← Book details Farin Ciki Sau Daya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
CHAPTER 3 OF 6

Babi na biyu.

Farin Ciki Sau Daya Part 1 Complete Hausa Novel · about 15 min read

.
Duk wanda zai ce ya ta6a ganin soyayya ta gaske....soyayya ta ban mamaki a duniya indai ya ta6a ganin soyayyar Ilham da Ma'aruf to labarin ta zai fara bayarwa.
.
Ba a dade ba duk wani mutum dake a layinsu Ilham ya san tayi wani saurayi wanda ake sa ran shine zai aureta. A wajen Ma'aruf Ilham bata tsaya kawai a masoyiyarsa ba." ya dauketa tamkar 'yar uwarsa ce ta jini, duk wani mutum da Ilham zata nunawa Ma'aruf ta ce dan uwanta ne, a wajen Ma'aruf shima dan uwansa ne. Bai ta6a mance sunayen mutanen da Ilham ta ta6a fada masa sunayen su ba a gidansu da 'yan uwanta na nesa da na kusa. Sbd ya daukesu da muhimmanci
.
Ma'aruf ya kan je gidansu Ilham ko tana nan ko bata nan. Idan tana nan yayi hira da ita, idan kuma bata nan sai ya zauna tare da yayyenta a qofar gida suyi hira, a nan zai wuni ya kai har dare, sbd ko'ina ya je in har baya kusa da Ilham baya jin dadi.
.
Ita kuwa Ilham sanin kowa ne cewar ko a cikin qawayenta idan har ana zancen samari da wahal ta tsoma bakinta tayi magana, amma tun haduwarta da Ma'aruf, tun sanda ta fara sonshi ta fara bada labarin shi a duk inda ta zauna. Qawayenta da ba unguwa daya suke da ita ba. Suka qosa su ga kowanene wannan Ma'aruf din, wanda Ilham ta dame su da zancensa, har sun fara gajiya da jin sa.
.
A wani bikin auren da wata qawarsu zata yi a 6atagarawa Ilham ta gayyaci Ma'aruf ta ce tana so yazo don ya gaisa da qawayenta. Ma'aruf ya yi mata alqawarin zai je. Yawancin qawayenta sun yi zaton Ma'aruf wani miloniya ne wanda yake hawa manyan motoci, sbd a yadda suka san Ilham bata kula kowa, ba qaramin mutum zai iya shiga xuciyarta haka duk ta rikice da soyayyarsa ba tayi ta zancensa a ko'ina
.
Sai da yamma da Ma'aruf ya je wajen bikin a qasa, yana sanye da kodadden shudin wando da takalmi (sandal) sai rigarsa mai dogon hannu. Da Ilham ta gabatar dashi a wajen qawayenta sai duk kunya ta kamasu.
.
Kowacce ta riqa mamakin me Ilham ta gani a wajen wannan saurayin. Me zai bata a rayuwa? Ta yaya ma zai iya riqeta? Don kuwa sun san mutane da yawa masu kudi sun dade suna son Ilham, bata amince masu ba." ta yaya kuma zata amshi soyayyar Ma'aruf wanda bashi da komai?
.
Ilham tana cike da farin cikin ganin Ma'aruf yazo wajen bikin. Bata damu da ganin samarin qawayenta da suka xo a manyan motoci ba." kuma bata ji kunyar gabatar masu da Ma'aruf ba tana murmushi.
.
"ga masoyina Ma'aruf da nake baku labarin sa, wanda nake so ki tayamu addu'a, Allah Ya cika mana burinmu mu zama mata da miji."
.
Qawayenta sukan kalli juna su rasa abin da zasu ce, sbd abin yana basu kunya.
.
.
.
Lp=10%%% FARIN CIKI SAU DAYA %%%
Page 10
.
Daga alqalamin
Shafi'u dauda Giwa
.
.
Tare da ni
Abu ihsan Bn ishak
(Madugun Taska).
.
"TASKAR GIDAN LITTAFI" bata amince da daukar shafin ba."
.
Qawayenta sukan kalli juna. Su rasa abin da zasu ce sbd kunya. Bayan Ma'aruf ya tayasu farin ciki da zai tafi sai Ilham ta rakashi har bakin titti inda zai hau mota ya koma gida kafin Ilham ta dawo gida idan sun gama bikin da daddare
.
Bayan Ilham ta dawo wajen qawayenta ne cike da farin cikin xuwansu masoyinta Ma'aruf' ta same su sunyi tsam' a tsaitsaye suna mamaki ta ce dasu
.
"bari ku ji wani abin dariya da ya faru tsakanina da Ma'aruf ynx nan da muka tafi na rakashi. na tambayeshi ne ya ya yaga bikin nan da muke yi? Me zai ce, shi ne sai ya ce da xuwansa ya ji ina ma da ace bikinmu ake yi ni dashi? Wai idan an tashi (engagement) dinmu, kwana uku kawai za a sa a daura aure."
.
Ilham tayi dariya
.
Babu wacce tayi dariya a cikin qawayenta
.
.
Duk abin da Ilham take so a rayuwarta shi Ma'aruf yake so. Haka itama tana son duk abin da yake so. Idan Ma'aruf yazo gidan su wajenta, Ilham ta kan bude falon mahaifinta su zauna suyi hira idan baya nan. Sau da yawa idan Ma'aruf yazo sun fi yin kallo. Ilham tana son fina-finan indiya fiye da kowanne irin fim. Shi yasa ba ta da wata tashar da take kamowa fiye da (Zee Aflam) indai ita kadai zata yi kallo.
.
A ranar da ta fara shiga da Ma'aruf falon gidan su suka yi hira da ta kunna kallo sai ta tambayeshi
.
"kana kallon fina-finan indiya kuwa?"
.
Ma'aruf ya dubeta
.
"me yasa kika yi min wannan tambayar?"
.
Ilham ta ce dashi.
.
"sbd ina sha'awarsu fiye da duk wani abu da zan kalla na debe kewa. Ban sani ba ko kai baka sha'awarsu."
.
A qa'ida Ma'aruf bai ta6a zama ya kalli fim din indiya ba sbd basu yi masa ba." in har kallo zai yi yafi son ya kalli (Wrestling) ko wasannin qwallon qafa.
.
Bai fadawa Ilham baya so ba." ya ce da ita.
.
"nima ina sha'awarsu...suna burgeni."
.
Ilham ta kunna musu kallo, aka fara nuno 'yan wasa. Ta fara sanar da Ma'aruf ra'ayinta akan jaruman da take so. Maza da mata, ta ji yayi shiru ya kasa magana sbd bai sansu ba." Ilham ta yi dariya ta bar abin a xuciyarta, ta fahimci Ma'aruf baya kallon fina-finan indiya, yaqi fada mata gsky ne, don dai ya goyu bayanta kada ya kushe mata abin da take so.
.
Washe gari da Ma'aruf yazo gidansu suka zauna a falo suna hira, sai Ilham ta kunna masu kallo har ta kamo tashar qwallon sai ya ce da ita ta canza tasha ta kamo masu fim din indiya suyi kallo. Ilham ta dubeshi ta yi murmushi
.
L"Ma'aruf na fahimci baka kallon fim din indiya, me yasa zaka 6oye min abin da baka so, don kawai Kaga ni ina so?"
.
Ma'aruf ya ce da ita.
.
"wa ya fada maki bana kallon fina-finan indiya? ina kallon su sosai."
.
Ilham ta yi dariya ta ce dashi.
.
"zan qure ka fa, kada mu fara kallo in tambayeka sunan wani ka kasa fada min."
.
Ma'aruf ya ce da ita.
.
"duk wanda kika tambayeni zan fada maki sunansa."
.
Ilham ta kamo tashar tana dariya, ta san cewar Ma'aruf bai san kowa ba a cikin jaruman indiya. tana kamo tashar suka iske ana tallar sabbin fina-finai masu fitowa. Jarumar da aka fara nunowa tana rera sassanyar waqa a cikin sahara, iska na kada dogon gashin kanta da kuma gyalenta mai shara-shara, tun kafin Ilham ta tambayeshi ya ce da ita.
.
"wannan ita ce Kareenah Kapoor, wacce 'yar uwarta itama tsohuwar fitacciyar jaruma ce wato Karishma Kapoor. Kareena tana daga cikin manyan jarumai mata a fagen fina-finan indiya. tayi fim din Bewafaa tare da Akshay kumar. Tayi Asoka, tare da Sharukhan. Tayi Khabi Khushi Khabi Gham tare da Hirthic da su Amita Bacchan."
.
Ilham ta yi mamakin yadda akayi Ma'aruf ya san wannan jarumar haka sosai, bayan ta san bai ta6a kallon fim dinta ba." xuwa can bayan ta gama waqar sai aka sake nuno wata jarumar tana wasa da shuke-shuke a wani qayataccen lambu. Ma'aruf ya ce da Ilham
.
"ita kuma wannan ita ce Aishwariya, wacce ta kasance tauraruwa sha kallon duk wani fim da zata fito sbd daukakarta. Ta yi fina-finai tare da duk wani jarumi dake tashe. Tayi fim da Devdas tare da Sharukhan. Wanda fitaccen daraktan nan ya bayar da umarni wato Sanjay Leela Bansalay. Sannan tayi fim din jordan Akbar tare da Hirthic. Fitaccen fim dinta wanda ake ganin babu kamarsa shine Aor Pyar Hogaya, wanda ta fito tare da Boby Deol."
.
Ilham ta bi Ma'aruf da kallo cikin kaduwa da mamaki. Ita kanta bata san duk wadann fina-finan da yake fada mata ba." aka sake nuno wani jarumin akan babur Ma'aruf ya ce da ita.
.
"wannan shi ne Abishek Bacchan shine ya auri ita Aishwariya, kuma shine dan tsohon jarumi Amitab Bacchan. Abishek yayi fim din Run ya yi fim din Drona, da kuma Doom 1 da Doom 2 ya fito a fim din Dus tare dasu...."
.
Ilham ta dakatar da Ma'aruf ta tambayeshi
.
"Ya akayi ka san wadann fina-finan da jaruman Ma'aruf? na tabbatar jiya da kazo nan baka san kowa ba a cikin jaruman fim din indiya. ba ka ta6a kallon fim dinsu ko daya ba." ya akayi ka sansu daga jiya xuwa yau?"
.
Ma'aruf ya dubi Ilham ya ce da ita.
.
"gsky ne Ilham, ban ta6a kallon fim din indiya ba ko daya, kuma ban san sunan ko daya ba a cikin jarumansu. Jiya ne da nazo wajenki na fahimci kina so, shi yasa nima naji ina so. Duk abubuwan da kika ji na fada maki, da kuma wadanda ma ban fada maki ba, nayi bincikensu ne a wajen mutane daban-daban na sansu daga jiya xuwa yau. A ynx ina sha'awar indiyan fim sbd naji kina sha'awarsu. Duk abin da kike so a rayuwarki Ilham nima shi nake so a rayuwata."
.
Ilham ta kasa magana. Ta qurawa Ma'aruf masoyinta ido. A lkcn ne ta tabbatarwa kanta cewar ba zata sake samun masoyi kwatankwacin Ma'aruf ba a duniya.
.
.
Lp=11%%% FARIN CIKI SAU DAYA %%%
Page 11
.
Daga alqalamin
Shafi'u Dauda Giwa
.
.
Tare da ni
Abu ihsan Bn ishak
(Madugun Taska)
.
"TASKAR GIDAN LITTAFI" bata amince da daukar shafin ba."
.
Ilham ta kasa magana ta qura wa masoyinta Ma'aruf ido. A lkcn ne ta tabbatar wa kanta har abada ba zata sake samun wani masoyi a duniya kwatankwacin Ma'aruf ba."
.
.
A zamantakewarsu Ma'aruf ya saba ko me ya samu tunanin shi na farko shi ne me zai yiwa Ilham wanda zai faranta mata rai da shi? Ma'aruf ya saba ya yi ta kashewa Ilham kudi da saye-sayen kayayyakin kyaututtukan soyayya. To amma Ilham ba ta san yaya yake qoqarin yi mata irin wadannan hidindimun ba a matsayin sa na wanda yake aikin bautar qasa.
.
Ilham tana so ta tambayi Ma'aruf amma tana jin kunyarsa. Sai da abokinsa Khalid ya ta6a bata wani saqo da Ma'aruf ya aiko shi sannan Ilham ta tambayeshi, ko ya san yadda Ma'aruf yake samun kudaden da yake kashe mata haka?
.
Khalid ya ce da ita.
.
"gsky Ma'aruf bashi da wata hanyar samun kudin da ta wuce dan alawus din da ake basu a inda yake aikin sa na (Service) sai kuma wata makaranta da yake xuwa yana taimaka masu a ranakun litinin da talata amma su bana jin yana amsar kudi. Kyauta yake yi musu."
.
Tun daga ranar Ilham ta fahimci duk abin da Ma'aruf yake samu a rayuwar sa akanta kawai yake qarar dasu baki daya. A lkcn ne tayi alqawarin ba zata qara amsar duk wata kyauta da Ma'aruf ya yi mata ba."
.
Tun daga ranar kome ya kawo ya bata, bata amsa, kuma duk sanda irin haka ta faru a tsakanin su sai ta fada masa ya daina yi mata dawainiyar komai. Ta gode! Ta gode!! Ta gode!!!..amma ba zata amsa ba."
.
Don kada ta riqa damuwa sai Ma'aruf ya daina bata kyautar komai. Ba a dade ba watan babbar sallah ya tsaya. Mahaifin Ilham ya tambayi 'ya'yansa irin kayan da za a siyasa a dinka da sallah. Kowa ya fadi irin kayan da yake so a saya masa. Ilham ta ce da mahaifinta ita tafi son atamfar England. Mahaifinta ya ce kada ta damu zai saya mata.
.
Sun yi wannan maganar da kwana daya, da wani a cikin yayyenta ya samu labarin irin atamfar da Ilham ta ce tana so a saya mata sa sallah, sai ya yi mata kutunguila ya soke alqawarin da mahaifinta ya yi mata.
.
Alh. Ayuba ya kira Ilham ya ce da ita.
.
"gsky atamfar nan da kika ce kina so ba zaki sameta ba Ilham. sbd nayi bincike an fadi mani bata da nagarta ga kuma tsada. Ynx ki bari a samu ko leshi ne na dubu uku a saya maki, ko kuma shadda, sai ki za6i wanda kike so a cikin biyun."
.
Ilham ta ji baqin ciki ya soki xuciyarta. Ta san wani ne ya je yayi mata wannan munafurcin a wajen mahaifinta. Don ya hana a saya mata atamfar da zata sa da sallah. Ilham ta ce dashi.
.
"Baba ka barshi kawai sai wani lkcn in ina da rabo na san wata rana zaka saya mani, tunda kayi niyya ba komai."
.
Ta tashi ta tafi tana share hawaye. Ta gwammace ta wanke tsofaffin kayanta ta ci sallar dasu. Ko ya akayi har Ma'aruf ya samu wannan labarin?... Kowa ya fada masa tayi wannan badaqalar da 'yan uwanta a gida? Ita dai bata sani ba, kuma bata fadawa kowa ba."
.
Saura kwana biyu sallah Ma'aruf ya xo gidansu ya sa aka kirata. A lkcn qarfe goma na safe Ilham ta fito cike da mamakin dalilin xuwan Ma'aruf wajenta da safe haka ko lfy har yake cewa tayi sauri ta zo? Da xuwanta Ma'aruf ya ce da ita.
.
"nazo ne ina so ki raka ni wani waje, amma zamu dade ba ynxn nan zamu je mu dawo."
.
Akwai yarda...akwai amincewa tsakanin Ilham da Ma'aruf. Bata yi ko kwalliya ba, haka nan ta fito da kodaddun kayanta, ta yafa qaramin gyalenta qafarta sanye da silifas. Ilham ta ce da shi.
.
"bari in shiga gida in canza kaya in sa takalmi, kaga silifas ne a qafata."
.
Ma'aruf ya ce da ita.
.
"ba komai, mu je a haka sauri nakw yi Ilham."
.
Ta ce dashi.
.
"shi kenan mu tafi.l"
.
Sai da suka fara tafiya taga ya tunkari wata qaramar mota (Civic) wacce ke a bakin hanya sannan ta fahimci shi ne ya zo da motar. Ma'aruf ya bude motar ya shiga kafin Ilham ta bude tata qofar ne ta tambayeshi.
.
"yaushe ka yi ciniki ban sani ba Ma'aruf?"
.
Ya yi dariya.
.
"ba tawa ba ce. Ilham ta wani abokina ne da muke zaune gida daya, shima corper ne."
.
Ma'aruf ya tashi motar, ya tuqa suka tafi.l Ilham tana zaune a gefe daya ya dauki hanya suka kama hanyar fita Katsina. Da taga gudun da yake yi yayi yawa, sai ta tambayeshi cikin wasi-wasi.
.
"wai ina zamu je ne Ma'aruf? naji ka xxe ba nisa kuma kana ta gudu, don Allah ina zamu je?"
.
Ma'aruf ya yi murmushi ba tare da ya dubeta ba ya ce....'
.
"kada ki damu kano zamu je, ai ba nisa ynxn nan zamu je mu dawo."
.
Ilham ta dafe qirji cikin mamaki.
.
"kano...? Ma'aruf ya baka fada mani ba, baka ganin yadda nake? Dubi fa silifas ne a qafata, dubi kodadden gyalen da na yafa. Gsky mu koma gida in canza kaya."
.
Ma'aruf ya juye ya dubeta ya ce.
.
"indai don takalmi da gyale ne ba sai mun koma gida kin canza wasu ba." naji kamar an ce ana sayar dasu a Kano."
.
Ilham ta roqeshi cikin natsuwa.
.
"ynx duk wannan wasan mu ajiyeshi a gefe daya. Ka fada mani gsky. Me zamuyi a Kano Ma'aruf?"
.
Ba tare da ya juyo ya kalleta ba ya ce da ita.
.
" zamu je mu sayi kayan sallah ne. Naji ance atamfar england kike so ki sa a wannan sallar. Shi ne zamu je ki za6i irin wacce kike so ki sa a wannan sallar a Kantin Kwari. Tun sanda labarin yadda kuka yi a gida ya sameni, na dauki alqawarin ko kaina zan sayar in samu kudi, sai kin ci sallah da irin kayan da kike so."
.
A sannan ne xuciyar Ilham ta shiga yi mata kirari:
.
Kin dace da masoyi Ilham....kin dace da mijin aure. Samun masoyi kwatankwacin Ma'aruf abu ne mai wahala a duniya.
.
.
.
Lp=12%%% FARIN CIKI SAU DAYA %%%
PAge 12
.
Daga alqalamin
Shafi'u Dauda Giwa
.
.
Tare da ni
Abu ihsan Bn ishak
(Madugun taska)
.
"TASKAR GIDAN LITTAFI" bata amince da daukar shafin ba."
.
Ilham tana hangenshi ya fito da qwallo, wasu yara manya 'yan aji shida suna biye dashi cike da murna, Ma'aruf ya jasu xuwa filin qwallon makarantar. Ya rabasu gida biyu, ya fara yi masu nasiha, sannan ya sa masu qwallon suka fara wasa, shi kuma ya zama alqalin wasa, ya riqa hura usir yana binsu a guje duk inda qwallon ta nufa,
.
Wasu yara biyu suka yi karo da suna suka fadi suna kuka. Ma'aruf ya tsayar da wasan, ya kama qwallon ya riqe ya dawo da hankalinsa kan yaran da suka ji ciwo. Ya lallabe su suka tashi, sauran yaran suka zo suka zagaye shi.
.
Ma'aruf ya duba raunin da kowanne ya ji ya riqa lallashinsu da kalamai masu dadi, sannan ya kira wani dalibin ya ce dashi ya je dasu ofishin hedimasta a sa masu magani a raunin
.
Ma'aruf yana son daliban kamar yadda suke son shi. Ilham ta sirare ta tafi, ta koma gida ba tare da ya ganta ba." a xuciyarta tana tunanin shin idan ta auri Ma'aruf, haka zai riqa kulawa da 'ya'yanta...'ya'yansu da zasu haifa? Haka zai zama uba na-gari mai adalci da tausayin 'ya'yansa? Haka zai riqa kyautata masu?
.
Sai da yamma da yazo gidansu ta ce dashi tana dariya
.
"Daxu na je makarantar da kake koyarwa, na dade ina kallon ka, baka ganni ba."
.
Ma'aruf ya ce....'
.
"kamar da gaske."
.
Ilham ta ce dashi.
.
"ka tuna lkcn da yaran nan da suke qwallo suka yi karo. Ka tsayar da wasan ka zo wajen su tare da sauran yaran da ke qwallon?"
.
Ma'aruf ya ce da ita.
.
"amma baki yi min magana ba in zo Ilham?"
.
Ta ce dashi.
.
"6oyewa nayi, dama bana so ka ganni. Na ga ka sha gudu kai da yara, ya tsamin jiki?"
.
Suka yi dariya
.
"Ai na saba, bana jin wuya a haka muke wuni muna wannan guje-gujen ni dasu."
.
Ilham ta tambayeshi
.
"kuma da gaske kyauta kake yin aiki a makarantar Ma'aruf' basu biyanka komai?"
.
Ya ce da ita.
.
"Ai ni na san kaina Ilham, ba don kudi nake yi ba, ina yi ne don in taimaki al'ummata da kuma qasata." Ilham ta bi shi da kallo, bata ce dashi komai ba." Ma'aruf ya qara da cewa. "lkc ya yi da ya kamata mutane su fahimci muhimmancin aikin taimakon kai-da-kai.... Duk a yadda ka samu kanka, to ya dace ka binciko irin baiwar da Allah Yayi maka, ka taimaki al'umma da ita ka bayar da taka gudunmawar."
.
Idan mutum ya kalli duniya zai ga cike take da kayayyakin more rayuwa, wadanda wasu mutane suka samar dasu da tunaninsu da basirarsu. Kodayaushe yana da kyau mutum ya jajirce shima ya ga ya samar da wani abu da zai amfani mutane koda qanqani ne....! Koda yaushe na kan dora rayuwata akan wata magana da na yarda sa ita wacce ke cewa."
.
"Hanya daya da zaka rayu har abada shi ne ka bar wani aiki na alheri a bayanka."
.
Ilham wacce ta qurawa Ma'aruf ido ta ce a xuciyarta
.
"Na kamu da so...na kamu da so..."
.
.
.
*** *** **
.
.
Chapter 3 · 0% Book details