Gabatarwa
Duhu Da Haske Part 1 Complete Hausa Novel · about 49 min read
DUHU DA HASKE by Sakina Isma'il Cameroon [6/21, 15:24] Mom Muwadda🥰: utilise ce lien pour intégrer mon groupe whatsapp : https://chat.whatsapp.com/kpwdzw5aq7c2pr2ncz3ujg
🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑
*DUHU DA HASKE*
*by*
*sakeena ismail cameroon*
*(mom muwadda*)
🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼
*marubuciyar*
*bazan zauna da kishiya ba*
*mijina attajira*
*mugun uba*
*sai na yanzu da aka fara mai suna duhu da haske*✍️
*kamar yanda na fara lfy allah ubangiji yasa na gamashi lfy*
page 1&2
bismillahi rahmani rahim
*******Zaune take a kan kujerar dake cikin office din kamar kullun sai juyi take akan kujerar,kallo daya zaka mata ka fahimci tana cikin damuwa, yau ma dai tunanin da ta tsabayin kullun takeyi...dama rayuwata zata canza?dama rayuwata zata koma kamar da?"duk da kuwa lokacin ma bawai ina cikin farinciki bane?amma gwara wancan lokacin akan yan...jin da tayi ana mata nocking kofar office din ne ya sata dawowa cikin haiyacinta"Shigo."
Ta fada kamar bata son yin maganar,
turo kofar aka yi aka shigo,ba tare da ta dena juyi akan kujeran ba,ba tare da kuma ta kalleta ba tace "Whatttt ?"
matashiyar buduwar da kallo daya zaka mata ka fahimci itta din seketariyar tace,ta bude baki kamar jira take ogar tata tayi magana nama,a take ta bata amsa kamar haka... "Ranki ya daɗe kin yi baƙi?"
Tsaki wacca aka kira da ranki ya dade taja hade da buga teburin dake gabanta da karfi har sai da seketariya ta tsorata, dagowa tayi hade da tire glass din dake idonta, sai ga fararen idanunta sun baiyana, zubawa budurwar dake gabanta idanu tayi lokaci daya kuma sai ta dauke idonta taga kallon budurwar da take yi.
Shiru seketariya tayi tana kallon ogar nata,
kyakkyawa,farace sosai dan saboda tsabar hasken da tayi ma har wani yellow- yellow take yi,tana da godon fuska da kuma dogon hancinta daya ƙawata fuskarta dashi sai karamin bakinta dake dauke da Pink din lips idan baka santa ba ma zaka dauka jambaki ta saka,amma a zahirin gaskiya ko powde bata sakawa balle jambaki da kwalli,amma duk da haka tafi wasu da suke mek up din haduwa da kyau.
dauke ido sakatariya tayi daga kallon ogan nata da takeyi, hade da juyawa da niyar barin office din sai taji ta kirata "Safna!". Ta kira sunan ta,
juyowa Safna tayi tana kallon ogan nata,amma sai taga kayanta ma take hadawa,da alama tafiya zatayi,
badan tasan halinta ba da zata iya cewa bata kirata ba ma.
har ta fudda rai zatayi magana sai kuma taji tana fadin... "Bazan iya ganin kowa ba".. Ta yi maganar a lokacin da take ficewa daga cikin office din.
baki bude Safna tabi ogan nata dashi hade da girgiza kai.
tana fita bata tsaya ko ina ba sai wajan ajiye motoci, kafin ta karasa wajan motarta ta kunna ta ,dan haka tana karasa wajan wani daya daga cikin ma'aikatanta ne yazo ya bude mata murfin motar,
numshe mai ido tayi kana ta buɗe su,wato alamar godiya,kafin daga visani ta shiga motar.
"Ba komai Madam a sauka lfy.." Cewar saurayin dan ya fahimci godiya tayi mai daya bude mata mota,saboda Babu wanda bai san halinta ba,na rashin yin magana.
batare da ta ce dashi komai ba tayiwa motar key hade da barin Company .
*Nasarawa J.R.A*
a gaban wani katon gida tayi hone,in na faɗa muku kyau da gidan yayi ma bata lokaci ne.
daya daga cikin security's din su ne yazo ya bude mata gate.
Shiga tayi ta motarta tanufi
wajan ajiye motoci taje tayi parking,sannan ta fito rike da hand bag dinta"da sauri security's din sukaxo suna mata sannu da zuwa,
kai kawai ta iya geda musu sannan ta juya da niyar shiga cikin gidan,sai ɗaya daga cikin security's din ya mika hannu da niyar karbo jakar hannunta, ta daga mai hannu hade da fadin..."Sau nawa zan gaya maka Yusuf?". Tana kaiwa nan ta bar wajan.
badan suna tade da itta ba, da sam bazasu taba fahimtar maganar ta ba,saboda in ta fara bata karasawa,
Saboda maganarta bata wuce kalma daya zuwa biyu,in kaga maganar ta ya wuce kalma biyu toh da ƙaninta take magana..
tana shiga palon ta tarar da wata mata fara amma kana ganin hasken nata kasan na mai ne ba hasken taba,sabanin na yer tata saboda itta kallo daya zaka mata kafahimci hasken tane ,harkalla Maman nata zata iya yi shekaru 45 zaune take ,akan kujera mai zaman mutun daya ta mika kafafuwanta akan daya daga cikin kananun teburin da suke tsakiyar palon,daya kuma kayan motsa baki kala- kala akai,dan in kaga yawansu ma zaka rantse na mutun goma ne,
nan kuwa itta ce kadai takeci,kuma bawai zata iya cinyewa su ba.
dagowa tayi tana kallon yer tata da ta shigo yanzu tare da fadin..." AFIYA ya naga kin dawo da wuri yau ?"
Maimakon AFIYA ta amsa mata sai ma kallon a bubuwan dake gaban Mamar nata da tayi tana girgiza kai,hade da barin palon ta wuce dakinta.
har tazo gaf da bakin kofar dakin nata sai ta sinkari muryar Mamanta na cewa...."Wallhy ki kiyayeni AFIYA yanzu ni zanyi magana kiyi min banza ?"
"Sorry Mama." Cewar AFIYA tana karasa shiga dakinta,hade da banko kofah da karfi.
"Ki karye kofar ai kudin naki ne sai ki canza wani Hajiya Fatima Maman AFIYA ta fada wacca aka fi kiranta da Hajiya Batulu mai abun mamaki.
*cikin layinsu afiya*
Majalisan cike yake kamar kullun,daya daga cikin samarin ne ya kalli sauran sai ya fara magana kamar haka.."Ni wllhy da zan samu Afiya ta amince ta aureni da wllhy na more,dan wllhy ina sonta".
"Tabbb! kai kuma Aliyu ka rasa wa zakace kana so sai karuwa?". Cewar daya daga cikin samarin.
toh ni ina ruwana da wani karuwancinta,ni dai in har zata amince ta so ni ,ta aureni ai shikenn,tunda na tabbata ko shogabangasa aka bashi Afiya da gudu zai amince wllhy,
ballantana ni da ba kowa ba,saboda kawai itta din karuwa,sai kuma akace baza'a aureta ba,bari na maka wata tambaya Faisal yanzu in ance ka kawo hujja kana dashi ne ?".Bani dashi Aliyu amma ai babu wanda baisan cewa ita ɗin karuwa ce ba." Cewa Faisal.
"Ai shikenan ni dai baza'aci naman wani dani ba." Aliyu ya fada yana mai mikewa,
"Ina kuma zaka je Aliyu?"Samarin dake wajan suka hada baki wajan tambayar Aliyu.
"Gida zan tafi".
"Yanzu dan kawai na fadi gaskiya shine zaka ce gida zaka tafi?."Faisal ya fada yana kallon Aliyu,
"Kaga Faisal ka rike gaskiyar ka." Aliyu ya faɗa haɗe da juyowa ya bar wajan.
"Kai ma dai Faisal kana da matsala wllhy kasan halin gayennan tsarai ba'a gulmar AFIYA a gabansa amma har yau ka kasa fahimtar hakan."Daya daga cikin samarin ya faɗa.
"Dan kawai yana sonta sai inƙi fadar gaskiya?
Ni a bunda yafi komai bata min rai ma shine wacca yake yi dan ita bata ma san yana yi ba." Faisal ya karashe magana cikin bacin rai shima,hade da mikewa.
"Ina kuma zaka je kai ma?"Zanje nayi shirin zuwa masallaci ."Faisal ya basu amsa hade dayin gaba.
"Toh ka jira mu tafi tare mana mu ma muje gida muyi alwalan mutafi masallacin ."
Musa ya fada shima yana mikewa dashi da Umar,
Ranar dai ahaka majalisan ya watse,
Gidan su AFIYA kuwa tana jin a bunda Mamanta take cewa amma uffam bata ce ba,dan tasan halinta tsarai.
Ajiye hand bag dinta tayi akan makeken gadonta ta shiga rage kayan jikinta,
Kallon dakin nayi,dakin yayi kyau ba kadan ba,duk da kuwa babu wani tarkace sosai a ciki,
Dan daga gado sai wardrobe sai kuma dressing mirror,sai abun ajiye ta kalma,da kuma na ajiye jakunkuna"sai dan karamin TV dake manne a bango.
Tana gama rege kayan jikinta ta fada toilet,
Wanka tayi hade da alwala sannun ta fito.
Mai ta dauka ta shafa,sai turaruka,
Gaban wardrobe taje
Bangaren kananun kaya ta bude,riga mara nauyi ta dauka,wadda rigar in ta saka bazai wuce guiwarta ba,ta saka
Bayan tagama shiryawa?"
Hijabi ta saka akan karamin rigar dake jikinta ta tada sallah
Sallar azahar da batayi ba tun dazu tayi, hade da la'asar da aka kira yanzu,
Bayan ta idar da Sallah tashi tayi ta nade sallayar ta ajiye,hade da tire hijabin shima ta ninkeshi ta maidashi ta ajiye amahalinta
fita tayi ta nufi kitchen,
Tana zuwa palo ta iski Mamanta Zaune har yanzu sai faman ciye- ciye take har yanzu,tazo ta wuce ta ba tare da tayi mata magana ba,
Da kallo Hajiya Batulu tabi yer tata dashi hade da girgiza kai.
*Kitchen*
Masu aiki ne guda uku suke ta faman aiki,daya na girki daya kuma na wanke -wanke,daya na mopping din kitchen din,dan in kaga kitchen din zaka ranse ba aiki akayi a ciki ba,saboda ko ina saff yake Babu dadti ko kadan,wannan umarnin AFIYA ce, Saboda kwata- kwata bata son ƙazanta ko kadan, saboda akwai wani lokaci da ta shigo kitchen din ta tarar ba'ayi wanke- wanke ba ƙuda sai bin kwanukan suke,fada tayi musu sosai a karshe dai ranar AFIYA bataci abincin gidan ba.
Sai da ta je restored ta ci abinci.
"Barka da wannan lokacin Hajiya."Masu aiki suka hada baki wajan fadi .
"Tnx". Ta furta a takaice, saboda kwata,-kwata bata iyayin godon magana saboda wahala yake bata
Kujera ta samu ta zauna ba tare da tayi magana ba,
"Hajiya kina bukatar wani abu ne ?."Cewar daya daga cikin masu aikin
"Coffee,." Ta sake fadi.
Kai mai aikin ta geda ta shiga hadawa AFIYA Coffee din,
Ba'a fi mintuna biyar ba ta kammala hada Coffee din dazo ta rusuna har ƙasa ta mika mata,
Karba AFIYA tayi,tana fadin..."Tnx USNA!."Murmushi USNA tayi tare da fadin.."Ba komai Hajiya asha lfy".Kai AFIYA ta geda hade da mikewa ta bar kitchen din.
Kara zuwa tayi ta wuce palon ta koma dakinta
Mamar ta sake bita da kallo,
A zuciyarta kuwa fadi take ni wllhy yanzu kam rashin maganarki Afiya ya fara bani tsoro,ta fada cikin ranta tare da mikewa,da niyar wuce sama jin muryar dan autarta ne ya sata dakatar da hawa saman da tayi niyar yi,
Wani yarone da bazai wuce shekaru 15 zuwa 16 ba ya taho da gudu da niyar rungumar mahaifiyar tashi ko mai ya tuna kuma sai naga ya tsaya hade da sosa keya,yana fadi "Mama sannu da gida."
Harara ta dalla masa tare da fadin... "Na dauka ai fado min zaka yi ai tunda Kai kayi girma amma baka san kayi girma ba". Ta fada hade da juyawa ta fara hawa matattakalar,
Jiki a sanyaye yaron ya wuce dakin yayarsa dan yaga motarta awaje yasan ta dawo.
Nocking yayi,amma shiru ba'a bude ba sai ana biyu aka bude,
Kasan cewa bacci ne ya fara daukarta shiyasa bataji ba ana farkon sai ana biyun taji.
Ganin kanin tane ya sata sakin murmuchi daya sa kyawunta kara baiyana,
Hannu ta bude mai atake kuwa ya fada jikinta yana sauke ajiyar zuciya kamar karamin yaro,
Harkanla sun kai 5 second a haka sai daga visani
Ta sakeshi hade da bashi hanya ya shiga ciki sannun ta maida kofar ta rufe,
Dakin ta koma ta tarar dashi zune akan kujeran gadon ya rafka uban tagumi,
Cikin mutuwar jiki ta karasa kusa dashi ta zauna,hade da tire mai tagumin da yayi,
Dagowa yaron yayi yana kallon yayar tashi cikin so da kauna,dan sai yazo wajanta yake samun farinciki.
"Whatttt? Ta tambayeshi kamar ana mata dole yin maganar,
Yaron bai amsa ba,sai da ta sake yin magana akaro na biyu, "Mama?"Ta sake cewa,kai yaron ya geda mata alamar eh,
"Okay sorry."
Kai kawai yaron ya iya gedawa,duk da kuwa ita ma yayar tasa bawai godon magana zatayi mai ba amma ko ba komai yana jin dadi zama ta ita, saboda in yana cikin damuwa tana kwantar mai da hankali,
"Kaci a binci ?"Kai ya girgiza alamar a'a,kai ta geda,hade da mikewa, ta fita tabar dakin.
Bata wani dau lokaci ba ta dawo hannunta rike da plate din a binci,da ruwan roba zama tayi a gefensa ta shiga bashi a bincin kamar karamin yaro,sai ana uhu ne ya rike hannunta ya juya kan spoon din zuwa bakin yayar tashi,
Kai ta girgiza alamar bataci,
"A'a Aunty Afi kema fa na tabbata bakici abinci ba,dan haka dan Allah! ki karba."Ba yanda ta iya,a haka dai ta bude baki ya sa mata a bincin,a haka dai suka shiga bawa juna har suka cinye a bincin,
Sun shaku sosai dan sai in suna tare suke dan samun farinciki,
"Kaje kayi wanka.", Ta fada hade da dauko wayarta zatayi kira,
"Aunty wa zaki kira kuma?."
"USNA."Ta bashi amsa
"Kawo plate din na kai tunda fita zanyi."Mika mai kawai tayi ba tare da tayi magana ba,
Karba yayi ya bar dakin,ita kuma ta koma ta kwanta tayi shiru kamar mai bacci....,
*Sakeena ismail Cameroon ce*✍️
*07049322735*
[6/21, 15:24] Mom Muwadda🥰: Utilise ce lien pour intégrer mon groupe WhatsApp : https://chat.whatsapp.com/KpwDZw5aq7C2Pr2NCZ3Ujg
🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑
*DUHU Da HASKE*
*By*
*Sakeena ismail Cameroon*
*(Mom muwadda)*
🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼
*Marubuciyar*
*Bazan zauna da kishiya ba*
*Mijin attajira*
*Mugun uba*
*Sai na yanzu da aka fara mai suna duhu da haske✍️*
Page 3&4
Free book
Bismillahi rahmani rahim
*******Karba yayi ya bar dakin, komawa tayi ta kwanta tayi shiru kamar mai bacci,nan kuwa ba bacci takeyi ba idonta biyu tana tunanin rayuwar duniya da kuma halin irin na mahaifiyasu"dan yanzu kam abun nata ya dena bata mamaki ma,tsoro yake bata,
Tana nan kwance tana tunani tunani har baccin barawo ya saceta,
Mohseen kuwa yana ajiye plate din da sukaci a binci dashi a kitchen dakinsa" ya wuce,cikin sanyin jiki ya tire kayan sa,ya shiga wanka.
Ba itta ta tashi daga bacci ba sai bayan magriba,tana tashi a gurguje ta shiga toilet ta watsa ruwa hade dayin alwala,ta fito ta shirya cikin kayan bacci riga da wando,sannun ta saka hijabi ta tada sallah,
Data idar da sallah azkar ta shigayi,a takaice dai ba itta ta tashi daga sallayar ba,har sai da aka kira sallar i'sha tayi sannun ta mike ta ninke sallar hade da tire hijab din jikinta"ta linke ta ajiye.
Zama tayi a kan gado hade da dauko Laptop dinta ta fara aikin daya rege bata samu tayi a kanfani ba.
Hannu ta sa ta dauki wayarta dake gefen gadon tayi dialing wata number,ana dagawa,naji tace.... USNA coffee tana kaiwa nan ta kashe kiran.
Badan komai tafi son USNA ta hada mata coffee ba sai dan duk cikin masu"aikin tafisu safta har ma da iya girki,shiyasa in dai harkan a binci ne toh itta takeyin komai.
Kuma bata shiga harkan da ba nata ba,da lilin dayasa tasu ta dan zo daya kenan.
Ajiye wayan tayi ta fara aiki,
Ba'a dau lokaci sosai ba sai ga USNA rike da coffee a hannunta" ta shigo bayan ta kwankwasa ta bata izinin shigowa,sannu tayiwa hajiyar tasu sannun ta bata Coffee ta tafi.
*Washe gari*
Kasan cewa tana fita motsa jiki kafin ta wuce wajan aiki shiyasa"yau ma dai ta shirya saff kamar kullun,cikin kayan motsa jiki,riga da wando,wandon ya dan dameta kadan daga sama,kasan wandon kuma a bude take,sai riga mai karamin hannu gashin kanta ta tufke,ta yanda in ta fita motsa jiki bazai da me ta ba.
Bayan tagama tufke gashin nata"wula mara nauyi ta dauka ta rufe kanta dashi,hade da rataya jakar goyonta"sannun ta fice daga gidan.
Badan komai yasa bata son motsa jaki a gidan ba,sai dan tafi son ta fita waje tasha iska,
Da lilin dayasa take fita motsa jiki a waje kenan,kuma uwa uba in har tana motsa jiki a gida zata ginda ganin kayan takaicin da zai bata mata rai a banza,itta kuma batason hakan ta faru,dan in har hakan ta faru ko taje wajan aiki babu wanin aikin da zata iyayi,
Kasan cewa safiya ce Shiyasa ba kowa a unguwar tasu"ko da yake ma koda rana ma mutane basu fiya zama sosai ba a unguwar,kasan cewa unguwar ta masu kudi ne,
Sedai kafin ka karasa cikin layin nasu akwai majalisan da samari sukeyi da yamma.
Gudu tayi sosai,dan har kalla sai data dau kusan rabin awa tana gudu sai daga baya ta sagaita da gudun da takeyi.
Tun data fara gudu take lura dashi duk da kuwa ba yau ne ranar sa na farkon daya fara zuwa wajan ba.
Kana ganinsa"kasan ba abunda ya kawosa wajan ba kenan,saboda yanayin yanda yake motsa jikin ma kasan ba sabawa yayi ba,
Ganinta da yayi ta samu waje ta zauna a kan daya daga cikin kujerun dake wajan da akayi da simenti ne ya sashi yanke shawara zuwa yau ya gaya mata a bundake cikin zuciyarsa,
Dan ya kamu da sonta sosai duk da kuwa da farko ba son allah da annabi yake mata ba,dan da farko saboda kudin da take dashi ne?yasa yake son ya aureta",amma a yanzu so gaskiya yake mata saboda AFIYA ta hadu ko ta wana bangare,
Dan ko da bata da kudi?zata samu samarin da suke sonta"ballantana yanzu ga kudi ga hutu daya zauna jikinta.
Zaune take ta fito da ruwan dake cikin dan karamin jakar goyon da take saka karamin tawal da take goge zufah dash da kuma ruwan da zatasha.
Balla murfin jarkan tayi ta kafa a bakinta akai da niyar sha sai taji anyi "sallama" a gabanta dagowa tayi dan ganin waye sai idanunta suka sauka akan na Aliyu,saye yake a gabanta ya kura mata ido kamar idon nashi zai fado kasa"
Kallo daya tayi mai ta tauke kai, ba tare da amsa sallamar da yayi mata ba,sai ma kara daga ruwan jarkan da tayi ta kafa a bakinta"ta fara sha,
Sai data sha kusan rabi sannun ta tire bakinta a kai,
Murfin ta maida ta rufe,hade da maida jarkan cikin jakar goyon data zo dashi,
Igiyar kambos din dake kafarta data kwance ne ta gyara,
Dagowa tayi da niyar mikewa sai ta gansa tsaye a gabanta"ga wani irin kallo daya kafata dashi"
Wani irin tsaki ta ja'a daya sa Aliyu dawowa cikin haiyacinsa,hade da tsotsa keye.
"Sorry ya fada?,
Nan ma dai bata kulashi ba, sai ma mikewan da tayi ta tsoma tafiya da niyar barin wajan,
Da sauri sauri ya soma bin bayanta"hade da fadin...dan allah dan annabi AFIYA ki saya ki saurareni nayi miki alkawari bazan wuce minti biyar ba, Aliyu ya fada yana karasa inda AFIYA take saye,dan tun lokacin daya hadata da Allah ta saya cak ta dakatar da tafiyan da takeyi?
Saboda itta mutun ne da bayaso a hadashi da allah,dan in har an hada ta da allah toh zance yakare.
Tana nan tsaye,itta bata tafi ba ?itta bata juya ba ?
Bai damu da rashin juyawan da batayi ba,shi dai tunda har ya samu ta saya ai shikenan,
A gaban ta yazo ya saya,tana ganin haka ta maida fuskarta ta dayan gefe tana jira taji mai zai fada mata ?
3 minute ta fada ba tare data kalli inda yake ba.
Ya fahimci inda maganar ta ya dotsa tsarai,wato tana nufin ya cinye mintuna biyu saura uku.
Dan haka,da sauri sauri ya soma magana kamar haka....wllhy AFIYA tun lokacin dana dora idanuna akanki naji kin kwanta min arai,naji duk duniya babu macen da nakeso sama dake!
Ina sonki AFIYA dan allah ki amince da soyayyata nayi miki alkawari bazan taba yaudararki ba... tun lokacin da Aliyu ya fara maganar so ta juya tana kallon shi,sabanin dazu dako inda yake bata kalla ba.
Aliyu yana da kyau babu laifi,duk da kuwa bakii ne shi,amma bakin nasa irin mai kyau din nan ne,fuskarsa na da dan fadi, yana da hanci dai dai misali,dogone amma jikin da yake dashi ne yasa ba'a ganin tsayin nashi sosai.
Dauke kai tayi daga kallon shi da takeyi,hade dayin tsaki,dan ba karamin haushin kanta taji ba,data saya tana kallonshi"dan itta kwata kwata kallon mutun bai dameta ba, saboda ko mata ma bata sayawa ta kura musu ido,ballan tana na miji?
Kallon agogon dake daure akan tsintsiyar hannunta tayi taga har takwas takusa,
Dan haka tafiya ta somayi da sauri da sauri, tana barin wajan,
Da gudu aliyu ya sha kabanta,yana fadin haba AFIYA taya zan baiyana miki a bundake cikin zuciyarta amma zaki tafi ba tare da kince komai ba?
Sorry,namakara ta fada..hade da ci gaba da tafiya.
Har ta fita daga wajan aliyu na saye awajan data barshi bai motsa ba,sai daga baya ya fara tafiya shima cikin mutuwar jiki.
Mahaifin aliyu ya kasance shima daya daga cikin attajiran unguwar tasu,badan komai yada Aliyu yake zaman majalisa ba,sai dan tun lokacin da allah yayiwa mahaifinsa rasuwa baffan su ya cinye dukiyar tare da matar babansu"kasan cewa shi- shi kadai ne a wajan mahaifiyarsa"matar mahaifinsa kuma yana da yaya kusan bakwai,da farko dai yaso yayi rigima dasu akan cinye mai gaado da sukayi,sai mahaifiyarsa ta hanashi tace ya kyalesu"wanda yake dashi ma ya mutu ya barshi ballanta dukiya,a haka dai aliyu ya hakura da dukiyar amma badan yana so ba,sai dan yiwa mahaifiyarsa biyayya.
Kasan cewa yayi karatu sosai yana da diploma shiyasa ya dauki ta kardun nashi,ya shiga nemon aiki amma babu inda bai je ba,amma bai samu ba,wata ranane yaji wani yana cewa mamar babansu ne ya hana a bashi aiki,saboda duk inda yaje nemon aiki ana kawo mata bayanin komai,
Shiyasa ya hakura da nemon aikin,ya mikawa lamuransa ga allah.
*Kunji lbrn aliyu kenan*
Tana zuwa gida a gurguje tayi wanka ta shirya cikin dogowar riga na materiale,sai ta yane kanta da karamin mayafi,
Tayi kyau sosai hand bag dinta ta dauka kalar ta kalmin kafarta,wayoyinta da key din motarta data dora akan dressing mirror ta dauka ta sakasu a hand bag dinta,
Sannun ta fice daga dakin bayan ta kulle dakin, zuwa tayi ta wuce palon ba kowa,
Bata saya ko ina ba sai wajan ajiye motoci,bude murfin motar tayi da niyar shiga sai taji kaninta Mohseen na kiran sunan ta,aunty Afi ! aunty afi!!dakatar da bude motar da tayi niyar yi tati, ta zuba masa idanu har ya karaso inda take,
Good morning aunty Afi? Mohseen ya fada,
Morning kanina ya kake?lfy lau aunty dama naga kamar fita zakiyi na shiga ki ajiye ni a school ne ?
Kallon sa tayi na yen second ni sai ta maida kallonta ga drave din dayake saye yana jiran Mohseen ya fito su tafi,
Sorry baba?"ta fada tana kallon baba drave .
Bata saya amsar baba drave ba ta kalli Mohseen ?hade da cewa...shiga mutafi,kai yaron ya geda jikin murna ya balla murfin mota ya shiga gaba ya zauna a mazaunin mai zaman banza.
Shiga tayi itta ma tare da yiwa motar key aka wangare musu gat ta ja'a motarta ta fice daga gidan.
Tuki takeyi cikin nitsuwa,suna hira jefi jefi,amma yawanci yiran na Mohseen ne yafi yawa saboda itta daga hummm sai uhumm,har suka karasa *ADo bayero*
*University*
5k ta fito dashi daga cikin jakarta ta mikawa Mohseen,cikin murna ya karba hade dayi mata godiya sannun sukayi sallama ya fita ya nufi cikin makarntarsu"itta kuma ta ja'a motarta ta wuce kanfani....,
*Sakeena ismail Cameroon ce*✍️
07049322735
[6/21, 15:24] Mom Muwadda🥰: Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/KpwDZw5aq7C2Pr2NCZ3Ujg
🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑
*DUHU DA HASKE*
*By*
*Sakeena ismail Cameroon*
*(Mom muwadda)*
🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼
*Marubuciyar*
*Bazan zauna da kishiya ba*
*Mijin attajira*
*Mugun uba*
*Duhu da haske* *typing*....✍️
Page 5&6
Free book
Bismillahi rahmani rahim
********Tana zuwa kanfani bayan tayi barking din motarta"ta fito ta nufi cikin kanfanin,tun kafin ta karasa ciki ma aikatan suke tayi mata sannu da "zuwa,itta kam ogan tasu kai da hannu kawai take daga musu" har ta karasa ciki,
Da yake ta cikin office din seketariya take wucewa kafin ta karasa cikin nata office din,dan haka seketariyarta na ganinta"ta taho da sauri ta karbi jakar hannunta suka wuce ciki,
Seketariya na gaba afiya na biye da itta a baya,har suka karasa gaban office din,sai da safna ta budewa afiya kofar ta fara shiga tukun sannun ta shiga itta ma hade da maida kofar ta rufe,
Lokacin tuni afiya ta karasa cikin office din ta zauna kan kujera,dan haka safna ma ta karasa ta itta ma ta a jiye mata jakar akan table din,
Takardun dannunta afiya tabi da kallo,daga baya kuma sai ta maida dubanta ga safna,
Safna na ganin haka ta fara bayani kamar haka...?ranki ya dade bakin da suka zo jiya ne suka bani wannan ta kartun sukace na baki,safna ta fada hade da mikawa afiya ta kartun,
Hannu afiya tasa ta karbi ta kardun,ta shiga dubawa, ganin a bunda tagani akai ne yasa ta mikewa da sauri hade da tire farin glass din data
saka a idonta wajan taimaka mata gani sosai,
Meyesa baki fada min sune suka zoba?ta fada tana kallon safna,
Wllhy ranki ya dade ina kokarin gaya miki sai kikace na sallamesu"cewar safna.
Kina da hayaniya safna! afiya ta fada kamar ba itta ce ta tambayeta yanzu ba.
Yi hakuri ranki ya dade,amma wllhy bada wata manufah nayi hakan ba, saboda na dauka inkin fita kingansu" zaki fasa tafiyan ki saurare su ne safna ta sake fadi.
Suna waje lokacin ?"eh suna zaune a office dina safna ta bata amsa"
Banga kowa....bata karasa maganar ba ta koma ta zauna dan wannan maganar da ta danyi kanta har ya fara tsara mata",
Go afiya ta fada tana kallon safna,dan gani take hadda lefinta hakan ta faru,
Sorry madam safna ta fada cikin sanyin murya hade da barin office din.
Kanta ta rike da dayan hannunta"daya kuma ta sa ta jawo wani kwalin da take ajiye magungunan a ciki,
Kama daga maganin ciwon siki ciwon mara kai gasu nan dai rututu, a ciki,
Hannunta data rike kanta dashi ta hada da dayan hannun ta shiga duba paracetamol, tana ganinshi ta dauka ta balla guda biyu ta jefa a baki hade da dauko ruwan jarkan dake saman table,ta balla murfin ta kafa bakinta tasha,sai data tabbatar maganin ya tafi sannu ta tire ruwan daga bakinta hade da rufe jarkan ruwan ta ajiye a inda ta dauka,
Laptop din gabanta ta bude ,bayan ta kunna ne ta shiga dube dube wani abu,dan ko ni kaina ma bansan mai ta dubawa a ciki ba,
Typing ta farayi a cikin laptop din,sosai ta maida hankali wajan typing din,kana gani zaka fahimci magana takeyi da wani kuma daga gani maganar na da mahimmanci saboda yanda ta nitsu sosai,ta maida hankali akai.
Ganin rubutun daya mata ne ya sata shiga cikin tashin hankali,
Wayarta ta dauka tayi dialing wata number,da kallo daya zakawa number din ka fahimci bata Nigeria bane.
Ba'a dauka ba sai ma
Kiran da tagani ana mata daga cikin laptop din dake gabanta" cikin mamaki take kallon kiran dan tunda take dashi bai taba kiranta" video call ba,dan haka kasa dauka tayi har kiran ta kashe,
Ba'a kara kira ba dan haka rufe laptop din tayi,tare tun da ajiye wayar dake hannunta" jingina kanta da jikin kujerar tayi,hade lumshe ido,tana juyi akan kujerar a hankali.
Tunani takeyi mai zai mata yake kiranta vidéo call,shi da yakeso ya taimakesu" wajan bungasar kasuwancin su mai Kuma nayin vidéo call?"
Tambayoyin data shiga yiwa kanta Kenan amma babu mai ansa mata su"
Ni kuma nace ..in banda abunki afiya kema kince zai taimakeki wajan bungasar kasuwancin ki, toh in baki dauki video call da yake miki ba ta yaya zai ganeki har ya taimakeki,bayan bai taba ganinki ba?"
Waya telephone dake gabanta ne ta dauka ta dannawa safna kira,
Tana dagawa tace mata ta sameta a office,toh safna ta fada tana mikewa,
Kafin ta ajiye wayar data kirata dashi safna ta shigo cikin office din,
Gani ranki ya dade,cewar safna, ohhh good sau nawa safna?"afiya ta fada tana kallon safna dake kallonta itta ma,
Dan har ga allah yau kam bata gane mai take nufi ma"
Duk da kuwa tafi sauran ma aikatan gane maganar afiya amma yau kam bata fahimci komai ba itta ma.
Fahimtar da afiya da tayi na cewa safna bata gane mai take nufi ba? ya sata fadin...afiya! ko aunty afiya!!
Murmuchi safna tayi,dan sai yanzu ta fahimci inda maganar afiya ta dosa"dan haka tace toh aunty insha allah.
Kowa ya jirani a dakin taro a kwai maganar da zamu tattauna anjima ki gayawa kowa,kai safna ta geda,hade da fadin..toh aunty zan gaya musu"
Da hannu tayi mata alamun zata iya tafiya,
Bayan fitar safna ta kira kowa a woyoyin office dinsu ta fada musu akwai taro anjima,
*Bayan awa biyu*
Ma aikane zaune a cikin dakin taron,
Daki ne babba sosai,dauke yake da wani doguwar teburi,sai kujeru dake zagaye a wajan,ko wana kujera da a bun magana a gabanshi,
Kus_kus sukeyi a saka ninsu,suna tambayar juna a bunda yasa ogan nasu ta tarasu a wannn lokaci,dan in har za'ayi taro?toh kamar gobe za'ayi ake gaya musu,
Allah dai yasa lfy cewa daya daga cikinsu,amin dai bello,wanda yake zaune kusa da shi ya amsa"
Takun ta kallaman da sukaji ne?ya tabbatar musu" da isowarta wajan,
Shiru dakin ya dauka kamar ba'a sune sukeyin magana dazu ba,sai sautin takalman tane kawai kakeji...ji kake kwas. kwas.kwas.kwas.
Kara sowa tayi ta zauna a kujeran da aka tanada domin oga,sai ya kasance tana fuskantar" kowa.,
Kallon su ta shigayi daya bayan daya,inda duk sanda idanunta ya sauka a kansu suke saukar da kai"kasa"sakama kon kwarjinin da take musu"
Dan su wani lokaci har mamakin abun sukeyi ma, saboda ko namiji albarka.
Sai da tagama kallonsu" saf ta tabbata kowa ya hallara a wajan sannun ta fara magana kamar haka....nasan bakusan da lilin dayasa na taraku a nan ba ?"
Bazan iya sayawa nayi muku dogon bayani ba,amma ga seketariya ta nan zata muku bayanin komai, tana kaiwa nan ta tura wata ta karda a gaban seketariya,tare da fadin...duk a bunda zan fada na ciki...
"Ku kiyaye aikin ku"
Tana kaiwa nan ta mike ta bar dakin taron, ta koma office dinta"
Bayan fitarta,safna ta soma karanta musu"a bundake rubuce a takardan kamar haka...ba kwa mai da hankali a kan aikinku, saboda wani babban mutun ya nemi taimaka mana wajan kara bungasar kanfanin nan amma kun rutsa komai,dan haka ku kiyaye gaba,ku mai da hankalin sosai wajan yin aiki, safna na gama karan tawa ta dago tana kallonsu,
Yanzu dan allah duk aikin da mukeyi ba dare? ba rana? amma take cewa mu mai da hankali a kan aikin mu wana irin maida hankali takeso muyi bayan wanda mukeyi ko so take mu dawo office din mu dinga kwana? hafsat ta fada cikin jin takaicin Maganar.
Wllhy lefin tane hafsat saboda jiya da bakin nan sukazo naje na gaya mata cewa tayi bazata iya ganin su ba,shine yanzu zatace mune bamuwa maida hankali itta ma safna ta fada,
A haka dai kowa yake tofah albarkacin bakinsa"da sukaga maganar ba mai karewa bane kowa ya tattara ya koma office dinshi..
*Bayan kwana biyu*
"Bayan ta tashi daga wajan aiki"
Tuki take cikin nitsuwa da kwarewa,ta hango wasu motoci na alfarma kusan guda shiga suka zo suka wuceta "a guje,
Mutane sai basu hanya sukayi,wani irin haushi da takaici ne ya cikata yanda suka wuce kamar zasu bike motarta"
Gefen titin ta gangaro tayi parking,tana tunani ko wa suka dauko cikin motar da bazasuyi komai a hankali ba,
Bata gama tunanin juci ba, taji wasu suna fadin .. Habib Muhammad Habib kenan,saurayin ya fada wai kana nufin shine dan Muhammad Habib?"watoh shogaban man petir,gaba dayan Nigeria!
Kwarai kuwa,cewar dayan,tun lokacin da suka fara magana idanunta suke a lumshe duk a bunda suke fada a cikin kunnuwanta"yake shiga,bata jira sun karasa maganar tasu ba tayiwa motarta ki ta wuce gida.
*Washe gari*
Bayan tagama motsa jaki,
Tafiya take tana duba a gogon dake hannunta"taga takwas har tayi,kasan cewa yau ta dan makara,dan haka ta fara tafiya da sauri da sauri da niyar barin wajan,sai taji ta bugi wani abu.
Washhhh taji an fada a lokacin da ta dago da niyar ganin a bunda ta buga din,idonta ne ya sauka a kan wani balarabe dake gabanta, shima a lokacin ne ya dago dan ganin waye ya buge mai goshi, sai idanunsa ya sauka akan nata "wani irin harbawa zuciyoyinsu"yayi a lokacin da idanunsu suka sarke cikin na juna,
Zuciyoyinsu ne ya hau bugawa da karfi,
A takaice dai sai da sukayi kusan bintuna biyar suna kallon juna sai daga baya afiya ta janye nata idon,tana fadin sarki ya tabbata ga wannan halintan dake gabana,
Abunda bata sani ba shine zancen zuci yafito fili,
Ji tayi yace...mai kikace?"dagowa tayi cikin mamakin daya kasa boyuwa a kan fuskarta"tana fadin dama kana jin Hausa ?"murmuchin gefen baki yayi daya kara saka afiya suman tsaye,dan ba karamin tafiyar da imaninta yayi ma,
Agefe guda kuma mamaki take sosai yanda balaraben dake gabanta ya iya hausa,
Yen yasansa ya hada biyu ya hada waje guda ya kyess tasu"ji kake kyes kyess haka sautin yake badawa,a take afiya ta dawo jikin hayya jinta"tare da fadin sorry!tana kaiwa nan ta fara takawa da sauri da sauri tana kokarin barin wajan....

*Duhu da haske typing* ...✍️
Page 7&8
Free book
Bismillahi rahmani rahim
******Bin mayanta yayi da kallo,har ta bacewa ganinsa"taba inda ta bugeshi"yayi yana yatsine fuska,dan sai yanzu yaji zafi a wajan dan har wajan ya dan kumbura,abunka da wanda bai saba da wahala ba ?"
Fasa motsa ciki da yayi niyaryi yayi,dama bai saba motsawa a waje ba,yau din ma bai san ta ya akayi yaji yana son motsa jikin a waje ba.
Juyowa yayi shima ya bar wajan,
Son ! wai sau nawa zan gaya maka bata son ka dinga fita ba tare yen kariya ba ?"wani mutun ya fada... sorry Dad! Habib ya fada yana dan kwantar da kansa"akan cinyar mutumin daya kirashi" da Dad !shafa kansa"mutumin ya shigayi shi kuma yayi lamo kamar karamin yaro,
Hummm dan Daddy yazo?sukaji an fada a bayansu"kallon inda sukaji anyi maganar Alhaji Muhammad Habib yayi,matarsa hajiya Maimuna yagani take saukowa,farace amma ba sosai ba,tana da kyau dai dai misali,sanye take da wani laces mai matsifar kyau da sada,tun daga wuyanta har izuwa hannayenta da kuma kunnenta"duk gwala gwalai ne,
Cikin yanga da kwarkwasa ta karasa saukowa,tafiya take tana karye kugu,har ta karasa gaban mijin nata"
Tun da ta fara wannan abun alhaji Muhammad Habib ya bude baki da hanci yana kallon ta, lokaci daya ya shiga matse kafafu kamar mai shirin yin fitsari, Habib na ganin haka ya mike daga kwancen da yakeyi ya zauna,
Hajiya Maimuna kuwa tana ganin alhaji ya fara mutsu mutsu,ta kalli wajan,da yake matsewa,
Ai kuwa abun kamar zai fita daga cikin wango,wani dariya ne ya kubce mata,ba shiri ta farayi babu ko kakkautawa,
Kallon inda take kallon Habib yayi,lokaci daya kuma ya dauke kai,hade da mikewa,
Cikin haushi da takaici ya fita ya bar palon ya wuce bangarensa"
Shifah da lilin dayasa baya son zuwa Nigeria kenan,saboda da zaran tagansu tare toh sai tayi duk yanda zatayi wajan gani ya bar wajan.
Palon nashi ya shiga,
Woww na furta a lokacin da idanuna ya sauka cikin palon,dan ba karamin kyau yayi ba,kallo daya zakawa palon ka fahimci ba makamin kudi aka kashe wajan kawatar da palon ba,
Daki ya wuce,nan ma dai ya hadu dan zan iya ce muku ma yafi palon haduwa,a zuciyata kuwa fadi nake daga gani Habib dan gata ne,gaba da baya.
Kayan jikinsa ya rage ya fada toilet,
Sai daya dau kusan mintuna sha biyar sannun ya fito daure da tawal a gukunshi"sai wani dan karamin tawal din da yake goge sumar kansa daya cika da gashi,
Gaban mirror ya je ya saya,ya shiga kallon kansa"Habib na da kyau sosai,
Dan kallo daya zaka mai ka fahimci ya hada jini da larabawa,
Yana da haske sosai,yana da godon fuska da kuma godon hanci da har yaso yayi masa" yawa saboda tsawo,
Lebensa jàne,fatar jikinsa kuwa kamar ka taba jini ya fito saboda haske da kuma hutun daya rasa fatar jikin nashi"
Yana da sumar kai sosai, sakamakon kyaran da yake samune ya sa gashin kara baki da kuma laushi
Nakurar busar da kai ya dauka ya shiga busar da kan nashi, saboda in yace zai bari ya bushe da kanshi zai iyayin awa daya,
Yana gama bushe wa ya dauki man da yake shafawa akan ya shiga shafawa,
Sai daya gama gyara gashi saf sannun ya shiga shafa man a jikinsa,
Bayan ya kammala duk a bunda ya kamata ne ya wuce gaban wardrobe dinshi,kasan cewa murfin wardrobe din glass ne shiyasa ya jashi a hankali ya budeshi,kananun kaya ya dauka riga da wango ya shiga shiryawa.
*Bayan awa daya*
Karan shiga motocin cikin kanfanin ne yasa jama an dake harabar kanfanin juyowa,suka zubawa motocin idanu har suka karasa cikin kanfanin sukayi parking,
Motoci ne!guda uku amma motan dake sakiya yafi sauran guda biyun tsata da haduwa,
Fitowa sukayi daga cikin motar,sanye suke da bakaken kote,iri daya, kallo daya zaka musu" ka fahimci cewa sudin masu"tsaro ne ? karasa gaban wannan motar dake sakiyarsu"sukayi daya daga cikin su ne ya bude bayan motar,
A hankali ya zira fararen kafafuwansa"dake sanye da wani kubashu mai shegen tsada da sheeki,sauke kafafuwan yayi kasa,"baki sake samarin dake wajen suke kallon wajan,suna jiran suga ma mallakin kafar,dan sun tabbata ko wayeshi"?
Babban mutun ne ?"
Kafin su gama tunaninsu"sukaga ya karasa saukowa daga cikin motar,
Suna ganin ya fito mai zasu fada... in ba masha allah ba,
Yana sanye da fararen kote da tishet,sai bakin wando,sai farin glass dake manne a idanunsa" "taku ya fara a hankali cikin kasaita, kamar baya son taka kasar ya nufi cikin kanfanin nasu"samarin suka bishi da kallo har ya bace musu"
Da suka zo bakin kofar shigane ya dagawa masu"tsaronshi" hannu alamu su saya daga nan,dan haka suka bi umarninshi suka saya,
Shikuma ya karasa shiga ciki,
Zo ?ya fada yana kallon wani sauranin da ya shigo yanzu,
Cikin mamaki saurayin yake kallonsa yana so ya gasgata da abunda kunnuwansa suka jiyo masa,
In har da gaskene abunda kunnuwansa yajiye masa toh hausa yaji wannan balaraben yayi?,
Fahimtar hakan da Habib yayi ne yasa shi fadin..eh cewa nayi kazo!
Saurayin na ganin haka kuwa ya karasa da sauri yana fadin gani ranka ya dade?
Ina ne offishin shogabanku?nan daka shiga ranka ya dade seketariyarta na ciki,
Saurayin ya fada yana nunawa Habib wani bangaren da yafi ko ina kyau a kanfanin,
Kai kawai Habib ya geda ya nufi wajan da saurayin ya nuna masa"
Safna na zaune taga balarabe a gabanta"jiki na rawa,ta shiga fadin sannu dazuwa yellabai kana bukatar wani abu ne ?mai kakeso ?"haka tayi mai tambayar duka a lokaci daya,
Murmuchi Habib ya danyi daya sa safna kiricewa,
Ina shogabanki?"ya fada da hausa yana kallon safna,
Zaro ido waje safna tayi tana kallon shi"dan tayi mamaki sosai da taji yayi mata magana da hausa,
Kasan cewa itta da turanci tayi mai magana,
Magana nake kin min shiru? Habib ya sake fadi cikin hade fuska,sai kace ba shine yayi murmushi a yanzu ba?dan yanzu kam abun ya soma bashi haushi"Shiyasa kwata kwata bayanson zuwa Nigeria,
Ga office din nata acan bari na gaya mata,
Safna ta fada tana dauko wayan téléphone dake gabanta,
Kafin kace me Habib har yayi gaba,baki bude ta shiga kallonsa"hade da dafe irji,
Shikenan yau kam zan rasa aikina ta fana hade da biyo bayanshi"tana fadin dan allah yallabai karka shiga ka bari na fada mata tukun zan iya rasa aiki na..?amma ina bai maji a bunda dake cewa ba ma,saboda ya riga da ya tura kofar office din ya shiga,ba tare daya saya ya nemi izinin shiga ba,
Juyowa yayi zai maida kofar ya rufe sai safna ta rike kofar hakan ne ya sashi sakin kofar ya shiga ciki.
A guje safna ta karasa ciki tana fadin...ranki ya dade kiyi hakuri nace ya ....safna bata karasa ba jin da tayi afiya na cewa....kaine ?"ta fada tana nunashi da yen yatsa,kece ?shima ya fada a yayinda idanunshi yayi tozari da kyakkyawar fuskarta"
Shiru safna tayi tana kallonsu"daga baya kuma sai ta fita hade da jà musu kofa,ta koma tata office din.
Amma meye kawoka anan ?"afiya ta fada,
Ai ke zan tambaya me kike anan ?shima habib ya bata amsa"
Wani irin murmuchi afiya tayi da daya sa dimpil dinta"lotsawa,
Sai daga baya kuma ta bude baki kamar batason yin magana tana fadin... taya zakaxo office dina zaka dinga tambayata meye kawoni nan, bayan kuma nan kanfaninane !ta bashi amsa"daga visani ta koma ta zauna,
"Bismillahi ta fada tana kallon Habib daya kafeta da idanu,
Bashi da zabin daya zuce zama din,dan shi kansa ya gaji da tsayuwan dan kafafuwansa har ya tsoma mai ciwo,dan haka kujeran ya jà ya zauna.
Sai data bari ya zauna sannun ta soma yin magana...ina jinka meke tafe dakai ?"
Memakon ya bata amsa"saima tambayarta da yayi shima...nifah na rasa gane komai?
Wai dama dake nake magana ?"
Ya fada yana kallon afiya,
Itta ma afiya bata amsa mai ba,sai ma kara masa tambaya da tayi...kaine H.M.H?"eh nine kina nufin kema kece afiya abubakar? eh nice,
Ikon Allah ya fada yana kallon ta,"amma banji labarin zuwanka ba.ta fada tana kallonsa"
Wllhy zuwan nawa ne ya taso,ga kuma wulakancin da kikayiwa mutanena rannan,dama so nake nazo na ganki ido da ido ki fada min dalilin dayasa kikayi musu"cin fuska ya fada yana hade rai kamar ba shine dazu yayi magana cikin sakin fuska ba.....

*Duhu da haske typing...✍️*
Page 11&12
Free book
Bismillahi rahmani rahim
********"Itta kam bata saya ta sauraranshi ba tayiwa motarta key ta bar wajan"yana nan tsaye sai juya katin dake a hannunshi"yake,yanayi yana murmushi,ya kai kusan minti biyar a haka sai daga baya ya karasa wajan nasa motar,ya bude ya saka kayan daya siya a dayan sit din,sannun ya zaga ta mazaunin drive ya shiga ya tada motar ya bar wajan,
Driving yake yanayi yana ci gaba da murmushin da yakeyi,can kasan makoshi ya furta...insha allah Nuriiii" ke tawace,"
Bazan iya komawa gobe"ba har sai kin amince dani,ya kara fadi.
*Bayan ya koma gida da daddare*
Sallama yaji tayi daga cikin wayar ya amsa gaisawa sukayi,amma sam bata gane waye ba"dan itta har tama manta da wani mai suna Muhammad !saboda itta kwanta kwata bata damu da samari ba,
Waye ta fada,shiru Muhammad yayi a zuciyarsa kuwa cewa yake karfah ace har ta manta dani ?"
A fili kuma cewa yayi Muhammad ne" Nuria !
Wana Muhammad ta tambaya,jikinsa ne yayi sanyi,amma ya dage yaci gaba da fadi...wanda kuka hadu a supermarket dazu kika bawa kati,ohhhh sorry wllhy na manta,ba komai ya gida lfy lau ta amsa"
Shiru ya biyo baya,da Muhammad yaga dai ba magana zatayi ba sai kawai yayi mata sallama, thanks ta fada tana kashe wayan,
Bin wayan yayi da kallo,ya zame ya kwanta akan gadon,
*Bayan kwana uku*
Kullun Muhammad sai ya kira Nuria sau uku zuwa sau biyar a rana tun bata sauraranshi har ta fara sauraranshi"saboda da farko wayan da yake mata gani take takura ce kawai,sai daga baya taga yanda ya damu da itta sosai kuma duk da bata kulashi amma bai taba fushi dai dai da rana daya yace bazai kara kira ta ba,
Kunsan dama hausawa sukace zuciya yana son mai kyautata basa"toh haka ce ta kasance a wajan Nuria ma, saboda irin damuwan da Muhammad yakeyi akanta ne ya sata fara sauraranshi"har ma su dauki lokaci sosai suna hira a waya,
Sakamakon wannan abun ne yasa itta ma ta fara jin soyayyar Muhammad din na shiga cikin zuciyarta"
Bangaren Muhammad kuwa ba karamin farinciki hakan ya sashi ba,
Saboda bashi da burin daya muce yaga ya mallaki Nuria,
Abbansa ya sha kiransa ya tambayeshi da lilin dayasa har yanzu bai dawo ba?"amma kullun amsar da zai bashi bai wuce...bangama aikin daya kaini ba abba,
Da abba ya gaji da jin magana daya kullun,ga kuma kwanakin daya bashi na nemo matar aure ta kusa cika,cemai yayi kar ya kuskura ya kai wannan kwanakin bai dawo ba,
Dariya Muhammad ya danyi, cikin kwarin guiwa ya fara magana kamar haka...karka damu abba insha allah na samu matar aure,kai dai kayi mun addu'a, Allah yasa ta amince,
Abba zai tambaya Muhammad yayi saurin fadin karka damu abba kai dai kayi min addu'a kawai, insha allah ina dawowa zan fada maka komai,da haka dai ya samu Abba ya dena takura masa"da kira,
*Bayan kwana biyu*
Ganin yanda Shakuwarasu"sai kara gaba yakeyi ne yasa Muhammad fadawa Nuria abundake cikin zuciyarsa game da itta,
Bai wani sha wahala ba ta amince"
Amma da taji garin da yake sai jikinta yayi sanyi, tace daker in iyayenta zasu yedda tayi nisa dasu"jin wannan Maganar ne yasa duk kwarin guiwa da Muhammad yake dashi karyewa,
Ganin yanda jikin Muhammad yayi sanyi ne yasa Nuria kwantar masa"da hankali,ta hanyar cewa... insha allah Muhammad in har Allah ya rubuta ni matarka ce"toh babu yanda zasu iya sai nayi aure a Nigeria !in har kaga bamuyi aure ba toh dama can Allah bai rubuta zamu zama mata da miji ba,
Da haka dai Nuria ta samu ta kwantarwa da Muhammad hankali,
Bayan yaji duk a bunda ta fada,cewa yayi insha allah ke tawace Nuria,
Murmuchi kawai Nuria tayi,tana kashe wayan,
Bayan Nuria ta sanar da iyayen ta"cewa sukayi saidai in dawo nan zaiyi da zama,amma su baza su taba yedda su barta ta tafi wata kasa ba, bayan kuma itta kadai suke dashi,
Amma takirashi yazo"
Kinsan Muhammad Nuria tayi ta fada mai iyayenta suna son ganinsa,da toh ya amsa"
Zaune yake a gaban iyayen Nuria,wacca take kirasu ummi! da Abie!
Shiru yayi bayan ya gaishesu"yana jiran yaji abunda zasuce akan aurensa"da Nuria,
Addu'a kawai yakeyi a cikin zuciyarsa Allah yasa su "amince"
Gyaran murya balaraben mutumin yayi,ya fara magana kamar haka... habibti ta fada min komai game da soyayyarku,
Kuma tun da naganka naji ka kwanta min arai,har naji zan iya baka yata ka aura,
Amma ina so ka sani cewa itta kadai muka mallaka a matsayin yah,babu a bunda Nuria ta rasa a rayuwarta,komai na rayuwa ta samu,kama daga ilimin addini har dana zamani duk, Alhamdulillah,
Badan komai muka barta take aiki ba sai dan ra'ayinta ne,
Saboda duk abunda takeso muma shi mukeso,
Dan haka in har da gaske kake son Nuria toh cedai ka dawo nan da zama,saboda bazamu iyayin nisa da yer mu ba,mutumin ya karashe maganar da iya gaskiyarsa,
Tunda mutumin ya fara Magana kan Muhammad yake kasa"sai da yaji maganar mutumin na karshe ne ya sa shi dagowa dan tabbatar da a bunda kunnuwansa suka jiyo masa"
Kai mutumin ya geda mai alamar haka ne"
Cikin sanyin jiki ya fara magana shima,toh nagode Abie kuma insha allah zanyi kamar yanda kace,zan koma Nigeria gobe,saboda dama a bunda ya seda ni kenan ?"
Insha allah duk yanda mukayi da abba na zakuji,yana kaiwa nan ya mike ya bar palon.
*Da daddare*
Habibi kana tunani iyayenka zasu amince ka dawo nan ?"Nuria ta tambayi Muhammad,wllhy in nace zasu amince nayi karya"in kuma nace bazasu amince ba "shima nayi karya,amma dai insha allah komai zaixo da sauki in allah ya yerda?"allah ya yerda"Ameen"Muhammaya amsa"
Washe gari har airport Nuria tazo ta kai Muhammad,cikin so da kauna" suka shigayin sallama, Muhammad na dago mata"hannu"kowacce na kwalla, addu'a yakeyi Allah yasa ba yau ne ganinsu ta karshe ba, Allah kuma yasa iyayensa"ko iyayenta su amince ya zo nan ya aure ta"duk da kuwa yasan da wuya iyayensa su amince,da dawowarshi nan,saboda kasuwancinsa"
A haka dai yake ta addu'a cikin ranshi har ya shiga jirgi ya dena ganin ta"
Jiki a sanyaye itta ma Nuria ta juya ta hau motarta ta wuce gida,
*Kanon damo Nigeria*
Yana sauka ya samu drive na jiranshi"dan haka fadowa kawai yayi cikin mota suka wuce gida,
Da daddare bayan sun gama dinner ne, suka tashi daga dinning din suka koma palo,
Yauwa Muhammad kai nake sauraro kace in ka dawo zaka fadamin komai"gyara zama Muhammad yayi akan carpet din,sannun ya kwashe komai,tun daga haduwar sa"da Nuria har yanda sukayi da mahaifin Nuria har izuwa yanzu da yake gabansu"
Whattt Abba ya fadi a lokacin da yaji maganar Muhammad ta karshe,
Gaskiya hakan bazai taba yuwa ba kasani Muhammad !ta yayama zasuce sedai ka dawo Dubaï !da zama wai saboda kawai kana son yer su"
Ka tuna fah Muhammad kai kadai namiji,ba wai fata nake ba,amma yanzu misali idan na fadi na mutu wa zai sayawa kannanka kana can?"toh kasani hakan bazai taba yuwa ba har abadan, Abba na kaiwa nan ya mike a fusace ya wuce dakinsa"Maama ma mikewa tayi ba tare da tace komai ba, tabi bayan mijinta"
Jiki a sanyaye Muhammad ya mike ya koma part dinsa"
Tabbas hakan bazai taba yuwa ba,duk da kuwa ina son Nuria amma ya zama dole na hakura da itta"in har bazasu amince na aurota ta dawo Nigeria ba"
Waya ya dauka ya kira Nuria ya fada mata duk yanda sukayi da iyayensa,ya kuma kara da cewa...ki sani fah Nuria na mijine yake auren mace ba macece take auren na miji ba"dan haka in har da gaske kike sona toh ki lallaba iyayenki,in kuma sunki amincewa dole mu hakura da juna,yana kaiwa nan ya kashe kiran.
Nuria ce zaune cikin kuka take fada musu yanda sukayi da Muhammad,ta kara da cewa in har basu yedda anyi auren nan ba mutuwa za tayi,
*Bayan sati daya*
Wasa wasa Muhammad ya kwanta rashin lfy,da aka kaishi a sibiti bayan gwaje gwajen da likitocin sukayi ne suka tabbatar musu da cewa Muhammad ya kamu da ciwon zuciya kuma sunyi bincike ba komai ne ya hadda sa masa ciwon ba sai dan akwai a bunda yake so da ba'ayi masa ba,dan haka in har suna son dansu ya rayu toh sai sunyi gaggawar yi mai a bunda yakeso,
Ba karamin tashin hankali su abba suka shiga ba, lokacin da sukaji bayanen likita,
Zaune yake dashi da wani amininsa, bayan yagama bashi lbrn komai,
Shiru Alhaji musa yayi sai can kuma ya gyara zama hade dayin murmuchi,dama damar da yake nema kenan kuma ya samu, dan haka ya fara magana kamar haka... alhaji Habib ina da maganin damuwarka amma bansan in zaka amince ba?"
Cikin zumudi alhaji Habib yace ka fada min zan amince in dai dana zai samu lfy,
Kara gyara zama alhaji musa yayi yaci gaba da magana,
Dama akwai yer autata da ta rege batayi aure ba,dan haka mai zai hana ka amince masa da auren Nuria take kowa din,kaga in yaso idan an tashi auren sai a hada masa da Maimuna,in yaso itta Maimuna ta zauna anan itta kuma wancan ta zauna a kasarsu,tunda haka sukeso,
Amma fah Muhammad bazai koma can ba cedai ya dinga kai mata ziyara lokaci zuwa lokaci, alhaji musa ya karashe maganar yana addu'a allah ya sa ya amince,
Wani irin murmuchi yaga Abba yayi, Yana fadin wllhy hakan ma yayi abokina, gaskiya nagode da wannan shawaran, murmuchi shima alhaji musa yayi yana mai jin dadin amincewa da alhaji Habib yayi cikin sauki,
Fadawa Muhammad Alhaji Habib yayi da cewa ya amince da auren amma hakan ba yana nufin ya janye maganar shi, akan komawar shi can ba?"a'a bai janye ba maganar tana nan,
Ya kara da cewa in antashi auren harda Maimuna zai hada ya aura,itta ta zauna anan wancan kuma ta zauna acan,in yaso sai ya dinga kai mata ziyara,
Kamar Muhammad bazai amince da auran Maimuna ba,sai Kuma daya tuna shi kadai hanyar da zai sa ya mallakar Nuria sai ya mallaki Nuria yasa shi amincewa,
Yana kuma addu'a Allah yasa Nuria ma ta amince,
Karban number Nuria abba yayi ya kirasu da kanshi,amma akayi rashin sa'a ba Nuria ce ta daga wayan ba,duk da kuwa dama can ba da itta yakeson yin magana ba,
Bayan ya gaisa da mahaifin Nuria né ya fada musa waye shi"ya kuma kara da cewa Muhammad ne bashi da lfy tun lokacin dana hanashi dawowa Dubaï da zama ya auri yer ku, nan ne suma suka fada masa suma suna a sibiti tun ranar da Muhammad ya fada musu bazai iya zuwa nan ya aureta ba,
Ikon allah abba ya fada ya Kuma kara kirmama soyayyar Nuria da dansa,
"Gaskiya suna son juna"
Shawaran daya yanke ne ya gaya masa,abun mamaki sai gashi cikin sauki Abie Nuria ya amince,da abba yaga ya amince ne yace insha allah zan samu lokaci nazo,toh Abie ya fada,sannun sukayi "sallama"
Sannun ya kashe waya da gudu Abie ya nufi dakin da aka kwantar da Nuria domin yi mata albishir......
*Sakeena ismail Cameroon ce*✍️
07049322735
[6/21, 15:24] Mom Muwadda🥰: 🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑
*DUHU DA HASKE*
*By*
*Sakeena ismail Cameroon*
*(Mom muwadda)*
🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼
*Marubuciyar*
*Bazan zauna da kishiya ba*
*Mijin attajira*
*Mugun uba*
*Duhu da haske typing*...✍️
Page 13&14
Free book
Bismillahi rahmani rahim
*******Ba karamin farinciki Nuria tayi ba"a lokacin da mahaifinta ya gaya mata iyayen Muhammad sun amince da auren su,amma da taji wai ba itta kadai zai aura ba,ba kuma dawowa zaiyi Dubaï da zama ba,yasa farincikin fuskarta daukewa,
Kwantar mata da hankali Abie yayi ta hanyar cewa..haba habibti ke da ba kasa daya kuke ba ?"bafah ganinta zakiyi ba"sedai wata rana idan kin kai musu ziyara kawai Abie ya fadi,
Haba Abie kaima fah kace"wata rana zan kai musu ziyara kaga kuwa akwai ranar da zamu hadu kenan ta fada hawaye na taruwa a cikin idanunta,
Haba habibti kifah sani ko kin amince ko karki amince bazasu taba janyewa daga aura masa yer Nigeria ba?"
Kinga kuwa in baki amince ba,auren wancan zaiyi ya kyaleki kinga kin resa shi har abadan dan haka gwara ma ki amince"
Shikenan Abie na amince ta fada tana share kwallan daya zubo mata"
Yauwa koke fah habibtina,ki kwantar da hankalinki kinga kina tare damu,
Insha allah mahaifin Muhammad din yace zaixo kwanan nan,
Da haka dai aka samu aka shawo kan komai,
*Bayan kwana uku*
Abba yaje yayi wa kawunshi daya rege mai daya filo bayani akan auren,anan ne kawu bala ya bawa abba shawara tunda abun yazo da haka ya fara zuwa can Dubaï din yayi komai in yaso shi da Muhammad kuma sai su saya anan in yaso idan an daura sai ya tafi can din,in yaso idan ya dawo sai itta ma Maimuna ta tare,tunda itta kasarsu daya,kuma anan yake kasuwancin sa,kullun suna tare,
Kamar yanda kawu ya fada hakan ce ta kasance,dan abba ya dafi can su kuma sun tsaya anan,
Rana daya aka daura auren Nuria da Maimuna,amma na Nuria aka fara daurawa dan haka itta ce uwar gida,itta kuma Maimuna itta ce amarya,dan haka sai Muhammad ya fara tarewa da Nuria sannun zai tare da Maimuna,
Ranar da aka daura aure"da dengin Maimuna suka ce suna jira su kai amarya da yamma abban Maimuna ne yayi musu bayanin cewa ba yau ne amarya Maimuna zata tare ba,ba kuma itta kadai aka daurawa Muhammad akwai wata a kasar Dubaï kuma da itta aka faka daurawa,kuma nata aka fara daurawa Kafin a daura na Maimuna! dan haka sai ya fara zuwa wajan ta ya dawo tukun in ya dawo sai itta ma ta tare,
Magana kawayen Maimuna da kuma yen biki suka din gayi,wai ta yaya yana gari aka daura musu aure da Maimuna amma zai sallake ya tafi can wata kasa,
Maimuna dai bata damu ba, dan tasan Muhammad yafi zama a Nigeria"kafin ma yaje Dubaï sai an dau lokaci,
Dan haka zatayi iya bakin kokarinta na ganin cewa bai koma Dubaï da wuri ba,
Da kawayenta sukaga bata damu ba, shine suka tambayeta dalilin rashin damuwar tata,da tayi musu bayani daya daga cikinsu"cewa tayi shegiyar kawata haba dama nasan ruwa bata tsamin banza, shiyasa kika barmu muke ta haukar mu _mu kadai,
Da haka dai suka karasa wunin nasu da daddare kowa ya watse sai yen uwanta da suka zo daga nisa kadai suka rege,
*Washe gari*
Wajan karfe goma jirgin su Muhammad ya daga zuwa kasar Dubaï,
Sanda ya shiga jirgi gani yake yau jirgin baya sauri dan so yake kawai ya ganshi a gaban sahibarsa,
Ni kuwa sakina nace haba angon Nuria wannan wana irin zumudi ne haka?"🤔🤩
*Bayan magriba*
Bayan ya sauka a hôtel din da abbansa yake?"
Dan babu yanda iyayen Nuria baduyi da shi ba akan ya sauka a gidansu"
Amma yaki da suka dame shi ma cewa yayi ya riga da ya bada kudin daki da haka dai suka kyaleshi amma badan suna so ba,
Wanka yayi yaci abinci,sai daya kammala komai abba ya zaunar dashi yayi masa nasiha sosai akan ya rike su amana ya kuma yi adalci,kar yaga yafi son Nuria yace zai dinga banban tasu a'a?dolen sane ya sauke nauyin Maimuna,kuma duk matansa ne"dan haka ya rike kowacce da amana,
Bayan yagama yi masa nasiha ne suka hau mota suka nufi hanyar gidan daya kama musu Kafin ya samu nasa gidan,
Tunda abun yazo a kurarran lokaci,
Maimuna ma dan yana da gidaje daya gina masa ne har guda uku acan shiyasa abun yazo da sauki,
Kasan cewa an rigada an kai Nuria dakinta,dan haka suna zuwa,suka tarar da itta da Abien ta itta ma bayan an gaisa ne"aka shiga yi musu nasiha sannun suka tashi suka tafi,
Ranar dai an sha soyayya sosai sai nan da nan Muhammad yake yi da Nuria,
*Bayan shekara uku*
Nuria ta haihu inda ta haifi danta na miji fari mai kyau gwanin ban sha'awa, kamarsa daya da mahaifinsa amma haske kam na mahaifiyarsa yayo, saboda shi Muhammad yana da haske amma ba sosai ba,dan kalarsa irin kalar nan ne da ake kira da wankan tarwada!
Yanzu haka watanshi sha tara a duniya,amma in kaga girman yaron sai ka dauka zaiyi shekara uku,
Muhammad duk karshen wata yana zuwa,duba su idan ya tashi komawa da kuke suke rabuwa da Habib wato sunan abba aka sa masa,
Badan yaron yayi kankanta ba da babu a bunda zai hanashi zuwa dashi Nigeria,
Nuria in ta dauki hutu a wajan aiki itta ma takanje musu lokaci zuwa lokaci,
Ranar farko da Maimuna ta fara ganin Nuria ba karamin kishi taji ba"
Dan Nuria tafi Maimuna kyau nisa ba kusa ba,
Duk da kuwa itta ma dai Maimuna bawai bata da kyau ba ne?"
Tana da kyau dai dai gwargwodo,kwai dai baza'a hada balarabiya da ba haushiya ba,
Abunda yafi konawa Maimuna rai shine bai wuce na yanda Muhammad yake nunawa Nuria da danta soyayya a gabanta ba ?"
Dan a bun yana kona mata rai sosai har gani take kamar cin fuskane"
*Bayan shekaru biyar*
A cikin shekaru biyar din nan a bubuwa deyewa sun faru a ciki kuwa har da rayuwar iyayen Muhammad da direvansu sunyi accident! Ta hanyarsu ta dawowa daga bikin da suka je daga kauye,wanda yer drevanshi ne take aure,shine drevan ya gaiya ce shi"daurin auren,kasan cewa Alhaji Habib mutumin kirki ne"shiyasa yace hajiya indo ta shirya suje tare suyi musu allah sanya alkhairi, shine dalilin su na zuwa,kauye,ashe basu sani ba mutuwa ne yake kiransu"dan daga abba har maama da drive ba wanda ya rayu daga cikinsu duk sun mutu,
Kannensa ma Allah ya basu sa'a basu je ba,da tuni abun har dasu zai faru,
Sunyi kuka sunyi kuka har sun gode Allah,
Dan kowa yaji mutuwar Alhaji habib Ibrahim, dan babu wanda bai sanshi a kasar ba"kasan cewar shi babban mutun,
Itta ma dai Maimuna tana da yara biyu a yanzu,aisha,da kuma mufeeda,itta Aisha sunan hajiya indo aka sa mata" wato mahaifiyarsu Muhammad mufeeda kuma sunan mahaifiyarsu Maimuna,
Mufeeda ce babba sai kuma Aisha,basu da tazara sosai,dan mufeeda tana da shekara daya aka haifi Aisha kasan cewa konika tayi,wai itta bata samu na miji ba,shiyasa tayi duk yanda zatayi ta kuma kara samun wani cikin Amma Still data tashi haihuwa macen ta kara haifa,abun ya batawa ran Maimuna sosai,
Ohhh ni sakina sai kace ke kike bada haihuwan ?kima godewa Allah tun da kinsa mu"
A haka dai rayuwa taci gaba da tafiya inda Habib yayi karatunsa a kasar Dubaï,dan acan yayi karatusa gaba daya,
Su kuma su aisha a nan kasar Nigeria!sukeyi,
Bayan sungama secondari aka kaisu kasar india,suka ci gaba da karatunsu acan,
Tun lokacin da habib yayi digirinsa na farko,mahaifinsa ya dorashi akan dayan kasuwancin sa,watoh kasuwanci da alhaji Habib ya bari seda a damfopi da leces,kasan cewa suna da babban kanfanin da suke da injin da sukeyin a tamfopin da leces din dashi,dan saboda tsabar kyau ma yasa kasashe daban daban suke zuwa suna tsarawa suje suciyar,
A yanzu haka suna da kanfani a Nigeria suna dashi a kasar Dubaï,kasan cewa Habib zamanshi yafi yawa a Dubaï ne yasa,aka samo mutanen da zai dinga kulan musu da kanfaninsu da yake nan Nigeria, shi kuma yana kula da wanda yake Dubaï,
Shi kuma mahaifinsa yana kula da gidajen man petir daya bude,da a yanzu haka gidajen man shi ya gaza ko ina"a Nigeria dalilin daya sa aka bashi shogaban man petir ta kasa gabaki daya kenan,
Dan yanzu bai ma fiya zama a kano ba"dan yafi zama a Abuja !
Kinji labarin Habib Muhammad Habib, kenan safna ta fada dana kallon afiya da tun da ta fara maganar take geda kai kamar kadangare har ta Kai aya,
*Cigaban labari*
Gaskiya babansa dan gatane dole shima ya zama dan gata"nagode sosai safna da labari,afiya ta fada tana duba agogon dake daure a hannunta"
Kai uhu tayi fah safna?"
Yanzu a bunda za'ayi kawai ki kulle office din ki sameni a mota sai na ajiyeki a gida tunda ni ma tafiya zanyi,
To aunty gani nan zuwa safna ta fada ,sannun ta fara hada kayanta,
Batafi mintuna biyar ba tagama hada su ta fito harabar kanfanin,ta nufi wajan ajiye motoci,tana zuwa ta shiga motar suka wuce"
Shiru babu mai magana har suka karasa kofar gidansu"safna,
Toh aunty nagode sosai,amma me zai hana mushiga tare ku gaisa da ammi na"a'a safna yamma tayi amma insha allah zanxo ranar lahadi tunda babu aiki sai mugaisa,toh aunty sai kinzo nagode sosai,safna ta fada tana shiga cikin gidansu ta karamin gete,hannu ta dagawa afiya a lokacin da take juye hancin motarta,
Bayan ya fita daga kanfanin ta"bai saya ko ina ba sai kanfanin su,ya jima a can dan sai daya shiga ko ina yaga ko ina normal sannun ya fito,
Sai daya saya yayi sallah sannun ya nemi restored mai kyau ya samu yaci a binci sannun ya wuce gida
Yana zuwa gida kai saye part dinsa ya wuce "yana zuwa ruwa ya wasa,bayan ya fito shiryawa yayi cikin farin tishet mai karamin hannu da kuma gajeran wando daya saya mai iya guiwa, sannun ya feshe cikinsa da turarukan masu sanyin kamshi,
Wayoyinsa ya dauka ya fita daga part din ,wata karamin kofa nagani ya shiga,
Sai kawai nagansa a cikin wani lambu mai masifar kyau,wajan da aka ajiye kujeru ya nufa ya zauna,
Hade da lumshe ido iskan dake wajan na ratsa shi,
Har kalla ya kai 2 second a haka sai daga fisani ya bude idanun nasa,wayoyinsa daya ajiye a kan teburin dake gabansa ne ya dauki daya daga ciki yayi dialing wata number,bugu biyu an dauka,
Sallama yaji anyi ya amsa sannun ya fara magana,ammi barka da wannan lokacin,ta daya bangaren aka amsa barka dai ibni!ya Nigeria yatsine fuska yayi kamar dama jira yake a sosa masa ida yake masa kai kayi dan haka a take ya somayin magana,wllhy ammi babu dadi kwata kwata,ni wllhy jibi ma zan dawo ya fada da harshen larabci, kuma dama tun dazu da harshen suke magana,.
Haba ibni! gidan mahifinka ne fah ka dena haka"
Haba ammi kefah naga alama ko kewata ma bakiya yi"saboda kwata kwata baki damu dana dawo ba,ya fada kamar zaiyi kuka,
Sorry ibni, ina missing dinka mana,kai dai kayi musu ko sati daya ne sai ka dawo,
Daker dai ya amince zaiyi sati daya,dan sai data hana da rarrashi sannun ya amince"Sallama sukayi ya kashe wayan........,
*Sakeena ismail Cameroon ce ✍️*

*Duhu da haske typing....✍️*
Page 15&16
Free book
Bismillahi rahmani rahim
*********"Sallama sukayi ya kashe wayan,maida wayan yayi ya ajiye akan teburin daya daukota dazu"gyara zamansa yayi ya jingana da jikin kujerar hade da lumshe ido,iskan dake kadawa a wajan na ratsashi a ko ina na cikin jikinshi,
Lokaci daya ya na yinshi ya fara sauyawa,a take kuwa ya mike da sauri sauri zuwa ciki,