← Book details Gidan Magajiya Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 3

Sashe 3

Gidan Magajiya Part 2 Complete Hausa Novel · about 6 min read

duk kan wata damuwar'sa ne matar yayi ya rasa ashe daman ya'ya rahama ne lumshe idanunsa yayi a yanzu ya ji sha'awar daman tare yake da yaran'sa sun zagaye shi suna shirme yana biye musu har muzabfar ya ƙarbi wayar be sani ba sai da ya kira sunan sa maxaiwa yayi yace

"me i saka ka karɓa muna hira....?,

cikin takaicin halin dan uwan nasa yana cikin damuwa ba zai iya faɗamai ba suyi maganar matsalar yace

"Miƙo min tayi tace ka kashe wayar baka magana....,
shiru Asif yayi muzabfar ya ci gaba da cewa Wallahi tu da na kiraka naji Muryar ka nasan ba gajiya bace Asif Kai wa kanka adalci mana inna rantsai ko kaffara bazan ba wannan damuwar da kake ciki Aysha ce sanadin shigar ka ka ƙara aure ba duka mata suka taru suka zama ɗaya ba mata nawa ne suke binka suna so ita ta samu tana wasarere da damarta uwa uba rashin haihuwa amma kullum kana jibgawa kanka aiki dan ya rage maka damuwa alhalin ba shine mafita ba ina jiye maka ranar da za awa gari A'isha ta saka maka ciwon zuciya kuma wallahi guduwa zatayi ta barka dan batayi kama da macan da za ta dauki responsible ɗin ka ba tun huri kafin kane mowa Kan ka mafita

Ajiyar zuciya ya sauke yace

"Ina jin ka ubana ci gaba....,

cikin dariya muxabfar yake cewa"ai na gama ƙi faɗi.....,

yashe wayar'sa yayi ganin muzabfar zai cika mai kunne shiga toilet yayi yayi wanka tare da ɗauro alwala da yake an fara kiran sallar magariba cikin sauri ya xura jallabiya be san lokaci yayi haka ba feshe jikinsa yayi da turare ya tsane kansa ya dauki carbi ya janyo kofar sa ya fito ganoj bedroom ɗin aysha yayi a buɗe kai da kai yayi ya fita abin mamaki motar ta bata nan kenan yaji tayi a zuciyarsa yace

kyama dawo da kafafunki ya fita daga gidan masallaci ya jufa kamar ance ya juyi da sauri mutumin dake binsa ya laɓe tasbihi ya ci gaba dayi har ya isa masallaci zama yayi kafin a kira sallahi yana salati to har aka kira sallar Isha be fito ba sai bayan an idar yayi shafa'i da huturi ya fito again har yanzu binsa ake waya ya ɗauko ya fara danne danne ya tura saƙo ya zura a aljihu ya ci gaba da tafiya wata farar mota ce ta dallemai ido saka hannu yayi ya tare saboda hasken yana neman ya kashe mai ido ba zato ba tsammani yaji harbi.....
Cikin ikon Allah be samesa ba fitowa sukai duk fuskokin su a rufe abin da basu sani ba abuja ba kamar local unguwa ce tuni ko wanne security ya fito da sauri suka shiga Mota suka fita a guje Allah ya temake ku ba a kama suba Asif kuwa ɓoyayi da yake ya yi wa jami'an tsaro waya sun tare ko wanne get ba za su iya fita ba shiga cikin gida yayi kai tsaye bedroom ɗin'sa ya shiga ya dafa kansa ya zauna ba wannan ne karon farko da aka fara akai mai hari ba amma wannan yafi muni Allah ne yayi da kwanan'sa a gaba da tuni yanzu wata maganar ake matsantawar abokanan gaba tana ƙara tsanani ya zama me mai dole ya bar wannan kujera yana son aiwatar da gaskiya amma hakan baza ta yuhuba.... ɗaukan wayar'sa yayi ya soma lalubo contact din abba Saboda tashin hankali kasa ganinsa yayi abin mamaki duk wannan karar harbin da security ɗin gidansa da suka ji ba wanda ya fito tamkar da haɗin baƙin su zamansa a cikin gidan matsala ne dan haka ya ajiye wayar akwatin sa ya dauko ya ɗauki duk wani abu me mahimmanci da briefcase ɗinsa ya fita ta cikin kofar sirri sai gashi a waje wata mota ya shiga ya tada ita...a guje ya fata ba tare da mutanan gidan sun sani ba

kan titi ya miƙa bazai je hotel saboda duk kan wani motsinsa akan idon matane yake bazai iya basadar da ba za a iya ganesa ba dafa kansa yayi tunani yayi wa kwakwalwar'sa yawa a she daman taƙa wani matsayi kamar ka taka haɗarin rayuwar ka ne baka da kwanciyar hankali kowa ya matsoka ga ni kake cutar da kai zai yi ji yake daman ya dawo da agogo baya rayuwar sa ta da me cike da aminci....ba wanda ya damu da shi zai shiga cikin mutane ayi wasa da dare amma yanzu fa bazai iya ba...

bashi da tsayayyan gidan kwana ko mai nisan dare haka zai fito ya koma wani gidan ya kwana bashi da hutu na kansa wani lokacin ma baccin baya yuhuwa meeting ɗin na dare ne dole ya fito.....

*Washegari*

da kyar ta iya tashi zaune shima hakan da dabara ta tashi bata san rana ce ko dare ba ga gurin shuro baka iya jin komai kamar ba gurin ba wanda yake shiga in ansa Mutum a saka shine ba futowa haka ta raya a zuciyar ta

ba abinci ba ruwa a yanzu zuciyar'ta ta bushe kallon ko wanne dan adam take mara imani

*Kano unguwar kofar mata*

Alan guburo lafiya naga kana ta shiri yawa me barin ƙasar....uwani ta tambaye shi

Gyara zaman malin malin ɗin'sa yayi yace

"jiya na manta ban faɗa miki ba munyi shawara ni da manjagara da mahaifin dinana da na rabi za mu tafi Abuja ko za mu sami bilin wa'yannan yaran kinga yau kwanan su uku ba wani labari gwara mu bi sahun'su....,

taya akai kuka san a Abuja aka ajiye su

Malam hamisu ne ya faɗamin domin ya je headquarter su tanan an tabbatar mai basa nan saidai yaje Abuja

To Allah ya kai ku lafiya amma Ni ina jeye muku arba da wayan nan mutanan kar fa su nan naɗe ku su tura cikin cel

Ashsha kaji mugun baki

jan bakinta tayi ta tsuke tana yi mai fatan dawowa lafiya ba tare da an cire mai kafa ba domin ita ta tsorata da ganin mutanan nan ko ɗigon rahama babu a fuskarsu yanzu tasan duk wannan jikin na magajiya ya zube babu shi domin tasan sace shi za suyi tas to ga yan ƙari nan yan zuwa shishshigi su kuma Allah ya fitar da su....

gama shirin'sa yayi tas ya gama yace

"Bani dubu goma a cikin kuɗin cinikin ki....,
ba musu ta ɗaga kwanon da take jefa kuɗin cinikin ta dauko mai kirgawa yayi ya tura a aljihu ya dauki yar jakar'sa yace

"To mu mu tafi zaki iya ganin na dade domin dole inga Ak sardauna na bashi hakuri ya sakar min yarana.....,

abin dariya ya bata tace

"Allah shugaban ƙasa ganin irin mutanan nan bafa ganin limamin unguwar ku bane....,

be tsaya jinta ba ya saɓa jakarsa ya fita cikin addu'a a kofar gida yaga mahaifin rabi da na dinana sai manjagara saboda yayi zaman Abuja kai tsaye waha mota sukai a ka kai su tashar da zasu hau motar Abuja suka hau aka fara tafiya ƙara maƙale jakar'sa kahu yayi saboda ɓacin rana

wata uwar tusa na kusa da shi ya yi da sauri kahu ya tushe hancinsa yace

"Haba bawan Allah me maƙon kace a tsaya za kai uzuri wane be san uzuri ba sai kai mana tusa a mota salon cikin mu ya ɓaci....✍️
Chapter 3 · 0% Book details