← Book details Duhu Da Haske Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
CHAPTER 3 OF 3

Part ɗinsa ya wuce direct ba tare da ya je wajan Iyayensa ba. Dan baya son takura musuduk da kuwa ya san yanzu yana Masallaci.

Duhu Da Haske Part 1 Complete Hausa Novel · about 88 min read

Yana shiga ɗakinsa kayan jikinsa ya rage sannan ya faɗa toilet domin kara watsa ruwa.


"Wanka da alwala ya yi sannun ya fito d'aure da tawul, sai dan karamin tawul da yak'e tsane kansa da shi.


Gaban mirror ya je, kujerar dake gaban mirror ya ja ya zauna, mai ya d'auka ya shafa kaɗan da turare ya mik'e.


Gaban wardrobe yaje, ya bud'e ya turo mlik din jallabiya da gajeran wando, ya saka, sannun ya d'au Sallaya ya shimfiɗa ya t'ada sallar i'sha.


"Yana idar da sallah, bayan ya yi addu'a ya mike ya nad'e sallayar, sannun ya cire jallabiya ya canza kaya zuwa kayan bacci.


Sannun ya hau gabon, bayan ya yi addu'ar bacci sai ya kwanta.


A part din Mami kuwa Mami ce"mkwamce Akan gado bayan ta itar da sallahr i'sha.


Sai Alhaji Muhammad ya shigo ɗakin da sallama a bakinsa.


"Assalamu alaikum?"


"Walaikum salam"

Mami ta amsa daga k'wancen da take.


Ƙarasowa ɗakin Alhaji Muhammad ya yi, ya rage kayan jikinsa shima ya hau kan gadon ya ja Matarsa ya runguma.

"Shine kika barni tun d'azu a part dina ina ta jiranki ko? "


"Haba hubby! ni wallahi kunyar zuwa nakeyi".


"Kaga dai muna da yara, bai kamata daga zuwana nazo na wucena tafi dakinka ba."


Toh ai nikam bana jin kunyar kowa saboda ina ganinki bazan iya hakura ko na minti goma ba, wallahi, dan haka na kawo kaina a taimaka a agaza min.


Ya faɗa cikin marairaice fuska, kai in ka gansa sa ka zaci Saurayi ne yake yiwa buzurwarsa magana.


Murmushi kawai Ammi tayiba tare da tayi magana ba"


Saboda itta kanta tayi missind din mijin nata sosai.


Jikinsa ta kara shiga kamar wata yer baby,murmushi Alhaji Muhammad ya yi ya kara rungumeta sosai a jikinsa.


Hannusa daya ya sa ya tire dan karamin wular dake kanta data rufe gashinta dashillloo


LYa shiga lshafa gashin nata a hankali, ture hannunta daga rungumar da tayi masa tayi ta kama bakinsa ta shiga bashi zazzafar kiss a baki.


Alhaji Muhammad duk ya rikice.


Masu karatu dama kunsan yanda fararen fata suka iya kiss😘in sun kama bakin namiji basa bari har sai sunga lips din yayi ja ta fara kumbura sannun suke bakinka🤣


Humm bari dai nayi shiru🤐


A daren dai sun ciyar da Juna dadi. Saboda Mami kullun kamar Budurwa haka take.


Bangaren Maman su Afiya.


Cikin farinciki ta kwana. Tunda taji za'a hada ta da 'Yyanta Zazzabin dak'e jikinta ya sauka, ko ma ince ta warke, dan lafiya lau ta kwana".


*Washe gari*


Zaune suk’e a kan teburin cin a bincin, gaba dayansu suna cin a binci. Ya shigo palon"


Kara sowa gaban teburin ya yi, ya gurkusa ya gaida Daddy.

"Good morning my Dad?"


Morning my son, ya ka kuwa? "(Alhamdulillah ) Daddy!


Mikewa ya yi ya rungume Ammi ta baya ya yi mata kiss a kumatu, kana yace... (Sabahul khair) Ammi? "Sabahul Nurr Habibi, ya gajiya? "


"Wallahi gajiya (Alhamdulillah ) masha Allah, Ammi ta fada.


Sai a lokacin ya kalli Mummy. Wato (Hajiya Maimuna) yace" Barka da safiya Mummy? "Barka dai ta amsa a takaice"sannun taci gaba da cin din da take ci.


Dan gidan Ammi ni baza ayi min kiss din ba sai Ammi ko?


"Haba Daddy Yanzu kishi kakeyi da Ammi.

Wani irin hararan watsa Daddy ya yiwa Habib.


Ammi ce ta karbi zancewajan cewa... kamar kasani"kuwa Habibi, kishi yake"haba har dake"Nuri!


Ammi bata ce Komai ba sai ma jawowa Habib kujera dake kusa da itta tayi tace.

"Oya maza zauna ka karya".


Murmushi Habib ya yi sannun ya zauna.


"Ya dai kannena?"


"Me kuma ya faru?"

"Ya kara jefah musu tambaya dan yaga duk sun hada rai.


Mufeeda da bata iya fushi ba tace.. Bro ba kai bane tun d'azu muk'e ta faman gaisheka amma ka sharemu ba"


Ayya Sorry my sisters wallahi banji bane"yanzu dai ba wannan ba, k'uyi sauri ku gama cin a binci ku sai ku rakani wani waje.


Cikin murna suka geda masa kai sannun suka ci gaba da cin a binci su".


*Dubaï


Kwana ta yi batayi wani baccin kirki ba"


Saboda kwana tayi tana gwada number wayar sa amma a kashe".


Haka ma na Ammi


Shi ya sa kwana tayi tana tunaninsa, saboda a kwana daya da bata ji muryarsa a gidan ba"jinta take" kamar shekara tayi ba taji muryarsa ba.


Duk da ba wani abu yak’e hada su ba amma ba karamin kewarsa tayi ba.


Kiran Safna tayi dan taji ya kanfaninta yake ciki, saboda kusan kwanan su uku basuyi waya ba.


Dan tun ranar da jirginsu zai tashi ta kirata ta damka amanar kanfani a hannunta,


Duk a bunda ya faru a kanfanin takan kirata ta fada mata, dama yanda suke tafiyar da komai. Suk tana fada mata.


Hello Aunty Afiya


"Naam Safna!ya k'ike ya gida, ya kuma kanfanina? "


Wallahi babu lafiya Aunty, gaskiya ya kamata ki dawo, dan da bakiya nan sai almubazzaranci akeyi da kudin kanfani, kuma abun takaici ma da taimakon Manaja! "suke aikata komai.


"Whattt!


"Wai kina nufin da hadin kan Manaja suke min barna a kanfani?".


"Eh sosai ma kuwa Aunty, jiya na gwada number dinki amma bata shiga dan kwana biyu muna samun mas'alar nertwok a nan"


"Shikenan bari na kira Y'aya Habib tunda yana gari, dan yaxyo jiya".


Tana kaiwa nan ta kashe wayan, ba tare da ta saya jin mai Safna zata ce ba.


*Fulanin jajirtattu ce*✍️
[6/21, 15:24] Mom Muwadda🥰: Utilise ce lien pour intégrer mon groupe WhatsApp : https://chat.whatsapp.com/FJyfKf65hJQApnYM0DV2BU

🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑


*DUHU DA HASKE*


*By*


*Sakeena isma'il Cameroon*
*(Mom Muwadda)*

🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼


https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️

*Marubuciyar*
*Bazan zauna da kishiya ba.*
*Mijin Attajira*
*Mugun Uba*
*Duhu da Haske... Typing✍️*


Page51&52


Bismillahi rahmani rahim


******* Tana kai wa nan ta katse wayan, ba tare da ta tsaya jin mai Safna zata ce ba.


Kano(Nigeria)


Kasancewar sun riga shi, fara cin abinci, shi ya sa suka riga shi kammalawa, "Toh yaya bari muje mu shirya kafin ka kammala cin a bincin."


Kai kawai ya gyd'a musu, kasancewa sun san halin shi tsarai in miskilancin nashi ya motsa, shi ya sa basu damu da rashin amsawarshi ba suka wuce d'akinsu.


Miƙe wa su Ammi da Daddy suka yi suka nufi palo, kuma dama itta Hajiya Maimuna ta dade da hawa sama, tayi musu karya akan cewa kanta ciwo yake mata, dan ta san in ba haka ta fada musu ba, baza su yadda ba.

Ya kammala cin a binci kenan yana goge bakinsa yaji wayarsa da ya dora kan teburin cin a binci ta fara ringing.


Can bangaren kuwa ajiyar zuciya ta sauke, a lokacin da taji wayan na ringing, sannun ta gyara kwanciyarta,
ɗaukar wayar ya yi ya duba ya ga sunan my Beauty ce ta ke yawo akan screen din wayar.


Dafe kansa ya yi daga nan ya furta "Sorry my beauty".


Sai da kiran ya katse sannun ya kirata.
Bugu ɗaya ta ɗauka.

"Hello yaya"

my Beauty , ya kike? "

"Ina lafiya lau".

"Amma me ya sa baka kira;ni ba?"

"Sorry Beauty,na gaji ne shi ya sa ban kunna wayata ba."

"Amma shine daga kai "har Ammi ba wanda ya kirani? "


"Sorry ba zamu sake ba, kinsa itta Ammi tama fini jin gajiyar amma na tabbata zuwa anjima Zata kiraki".


"Shi kenan Allah ya sa. Ameen ya amsa".


"Yauwa yanzu muka gama yin magana da Safna take bani labarin cewa wai Manaja ya hada baki da wasu Ma'aikatan! suna ta min barna da kudin kanfani".


"Subhanallah."

"Ni bamma san ya akayi kika bawa amanar kanfani a hannun mace ba wallahi".


"Ga maza rututu a kanfani, amma. Ki rasa wa zaki bawa sai Mace?"


"Toh ai nafi yanda da itta ne" Shi ya sa na bata."


"Shi kenan bari zanje na duba, duk a bunda ake ciki zan sanar miki, tunda nan da sati daya in sha Allah zaki dawo kasarki".


Cikin murna da farinciki nace,

" Wai da gaske nan da sati daya zan koma. gidanmu? "


"Eh Ko bakiya so?"


Shiru nayi ba tare dana bashi amsa ba.


Dan babu a bunda na tuna sai halin Mamana.


Kamar Habib ya san tunanin da na ke yi, sai yace" Kinga beauty ki kwantar da hankaliki.


"Ai kina da data ko?" "Eh ina da shi".
Okay toh maza- maza kunna datan zan tura miki wani abu".


Kai ta gyd'a sannan ta kunna data, ai kuwa yana online shima, babu bata lokaci ya tura mata bidiyon Mama wanda akayi mata kwanakin baya da suka wuce, wanda take cewa tana son 'yayanta su dawo tayi na dama bazata sake ba.


Dan lokacin bata wani canza sosai ba.


Dan yasan tsarai in ya ce zai tura mata na jiyan nan zata iya yin kuka, shi kuma ya tsani kukanta sosai, dan jin kukan nata yake har cikin ransa, gashi kuma baya ma. Kusa ballantana ya rarrasheta.


Buɗe bidiyon daya tura mata tayi, sai taga bidiyon Mama ce


Tashi daga kwancen da ta ke tayi, ta shiga kallo,
Ta nitso sosai wajan
kallon bidiyon.


Tun kafin ta karasa ganin bidiyon. Wayayen farinciki suka soma silalo mata daga cikin idanu.


Dama bai kashe kiran ba.
Dan haka yaji sautin kukan nata.

"My Beauty me haka?
Allah da na san zaki kuka da ban turo miki bidiyon nan ba."
"Ka yi hakuri, Kukan murna na ke yi 'ya Habib."


Ajiyar zuciya ya sauke a lokacin da yaji ta ce masa ba kukan data saba takeyi ba.


"Duk da haka ba kuka ne ya ka ma ta kiyi ba ya
Kamata ne ki daga hannunki sama kiwa Allah godiya daya nuna mana wannan ranar".


Murmushi tayi. Kana ta shiga share hawayen daya zubo mata.


Sai da ta tabbata babu ko d'igon hawaye akan idanunta, sannun tace.

"Yauwa yaya na share hawayen nawa".


"Okay good"


"Yanzu dai bari naje kanfanin naga mai abun yi, kafin ki dawo."


"Toh shikenan Yaya Habib na gode, Sai ka dawo".


"Okay bye, sai na dawo zan kiraki."


"Okay" ta faɗa


Sannan ta katse wayan.


D'agowa ya yi yaga 'kannensa tsaye akansa.


Hade rai ya yi kana ya ce, "Kallon me kuke min haka, Kamar mayu".
"Haba Bro Yanzu mune mayu? "


"Toh ba dole na kira ku da mayu ba, "kun wani kura min ido sai kace ba wayeyyo ba".


"Toh ai Bro tun dazu muka shirya muna ta maka magana bakaji ba. Sai faman waya kakeyi."


"Toh sai kuma a kace ku saya ku kura min ido? "

"A'a Bro"kayi hakuri."

"Naji mu tafi"


Murmushi sukayi sannun suka wuce tsakiyar palon.
Sai da suka saya suka yiwa su, Daddy sallama sannun suka wuce.


Suna shiga mota, maigadi ya bude musu gate suka fita, ya nufi kanfani, dan so yake ya fara zuwa kanfanin tukun, kafin ya dawo ya dauki Mama.


Comments and share pls😍👏


*Fulanin jajirtattu ce*✍️
[6/21, 15:24] Mom Muwadda🥰: Utilise ce lien pour intégrer mon groupe WhatsApp : https://chat.whatsapp.com/BoEGaUYscLHDtLr41wYFFI

🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑


*DUHU Da HASKE*


*By*


*Sakeena isma'il Cameeron*
*(Mom Muwadda)*


🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼


https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️

*marubuciyar*
*Bazan zauna da kiya ba,*
*Mijin attajira*
*Mugun uba*
*Duhu da haske typing... ✍️*


Page 53&54


Free book


Bismillahi rahmani rahim


**********Su na shiga mota, maigadi ya buɗe mu su gate ya ja motar, su ka fita su ka nufi kanfani, don so ya ke ya fara zuwa kanfanin kafin ya dawo ya ɗauki Mama,


Kasan cewa ba bu go'slow a hanya shi ya sa nan da nan suka isa kanfanin,


Kasancewar ba bu wanda bai san Habib Muhammad Habib ba, shi ya sa su na ganinsa su ku sauka cikin mota da shi da 'kannensa, maaikatan dake wajan su ka ƙara so in da su ke, sannun su ka durƙusa su ka gaishe su, hannu kawai ya ɗaga mu su sannin ya wuce ciki, su ma su Ai'sha su na gama amsa gaisuwar su su ka mara mishi baya su ka nufi cikin kanfani


Su na shiga su ka tarar da wani Saurayi da bazai wuce shekaru 23 ba zaune a inda ya saba ganin Safna da alama shine a matsayin saketare a yanzu, Safna kuma ta koma Offince ɗin Afiya tun da ita Afiya ta damƙawa amanar kanfaninta kafin Allah ya dawo da Ita
Saurayin na ganin Habib ya miƙe ta re da rusunawa ya gaisheshi "Sannu da zuwa Sir."


"Y'auwa sannun ka dai."

"Bismillah Sir da ma Safna ta fadya min zuwanka."
Saurayin ya faɗa
Juyowa Habib ya yi ya kalli k'annensa ya ce"yauwa Mufeeda ku zauna ku jirani yanzu zan fito."
"Toh Bro sai ka fito." Mufeeda ta faɗa haɗe da jawo ɗaya da ga cikin kujerun da ke wajan ta zauna,
"NI dai binka ciki zan yi dan ban san lokacin da za ka fito ba." Ai'sha ta faɗa ha ɗe da marawa Habib da ya fara tafiya da niyar shiga office ɗinn baya,
jin abinda Ai'sha ta ke cewa ne ya sa shi tsai da tafiyar da ya ke yi ha ɗe juyowa, wani irin kallo ya yi mata da har ya sa hanjin cikinta kaɗawa, ba shiri ta ja kujeran da ke kusa da ita ta zauna,
Juyowa ya yi ya karasa office ɗin,ba tare da ya tsaya kwankwasa wa ba ya tura ƙofar ya shiga, ya mai da shi ya rufe,
tun da ya shigo su ke kallon sa har ya ƙara so gaban su,
Habib kuwa kallo ɗaya ya yi mu su ya ɗauke kai,
"Sannu da zuwa yellabaï." Safna ta faɗa ha ɗe da miƙewa tsaye, sannan ta ci gaba da cewa "bismillah ga kujera ka zauna." ta faɗa ta na nuna mai kujerar da ta miƙe akai,
Habib bai zauna ba, sai ma kallon Basira da ke zaune a dayan kujerar ya yi sannan ya mai da kallonsa kan Safna ya ce "Waye wannan Ko ita ma Ma'aikaciyar ku ce?." kafin Safna ta buɗe baki ta yi magana Basira ta rigata cewa "hy Sir ka mantani ne.?" ta faɗa ta na turo ƙirji gaba ha ɗe da kashe mai ido ɗaya
" Tambayar ki ni ke kin yi shiru." Habib ya faɗa fuskar nan kamar bai taɓa dariya ba,


"Yellabaï Yayar k'awata ce ta kawo min ziyara."


"Nan gidanku ne da za ta kawo miki ziyara,?"


"A'a Yallaɓai ba gidanmu bane."


"Toh da ga y'au kar na ƙara ganin wata ta zo miki nan da sunan ziyara, duk wadda ta ke son je miki ziyara taje gidanku Kinji ni.?"

"Eh naj.i"

"Good!. "

Mai da dubansa ya yi kan Basira kana ya ce"ke malama tashi kifita kuma in kin fita karki sake dawowa nan wajan da sunan ziyara." da sauri Basira ta geyɗa kai ha ɗe da miƙewa har ta na tuntube,

Aguje ta zo ta wuce su Mufeeda ta bar wajan,
"Sis kinga wata ta fito a soro ce da alama Bro ne ya yi mata wannan fadan nashi."

Mufeeda tayi maganar ta na dariya
Taɓe baki Ai'sha ta yi ba ta re da ta ce komai ba,


A cikin office kuwa ƙara sowa Habib ya yi ya zauna akan kujerar da Safna ta nu na mai d'azu, sannun ya nu na mata ita ma kujerar da Basira ta ta shi akai da hannu alamun ta zauna.
Ai ba shiri ta ƙarasa ta zauna,


Sai da su ka ɗau kusan 3 minunt a haka sannun ya fara magana kamar haka "d'azu Afiya ta faɗa min kin kirata kin faɗa mata cewa ana barnan kuɗi a cikin kanfanin nan."
"Eh haka ne Yallaɓaï."
"Saboda mi ba ta d'au amanar kanfanin ta bawa kowa ba sai ke.?"

"Saboda ta Yadda dani kuma ta tabbata zan kulan mata da kanfanin shi ya sa ta bani."


"Good."

"Toh amma me ya sa kikaci amanarta.?"


"N.. N... N... Ni kuma Yallll... La ɓaï?"Safna ta ha ɗa kalmar nu ɗin da kyar wajan furtawa, don yanzu kam ta fara tsorata da Habib mutun kamar mai aljanu,


"Mu nawa ne a nan da za ki tambayen.? "


"Mu kadai ne."

"Toh amsa min tambaya ta."


"Toh.toh.toh zan amsa."

"Ina jinki."


"Dama........


Toh fah safna dama me? 🤔


Fulanin jajirtattu ce✍️


Comments and sharee pls👏
[6/21, 15:24] Mom Muwadda🥰: 🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑


*DUHU DA HASKE*


*By*

*Sakeena isma'il Cameeron*
*(Mom Muwadda)*
*Marubuciyar*
*Bazan zauna da kiya ba*
*Mijin Attajira*
*Mugun Uba*
*Duhu da Haske typing... ✍️*


tilise ce lien pour intégrer mon groupe WhatsApp : https://chat.whatsapp.com/BoEGaUYscLHDtLr41wYFFI


https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauki. ✏️


Page 55&56


Free book


Bismillahi rahmani rahim


**********"Mu ka d'ai ne".
"Toh amsa min tambaya ta.
" Toh Toh Toh zan amsa"
"Ina jinki? "
"Dama Manaja ne ya min bara zana cewa in har ban ba shi had'in kai ba sai ya min a bunda bazan ta'ba mantawa da shi a rayuwata ba"
"Hadin kai na me zaki bashi?"


"Dama...." Magana Safna ta fara yi ya dakatar da ita ta hanyar d'aga mata hannu, wayarsa ya d'auka ya danna recoding sannun ya ya:ce" Zaki iya ci gaba ina jinki".
"Dama a kwai wata rana da na tashi yin lissafin abubuwan da a ka siya sai na ga kaya dayawa ya 'bata, dan kusan a tampofi guta dari da ashirin da lesis guda amsin da nayi bincike na gano cewa ashe ma da sa hannunsa kayan suka 'bata, shine na je nayi masa magana na kuma k'ara da cewa in har bai sa an dawo da kayan nan ba sai na fadawa Aunty Afiya.Da farko ya fadamin cewa kar na fada in sha Allah zai biya kud'in kayan tun da ya riga da ya siyar da kayan
Da haka dai muka bar zancen akan cewa zai biya kud'in kayan da suka 'bata".


"A haka na koma office d'ina, watoh office Aunty. Bayan an tashi ne na fito da niyar in samu abun hawa sai muka had'u da shi_shima zai shiga motarsa ya wuce gida shi ne ya ce in baza na damu ba mai zai hana in shiga ya ajiye ni a gidan daga nan ma sai ya je banki ya ciro kud'i ya mayer wa kanfani".


Jin cewa zai mayar da kud'in kanfani ne ya sa ni amince wa na shiga muka wuce".


"A bunda ban sa ni ba shi ne a she ba haka ne a ransa ba.Muna hawa titi ya kalleni ya ce min "Bismillah ga ice cream, kasan cewa ina son ice cream sosai a rayuwa ta shi ya sa ba musu na kar'ba na fara sha.
Shan ice cream ne ke da wahala sai kawai na ji ina jin wani irin baccin da ban taba ji irinsa ba"
"Babu 'bata lokaci kuwa na bingire a wajan sai bacci.Daga nan kuma ba san a bunda ya faru badan lokacin da na farka gani na nayi a wani d'aki
Kalle-kalle na shiga yi
Sannan na ce wai waye kamo ni nan gidan?"

"Na tambayi kai na a lokacin dana farka na ganni a wani d'aki.


"Shiru nayi ina tuna lokacin da yace min na shiga mota ya kai ni gida
Ina cikin wanan tunanin ne ya fito daga wanka daga shi sai tawol a kan k'ugunsa, ina gani haka jikina ya d'auki rawa dan tuna nake ban taba ganin na Miji a haka ba.


"K'arasowa ya yi gabana yana dariya sannan ya hau gadon ya finciki hijabin dake cikina da karfi, sai na fada jikinsa, k'ok'arin kwace kai na na shiga yi amma na kasa, dan ba karamin riko ya min ba,
magana ya fara min kamar haka."

"Ke ki tsaya ki saurare ni in kuma ba haka ba...."

Bai k'arasa maganar ba na ga ya fara l'alubata, wani irin riko ya yi wa k'irjina nan da nan kuwa na fahimci mai yake nufi wato yana nufin in har ban saya na saurare shi ba zai min fiyad'e!"
Ba shiri na ce "Ina jinka ka fad'i koma mene ne zan yi in har zaka bar ni da mutunci na"


Wani irin dariya ya kara shekewa da shi sannan ya gyara zama ya fara magana kamar haka;
" Dama so na ke ki janye maganar nan".

"Waca magana kake magana akai?"
"Maganar da muka yi d'azu na cewa lallai sai na biya kud'in kayan nan da na sata"

"Toh ai ni a tunani na mun riga da mun gama wannan maganar, tun da har kace zaka je ka ture kud'in a Banki ka mayar musu"
" Ke a tunaninki zan bayar?"."toh bari kiji ko sisi bazan bayar ba
Dan haka kar ki kuskura ki cewa Afiya ni ne na d'auki kayan nan in ba haka ba kuma, sai na zubar miki da mutuncin ki da kike tak'ama da shi in ya so sai muga ya zaki yi, ko Afiyan ce zata dawo miki da budurcin"

"Wallahi in dai zaka barni da mutuncina na tafi gida Allah bazan fad'i ba
"Kuma dama ni ka d'ai na sani dan haka na jan ye komai ba zan fada ba"
Shi ke nan bari na shirya sai na mai da ke gidan ku, amma zan rufe miki fuska"


Kai na kawai na gyad'a masa sannan ya mik'e ya d'auki kayan sa,ya koma toilet ya shirya ya dawo d'akin ya d'auki key d'in motarsa da wani kelle ya rufe min fuska muka fito ya bude min mota ya taimaka min na shiga sannan ya ja motar muka bar gidan.


Can nisa da layin mu ya yi parking sannan ya bud'e min fuska , sai daya kara jadda da min cewa in har na tona masa a siri shi ma sai ya lalata min rayuwa. Sannan ya bar ni na fita ya ja motarsa a guje ya bar layin
Ni kuma na k'ara sa gida"

"Da na je gida,da Mama ta ga ba kamar yanda ta saba gani na kullun in na dawo daga wajan aiki ba shi ne ta tambaye ni lafiya? Nace mata kai na ne yake min ciwo, shi ne ta ce na je na samu magani na sha sai na kwan ta, na amsa mata da toh sannun na mike na shiga daki".


"Tun ranar ban kara yiwa Manaja maganar biyan kudi ba"

"Amma kuma duk lokacin da na tunani cewa ga a bunda Manaja ya yi kuma ban gayawa Aunty ba,sai in ji kamar amanar ta naci"

"Kullun Ummana na lura da ni, dan haka wata rana ta tambaye ni me ya ke damu na, kasan cewa ban iya k'arya ba shi ya sa na kwashe komai na fad'a mata amma abu d'aya na boye mata shi ne d'auka na da Manaja ya yi ya kai ni gidansa ya yi min bara zana da in har na tona masa asiri zan rasa budurci na, shi ka dai na boye mata saboda na san in na fad'a mata ba kara min fada zan sha ba,na rashin gaya mata da wuri da ban yi ba".

"Ummata ce ta bani shawara cewa na fada wa Aunty Afiya komai, dan shiru da nayi zai iya j'awo min babbargas'ala".


"Shi ya sa yau ina zuwa kanfani na kira Aunty na fad'a mata komai"


Ajiyar zuciya Habib ya sauke sannun ya koma ya zauna, dan tun d'azu ya ke saye, saboda abun ba kara min bata masa rai ya yi ba.


"Y'auwa kina ji na?"

"Eh ina jinka Yellabaï!"


"In mun fita kar kiyi a bunda zai sa ya gano cewa kin fada min wannan maganar".


" Toh Yellabaï! "

"Saboda a kwai wani shiri da nake son yi kafin gobe".


"Ni na wuce in lokacin tashi ya yi ki wuce gida ke ma"

"Toh yallabï!"


Shi kuma Habib na gama fad'ar haka ya sa hannu ya d'auki wayoyin sa daya ajiye kan teburin sannun ya bar offince din.


*Fulanin jajirtattu ce✍️*


Comments and share pls👏
[6/21, 15:24] Mom Muwadda🥰: 🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑


*DUHU DA HASKE*


*By*

*Sakeena isma'il Cameeron*
*(Mom Muwadda)*
*Marubuciyar*
*Bazan zauna da kiya ba*
*Mijin Attajira*
*Mugun Uba*
*Duhu da Haske typing... ✍️*


tilise ce lien pour intégrer mon groupe WhatsApp : https://chat.whatsapp.com/BoEGaUYscLHDtLr41wYFFI


https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauki. ✏️


Page 57&58


Free book


Bismillahi rahmani rahim


********** Habib na gama fad'ar haka ya sa hannu ya d'auki wayoyin sa daya a jiye akan teburin sannun ya bar office din.


Bude kofar ya yi ya fita ya bar office din,


" Ni wallahi sister in ba zaki tafi gida ba ni zan tafi"Ai'sha ta yi maganar,dan ba karamin haushi taji ba da Habib ya shiga ciki tun dazu ya barsu zaune.
"Wallahi nima na gaji.amma mu dan kara ko da minti goma ne in bai fito ba sai mu fati"Mufeeda ita ma ta fada,dan ita ma harga Allah ta gaji,
"Ni wallahi da ya sani gidan Aunty Maryam ya kai mu" Mufeeda ta kara fada.
"Ƙe kuwa sister me zaki yi a gidan Aunty Maryam tunda baki da sa'arki a can da zaki ce zaki je wajanta"
"Wajan Aunty Maryam zan je mana.kuma da ki ke cewa babu sa'a ta a gidan Aunty Maryam,ita Ai'sha ba sa'ata bace ba ne?".
"Jiki tsoron Allah sis.yanzu dan Allah Ai'sha sa'arki ce?"ke yanzu har kina sha'awa Zama sa'ar Aunty Ai'sha ?"
"Toh me a ciki ita ba mutun bane?".
"Kin ga karki fassa'rani,gani nayi kin fita yarinta da komai,ba dan wannan abokin Oncle Safwan yace yana sonta bama da har yanzu bata samu mijin aure ba,dan wallahi ta fara sufa,kin ga fah ta kusa 30 dan yanzu tana 27!"
Ai'sha ta kare magana.
Wallahi Ai'sha ki dena "wannan halin naki,yanzu dan Allah ya dace ki dinga fadar haka?"ai ko ba komai yanzu kam ta samu Kuma zata yi aure"
"Kuma da ki ke cewa bata samu mijin aure da wuri ba,mu mun samu ne?".
"Kinga sister karki hada ni da ƙe dan kin san sarai na fiki kyau da komai,kuma da ki ke cewa mu ma bamu samu ba,ni kinfi kowa sanin ina da shi kuma in sha Allah kwa nan _nan zai turo kuma dama can nice ban bashi dama ba".


Tabe baki Mufeeda ta yi hawayen da take rikewa tun dazu suka samu damar zubowa,dan ita abu kadan yake sata Ku ka,


Tun ɗazu Habib ya karasa wajan su ya ji suna magana,Shi ya sa bai yi magana ba,sai ma hannunsa da ya zuba jikin aljiwu,kasan cewa dama ɗabiyar sa ce yin hakan.


Gyaran murya ya yi duka suka dago suka zuba masa ido.


Saurin goge hawaye Mufeena ta yi dan ta san sarai in yaga hawayen sai ya tabbayeta me ya sa ta ku ka.

“Sorry na barku kuna ta jira na.ku tashi mu tafi ina so na kammala duk a bunda zan yi kafin 1 na rana".


Miƙewa suka yi,suka soma barin offince din Saketara sai suka ji muryarsa ya yi magana "ke Ai'sha juyowa Ai'sha ta yi tace"na'am Bro Mufeeda sa'ar kice ?"a'a ba sa'ata bace.toh me ya sa ki ke mata wani abu kamar kin samu sa'ar ki?"
"Ba komai Ai'sha ta kara cewa.
"Toh bata haƙuri, haƙuri fah kace Bro?"eh haƙuri nace.ko ba zaki bata ba ?"
"Ban ce ba, amma fah da shekara ɗaya fah kawai ta girme ni,ko da wata daya ta girmeki Ƴayar kice dan haka ki bata haƙuri"
Turo baki gaba Ai'sha ta yi sannun tace "ki yi haƙuri"

"Ba komai ya wuce"

“Mu tafi toh mara kunya"

Sumsum tabi ta kefan su ta fita kamar mutafiki.


Suma fita suka yi. bayan ya yi sallama da sakatare.


Suna barin kanfanin ya wuce gidansu,a gaban gate din gidansu ya yi parking ya juya ya kalli Ai'sha dake zaune a bayan mota "ƙe Ai'sha"ɗagowa Ai'sha ta yi ta amsa da "na'am Bro"
"Sauka ki wuce gida".

"Toh Bro ku kuma ina zaku je?"."ina ruwanki fita nace "


Tabe baki Ai'sha ta yi sannun ta fita ta shiga gida ta karamin gate.

Shi kuma Habib ya yi ravas suka kuya ya bar wajan ya nufi gidan su Afiya.


"Bro ina zamu ?"Mufeeda ta tambaya cikin sanyin murya.
"Ina so zan dauko wata yer uwar mu anan sai ki kai ta salon da kuma gyaran jiki,dan ta sha jinya kwana biyu tana kwance ba ta da lafiya,duk ta canza,kuma kinga ta kwana biyu bata hadu da yan uwa ba,bai kamata su ganta haka ba"
"Haka ne kam Bro".
"Amma me ya sa baka taba kawo mu wajan ta ba?".

"Ina na ganki da zan kawo ki dududu yaushe ma ku ka dawo Nigeria!"

"Haka ne Bro "


"Bari na kira Yusuf ya gaya mata ta fito mu tafi dan nasan ta dade da gama shiryawa"ya fada yana dauko wayarsa daya ajiye a gefen sa,


Kiran Yusuf ya yi yana dagawa yace "y'auwa Yusuf ki faɗawa Mama ina kofar gida ta fito mu tafi"ta can bangaren Yusuf ya amsa da"toh yellabaï!"


Kashe wayan ya yi ya jingina bayansa da jikin kujeran ya lumshe kyawawan idanunsa.


Tunani ne kala _kala a ransa kuma gaskiya ya na nemon ma fita.


*Cikin gidan su Afiya*


Yusuf ne ya shigo cikin palon da "salama"kana ya kalli Mama dake zaune kan kujera tun ɗazu ta shirya ta na jiran Habib ya zo ya kai ta wajan dan autanta,
Kallon Mama Yusuf ya yi yace "Mama ga yellabaï ya zo yana bakin gate ya ce na fada miki ki fito".


Ai Mama na jin haka ta miƙe tana cewa "mu je toh Yusuf"!kai Yusuf ya geɗa sannun ya bi bayan Mama suka fita.


Kasan cewa Mama na da kaya masu sada da Afiya take siyo mata Shi ya sa ta fito fess kamar masu kudi,se dai kawai raman da kuma baƙi da ta yi ne kawai ya dan kwaf sa mata.


Fitowa suka yi Habib na ganin su ya fito daga mota, rusunawa ya yi ya fara gaida Mama "Mama ina kwana?"."lafiya lau yellabaï"dan Allah Mama ki dena kirana da yellabaï ki kira ni da sunana Habib in har kina so naji dadi"
Mama zata yi magana Habib ya yi surin Katse ta ta hanyar cewa"Mufeeda ga Mama ki fito ku gai sa "kai Mufeeda ta geda sannun ta sauko daga cikin mota ta shiga gaida Mama,"Mama ina wuni lafiya lau alhamdulillah ƴata ".
"Habib kanwarka ce ?"

"Eh Mama kanwata ce"


"Ma sha Allah"


"Bismillahi!Mama shiga mota mutafi "
"Toh ɗana"Mama tace sannun ta shiga bayan mota da Habib ya bude mata ta shiga,ya rufe ya zaga zai shiga ta ma zaunin dreve sai Yusuf ya riga shi shiga"kaga Yusuf koma ɗayan sit din ka zauna ka bani na tuƙa".

"Gaskiya yellabaï ka yi haƙuri amma ni zan tuka dan bazan taba barin ka tuƙa mu ba, bayan muna tare "


Habib bai sake magana ba ya koma dayan sit ɗin ya shiga Yusuf ya ja mota suka bar layin....


*Fulanin Jajirtattu ce*


Comments & share pls👏
[6/21, 15:24] Mom Muwadda🥰: 🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑


*DUHU DA HASKE*


*By*


*Sakeena Isma'il Cameroon*
*(Mom Muwadda)*
*Marubuciyar*
*Bazan zauna da kishiya ba*
*Mijin Attajira*
*Mugun Uba*
*Duhu da Haske typing...✍️*

Utilise ce lien pour intégrer mon groupe WhatsApp : https://chat.whatsapp.com/BoEGaUYscLHDtLr41wYFFI

https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️


Page 59&60


Free Book


Bismillahi rahmani rahim


**********Habib bai sake cewa komai ba ya koma dayan sit din ya shiga ya zauna Yusuf ya ja mota suka bar layin,
A wani ƙaton shagon da aka rubuta a samansa beauty Salon and gyaran jiki ne Yusuf ya yi barking ,dan tun jiya da daddare ya faɗa masa in da zasu fara zuwa kafin a je gidan Aunty Maryam,

Wata jaka daya fito da shi daga gida ne,ya buɗe,tattausan hannunsa ya saka ya d'au banɗir ƙuɗi guda biyar a ciki,in da a ce za'a irga zasu iya kai rabin million,wata leda mai kyau ya ɗauka a cikin motar ya saka ƙidin a cikin sannun ya juya bayan shi,yace "tek sister"!karɓa Mufeeda ta yi sannun ya ci gaba da cewa "y'auwa kuje ayi duk abunda ya ɗace"."okay Bro Mufeeda ta faɗi haɗe da juyowa ta kalli Mama gake gefan ta ta ce "sauko muje Mama"kallon ta Mama ta yi sannun ta ce"ƴata nan ne Mohseen nawa ya.....bata karasa ba Habib ya kase ta ta hanyan cewa"Mama kawai ki bita ku shiga kuma dan Allah ki bari ayi miki duk a bunda ya ɗa ce in har kina so na cika miki alkawarin da nayi miki jiya kuma muna gama da nan ma a sibiti zan kai ki a kara duba jikin ki da kyau a baki magani"."Toh na amince zan bita mu shiga cikin amma dan Allah ba sai ka kai ni a sibiti ba,dan wallahi na warke"
"Shi ke nan Mama naji Amma sauka ku je anjima kaɗan zan dawo, kallon Mufeeda ya yi sannun ya ce yauwa sister in kun kusa gama wa ki yi min waya "
"Toh Bro"Mufeeda ta amsa sannun suka fita suka nufi cikin wajan.
Jinginar da kansa ya yi da jikin kujerar motar ya lumshe ido,ganin da Yusuf ya yi ba magana zai yi ba ne ya sa shi buɗe baki yace "yellabaï anan zamu jira su ne ?"
A'a ya faɗa a takai ce,taɗa mota Yusuf ya yi,ya bar wajan a zuciyarsa kuwa faɗi yake'yau kuma muskilancin ya motsa ke nan
Sai da suka hau titi sannun ya juya ya kalli Yusuf kana ya ce "kanfanin mu zaka kai ni"
"Toh yallabai amma kasan ban san kanfanin ba"
"Muje zan nuna maka"

"Toh yellabaï"

Kotan ce ya shiga yi masa har suka kara sa kanfanin na su.

A wani babban gini naga Yusuf ya yi barking,kallon ginin Yusuf ya shiga yi dan tun ylda yake bai taba ganin kanfanin irin sa ba a (Kano)

Ma aikatan wajan na ganin shigowar motar suka tawo dan sun san dan Alhaji Muhammad Habib Ibrahim ne ya zo,

Kowa sai zuwa ya ke yana kwasar gaisuwa,shi kam Habib hannu kawai yake ɗaga musu sannun ya juya ya kalli gefen sa inda Yusuf ya ke saye kana ya ce "mu je"
Kai Yusuf ya geɗa masa sannun suka wuce ciki,sama suka hau kasan cewa sai an wuce office din sakatare kafin a karasa office din sa shi ya sa suna shiga office din saketare ya miƙe saye haɗe da rusunawa ya shiga yi musu sannu da zuwa "Welcome Sir"
"Thank you"ya amsa a takai ce

"Sannu da zuwa"saketare ya yi wa Yusuf ma"amsa wa Yusuf ya yi cikin sakin fuska sannu ya ce "ya aiki?"da alhamdulillah sakerate ya amsa.


"Muje Sir"


Kai Habib ya geɗa sannun ya bi bayan sakerate, Yusuf ma bin bayan su ya yi,suka shiga ciki


Ina yin ido huɗu da office din babu a bunda nake furkawa sai "wow da ma sha Allah" Kaɗai nake furtawa,dan ba kara min kyau office din ya yi min ba.
Duk da bai kai office dinsa dake (Dubaï)ba amma shima wannan din na da kyau sosai,
Zama Yusuf ya yi akan kujerar dake fuskantar na Habib,
Sannun shima ya karasa kan nashi kujerar sai daya saka hannun shi ya shafa wajan don ya tabbatar an goge masa yanda ya ke so,dan wannan ɗabiyar sa ce nayin hakan.


Yana shafawa ya dago ya kalli saketare dake saye cikin bacin rai ya fara magana "wai dama baka sa an share min office din nan ba ka bar ni na shig a haka har ka ke kallo na_ na bar baƙo na ya zauna akai?"
"Sorry Sir an share jiya ganin da nayi ba anfani aka yi da office din ba ne ya sa ban sa an share y'au ba".
"Kalle ni da kyau Paisal kafi kowa sanin bana son kazan ta,kai nifah in dai akan kazan ta ne zan iya bata wa da mutu kai Yusuf ka tashi mu tafi ka kuma yi hakuri da ɓata maka kayan da ya yi"yana kaiwa nan ya juya ya bar wajan


Baki sake Yusuf ya ke kallon Habib dan tunda ya ke dashi bai taba ganin ya yiwa wani faɗa ba.


Shi a bunda yafi komai bashi mamaki ma bai ga datin da office din ya yi ba ballanta na ya ce zai ɓata masa kaya.


Shanye mamakin sa ya yi ya miƙe ya bi bayan sa dan shi Habib har ya ma bar office din,haka ma saketare
Dan ya bi bayan sa yana bashi hakuri
"Shi ke nan naji amma karka sake min haka,ka saka a share min gobe da safe kafin na shigo office"toh Sir in sha Allah bazan sake ba"
"Good"


Habib ya faɗi sannun ya juya ya kalli Yusuf daya karasa wajan yanzu sannun ya ye "mu je Yusuf"!

"Toh yellabaï"

Suna barin kanfani ya umarci Yusuf da in ya ga supermarket ya saya


Yusuf na ganin katon supermarket ya yi barking sannun ya juya ya ce "yellabaï wani abu zan siyo maka ne?"
Ba tare daya bawa Yusuf amsa ba ya balla murfin motar ya fita sannun ya ce"biyo ni"
Kai Yusuf ya geɗa sannun ya fito daga cikin motar ya bi bayan shi suka shiga ciki.


Bangaren kayan maza ya nufa,wasu riga da wando ne mai masifar kyau da sada ya tiro ya miƙawa Yusuf karɓa Yusuf ya yi kana yace "shiga ciki ka goda"ya faɗa hade da nuna masa wani dan karamin daki da ake shiga ana goda kaya
Baki Yusuf ya buɗe da niyar yin magana ya daga mata hannu sannun ya kara nuna masa dakin,
Ba yanda Yusuf ya iya haka ya wuce ya shiga dakin,babu jima wa Yusuf ya fito ya yi kyau sosai dan in kagan sa zaka d'auka shima dan gidan masu ƙuɗi ne,sai in ka kalli fuskarsa ne zaka fahimci shi ba dan gidan masu ƙuɗi ba ne ,amma bayan wannan babu komai,dan Yusuf kyakkyawa ne,yana da kyau dai dai gwargwado,duk da kuwa baƙi ne amma ba can_ can ba,


Murmushi mai kyau Habib ya yi sannun ya furta "ma sha Allah ka yi kyau sosai Yusuf"


"Na gode yellabaï amma banga mai kayan nawa ya yi ba da har zaka sai min wannan"


Habib bai ce komai ba sai ma barin wajan daya soma yi,ganin hakan da Yusuf ya yi ne shima ya yi saurin bin bayan sa da wayen nan kayan daya tire.

Wajan biya ya je ya biya sannun ya mikawa Yusuf sauran ledan suka bar wajan

Suna fita yaga wasu ma barata ya am shi soffin kayan da Yusuf ya tire ya mika musu, godiya suka shiga yi masa shi kam bai saya amsa musu ba ya yi gaba abun shi,


Baki sake Yusuf ya bi bayan Habib da kallo,dan shi bai ga a bunda kayan ya yi ba da har zai bawa mabarata.


A wajan Salon kuwa,gyaran jiki aka yiwa Mama sai wanki kai da kitso, ba kara min kyau Mama ta yi ba,ga kuma wani irin kamshi da take yi,kasan cewa Mama ba wani babba bane sosai ba, shi ya sa in ka ganta sai ka dauka amarya ce,


Dan ko Ammi da Mommy da Aunty Maryam zasu girme ta,


Da Mufeeda ta ga an kusa kamma lawa Mama kitso ne ta d'auri waya ta kira Habib domin ta sheda masa cewa sun kusa gaba wa,

Kara sowar su Habib ke nan daga wajan ya d'auki wayan zai kira Mufeeda sai yaga kiranta ya shigo cikin wayarsa,yana ɗaga wa ta ce "Bro mun kusa gama wa"
"Okay ina waje"

"Toh Bro sai mun fito"

Bai amsa ba ya kashe waya.


Bai fi minti 5 ba suka gama Mufeeda ta biya mai Salon ƙuɗin ta sannun suka fito,


Suna fita kuwa suka hango motarsa

Kara sowa suka yi ta buɗewa Mama bayan mota ta shiga sannun ita ma ta buɗe ɗayan sit ɗin ta shiga sannun Yusuf ya ja motar suka bar wajan......


*Fulanin Jajirtattu ce*


*Comments & share fisabilillah*👏
[6/21, 15:24] Mom Muwadda🥰: 🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑


*DUHU DA HASKE*


*By*

*Sakeena Isma'il Cameroon*
*(Mom Muwadda)*
*Marubuciyar*
*Bazan zauna da kishiya ba*
*Mijin Attajira*
*Mugun Uba*
*Duhu da Haske typing...✍️*

Utilise ce lien pour intégrer mon groupe WhatsApp : https://chat.whatsapp.com/BoEGaUYscLHDtLr41wYFFI


https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️


Page 61&62


Free Book


Bismillahi rahmani rahim


***********K'arasowa suka yi ta buɗe wa Mama bayan mota ta shiga sannun ita ma ta buɗe ɗayan sit din ta shiga Yusuf ya ja motar suka bar wajan.

Ba su tsaya ko ina ba sai kofar gidan Aunty Maryam fitowa duk suka yi daga cikin motar,kallon Mama Mufeeda ta yi kana ta ce "Mama kizo mu shiga ciki".
"Toh mu je"
Mama ta fadi cikin zumuɗi dan babu a bun da take son gani a yan zu sama da Muhsin dan ta yi kewarsu sosai daga shi har Afiya.


Kara min gate din suka nufah sai Habib ya dakatar da su ta hanyar fadin "ku dan tsaya sister"!

Dakatar da tafiyan suka yi ya ciro waya daga cikin aljiwun shi ya shiga nemo number "Aunty Maryam yana ganin number d'in ya ya danna mata kira amma har ta tsinƙe ba ta ɗaga ba.

Ita ko Aunty Maryam tana nan tare da baƙi shi ya sa gaba ɗaya bata ji kiran ba, saboda bata ma san inda ta ajiye wayan ba ma.


Shi kuwa Habib ganin da ya yi har 2 miss call ya yi mata bata d'auka ba ne ya sa shi mai da wayarsa cikin aljiwu

Muhsen ne ya shigo ɗakin da gubu ya na faɗin "Mommy ana ta kiran ki tun ɗazu".Mommy da take ta faman shirye- shirye yan da za'a gudanar da Kamu gobe ne ta juyo ta ce "Wa ya ke kira na Boy?"
"Mommy my Son naga ni"
"Maza bani wayan na kira shi dan Habib bai cika kirana haka Kawai ba sai da dalili"

Mik'a wa Aunty Maryam waya Muhsen ya yi ya juya zai tafi sai kuma ya tsinci kansa da dakatar da tafiyan saya wa ya yi ya na kallon Aunty data fara magana a waya"Sorry Son abubuwa ne suka min yawa shi ya sa ban ji kiran da ka min ba".
"Okay dama muna tare da Maman Muhsen ne shi ya sa na ce bari na kira ki kafin mu shigo ciki".
Okay ka yi kyan kai,bari na d'auko key din bangaren Abban Safwan sai na buɗe mana can dan nan part dina akwai muta ne sosai kuma na san baka son muta ne ga shi kuma kana tare da Maman Muhsen"
Lumshe ido ya yi ya buɗe su dan har ga Allah baya nin da take masa sun ishe shi gaba ɗaya.


"Okay" ya faɗa haɗe da kashe wayan dan ya san part din Abban su Safwan d'in shi ya sa ya kalli Mufeeda "ya ce ku zo mu shiga"

Ya juya ya kalli Yusuf ya ce "y'auwa Yusuf ka d'an jira ni yan zu zan fito mu tafi"
"Toh yellabaï a fito lafiya"
Kai kawai ya geɗa sannun ya wuce ciki ya bi bayan su Mufeeda da tuni sun shiga.
"Ke Mufeeda kuxo mu je ba a nan ta ke ba"
Kai Mufeeda ta gyaɗa kana suka bi bayan shi suka nufi part din Abban Safwan.
Suna zuwa suka tarar da Aunty Maryam na ciki dan shigowar ta part din ke nan tare da Muhsen


Dan bayan ta gama waya da Habib ne ta ce wa Muhsen ya zo su je part din Abban ya taya ta d'auko wani abu ya ce "toh"
Sannun ya bi bayanta suka zo.


K'arasowa Aunty Maryam ta yi baƙin kofar shiga palon ta shiga yi wa Mama sannun da zuwa "sannu da zuwa Maman Afiya dan ba zan ce miki Maman Muhsen ba tun da yan zu Muhsen ya za ma nawa"Aunty Maryam ta faɗi tana dariya.
Mohsen dake z'aune sakiyar palon ya na dadda waya ne ya dago ya zuba wa Mama idanu,sanun ya miƙe cikin farinciki ya nufo ta da guɗu har ya k'arasa gabanta ya buɗe hannayensa biyu da niyar yi mata oyoyo sai ya tuna lokacin da ya ke gida in ya dawo daga makaranta in ya zo zai rungumeta ta ke hana shi din nan,sai kawai ya ja baya yana murmushi haɗe da cewa "Mama sannu da zuwa"
Jikin Mama ne ya yi san yi sosai tabbas ta san dalilin daya sa Muhsen yaƙi rungumarta,
cikin zuciyarta ta furta ya Allah ka ya fe min na tuba'
Mufeeda kam gaba ɗaya ta cika da mamaki, tambayoyi ne kala _kala a zuciyarta amma babu mai amsa mata shi.

Mama kam hawayen na dama ne ya shiga sauko mata daga kan kumatunta.
Habib da Aunty Maryam kuwa tausa yin Mama da Muhsen ne ya kama su,sun san cewa ta yi na dama sosai.
Kallon Muhsen Habib ya yi kana ya ce "Muhsen ba kaga Uncle ba ne ?"
"Sorry Uncle ina wuni ina Aunty Afiya ta ke me ya sa baka zo da ita ba?".
"Sorry zata xo kwa nan_ nan"


"Amma kafin nan ina so ka je ka rungumi Mama dan na san ita ma ka yi kewarta sosai"


"Toh Uncle ina son rungumarta amma bata so"
"A'a ita ma tana so ka je ka gwada zaka gani"


"Da gaske ita ma tana so?"
"Eh tana so je ka kawai" Karasowa Mohsen ya yi ya tsaya gaban Mama amma ya kasa rungumar ta,

Hannu Mama ta buɗe wa Muhsen tana murmushi shi ma Mohsen murmushi ya yi haɗe da faɗa wa jikin Mama.


A tare suka s'auke a jiyar zuciya.


Allan sarki saka nin ɗa da uwa sai Allah 😢


"Aunty ina wuni "Mufeeda ta faɗi lafiya lau Mufeeda ya gida?"

da"alhamdulillah"Mufeeda ta amsa, Aunty ina Aunty Ai'sha Amarya?"
"Tana ciki ta yi fushi daku daga ke har Mamana ba wanda ya zo".

"Ayya Aunty ku yi haƙuri"
"Bani zaki ba wa haƙuri ba.yer Uwarki zaki je ki ba wa tun da ku ba kwa son zumunci"
"Toh tana ina na je na ba ta?".

Kwatan tawa Mufeeda taƙin da Amarya ta ke ta yi
Juyowa Mufeeda ta yi ta nufi cikin gidan.
"Toh ku shiga ciki mana Maman Afiya"!

"A'a ni kam ba shiga zan yi ba akwai wani abu da nake so na je na yi"


"Kai dama aikin ka ke nan"

"Allah!ya kyauta ya kuma nuna min ranar da zaka dinga zama cikin muta ne ana hira da kai kamar kowa"


Ɗan guntun murmushi ya saƙi da ya saya iya labensa,kana ya kalli Mama ya ce"y'auwa Mama Yusuf zai xo ya d'auke ku anjima"

Baki Mama ta buɗe da niyar yin magana sai Aunty ta riga ta cewa "ai baka isa ba, babu inda Mama zata je har sai an kammala biki dan haka in Yusuf ɗin ya zo sai dai ya d'auki Mufeeda amma Mama kam tana nan"


Okay ai shi ke nan Aunty duk a bun da ki ka ce shi za'a yi, Mufeeda ma dan bata faɗa wa Mommy ba da har ita zan bar ta ta kwana tun da tare suka zo"


*Bayan kwana uku*


Washe gari Ammi ita ma ta je gidan Aunty Maryam anan ne suka haɗu da Mama.Mama ta ji dad'i haɗu wa da Ammi sosai kuma ta yi mata godiya sosai akan irin a bubuwan alkhairi da ta yi musu da ita da dan ta.


Ammi ba ta kwana a gidan Aunty Maryam amma kullun tana zuwa wuni sai dare take koma wa gida.


Ita kam Mommy in ta zo ma ba ta wuni take tafiya gida,kuma bai fi sau biyu ta je ba tun da aka fara biki.


Anyi biki lafiya an watse inda Amarya Ai'sha ta tare a gidan Mijinta Aliyu da ke (Kabuga)


Mohsen kuwa d'a Aunty Maryam ta ce baza ta ba wa Mama shi ba amma da suka zauna suka tattauna da Ammi da Daddy sai ya ce a barta ta tafi da shi ta yan da zai samu ya shaku da mahaifiyarsa sosai,tun da wan can zaman da suka yi ba wata shakura a saka nin su na sakanin uwa da ɗa.


Wannan shi ne dalilin da ya sa Aunty ta bar Mama ta tafi da Mohsen,


Amma fah Ibrahim ma ya ce ba zai z'auna ba sai ya bisu,a haka dai duk suka bi Mama suka tafi.


A kwana ki kaɗan aka dawowa da Mama komai nata har ma da yer aikin ta Husna!


Habib ya so ya dawo mata da dukkan 'yen aikinta amma ta ce ita bata so yer aiki ko ɗaya, wai ita ma zata iya yin aikin ta da kanta ba sai masu aiki sun mata ba.


Habib ya ji daɗin hakan sosai kuma ya kara tabbatar da cewa lallaï Mama ta shiryu.


Sai da Habib ya sa baki kafin Mama ya amince aka dawo mata da Husna.


*Bayan kwana ɓiyu*


Gobe ne su Habib za su koma ( Dubaï)kuma a goben zasu cika sati ɗaya a (Kano)


Dan so suke su koma saboda bikin Habib da Nadra saura sati uku,shi ya sa ma tare da Daddy da kuma su Mufeeda za su tafi.


Ammi ce ta je gidan su Mama dan tun da ta zo bata je ba,


Ammi ta jima sosai a gidan Mama sun yi hira sosai sai da yamma Habib ya zo ya maida ita gida.....


*Fulanin Jajirtattu ce*✍️


Comments and share fisabilillah 👏
[6/21, 15:24] Mom Muwadda🥰: 🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑


*DUHU DA HASKE*


*By*

*Sakeena Isma'il Cameroon*
*(Mom Muwadda)*
*Marubuciyar*
*Bazan zauna da kishiya ba*
*Mijin Attajira*
*Mugun Uba*
*Duhu da Haske typing...✍️*

Utilise ce lien pour intégrer mon groupe WhatsApp : https://chat.whatsapp.com/BoEGaUYscLHDtLr41wYFFI


https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️


Page 63&64


Free Book


Bismillahi rahmani rahim


***********Ammi ta jima sosai a gidan Mama sun yi hira sosai da yamma Habib ya zo ya maida ita gida,


*Bari mu leƙa gidan su Basira*


Kwan ce ta ke a gidan su kusan wata biyu ke nan bata da lafiya,shiru ta yi kanta na sama ga hawayen da suke ta faman ambaliya da ga kan kuncinta, ta shiga magana ita Kaɗai "Najib me ya sa zaka min haka?tun da na ke ban taɓa jin ina son mutun sosai kamar ka ba,duk da kuwa ba yau ne na fara soyayya ba,na yi soyayya da mutane daban _ daban amma ban taɓa haɗuwa da wanda ya kwanta min a rai sosai na ji ina so na aure shi ba sai kai,sai kuma Habib Muhammad Habib,shi ƙad'ai na ji ina so kuma so na aure na ke masa,a lokacin da nagansa da wata na ji babu dad'i amma da na haɗu da kai Najib!a kwana ki kaɗan da na yi ta re da kai sai na nemi soyayyan da na ke yiwa Habib na rasa, amma shi ne zaka min haka?ka ce zaka zo baka zo ba har yan zu gashi wayan da muke yi yan zu ko shima babu me ya sa _me ya sa zaka min haka,dan Allah ka taimaka ka dawo gare ni "Ta kara she maganar haɗe da sakin kuka mai ban tausaya yi,


Wani irin tsawa Basira ta ji an ɗaga mata ɗago wa ta yi da s'auri mahaifinta taga ni tsaye a bakin ƙofar shiga ɗ'akin nata,hannu ta saka akan fuskarta ta shiga go ge hawanyen da ta ke zubuwa da ga kan kuncinta haɗe da k'irk'iro murmushi,


"Daddy sannu da dawo wa"?mai ma kon mahaifinta ya amsa mata sai ma binta da kallo daya shiga yi,takowa ya soma yi har ya ƙara so inda ta ke zaune,hannu ya sa ya wanke ta da mari lafi'yayyu har guda ɓiyu akan kuncinta,dafa wajan ta yi haɗe da miƙe wa tsaye, "To marar kunya ko zaki rama ne.?"


"A'a Daddy ba zan rama ba amma na yi mamaki sosai da marin da ka yi min dan ni kwata _kwata ban san mai ma yi ba.?"


Murmushi tak'aici mahaifin Basira ya yi kana ya ce "Ubanki ki ka yi na ce Ubanki ki ka yi yanzu ke baki ji kun ya yi min wannan tambayar ba?ni bazan miki baki ki kara lalacewa ba amma abu guda ɗaya da zan gaya miki shi ne ki g'agg'auta nemo wanda ya yi miki wannan ciki in ba haka ba zan d'auki mummunar mata ki a kank'i,kuma ko da wasa kar na ga k'afarki ta taka ko ƙofar gida ne".Ya na kaiwa nan ya juya ya bar ɗakin


Cikin mutuwar jiki Basira ta koma ta zauna gefan gadonta ta yi shiru ta na tunani mafita


*Mufeeda 9h na dare*

Kwance ta ke akan gadonta Ai'sha kuma ta na wanka,

Waya ta ke ta na cewa "humm Yaya Yusuf tun lokacin da ka dawo dani da ga gidan Aunty Maryam na baka number d'ina na ce in ka je gida ka kirani baka kira ni ba, yau ma saboda ni na kiraka da bansan san da zaka kira ni ba,k'ila ma tun ranar dana baka number d'in ka y'edda ita"


"A'a wallahi ba haka ba ne Ranki ya daɗe kawai dai tsoron kiran ki na ke"
"Tsoro kumaYayaYusuf"?."Ehwallahi""Toh tsoron me?""Kinfi kar'fi na Ranki ya daɗe ta ya zan kira ki bayan ni ba kowa bane""Gaskiya Yaya Yusuf ban ji dad'i wannan maganar ba"


"Sorry in na ɓata miki rai amma gaskiya na faɗa ni dan Allah ki de na kirana ma dan in yayanki ya ji bazai ji dad'i ba" Yusuf na kaiwa nan ya katse kiran.


"Hello! Hello!"


Mufeeda ta shiga fadi amma ta ji shuru ta na duba wa ta ga ya katse kiran,jiki babu kwari ta miƙe dan ta na so ta je wajan Habib su yi magana saboda gobe in sun tafi Dubaï ba lallaï ne ta ganshi ba.


Mayafinta ta d'auka ta yafa har ta saka hannu zata buɗe kofa ta ji Ai'sha na mata magana juyowa ta yi ta kalle ta,ta na nan tsaye bakin ƙofar fita toilet ɗin da ga ita sai wata ƙaramin tawol da ko ciny'oyinta bai gama rufe wa ba


"Me ki ke kallo na?" cewar Ai'sha


Tsakii Mufeeda ta saƙi haɗe da buɗe Ƙofa ta fita ta maida ta rufe ta nufi bangaren Habib ta na addu'a Allah ya sa bai yi bacci ba


Kwan ce ya ke akan gado ya yi ruf'da ciki ya na waya,kallo ɗaya zaka masa ka fahimci cewa wayan da ya ke yi ba kara min dad'i ya ke masa ba,dan ko ya na yin yan da yake rufe idonsa ma zai tabbatar maka da hakan.


"Wallahi na yi missed dinku sosai Yayana baka ji yanda na matsu safiyan nan ta yi na ganku kun dawo ba"


"Hummm really my Beauty!"?


"Yeah"


"Nima haka amma ta ya zan yadda kin yi missind d'ina?"


"Ka bari in ka dawo zaka ga yan da na rame"


"Rame wa kuma ?"


"Eh mana"


"Toh ni dai gaskiya in har na dawo na tarar kin rame ba zan ji dad'i ba"


"Toh kaga ni,shi ya sa na ce maka kai baka yi missind d'ina ba"


"Na yi mana sosai _sosai"


"Ban yadda ba"


"Na san missind d'in Nadra kawai ka yi baka yi na kanwarka ba"


Jin ta ambaci sunan Nadra ne ya sa lokaci ɗaya mod d'insa ya canza,haka ma murmushin da ya ke yi


"Hello! Yaya kana ji na kuwa?"


"Eh ina jin ki"


Ya faɗa sai kuma ya ji ana mai nocking


"Beauty ina zuwa nocking ake min"


Bai jira amsar ta ba ya katse Kiran ya miƙe ya nufi bakin ƙofar dan ganin wa ya ke masa nocking kofa a wannan lokacin.


Yana zuwa bakin kofah ya sa hannunsa ya buɗe kofar,


Mufeeda ya gani saye a bakin kofah,


Haɗe rai ya yi ya shiga tambayar ta

"Ke kuma lafiya zaki zo min da daɗɗare"


"Sorry brother magana zamu yi please "


Mufeeda ta faɗa haɗe da mar'air'ai ce fuska


Matsa mata ta yi ta shiga ciki ya rufo kofar ya koma ya z'auna gefen gadon,ita kuma ya nuna mata kujera ya ce ta "z'auna".


"Ina jin ki mene ne ?".


Magana Mufeeda ta fara yi kamar haka......


*Fulanin Jajirtattu ce*


Comments and share fisabilillah👏😍
[6/21, 15:24] Mom Muwadda🥰: 🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑


*DUHU DA HASKE*


*By*

*Sakeena Isma'il Cameroon*
*(Mom Muwadda)*
*Marubuciyar*
*Bazan zauna da kishiya ba*
*Mijin Attajira*
*Mugun Uba*
*Duhu da Haske typing...✍️*

Utilise ce lien pour intégrer mon groupe WhatsApp : https://chat.whatsapp.com/BoEGaUYscLHDtLr41wYFFI


https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️


Page 65&66


Free Book


Bismillahi rahmani rahim


**********Magana Mufeeda ta fara yi kamar haka "Bro da ma akan Yusuf ne..." Ta faɗa sai kuma ta yi shiru ba tare da taci gaba ba


Tun da yaji ta ambaci Sunan Yusuf ya kafe ta da da ido,lokaci ɗaya kuma ya saki guntun murmushi, sai kuma ya tamke fuska kamar ba shi ne wanda ya yi murmushi a yan zu ba.


"Ke in ba zaki magana ba ki tashi ki tafi ni bacci nake ji" Taji ya faɗa,tana son ci gaba da yi masa baya ni amma tana jin kunya, kai bata ma san ta ina zata fara ba.


Wani tunani ne ya zo mata a kai dan haka wayarta dake hannunta ta kunna haɗe dayin dealing number Yusuf, Yusuf da ke kwance bacci har ya soma d'aukarsa yaji wayarsa na ringing, dan guntun tsaki ya ja sannan ya daga wayan ba tare daya tsaya duba mai kiranshi ba, ya saka a kun ne ya yi shiru ba tare da ya yi magana ba.


"Yaya Yusuf ni ce." Mufeeda ta faɗa buɗe ido Yusuf ya yi sosai ya ta shi daga K'wacen da yake ya z'auna kana ya soma magana "Haba ranki ya daɗe daya zaki min haka dan Allah dan annabi ki kyaleni,ki baki mu dinga gaisawa in na zo wajan yayanki dan wallahi kinfi karfina bai kamata ki dinga waya da mutun iri na ba wanda bashi da komai"
Ya kara she maganar.


Kasancewa a handprin Mufeeda ta saka wayan shi ya sa Habib ya ji duk a bunda ya fada,kashe wayan Mufeeda ta yi dama a bunda take so ya fada ke nan kuma ya fad'a.


"Bro zan tafi yanzu tunda ka ji mai ya kawo ni wajanka"Ta faɗa ba tare data tsaya jin mai zai ce ba ta fita ta bar ɗak'in.


"Ma sha Allah!"


Ya furta had'e da sakin murmushi,kana ya miƙe ya je kashe duka fiti'lun dake ɗakin sannun ya hau gado, bayan ya yi addu'a ya k'wanta ya ja bargo ya rufe cikinsa da shi,babu jimawa bacci ya d'auke shi.


*Washe gari*


Tun da ya yi Sallah a subaha bai koma ba, k'arasa shirya kayan sa ya yi,bayan ya kamma'la wanka ya shiga bayan ya fito ya shirya cikin farar jallabiya ya naɗa wannan rawanin da (larabawa ( suke nadawa a ka sosai ya yi kyau ya fito a (Balaraben) sak!


Fita ya yi ya nufi cikin gida domin yin breakfast,


Bayan sun gama breakfast suka ɗunguma zuwa airport,


Basu wani jima sosai a airport ba jirginsu ya ɗaga zuwa kasar (Dubaï)


Kasancewa ita Hajiya Maimuna(Mommy)bata je ba dan ko airport ma bata raka su ba, ta ce ita sai biki saura kwana uku zata zo, Daddy ta buɗe baki da niyar yin masifa sai Ammi ta hanashi ba yanda ya iya a haka ya gyale ta.


*Dubaï Abu Dabi*


Tunda na tashi da safe ban koma ba sai shirye_ shiryen dawowar su Ammi nake ta fama yi,dan y'au duk wanda ya ganni zai gane cewa ina cikin farinciki


Su Ummi da Abe sai dariya suke min,


Bayan na taya masu aiki girin mun yi mun gama ne na koma dakina na je na yi wanka, da sallahr azahar,dan har an kira.


Palo na koma ina zuwa na tarar da Nadra da mahaifiyarta sun zo,gaida mahaifiyar Nadra na yi sannun muka gaisa da Nadra


Kallon mu Abie ya yi kana ya ce"ku tashi mu tafi lokaci ya kusa"


Baki muka had'a muka ce "Toh" Sannan muka mike muka nufi wajan ajiye motoci,mota uku muka d'auka,


Na Nadra dana driver sai nawa,dan nima yanzu na iya tuƙi.


Bamu jima da zuwa airport ba jirginsu ya sauka.


*Bayan minti 10*


Hango su muka yi suna saukowa daga cikin jirgi,


Mikewa dukan mu muka yi muka nufosu muna murmushi,suma murmushin suke yi.


Muna zuwa kafin na je wajan shi Nadra ta rigani zuwa ta rungumeshi,


Dan haka wajan Ammi na je na runguma,shafa kaina Ammi ta yi tana murmushi,"Ammi na yi kewarki sosai""nima na yi kiwarki habibti"


Kafin ka ce me Shima ya haɗa daga ni har Ammi ya runguma,a tare muka sauke a jiyar zuciya


Shafa kanmu Ammi ta yi sannun ta shiga daga Habib daga rungumar da ya yi mana.


"Beauty a hakan ne ki ke cewa kin yi missind d'ina?".


"Watoh mu baza'a kulamu ba ke nan?"


Mufeeda ta faɗa.


Ai'sha kam saboda takaici ma kasa magana ta yi,dan ita bata raina abu ko kaɗan


Jin hakan da Nadra ta yi ya sa ta fadin "hey!ya kuke ya anya?".


Cikin sanyin murya Mufeeda ta amsa,da "Alhamdulillah"!


Ai'sha kam tsaki ma ta ja haɗe da barin wajan ta nufi wajan su Ummi da Abie domin gaishe su,


Dan duk iskancinta tana girmama manya.


Saboda dama Daddy tunda suka s'auka daga cikin jirgi ya wuce wajan su Abie domin kwaso gaisuwan sirkai.


Dan murmushi na yi sannun na karasa inda Mufeeda ta ke saye kafin ka ce mai na faɗa jikinta na rungumeta sam a jikina,


Kai in kaga yanda na yi sai ka d'auka na santa,nan kuwa iya kacina hoto,dan ina ganin hoton su a gidan su Habib da suka yi su duka har ma da Mommy a ciki, shi ya sa kallo ɗaya na yi musu naga ne su ne,


Daskarewa Mufeeda ta yi a wajan ba tare data rungume Afiya back ba.


Sakin Mufeeda na yi kana na ce "Sorry sis welcome?"


Murmushi jin dad'i Mufeeda ta yi kana ta ce "thank you""amma kina da kirki"


"Na gode! Amma kema kina da kirkin ai"


Murmushi kawai Mufeeda ta yi,


Matsowa wajan Maman Nadra Habib ya yi ya gaisheta,ta amsa cikin sakin fuska haɗe da yi masa ya hanya ya ce alhamdulillah"!


Bayan angama gaisawa ne suka shiga mota suka dunguma zuwa gida....


*Fulanin Jajirtattu ce*✍️


Comments and share pls😍👏
[6/25, 15:08] Mom Muwadda🥰: 🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑


*DUHU DA HASKE*


*By*

*Sakeena Ismail Cameroon*
*(Mom Muwadda)*
*Marubuciyar*
*Bazan zauna da kishiya ba*
*Mijin Attajira*
*Mugun Uba*
*Duhu da haske typing...✍️*

Bi wannan mahaɗi don shiga guruf ɗin WhatsApp ɗina: https://chat.whatsapp.com/K0ug6sIXtuyFaEI3q27XDx


https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️


Page 67&68


Free Book


Bismillahi rahmani rahim


**********Bayan angama gaisawa ne suka shiga mota suka dunguma zuwa gida, Habib ya shiga motarsu Nadra da shi da Ai'sha da ba haka ta so ba,dan kwata_ kwata ita bata shiri sosai da Nadra saboda girman kan da take da shi,wannan din ma saboda Habibi ne ya ce ta shiga shi ya sa ta shiga amma ba a son ranta ta shiga ba.


Daddy kuma motarsu Abie ya shiga da shi da kuma Abie,su ɓiyu da dreve uku.


Ammi da Mufeeda da Ummi kuma a mortar Afiya suka shiga, Ammi da Ummi na baya Mufeeda na gama sai Afiya dake tuki.


Sorry masu karatu na manta a wancan page din na ce Afiya ta koyi tuki,bayan kuma ta riga data iya tuƙi tun tuni.kun san a bubuwa sun yi yawa akan nawa 😹


*Gidan su Habib*


Kasan cewa su Mufeeda suna da dakinsu shi ya sa muna zuwa gida suka nufi dakinsu domin watsa ruwa,


Wanka suka je suka yi su duka har da Ammi da Daddy,


Bayan sun gama suka fito suka ci a binci


Ranar hira sosai aka sha sai da yamma Nadra da mahaifiyarta suka tafi gida


Ina lura da Yaya Habib yanda ya ke satar kallo na


Muna son mu keɓe mu ɓiyu amma ba hali tunda su Mufeeda da Ai'sha suna nan


*Bayan sati ɗaya*


Shirye _shiryen biki ake sosai babu kama hannun yaro,kana ganin zaka gane bikin 'yen gata ake yi,


Dan daga Nadra har Mahaifiyarta gidan suka dawo suka haɗe ana ta shirye _shirye tare kun dai san bikin fararen fata,in ana biki daga iyayen ango har dana Amarya duk haɗuwa suke waje ɗaya


Gyaran jiki ake wa Nadra sai naga abun ba kara min burge ni ya yi ba, Ammi na lura da ni sosai ta yan da nake kallon yan da ake wa Narda gyaran jiki ɗin kuma ta fahimci abun ba kara min burge ni ya yi ba.shi ya sa ta ce nima na zauna ayi mun,


Zo kaga murna a waje na,su Mufeenda mai zasu min banda dariya,


Ana haka ne sai Ammi ta ce suma su Mufeeda su z'auna ayi musu,a haka muka z'auna aka yi mana gyran jiki na bam mamaki,


Rana ɗaya aka min amma ba kuga yanda na koma ba dan gyaran cikin ba maramin karbata ya yi ba


Su Mufeeda sai ya ba gyaran jikin nawa suk'e ta faman yi,har cewa suke wai mai gyaran jiki na sane ta yi nawa tafi nasu kyau


Ni dai babu a bunda nake yi sai murmushi


*Kano*


*Gidansu Basira*


Tun lokacin da mahaifinta ya ce zai d'auki mummunar mataki a kanta in har bata nemo wanda ya yi mata cikin nan ba.


Shi ya sa tun ranar ta ke ta faman gwada number Najib amma bata shiga.


Bangaren manaja Afiya kuwa tun washegari ranar da Habib ya je company ya kawo 'Yen sanda aka kama Manaja aka kulle a police station ance baza'a sake shi ba har sai ya biya kudin company daya ci sannun za'a sake shi.


Sai daya yi kusan Sati ɗaya a kulle sannu ya biya kudin aka sake shi
Amma kafin a sake shi sai da aka masa kashesi sosai akan kar ya kara shiga harkan Safna in kuma ya shiga zasu d'auki mummunar mataki akan sa yace in sha Allah bazai shiga ba a haka dai aka kyale shi ha tafi.


*Gidan su Mama*


Shirye _shirye tafiya kasar(Dubaï)ake ta yi duk wanda ya ga Mama zai gane cewa tana cikin farinciki,


Kallo kuma ɗaya zaka mata ka fahinci cewa ta canza ba Kamar wancan Mama da aka sani a baya ba


*Dubaï*


Gidan cike yake da dangi da kuma 'yen uwa da abokan arziki,sai kai kawo suke a cikin gidan,kowa da abunda yake yi


Su Nadra da Afiya ne zaune a dakin da aka wara musu na gyaran jiki,jikin Kowa sai sheƙi da walkiya yeke yi, amma na Afiya yafi nasu yin sheƙin dan gyaran jikin ba kara min karbarta ta yi ba


Duk da kuwa Nadra tafi Afiya hasken fata na masayinta na: Balarabiya)amma sakama kon gyaran jiki da aka yiwa Afiya sai ta zo tafita haske.


Y'au ne su Mama dasu Aunty Maryam da Hajiya Maimuna( Mommy)zasu diro kasar:Dubaï)kowa yasan da zuwan su amma banda Afiya,dan an ce kar a gaya mata saboda so suke su yi mata bazata shi ya sa ma ba wanda ya je d'auko su a airport sai Daddy kawai da Habib suka tafi


*Bayan awa ɗaya*


Suna s'auka daga cikin motar ta nufi dakinta dake cikin gidan dan bata son a dame ta,da kallo Daddy da Habib suka bita dashi haɗe da girgiza kai,


Mama kuwa tunda suka shiga farfaɗiya gidan take baza ido taga ta inda Afiya zata bullo amma shiru,jikinta ne ya fara san yi,dan tuna ni take ko har yanzun bata haƙura ba?fahimtar hakan da Habib ya yi ne ya sa shi sakin murmushi haɗe da kamo hannunta ya ce "Mama zomu je kiga wani abu".Kafin Mama ta yi magana tuni Habib ya ja hannunta suka nufi cikin gidan,bai saya ko ina ba sai dakin da ake wa su Afiya gyaran jiki,kuma dama shi ma yana son ganinta saboda ya kwana ɓiyu bai sata a ido ba shi ya sa duk ya rame babu a bunda ake fani sai dogon hanci da idonsa da ya kara wani irin haske,shi ya sa yabi ta wannan hanyar saboda shi ma ya samu ya ganta.


Suna zuwa ya turo kofar a hankali suka shiga ya mai da kofar ya rufe suka karasa cikin dakin.


Matar da take musu gyaran jiki ne ta kalle sa sannun ta fara magana da Larabci)kai kuma Habib ba na hanaka shigo dakin nan ba"?" Sorry wallahi Mama na raka taga Beauty". Ya fada ya shiga kallon dakin kamar yana nemon wani abu,sai ɗaya karewa ɗakin kallo saf amma bai ganta ba.


Dan sai su Narda kawai da su Ai'sha da Mufeeda da suke zaune Ai'sha da Nadra wayoyinsu suke danna wa sai Mufeeda da take kwance akan kujera mai zaman mutun uku.


Ganin Mama da su ka yi ne ya sa su kallonta suka fara gaishe ta "Mama sannu dazuwa ya anya Ai'sha ta faɗi"."Lafiya lau"Mama ta amsa, Nadra ma gaisheta ta yi sama_ sama taci gaba da dadne dadnen wayan da take yi "Da lafiya" Mama ta amsa, Mufeenda ce kaɗai ta miƙe ta zo ta fada jikin Mama tare da faɗin"Laa Mama a she kun kara so babu ko labari ina Mommy da Aunty Maryam?".Shafa kanta Mama ta yi tana murmushi,"Mommynku tana dakinta ta ce bari ta je ta wuta Aunty Maryam kuma suna Palo da su Mohsin".Ai Mufeeda na jin haka ta saki Mama ta ruga a guje ta fita ta bar dakin ta nufi palo, dariya Mama ta saki, Habib kuwa kai kawai ya girgiza dan ya na son Mufeenda sosai babu ruwanta shi ya sa yake damuwa da damuwarta,


Kallon Ai'sha Habib ya yi cikin haɗe fuska ya ce "ina beauty take"?."tana wan.... Ai'sha bata karasa magana ba suka ji na buɗe kofar toilet ɗin na fito d'aure da tawol a irjina gashina sai ɗigan ruwa ya ke,takowa na fara yi na nufi cikin palo ban kula da su ba har sai dana karasa sakiyar palon sannun idanuna ya s'auka akan mahaifiyata wani irin ihon murna na saki haɗe da nufota da s'auri wanna ruwan dake ɗigawa akaina ne na taka zan faɗi ya yi s'aurin riko ni ta faɗa irjinsa,rufe idona nayi ina jiran na jini a kasa sai kawai naji ni akan wani abu mai l'aushi a hankali na shiga buɗe idona har na karasa budesu tar akan kyakkyawar fuskarsa,gyaran murya Ai'sha ta yi ta kalli Nadra da kallo daya ta yiwa su Habib ta d'auke kanta taci gaba da danna wayarta,mikewa ta yi ta karasa gaban mu kara yin gyaran muryan ta yi dan wancan wanda ta yi bamu jiba, s'aurin janye jikina na yi daga na Habib haɗe da yin s'aurin karasa inda hijabina take na d'auka na saka dan tunda naƙe da shi bai taba ganina haka ba sai y'au


Juyowa Mama ta yi da niyar barin dakin sai na kira sunan ta "Mamana".Dakatar da bude kofar da Mama ta ke k'oƙ'arin yi ta yi haɗe da juyowa,da guɗu na karasa gabanta haɗe da rungumeta sam a jikina ina sakin kuka "Haba Mamana baki kiwata ba ?".Shafa kaina Mama ta yi haɗe da rungume ni sosai a jikinta da shiga faɗin "na yi kiwarki sosai ma Afiyata dan Allah ki yafe mi"....Bata karasa ba taji Habib ya ce"me haka Kuma Mama ?"Ya yi maganar yana satar kallon su Ai'sha da Nadra ke Ai'sha kimma je kin yiwa su Aunty da Mommy sannu dazuwa kuwa?"A'a Bro ban je ba""Toh Tashi maza jike ki yi musu ki dawo".Kai Ai'sha ta geɗa haɗe da mikewa ta sa takalmin ta ta fice daga ɗakin


Mama ta fahimci me ye sa baya son ta yi Magana shi ya sa ita ma bata ci gaba da magana ba sai da Ai'sha ta bar ɗak'in,kasan cewa Nadra da mai gyaran jiki basu iya (Hausa) ba shi ya sa bai damu da su fita ba "Mama ga waje ki z'auna bari na je na dawo ya faɗa haɗe da ficewa ya bar dakin ya ja musu kofah.


Bayan fitar Habib ne Hajiya mai gyaran jikin ita ma ta miƙe ta bar dakin dan ta fahimci cewa Habib ya bar dakin ne saboda yana bukatar barin Afiya ta tattauna da Mahaifiyarta,

Nadra ce dai taki tafiya dan tana z'aune a dakin


Mama bata damu da rashin fitarta ba.ta kamo hannun Afiya ta shiga nemon yafiya a wajan ta,cikin kuka take faɗin"Dan Allah ƴata ki yafe min na yi na damar a bubuwan dana aikata muku a baya dan Allah ki ya fe min Afiya""Haba Mama na yafe miki kuma ni dama can ban riƙe ki ba dan haka dan Allah nima ki yafe min"


Ana haka ne Mohsin ya shigo dakin da guɗu yana faɗin "Aunty Afiya oyoyo""Oyoyo ɗan ƙanina ka ce har da kai aka zo?"."eh mana Aunty tare muka zo har ma da Aunty Maryam"Mohsin ya bata amsa haɗe da karasowa kusa da Afiya rungumesu na yi gaba ɗayansu daga shi har Mama muka s'auke ajiyar zuciya a tare.


*Bayan kwana ɓiyu*


Mama ce da Ammi z'aune a daki sai ni da nake z'aune a gefensu tun dazu suka kirani amma sun ki ce min komai,


Sai da aka d'au kusan mintuna biyar kafin Mama ta fara magana,"Afiya!"Mama ta kira sunana"Na'am"na amsa,kinsan yanda a bubuwa suka kasan ce a baya kuma kinsan a bunda ya faru da ke duk da kuwa nice cilar jefaki ciki,dan haka tunda yanzu farincikin mu ya dawo kamar da a lokacin da Abbanku yana raye"


"Nasan baki san dalilin daya sa na zo nan Dubaï ba ko?"."Eh Mama ban sani ba amma na d'auka bikin Yaya Habib ki ka zo da kuma ganina""Eh kusan hakan amma babban a bunda ya kawo ni garin nan saboda har da auren ki saboda lokacin da Amminki ta zo :Nigeria)mun z'auna mun tattauna sosai da ita anan ne muka yanke shawara mu haɗa ki da wani dan uwan Mamar Nadra tunda yaron yana da hankali da nitsuwan da kuma sanin ya kamata Amminki ta yaba da halinsa sosai"


Wani irn faduwar gaba naji a lokacin da Mama ta furta maganar aure.


Sai ta kaina na yi na kirkiro murmushi dan bana so na bata musu rai dole na amince da zabin da suka min saboda bazan taba watsa musu kasa a ido ba,


"Baki ce komai ba habibti"Naji Ammi ta faɗa "Haba Ammi ni a ganina bai kamata ku zaunar da ni kan wannan maganar ba ku sani cewa ku fah iyayena ne dan haka duk a bunda kuka yanke a kaina dai_ dai ne""Haka ne habibtina Allah ya miki albarka ya sa ki rabu da mu lafiya".Da ameen na amsa sannun na biƙe na bar daƙin


Ina fita ban saya ko ina ba sai daƙina ina shiga na ja kofar na rufe da key na faɗa kan gado na saki wani irin kuka mai ban t'ausa.


*Bayan kwana uƙu*


An d'aura auren su Nadra sai kuma ni da wannan mutumin da bansan ko waye shi ba,dan s'au ɗaya na taba ganin sa,yana da kyau sosai amma gaskiya ni Yaya Habib yafi min shi.


Da daɗɗare aka shirya ni saf Nida Nadra,sai da aka yi mana nasiha sosai sannun aka kaimu gida jen mu,


Nadra aka fara kai kafin ni "


Bayan an kaini aka barni tare da su Mufeeda da Ai'sha,su din ma daga baya sulalewa suka yi suka tafi suka barni ni ɗaya,


Ina ganin haka na saki kuka ina tunani'yanzu shi ke nan anan zanci gaba da zama bazan koma kasata ba?yanzu shi ke nan na rasa Yaya Habib har abadan way Yaya Habib way.me ya sa zaka min ha...ban karasa maganar zuci ba sakama kon kukan dayaci karfina kuka nake mai suma zuciya,jin da na yi an buɗe kofar dakin ne ya sa ni kara s'autin kuka na


Takowa ya shiga yi ya nufo inda nake gadan_ gadan...


Su Afiya an zama Amarya 🥰💃


*Fulanin Jajirtattu ce✍️*


Comments and share fisabilillah 👏😍
[6/26, 20:15] Mom Muwadda🥰: 🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑


*DUHU DA HASKE*


*By*

*Sakeena Ismail Cameroon*
*(Mom Muwadda)*
*Marubuciyar*
*Bazan zauna da kishiya ba*
*Mijin Attajira*
*Muguna Uba*
*Duhu da Haske typing...✍️*

Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/K0ug6sIXtuyFaEI3q27XDx

https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️


Page 69&70


Free Book


Bismillahi rahmani rahim

Takowa ya shiga yi,ya nufo in da na ke gadan _gadan jin kamshi turaren mutumin da bazan taba iya tire shi a cikin zuciyata da kuma manta wa dashi ne ya sani sai da kukan da na ke yi na dago fararen zara_ zara idanuna wanda sabar kukan da na yi ne ya sa shi janza kala juwa ja,dagowa nayi dan tabbatar wa kaina a bunda na ke ji.


Ɗagowan da na yi ya yi dai _dai da karasowar sa in da naƙe,ajiya mamaki na na yi na miƙe zunbur na faɗa cikinsa haɗe da saƙin kuka mai suma zuciya cikin kuka nake cewa Yaya Habib nasan ba za ka bar ni ba na san ba za ka taba barina a wannan gidan ba na san ba za ka taba bari na z'auna da mutumin da bana so ba duk a cikin kuka na yi wannan maganar dan a tunanina na d'auka zuwa kawai ya yi ya ganni ne,shafah baya na ya shiga yi haɗe da runtse idanu,dan bayan son jin kuka na ko kaɗan saboda har cikin rantsa ya ke jin kukan,


Bai dena shafah baya na ba har sai da na yi shuru sannun ya dago, haɗa ido muka yi na yi s'aurin sunkuyar da nawa idon kasa hawayen ya shiga share min sai daya share shi tasss sannun ya soma magana "Beautyna me ye sa kika ce haka?me ya sa bakiya son wanda aka aura muku aure tare da shi?"Duk a lokacin ɗaya ya yi min wannan tambayar


Shuru na yi ba tare dana bashi amsa ba.


Shi kuwa Habib ba dan komai ya sa ya min wanna tambayar ba sai dan so ya ke ya tabbatar ina son shi ko kuwa


"Shi ke nan bari na tafi tunda ba za ki faɗa min ba"Ya yi maganar haɗe da juyowa zai tafi


Wani irin runguma na yi mishi ta baya,cikin kuka na shiga faɗin"wallahi Yaya Habib bana son wancan mutu min kai nake so dan Allah karka tafi ka barni anan.dan Allah ka tafi dani"Wani ya irin murmushin farinci Habib ya saƙi a lokacin da yaji Afiya na cewa ita shi take so,


Juyowa ya yi ya rungumeta sosai kamar akwai wanda zai kwance masa ita


"Beauty da gaske ni ki ke so?"Mayafin dake jikina na saka na rufe fuskata da shi ina murmushi,dan har ga Allah bansan ta ya aka yi na faɗi hakan ba


Kiss ya sakar min a goshi kana ya kamo hannuna ya yi hanyar toilet da ni,nidai binsa kawai na yi har bakin toilet din,


"Shiga ki yi alwala ina zuwa"yana kaiwa nan ya juya zai bar wajan na riƙo hannunsa na fara magana"dan Allah karka tafi ka barni""Ba tafiya zan yi ba Beauty ina nan tare da ke har karshen rayuwata""taya zaka ce kana nan tare da ni har karshen rayuwarka bayan kun riga da kun aura min wannan mutumin?""ni ne nan mijinki Beauty ni aka aura miki"idona na zaro waje ina faɗin da gaske Yaya Habib?""Eh da gaske " Ya faɗi yana lakutan dogon hancina,"Toh amma me ya sa su Mama suka ce wancan zan aura ?"hannunta ya kara kamowa suka dawo cikin dakin,gefen gado ya zaunar da ni shima ya z'auna duka hannayena ya kamo ya hada da nasa ya shiga murzawa a hankali,sai daya d'au kusan mintuna biyar a haka kafin ya fara mani labari.


*Satin uku da suka wuce*

*(Nigeria)*


Mama ce z'aune a palo tare da Ammi suna hira Ammi ta ce "y'auwa Oum Mohsin akwai maganar da nake so mu tatt'auna kafin na wuce (Dubaï)""Toh ina jinki Ammi"?" Mama ta faɗi gyara zama Ammi ta yi kana ta fara magana"Dama akan Beauty da Habib ne saboda na ga suna son junan su sosai duk da kuwa basu taba furtawa juna ba amma na gama fahimtar hakan"."Toh yanzu ya za'a yi dan naga dai an riga da an yiwa Habib baiko da yer uwarta kuma da bakinki kika faɗa min haka kwana kin baya kinga dai bazai yu a bashi mata har guda biyu ya aura a lokaci daya ba""Eh na sani akwai maganar da na yi da su Abie kwana kin baya""Wana irin magana?""Dan gyara zama Ammi ta yi sannun taci gaba da magana "dama Nadra akwai wani dan uwan mamanta da yake sonta kuma ita ma yanzu tana son shi ɗa bata son shi Habib take so saboda akwai shakuwa sosai a sakaninta da Habib toh a lokacin mun d'auka soyayya ce har muka z'auna da iyayenta muka tatt'auna muka yanke shawara muyi musu baiko,anyi baikon su da 'yen watan ni kaɗan sai Habib ya taho da Beauty kasar (Dubaï) irin kulawa da kuma soyayya da Habib ya ke nuna wa Beauty ne da ita kanta Beautyn take nuna masa ko a gaban Nadra nunawa juna suke yi ne ya sa muka sake zama tare da iyayen Nadra dama ita kanta Nadran muka yanke shawara s'auke baikon da muka yi musu,anan ne Nadra take cewa ita ma ɗa ko ba'ayi wannan zaman ba ma ta fasa auran Habib dan a yanzu babu soyayarsa Habib a cikin zuciyata kwata_ kwata a yanzu sai na 'yen uwantaka kawai,anan ne muka yanke shawara bawa wancan dan uwan nata dama turo wa bayan ya turo ne aka saka rana dai _dai da lokacin da za'ayi bikin Habib din da Afiyan shi ya sa na ce in sha Allah in na zo Nigeria zan z'auna dake mu yi magana naji ra'ayinki akan maganar auran na su?".Ammi ta k'are magana ajiyar zuciya Mama ta s'auke kana ta fara magana"Ni dai duk a bunda ku ka yan ke akan Afiya dai _dai ne tunda ku ne iyayenta a yanzu ni dai iya kacina na yi musu addu'a da kuma fatan alkhairi Allah kuma ya sa za'a yi damu"


"Ameen ya Allah!Na gode sosai Oum Mohsin"


"Ni ce da godiya dan babu a bunda zan iya cewa sai godiya Allah ya saka muku dama fificin alkhairi"


"Ameen" Ita ma Ammi ta amsa


Dagowa ya yi ya kalleni kana ya ce"kinji yadda aka yi ke nan?""Eh na ji amma ya aka yi kai an gaya maka ni ba'a gaya min ba?"kai Beauty sarkin tambaya toh ni ɗin ma saboda ranar nazo d'aukar Ammi ce na zo zan shiga palon naji suna tatt'auna wa shi ya sa na saya naji komai kinji yanda aka yi naji ke nan?"


"Toh da kaji me ya sa baka faɗa min ba"


Hancina ya dan ja Kana ya ce"saboda so muƙe muyi miki bazata ne shi ya sa"


Baki na buɗe da niyar kara yin magana ya rufe min baki ta hanyar ɗora manuniyar yen yatsunsa akan laɓena ya furta"shiiiiii!......


*Fulanin Jajirtattu ce*✍️


Comments and share fisabilillah 👏😍
[6/29, 23:25] Mom Muwadda🥰: 🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑


*DUHU DA HASKE*


*By*

*Sakeena Isma'il Cameroon*
*(Mom Muwadda)*
*Marubuciyar*
*Bazan zauna da kishiya ba*
*Mijin Attajira*
*Mugun Uba*
*Duhu da Haske typing...✍️*

Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/K0ug6sIXtuyFaEI3q27XDx

https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️


Page 71&72


🔚🔚🔚🔚


Free Book


Bismillahi rahmani rahim


*********Baki na buɗe da niyar kara yin magana ya rufe min baki ta hanyar ɗora manuniyar yen yatsunsa akan laɓena ya furta "shiiiiii!"


Shiru na yi ina kallon sa "gaskiya Beautyna kin ko yi surutu""ni ɗin?"Na faɗi ina nuna kai na""sosai ma kuwa gaba ɗaya su Ammi sun ɓata ki da suturu yan zu dai ba wannan ba ki tashi ki je ki yi alwalan nan dana sa'aki""Toh"Na faɗi ina miƙewa bina ya yi da kallon so har na shiga toilet, shi ma miƙe wa ya ƴi ya bar ɗak'in, ɗakin daƙe kusa da nawa ya shiga babu jima wa ya dawo dakina lokacin kuma tuni na yi alwala na har na fito ya na shiga ɗ'akin muna haɗa ido ya sakar min murmushi kana ta ce "y'auwa shimfiɗa mana sallaya mu yi sallah"Abun sallah na d'auƙo na shimfiɗa mana sannun ya ja mu sallah! sallah raka'a ɓiƴu muka yi muna itar ya kama kaina ya min addu'a sosai har dana zaman lafiya.


*Bayan mintuna arba'in*


Munci a binci kala_kala irin nasu na (Larabawa) saboda su ba kaza ake kawowa amarya ba a can,tun da kullun suna cinta a gida jan su, shi ya sa su bazu san kawowa amarya kazan amarci ba


Har wanka mun yi amma ba tare ba dan ya ce mu shiga mu yi tare naƙi amin cewa shi ne ya tafi dakinsa ya je ya yi ya dawo,


Na tire kaya na ke nan ya rage daga ni sai pand dan har da bra ma na tire saboda ban iya bacci da bra ba,na saka kaina ke nan da niyar saka rigar baccin sai zaren rigar ya makala min a kunne ina ta ƙ'ok'arin tire wa amma ta kasa,ya na shiga cikin ɗakin idonsa ya s'auka akan manya _manya books dina farare tass sai sheƙi suk'e lokaci ɗaya idanunsa suka canza l'auni zuwa ja tabbas shi ma bukaci ne sosai wani lokaci kwana ya ke da ciwon mara amma a haka ya ke d'aure wa, ƴ'emmata deyewa sun sha kawo mai kan su amma bai taba basu fuska ba.


Cikin san yin jiki ya shiga takowa a hankali ya nufi in da naƙe


Ba zato ba sammani na ji an rikoni ta baya,kamshin turaren sa daya jika min hanci ne ya tabbatar min da shi ne,


Wani irin ihu na saki haɗe da faɗin "Haba Yaya Habib babu kyau fah ya zaka min haka dan Allah dan annabi ka sake ni"Na kara rike kunnena daya makale da zaran riga ta


"Ki tsaya in tire miki kar ki ji ciwo" Ya faɗi a hankali a cikin kunnena ya na yin yan da ya yi maganar ne ya sa tsigar jikina ta shi,shi ya sa ban kara tanka masa ba har ya tire ya na tire min zaran ya tire ɗan kunnen shi ma ya ajiye su a gaban mirror tun da muna kusa da mirror.


Rigar kuwa ya je fah shi a ƙasa sai a lokacin ya karewa jikin nawa kallo sosai dama irjina dan ina da irji sosai tabar kalla,wani irin numfashi ya ja haɗe da saƙina ya zauna kan carpet din ɗak'in,gani da na yi ya saƙe ni ne ya sani s'aurin juyowa na nufi in da ya ajiye min rigata na dur'kusa na d'auki rigar zan na ɗago ke nan da niyar miƙewa naga sai riƙe mararsa ya ke ga idonsa da ya yi wani irin ja,cikin ruɗewa na karasa gaban shi,shi kuwa Habib idonsa ne ya ƙara s'auka kan irjina ba sai kawai naga ya kara jan numfashi ba haɗe da kwamciya a kasa ya na riƙe mararsa,


Ni kam kwata kwata ban fahimci komai ba,

Kuka na saƙi na shiga jijjiga shi haɗe da kiran sunan shi "Yaya Habib! dan Allah ka de na min haka ka de na min wannan wasan ba na so dan Allah ka dena"Ba tare ɗaya yi min magana ba ya mika min hannunsa babu musu na saka nawa hannu ya saka ragowan karfin da ya ke da shi ya ja ni na faɗa cikinsa hannay'ensa ɓiyu ya haɗa ya rungume ni sosai a jikinsa ya na s'auke ajiyar zuciya.


Wasu abubuwan da ba'a taba yi min su ba na ji ya na min,tun da lokacin da oga Jabir ya yi anfani da ni ba'a cikin hankalina naƙe ba tun da magani ya zuba min a lemo na sha


Cikin kuka na ke cewa "dan Allah ka bari ba na so da zafi dan Allah kar ka yi""shi ke nan Beauty na bari amma ki sani in har baki bani ba mutuwa zan yi"Ya faɗi haɗe da miƙe wa daƙer ya hau gado ya kwanta ruff da ciki,


Cikin tashin hankali na bishi kan gadon ina faɗin dan Allah ka yi haƙuri zan baka a bun da ka ke so amma dan Allah karka mutu ka barni ba zan iya rayuwa babu kai ba.ina jikin DUHU kai ne ka kawoni cikin HASKE dan haka dan Allah karma min haka dan kai HASKE na ne ba'a tafiya cikin DUHU sai da HASKE"Na k'are magana ina sakin kuka mai ban t'ausa yi,kin tabbata zaki bani,kai na kawai na geɗa masa ba tare da na yi magana ba,kara jawo ni ya yi jikinsa,


A tak'ai ce dai ranar sai da Habib ya mai da ni matarsa sannun ya kyaleni,


Kala mai soyayya kam na shata kala _kala dan a cikin kalamai soyayya babu a bun da ya rage wanda bai gaya min ba.

Haka ma albarka shima na shata sosai


Ba karamin wahala na sha ba a wajan sa


Bangaren Habib kuwa badan Afiya da bakinta ta bashi labarin a bun da ya faru da ita ba da zai ce ita mudurwa ce,


Saboda yan da ya samu wajan a rufe Kamar budurwa,


Cikin farinciki ya d'auki abarsa sai toilet,ruwan mai zafi ya haɗa ya sata a ciki sai daya tabbatar ta ji s'auƙi abun sannun ya fito ya barta a cikin toilet din ta samu ta yi wankan tsarki,


Zanin gadon ya tire ya d'auko wata ya shimfiɗa musu,sannun ya koma toilet din ya t'aimaka mata ta fito.


Sai daya tsaya ya t'aimaka mata ta shirya ta k'wanta sannun shi ma ya shiga ya yi wankan ya fito ya shirya bayan ya yi musu addu'a ya kwanta ya ja musu bargo,ya rungumeta sai bacci

Ranar dai cikin farinciki da k'aunar juna suka yi bacci


*Bayan sati biyu*


Su Mama da su Daddy sun koma (Nigeria)


Ranar da za su koma ba karamin kuka na sha ba,
Ni yan zu shi ke nan na dawo kasar (Dubaï)da zama ba zan sake koma wa (Nigeria) ba sai da Habib da su Daddy suka rarra she ni suka kuma kara da cewa taya zan ce ba zan kara koma wa (Nigeria) ba bayan kuma daga ni har mijina dukan mu 'yen (Nigeria) ne dan haka na kwantar da hankalina,da haka dai suka shawo kaina har na haƙura na dena kuka


*Bayan shekara ɓiyu*


*Kano Nigeria*


*Gidan su Basira*


Basira ta haifi cikin shegen da aka yi mata, kana ganin yarinyar kaga ubanta watoh Najib dan farace sosai yarinyar,san da take da cikin kullun cikin fargama take saboda batasan cikin waye daga cikin ba.na Mahmud ne ko na Najib saboda ta saɗu da Mahmud ranar da zata tafi kasar Dubaï,amma tun ranar data haifi yarinyar taga farace sosai yarinyar hankalinta ya dan kwanta,


Tana haifar yarinyar da wata biyar Babanta ya ce lallaï sai ta je ta nemo uban yarinyar data haifa musu a gida in ba haka ba kuma sai ya tsine mata in ya so ta bi duniya.


Hankalin Maman Basira ya tashi sosai,shine taiwa Baban Basira magana daya janye maganar da ya yi amma tana gama magana ya ce mata ita ma in ta kara magana zai s'auwaƙe mata in ya so ta d'auki Basiran su koma gidan su tare da ita,ai Maman Basira na jin haka ta yi tsit da bakinta bata sake furta komai ba.


Haƙuri sosai Basira ta shiga bawa mahaifinta daƙer ya haƙura,


Ƙuɗin jirgi zuwa ( Dubaï)ya biya mata ya ce ta je ta nemo duk in da uban ƴerta ya ke ta bashi ƴersa ta dawo tazo ta nemi mijin aure ta yi aure in kuma ba haka ba sai ya koreta daga gidansa,cikin rawar jiki Basira ta amince


*Bayan kwana biyu*

Bayan kwana ɓiyu Basira ya je Dubaï,kasan cewa bata san gidan su Najib ba shiyasa tana sauka a kasar ta nufi hôtel din da ya ke aiki,ta na zuwa kuwa ta nuna musu hotonsa,anan ne masu hôtel din suke sh'aida mata cewa shekara ɗaya da suka wuce ya bar aiki anan,amma sun yi mata kwatancen gidan shi ta tafi


Basira ta je gidan su Najib kuma ta yi sa'a data je ta nuna wa Najib Babyn data haifah ba'a wani sha wahala ba ya karbi yarinyar hannu ɓiyu,kuma data faɗa masa a bun da mahaifinta ya ce in ta dawo zai mata aure shine ya yan ke shawara binta Nigeria a yi musu aure duk da bashi da ƙudi sosai a hannunsa amma gwara ya je a haka,a hakan dai suka yan ke shawara nan zuwa jibi zasu je Nigeria,


Basira ta ji dad'i sosai,kuma ta kira mahifinta ta yi masa baya nin komai


Bayan kwana ɓiyu Najib da Basira suka je (Nigeria) mahaifin Basira da ya ga Najib jikinsa ya yi san yi sosai,dan ba irin mijin da ya ke burin aurawa ƴayansa ba.


Saboda shi dan gidan mutunci da kuma tarbiya ya ke son bawa ƴayansa,ga shi kuma shi Najib kallo daya zaka masa ka gane ba wani tarbiyan kirki ya ke dashi ba,dan daga yana yin askin kansa ma zai tabbatar maka da hakan,amma ya na yin yan da abun ya zo ne ya sa ba'a wani d'au lokaci ba ya abince


Baban Basira ya cewa Najib ya sanar wa da magaba tansa suzo a yi maganar auran nashi,shi ne ya ce mahaifinsa ya daɗe da rasuwa dan tun ya na shekara goma sha ɓiyar Allah ya yir masa rasuwa


Mahaifiyarsa ƴar kasar (Sudan)ce mahaifinsa ne balataben kasar (Dubaï)shi ya sa lokacin da Mahifinsa ya rasu da mahaifiyarsa ta ce ya zo su koma kasar (Sudan) yaƙi amince wa,dan shi ya tsaba da kasar (Dubaï)a haka dai mahaifiyarsa ta tattara na ta eh na ta ta koma kasar (Sudan)ta bar shi a (Dubaï) ƙuɗin da mahaifinsa ya bari ne ya shiga yin bushasha da shi har ya cinye su tass daga baya ya z'auna ba shi da ko sisi


Wannan shi ne dalilin ɗaya sa ya shiga nemo aiki ke nan


Babu in da bai je nemon aiki ba amma bai samu ba sai a wannan hôtel ɗin da suka haɗu da Basira.


Najib ya faɗa wa mahaifin Basira labarinsa,amma bai faɗa masa cewa mahaifinsa ya bar dukiya mai yawa ya cinye su ba.


Yana gama faɗa wa Baban Basira Baban Basira ya ce "Allah!ya yi masa rahma ya amsa da "ameen kana ya kara da cewa ya kira ɗaya daga cikin kawun nan sa,anan ma dai ya ce bashi da number dinsu


Shiru Baban Basira ya yi ya rasa mai zai ce, sai kawai ya ce"toh shi ke nan ka je ka same su ka faɗa musu in ya so sai ku taho tare"Baki Najib ya buɗe da niyar yin magana sai Basira ya yi wa Mahifinta magana da Hausa tun da shi Najib baya jin (Hausa)sai Turanci : da kuma (Larabci)kawai ya ke ji,shi ya sa Basira ta yi wa mahifinta magana da (Hausa)kaga Abba ka zama waliyinsa kawai a yi a d'aura auran dan wallahi in ya tafi ba lallai ne na kara ganinsa ba


Dan nisawa Baban Basira ya yi kana ya ce "yan zu in na ce zan zama wakilinka kana so?".Shiru Najib ya yi na y'en mintuna kana ya ce "eh ina so"shi ke nan zan baka daki a nan gidan kafin zuwa kwana shiɗa saboda so na ke a haɗa d'aurin auren dana ƴar uwarta Naja'atu,kai Najib ya geɗa kana Baban Basira ya ce wa Basira ta je da shi ta kai shi ɗaki na musamman da zai z'auna kafin lokacin,kai Basira ta geɗa sannun ta raka Najib ma s'aukinsa.


Bayan kwana shiɗa aka d'aura auran Najib da Basira sai kuma Naja da Yayan Safna kawarta aka aura musu aure.


Ita ma dai Safna kusan watan ta ɓiyar da aure


Bayan an d'aura auransu Basira Najib ya d'auke ta suka wuce Sudan din,amma sai da aka haɗa ta da wata goggonta watoh ƙanwar mahifinta saboda sun ce ba za su barta ta tafi daga ita sai Najib ba.


Sai da goggon Basira ta je (Sudan)taga in da gidan su Najib ya ke sannun ta dawo (Nigeria)


Ba lefi sun samu tarba sosai a wajan mahaifiyar har dama s'auran y'en uwanta Najib dan tana da kirki sosai,da taga Basira da yarta kamar ta haɗiye su saboda so


Najib da Basira sun yiwa Maman Najib karya kan cewa sun daɗe da aure saboda ba sa so su fada mata cewa tun kafin aure suka haihu.


Mohsin da Ibrahim dan gidan Aunty Maryam sun kara girma sosai dan s'aura shekara ɗaya ma kacal ya rage musu su kammala makaranta


Bangaren Ai'shan Aunty Maryam ma ta na z'aune lafiya da mijinta Aliyu a yan zu haka suna da yaro Huda ɗaya.


Bangaren Mufeeda sosayyarsu da Yusuf ya yi nisa sosai har ma manya ya shiga maganar anyi angama har ma an saka rana a yan zun haka s'aura wata ɗaya kacal ya rage ayi bikinsu dan har dana Ai'sha kanwarta za'a haɗa


*Dubaï Abu Dhabi*


"Habibti zo kiga wani abu"."toh gani nan zuwa"Na faɗi da s'auri na fito daga cikin kitchen din na nufo ɗakin dan a zatoh na_ na d'auka ko barna Zarina ta ke min ne dan ya wanci in ya min wannan kiran toh ba lafiya ba,


Abun mamaki ina zuwa na tarar da Zarina bata ɗakin,kara sowa na yi gefen gadon ina cewa Habibi gani"shiru ya yi kamar mai bacci dan a kwance ya ke akan gado ga kuma idonsa dake rufe kamar mai bacci,


"Shi ke nan bari na koma naci gaba da girkina tun da bazaka faɗa min dalilin ɗaya sa ka kirani ba"Na faɗi haɗe da juyowa zan tafi ya riko hannuna ya jani na faɗa irjinsa kara ya saƙi "washhh! a lokacin dana faɗa jikinsa"wallahi habibti zaki karya ni"Ya faɗi ya na kara jani a jikinsa,haba yan zu duka_ duka jikin na wa _nawa take da zaka ce zan karya ka"wani irin hararan wasa ya tallamin kana ya ce "ba ki ga yan da ki ka koma ba tabar kallah!"Na ji ni dai faɗa min dalilin ɗaya sa ka kira ni?"."Toh shi ke nan kawo kunnanki na faɗa miki dan bana son kowa ya ji""Haba habibi mu ɓiyu ne fah kawai anan kuma sai na kawo kunnena"."Eh mana ke dai kawo na gaya miki"kwantar da jikina na yi dai_ dai nashi kana na matso da kunnena s'aitin bakinsa na ce"Toh fada min""Toh" ya furta kana sai ya ciji kunnen nawa kaɗan wani irin kukan shogoɓa na saƙi sannun na ce "habibi me haka?".na faɗi ina turo baki gaba,dongon hancina ya ja kana ya shiga yi min wasu abubunwan mai yiwan fassara sai a lokacin na ga ne dalilin kiran da ya min,wani tunani ne ya zo min dan haka na ce "Habibi kasan mene ne kuwa?"Kai ya girgiza min alamar bai sani ba,kwana kin baya da muka je Nigeria na je gidan Ai'shan Aunty Maryam mun haɗu da mijinta ashe ma mijin tsohon saurayina ne"wani irin kishi ne ya taso wa Habib kana ya buɗe baki daƙer ya ce "toh in kin je (Nigeria)kar na saƙe gani kin je gidana su"murmushi na dan yi haɗe da ja hancinsa,kana na ce "tsarkin kishi toh ba saurayina ba ne.ya dai taba cewa ya na sona a lokacin da naje zuwa mutsa jiki,in na muka fara haɗuwa da kai toh acan shima muka haɗu""toh da kuka haɗu mai ya ce miki"?".cewa ya yi ya na so na shi ne na haɗa rai na ce masa ya je zan neme shi tun lokacin bai saƙe ganina ba sai ranar dana je gidan su muka haɗu a can,da muka haɗu ya nuna Kamar bai sanni ba nima na nuna kamar ban taba ganinsa ba""ummm sai yan zu na ji magana"Habib ya faɗi ya na ci gaba da abubun daya fara mim ɗazu


"Habibina girkifah na ke yi"Na faɗi.bai tanka min ba sai ma daga ni da ya yi daga jikinsa ya miƙe ya bar ɗak'in babu jimawa ya dawo,


"Na je na kashe miki gass din"zan yi magana ya haɗa bakinmu waje ɠuda ya ginda kissing


Ni kam fitowa na yi na ja musu kofah na kara gaba dan mu ba mu iya wannan abun ba 🏃‍♀️😂🤌


*Bayan sheraka ɓiyar*


An yi bikin Yusuf da Mufeenda haka ma Ai'sha kanwar mufida a yan zu haka Mufeenda na da Yaya ɓiyu mace dana miji,in da Ai'sha kanwar Mufeeda kuma take da ƴah mace ɗaya sai tsowon cikin da take da shi a yan zu


Habib ya mallakawa Yusuf companyn Afiya,sai da ya yi da gaske kafin Yusuf ya amince ya karbi companyn


Ya budewa Afiya wani katon company a (Dubaï) ya saka maikata sosai a ciki way'en da zasu dinga kullar mata da companyn, saboda ita ba kullun take zuwa ba


*Bangaren Basira*


Tun lokacin da aka d'aura musu aure tare da Najib soyayya wata daya kawai suka yi,ya dinga kawo mata 'ƴammata kala _kala a gida ya zo ya kwata da su,wani lokaci ma in ya sha giya a gabanta ya ke kwanciya da su din


Ana haka ne ya kwanta rashin lafiya ana kaishi a sibiti aka shai da musu cewa Najib na d'auke da cutar mai karya garkuwan jiki,tun da Basira ta ji wannan labarin take kuka sai tsinewa Najib ta ke wai shi ke nan ya lalata mata rayuwa ya sa mata cuta maganganu dai ga su nan kala _kala


A haka dai ta dawo gida ta zo ta haɗa kayanta ta wuce tasha ta shiga mota sai garin (Kano)


Tana dawowa ta fadawa mahifinta a bun da ya ke faruwa duk suka shiga tashin hankali anan ne mahaifinta ya shiga yin magana kamar haka "kin ga a bunda na ke gaya miki ko amma ki ka ƙi y'edda sai da ki ka je ki ka jajibo mana wannan cikin da kuma wannna mutumin yan zu ga irinta nan.


Basira bata yi magana ba a haka ta wuce a sibiti tana zuwa aka mata tess anan ne aka tabbatar mata da cewa ita ma ta kamu da cutar da aka faɗa mata suma ta yi a sibitin sai da aka yayyafa mata ruwa sannun ta farfado bayan an bata maganin da zata dinga sha aka kira mahifinta ya zo ya tafi da ita gida


*Bayan wata uƙu*


Suka ji labari Allah ya yi wa Najib rasuwa,


Ita ma dai Basira duk ta rame ta yi baƙi duk ta fita daga cikin hayyacinta


Tana cikin taƙ'aba ita ma Allah ya yi mata rasuwa


Iyayenta sun yi kuka har sun gode Allah!


*Bayan shekara ɓiyu*


*Kano Nigeria*


*Aminu Kano international airport*


Mama ce da Ammi da'a yan zu sufah ya fara kama su ne suk'e sallama rungume juna suka yi kana Ammi ta ce "Oum Mohsin sai mun sake zuwa sunan ɗan Mohsin Kuma tun da yan zun mun zo biki


Murmushi Mama ta yi sannun ta ce "Haba dai in sha Allah kafin nan zaku dawo ko kin manta matar ibarahim ta kusa haihuwa ne"?"Eh haka ne kuma. toh Allah ya s'auke ta lafiya"Da"ameeen Mama ta amsa


Zuwa na yi na rungume Mama ina cewa "toh Mama sai mun saƙe zuwa"Shafah kaina Mama ta yi sannun ta ce "Ameen ya Allah!Allah ya kai mu""Ameen nima na amsa.


"Sitti!Oum fah ta yi girma ki ce mata ta dena yiwa Mama haka" ƴaron da bai wuce shekaru uƙu ba ya fada,


Dan a yan zu Afiya ta na da ƴaƴa uku maza ɓiyu mace ɗaya,a yan zu haka ta bar guda biyu a gida da kara min kawai tazo


Dan way'en can sun yi girma dan macen mai suna Nuria(Zarina)a yan zu tana da shekara 8 sai ta biyu mai suna Abubakar (Munif)na da shekara 6 sai wanda aka zo da Shi mai suna Muhammad(Fauzan)wanda aka zo da shi mai shekara huɗu


Dariya Ammi ta yi kana ta ce y'auwa gaya mata dai my boy ko zata dena


Dariya suka yi su duka sannun suka kara yiwa juna sallama suka nufi in da jirgi da za su hau ya ke,


*Cikin jirgi*


Ammi da Fauzan na gabam mu_mu kuma muna bayan su shi ya sa basa ganin a bun da muke yi


Kwantar da kaina na yi kan kafaɗunsa haɗe da kurawa kyakkyawar duskarsa idanu,shima ni ya ke kallo,murmushi muka sakarwa juna kana ya furta "I love you my wife"Lumshe mai ido na_ na yi sannun na ce "I Love you more H.M.H" murmushi ya saki sai ya tuna lokacin da naƙe kiran sa da sunan ya matso da bakinsa s'aitin kunnena ya furta "Afiiiiiiii! A hankali 🥹❤️


Nima fah Sakina na ce "Afiiiiiiii! 😂Atoh nima baza'a barni a baya ba 😂😂🤌


Alhamdulillah!
Alhamdulillah!!
Alhamdulillah!!


Duka_ duka anan na kawo muku karshen Wannan littafin nawa mai suna DUHU DA HASKE 🥹


Abun da na faɗi dai _dai Allah ya sa mu amfana da shi😍


Wanda na faɗi ba dai _dai ba Allah ka yafe min da ni da masu karatu gaba ɗaya,


Ina yinku sosai masoyana masoyan❤️😍 littatafai na 📚


Godiya tamu samman ga kungiyarmu ta Jajirtattu💪 Allah ya saka muku da alkhairi ya biyaku da gidan Aljanna Ameen 🥰 Allah ya kara hada kanmu 😍


Sai mun haɗu a wannan sabon Book d'in dana fara mai suna :Ni DA KaNIN MIJINA,karku bari a baku labari dan salonsa shima daban ne dana s'auran🥰


Zan yi missind din su Afiya da ɗana Habib 🥹😩


*Fulanin Jajirtattu ce ✍️*
[6/30, 14:29] Mom Muwadda🥰: Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/KpwDZw5aq7C2Pr2NCZ3Ujg


🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑


*DUHU DA HASKE*


*By*


*Sakeena ismail Cameroon*
*(Mom muwadda)*

🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼


*Marubuciyar*
*Bazan zauna da kishiya ba*
*Mijin attajira*
*Mugun uba*
*Duhu da haske typing*...✍️

Page9&10


Free book

Bismillahi rahmani rahim

******"Ya fada yana hade rai kamar ba shine dazu yayi magana cikin sakin fuska ba,cikin sanyin murya ta fara magana..kayi hakuri Mr H.M.h!amma wllhy ba haka bane ?


Toh in ba haka ba?ya ne ?ya tambaya? yana tsare ta da idanu,sunkuyar da kanta tayi kasa dan bazata iya jure ganin kwayar idanunsa ba, saboda kwarjinin sa yayi yawa,


Ke nake sauraro ? Habib ya sake fadi,wllhy lefin seketariya ta ce,bata gaya min,sune suka zo ba,


Karfa ki renamin hankali afiiii!


Lumshe ido tayi a lokacin da yake kiran sunan nata"dan ji take duk duniya babu wanda ya iya kiran sunanta sama da shi"saboda yanda ya kira sunan nata ba karamin dadi sunan yayi mata"ba,


Mutanena sun fada min kingansu a lokacin da kike barin office!


Sabota sun tabbatar min da cewa har gabansu"kikazo kika wuce kika fita,


Amma shine yanzu zakice lefin seketariyarki ce"


Rasa bakin magana afiya tayi dan yanzu kam surutun nasa"ya soma damunta"


Mutun sai tsurutun tsiya?

Ta fada a kasan makogoro,


Abunda bata sani ba shine,habib irin mutanen nan ne masu ji,dan ko maganar zuci kayi yana ganewa,


Humm yanzu maganar da nakeyi ne shine tsurutu?"Habib ya fada yana kallon afiya,


Dagowa tayi cikin mamaki tana fadin wllhy ban....bata karasa ba,ya daga mata hannu,


Karki kuskura ki rantse akan karya,yana kaiwa nan ya mike,


Ya fara kokarin barin office din,har ya kai bakin kofah sai ya tsinkari maganarta tana fadin...dan allah Mr H kayi hakuri,ka dawo muyi magana,


Karki damu Habib Muhammad Habib in yayi niyar taimako baya janyewa,ya fada ba tare daya juya ba,dan haka hannu yasa ya bude kofar ya fice.


Habib Muhammad Habib !haka afiya ta shiga mai maita sunan akasan lebenta"


Wai yana nufin shine Habib Muhammad Habib da nakejin lbr,wai dama shine yazo jiya naji samari na magana,ta fada,


Tabbas shine,dan sai yanzu na gane dalilin dayasa ya saka HMH, Habib Muhammad Habib !kenan ta fada, hade da mikewa,


Kayanta ta fara tattakawa tana saka a jaka,


Bayan ta gaba fita tayi,ta samu safna a office dinta,tana aiki a wasu ta kardu.


Safna ni zan wuce,ta fada tana kallon safna,

Aunty tun yanzu?


Eh,bana jin dadi wannan mutumin yazo ya samin ciwon Kai da wannan hayaliyar nashi"


Kina nufin wannan balaraben safna ta tambaya, eh shi fah,

Ko kin sanshi ne? afiya ta tambayi safna,

Zaro ido waje safna tayi tana fadin tabb aunty ni asu wa da zan san babbar mutun kamar wannan,


Shikenan,na tafi,toh aunty allah ya kiyaye "Ameen afiya ta fada a lolacin da take kokarin barin office din"har ta zo bakin kofah,kome ta tuna sai ta juya tana fadin...safna kina jin lbrn Habib Muhammad Habib,da sauri safna ta mike tana geda kai,tare da fadin karfa ace wannan shine aunty?


Tabbas shine safna,


Haba dole yayar kawata ta damemu da sunanshi"


Kikace me safna?"afiya ta fada tana dawowa cikin office din.


Kina nufin yayar kawarki tasan Habib,

Eh aunty,amma fah shi bai santa ba,itta ce dai take haukanta itta kadai,saboda sun taba shiga jirgi tare,toh tun a lokacin take sonshi"shiyasa ma har yanzu batayi aure ba.


Ni ba wannan na tambayeki ba safna,


Toh aunty kece fah kika tambayeni,toh naji gayamin tasan komai akanshi ne ?"shiru safna tayi kamar mai nazari,

Sai kuma tace a'a aunty lbrn sane kawai ta taba bamu ni da Naja kanwarta,

Good afiya ta fadi,tana jawo kujerar dake cikin office din ta zauna,


Bani lbrn naji,?"yau kuma aunty kece da jin lbr?


Dakata safna zaki bani ko bazaki bani ba natashi na tafi?"


A'a yi hakuri aunty allah ya wuci zuciyarki,ni na isa ince bazan baki ba,bari ma kigani,safna ta fada itta ma ta koma ta zauna.


*Labari*


Alhaji Habib Ibrahim babban dan kasuwa ne tako waca fenni,


Irin mutanen nan ne da ake kira kome da ruwanka,ya shahara sosai ta fennin kasuwanci, yana da yara guda uku, Muhammad ne babba,sai Nabila,sai Maryam autarsu"


Matarsa daya hajiya aisha wacca akafi sani da hajiya indo!


Sun bawa yaransu tarbiya dai dai gwargwodo,


Ga kuma ilimin da suka samu,daga boko har arabiya,


Kasan cewa Muhammad shi kadai ne namiji kuma shine babba a cikin yaransa"shiyasa ya gaji mahaifinsa ta harkan kasuwanci,kasan cewa shima ta fennin kasuwancin ya karanta shiyasa abun yazo mai da sauki,dan tunda ya fara harkan, kasuwanci komai nasu ya karaci gaba,dan duk garin babu wanda bai san alhaji Habib Ibrahim ba,


Wani kata faren kanfani seda a tamfofi da lesika suka bude,


Akwai wata rana da Muhammad yake zaune da abokinsa"auwal,anan ne auwal yake bawa Muhammad lbrn irin kudaden da yake samu ta harkan seda man petir,ya kuma kara da cewa mezai hana shima bazai gwada ya gani ba,da farko dai Muhammad kin amincewa yayi,saboda a cewarsa suda suke da wayennan kudaden wana kudi kuma suke bukata,


Auwal yace haba abokina ta yaya kudi zasuyi yawa,


Da Muhammad yaga auwal ya nace,sai yace mai insha allah zaiyi shawara da mahaifnsa duk yanda sukayi zai gaya masa"da haka dai suka rabu,


Bayan Muhammad ya gayawa mahaifinsa yanda sukayi da auwal shima yayi na'am da maganar,dan haka yacewa Muhammad yaje ya tambayi auwal in za'a fara sana'ar kamar nawa za'a bukata?"


Bayan Muhammad yaje ya gayawa auwal yanda sukayi da mahaifinsa yaji dadi sosai,dan haka ya gaya masa kudin,sannun shima Muhammad yaje ya fadawa mahaifinsa"


*Bayan wata biyu*


An kammala komai inda Muhammad ya bude gidan mai,yasaka mutane yana mai aikin,shikuma yana kula da kanfanin mahaifinsa"


Wasa wasa a cikin shekara uku,sai ga Muhammad ya mallaki gidan mai har guda shiga,dan ba karamin karban sa sana'ar yayi ba,


Shiyasa auwal ya fara kishin Muhammad,duk da kuwa shima yana samu amma na Muhammad ya bashi mamaki sosai,har yayi na damar bashi shawaran seda man petir,


Muhammad yaga canji sosai wajan auwal,dan abukantakarsu"ya faka ja baya,kuma a duk lokacin da Muhammad zai tambayi auwal dalilin canzawar shi cewa zaiyi babu komai,


*Bayan wata biyar*


Yanzun kam Muhammad ya fahimci kishi auwal yakeyi dashi"amma har yanzu,bai dena zuwa wajan auwal ba"duk da kuwa shi auwal a yanzu baya zuwa wajan Muhammad,kuma in Muhammad din yaje wajanshi,ba wani kulashi yake ba,

Tun Muhammad yana jure wulakancin da auwal yake masa"har ya kasa ya hakura shima ya fita sabgarshi"


*Bayan wata biyar*


Alhaji Habib Ibrahim ne zaune a palo tare da matarsa hajiya indo"


Sai Muhammad dake Zaune a kasan carpet din,yana jiran yaji da lilin dayasa mahaifinsa ya kirashi"

Gyaran murya alhaji Habib yayi ya fara magana kamar haka... Muhammad kafi kowa sanin cewa kaine babba kuma kai ka dai namiji,allah ya baka komai na rayuwa ilimin addini dana zamani duk ka samu babu wanda baka samu daga ciki ba"


Dan haka ina so ka kawomin matar aure nan da sati biyu, saboda na gaji da ganinka a haka, Alhaji Habib ya karashe maganar,


Tunda mahaifinsa ya fara magana kansa yake kasa"bai dago ya kallesa ba har ya kai aya,dan wannan dabiyarsa ce,


Shikenan abba insha allah zanyi abunda kace,


Masha allah allah yayi maka albarka, Ameen Muhammad ya amsa"


Zaka iya tafiya alhaji habib ya fada,

Toh nagode abba Allah ya kara girma?"Ameen"abba ya amsa shi kuma Muhammad ya mike ya bar palon.


*Bayan kwana shabiyar*

Muhammad yau sati biyu har da kwana daya bakace komai ba,


Dan haka ina so na sani inda maganarmu ta kwana?"


Wllhy abba ban samu ba amma insha allah ina ci gaba da nemowa,


Haba Muhammad yanzu so kake kace min har yanzu baka samu ba,wai kai ko kunya ma bakaji?"kannenka duka sunyi aure amma kai har yanzu,kayi hakuri abba,kaga malam ba hakuri zaka saya bani ba,matar aure nace ka nema,dan haka na kara baka sati daya,in har baka kawo ba,ni da kaina zan zabo maka wacca ta dace da kai,dan haka kana dawowa daga tafiya Dubaï da kace zakayi,ka gabatar min ta matar da zaka aura,tashi ka tafi na sallameka, alhaji Habib ya fada,


Jiki a sanyaye ya mike ya bar palon,


*Bayan kwana biyu*

*Dubaï ,habu dabi*


Tun lokacin daya shigo supermarket din yaganta tana siyayya,kuma da alama takusa gamawa,dan haka sauri yayi shima ya dauki a bunda yake da bukata"lokacin kuma har ta wuce wajan biya,dan haka shima da sauri saurin sa ya karasa wajan biyan,kudi ta fido dashi da niyar biya ya rigata ajiye magodan kudi a gaban masu biyan hade da cewa....gashi ku hada nawa da nata duka ku dauka anan,in bai isa ba kuma sai a karo,ya fada da harshen larabci,saboda ya iya sosai shima,


Da yake yana yawan zuwa"Dubaï,


Murmuchi saurayin yayi yana fadin haba yellabai ai wannan kudin tamayi yawa"dan na tabbata kana da ragowar canji ma a ciki,


Okay shikenan ka saka mana kayanmu a leda, in yaso ka rike canjin, Muhammad ya fada yana kallon saurayin,godiya saurayin yayi ya shiga hada kayan,


Yer matashiyar budurwar da tun da suka fara magana bata saka musu baki ba ?tayi magana..kaga ka dauki iya nasa kudin ni ina da kudin da zan biya ta fada tana mika mai kudin dake hannunta"


Hannu biyu Muhammad ya hada yana rokonta,kinga dan allah dan annabi karki maida hannun kyauta baya,kinga babu kyau maida hannun kyauta baya,shiru tayi,bata ce dashi komai ba,kudin data fito dashi ta mayer cikin jakarta,tare da dauko kayan da aka saka a leda, sannun ta fice daga cikin supermarket din,


Da sauri sauri ya karbi tasa ledan yabi bayanta"


Da yayi niyar yace mata dazo ya rege mata hanya,sai kuma yaganta da mota"


Bude bayan mota tayi ta saka kayan data siya a ciki,sannun ta zaga ta mazaunin dreve ta bude murfin da niyar shiga sai taji Muhammad na magana....kinga pretty kisaya dan allah,sayawa tayi cak da shiga motar da tayi niyar yi,har ya karasa wajan da take saye,


Sunana Muhammad Habib Ibrahim,ya fada,

Badan komai ya gaya mata sunansa ba"sai dan yana so itta ma ta fada masa"nata sunan,


Fahimtar da tayi ne yasa ta murmusawa, tare da fadin... Sunana muriya ?woww suna mai dadi, thanks ta fada a yayinda take shiga cikin motarta,hade da jawo murfin motar da niyar rufewa,


Saurin rike murfin motar yayi yana fadin dan allah number wayarki,yatsine fuska tayi hade da turo dan karamin bakinta mai ja lebe gaba,

Pls ya fada hade da hada hanna yensa biyu alamar roko,


Kate dinta"ta dauka a cikin motar ta mika masa"hannu na rawa ya karba,yana godiya,itta dai bata saya ta saurareshi ba tayiwa motarta key ta bar wajan..........


*Sakeena ismail Cameroon ce ✍️*


07049322735
Chapter 3 · 0% Book details