← Book details Gidan Gandu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 37 OF 41

Sashe 37

Gidan Gandu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

*+______________________+*
*ABIN YABO BOOKSHOP*
Kasuwar Rimi Kano
Tel:📞 *07038339244*

❤❤SADY-SAKHNACEH❤❤

Kar ku manta da

#comment
#share
#like
#follow.

____** *GIDAN GANDU* **____
❤❤By sadi-sakhana❤❤

Wattpad username:SAKHNA03

❤34❤

"Haba manjo ka gyara hannun mana na gyara maka rigar,wallahi hadda ragwancinka ma yamzu kam tunda ciwon ya warke ai sai ka barni na ji da y'ay'anka ma"
"Wai ni kulu meyasa kika sanjane kullum cikin fada,nikam bana cemiki bazna kara shaye shaye ba,zan nemi sana'a na dungayi"
"Yah rage naka kuma,in kanaso ma ka cigaba"
Shiru yayi yana jinta shidai bukatarsa ta zubo masa wainar da takeyi ta rana yah ci tukunna komai ma sai ayi.
Hakan kuwa akayi tana zubowa yah yagyara hannun yanan dandanar miyar ganyen masar yana antayawa a bakinsa,koh maganarsa ba kaji,
"Hmm Gaskiyah nayi sa'a dana sameki dan naji ance sule har yanzu baya tashi.

~~~wani bakin tsuntsune yake ta bita mai kama da hankaka a wani waje mai surkukiyar gaske,dubawa tayi taga babu komai a jikinta sai wani farin yadi an yane jikinta daahi.
Ganin babu mafita ne yasata furmawa da gudu shikuwa ya bita a baya yana wata irin kara mai ratsa cikin kunnuwa.
Sun dad'e suna gudu har suka iso wani waje da hanyar bazata bulle ba sai wata babbar katanga wanda iyah ganin mutum baya iyah ganin keshenta.
*****
A can kuwa cikin sukukiyar daji da kuma tsohon dare,mutane biyu ne a zaune wanda saboda maita da kuma san abin duniyah basa da niyyar kwanciyha bacci irin na kowane san adam.
Sameerah ce ta kalli bokan da yake mata aiki tace,
"Toh yanzu kana ganin aikin zai yiwu kuwa?"
"Eh zai yiwu mana,yanzu haka tana can tana mafarki saboda munyi nasarar kama kuruwarta tun dazu,yamzu wancan tsuntsun da kike gani wanda muka tsireci da allurah uku bayan mun saka masa gashinta a cikin bakins kafin mu kasheshi,toh ruhinsa zai bayyana a cikin mafarkinta duk inda kuma yah ji mata ciwo toh bazai warkeba saidai ciwon ya cigaba da yaduwa irin na uwartah"
Leka kwaryar da take gaban bokan sameerah tayi dan ganin menene a ciki,idonta ne yayi tozali da video abinda yake afkuwa a cikin mafarkin sameemah,dadai inda bokan yasaka wani abu mai kaman katanga a gabanta saboda hana ta damar wucewa.
~~~,duk da gudun da tayi amma babu alamar gajiyah ko haki a cikin jikinta,saidai rashin ganin hanyar dazata cigaba da gudun yasa ta juyah tana kallon bakin tsunstun dayake nufowa wajen ta cikin saurin gudu da yafi na karfin tsuntsaye a gaske,saisa yazo daff da itah kafin tah mika hannunta tareda cewa,
"Tsaya Haka angama wasan. Yakai wannan *BAKIN RUHI*,(littafin marubuciyah oum hairan). Kayi kuskuren biyonin har wannan wajen,daga inda kake in jiyowa wani bangare na jikina a tareda kai,dan haka in umarninka daka tsaya a inda kake,idan kuma kayi gangancin matsowa toh mutuwar ma sai ta fimaka sauki"
Cak ya tsaya a wajen yana daddaga fuka fukansa kaamn yaga uban gidansa, masawa tayi inda yake tareda cewa,
"Yaron kirki ace dai kana jin magana"
Daga idonta tayi wanda yayi za kaman jini tana kallon sama,dadai wajen da su sameerah suke kallonta,gashin kanta ma yana dagawa a iska tamkar fatalwar data fito daga sabon kabari.
"Kinyi kuskure daga ke harshi din,a tunaninku bansan duk abinda kukeyimin bane?,nasani dukka kuma ba barku zanyiba ku tafi a banza,tunda yanzu har kun fara yin bakin asiri da kuma ruhin ba bayyi muku komai ba,duk da nakan dauki ruhi amma bana taba ruhin da baida laifi koda kuwa naso hakan,amma ku kunsaka kanku ciki saboda ku azzalumaine masu cutar wa.
Hhhhhhahhha kana nan yan iska kuna tunanin zaku iyah yimim wani abu a duniyar mafarkine wanda take itama duniyata ce?,kai daga nan inaso ka kayanka hannunka har sai jininka ya gama zubewa,ke kuma bazan yimiki komaiba kinci albarkacin yan uwantaka amma zaki karbi naki hukuncin koh ba yau ba kuwa,idan na barki da halin da kike shirin shiga ma ya isheki,sannan idan kin dawo ki gargadi uwarki abinda na fada miki
cewa karta kuskura ta sake shiga gonata,idan kuma wani ya ji a binda yafaru anan wajen toh sunanki matacciyah".
***
Abin bai kara bawa sameerah mamakiba saida taga yanda bokan yah dauki wuka ya yanka wuyahsa da itah,sannan jinin yana tafiyah direct zuwa cikin kwaryar wajen da sameemah take.
Ko motsi kasawa tayi har jinin bokan yah kare yah fadi a wajen,itah kuma kwaryar ta fashe,wani dogon numfashi sameerah taja kafin tah tashi ta furma da gudu zuwa cikin gari a kafarta duk da tsohon daren.
Tashi tayi daga baccin duk da har sannan gari bai wayeba dan koh assalatu ba ayiba,hankalinta kwance ta tashi ta debo ruwa ta sha kafin koma ta kwanta,saidai babu alamar bacci a idonta dan haka kallon rufin dakin kawai takeyi,idan ta tuna wanj abu sai tayi Murmushi wani kuma tah jijjiga kai.
Tana bude idonta sukayi tozali da sameerah wanda ta dawo da asuba tah zo daukar wani abu dakin,dan tunda ta dawo ba yanda ba'ayi da itha na amma daga ta doso dakinnan su sai jikinta yafara karkarwa saboda tsabar tsoro,sannan an tambayeta mai yah faru tace kuma babu komai,sai aka barshi da inaga gamo tayi a hanyarta ta dawowa,itama da taji mai suka ce sai ta amsa musu da cewar hakanne.
Toh yanzun ganin rana ta farayi amma sameemah bata fitoba ne yasakata shiga dakin da sanda domin daukar kayanata dan wancan din duk sun yage a hanyar dawowa daga jejin cikin hali na fitar hankali.
Saidai kashh rashin sa'a,tana shigowa itakuma sameemah tana tashi,karkarwa kafafunta suka farayi har sun gaza daukarta gabadayah,bajewa tayi a tsakar dakim har sannan idonta bai bar kan sameemah bah.
"Ke miye kike min kallo kaman kinga aljani"
"Bbbbbba bbbbbbu shhshshugabata dama kaya nazo dauka kuma banaso na tashaki a bacci,kiyafeni dan girman allah kiyimin rai"
"Hmm banace miki kar naji ba maganar nan a bakin kowa ba,toh ciki harda bakinki,gobema ki sake gigin yin shashancinki akai,dalla jita kaman kinsan allah ke,da kike hadani dashi nayimiki rai"
"Ahah na tuba kiyimin rai,in da san samu ma ki daukeni aiki a karkashinki koh kuma ki hadani da mai miki wannan aikin nasan tabbas babane a harkar"
Wata harara sameemah ta watsa mata kaman idonta zai fita tace,
"Lallai dan adam kayan allah ,wato baki daddara ba koh?,toh wallahi idan kika sakemkn wannan zancen koh kika fadawa wani toh zanjiji sarai,kuma hukuncin bazai miki dadi ba kkh kadan"
Tun kafin tabari ta karisa sameerah ta yunkura da sauri tah fice a dakin har sannan jikinta rawa yakeyi kaman tasha tsimin yan farautan.
Saboda maganar da sukeyi da sameerah har sameemah tah manta davzuwa gidan su surayyah da zasuyi itah da kawun burgun saboda tambayo masa izini,daga wayar tayi domin kiran burgu dan taji koh kawunnnasa yah shiryah dan itah bata son zuwan daren ta fiso ta gama da wannan babin kawai.
Tashi tayi tah fara shiryawa jin zuwannasu yana nan ba'a canja ba.
Dayake Surayyah ta sanar da zuwan su sai aka fara shirin taryarsu tunda wuri,dan haka lokacin da suka shigo kowa yana gidan harda babanta shima yau bai je aiki ba.
Toh wata sabon gani surayyah ta fada a ranta ganin yanda sameemah tasha wani uban hijabi mai alkyabba kaman ba itah ba saboda koh a tairihi babu wanda yah taba ganin tasaka,"gaskiyah koba komai na samu matsayi a ran shugabrtawa alalmu ya nuna ta karbi tayin zamana kanwa a wajenta"
Har suka wuce falon baki inda akayimusu shiri bakin Surayyah bai rufuba dan farincikin ganin su sameemah,koh yaushe suka hada ido sai tayiwa sameemah Murmushi itakuwa koh sau daya bata sau fuska ba bare kuma tayi mata magana,hakan bai damu surayyah ba koh kadan saboda tasan haka take,kuma itah haka kawai sameemah take burgers Kodak bata yimata komaiba.
Maganar abinda yah tarasu suka farayi bayan kowa yah kammala abinda zaiyi.
Babantane yafara magana bayan yah bude taro da addu'a.
"Toh da farko tun banji abinda yah taraku anan wajen ba hankalina a kwance yake,don yanayin da kukazo da kuma yamda kuka sananr damu zuwanku akan wata muhimmiyar magana nasan abin alkhairi ne,dan haka zamuso muji abinda yake tafe daku"
Alhaji isah yayan mahaifin burgu shiya fara jawabi kafin yah fara magana da jawabi duk da bai fito fili ya fadi abinda yake ransaba.
Haushine yakama sameemah ganin yanda suke tah jan magana guda daya ana ta bata lokaci ,dan dama tun sanda shigo bata ce komaiba,katsewa kawun burgun tayi tareda numfasawa tana kallon agogonta tukun kafin tafara cewa,
"A takaice dai a daina wani bata lokaci,ni sunana sameemah nasan kunsan sunan koda fuskata zatayi muku wuyahr sani,sannan kuma nice shugabar kungiyar da yaranku suke ciki kafin yanzu kuma suna karakshi kuwata ta kungiyar vigilantee,kuma dukkanku saida kuka amince kafin na fara aiki dasu,wanda hakan ya nuna kun yarda dani a kusa da yaranku.
Sun zo sun sameni akan nayi magana da ku amatsayin iyayensu saboda su basuda karfin gwiwar tunkararku saboda abubuwan da suka faru,abayah.
Sun ce su na son junansu kuma kuma burunsu shine hakan yakaisu ga aure,shin kun amince???.
Shiru wajen yayi kowa yana nazari,ganin hakanne yasa sameemah cigaba da cewa,
"Ni nazo a matsayi guda hudune,na farko amatsayin shugabrsu na biyu a matsayin yar aikar sako,na uku a matsayin abokiyar Ahamd(burgu)na hudu kuma a matsayin yaya ga Surayyah kuma yar uwa,wanda jiyah ta rokeni akan na zamo tamkar yaya a gareta kuma na amince,dan haka ni na amince da kasancewarsu tare saboda hakan abune mai kyau wanda ake fatan yah dore"
Kowa ma dayaji abinda sameemah ta fada kuma sun san dagaske takeyi sai kawai suka amince har aka fara shirye shiyen yanda abin zai kasance,daga haka taro yah kare kowa yah tafi nasa harkar.
Dadai lokacin da sameemah tazo fita daga zauren gidan taji an rungumeta ta baya,ko bata fada ba tasan mai aikata hakan,muryar surayyah tah tsinkayo tana cewa,
"Nagode sosai da kokarin da kikayimana anty sameemah,ina lekawa duk naji abinda kika fada,hakika ko kowa bazai alfahari dake ba ni ina alfahari dake antyna.
Har cikin ranta sameemah tah ji dadin abinda surayyah ta fada,amma a fuskarta iyah karamin Murmushi tayi tareda cewa "nagode"atakaice kafin ta fice.

*+______________________+*
*ABIN YABO BOOKSHOP*
Kasuwar Rimi Kano
Tel:📞 *07038339244*

❤❤SADY-SAKHNACEH❤❤

Kar ku manta da

#comment
#share
#like
#follow.

____** *GIDAN GANDU* **____
❤❤By sadi-sakhana❤❤

Wattpad username:SAKHNA03

❤35❤
Chapter 37 · 0% Book details