← Book details Farin Ciki Sau Daya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
CHAPTER 4 OF 6

Babi na uku.

Farin Ciki Sau Daya Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read

.
.
Da kowa yaga abin dai da gaske suke yi. Ilham da Ma'aruf sun riqe soyayyarsu da hannu bibbiyu, suna son junansu kamar su hadiye kansu sai Alh. Ayuba ya kira Ilham ta same shi a falonssa ya ce da ita.
.
"Ilham duk abin da ki ke ciki ke da yaron nan da yazo bautar qasa, ban ta6a cewa da ke komai ba." ina ganin lkc ya yi da ya kamata in yi magana da ke akan wannan al'amarin."
.
Ilham ta sunkuyar da kanta bata ce komai ba. Alh. Ayuba dake zaune akan kujera ya ci gaba da cewa.
.
"na fahimci yadda kuka shaqu ke da shi, kuma a yadda naga alama da gaske yake yi. To amma kin kuwa tsaya kin yi tunani sosai akanshi Ilham? Kina jin idan ya aureki zai iya riqe ki da mutunci? Ki a lamarin ku na yara baku tsayawa ku ba komai lkc, kuna matuqar yanke hukunci matuqar xuqatanku suna son wani abu. Me kika fahimta a game dashi, wanda ya baki qwarin guiwar jin shi mutum ne na-gari kuma zai iya riqe ki tsakani da Allah?"
.
Ilham ta yi ajiyar xuciya. Ba tare da ta dago kai ta dubi mahaifinta ba." ta ce da shi a sanyaye.
.
"Baba kowa yana shaidar Ma'aruf a unguwar nan, ko mutane ka tambaya zaka ji ance yana da mutunci da...."
.
Alh. Ayuba ya dakatar da 'yarsa Ilham
.
"zancen shirme kenan! Don mutane sun ce yana da mutunci sai ki dogara da haka?
.
.
Lp=13%%% FARIN CIKI SAU DAYA %%%
Page 13
.
Daga alqalamin
Shafi'u Dauda Giwa
.
.
Tare da ni
Abu ihsan Bn ishak
(Madugun Taska)
.
"TASKAR GIDAN LITTAFI" bata amince da daukar shafin ba."
.
Ilham tana hangenshi ya fito da qwallo ya riqeta da hannunsa biyu, wasu yara 'yan aji shida manya suna biye da shi cike da murna. Ma'aruf ya ja su xuwa filin qwallon makarantar. Ya raba su gida biyu, ya fara yi masu nasiha, sannan ya sa masu qwallon suka fara wasa, shi kuma ya zama alqalin wasa, ya riqa hura usur yana bin su a guje duk inda qwallon ta nufa.
.
Wasu yara biyu suka yi karo da juna suka fadi suna kuka. Ma'aruf ya tsayar da wasan, ya kama qwallon ya riqeta ya dawo da hankalinsa kan yaran da suka ji ciwo. Ya lallashesu, suka tashi, sauran yaran suka zo suka zagaye shi.
.
Ma'aruf ya duba raunin da kowanne ya ji ya riqa lallashinsu da kalamai masu dadi, sannan ya kira wani dalibin ya ce da shi ya je dasu ofishin hedimasta a sa masu magani a raunin
.
Ma'aruf yana son dalibansa kamar yadda suma suke son shi. Ilham ta sirare ta tafi, ta koma gida ba tare da ya ganta ba." a xuciyarta tana tunanin shin idan ta auri Ma'aruf, haka zai riqa kulawa da 'ya'yanta..'ya'yansu da zasu haifa? Haka zai zama uba na-gari mai adalci da tausayin 'ya'yansa? Haka zai riqa kyautata masu?
.
Sai da yamma da yazo gidan su ta ce dashi tana dariya
.
"Daxu na zo makarantar da kake koyarwa, na dade ina kallonka, baka ganni ba."
.
Ma'aruf ya ce....'
.
"kamar gaske." Ilham ta ce dashi. "ka tuna lkcn da yaran nan da suke qwallo. Suka yi karo ka tsayar da qwallon ka je wajen su tare da sauran dalibai?"
.
Ma'aruf ya ce da ita. "amma ba ki yi min magana ba in zo Ilham?" ta ce da shi. "6oyewa na yi, dama bana so ka ganni. Na ga ka sha gudu kai da yara. Ya tsamin jiki?" suka yi dariya tare.
.
"Ai na saba, bana jin wuya a haka muke wuni muna wannan guje-gujen ni da su."
.
Ilham ta tambayeshi "kuma da gaske kyauta ka ke yin wannan aikin a makarantar basu biyanka komai?"
.
Ya ce da ita. "Ai ni na san kaina Ilham. ba don kudi nake yi ba, ina yi ne don in taimaki al'ummata da kuma qasata." Ilham ta bi shi da kallo bata ce komai ba, Ma'aruf ya qara da cewa. "lkc ya yi da ya kamata mutane su fahimci muhimmancin aikin taimakon kai-da-kai.... Duk yadda ka samu kanka, to ya dace ka binciko irin baiwar da Allah Ya yi maka, ka taimaki al'umma da italian ka bayar da taka gudunmawar." idan mutum ya kalli duniya, zai ga a cike take da kayayyakin more rayuwa wadanda wasu mutane suka samar dasu da tunaninsu sa basirarsu. Kodayaushe yana da kyau mutum ya jajirce shima ya ga ya samar da wani abu da zai amfani mutane koda qanqani ne....! Kodayaushe ina dora rayuwata akan wata magana da ke cewa. "Hanya daya da zaka rayu har abada ita ce ka bar wani aiki na alheri a biyanka.
.
.
.
*** ***
.
.
Chapter 4 · 0% Book details