← Book details Gidan Magajiya Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 1 OF 3

Sashe 1

Gidan Magajiya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

*GIDAN MAGAJI YA*
Oumyasmeen

*BOOK 2*

_Allah isa yadda na fara lafiya Allah isa na gama lafiya ina godiya masoyana bazan iya biyan ku ba har abada_

Episode 21-22

Da tasan wannan rana zata zo da ta yanke alakar'ta da ko wanne ɗan iska sai yanzu ta gane gaskiyar maganar da kahu yake faɗa mata kullum ki dena tara ya'yan Allah ya shirya mana ina jiye miki ranar da za su dauko miki abin da baki zata ba su goga miki kashin kaji daga kanta sama tayi ba abin da take iya gani saboda duhu lumshe idanuwanta tayi miƙewa tayi ta zauna amma ina ba damar haka ala dole ta koma ta kwanta
iya tsinuwa Asif ya shata ba iyaka daman ita ta dade da sanin duk wani me aikin force bashi da imani.....ko dan uwanta ne ai ta rabu dashi abin tsorone

*🤔tab*

Gurin dinana kuwa da sauke dakin da aka sa shi cel ne yana da fadi kuma shi da rabi aka sa shi sunyi haka ne ko za su ƙara jin wani abu sosai dinana ke kuka yace

"Rabi kin ga irin kaddarar da kaska ya samu ko...?,

Rabi'u dai wanne irin rabi

da sauri dinana ya ɗago tun da aka shigo da shi be shi yayi magana ba da badaki ɗaya aka sa su ba dariya ce ta kubce mai duk kuwa da halin da yake ciki kan rabi da yaci jal ya koma yadda yake bakin nan ko jambaki babu idonsa yayi ziri ziri me zai yi in banda dariya yace

"wayyo Allah huya ta sauka ki rabi kin ga kuwa yadda kika koma sai hawaye ya zobo mai ya share ya ci gaba da cewa zan so ace wannan abin tare muke gabaki ɗayan mu muyi faɗa muyi wasa Allah sarki kahu ko za mu ƙara ganawa ko rabuwar kenan Allah ka duba mu ka fitar da mu Allah kasani abin da ake tuhumar mu da shi bamu aikata ba Allah wannan wata jarabawa ce da muna da rauni Allah ka bamu ikon cinye ta

kai rabi ya jingina a jikin bango yace

"Amin ko wanne hali magajiya take gwara mu an hada mu tare ita fa Allah ya tsinewa kaska....,

Amin ya Allah daga nan sukai shiru

duk hirar nan da suke Asif na ganin'su a cikin laptop ɗin'sa biron hannun'sa ya ajiye ya jingina da jikin kujerarsa wayarsa ce tayi ringing ganin me kiran ya ƙi da gawa har yanzu mamaki yake Aysha ce zata kashe mai waya saka yayi a meeting ya ajiye ta ya ci gaba da aikinsa...

*Kano.....*

yinin ranar haka kahu yayi shi ba dad'i kallon Sama'ila yayi da yake kuka yace

"kai hakuri wallahi inhar sun yi bincike sun ga basa hannunsu kamar an sako sune su hukumar dss basa kama mutun ba tare da sunyi bincike ba in sun kama shi ma za su ƙara bincike nasan magajiya baza ta aikata haka ba kamar an yi an gama....,

ci gaba yayi da kukansa domin daga ita sai kahu suka rage mai a duniya kahu baya haihuwa sau daya ya haihu a wannan fadan na boko haram a gabansa aka yanka ɗan da ya haifa me shekara goma sha biyar sa'an sama'ila wani zubin yana sane yake biyewa su dinana dan ya kawar da radadin zuciyar sa da damuwarsa kallon uwani yayi yace

"kinga gobe bamu da abincin ci ke zaki fara sai da duk abin da magajiya ke yi kafin ta dawo dan murufawa kan mu a siri......ai kai kasan duk inda take karbo kaya ko....? Muci abinci mu ajiye mata sauran kuɗinta....,

eh na sani Sama'ila ya basa amsa

Ajiyar zuciya uwani ta sauke tace

"To Allah ya kai mu yau da dare sai inyi...dan mu tashi da abin da za muci...,

amin ya Allah sumayya ce ta shigo kallon gabas tayi ta shiƙe da dariya tace

"kahu kaga ikon Allah ko aminai uku an tarkata su Allah ya sa ma su dawo ta faɗa tana jin wani dad'i aranta daman magajiya ta tokare mata a rai komai ita kowa ita ga uban ciniki da take....,

kallon ta kahu yayi cike da mamaki saunawa magajiya ke ciyar da ita ko kamata akai ita ke zuwa bilinta dan adam kenan Allah ka rufa mana a Siri Ka bawa maƙiyan mu kunya wannan kadan daga cikin halin dan adam wani burin'sa yagan ka kullum a cikin huya yace

"Hassada da me rabo take ce baka samin nasara ta cikin sauki kar kiyi mamakin wannan shine silar arzikin ta kar ki mamakin wannan abin shine silar daukakar ta da haka Ubangiji yake komai yana da sanadi.....,

Wani kallo tayi mai tace

"Gyara bakin ka kahu gidan yari naje ba sau daya ba sau biyu ba Ni zan faɗa maka wani gidan yari Allah ya rufa maka asiri kar ta dawo da cikin shege domin wasu a cikin su ba mutanan kirki bane.....,

Bakin ki ya sari danyan kashi Allah ba zai jarabbe mu ta wannan fannin ba insha Allahu tana tare da Allah da mala'ikon'sa wallahi wannan abin kamar a kunnan'ta

wata dariya tayi ta fita fitar ta ba dadewa su saudat suka shigo da dan a shararle sai manjagara kuka sosai suke haka suka hunarwa kahu bayan sallar la'asar suka bar gidan inda uwani tace musu za tayi abinci da waina suka ce sai sun dawo daman baka gane masoyin ka sai kaddara ta hauka

*Allah Ka hadamu da masoyan mu na hakika*

*NNDC quarters*

Kabiru wallahi kashedi nayi maka kaga danka ASIF kai mai magana ya fito da matar aure dan kaf dangin mu ba juya ka tsaya ka zuba ido kai da shashashar matar ka....

ƙasa yayi da kansa yace

"Insha Allahu zan masa magana...,

goro ta ɓantara tace

"karma kai masa na kusan zaɓo dalleliyar budurwa a cikin kannan'sa yarinya sharaf yadda waccen saunar zata ji haushi in aura mai badai ina da malam liman ba rana tsaka wallahi za kuji ana sanarwa danni har lefe na gama haɗawa...,

da sauri ya kalleta gaskiya abin hajiyar tasu azimin ne yace

"godiya muke Allah ya ja daranki....,

banza tayi mai tana ci gaba da cin goron ta can ta dube'sa tace

"zaman me kake kuma bayan mun gama magana....?,

tashi yayi yace Allah hucu zuciyarsa ki na zata da wani abin ya sakai ya fita....,

jidda ce ta shigo tare da inteesar suka zauna suna kallo ya akram ne ya shigo da ayman suna hira sallama sukai hajiya ta amsa bakin'ta a washe tace

"a'a yan samari yau kune a gari...?,

zama sukai ayman yace

"eh wallahi Abuja tayi mana zafi haba aikin Company sai da hutu dan ma ogan namu be sani ba jibi za mu koma....,

Innalillahi haka kuka baro mai dukiya kuka tawo ita waccan shashashar ta maƙale kafa ba iya kular mai da ita za tayi ba....to wallahi kamar akunnan sa danni ba'a munafurci dani wallahi

Akram yace

"Kasan halin hajiya faɗi ce ba a tambaye ta ba me isaka Kai Mata wannan zancen dazu na kirashi na faɗa mai ya fada yana kifta ido...,

Karab a idon jidda sanin baya wasa da su bakamar ya ayman ba tayi shiru da bakin ta halin su daya da ya asif shima ba shi da kirki kai hajiya ta gyada yan masifar basa kusa tashi jidda tayi tace

"Hajiya bacci zanyi...,

wata harara hajiya ta watsa mai tace

"zo ki kwanta akai na yau nake jin wani tsohon kinibibi da ba hucewa kike ki kwanta ba shine zaki wani ce bacci kike ji a'a suma kike yi huce ki tafi gidan ku yau bazaki kwanar min ba kibi ki daddanne ni.....salon ki karya min kashi....,

kuka jidda ta kusan sawa ta killi hajiya ta zata huce dakin hajiya akram ya daka mata tsawa ya nuna mata hanya yace

"zo ki huce me ta ce miki...,

kamo jidda hajiya tayi tace

"to me halin uban gidana ku dai sai addu'a da nake cewa zan baka jidda ashe wata ran kashi zan tarar.....tab da sake....,

haɗa rai Akram yayi yace

"Allah ya rufa a siri nii...hajiya karfa ki fara ai wannan salon raini ne....,

Ubanka kai da rainin dan uwarka nawa ubanka ya auri uwarka nace ko da sauri ayman yace

"haba hajiya da fa yara a gurin nan be dace ba....,

Allah ya rufa a siri ta ja bakin'ta tayi shiru dakin shiru yayi a fakaice akram ke ƙarewa jidda kallo yarinyar bata da makusa inba Dan rainon hajiya bace sai addu'a kafin ya tafi chaina zai lallaɓa hajiya a tsaida magana ci gaba da kallo inteesar tayi ɗagowa tayi suka haɗa ido da ayman murmushi yayu mata yace

"zo kiga wata sabuwar game da na ɗauko...,

ba musu tazo haka jidda suka sa shi a tsakiya suna kallo tsawa akram ya dakawa jidda yace

"Baccin ke nan gaskiyar hajiya da tace na kinibibi ne ke inteesar ku tashi kuje kuyi bacci gobe a kwai makaranta....,

ba musu suka tashi jidda rannan a ɓace kamar za tayi kuka ta kusan fita tace

"Ya Ayman Dan Allah gobe zaka bamu yi....,

Eh zan baku

to wayar fa yau she zaka siya mana

sai babban yaya ya yarda

tab kawai ka fito fili kace baza ka siya ba ko inteesar in ta babban yaya ne mu mutu bamu da waya tana faɗar haka ta fita Akram

na'am hajiya

Akram

amsawa ya ƙarayi ta ƙara kiran sunan sa tace

"Saunawa na kiraka...,

Uku hajiya ya bata amsa tace

"Wallahi kafita a sabgar jikokina in ba haka ba zan ɓatar maka...,

To yace ya ci gaba da danna wayarsa haka ma ayman halin hajiya sai hakuri ba wanda ta kyale......

*Abuja osokoro*

Cikin sauri yake haɗa komai da zai buƙata a gida ya saka a cikin brief case ɗin'sa ya zuge wayar'sa ce ta kawo haske dubawa yayi yaga wanda ya bawa receip ɗin nan ne yayi bincike ya ɗauka cikin girmamawa yake cemai

I researched it and sent you a photo of the two people who touched him, and the numbers on his body are now not working ...
ya ci gaba da cewa

but no matter which number there is information about its location

dad'i yaji ganin binciken bazai dau ki tsahon lokaci ba yace
Chapter 1 · 0% Book details