Sashe ne na musamman tsararre ya ji furnitures da komai da komai masu tsada da É—aukar ido
Haihuwa-Da-Hanji-Complete Hausa Novel · about 43 min read
amma shi bai wani burgeshi ba tunda ba tatse É—in shi bane, É—akuna huÉ—u ne a sashen ya nufi
wanda sarkin gida ya nuna mishi shine nashi ya shige ba tare da ya ce mishi komai ba yayinda
sauran dogaran suka kafe a bakin mashigar sashen.
Komai kuwa akwai ko da ya buÉ—e wardrobe kaya ne kala kala kawai gasu nan, manya da
kananu Dukda ya san idan ba a cikin sashenshi ba a yanzu saka kananun kaya ma yayi yawo
da su a cikin masarautar ya haramta mishi, kayan jikinshi ya zame ya shiga wanka ya jima
sossai kan ya fito ya shirya cikin karamin three quater baka da wata karamar riga fara ta kama
shi ta fitar da surarshi na cikakke kuma karfaffen namiji, wayanshi ya zara ya fito parlor sai ya
samu an cika dining É—in da kuloli na alfarma wanda ya san abinci ne ciki.
Gyaran murya yayi da hanzari dogarin dake dab kofa ya faɗo ciki ya zube ƙasa
"Allah ya ja da zamanin Ciroman fombina, Allah ya kare gabanka da bayanka ubangidana, gaba
salamun baya salamun naka faÉ—a ne namu cikawa...."
Hannu ya É—aga mishi
"Daga ina aka kawo wannan?"
Ya jefa tambayar yana É—ora kafa É—aya kan É—aya a lokaci daya yana dan karkaÉ—awa idanunshi
zube a kan screen É—in wayanshi
"kuyangin Uwar magajin sarki ne suka shigo dashi ranka ya dade...."
"Ku tattara ku fitar min, daga yanzu ban amince a shigo min da abincin ko wani sashe ba don
ba na buƙata!"
Cikin ba da umarni yayi magana hakan ya sa dogarin sake zubewa
"An gama sadaukin maza..!"
Da wuri yaje ya fara tattare wa shi kam yana zaune shiru don ya gwada Layin Afeefah bai shiga
ba na Abeeha kira daya ya mata bata É—aga ba kuma bai sake kiran ba.
Damuwar shi yadda mai martaba ya ba da umarnin dawowanshi kenan ya san ba zai taba
amincewa ya tafi ba amma kuma idan ya zauna kaman bai yi adalci ba, bai kamata kawai su
Uncle Musa su ji cewa ya dawo gida ba dole yana bukatar komawa da su su san asalinshi ya
tattauna da su da tsara yadda za'a tafiyar da rayuwar su Abeeha da yake jin banda aure babu
wanda ya isa ya ce zai karbi riƙon Abeehar don kawai ya dawo gida har yanzu shi a jinin Maami
yake kallon kanshi kuma a hakan yake so ya tabbata don haka dole ne ma ya ga sarki.
Time ya kalla karfe tara ne kwata kwata da mintuna ashirin, Dukda baccin da ya tarar mishi dole
yaje ya ga sarki ya san karfe goma zai koma turakarshi don fara shirin tafiya masallaci, Miƙewa
ya yi ya koma É—aki ya shirya cikin wasu navy blue kaftan da ya sha É—inki irin na sarauta, ya saka
hular da ta dace da kayan ya zura takalmi ya fito hannshi riƙe da waya amma sai ya tattaresu
ya goya a baya ya fice daga sashen dogaran na ganinshi suka rufu za su bi shi ya juyo ya kalli
shugabansu.
"Sunanka?"
"GaabÉ—o ranka ya dade" (Joy yake nufi)
"sauran su zauna kai ka biyo ni"
Yana kai nan ya juya da sauri GaabÉ—o ya bishi har turakar mai martaba duk inda ya ratsa
hadimai za su zube suna kwasar gaisuwa kai kawai yake É—aga musu, sai da aka sanar da
isowarshi kan ya shiga, ya ci sa'a mai martabar ma na son ganinshi da kallo yake ta Binshi har
ya zauna a ƙasa kaman yadda me martaba ke zaune cikin shimfida na alfarma ya kishingida da
tun tun.
"Abeey barka da wannan lokaci"
"Barka dai Ciroma, na san ka ji hukunci na kuma kana tunanin bai maka daaÉ—i ba amma abin
da zan iya cewa kenan Sameer ba zan bari ko kusa ka sake subuce min ba, Kukan BOÆŠEJO
da ma sautin kalangun gado sun isa su tabbatar maka da cewa kai ne mai jiran gado"
Numfashi ya ɗan sauƙe yace a hankali
"Abeey ka yi haƙuri da abin da zan faɗa ba zan saɓa umarninka bane amma zuri'ar da na ajiye
a chan sun fi karfin na sanar da su cewa na dawo nan a waya, É—iyar su ta zame min uwa da
uban da na rasa a rayuwata tsawon shekaru ashirin da shidda bata taɓa gajiyawa da hidimata
ba, bata taɓa min kallon banza ko Harara da sunan tsana ko kyara ba, ta gatanta ni ta fifitani
fiye da komai da ta mallaka a duniya ciki har da miji da 'ya'yan cikinta, Abeey duk yadda zan
fasalta maka irin son da Mammi tayi min ɓata baki ne duk kuma ta yi bata san ni waye ba har
sai da take kwance a gadon mutuwarta a haka roƙona tayi da in dawo in samu farin cikin da na
rasa, in dawo in ji uzurin...." Sai bai ce komai ba ya duƙar da kai.
Hadiye abin da ya taso mishi yayi kan ya cigaba
"Ban shirya dawowan ba na riski labarin ɓatan Aisha bayan ma ƙiran da shugabanmu yayi min
na ina cikin team da aka yi assigning wannan aiki na taho ne ba da shirin dawowa b.."
"Muhammad Sameer"
LaamiÉ—o ya kirashi runtse ido yayi don ya san bai amince bane.
"Ka ba ni labarin abinda ya faru daga barinku gidan nan da mahaifiyarka, na dai san ta nemi
izinin tafiya chan mambila wurin dangin mahaifiyarta kuma na bata izini da driver da kuma
amintacciyar Kuyangarta sai labari marar daaɗi aka dawo min dashi da sunan ka ɓace a
tsaunukan mambila an neme ka an rasa na kwashe tsawon shekaru ban bar kowani hukuma
sun huta ba da neman ka har wasu suka zartar da cewa ka mutu ni ban yarda ba hakan ya sa a
kullum nake Adu'a duk juma'a nake sadaka duk goman karshe na kan manta kaina ina rokar
maka kariya da nasara a duk inda kake da Fatan Allah ya bayyana min kai ya tsare maka
imaninka me ya faru? Meyasa daga kalamanka na yarda Ammienka na da hannu dumu dumu
akan abin da ya faru?"
Kanshi na a ƙasa ya shiga magana kana jin ɗaci a saman harshenshi a kuma hankali yake
maganan
"Abeey bayan mun yi muku sallama mun bar nan tafiya ne mai nisan gaske muka dauka ba tare
da na san inda muka nufa ba, na taɓa zuwa mambila sau ɗaya don haka inda muka nufa bai
min kama da hanyar ba, idan nayi bacci na gaji na farka na tambayi Ammie har yanzu bamu isa
ba sai ta mayar da ni jikinta ta rungume tace har yanzu da saura ban sani ba ashe nesanta ni
take da asalina, nesanta ni take da inda na fi wayo da kuma farin cikina duk ku biyu, yamma ne
sossai muka isa inda ban sani ba hatta yaren su kaÉ—an kaÉ—an nake ji shima saboda akwai wasu
kuyangai dake yi anan ina sha'awar iya yaruka na saka su a gaba ina koyo, ko da ta saka driver
tsayawa kuka take yi ta bani ƙullin kayan marmari da abinci waenda basa lalacewa da wuri cikin
guzurinmu tace in riƙe, muka sauka muka bar driver da Kuyangarta Kande a mota mun yi tafiya
sossai har muka kawo gefen wani juji da babu hada hadar mutane sossai ta kalleni.
"Ka yi haƙuri ɗana ina sonka amma dole ta sa zan rabu da kai babu yadda na iya!"
A karye na ce mata
"Ammie Meyasa tunda muka fito kike kuka? Meyasa za mu rabu? Me muke yi anan?"
Ta ja numfashi tana share hawayen dake kara gangara tace mini
"Nan shine inda na ji ya kwanta min ka cigaba da rayuwa, ka yi aiki kaman na jaruman maza ka
nema da kanka ka samu har ka tsaya da kafafunka, idan da rabon mu gana watarana za mu
gana amma a yanzu ka cire cewa kai ɗan sarki ne jikan sarki, ka jingine ka taɓa sanina ko
mahaifinka, ka manta ka taɓa ko da amsa suna Ciroma Sameer ka samu sabuwar rayuwa zan
maka sdu'a ba zan gaji ba amma daga yau ka gama zaman masarauta..."
Hankalina ya tashi da kalaman ta na rikice ina tambayarta
"Meyasa Ammie? Me yasa zan manta ku? Meyasa zan manta Abeey?"
"Saboda Dole ne Sameer!"
Ta daka min tsawar da bata taba min irinshi ba Dukda na razana kuma kuka ba ya daga cikin
al'amarina ban san na fashe da kuka ba na riƙo hannayenta ina roƙonta kar ta bar ni anan ban
san kowa ba, kar ta bar ni anan ba zan iya rayuwa ba Ammie ta zame hannunta ta tureni har na
faɗi na rarrafa ba tare da na damu ba na rike kafarta ina kuka sossai da roƙonta ta tafi da ni
amma ce min tayi
"Ko a mafarki ka biyo baya na ba zan taɓa yafe maka ba Sameer!"
Baya baya nayi na zube a ƙasa a zaune ina kallonta har ta ɓace min, na ji na tsani duniyar na ji
na tsani kowa da komai kuma a lokacin zuciyata ta kafe Abeey na ji ba zan iya sake yi mata
kuka ba tunda bata so na ta tsaneni, babu abin da yafi kona min rai irin bolar dake gangana nan
uwata tace min in ci gaba da rayuwa, nan fa ta zaɓa min. A inda ta barni anan na zauna har
dare ban motsa ba dare da naga karnuka na zuwa wurin cin abinci na bar musu duk abinda ta
bani don ba zan iya amfani dasu ba na koma wani gini da ba'a ƙarasa ba na zauna daga ranar
na rasa bacci na Abeeyy daga na rufe idanu kalaman ta su ke farautar numfashina....A ranar
Ammie ba rabuwa da ni kawai tayi ba ta kashe ruhi da zuciyata kisa mafi muni na yi kwana biyu
ban iya cin komai ba sai ruwa kan wani almajiri ya ja ni muka fara sana'ar wanke gilasan mota
Dukda ban taɓa mishi magana ba amma shi yana min surutu sossai, kayan aikin nashi ne idan
ya gaji zai bani in yi ko kwanaki goma ba'a yi ba garin wanke gilasai mota ta kaÉ—e shi ya rasu,
kayan aikin nashi na cigaba da amfani da su har Allah ya haÉ—a ni da Mammi.."
Nan ya cigaba da bashi labarin komai da komai mai martaba banda hawaye babu abinda yake,
a lokacin da ya zo rasuwar Mammi sai da hawaye ya ziraro mishi ya sa hannu ya É—auke jijiyoyin
kanshi duk sun tashi raÉ—a raÉ—a idanunshi sun yi ja sossai da sossai.
Shiruuu ne ya ratsa parlorn fiye da mintuna biyar Abeey a hankali ya ce
"Mahaifiyarka ta cuce ni ta ci amanata Sameer! Ban san me zan yi na huce wannan zafi da
raÉ—aÉ—in da nake ji ba... Bata da uzurin bani na wannan laifi da ta aikata. Hakika na so Mammin
ka tana raye in ganta ido da ido in yi mata tarin godiya marar adadi akan kaunar da ta nuna
maka sai dai kash! Allah bai taɓa barin wani don wani yaji daaɗi ba idan ajali ya zo babu mai
ƙara ko da second guda ne sai an tafi, a yanzu ma bata ɓaci ba za mu tabbatar mun yi tarin
abubuwan alkhairi masu yawa da sunanta don ladar ya je mata a makwancinta. Allah ya musu
rahama ita da mai gidanta ya sada su da annabin rahama"
Ya amsa da ameen
"ÆŠauki ipad É—in chan ka kira min Mahaifinta video call za mu yi magana"
Ipad É—in ya dauka ya saka numbern uncle Musa ya kira aka taki sa'a yana online ya É—aga zaune
yake da Uncle sanusi da Uncle Mansur suna tattaunawa ganin fuskar Rayyan ya sa suka
yalwatu da fara'a ya shiga gaishe su yadda ya saba suka amsa kan ya mayar da fuskar kan
fuskar Abeey ba tare da ya ce komai ba.
"Assalamu Alaikum warahmatullah..."
Amsawa suka yi suna ta kallonshi kan Uncle Mansur ya zare idanu
"LaamiÉ—on Fombina mai girma Muhammadu Modibbo Aliyu.."
Duk sai lokacin suka ɗago suka shiga gaishe shi da girmamawa don shima ba ƙarami bane idan
bai girmi uncle Musa ba za su yi sa'anni. Sannan ko babu girman shekaru akwai na mulki da
sarauta mai girma.
"Na yi muku laifi ina Fatan za ku yi haƙuri ku yafe min kuma ku dubi uzurina, kaman yadda kuka
sani sunana Muhammadu Modibbo LaamiÉ—on daular kudu maso arewacin Kasar nan, a cikin
tarihina ina da ɗa namiji tilo da ya ɓace da kananun shekaru inda an yi neman duniya an rasa
shi sai satuttuka da suka wuce Allah ya bayyana min shi. Wannan yaro ba kowa bane face É—an
Æ´ar wurin ku mai rasuwa wato Rayyan a chan anan kuma Muhammadu Sameer"
"Allahu Akbar kabiran! Allah mai girma! Allah mai yadda ya so iko sai Allah ashe dama Rayyan
É—anka ne? Kai Alhamdulillah wannan abu na farin ciki ne Alhamdulillah ina ma Mamanshi na
raye ta ga wannan rana..."
Uncle Musa ke fada cikin tsananin farin ciki suka shiga taya su murnar saduwa da juna. Bayan
gama barka da jaje Mai martaba ya É—ora
"Laifin da na muku shine na sanar da ku a waya, shi Ciroman ya so ya je ne don martabarku ya
shallake haka a gareshi amma ban ba da goyon bayan hakan a yanzu ba, zai iya zuwa ziyara
ko wasu kananun al'amura da bai kamallah ba amma sai ya gama blending da dangi ina fata
hakan bai ɓata muku ba, in shaa Allah zan yi tattaki na zo da kaina na kawo ku kuga inda yake"
Uncle Musa ya ji daaɗin martaba da ƙimar da aka basu yace
"Ba sai ka zo ba ranka ya dade da kanmu za mu zo har nan mu taya ku murna in shaa Allahu"
"Sai abu na ƙarshe ban san ko za'a yi min wannan alfarma ma"
"Alfarmar ka ya wuce ka roƙa mai martaba sai dai umurni"
Uncle sanusi ya faÉ—a don basu taba zaton sarkin haka yake da saukin kai da iya mu'amala ba
Dukda tarin dukiya da irin rigar mulkin da yake ciki hakan bai hana shi yi musu magana cikin
girmamawa da fahimta ba.
"Idan za ku taho É—in ba matarshi kawai za ku taho da ita ba, za ku taho min da 'ya'yana Jannah
Da Abeeha ita jannah za ta koma ne kawai saboda auren dake kanta Abeeha kuwa ta zama
tawa aure ne zai fitar da ita daga wannan gida bi'izinillahi"
Sun gamsu suka yi godiya don martabarsu ne Dukda suna da dukiyar da zasu iya rike Abeeha
amma Mammi Rayyan ta barwa shi kuma duk inda Rayyan yake dole ta zauna dashi...
Bayan sun ajiye kan sadarwan Mai martaba LaamiÉ—o ya dubi Ciroma
"Alhamdulillah! Yanzu ka je kayi shirin juma'a idan an sauƙo akwai media team da suke son
ganawa da rundunarku da kuka ceto su Aissatou to amma su sun tafi bayan na sallamesu don
komawa ga iyalan su bayan sun bar nan shugabanku ya kira ni akan ba za su iya zama har
Washegari ba dole na wakilta Galadima ya je ya min godiya ya kuma sallamesu kai za ka
gabatar da shirin madadin ku gabaÉ—aya"
Bai so ba amma ya ya iya dole ya amsa ya yi godiya ya miƙe ya fice.
Yau suka yi finals jiya garin gigin baccinta an dauke musu wuta kuma ba'a yi rana ba don ruwa
suka samu basu samu chargy a solar ba kan a kunna gen ta tafi fitsari ta jefar da wayanta a
ruwa, ta ji haushi saboda bata da wayan kallonshi tunda ba ya kira yanzu, sossai take jin
kewanshi kaman sun wani saba sukuku ta shigo parlorn abin da ya kamata tana murnar
kamallah secondary da aka yi da kyar amma damuwar da zuciyarta ke ciki ya hana ta.
A babban parlor ta samu Abeeha na kai da komo wa tamkar ruwan cikin kwano ta kasa zaune
ta kasa tsaye ganin Afeefah yasa ta daka tsalle ta riƙo hannayenta
"Afeefah mun warke... Innalillahi wainna ilaihi rajiun khaihhh farin ciki zai kashe ni...! Afeefah
Albishirrinki.."
Cike da zumuÉ—i take maganan har jikinta na rawa
"Goro.."
Ta faÉ—a cike da mamakin me ya saka Abeehar farin ciki haka
"Afeefah kin zama Gimbiya matar yarima ko in ce Sarauniyar gobe matar Saraki... Ashe Saraki
da Mammi ke kiran Ya Rayyan ba'a banza ba? Afeefah mijinki ashe É—an babban sarki ne mai
tarin daraja da tushe me kyakyawar asali? Ashe ya Rayyan jinin sarauta ne ke yawo cikin
jikinshi? Kaii amma Allah ya isa wa mahaifin yarinyar nan da ya kalleshi yace kila ba tsatso mai
kyau aka samo shi ba ya ci mutuncin sarauta.."
Afeefah dai ta kafe a tsaye tana ta kallon Abeeha na zuba chan tace
"Anya Adda Abeeha lafiyarka kuwa? Wani irin magana kike tayi ba kan gado...? Wani yaya
Sarakin?"
*Wayyo Hannun mar'atussaliha😩
🖤Gureenjoh🖤
HAIHUWA DA HANJI
(A True life story)
Fatima Muhammad Gurin
(Gureenjoh)
Wattpad-Gureenjo6763
Arewabooks-Gureenjoh
ADABI WRITERS ASSOCIATION
*FREE BOOK*
*47*
"Yaya Rayyan mijinki nake magana a kai girlll wlh da gaske nake miki yanzun nan Baba Musa
ya ƙira ni yake cewa za mu shirya tafiya Fombina gobe sun sayi tickets already, ya ce mu shirya
kaya kuma mu kintsa komai don za mu iya É—an jimawa bamu zo kd ba."
Bata san me ta ji ba a lokacin mamaki ko tsananin farin ciki, tayi matukar taya shi murnar
reconsiling da iyayenshi don dole su É—in su ne dolenshi ko ba jima ko ba dade, ashe yana da
alaƙa da sarauta? Fuskarta cike da murmushi tace
"Alhamdulillah Allah mun gode maka"
Wani sashe na zuciyarta kuma tsoron tafiyar take don bata san me kuma zata tarar ba, hakika
ta fi jin natsuwa da kwanciyar hankali a gidan na Mammi, sai ta fara tunanin idan basu karɓeta
ba fa? Dama gashi ba sonta yake ba kila suna ce mishi ya rabu da ita zai rabu da ita a yadda ta
san tsarin gidan sarauta.
Abeeha ta wuce ta shige sashensu zuwa É—akinta ta samu bakin gado ta zauna
"Allah mai girma annabi mai dumbin daraja! Yanzu ni ce Afeefah ke da matsayin matar É—an
sarki mai daraja a wannan ƙasar? Anya? This is too good to be true... Hankali ba zai kama ba ni
Afeefah dai ta Dutsen-wai annoba Mayya ajalin duk wanda ya raɓe ki!"
Bata san adadin lokutan da ta dauka zaune a wurin ba har lokacin sanye da uniform don ba
sallah take ba bare tayi tunanin azahar da aka idar a wasu masallatan, tana nan zaune sai ga
Abeeha ta shigo da sauri bayanta jannah tana cewa
"Zo ki ga wani abu Khaihh Ya Rayyan duniya ne! Sarakin Maammi ne a gasken gaske an tashi
kaina!"
****
Yana fita daga sashen Laamiɗo Saleem ya ƙira yana tafiya a hankali suna magana sun jima
sossai suna wayan Saleem ya san komai a kanshi ya kuma taya shi murna kwarai shima kuma
yana cikin masu tahowa gobe ɗin, idanun Rayyan ne suka sauƙa akan Fulani Adama dake
tahowa hanyar sashen mai martaban, bai wuce ba sai ya tsaya yana cigaba da wayan
idanunshi na a kanta yadda take tafiya cike da izza da takama bayi da kuyangi na zube mata ko
kallo basu isheta ba É—auke ido yayi ya cewa Saleem
"Zan saka maka wani abu ka sallami duk ma'aikatan gidan ka kuma ba su haƙuri na barin aikin
ba tare da an sanar da su da wuri ba, za'a basu abin da zai ishe su jarin wata sana'ar in shaa
Allah. Please a rufe komai yadda ya kamata don zan dawo ba na zo kenan ba!"
Kalamanshi na karshen karab a kunnenta, idanu ta zuba masa Dukda kaÉ—uwar da tayi na
namijin da ta gani a gabanta ta wani sashen ta ɗan ji sanyin kalaman nashi har hakan bai ɓuya
a kan fuskarta ba sai da tayi murmushi ya sake kawar da idanu a kanta yace
"Na gode Saleem za mu yi magana please ka sanarws Sulaiman kafin na ƙira shi, Sai na ganku
a gobe É—in..."
Yana sauƙe wayan ya kalleta
"Barka da wannan lokaci Mama..!"
Ya faÉ—a da É—an murmushi mai dauke da dumbin ma'anoni.
"Ashe rai kan ga rai Sameer? Ko da shi ke na zaci ka manta da mu gabaÉ—aya ai shiyasa ban ga
ka kawo gaisuwa ba..."
Har lokacin yana dan murmushi yace
"Wani abin ake mantawa amma wani ya fi ƙarfin mantuwa Mama, zan zo in shaa Allahu ban
gama warware gajiyar aiki bane. Na bar ki lafiya"
Yana kai nan ya wuce ta GaabÉ—o ya bishi da sauri.
Da kallo ta bi bayanshi sama da mintuna biyu kan ta juya ta nufi sashen na mai martaba.
****
Saleem na sauke waya ya kalli Mommy dake zaune cikin kujera a sabon gidansu da suka dawo
komai na ciki sabo ne kuma a tsare gwanin kyau da É—aukar ido yace
"Mommy kin ji ikon Allah ko?"
Duk su Sameera idanu suka mayar kanshi mommy tace
"Me ya faru?"
"Mommy ashe Rayyan jinin sarauta ne, mahaifinshi shine LaamiÉ—on Fombina."
"Da gaske kake ko wasa?"
Cike da dumbin mamaki mommyn ta jefa mishi tambayar
"Wallahi da gaske mommy yanzu haka yana masarautar su ashe ƙanwar shi ce aka yi
kidnapping suka je suka samu sa'ar tseratar dasu, gobe duk su Afeefah za su tafi chan nima
yanzu zan sayi ticket"
"ikon Allah ikon gaske, wato a wannan duniya ka kalli mutum ne kawai baka san waye shi ba,
No wonder yake da É—abi'ar sarautar... Ikon Allah wannan abin mamaki dayawa yake"
Sadiqa tace
"Oh wa zai tuna Afeefah za ta iya sa'ar zama matar irin wannan mutumi? Yanzu mu fa ko
kallonshi sai da hanya...waye bai san irin tarin dukiyarsu, karfin mulkinsu da izzarsu ba!"
Samha tace
"Gaskiya tayi dace kam tsuntsu daga sama... Mun mata murna Allah ya cigaba da basu zaman
lafiya haÉ—e da zuri'a dayyaba"
Duk suka amsa da Ameen amma mamaki da tsoron Allah na sake rufe su rufff.
Saleem ya miƙe ya fice daga gidan.
****
Kitchen ya shiga kai tsaye bayan shigarshi sashen ya dafa indomie don babu abinda babu na
girki cikin babban kitchen É—in komai na zamani komai kuma fess kaman ka lashe don walwali, a
plate ya juyo ya dawo parlor hannunshi É—aya rike da ruwa yana gama ci ya mayar da kwanonin
ya wuce É—aki bai samu ya Kira Abeeha da ya ga missed call nata ba saboda lokacin masallaci
dake kokarin ƙurewa ya sauya kaya zuwa wasu Fararen jumpha hadadden ɗinki 'yar ciki da
babbar riga ya fita yayi kyau ainun daga ka ganshi zaka san yaro da kuÉ—i ne abokin tafiyar
manyan, ga sarautar amma ya tafi da tsantsar wayewa, ilimi da sanin kan tsarin shiga.
Hula da takalmin da ya saka duka farare fatarshi sai shining yake Dukda ma ya É—an yi duhu
kaÉ—an saboda zaman da suka yi daji amma fess yake ba ma zaka gane ba idan ba ka san shi
ba, turare ya feshe jikinshi da su kala daban daban kan ya zari wayanshi ya fito tuni duk suka
miƙe dogaran suka fara zabga mishi kirari ya ɗaga musu hannu don bai cika so ba yayi gaba
suka rufa mishi baya har mota, Dukda masallacin ma a cikin masarautar yake sai dai akwai 'yar
nisa don haka dole mota ya shiga suka yi har motoci uku da dogaran suka nufi masallaci.
Mai martaba na shiga shima ya iso ya shiga nan aka fara huduba bayan an gama tsaf aka
gabatar da sallah kaman yadda addini ya tanada aka yi adu'o'i kan aka shiga watsewa a
hankali, daga nan fada suka nufa don sarki na son ganinshi yana isa gaban manya jagoran
addini da al'ada na fulani wato LaamiÉ—o ya gabatar dashi a matsayin Ciroman Fombina kuma
Yarima Fuunange na ƙasar Fombina (Yariman Matasa) a take aka mishi rawani fari ƙal mai
kamshi wow ya fita kaman ka sace shi ciki, kasancewar wurin akwai yan jarida kala kala tuni ya
fara zagaya duniya.
Turaki ne ya karɓi abin magana ya gabatar da kanshi kan ya ce
"Ciroma alhakina ne da in sanar maka aikin matsayinka, na san ka riga ka san Ciroma shine
wanda aka É—auka matsayin É—an gado ko mai jiran gado. Yarima Fuunange wato Yariman
Matasa kuwa mun bar maka goben matasan mu ne a hannunka, kai ne shugabansu wurin
ganin sun cimma al'adar mu na fulani bisa kan daidai wato:
• Koyon Pulaaku (hakuri, ladabi, kunya, jarumta).
• Koyon sana'a ko aikin iyaye (kiwo, noma, ko fatauci).
• Haskawa a cikin al'umma ta hanyar waka, rawa, da wasan al'adu da gargajiya.
Muna yi maka Fatan alkhairi da Fatan Allah ya baka ikon sauke wannan nauyi da aka É—ora
maka"
Tuni sarkin busa ya fara busa algaita mai daaÉ—in sauraro dogarai suka shiga jefo kirari daban
daban, ya miƙe tsaye ya isa gaban mahaifinshi yayi godiya ya juya aka yi mishi rakiya da
wannan busa da sarewa
"Taaakawarka lafiya É—an sarki jikan sarki kuma uban sarkin gobe, kaaaareka Ciroman duk
duniya Yariman Matasa gaba saalaamun baya salaaamun, maƙiyanka fadawarka ɗaawisu
sarkin ado... Kyaun É—a shi ne ya gaji mahaifi kaareka Ciroma"
Abin da ake ta nanatawa kenan busa da sarewa na tashi har parlorn baƙin shi na sashenshi
inda anan zai gana da 'yan jaridar da suke jiran shi kan aikinsu.
Zama yayi ya É—ora kafa É—aya kan É—aya yana dan lumshe ido ya buÉ—e saboda gajiyar da yayi ga
chan ƙasan ranshi wani abu na mintsininshi na kewar abin da zuciyarshi ke mararin ko da
sauraron muryarta ne bai samu dama ba.
"Ranka ya daÉ—e Dukda abin da ya ajiye mu anan daban sai dai za mu fara ne da taya ka
murnan shigowa cikin ahalinka lafiya, shin me za ka iya cewa akan farin cikin da kake ciki a
yanzu? Menene kuma ya zama babban mukamin bayyanarka a wannan lokaci?"
Murya ya É—an gyara bayan yayi sallama da Fatan alkhairi kan ya furta
"Komai lokaci ne na yarda da wannan, sannan bafulatani yace Munyal deefan hayre, ko va'i fu
jippan"(mai haƙuri kan dafa dutse kuma duk nisan jifa ƙasa zai dawo)"
Amsar kenan da ya bayar, dan jaridar ya zaci zai kara wani abu amma sai ya ji shiru sai yace
"Masha Allah, Toh bari mu koma abin da ya ajiye mu anan shin menene ya faru? Ta ya aka yi
taron al'umma suna jiran ganin waennan miyagu sun kasance Fulani kaman yadda aka jima
ana yi wa Fulani kuÉ—in goro sai kuma aka haihu a ragaya?"
"Dama chan kulba ta jima tana ɓarna ana cewa jaɓa ce, bana manta ina da wani shugaba a
baya da sanadiyar kudin goro da ya mana ban taɓa furta mishi ni bafulatani bane amma ya kafa
min karar zuka ban ci mishi ba ban sha mishi ba, hakika wannan irin zato na duk bafulatani É—an
ta'adda ne ya jima yana ciwa dayawa tuwo a ƙwarya.
Ba a tuna baya in ji masu iya magana wai gyartai ya ci sarauta, a lokacin da duniya ke kwance
kabilu mabanbanta kan shiga rugagen Fulani ayi wasa tare, a ci abinci tare a sha kindirmo a
dalilin haka har zumunci ya ƙullu sai auratayya ta shiga tsakani. Da tafiya tayi tafiya a sannu
sannu aka fara kwacewa Fulani shanu da matayensu a rugage kafin komai ya ta'azzara da abin
ya fara zuwa gidan gona da kauyuka sai aka yi musu kuÉ—in goro aka far musu da kisa na kan
me uwa da wabi wanda kan iya É—arsa É—aukar fansa, dayawa daga cikin Fulanin da suke rayuwa
a daji babu ilimin addini ba na zamani, malamai babu ruwansu da kai da'awa, gomanti babu
ruwan ta da samar da ingantacciyar ruwa ko makarantun zamani, aka kwace sandunansu na
kiwo aka damƙa musu makamai saboda wani ƙudiri kawai na samun duniya a ji daaɗin cin ta da
tsinken sakace.
A hankali ringingimu suka fara yawa ta yadda zaman lafiya yayi mana ƙaura hakan ya shafi har
waenda basu ji ba basu gani ba, shi fa ɗan ta'adda bashi da ƙabila, yare, addini ko jinsi in dai
mutum bai da imani ko wanene shi bahaushe, Fulani, kanuri, yoruba ko igbo zai iya kasancewa
É—an ta'adda hasali ma ku sani ba Fulani bane suka aikata mana wannan ta'asar idan ma su ne
suka aikata wa wasu daga cikin mu a wannan karon ba su bane don ma turanci ne tsantsa a
bakin waennan, makamai da abincin da suke ci be yi yanayi da na bafulatanin ruga ba sai na
wayayyen mutum É—an zamani amma kuma idan zasu yi hausa su kan yi da sigar harshen Fulani
Lallai an jima ana ruwa ƙasa na shanyewa."
ÆŠan jaridar cike da gamsuwa yace
"Barka da Yariman Matasa Ciroman Fombina, hakika gwalagwalan kalamanka sun fi yanayi da
na hikima Allah ya sa mu gane. Toh wace hanya kake gani za'a bi wurin dakile wannan al'amari
da ya ta'azzari al'umma yake kuma lalata musu Matasa?"
"Hanyoyin masu sauƙi ne ga al'umma amma masu wuya ga gomnati don zai kawo musu cikas
amma idan al'umma suka tashi suka yi aiki a tare za'a iya maganceta cikin sauƙi, hanyoyin za
su iya haÉ—a wa da
• Karfafa tsaro da sa ido a kan dazuka da
hanyoyi.
• Ƙara horo da kayan aiki ga jami'an tsaro.
• Bincike da hukunta masu laifi cikin hanzari.
• Ƙarfafa al'umma da aikin yi ga matasa.
• Ƙarfafa haɗin kai tsakanin al'umma da hukumomi - wato tsaro na gari.
• Ƙin biyan kudin fansa - domin rage ribar garkuwa"
Yana maganan ne yana ƙirgasu da yatsun shi cikin aji da iya magana.
Kanshi duk ya ishe shi da ciwo da kyar ya gama sallama da mutane yayi la'asar ya shiga ya
kwanta yana lumshe idanunshi da suke mishi nauyi ainun duk yadda ya washi baccin yamma
bai san ya É—auke shi ba don ya sha magani ga gajiya da ya tarar mishi.
***
Idanu kawai Afeefah ke Binshi dashi tun sanar da dawowanshi hasko shi da aka yi ana mishi
sarautar Yariman Matasa da ma hirar da aka yin don live ne a manyan jaridu har international,
Fatan alkhairi da ake Binshi da shi da yabon da yake sha duk suna kallo a ipad É—in Abeehar, ita
dai ta rasa me ke damunta ma hawaye kawai ta fara tsabar feelings É—in sun zo mata daban
daban, ya mata kyau ba ƙarami ba yadda kuma ya mata ta san yayiwa yanmata dayawa, kishi
na taso mata sai kuma ta shiga damuwar anya ma a mace ya dauƙeta? Don ko ta wani ɓangare
tana ganin ita É—in ba tsararshi ba ce, tun daga tsatso, asali, ilimi, dukiya da kuma mulki ba ta
inda tayi matching da shi kenan 'yan uwanshi za su iya ware ta yadda take jin labarin gidan
sarauta?
Meyasa be neme ta ba? Sukuku haka su Abeeha suka taya ta haÉ—a kayanta akwati biyu suna
ta surutu bata ce musu komai don faÉ—uwar gaban da take fama dashi kaÉ—ai ya ishe ta, ko da
suka bar É—akin kifewa kawai tayi ta saki kukan da bata san na menene ba, ko abinci bata ci ba
tayi kuka ta koshi har bacci ya É—auketa a haka wuraren bakwai na dare.
****
Shafa fuskar ipad É—in take da ake nuno hiran tana kuka, tana ganin yadda yaronta ya girma ya
zama mutum, tana ganin tarin baiwa da nasaba da Allah yayi mishi tana jin guilt na tauye mishi
wannan hakki tun daga yaranta, tana tuna yadda ta zame kafafunta daga cikin hannunshi tana
tafiya ta barshi a bakon wurin da bai san kowa ba.... Bata ga laifinshi ba don bai zo inda take ba
itama kunyar fuskantar shi take ji kaman ta nitse.
Turo kofan aka yi aka shigo, ta É—aga kai ta kalli Aisha, Matashiyar kyakyawar yarinyar da ke
tsananin kama da Rayyan É—in ta iso gangarta
"Ammi Meyasa kike son sakawa kanki damuwa har haka? Baya nan kullum kuka da tunani ba ki
samu cikakken farin ciki ba ya dawo ma baki huta ba? Gashi shi ko ya damu dake tunda bai
tako kafarsa ya zo inda kike ba?"
"Aisha bashi da laifi don bai zo ba, baki san me na aikata mishi bane"
"ko me kika aikata mishi uwa fa uwa ce Ammi don Allah tunda ya bayyana cikin koshin lafiya
yana ci yana sha kuma babu abinda ke damunshi ki bar wannan kuka haka ki nemi natsuwar ki"
Da lallami tayi maganan, Ammie tayi murmushi mai ciwo sati uku kenan ko kallonta mai
martaba bai sake yi ba bare har yayi magana da ita, ta san tayi kuskure amma su saurare ta
kan su yanke kowani irin hukunci, tana kuma ganin Aishan bata san zafin dake cikin
Abandoning bane ta tashi gaban iyayenta da gatanta shiyasa take wannan magana amma ita ta
san dole sai an dauki lokaci Sameer zai sauƙo.
Karfe shidda ya tashi ya watsa ruwa yayi sallah kan ya kira Abeeha ta É—auka suka gaisa kan
yace
"Me kaman Muryar jannah nake ji?"
"Eh Yaya ta zo ne da shirin tafiya akan gobe kawai sai mu wuce airport daga nan"
"Me zai faru idan goben kuka haÉ—u airport da ita? Mijin yarinyar nan na sakacin barin matarshi
sakaka tana yadda take so fa... Ina Afeefahh?"
Miƙewa tayi
"Bari na kai mata tana ɓangarenku"
"Wayanta fa me ya same shi?"
"Ruwa ne ya shiga sai ya É—auke Yaya"
Bai ce komai ba chan kuma ya fara ja mata kunne akan su tabbatar basu bar komai da zai iya
lalacewa a gidan ba tana amsawa har ta tura É—akin Afeefah da sallama.
"Yaya ta yi bacci fa in tashe ta?"
Ya É—an yi shiru yana jin ba daaÉ—i kaman ya ce eh sai kuma yace
"Kyaleta..amma sallah fa?"
Sai tayi shiru ya fahimta don haka yace
"Shikenan! Da safe za mu yi magana"
Ta mishi sallama ya katse wayan ita kuma ta fice daga dakin.
🖤Gureenjoh🖤
HAIHUWA DA HANJI
(A True life story)
Fatima Muhammad Gurin
(Gureenjoh)
Wattpad-Gureenjo6763
Arewabooks-Gureenjoh
ADABI WRITERS ASSOCIATION
*FREE BOOK*
*48*
Washegari saboda tarin gajiyar da ke jikinshi bai iya ya farka ba tun bayan Sallar asuba sai
wuraren karfe sha É—aya, ko da ya kalli time ya san any moment from then sun kusa isa already
Mai martaba ya tanadar da duk motocin da za su É—auko su daga airport da ma masauki har da
abin da zasu ci kan ya zauna da su gabaÉ—aya yadda ya shirya.
Wannan dalili ya sa kawai ya shiga wanka a natse yake komai cikin sarauta da ya bi jiki, ya fito
ya shirya cikin manyan kaya mint green ne yadin mai É—an duhu ya mishi kyau ainun ya feshe
jikinshi da turaruka kan ya fito parlor sai karab idanunshi suka sauƙa akan kuyangi har biyar da
suke zaune daga chan kusurwan parlorn bai tanka su ba ya shiga kitchen ya haÉ—a tea ya fito ya
zauna tare da crossing legs nan suka fara kwasar gaisuwa kai ya gyaÉ—a kan ya yi kiran GaabÉ—o
yana cigaba da sipping tea din yana karkaɗa ƙafafu.
"Wa ya aiko su?"
"Uwargida Fulani Adama ce ranka ya dade ya baka yawan rai"
Ya amsa
Bai É—ago ba idanunshi na kan waya yace
"Duk su bani wuri ba na son ganinsu ka kuma tabbatar basu sake shigowa sashen nan ba"
Da sauri ya amsa ya juya ya kallesu tuni suka miƙe suka tafi ɗin.
Ba'a jima da tafiyan su ba sai ga kira daga mai martaba dole ya miƙe ya nufi sashenshi, a
zaune ya same shi shima ya samu wuri ya zauna ya kwashi gaisuwa
"Mamanka ta kawo min ƙararka, Meyasa ka kori kuyangin da aka tura sashenku? Ka dai san ko
kai baka buƙata matarka tana buƙatarsu saboda hidima"
"Basu yi min bane ranka ya daÉ—e"
Murmushi mai martaba yayi
"Toh shikenan zan yi magana da jakadiya sai ta kawo maka wasu"
Shi dai idan ba don mai martaban ba da ba wata da za'a tura mishi shashe amma bai ce komai
ba.
"Baƙinmu za su iya sauka cikin kowani lokaci motoci na nan suna jiransu a Airport da Wambai
da shi na wakilta ya tarbe su saboda muhimmancinsu"
Ko kan yayi magana aka fara sanarwar Shigowar Mahaifiyarshi Dukda yadda gabanshi ya faÉ—i
zuciyarshi ya chanza bugu hakan bai sa ya É—ago kai ba kanshi na kasa har ta samu wuri ta
zauna ta mayar da kanta ƙasa a hankali hawayenta ke diga bisa kan kyakyawar shimfidar
parlorn.
Shiru wurin ya É—auka kan a hankali Rayyan yace
"Barka da safiya ranki ya dade"
Bai jira amsarta ba ya miƙe zai fice tayi saurin ɗago kai tace
"Sameer...!"
Chak ya tsaya yana jin sunan har cikin ranshi sai dai yana tuna ranar da ta mishi umarnin cewa
ya manta da ya taɓa amsa wannan sunan, ya manta ya taɓa sanin su a rayuwarshi.
"Kaico na! Kaicon uwar da É—an ta ba zai iya É—aga idanu ya kalleta ba saboda wani tabo da ta
samar masa mai wuyar warkewa, Don girman Allah ka dawo ka zauna ka saurare ni, Mai
martaba ka yi min alfarmar tsayuwa ka ji uzuri na idan kai kana fushi shi yana fushi wani hali
kuke so in shiga? Wani hali kuke so ku riske ni a ciki kan tausayina ya darsu a ranku ku ji cewa
za ku iya min uzuri? Ni fa uwa ce ni kaÉ—ai na san irin zafin É—aukar ciki, rainonsa zuwa
haihuwarsa da gayya ba zan salwantar da rayuwarka ba Sameer, da gayya ba zan ƙuntaci
kaina tsawon shekarun nan ina kuka da hana kaina bacci wurin roƙon ubangiji ya baka
ingantacciyar rayuwa da farin ciki ba... Don Allah ku saurareni ko da sau É—aya ne"
Tausayinta ne ya rufe mai martaba Dukda haushin ta da har yanzu yake cike a cikin zuciyarshi,
wlh in bai ce har tunanin sakinta yayi ba yayi ƙarya kasancewarta macen da ya fara so kuma
har abada yake jin sonta daban cikin matanshi bai sa yaji cewa zai iya yafe mata abinda tayi
mishi ba amma a yanzu tausayinta ne ya fara rinjagayar fushin, kallon Rayyan da bai motsa ba
bai kuma ya dawo ya zauna ba yayi yace
"Ciroma samu wuri ka zauna"
A dole ya zauna ko sau daya bai kalleta ba don idan ya kalleta zai iya jin zafi da raÉ—aÉ—in shi ya
ƙaru kaman yanzu yake tuna yadda ta jefar dashi aka ce zuciyar yaro babu mantuwa a daidai
lokacin da yake jin daaÉ—in rayuwarshi yake kuma da gatan shi ta zabi mayar dashi marar galihu
har ma ana kallon idanunshi ana mishi zancen kila shi É—in shege ne marar uba! Idanu ya runtse
kukanta har ranshi yake ji amma baya jin kukan a matsayin uzuri.
"Ban san ta ina zan fara ba amma na san duk kun san cewa a wannan gida na sarauta aka
haife ni amma ban tashi nan ba kasancewar mahaifiyata ta rasu ina da kananun shekaru, na
koma wurin dangin mahaifiyata da zama ta yadda duk wani tuggu, makirci ko fuska biyu na
gidan sarauta ban sanshi ba, i was a care free person with a pure soul ina rayuwa kaman
kowacce mace ba tare da na san akwai alkawarin auren sarkin gobe a kaina ba kasancewar
mahaifina Galadima kuma har yanzu gidanmu ke sarautar Galadima, ina da shekaru goma sha
huÉ—u Yaya Maudo ya turo kuyangi na musamman don su fara horar dani zaman cikin
masarauta da ma abin da ya kunsa Dukda a lokacin kana da uwargida wacce itama duk jini
É—aya ne tunda daga Makama har Madaki sarautar gidansu ne kuma kun fi kusa kusa sossai don
First cousins kuke har gobe idan babu jininka wani daga gidansu yana da damar zama Sarki.
Kana kuma da Fulani Aminatou da aka baka ita daga masarautar Kamaru Dukda Na samu
maganganu masu yawa akan masarautar na shigo ne a mace ta uku da shekaru sha shida
kachal, kai shaida ne irin wahalar da na sha kafin nayi blending da rayuwar cikinta ban shekara
biyu ba ka cike mata huÉ—u, dukkanmu daga kan Fulani Adama har Fulani Salimah babu wanda
ya taɓa ko da ɓatan wata ne, dayawa sun fi damuwa da ita kasancewar ta fi mu jimawa tsawon
shekaru kusan goma kuna tare, kwatsam na samu juna biyu an yi farin ciki kwarai kuma babu
wanda bai sani ba ana kuma tattalin wannan ciki watanni biyu zuwa uku nayi mummunan
mafarki ko da na tashi ciki ya bare duk mun yi bakin ciki amma muka sallamar Allah ne ke
bayarwa kuma shi ya karba kayansa abin mamaki sai da na jera ɓari biyar a ƙasa da shekaru
biyu, abin ya dame mu duka neman taimako da adu'o'i babu abin da bama yi har na sake
samun wani cikin wanda kai ka hana mu fitar da zancen na tafi Mambila ban dawo ba sai da
jaririna É—an watanni har uku kowa yayi mamaki Dukda an zargi hakan don jimawa ta kuma an yi
ta kananun maganganu ban damu ba don zuciya É—aya na É—auki kowa, abin bakin ciki yaron nan
Aliyu na watanni biyar ya ce ga garin ku... Babu wanda ya san halin da nayi going through sama
da kai mai martaba Dukda dukkanmu mun san ba haka kawai bane amma muka bar wa Allah
kwatsam cikin Sameer ya bayyana wanda daga ni har kai bamu san da zaman cikin ba ma sai
da yayi watanni kusan biyar.
Babu irin wahalan da ban sha ba, babu irin ciwon da ban yi ba kaman ba zan rayu ba kaman
zan rayu har Allah ya kawo min shi duniya, mun yi Adu'a kuma mun sa idanu da tsaro sossai
kasancewar ranar da na haife shi kwana BOÆŠEJO tayi kukan murna Ganguna suka yini
dokawa na maraba da sarkin gobe, Dukda hakan sau uku cikin shekaru biyu na Sameer ana
poisoning É—in shi da fargaba nake kwana nake tashi, kullum damuwata kar a samu nasara a
kanshi mai martaba na rokeka sau ba adadi mu nesanta shi da masarautsr nan don ba zan juri
rasa shi ba amma haƙuri da Adu'a shi kace mu cigaba da yi ba zaka iya nesanta da shi ba,
kowa ya san Sameer ya taso ne kaifi ɗaya ga zuciya da jarumta, tun yana ƙarami ya san
menene sarauta kuma ya san makiya da masoya Dukda haka bai tsira ba yana da shekaru
huÉ—u ya ci poison da ya kwashi wattani tara bai san wanene a kanshi ba har mun fidda
tsammani Allah ya sauko mishi da waraka ya farka, tsakani da Allah tun daga sannan na saka a
raina cewa zan nemi hanyar bullewa don samun ya tsira da rayuwarshi, a haka na yanke kaishi
ƙasar Hausawa na san namiji ne zai iya rayuwa kuma zan dawo in ta mishi Adu'a har karshen
numfashi na.
Wannan decision da na yanke daga ni sai Drivern da ya kaini wanda kusan amintaccen gidan
mu ne da kuma kuyangata Kande da na san har abada ba zasu taba faÉ—a ba idan ba ni ce na
faÉ—a ba, saboda in tseratar da rayuwarshi ya sa...."
Katse ta yayi yana jin gabaÉ—aya mood dinshi na sake sauyawa zuciyarshi kaman akan wuta
"Hakan ya sa kika yi mai gabaÉ—aya da rayuwata wai HAIHUWA DA HANJI ko? Kika kashe ni da
raina Ammie... Har yau ina tambayar kaina me nayi da na chanchanci hakan ashe wannan ne
dalilin? Idan ba don mutanen kirkin da na haÉ—u dasu waenda suka zama ba ni da tamkarsu a
sanadiyarki ba zan iya cewa gwara na mutu da irin rayuwa cikin tsananin duhu da na yi a baya
don bashi da maraba da rayuwa cikin ƙabari, Mahaifina da irin darajar shi da ƙimarshi an kalleni
an ce min shege marar tsatso sau babu adadi wasu in ji wasu ban ji ba babu wanda ya fi tsaya
min sai da aka hana ni aure saboda wannan dalili, kullum ina wurin likita ban taɓa bacci lafiya
na tashi lafiya ba shine rayuwar da kike tunani ya inganta mini?"
Hawayen da ya tarar mishi a idanu ya mayar ya miƙe kawai ya fice daga sashen, Ammie dake
kuka sossai sai ji tayi mai martaba ya dafa kafaÉ—unta ya É—aga ta sama sai kawai ta rungumeshi
tana ci gaba da kuka mai tsuma rai.
"Haƙiƙa kin yi kuskure amma har da laifina ciki, na sani ina da tarin makiya na ciki da waje, na
san irin ciwon da kike ji a duk sadda kika rasa cikin ki na kuma san me kika yi facing a rasuwar
yar ki ta fari Dukda mace ce, duk jinyar da Sameer yayi tare muka yi kuka amma ban yi tunanin
nesanta ni dashi bane ba saboda bana son ya tashi a rago, na so ya san idan ya rayun ma cikin
wuya da tsanani abinda yake gabanshi zai fi hakan, na so ya goge ne barazana ya zame mishi
tamkar kuda da zai iya bugewa da tafin hannunshi ta inda na so kaina kenan na mance raÉ—aÉ—in
da uwa za ta iya ji a sadda aka cutar mata da rayuwar da, amma FaÉ—imatu da sai ki tuna da
idan rayuwarshi ya lalace fa? A wanchan wurin da kika ajiye shi zai iya zama É—an daba, ko ya
zama dan ta'adda ko dai ya faÉ—a wani mawuyacin halin da zai karar da rayuwarshi cikin mugun
yanayi wanda duk alhakin zai iya zama a kanki ne!"
"Sai da na bar wurin na fara wannan tunani mai martaba, haƙiƙa na yi ragon azanci wlh nayi
nadama daga lokacin bayan kwana biyu da dawowar mu bana iya ko runtsawa gashi kana cikin
halin ciwo da damuwa na tura driver sai dai ya dawo ya ce min bai same shi ba duk inda ya
duba bai ganshi ba, daga ranar Adu'ata ta koma a kanshi na roki Allah kar ya bar min shi
rayuwarshi ta tabarɓare na roki Allah da yakinin zai dubi zuciyata ya raya min shi har ma na
samu cikin Aisha ban yi wani farin ciki ba, itama babu wanda ya san cikinta don kowa ya san
ina jinya bana zuwa ko ina bana rabo da hijabi da chasbaha sai haihuwarta aka ji, nayi hamdala
ganinta mace barazanar ta kuma ya zo min da sauƙi. Don Allah ka gafarceni ranka ya dade! Na
tuba"
Ya ja ta suka zauna ya riƙe hannunta.
"Na yafe miki FaÉ—imatu na yafe wlh, wannan damuwa da kukan duk ya dameni ya hanani
sukuni..."
Yayi maganan yana share mata hawayen fuskanta, numfashi mai nauyi ta sauƙe.
"Saura Sameer...!"
Ta faÉ—a da wani yanayi.
"kar ki damu zai sauƙo ne a hankali, don ma rayuwarshi bata lalace ba Alhamdulillah"
"Ya baka labari?"
Kai mai martaba ya gyaÉ—a nan ya shiga bata labarin abin da ya faru kabb yadda Rayyan ya
bashi labari, tayi kuka sossai ta yi wa Mammi Adu'o'in da bata san iyaka ba, taji kaunar jannah
da Abeeha tun kafin ta gansu taji cewa sun samu uwa har sai itama kasa ya rufe mata idanu in
shaa Allahu yadda bata bar yaronta yayi maraicin uwa ba suma ba zasu yi ba.
Ta roki mai martaba da ya bata riƙon Abeeha har tayi aure ya ce
"wannan na ga yaron ki ne Fulani..! A yanzu kam bana tunanin zai amince bamu san gaba ba"
Mai martaba ya ce
"Amma ya kike tunani batun Zara'u kuwa? Kin san a yanzu da ya bayyana za'a saka mana ido
ne a jira a ga me za mu ce tunda yarinya dai ta riga ta isa aure, kina ganin zai karbi auren?"
"Ranka ya daÉ—e kai ka karance shi tun daga dawowarshi zuwa yanzu na dai san shi tun yana
ƙarami da kafiya da taurin kai ban san ko ya chanza a hakan ba amma zan roki wani alfarma,
ko da ya amince Don Allah batun jiyan matarshi da ka bani labari a barshi a rufe kaman yadda
shima ya roke ka, mu ne kadai ke da alhakin sani a yanzu labarin na fita babu kananun
maganganu da ba zaka ji ba, hakan zai iya zame mata barazana a zamanta cikin masarautar
nan"
Ya gamsu kuwa, su basu wani damu da jiyanta ba don sun yarda Mammi bata mishi zaɓen
tumun dare ba kuma tunda ta gamsu da ita suma sun gamsu.
Miƙewa Ammie tayi
"Zan je na zaɓi kuyangin da zan tura musu da kaina, kuma zan tabbatar da cewa ba'a samu
kuskure a hakan ba"
Ya gyaÉ—a kai
"Ki kwantar da hankalinki da fushin shi zai sauƙo with time musamman idan macen kirki yake
dashi na tabbatar ba zata barshi ya cigaba da fushi dake ba nima kuma ba zan barshi haka ba"
Tayi murmushi ta gyaÉ—a kai kan ta fice.
Ta isa sashen kuyangi da kanta ta nemi kande ta nuna mata jikokinta ta zaɓi guda biyu da
kuma É—iyar wata Kuyangarta sa'ade ta tura su sashen Afeefah da sunan sune nata amintattun
kuma ta tabbatar ba zasu cutar dasu ba, bata ma isa sashen ta ba ta samu labarin isowar baƙin
masu muhimmanci.
Ko da isowarsu Rayyan na tsaye a harabar masaukinsu inda ya tabbatar da komai ya tafi
yadda ya kamata kuma masauki ne mai kama da apartment da babu wanda zai takura wani
komai da komai akwai intact, hannayenshi harÉ—e a kirjinshi ya zubawa motocin idanu kawai
yana so yayi tozali da ita ne ko zai samu sassauci, yadda yaji kewanta musamman a yau da ya
san tana zuwa gareshi Allah ne kadai ya sani, kaman kuwa ta sani ita ta fara buÉ—e side É—in da
ke fuskantarshi ta sanyo kafa waje ta sauƙo, lumshe idanu yayi yana jin wani chill abu na ratsa
shi daga inda yake tsayen, sanye take da wani 2 in 1 Abaya fari da ja da ya mugun amsarta.
Gyalen mai bakin lace ne sai ta kawo lace É—in Goshi kan ta zagaye sauran ya bar
dankunnayenta Red colour fashion waje amma wuyanta ruff yake a rufe, hannunta jan jaka
haka takalmin kafarta ma Red ne sossai ya shagala da kallonta sam bata lura dashi ba, ta riƙe
kofan Jannah ta sauƙo tana tsokanarta akan ta rufa mata asiri kar a ga Gimbiya na buɗe mata
kofa a zane ta ita kuma tana dariya tayi mishi kyau kwarai zuciyarshi sai motsi yake, da kyar ya
iya kawar da kanshi ya mayar kan su Uncle Musa kan ya nufe so ba tare da ya bari ya sake
kallonta ba don urge na jin ta jikinshi yaji yana ji kallon kawai ya mishi kaÉ—an, yana so yaji
ni'imtaccen kamshinta a hancinshi, yana so yaga tana kallonshi da wannan tsoron a idanunta
mai maiƙo idan ta tara hawaye, yana so yaji tana mishi magana a karye cikin tsoro da ya zama
Shagwaɓa ko jan hankali a wurinshi amma duk ya bar wa anjima.
Fuska a sake ya tarbe su, ita kuma sai da ya isa ya É—an yi hugging Saleem kan ta yi noticing É—in
shi gabanta na ta dukan tara tara don tunda suka shigo gate É—in masarautar ta rasa natsuwa,
kanta har lokacin ya kasa dauka da ita ce matar magajin wannan masarauta mai girman gaske
da ƙawa, mai tarin kuyangi, dogarai, bayi da hadimai. Mai dumbin tarihi motocin da aka dauko
su ma kawai abin kallo ne sai dai ta ji jikinta ya sake sanyi ƙalau ganin ko kallon inda take bai yi
ba.
Gaabɗo ya kalla da sauri ya zube ƙasa
"Allah ya baka yawan rai!"
"Yi wa Uwar É—akin ka iso zuwa sashenta"
Yayi maganan yana dan kallonta sai suka haɗa idanu, kanta ta mayar ƙasa Gaabɗo ya matso
ya zube gabanta don kallon da ya mata ya faÉ—a mishi ne wacece a cikinsu.
"Lale Maraba da Uwar É—akina Zinariyar masarauta mai daraja fiye da tagulla.. Maraba da
hasken Masarauta mai haske tamkar farin wata... Sannu da isowa Gimbiyarmu Gatan Fada!
Gimbiya mai rairayi cikin gaskiya...maƙi gani sai dai ya kau da idonsa hasken rana kike hannu
baya karewa.. Allah ya ja da zamanin hasken zuciyar Ciroman duk duniya!"
Duk sai ta rikice ta rasa ma me zata ce ta gigice ta kamo hannun Abeeha ta riƙe.
"Barkanka dai!"
Ta faÉ—a cikin rawar murya, Abeeha da Jannah sai dariya suke danne wa don tuni Rayyan ya
jagoranci su Uncle sun shige ciki, yadda Afeefar duk tayi wuri wuri ne na rashin sabo ya saka su
dariya shi dai cikin ladabi yayi gaba suka bi shi wasu dogaran suka É—ibo kayakinsu har zuwa
sashenta.
Kuyangin na zaune sai ga su duk zubewa suka yi suka fara miko gaisuwa ita Afeefah kuka ne
kaÉ—ai ya rage bata yi ba, Jannah ce tace
"Wacece shugaba a cikin ku?"
Suka nuna sa'ade
"Nuna mana É—akin uwar É—akin naku tana so ta huta"
"An gama ranki shi dade"
Ta miƙe don da suka zo suka sanar da mahaifiyar Ciroma ce ta turo su Gaabɗo bai hana su ba
kuma shi ya nuna musu É—akunan masu Æangaren É—ayan suka kaita yayinda Abeeha da Jannah
suka shiga daya don su yi wanka su dan huta.
🖤Gureenjoh🖤
HAIHUWA DA HANJI
(A True life story)
Fatima Muhammad Gurin
(Gureenjoh)
Wattpad-Gureenjo6763
Arewabooks-Gureenjoh
ADABI WRITERS ASSOCIATION
*FREE BOOK*
*49*
Bayan sun yi wanka suka fito parlorn, sun samu an jere musu abinci gashi nan kala kala suka
zauna Afeefah na shirin serving ɗinsu ɗayar hadimar tayi saurin karɓa
"Ranki ya dade duk wannan ba aikin ki bane"
Shiru tayi tana kallon ikon Allah har ta gama serving ta koma chan gefe ta zauna.
"Ni kam ina ganin ikon Allah"
Sai lokacin ta tanka, Jannah tace
"Ina baki labari kina ganin wasa nake yarinya, kin san ina karanta royal stories sossai wannan
kadan kika gani"
Abeeha tace
"Ni fa in na samu irin gidan nan miƙe kafa zan ko wanka sai an min"
Jannah ta maka mata Harara
"DaaÉ—i na dake ragwantaka, kar ki sa in miki adu'ar aure inda za ki É—ora tukunya lamba goma"
"Allah ya kiyaye ya kyauta wlh"
Ita dai Afeefah dariya take musu chan tace
"Ni dai kin san Allah duk waennan abubuwan basa burgeni, ni fa na fi so in yi rayuwata ba
takura amma yanzu duk jina nake wani iri wlh"
"za ma ki saba ne yarinya"
Suna yar hirar su har suka gama suka dawo cikin parlor.
"amma fa sashen nan naku wlh ya haɗu ƙarshe, ni kayakin nan ma na kasa tantance irin
masifar tsadarsu ji kujera kaman bread tsabar taushi"
Abeeha tayi maganan Afeefah tace
"Kema kenan da kuka saba yawace yawace har kasashe ni ko da na shiga bayi sai da nayi
kauyanci, wai ni Afeefah ce cikin masarauta har wani zube min ake a ƙasa abin nan ya kasa fita
a raina"
Jannah zata yi magana sai suka ji sallama.
Dukkansu kofan suka mayar da hankali wata doguwar matsakaiciyar macece mai cike da
kamala ta shigo sanye da rantsatsen alkhyabba fari tass daga ka ganta ka ga mulki fuskarta
dauke da fara'a bayanta wasu 'yan mata biyu ne sanye da dogayen riguna suma kyakyawa don
duk ruwan Fulani garesu.
Kallo daya suka yi mata suka hangi kamanninta da Aliyu kan ma suyi magana kuyangin ta sun
zube suna kirarin da ya sa suka fahimci wacece Dukda Sameer suka ji ake kira.
Dukkansu suka yi yunkurin kaiwa kasa don gaisheta tayi saurin rike Abeeha da Afeefah ta É—ago
su kan ta É—ago jannah duk ta rungumesu
"Barkanku da zuwa 'ya'yana, Maraba lale da isowa masarautar Fombina"
"Mun gode mama"
Suka fada duka da murmushi a sadda ta sake su suka zauna tana rike da hannun Afeefah
Dukda bata ma san wacece wace ba a cikinsu amma dai duk sun kwanta mata ganinsu hakan
"Sannunku da zuwa"
Aisha ta faÉ—a suka amsa da godiya.
Zarah tace
"Sannunku dai"
Itama suka amsa.
"Ni sunana Ammi ku daina cewa Mama akwai mamar taku Fulani Adama za ku je ku kai mata
gaisuwa anjima, wannan ita ce Aishatu ƙanwar Sameer Yayanku su biyu Allah ya bani kan
ɓacewarshi sai wannan ɗiyar wurin Makama cousins suke da su Sameer ko in ce Rayyan
yadda kuka saba faÉ—a. Ina fata za ku dauke ni matsayin Uwa da kuka yi rashi gabaÉ—aya. Allah
ya gafartawa Mammi ya kai haske makwancinta"
Suka amsa da Ameen kan jannah tace
"Ni ce Jannah, wannan kuma Abeeha ita ce kanwata Ga Afeefah ita ce matar Ya Rayyan"
Ammi tayi murmushi tana kallonta
"Masha Allah, Allah ya cigaba da baku zaman lafiya ya kawo zuri'a masu albarka" kunya ya
hana Afeefah amsawa
"Da ma na kasa haƙuri ne nace dai bara na zo na ganku, Abeeha duk abin da kuke so ko ya
shige muku duhu ku kama sa'ade za ta kawo ku har inda nake ku tambayeni kun ji? Ke kam ma