayya kan inda suka fito amma dai an fi karkata kan manyan ra'ayoyi
guda uku.
Ra'ayin Africa ta yamma, Yawancin masana sun ce Fulani 'yan asalin yankin
Senegal ne da Mauritania, daga nan suka bazu zuwa Nijar, Mali, Najeriya da sauran kasashe.
Ra'ayin Arewa(Africa ta Arewa), Wasu sun danganta asalin su da yankin Masar ko Sudan, suna
ganin sun shigo cikin Sahara tun
zamanin da.
Ra'ayin haÉ—e da larabawa, wasu sun danganta asalin su da haÉ—ewar 'ya'ya tsakanin mutanen
Africa da Larabawa, musamman saboda musulunci da kuma tsananin tsarkin jini da suke
riƙewa.
Gaskiya kusan duka Fulani Musulmai ne, tun da musulunci ya shiga Afirka ta Yamma ta hanyar
su.
Sun taka rawar gani wajen yaÉ—a addinin Musulunci musamman Shehu Usman dan Fodiyo
wanda ya kafa Daular Sakkwato a karni na 19.
Fulani suna da É—abi'u da al'adu na musamman da suka bambanta su:
1. Rayuwar Makiyaya (Nomadic / Pastoral
Fulani)
Mafi shahara a duniya saboda kiwon shanu.
Suna yawo daga wuri zuwa wuri suna neman ciyawa da ruwa. Wannan ya sa ake kiran su
Bororo'en.
2. Fulani Masu Zaune (Settled Fulani)
Su ne suke zaune a birane da kauyuka, suna noma, kasuwanci da neman ilimi tare da yaÉ—a ta.
Su ake kira Fulbe Na'i ko Fulbe Gidda.
3. Mutunci da Tsarkin Jini (Pulaaku)
Pulaaku shine tsarin dabi'a da falsafar
Fulani. Kuma suna da ababen sha'awa da suka kunsa wanda sun haÉ—a da:
• Munyal (hakuri)
• Semteende (kunya da ladabi)
• Hakkilo (hikima)
• Ngorgu (jarumtaka).
A ƙarƙashin wannan yanki da mutanenta suka kasance rabi da kwata Fulani (Pulaaku) aka kafa
Masarautar fombina, masarautar tana ƙarƙashin Lamidon farko ta ƙasar Modibbo har wa yau da
jininshi ne ke mulkarta, ya kasance daga ragowar daulolin Fulani da suka wanzu tun daga
Usmanu ÆŠanfodiyo.
Ƙatuwar masarauta ce da idan na tsaya misalta muku girmanta da kyawunta zamu kwana muna
abu daya bamu gama ba. Cikin Masarautar gari ne guda da ke ɗauke da ɓangarurruka daban-
daban kama daga kan Fada, ɓangaren sarki da
iyalinsa, Galadima, madaki, wambai, Turaki, Makama sarkin faÉ—a, Sarkin yaki da ma kowani
mukami mai matsayi da ƙima a sarauta, inda kowa sashinsa ke tareda nasa iyalin daidai
matsayin kowa.
Kuyangu, bayi da Fadawa ma nasu gashin kan suke ci a Sashukansu na musamman inda suke
gudanar da rayuwarsu bayan sun taso daga wurin ayyukansu na yau da kullum. Kitchen kuwa
fankacece suke dashi inda ake general abinci a kai wa kowani ɓangare nasu dukda kuwa
kowani ɓangare akwai kitchens ciki. Akwai asibiti mai zaman kanshi cikin wannan masarauta da
ma'aikata ƙwararraru akwai kuma Makaranta da aka yi musamman sabida ma'aikatan
masarautar da iyalansu dake amfanuwa.
Kodayaushe kashigo Masarautar za ka samu ko wani ɓangare ana hada-hada ana kai kawo.
Fadawa na fada, kuyangu da bayi na wuraren ayyukansu, Dogaraye na aikin ba wa Masarautar
tsaro dare da rana ayayinda Masu Masarautar daukansu ke aiki ka'in da na'in wurin ganin sun
kawo cigaba a Masarautar da al'umman gari baki daya.
A zamanin nan da Garkuwa da mutane ya zama ruwan dare a wasu yankunan, abu ne da kan
tada hankali kuma matsala ce ga kowani zamantakewa da tsaro, babu ƙabila ko yare, babu
namiji ko mace, babu babba bare yaro haka ta shigo cikin wannan Daula ta Fulani ta kutsa kai
har cikin masarautar saboda an wayi gari da tashin hankalin garkuwa da Ƴa ɗaya tilo da
LaamiÉ—o Muhammadu Modibbo ya mallaka a wannan duniyar.
Wannan matsala ta saka LaamiÉ—o girgiza har ta kai yana tuna wani al'amari da ya faru a chan
baya da ya haddasa ciwon da yake fama da shi a tsaitsaye shekara da shekaru tashi,
kasancewar shi nagartaccen sarki, Laamiɗo Mutum ne wanda ya gina al'umma mai gwaɓi,
mutum ne da kowa ke rububin ganinshi don agajinshi, Mutum ne da kowa ke son haɗa alaƙa
dashi don Arzikinsa. Kyawawan halayensa ya sa ya zamana kowa ya shiga jimami a tare dashi
hakan kuma ya ba da gudummawar Gomnati na tura manyan ƙwararrarun sojoji don aiki akan
wannan lamari.
Ko da Shigowarsu cikin masarautar a Motocinsu saboda an fara isar da su fada ne domin su
huta su kuma fara bincike daga tushe, Rayyan ne ya zama na ƙarshe wanda ya buɗe murfin
motar sanye yake da full khaki na sojoji fuskar nan kaman ko yaushe a matuƙar haɗe Dukda ma
idanunshi masu É—aukar hankali da kuma karan hancinshi ne ya bayyana kasancewar akwai
facemask maƙale a fuskar tashi, yana ajiye ƙafa kan daɓen ƙasan masarautar Wani irin guguwa
mai ƙarfin gaske da ƙura ya fara tashi a take wani kalar sautin kuka marar daaɗin ji ya karaɗe
kunnuwan ahalin masarautar har ya kai ga gigita su.
"BOÆŠEJO!"
Kusan shine sunan da bayi, dogarai da kuyangi ke ta ambata a ruÉ—e, BOÆŠEJO wata macijiyace
na gado wacce take da shekaru sama da É—ari tana kuma rayuwa a cikin wannan masarauta
kaman laƙani ce na wannan masarauta kuma BOƊJO bata kuka babu dalili ta kan yi sau ɗaya
idan yayi tsanani sau biyu a kowani bayan lokaci mai tsawo. Kasancewarta Jajazir a jiki da
idanu masu firgici da banda sarki ko magajin sarki babu mai iya arba da ita ya wanye lafiya ya
sa aka saka mata suna BOÆŠEJO dake nufin kalar JA.
Wasu da ba ma su taɓa jin irin wannan kukan mai firgici da tayar da hankali haɗe da ƙura mai
tsananin duhu ba duk sun ruÉ—e, a take manyan fada suka ba da umurni mai girma na rufe
kowacce kofofin masarautar kar kowa ya fita akwai matsala, abin mamaki BOÆŠEJO na yin shiru
sansanin bai kai ga watsewa ba wani irin kiÉ—an Serewo (Algaita), Tambin (Ganguna) Da Hoddu
(kalangu da sarewa) masu mafisar ƙarfi da daaɗi suka shiga tashi cike da sautin da idan ka ji ka
san wannan ba dai mutum ke yi da baki ba, sojojin duk da yau ne karon su na farko a irin
wannan yanayin sun yi tunanin ma sumame ne ko wani abu don kukan BOÆŠEJO babu
biladaman da ba zai kaÉ—awa Æ´ar hanji ba.
Shi kam baya ya koma ya jingina da motar tare da lumshe ido kunnuwanshi na jiye mishi irin
rububin da ake da umurnin da sarkin gida ke bayarwa na a binciko duk wani baƙo da ya shigo
masarautar a yau ana son ganinshi a faÉ—a matukar namiji ne da gaggawa umurnin LaamiÉ—o ne,
a take fadar ta zama babu shiga babu fita.
Wambai ne ya tuna da su don kusan aikin wambai kenan karbar baƙi da kulawa da al'amuran
masarauta da sauri ya taho wurin shugabar tafiyar wanda General ne kuma abokin aiki ne ga
Rayyan ba wai shugabanshi ba, hannu ya bashi suka gaisa yana bashi hakurin abin da ya faru
da yadda aka manta dasu, General É—in yace
"Ranka shi dade ai mu ba ƙaramin tsorata muka yi ba da wannan al'amari mun zaci sumame ne
ake shirin kawowa hanyar sanarwar taku kenan!"
Wambai na murmushi mai nauyi da ma'ana mai tarin yawa yace
"Wannan kuka da kuka ji na macijiyar gadon wannan masarauta ce ta kan yi kukan nan a duk
ranar da aka haifi Ciroma wato magajin sarki, haka ma wannan kiÉ—an kalangun kayan kida ne
da suke zaune sama da shekara da shekaru da kansu suke buga kansu a duk ranar da aka
haifi ciroman wannan masarauta."
Yana musu iso suka fara takawa zuwa ciki tunda ƙurar ya lafa sossai General ɗin yace
"Toh Masha Allah, an samu ƙaruwa kenan?"
"Ko kuma nesan da muka jima cikin tsumayi ta matso kusa ba, bismillah ku zauna za'a kawo
muku ruwa"
Zama suka yi bai ba General din damar sake magana ba ya fice.
LaamiÉ—o dake tsaye har yanzu tun fara kukan BOÆŠEJO ne jiri ya kwashe shi ya tafi zai faÉ—i a
sadda Sarkin ƙofa ya zo ya tabbatar da ba baƙin da suka shigo masarautar a wannan lokacin
Galadima yayi saurin tare shi.
"Allah rene (Allah ya baka kariya) bi a hankali, Sannu!"
"Galadima ka fa ji kukan BOÆŠEJO ka ji kalangu taya za su yi motsi a banza tsawon shekaru
talatin da É—aya kenan basu yi kuka ba, dole ku je ku nema min Ciroma wlh shi ne!"
Dukda a hankali yake maganan kusan kowa a fadan na ji don sun yi tsittt ne, sun san ba lafiya
ya cika ba a kwanakin sannan rabon da yayi dogon magana haka tun da aka sanar da shi ɓatan
Gimbiya Aissatou(Aisha, na yi pronouncing yadda Fulani suke pronouncing ne).
Turaki ne da aikinshi ya zama ba sarki shawara yace
"Allah sene (Allah ya yalwataka da farin ciki) ko za'a bincika cikin baƙin sojoji da suka taho
wannan ƙasa tamu? Don da alama baƙin cikinmu ne ke gab da yayewa."
Tsam ya miƙe a take dogaran da suke tsaye gefen hagu da damanshi suka fara jefa kirarin
"Gyaaaaraaa kintsi da kyau..! Taka lafiya mai talakawa"
"wambai kaini wurinsu"
"Allah ya baka yawan rai ba za'a yi ƙir...!"
Hannu kawai ya É—aga mishi, a take manyan fada da duk suke tsaye suka rufa musu baya don
tuni wambai ya shiga gaba.
Yalwataccen parlor ne mai cike da kayan alatu na sarautar zamani, an cika gabansu da tarin
kayan itacuwa da ma ababen alfarma har da su ɓiradam ɗanyen tatsa, sun yi nisa da ci amma
shi kam yana zaune ne kawai idanunshi zube a wuri guda, fuskarnan tayi ja idan ka zuba mishi
idanu za ka fahimci baya cikin natsuwarshi don karfin hali ne ya ajiye shi wurin.
"Gyaaara kintsi da kyau..!"
Da ke ta ƙarato su ne yasa suka fahimci kaman mai martaban ne da karan kanshi ya taho
hakan ya sa duk suka miƙe tsaye, General ɗin ne ya taɓa Rayyan hakan ya sa shima ya miƙe
ya mayar da kanshi ƙasa yana jin yadda zuciyarshi ke tseren gudu, Laamiɗo ya shigo parlorn
tuni kwarjini da girman matsayinshi ya saka su sake natsuwa, tsabar yadda yake jin a lokacin
zai iya mutuwa idan bai yi ido huÉ—u da cikar Muradin shi ba binsu ya fara yi É—aya bayan É—aya
yana kallon fuskokin su, jikinshi har rawa yake idanunshi sun cika tafff da kwallar marari da
bege.
A lokacin da ya iso kan Rayyan ya tsaya kawai yana kallon irin tsawon Fulani da yake dashi,
bambancin ya gina jikinshi hakan ya É—an rage mishi tsawon kaÉ—an amma Dukda haka ya ma
kere Lamidon da kaÉ—an.
"Babana!"
LaamiÉ—o Ya faÉ—a cikin wani karyayyen murya yana kai hannunshi ya dafa kafaÉ—ar Rayyan da ya
saka shi dolen É—ago idanunshi da suka cika da kwallah masu zafi suka haÉ—a idanu.
Jiri ne ya kwashi LaamiÉ—o ya tafi kaman zai faÉ—i tsabar wani abu da ya dake shi sai Rayyan yayi
saurin sa hannu ya tare shi yana É—aga idanunshi sama don hana hawayen shi zuba amma
inaaa sun riga sun taho, LaamiÉ—o ya fusge facemask din dake fuskarshi cikin harshen fulatanci
yake cewa
"Babana kaine? Da gaske kai ne a gabana? Sameeer..."
Za ka iya fahimtar ruÉ—u, farin ciki da tarin damuwa duka a cikin Muryar tashi.
A hankali Rayyan ya ce
"Abeey!"
Sai LaamiÉ—on ya rungumeshi shi kuwa ya É—ora kanshi a kan kafaÉ—ar shi yana barin hawayen
shi zuba cikin wani irin yanayi marar fasaltuwa, tuni jama'ar parlorn suka fara fita sai da aka
watse tas aka bar su su biyu kachal rungume da juna, kan kace kobo kunnuwan masarauta sun
fara aiki inda sashe sashe, bayi bayi, kuyangi kuyangi ake ta zancen dawowar Ciroma Sameer
Muhammad Modibbo cikin masarautar bayan shekaru ashirin da shidda da ɓacewar shi.
Babbar macece mai cike da wani irin izza da ƙasaita da kana kallonta sai gabanka ya faɗi, bata
da fara'a ko na miskala zarratin haka komanta tana yi ne cikin isa da wani irin mulki da ta saba
shimfiÉ—awa cikin masarautar shekaru da dama, Fulani Adama kenan uwargida ga LaamiÉ—o
kuma uwar É—akin duk wata mace da zata shigo gidan ko a mata ko a kwarkwara tana da irin
izza da har kan ba mutane tsoro, ga kafaffen zuciya da salo salo wurin shimfida mulkin son rai
da samun duniya a tafin hannu.
Jeka-ka-dawo take a tsararren falon nata, sanye cikin shigan alfarma da kamshi na musamman
tun kukan BOÆŠEJO na farko taji kaman an tsire mata zuciya ne hakan yasa ta kasa zaune ta
kasa tsaye, duk wani abinda zai hana Fulani Adama natsuwa ba ƙarami bane, Shigowar
Amintacciyarta da gudu yasa tayi hanzarin Juyowa tana zuba mata firgitattun idanunta masu
kaÉ—a 'yar hanji.
"Allah ya ja kwanan Fulanin LaamiÉ—o, farin ciki masarauta, Uwargida kuma hasken zuciyar
LaamiÉ—o uwar yarima da yardar..."
"Bana son ɓata lokaci Menene ya faru? An yi baƙi ne? Me ke shirin faruwa ne Balki?"
"Gobara daga kogi ranki shi dade..."
Baya baya tayi ta kai zaune cikin tsadaddun kujerunta hannayenta duk biyu dafe da Goshi.
A chan wani tsararren sashe cikin wasu kujerun alfarma Fulani FaÉ—imatu ce zaune fuskarta
Jajazir idanunta har sun jirkice Dukda tsaf take cikin shiga ta alfarma da ƙawa kallo ɗaya za ka
yi mata ka san cewa ba ta cikin natsuwar ta kukan BOƊEJO kaman ƙara mata damuwa cikin
damuwarta yayi don ta gigice ta kasa zaune ta kasa tsaye a sadda Kuyangarta ta shigo ta zube
ƙasa
"Allah ya kara miki lafiya da yawan rai, Allah ya kare gabanki da bayanki"
"Menene kande? Me ke faruwa?"
"GIZO BA YA HANA RUWA GUDU...! Zakarar da Allah ya nufa da chara..."
Dafe zuciyarta tayi tana fashewa da rikitaccen kuka mai tsuma rai.
🖤Gureenjoh🖤
HAIHUWA DA HANJI
(A True life story)
Fatima Muhammad Gurin
(Gureenjoh)
Wattpad-Gureenjo6763
Arewabooks-Gureenjoh
ADABI WRITERS ASSOCIATION
*FREE BOOK*
*45*
"Babana...Sameer ka gane ni?"
LaamiÉ—o ya faÉ—a har lokacin gani yake kaman mafarkin da ya saba ne yana motsawa zai iya
ganin Rayyan ya ɓace, rauninshi ne ke sake bayyana a gaban dattijon wanda dama tun yaranta
shi ne mutum É—aya jal dake ganin hawayen shi sai Baba Maudo wanda ke matsayin Galadima
kuma É—an uwa na jini ga mahaifiyarshi.
Hannun Abeey ya riƙe ya zaunar da shi tare da yunkurawa ya kai ƙasa kan gwiwowinshi
gabanshi kanshi a ƙasa a hankali ya furta
"A gafarceni taƙawa"
Riƙo hannunshi Abeey yayi ya ɗago shi ya zaunar dashi gefenshi yana jefar da duk wani
formalities na sarki don a yanzu uba yake.
"Da gaske ne kenan..! Kai ne da gaske nake gani Sameer? Ina ka shiga ka manta da asali? Me
ya fitar da kai daga cikinmu ya nesanta ka? Wani irin rayuwa kayi a wani wurin da babu mu har
zuwa wannan lokaci Sameer? Na yi nema! Na yi nema har yau ban fidda ran ganinka ba ashe
da rabon sake ganinka kafin in bar duniya!"
Yana maganan yana ta duba jikinshi ko zai ga wani alamun wahalar rayuwa amma ya ganshi
fes kuma fresh don ko daga tafin hannunshi da ya riƙe ya fahimci yana cikin hutu da jin daaɗi
Dukda haka sai da ya tambaya zamanshi Uba mai cike da yunwar ganin É—an shi namiji É—aya tilo
da ya mallaka a duniya.
"Abeey ka kwantar da hankalinka don Allah, ni ne! Sameer ne a idanunka ba zan jefar da sunan
da ka yi min yanka ba sai dai Rayyan ne a idanun duniya wanda shi ne sunan da hasken
rayuwata kuma wacce ba ni da kamarta a wannan duniya ta bani... Abeey Aisha tana chan
hannun azzalumai shine abin da ya kawo mu duk wannan za mu yi daga baya na tabbatar
Abokan aikina suna chan suna jira na"
Kallonshi kawai Abeey ke yi yadda yake jera maganan da rashin cikakken fara'a mai tsanani da
ya kamata ya gani a fuskarshi.
"Aisha na da muhimmanci kwarai kasancewarta mace cikin miyagu amma kai ma kana da
muhimmanci Ciroma... Mahaifiyark.."
Da sauri ya katse shi
"Abeey...!"
Sai yayi shiru don bai saba katse maganan mai martaba ba, duk jimawanshi wani wurin an haife
shi ne cikin masarautar kuma ya tashi da horo mai tsanani da kuma jarumta na asalin 'ya'yan
sarki waenda ake musu mafarkin sarauta a gaba don haka yana sane da komai bai manta ba.
"Abeeyy ka yi haƙuri ka gafarceni ka bar maganarta for a while ina cikin farin cikin ganinka cikin
koshin lafiya, adu'ar da nake ta yi kenan duk ranar da zan riskeka in riskeka cikin lafiya da
kuzari in ga wannan farin cikin dake shimfide bisa kamilallayar fuskarka, ka haske ni da
annurinka, ka cika ni da kwarjininka ka min hirar tarihin Fulani masarautunsu da ma
al'adunsu..."
Muryarshi ne ke rawa ya mayar da kanshi ƙasa yana datse harshe don kuka ne ke zuwa mishi
mai ciwo, shi kaÉ—ai ya san irin raÉ—aÉ—in kewar mahaifinshi da yayi a wannan duniyar, shi kadai
ya san irin halin da ya shiga na rashin shi kusa dashi ba tare da ya bari damuwar shi ya fita fili
ba don ya san shi aka fi cuta, an cutar mishi da mahaifi ainun da baya tunanin zai iya yafe wa.
Mai martaba ma hawaye yake zubarwa, amma fahimtar wani abu da yayi ya sa bai iya sake
magana ba suka yi shiru. Chan da É—an jimawa ya ce
"Aisha! Ta ya ta ɓace Abeey?"
"Makaranta suka tafi da 'yar uwarta Zara'u akan suna da jarabawa dake ƙaratowa za su kai
yammaci Dukda sun san ban yardar musu kaiwa dare a waje ba Fulani Adama ce ta ba su go
ahead a kan za su dawo ba tare da na sani ba hakan ya sa suka yi dare har wannan al'amari ya
faru anan yankin makarantar tasu dayake daga su sai Driver shima a raunane yake yana asibiti
kwance"
"In shaa Allahu za mu tabbatar babu abinda ya same ta, lafiya za ta fito."
"Ku tabbatar da hakan Ciroma. Allah ya taimaka amma za ka dawo ko?"
Ya kalli Abeey.
"Zan dawo ko don saboda kai Abeey..."
Kallonshi kawai Mai martaba yake yi yana ayyana abubuwa masu dumbin yawa a ranshi. Ya
girgiza kai
"Ba saboda ni ba dole ka dawo Sameer saboda al'ummarka da suke jiranka dole ka dawo
saboda ba zan iya cigaba da nesanta da kai ba tunda Alhamdulillah kana raye cikin koshin
lafiya."
Ba tare da ya É—aga kai ba ya ce a hankali
"Wannan magana ce mai tsawo ranka ya dade ya kuma ba ka yawan rai, ina da family ina da
kanne da suka dogara da ni sannan ina da Mata duk basu san wanene ni ba..."
Murmushi mai ciwo mai martaba ke yi duk Sameer ya taka waennan matsayi har ya kai ga
Auren wata a waje ba Zara'u da aka bashi tun daga ranar da aka haife ta ba, yana da wasu
zuri'ar da suka zama priority a gareshi da har bai iya ɓoye wa ba hakan ya sosa mishi rai ainun
haƙiƙa ba zai bar duk abin da ya nesanta shi da Sameer ya sha a banza ba, Sameer dake da
sunan babanshi amma yake ture sunan yake makala Rayyan bayan ga asalinshi, da kyar ya
hadiye wani abu mai É—aci
"Ina jiranka Ciroma, zan jira har ka dawo da ƙanwar ka cikin gidan nan daga nan za mu ɗora"
Kai Rayyan ya gyaɗa suka sake yin shiru na tsawon lokaci kan mai martaba ya miƙe tsaye
Rayyan ma ya miƙe kanshi ƙasa ya furta
"Allah ya baka yawan rai ya ƙara maka lafiya da imani!"
Kai kawai mai martaba ya gyaÉ—a bai ce komai ba ya fice dogarai dake bakin kofa suka fara
zabga kirari har ya wuce.
Rayyan ya É—auki facemask É—in shi ya mayar, ya zare bakin shade dake gefen aljihunshi ya saka
ya gyara hulanshi ya fito daga parlorn, yana bayyana a waje hadimai da dogarai suka shiga
zubewa.
"Allah hokke jam (May Allah give you peace) Ciroma Sameer É—an LaamiÉ—o jikar Modibbo...
Girman ɗa gado, Ɗan sarkin da ya san Allah, Ɗan sarkin da yayi haƙuri Ɗan jarumi gadon
jarumta Ruwan sanyi mai dafa ganda... Murucin kan dutse baka fito ba sai da ka shirya Gobara
daga kogi magani naka Allah, Damisa ba'ai maka kallon banza, sarauta dole in babu ku gari ya
watseee.."
Sossai ya sake kamewa wannan jinin na sake bayyana kanshi da kanshi, takawa yake kaman
ba zai tafi ba cikin sarauta har ya isa ga motar sauran sojojin da suke jiran shi da kallon
mamakin al'amarinshi musamman waenda suka san shi su ke Binshi bai cewa kowa komai ba
daga hadiman har sojojin ya shiga ya zauna suka fice daga fadar.
Kai tsaye mai martaba sashen Fulani FaÉ—imatu ya nufa dayawa suna mamaki don baya zuwa
sassan matan sai dai su suje amma sun mishi uzuri kasancewar sun san iyaye ne da suke cikin
murnar bayyanuwar É—an su namiji tilo, wasu daga cikin gulmammu har an fara tambaye
tambayen Meyasa bai je ga mahaifiyarshi kuma ya bar masarautar? Wasu na ganin barin shi da
LaamiÉ—o yayi ya tafi ganganci ne.
Tana zaune har lokacin kuka take ta fara jin sanarwan zuwan mai martaba sashen ta, da sauri
ta miƙe tsaye daidai yana shigowa ya tsaya ya zuba mata idanu yana kallonta chan ya ce
"FaÉ—imatu Me kika aikata?"
Kanta ta mayar ƙasa tana sake sakin kuka cike da tarin nadama da kunyar mai martaba.
"Ashe kukan nan da kike shekara da shekaru ba na rashin É—a bane sai na yunkurin lalata
rayuwarshi? Me na miki da kika zaɓi azabtar da ni da hannayenki Faɗimatu? Me na miki da kika
zaɓi gani na cikin ciwo da azabar rashin ɗa tsawon shekaru ashirin da shidda? Me kika mishi da
ko magananki baya ƙaunar ya ji anyi? Kin san zuciyar bafulatanin da aka hasala?? Kin san yara
nawa ne da zuciya ya dibe su suka tafi tafiya na har Abada sun ki waiwayan baya? Ba sai na
faÉ—a miki ba kin san wanene Bafulatanin mutum... Amma ina so ki san abu É—aya na gode Allah
da ya amsa min adu'ar dawo min da Sameer ba zan taɓa mishi dole ya kalleki ba idan baya
so..alhakin mu da kika dauka kuma wannan tsakanin ki da rabbissamawati"
Sossai take kuka tana girgiza kai, mai martaba masoyinta ne in ta ce bai kaunaceta ya É—aga
darajar ta cikin mata da kwakwarayenshi ba ta yi ƙarya, duk wata kulawa ya bata ya tausaya
mata dukda yana cikin damuwan shima amma ya rarrasheta a lokacin da yake tunanin za ta fi
shi jin zafin ɓatan danta, kwarai ta fishi ita da bata san inda yayi ba bayan nan ita da alhakin shi
ke maƙale a wuyanta na tsawon wannan shekarun zuciyarta bai huta ba, idanunta basu tsagaita
da zubar kwallah ba.
"Ranka ya daÉ—e ka gafarceni, ka tsaya ka saurari uzurina don Allah..."
ÆŠaga mata hannu yayi
"Ba ki da uzuri FaÉ—imatu baki dashi..! Babu uzurin da zai wanke bakin cikin da nake ciki a yanzu
you were the last person i've expected that from, am very disappointed..."
Katsewa magananshi yayi jin sanarwar isowar Fulani Adama, da kuka ta shigo
"Alhamdulillah! Alhamdulillah!! Allah mun gode maka ya Allah da ka share mana hawaye ka
amsa adu'ar mu ashe Magaji na raye? Ashe muna da rabon sake ganawa? Mai martaba
sashen ka nayi don wannan babban abin murna ne sai ake sanar min kana nan ashe... Ina
yake? Ina Sameer in ga yadda ya sauya ya zama mutum cikakke?"
Har yanzu idanunshi da suka sauya suna kan Fulani FaÉ—imatu kan ya janye ya kalli Fulani
Adama yace
"Alhamdulillah yana nan lafiya Fulani, a yanzu ya tafi abinda ya kawo shi wato tseratar da
kanwanshi."
"Alhamdulillah! Ashe rayuwa ya inganta Soja ne ashe?"
"A sojojin ma ba laga-laga ba. Na bar ku lafiya"
Yana kai nan ya juya ya fice.
Ta kalli Fulani FaÉ—imatu tana murmushi
"Barka na taya ki murna FaÉ—imatu"
"Ai ke ce uwa a gareshi Fulani ke ya kamata mu taya murna.."
"Kwarai kuwa! Gashi ya zo a gaɓar da matarshi ma ta isa aure gwara da muka jinkirta aurar da
zarah ashe alƙawari zai cika"
Kai ta gyaÉ—a bata iya tace komai ba don a gigice take, ta sake murmushi tana ta kallonta kan ta
juya ta fita, zubewa Fulani FaÉ—imatu tayi kan kujera bata zaci lamarin zai kai haka ba, kuruciya
ne da buƙatar uwa na ganin ta ba abinda ta haifa kariya ya sa ta aikata bata zaci abin zai zama
mata haka ba sam, tun daga ranar take nadama har yau.
Ko motsi bata sake yi ba sai ga Fulani Aminatou itama murna ta zo tayi mata bata kai ga fita ba
sai ga Fulani Salimah itama ta mata murna duk amsawa take amma tana sane da wanda ya kai
ciki da wanda bai kai ba Dukda duk yanzu ba sune gabanta ba.
Duk rubibin da ake
Madaki da Makama suna zaune ne tamkar a kan ƙaya fata kawai suke sarki ya ce ya sallame
su su samu su keɓe aiko Galadima na sanar da tashin Fada kai tsaye su biyun ganawa suka
nemi yi da Fulani Adama.
"Balki ki sanar da su ba yanzu ba da kifi ya riga ya ruɓe su bari sai ya daina wari za mu
tattauna"
Da sauri amintacciyarta bilki ta amsa
"an gama Allah ya baki yawan rai"
Tana kai nan ta fice taje ta kai saƙon suka kalli juna suka juya suka tafi babu mai uhm bare uhm
uhm.
****
Shi kam Rayyan komai ya watsar suka shiga kokarin ganin sun tsara yadda za su kubutar da su
Aishatu cike da hikima irin ta squad É—in tasu na musamman da aka turo wannan aiki, lokaci
lokaci ya kan yi tsaki kaÉ—an har dai aka gama kuma akwai alamun nasara don sun samu haske
sossai daga ƙiran da aka yi na biyu.
Bayan sun gama zaman ya nufi É—akinshi kai tsaye wanka yayi saboda gajiyar da yake ji ainun
jikinshi, ya fito ya shirya cikin kayan baccinshi ya nufi gadon ya kai kwance kaman jira ya fara jin
ta jikinshi, emptiness da bai san na menene ba ke ratsa shi ji yake gadon yayi mishi faɗi ƙwarai,
shafa cikinshi yayi da bai ci komai ba tun safe da tana nan da ta fara mishi puppy face tana
roƙon shi ya ci wani abu wane cikinta ne tsintar kanshi yayi da ɗan murmusawa a fili yace
"Yarinyar ta cika tsoro"
Yana maganan yana tuna idanunta in ta ji muryarshi ko idan yayi mata tsawa. Daga karshe da
ya ga ba zai iya bacci ba dole ya tashi ya sha coffee ya koma ya kwanta ya janyo wayanshi ya
tafi numbern ta da ya karɓa da safe kawai ya yanke bin shawarar zuciyarshi na ko muryarta ne
yaji ya danna wa ƙira.
Tana kwance tun tuni ko shirin bacci bata yi ba, takardu ne gabanta amma ta kasa karatu sai
tunaninshi take ya je lafiya? Ya ci abinci? Sun fara aikin? Ta rasa natsuwa duk adu'arta na
salollin yinin akan Allah ya kare mata shi ne ya bashi sa'a a duk abinda ya sanya gaba, tana
nan tana juye juye a kan gadon sai ga ƙiran shi bata san Layin ba don bata dashi.
"Waye ke kirana ƙarfe sha ɗaya?"
Tayi tambayar tana sake kallon lokaci kaman ba zata É—aga ba ta zo dagawa ya yanke, ya sake
ƙira karo na biyu dole ta ɗaga ta makala a kunne bata yi magana ba shima sai bai yi ba suka yi
shiru suna sauraron numfashin juna, chan tace
"Waye ne? Meyasa ake kira a irin wannan lokaci?"
Ya tsinci kanshi da wani kalar murmushin da bai fi second biyu ba, ashe ta iya tsiwa shi ne take
yi wa puppy eyes na tsoro.
"Idan babu abin faÉ—a zan kashe don ina da abin yi..."
"Ba ki iya sallama ba?"
Daram gabanta ya faɗi tayi saurin Miƙewa zaune tana sake riƙe wayan da kyau Ya Saraki ne,
tuna abin da ta faÉ—a da farko yasa tayi saurin cewa
"Kayi haƙuri ban san kai ba ne Assalamu Alaikum warahmatullah"
Ya amsa sallamar
"Me kike yi ba ki yi bacci ba har wannan lokaci?"
Ta kalli takardun gabanta tana mamakin yadda ya ƙirata har yana ɗan magana Dukda maganan
kaman za'a yi kaman ba za'a yi ba yake jefowa.
"Abu nake yi ne shiyasa ban kwanta ba."
Shiru yayi idanunshi a lumshe yana sauraron muryarta.
"Abin babu suna?"
"Karatu!"
Ta amsa suka É—an yi shiru ita dai har hannayenta sun haÉ—a zufa nervousness da kyar ta fitar da
abin da ke ranta kan yayi magana ta ce
"ka isa lafiya?"
BuÉ—e idanunshi yayi ya zubawa wuri guda Mammi ce ke faÉ—o mishi a duk sadda motsin yarinyar
nan ya shige shi sai ya rasa Meyasa yake tuna Mammi, yanzu haka abinda yaji Allah ne kadai
ya sani. Mammi ce kaÉ—ai duk inda zai je sai ta tabbatar da isan shi lafiya, ita ce yake yawan jin
wannan kalmar daga Bakinta ba wata ba.
Jin shirun yayi yawa tace
"Hello!"
"Lafiya! Ki ajiye abin da duk kike ki kwanta"
Ta amsa da Toh
"Kar ki kashe!"
Chak ta tsaya da yanke call din ya É—an kausasa murya
"Ke kika ƙira ne da za ki kashe?"
Ta haÉ—e lips É—inta shi dai ba'a yi mishi ba za'a zauna dashi a wanye lafiya ba.
"Afuwan"
Ta faɗa chan ƙasa a hankali da ya saka shi sake lumshe idanu.
Miƙewa tayi da wayan a kunne ta tattare duk takardun ta saka a speaker kar yayi magana bata
ji ba ta shiga uku ta chanza zuwa kayan bacci ta kashe wuta taje ta hau gado.
"Na gama."
Duk motsinta yana ji.
"Ba kya alwala ne idan za ki yi baccin?"
"Manta wa nayi!"
Bai ce komai ba taje tayi alwalan ta zo ta zauna tayi Adu'a ta shafa duk yana jinta kan ta kwanta
tayi shiru.
Bacci ne ya ci karfin idanunta don bata saba hira ba saboda bata yin baccin da safe ko rana ta
riga ta saba tun chan. Cikin Muryar bacci tace
"Sai da safe ya Saraki"
Ya ja numfashi a hankali don Muryar ya isa inda bai kamata ya isa ba, yana sauraron komai har
tayi bacci kan ya katse ƙiran ya ajiye wayan kan kirjinshi da kyar baccin ya ɗauke shi cike da
tunanunnuka.
🖤Gureenjoh🖤
HAIHUWA DA HANJI
(A True life story)
Fatima Muhammad Gurin
(Gureenjoh)
Wattpad-Gureenjo6763
Arewabooks-Gureenjoh
ADABI WRITERS ASSOCIATION
*FREE BOOK*
*Masu tambayar daga farko a yanzu za ku yi haƙuri ku jira a ƙarasa don abin da ya saura babu
yawa sossai a haÉ—a doc ayi distributing gabaÉ—aya because pages almost 50 ba abu bane mai
sauki in ta forwarding please bare with me*
*46*
Kwanakin da suka biyo baya sun zo mishi da tarin ayyuka haÉ—e da zirga-zirga ta yadda ma wani
daji suka koma suka yi camping don dai ganin an ceto su Aisha a hannun waennan Ƴan
garkuwa da mutane, inda yake ko service babu hakan ya sa ya manta rabon da su yi waya ko
da Abeeha ce kuwa bare Afeefah da sau biyu ya taɓa kiranta gashi har an ci tsawon sati uku
suna abu ɗaya ba su ƙare ba, sun yi namijin kokari duka team ɗin wanda suka hada har da
taimakon wasu airforce, polisawa da 'yan sa kai da ake cewa Hunters a cikin sati na huÉ—un
suka samu gagarumar nasara bayan kubutar dasu sun kubutar da dayawa daga cikin waenda
abin ya ritsa dasu kuma sun samu nasarar hallaka dayawa daga cikin miyagun.
A yau da ya kasance Juma'a suka iso cikin garin Fombina zuwa masarauta, kai tsaye aka musu
iso don an san da isowarsu kuma an shirya musu tarba na musamman, ko bai nuna ya san
Aishan ba ma itama daga ita har Zara da yake a tsorace suke har lokacin ba tantance kowa
suke yi ba sai da suka gansu tsakiyar masarauta kai tsaye sashen Uwar É—akinsu Fulani Adama
aka yi dasu ta fito ta rungumesu tana hamdala nan suka saki kukan da ya gama cin su a rai.
Shi kam Rayyan na cikin baƙin fada inda sarki ya nemi da su koma masaukinsu su huta kafin ya
gana da su ko zuwa dare don yanzu yana ta samun baƙin taya murna daga kananan
hukumominshi da na shuwagabannin rugagen dake kewaye da Daular fombina, Rayyan ya
tashi zai bi bayansu LaamiÉ—o yayi gyaran murya ya furta
"Ciroma!"
Chak ya tsaya, ya dawo da baya ya koma zaune
"Allah ya baka yawan rai!"
"Bisa tsarin umurnin da na yanke, ka shigo kenan Sarkin gida zai maka rakiya zuwa sashenka
an tanadar maka duk wani abin da zaka buƙata ka je ka huta iyayenka na bukatar ganawa da
kai."
Da wani irin hanzari ya ɗago ya kalli mai martaba sai kuma ya mayar da idanun ƙasa ganin duk
idanun manyan fada na a kanshi, Miƙewa yayi
"Na barku lafiya!"
Daga haka ya fice sarkin gida yayi saurin mara mishi baya, a wajen ma dogarai shidda ya gani
sun rufa mishi baya kuma ya san sune aka yi assigning don kare lafiyarshi haka kawai yaji
kaman an takura shi.