← Book details Deen Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
CHAPTER 4 OF 4

Part din Aunty Raliya taqara komawa don achan ne kadai babu mutane ta bude falon da makullin hannunta tashiga ta rufo

Deen Part 1 Complete Hausa Novel · about 921 min read

Saida tafara gabatar da sallar xuhr don dama da alwalarta tafito wanka dazu

Sannan itama tafara shiri shap2 don kar Deen yazo bata gama ba


Angon bikin ne tasa Atamfa mai shegen kyau taji dinkin doguwar riga wanda yayi mata dass ajiki


Sannan ta zauna ta tsara makeup dinta daya dace sosai da fuskarta sannan tafara daurin dan kwali


Tana cikin daurin taji hayaniya daga waje sai kuma 6uda dake tashi a can cikin gidan


Murmushi zee tayi ta cigaba da daurinta acikin zuciyarta tana masu addu'ar zama lafiya.


Saida tagama ta tashi ta feffeshe jikinta da turare mai sanyin qamshi sannan ta yafa yalolon gyalenta stylishly a kafada


Linke kayan data cire tayi ta zuba a leda ta ajiye dakin yara sannan tafito da sauri don hayaniyar gidan sai qara sama sama take.


Rufe mata gidan tayi sannan tafito tana tafiyarta kamar yadda tasaba tana duba wayarta dake vibrating


"Hajiya Zainab!"

Taji an kira sunanta abaya


Juyowa tayi sai taga wani cousin dinta ne ke kiranta

Kauda kai tayi kawai bata amsa ba tana qoqarin sake dialing number Deen don shi yakira


"haba Aunty zee, meya kawo fada babu gaba? Magana fa nake maki"


"don kana min magana sai akace dole saina saurareka?" tafada tana qoqarin dialing number still tana cigaba da tafiya


Saurin shan gabanta yayi yana cewa
"tuba nake ranki ya dade, haba sisi nifa yayanki ne be kamata kina yarfani ba"

Wani kallon ta makamashi na wasa tace
"kaine yayan wa?"

"yayanki, idan kina gardama muje mu tambayi mummy"

"A'a daddy zamu tambaya ba mummy ba" tafada tana qara dialing number Deen don ba'a daga wancan kiran ba

"eh muje a tambayeshi daddyn, zakiji abinda zaice. Yarinya bar ganinki haka kin wani zabge to har naman sunanki Saida naci wlh da wayau na aka haifeki"

Sauke wayar tayi daga kunnenta ganin ba'a daga ba again sannan ta kalli cousin din nata tace
"inyee, congratulations tunda kaci naman sunana sai kaje ka rattaba Hakan cikin littafin tarihinka Saidai ko me zakayi bazai chanza ni yayarka bace, haka kowama kecewa" tafada tana mashi gwalo


"marassa hankali ba, don sun ganni da dan jiki? Su kalli fuskata dakyau zasu ga bata yau bace wlh, wadannan tamoji tamojin kadai ya ishesu amsa"

Dariya tayi tace
"ai alarrama anbar duba fuska yanzu, tsawo ake dubawa mallam don haka kazo mu taimaka mu sanmma tsawo" tafada tana mashi Dariya

"Kutt.. Amma fa kin qoshi saura ki dora da juice, wato ni kike ma shairin tsawo ko?" yafada cikin jin haushi

Juyawa tayi tafara tafiya tana cewa
"niba sharri nayimaka ba, Gaski... "


Maganarta ce ta maqale lokacin dasuka hada idanu dashi daga can jikin gini ya jingina da bango ya harde hannayenshi a qirji ya zubamata idanu... ✍️


Kuyi hqr jiya kunjini shiru, jiya bananan ne shiyasa ban samu zaman typing ba 👏


Ummin fasihu
8/2/21, 9:37 PM - Buhainat😝: *🙍🏻‍♂️DEEN 🙍🏻‍♂�*


*043*


*THE PROPOSAL*


Jitayi numfashinta yakusan daukewa saboda yadda ya tafi da imaninta


Sanye yake cikin farar shadda riga da wando irin na samarin nan wanda zakaga rigar da kadan ta wuce gwiwa, anyiwa wuyan rigar siririn aiki da dark blue din zare a wuya dakuma tsakankanin qirji sai kuma saman aljihu

Kanshi sanye da hular dara kalar aikin kayan sai takalmi farare sai usual agogonshi data sanshi dashi daure a hannunshi


Karo na farko data fara ganinshi da manyan kaya kenan sai taji dama su yake sawa don sosai yafito acikinsu yayi wani irin breathtaking kyau


"waye shi din?" taji muryar cousin din nata kamar daga sama

Hakan yasa tayi saurin dawowa daga duniyar kallon Deen ta kalleshi sai kuma tasake kallon inda Deen yake

"muje.. He's a friend" tafada tana wucewa

Dan Jimm cousin din yayi sannan yabi bayanta suka nufi Deen din da haryanzu be Janye idanunshi ba daga kanta


Qarasawa tayi gabanshi cikin murmushi, sai yaji kaso mai yawa cikin 6acin ran dayake ciki yabi iska

"hey.. " tafada tana dan daga mashi yatsu

Dagowa yayi daga jinginen dayake yana murmushi
" hyy"


"ashe kana nan, inata kiranka no response" tafada hankalinta Kwance

"oops na manta ban fiddata daga silent bane, nasata a silent ne dazamu shiga masjid" yafada yana kallon cousin din zee da shima shi yake kallo kowa da irin expression dinshi a fuska

Ganin wanda yake kallo yasa ta juya ga cousin dinta
"Umar meet Deen.. Kamaldeen, a friend"

Murmushi Umar yayi mashi dryly yana miqa mashi hannu

Miqa mashi nashi Deen yayi shima suka shiga yin musabaha

"Deen, this is Umar.. My cousin"

Dan murmushi yayi na gefen baki sannan yace
"ashe shine? The guy.. Nice to meet you" yafada yana yiwa Umar murmushi

Shima dan murmushin yayi yace
"you're welcome" Sai suka sauke hannunsu gabadaya

Umar ne yajuya ya kalli zee datayi kamar wanda ruwa ya cinye don sarai tasan inda maganar Deen ta dosa


"ok sisi, bari natafi, see you" inji Umar


Dan murmushi zee tayi mashi tana cewa
"yeah, see you"


Besake kallon Deen ba yayi gaba ya barsu anan


Binshi da kallo Deen yayi yana jin zuciyarshi na mashi zafi sannan yajuyo ya kalli zee

Cikin basarwa zee tace
"you're welcome to Ruma, so ya kaga garin?"

"Amazing" yafada simply still yana kallonta


Murmushi tayi tace
"to muje ciki ku gaisa dasu mummy ko?"

"is that necessary?" yafada still babu irin wannan walwalar tashi attatare dashi

"yeah, ba kace kun gaisa da daddy ba? Bazata ji dadi ba idan taji kazo bakaje kuka gaisa ba"

Kada kai yayi sai yace
"muje to"


Tare suka jera suka nufi cikin gidan Saidai babu mai magana acikinsu

Zee ta lura fushi yake but he's trying wajen 6oye Hakan

Ita Dariya ma yabata, ita wlh tama manta da wani batun cousin dinta data ta6a yimashi don dama qarya ce kawai don tabashi haushi lokacin yasa tafadi Hakan ashe shi be manta ba

Da ta tuna Da ko introduction din ba zatayi ba Amma kuma a qasan zuciyarta dadi taji ganin yadda yake kishinta, tana son mutum mai kishin abinshi wanda beson wani abu ya ra6eshi ko yaya ne Hakan na daya daga signs of qauna.


Wani wuri inda babu jama'a sosai suka tsaya

"bari nayiwa mummyn magana"

Kada mata kai kawai yayi ta juya ta wuce yabita da kallo

Hannu yasa ya cire hular kanshi yadan yamutsa lallausan gashinshi sannan ya maida hular ya sake harde hannayenshi a qirji


Ganinta da wani ya 6ata mashi mood sosai, kafin lokacin murna yake da doqin Ganinta amma kuma ganinta da wani har tana mashi Dariya yasa duka murnar komawa ciki yaji ya rage kuzari sosai


Cigaba da jiranta yayi yana dan kalle kalle

Can sai ya hangosu sun taho da mummy da zee dake dauke da sultan d'an Aunty Raliya.


Ganin mummy yasa Deen qara gyara tsayuwa murmushi yana forming a fuskarshi

Qarasowa su mummy sukayi, mummy na cewa
"wai patient ne haka?" Cikin fara'a


Murmushi Deen yayi har Saida dimple dinshi na gemu ya losta sannan ya tsugguna yana gaida mummy

Sai mummy taji kanta yaqara girma

"haba tashi mana kamal, yasu kaka?"

Tashi yayi yana murmushi yace
"Tana lfy lau mummy, tana gaidaku ma" yafada yana kasa hada ido daita


Murmushi mummy tayi tace
"Allah sarki, muna amsawa. Munyi rashin kirki bamu tura mata I.v ba"


Murmushi kawai Deen yayi yarasa abinda zaice


"to idan katashi tafiya ayimin magana please, bari nakoma na ida abinda nakeyi" inji mummy

Dan russunawa Deen yayi yana cewa
"to mummy, afito lfy"


Murmushi kawai tayi ta juya ta tafi


Saida yaga ta tafi sannan ya dago ya kalli zee dake kallonshi murmushi a fuskarta


Hade rai yayi ya kauda kai gefe


Dariya ne ya kufce mata ta rufe bakinta da tafin hannu tanayi, sultan din hannunta ganin tanayi sai shima ya kwaikwayeta ya rufe baki da hannu shima yana Dariya

Hakan yasa Deen murmusawa sannan ya miqoma sultan din hannu


Da gudu yatafi don dama shi beda kiwuya ko kadan, daka miqomashi hannu zai taho yana 6angale baki


Amsarshi Deen yayi yana lakutarmashi hanci ya Hade goshinsu yana girgiza kai yana mashi Dariya shima sultan din na 6angalar Dariya


Zee dake kallonsu cikin sha'awa takama murmushi acikin zuciyarta tana hasko Deen dauke da baby dinsu yana mashi/mata wasa


Yatsa sultan yasa a kwarin gemunshi yana cigaba da Dariya

Murmushi Deen yayi mashi yana jin qaunar yaron har cikin ranshi don shima allah ya yishi da mugun son yara ko don shima shi kadai ne?


Dagowa yayi ya kalli zee dake kallonsu itama murmushi a fuskarta

Harararta yadanyi sannan yasake kauda kai

Murmushi tadanyi tana dan girgiza kai sannan tace
"let's go"

Dagowa yayi ya kalleta kamar zaiyi magana saikuma yafasa yabita suka fara tafiya sultan sai gwaranci yara yake mashi shikuma yana biyemashi


Part din Aunty Raliya suka wuce, a balgony ta ajiye musu kujeru biyu farare sai tashiga ciki ta dauko daya daga stools dake gefe gefen kujerun Aunty Raliya ta fito

Zuwa tayi zata ajiye yayi saurin amsar mata ya ajiye inda yaga zata ajiye yana wani qara hade cikakkun girarshi

Murmushi tayi kawai.

Daidai nan wata yarinya tashigo gidan bazata wuce yar shekara 13 ba, itama tasha ankonta na bikin


Da sallama yarinyar tashigo hannunta dauke da tray an rufeshi da wani white clean sheet


Amsawa sukayi gabadaya suna kallonta

Gaidasu duk tayi suka amsa sannan tazo ta dora tray din bisa stool din zee na taimaka mata

Miqama sultan dake bisa kafan Deen hannu yarinyar tayi

Saurin lafewa yaron yayi ajikin Deen yana 6ata fuska

Dariya Deen da yarinyar sukayi zee kuma tayi murmushi

"shikenan, zamu hade ne, zaka gane ni kayiwa kiwuya" inji yarinyar tana Juyawa ta tafi


Bayan fitarta zee ta yaye farin kyallen tray din saiga snacks da drinks sun bayyana

Dago glass cups dake kife tayi ta bude drink din ta tsiyaya masu ta ajiye mashi nashi gabanshi ita kuma ta dauki nata tafara sipping ahankali


Shiru ya biyo baya idan ka cire gwarancin sultan daketa yima Deen qiriniya akan qafa sai tumurmusa mashi shadda yake shikau Deen ko ajikinshi saima murmushin dayake mashi.


Dagowa yayi ya kalli zee yaga drink dinta take sipping ahankali idonta akan waya

"kinyi kyau" yafada ahankali

Dagowa tayi daga wayar hannunta ta kalleshi taga still fuskarshi babu walwala kamar ma bashi yayi maganar ba

"thanks, kaima haka" tafada tana qara kai kofin a baki

"nima me?" yafada yana kallonta

"yadda kace" tafada tana juya ido

Dan murmushi yayi
"ni ai Gaskiya nafada bawai nafada ne kawai don kiji dadi ba"

"nikuma don kaji dadi na fada? Nima Gaskiya nafada"

"haba dai, kina nufin nayi kyau?"

Murmushi tadanyi mai sauti sannan ta Kada kai kawai


Daga kafadu yayi yace
"amma ai ban kaishi haduwa ba" yafada yana dan ta6e baki

Dagowa tayi ta kalleshi
"wa kenan?"


"kin fini sani... *your man*" yafada yana qara ta6e baki


Murmushi kawai tayi batace komai ba shikuma ba abinda yakeso ba kenan soyake tafadi wani abu dazai dan sanyaya mashi zuciya daga zafin kishin dayakeji a zuciya

"shi ai naga har Dariya kike mashi nikau sai shan qamshi kike min" yasake fada yana kauda kai

Dariya yabata sosai Hakan yasata yin murmushi mai sauti kawai batace komai ba, Hakan yasake quleshi


"kuma wajen introducing dina wajenshi wai *my friend* amma shi kin iya kiranshi *my boyfriend*, adai dinga tsoron allah" yafada yana daukar cup din gabanshi a fusace yana sha


Sauke kai qasa zee tayi tana Dariya marar sauti

"ko banza nafishi tsawo, wani dunqul dashi"


Dariyar zee ce tafito fili tashiga yi Babu kakkautawa

Qara tamke fuska yayi ya kauda kai yana sipping din juice din cikin kofin

"am smelling something here... Jealousy" tafada tana Dariya


Harararta yayi
"it's not funny"

"it is, jealousy!"


"babu komai, ai so ke kawo kishi amma ni na lura ma ni kadai ke haukana babu wani sona dakike" yafada yana kumburi

Murmushi tayi tace
"haka dai kace"

"haka dai ne, ba gashi ba kina kula wani babu ruwanki da halin da zan shiga" yafada yana kauda kai don sosai abin yayi mashi zafi don dai shi ba gwanin fushi bane koma gwanin fushin ne bejin yana iya yimata


"dan uwana ne fa"


"kuma boy friend dinki ba"


"wai wa ya gayamaka shine? Bashi bane wannan"

"wato haryanzu akwai wancan din kenan kuma haryanzu boy friend din naki ne"


"my goodness! Dama haka kake?"

"nafi Hakan ma Indai akanki ne " yafada yana kauda kai


Murmushi kawai tayi tace
"nidai banida wani boy friend, inka yarda Amma"

Saurin juyowa yayi ya kalleta ya marairaice
"kice wlh, wlh bakiji yadda zuciyata ke zafi ba"

Dariya tayi

"wlh ba abin Dariya bane, wlh bakiji yadda naji ba danaga kina washe mashi baki"

Dariya tasakeyi tace
"he's only my cousin, sokake naita zare mashi idanu? Afterall me zanyi da guntu bayan inada iroko tree"


Harya fara washe baki Amma jin tace iroko tree saiya tsuke fuska

"nine iroko din?"


Dariya tashiga yi tana rufe baki da hannu

"tsawon iroko ai marar kyau ne, ni banaso"


"to ai naga irin tsawon gareka?"

"wa? Ni? God forbid, kinsan yadda iroko tree yake kuwa, siriri sai mugun tsawo? Allah ya kiyaye"

Murmushi mai sauti kawai tayi

"nidai don Allah ki fita harkar shi please, ba don ni ba please" yafada yana sake marairaicewa

"ai na gayamaka, me zanyi da gajere?"

"babu, wlh ko guntu ne ga hancinshi kamar gajeren wando, qofofin hancin kamar kofar durbi, with that tiny tiny eyes nashi kamar na yan china"


Dariya sosai zee keyi ganin yadda ya daddage yana kushe bawan allah, imagining take da agabanshi yake fadin haka da kau sun kwashi yan kallo


"Allah Gaskiya nake fadamiki, Is better you choose wisely karki za6i wanda zai saki haihuwar masu zubin emmanuella"


Dariya tasakeyi tana girgiza kai
"Allah Deen bakajin magana"

"Gaskiya na fadamiki ai, ato"

Murmushi tayi sannan ta nuna mashi snacks din da be ko ta6a ba

"Sai kince kin daina kula kowa sannan"

"dama ai ba kula kowa nake ba kaidai ke ganin haka Afterall da wane zuciyar zan so wani bayan ni kaina banida iko daita sai yadda akayi daita" tafada tana ta6e fuska


Wani farinciki ya ratsa zuciyarshi nan take murmushi ya gauraye fuskar

"dagaske?"

Murmushi kawai tayi tasake turamashi snacks din gabanshi batareda tace komai ba

Daukar daya daga cookies din gabanshi yayi ya dan gutsira still yana murmushi
"thank you" yafada yana mata winking


Kauda kai tayi tana murmushi kawai


Cigaba sukayi da firarsu kamar babu abinda yafaru kowanne fuskarshi da annushuwa shikau sultan wasanshi kawai yakeyi abinshi


Sosai Deen yaci snacks din don shi dama bejin kunyar cin abinci ko a ina ne, idan dai kaga yaqi Sakin jiki yaci abinci sosai to be yarda da tsaftar abincin bane shiyasa ko a school yafi mu'amala da snacks, biscuit, chips e.t.c


Basu sake jimawa ba suka tashi don tafiya yace zaiyi don 4 saura kuma kaka tariga tayi warning dinshi akan kar yayi dare


Tare suka qara jerowa Deen riqe da sultan dake barci a kafadarshi

Duk inda suka bi sai anbisu da ido ana wondering waye wannan tareda zee


A inda yajira dazu tayima mummy magana yasake tsayawa

Amsar sultan din zee tayi Deen nacewa tabi ahankali kar taji ciwo don jiyake da yana iya shiga daya kai mata shi har cikin gidan

Batace mashi komai ba tajuya ta wuce cikin gidan


Can ba'a jima ba sosai yaga mummy da zee sun fito

Sauke idanunshi yayi qasa yana dan murmushi har suka qaraso wajen

"Kamal har zaku tafi?"

Cikin girmamawa yace
"eh mummy naga marecen yafara kuma kakata tace karna kai dare"

"aikau dai babu kyau tafiyar dare, to bari na kira rabi'u yazo ya kaika"

"laa mummy, da kin barshi zan dan biya kasuwa ne sannan na wuce tasha saina hau motar acan"

"to basai ya biya dakai ba? Zai Mafi sauqi"

Shiru yayi don besan abinda zaice kuma ba

" ga wannan ka kaima kaka, kace ina gaidata"


Nauyin ta dayakeji yasa ya amsa yana mata Godiya don yasan ko yaqiya saita tilastashi

Cema zee tayi ta hada shi da rabi'un saiya wuce dashi sannan sukayi sallama mummy ta koma ciki


Kallon juna sukayi sukayi murmushi sannan suka taho


"muje ka gaisa da amarya?"

Wara idanu yayi yace
"No please, please mutafi mutane sunyi yawa Wurin"

Daga kafadu tayi suka wuce

Basu sha wahala ba sukaga rabi'u kuma dama mummy takirashi ta gayamashi so babu 6ata lokaci kawai suka wuce mota.

"yaushe zaki dawo?"


"Nan da just 1 week"

Wara idanu yayi yace
"one week! Lokacin na mutu da kewarki kenan"

"daidai kenan"

"nidai please yaushe zaki dawo kinga ga school you'll miss alot"


"zan dawo very soon insha allah tunda ai anyi abinda ya kawomu sai yan ide iden da ba'a rasaba"

Bude murfin gaba yayi amma be shiga ba yace
"ok allah ya maidoku lfy and please, don Allah karki kula kowa, please"

Murmushi tayi
"insha allah"

"inso samu ne ma karki je dinner nan"

"saifa naje"


"to kije but please karki kula kowa please"

Rolling idanunta tayi tace
"to"


"promise?"

"promise"


Murmushi yayi mata sannan ya shiga motar yaja murfin ya rufo


Ganin Hakan yasa rabi'u dake cikin mota Tundazu tada motar


Dagama juna hannu suka shiga yi

Alamu yayi mata da saisun yi waya ita kuma tayi murmushi kawai, rabi'u yaja suka fice daga gidan

Ajiyar zuciya ta sauke bayan taga firarsu daga gidan sannan ta dawo ciki.


Lokacin data sake komawa dakin da amarya take Saita iske Aunty Feenah ma bata ciki sai yanmatan amarya daketa maida yadda akayi wasu kuma nata sallar asr

Ganinta yasa sukayi mata caa suna tambayarta waye suka ganta tare dashi

Qin basu amsa tayi saima biyemasu datayi sunata chafta kafin daga baya ma ta baro masu dakin takoma can part din Aunty Raliyar tayi ta kauda abubbuwan dasukayi amfani dasu dazu ta dauro alwala itama ta gabatar da sallar asr

Tana zaune bisa sallaya bayan tagama sallar ta Fiddo wayarta ta kunna tashiga gallery, tashiga wani folder nan take hotunan Deen cikin shigarshi ta dazu suka bayyana


Murmushi tayi tafara binsu daya bayan daya tana kallo

Dik aciki babu wanda ya nuna alamar yasan an daukeshi

Duk yawancinsu hankalinshi nakan sultan dake hannunshi suna Dariya sosai


Bïñ hotunan taitayi da kallo don ba qarya sun dauku dukda a sace akayi daukar kuma duk babu na banza aciki


Murmushi tayi sannan tafita daga gallery din tashiga message tayi mashi short safe journey sms ta tura mashi sannan ta tashi ta fita


*7:30pm*


Gida fa ya hargitse duk inda kayi hayaniya ce kawai na mutane yan zuwa dinner.


Duk wanda zaka gani cikin shigar anko din dinner zaka ganshi pink and blue

Koina ya cakude motoci sai daukar mutane suke zuwa dinner


Can na hango zee tafito tana zuge wata guntuwar jakkarta mai shape din heart pink colour, itama taci adonta cikin doguwar rigarta ta anko din gyalenta a sagale da hannu, kan nan yasha daurin head.


Saurin qarasawa jikin wata mota tayi don dama ita kadai suke jira ta bude back seat tana basu hqrin bata masu lokacin datayi ta shiga ta zauna sannan ta rufo, nan da nan aka tada motar suma sukabi ayarin motocin dake fita daga gidan zuwa dinner


Dinner tayi dinner, ansha shagali sosai a dinner ba qarya inda amarya da ango suka fito suka zama taurari acikin tarin al'umman wajen.

Zee kau samari ne suka yimata caa kowa burinshi yasamu shiga amma kamar yadda tayiwa Deen alqawari babu wanda ta kula acikinsu haka sukayi suka gaji suka barta

Ba'a wani dade sosai ba a dinner don 10:00pm nayi aka tashi, motoci suka shiga jigilar mutane zuwa gida

Itama amarya gida aka maidota badon ran Auwal yaso ba don shi da so samune abashi amaryar shi a lokacin suyi tafiyarsu amma ya ya iya dole ya hqr tunda da yau da gobe duk daya ne.


Washegari ranar kai amarya dakinta


Sai wajajen 5pm motocin daukar amarya suka iso

Saiga amarya daketa cika bakin ba zatayi kuka ba da kuka sha6e sha6e, dakyar aka 6an6areta daga jikin Umma dake hawaye itama aka fita daita su kawunnanta sukayi mata fada sannan aka shiga daita mota

Su zee dama an riga an shishige mota fitowar amarya kawai ake jira


Ajere motocin suka fita suka wuce gidan amarya.


Masha allah, gidan amarya yayi kyau sosai, ba wani babban gida bane sosai amma an tsarashi gwanin burgewa ga jeren Aunty Feenah ya mugun dacewa da sanfarin gidan Hakan yasa gidan yaqara badawa


Saida su zee suka gama zagayen gida suna santi sannan tabi su Aunty Raliya suka dawo gida duk kuwa da yadda Feenah tayi tayi daita tabari sutaho da qawayenta dake jiran zuwan ango amma taqi, tabi su Aunty Raliya tana Dariyar Feenah dake cewa zasu Hade ne zatasan ita tayiwa rashin mutunci. To amarya fatan mu dai allah yabada zaman lfy yakawo dattin daki.


Saida su zee suka qara kwana biyu a garin sannan suka dawo gida.


Zokaga murna wajen Deen don dama duk lokacin da sukayi waya sai yayi mata complain din ta tafi ta barshi cikin kewa.


Dawowar zee yasake bude wani fage na soyayyarsu da Deen

Soyayya suke nunama juna tsantsarta suna jin idan babu daya daga cikinsu dayan bazai iya rayuwa ba.


Ana haka suka shiga watan masoya wato february na watan bature inda aciki ke akwai ranar masoya wato VALENTINE DAY


Tunda aka shiga watan kowanne masoya suka shiga tanadi wa wannan ranar ciki hardasu Deen, wadanda basu ta6a celebrating din ranar ba sai a wannan karon.

Kowa shirye shirye yake wa ranar suna looking forward to ranar cikin doqi.


*14th FEBRUARY 20...*


Yau takama ranar laraba, ranar da duk wasu masoya ke dakon zuwanta.


Ranar da kowanne keson gwadama masoyiyarshi ko masoyinta matsayinshi ko matsayinta a zuciyarsu.


Hakan take a wajen su Deen ma


Zaune suke a usual Wurin zamansu dake very quiet sai tsuntsayen daketa kai kawo a wajen


Zaune suke suna facing din juna kowanne sanye cikin kaya jaa da fari

Zee na sanye cikin wata english gown A shape wanda akayi slashing */* gaba rigar, bangaren dama kalar fari na haggu kuma jaa sai gyalen data yafa a kanta fari, takalmi ma Hakan.

Shikuma Deen sanye yake da farin jeans trouser ya dora top jaa takalmi ma jaa


Sosai sukayi kyau acikin wannan shigar kamar ka sacesu


Zaune suke sun jejjera kwalaben drinks a gabansu sai cards na kalaman soyayya da suka mimmiqar dasu tsaye a gefe gefen kwalaben sai wani kwalin chocolate da chocolate candy ke aciki duk qananu masu shape din heart suna dauka da daddaya suna ci suna fira suna Dariya cikin nishadi.


Kallo daya zaka masu kagane suna cikin farinciki sosai, farincikin da zasuso dawwama aciki har abada.


Ana haka, Deen ya dago ya kalli zee dake sipping din drink din hannunta.

Ganin ya kafeta da idanu yasata ajiye kofin hannunta itama tana kallonshi murmushi a fuskarta


"Zainab, you're the best thing that ever happened to my life, shigowarki rayuwata tasa ta dad'a kyawun kammani, jinake kamar mu kasance ahaka har abada, daga ni saike sai tsuntsayennan, zaune haka muna kallon juna, har abada"


Murmushi zee tayi sannan tace
"kai fitila ne, aguna.

Na dade ina tunanin dalilin dayasa burina na karatu awaje be cikaba, ina wondering meyasa qaddara takawoni nan ba inda zuciyata ke muradi ba.

Ashe haske ne, wani haske ne dake qoqarin haskaka mani rayuwata ya hana faruwar Hakan, kuma ba kowa ne wannan hasken ba face kai

Ka haskaka mani rayuwata, ka cetoni daga halaka, ka taimaka wajen bidani hanya miqaqiya, ka nusar dani meye soyayya ta Gaskiya and finally I was glad mummy ta hanani fita waje karatu don data barni da banyi gamo da wannan hasken ba, da haryanzu ina cikin duhu ina lalube"


Murmushi Deen yayi sosai wanda ya lotsar mashi da dimple dinshi

"inasonki Zainab, yanzu, da'iman abadan"

"nima ina sonka, ada, Ayanzu, da'iman, abadan, abada"

Dariya sukayi tare cikin jindadi suna jin wani irin farinciki na huda zuciyarsu

"one minute" inji Deen

Saiya karkata ya zaro wani dan qaramin red box dake cikin aljihunshi

Dagowa yayi ya kalleta yaga itama shi take kallo

Murmushi yayi mata sai taga ya tashi tsaye sannan yayi mata alamar itama ta tashi

Tashi itama tayi ahankali tana jin yadda zuciyarta ke bugawa sosai

Ahankali taga yafara rage tsayi har yakai kan gwiyagunshi


Runtse idanunta tayi gam tanajin wasu irin emotions na building a zuciyarta

"will you marry me?" taji muryashi tace haka a tausashe

Bude idanunta tayi ta kalleshi still on his knees, box din abude tana hango kyakyawan zoben ciki.


Sake kallonshi tayi takasa cewa komai sai hawayen dake forming a idanunta

Ahankali ya ciro zoben dake cikin box din sannan ya dago yana kallonta
"marry me, please"

Yanayin yadda yafadi a marairaice yasata yin Dariya hawaye na saukowa a idanunta ta miqamashi hannunta ahankali tana share hawayen dasuka sauko mata still murmushi a fuskarta


Ahankali ya tallabo tafin hannunta cikin nashi sannan ya zuramata zoben a yatsarta na biyun qarshe

Jitayi qaffafuwanta bazasu iya daukarta ba Hakan yasata xamowa itama tayi kneeling ta rufe fuskarta da taffukan hannunta tana shesheka ahankali

Shima kallonta yakeyi yanajin zuciyarshi na raunana, yanajin kamar ya rungumota a qirjinshi ko zaiji sauqin abinda zuciyarshi ke mashi

Haka kawai su biyu kejin kamar wannan shine happy moment dinsu na qarshe, dalilin da yasa zuciyoyinsu ke basu Hakan ne basu saniba

"I love you" yayi maganar kusan cikin rada

Dago fuskarta tayi daga tafukan hannunta ta kalleshi da bloodshot idanunta

"please don't leave me, no matter what" itama tafada cikin karyewar zuciya

"never, I will never" yafada yana jin kamar shima yayi hawayen, idanunshi shima sun Kada

Share hawayen fuskarta tayi sannan ta jawo jakkarta ta bude taciro wani box itama jaa Saidai yafi na Deen girma

Dagowa tayi ta kalleshi taga shima ita yake kallo

Murmushi tayi mashi daidai saukar wani hawayen saikuma tayi saurin sharewa da bayan hannu sannan ta bude box din carefully


Dagowa tayi taga shima kallon abinda ke cikin box din yake sannan ya dago ya kalleta


Bands ne guda biyu aciki jere jajjaye, daga tsakiyar band din akwai wani heart shaped bud

Ahankali ta cirosu tana nuna mashi murmushi a fuskarta

Kallonsu yayi sannan ya kalleta shima murmushi na forming a fuskarshi

Ajiye daya tayi ta riqe daya ta lalubi wani botton ajikin bud din band din nan take tsakiyar band din take kamar fuskar agogon hannu yashiga bada wuta yana bada rubutun
_*Deezeen*_
Idan kuma ya dauke yasake dawowa sai yabada
_*together forever*_


"wow!" Deen yayi exclaiming yana kallon band din cikin sha'awa


Nuni tayi mashi ya miqo hannunshi

Miqawa yayi yana murmushi

Ahankali ta daura mashi a wrist dinshi saigashi yayi mashi d'ass a hannu gwanin kyau


Shima duqawa yayi ya dauko dayan dayan ta miqamashi hannunta itama ya daura mata ahankali

Murmushi sukayi ma juna sannan suka jera hannayen nasu mai band din kusada juna suka danna dan qaramin botton din nan take haske yakawo da rubutun
_*DEEZEEN 💞*_
Da
_*TOGETHER FOREVER❤️*_

.... ✍️


UMMIN FASIHU 🧚🏻‍♀�
8/2/21, 9:38 PM - Buhainat😝: *🙍🏻‍♂️DEEN 🙍🏻‍♂�*


*044*


*ASAAD*


Kwance take kan gado ruff da ciki kaffafunta asama tana dan wasa dasu


Ring din yatsarta ta qurama ido wanda yawancin lokuta irin haka idan tana zaune bata komai saita tisa zoben agaba tana kallo tana jin wani shauqi na musanmman na tasomata


Kwantar da kanta tayi akan filo tayi lamo tareda qure waje guda da ido ita kadai tasan abinda ke kai kawo a kwakwalwarta


Knocking da akayi a kofa ya dawo daita daga guntun tunaninta.


Kallon kofar tayi sannan ta miqe zaune

"yes?"


Turo kofar akayi aka shigo sai taga ashe mummy ce


Sauko da kaffafunta tayi qasa tana cewa
"mummy?"


"ki shirya kinyi baqo yana falon baqi" inji mummy


Dan daga girarenta zee tayi tace
"baqo kuma?"


"eh, Kiyi maza karki 6atawa mutane lokaci " inji mummy tana Juyawa zata tafi


Binta da kallo zee tayi harta fita tana wondering wane irin baqo kuma da daren nan

Duba agogon bangon dakin tayi taga 8:30pm sai kuma ta tashi don yin yadda mummy tace


After dress baqa kawai ta dora kan kayan jikinta ta yafa gyale sannan tadan gyara fuskarta tayi spraying turare a jikinta sannan ta dauki wayarta ta fita


A qasa ta tarar da mummy

"yauwa dauki wadannan kitafi dasu" inji mummy tana nuna wani tray dake kan centre table din falon


Tsayawa zee tayi tana kallon tray din dake dauke da kayan motsa baki cikin mammaki

"ko bakiji ba" inji mummy tana hade rai

Wucewa zee tayi wajen tray din not saying anything ta dauki tray din ta nufi hanyar fita

"behave yourself ok? Karki saki ki 6atamin rai" taji mummy na fadin Hakan a bayanta

"to" kawai tace ta ida ficewa tana jin wani haushi a zuciyarta

Ko ba'a fadamata ba tasan wani ne yazo wurinta don dama ansaba hakan donma sundan ja baya yan kwanakinnan saboda bata kulasu ko sunzo din, da kenan da batada Deen bare yanzu.


Ta6e baki tayi ta qarasa guest room din tayi knocking ahankali sannan ta tura kofar tana sallama


Ahankali taji an amsa cikin masculine voice

Qarasa Shigowa falon tayi batareda ta kalli gefen da mutumin ke zaune ba ta qarasa centre table din dakin ta ajiye tray din sannan ta nemi kujera dan nesa dashi ta zauna


Sai a sannan ta dago tadan kalleshi sama sama ta kauda kai

"Sannu" tafada ahankali tana gyara zamanta


Sai a lokacin shima gayen ya Janye idanunshi daga kan wayar hannunshi ya kalleta itama sama2 ya kauda kai yana cewa
"sannu"


Wani abu taji ya tsayamata a maqoshi amma saita hadiye ta koma itama ta jingina da kujerarta tafara latse latse a wayarta


Shiru dakin yasake dauka banda qarar a.c babu abinda ke tashi dakin

Sun kusan minti 20 ahakan wayar zee tafara ringing cikin low tone


Ko bata duba ba tasan ko wanene don dama shi kadai keda wannan ringing tone din


Dan murmushi tayi Saida takusan katsewa sannan ta daga ta kara akunne


"Ranki ya dade" taji cool voice din Deen na fadin Hakan tacikin wayar


Murmushi tayi sannan tace
"tareda naka"


Shima murmushin taji yayi yace
"barka da daren juma'a"

"barkanmu dai, where is my kaka?"

"Your kaka tana dakinta Dakyar nasamu na faki idonta nafito"

Dan wara manyan idanunta tayi
"kafito? Katafi ina?"

"ina kofar gidanmu, inason jin muryarki ne kuma dataga na shiga daki zata biyoni taga ko menene so I decided gwara na gudo waje"


Dariya zee tayi ahankali tace
"kai ko? Allah yasa ta leqo ta ganka wajen to"

"babu ko wuya Indai kaka ce, ni wlh nagaji yakamata ta dinga kyaleni Hakan tunda na girma amma kullum cikin samin ido take kamar qaramin yaro" ya qarashe a dayan bangaren yana kumbura fuska

Dariya tasakeyi ahankali sannan tace
"wulaqanci? Yanzu kaka kake cewa tana samaka ido?"


"to, ai Gaskiya ne, am very sure da cikin gida nake da yanzu tabiyo sahu tana _kyakyawana? Lfy ka qunqume daki?_" yafada yana kwaikwayon maganar kaka


Rufe bakinta zee tayi tana Dariya ahankali sannan tace
"ka qaddara kayi a gabanta, takanas zanzo gidan na fadamata"


Shima dariyar yayi yace
"dakau kin ja ta zaneni radam"

Wara idanu tayi
"dagaske? Tana iya dukanka?"

"sosai ma, ai haryanzu kallon dan 5yrs takemin, tsaf zata zaneni nikuma naita kuka 😭" ya qarashe maganar da muryar kuka

Murmushi mai sauti tayi tace
"nikuma naita Dariya ba? ina maka waqar mai kukan banza"

Kumbura fuska yayi
"hakama zakice?"

"eh mana, bayan haka ba har videoing dinka zanyi na dora a social media with caption *crying kaka's boy*"


Sake hada gira yayi
"ashe dai bakya sona"

"Sai yanzu ka sani?"

"sadly yes"

Murmushi tayi
"am glad yanzu kasani"


"hmm marar M... Wai kinsan wani abu?"


"A'a saika fada"


"dazu nayi composing wata waqa, bakijita ba, very muah!" Yafada cikin doqi

Dariya marar sauti tayi
"har kasan tayi dadi?"

"bani nayita ba?"


"don kai kayita ai bakai zaka yabeta ba sai kabari wadanda suka jita su yabeta"

"to ai shiyasa zanyimiki kijita"

"to shikenan, ina saurare"

Gyaran murya taji yashiga yi Hakan yasata fara Dariya marar sauti, kamar kau yasani sai yace

"to ai ina iya farawa kuma kiyita yimin Dariya"

Dariyarta ce tafito fili

"hmm there you go" inji Deen yana hada rai

"ni Dariya nayi, bafa Dariya nayi ba"

"ba Dariya ba kikayi? Ni kurma ne?"

"to sorry, inaji"

Jitayi yaqara gyaran murya ita kuma taqara kasa kunne murmushi a fuskarta

"to ai kuma kina iya cewa baitin is so long"

"ni yaushe nacema zance Hakan?"

"na sani ne ai, kina iya kushemin abuna duk yadda nakeji daita kau"

Dariya tasakeyi sai taga kamar inuwa inuwa a gabanta Hakan yasata dago idanu sai taga mutumin ne ya miqe tsaye


Dan wara idanu tayi don ita harga allah ma ta manta da akwai wani a dakin

Ganin zaiyi magana yasata saurin cewa Deen
"excuse me Deen, I'll call you later" tafada tana katse kiran batareda ta tsaya jin Amsarshi ba


Saurayin dake kan wuya akan wulaqancin datayi mashi yace
"zan tafi, thanks"

"thanks too, agaida gida"


Kada kai yayi kawai yana cizon lower lip dinshi sannan yafita a fusace leaving the door open


Binshi da kallo tayi harya fita sannan ta sauke Ajiyar zuciya tana rolling idanunta sannan itama ta tashi ta nufi tray data ajiye wanda ko ta6ashi ba'ayi ba ta dauke tana ta6e baki tafito ta maido kofar ta rufe.


Luckily bata tarda mummy falon ba hakan yasa tawuce da tray din kitchen taba daya daga cikin maids din ciki tafito


Tana fitowa taci karo da mummy dake sakkowa daga stairs Hakan yasa gabanta yadan fadi


"harya tafi?" inji mummy tana kafeta da idanu

"eh, yatafi yanzu yanzunnan" inji zee tana rarraba idanu kamar marar gaskiya


Mummy bata sake cewa komai ba tazo ta wuce ta tashige kitchen Hakan yasa zee sauke Ajiyar zuciya sannan itama ta nufi sama


Saida tagama shirin barcinta sannan ta haye gado bayan ta qure a.c din dakin


Wayarta ta dauka ta lalubo number Deen takira kamar yadda tace mashi

Kamar kau jira yake a ringing na biyu ya dauka yana sallama

Lumshe idanu tayi ahankali ta bude sannan ta gyara kwanciyarta tana amsa sallamar


❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️


Dagowa daddy yayi yana kallon zee data zauna yanzu murmushi a fuskarta.


"daughter ta" yafada shima yana mata murmushi

"na'am daddy na" tafada cikin shagwa6a


"ya weekend?"

"alhamdullilah daddy na" tafada tana murmushi


"kinsan abinda yasa nayi kiranki?"


"A'a daddy"


Gyara zama daddy yayi Yayinda mummy haryanzu bata dago ta qara kallonta ba Tun amsa gaisuwarta datayi, ita gani ma tayi kamar fushi take


"jiya wani yazo wurinki ko?"


Jimm zee tadanyi fara'ar fuskarta na dan tafiya

"eh daddy" tafada ahankali


"masha allah, ya fadamaki ko wanene?" inji daddy again


Shiru tadanyi sai kuma ta girgiza kai ahankali

"To sunanshi ASAAD, d'a ga babban aminina kuma abokin kasuwancina Alhaji Abubakar"


Dagowa tayi ahankali ta kalli daddy, ita sai yanzu ma ta tuna Da maganar data ta6a ji daddy nayi da mummy akan d'an Alhaji Abubakar din

No wonder, dama tasansu tasan halinsu na jin kai, shiyasa ma jiya qila yafara daddaga mata kai besan idan dagin kai ne gidanshi ne yazo.


"yau da safe ya kirani yana gayamin abinda yafaru a tsakaninku, banji dadi ba Amma kuma laifina ne da ban sanar dake zuwanshi ba dakuma gayamaki ko shi waye, I think duk Hakan yajawo matsalar tun farko.

Shiyasa nace bari na kiraki nayimiki bayanin komai dalla dalla yadda zaki fahimta"


Shiru dakin ya dauka babu mai cewa komai Hakan yasa daddy cigaba da cewa
"kamar yadda na fadamaki sunanshi Asad, First born din Alhaji Abubakar.

Yaro ne haziqi don Yanzu haka yagama masters dinshi ne a qasar india ko sati biyu beyi da dawowa ba kuma insha allah next week zai fara aiki a daya daga cikin manyan companies din babbanshi a matsayin mai jagorantar kamfanin

Asad yana da komai da kikeso bama ke kadai komai da kowacce mace zata so shiyasa nama fara tunkararki da wannan maganar

Bayan haka kuma faruwar Hakan zai qara qulluwar zumincinmu dake tsakanina da Alhaji Abubakar kuma zamu qara girma da qima a idanun juna

Nasan jiya rashin sani ne yasa kika qi kulashi Hakan ma nagayama Alhaji Abubakar din amma zai qara dawowa yau sai ku fuskanci juna dakyau"


Shiru dakin yasake dauka zee bata dagoba kuma ba tace komai ba

"baki ce komai ba dear"


Sai a sannan ta dago ta kalleshi sannan tace
"Dad... I think basai yasake dawowa ba"

Shiru daddy yayi yana kallonta sai kuma yace
"basai yasake dawowa ba kamar yaya?"

"saboda ko yasake dawowa din bazamu fuskanci juna ba"


Shiru dakin yasake dauka, haryanzu mummy batayi magana ba Saidai wani kallo datake jifan zee dashi, zee na ankare da kallon amma taqi kallon gefen mummyn don karma tarasa qwarin gwiwarta

"meyasa?" inji daddy yana kallonta yanayin rashin jindadi na bayyana a fuskarshi

"saboda bana sonshi Dad..."

"ke!! Wato haryanzu bakida hankali ban saniba? Ina maki kallon wacce tafara hankali ashe haryanzu da saura?!" inji mummy a matuqar fusace

Sauke idanunta zee tayi tana dan qara shigewa kusada daddy

"ya isa maimuna" inji daddy Ahankali


"ya isa din me? Yarinya shikenan bazata ta6a hankali ba, don gidanku ke kika haifemu ko mu muka haifeki dazaki maidamu shashashai? Duk wanda yazo da abinda zakice? Dama ina ganin dawowarki jiya nasan ba lau ba ke kenan Duk wanda yazo beyi miki ba? Me kika dauki kanki? Ko atunaninki cigaba zakiyi da zama damu har abada!"

Daddy ne yaqara katseta da
"haba Maimuna, ya isa Hakan mana, daga fadin ra'ayinta saiki hauta da fada?"


"haka ma zakace Alhaji? Yarinya shikenan sai abarta tayita abinda taga dama babu kwa6a? Dama kai ka lallatata ai, idan ba Haka ba tsabar wulaqanci duk wanda yazo sai tace bata sonshi, sotake mu tisata gaba muyita kallo kenan har ta tsofe a gida?

To bari kiji, diya mace qa'idattacen lokaci gareta, wlh tun kinada sauran damar ki ki rufama kanki asiri ki za6i miji tun kafin yazamo ke ke neman ayi za6i dake" inji mummy cikin mugun 6acin rai

Shima daddy da ranshi yafara 6aci yace
"haba Maimuna? Wannan meye to kike mata? Baki ne ko me dazakice zata zama ita za'ayi za6i daita? Wannan maganar kwata2 be dace ta fito daga bakinki ba a matsayinki na Uwa"

Kauda kai kawai mummy tayi tana huci itakau zee banda hawaye babu abinda takeyi


Juyowa daddy yayi Wurin zee daketa dauke hawayenta cikin sassauta murya yace
"daughter?"


Dagowa tayi ahankali ta kalleshi da watery eyes dinta
"bakya sonshi ko kika ce?"

Ahankali ta gyada kanta avoiding mummy's gaze


"to masha allah, Zainab ni mahaifinki ne kuma mai son farincikinki, bazan ta6a yimaki dole ba, na riga da na dauki alqawarin auramaki muradinki ba don komai ba sai don dorewar farincikinki wanda nima shine nawa

So karki wani damu, ni bazan yimiki bakin ki tsofe agida ba kuma bazan miki bakin kizama za6in wasu ba, insha allah saikin za6a kin darje da kanki kin kawoshi da kanki nikuma na cika miki burinki ta hanyar auramaki shi"

Farinciki ne ya mamaye zuciyar zee Yayinda mummy kuma ta kauda kai cikin tsananin takaici

"Thank you so much daddy... Kuma.. Dama ni yanzu akwai wanda.. Nakeso" tafada ahankali

Ba daddy kadai ba har mummy Saida ta waigo ta kalleta sai kuma suka kalli juna sannan suka maida kanta again

"menene?" inji daddy unbelievably

Murmushi kawai tayi ta Kada mashi kai tana sunne kai, karo na farko data fara jin kunyar daddy


Washe baki daddy yayi

"masha allah, to kingani ko? Kinga abinda nake fadamaki, baki bari yarinya tagama fadin abinda zata fadaba kinyi jumping to conclusion" daddy yafada yana kallon mummy data qara kauda kai


Cikin farinciki yajuyo gun Zainab dataji wani sanyi na ratsa zuciyarta yace
"wanene shi to? Gayamin everything about him"


Murmushi zee taqarayi a kunyace tana jin wani yaqini a zuciyarta

"Daddy kaima ka sanshi ai"

Dan wara idanu yayi
"dagaske? Tofa, to wayeshi din?"


"School mate dinane, Sunanshi DEEN"


Tsittt dakin yayi


Kallon kallo aka shigayi tsakanin mummy da daddy Saidai kowa da kalar kallonshi

Daddy kallon rashin fahimta mummy kuma kallon mammaki

"Kina nufin Kamaldeen?" inji mummy a mammakince


Bata dago ta kalleta ba ta kada kai alamun eh

Sake kallon juna mummy da daddy sukayi

"wai wanene Hakan?" inji daddy in confusion

Shiru mummy tayi tama kasa cewa komai

"daku fa nake"

"ta fadamaka mana, tunda itace mai maganar" inji mummyn tana kallon zee

Maida kallonshi yayi akan zee din dake kallonsu itama

"daughter na, kiyimin bayani, ni banganeba haryanzu"

Zee da jikinta yafara sanyi tadan tattaro kingin kuzarinta sannan tace
"Kamaldeen, wanda yayi rescue dina a wajensu Master, wanda ya kwanta hospital ta dalilin incident din"


Diff... Wutar daddy ta dauke na wucin gadi

"What?!" Yafada in shock... ✍️


*please Manage 👏, yau Dakyar nasamu nayi wannan biki garemu kuma jiya ma ban samu zaman yiba, sanin cewa kuna nan kunata jira yasa nadanyi wannan don jiya ma ba'ayi ba

Ayi hqr, da babu gwara babu yawa

Natafi cin shinkafar biki

🚴🏻‍♂️🚴🏻‍♂️🚴🏻‍♂️🚴🏻‍♂�


Ummin fasihu 🧚🏻‍♀�
8/2/21, 9:38 PM - Buhainat😝: *🙍🏻‍♂️DEEN 🙍🏻‍♂�*


*045*


*THE CHALLENGE*


Dagowa zee tayi tana kallon daddy jin yadda yayi magana sai gani tayi shock ne written all over his face, sai taji jikinta yayi sanyi


"I.. Don't get you" inji daddy yana kallonta cikin son gasgata abinda kunnuwanshi suka jiye mashi

Shiru tayi takasa cewa komai

"wa kike nufi, I don’t get you" daddy yasake fada


Hadiye wani abu daya tattaru a maqoshinta tayi sannan tace
"wannan Deen din wanda keda pneumonia wanda aka kwantar dashi asibiti dalilin attempt dinsu master akaina"


Ganin yayi shiru yana kallonta yasata yin tunanin ko haryanzu be gane bane Hakan yasata qara cewa
"yace kunma Hade a wajen daurin auren Aunty Feenah Har kuka gaisa ma, wannan mai grandmom din?"


"daughter are you ok?" inji daddy yana Binta da kallon mammaki

Itama kallon rashin fahimta tashiga yimashi

"ki rasa wanda zakice kina so sai wannan yaron?" inji daddy still cikin mammaki

Gaban zee yashiga harbawa ahankali ta cigaba da kallon daddy batareda tasan na cewa ba

"wai maimuna bakiji abinda muke cewa bane kikayi shiru?

Wai kinsan wa take nufi?
Wannan yaron? Wannan poor yaron? Yaron wannan tsohuwar? Shi wai take so"


Bugun zuciyar zee yashiga qaruwa tana zuciyarta na dan fara nauyi

"haba Zainab, haba Zainab, da kyanki da matsayinki da arziqinki ki rasa wanda zakice kina so sai wannan flirty poor guy?"


Dagowa zee tayi ta kalli daddy tana jin zuciyarta na Bugun daya kusan faso qirji


"Duk masu kudin dake zuwa nemanki? Duk masu matsayin dake zuwa nemanki, duk freaking rich, classic guys nake sonki ki rasa wanda zakice kina so sai wannan?"


"b..but daddy, meye aibunshi?" inji zee cikin rawar murya


Sake Binta da kallon mammaki daddy yayi not believing what he's hearing

"mene? Meye aibunshi kikace? Wai daughter when did you change? Yaushe kika chanza? Magangganunki sam basuyi kama da naki ba"


Itadai mummy kasa cewa komai tayi sai kallonsu kawai datakeyi


"daddy ni aganina what matters is Good characters not wealth" inji zee dakeji kamar tayi kuka


"wai yaushe kika chanza daughter? Ni dake munsan qualities din dakike buqata a namiji, wanda kike ambata min yanzu bana tunanin yanada ko daya"

"that was then daddy, wancan tunanin na da ne, yanzu na gane ba duk kyalekyali keda amfani ba, what matters most is Good heart"


Shiru daddy yayi kawai yana kallonta, this is the least he has expected


Ajiyar zuciya daddy ya sauke sannan yace
"kije ki sake tunani Daughter, amma wannan ba za6i bane"

Yana kaiwa nan ya miqe ya shige quryarshi


Binshi da kallo both zee da mummy da Tundazu takasa magana sukayi harya shige ya rufo kofar


Mummy ce ta maido dubanta kan zee Hakan yasata sunkuyar dakai tanajin wasu hawaye na taruwa a idanunta


Mummy batace komai ba itama ta tashi tabi bayan daddy suka barta zaune nan ita kadai


Bin mummyn tayi da kallo itama harta shige

Kafe kofar dasuka rufo tayi da idanu zuciyarta na lugude

Koda wasa bata ta6a kawoma ranta soyayyarsu zata samu matsala ta wannan sigar ba

She thought ko mahaukaci takawoma daddy a matsayin wanda takeso zai auramata shi don farincikinta, bata ta6a tsanmmanin wannan reaction dinba daga gareshi


Ahankali ta miqe itama tajuya ta nufi kofar fita daga falon tana share fuskarta da bayan hannu.


***


"nifa sai inga wannan abin duk bekai na tashin hankali har haka ba" inji mummy tana kallon daddy dake zaune Tundazu rai a jagule


Dagowa yayi ya kalleta
"bekai na tashin hankaliba kikace? Kinsan meke shirin faruwa kuwa? My only daughter in love with a mere street guy? Kema kinsan Hakan ba mai yiwuwa bane"


"Alhaji please calm down, wannan abin ahankali yakamata abishi bada zafi zafi ba, kamata yayi a zauna ayi tattaunawa ta fahimta akanshi"

Wani kallo yayima mummy
"wane tattaunawa? Kema kinsan ko me za'ayi diyata bazata auri irin wannan mutumin ba.

The whole diyar Dan Faranshi? Diyarshi tallin qwall? Ina?"


Shiru mummy tayi takasa cewa komai, she's confused also, itama burinta Zainab ta auri wani ko dan wani wanda Hakan daidai yake da qarin qima da mutuncinsu na masu arziqi amma ambatar suna Deen da zee tayi yasa zuciyarta tafara rawa akan wannan ra'ayin nata, Hakan yasa yanzu ita kanta batasan wanda take goyon baya ba, Zainab ko Daddy.

"ni ina nan ina jiran takawo za6inta, I thought it will be the best, ashe am mistaken? A tunanina duk wandanda ta kora mafiyinsu zata kawo ashe ba Haka bane? Taje can an huremata kunne, am very sure wannan ba ra'ayin ta bane wlh, wannan harda zuga da hurin kunne, ai nasan diyata ciki da bai. Babu yadda za'ayi ace wannan shine za6inta, babu.

Wannan kawai hurin kunnene irin na maza and I will never tolerate it, zan koyama mutum hankali ne koma wanene, babu ruwana" yafada cikin tsananin 6acin rai


Ajiyar zuciya mummy datayi zugum Tundazu tayi tace
"to allah ya kyauta"


Beko kalleta ba ya tashi ya nufi toilet din dakin.


Cikin sanyin jiki tafito daga part din daddy takoma part dinsu

Ahankali tashiga hawan matattakalan benen harta qarasa sama

Dakinta ta nufa Direct ta bude tashige ciki ta maido ta rufe sannan ta nufi gadonta ta zauna a gefenshi


Shiru tayi ta qurawa waje guda idanu, zuciyarta keson kawomata wani tunani amma taqi bata damar Hakan, taqi yarda taba kowanne irin tunani damar yin tasiri a ranta

Abu daya kawai ke qarfafa mata gwiwa

Shine Farincikinta shine na daddy itakuma batada wani farinciki daya wuce Deen Hakan na nufin dole daddy yayi accepting din Deen idan har yanason dorewar farincikinta kuma a wannan ga6ar ne batada tantama akai, daddy na iya sadaukar da komai akan farincikinta ciki harda farincikinshi, Hakan ne yaqara qarfafa mata gwiwa akan Deen Amma kuma ta rasa dalilin dayasa kuma zuciyarta ke rawa akan haka, tarasa dalilin dayasa take fargaba dukda tabbacin datake dashi, ta rasa meyasa takeji ajikinta wani abu marar dadi zai faru daita, dasu, ita da Deen.


Ringing din wayarta yasata sauke wata Ajiyar zuciya tana lumshe idanu tareda budewa

Shine, ko bata duba ba tasan shine.

A halin yanzu babu muryar wanda take buqatar ji kamar tashi haka zalika kuma babu wanda bata fatan yaji muryarta ahalin yanzu kamar shi

Jin Muryarshi zai kawo sauqi wa zuciyarta shikuma jin muryarta zai jawo fargaba da rashin kwanciyar hankali gareshi


Kiran farko ne ya katse, ba'a jima ba wani yasake Shigowa

Cigaba da kallon wayar take tana bin sunanshi dake motsi a screen din da kallo batareda ta Ko motsaba har itama ta katse

Daukar wayar tayi dafarko kamar ta kashe sai kuma ta chanza shawara ta sata a silent ta ajiyeta kan bedside locker itakuma ta zame ta jingina da frame din gadon

Idan akwai abinda bataso to tashin hankalin Deen ne don haka dole ta hadiye kwadayin jin muryar tashi ta zauna da nata damuwar ita kadai don tasan dayaji muryarta zaisan babu lafiya kuma zaiso tilasta mata ta fadamashi abinda ke faruwa wanda ita a ganin ta bashi da amfani don abune da bazaiyi wuyar warwarewa ba, tasan daddynta so batada case.
This is just a minor challenge.


*08:35pm*


Kwance take kan gadonta tana danne dannen wayarta tana iyakar qoqarinta na ganin ta kauda duk wani damuwa dake son yin tasiri a zuciyarta Saidai dannar wayar kawai take amma ita kanta bata gane me takeyi da wayar ba


Knocking din kofarta taji anyi

Dago kai tayi ta kalli kofar batareda tace komai ba

Gani tayi an murda handle din anshigo dakin

Mummy ce


Sauke kai tayi cikin zuciyarta tana cewa itafa bata jin yinwa ko an tilastata bawani abin kirki zataci ba

"dress into something decent ki sauko kinyi baqo" inji mummy babu alamun wasa


Saurin dagowa tayi ta kalli mummy
"baqo kuma mummy?"

"eh baqo kuma"

"but I thought..."

"look karki 6atawa mutane lokaci, Kiyi abinda nace yanzu!"


Saurin sauko da kaffafunta tayi daga kan gadon don tasan halin mummy idan ranta ya 6ace

"nabaki 5 mins Kiyi ki fito tun kafin ranki ya 6aci" inji mummy sannan tajuya ta fita

Binta da kallo zee tayi harta fita ganin Hakan yasa tafara dirje dirjen kaffafu aqasa tana kukan ta6ara


"ni ya kukeson nayi ne nace banasonshi banasonshi inada wanda nakeso, haan!" tafada tana hucin kukan datakeyi


Sai kuma ta tashi a fusace tanufi wardrobe ta budeshi da qarfi taciro wata baqar gown ta dorama nightie din jikinta ta yafa gyale tadan fesa turare sannan ta fita looking so angry.


A falon ta tarda mummy ba ita kadai ba harda daddy zaune bisa kujerar dake facing stairs


Bata kalli ko daya daga cikinsu ba tawuce centre table din dake akwai tray mai dauke da kayan motsa baki sama ta dauka ta fice batareda ta yarda ta kalli gefensu ba.


Binta da kallo duk sukayi sannan suka sauke Ajiyar zuciya

"Alhaji baka ganin kamar dolen dakace baxaka yimata ba shi kake niyyar yimata?" inji mummy


Shiru daddy da ranshi ke duk a jagule yayi can sai yace
"haryanzu ba dolen zanyi mata ba, idan basu daidaita ba still zan bata damar samo wani amma ba wannan yaron ba ko makamancinshi, ta nemo miji gidan manya gidan mutunci ba inda zan kaita ba inkasa cin abinci ba saboda tunanin ko ita tasamu abin sakawa aciki"


Ajiyar zuciya mummy ta sauke not knowing what to say don haryanzu batada ra'ayi acikin wadannan ra'ayoyin biyu wato na daddy da na Zainab, Itadai fatanta dai allah ya tabbatar da wanda yafi alhairi


***


Da sallama tashiga guest room din ma wannan karon


The same voice daya amsa sallamarta ta jiya ta amsa yau ma


Bata yarda ta kallo gefen dayake ba ta nufi centre table din Wurin ta ajiye tray din datake jin kamar ta sakeshi Tundazu

Kujerar da ta zauna akai jiya tasake akai yau tayi crossing kaffafunta tafara dannar wayarta


Tunda tashigo yake Binta da kallon qasan ido ganin yau batada niyyar tankamashi yasashi cewa

"sannu" kamar mai ciwon baki


Ahankali ta dago ta kalleshi saikuma ta maida kallonta akan wayarta
"yauwa" tafada itama kamar wanda aka tilasta


Shiru yaqara biyo bayan haka. Ita hankalinta na kan waya shikuma hankalinshi na kanta yana studying dinta


Sun kusa minti 15 ahakan sannan Asaad ya gyara zamanshi a kujerar dayake akai

"Am Asaad Abubakar Dikko by name, ni d'a ne ga Alhaji Abubakar Dikko, a graduate with masters certificate a fannin business, and you?" yafada yana tsareta da madaidaitan idanunshi

Sai a lokacin tasake Dagowa ta kalleshi sama sama tasake Janye idanunta

"Am Zainab.. Zainab Dan faranshi" tafada a taqaice


Kada kai yayi

"Good, hope kinsan dalilin zuwa na nan?"

"zan sanine bayan ka sanar dani"

Dan murmushi yayi na gefen baki sannan ya kada kai yana dan mere baki

"well, ni nasani kuma zan sanar dake dukda nasan kema kin sani"

Dan daga kafadu cikin qara ta6e baki yace
"I was sent here by my Dad, akwai abinda suke son qullawa tsakanina dake for their benefits don Hakan zai qara zumuncinsu da amincinsu kamar yadda sukace, shiyasa aka turoni don wai mu fahimci juna which I think bazai yiwuba don ni atsarina mata Africans basuyimin ba kwata2, primary dina kawai nayi a Africa, secondary dina nayishi ne a france, nayi first degree dina a uk and yanzu na qarqare masters a India

A duk cikin qasashennan babu baqaqen fata duk jajjayene wataqila shiyasa kwata2 bana ra'ayinsu, babban burina shine auren one of those jajjayen ba baqaqen Africans ba dukda ke naga you're not that black" ya qarashe yana dan ta6e baki

Zee tunda yafara ta maida hankalinta kanshi tana kallonshi dumpfounded

"so nazo nan ne ba don mu fuskanci a sigar da tsoffafinmu keso ba sai don mu fuskanci juna na ainahi wato sanin ra'ayin juna akanmu, ni kinji ra'ayi na, so samu kiyi co-operating mu samawa kanmu mafita"


Wani murmushi ya su6ucema zee tadan kauda kai tanayi

Bece komai ba sai cigaba da kallonta dayake yana jiran jin me zatace

Dagowa tayi taqara kallonshi sannan ahankali tafara magana
"A ganina a smart guy with sharp brain tun zuwanshi na farko a wajen budurwa zai gane yasamu kar6uwa ko be samuba.

Me haja shike buqatar talla.

Gaskiya ra'ayinmu yazo daya don nima ban cika ganin mutuncin desperate African a qasashen masu jajjayen fata ba. Wadanda basa kishin kansu bare akai ga kare martabar asalinsu, bana masu kallon mutane at all saboda a qasarsu sunfita sahun mutane saboda basa kishinta a can inda suke marari kuma ba'ayimusu kallon mutane.


Nayi primary school dina a Nigeria, Secondary school ma haka, and now nakusan graduating still a beloved qasata Nigeria and after that ko zanyi aiki I'll proudly reject kowanne offer na kowane qasashe musanmman na jajjayen and proudly stick to my beloved country Nigeria kuma ko zan fita din it will be within Africa din not outside.

So inajin there's no need of worrying tunda ra'ayi yazo daya and am glad it does don ni dama ba kowanne namiji nake ma kallon namiji ba" tafada itama tana dage kafadu kamar yadda yayi dazu.


Tsit dakin yayi

Kallonta yake babu kyaftawa, yama rasa mai zaice ko zaiyi.


Ganin shirun yayi yawa kuma baida niyyar cewa komai ko motsawa yasata sake dagowa ta kalleshi

"mr.... Yama sunan?

Well, whatever. I think tunda mungama fuskantar juna yakamata musan inda dare yaimana ko? As you can see am sleepy already, ko da wata maganar ne?"

Cije lower lip dinshi kawai yayi ya Janye idanunshi akanta

"No, I don’t think so" yafada saikuma yatashi tsaye yana pocketing hannayenshi
"Good night"

"yeah, mu kwana lfy" tafada itama batareda ta kalleshi ba


Zuwa yayi ya wuce ya bude kofa ya fita ya maidota da qarfi har Saida zee tadan dode Kunnuwanta

"stupid fool!" tafada tana bin kofar da harara tareda jan dogon tsaki

Sai kuma tahau Dariya, wai jajjaye yakeso gashi shi kamar gawayi, saikuma ta cigaba da Dariya tana tunanin yan wahala fa yawa garesu a duniya, ita ko dauramata shi akayi a qafa saita kwanceshi ta yar don babu abinda zatayi dashi

Tsaki tasake ja sannan ta miqe tafito itama daga dakin ta nufi cikin gida


Luckily babu kowa falon Hakan yasata hayewarta sama ta maido dakinta ta rufe ta cire gown din saman nightie dinta ta qure a.c ta baje tana fesar da iska daga bakinta.

Bata dadeba ahakan barci yayi gaba daita saboda dadin iskar dake shigarta


*WASHEGARI*


Zaune take tana waya da Deen daketa yimata mita wai jiya yaita kiranta bata dagawa har hakan yaja yakasa samun isashen barci itakuma tana yimashi Dariya

Jitayi anyi knocking din kofarta aka bude aka shigo

Ganin daddy ne yasata saurin katse wayar batareda ta shirya ba ganin yanayin daddyn

"Daddy?"

"Why? Meyasa zaki yimashi haka? Yes nasan bakya sonshi amma abin har yakai kicimashi mutunci? Beci yaci arziqin mahaifinshi ba Zainab?"

Gaban zee ne yafadi Hakan yasa ta saukar da kaffafunta qasa ta miqe tsaye

"Dad meke faruwa ne?"

"look, karma ki fara, nasan ki nasan halinki, tsaf zaki iya finma abinda yace"

"daddy ni me nace? Shi be fadamaku abinda yace ba? Wai he hate Africans wai bayason baqar mace?

"koma me yace be kamata ki kirashi da dabba ba ko don albarkacin amincin dake tsakaninmu da mahaifinshi"

"dabba? Ni yaushe na kirashi dabba daddy?"

"kin fini sani tunda ke kika fada don nasani tsaf zaki fadi fin haka amma ko babu komai ya kamata ko beci darajar mahaifinsa ba ni yaci daraja ta tunda ni na gayyatoshi"

"daddy.." tafada cikin rawar murya idanunta na kawo kwalla

"ba komai ai, laifinane, kinriga kince bakya sonshi nikuma na saki kije wajenshi dukda Hakan, babu komai, tunda baki sonshi fine, bazan tilasta miki shi ba, kije ki samo wani na aura miki amma banda wannan yaron, kin dai jini ko? Banda wannan yaron ko wani talaka irin shi don bazai ta6a yiwuwa ba, so ko shi ke zugaki that won't change anything bazan ta6a hada zuri'a da tallaka ba wlh, tsakanina dasu sai kyautatawa da taimako idan naga dama amma bana alaqa ta surukantaka, never!"
Yana kaiwa nan yajuya yabar dakin a fusace


Binshi da kallo zee tayi harya fice ya maido mata kofarta


Ahankali tayi baya baya ta zauna jagwab kan gadonta tana sauke numfashi ahankali

_meke shirin faruwa daita ne?_

_meyasa wannan case din data raina keson girmama?_

_what went wrong?_


Hannu tasa ta shafo kanta zuwa baya cikin tsananin damuwa

Tanaji tana ganin wayarta nata ringing da tone din Deen Amma takasa dagawa... ✍️


Ummin fasihu 🧚🏻‍♀�
8/2/21, 9:38 PM - Buhainat😝: *🙍🏻‍♂️DEEN 🙍🏻‍♂�*


Hhh yau ga post din dare, Gaskiya yau typing ya wahalar dani 🥺


*046*


*THE CHALLENGE 2*


Wunin ranar haka ta qarasheshi rai a jagule, kwata2 tarasa abinda ke mata dadi.


Sosai fushin daddy da alwashinshi ya tsoratar da ita abinka da bata saba ganin haka ba


Da mummy ce tazo tayi mata wannan hargagin bazaiyi tasiri a ranta ba kamar yadda na daddy keyimata yanzu don ita mummy dama ta saba da ganin Hakan agareta amma daddy zata iya cewa tunda tayi wayau bazata iya tuna ranar da ya ta6a yimata fada ba shiyasa yanzu abin ya dameta fiyeda zatonta


Yinin ranar haka tayishi a dakinta ko abinci akazo akayi mata Maganarshi Saidai tace a hauro mata dashi sama kuma cikin sa'a mummy bata tankamata ba akan hakan, qila itama fushin takeyi


Wayarta kau kasheta tayi don tasan Deen bazai barta ta numfasa ba da kiraye kirayenshi gashi ita bata cikin mood din Waya dashi kwata2 don batama son ya fuskanci wani abu gameda abinda ke faruwa


Da daddare bayan wajajen 9:14pm tafito daga dakinta, tasan yanzu daddy na can yana kallon news while mummy na dakinta tana shiri

Dama wannan lokacin ta ware don tasamu daddy suyi magana takuma bashi hqr akan abinda yafaru.


Saukowa qasa tayi ta fita daga part din gabadaya ta nufi part dinshi tana saqa da warwara akan abubbuwan data shirya zata cemashi.


Doorbell ta latsa sau biyu a na ukun ne taji muryar daddy ta cikin dakin yana bada izinin Shigowa


Saida taja numfashi ta fesar sannan ta murda handle din ta tura kofar ta shiga da sallama.


Dagowa daddy yayi daga kallon labarai da yake a t.v yana amsa sallamarta


Ahankali ta qaraso cikin dakin cikin sanyin jiki tana jin hawaye na kawomata

Daddy kau kafeta da idanu yayi harta qaraso tsakiyar dakin Hakan yasa ya miqamata hannu alamun tazo ganin Hakan yasata da saurin qarasawa ta riqe hannunshi ya zaunar daita gefenshi


Dora kanta tayi a kafadarshi tafara sheshekar kuka ahankali Hakan yasashi dan rungumota a jikinshi yana rarrashinta ahankali


Saida ta dan tsagaita kukan nata sannan daddy yace
"am sorry shaleleta, nine ko?"


Ahankali ta girgiza kai
"nice daddy"


"bake bace, nine. I shouldn't have yell at you" yafada yana shafa kanta ahankali cikin sigar rarrashi


"A'a daddy, duk ni naja ai, da ban biyemashi ba Amma naji haushi ne dayace wai beson Africans bayan shima African din ne
Shiyasa nikuma nace mashi bana son wanda baya kishin kansa bare asalinsa don ni bana masu kallon mutane, shikenan fa abinda nace" tafada cikin muryar kuka


Murmushi daddy yayi ya sake rungumota a jikinshi
"na yarda dake daughter don baki yimin qarya, I know you amma kuma shima ai ba qarya yayi ba, baki fito fili kika kirashi da dabban ba amma shi ya gane abinda kike nufi tunda ba qaramin yaro bane, idan bakayima mutum kallon mutum ba To kallon dabba zakayi mashi cikin dayan biyu amma babu komai, karki damu nima dazu don raina ya 6aci ne shiyasa kikaga nayi reacting haka amma kar Hakan ya dameki, komai ya wuce, shima Alhaji Abubakar din be dauki abin da zafi ba tunda ko dazu muna tare dashi, so no need to worry"


Dagowa tayi ta kalleshi da watery eyes dinta fuska a marairaice tace
"daddy ka yafe min?"


Dariya daddy yayi
"ni dama ai bakiyimin komai ba, kima bar damun kanki kinji, pretend nothing happened"


Murmushi tayi cikin jindadi taqara kwantar da kanta akan kafadarshi tana lumshe idanu shikuma yayi mata kiss a tsakiyar kai sannan ya maida hankalinshi ga kallon dayakeyi


Shiru dakin ya dauka na wani lokaci babu abinda ke tashi dakin sai muryar yar jaridar dake karanto labaran duniya cikin t.v din.


Daddy hankalinshi kacokam yana kan news din itakuma zee saqa da warwara take akan yadda zata tado maganar Deen Amma takasa sanin ta ina zata fara


Haka sukaita zama har Saida aka gama news din

Ganin dai wannan shine daidai lokacin daya kamata ta tado maganar don mummy na iya Shigowa a kowanne lokaci yasata dan muskutawa ta daga kanta daga kafadarshi

"yadai? Barci ko?" inji daddy cikin kulawa

Murmushi kawai tayi sannan ta kuma sauke idanunta qasa tana wasa da yatsunta ta Wani yi kalar tausayi

Ganin Hakan yasa daddy riqo hannunta datake wasa dashi din yace
"tell me, wani abu ke damun ki?"


Shiru tayi kuma bata dagoba

Qara squeezing hannunta yayi
"tell me" yafada a tausashe


Hadiye wasu yawu ahankali sannan tace
"daddy, dama...maganar Deen ne.... Please daddy.."

"I thought mun riga munyi closing wannan chapter dake" daddy ya katseta da fadin Hakan


"daddy, wlh Deen beda matsala ko kadan, he's very nice and innocent, gashi yanada ilimi both boko da Arabic and he loves me so much more than I did to him"


"so? Don duk yanada wadannan abubbuwan Hakan na nufin zai iya riqeki? Anacin ilimi ne? Ko ana saka kyawawan hali? Meye aikinshi? Nawa yake samu a wata? Sune abubbuwan daya kamata ki gayamin"


"daddy he's still under-graduate wannan shine last year dinshi a school kuma yace min yana practicing carpentry work irin na funitures yana dan samu anan kuma ai kafin lokacin yagama school nasan ma yasamu aiki"

"carpentry? Nufin ki kafinta zaki aura? Diyar dan faranshi a matsayin matar kafinta?"

"daddy I told you zai samu aiki kafin lokacin" tafada kamar tayi kuka


"yaushe? A wannan Nigeria din kikeda yaqinin samun aikinshi da wuri? Masu kwallin degree har masters nawa ne ke kan titi Suna yawo kullum don neman aiki? Wasunsu sunfi shekaru biyar suna buga bugar neman aikin haryanzu basu samuba, ahaka zakiyita jiranshi har saiya samu aikin wanda allah kadai yasan lokacin?"


"Daddy, kana da companies dayawa, yanzu haka akwai dayawa dakake ginawa, kullum cikin daukan ma'aikata kake, a ganina samun aiki bazai yima wanda nakawo wajenka a matsayin wanda nakeso wuya ba don ko wasu nakawo Koda bansansu ba kawai nayi niyyar taimakonsu nakawosu wurinka gani nake zaka iya sama masu aiki a cikin kanfanoninka bare wannan"


Murmushin manya daddy yayi
"yanzu na gano komai, kuma na tabbatar da abinda nake zargi.

Wato dama don kudinki yake sonki, don yasan ke diyar wani ce wanda idan ya ra6a yasan zai kwashi arziqi, tunda harya fara sanya maki tunanin ni zan samomashi aiki"

"haba daddy" zee tafada hawaye na kawomata

"wlh daddy, kaji na rantse? Bamu ta6a wannan maganar dashi ba hasalima bayada kwadayi ko kadan wlh, abin hannun mutum be cika damunshi ba"


"haka zai nunamaki ai amma a zuciyarshi akwai wata manufa ta daban, auran jari yakeson yi dake yadda shima zai ra6i arziqi, nawa akayi? Nasha ganin irin case dinnan a wurare da dama, sai yaro yazo ya hurema diyarka kunne ya kasance ta aminta dashi dari bisa dari, ta nace sai an aura mata shi sai angama sannan tazama itace abin wulaqantawa na farko a Wurin shi sannan kuma yafara planning yadda zai handame komai nata yadawo qarqashinshi, that's it, that's their aim"


Hawaye sosai zee keyi tunda yafara maganar

"haba daddy, why zaka siffantashi da wadannan munnanan aiyukan? Don baka sanshi bane, da kasanshi da bazaka ta6a fadin haka akanshi ba" tafada cikin kuka

"kema ai iya abinda yakeso kisani gameda halinshi yabari kika sani, dama bari zaiyi kisan qudurinshi? Koko cemaki akayi hali a fuska ake ganewa, Zainab you're too young, bakisan komai ba a rayuwarnan.

Ni nasan duniya kuma nasan mutanen cikinta, huldata ta yau da kullum yasa nasan mabanbantan halayen yan Adam

Ba kowanne murmushi ke amsa suna murmushi ba, wani murmushin na mugunta ne, don mutum yayi looking innocent ba hakan na nufin he's innocent din har cikin zuciyarshi ba

Kin riga kin makance a soyayya, ya riga ya burkita tunaninki, bazaki iya gane komai ba yanzu don bakya a hayyacinki

amma ni ina a hayyacina kuma bazan ta6a folding hannayena ina kallonki ki fada halaka ba, never!

Don Haka ma mubar wannan maganar don rayyuka ne kawai zasu 6aci don abune da bazai ta6a yiwuwa ba"


Kuka sosai zee keyi, tama rasa abinda zatace

Bata ta6a sanin haka akeji ba idan akaqi fahimtarka, bata ta6a sanin haka akeji ba idan aka soki masoyinka ba aka laqamashi abinda kasan bazai ta6a iyawa ba


Wai Deen daddy ke cewa saboda kudi yake sonta, yaudararta kawai yakeyi saboda kudinta, how? Mutumin da abin duniya basa gabanshi? Be damu da abin hannun mutum ba? Tayaya?


Shigowar mummy da sallamar ta yasa duk suka dago suka kallo kofar


Mummy tadanyi Jimm ganin expression din fuskokinsu, zee idanu jajur ga hawaye a fuskarta shikuma daddy alamun 6acin rai a fuskarshi


Qarasowa tayi cikin dakin Hakan yasa zee miqewa tsaye

"Saida safenku" tafada idanunta a qasa sannan ta juya ta fice dakin


Binta da kallo duk sukayi harta fita

Maida kallonta mummy tayi akan daddy Saidai ko damar yin magana be bata ba shima ya tashi ya nufi bedroom dinshi rai 6ace.


Da gudu ta nufi gadonta ta fada akai ta cigaba da kukan datake


Tarasa meyasa daddy bazai tsaya ya fahimceta, tarasa meyasa daddy yayi ma abin mummunar fahimta.


A ranar barci rabi da rabi tayi sai can gab da asuba wani barci mai dadi ya dauketa Hakan yasa Saida mummy tasha wahala kafin tasamu ta tashi sallar asuba.


Koda tagama komawarta barci tayi bata farkaba sai wajajen 8:30am shima don mummy ce ta sake tadata.


Wanka tashiga tayi sharp sharp tafito ta shirya ta tsara makeup dinta sannan tafito cikin shirin school ta sauko qasa


A falo ta tarar da mummy, gaidata tayi ta amsa sannan ta nuna mata dining area tace taje tayi break

Babu musu tawuce don tasan dole tayi inba haka ba ranta ne kawai zai 6aci a banza


Tadan ci babu laifi sannan ta taso tazo tayiwa mummy sallama sannan tafice.


*UMYU*


Qarfe 9 da yan mintuna suka isa makarantar


Tana jin anyi parking ta bude lumssasun idanunta ta dan kalli waje sannan ta miqe zaune daga jinginen datake da kujerar motar ta tsaida waqar datake ji ta bluetooth din kunnenta


Jitayi an bude mata kofa Hakan yasata daukar jakkarta tafara yunqurin fitowa.


Dago kan da zatayi sai taga ashe Deen ne ma ya bude kofar, yana tsaye riqe da murfin motar yana kallonta


Dan wara idanunta tayi alamun dama kaine

Shikuma yayi mata murmushi tareda ja da baya yana bata hanya don saukowa


Ahankali ta sauko tana kallon smiling face dinshi tana jin damuwarta na yayewa a hankali.


Saida ta ida fitowa sannan ya maida kofar ya rufe sannan ya juyo wajen ta yana mata murmushi yace
"Good morning"

Murmushi kawai tayi mashi sannan tace
"ya weekend?"

"Bad.. That's the most boring weekend I've ever had"


Dan wara idanu tayi
"dagaske? Meyasa kace haka?"


"zan gayamiki, but first mutafi tukkuna"

Hannu ya miqamata yana dan russunawa
"may I?"


Tasan abinda yake nufi Hakan yasa tabashi jakkarta itama ta miqamashi hannu ya doro mata littatafanshi akai


Murmushi sukayima juna sannan suka nufi cikin school din.


Basu yada zango a koina ba sai library don dama yau sunyi zasu dan ta6a karatu

Kwana biyu soyayya ta hanasu karatu, da sun zauna sai su bige da firar soyayya before you know it lokaci ya tafi hakan yasa suka yanke shawarar fidda ma kansu timetable din karatu inda zasuyi scheduling komai yadda ya kamata.


Usual seat dinsu suka zauna kowa na ajiye abin hannunshi bisa desk


"Tundazu nake jiran zuwanki"

"to? Amma ai am not late ko?"

"you're not late amma son ganinki ne yasa naga kamar kinyi late din"


Murmushi zee tayi batace komai ba


"how's your weekend?"

"cool.. Kaifa?"

"not that cool" yafada yana yatsine fuska

"why not?"


"I was missing you, most especially muryarki, wai me yasamu wayarki?"

"kajita kashe jiya?"

"yes, tunda mukayi wayar nan da safe naketa neman wayarki amma shiru, what's wrong?"


"matsala tadan samu shiyasa, muna cikin waya ta dauke sai screen din yabar kawo haske sai kawai na badata aka gyaromin" tafada tana daukar jakkarta dake gabanshi ta fara zuge zip din


"ayyah, I thought as much. But are you sure you're ok?"


Dagowa tayi daga bude jakkar datake
"Me ka gani?"

Daga kafadu yayi
"kawai naga kamar you're not ok ne, kinmin wani iri"

Murmushi kawai tayi ta cigaba da leqa jakkarta

"then idanunka sun fara ciwo" tafada cikin tsokana

Murmushi shima yayi yace
"babu mammaki"


Ciro handout da wani littafin tayi tana cewa
"yanzu dai mufara, karka shagalar damu da surutunka"

Harararta yayi yafara Ciro Littafi shima
"ni dake wa yafi surutu?"

"ni dakai"

Dariya sukayi atare sannan duk suka bude Littatafan suka fara duddubawa


Sun dan jima ahakan kafin lokacin shiga lecture din zee yayi ta wuce ta barshi anan shima yana duba nashi Littatafan kafin shima lokacin shiga class din nashi yayi shima ya tashi.


Babu laifi zuwanta school a yau ya ragemata damuwarta sosai kuma ta cigaba da iya qoqarinta wajen 6oye damuwarta don ganin Deen be fahimci komai ba dukda dai yini yayi yana mata mitar shidai sai yaga kamar she's not ok

Abin na bata mammaki don sosai take qoqarin pretending komai is ok amma sai yace tayi wani iri kamar something is wrong, idan yace Hakan saita tsokaneshi akan qila idanun ke buqatar doctor sai suyi Dariya Hakan kuma bazai hana yasake yimata maganar ba idan yasake kallon fuskarta.


Sai wajajen 3pm bala yazo daukar zee


Har motar Deen ya rakota kamar yadda suka saba tun bayan fara soyayyarsu


Shi ya bude mata kofar tashiga sannan ya rufo mata yana cemata sai sunyi waya

Kada mashi kai kawai tayi tana murmushi


Dage tinted glass din motar tayi takoma ta jingina da kujera tana kallonshi

Jin an tada motar yasa Deen dake waje fara daga mata hannu dukda baya hangenta


Bïñ hannun tayi da kallo tana kallon band din data dauramashi ranar valentine

Saita maido kallonta kan nata itama

Ahankali ta danna dan botton din fuskar abin yakawo wuta
_*DEEZEEN 💞*_

tasake dannawa

_*TOGETHER FOREVER ❤️*_


Murmushi tadanyi ta dago tana kallon Deen jin motar tafara tafiya

Har a lokacin daga mata hannu yakeyi har Saida suka fita daga school din


Ajiyar zuciya ya sauke sannan ya maida hannayenshi cikin aljihu yana cigaba da bin inda suka bi suka fita da kallo kafin daga baya yajuya yakoma inda yafito.


Tun daga ranar da sukayi magana da daddy tashiga wasan 6uya dashi


Idan tasan yana wuri bata yarda tafito wurin haka ma idan ya ritsata gaisuwa ce kawai a tsakaninsu babu irin wannan wasan nasu


Da farko tayi tunanin itace ta dauke mashi wuta sai daga baya taga ashe shima Hakan take a wajenshi don maimakon ya damu kamar yadda yasaba yi duk lokacin da take fushi akan abu sai taga tayi biris daita kamar ma besan tana yi ba wanda Hakan na nuna alamun babu gudu babu ja da baya a Maganarshi.


Hakan yaqara sakata cikin damuwa, don tasan muddin aka rabata da Deen to rayuwarta ta tagayyara don Deen shine farincikinta, idan babu shi zata qarasa rayuwarta ne babu ko digon farinciki.


Ta rasa yadda zata 6illowa daddy ya fahimceta yakuma fahimci Deen don taga alamun ma kwata2 Deen be yimashi ba don ko Maganarshi bayason ana tadawa a gidan.


Rannan data rasa yadda zatayi saita yanke shawarar samun mummy da maganar

Batasan ra'ayin mummy akan wannan case din ba amma sai taga kamar mummy na son za6inta duba da yadda bata nuna rashin amincewa ba akan Hakan kamar yadda daddy yayi.


Ranar Saida tagama sallar asr sannan ta tashi bayan tagama bitar abubbuwan dazata gayawa mummy din


Direct dakinta ta nufa don bataji fitowarta ba Tun bayan shigarta sallah


Ahankali tafara knocking acikin zuciyarta kau tana addu'ar samun nasara

Tasan idan har mummy ta goyi bayanta to abin zaizo da mugun sauqi don zatasan yadda zatayi convincing din daddy kamar yadda tasaba a abbubuwa da dama.


Saida tayi knocking uku sannan aka bata izinin shigowa


Ahankali ta murda handle din ta tura kofar tashiga da sallama a bakinta


Mummy dake ninke sallayarta ta dago ta kalleta ta amsa sallamarta sannan ta cigaba da ninkinta ta ajiye a ma'ajiyarta.


Qarasowa zee tayi jiki a sanyaye kamar ta allah sannan ta zauna bisa sofa dake dakin


Zama itama mummyn tayi a gefen gadonta tana kallonta, kallo daya zakayimata kasan tana cikin damuwa

"yes? Meya faru ne?" inji mummy a tausashe


Hakan yasa taji zuciyarta na raunana


Shiru tadanyi tana jujjuya abinda zatace sannan ta dago ta kalli mummyn

"mummy... Dama akan.. Maganar Deen ne.." saikuma tayi shiru


Itama mummy shiru tayi tana kallon ta kawai

"mummy, daddy kwata2 yaqi fahimta ta, wai saboda kudi Deen kesona kuma wlh ba Haka bane hasalima shi bema damu da abin mutum ba, idan ma ka bashi baya son amsa.

Deen na sona sosai mummy, bazai ta6a yaudarata ba kamar yadda daddy ke cewa saboda bema san yadda ake yaudarar ba

Babu ruwanshi, he's so innocent, shine silar gyaruwan wasu daga halayena marassa kyau, shi yafara saitani a hanya mai kyau batareda nasan saitanin yake ba.

He's always there for me, yana taimakona a karatu sosai mummy, sosai.

Shi yafara sona tsakaninshi da allah tun kafin ma yasan sona yake.

A school babu mai sona harta wadanda nakema daukar qawaye, duk kowa qina yake sai shi kadai dukda abubbuwan danayi mashi marassa kyau"


Saita fara bata labarin farkon haduwarta dashi dakuma haduwarsu ta biyu da abinda yafaru

Ta cigaba da bata labarin yadda ta maida shi errand boy dinta har zuwa lokacin da case din assignment dinta ya hadasu da kwanciyar asibiti data jamashi

Ta gangaro zuwa yadda suka shirya dakuma yadda yafara nunamata kuskuren da takeyi har ta gangarowa zuwa ranar da abinnan yafaru tsakaninta da master.


Labarin take badawa tana kukan da batama san tanayi ba

Ta cigaba da cewa
"mummy har waya na siyamashi lokacin da za'a sallameshi ganin bayada waya tashi ta fadi a wancan ranar amma yaqi amsa Saida nayi fushi sosai sannan ya amsa kuma bama amfani yake daita ba don tun daga ranar ban qara ganinshi da ita ba

Be ta6a roqona yar biyar ba, kuma bayaso nabashi, ko tashi mukayi daga makaranta Saidai yayi min karyar akwai abubbuwan dazai tsaya yi a makarantar duk don kar nace yazo mu rage mashi hanya.


Mummy tayaya za'ace saboda kudina yake sona? Wlh ni nasani soyayyar Gaskiya yakemin mummy, idan narasa shi bazan ta6a samun wanda zai soni ko rabin son da yakemin.

Please mummy kisa baki, kema ai kinsan halinshi, he's very nice and obedient.

Aunty Feenah ma tasan shi da ita da yaya Auwal suma duk sunce yanada kyawawan halaye don su sukama gayyaceshi a bikin su kima tambayesu kiji, wlh babu ruwanshi, bazai ta6a yaudarata ba mummy"


Tunda tafara maganar mummy ke kallonta

Lallai Zainab, ba qaramin kamu soyayyar Deen tayimata ba, ji yadda tabi ta rikice


Ita dama tun a hospital tafara zargin Hakan amma sanin halin zee na high taste dinta akan namiji shiyasa bata ta6a kawoma ranta soyayyar ce dagaske


Ajiyar zuciya mummy ta sauke sannan ahankali tace
"Zainab, nima nasani, Deen bazai yaudareki ba Amma abinda nakeso kisani shine, baka kwallafawa ranka abu kace dole dole sai abin don Mafi yawancin abubbuwan da mukeso baya zama alhairi agaremu shiyasa allah ke musanya mana da wani abin, idan mukayi hqr sai kiga munci ribar haqurin.


Zanyi mashi magana kamar yadda kika buqata amma kuma inason kisa a zuciyarki koma menene idan har Kamal mijinki ne to saikin aureshi idan kuma ba mijinki bane ko duniyar nan zaki gayyato suyima daddyn magana Hakan bazai faru ba

Abinda nakeso ki dinga yi shine addu'a, ki dinga addu'ar allah ya za6amiki abinda yafi alhairi bawai ki nace Lallai lallai sai shi ba, idan shine yafi alhairi allah ya za6amiki shi idan kuma bashi bane to allah ya musanya miki da wanda ya fishi, kinji ko?


Kada kai tayi ahankali acikin zuciyarta tana cewa insha allah shine ma wanda yafi alhairin


Cigaba da yimata nasiha mummy tayi mai kwantar da hankali wanda Hakan ya rage mata kaso Mafi yawa na damuwar ta kafin daga baya ta sallameta akan zata sameshi tayi mashi maganar, kawai tayi addu'ar allah yasa ya gane don ita tana maraba dashi a matsayin suruki don hallayarshi ta dade tana burgeta.


Da wannan zee taqara samun qwarin gwiwa, tashiga addu'ar allah yasa qarshen case dinnan kenan, allah yasa ya fahimta.


***


Suna Kwance suna dan fira irin na kafin barcin nan cikin nishadi

Mummy nata son yimashi maganar su Deen Amma tarasa ta ina zata fara don a kwana biyun nan ta fuskanci idan akwai maganar wanda ke 6ata mashi rai to na Deen ne


"jiya ma munyi waya da Ummu batool ai tace tana gaisheka wai ta nemi number ka bata shiga" inji mummy


"ita ta nemi number ta Ko ni na nemi number ta? Tunfa shekaranjiya nake neman number ta bata shiga" inji daddy


"nima haka nace mata don nima na nemeta ban samu ba wai ashe layi ta chanza, jiya ma da sabuwar number ta kira"

"ayyah to duk ya suke? Yasu batool?"

"Duk suna lfy lau ai har gaisawa mukayi da batool shi yayan nata ne bayanan yana wajen aiki"

"ai wadannan yaran naso naga lokacin da zasu dinga zuwa nigeria frequently musanmman babban, rabonshi da nigeria ai za'ayi shekara biyar ko?"

"ko fi ma, ai kasan halin aikinsu they're always busy gwara gwara batool ita ana dan zuwa daita dukda itama wani sa'in school na hanata zuwa"


"ai babu komai, insha allah lokaci zan fidda mu kwasa dukanmu muyimusu zuwan bazata"

Yar Dariya mummy tayi tace
"dakau mun kyauta, ai yakamata a dinga tunawa da zuminci ko yaya ne bawai business ba kowanne lokaci"

"to? Dani ake kenan?"

Yar Dariya taqara tace
"ni bance ba Saidai idan tsarguwa kayi"


"har tsarguwar ma nayi tunda nasan dani ake"

Dariya sukayi sakeyi atare


Shiru yadan biyo baya

"diyarka fa nacan, kodayaushe very moody, abinci ma saina tilasta mata takeci, na rasa gane kanta"


Nan take mood din daddy ya chanza

"ai dole kiga Hakan tunda tana can kullum wancan yaron na zigeta"


"Yana zigeta kamar ya?"


"hmm, ai duk motsinsu yanzu akan kunne na yake don tun ranar da mukayi maganar qarshe akanshi daita nasamu balarabe nayi mashi Tambayoyi akansu yace min shidai ada lafiya lau take huldarta ita daya amma daga baya ya dinga ganin yaron na liqemata wai har budemata mota yake idan zata shiga ma Hakan wai harda riqe mata jakka.

Bayan naji daga gareshi na sallameshi na kuma samu wani akan ya dinga samin ido akansu a school din and the same amsa dasamu dana bala harda ma qari wai duk inda zataje yana maqale daita har hotunansu ma Saida ya daukomin don su zama evidence.

Gabadaya ya shiga rayuwarta kullum da irin zugar da yake mata yana huremata kunne yana nuna mata wai sonta yake itakuma dayake she's dull takasa ganewa, mataki zan dauka akai tsatsaura kau, lokaci kawai nake jira" yafada cikin 6acin rai


Kan mummy ya kulle

"ni sai inga kamar wannan duk misunderstanding ne, yaron is very calm and quiet, kamar bazai iya Hakan ba"


"hmm wai ke kenan da kike babba bare ita da take qarama, kice inbar ganin laifinta don bata gane abinda nake nusar daita ba tunda kema gaki kin gaza ganewa"

"ba Haka bane Alhaji, Zainab ta sameni tagayamin komai kuma da gamsu dasu, wlh daddy a kallo daya idan kayima yaron zakasan yanada nutsuwa sosai, bakaga Zainab ta chanza ba taqara hankali a yan kwanakinnan? Tafada min duk shine sila bayan Hakan ga siyarda rayuwarshi dayayi wajen cetonta a wannan incident din nasu a school, da ba don shi ba da wani labarin mukeyi daban yanzu"


Daddy dayayi sakato Tundazu yana jinta ya girgiza kai cikin takaici
"ansha fadamin mata basuda hankali amma ban ida yarda ba sai yanzu.

Wato ta nan kuma ya 6illo? Dama ai shi tallaka be ta6a taimako don Allah ba, dole don ribar kanshi yakeyi Yayinda mu kuma sukeso mu kyautata masu don Allah

To idan maganar taimakon ta dayayi ne yazo yayi naming price dinshi ko nawa yakeso zan bashi, ladar taimakonta dayayi, ba shikenan ba?

Yazo ya fadamin ko nawa yakeso zan bashi amma wlh diyata tafi qarfinshi, diyata matar manya ce!

Kuma shiriya ta allah ce idan baki sani ba, dama can nasha gayamiki yarinta ke damun ta zata bari kece baki yarda ba shine kuma yanzu da shiriryar tazo zaki alaqanta ta da wani can, dama mutum ke shirya mutum ba allah ba?"


Mummy da duk ranta ya jagule akan magangganun da daddy ke fadi tace
"Alhaji ba Haka bane..."

"to yaya ne? Yaro yabi ya kallalameku da qarya da komai kun yarda dashi?

Nifa matafiyine mai shiga jama'a daban daban mai kuma hulda da juma'a masu mabanbantan hallaya.

Na fiku sanin me duniya take ciki.

Ke kanki kinsan case din Alhaji Hassan da surukinshi wanda haryanzu abu yaqi ci yaqi cinyewa

Shima ba ta wannan sigar yazo ba ya kwantar dakai ya ruda diyar mutane aka bashi ita

Yanzu kullum gasucan hanyar court suna sintiri ya danne duka dukiyarta yasa ta chanza komai nata da sunanshi ya handame komai, ko zakice baki san da Hakan ba?" yafada cikin hayayyakowa


Shiru mummy tayi takasa cewa komai

"shifa tallaka a duniya bayada babban maqiyi kamar mai arziqi don gani yake be kamata shi a hanashi ba wasu kuma abashi besan komai ikon allah ne ba muma bamu mukayi wa kanmu ba.

Kullum burinshi tayaya zai ra6emu ya kwashi na kwasa ya gudu

Babu wata soyayya a tsakanin tallaka da mai kudi duk qarya ce don kowacce qwarya da abokin ragayarta.

Idan har kikaga Hakan to akwai cuta aciki musanmman irin wannan case din da ita macen itace mai kudin, dama ace namijin shine mai kudin da da sauki don ana saran zai iya controlling dinta amma a wannan case din fa? Ita kanta kacokam a qarqashinshi take inaga maganar dukiyarta?

Saboda haka na riga na ajiye magana kuma ta ajiyu

Tunda kika ga nayi burus daita dukda nasan halin datake aciki Hakan ya isa ya nuna miki babu gudu babu jada baya a wannan maganar don bazan ta6a barin inzama silar cutar da diyata daya da allah yabani ba.

Don haka taje taita nema, ni ba matsa mata zanyi ta kawo miji dawuri ba, she should take her time wajen Fiddo wani responsible one bazan damu da tsawo lokacin dazai dauka ba Amma batun wannan yaron abu ne da bazai yiwuba wlh.


Kuma shima zan sameshi, zan bashi damar rabuwa daita ta lallama idan kuma yaqi zan gwadamashi true colour dina, zai gane ba kowanne mai kudi ake jadashi a wanye lfy ba"

Yana kaiwa nan ya juya ya gyara kwanciyarshi ya rufe jikinshi har kai ranshi na qara 6aci yana kuma qara jin tsanar Deen a zuciyarshi


Shiru mummy tayi takasa cewa komai, sosai ranta ya jagule taji komai ya sake kwa6e mata, batasan daddy yayi nisa har haka ba, nisan da bazai ta6a jin kiraba inba wani iko daga allah ba.


Gyara kwanciyarta itama tayi ta lumshe idanunta batareda ta qara cewa komai ba ta cigaba da saqa da warwarar wannan rikittacen al'amarin a zuciyarta... ✍️


Ummin fasihu 🧚🏻‍♀�
8/2/21, 9:38 PM - Buhainat😝: *🙍🏻‍♂️DEEN 🙍🏻‍♂�*


*047*


*THE PROMISE*


Washegari Zee tayi ta jiran feedback daga wajen mummy amma shiru don ko makamanciyar maganar mummy bata tadomata ba

Haka ta haqura ta wuce school ranar tana tunanin qila bata kaida yimashi maganar ba, haka ta haqura a zuciyarta tana fatan koma da yaushe zata mashi maganar allah ya dorasu a kanshi.


A school ma ranar tare suka wuni da Deen wanda bayada lecture ma kwata2 a ranar kawai zuwa yayi don ita.


Sunyi karatu sosai don yanzu sun koma kamar da karatu suke babu kama hannun yaro don exam is at the corner dukda da dan saura ga lokacin.


Sai bayan zuhr sukayo gida inda su zee ne suka fara tafiya sannan shima daga baya yafito yasamu abin hawa shima ya wuce unguwarsu.


Deen hankalinshi Kwance yake gudanar da al'amuranshi don ko kadan besan abinda ke faruwa ba a 6angarensu zee ba.

He never saw anything like that coming shiyasa yake gudanar da al'amuranshi hankali Kwance.


Ya dade yana daily addu'o'in shi daya saba duk bayan kowacce sallah sannan ya shafa.


Saida ya dan qara yin Jimm a masallacin kafin daga baya ya tashi ya fito.


Babu mutane sosai a wajen masallacin Hakan yasa ya zura takalminshi kawai ya fito daga masallacin don komawa gida don dama shi daga masallaci sai gida, salmanu yasha tsokanarshi wai kamar mace ko irin fitowa wajen mai shayi beyi yadan rage dare yafison daya gama sallar isha'i yakoma ya qunqume gida kamar matar kulle

Shidai be ta6a tanka mashi ba Saidai yayi Dariya kawai a wuce wajen don shi bejin zai iya wannan zaman na majallisar mai shayi duba da yadda kodayaushe wurin ke cike da matasa anata hayaniyar cafta irin nasu na maza, shi idan yaje ma ai ciwon kai zai jama kanshi a banza saboda hayaniyar wajen, gwara shi salmanun dayaga zai iya yayi.


Tun daga nesa ya hangi wata mota parke a daga dayan gefen santarsu daidai gaban gidan Mallam Nasiru


Be kawo ma ranshi komai ba ya cigaba da tahowa kai a qasa yanata lissafe lissafe a zuciyarshi


Daidai yayi hanyar shiga gidansu yaga an dallareshi da hasken motar

Dan juyowa yayi yana kallon motar yana dan kare fuskarshi saboda yadda hasken yayi reflecting din fuskarshi

Kamar kau mai motar ya sani sai gani yayi an kashe hasken

Sake Juyawa yayi zai wuce aka qara dallaro hasken wannan karon harda dan horn Hakan yasa ya qara tsayawa ya juyo yana kallon motar.


Gani yayi an bude murfin mazaunin driver wani ya fito.

Tsayawa yayi yana kallonshi har ya tsallako 6angarenshi ya qaraso wajenshi sai a sannan ya lura da fuskar mutumin, bala ne drivern zee.


Qarasowa bala yayi wajenshi cikin fara'a ya miqa mashi hannu shima Deen ya miqa mashi hannu yana murmushi suka gaisa


"Tundazu muke nan muna jiranka, wani yaro yace mana kana masallaci"


Murmushi kawai Deen yayi tareda Kada kai alamun haka ne

"lafiya dai ko?" inji Deen yana kallon motar dake can gefen titin parke


"lfy qalau wlh, kawai Alhaji ne keson ganinka, mu qarasa idan babu damuwa yana ciki" yafada yana nuni da motar


Qara bin motar Deen yayi da kallo sannan ya kalli bala yayi mashi dan murmushi yace
"ba damuwa, muje"


Atare suka sake tsallakawa dayan barin da motar take suka nufi inda motar ke a parke


Saida suka qaraso sannan bala yayi saurin Qarasowa ya bude back seat saiga daddy ya bayyana a zaune takardar jarida a hannunshi yana dubawa


Jin an bude kofar yasashi Dagowa daga kallon jaridar dayake ya kallesu.


"Gashi nan Alhaji" inji bala yana komawa daga baya yadda Deen zai bayyana ga Alhajin


Ganin daddy yasa Deen jin kunya don be ta6a tunanin shine ba

Fuska dauke da murmushi Deen ya zame qasa ya tsugunna yana gaida daddy cikin girmamawa.


Sai ji daddy yayi wani iri don rabon da ayimashi irin wannan gaisuwar harya mance

Sai kuma yayi saurin kawar da zancen a kanshi yana tuna tattaunawar da sukayi da Alhaji Abubakar dazu har yana cemashi talaka babu abinda bazaiyi ba na kwantar da kai duk don yasamu shiga domin suna iyayin komai don cikar burinsu.


Kawar da wannan tunanin yayi yashiga amsa ma Deen cikin fara'a yana cemashi ya tashi.


Tashin Deen yayi cikin sunkuyar dakai don shi harga allah kunyar daddy yakeji sosai


"zagayo abokina, zuwa nayi mu tattauna" inji daddy cikin fara'a


Gaban Deen yadan fadi da jin Hakan, badai yasan komai ba? Wayyo ya zaiyi da kunya?


Haka dai ya zagayo din kamar yadda ya buqata, ya bude kofar dayan gefen ya shigo ya zauna a darare yana dan wasa da band din hannunshi kamar irin amaryar nan idan ana siyan baki duk yabi ya takura.


Ajiye jaridar hannunshi daddy yayi ya gyara zama ya juyo yana kallonshi yana kallon yadda yakasa sakewa kwata2, sai yadanyi murmushi


"Kamal ko?" inji daddy yana kafeshi da idanu


Dagowa Deen yayi ya dan kalleshi sai kuma yayi murmushin tabbatar da Hakan


"Ina wuni Alhaji" yasake gaidashi a karo na biyu


Dan murmushi daddy yayi yace
"lfy lau, ya mutanen gida?"


"Duk suna lfy lau

"ya school? Ana dai maida hankali sosai ko?"


Murmushi Deen yayi yace
"insha allah daddy"


Shima daddyn murmushin yayi yana Kada kai
"to allah ya taimaka"


Da amin Deen ya amsa trying so hard wajen controlling nervousness dinshi


"dama wata yar magana ce takawoni wajen ka ko ince alfarma"

Dagowa Deen yayi ya kalleshi in surprise sai kuma ya maida kanshi qasa bece komai ba

"naji ance kai abokin yarinyata ne sosai kodayaushe ma kuna tare ko?"

Sake Dagowa yayi ya kalleshi again sai kuma ya sake sauke idanunshi
"eh daddy"


"dakyau, dama wata alfarma nazo nema awajenka akanta nasan kai kadai zaka iya yimin Hakan"

Shiru Deen yayi be kuma dagoba saima jin maganar daddy dayake wani banbarakwai, wai alfarma, ina shi ina yiwa mutum irin wannan alfarma?


"Dama akan Zainab ne, kwanan nan narasa gane kanta gabadaya, ta tsiro wasu hallaye da ba nata ba, bansan inda matsalar take ba ko itace ta chanza ko chanzata akayi oho?"


Qara Dagowa Deen yayi ya kalli daddy saikuma ya sauke idanunshi
"Wani abu takeyi ne?"

"Abubbuwa ma kai, lokaci daya yarinya ta chanza? babu irin wannan biyayyar ta da da jin magana ta, tabar saurarona ma bare tabi abinda nake nunamata"


Hankalin Deen ne yafara tashi kuma Hakan ya nuna a fuskarshi

"ya sallam! To meyasa?"

"nima shine ban sani ba Amma nafi kyautata zaton huremata kunne akeyi don ada ba Haka take ba.


Munyi maganar wani yaro daita, ita tama kawoshi da kanta tace tana so nakuma aminta da Hakan saboda yaron nagarttace ne sosai, yanada kyawawan hallaye ga tarbiya, yana sonta sosai itama tana qaunarshi


Lafiya lau muka tsaida magana da manyanshi akan idan tagama school za'a aura mashi ita

Amma kwatsam lokaci daya Abubbuwa suka fara chanzawa, bata saurararshi yanzu, bata bashi damar ganinta ko yin waya daita.

Tabi ta chanza a yan kwanakinnan duk mun rasa gane kanta, bata sauraron maganarmu sam bare tayi amfani daita kuma da ba Haka take ba, Zainab yarinya ce mai sauraron maganar iyayenta most especially ni amma yanzu ta chanza tayi fatali da duk tarbiyar da muka bata.

Mun rasa yadda zamuyi mata don sosai yaron yake cikin damuwa saboda yana sonta sosai amma duk yadda mukaso ta fahimcemu ko ta fahimtar damu meye matsalar taqiya.

Shiyasa danaji ance kai abokinta ne sosai kusan ma kullum tare kuke yasa na yanke shawarar zuwa wajenka wataqila ka iya abinda ke neman gagararmu"


Tunda Daddy yafara magana wutar Deen ta dauke diff, kanshi yafara jujjuya mashi ahankali, fadin tashin hankalin da zuciyarshi ta fada 6ata baki ne, jin magangganun daddyn yakeji kamar a mafarki


"shiyasa nazo wajen ka, please ka jawo ra'ayinta akan Hakan tunda naji ance kai abokinta ne, kana iya yin abinda mu muka gagara yi, ka kuma samata ido kaga ko wani ke zugata don ni nafi tunanin Hakan, ta yiwu wani ko wata ke zugata yana dorata a keken 6era da nufin kaita yabaro.

Please do this for me, kaji d'ana?" yafada yana kafeshi da idanu cikin son karanto yanayin dake fuskarshi kuma yasamu abinda yake nema don tsagwaron tashin hankaline rubuce all over fuskarshi


"bakace komai ba kamal" inji daddyn still yana kafeshi da idanu


Sai a lokacin Deen yadan qaqaro murmushin yaqe yahau yi

"insha allah daddy.. I'll try my best"

Murmushi sosai daddy yayi cikin nuna farinciki sosai

"yauwa d'ana, naji dadi sosai, allah yayi maka albarka, don Allah ka kulamin daita sosai, ka nusar daita sosai idan ma kaga alamun zugata akeyi to let me know, sai na tabbatar na koyawa munafukin hankali don na tsani munafurci kana gani na nan, duk yadda muke da mutum daya munafurceni to wlh nagama dashi kuma zamu sanya kafar wando daya ne dani dashi"


Kasa dago kai Deen yayi don jiyayi kamar ma dashi yake, gudu sosai zuciyarshi take acikin zuciyarshi yana lissafa cewa kenan shine mai huremata kunnen, da daddy yasan da Hakan da da wane ido kuma zai kalleshi?

Hakan yasashi jin duk ya takura, a zahiri sauraronshi yake amma a badini duk bayama gane abinda yake cewa.

Dakyar dai yasamu yagama magangganun shi yana kuma qara jaddada mashi ya taimaka mashi wajen ganin sun shawo kan matsalar.

Da insha allah kawai Deen ke amsawa batareda ya iya hada idanu dashi ba


Godiya sosai daddy yayi mashi yana Tambayar kaka shikuma yana amsa mashi da tana cikin gida


"to my regards to her"

Sai kuma ya karkata gefe ya shiga lalubar aljihunshi

Shidai Deen besan yana yi ba don kanshi na qasa haryanzu yana sake jujjuya magangganun daddy a ranshi


"ga wannan babu yawa" yaji daddy na fada

Dan Dagowa yayi sai yaga ashe kudi yake miqomashi


Dan murmushi yayi sannan ya girgiza kai ahankali
"A'a daddy, ngd qwarai"


"haba ka amsa mana" inji daddy

"don Allah daddy kabarsu"


"meyasa? Ko sun maka kadan ne?"

Sake Dagowa yayi ya dan kalleshi sai kuma ya sauke idanunshi

"ba Haka bane daddy, kaka batason haka, zatayi fada kayi hqr"


Dan ta6e baki daddy yayi ya maida kudin a aljihunshi

"to shikenan ai, babu damuwa, ngd kaji, please kayimin qoqari akan Hakan"

"insha allah daddy"

"bari mu wuce, dare sai qara yi yake"

"to" inji Deen yana fitowa daga motar dama bai rufe kofar ba


Maido mashi kofar yayi ahankali ya rufe yana mashi sallama da fatan isa gida lfy shikuma daddy ya daga mashi hannu kawai yana murmushi bala yaja motar sukayi gaba


Bïñ motar yayi da kallo harta fice daga layin nasu

Lumshe idanu yayi ahankali ya bude yana jin kanshi na wani irin saramashi.

Meke shirin faruwa ne?

Wanene Zainab keso har aka tsaida maganarsu?

Wake huremata kunne?


Bayada wanda zai bashi duk wadannan amsoshin Hakan yasashi Juyawa jiki a sanyaye yashige cikin gida.


Koda ya shiga Saida kaka ta tambayeshi dalilin dadewarshi awaje yau sai cemata yayi suna dan fira ne da salmanu.


Duk yadda yaso 6oye yanayinshi ga kaka Saida ta gano sauyin yanayinshi

Hakan yasata Tambayar shi meke damunshi, babu komai yace mata ganin zata matsa mashi yasashi cewa barci yakeji sosai jikinshi duk ciwo yake mashi.


Jin Hakan yasata gabatar mashi da abinci da sashi yadanci ba laifi sannan ta rakashi har daki ya kwanta bisa katifarshi tana jera mashi sannu.


Saida taga barci ya daukeshi sannan ta taso ta fito daga dakin ta cigaba da yan qananun aikace aikacenta don Allah ya taimaketa tunda marece sukayi tatar qullin kokonsu.


Saida tagama duk diminiyarta sannan ta daura alwalla tashige nata dakin itama ta rufo kyaure.


A bangaren Deen kau barci qauracewa idanunshi yayi, dama pretending yayi kamar yayi barcin don kaka ta kyaleshi tana fita ya bude idanu ahankali ya tsurama saman rufin dakin ido.


Ya rasa meke mashi dadi a zuciyarshi, ya kuma rasa yadda zai fassara magangganun daddy.

Dama zee tanada wanda takeso aka har aka tsaida magana dashi kafin yashigo da tashi manufar akanta?

Koko dai za6amata akayi daga baya?


Zainab na son mutumin dagaske kamar yadda daddy yace?

Koko shi take so?


Meyasa bata ta6a yimashi magana makamanciyar wannan ba?


Meyasa bata ta6a cemashi an tsaida maganar ta da wani ba?


Daren ranar Deen kasa rintsawa yayi saboda damuwa

Yarasa me keyimashi dadi, ya kasa Kamo bakin xaren al'amarin, yadda yaga rana haka yaga dare.


*WASHEGARI*


Still haryanzu mummy bata yimata maganarsu ba dukda kau kasa kunnen datake tayi tun jiya, abinda bata saniba shine bata kaiga gayamashi bane koko ta gayamashin Itadai ce bata bata feedback ba?


Tana son Tambayarta kuma tanajin tsoro Hakan yasata haqura ta cigaba da kasa kunne da jiran tsanmmani.


Shirin school tayi a gagauce don yau tanada morning lecture


Koda ta sauko breakfast tayi sama sama ta tashi tayi sallama da mummy tafito, babu 6ata lokaci suka shige mota ita da bala suka fice daga gidan.


*UMYU*


Koda ta isa school saura minti biyar su shiga aji Hakan yasa tayi ma ajin tsinke Direct


Mintuna 40 lecture din ya daukesu sannan suka fito daga class din


Rataya jakkarta tayi itama ta biyo ayarin masu fita daga class din itama tafito.


Direct wajen zamansu tanufa tana tafiya a gajiye tana tare goshinta da wani littafin saboda hasken rana dake reflecting goshin nata.


Tun daga nesa ta hangeshi zaune ya juya mata baya


Ahankali ta qaraso wajen tana kallon bayanshi tana jin soyayyar shi a kowane magudanar jininta


Ganin kamar besan da isowarta ba yasa ta qarasa bayanshi cikin sand'a ta dan duqa saitin kunnenshi tayi tafi da qarfi


Aikau firgigit yayi yayi saurin waigowa Hakan yasa tashiga yimashi Dariya tana toshe bakinta


Dan murmushi yayi sai kuma ya juya ya cigaba da kallon inda yake kallo

Qarasowa tayi ta zauna itama tana dan basu space tace
"scary mouse, har kaji tsoro ko?"

Kallonta yasakeyi ya danyi murmushi sai kuma ya qara dauke kai


"tunanin me kakeyi harna qaraso baka jini ba?"

Girgiza kai yayi batareda ya kalleta ba bece komai ba

"yaushe ka iso school?

Juyowa yayi ya kalleta again, ahankali ya bude baki yace
"dazu" a takaice


Tsayawa itama tayi tana kallonshi don sosai kallonshi yabata mammaki

Babu wannan fara'ar babu murmushi babu sakewa dukda fuskar ba adaure take ba but look dinshi is very formal.

"ya dai?" tafada tana kallonshi cikin ayar tambaya


kauda idanunshi yayi daga kanta yana cewa
"daidai"


"what's wrong?" tasake tambaya

Juyowa yayi yasake kallonta, kallon da yasa hanjinta dan kadawa don kallon yana dauke da ma'anoni daban daban

"babu, wani abu kika gani?" ya Tambaya yana cigaba da yimata irin kallon


Shiru tayi da farko saikuma tace
"kamar you're not alright"

Wani slight murmushi yayi sannan ya dauke kanshi, shima kamar bazaiyi magana ba sai yace

"am alright, kawai na gano wani abu ne"


"Wani abu? Wane abu?"


Yan tsakuwa ya tsinta a gabanshi qwara biyu ya tilla daya can nesa
"abinda ake 6oyemin" yafada yana tilla dayan ma


Shiru tayi tana kallonshi kawai takasa cewa komai

Qara tsinto daya yayi ya riqe yana kafeshi da idanu kamar mai karanta wani abu jikinshi sai kuma ya danyi murmushi

"yanzu nasan komai, na daina lalube" yafada yana tillashi shima


Jikin zee ne yadanyi sanyi kamar bazata iya cewa komai ba sai kuma tace
"wai meke faruwa ne Deen? Are you ok?"


Juyowa yayi ya kalleta da idanunshi dasuka fara kadawa
"nayi kama da wanda ke ok? Am not"


"then.. What's wrong? Sai magana kake marassa ma'ana aguna, meke faruwa ne?"


"kin fini sani Zainab, kinsan komai and that's what hurts me more, 6oyemin dakikayi"


Kallon idanunshi datake yasa nata ma kadawa tanajin yadda zuciyarta ke bugawa sosai

"mena 6oyemaka?" tafada cikin rawar murya


"da ace baki sani ba da bazan ji komai wajen gayamiki ba Amma kinsani Zainab, kinsani.
Kuma barina a duhun da kikayi yafi komai yimin ciwo"


Hawaye ne suka taru a idanunta
"waya gayamaka?"


Dan murmushi yayi mai ciwo tareda kauda kai
"sanin Hakan beda muhinmmancin"


"don Allah ka gayamin, please" tafada tana qoqarin danne hawayenta


"it doesn't matter Zainab, bayada wani fa'ida" yafada yana qara kauda kanshi yana jin zuciyarshi na zafi sosai


Sauke idanunta tayi qasa Hakan yaba hawayenta damar digowa kan skirt dinta


"nayi Hakan ne don karka shiga damuwa, nayi tunanin zan iya solving abin ne ni kadai" tafada ahankali batareda ta dago ba

"amma ai abin nima ya shafeni, nima inada right din sanin kome ke faruwa Koda abin zai bugarmin da zuciya" yafada shima batareda ya juyo ya kalleta ba


Ahankali ta tsane idanunta sannan ta dago ta kalleshi
"am sorry, kamar yadda nafada dazu nayi Hakan ne don karka shiga damuwa"


Shima juyowa yayi ya kalleta
"ni idan ban shiga damuwa ba shi wanda kika bari da broken heart ya zaiyi da rayuwarshi?"


Kallon rashin fahimta tayi mashi
"wa kenan?"


Murmushin takaici yayi
"da kinsani da kinbar pretending saboda nariga nasan komai, everything"


"pretending kuma? Ni bansan abinda kake magana akai ba"


"really? Kenan kin manta da wanda aka ajiye maganarku dashi tare?"


"mene? Aka ajiye maganar me?" tafada in confusion


"maganar aurenku, kina sonshi, keda kanki kika kawoshi wajen dad dinki aka kuma ajiye magana akanku, ko shima kin manta" yafada zuciyarshi na quna


"what? This is crazy! Yaushe aka badani bansaniba?


Murmushin takaici kawai yayi ya kauda kai


"Tambayarka nakeyi Deen, waya gayamaka haka?"


"wanda bazai ta6a yimiki qarya ba, so is better kibar pretending" yafada cikin qunar zuciya

"Daddy?"


Juyowa yayi ya kalleta da idanunshi da haryanzu basu washe ba saikuma ya kauda kai


Dafe goshi zee tayi kawai tayi shiru

Saikuma ta dago ta kalleshi
"dame dame ya gayamaka?"


"dama akwai wasu abubbuwan da be gayamin ba?" yafada cikin qaryewar zuciya yana kallonta kamar zaiyi kuka

Jin tayi shiru batace komai ba Saima kallonshi datake itama yasa yace

"don Allah ki gayamin, zanfi son inji daga bakinki bawai daga wani wajeba, qila zafin bazai kai yadda zanji ba idan nayi discovering Hakan a bakin wani"


Sosai yabata tausayi Hakan yasa wasu hawayen sake taruwa a idanunta


"dagaske ne kina sonshi kuma an tsaida maganar ku? Yaushe ne Hakan ya faru? Kafin muhadu ko kafin mufara soyayya ko bayan Hakan? Don Allah ki bani wadannan amsoshin ko zan samu rintsawa yau"


Kauda kai tayi tana dauke hawayenta dasuka kusan gangarowa

"ba Gaskiya bane, tunda nake ban ta6a soyayya ba sai akanka kuma bazan ta6a sharing soyayyar ka da wani ba"


Dukda be yarda ba Amma kuma yaji sanyi, yaji zafin zuciyarshi ta dan ragu


"amma ai bazai yimiki qarya ba"


"zai iya komai don ya rabamu"


Kallonta yayi cikin tashin hankali
"ya rabamu, dama yasan da maganar mu"


Dagowa tayi ta kalleshi
"yasani, sosai ma bama shikadai ba, harda mummy"


Shiru yayi yana kallonta da mammaki

_*shiyasa nazo wajen ka, please ka jawo ra'ayinta akan Hakan tunda naji ance kai abokinta ne, kana iya abinda ya gagaremu ka kuma samata ido kaga ko wani ke zugata don ni nafi tunanin Hakan*_


Girgiza kai Deen yayi bayan ya gama tuno wadannan kalaman na daddy

"anya Zainab daddy yasani kuwa? I don’t think so" yafada yana girgiza kai


Dan murmushi tayi sannan tace
"meya fadamaka? Ka gayamin"


Shiru yayi kamar bazai gayamata ba sai kuma ya sauke Ajiyar zuciya ya shiga labarta mata yadda sukayi da daddy jiya daddadare


Dan murmushi zee tayi mai ciwo sannan tace
"kasan abinda yayi?"


Girgiza kai Deen yayi ahankali batareda yace komai ba


"warning dinka yayi indirectly akan ka rabu dani"


Tsayawa yayi kawai yana kallonta yana jujjuya maganar ta


"Deen daddy beson tarayyarmu, duk hanyar danasan zanbi na fahimtar dashi nabi amma yaqi fahimta ta, I tried and am still trying amma banganin alamun nasara, bansan ya zanyi ba kuma" tafada qara tsane idanunta

"naqi fada maka ne don banaso hankalinka yatashi, a ganina komai zai zama daidai kafin ka ankara, bansan zaije yasameka ba"


"don Allah ki fadamin abinda ke faruwa, komai.

Karki ragemin komai, don Allah" inji Deen


Shiru tayi hawaye na cigaba da sauko mata batareda tace komai ba

"Zainab ki tuna wannan abin mu biyu ya shafa, be kamata ace daya na cikin duhu ba, don Allah ki taimaka ki gayamin" yafada pleadingly


Cije lower lip dinta tadanyi sannan tafara bashi labarin duk abinda yafaru, daga zuwan Asaad har zuwa rashin amincewar daddy akan za6inta da dalilin haka, tiryan tiryan tabashi labarin komai har zuwa yanzu dasuke zaune


Shiru wajen ya dauka na wani lokaci

_*ka nusar daita sosai, idan ma kaga alamun zugata akeyi let me know, sai na tabbatar na koyawa munafukin hankali don na tsani munafurci kana gani na nan, duk yadda muke da mutum daya munafurceni to wlh nagama dashi kuma zamu sanya kafar wando daya ne dani dashi*_


_*ta yiwu wani ko wata ke zugata yana dorata a keken 6era da nufin kaita yabaro*_


Ajiyar zuciya Deen ya sauke, sai yanzu duk ya gane inda magangganun daddy suka dosa

Tabbas warning ne, warning yake mashi indirectly amma shi yakasa ganewa, to dama tayaya zai gane bayan besan komai ba gameda abinda yake faruwa?
Babu makawa shine daddy ke nufi da yana zugata yana huremata kunne yana so yakaita ya baro.


"Deen kar Hakan ya dameka, wannan abin duk yayisu ne don be fahimceka ba, amma ina ji ajikina watarana zai fahimta, very soon"


Dagowa yayi ya kalleta
"Zainab daddy yanada Gaskiya, yafimu hangen nesa tunda gashi ya hango abinda duk bamu hango ba, Ya hango future dinmu.

Zainab akwai banbanci sosai a yanayin rayuwar da taki, ke kinsaba da akwai, kin saba da wadata a kodayaushe Yayinda ni a nawa bangaren ba Haka bane, mu abu biyu muka saba dashi, samu da rashi"


"Deen kaima kasani, ni kai nakeso ba abinda ka mallaka ba ko zaka mallaka, kaine farinciki na, farinciki yafi gold and sliver"

"Zainab, abin saukin fada gareshi a baki Amma wuya a experience, ina sonki zee, soyayyar da babu sirki ko kadan aciki, ba don komai naki ba Zainab kuma ina iyayin komai don na faranta miki amma Tambayar anan shine zaki samu farinciki a duniya ta? Duniyar da babu bushasha babu ababen more rayuwa kamar wanda kika taso aciki? Zaki iya zama a irin gidan danake zama? Zaki iya cin irin cimarmu, zaki iya shan ruwanmu? Zaki iyasa irin suturarmu? Zaki iya?"


"Zan iya, kuma fa mutane ne kuma kuna rayuwa da duk abubbuwan daka lissafomani naku cikin farinciki.

Rayuwa a kango tareda kai kamar rayuwa ne acikin mansion mai cikeda kayan more rayuwa

Rayuwa batareda kai ba a mansion kamar rayuwane acikin kango Deen.

Ina sonka a yadda kake kuma zan iyayin komai a dalilin son ka, zan ci cimarku zansha ruwanku nakuma saka suturarku don wata rana ba kasancewa zanyi babu ci babu sha Saidai ni nazama cima ga wasu hallitun, namana yazama abincin wasu qannanun dabbobin, suturata kuma daya ce ta Gaskiya wannan farin kyallen, so why zance bazan iya Hakan ba Tun a duniya, idan ban iya yiba a duniya zanyi don dole idan na mutu"


Kallonta yakeyi yana jin qaunarta na hudamashi koina na zuciyarshi


"nidai kawai sonake kayi min alqawari cewa baxaka ta6a barina ba no matter what, kowanne abu yanada qalubalenshi, wannan yana daga cikin qalubalen soyayyar mu kuma zamu tsallake da taimakon juna"


"Zainab bazan ta6a barinki ba duk rintsi, zan jajirce a soyayyarki babu gudu babu ja da baya, insha allah zamu tsallake wannan qalubalen dama duk wanda zaizo a gaba dukda bama fatan Hakan"


Bude hannu tayi ta miqo mashi tana kallonshi
"promise me, promise you'll never break my heart"


Kallon hannun nata yayi sannan shima ya dora nashi hannun asama suka damqe najuna

Shima yana kallonta cikin ido yace
"I promised, I promised I'll never break your heart, never!"... ✍️


Ummin fasihu 🧚🏻‍♀�
8/2/21, 9:38 PM - Buhainat😝: *🙍🏻‍♂️DEEN 🙍🏻‍♂�*


*048*


*THE PROMISE 2*


Sun dade suna tattauna yadda zasu 6illowa al'amarin, da yadda zasu samu shawo kan dukkan muhinmman mutanen da zasu buqaci amincewarsu a wannan tafiyar tasu.

Sai a sannan zee ta yarda da wannan karin maganar ta bature na
*a problem shared is a problem solved*

Sai gashi abin yayi juye yazama mai sauqi agaresu, ita datake 6oyewa don karya shiga damuwa sai gashi saninshi yakawo masu mafita


Basu tashi school din ba sai wajajen 3pm kuma kamar yadda yasaba shi ya rakota mota yakuma bude mata kofa tashiga.

Yana jin idanun bala akanshi yana kuma lura da kallon dayake binshi dashi amma ya share don he's ready for everything.


Yana tsaye yana kallon motar yana daga mata hannu har suka fice daga school din.

Ajiyar zuciya ya sauke yana jin wani qwarin gwiwa a zuciyarshi, yes he'll fight for his love, insha allah bazai gaza ba.


Shima fita yayi ya samu abin hawa yahau shima ya kama hanyar unguwarsu.


***


Da sallama yashigo gidan hannunshi riqe da cazbaha, forehead dinshi kuma da alamar qasa alamun daga sallah yake


Kaka dake zaune a tsakar gida bisa tabarma saboda zafin da akeyi ta amsa sallamar shi


Qarasowa yayi ya cire takalminshi shima ya zauna gefen kaka yana sauke Ajiyar zuciya

"ya dai?" inji kaka


"na gaji" yafada yana yatsine fuska

"kamar wanda yayi wani aiki?"

Murmushi kawai yayi bece komai ba


Shiru Wurin ya dauka sai kuma ya matso gaban kaka yana tayata tsintar waken datakeyi


"Kaka?"

Dagowa tayi ta kalleshi
"na'am"

Sai kuma yayi shiru yarasa ta ina zai fara

"ya kuma kayi shiru? Wani abu?" inji kaka tana kallonshi cikin kulawa


Murmushi yayi saikuma ya rufe fuskarshi da taffukan hannunshi

"Tofa? Meye kuma haka kakeyi kamar wata amaryar qauye?"

Dariya Deen yayi yana cewa
"kai kaka"

Itama dariyar tayi tace
"ai Gaskiya ne, kana wani rufe fuska kamar gaban surukarka"


Murmushi yayi yace
"kika sani ko gwada yadda zanyi agaban surukar tawa na keyi?"

Dariya kaka tayi
"kuma fa, to ai sai kabari kafara yin surukar sannan"


Murmushi yasakeyi
"Kika sani ko nayi din"

"Me din?"

"surukar"


Wani kallo tayimashi ta cigaba da abin take tana cewa
"ahakan?"


Gyara zama yayi cikin zumudi yace
"Allah kaka"

"Allah me?"

Sai kuma ya sake rufe fuskarshi
"nayi maki suruka"


Tsayawa tayi tana kallonshi babu kyaftawa

Jin shiru yasa yadan leqo a tsakankanin yatsun dake fuskarshi

Janye hannun yayi daga fuska ya kalleta
"bakice komai ba"


"yo aini ban gane ma inda ka dosa ba" tafada still tana kallonshi

Yar Dariya yayi sannan yace
"to kawo kunnenki kiji"

Da sauri kau ta miqa tana murmushi

Rada yashiga yimata a kunne sai naga idanun kaka sun qara budewa

"iyee! Wai dagaske!" tafada unbelievably


Sake rufe fuska yayi yana Dariya


Tashi tayi babu shiri tana rangada gud'a

"Ayiririririririririririririririririiiiiii! Kai amma allah na gode maka, kace me?" tafada cikin tsananin farinciki

"kai kaka Kiyi ahankali kar ajimu a waje"

"a jimu a wajen, Ayiririririririririririririririririiiiiii!! Wannan ai abin son kowa yajine, abin alhairi? Kai amma allah na gode maka, iyee! Kai dole ma nayi sujjadar Godiya ga allah "


Sai tayi qasa ta kai goshinta qasa


Deen dai kallonta yake kawai fuskarshi beaming with smile

Saida ta dago sannan ta cigaba
"Allah ya tabbatar da alhairi kyakyawana, kyakyawana zaiyi aure, kyakyawana yasamu wacce yakeso, kyakyawana ya girma, ashe da rabon zanga bikinka kyakyawana, da rabon qila zanga 'ya'yanka" Sai kuma ta fashe da kuka tana rufe fuskarta da ha6ar zaninta


Dariya Deen yayi
"kai kaka, kuka kuma?"

Dagowa tayi ta kalleshi cikin kukan tace
"dole nayi kuka, dole ne 😭"


Dariya yasake yi don shi Dariya ma ta bashi

Saida tayi mai isarta sannan ta koma ta zauna ta fuskanceshi dakyau tana maida tray din waken dasuke gyarawa baya tace
"to yanzu gayamin wacece surukar tawa? Wace yar albarkar ce mai sa'ar kyakyawan sardidin jikan nawa"


Dariya yaqara yi zuciyarshi qall
"kai kaka"


"eh mana, ai duk macen datayi sa'ar samunka to tagama dace a duniya saikuma ta nemi lahira, ba cika baki ba jikana namiji ne daya tamkar dubu, ga kyawun hali ga kyawun fuska

Kamalele kamala, kamaladini mai kamala takoina, fari mai farin aniya!

Gayamin dan sardidin kyakyawana Wace santaleliyar tayi sa'ar duniya wajen za6enka?"


Dariya Deen keyi sosai tunda tafara maganar don yana jin dadi idan kaka na mashi kirari

"wannan kirarin duk nikadai kaka?"

"ai ka cancanci fin haka dan kyakyawana, Gayamin wacece?"


"ai kinma santa kaka?"

"to? Ba mammaki kau amma dai gwara ka fadamin nasan ko ainahin wacece"

Murmushi Deen yayi
"Aminiyarki ce kaka"


"Aminiyata kuma?" tafada cikin rashin fahimta

"eh, Zainab"

"Zainab.. Zainab.. Zainab" tafada cikin son tunano mai sunan


"kai kaka Gaskiya kinfara tsufa wannan mantuwa haka? To Zainab yar makarantarmu dinnan, diyar mummy wadanda muka zauna asibiti dasu"


Wara idanu kaka tayi
"wacece? Kana nufin wannan Zainab din?" tafada tana waro idanu


Murmushi yasake yi
"Ashe kin gano? To ita"


Ahankali fara'ar kaka tafara ragewa a fuskarta mammaki ya maye gurbin murnar


Ganin wannan chanjin yasa shima fara'arshi ragewa

"yadai kaka?"


"bakada hankali ne? Wace yarinya kake nufi? Wannan diyar masu kudin?" ta tambaya still a mammakince

"eh kaka ita din"


"a wane duniyar mahaukatan Hakan zai yiwu? Ko kai bakasan kosu waye ba?"

Murmushi yayi yace
"Kaka nasan kosu waye mana, ai ba wannan ne abin dubawa ba hallarcin Hakan za'a duba"


Sakato tayi tana kallonshi
"to don kai kana sonta cemaka akayi zata soka ne?"


Murmushi Deen yaqara yi sannan ya matso kusa ya kama hannayen kaka ya riqe

"mezai hana taso ni kaka? Maganar ma damuke yanzu su daddy da mummy duk sunsan da zancen"


Sakin baki kaka tayi tana kallonshi kamar yau tafara ganinshi tama kasa cewa komai


Sakin hannunta daya yayi yadanyi waving a fuskarta
"kinyi shiru kaka"


"dole inyi shiru kyakyawana, ka tabbatar da abinda kake cewa kuwa"


"wlh kau kaka na tabbatar, wlh duk sunsan da maganar" yafada cikin zumudi

"ikon allah" inji kaka cikin mammaki saikuma taji kaso sittin na cikin murnarta yabi iska

Qara ruqo hannayenta Deen yayi sosai yace
"to kaka ya naga baki murna kuma?"


"ai kyakyawana abin ne yazo min wani iri, anya kau baka debo da zafi ba?"


Qara damqe hannunta yayi
"haba kaka, komai mai yiwuwa ne muddin allah be haramta ba"


"hakane, amma sai inga kamar yarinyar tafi qarfin ka, bakaga daga gidan data fitoba? Ya zakayi daita?"


Dan murmushi yayi
"kamar ya yaya zanyi daita kaka?"


"Ato ai dole nace haka, yarinya tasaba da akwai, ga cima mai rai da lafiya kullum cikin wadata take ya zakayi daita idan ka aureta? Wai ita ma tace maka ta amince dakai ko kuwa?"


"eh kaka, nima tana sona kuma ta amince ta zauna dani akowanne hali, tana sona sosai tsakani da allah"


Shiru kaka tasake yi sai kuma tace
"to iyayenta fa? Sun amince suma?"

"eh mana kaka, duk sun amince, duk sun yarda" Yafada yana murmushi yana kallonta yanason yaga fara'arta ta dazu tadawo


"ikon allah, to allah yaza6a Mafi alhairi, allah ya tabbatar da alhairi" tafada incheerfully


"to amma kaka yanaga bakya murna irin na dazu?" yafada yana 6ata fuska

"ina murna mana, ina murna sosai, kawai dai ina fargabane kar muna zaman zamanmu mujawoma kanmu matsala" tafada tana jawo tray din waken ta cigaba da tsinta


"insha allah kaka babu wata matsala, ki tayamu da addu'a kawai" yafada shima yana saka hannu a tsintar

"to allah ya tabbatar da alhairi, ai addu'a muna yimuku kullum kuma zamu cigaba dayi"

"yauwa kaka ta" yafada suna cigaba da tsintar yana cigaba dayi mata firar zee


Itadai sauraronshi kawai take amma kwata2 hankalinta yaqi kwanciya da za6in nashi, ba don batayi mata ba sai don fargabar faruwar abinda bata shirya mashi ba kuma bata fatan ya lokacin ya riskesu nan kusa har abada.


*ZEE*


A bangaren zee kuwa sai bayan dinner taje tasamu mummy har daki don yanzu don dole mummy tazama makusanciyarta saboda ra'ayinsu dayazo daya.


Anan ne tasamu mummyn ta zauna ta fadamata duk yadda sukayi da Deen da safe dakuma yadda daddy yaje wajenshi jiya.


Ajiyar zuciya mummy ta sauke sannan ta kalli zee tace
"Zainab, Gaskiya wannan maganar tawuce duk yadda kike tunani, ni aganina gwara kawai ku haqura da juna saboda Gaskiya daddy bada wasa ya dauki maganar nan ba"

Gaban zee ne yafadi
"mummy... Na haqura dashi kikace?" tafada cikin rawar murya


"qwarai Zainab saboda Gaskiya wannan al'amarin ba qaramin al'amari bane, dukda daddy be fahimci wasu abubbuwan ba shima ta Wani bangaren yanada Gaskiyarshi akan wannan al'amarin don idan kika tsaya kika natsu kika duba zakiga duk wannan abin dayakeyi duk saboda ke yake yinsu, he's making sure kar ayi abinda baza'azo ana regretting nan gaba ba.

Shi aure babban al'amari ne idan babu sanyawar albarka daga daya daga cikin iyayen both macen da namijin abin na iya juyewa yazama something else don haka Kiyi hqr kiyita addu'a idan kamal dinne mafi alhairi a wurinki to allah ya ganar da daddy idan kuma bashi bane allah ya za6a maki Mafi alhairi, insha allah zaki samu mai sonki sosai wanda zai Mafi kamal din sonki"

Tashin hankali!!


Kuka zee tafashe dashi sai gata on her knees

"Mummy please, karki ce haka. Ke kadai ce last hope dina please karki karaya, karki karya min gwiwa please.
Wlh Deen shine Mafi alhairi gareni please don't say that"


Sakin baki mummy tayi ganin yadda ta rude lokaci guda

"meye haka Zainab?" tafada a mammakince

"mummy don Allah karki bar bayana, please... We can do it, we can convince daddy, don Allah karki ce na haqura da Deen, bazan iya ba" saikuma ta zauna ta Hade kanta da gwiwa ta cigaba dayin kuka, idan mummy ta bar bayanta ya zatayi? She's her last hope.


"haba Zainab, saboda namiji zaki zauna kina irin wannan abin kina kuka? Inji dai bake ke forcing kanki agareshi ba?"

Dagowa zee tayi fuska sha6e2 da hawaye

"mummy wlh A'a, shima yana sona, bani ke cusa kaina ba, he loves me more than I do to him"

"then sai Kiyi hqr ki tsaya kiga yadda allah zaiyi daku, idan da rabon ku mallaki junanku zakuyi Hakan idan kuma babu babu yadda kuka iya dole ku hqr da juna.

Shi musulmin qwarai da tawakkali aka sanshi da kuma daukar qaddara"


Kasa cewa komai tayi sai cigaba da sobbing datayi

"kije ki cigaba da addu'ar za6i na alhairi don kuka won't change anything da yanayi da mutane da dama bazaki gansu da damuwar komai ba.

So is better ki riqe du'as don shikadai zai taimakeki nima zan tayaki kuma zan sake yimashi magana nima bawai na karaya bane kawai dai sonake na fahimtar dake ba kowanne abu da ka qwallafawa rai kake samu ba, kinji ko?"


Kada kai kawai tayi ahankali cikin matsar hawaye

"Good, yanzu tashi ki tafi and wipe your tears don basuda amfani, what matters most is du'a"

Qara Kada mata kai tayi sannan tashare hawayenta ta tashi tana jin kamar jiri zai kwasheta


"Don't worry kinji zan sake mashi magana insha allah zai fahimta" tafada cikin son qara kwantar mata da hankali

Qara kadamata kai zee tayi sannan tayi mata sallama ta fita

Binta da kallo mummy tayi cikin tausayawa saikuma ta girgiza kai ahankali ta cigaba da abinda takeyi.


Tana shiga dakin tayi wajen gadonta da gudu ta fada akai.


Sauran kukan da bata ida a dakin Mummy ba ta cigaba dayi

Jitayi kamar ta riga ta rasa Deen din ma

Wannan wane irin abu ne? Ko kadan bata ta6a kawoma ranta zata samu matsala irin wannan a soyayyarsu ba


Tariga ta dogara da maganar daddy na bazai mata dole ba duk wanda takawo zai kar6a hannu bibbiyu, bata ta6a tunanin banda talaka ba ko dayake ita kanta idan aka gayamata zata so talaka a lokacin qaryatawa zatayi, kawai lokaci daya ta makance a soyayyarshi makantar da bata tunanin zata ta6a bude ido nan kusa.


Aunty Feenah ce tafado mata arai, sotake ta kirata ta gayamata komai ko zataji sauqin abinda takeji ko kuma tabata shawarwaru kamar yadda tasaba

Amma saita tuna basama qasar, tun bayan wata daya da auren suka shilla honeymoon gashi batada number ta tacan kuma Koda tanada ita bekamata ta kirata ba a irin wannan lokacin ba, be kamata ta takura masu ba Suna tsaka da cin amarcinsu.


Ringing din wayarta ya katse ta daga tunane tunanen datakeyi

Wani sanyi taji a zuciyarta tun kafin ma ta duba mai kiran.

Ganin zata tsinke yasata saurin dauka ta daga kiran ta kara phone din a kunne bayan tayi iya qoqarinta na gyara yanayin ta don batason ya fuskanci halin datake ciki ko kadan batason ta saremashi gwiwa shima.


Saida suka gaisa sannan Deen cikin zumudi yashiga gayama zee yadda sukayi da kaka da amincewarta 💯 harda qarin maggi da gishiri a labarin don yaqara bada armashi.


Nan take zee taji duk damuwar ta ta yaye itama tashiga murna


Sun dade suna firarsu kamar basuda wani problem a rayuwa sannan suka rabu dakyar ba don sun so ba sai don barcin daya addabi idanun kowannensu


Sallama sukayiwa juna akan sai gobe idan sun hade a makaranta sannan suka katse kiran kowanne zuciyarshi wasai


Babu dadewa duk barci ya kwashesu mai cike da mafarkan juna


Kingin ranakun dasuka biyo baya sunzo very smoothly for the two lovers


Kwata2 sun manta da damuwarsu sun dauki damuwarsu sun ajiyeta a gefe sun cigaba da gudanar da soyayyarsu tsabtataciyar cikin salo na burgewa da ban sha'awa.


Soyayya suke bugawa wacce tafi ma tada, irin soyayyar nan mai tsayawa a rai kamar zane akan dutse wanda baya ta6a goguwa.


Basuda damuwar komai idan ma suna da ita to qila sun manta da ita don kwata2 basama kawota a jadawalinsu sam, rayuwarsu sukeyi kamar dama subiyu ke a duniyar basa tunawa da komai da kowa.


A bangaren iyayen kau abin dai babu yabo ba fallasa za'ace, haryanzu daddy shiru yayima biris da zancen Haka ma mummy bata qara tada zancen ba

Kaka ma ba laifi amma bawai ida Sakin jiki tayiba da wannan relationship din nasu ba don haryanzu hankalinta be ida kwanciya dashi ba

Taso ace Deen yasamo daidai shi ko don kaucewa matsala anan gaba, matsalar da basusan iyakar ta ba Amma ganin yadda Deen ya saki jikinshi dakuma yadda yake nuna tsananin qauna akan Hakan yasata 6oye damuwar ta ta cigaba da binsu da addu'ar za6i na alhairi.


Everything was going smoothly kwatsam wata rana zee na Kwance daki waya a kunnenta taji an banko kofa anshigo a fusace.


Saurin juyowa tayi cikin mammaki sai ganin daddy tayi kamar an jefoshi dakin sai suraci yake.


Saurin tashi zaune tayi zumbur batareda tama tuna Da katse kiran dasukeyi ba.


"daddy?" tafada ahankali tana kallonshi da kuma mummy datake bayanshi daga bakin kofa


Da yatsa daddy ya nuna zee

"wato ke bakya jin magana ko? Duk abinda nake gayamaki ta kunnen dama yake shiga yafita na haggu ko?

Dama bakida hankali bansaniba?! Ina nunamaki hanya kina rufe ido!

Kinje kina biyewa wancan dan iskan yaron ya huremaki kunne ya bushe maki idanu bakya ganin kowa da mutunci ko?!! Eh!

Kullum kinacan banda qara liqemashi babu abinda kikeyi ko? And itama Good for nothing uwarki babu abinda takeyi sai goyon bayan ki ko?!!"


Sosai zee ke kuka ganin yadda daddy ya burkuce mata sai tsawa yake mata abinda be ta6a ba

"daddy don Allah kayi hqr wlh ina sonsh.."

"will you shut that your dirty mouth up! Are you stupid! Ina maki magana kina yimin zancen banza zancen wofi!!"


Yadda ya hayyayaqomata kamar zai maketa yasata saurin yin baya ta zauna kan gado tana shigewa jikin frame din gadon tana wani irin kuka cike da tashin hankali.


"harni zaki fadawa soyayya?! Ni zaki fadawa kina sonshi! Soyayyar banza soyayyar wofi?! Soyayyar dakike mashi yakai wacce nake maki ne! Soyayyar da yake maki takai kwatar wanda nake miki?!
Wato ni kuka maida shashasha ma ashe, ni inacan ina haukana ku kunacan kuna abinda kuka ga dama babu abinda ya dameku"


"am disappointed in you Zainab, very disappointed.

A tunanina Koda ban kawo maki hujjar komai ba na hanaki kula wannan yaron haka kawai zaki rabu dashi ko don farincikina kamar yadda nasha sadauqarda farincikina saboda naki.

Amma da hujjata da komai kuma duk abinda nakeyi akanki nakeyi don kar rayuwarki ta tagayyara amma shine zaki debo qasa ki 6ullamin a idanu, kin mance da soyayyar danake miki kin manta da qaunar danake miki kin fita harkata duk saboda wannan kwadayayyan yaron, duk saboda dadin bakin dayayi miki ko!!"

Kada kai yayi yana murmushin takaici
"to wlh bazai yiwuba, zan dauki mataki, mummuna kuwa akanshi, tunda nabishi ta girma da arziqi bejiba, I'll have to show him my true colour, don haka daga yau karki qara fita daga gidannan kije koina, ko school na hana, zanyi maganinku ne wlh, shashashan banza!!"

Yana kaiwa nan ya kada babbar rigarshi ya fice daga dakin kamar zai tashi sama itama mummy ba don tayi saurin matsawa ba da yayi gaba daita.


Bin bayanshi mummy tayi da kallo harya fita yamaido masu kofar da qarfi.

Maida kallonta tayi kan zee dake takure akan gadon haryanzu tanata kuka kamar zata shide


Ajiyar zuciya ta sauke cikin rashin sanin abin yi sannan itama ta nufi kofa ta bude ta fita


Qara fashewa da wani kukan tayi tana Hade kanta da gwiwa, sosai takejin wani zafi na ratsa kowanne lungu da saqon zuciyarta tana jin yadda take fidda hucin zafi.


Zamewa tayi ta kwanta tana cigaba da kukan da tasan shi zai sata jin sauqin abinda takeji a zuciyarta.


Bata san iya tsawon lokacin data dauka ahaka ba sai jitayi anfara kiraye kirayen sallar magrib


Dakyar tasamu ta tashi tayi alwala ta gabatar da sallar

Tana nan zaune aka fara kiraye kirayen isha'i nan ma ta tashi ta kawota tayi addu'o'i sosai akan allah yakawo masu mafita sannan ta tashi ta koma kan gado ta kwanta tana jin yadda kanta ke saramata.


Duk yadda taso yin barci kasawa tayi don kwata2 barcin ya qauracewa idanunta ga wani irin ciwo da kanta ke mata na kukan datasha.


Wayarta ta laluba ta kunna sai taga duration din wayar dasukayi da Deen ke samar screen din wayar.


Lissafi tayi da lokacin dasuke wayar da lokacin da daddy yashigo saita ga ashe ma bata katse kiran ba bayan shigowarshi, Saida aka qara 10mins kafin kiran ya tsinke wanda cikin dayan biyu ne, ko shi ya katse ko kuma kudinta ne suka qare, idan haka ne that means yaji duk yadda sukayi da daddy?


Rasa mai bata amsar tayi sai kawai ta dannama number shi kira Saidai tun kafin aje ko ina taji ana cewa number datake kira bata shiga

Qara bugawa tayi bayan wancan ya katse nan ma amsa daya ce, the number is not reachable.

Kashe wayar gabadaya tayi ta tura qarqashin pillow ta koma ta kwanta tana cigaba da kukan zuci.

Wannan wane irin abu ne da maimakon yaci baya sai qara cigaba yake?


She can't believe yau ita daddy ya tsaya yayi ma tass haka, kuma ta tabbata da ta tsaya jayyaya dashi babu abinda zai hana ya wanka mata mari saboda yanayinshi kawai ya nuna yakai maqurar qurewa a 6acin ranshi

Sosai fadanshi da barazanar shi na daukan mummunan mataki akan Deen ya tsaya mata arai, Hakan yasa bata wani samu isashen barci ba a ranar duk rabi da rabi tayi kuma marassa dadi.


Washegari ta tashi da zazza6i, yau lahadi babu school gashi ta tashi da menstrual cramps wanda ke nuna alamun zata samu menstrual flow dinta a kowanne lokaci.


Bayan ta samu tayi sallar asuba dakyar takoma kan gado ta kwanta ba don tana jin barci ba sai don she's too weak har a lokacin.


Ta dade ahaka lamo kan gado can taji an bude kofar dakinta an shigo.

Batasan ko wanene ba kuma bata bude idanu ba don ganin waye


Jitayi anzo bakin gadon ta kuma ji alamun zama bisa bedside locker din wajen

Dumin hannu taji a wuyanta Hakan yasa ta sauke Ajiyar zuciya ta bude gajiyayyun idanunta tana kallon mummy dake ta6a wuyanta

"Are you sick?" inji mummy tana qara feeling temperature dinta


Lumshe idanu kawai zee tayi batareda tace komai ba


"tashi muje kici abinci kisha magani"

Yamutsa fuska tayi zatayi magana mummy ta girgiza mata kai alamun karta fara saikuma taqara cewa
"tashi mutafi"


Babu yadda ta iya haka ta tashi dakyar tanajin kamar taita kuka.

Saida tafara yin brush sannan ta dawo ta zauna don daga baya ma sama aka kawomata abincin.


Ta danci da dan yawa bisa takurawar mummy sannan tabata maggunguna tasha harda na period dinta saboda ta mata complain din ciwon cikin.


Saida ta shanyesu duka sannan takoma ta kwanta tana jin yadda kanta har lokacin ke harbawa


Bata dade da kwanciyar ba barcin da bata samu yiba tun jiya ya dauketa.


Lokacin da ta tashi har menstrual flow dinta yazo Hakan yasa ta tashi ta shige toilet don babu laifi tadan ji qarfi qarfin jikinta tayi wanka tayi packaging kanta sosai sannan ta dawo ta zauna gefen gado.


Wayarta dake kashe tun jiya ta lalubo ta kunnata tashiga call log taqara buga number shi Saidai this time around sai sukace tana switch off.

Komawa tayi ta jingina da frame din gadon ta lumshe idanu tana jin daci a ranta, this is the toughest time in her life.


Aranar ko kofar dakinta bata fita ba abinci Saidai a biyo ta dashi daki kuma dole taci don mummy ke tsareta sai taci.


Har dare number Deen bata shiga abinda be ta6a faruwa ba hakan yasa taji hankalinta yaqi kwanciya babu abinda ke fadomata arai sai kalmar daddy na saiya dauki mataki akai mummuna, Hakan ba qaramin samata fargaba yakeba a zuciya


A daddafe dai tasamu gari ya waye.

Tunda wuri tayi shiri don babban burinta shine taje ta ganshi a school ta tabbatar da lafiyarshi don jiya dashi ta kwana a ranta

Saidai me Koda ta sauko saita nemi bala ta rasa Koda ta tambayi security sai cewa yayi be isoba har lokacin


Komawa cikin gida tayi ta zauna a falo tashiga neman number bala amma bata shiga, tafi awa nan tana zaman jira amma shiru gashi ita bata iya driving ba.


Ganin abin na neman zama rainin hankali sai ta tashi ta sake fita da niyyar samun adaidaita kawai tayi tafiyarta

Saidai me firr security yaqi bude mata gidan wai daddy yabashi umarnin kar yabari ta fita.


Sosai abin ya quleta Hakan yasa tashiga zazzaga mashi bala'i akan ya bude mata gidan tafita gidan na ubanshi ne?

Saidai dik masifarta da hayaniyarta ko gezau securityn beyiba dama ta dameshi saiya shige dan dakinshi ya rufo kofa.


Juyawa itama zee tayi tashiga cikin tana kuka sosai, Direct dakin Mummy ta nufa taje ta tardata tana yan lissafe lissafenta


Fadawa tayi jikinta tana kuka sosai tana roqonta tazo tasa security ya bude mata gida


Ajiyar zuciya mummy tayi tace
"Zainab, bakiji abinda daddyn naki yace bane? Cewa yayi bazaki qara fita daga gidan nan ba Koda kuwa school zaki, Kiyi hqr kawai harya sauko"


Kuka zee ta cigaba dayi
"mummy am scared, tun shekaranjiya number Deen bata shiga, kar ace daddy yayi mashi wani abin"


"babu abinda zaiyi mashi insha allah, kawai shawarar dazan baki yanzu itace kibar batun Deen for now, muddin kinason zaman lfy don daddynki ya dauki abin da zafi fiyeda tunaninki"


Da wannan kalmar zee ta tashi ta koma dakinta ta kwanta ta tattakure waje daya kamar marainiya.


Tun daga ranar farinciki ya kaura a rayuwar Zainab, tun tana attempting fita daga gidan ana hanata har ta haqura ta bar ma fitowa kwata2 daga dakinta.

Kullum yini take cikin dakinta tana kuka babu abinda yafi daga mata hankali kamar jin Deen shiru har lokacin, yanzu sati daya kenan da faruwar Hakan amma haryanzu number shi is switch off, sosai Hakan ke daga mata hankali.


Cikin wannan kwanakin sai gashi tayi wata ramar dole, sai acikin kwanakin taqara tabbatar da bazata iya rayuwa batare dashi ba don ita kadai tasan yadda takeji a yan kwanakinnan da bata sanyashi a ido ba kuma bataji muryashi ba.


Ana haka ranar data cika kwana goma da faruwar komai tana zaune waya a hannunta ta lalubo number Deen ta tsaya ta kuramata idanu kawai tana kallo

Kamar da wasa ta dannama number kira batareda sa ran zata shiga ba

Kamar a mafarki kawai sai taji tafara ringing


Wara idanunta tayi cikin mammaki bugun zuciyarta na qara gudu


Saidai harta tsinke ba'a daga ba


Hannu na rawa taqara bugawa tana miqewa tana jin kamar zuciyarta zata tsinke saboda bugawar datake


Saida ta jera kira uku, ata hudun ne taji an daga


Kasa cewa komai tayi sai rarraba idanun datake zuciyarta na mugun gudu

"Zainab..." cool voice dinshi ta ratsa kunnenta


Rufe bakinta tayi da tafin hannunta takoma ta zauna bisa gadon da6as


"Hello? Zainab?" tasake jin Muryarshi nacewa Hakan


Hawayene suka shiga taruwa a idanunta still takasa cewa komai
"Zainab is this you? Please say something"

Lumshe idanu tayi tana ba hawayen idanunta damar gangarowa

"Deeen..." Sai kuma tashiga yin sheshekan kukan da batasan yazo mata ba


"Zainab, are you crying? Please kibari kinji? Kar zuciyata ta buga, am ok kinji" taji yafada shima a cikin wani irin murya mai matuqar rauni


"Deen ina ka shiga? Nakusan mutuwa saboda fargaba, meya faru da wayarka?" tafada cikin kuka


"am ok zee, babu abinda yasameta kawai babu charge ne" yafada cikin son kwantar mata da hankali

Girgiza kai tayi
"No Deen, you're not ok, gayamin meya faru me daddy yayi maka"


"babu komai Zainab, babu abinda yayi min, I love you and I'll never back off, no matter w..."

Sai kuma taji shiru


"hello? Hello! Deen! Kana jina?" tafada tana sake miqewa hankali tashe


"eh yana jinki, mallama me kuma kike nema da jika na? Me kuma yasaki nemanshi?"


Baki na rawa zee tace
"k.. Kaka?"


"eh nice, kaka ce. Nagode ma allah da kika gane Hakan, meye kuma kike nemanshi bayan duk abinda kukai mashi? Eh!"

Kasa cewa komai tayi sai bakinta dake rawa amma takasa furta komai

"to ahir dinki wlh, karki qara kiran yarona a waya, kifita harkar shi wlh don shima yariga ya gama dake dama ai qarfin hali ne irin nashi banda Hakan ai ke ba kalar matar dazai aura bace.."


Muryar Deen taji daka can baya yana kiran sunan kaka

Muryar kaka taji tana cigaba da cewa
"menene? Menene kake hanani magana? Kabari nayi mata wonin

Kina jina? Wlh ki fita harkar jikana kina jina ko? Mu ba kowan kowa bane bamuda wadanda zasu tsaya mana idan kika jefamu a chakwakiya, muna zamanmu ne cikin rufin asirinmu da wadatar zuciya, muna zamanmu cikin farinciki don Allah karki tarwatsa mana shi, don Allah ki kyalemin yaro kije kema allah ya hada ki daidai ku masu kudi muma haka, mun gode da duk dawainiyar dakukayi mana da qaunar da kuka gwadamana amma dan allah karki sake nemanmu, ba don mu ba don Allah"


Kittt.... Taji an katse kiran


Ahankali ta Saki wayar hannunta ta fadi sannan itama ta zame ta zauna kan bedside locker tana kafe waje guda da ido... ✍️


Ummin fasihu 🧚🏻‍♀�
8/2/21, 9:38 PM - Buhainat😝: *🙍🏻‍♂️DEEN 🙍🏻‍♂�*


*049*


*THE ACCEPTANCE*


Maida kanta tayi baya ta jinginashi da bangon bayanta tareda lumshe idanunta


Ita kadai tasan abinda cikin, duk yadda zata musaltashi bazai misaltu ba.


Ta dade sosai ahakan sannan ta bude idanun ahankali ta qurawa saman p.o.p. Din dakin idanu.


Batasan iya lokacin data dauka ahaka ba sai jitayi ana bubbuga kofar dakin


Maida idanun tayi again ta lumshe batareda ta Ko motsa ba.


Bude kofar akayi mummy tashigo

Ganinta zaune akan bedside tana kallon sama yasata ida Qarasowa dakin

"Zainab?"

Bata motsa ba bare ta nuna alamun taji

Ida Qarasowa tayi tadan bubbuga mata kafada
"ke Zainab?"


Sai a lokacin ta bude idanunta dasukayi jawur sannan ta sauke kanta qasa tana cije lower lip dinta


"lfy?" inji mummy tana kallonta


Girgiza kai kawai tayi ahankali batace komai ba

"ki bude baki kiyimin magana mana"


Ahankali ta bude bakin cikin muryar da ita kanta batasan tanada ita ba tace
"lfy lau"


Tsayawa mummy tayi tana kallonta, sosai take bata tausayi amma ya ta iya? Ita kanta daddy fushi yake daita bayama mata magana bare ace zata iya wani abu akai

"kinci abinci?" ta tambayeta a tausashe

Kada kai tayi saikuma ta qara bude baki tace
"eh"

"Good yanzu ki tashi kiyi sallah kinga anfara kiraye kiraye"

"to" tafada ahankali


"tashi to" inji mummy tana dan ja baya don bata damar tashi


Ahankali ta dafa gefen bedside locker din ta tashi tsaye saikuma tayi baya zata zube mummy tayi saurin tarota


"subhanallilah! Are you ok? Jiri kikeji?"


Qoqarin miqewa tsaye tayi tana girgiza kai ahankali Saidai ta kasa tsayawa

"zauna, zauna anan" inji mummy tana kaita gefen gado


Zama tayi takoma ta jingina da gadon tana sauke Ajiyar zuciya

"bakida lfy ne Zainab?"

Idanunta a lumshe ta girgiza kai tana sauke numfashi ahankali

"jiri kikeji?"


Ahankali ta Kada kai
"sannu, bari naje na hadomiki tea kisha saikisha magani ki kwanta anjima kyayi sallar" tafada cikin tausayawa


Itadai zee batace komai ba kuma bata bude idanun ba sai sauke numfashin data cigaba dayi ahankali.


Ahaka taji alamun fitar mummy


Wasu hawaye ne suka kufto daga rufaffun idanun suka gangaro, batayi qoqarin hanasu gangarowa ba don itama tana da buqatar zubdasu Hakan yasa tabasu damar zuba iya son ransu.


Bata san dawowar mummy ba sai jitayi an dafa kafadarta

Bude jajjayen idanun tayi ahankali ta kalli mummy taga itama mummyn kallonta take


"menene kuma Zainab?"


Sauke idanunta tayi a qasa sannan ta girgiza kai ahankali


"Wani abu yafaru kuma?"

Sake girgiza kai tayi ahankali wasu hawayen nasake zubowa

Ajiyar zuciya mummy ta sauke sai ta ajiye mug din tea din hannunta ta zauna kusada ita

"Zainab komai yayi zafi maganinsa allah, don Allah kibar takurawa kanki haka, insha allah komai zai warware, komai zai zama tarihi" tafada cikin sigar rarrashi


Itadai batace komai ba kuma batayi motsiba

"ki zama mai daukar kaddara Zainab walau mai kyau ko akasin haka, kibar sama kanki damuwa arai Hakan na iya affecting lafiyar ki, Kiyi hqr kinji? Insha allah idan kamal mijinki ne babu abinda zai hana ki aureshi amma idan kika cigaba da sama kanki damuwa komai ma na iya faruwa"

Haka taita yimata nasiha, Itadai zee nata saurare batace komai ba har tayi ta gama


Tea din tabata tasha sannan ta bata magungguna suma ta sha sannan tasata kwanciya yadda maganin zaiyi aikinshi yadda anjima zata tashi da qwari qwarin jiki.


Kwanciyar tayi Saidai ko kadan barci be nufo idanunta ba


Haka taita kwanciya har mummy tasake dawowa dakin


Da taimakonta ta tashi tayi alwala tayi sallah sannan ta sake tilasta mata tadanci abinci sannan ta koma ta kwanta.


Haka ta qarasa Wunin nan rabi a Kwance, sosai jikinta ya saki tanajin batada qarfi ko kadan.


Da daddare ma Dakyar tasamu wani barci marar dadi ya dauketa can cikin dare.


Washegari da wani zazzafan zazza6i ta tashi, jikinta yayi ringis sai fidda hucin zafi yake.


Lokacin da mummy tashigo don tadata rikicewa tayi ganin halin da ta tararda Zainab.


Babu shiri tafita ta nufi part din daddy gudu gudu sauri sauri.


A falo ta tarar dashi zaune sanye da brown jallabiya yana qoqarin Kamo tasha

Ganin yadda tashigo a rikice yasashi dakatar da abinda yakeyi yana kallonta da ayar tambaya


"Alhaji zoka gani, Zokaga halin da Zainab ke ciki"


Gaban daddy yafadi Hakan yasa yayi saurin miqewa tsaye yana Sakin remote din hannunshi

"meya faru? Meya sameta?" yafada yana yin gaba batareda ya tsaya jin amsoshin tambayoyinshi ba

Maramashi baya itama tayi suka fito daga part din


Kusan lokaci daya suka sake Shigowa dakin nata inda take Kwance yadda mummy tabarta.


Da sauri daddy yayi bakin gadon ya zauna yana kamo hannun Zainab din


Jinshi rauu da zafi yasashi wara idanu a rikice shima


"Daughter? Daughter! Innallilahi waina ilaihi rajiun" yafada yana dorota jikinshi

Kallon mummy dake tsaye itama gefe hankali tashe yayi yace
"wai meke faruwa ne? Meya sameta?"


Jitayi Tambayar ma tabata takaici sai tace
"ka fini sanin meke faruwa, idan kayi sanadin rasa yar dayar da allah yabamu ai sai kowama ya huta" tafada hawaye na cicciko idanunta


Maida kallonshi yayi akan zee dake sauke numfashi mai zafi ahankali tama kasa bude idanu tsabar yadda takejin jiki


Wayarshi yayi saurin lalubowa a aljihu yashiga kiran family doctor dinsu

Ba'a daga ba a kira na farko ba sai ana biyu


Sallama Dr yayi daga dayan bangaren

"Dr ba lfy, ga daughter na nan in a critical condition, I badly need your help"

Cikin rikicewa shima Dr a dayan bangaren yace
"innallilahi waina ilaihi rajiun! Meya sameta? Ganinan zuwa yanzu"


"No, bari muzo, bazamu iya jira ba muhade a hospital kawai"

"ok.. Ok sir, nima yanzu zan kamo hanya saikun iso"


Katse kiran daddy yayi ya kalli mummy

"maza dauko mata hijab dinta"

Da sauri Mummy ta bude closet dinta ta ciro mata yar madaidaiciyar hijab dinta da taimakonta dana daddy suka samata sannan daddy ya tashi daita ajiki ta tallabeta kamar ya dauki jaririya.


Daddy ne agaba mummy abaya kallo daya zakayi musu kasan a mugun rikice suke


A back seat ya shimfidar daita mummy tashiga itama ta dora kanta a cinyarta sai daddy yakoma mazaunin driver ya bude yashiga yana danna uban horn tun kafin ma ya ida zama sosai


A rikice security yafito, Ganin an tada mota yasa ya tsaya yana kallon motar dazata juyo don ganin su wanene


Hango daddy dayayi a mazaunin driver dakuma nuni dayake mashi na ya bude masu gate yasashi rugawa da gudu ya shiga wangale masu gate din.


Da gudu daddy yaja motar suka zo suka fice suka halba titi.


Sosai daddy ke tsula gudun tsiya akan titi donma gari be ida wayewa ba babu motoci sosai akan titin


Cikin dan qanqanin lokaci suka isa inda kusan shigowarsu tareda Dr din.

Da sauri Dr yafito daga motarshi yanufo tasu da gudu daidai shima daddy ya fito

"Alhaji meke faruwa ne?"

"Tana ciki" inji daddy yana bude seat din baya

Leqawa Dr din yayi saikuma yayi cikin hospital din da sauri

Da taimakon mummy aka fiddota daga cikin motar daidai nan Dr yadawo da wasu nurses jaye da gadon gurgura marassa lfy


Ahankali aka dorata akai sannan aka shiga gurgurata zuwa cikin asibitin mummy da daddy biyedasu cikin tashin hankali.


A wajen ward dinda aka shiga suka ja burki kowa yayi cirko cirko cikin tashin hankali


Da taimakon nurses din aka maida ta kan gadon cikin ward din sannan Dr din yashiga bata taimakon gaggawa don sosai jikinta yayi mugun rauu kamar a oven.


Zainab najin duk abinda akeyi amma she's too weak don ko bude idanunta ma takasa, jin kanta take kamar ta cireshi ta jefar ko zataji sauqin abinda takeji


Sun kusan awa akanta sannan suka samu daidaita temperature dinta aka kuma daura mata drip.


Saida Dr yagama komai Sannan ya juya da niyyar fita yasamu su daddy dayasan suna can cikin tashin hankali

Jiyayi an kama ha6ar rigar shi Hakan yasashi saurin juyowa.

Zee ce riqe da rigar amma still idanunta gamm a rufe

Saurin dawowa wajenta yayi yana cewa
"Zainab, menene? Gayamin how are you feeling? Ina ke miki ciwo?"


Hawaye ne suka gangaro daga ruffafun idanunta

"sorry ok, zaki samu sauqi, ko nakira daddy?"


Ahankali ta girgiza kanta still idanunta a rufe sai kuma tashiga motsi da baki Hakan yasa yayi saurin duqowa don yaji me zatace

"z..zan mutu"

"bazaki mutu ba Zainab, insha zakiji sauqi, kinji?"


Girgiza kanta tayi ahankali wasu hawayen nasake gangarowa

"zan mutu ne, zan mutu idan baka taimaka min ba" tafada cikin dashashiyar muryarta

"zan taimaka miki, kinga ma gashi nan ina taimaka miki ko? Kiyi hqr zakiji sauqi, be strong"


Sai a lokacin ta bude jajjayen gajiyyayun idanunta da har lokacin ke zubda hawaye

"zan rayu ne idan ka taimaka min, ina neman alfarma awajenka Dr, please"

Tsayawa Dr din yayi yana kallonta na wani lokaci sannan yace
"Alfarmar me Zainab"

Hadiye wasu yawu tayi ahankali sannan tace
"kacemasu daddy jinina ya hau, hawan da zai iya bugar da zuciyata, kacemasu zan rasa rayuwata, kacemasu zuciyata takusan bugawa, kace muddin basu bani abinda nake so ba zasu rasani" Sai kuma tafashe da kuka


Tsayawa Dr yayi yana kallonta kawai yakasa cewa komai

"Duk wadannan abubbuwan dana lissafa zasu faru dani soon Dr, zan iya rasa rayuwata soon, ba hakan nakeji ba, wahalar dazani sha nake tsoro, don Allah ka taimakeni, ka ceci rayuwata, ka fadamasu Hakan ko zasu tausaya min su bani abinda nake so"


Sosai jikin Dr yayi laqwas sai kallonta yake cikin tausayawa

Qara kallonshi tayi
"don Allah kar kace A'a Dr, don Allah"


❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️


Safa da marwa daddy ketayi tsakanin farkon ward din zuwa qarshen shi Yayinda mummy ke zaune kamar akan qaya ta buga tagumi kowannensu jini akan akaifa.


Jin budewar kofa yasasu saurin dagowa gabadaya


Ganin fitowar Dr yasasu saurin tahowa wajenshi da sauri

"Dr ya? Ya take yanzu?" inji daddy cikin rikicewa

"karku damu, calm down please, komai zai tafi normal" inji Dr cikin sigar kwantar masu da hankali


"yanzu yaya take aciki Dr, don Allah ka gayamana"


"zan gayamaku yanzu ma kuwa, but mutafi office tukkuna" yafada yana nuna musu hanya nan duk suka rankaya suka nufi office dinshi

Zama yayi a kujerar shi suma suka zazzauna a kujerun dake facing desk dinshi suka zuba mashi idanu cikin neman qarin bayani


Gyaran murya Dr yayi sannan ya zare glasses din idanunta yana kallonsu

"meke damun Zainab ne?" inji Dr


Kallon juna mummy da daddy sukayi sannan suka sake kallonshi

"kamar yaya? Abinda ke damunta ai kai zamu tambaya tunda kai ka dubata" inji mummy


Ajiyar zuciya Dr ya sauke sannan ya koma ya jingina da kujera yace
"abinda yasa na tambayi Hakan saboda naga alamun tana tattare da damuwa ne sosai wanda Hakan ke barazana ga lafiyarta"


"Me Hakan ke nufi Dr?"


Tasowa Dr yayi yayo gaba ya dora hannuwa akan desk dinshi yace
"am sorry amma diyarku tana cikin tsananin damuwa wanda Hakan ya ta6a lafiyarta sosai don a halin yanzu jininta ya hau fiyeda qima wanda Hakan barazana ce ga lafiyarta sosai, zuciyarta na cikin matsala don ba don kun kawota dawuri ba da komai na iya faruwa"


Rufe baki mummy tayi da hannu tana gasping Yayinda daddy yaita maimaita kalmar innallilahi


Ganin yadda suka rikice yasashi cigaba da cewa
"yanzu haka Dakyar nasamu nashawo kan al'amarin, yanzu nayimata allurar barci don tasamu peace of mind yadda zamu samu jinin ya dan sauka"


"innallilahi waina ilaihi rajiun"inji daddy cikin tashin hankali


"ka gani ko? Kaga irin ta Ko? Ai shikenan, saika kasheta kowama ya huta" inji mummy cikin kuka sai kuma ta tashi ta fice daga dakin da sauri


Binta da kallo duk sukayi sai kuma daddy ya dafe kai yana sake ambaton sunan allah


Shidai Dr cigaba da bashi hqr yayi da kwantar mashi da hankali.


Dagowa daddy yayi da idanunshi dasuka Kada ya kalli Dr yace
"meye mafita Dr? Banason rasata, she's the only child I got" inji daddy cikin tsananin damuwa


"ka kwantar da hankalinka Alhaji, insha allah bazamu rasata ba, insha allah zata warke sumul kamar bata ta6a ciwo ba Amma fa kuma Saida taimakon ku, idan har ana son komai ya daidaita jininta ya sauka dole sai an magance matsalar Dake damunta don damuwa da tunani duk suka jawo wannan abin, dole a guji abinda zai qara sata damuwa har hakan yasake tasiri a zuciyarta don akwai matsala sosai"


Furzar da huci daddy yayi daga bakinshi yana lumshe idanu


Ya dade ahakan batareda yace komai ba sai kuma can ya miqe tsaye yana cewa
"shikenan Dr, muna iya ganinta?"


Shima Dr miqewa yayi
"sure, amma kamar yadda nace maka nayimata allurar barci yanzu haka ma barcin take"


"ok babu matsala muje mu ganta din"


Atare suka fito suka sake nufar ward din da zee ke Kwance.


Iske mummy sukayi aciki zaune gefen gadon da zee ke Kwance ta riqe hannunta daya tana kallonta


Tunda tajuyo tayimasu kallo daya bata qara kallonsu ba.


Qarasowa sukayi suma bakin gadon suka tsaya

Kallon zee da idanunta ke arufe daddy yayi cikin wani yanayi yana hango ramar datayi acikin yan kwanakinnan.


Sun dade a tsaye babu mai cewa uffan acikinsu can sai daddy ya juya ga Dr din yace
"Dr please take care of her, abata duk kulawar datake buqata"


"insha allah Alhaji, it's my duty though"

Kada kai daddy yayi sukayi musabaha sannan yajuya yafita.


Saida Dr yaqara dubata ya duba yadda drip din ke tafiya yaga komai normal sannan ya juyo kan mummy dake zaune jigum Tundazu


Rarrashinta da kwantar mata da hankali yaitayi yana assuring dinta komai zai daidaita sannan yafita yabarta da zee din a dakin.


Tunda daddy ya fita be sake dawowa ba sai wajajen 1 na rana kuma har lokacin bata farka ba.

Wannan karon ma ko gefen daddy mummy bata kalla ba har yagaji da tsayuwarshi yasake fita.


Wajajen 2pm wata maid takawo masu abinci asibitin bisa umarnin mummy.

Wajajen uku saura mummy na zaune gefen gadon zee tayi nisa a tunani sai jitayi kamar ana motsi


Saurin maida kallonta tayi ga zee taga itace ke motsin sai qoqarin bude idanunta takeyi


Saurin matsowa kusa mummy tayi tana Kamo hannunta

"daughter?" tafada cikin doqi


Ahankali zee taita kyafta idon gabadaya kafin daga bisani ta ida budesu ahankali


Ganin mummy tayi akanta tana kallonta tana murmushin murna

"Zainab kin farka?"


Batace komai ba sai lumshe idanunta datayi tasake budewa tanajin jikinta so weak


"bari na kira Dr kinji? 1 minute"

Daga haka saita juya ta fice daga ward din


Sake maida idanun tayi ta lumshe tana inhaling da exhaling ahankali.


Ba jimawa mummy tadawo tareda doctor

Babu 6ata lokaci yashiga duddubata


Saida yayi making sure komai is ok sannan ya kalli mummy yace tayi mata brush abata liquid abu mai dumi sai tasha magani.


Da to mummy ta amsa ta tashi shikuma Dr yafita


Da taimakon mummy zee tayi brush sannan tadawo ta hada mata kakkauran tea tana bata cikin kulawa


Sosai zee taji sanyi ganin yadda mummy ke nuna kulawa sosai gareta abinda ta manta rabon da tayi mata ko dayake bata Sakin jiki daita bare tasamu kulawar kullum daddy daddy ko mummy tayi yunqurin yin wani abin sai taqi Sakin jikinta kamar tana tareda wata bare amma yanzu gashi da aka 6ata da daddyn dole aka dawomata.


Saida tashanye tea din sannan mummy tasake kiran doctor din don yabata maganin

Tana cikin shan maganin daddy yashigo dakin.


Tunda taji muryashi ta sunkuyar dakai takasa dagowa ta kalleshi dukda wani feeling datakeji na daban ajikinta


Qarasowa daddy yayi cikin murna yanata hamdala dakuma godewa Dr sannan ya matso kusada zee da har lokacin kanta na a sunkuye

"daughter na?" ya kirata a tausashe

Sai jitayi hawaye sun kawomata a idanu

She missed him, so very much, batasan dahaka ba sai yanzu

"ya jikin?" yafada yana dafa kanta

Kada kai kawai tayi alamun da sauqi batareda ta dago ba don batason yaga hawayenta

Zama daddy yayi gefen gadon shima yana facing dinta ya kafeta da idanu while ita kuma ta kafe yatsun hannunta da idanu


Kamo hannun nata yayi ya riqe yace
"daughter na? Fushi kike da daddyn ki?"


Hawayen datake ta riqewa ne suka 6alle mata batareda ta shirya ba

Jawota yayi jikinshi ya rungumeta Hakan yasa tafara shesheka

"am sorry, am so sorry kinji, am sorry I hurt you, please forgive me" yafada yana patting bayanta itakuma tana cigaba da kukanta

Dago fuskarta yayi yayi kissing goshinta

"ina sonki daughter, bazan iya gangancin dazai sa na rasaki ba don idan narasaki kamar nima na rasa kaina ne, zan qara wata sadaukarwar daughter, zan sadaukar da farincikina Domin naki kamar yadda nasaba.

Na amince, na amince daughter, you can have Deen, allah yasa Hakan shiyafi alhairi"


Batasan lokacin da ta kwace kanta daga rungumar da daddy yayi mata ba tana kallonshi mouth agape


Itama mummy kallon daddy take idanu waje kamar zasu fado daga socket dinsu


Kada mata kai daddy yayi yana murmushi sweetly sannan ya kamo hannunta ya riqe

"ina iya bayar da komai saboda ke amma bazan iya bada ke ba saboda koma menene.

Bazan ta6a yafewa kaina ba idan na rasaki ta dalilin selfishness dina

Bazan ta6a rayuwa cikin farinciki idan babu ke acikinta ba


Kiyi hqr my daughter, I was selfish, I hurted you fiyeda tunani na

Nida ya kamata na kareki daga cutarwa da dukkan rayuwata saiya kasance nike cutar dake, am sorry, forgive your daddy"


Fadawa jikinshi zee tayi tana kuka sosai tana girgiza kai, she can't believe abinda Kunnuwanta ke jiyemata, kodai mafarki takeyi?


Bubbuga bayanta daddy yashiga yi yana rarrashinta sannan ya dagota yayi cupping fuskarta

"ya isa hakanan zee, Deen is now yours" yafada cikin murmushi

"D..dagaske?"


"bari kigani"

Saiya kalli kofa yace
"son!! Bismillah son!"


Duk maida kallonsu sukayi ga bakin kofar zee na jin yadda zuciyarta ke bugawa kamar zata faso qirji


Gani sukayi an murda handle din daga waje sai aka fara turo kofar ahankali

"Assalamu alaikum..." taji cool voice dinshi ya daki Kunnuwanta


Lumshe idanu tayi tasake budewa daidai shima ya ida Shigowa


Idanunta ne suka fada cikin oily bright eyes dinshi dake shining as ever.... ✍️


Juma'at mubaraq in advance � 🌜


Ummin fasihu 🧚🏻‍♀�
8/2/21, 9:38 PM - Buhainat😝: *🙍🏻‍♂️DEEN 🙍🏻‍♂�*


*050*


*THE INTRODUCTION*


Kasa ko kyafta idanu tayi akanshi kamar yadda shima Hakan yake a wajenshi.


Basusan sunyi missing juna ba har haka Saida sukayi arba da juna


11days, kwana shadaya rabonsu dasa juna a ido abinda be ta6a faruwa ba Tun bayan fara soyayyarsu.


Hakan yasa yanzu dasukayi arba da juna suka kasa Janye idanunsu akan juna


Ahankali ya tako still idanunshi akanta har ya iso bakin gadon shima daga bayan daddy.

Janye idanunshi yayi daga kanta sannan ya duqa ya gaida mummy


Cikin fara'a mummy ta amsa mashi tana sakejin qaunarshi har cikin zuciyarta

Miqewa yakeyi yana Tambayar mummy ya me jiki tana amsawa da da sauqi sannan suka gaisa da Dr yana tsokanarshi wai badai patient dinshi bane ya murmuje haka

Shidai murmushi kawai yayi yana sunkuyar dakai yana dan satan kallon zee da itama ta sunkuyar dakai ta wutsiyar ido.


Da daddaya suka fara barin ward din har yarage daga Deen sai zee


Dagowa yayi ya kalleta sai yaga haryanzu kanta a sunkuye yake sai yadanyi murmushi sannan yaja kujerar da mummy ta tashi akai ya zauna.


Tana jin yadda idanunshi ke piercing din fuskarta amma taqi Dagowa saima jujjuya Ring dinshi dake yatsarta datake yi


"ya jiki?" taji yafada ahankali

Ahankali ta Kada mashi kai batareda ta dago ba


"I missed you" taji yaqara fada


Ahankali ta dago itama ta kalleshi Saidai batace komai ba sai cigaba da kallonshi datayi


"kin rame" yasake fada ahankali

Hakan dayace yasa itama ta hango nashi ramar

"you too" tafada ahankali itama


Murmushi yayi
"dole na rame, kwana na 11 banga abincin ruhi na ba"


Dan murmushi tayi tana sadda kai tanajin duk wata damuwarta na fecewa daya bayan daya.


"am sorry for what kaka said, naso na dakatar daita amma taqi yin shiru" yafada yana kwa6e face

Dagowa tayi ta kalleshi
"da Gaskiyarta ai, wataqila wani abin daddy yayi muku"


Girgiza kai Deen yayi
"babu abinda yayimana kawai rudun tsufar kaka ne, daddy is very nice"


Dan murmushi zee tayi
"ka fadamin Gaskiya"


"na ta6a miki qarya?"


Shiru tayi don ta tunano ko ya ta6a din saiya katse mata tunanin da

"hankalina ya tashi sosai lokacin da kuka gama wayar da kaka, gashi inason miki magana amma kaka ta cire layin ta karya dole nafita wani shagon kati na ari wata wayar nakira but ba'a dagawa tun lokacin hankalina ya ida tashi don zuciyata na fadamin ba lfy. Jiya ko barci banyi ba"


Murmushi kawai tayi tana kallonshi not saying anything

"am glad you're ok now and am glad baxamu qara yin nisa da juna ba, daddy ya amince" yafada cikin doqi


Fadada murmushin ta itama zee tayi sai kuma ta dan 6ata fuska

"what?" inji Deen yana dan daga mata gira

"Kaka fa" tafada tana marairaice fuska


Dariya yayi
"Kaka too is ok with everything"


"dagaske?

"yes, sunyi magana da daddy dama duk rudun tsufa ne" yafada yana Dariya

"to don Allah me daddy yayi muku, naji tafadi Hakan jiya"

"babu komai fa nace miki"


"please tell me" tafada a marairaice


"please stop asking" Shima yafada yana karya wuya


"is it really bad?"

Daga kafadunshi yayi yace
"not that bad"


Zata sake magana ya katse ta ta hanyar cewa
"shhh, Kiyi shiru ba'ason marar lfy yana surutu"


Harararshi tayi zata sake magana yace
"shhh, Kiyi shiru, ni zanyi maganar kekuma sauraro ne naki, ok?" yafada yana dan Hade gira


Murmushi tayi ta kauda kai

Jin shiru yasa tasake juyowa ta kalleshi sai taga shima ita yake kallo

Daga gira daya tayi alamun ya?

Sai yayi mata murmushi
"I love you" yafada in whisper

Sauke idanunta tayi tana murmushi

"I love your face, your smile, your everything, don Allah ki warke dawuri mukoma school yadda zamu dinga hadewa kullum, kewarki nason kasheni"


Murmushi tasakeyi
"ni zan warkar da kaina?"


Girgiza kai yayi sai kuma ya bude taffukan hannunshi cikin sigar addu'a yace
"ya rabb kaba wannan baiwar taka lfy yadda zamu dinga zuwa school muna ganin juna kullum

Allah kasa ta maida qibarta karta tsaya haka kamar sugar cane"

Wara idanu zee dake sauraronshi Tundazu tayi tace
"kutt.. Nice sugar cane"


Jada baya yayi da kujerar yana Dariya

"sorry, to kamar fish bone"

Qara Wara idanun tayi shikuma ya cigaba da yimata Dariya.


Sun dade ahakan suna fira suna Dariya har mummy tashigo ta iskesu


Sosai mummy tayi mammakin ganin yadda ta gyagije kamar ba ita ba, fuskarta beaming in smile, sai a lokacin itama taqara jinjina soyayyarsu takuma qara tabbatar wa Deen shine farincikinta


Deen be qara dadewa ba yayi musu sallama yatafi don tareda yimusu alqawarin zasu dawo da kaka anjima


Ji Zainab tayi kamar tace mashi kar yatafi shima jiyake kamar kar ya tafi haka dai sukayi sallama rai babu dadi yatafi.


Sai a lokacin ta tashi tayi alwalla ta rama sallolinta na asuba dabatayi ba da zuhr sannan ta hada da asr da ake cikin yi lokacin.


Tana gamawa mummy ta gabatar mata abinci kuma taci sosai tasha magunggunanta


Kallo daya zaka mata ka fuskanci tana cikin farinciki dukda haryanzu zuciyarta na dar dar akan wannan al'amarin musanmman ma a 6angaren kaka da bata tabbatar da nata amincewar ba.


Sai wajajen biyar daddy yasake dawowa hospital din da siyyayar abubbuwan dayasan tanaso wanda mostly duk fruits ne, ya shaqo babbar leda dasu.


Sosai daddy yashiga tarairayarta fiyeda yadda yake mata ma da, tun bata ida Sakin jikinta dashi ba har ta gyagije suka koma yadda suke


Yana taredasu har magrib sannan ya tashi ya fita


Sai bayan isha'i yadawo tareda Deen da kaka dasuka Hade a waje


Tunda zee tayi ido hudu da kaka ta maida kanta qasa tanajin yadda gabanta ke faduwa don ita tunda ta fahimci kaka bata shiri da wanda ya ta6a mata Deen take taka tsantsan daita don ga dukkan alamu zatayi masifa


Saidai ga mammakinta sai taga akasin abinda tayi tunanin gani don lfy lau aka gaisa tayi mata ya jiki cikin fara'arta data saba yimata don harda guzurin kayan fruits datayo mata

Ganin Hakan yasa ta dan saki jikinta itama

Fita daddy yasake yi don yin magana da Dr don Gaskiya beson su kwana asibitin tunda taji sauqi gwara su koma gida duk yan ide iden da ba'ayi ba Dr yabiyosu har gida a ida.


Hira sosai kaka da mummy keyi kamar babu abinda ya faru, kwata2 babu wanda ya tada maganar misunderstanding din daya faru tsakaninsu saima firar duniya dasuke tayi abinsu


Sukau mutanenku yan saurare ne kawai, sun kasa kunne sai sauraron hirarsu mai cike da ban Dariya suke idan akayi abin ban Dariya sai su kalli juna suyi murmushi


Sun dan jima ahakan daddy yasake Shigowa tareda Dr

Saida aka sake gagaisawa sannan Dr yaqara dubata yaga komai normal sannan ya rubuta masu sallama bayan ya basu maggungunanta


Daga zee har Deen babu wanda yaji dadin sallamar don that means su da haduwa sai a school kuma


Sai wajajen 10 saura duk suka fito lokacin har daddy yasa an kawo wata motar dazata sauke su kaka gida.


Cikin farinciki da aminci suka rabu su kaka suka hau motar da bala zaija sukuma su daddy suka hau dayar motar inda daddy ne zai jasu sannan suka fito daga asibitin gabadaya kowa ya dauki hanyarshi.


Da kanshi daddy ya raka zee har dakinta yana lalla6ata kamar wata kwai


Saida ya zauna suka qara dan fira sannan ya tashi ya fita bayan sun yima juna Saida safe


Saida tayi wanka tayi shirin barci sannan ta haye gado ta kwanta don dama tariga taci abinci a can haka asibitin tasha maganinta.


Kwanciya tayi shiru idanunta akan p.o.p.

Takasa yarda haryanzu wai daddy ya amince da Deen.

Just like that? Saikuma ta tuna irin qaunar da daddy ke mata tabbas bazai ta6a barin ya rasata ba muddin yana da yadda zaiyi ya ceci rayuwarta

Murmushi tadanyi, da tasan da Hakan da duk ba'a kai yanzu ba, da tuntuni zatayi faking sickness din amma dukda haka alhamdullilah, what matters is ya amince din don haka bata tunanin tanada wata matsala a rayuwa.


Tunawa tayi da wayarta Hakan yasa ta miqe zaune tana waige waigen inda zata ganta

Can qasan gado ta hango ta tafiddo ta.

Danna power botton tayi sai taga takawo haske amma charge dinta yayi low


5 missed calls tagani a gaban screen din

Swiping tayi ta shiga call log sai taga baquwar number ce mai kiran

Har tafara tunanin waya kirata saita tuna Da Deen yace ya nemeta da wata wayar da ya aro, tabbas shine kenan.

Danna ma ainahin number Deen din kira tayi dukda taji yace kaka ta karya layin

Kamar kau yadda ta zata bata shiga ba hakan yasa ta kashe wayar gabadaya ta jonata a chaji takoma ta kwanta tana jin zuciyarta wasai


Bata wani jima ba barci ya sadado yayi gaba daita


Washegari garas zee ta tashi sai dan abinda ba'a rasaba.

Har daki daddy yazo dubata yakuma sata taci abinci yabata maggungunanta tasha.

Sosai yake kulawa daita kamar kwai

Yana nan zaune daita har wajajen 9am lokacin da Dr yashigo Domin duba lafiyar ta

Saida ya duddubata yaga komai normal sannan ya qara jaddadamasu akan ta cigaba da shan maganin akan lokaci insha allah zata ida warwarewa.


Tare da Drn daddy yafita don dama shi yake jira yazo ya duba mashi diyarshi kafin ya fita aiki.


Sai a sannan zee tasamu damar fitowa daga dakin itama tafara biyawa dakin Mummy suka gaisa sannan tadawo falon qasa ta zauna.


Tana ahakan wajajen 12pm kira yashigo wayarta

Dubawa tayi taga baquwar number ce

Kamar karta daga saikuma wani tunani yazo mata saita daga aikuwa hasashenta ne yazamo Gaskiya don Deen din ne


"patient"


Murmushi tayi
"waye Hakan?"

"kinfini sani, yaya jikin?"

"alhamdullilah, naji sauqi sosai"


Sautin murmushin shi taji
"masha allah, allah yaqaro sauqi"


"Amin ya allah" ta amsa tana yin filo da hannun kujerar datake akai


"yasu mummy?"

"mummy lfy lau, ina my kaka?"


"Your kaka tana nan lfy lau tana gaidaki da jiki"


Murmushi tayi
"ina amsawa sosai, nima ina gaida ta"


"to zataji... Baki tambayeni ba"


Dan daga gira tayi
"Me?"


"this strange number"

Murmushi tayi
"yanzun ma aro kayi?"


"nop, siyan wani layin nayi so you better save it"

Yadda yaqarashe maganar bossily yasata Dariya

"yes boss!" tafada tana Dariya


Shima dariyar yayi

"yaushe zakiyi resuming school?"

Daga kafadu tayi
"Don't know, qila saina ji sauqi"


"O'O! Ba kinji ba?"


"O'O! Ban ida warwarewa ba" tafada cikin kwaikwayon Maganarshi


Ko bata ganshi ba tasan 6ata fuska yayi
"please get well soon, am missing you badly"


Murmushi tayi kawai amma gani take duk missing dinta dayake bekai wanda takeyi ba

"insha allah" tafada tana murmushi

"kinga exams nata matsowa, we have alot to cover"


"yeah, insha allah ai Dr ma yace naji sauqi sosai saura strenght dina ya dawo"


Jitayi yace
"Ya rabb kadawo mata da strenght dinta ta tashi tajita da qarfi kamar super man"


Dariya tayi tace
"da kaine punching bag dina na farko"

Wara idanu yayi daga can 6angaren

"Ca6 baxaki iya ba"

"why not?"


"saboda fuskata ba don punching akayita ba, bazaki iya dora ko yatsa daya akanta ba da sunan duka bare naushi"


"Me zai hana?"


"kyawun ta mana"


Dan wara idanu tayi
"fahari ko?"


"No, Gaskiya ce ai"

"tayaya to kasan tanada kyau"


"nasani mana, ba ina duba mirror ba"


Dariya ya bata amma batayi ba

"haba? Namiji dama na duba mirror?"

"baya dubawa dama?"

"haka nazata"

"to nidai ina dubawa"


"to kuma yaya akai ka gane kyawun?"


"ba nagani a mirror ba?"


Dan gasping tayi cikin mammaki 😱
"dama mutum idan ya kalli kanshi a mirror yana gane kyawunshi?"


Cikin confusion yace "ke idan kika kalli mirror bakya ganin kyawunki?"


Dariya tayi marar sauti sannan tace
"A'a ni ban ta6a gani ba"


"to me kike gani?" ya tambaya confused


"kawai dai nasan nice, thats all"

"bakya kallon large white eyes dinki, da pointed hancinki da qaramin red lips dinki da cute kumatunki da long lashes dinki, duk bakya tsayawa kallo?"


Dariya taqara yi tana rufe bakinta don karya ji

"ni duk bana gani kawai nadaisan nice kawai and the moment na ajiye mirrorn saina mance yadda fuskar take"


Wara idanu yayi
"yanzu bakya gane fuskarki without mirror"


"ko kadan, kai kana ganewa ne?" tafada tana qumshe Dariya jin ya dauki abin serious


"Are you kidding me? Tayaya za'ayi na mance fuskata? Nine fa?"


"abin mammaki, kenan kana iya gane kanka? Tayaya zaka iya riqe fuskarka ba Saidai wani ya riqemaka ba tunda ba ganin kanka kake ba?"

Qara shiga confusion yayi yace
"to Saidai idan bakida lfy amma tayaya za'ayi ki kasa gane fuskarki?"


Dariyar datake riqewa Tundazu ya kuce mata tashiga yi


Ajiyar zuciya ya sauke


Cigaba da Dariyar tayi

"Gaskiya yakamata Dr yaqara duba ki, I wonder yadda ma akayi na yarda da maganar ki tunfarko bayan nasan bakida lfy"


Wara idanu tayi still tana Dariya

"nice banida lafiyar?"

"ga zahiri?" Shima yafada yana Dariya


Haka sukaita firarsu Saida yan kudin da Deen yasa suka qone sannan.


Bata sake bugamashi ba ta tashi ta haye sama don tasan idan ta bugamashi kuma sai allah yayi don ita ko awa zasuyi kudin bazasu qare ba gashi idan suna waya basu iya taqaita ta ba don dasun fara mancewa da komai suke sai kansu kadai


*fast forward*


A cikin kwanaki uku zee ta warke sumul kamar bata ta6a ciwo ba


Sosai take samun kulawa a wajen iyayen nata musanmman daddy dayake riritata fiyeda yadda yakeyi ada.

A bangarenta da Deen kau sai abinda yayi gaba don kodayaushe suna maqale awaya suna firarnan tasu mai antaya kowannensu acikin nishadi.

Ata koina komai tafiya yake masu so smoothly sun mance da wata aba wai damuwa.


A ranar da yakama kwana biyar da kwanciyar zee hospital wanda yayi daidai da ranar asabar da daddare lokacin kwanciyar su mummy.


Suna Kwance suna firarsu kamar yadda suka saba

Daddy ne ya qara fuskantar mummy sannan yace
"ya kika ga daughter na yanzu? Very cheerful and lively"


Murmushi mummy tayi
"hmm kaidai bari, ai yaran zamanin kenan, baka yimasu dole idan kuma kayi kai zaka fara ganin sakamakkon shiyasa muddin kasan abinda sukeso mai kyau ne kawai ka miqa wuya"


"ai naso nayi ganganci maimuna, dana rasata ai shikenan na shiga uku"

Dariya mummy tayi ganin yanayin daya fadi ya shiga ukun.


"Ato ai kaine wani sa'in baka jin shawara, wlh ni tunda ta ambaci sunan yaron nan naji hadin yayi min don Gaskiya yaron yanada wata baiwa da ba kowanne keda ita ba, ga nutsuwa uwa uba ladabi. Wlh tun a asibiti halayyar yaron nan ke burgeni Gaskiya kaka tayi qoqari"


Murmushi daddy yayi
"ai nima naso tafka babban kuskure, don nagartar yaron na tabbatar da nagartar shi kawai selfishness ne dakuma burin dana dauka na dorawa auren daughter na ne, I thought hamshaqin mai kudi zata kawo shiyasa data kawo wannan naji nakasa yarda"


"ai kudi ba shine farinciki ba, yara nawa suke auren masu kudin amma kaga babu kwanciyar hankali? Kaga sai bushewa suke a tsaye bayan akwai komai na more rayuwa a gidan, kawai fatan miji nagari shiya dace ga kowacce diya mace ba bawai kudi ba don wasu ga kudin amma rashin kwanciyar hankali ya hana sucisu cikin jindadi" inji mummy


"ai duk na gane Hakan yanzu, na zauna nayi karatun ta nutsu nagano money is not everything kuma nayi bincike akan hallayarshi nasamu nagarttatun result, shiyasa na yanke shawarar gayamashi ya turo ranar laraba idan allah ya kaimu"


A mammakince mummy ta juyo tana kallonshi

"turowa kuma?"

"yes, yaturo ayi Introduction"

"but why the rush?" inji mummy still cikin mammaki


"hmm ke baki san halin da ake aciki bane
Allah yayiwa diyarki farinjinin masoya, mutanen dake tunkarata da son abasu ita ko wa 'ya'yansu ko wa kansu basuda iyaka, kullum cikin atracking dina suke akan maganarta amma saboda nayi alqawarin bazan yimata dole bane yasa duk bana maida hankali akai Saidai nace suje su tunkareta idan ta amince dasu to ni banida matsala

Dukda Hakan ban tsiraba kullum cikin zarya ake wajena shiyasa na yanke shawarar kawai sawa zanyi yaron datake so ya turo a daidaita magana kinga duk wanda yaji an badata bazai qara damuna ba"


Shiru mummy tayi sai kuma ta Kada kai
"kuma fa hakane, amma sai inga yayi wuri dayawa abari takusan gama school mana"

"ai ba auren za'a daura ba bakuma sa biki za'ayi ba kawai introduction ne, ma'ana suzo neman auren ta ya kasance an tsayar da magana, kinga idan shi yayi graduating yafara service sai asa bikin lokacin dazai gama service sai a daura auren dama kuma nariga na fidda post dazan bashi a daya daga cikin companies dina kinga sai suyi settle down ga mata ga aiki, ko yaya kika gani?"


Tuni mummy tahau fara'a batasan sanda ma tayi mai half hug ba

"perfect! Hakan yayi sosai wlh, kai amma naji dadi"


Murmushi daddy yayi ganin yadda mummyn ke murna sai yace
"kinga basai acemashi ya turo wannan larabar ba, basai sun takura kansu ba da kawo kudi yanzu duk mun zama daya kawai fatanmu allah yasama abin albarka"


"Amin ya allah Alhaji, Gaskiya bansan yadda zan iya musalta maka farincikin danake ciki ba, am supper happy, at last nafara jiyo qamshin auren diyata"


Dariya daddy yayi ganin yadda ta rikice don murna sai yace
"wayaga uwar amarya"


Jujjuya idanu tayi
"hmm za'ayi abu" tafada cikin cin buri


Dariya daddy yasake yi yace
"to yanzu sai agayama su mutanen Ruma ko sai asamu kosu yusuf suzo"


"har saisun zo?"


"yo ba diyarsu bace? Ni nan kinsan banida yayye ko qanne maza sai only qanwata JAMILA(ummu batool) kuma ba anan qasar suke ba bare nace mijinta ya wakilceta

Kinga idan daya daga cikin kawunnan nata na Ruman suka zo sai nasamu aboki ko daya nima ayi zaman tunda kawai introduction ne basai anyi wani gayya ba"


"hakane wlh, Gaskiya tsarin yayi, allah ya taimaka yasa ayi taro lfy a watse lfy"


"Amin amin Hajiya ta, insha allah bikinnan zai zama one in town, zamu jijjiga Katsina"

"Allah Alhaji na" tafada cikin tsananin jindadi

"Allah hajiyata"

Da wannan firar suka kwanta a ranar kowa zuciyarshi fess.


Washegari ummu batool ce ta fashe kwan wa zee don ita batasan anayi ba Saida ummu batool din ta kirata tana kodata tana cewa tun saura wata biki zasuzo nigeria su tare don sune amara qirjin bikin

Tace ba don daddy ya hana ba da dasu za'ayi introduction din


Itadai zee haka taita biyemata da Dariya ba don ta fahimci zancen nata ba Saidai kawai tadanyi Dariya cikin wayancewa

Saida suka gama Gaisawa da ummu batool din sannan taba batool din itama suka gaisa da zee inda itama take tsokanar ta da sunan amarya

Ahaka dai tasamu a daddafe tagama wayar sannan ta tashi da gudu tayi dakin Mummy


A rikice take gayama mummy yadda sukayi dasu ummu batool tana Tambayar me suke nufi


Murmushi mummy tayi na manya sannan ta fadamata abinda ke shirin faruwa.


Zee was so shocked, dumpfounded, Happy, tama rasa wanda ya rinjayi wani a feelings din


Tambayar mummy tayi tace tun yanzu? Sai mummy tayi mata bayanin da daddy yayi mata itama jiya.


Murna a wajen zee ba'a magana don Tsalle tayi ta rungume mummy tana ihun murna babu ko kunya


Tureta mummy tayi daga jikinta sannan ta fattatakota waje wai tafitar mata a daki tunda batada kunya


Dakinta zee takoma tana cigaba da tsallen murna, she can't believe wai Deen zaizo neman aurenta ne


Dafarko harta dauki waya zata kirashi saikuma ta tuna ba ita ya kamata tafara breaking din news din ba atsakaninsu shi ya kamata yafara

Hakan yasa ta maida wayar ta ajiye ta cigaba da murnarta


Koda daddy yadawo da marece har daki tabi shi Domin bayyana mashi farincikin datake ciki don dama ita bawani kunyarshi takeji ba


Sosai daddy shima yaji dadin ganin irin murnar datayi yana kuma alfahari da kanshi ganin ya wanke mata zuciya tass.


Sai daddadare tasamu kiran Deen wanda dama wayar na hannunta tana kallonta every now and then don ganin ta inda kiran zai shigo.


Duk yadda tayi tunanin Deen zaiyi murna Saida ya wuce nan don har abin Saida yasata shauqi

Sosai yake bayyana murnarshi yana cewa yana jin kamar ya jawo ranar tazo ko zai huta don bayada tabbacin zai samu isassun barci cikin dararren nan na kafin ranar


Itadai zee Dariya Kawai take mashi tana sauraron sambatun nashi tana kamar babu wanda yakaita farinciki a duniya.


Yan Ruma labari yakai musu, sosai sukayi murna da wannan al'amarin don sai bugowa ake tayi ana allah ya sanya alhairi dukda bawai bikin za'asa ba sai aka wakilci kawu yusuf don yaje don dayan bayama garin.


Shiri akeyi sosai na ranar a gidan su zee, kowanne ka gani kasan cikin farinciki yake don ace labarin zuciya a tambayi fuska, kallo daya zaka ma ahalin gidan suna cikin jubilation


A bangaren zee da Deen wata sabuwar soyayya ce suke shimfidawa ta waya

Koda yaushe maganar Deen bata wuce ya qagara ranar tazo, jiyake kamar ya tariye ranakun azo daidai ranar

Itadai Saidai tayi ta yimashi Dariya tace ya cika zumudi.


*WEDNESDAY*


Tunda safe aka fara shirye shiryen tarbar baqi

Sosai aka gyara gidan musanmman can 6angaren baqi don anan za'ayi zaman wanda aka fidda za'ayi qarfe 3:00pm


A kitchen kuma kayan snacks ake hadawa na musanmman saboda baqi


Tun 12pm Kawu yusuf ya qaraso daga Ruma.


Yasamu tarba mai kyau wajen mummy da daddy

Anan aka kira mashi Zainab da tazo tanata wani sunne sunnen kai wai ita kunya


Tsokanarta kawu yusuf yashiga yi su daddy nayimata Dariya itakau Saidai ta sunne kai tana murmushi


Saida sukaci abinci sannan daddy da kawu yusuf suka fita sallar zuhr


Lokacin dasuka dawo yayi daidai da lokacin da abokan daddy suka iso duk manyan mutane, da Alhaji Abubakar (baban Asaad) da wani Alhaji bello.


Wucewa sukayi bangaren daddy suka zauna sunata firarsu na manyan maza ana raha an cika masu gabansu da kayan motsa baki Suna ci suna fira suna jiran isowar mutanen Deen.


*03:15pm*


Zaune zee take gaban dressing mirror tana qarasa daurin dankwalin kanta tana humming waqa ahankali cikin nishadi


Jitayi an murda kofa an turo Hakan yasa tadan dakata tajuyo tana kallon mai shirin Shigowa


Mummy ce Hakan yasa tayi saurin sadda kai don kunyarta takeji sosai

Qarasowa mummy tayi wurinta ta tsaya

"mummy welcome" tafada cikin jin kunya


"yauwa, nace kunyi waya dashi ne?" inji mummy fuska babu walwala

Cikin rashin fahimta tace
"waye?"


"Kamal mana, yabar mutane Tundazu sunata jira shiru ko besan lokacin da akayi fixing bane?"


Gaban zee ne ya yanke ya fadi

"b.. Basu zoba?" inji zee cikin dan rawar murya


"da sunzo da kin ganni anan? C'mmon bugamashi kiji lfy suka tsaida mutane haka?"


Saurin tashi tayi jiki na dan rawa ta jawo wayarta dake kan gado tashiga laluben number shi wanda last call dinsu jiya daddadare ne Dakyar ma suka rabu a wayar don qin bari yayi su ajiye wayar dukda yadda wayar shi ke mashi low battery daga qarshe ma kiran katsewa tayi wanda bata raba dayan biyu chajin ne ya ida qarewa ta mutu


Danna ma number kira tayi amma aka bata amsar _switch off_


Dagowa tayi ta kalli mummy taga itama ita take kallo

"ya dai?" inji mummy

"wai akashe" inji zee


"akashe? Why zai kashe wayar shi a irin wannan ranar?" inji mummy wanda Alamu sun nuna tafara fusata


"wlh ban sani ba Amma jiya damuke waya yayi min complain wayar babu chaji don sai warning suke mashi, qila mutuwa tayi" tafada tana jin zuciyarta na gudu har lokacin


"ta mutu kuma shine bazaisa charge ko yakai a samashi ba?
Mutanen nan tun after 2 suke anan zaune amma ace haryanzu shiru? Uku kusan da rabi?"


"bari na sake gwadawa" tafada tana qara danna mashi kiran amma the same amsa ne
_switch off_


Daidai nan daddy shima yashigo dakin cikin shigarshi ta alfarma da yayi musanmman domin ranar

"wai ya haka? Daga aikoki kema shiru?" inji daddy yana kallon mummy


"hmm gamunan munata neman number yaron muji lfy mukaji shiru amma wai switch off?"


"number tashi?" inji daddy

"eh mana" inji mummy cikin takaici


"muga number daughter" yafada yana qarasawa wajen zee daketa faman sake re-trying number

Shima kira yayi amma amsar dayace, akashe take.


"to babu number wani nashi dakuka sani? Ko kaka?"


"Kaka batada waya" inji zee cikin sanyin jiki


"muga number" inji mummy

Kallon number tashiga yi

"wannan ai ba number bace ba" inji mummyn


"ai ya chanza layine wancan ya fadi" inji zee dake jin kamar tayi kuka


Ajiyar zuciya daddy ya sauke sannan ya duba agogon hannunshi


"yanzu 3:40pm bari mushiga sallar asr qila kafin mufito sun iso maybe wani abu ya tsaidasu, allah yasa lafiya"

Duk shiru sukayi jigum babu mai amsawa

"ku saki ranku mana, insha allah they're on their way, kuma kuje kuyi sallan kafin mugama zasu iso"

Da Hakan ya juya ya fita.


Kallon juna zee da mummy sukayi saikuma zee ta sauke kanta qasa

Ajiyar zuciya itama mummy tayi tace
"kije kiyi sallar gashi kin 6ata fuskar da kwalliya sai kije ki wanke"


"ai inada alwallata" inji zee a sanyaye

Ta6e baki mummy tayi ta fice itama


Komawa zee tayi ta zauna gefen gado tana tunanin meyasa haryanzu mutanen Deen basu qaraso ba?


Bata daddara ba taqara dago wayar hannunta taqara dannama number shi kira amma still *switch off*..... ✍️


Ummin fasihu 🧚🏻‍♀�
8/2/21, 9:38 PM - Buhainat😝: *🙍🏻‍♂️DEEN 🙍🏻‍♂�*


*051*


*THE LETTER✉️*


Sauke wayar daga kunnenta cikin damuwa


To ya akayi haka?

Ita a tunaninta ma su mutanen Deen din su zasuyi jira basu za'a jiraba duba da yadda Deen ke zumudin abin.


Meyasa wayar shi take a kashe? Koda jiyan ta mutu ai yaci ace yanzu yasamu charge koma ina ne.

Anya kau lfy?


Ta jima tana wadannan tunane tunanen sai kuma ta tashi tashige toilet ta wanke makeup dinta sannan ta daura wata alwallar tafito tana jin zuciyarta babu dadi


Shimfida sallaya tayi ta hau kai ta tada sallah.

Tun kafin ta ida mummy tasake Shigowa dakin ta zauna gefen gado tana jiranta.


Sallame sallar tayi sannan ta juyo ahankali ta kalli mummy

Expression din fuskar mummy kadai ya isa yabata amsarta

"wai what's all these ne? Yanzu 4:10pm amma haryanzu basu qaraso ba, qarin har awa daya da Mintuna? Kamata yayi ace Koda matsala aka samu su bugo sufadi atleast Hakan zai fidda zuciyoyinmu daga wasiwasi" inji mummy Cikin 6acin rai


Sadda kanta kawai zee tayi qasa tana jin hawaye na kawo mata, tama rasa wane tunani zatayi


Ringing wayar mummy ta dauka Hakan yasa taja Tsakin takaici kafin ta ciro wayar ta duba mai kiranta

Daddy ne


Dagawa tayi ta qara a kunne

"ya ake ciki yanzu?" inji daddy a wancan bangaren


"hmm nima bansaniba, wannan ai wulaqanci ne a tara manyan mutane a shanyasu? Idan sunsan basu shirya ba ai kamata yayi su sanar tun wuri a daga ranar"


"yanzu dai calm down maimuna, bari na aika bala yaje ya gano ko lfy?"


"haba Alhaji, kamar muna neman kai daita? Ina aka ta6a haka? Kawai a kyalesu ka sallamesu"


"A'a maimuna, ta yiwu wani abin yafaru wanda dole Hakan ya tsaidasu kuma basuda hanyar reaching dinmu bare su bugo su gayamana, muyi musu uzuri, shima balan ai ba shiga zaiyi ba, kawai zuwa zaiyi as C.I.D ya gano me gidan yake aciki"


Shiru mummy tayi amma allah yasani ranta a mugun 6ace yake


"bari nasan abinda zan gayamasu baqin don Gaskiya suma sun fara qosawa da wannan al'amarin kafin nan bala yadawo sai muji daga gareshi"


"to shikenan" inji mummy Cikin cinkushewar rai sannan suka katse wayar atare


Kallon zee da haryanzu kanta ke a sadde tayi sai kuma ta tashi ta fita daga dakin


Dagowa zee tayi tabi mummy da kallo da watery eyes dinta don tunda ta sadda kai take hawaye.


Tashi tayi daga kan sallayar ta ninketa ta ajiye sannan taqara daukar wayarta taje daidai bakin window inda ake iya hangen harabar gidan daga nan ta yaye labulen tana kallon harabar tanan


Daddy taga yana magana da bala sannan taga balan yanufi parking space shikuma daddy yakomo cikin gida


Ajiyar zuciya ta sauke sannan ta maida hankalinta akan wayar hannunta ta cigaba da kiran number Deen din amma shiru.


Wasa wasa har qarfe 5pm shiru babu mutanen Deen babu alamun su


Zainab tana tsaye still a bakin windown tana kallon harabar gidan kamar mai son ganin ta inda zasu 6illo.


Jitayi anyi horn a gate din Hakan yasata zabura ta qara yaye labulen tareda zubama gate din idanu zuciyarta na bugu sosai


Hango security tayi ya fito da gudu ya nufi gate yafara qoqarin budewa


Babu addu'ar da batayi ba a zuciyarta na allah yasa su ne amma sai me?


Sai gani tayi motar da bala yafita daita ne tadawo.


Qurawa motar idanu tayi in utmost disappointment tana jin kamar zuciyarta zata fashe.


Bala ne taga yafito daga motar sannan taga ya dan yi danne danne a wayar shi ya kara a kunne


Be dade yana magana ba ya sauke wayar ya cigaba da tsayuwa a inda yake


Can jimm kadan saiga daddy yafito yazo ya tarda bala din inda yake tsaye


Gani tayi suna magana, dukda batajin abinda suke cewa tasan koma menene ba alhairi bane duba da yanayin fuskar daddy.


Gani tayi daddy ya dafe kai yayi shiru saikuma ya cigaba da magana kamar ma a 6acin rai yana yi kamar zai make balan shidai balan kansa a qasa yake bece komai ba


Can kuma daddy ya juyo a fusace ya nufo hanyar cikin gida


Sakin labulen tayi ta dawo ahankali kamar wanda kwai ya fashe mawa aciki ta xauna gefen gado tayi wa waje guda quriii.


Ba'a jima ba taji an bude kofar dakinta an shigo


Dagowa tayi ahankali tana kallon daddy daya shigo din


"daughter wai what's going on ne?"
Cigaba da kallon daddyn tayi don ita kanta Tambayar da taso yimashi kenan


"na aika bala gidansu amma yadawo ya fadamin wai gidan a rufe da kwado wai ya tambayi mutane sunce suma basusan whereabout dinsu ba, meke faruwa ne?" inji daddy


Kasa ko kyafta idanu akan fuskar daddy tayi

_kofa arufe da kwado? Me kenan?_


"am talking to you Zainab kinyi shiru kin quramin ido, yaushe rabon da kuyi waya?"


Cikin wata murya da ita kanta bata tantance ko tata bace tace
"jiya... Jiya da daddare"


Daidai nan mummy tashigo dakin


"wai ya ake ciki ne?" inji mummy tana kallonsu


Ignoring dinta daddy yayi ya cigaba da yima zee magana

"da kukayi wayar be fadamiki wani abu ba, something concerning taron yau?"


Tunawa tayi da kadan daga cikin magangganunshi na jiya

_gobe ne ko?_

Murmushi tayi kawai batace komai ba

_gobe ne ranar, wannan daren zai kasance daya daga cikin tarihin rayuwarmu, dare mai tsayi, mai duhu mai cike da jira. Nasan wannan daren zai kasance mafi tsayi agareni, zan qarara gari ya waye ko zai yaye min duhu da damuwar zuciyata amma zaiqi wayewa sai nayi jira jiran da bansan adadin shi ba_

Murmushi tasakeyi tace
_karka damu duk nisan dare ai gari zai waye, duk jiran dazakayi mashi kasa a ranka a kowanne passing seconds ragewa yake safiya kuma na kusantowa, fatan mu anan shine allah yakai mu da rai da lfy_


Sai yace
_amin Zainab, amin zanso yayi saurin wayewa Zainab, zanso yayi saurin wayewa kafin zuciyata ta gaza hqr ta buga_


Dariya tayi mashi sannan tace
_bazata ma buga ba baban zumudi_


Murmushi mai sauti taji yayi sai yace
_I LOVE YOU_


"wannan wane salon wulaqanci ne ana miki magana kinyi shiru?" inji mummy a fusace

"A'a maimuna ki kyaleta babu ruwanki, dani da ita muke magana" inji daddy sannan yasake maida hankali kanta

"inaji daughter, kunyi wata magana data shafi yau"


Girgiza kai tayi ahankali sannan tace
"A'a saima zumudin dayake yi wai he can't wait gari ya waye"


Duk shiru dakin ya dauka

"wai Alhaji balan yadawo ne?" inji mummy


"eh amma wani abu wai ya tarda gidan arufe wai kuma ya tantambaya wai suma haka suka wayi gari sukaga gidan"


Shiru dakin yasake dauka babu mai cewa komai.


Sun dan jima ahakan daddy ya saki Ajiyar zuciya sannan ya kalli agogon hannunshi

"6 saura minti biyar"


"Alhaji kawai ka sallami mutanen nan, ba zuwa zasuyi ba" inji mummy Cikin dacin rai


Shiru dakin yasake dauka

"innallilahi waina ilaihi rajiun, yanzu ta ina zan fara musu bayani ma?" inji daddy cikin tsananin damuwa


Zee kanta na sadda takasa controlling din hawayenta


"ya zamuyi kawai afadamasu meke faruwa babu wani 6oye 6oye, sun dai maida mu qanannun mutane kawai" inji mummy Cikin dacin rai


Jigum suka sakeyi kowa rai babu dadi saikuma daddy ya juya

"bari naje na barosu su kadai"

Saiya juya ya fita


Itama mummyn Jigum tayi tana kallon wuri guda saikuma itama ta bude kofar tafita.


Baya zee tayi ta kwanta kan gadon ta kafe p.o.p din saman, tama rasa tunanin da zatayi


A bangaren daddy kau zuciya ba dadi yayi musu bayanin komai nan take suka shiga jajantawa duk zuciya babu dadi inda suke Fatan allah yasa dai lfy.


Haquri daddy yayi ta basu akan zaman jiran gawon shanun da sukayita yi sukuma suna nuna babu komai ai Indai lfy tau alhamdullilah kuma idan suka dawo aka sake fixing rana a sanar dasu zasu dawo insha allah.


Da Alhaji Abubakar da Alhaji Bello suka wuce shikuma Kawu Yusuf don dole daddy ya riqeshi akan yabari sai gobe yatafi tunda har magrib tayi, haka ya haqura ba don yaso ba.


Tare suka wuce masjid don yin sallar magrib suna tafe suna firar dalilin dayasa mutanen Deen basu zo ba Suna fatan allah yasa dai komai lfy.


A bangaren zee kau sosai abin ya tsaya mata a zuciya takasa komai

Ta rasa aciki me yafi damunta, rashin Zuwansu mutanen Deen ko rashin sanin halin da yake ciki.


Banda hawaye babu abinda takeyi Dakyar tasamu itama ta tashi tayi sallar magrib ta kuma zauna anan tayi nisa a tunani har akayi sallar isha'i taje ta chanza alwalla tadawo ta miqata itama.


Komawa tayi saman gado ta zauna jigum waya a hannunta har lokacin bata haqura da neman number tashi ba.


Tana ahaka maid tashigo dakin akan ta sauko dinner is ready

Cemata tayi ta tafi batajin yunwa

Jin haka yasa daddy zuwa dakin nata da kanshi ya lalla6ota dakyar yasamu ta fito dining din.


Saida ta gaida mutanen wajen cikin dashashen muryarta sannan ta zauna a kujerar da daddy yaja mata baya


Zuba mata abincin daddy yashiga yi yana cewa
"daughter please ki saki ranki, ki tuna da problem dinki, kibar saka abin arai sosai insha allah komai will be ok, kinji?" inji daddy Ahankali cikin sigar rarrashi


Batace komai ba sai riqe fork din datayi tana dan motsa abincin ahankali


Kawu Yusuf yace
"Gaskiya ne diyata, karki bari abin ya dameki kinji? Insha allah zamu ji daga garesu soon"


Itadai mummy ko dagowa batayi bare ta Ko kalli gefenta, abincinta kawai takeci amma ita kadai tasan irin 6acin ran datake aciki yau.


"amma fa abin da daure kai, ina zasuje haka daxaisa suyi watsi da abu mai matuqar muhinmmanci irin wannan?" inji daddy


"nima abinda ya daure min kai kenan Alhaji, koma menene kamata yayi su sanar sai ayimusu uzuri da lamunin daga ranar zuwa wani lokacin amma ai ba Haka akeyi ba ka tara mutane ka koma gefe kayi shiru ka barsu a shanye ba"


"hmm to mudai fatanmu allah yasa lfy, duk wani abu dazai biyo bayan wannan mai sauqi ne" inji daddy


"Amin fa Alhaji, fatanmu kenan" inji Kawu Yusuf din.


Haka suka qaraci firarsu da daddy da Kawu Yusuf su mummy iyakarsu sauraro don babu wanda ya iya tankawa cikinsu, su kadai sukasan abinda sukeji a zuciyoyinsu.


A daren ranar kasa isashen barci zee tayi, banda juyi daga farkon gado zuwa qarshenshi babu abinda takeyi


Kwata2 takasa samun kwanciyar hankali bare salamar ruhi, ranar Saidai tayi barci rabi da rabi tasamu gari ya waye a daddafe.


*WASHEGARI*


Saida Kawu Yusuf yakai har 12 rana don jiran jin ko zasu samu wani feedback daga family dinsu Deen Amma shiru Hakan yasa yayi musu sallama ya kama hanyarshi ta komawa yana cewa duk yadda akayi sun gayamashi ta waya.


Ranar ma haka ahalin gidan suka wuni cikin baqinciki don kwata2 babu alamun su Deen nada niyyar zuwa ko kira aji yaya ake ciki taqamaimai.


Izuwa yanzu hankalin zee yafara tashi don ita yanzu ba rashin zuwan nasu ne yafi damunta ba rashin sanin halin da suke ciki yafi damunta gashi haryanzu numbershi bata shiga kwata2, daga jiya zuwa yau amsa dayace duk lokacin data buga wayar, switch off


Tun tana daurewa tabar abin iya cikinta har takasa ta tunkari daddy da maganar don ko giyar wake tasha bazata ta6a nufar mummy da wannan maganar ba don haryanzu mummy bata sauka daga 6acin ran datake aciki ba


Koda ta fadama daddy abinda ke damunta dakuma fargabar kar ace ba lafiya ba sai shima ya damu yana jin Gaskiya ya kamata a bincika Hakan yasa ya qara aika bala unguwar tasu Deen don ganin ko sun dawo gidan


Amma daya dawo amsa daya ce haryanzu, gidan a kulle yake still da kwado kamar dai yadda ya ganshi jiya.


Sosai hankalin zee yaqara tashi.

To meya faru?

Ina suke?

Yaushe zasu dawo?

Dama sauran tambayoyi da dama keta kai kawo a qwalwarta wanda duk babu mai bata amsoshinsu.


Ganin yadda ta tashi hankalinta yasa shima daddy shiga damuwa sosai don shi yanzu baya qaunar abinda zai sakata a damuwa saboda maganar Dr dayayi akan a kiyayi barinta cikin damuwa, he can't afford to loose his only daughter just like that Hakan yasa yaita rarrashinta da kalamai na kwantar da hankali yana assuring dinta insha allah gobe zaije shima da kanshi yagani da kanshi.


Hakan yadan kwantar mata da hankali har tadan samu taci abinci kadan wanda shima tutturawa kawai tayi bawai don dadi ba don kwata2 rasa abinda ke mata dadi a duniya tayi ga wani fargaba ta musanmman data addabi zuciyarta


Mummy kau duk abinda suke ko kallo basu isheta ba don ita tun jiya zuciyarta ke cinkushe.


Tarasa ma a wane siga zata kalli wannan al'amarin

Qin zuwa sukayi da gangan koko akwai dai abinda ke faruwa?


Sosai ranta ke a dagule saboda wannan abin daya faru Saidai kuma haryanzu takasa dora laifin akan Deen ta kuma kasa yarda da abinda zuciyarta ke saqamata na kodai Deen yaudarar zee yake dama bawai auranta yake so yayi ba?

Da wannan tunanin yazo mata sai tayi saurin kawar dashi tana girgiza kai don Gaskiya Deen beyi kama da mayaudari ba kuma tana hangen soyayyar zee a idanunshi tsantsarta, to a ina matsalar take? Tabbas akwai lauje cikin nadi.


Washegari kamar yadda daddy yayi ma zee alqawari wajajen bayan 12pm na rana ya shirya tsaf don zuwa dubowa shima don tunda gari ya waye zee ta matsa mashi akan Hakan


Itadai mummy haryanzu batace uffan ba akan komai ba, yima takeyi kamar batasan sunayi ba.


Har parking space ta raka daddy din tana jin kamar tace zata bishi itama suje su dubo tare.


Saida taga fitarshi daga gidan sannan ta juyo a sanyaye tadawo falo ta zauna a kujerar da take facing kofar Shigowa ta raku6e ta zubama kofar idanu tana jiran ganin ta inda daddy zai dawo.


A lokacin idan kaga Zainab dole tabaka tausayi, tawani yi laushi ta sururuce, kallo daya zaka mata kasan tana cikin damuwa sosai.


Ta dade anan zaune tana counting down din seconds daya gota ma agogo tana jiran ganin dawowar daddy, deep down kuma addu'a kawai takeyi allah yasa adace don yanzu idan akwai labarin da zaisata cikin matuqar farinciki to na ganin Deen ne, kawai ita dai burinta aganshi a tabbatar da lafiyarshi lau.


Har 2pm ta gota daddy be dawo ba hakan yasa ta tashi don dole ta wuce sama don yin sallar zuhr.


Tana zaune akan sallaya ta gama sallah taji horn din mota a bakin gate


Aikau babu shiri ta tashi tsaye tanufi windon nan da sauri ta yaye labulen


Motar daddy ta hanga tashiga parking space.


Sakin labulen tayi ta juyo tanufi kofa da sauri.


Budewa tayi ta fita ta sauko stairs din tana tsallakesu da bibbiyu harta samu ta ida saukowa.


Daidai takai hannu a handle aka murda handle din daga waje aka turo kofar.


Jan burki daddy yayi da farko ganinta a bakin kofar saikuma ya Kamo hannunta ya maida kofar ya rufe ya shigo falon still jaye da hannunta

"daddy ka ganshi? Daddy sun dawo? Are they ok?" abinda take fada kenan tana Binshi har suka qaraso wajen wata kujera mai daukar mutum biyu ya zaunar daita.


"daddy ya akayi ka dade? Sun dawo ne? Nasan sun dawo ko?"


"shhh ya isa hakannan sweetheart kinji? Ya isa, now shaqi numfashi..."


Shaqa tayi yadda yace


"to fesar... Yauwa to qara Shaqa... To fesar...

Yauwa daughter na, ki daina magana babu ko sayawa numfashi kinji, it's not Good for the health"


"daddy... Deen" yadda tayi maganar yasa yaji jikinshi yayi sanyi sosai


"daddy please say something, ka gansu ko?" taqara fada tana kallonshi da gajiyayyun idanunta wadanda sukayi jaa sosai bawai don kuka ba sai don tashin hankali da rashin isashen barci


Cupping fuskarta daddy yayi a hannunshi Hakan yasa zee zubamashi idanu itama tana kallonshi


"dear, please calm down, banaso kina tada hankalinki"


Tunda yafara maganar tashiga Kada kai yana gamawa tace
"to daddy, to nabari, please tell me, where is he?"


Tausayinta yasake lullu6e daddy ganin kamar ma ba'a hayyacinta take ba.


Dagowa yayi ya kalli mummy da itama saukowarta kenan ta tsaya daidai bakin stairs itama tana kallonsu.


Maida kallonta yayi akan Zainab din daketa kallonshi itama tama kasa hadiye miyau don fargaba


Sake Cupping din fuskarta yayi ahankali sannan yace
"Zainab karki tashi hankalinki kinji? Please"


Banda Kada kai babu abinda takeyi cikin sauri tana kallonshi

"dear haryanzu basu dawo ba, gidan arufe da padlock kuma babu wanda yasan inda suka tafi da lokacin da suka tafi kawai wayan gari sukayi sukaga babu su a gidan, har mai gidan daya basu haya Saida aka hada ni dashi amma shima cewa yayi besan komai gameda tafiyarsu ba don bawai kudinsu ne yaqare ba Suna da kingin kudi harna wata 3 a wajenshi.


Abin dai da daure kai, bansaniba qila travelling sukayi garinsu ko something like that"


_wow! I love travelling!_


_nima zanso watarana nayi tafiya wani wuri_


Tunawa tayi da maganarsu ta kwanaki

To amma ina zasu tafi yanzu ana school, lokacin da ma exams keta matsowa?


"Daddy please ina zuwa, nima zanje nagani" tafada pleadingly

"Me zaki gani?" inji daddy

"gidan nasu, please bazan samu rest of mind ba idan ban gani ba"


"kina hauka ne?! Ina kika ta6a ganin anyi haka? Ace saurayi ya turo magabatanshi yaqi turowa kuma don rashin sanin ciwon kai sai budurwar tabi shi har gida?" inji mummy tana qarasowa dakin


Sadda kanta zee kawai tayi qasa not saying anything Saidai ita kadai tasan abinda zuciyarta keyimata


"kawai a kyalesu aga iya gudun ruwansu, ai zasu dawo kuma am betting you zasu zo har nan su fadamana komai" inji mummyn tana zama itama kan kujerar kusa dasu


Ganin yanayin zee yasa daddy cewa
"tashi ki shirya mutafi"

Saurin dagowa zee tayi ta kalleshi trying to believe what she heard

"haba Alhaji, ya zakace haka kuma?" inji mummy


"maimuna kinsan condition din yarinyar nan tunda dake akayi mana bayani, why zan bari najama kaina bala'i? Idan zuwan zai saka hankalinta ya kwanta, fine"


"to amma saboda allah Alhaji wannan ai xubar da qima ne"


Kallon zee da murnarta tafara komawa ciki daddy yayi yace
"jeki shirya ki sauko mutafi"


Aikau kamar akan qaya take dama tayi saurin miqewa ta wuce sama da sauri


Daddy ne ya kalli mummy
"please maimuna kabari taje tagani for herself, Hakan zaisa hankalinta kwanciya"


"amma Alhaji idan kukaje akayi daidaitoni sun dawo fa? Sai kawai suga kunje nemansu, suruki da budurwar da za'azo neman aurenta aka fasa sun biyo saurayi har gida? Wannan ai xubar da mutunci ne"


Dan murmushi daddy yayi sannan yace
"ni lafiyar diyata ta fiyemin komai, ina iyayin fiyeda Hakan ma saboda ita"


Daidai nan zee ta sauko daga sama ta chanza kayan jikinta zuwa blue black jallabiya


Tashi daddy yayi shima ya miqo mata hannu ta taho ta kama hannun tana avoiding idanun mummy


Tasan abinda takeyi ba girmanta bane kuma ba ajinta bane amma ya ta iya?


Abinda zuciyarta ke ingixata tayi kenan kuma a halin yanzu batada wani za6i sai na bin umarnin zuciyar tata don kwata2 a wannan fannin bata iya controlling dinta.


Ficewa sukayi daga falon mummy na binsu da kallo.


Parking space daddy ya nufa riqe da hannunta Hakan yasa bala dake can wajen security rugowa da gudu ya rigasu isa motar ya bude masu backseat.


Da daddy yaso yayi driving din sai kuma yafasa ganin balan duk sai suka shige backseat din ya rufo musu kofar sannan shima ya zagaya mazaunin driver ya bude yashiga.


Tada motar yayi sannan yayi reverse ya kama hanyar gate din da security yariga ya wangale musu suka fice daga gidan.


Tafe suke cikin normal speed motar tayi tsit bakajin komai sai alamun tana tafiya da zakaji


Zee a bangarenta a matuqar darare take, a qagare take su iso unguwar dukda yadda zuciyarta ke qara gudun bugu duk kusancinsu da unguwarsu Deen din.


Daddy daya lura da uneasiness dinta ya damqe hannunta acikin nashi Hakan yasa ta juyo ta kalleshi


Kada mata kai yayi alamun ta kwantar da hankalinta


Dry murmushi tadan yimashi tareda Kada mashi kai shima ta Janye idanunta ta maida kan glass din gefenta.


Basu qara jimawa suna tafiya ba suka qaraso unguwar tasu.


Bugun da zuciyarta keyi sai ya linka na dazu


Tanaji bala ya sauko daga motar sannan ya zagayo ya bude masu

Daddy shi yafara fita sannan ya miqo mata hannu.


Cikin sanyi itama ta miqa hannun nata ta kama nashi sannan tafito da taimakonshi.


Ganin Hakan yasa bala maida kofar ya rufe ya matsa gefe.


Dagowa zee tayi ta kalli kofar gidansu Deen din wanda kamar yadda masu zuwan ke fadi rufe take da qaton kwado


Qurawa kofar idanu tayi ko kyaftawa babu tana jin yadda zuciyarta ke bugawa sosai


"basu nan, tun wancan jiya din muma munzo siyan koko basunan" suka tsinkayi muryar yar yarinya tana fadin haka


Duk juyowa sukayi suka kalleta Hakan yasa yarinyar tasha jinin jikinta

Kafin wani cikinsu yayi magana harta juya ta arta a guje.


Binta da kallo duk sukayi ahakan sukaji muryar wani mutum nacewa

"A'a Alhaji, sake dawowa kayi?"


Sake juyowa sukayi kan mutumin (mallam Nasiru) daddy yace
"wlh kau ka ganmu munsake dawowa? Dawowa mukayi muga ko za'a dace da sun dawo"


"wlh kau Alhaji kaga dai basu dawo ba, abin da matuqar daure kai don wlh ranar daren da zamu wayi gari muga gidan a kulle tareda Deen din muka fito daga massalaci bayan sallar isha'i kuma Koda wasa be gayamin zasuyi tafiya ba bare inda zasu din abinda basu ta6a yiba don wlh kamar yan uwan juna haka muke komai namu sun sani suma haka, bansan ya akayi ba wannan karon" inji mallam Nasiru


"to ko wajen wasu danginsu suka je ko yan uwa haka? Kasan inda wasu nasu haka suke?" inji daddy


Girgiza kai mallam Nasiru yayi
"Gaskiya A'a don tun Zuwansu nan unguwar duk kusancinmu bata ta6a nuna mana wani nasu ba ko yan uwansu bare akai ga maganar inda suke kuma bamu ta6a ganin wasu nasu sun kawo masu ziyara ba"


Shiru wajen ya dan dauka

"to sun kai shekaru nawa da dawowa nan?" inji daddy


"Ca6! Gaskiya sun dade sosai don aqalla sunkai shekaru goma sha biyu a nan lokacin tun banma dade da aure ba"

"kuma ace duk lokacin babu wani nasu daya ta6a zuwa masu?" inji daddy cikin alhini


"to banace ba Alhaji tunda qila suna zuwa ko su sukan je mune bamu sani ba Amma dai bata ta6a gwadamana wani ko wata a matsayin yan uwansu ba"


Daidai nan wani saurayi ya qaraso wajen yana masu sallama


Duk juyowa sukayi wajenshi suna amsa sallamar

"A'a salmanu kaine?" inji mallam Nasiru

Cikin murmushi ya amsa da eh sannan yashiga gaidasu sukuma suna amsawa


"dama yanzu ina gida zan fita qanwata rahma tashigo gida aguje wai ga wasu masu mota can kofar gidansu Deen shine nace bari nazo qila kune wadanda nake nema"


Duk maida hankalinsu sukayi akanshi gabadaya


Kallon zee salmanu yayi yace
"kece Zainab?"


Gaban zee ne ya fadi

Kasa amsawa zee tayi sai kallon daddy datayi tasake maido kallonta akan salmanun


"eh itace dan samari, fatan dai lfy?" inji daddy


"eh lafiya lau, dama Deen ne yabani saqo wai idan wata Zainab tazo inbata"


Gaban zee yaqara yankewa ya fadi tanajin zuciyarta na qara speed


Karkatawa yayi ya zura hannu aljihu yana cewa
"wlh ranar talata da daddare yabani bayan mun fito daga massalaci wai don Allah wata Zainab zatazo wai inbata dana tambayeshi shi me zai hana yabata sai cewa yayi ai tana iya zuwa shikuma a lokacin yatafi school gashi saqon nada matuqar muhinmmanci bazai yiwu taje ta dawo ba

To tun lokacin na amsa sai kuma aka wayi gari gidansu a kulle.

Haka na wuni ranar ko aiki banje ba don gudun kar natafi yarinyar kuma tazo gashi yace saqon nada matuqar muhinmmanci, to amma shiru har dare banga wulgin kowa anan ba

To shine naketa ajiya kuma ina dan zagayowa ina kuma sa qannena suna dubamin ko wata zatazo nemanshi.

To yanzu ma na dawo gida ne naci abinci ina shirin fita rahma tashigo aguje wai ga wasu masu mota can kofar gidansu Deen shine nace bari nazo nagani ko za'a dace" ya qarashe zancen yana Miqama zee wani brown envelope daya zaro daga aljihun wandonshi

"ki duba kigani ko naki dinne" yafada yana sake miqa mata


Kasa amsa tayi sai kafe envelope din datayi da idanu Tanajin kamar zuciyarta zata faso qirji saboda bugu


"dear ki amsa ki duba" inji daddy cikin sanya qwarin gwiwa


Kallon daddyn tayi sannan taqara kallon wasiqar, sannan ahankali ta dago hannunta dake rawa rawa ta amshi envelope din.

Jujjuya envelope din take a hannunta tana fargabar budewa

Dafa kafadarta daddy yayi Hakan yasa taqara Dagowa ta kalleshi

Kada mata kai yayi cikin qarfafa gwiwa Hakan yasa ta sauke wata nannauyar Ajiyar zuciya sannan ahankali hannu na rawa ta farke envelope din taga wata ninkakkiyar farar takarda ta bayyana


Gabanta ne yasake tsinkewa

Duk ita mutanen wajen suka zubama ido in curiosity suma


Zare takarda tayi tasaki yagaggen envelope din aqasa


Ahankali ta shiga warware takardar hannunta hannunta na rawa, zuciyarta na rawa kai komai ma nata rawa yakeyi da za'a auna jininta a lokacin da ta tabbatar da za'a ga yakai maqurar hawa.


Unique handwriting din da shikadai tasani dashi yafara yima idanuwanta maraba


Ahankali tafara bin abinda yake cikin takardar tana karantawa


_*Nasan lokacin da wannan takardar zatazo miki na riga nayi nisa.*_


_*Bansan me zance maki ba, bansan ta ina zanfara ba, bansan da wadanne kalamai zanyi amfani dasu ba*_

_*daren ranar danake rubuta wannan takardar shine mafarin duhun rayuwata, Koda gari ya waye wa kowa ni bazai waye min ba, ba yanzu ba kuma bana jin lokacin zai ta6a zuwa*_


_*zan cigaba da kasancewa a duhun ne qila har ahada, Domin nariga nayi nisa da hasken dazai haskaka min rayuwata*_


_*ina sonki*_

_*nasan yanzu ba lallai bane ki yarda da Hakan ba kuma nima ban cancanci na fadamiki Hakan ba*_


_*amma that's the pure truth.. Ina sonki, zan cigaba da sonki, wataqila ma sonki ne ajali na*_


_*am sorry... For every thing.. Da abubbuwan danasaki fuskanta da wanda zan saki fuskanta*_


_*kin dauki zuciyarki dunqullala kin bani amana nikuma na raratsata ta zuba a plate na maido miki*_


_*ban cancanci yafiyarki ba zee, ban cancanci gafararki ba Amma Hakan bazai hanani neman gafararki ba*_


_*ki yafemin Zainab... Don Allah.. Ba don niba.. Don girman allah👏😭*_


_*natafi.. Am gone.. Maybe forever maybe not*_


_*I LOVE YOU*_


Ahankali takardar ta sulale daga hannunta

"daughter!!" taji muryar daddy na cewa haka da qarfi sai kuma taji an riqota gamm


"innallilahi waina ilaihi rajiun! Zainab! Ki bude idanunki ki kalleni, please don't do this" tasake jin muryar daddy sama sama ana dan bubbuga mata kumatu

Amma the more takeson bude idanun the more yake qara rufewa

"Zainab!! Innallilahi waina ilaihi rajiun! Jama'a ku taimaka min! Zainab!!"


"DEEN..."

Kalmarta ta qarshe kenan idanun suka rufe ruff... ✍️


Ummin fasihu 🧚🏻‍♀�
8/2/21, 9:39 PM - Buhainat😝: *🙍🏻‍♂️DEEN 🙍🏻‍♂�*


*052*


*HEARTBREAK 💔*


_jiya kasa yiwa kowa reply nayi_


_Everyone is saying why? Why? Why?_


_that's destiny kuma komai yanada reason na faruwarshi kuma idan akasa hqr ahankali ahankali komai zai warware_

_dama tun farko nariga na fada cewa wannan story din ya qumshi, true love, heartbreak da sadaukarwa. Don haka sai kuyi hqr don yanzu muka fara zuwa inda na dade inason muzo, insha allah komai zai warware and Gaskiya zatayi halinta sooner or later_

_sorry for the heartbreak 😞_

_Hajiya am'ash mai jiran sai komai ya warware sannan ta cigaba da karatu, comgratulations, qila sai munzo semi-final zakiyi joining dinmu 😆_


Dagudu security din gate din asibitin ya qarasa gate din ya shiga wangale masu gate din.


A tsiyace motar tashigo harabar asibitin, maimakon tayi parking space sai tayi hanyar entrance din hospital din ta tsaya few feet da tudunkar entrance din.


Already su likitoci da nurses duk sun fito nurses din riqe da dan gadon nan na gurgura marassa lafiya


Kofar baya aka bude sannan daddy yafara qoqarin tattarota ya dauketa amma yakasa saboda rawar da jikinshi yakeyi


Ganin Hakan yasa su likitoci matsowa suma da taimakonsu aka fiddo zee da komai nata yasaki kamar gawa don idan bama lura kayi ba sai kace ma bata numfashi kwata2


Akan gadon aka dorata sannan duk aka shiga turata dagudu aka nufi cikin hospital din


Duk inda suka wuce sai mutanen dake kai kawo wajen sun tsaya suna kallonsu don ganin yadda ake gurguro gadon da mutanen dake Binshi dagudu ya isa ya nuna cewa koma wa ke saman gadon yana cikin very critical condition.


Emergency room suka nufa, tun kafin su qaraso aka bude masu kofa kuma suna shiga aka rufo kofar wanda Hakan yasa su daddy da bala jan burki bakin kofar.


Dafe kanshi daddy yayi ya juya yashiga yin safa da marwa cikin mugun tashin hankali.


Shima bala was restless, shima tashin hankaline rubuce koina a fuskarshi.


Acan kau a wani daki aka shigar daita akayi transferring dinta daga gadon mai taya zuwa na cikin dakin.


Nan take likitocin guda uku suka rufa akanta suka fara baje basirarsu wajen ganin sun shawo kan matsalar


Na farko numfashinta dayayi mugun qasa suka shiga qoqarin jawoshi su daidaitashi.


Sosai suke aikin babu kama hannun yaro suna iya bakin qoqarinsu na ganin sunyi saving life dinta don ahalin yanzu tana cikin very critical condition.


Daddy kau kasa tsayawa wuri guda yayi, safa da marwa kawai yakeyi cikin tsananin tashin hankali, idan ya kalli kofar da aka shiga da zee sai yaji kamar yaje ya 6allata yashiga yaga wane hali take ciki.


Babban tsoronshi shine kar ciwon ta ya tashi wanda Dr yafada musu wancan karon, he's scared, bazai iya musalta rayuwa babu sanyin idanunshi Zainab

"Hasbunallah wa ni'imal waqeel! Innallilahi waina ilaihi rajiun! Innallilahi waina ilaihi rajiun! Ya allah help me, don’t take her away From me now, not now please, I can't take it" yafada cikin tsananin tashin hankali still yana zirga zirganshi


"Alhaji kayi hqr, insha allah zata tashi, insha allah allah zai tashi kafadunta" inji bala cikin tausayawa da son qarfafa mashi gwiwa


Ko kallo be isheshi ba ya cigaba da zirga zirganshi yana cigaba da sambatunshi


Sosai likitocin suka jigatu kafin su samu su daidaita numfashinta don dole suka maqalamata abin oxygen a hanci wanda zai taimaka mata wajen numfashi


Sosai jikin family Dr dinsu yayi sanyi liqis don qaryar dasukayi wancan karon itace ta tabbata

Jinin zee yayi mugun hawa, hawan da ba'aso saboda hadarinshi.


Saida suka shafe fin awa sannan suka samu komai yadawo daidai suka fito kowannensu na sharce zufa


Daddy na ganin sun fito ya nufosu da sauri kamar zai kifa qasa

"Dr ya ake ciki? How's my daughter?" yafada ajere


Daya daga cikin doctors din yace
"calm down Alhaji, komai yadawo normal yanzu insha allah"


"to muje naganta, I want to see her" yafada zaiyi hanyar dakin da aka kwantar da ita din

Taroshi ainahin Dr dinsu yayi yana cewa
"A'a sir, not now yanzu ba'ason kowa yashiga wurinta, ka kwantar da hankalinka insha allah she's safe now, muje office mu tattauna"


Dakyar suka samu ya haqura da shiga din yabisu office din don tattaunawar kamar yadda sukace.


***


"inajinku Dr(s), don Allah karku fadi abinda zai bugarmin da zuciya" inji daddy da kallo daya zakamashi kasan yana cikin tension sosai


Daya daga cikin likitocin ya sauke Ajiyar zuciya yace
"Alhaji ka kwantar da hankalinka kuma kasa aranka dik abinda yasamu mutum jarabtace daga allah, da lafiya da rashinta dik na allah ne..."


"Duk nasan da wadannan Dr, basu na tambaya ba, lafiyar diyata nakeson ji" inji daddy cikin qosawa


Dayan likitan yace
"alhamdullilah Alhaji, yanzu mun samu mun shawo kan komai, dama jininta ne yayi mugun hawa, hawan lokaci daya wanda Hakan keda matuqar hadari don a wasu unlucky case din sai kaga mutum ya fadi sanadiyar Hakan ya tashi da mutuwar 6arin jiki amma alhamdullilah nata yazo da matuqar sauki plus ankawota asibiti da wuri an takama abin burki cikin gaggawa, saikuma numfashinta dayayi qasa sosai yana neman seizing shima mun samu shawo kan Hakan yanzu Hakan tanacan maqale da abin oxygen wanda ke taimaka mata wajen daidaita mata numfashinta"


Dafe kai daddy yayi yana kallon saman desk din gabanshi not saying anything, shi kadai yasan halin dayake ciki


"kayi hqr Alhaji, insha allah all will be well" inji wanda yagama bayanin yanzu


"to yanzu ina iya ganinta please" inji daddy


"No Alhaji, kayi hqr don Hakan sa6ama doka ne, tana intensive care yanzu babu mai shiga wajenta yanzu sai doctors"

"Koda ba ciki ba, Koda tawaje zan hango ta ina dai son ganin halin datake aciki ne" inji daddy


Kallon juna likitocin sukayi sai family Dr dinsu yayi Ajiyar zuciya yace
"muje Alhaji"


Jin Hakan yasa Alhaji miqewa da sauri Dr din yayi gaba shikuma Alhajin yabishi abaya suka fice daga office din


Kamar yadda sukayi lokacin da aka kwantar da Deen a asibitin haka akayi wannan karon ma


Recording room suka wuce inda anan aka haskoma daddy dakin da zee ke Kwance


Ganin zee Kwance kamar bata numfashi maqale da wannan abin a hanci ba qaramin girgiza zuciyar daddy yayi ba


Qurawa Mafi soyuwar diyarshi ido yayi yana jin kamar ya dauke mata ciwon ya maido jikinshi.


Idanunshi daya quramata sun kada sosai zuciyarshi banda zafi babu abinda takeyi


Juyawa yayi don bazai jure kallonta a wannan halin for a long time ba


Bude kofar wajen yayi ya fita.


Bala dake zaune Tundazu ganin daddy ya fito yana tafiya kamar wanda zai tashi sama yasashi saurin miqewa tsaye


Ganin waje ya nufa yasa shima yin saurin take mashi baya.


Dagudu ya rigashi isa motar ya budemashi.

Shigewa yayi batareda ya kalleshi ba yana daddana wayarshi at the same time.

Rufo mashi bala yayi ya zagaya dagudu gaban motar ya bude yashige shima

Tada motar yayi daidai lokacin dayaji daddy na cewa

"wlh bazan bar yaronnan ba, duk inda yashiga sai an nemoshi kuma wlh wani abu yasaki yasamu diyata just hold yourself responsible tunda harda hadin bakinki wajen cutar ta!"

Kana jin yanayin yadda yake magana zakasan ranshi a matuqar 6ace yake

"just shut up! Duk ba ke kikafi bada gudunmawa a komai ba?! Dama ni tun farko ban yarda dashi ba Amma kika nace, kuka nace! To gatacan ya kasheta, ga gawarta can hospital saiki zuba ruwa qasa kisha, dama ai ba sonta kike ba! Mtcheew"

Ya katse kiran cikin qunar zuciya yana huci


Kallon bala dake driving yayi sai ya daka mashi tsawar da yakusan sawa ya saki sterring din


"gidan ubanwa zaka kaini! C'mmon kaini police station! wlh zai san ya ta6a jinina! Saisan Jinin dan faranshi ya ta6a!"


Shidai bala daya samu ya iya ruqo sterring din daga kufcewar dayaso yi yayi u-turn ya kama hanyar nearest police station kamar yadda ya buqata


Sosai hankalin mummy ya dugunzuma ya tashi

Babu abinda ta fahimta a magangganunshi sai gatacan ya kasheta, ga gawarta can hospital

Gawar wa?

_wa suka fita tareda shi?_ zuciyarta ta tambayeta

_Zainab?!_


Babu shiri ta bude daya daga cikin locker dinta ta zari makullai ta Ciro na mota aciki ta figi gyallenta ta yafa ta fice daga dakin hankali tashe


Saukowa tayi qasa ta wuce kofar fita cikin sauri ta bude ta fita ta maido ta rufo


Parking space ta nufa ta danna remote din car key din don rikicewa ma ta hana tasan makullin wace mota ta dauko


Motar dataji tayi tsuwa ta nufa ta bude mazaunin driver tashiga sannan ta maida ta rufe sannan ta tada motar tafito daga parking space din tazo tawuce security din daya bude mata gate din ta fice in speed.


A bangaren daddy kau suna isa police station ya sauko ya shiga ciki kamar zai tashi sama


Kasancewarshi na babban mutum kuma shahararre yasa babu 6ata lokaci aka hada shi da d.p.o kamar yadda ya buqata.


Anan ne yayi stating qarar Deen daya kawo ya hada da qarya da Gaskiya ya fada aka rubuta


Sannan yasa a nemoshi duk fadin Katsina dama kewayenta yakuma yimasu albishir din kyauta mai tsoka muddin suka samo mashi shi.


Abinka da abin manya nan da nan aka bazama neman Deen, aka bugamashi tambarin *WANTED.*


Ganin komai ya tafi yadda yakeso saiya baro police station din yadawo asibitin


Suna yin parking ya bude kofar motar yafito batareda ya jira bala ya zagayo ya budemashi ba.


Direct emergency ya nufa ya kama hanyar ward din zee.


Tun daga nesa ya hango mummy zaune akan bencin dake kofar ward din


Ranshi ne yaqara 6aci Hakan yasa ya qara tamke fuskar kamar hadari


Dagowa mummy tayi da idanunta dasukayi jajur wanda da alama itama kukan tayi ta kalli daddy daya qaraso wajen.


Kasa yimata masifar dayayi niyyar yimata yayi sai kawai ya cigaba da binta da mugun kallo mai cike da haushi da takaici


Sauke kanta tayi qasa itama tana share hawayen dasuka sake gangaromata.


Juyawa yayi kawai ya kalli gefe yana jin 6acin rai har lokacin

Haka yaita tsayuwa yana kallon gefe itakuma tana zaune kanta a qasa babu mai cewa uffan


Can dai daya gaji da tsayuwar saiya wuce ya kama hanyar dazata sadashi da office din Dr din nasu.


Cikin gari kau neman Deen ake takoina, bincike akeyi babu kama hannun yaro yadda kasan wani kasurgumin 6arawon daya kufce suke nema.


Har school Saida yansandan sukaje bincike aka dauko masu file dinshi inda anan dinma basu samu wani gamsashen information dazai basu hint din inda yake

Acan unguwarsu ma akwai yansandan da aka tura can

Inda anan aka kirawo mai gidan da suke zaman hayan gidanshi


Tambayoyi harna innanaha Saida sukayi ma mutumin sai abinma yayi kamar zai juye kanshi don sai tuhumarshi suke wai ya za'ayi yaba wadanda besaniba kuma besan kowa nasu ba haya?

Haka aka taru a kofar gidansu Deen din anata abu guda inda shima mallam Nasiru akaso shafa mashi shima wai ai shima yanada kusanci sosai dasu don haka dole yasan wani abu gameda guduwansu.


Abu dai ya cakule ya rikice don tuni unguwar ta dauki shelar ashe su Deen yan danfara ne? Danfara sukayi suka gudu gashi anzo ana nemansu ruwa ajallo


Kan kace me? Maganar tayi spreading kamar gobara a busassun ciyayi, inda Mafi yawancin mutane suka yarda suna allah wadai dasu, qalilan kuma basu yarda ba Suna cewa sharri ne ciki harda baaba abu data yini kuka.


Daga baya dai 6alle kofar akayi aka shiga gidan aka bincikeshi kaff


Komai na gidan na nan except kayan sawansu Hakan yasa aka maida aka kulle akan zasu dinga dawowa akai akai don bincike suka kuma sanar duk wanda yaga wulginsu yayi maza ya sanar dasu don cafkesu.

Sosai jikin mallam Nasiru yayi sanyi dama mutanen unguwar gabaki daya.

Matar mallam Nasiru kau itama kuka taitayi tana rantse rantse akan wlh qazafi ake musu babu yadda xa'ayi Deen ya iya danfaran mutum.

Haka dai unguwar nan ta Wuni da zancen bayin allah nan a bakunan mutanen unguwar, abu dai babu dadi


A bangaren zee kau har dare bata farfado ba


Da farko likitocin cewa sukayi suna iya tafiya basai an kwanan mata ba Amma cikin daddy da mummy aka rasa wanda zai yi yadda suka ce din


Anyi rarrashi anyi komai amma ko motsawa daga inda suke basuyi ba hakan yasa aka kyalesu kawai aka basu wani ward din dake gefen na zee don suyi spending dare aciki.


Haka suka kwana a asibitin ko kalma daya bata shiga tsakanin mummy da daddy ba.


Shi daddy najin haushin mummy don gani yake duk itace silar komai itakuma mummy damuwar datake cikima ya isheta kaya.

Haka sukayi kwanan zaune duk babu wanda ya iya barcin kirki ita mummy daga baya ma wajajen 4am ta tashi tafara nafilfilu har asuba tayi ta dora da sallar asuba shikuma daddy ya fice massallaci.


A taqaice dai Saida zee ta kwana biyu a wannan dakin da ba'a shiga ganinta a kwana na uku aka chanza mata ward inda lafiya lau ana iya zuwa ganinta Saidai shima banda hayaniya izuwa lokacin anriga ancire mata abin oxygen din hancinta don tana iya breathing da kanta


Izuwa lokacin duk yan uwa da abokan arziqin su mummy da daddy sun sani

Yan Ruma dama yan uban su daddy labari yakai musu Hakan yasa sai tururuwar zuwa ganinta akeyi.


Daddy su biyu mahaifiyarshi ta haifa dashi da qanwarshi Ummu batool sannan tafita daga gidan inda anan tabar daddy wanda yasha wahalar matar uba da yaranta sosai.

Be samu sauqinsu ba Saida yashiga secondary school aka sakashi boarding, to tun lokacin yaja baya Sosai da yan uban nashi dama gidan uban nashi gabadaya don ko hutu akayi gidan da mahaifiyarshi ke aure nan yake zuwa ko kuma yayi hutunshi a school din.


Ana haka allah yayiwa babbansu rasuwa lokacin yana S.S 2

To rashin mahaifin nashi a gidan yasa ya ida qauracewa gidan don Koda aka raba gado ya tsira da daki daya acikin gidan siyarwa yayi ga babban wansu don a lokacin idan akwai abinda ya tsana to gidan ne da ahalin ciki.


To ahaka daddy ya cigaba da karatunshi mahaifiyarshi na taimaka mashi da mijinta shima kuma yana yan buga buganshi har yasamu ya qare secondary school din ya shiga jami'a inda yashiga course din business saikuma ya hada karatun da zuwa kasuwa inda ya kasance yaron shagon wani babban dan kasuwa a kasuwar garin nasu.


Ahaka ahaka har yayi graduating lokacin ya goge sosai a harkar business shiyasa Koda shima yafara cikin qanqanin lokaci abin ya bunqasa allah yasamashi albarka a harkar, abin yaita gaba gaba har yakai matsayin dayake aciki yanzu.

Shekara daya da yin auren daddy da mummy allah yayiwa mahaifiyar daddy da mijinta rasuwa a wani hadarin mota dasukayi a lokacin zasu kai ziyara garinsu mijin.

Shiyasa yanzu bayada dan uwa makusanci sosai kamar Ummu batool wanda ke aure Dubai tanada 'ya'ya biyu, namiji da mace
Namijin mai suna Abubakar sadeeq amma kasancewar sunan uban mijin Ummu batool ne dashi sai aka sakaya sunan ana kiranshi da *Aymaan* ita kuma macen sunanta Fatima amma itama ana kiranta da *Batool*


Tsakanin daddy da yan ubanshi babu yabo babu fallasa ana dan zuminci sama sama kuma dama suma mahaifiyarsu ta dade da rasuwa kuma duk yawancinsu ba agarin suke ba musanmman matan wadanda aure ya kaisu wasu wuraren.

Bama cika sanin halin da junansu suke cikiba inba ta kama ba don sosai zumincinsu keda rauni bama zaka ta6a cewa sun hada uba ba.


To a wannan case din yarasa wanda ya gayamasu ma don shidai be gayamasu ba Saidai kawai yaga wasunsu sunzo dubiya.


A bangaren abokan aikinshi ma duk sun zozzo inda amininshi baban asaad shine gaba akan komai don shima sosai ya nuna damuwarshi akan hakan don yama kusan fin daddy nuna damuwa.


Suma yan Ruma sun zozzo ganinta inda duk yawancin wanda yaji labarin abinda yafaru sai ya jajanta inda mafiyancinsu ke xagin Deen dama yima samari gabadaya kudin goro acewarsu dama samarin yanzu duk tarin mayaudara ne da wuya kasamu mai so don Allah


A bangaren yansanda kau haryanzu neman Deen suke Saidai cikin kwanakinnan ko mai kama dashi basu gani ba kuma har lokacin basu samu wani kwakwaron hint ba na inda zasu ganshi


Kwanan zee biyar a asibitin a daren kwana na biyar din ta farka.


Lokacin mummy nakan sallaya ta idar da sallar isha'i kenan kamar ance ta juyo sai gani tayi tanata marr marr da idanu alamun sotake ta budesu


Ganin Hakan yasa ta tashi da sauri tazo bakin gadon tana kallonta.

"Zainab" ta kira sunanta

Cigaba da qoqarin bude idanun zee tayi Hakan yasa mummy ta juya ta fita daga dakin don kiran doctor


Fitar mummy keda wuya idanunta suka bude ahankali.

Hasken dakin daya haske mata idanu yasa taqara maidasu ta rufe can kuma taqara budesu ahankali tana jin yadda sukeyi mata wani yaji yaji.


Ahankali take wurwurga idanun nata don tantance inda take.


Bata ida tantancewa ba mummy da doctorn dataje kirawowa suka shige shigo dakin.


Saurin Qarasowa bakin gadon sukayi gabadaya suna kallonta itama tana kallonsu kamar mai son karantar wani abu a fuskokinsu

Babu 6ata lokaci Dr yashiga dubata ita kuma zee ta maida idanunta ta rufe trying very hard wajen son tuno abinda yafaru


_gobe ne_

Ta tuna Maganarshi ta last call dinsu dasukayi a daren ranar introduction


_I LOVE YOU_
ta tuno kalmar qarshe data karanta a wannan takardar


_natafi... Am gone... Maybe forever.. Maybe not_


Ahankali ta bude idanunta lokaci guda dukkanin abubbuwan dasuka faru suna rushing back a kwalwarta


_I LOVE YOU_
itace kalmar qarshe data karanta daga haka batasan abinda yasake faruwa ba sai yanzu data bude idanunta


And then she realize, she realize cewa yafadi Gaskiya.. Yafadi Gaskiya dayace ya rarratsa zuciyarta into pieces don yanzu haka abinda takeji kenan

Jin zuciyarta take kamar glass din da ake rarratsewa into tiny tiny particles


Zuciyarta taji rauni, mummunar rauni don yanzu haka bleeding take, unstoppable bleeding


Kuma the worst thing shine wanda duk duniya tafi so tafi bama yarda shine silar wannan raunin

Shine ya luma mata kaikaifan wuqa a qahon zuciya ya barta aciki yayi tafiyarshi


_*DEEN*_.... ✍️


Ummin fasihu 🧚🏻‍♀�
8/2/21, 9:39 PM - Buhainat😝: *🙍🏻‍♂️DEEN 🙍🏻‍♂�*


*053*


*INCOMPLETE*


Ahankali ta maida idanun ta lumshe tana hadiye yawu ahankali.


Zafi takeji, zafi mai mugun radadi a zuciyarta, jitake kamar ana gasa mata zuciyar ne a oven kuma ana tarfa mata narkakkiyar darma.


Abinda takeji bazai iya musaltuwa ba koda zata musalta bazaka ganeba inba kaima tsintar kanka kayi aciki irin halin datake ciki kayi ba wanda bata fatan ko maqiyinta yashiga irin halin data shiga


"sannu Zainab" inji Dr yana kallonta


Bata bude idanunta ba Haka ma bata motsa ba bare asa ran zata amsa


"Me kike ji yanzu? Kina jin wani ciwo?" inji Dr din again yana kallonta keenly


Nan ma ko motsawa batayi ba


"Zainab.." taji tender voice din mummy


Ahankali ta bude lumssasun idanun nata ta dagasu ta zubama mummy din


Wani irin tausayinta ya tsirgama mummy ganin irin kallon datake mata, a very painful look


Sanin abinda tafi buqata yanzu yasata Qarasowa ta zauna gefen gadon ta kama hannun zee dake daure sa cannula tana kallonta

Itama zee ita take kallo babu ko kyaftawa

Ahankali mummy ta jawota jikinta tabata warmly mother's hug wanda ta rabu da yimata


Wani nannauyan Ajiyar zuciya zee ta sauke tana qara cusa kanta a wuyan mummy

Lumshe soyayyun idanunta tayi tasake budewa


Da ada ne da yanzu tafara hawaye ko kuka amma yanzu shiru kakeji, sotake tayi amma ya gagara, idanunta sun bushe, zuciyarta ta soye, kukan is nowhere to be found


Dagota mummy tasakeyi tana kallonta, lumshe idanu zee taqarayi ta bude su akan fuskarta itama

"Are you ok dear?" inji mummy tana kallonta cikin kulawa


Wani dan murmushi ya kufce mata wanda kallo daya zakamashi kasan murmushi ne mai ciwo


Ji mummy tayi kamar tayi mata kuka, dukda bazata iya cewa tasan exactly abinda zee keji a zuciya ba Amma tasan dole yanzu she's in pain


"meke yimaki ciwo? Kifada kinga sai Dr ya dubaki" inji mummy tenderly


Kama hannun mummy zee tayi ahankali sannan ta dora saitin zuciyarta daketa halbawa in speed


Saurin kauda kai Mummy tayi sanadiyar hawayen dasuka kuftomata sai kuma tajuyo tajawo Zainab a jiki ta rungume qamm

Qara cusa kanta zee tayi a wuyan mummy ta maida idanunta ta lumshe tana sauraron sheshekar mummy tana jin dama ita allah zaiba damar yin irin wannan kukan ko ba komai zata hawayen zai wanko kadan daga cikin raunin dake zuciyarta


Dr din ma kallonsu yake cikin tsananin tausayawa, jikinshi duk yayi sanyi


Saida mummy ta share hawayenta ta bayan zee sannan ta dago fuskarta dago zee daga jikinta tayi cupping fuskarta


"Kiyi hqr kinji? Allah na tareda masu hqr, insha allah komai zai wuce maki kamar be ta6a faruwa ba, be strong and move on. Dama tun tasowarki badashi kike rayuwa ba, daga baya ne yashigo rayuwarki yanzu kuma ya tafi, ki dauki Hakan kamar haduwar hadarin kaka ne, ya hada kuma ya baje ya 6ace 6att kamar ba'ayi ba

Ki dauki naki case dinma Hakan, ki dauka baki ta6a rayuwa dashi ba, karki bari abinda yayimiki yayi tasiri aranki da har zaiyi pinning dinki down, fight Zainab! Fight the feelings and move on!"


Mummy batasan hawaye take ba Saida taga zee takai hannu tana sharemata Hakan yasa ta sake jawota a jikinta tasake rungumeta


Lumshe idanu zee tasakeyi tana jin inama inama

Inama abubbuwan da mummy ke lissafowa yanzu suna da sauqin yi

Inama tana iya yakiceshi kamar yadda tace ta cigaba da gudanar da rayuwarta kamar da, inama inama 😭


Ahankali ta bude idanunta sai suka sauka acikin na daddy sake tsaye bakin kofa Tundazu basusan shigowarshi ba


He looked very sad and disturbed, idanunshi shima sun Kada sosai yana kallon diyar tashi with pain all over his face


Tashi tayi daga kafadar mummy tana cigaba da kallon daddy.

Hakan yasa mummy Juyawa inda take kallo taga ashe daddy ne


Ahankali daddy shima ya qaraso bakin gadon ya zauna shima kusada mummy ya Kamo hannunta guda

"daughter" yafada a matuqar sanyaye


Cigaba da kallonshi shima tayi kamar mai karantar wani abu A fuskarshi

"come dear, come" yafada yana miqomata hannayenshi duka biyun


Ahankali ta matso ta shige cikinsu a sanyaye daddy ya rufesu a bayanta


Rasa da wadanne kalamai zaiyi amfani dasu wajen rarrashinta yayi Hakan yasashi cewa
"Am sorry daughter, am so sorry!"

Qara narkemashi ajiki tayi tana qara rufe idanunta


Sun dan jima ahakan sannan sukayi breaking hug din suka ba Dr din damar dubata dakyau


Saida yagama dubata yayi mata Tambayoyi wanda mostly duk qin amsawa tayi Saidai idan yace meke yimata ciwo ta nunamashi saitin zuciyarta kawai don ita kadai kemata radadi jitake kamar a ciremata ita ta huta.


Cewa Dr yayi ahada mata tea a bata tasha kafin yadawo yaqara yimata allurar barci don sosai zata taimaka mata wajen ragemata damuwa wanda itace sanadin ciwon zuciyar datake complaining din


Yadda yace din akayi

Kakkauran tea aka hada mata daddy ya amsa yana bata a baki tanasha har Saida yafi rabi sannan ta kauda kai alamun ta qoshi

Ganin Hakan yasa daddy kiran Dr din yazo ya harhada alluran dazaimata yayi mata su


Ba'a qara minti biyar ba wani barcin yazo yaqara yin awon gaba daita.


A lokacin ne daddy yasamu damar kiran yan uwa da abokan arziqi yana masu albishir farkawarta, sai washe baki yake cikin farinciki


*WASHEGARI*


Tunda garin allah ya waye mutane keta tururuwar zuwa ganin zee


Daddy baki be rufuwa baya zaune baya tsaye kodayaushe yana kan hanyar rako yan dubiyan ganinta ko kuma raka masu tafiya waje


Sosai manyan mutane keta ziyarta asibitin don Saida kowa yasan da Hakan yau ga sadakar da mummy tasa akayita yima mutane patients na take away din jollof da swan water dukda dai suma patients din ba baya ba don saika tara kake iya zuwa irin wannan asibitin.


Zee kau haryanzu babu uhm ba uhm uhm, duk wanda yazo dubanta Saidai tabishi da idanu, idan kuma ana yimata ya jiki Saidai ta amsa ta hanyar lumshe idanu ta bude kawai


Kayan dubiya kau tashasu qumshi qumshi don duk wanda yazo ganinta saiya ajiye mata qatuwar ledar kayan dubiyan shi


Acikin masu zuwa dubata harda Asaad da qannenshi biyu mata

Yanmatan sai wani daddage hanci sukeyi kamar yadda suka saba, Asaad mane ke da dan sauqi sauqi don shi ya nutsu sai kallon zee da duk basu isheta kallo ba yakeyi kamar zai hadiyeta.


Haka suma suka qaraci zamansu har lokacin tafiyarsu yayi inda anan Asaad ya ajiye mata damin kudi a gefenta sannan shima yabi bayan masu fita


Yadda bata kalli kudaden ba Haka shima wanda ya ajiyesu din bata kalleshi saima maida idanu datayi ta lumshe tana sauraron yadda daddy keta yabon kirki da hankalin Asaad.


Haka dai suka qarasa Wunin ranar cikin yin baqin yan dubiya don da wasu sun shigo sai wasu su fita haka sukaitayi har dare sannan abin ya lafa itakuma zee sai a lokacin tasamu nutsuwar yin tunaninta dakyau.


Saidai bata dade dafara tunanin ba Dr yasake dawowa yayi mata allurar barci don tunanin ne ba'ason tafiye yi a wannan condition din shiyasa akama bari yan dubiyan sukaita zuwa ko sun Janye hankalinta daga tunanin yanzu kuma da babu su sai akayi mata allurar don tayi barci tasamu rest of mind.


Washegari kau baqi yan Ruma ne suka sake dawowa ciki harda Umma

Sosai Zuwansu yadan debe mata kewa musanmman ma da akazo da yaran


Haka taita wasa da sultan da aka doromata shi saman gadonta kamar yadda ta buqata tanayi tana sauraron su mummy da su Aunty raliya daketa firarrakinsu


Duk lokacin da ta kalli sultan sai ta tuna Da ranar da Deen ke wasa dashi acan Ruma lokacin bikin Aunty Feenah


The smile, the dimple, fararen haqoran, the pink lips da kwantaccen sajenshi, dukkansu sai flashing sukeyi a idanunta


Ahankali ta hada goshinta dana sultan kamar yadda Deen yayi wancan karon

Bangalewa sultan yayi da Dariya kamar yadda yayi wancan lokacin, itama tsintar kanta tayi tana murmushi


Ahankali yadda ita kadai zata iya jin abinda take cewa tafara magana


"Bansan abinda yasa ake kiranshi karayar zuciya ba(heartbreak)

Jinake kamar wani sashe na jikina ma ya karye"


Qara bangale mata baki sultan da besan abinda take cewa ba yayi, itama murmushi mai ciwo tayi sannan ta cigaba da cewa

" Wasu na cewa da ciwo ka jira wani


Wasu na cewa da ciwo ka manta da wani

Amma Mafi ciwo aciki shine karasa abinda zakayi aciki

Ka jira?

ko ka manta?"


" Ka yimin rauni fiyeda yadda na cancanta, dama haka kakeda mugunta?

Naso ka fiyeda yadda ka cancanta
Dama haka shashanci na yakai?"

Hannu sultan ya dago ya dora akan bakinta ita kuma ta bude bakin ta dan yimashi cizon wasa

Saurin zare yatsarshi yayi daga bakin nata yana dan 6ata fuska dukda ba sosai ba ta ciza

"The worst feeling is not being lonely, it's being forgotten by the one you'll never forget" taqara fada cikin rada tana kallon puppy face din sultan


Fashewa sultan din yayi da kuka hakan yasa hankalin mutanen dakin dawowa kansu


"oh ni sultan ka cika rigima wlh, kawoshi karya dameki" inji Aunty Raliya tana zuwa wajenta ta daukeshi


Zee batace komai ba sai komawa datayi ta jingina da jikin gadon ta lumshe idanunta tana cigaba da sauraron firarrakinsu.


Yau kasancewar surukar daddy na asibitin Hakan yasa yau ba'a zauna asibitin ba wai saboda kunya Saidai kiran dayaitayi ma mummy dik lokacin da yaso jin muryar zee sai ta bata su gaisa dukda ba magana take ba sosai don daga farkawarta zuwa yanzu za'a iya qirga magangganunta datayi


Sai can da marece wajajen 5pm su Umma sukayi shirin tafiya inda kafin sutafi Saida kowanne yaita yimata nasiha da rarrashinta akan tayi qoqari ta manta dashi tayi moving on

Jinsu kawai take amma a zuciyarta tasan Hakan da kamar wuya don a dare guda zaka iya kamuwa da son mutum amma zaka iya 6ata shekarun rayuwarka batareda ka iya mantawa dashi ba

*MANTUWA* kalmace mai sauqi wajen fada a baki Amma mai matuqar wuya a aikace.


Washegari da zee ta cika kwana takwas a asibitin Ummu batool ta dira Nigeria


Sosai su daddy sukayi mammakin zuwan nata don bata sanar dasu zatazo ba saboda sanin halin daddy yana iya cewa basai tazoba itakuma bazata iya ba don gashi dama ta dade rabonta da Nigeria kuma ga rashin lafiyar zee wanda take jinta kamar ita ta tsungunna ta haifeta shiyasa Koda ya fadamasu tafara shirye shiryen tahowa Nigeria din batareda yasani ba.


Sosai ta tausayawa zee data ganta don acikin yan kwanakinnan ta chanza sosai

She's no more that active Zainab din ta koma wata silent and dull daita, ga ramar datayi acikin yan kwanakinnan wanda ya bayyana sosai


Sosai Ummu batool ta tausaya mata don harda kukanta tana cewa sai allah yasaka mata shima kuma haka


Itadai zee bata cewa komai kamar yadda ta saba a kwanakinnan Saidai deep down tanajin zafi idan aka soki Deen ko aka zageshi, ta rasa meyasa


Saida suka qara kwana biyu a asibitin kafin a sallamesu

Cikin kwana biyun nan Saida asaad yasake zuwa dubata kuma kamar wancan karon ya tisata gaba yanata kallo ko me yake kallo a jikin baqar African oho?


Haka ma babanshi Alhaji Abubakar, kusan kodayaushe tare suke tareda Alhaji Farouq don duk cikin ma abokan daddy Alhaji Abubakar yafi tsayawa taredashi a wannan halin shiyasa daddy ke qara jin qaunarshi a cikin zuciyarshi yakuma qara aminta dashi ganin yadda dukda butulcin da diyarshi tayimashi Hakan be hanashi tsayawa a side dinshi ba a lokacin buqata, da wani ne da gefe zai koma yana yimasu Dariya.


A ranar dasuka cika kwanaki goma sha daya aka sallamesu daga asibitin, lokacin zee ta murmure sosai physically Saidai ciwon da ba'a iya gani wato na zuciya.


A ranar saboda murna Saida daddy ya shirya yar kwarya kwaryar party na welcoming dinta home duk don ya faranta mata

Haka ma'aikatan gidan suma sukaita zuwa yimata barka da dawowa

Ita dai iyakarta dan murmushi daga kuma Hakan zata maida fuskarta yadda take.


Da daddare ma Ummu batool biyota tayi dakinta acewarta itama nan zata kwana wanda tayi Hakan ne a hikimance don kar abarta ita kadai har tasamu damar fara wannan tunanin da ba'aso din

Saidai abinda basu saniba shine shi abu idan yana a rai ko kasamu nutsuwa ko baka samu ba yana ranka kuma dole ka tunashi a kowanne motsin da zakayi


Kuma rashin ba zuciya damar nutsuwa tayi tunanin abinda ke qumshe a cikin ta shike jawo ta cinkushe ka rasa me keyima dadi a duniya


Zee ta chanza sosai, idan nace sosai ina nufin sosai da sosai


Ta tashi daga wannan zee din mai tsiwa, classic mai yawan ado da kwalliya takoma so silent, moody and simple


Rabon da ta zauna da niyyar yin kwalliya Koda simple makeup ne tun ranar introduction dinsu da za'ayi

Yanzu dai data samu tayi wanka ta zura duk abinda ya tari gabanta shikenan sai takoma ta nade a gado ko kuma ta zauna tayi shiru kamar kurma.


Sosai take ba su daddy tausayi shiyasa duk suke iya qoqarinsu wajen ganin sunyi cheering dinta up.

Haka kawai daddy zai kwashesu da zee da mummy da Ummu batool su fita park ko shopping ko cinema duk don cheering dinta up.

Mummy ma yanzu babu batun daure dauren fuska don wani sa'in ma Sai kazo ka taddata zaune tanata bata labari kala kala duk nasa nishadi


Haka ma Ummu batool wanda haryanzu tare suke kwana dakinta, itama tana iyakar bakin qoqarinta wajen ganin ta debemata kewa takuma sanyata nishadi


Saidai abinda basu saniba shine gangar jikinta ne kawai taredasu, ainahin ruhinta na taredashi ya tafi dashi

Without Deen she's incomplete and she'll never be complete.


***


Zaune suke a falo dukkansu ana kallo ana fira, zee a kwance tayi pillow da cinyar Ummu batool idanunta a lumshe dukda ba barcin take ba


Dagowa Ummu batool tayi ta kalli daddy da mummy tace
"Yaya da matar yaya, akwai wata magana dake son fadamaku amma ban saniba ko zakuyi maraba daita ba"


Duk maida hankalinsu sukayi akanta, mummy tace
"haba in-law kifadi koma menene mana, kinsan kinfi qarfin komai a wajen mu"


Murmushi Ummu batool tayi sannan tasa hannu ta shafa kan zee da idanunta ke a lumshe har lokacin

"mezai hana idan natashi komawa Dubai natafi da daughter ta? Aganina idan ta cira daga nan zataji sauqin abin sosai kuma zatayi saurin mantawa"


Duk shiru sukayi babu wanda yace komai, ganin Hakan yasata cigaba dacewa

"kuma kunga acan bazata kasance lonely ba, ga batool ga aymaan duk zasu debemata kewa, sai inga yafi taita zama anan, zuciyarta bazata yi saurin healing ba kamar idan tabar nan din"


Shiru wajen yasake dauka can sai daddy yace
"to banqi ta taki ba sister, amma karatunta fa? She's in 300level yanzu, baki ganin tafiyarta ba kamar watsarda wadannan shekarun data diba tana karatun bane?"


Murmushi Ummu batool tayi

"yaya kenan, to kai kanada tabbaci zata iya cigaba da karatun yanzu? Kuma a the same makarantar? Kufa kukace acan suka hadu kuma acan ne wajen haduwarsu kusan kodayaushe, bakwa ganin Koda taso manta komai zuwanta makarantar zai dinga dawo mata da memories din baya?"


Nan ma shiru sukayi

Sai ta cigaba dacewa

"amma idan can ne zamu sama mata wata makarantar Koda school of nursing ce, kuma zatayi saurin moving on acan don can garine dayasha banban da nan kuma haka ma mutanen ciki ba na nan bane, zatayi saurin manta past dinta, ga kuma batool zata debemata kewa sosai amma nan fa? Batada wani sublings ita kadai ce ko wannan ma kadai ya isheta"


Duk shiru suka sakeyi suna jujjuya maganar kuma suna hango tsantsar Gaskiyarta aciki, tabbas idan Zainab ta cirama qasarnan komai zaifi zomata da sauqi kuma zatayi saurin mancewa da past dinta.

Daddy ne yasake cewa
"hakane lil sis, abinda kika fada haka yake kuma muma zamuso tayi moving on, mun gaji da ganinta ahakan amma matsalar anan shine ita, anya zata yarda kuwa?"


"eh daddy" inji zee dake bisa cinyar Ummu batool still idanunta arufe


Duk juyowa sukayi suka kalleta itama daidai nan ta bude idanunta sannan ahankali ta miqe zaune tana kallonsu


"daddy na amince, zanbi Ummy (haka dama take kiran Ummu batool), inason nayi nisa da nan, inason intafi wani wajen, Hakan zaisa naji sauqin abinda nakeji.

Daddy, mummy please ku yarda, ku yarda ta tafi dani, please" tafada a sanyaye tana kallonsu da lumssasun idanunta da haryanzu haskensu be dawoba bawai don kuka ba A'a sai don rashin kukan don tunda abin yafaru bata zubar da ko digon hawaye ba da sunan kuka.


Ajiyar zuciya daddy ya sauke sannan yace
"Hakan zaisaki farinciki?"


Da sauri zee ta kadamashi kai cikin doqin da rabonsu da ganin irinshi a fuskarta har sun manta


Kallon juna daddy da mummy sukayi sukayi murmushi

Daddy yace
"shikenan, as you wish princess. Allah yasa Hakan shiyafi alhairi"


Ga mammakinsu sai sukaga wani qayattacen murmushi ya su6uce mata wanda rabon da su ga irinshi a fuskarta harsun manta... ✍️


Kwana biyun nan Saidai kuyi hqr dani, bana samun yin typing da wuri am kinda busy these days


Ummin fasihu 🧚🏻‍♀�
8/2/21, 9:39 PM - Buhainat😝: *🙍🏻‍♂️DEEN 🙍🏻‍♂�*


*054*


*DUBAI 🌇*


Cikin dan qanqanin lokaci su Ummu batool da Zainab suka fara shirin juyawa Dubai


Sosai Zainab ke zumudin zuwa qasar don koyaya take moody idan ka tado mata maganar tafiyar sai kaga tadan washe ba kuma ke jawo haka ba sai ganin datake databar qasar barinta zatayi da duk wani damuwanta


Siyayya sosai sukayi na tafiyar a bangaren daddy kuma yaje yayi musu settling komai na tafiyar.


Ranar da saura kwana biyu tafiyar sukaje zaga dangi don zee tayi bankwana dasu ciki harda yan uban daddy dake garin, su mutanen Ruma kau Saidai sukayi bankwana ta waya don lokacin yariga da ya qure bare suje kuma dama ai yan Ruman basu dade dazuwa ba.


Ranar daren dazasu bar qasar kasa barci zee tayi.


Ranar kwana tayi kuka, kukan da batayi ba tun faruwar wannan abin.


Toilet tashige ta kunna shower tashiga ciki tayita kukanta har Saida muryarta ta disashe

Ko daddare ma kasa rintsawa tayi, tana Kwance lamo kamar mai barci amma ba barcin take ba

Rayuwar dasukayi da Deen kawai take tariyowa a kwalwarta From A-Z

Tayi kukan da bata ta6a yiba a wannan daren shiyasa koda ta tashi washegari idanunta sukayi suntum suka kumbura


Su mummy basuyi mammakin haka ba don sunsan kukanta mai dalili ne, gwara ma tayi ta wanko abinda ke zuciyarta da ta barshi a daskare a wajen.


Jirgin qarfe 12pm zasu bi Hakan yasa sukabar gida Tun qarfe 11:15am suka dauki hanyar airport.


Tafiya suke sunata fira cikin raha ana Dariya banda zee da idanunta ke kafe akan glass din motar na gefenta tana kallon masu wucewa, tana yiwa Nigeria kallon qarshe don ta qudura a ranta ita da Nigeria kuma sai wani ikon allah


11:30am dot suka shigo filin jirgin saman


Parking daddy yayi a parking space sannan duk suka bubbude koffofin motar suka shiga fitowa.


Zee ce qarshen fitowa.

Wani iska ne ya bugi fuskarta Hakan yasa ta lumshe idanunta tana shaqar iskar sannan tasake budesu


Su daddy ke fiddo trolley dinsu daga cikin motar Yayinda itakuma ke bin harabar airport din da kallo ba wai na qauyanci, A'a na bankwana, tana bankwana da her beloved country Nigeria inda zata tabar mutane masu matuqar muhinmmanci acikinta wanda bata jin zasu qara haduwa nan kusa Saidai idan su zasu bita can.

she's gone too, maybe forever, maybe not.


12 saura minti goma su Ummu batool da Zainab sukayi bankwana dasu daddy


Rungume zee su mummy sukayi in turn duk suna iya qoqarin ganin basu bayyana rauninsu ba ta hanyar xubar da hawayen dake forming a idanunsu.


Itadai zee barin nata tayi suka gangaro don bataga amfanin riqesu ba

Saida sukaji ana qara sanarwa sannan suka haqura da bankwanan suka juya Ummu batool riqe da hannun zee suka fara tafiya


Tunda suka fara tafiya zee bata qara waigowa ba har Saida suka kai daidai kofar dazasu shiga cikin inda passengers din keta shiga sannan ta waigo


Su mummy da daddy ta hanga can nesa tsaye still suna kallonta, dan murmushi tayi musu dukda batada tabbacin zasu gani saboda nisan dasuka yima juna sannan ta juya suka ida shigewa.


Mummy ce ta dora fuskarta akan kafadar daddy hawayenta na gangaro mata

Dafe bayanta daddy yayi idanunshi akan kofar da suka shige shima yana trying very hard don ganin yayi controlling emotion dinshi.


Ahankali zee kebin Ummu batool dake riqe da hannunta still suka isa inda ake tantancewa aka tantancesu suma sannan suka shige ta inda zasu bi su 6illa filin da jirgin da zasu hau yake.


Babu 6ata lokaci suka shiga jirgin suka nemi seat number dinsu suka zauna, zee na daga ciki daidai window Ummu batool na kusada ita.


Tunda ta zauna ta maida kanta baya ta jinginashi da kujerar datake akai ta lumshe idanunta


_*Xainab bazan ta6a barinki ba duk rintsi, zan jajirce a soyayyarki babu gudu babu ja da baya*_


_*I promised, I promised I'll never break your heart, never!*_


Jitayi anfara announcing akan a daura seatbelt jirgin na shirin tashi

Tana jin Ummu batool ta jawo belt din seat din nata tana dauramata Hakan yasa taki bude idanun


_*Zainab ina sonki, yanzu, da'iman, abadan*_


_*please marry me*_


_*am sorry... For everything*_


_*natafi.. Am gone.. Maybe forever.. Maybe not*_


Jin Sautin tashin jirgin ne yasata bude jajjayen idanunta Ahankali


Kallon window din gefenta tayi tana hangen waje ta nan


Dagawa jirgin yafarayi har ya ida barin qasa

Kurawa waje ido tayi tana ganin yadda suke qara yiwa qasa nisa


"bye.." tafada ahankali daidai da gangarowar wasu hawaye masu zafi


"Natafi... Maybe har abada.. Maybe not"


_safe journey ✈️_


❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️


*DUBAI (Abu dhabi)*


Tafiyar awa bakwai sukayi kafin su iso Qasar Gamayyan Larabawa wato Dubai, a birnin tarayyar qasar wato Abu dhabi.


Agajiye suka fito daga jirgin don ba qarya sun zaunu

Dare ne a qasar don lokacin har 10 ta dan gota Saidai garin tarr yake da hasken fitilun streetlights kamar da rana, mutane sai hada hada akeyi wanda mostly Larabawa ne


Amsar trolley dinta zee tayi hannun Ummu batool dake Miqamata ta Fiddo abin ja din tashiga ja tana bin bayan Ummu batool datayi gaba waya kare a kunnenta


Tafiya take tana dan qarema Wurin kallo a fakaice tana hango tarin banbancin dake tsananin nan da qasarta Nigeria

Gashi duk wanda zakaji ya bude baki yayi magana to larabci ce ziryan ta


Cigaba da bin Ummu batool tayi har suka ida fita daga airport din wanda Hakan yayi daidai da gama wayar Ummu batool

Juyowa tayi ga zee tayi mata murmushi
"marhaban biki bintii! Welcome to Dubai, qasar farincikin ki"

Murmushi zee tayi tana Kada kai kawai


"muje can mujirasu, sunce suna dab da isowa" inji Ummy tana nufar wata rumfa daga gefensu na dama

Itama zee jan akwai ta tayi tabita abaya kamar raqumi da akala

Gwadama zee inda zata zauna Ummy tayi ta zauna sannan itama ta zauna kusada ita tana qara daddana wayarta


Karawa a kunne Ummy tasakeyi da alamu kira take


Magana tafarayi da larabci tana dan sirkawa da hausa

Hausar datake dan jefawa aciki yasa zee gane ashe kwatancen inda suke takema wanda take wayar dashi

Can sai ga wata baqar mota tazo ta paka daga dayan side din


Ummu batool na ganin motar ta gyara yafin gyalenta tana cema zee ta tashi su Abbu sun iso


Wayar Ummy tasake daukan qara Hakan yasa ta daga tana kama trolley dinta itama tayi gaba zee da itama ta miqe tsaye tabi bayanta


Tsallakawa dayan gefen sukayi suka nufi baqar motar


Kafin su qarasa aka 6alle murfin kofar mai zaman banza wata budurwa wanda bazata wuce tsarar zee tafito sanye da arabian jallabiya ta yane kanta da veil din rigar irin yanin Larabawa

Bangaren driver kuma wani babban mutum ne yafito shima sanye cikin farar jallabiya da hula tashi da qwaqwa a kanshi


Kallo daya zee tayi musu ta shaidasu, Abbu ne da batool.


Da sauri batool ta taresu ta rungume Ummy tana tsuwar murnar dawowarta tana Dariya Ummy ma na tayata

Abbu ne ya qaraso wajen shima fuska fall murmushi yana yima batool magana da larabci da alamun tsokanarta yake don nan da nan ta cinno baki Ummy kuma na cigaba da yimata Dariya


Maida kallonshi yay akan zee dake kallonsu tundazu cikin fara'a yace
"lale marhaban yayata"


Murmushi zee tayi don dama hakan yake kiranta kasancewar sunan yayarshi gareta


Dan russunawa zee tayi tana gaidashi cikin murmushin yaqe shikuma yana amsawa da fara'a yana tambayarta ya suka baro su daddy tana amsawa da lfy lau


Batool ce tasaki Ummy ta nufi zee cikin murna ta rungumeta itama tana dan tsallen murna


Dan murmushi kawai zee tayi batace komai ba

Dagowa batool tayi daga rungumarta datayi

"ashe da gaske dake za'azo? Wlh dafarko ban yarda ba na zaci jana akeyi" inji batool din cikin hausarta dake radam don dukda anan aka haifesu iyayensu basuyi sake sun bari yarensu ya kufce masu ba.


Murmushi zee kawai tasake yi batace komai ba


"to ai yanzu da kika ga zahiri kin yarda ko?" inji Ummy tana yin gaba da kayanta

Saurin amsar trolley din hannun zee batool tayi da hannu guda takuma sarqaho hannun zee da dayan suma suka shiga bin su Abbu dasukayi gaba tana cewa

"eh Ummy na! Yau yaya zaisha haushi, nasamu wacce zamu dinga hademashi kai" tafada tana Dariya


"ko wacce zasu dinga hademaki kai ba" inji Abbu dake saka trolley din a booth


Dan kumbura fuska batool tayi saita juyo ta kalli zee dake sauraronsu tace
"wai ukhty zee? Aini zaki za6a ko? Akhie bayada kirki ko kadan"


Murmushi kawai zee tayi tana jin Ummy na bata amsa da
"ai ke kinada kirkin ko? Ni ki kyalemin diya tasha gajiya kina damunta da surutu, babu abinda zatayi cikinku, ku dai da kuka saba sai kuyita fama"

Tura baki batool tayi tana cewa
"kai Ummy, ke dama da kin samu wata saiki mance da ni yar gaban goshinki ce" tafada tana shigewa shiga bayan motar bayan zee Tariga ta shiga

"yaushe? Aini tuni na mayar dake bayan qeya dake da yayan naki, ga yar gaban goshi na nan" tafada tana nuna zee daketa murmushin dramarsu

6ata fuska batool tasakeyi sannan ta kalli Abbu dake qoqarin tada motar

"Abbie, kaji ko?"

Dariya Abbu yayi yana cewa
"kyaleta, Aini ko me za'ayi auta ta itace da muqamin kujeran goshi na, itace ta gaban goshi na always" yafada yana tada motar


Dariyar jindadi batool ta fashe dashi sannan ta juyo wajen zee dake kallonta tayimata gwalo wanda Hakan yasa murmushi qara su6uce mata dama tuni ba Tun yau ba tasan halin batool, drama Queen ce ta gidan gaba


"to kinji kibar wani jin dadi, nima akwai masu sona" tafada tana gwalemata idanu


Dariya duk mutanen motar sukayi banda zee datayi murmushi kawai, Abbu yaja motar suka bar harabar Airport din


Tafiyar da batakai ta minti tallatin ba sukayi suka qaraso gidansu


Horn Abbu ya danna a bakin gate din gidan nasu


Ba'ayi seconds 20 ba aka wangale masu gate din


Danna hancin motar Abbu yayi cikin gidan suka shige


Direct parking space Abbu ya nufa yayi parking a kusada wata mota dake a wajen

Bubbude koffofin motar sukayi duk suka firffito


Kallon parking space din ummy tayi sannan tace
"Aymaan bayanan ko? Naga banga motarshi na"


"hmm yana hospital, wai yau night garesu" inji batool dake gyara gyalenta


Girgiza kai ummy tayi
"workaholic kenan, ni ban ta6a ganin wanda ya tattara dukkan imaninshi yaba aiki ba kamar Aymaan"


"to yaya kikeson yayi? Yaita zaman gida kamar mace? Karki manta yadda aikin likitanci yake musanmman irin wannan bangaren nashi na gynecology, ceton rayyuka yakeyi kuma dukda albashinshi nasan yanada lada awajen allah" inji Abbu yana ciro kayan bayan booth

"dukda haka Abbu, abin yayi yawa, gana fa gani wani lokacin ba lokacin aikinshi bane amma kuma a kirashi yakuma je, wani sa'in ma baida taqamaimai lokacin kanshi idan ba weekend ba" inji ummy tana kama hannun zee suka nufi cikin gida gabadaya


"ai saboda qwarewarshi tasa ake yawan nemanshi har haka, ke ba abin murnar ki bane ace danki is a professional doctor wanda ake jidashi a daya daga cikin shaharrarun asibitocin dubai?"


Dan ta6e baki ummy tayi tace
"dama ai kai ke daure mashi gindi shiyasa yake abinda yakeyi din, ku kuka sani ai, like father like son"


Murmushi duk sukayi daidai lokacin da suka qarasa shiga cikin gidan.

Dayake a gajiye suke kuma dare yayi basu wani tsaya jan zance ba ummy tasa batool ta wuce da zee dakinta da yanzu zai zama nasu su biyu akan cewa za'a biyo su da dinnersu sama.


Bankwana sukayima juna batool tayi gaba jaye da trolley din zee itakuma zee na take mata baya Yayinda ita kuma ummy tawuce tareda Abbu part dinshi


Sama suka hau inda anan sukaci karo da dakuna uku ajere


"kinga dakin ummy nan" batool tafada tana nuna dakin farko

Wucewa sukayi zuwa na tsakiya
"kinga dakinmu nan"

Sannan ta nuna na qarshe
"kinga dakin akhie, dayake farin kura ne saboda tsoro saiya za6i abarmashi na quryar yadda duk abinda zai faru saiya fara taddamu kafin ya taddoshi besan mu damuke kusa kusa da stairs ba munfi samun opportunity din guduwa idan ma abin tsoron yazo shi kafin ya 6a66aka ma mun bar layin unguwar"


Murmushi mai sauti zee tayi batareda tace komai ba


Bude kofar dakin tayi ta tura ta sannan ta koma gefe tana cewa
"welcome to the princess chamber" tafada tana bowing dramatically


Shigowa dakin zee tayi still murmushi a fuskarta tana yan kalle a dakin.


Komai na dakin pink ne yayi kyau sosai dukda bekai nata na Nigeria girma da tsari ba


"to ya kika gani?" inji batool tana daga gira daya


"fabulous" inji zee tana wuceta taje ta zauna gefen gado tadan jinginar da kanta a frame din gadon cikin gajiya


"yes! Dama nasan you'll like it, bari allah ya kaimu gobe na gwada miki na akhie sai ki tantance mana wanda yafi kyau da tsari, kullum cikin rigimar muke babu mai raba mana gardama to yau ga raba gardama nan tazo"


Zee da duk ta qoshi da surutunta ta dago daga jinginen datake tace
"where's the toilet?"


"there, me zakiyi?" tafada tana nuna mata kofar toilet din


Tashi zee tayi tsaye tana warware gyalen kanta tace
"wanka, am tired and sleepy"


"ok bari na hadamiki ruwan" inji batool tana nufar hanyar toilet din

"No please, zan hada basai kin wahalar da kanki ba" inji zee


"Karki damu, nima na baqunta zan miki don kice am nice amma kina ganina nan shegen san jiki gareni, gwara kibari nayi maki yau din don wata rana da kudinki ba zaki nemi nahada miki naqiya" tafada tana shigewa toilet din


Dan murmushi tayi tana ta6e baki sannan ta cigaba da rage kayanta


Closet din batool din ta bude ta dudduba can ta hango towel din datake nema ta dauka ta daura daidai lokacin da batool tafito daga toilet din


Bata cemata komai ba tawuce toilet din don sosai take buqatar wankan ga barcin dake idonta sosai shima


Cikin yan Mintuna tayi wankan ta fito saita tararda batool har tayi shirin barci glass cup din fresh milk a hannunta tana kur6a


Qarasowa tayi tana niyyar jawo trolley dinta ta ciro kayan barci batool ta nuna mata nata data riga ta ciro mata

Godiya tayi mata ta daukesu ta saka tayi amfani da roll on din batool sannan itama tazo ta dauki nata glass of milk din ta zauna gefen batool tashiga sha


Tasha fin rabi sannan ta ajiye lokacin batool ta fita

Bata tsaya jiran komai ba ta dauki remote din dakin ta qure a.c din sannan ta haye gadon ta jawo bargo ta lullu6e tana sauke Ajiyar zuciya


Lokacin da batool tadawo har barci yayi awon gaba daita don dama agajiye take liss


Daukar remote din batool tayi ta rage sanyin a.c din sannan itama tahau gadon ta kwanta batareda ta rufa ba, itama cikin qanqanin lokaci barci yayi gaba daita.


*WASHEGARI*


Sosai zee taji dadin barcinta na jiya don tun bayan abinda yafaru bata qara barci irin na jiya mai dadi ba, shiyasa da safe ta tashi garass


Suna gama sallar asuba batool tajata suka sauka qasa don hada breakfast


Sosai Hakan ya burge zee don agidan basuda yar aiki ko guda sai maigadi kawai Komai su sukeyi da kansu.


Hada breakfast din suke batool nata zuba kamar radio itakuma zee na aikin sauraronta

Cikin dan qanqanin lokaci suka gama suka kuma jeresu a dining


Komawa sukayi sama sukayi taking turn Wurin yin wanka da brush sannan suka shirya


8:00am daidai suka sauko qasa don yin breakfast kamar yadda yake a al'adarsu


Lokacin suma su ummy da Abbu sun fito suma cikin shirinsu Hakan yasa duk suka hallara dining area din


Batool ce tayi serving dinsu gabadaya

Itadai zee duk cikin kayan shayi kawai ta iya sha da toast bread tabar musu kingin kayansu na larabawa


Sosai taji dadin zaman yin breakfast din don sosai suka nishadantar daita da firarsu

Itadai murmushi ne nata idan akayi abin Dariya bata tsoma bakinta sai an sakota a zance kuma Koda an sakota a taqaice take bada amsar


Ahaka suka gama breakfast din su ummy suka dawo falon sukuma su zee din sukayi clearing din table din suka dawo sukayi joining iyayen a falon aka dasa firar


Sai can wajajen 9am Abbu ya tashi don zuwa shirin fita ummy tabi bayanshi saiya rage saura batool da zee


Cigaba da ba zee labaranta da basu qarewa batool tayi zee na sauraronta can batool tayi excusing kanta wai ta manto wayarta sama zataje ta dauko tadawo


Kadamata kai kawai zee tayi tanajin dadi atleast kunnuwanta zasu huta kafin ta dawo

Ajiyar zuciya ta sauke bayan wucewar batool tana mammakin yadda komai yafaru so fast qaddara takawota nan bawai da niyyar ziyara ba ko komawa nan kusaba sai don zama na adadin lokacin da itama bata sani ba

Ajiyar zuciya ta sake saukewa sannan ta miqa hannu ta dauki wani daily magazine dake kan centre table tafara budewa tana going through dinshi.


A gajiye ya turo kofar falon yana tafe yana jan qafa alamun gajiya


Lapcoat dinshi matse a qasan hannunshi na dama briefcase kuma riqe a hannunshi na haggu


Sallama yayi ciki ciki yana yayatsine fuska alamun liss yake ya ida Qarasowa cikin falon


Hangota yayi zaune hankalinta gabadaya akan littafin dake hannunta bama tasan da shigowarshi ba

Ajiye briefcase din hannunshi yayi ya tsaya ya riqe kugu yana kallon bayanta don baya dama ta juya mashi


Cije lip din qasa yayi sannan ya ajiye Lap coat dinshi yafara tahowa cikin sanda ta bayanta


Zee batasan wainar da ake toyawa ba sai kawai jitayi fitt an fige magazine din hannunta ta baya


Kafin tayi motsi kuma aka rufe mata idanu duka biyun da hannuwa ta baya


Qara tasaki don sosai abin yazo mata so sudden takuma tsorata sosai


Duk yadda taso cire hannunshi daga idanunta kasawa tayi don ya hanata yin Hakan


Hannunta tafara miqawa tasama don lalubawa taji ko wanene, tasan dai bai wuce batool amma data kawo hannu saiya zame yana qumshe Dariya


Daidai nan batool ta fito daga daki tanufo qasa

Abinda tagani yasata Wara idanu kamar zasu fado


"Akhie!" tafada cikin tsantsar mammaki


Saurin dagowa yayi ya kalli inda yajiyo muryar batool ya ganta can tsakiyar stairs tana kallonshi baki bude


Gabanshi ne yafadi, idan wancan batool ce to wacece wannan? Abinda qwalwarshi ta tambayeshi kenan


Babu shiri yayi saurin cire hannunshi daga face din zee yaja baya yana kallonta


Kyafkyafta idanu zee tashiga tana miqewa itama tsaye

Hannu tasa ta murza idanunta yadda ganinta zai dawo sannan ta bude idanun ta juyo ta inda aka rufemata idanun


Turuss tayi ganin wanda bata ta6a expecting ba

Dan Wara idanu tayi tana kallon yadda shima ya Wara idanu yana kallonta sai kuma ta maida kallonta ga batool da itama haryanzu tana a inda take tana kallonsu... ✍️


Manage 👏


Ummin fasihu 🧚🏻‍♀�
8/2/21, 9:39 PM - Buhainat😝: *🙍🏻‍♂️DEEN 🙍🏻‍♂�*


*055*


*DR AYMAAN*


Janye idanunta tayi daga kan batool tasake maidowa akanshi

Cikin daburcewa yafara bata hqr cikin harshen larabci

Dariyar batool ce ta dakatar dashi

"batajin larabci akhie, she's hausa" inji batool tana Qarasa saukowa tana Dariya


Sake kallon zee yayi yace
"ohh, please kiyi hqr, nayi tunanin wancan ce am sorry"


Sauke idanunta kawai zee tayi batace komai ba


Batool ce ta qaraso tana cigaba da Dariya

"shiyasa akace idan zaka gina ramin mugunta ka ginashi gaj..."


Bata qarasa ba ya fincikota ya kama kunnenta

"ni tsaranki ne?" yafada cikin larabci yana qara murda mata kunnen


Qara batool tasa tana matse ido cikin jin zafi

"wayyo akhie kunnena!"


Qara twisting din kunnen yayi yana cewa
"bani kike gayawa magana ba?"


Qara da tsuwa batool taita yi tana qoqarin qwace kunnenta amma takasa


Zee tunda suka fara take jinta uncomfortable, ga qarar batool datake ji har cikin dodon kunnenta

"amm... please leave her mana" inji zee tana kallonsu


Jin abinda tace yasa ya dakatar da murdawar dayake yiwa kunnen ya tsaya yana kallonta batareda ya saki kunnen ba


Ganin Hakan yasata dauke kanta gefe


"ka sakeni mana tunda tace ka kyaleni" inji batool tana 6ata fuska


Sakinta din yayi bayan ya gallamata harara yace
"ta ceceki da yau saina cire kunnen"

Yafada yana qara satar kallon zee da bata qara kallon gefensu ba Saima zamanta datayi


Da idanu Aymaan yayiwa batool nuni da wacece wannan?


Dariya batool tayi ta koma daga gefen zee din tace

"wai kinji uktie wai gulmarki yake da idanu"


Wara idanu Aymaan yayi sai ya nufota Hakan yasa ta qara Sakin qara ta ruga shima yabita suka fara zagayen falon


Tsayawa zee tayi ta saki baki tana kallon ikon allah don ita abin nasu ma mammaki yake bata

"afuwan akhie, afwan!" inji batool tana tana zillewa

"wlh yau zaki gane kurenki, yaushe nayi gulmarta?" yafada yana qoqarin tarota

"wlh bakai bane, bakai bane" tafada tana qara zillewa


Suna haka su ummy da Abbu suka shigo falon, Abbu cikin shigarshi na suit da alamun aiki zai fita


"ya subhanallilah! Meye haka?" inji ummy


Hakan yasa suka dakata daga abinda suke


"wlh ummy kiyimashi magana" inji batool kamar zatayi kuka


"Kun fara ko? Wai yaushe ma kadawo Aymaan?" inji Ummy


Hade gira Aymaan yayi
"yanzu yanzunnan kuma wai daga zuwana saita jamun sharri Wurin wannan" yafada yana nuna zee da haryanzu ke kallonsu


Tsaki ummy taja ta qaraso falon

"Allah ya shirya ku agaban baquwarma saikun saida halin, kun girma bakusan kun girma ba" tafada tana wucewa Wurin zee


Sosa lallausar sumarshi Aymaan yayi

"baquwa mukayi ne ummy?"


Dago zee ummy tayi sannan ta juyo ta gallamashi harara
"ba baquwa bace yar gidace kana ganinta nan don yanzu tama fiku iko da gidan"


"haba dai ummy, wannan wasane ko akhie?" inji batool


Gallamata harara Aymaan yayi yace
"ni meye hadina dake da zaki tambayeni? Tafiki iko da gidan, me zakiyi?"


Kumbura fuska tayi kamar zatayi kuka


Dariya Abbu dake sauraronsu Tundazu yayi yace
"Allah ya shirya ku, nidai karku koyawa yayata wannan halin naku, tana yar saliharta itama ta koma burkakka"


Dariya duk sukayi itakuma zee ta sauke kai tana dan murmusawa

Matsowa Aymaan yayi kusada Abbu cikin rada yace
"Abbu wai wacece?"


Murmushi Abbu yayi yace
"ai dole ka tambaya, kaida bakasan kusan mafi yawa cikin danginka ba.

To Zainab ce ta gidan daddy, daddyn Nigeria"


Wara idanu Aymaan yayi saikuma ya qara kallon zee da bashi take kallo ba

"you mean diyar Daddyn Nigeria?"

Kada mashi kai Abbu yayi in affirmation

"wannan yar yarinyar? Yaushe ta girma haka?" inji Aymaan cikin mammaki


Dagowa zee tayi jin abinda yace sai suka hada ido

Hararar da batasan tayi ba ta gallamashi don sosai taji haushin kiranta da yar yarinya dayayi

Ganin Hakan yasashi kauda kai yana Sosa qeya bakinshi dauke da murmushi


Dariya duk aka dauka falon ummy tace
"ba dole kayi mammaki ba? Yaushe rabonka da Nigeria? Almost 6years ba dole ta chanza maka ba?"

Qara satar kallonta yayi yaga bama gefen shi take kallo ba

"hmm ai zanje kwanan nan" yafada yana wucewa dining

"kamar duka kenan" inji ummy

"Allah kau ummy, bari aiki ya dan lafa, zan baku mammaki" yafada yana jan kujera daya ya zauna

"hmm allah yasa" inji ummy

"Amin dai ummy" batool ta amsa


Dagowa Aymaan yayi ya watsamata mugun kallo
"ba na hanaki sakamin baki a magana ba?"

Turo baki tayi ta koma bayan ummy

"bazaki zo Kiyi serving dina ba?" yasake fada yana huro hanci

Qara turo baki tayi sannan tazo ta wuce kitchen

Binta da kallo yayi sannan yayi kwafa ya juyo sai caraff suka hada idanu da zee, da sauri ta kauda kanta tana dan ta6e baki

"Daga zuwa sai cin abinci baka freshening up" inji ummy da tayi gaba jaye da hannun zee


"zanyi idan nagama, darabanil ju'i" yafada yana shafa cikinshi fuska a marairaice

"acici" inji ummy tana jan hannun zee suka nufi wajen Abbu

"muje mu raka Abbu kinji 'yata"

"to ni natafi, ma'asallama" inji Abbu

Fatan tsari Aymaan yayi mashi sannan suka fice gaba daya, Abbu a gaba ummy da zee abaya

Binsu da kallo yayi har suka fice sannan yadan daga kafadu

Batool ce tafito da kayan break wanda dama an fidda mashi nashi an ajiye incase idan yadawo


Zuwa tayi tana jerawa still fuskarta a kumbure

"tazo nan hutu ne?" inji Aymaan

"wa?"


"baquwar" ya amsa yana kallonta


Daga kafadu tayi tace
"kusan haka amma zata dan jima kadan"


Daga girarenshi yayi yace
"masha allah, kice mun qara yawa amma naga kamar bata magana, meyasa?"

"bari tadawo na tambayar maka ita"


Yiyayi kamar zai maketa tayi saurin ja baya da serving spoon a hannunta tana Dariya


Kwafa yayi kawai yajawo abincinshi yayi basmallah yafara ci


Acan waje kau har mota su ummy suka raka Abbu


Sallama sukayi da zee tana mashi fatan dawowa lafiya sannan ta juyo ta dawo ciki tabar ummy can tareda Abbu suna magana


Da sallama tasake Shigowa falon

Dago kai Aymaan da yanzu saura shikadai a falon yayi yana kallonta ya amsa

Kallonshi itama sukayi suka hada ido saita kauda kai

Stairs tanufa batareda ta yarda ta qara kallon gefenshi ba dukda yadda takejin idanunshi akanta


Binta da kallo yayi harta haye saman sannan yasake daga girarenshi biyu ya kada kai ya cigaba da cin abincinshi


A daki zee ta tararda batool Kwance tana waya cikin harshen larabci


Zama tayi gefen gadon tana sauraron batool din absentmindedly


Idanunta ne suka sauka akan Ring din yatsarta dake sheqi sanadin hasken rana dayayi reflecting akanshi ta window din bayanta


Qurama zoben idanu tayi tunanuka kala kala na kai kawo a kwalwarta


Yanzu Deen na ina? Me yakeyi? Yana tunawa da ita kau? Koko ya riga ya shafe babinta a tarihinshi? Yana cikin farinciki koko akasin haka?
Yana kewarta? Koko bayayi?


Ta yarda ta biyo Ummu batool nan ne don aganinta zata iya mancewa dashi with time, amma daga jiya zuwa yau tafara tantamar yiwuwar Hakan

Don duk motsin da zatayi saiya fadomata arai, duk blinking idanun da zatayi sai yayi mata gizo a idanu

Anya zata iya mantawa dashi? Anya?

She doubt it, tana tantama sosai akan haka, don Deen acikin zuciyarta yake, yariga yabi Jinin jikinta, mantawa dashi daidai yake da musanya zuciyarta da wata wanda babu Deen aciki kokuma musanya jininta da wani wanda babu shi a gudanuwarshi


Jitayi an dafa kafadarta Hakan yasa ta dawo daga duniyar tunanin data lula


Batool ce zaune kusada ita tana mata murmushi

Kamo hannunta batool tayi tana kallon zoben yatsarta itama

"shi yabaki?" inji batool tana kallon Ring din

Dago idanunta zee tayi ta kalleta batareda tace komai ba

Itama batool ta dago tana kallonta sai tadanyi murmushi

"yanada kyau sosai" tafada tana dan Kada kai

Nan ma batace komai ba

"sister, wani lokacin you have to let go abinda kake matuqar so sosai, ba wai don son ranka ba sai don Hakan shi zai fiyemaka alhairi.


Wani sa'in abubbuwa masu kyau basu cika zama masu amfani ba, misali wannan zoben dake hannunki

Kina Ajiyarshi ne bayan kinsan bazai amfaneki da komai ba Saima ya jefaki a wani hali idan kika kalleshi, why not ki cireshi tunda kema sanin kanki ne be cancanci zama a yatsarkiba yanzu"


Dan murmushi zee dake kallonta Tundazu tayi saikuma ta maida kallonta akan zoben

"a tunaninki cireshin zai sauya wani abin ne?"

Saita girgiza kai

"babu abinda zai chanza, babu.

Rashin shi ne ma zai jawo wani abin"


Kallon zoben tasakeyi

"idan na kalli Ring din sai natuna da ranar, ranar dayake gabana, zube a gwiyagunshi begging me to marry him.

The love, affection, seriousness dana gani a qwayar idanunshi a ranar yana sani tantamar abinda nagani a takardar da yabani, yana sani tunanin anya shi ya rubuta takardar, da hannunshi?

But sadly shine, shine, dalili kuma shine ban sani ba, abinda yafi komai tsayamin arai kenan.

Meyasa zai tafi batareda gayamin atleast dalili qwara daya ba? Meyasa?

Atleast yafada min Koda kuwa zuciyata ce zata buga, Koda qarya zaiyi min yayimin amma bawai yatafi hakannan ba, leaving me like a lost cat in the jungle"


Batasan hawaye takeyi ba Saida batool ta jawo ta ajikinta tana share mata su


"it ok zee, nasan yadda kikeji.."


"baki saniba batool, kuma bazaki ta6a sani ba sai idan kin tsinci kanki a wannan halin, nikuma bana maki fatan haka"


Qara rungumeta sidely batool tayi sannan tace
"ki gayamin, ki gayamin tarihin soyayyarku"


Girgiza kai zee tayi

"A'a, nima da nasan abinda zanyi inmanta da tuni nayi Hakan"


"unfortunately baki sani ba, amma kuma idan kikayi sharing dinshi da wani zakiji sauqi.

Tunda abin yafaru kin ta6a zaunar da wani kinyi pouring out abinda ke a zuciyar ki?"


Ahankali zee ta girgiza kanta

"you see? Fadama wani damuwarka ma yana rage damuwa.

Problem shared is Problem solved.

Idan kin fadamin zaki samu abu daya zuwa biyu

Nafarko zuciyarki zata rage nauyi saboda kinyi pouring out abinda ke cinkushe a cikinta wanda ke hanaki saqat

Na biyu kuma, who knows wataqila ina iya hango maki wani abu a soyayyar taku ko kuma na sama muku solution, bawai don am perfect ba saidon kowa da irin nashi baiwar da hangen"


Murmushi mai ciwo zee tayi tace
"zan fadamiki saboda dalili na farko da kika fada, wato don naji sauqin abinda nakeji a zuciyata

Amma batun samun solution ba be tasoba, sai idan akwai Problem ake samun solution, anan babu wani Problem idan ma akwai to bansaniba, tayaya za'a samu solution din?"


Ajiyar zuciya batool tayi tace
"to shikenan, ki fadamin din, am all ears"


Itama zee Ajiyar zuciya ta sauke sannan ahankali ta maida kallonta akan zoben hannunta


"Sunanshi DEEN... KAMALDEEN MUHAMMAD...."


****


Ummy ce tashigo falon bayan taga tafiyar Abbu


A dining din ta iske Aymaan yanata aika abincinshi hankali kwance


Qarasowa wajenshi tayi taja kujera itama ta zauna

"Likita bokan turai" inji ummy cikin tsokana


Murmushi yayi sannan ya dauki glass cup din gabanshi yayi sipping ruwa

"Umminmu! Ashe jiya zaki dawo da nasani da banje aiki ba"


Harara ta gallamashi
"kamar duka kenan"

Dariya yayi
"Allah ummy jiya munshiga busy sosai, surgery hudu nayi da daddaren nan"


Girgiza kai Ummy tayi
"Allah sarki, ai mata na shan wuya, haihuwa yaqin mata, allah yasa kowacce tagamata lfy"

Sipping ruwa yasake yi sannan ya amsa da amin

"kaga qanwarka ko?" inji ummy tana kallonshi

"baquwa?"


Harararshi tasakeyi
"sunanta kenan?"

"I don’t know her name ai"


"shame on you, ace bakasan sunan cousin dinka ba"


Sosa kai yayi yana dan 6ata fuska
"kai ummy"

"to ai Gaskiya ce, to sunanta Zainab"

"oh kinga kina fadi na tuna, ai na santa lokacin danaje Nigeria last ai naganta lokacin yar qarama ce nasan bazata wuce 15 ba kuma she's a talkative tana magana sosai gashi batajin magana amma yanzu ta chanza sosai, naga ko magana batayi, ko haka girman yazo mata?"


Murmushi ummy tayi
"eh to, kasan ana qara girma ana qara nutsuwa, tabbas ta nutsu Saidai wannan nutsuwar haka bata lafiya bace don kamar yadda kace magana ma wuya take mata gata always moody"


Ajiye spoon din hannunshi yayi
"to meya faru? Meya maidata haka to?"


Ajiyar zuciya ummy tasakeyi tace
"she's heartbroken"

"heartbroken?" inji Aymaan yana kafe maman tashi da hazal eyes dinshi


"yes, wanda takeso ne ya yaudareta, kwanan nan ba kaji muna maganar introduction daza'ayi a Nigeria ba?"

"yes, naji kuna discussing dinshi da Abbu"

"to itace, yaron asalinshi dan talakawa ne don koko da qosai suke saidawa for living

Sun hadu da Zainab dinne a school and they both fell in love

Amma da maganar tazo wajen daddy saiyaqi yarda saboda yaron ba Dan masu hali bane plus yana gudun ace ba sonta ba yake kawai yaudararta yake yana sonta saboda kudin da mahaifinta kedashi

Daddy yayi iya qoqarinshi don ya rabasu amma a banza don she's deeply in love with the guy don a sanadin haka ta kamu da hawan jini saboda damuwa.

Ganin babu sarki sai allah yasa kawai ya yarda yakuma cema yaron ya turo magabatanshi suzo ayi introduction idan dagaske yake.

Lafiya lau aka fidda ranar introduction din har ya bugomin nan munata murna

Saidai ranar da aka fidda don yin introduction din babu yaron babu magabatan nashi babu alamunsu.

An jira anjira shiru gashi wayar yaron bata shiga

Ganin Hakan yasa daddy aika drivernshi don ganowa ko lfy?

Wai dayaje saiya iske gida garqame da kwado

Aranar dai Saidai aka watse ba'ayi introduction din ba

Washegari shiru, babu su babu alamar su

Hankalin Zainab ya tashi don tana sonshi Sosai fiyeda tunaninka

Ganin ta tashi hankalinta yasa daddy shiryawa washegari yaje yagano da kanshi and the same story ya tarar still gidan kulle

Zainab dai taqi yarda ta nuna tanaso taje tagani da kanta

Koda sukaje din saita tarar da abinda suka tarar suma, suna ahaka wani abokin yaron yazo wajen da shar6e6iyar envelope wai gashi inji yaron da sukaje nema

And could you believe what she saw inside?

Letter ne ya rubuta yana magangganu marassa kan gado wai he's gone wai tayi haquri wai he's gone forever"


"what? But why?" inji Aymaan

Watsa hannuwa ummy tayi
"oho, beyi stating dalili qwara daya ba nayin Hakan, kawai wai he's gone.

Anan take tayi collapsing a wajen daga nan aka kwasheta sai hospital

Saida tayi kwana uku kafin ta farfado, blood pressure dinta yayi high ga difficulty in breathing.

Dakyar aka shawo kanta a kwana na uku ta farfado kuma daga ranar takoma haka, babu uhm babu uhm uhm, yanzu ma fa wai da dan sauqi ne ma tunda idan akayi magana tana amsawa da kau bata magana Saidai tayi smiling painfully.

Ganin Hakan yasa kawai na yanke shawarar tahowa daita nan don am very sure zatafi saurin healing nan bisa ga can, don ko babu komai ta chanza environment. Shiyasa kaga na taho daita har lokacin da zata warware kamar babu abinda yafaru"


Sosai jikin Aymaan yayi sanyi, nan take yaji abincin gabanshi ya fita ranshi

"so sad" yafada ahankali

"very sad indeed wlh, donma kamar yadda nafada maka ta dan warware da lokacin danaje Nigeriar ne da sai kayimata qwalla"


Wani zafi Aymaan yaji ya ziyarci zuciyarshi nan take yaji ya tsani koma waye wannan mayaudarin


"amma wannan ya cika butulu wanda besan alhairi ba, ko babu komai ko don soyayyar Gaskiya data nunamashi be kamata ya badamata qasa a idoba"

"hmm ai kai kasan da Hakan shi besaniba"


Shiru yayi ya cigaba da huci, yana jin ranshi na 6aci sosai

"shiyasa nazo daita nan don tasamu sallama, Aymaan wannan aikin tareda ku zamuyishi, help her, help her forget her past, mu Hade qarfi wajen ganin mun mantar daita past dinta, tayi moving on kamar babu abinda yafaru"

Dagowa Aymaan yayi ya kalli ummy
"yes ummy, we'll do everything, everything wajen ganin mun mantar da ita past dinta, I assure you, insha allah zata yi farinciki fiyeda da"


Murmushi ummy tayi cikin jindadi
"barakallahu fika Aymaan, allah yayi muku albarka gabadaya, idan kukayimin haka kun biyani wlh"


Wani qayattacen murmushi Aymaan yayi yace
"karki damu ummy, wataqila dama basu daceba, wataqila ba alhairi bane agareta shiyasa allah ya kawar dashi, insha allah zata samu wanda ya dace daita, insha allah zatace gwara da akayi hakan, shikuma zaiyi nadama har qarshen rayuwarshi"


Murmushi jindadi ummy tasakeyi
"Alhamdullilah! Allah yasa Hakan Aymaan, allah ya tabbatar mana da alhairinsa"

Da amin Aymaan ya amsa yana daukar ruwan gabanshi yakai baki

"bari naje sama ok? Kayi sauri ka qarasa abincin karya huce" tafada cikin yanayin farinciki

Kadamata kai yayi kawai yasake jawo abincin gabanshi


Ganin Hakan yasa ummy wucewa tana jin wani madaukakin farinciki a ranta, tabbas da alamu haqanta zai cimma ruwa, taga alamun abinda takeso zai faru, idan kau Hakan yafaru sai tafi kowa murna a duniya.


Aymaan kau tana wucewa ya ture abincin gabanshi ya koma ya jingina da kujerar bayanshi ya harde hannayenshi a qirji


Fuskarta tayi mashi gizo a idanu, yes! She's in pain, yaga Hakan a fuskarta, to amma wane asarrare ne marar hankali da zai rasa wanda zaiyi hurting sai damsel irin wannan

Wani kayattacen murmushi ya su6uce mashi

Lallai, to koma waye yayi sakaci, sakacin dazai qare rayuwarshi yana cizon yatsa, har qarshen rayuwarshi, he'll make sure he did that.... ✍️


_wasa farin girki🤸🏻‍♀️_


Ummin fasihu 🧚🏻‍♀�
8/2/21, 9:39 PM - Buhainat😝: *🙍🏻‍♂️DEEN 🙍🏻‍♂�*


*056*


*KADDARAR SO ❤️*


Kuka sosai Batool keyi lokacin da zee takai aya a labarin soyayyarsu da Deen datake bata


Jawota tayi jikinta suka rungume juna suna cigaba da kukan atare.


Sun dan jima ahakan sannan sukayi breaking hug din

"Am sorry" inji batool tana kallon zee idanunta jiqe da hawaye

Girgiza kai zee tayi tace
"Don't be"


"labarinku is so touching, rabuwarku is so disheartening" inji batool


Kada kai kawai zee ta iya yi tana share hawayenta da bayan hannu

"Inaji ajikina ba laifinshi bane zee, inajin koma menene ba da son ranshi ba ya barki"


Dan murmushi zee kawai tayi tace
"nima Hakan nake tunani don na yarda da soyayyarshi agareni amma koma menene yakamata ya gayamin, who knows muna iya working together musama ma kanmu mafita, koma menene be kamata ya karya alqawurranshi da yayi min ba"

Kada kai batool tayi tace
"Kiyi hqr zee, nasan duk inda yake shima yana can yana kewarki kamar yadda kike kewarshi"


Girgiza kai zee tasake yi
"I don’t miss him, I miss who I thought he is"

"kibar fadin haka zee, insha allah watarana qaddarar data rabaku zata qara hadaku and at that time zai fayyacemiki komai"


"babu qaddarar dazata sake hadamu batool, mun riga mun gama da juna a duniyar nan, shi yana Nigeria ni ina nan, bazan koma Nigeria ba kamar yadda shima bazai ta6a zuwa nanba, tell me, tayaya qaddarar zata hadamu"


"zee kenan, qaddara ta wuce tunaninki musanmman qaddarar so, you dont know what allah have in stock for you dahar ya rabaku, wataqila ba alhairi bane agareki ko kuma akwai wata manufa akan Hakan"

Daga kafadu kawai zee tayi tace
"mubar maganar haka, atleast na danji sauqin zuciyata danayi sharing damuwata, nagode"

Murmushi batool tayi
"never mind, amma idan bazaki damu ba zan dan nemi alfarma awajenki"

Komawa Zee tayi ta jingina da frame din gadon tace
"Inaji"

"please idan kinada picture din gayen ki gwada min inason ganinshi"

Shiru zee tayi

"please.." inji batool pleadingly


Dan murmushi tayi sannan ta nuna mata wayarta dake kan mirror

Da sauri batool ta tashi ta dauko wayar ta miqa mata

Girgiza mata kai tayi tayimata nuni da ta bude

Swiping wayar kawai tayi ta bude don dama ita bata sakawa waya security

"ki shiga gallery"


Yin yadda tace tayi

"shiga folder mai suna DEEN"


dubawa tayi saita ga folder saita danna ya bude


Hotuna tagani masu yawa duk sun bubbude

Na farkon ta danna nan take smiling face din Deen ya mammaye screen din wayar

Dan Wara idanu batool tayi tana gasping
"woooow!" tafada ahankali tana qarema fuskarshi kallo

Itadai zee mayar da idanunta tayi ta rufe kawai tana sauraronta

Wuce hoton na farko tayi na biyun ya bayyana nanma Saida tayi gasping

Haka taita bin hotunan daya bayan daya wanda duk hotunan fuskarnan dauke take da wannan murmushin nashi mai tafiya da zuciyar mutane kuma ga dukkan Alamu ma babu hoton da aka dauka da saninshi, wani Wurin yana magana ne, wani Wurin idanunshi nakan littafin dake hannunshi, babu wanda yafi burgeta sai wanda akayi mashi yana dauke da sultan suna Dariya.


Saida tagama going through duka sannan ta dago ta kalli zee da haryanzu idanunta ke a lumshe

"wow sis, Gaskiya guy dinnan ya hadu, dole rashinshi yasa ki shiga hali" inji batool cikin santi

Bude idanunta zee tayi ta gallamata wata muguwar harara sannan ta maida idanunta ta rufe

Dariya batool tayi tace
"Allah kau karki ji wasa sis, wannan na sameshi ai tusashi gaba zanyi ina kallo inajin dadi, ko laifi yayi min dana kalli fuskarshi zan huce, wayyo allah amma ya hadu dama ana samun ire iren hot guys dinnan a Nigeria?"


Banza zee tayi ta kyaleta kawai

"wayyo, aikau Ahmed nafasa sonka, Nigeria zani! Wayyo hot Nigerian guys inanan tafe"


Dan murmushi ya su6uce ma zee, sosai shirmen batool ke bata Dariya, haka taita sauraronta tayita zuba ita kadai ko gajiya batayi.


*AYMAAN*


Aymaan kau da maganar zee ya yini ya kwana ya kuma tashi

Sosai abin ya tsaya mashi arai.

Ga wani gizo da fuskarta keyi mashi duk lokacin daya motsa.

Tunawa yayi jiya a wajen dinner

Kasa concentrating yayi akan abincinshi banda satar kallonta every now and then babu abinda yakeyi


Itakau batama san yana yi ba don bayan Gaisawar dasukayi sama sama ko gefen shi bata qara kallo.


Koda ya dawo sallar asuba shirin fita asibiti ya hau yi don yau aikin safe garesu.


Qarfe 8:00am yafito daga dakinshi cikin shigarshi ta qanannun kaya, baqin dogon wando da farar shirt yaci zanzaro ga lapcoat dinshi dake sagale da hannunshi sai briefcase riqe da dayan hannun.

Yayi kyau sosai a shigar ga wani irin cool qamshi dake tashi a jikinshi


Fara saukowa yayi daga stairs din Waya kare a kunnenshi yana amsa kira har ya ida sauka.


Dago idanunshi yayi sai suka sauka akan zee dake jejjera flask akan dining table


Kafeta da idanu yayi yana kallon every movement dinta Yayinda can qasan zuciyarshi yake jin wani feeling da bazai tantance kona menene ba


Zee dake aikinta hankali kwance tadan dakata jin kamar ana kallonta

Ahankali ta dago sai caraff suka hada ido dashi tsaye a inda yake yana kallonta itama


Ahankali yadan sakarmata wani cool murmushi

Dauke kai tayi kawai ta cigaba da abinda takeyi

Hakan yasa ya qara fadada murmushin shi sannan ya nufo dining area din


Jan kujera dake facing dinta yayi bayan Qarasowarshi ya zauna still yana kallonta


Bata dago ba ta kalleshi haka kuma bata dakatar da abinda takeyi ba

"sabahal khair ukhtie" yafada jovially


Sai a sannan ta dan dago ta kalleshi, kamar bazata yi magana ba sai kuma ta motsa bakinta ahankali tace
"sabahan-nurr"


Dan Wara idanunshi yayi jin ta maido mashi da larabcin

"dama kinajin arabic?" ya tambaya yana kallonta

"No" tafada tareda Juyawa tabar wajen


Binta da kallo yayi harta shige kitchen din, daga girarenshi yayi sannan ya danyi murmushi ya kada kai sannan ya sa hannu yajawo abubbuwan kan table din yana bubbudewa don serving kanshi.


Yana cikin cin abincin ne suka sake fitowa daga kitchen din da zee da batool


Dagowa yayi daga shayin dayake sipping yana kallonsu har suka qaraso

"sabahal khair Akhie" inji batool cikin fara'a

"sabahan-nurr" yafada yana dan satar kallon zee dake dora tray din hannunta kan table din

"yau kuma tunda safe zaka fita?" inji batool tana taya zee jejjera abubbuwan dasuka kawo

"ga zahiri?" yafada a taqaice yana sipping shayinshi ahankali yana satar kallon zee ta saman kofin

"da ace yau lecture din safe gareni da kayi dropping dina"


Dagowa yayi ya gallamata harara yace
"ke da wa?"

Dariya tayi

"Don't even try that, rannan ma dakikaga na kaiki don ummy tayi magana ne shiyasa amma wlh kika qara yimin Hakan zan daukeki ne naje na watsar gefen titi babu ruwana"


Dariya batool tasakeyi tace
"babu komai saina tashi na nemi cab ya qarasa dani school din, what matters shine kadai tuqani"

Dagowa yayi ya gallamata harara Hakan yasa ta koma bayan zee datayi kamar batasan sunayi ba tana Dariya

Kwafa yayi sannan ya turama zee plate dinshi
"zubamin wannan kadan ukhtie"

Kallon plate din tayi saikuma ta dan jawoshi tashiga zubamashi

Saida yaga yakai daidai yadda yakeso yace
"yauwa ukhtie, shukran. Ke kuma ki koyi yadda ake girmama na gaba kamar dai ita" yafada yana nuna zee

Ta6e baki batool tayi tace
"nima ai inayi, Ganine ba'ayi"


"a ina kike yi? Kin maidani abokin wasanki, shi yaya girmama shi akeyi sosai, don babban wa uba ne, koba haka ake cewa ba ukhtie?" yafada yana maida kallonshi kan zee

"yes" tafada simply sannan tajuya ta bar dining din ta nufi stairs


Binta da kallo duk sukayi sannan suka kalli juna

Qumshe Dariya batool tayi tana rufe bakinta da tafin hannunta

Wani kallo ya watsamata yace
"bar nan"

Da sauri tabar wajen tana cigaba da qumshe dariyarta tabi bayan zee


Kwafa yayi sannan ya maida hankalinshi akan abincin gabanshi ya cigaba da ci


Bai qara 6ata lokaci ba ya tashi ya fice daga gidan.


Tunda yashigo hospital din aketa gaidashi, duk inda ya gitta sai an gaidashi shikuma yana amsawa cikin fara'a


Aymaan kenan, kyakyawan namiji mai cikar haiba da kamala, mutum ne faran faran ga yawan wasa da sakewa wanda Hakan yasa yakeda farinjinin mutane sosai

Aymaan ba fari bane haka zalika ba baqi bane, he's chocolate in complexion, chocolate dinma irin mai sheqin nan.


Dr Aymaan qwararren likitan mata ne wanda ake jidashi a daya daga cikin manyan asibitocin dubai saboda qwarewarshi da hazaqa da allah yayi mashi


Yayi suna sosai a asibitin dama sauran asibitocin qasar don sosai kingin asibitocin ke kwadayin samunshi a asibitinsu suma kuma sunsha kawo mashi tayin yadawo asibitin su akan farashi mai tsoka amma yayi turning down request dinshi politely don idan akwai abinda ya tsana to cin amana ne?


Ko patients sunfi son Dr Aymaan ya dubasu saboda qwarewarshi wajen aiki dakuma iya mu'amallantar patients dayayi, gashi qwaro ne a fannin aikinshi don wani lokacin idan wasu likitocin suka kakare to shi ake kira kuma cikin ikon allah da yazo komai zai warware. Shiyasa mafi yawancin lokuta ma bayada timetable na kanshi na aiki don ko lokacin aikinshi bane ana iya kiranshi at anytime kuma yatafi batareda gardama ba


Aymaan allah yayishi da tausayi musanmman akan mata.

Yana matuqar tausaya masu kuma beson abinda zai ta6asu don idan akwai abinda beso to kukan mace ne idan kuma akwai wanda ya tsana to mai sa mace kuka ne, duk wanda yasan Aymaan yasanshi da wannan tausayin na mata ko don shi likitansu ne kuma yasan matsalolin da suke fama dasu?


Akwai lokacin daya ta6a yiwa wata mata aiki dazata haihu don takasa haihuwar da kanta, haihuwar matar tabiyu kenan


Cikin sa'a akayi aikin lafiya aka gama lafiya don har Saida ya gwadama matar diyar daya Ciro yana Tambayarta me tasamu dayake aikin na ido biyu akayi.

Lafiya lau ta amsa mashi da mace aka samu Hakan yasa yabada diyar akaje wajen gyarata shikuma yafita yima ahalin matar albishir din yin aikin successfully.


Sosai ahalin sukaita murna suna godewa allah shikuma suna sanya mashi albarka.

Da farinciki ya dawo dakin da take Saidai me? Sai ya tarar matar nata kokowa da numfashi nurses nata qoqarin bata taimakon gaggawa.

A rude shima ya shiga iya qoqarin shi wajen ganin numfashinta ya daidaita Saidai kana naka allah na nashi don ko minti biyar bata qara ba a duniya ta rasu


Sosai mutuwar ta girgiza Aymaan a lokacin.

Sunfi Mintuna 10 ahaka dashi da nurses din dakin dasukayi cirko cirko cikin rashin sanin abin yi


Daga baya Dakyar ya iya summoning courage yafita Domin sanar da ahalin nata

Saidai ganinsu sunata daukar jaririyar anata murnar qaruwa

Sosai gwiwarshi ta sage yaji zuciyarshi ta karye

Koda sukaga Hakan sai suka fara Tambayar shi lfy?

Dakyar ya iya danne abinda yakeji yayi breaking din labarin mutuwar matar garesu

Dayake ba masu qarfin imani bane sai suka hau koke2 da iface iface har wata ma ta sha qwalarshi tana cewa qarya yakeyi ba yanzu yazo ya sanar dasu lafiyarta lau ba

Nan fa akazo aka taru mutane nata rarrashin ahalin mamaciyar suna yimusu tuni da qaddara.

Aymaan kau be cewa komai sai hawayen dayake wanda ba komai ya jawo Hakan ba sai kukan da jaririyar keta tsanyarawa.

Sosai jaririyar tabashi tausayi don bilhaqqi da Gaskiya take kukan kamar tasan abinda yafaru

Ganin Dr Aymaan na hawaye yasa duk jikin mutanen wajen yin sanyi suna kallon yadda ya dauki jinjirar yana kallo yana hawaye.


Saida ya dauki kwanaki sosai kafin abin yasakeshi kamar yadda yasaba dik lokacin da patient ya mutu a hannunshi.


Babu wanda besan wannan halin nashi na tausayi ba a fadin asibitin


Hakan yasa Koda yaji labarin zee sai yaji ta mugun bashi tausayi kuma yaji ya tsani wanda yaudareta don shi aganinshi mata hallitu ne na musanmman wanda ya kamata ayi treating dinsu specially don a gurinshi mata sune gift of life.


Aymaan yanada abokai wadanda shi kansa besan iyakarsu ba Amma acikinsu akwai babban amininshi wanda alaqarsu tawuce abota kadai ta koma kamar ta yan uwantaka.

Sunan aminin nashi AHMAD JUNAID, dan kasuwa kuma P.A a companin babanshi

Tare suka taso tun suna yara kuma tare sukayi karatu a makaranta daya sai course dinsu kawai daya banbanta


Sosai suke abota mai tsafta wanda Hakan yasa tun suna qananu suka qulla zuminci tsakanin iyayensu suma don sosai iyayen Aymaan da Ahmed ke zuminci

Zuminci yaqara karko ne lokacin da Ahmad da batool suka fara soyayya.

Babu wanda beyi farinciki ba da Hakan don ko babu komai Hakan zai qara qarfafa zumuncinsu kuma zai qara girmama abotar dake tsakanin Aymaan din dashi Ahmad din, Wannan kenan.


Sai da marece sosai sannan yabaro asibitin

Akan hanya ya tsaya yasayi kayan maqulashe da fruits sannan ya wuce gida.


Parking yayi a parking space sannan ya bude motar yafito

Kamar kullum lapcoat din na sagale a hannunshi ya riqo briefcase dinshi da dayan hannun

Rufe kofar yayi sannan ya zagaya ta dayan bangaren ya bude back seat ya Fiddo ledar tsarabar daya siyo yasake maida kofar ya rufe ya kulle motar gabadaya da key din hannunshi sannan ya juya ya nufi cikin gida


Da sallama yashiga falon, babu kowa aciki Hakan yasashi nufar stairs kawai yanufi sama

Yana qarasa hawa saman itakuma ta fito daga dakin

Turus tayi ganinshi haka unexpected

Murmushi yayi mata, bata mayar mashi da martani ba Haka kuma batayi magana ba sai kauda kai datayi.

"hyy, slm alaiki" yafada cikin murmushi


Qara Dagowa tayi tadan kalleshi saikuma ta dauke kai

"wa'alaika sallam" ta amsa tana shirin wucewa

"here" yafada yana miqa mata ledar hannunshi

Kallon ledar tayi takuma kalleshi da alamun tambaya

Murmushi yasake yimata
"tsarabarku ce, ke da batool"

Kamar bazata amsa ba sai kuma ta miqa hannu ta amsa
"thanks"

"afwan, haza wajibi" yafada yana mata murmushi

Juyawa tayi batareda taqara cemashi komai ba takoma dakin

Murmushi yasake yi ya dan shafa lallausar sumarshi sannan shima ya wuce dakinshi.


A dinner ma yau haka yabi ya takura mata da kallo donma kallo bemata komai Tariga ta saba dashi shiyasa bata maida hankaliba kanshi.

Duk abinda yasan zai jawo suyi musayar magana shi yakeyi don ko yaya ne sai yayi yadda yayi ya sanyota cikin Maganarshi


Haka ya cigaba dayi acikin kwanakin dasuka biyo baya.


Sosai yake qoqarin janta ajiki by behaving freely around her amma kwata2 taqi bashi hadin kai, magana ce idan yayi mata ta amsa a taqaice daga haka kuma zataja bakinta tayi gumm

Saidai Hakan be sanyaya mashi gwiwa ba ko kadan kuma besa yafasa janta ajiki ba, everyday idan zai dawo saiya dawo masu da tsaraba, wani sa'in kuma ya kwashesu da ita da batool sufita outing ko shopping wanda acewar batool albarkacin zee take ci don da don ta itace Saidai ta ru6e bata fita shopping ba Indai shi zai kaita

Ahankali ahankali tadan fara sabawa dashi don Aymaan mutum ne matuqar iya zama da mutum komai baudadden halinshi, idan ya lura da yadda kake to baya damuwa da duk abinda zakayi zai bika ne a yadda kake har ku fahimci juna.

Ahankali zee tafara dan Sakin jiki dashi don wani sa'in suna dan fira sama sama.

Ga packs packs daya saba mata da zuwa duk lokacin da yake free

Sosai Aymaan yasan takan gari kuma yasan wuraren shaqatawa masu sanya nishadi wanda duk idan ya kaisu sai zee ta nemi damuwarta tarasa.

Hakan yasa har qagara take taji yayi masu magana akan su shirya suje yawo.


Kasancewar lokacin da zee tazo dubai duk higher institution sunyi nisa a semester dinsu don gab ake da zana exams Hakan yasa aka bari sai anyi hutu an koma sannan a sama mata replacement itama.


Cikin yan kwanakinnan zee ta dan warware, yanzu lafiya lau za'a zauna ayi fira da ita harda dariyarta, tasaba da wannan ahalin sosai musanmman batool data koma mata kamar wata bestie don bata jin komai wajen sharing damuwar ta da ita


Aymaan kuma haryanzu dai bata ida Sakin jiki dashi ba don basu yan tsokane tsokane yadda yakeyi da batool don koya tsokaneta Saidai tayi murmushi kawai ta kauda kai


Shikau Aymaan Hakan baya damunshi don ko gwasaleshi tayi baya nuna yaji haushi haka zai bita yadda takeso don a zauna lfy


Ahmed ma yasan da zaman zee a gidan don gidan Wurin zuwanshi ne sosai kamar yadda shima Aymaan ke zuwa gidansu Ahmad din sosai

Sau biyu suka ta6a ganin juna amma kusa kullum da kalar labarinta da Aymaan zai bashi

Shidai nashi saurare idan kuma yagama yaita yimashi Dariya yana tsokanarshi akan koya afka ne, duk lokacin dayace Hakan Saidai Aymaan yayi mashi kallon uku saura kwabo ya watsar batareda yace mashi uffan ba.


*1 MONTH LATER*


"nifa zan tafi Allah" inji zee dake bakin kofa tana kallon batool fuska a tsuke

"haba habibty, don Allah Kiyi hqr saura kadan fa, idan kika fita wlh tafiyarshi zaiyi bazai tsayani ba" tafada tana cigaba da kiciniyar daure igiyoyin takalminta


"kema mugun nawa gareki wlh, tun yaushe kike abu guda kin kasa gamawa anbar bawan allah yanata jira"

Tashi batool tayi bayan ta ida gyara takalmin tace
"kice dai kawai zumudi kike mutafi bawani an tsaida bawan allah mu mukace muna zuwa? Shi yace muje mu shirya mutafi"

Kwafa zee tayi ta juya ta bude kofar ta fita.


Saurin feffesama jikinta turaren hannunta batool tayi ta ajiye ta maramata baya da sauri


Qara duba agogon hannunshi Aymaan yayi a karo na ba adadi yana wondering wane irin shiri ne Hakan sukeyi haryanzu basu fitoba

Sanye yake cikin farin wando da sky blue din riga mai ratsin fari sai takalma farare, yar sumar kanshi tasha gyara sai salqi take


Jin taku a stairs yasashi Dagowa ya kalli wajen


Lumshe idanu yayi akanta yasake budewa cikin zuciyarshi yana fadin "masha allah"


Sanye take cikin dark blue arabian gown da duk jikinta stones ne sai gaban rigar da stones din yafi yin da6a da6a, rigar mai irin faffaden hannun nan ne mai jela sai gyalen rigar data yana akai irin na larabawa wanda sukeyi harda saman ha6a


Purse fara ce a hannunta sai takalmi suma farare wanda bakama hangensu sosai sai idan tana tafiya saboda tsawon rigar


Besan kallonta yakeyi ba har Saida yaji muryar batool na cewa
"Akhie!! Ko mun fasa fitar ne"

Da sauri ya dawo duniyar kallonta daya shiga ya juyo ya kalli batool dake tsaye riqeda qugu tana kallonshi

Harararta yayi sannan ya miqe tsaye yana cewa
"ni tsaranki ne? Kin gama tsaida mutane kuma shine yanzu zaki ishesu da ihu?"

Dan Wara idanu batool tayi
"na tsaida mutane ko ta tsaida mutane, Tundazu ita nake jira tagama Tambayarta kaji"

Juyowa zee tayi tana kallonta a mammakince jin yadda ta laftamata qarya qiri qiri

Ganin Hakan yasa Aymaan yayi kamar zai maketa yana cewa
"munafuka, sharri zakiyi mata ko? To wlh kibi ahankali kar nace banda ke a tafiyar nan"


Turo baki batool tayi
"nidai dama nasan ba'a sona"


"gwara da kika san Hakan, ukhtie mutafi kinji?" yafadawa zee

Saida zee ta danyi mata gwalo a fakaice sannan ta taho suka wuce da Aymaan

Binsu da kallo batool data cika famm tayi saikuma tayi Kwafa tabi bayansu, da tana iya zuciya da tayi tafasa binsu amma tasan ko tayi ita keda asara ba suba


Awaje ta taddasu zee harta shiga bangaren mai zaman banza Aymaan ya maida kofar ya rufe gently

Qara kumbura fuska tayi sannan tazo sumi sumi ta bude back seat ta shiga

Ta6e baki Aymaan yayi shima ya zagaya mazaunin driver ya shiga ya tada motar sannan suka fice daga gidan.


Tafiya suke babu mai cewa komai a motan daman batool itace aku mai bakin magana cikinsu to yau kuma fushi akeyi shiyasa Aymaan ya kunna wani disc na waqar maheer zain jin yadda motar ta dauki shiru.


Basu jima ba suka iso wani babban pack

Tun daga waje zaka gane pack din ya hadu kuma bana qanannun mutane bane.

Parking space Aymaan ya nufa ya nemar ma motarshi Wurin parking ya pakata sannan duk suka firfito


Sosai zee taji farinciki ya lullu6eta don ko ba'a fadaba tasan pack din ya hadu.


Wajen siyan tickets suka nufa ya siya masu sannan suka wuce ciki

Saida suka babbada tickets din sannan suka wuce ciki.


Sosai farinciki yasake lullu6e zee don suna shiga taji Wurin yayi bala'in yimata

Har mammaki take na yadda Aymaan yasan wuraren shaqatawa masu qayatarwa irin haka.

Batool dake fushi tuni itama ta warsaqe suka shiga yawonsu.


Sosai sukayi enjoying lokacinsu don sun yayyawata sosai don pack din babba ne yana Hade da zoo da restaurant ma, ga beach daga can qarshen Wurin.


Saida suka sha yawo suka gaji sannan suka samu wuri kusada beach din suka zauna shikuma Aymaan yawuce don samarmasu ice cream da sukace suna so.


Labari zee da batool suka cigaba dayi cikin nishadi suna kallon ruwan gabansu suna jiran dawowarshi

Dan shiru zee tayi kamar mai tunani

Ganin Hakan yasa batool cewa
"ya dai?"

"wlh dazu dazamu shigo daidai wajen wasan yarannan naga ana siyarda burger, ina son burger sosai wlh, kallo daya nayimata ta biya raina don rabona daita tun a Nigeria"


"shine kuma bakiyi magana ba muka tsaya muka siya?"

Dan yatsina fuska tayi
"banson tsaidamu ne amma bari kigani kafin yadawo zanje nasiyomana" tafada tana yunqurin tashi

"A'a kibari yadawo saiki fadamashi saiya siyamana" inji batool

Harararta zee tayi tace
"tunda gashi bawa ko? Nidai natafi I'll be back in a jiffy" tafada tana wucewa

"ok saikin dawo" batool ta amsa sannan ta maida hankalinta kan ruwan gabanta ta cigaba da kallo.


Dakyar zee ta iya gano inda taga burger dazu saboda girman wajen donma tana bin signboard suna nuna mata hanya


Burger manya biyar tasa akayi mata wrapping sannan taciro kudi tabiya aka bata


Chanjinta aka bata ta amsa tajuyo tana zura kudin a cikin purse dinta

Batayi auneba taji tayi qaro da abu wanda Hakan yasa ledar burger dinta faduwa

"ya sallam!" tafada ahankali tana kallon burger dasuka watse a qasa

Juyawa tayi ta kalli mutumin da sukayi karo dashi wanda yaqara gaba kamar ba mutum ya buge ba.

Ganin yayi nisa yasa ta buga Tsaki cikin jin haushi ta duqa tafara tattara burgern ta


Cak ta tsaya da tsintar datakeyi lokacin da wani abu yayi crossing qwalwarta


Ahankali ta tariyo abinda yafaru yanzu a kwalwarta.

Koda sukaci karo ta dan kalli fuskarshi sama sama kafin ta maida a kan burgern ta dake watse a qasa

Wani irin bugu zuciyarta tayi

Zumbur ta miqe tsaye tayi saurin Juyawa Saidai babu shi babu alamunshi.


Cikin fitan hayyaci ta shiga ratsa mutane da gudu gudu sauri sauri tana waiwaigawa don ganin ta inda zataga koda wulginshi ne

Saidai babu shi babu 6il6ishinshi.

Haka ta cigaba da ratsa mutane wasu ma bangajesu takeyi bata saniba, zagi kau tashashi Saidai a banza don batasan sunayi ba, Kunnuwanta sun dode, idanunta sun rufe, hankalinta yayi qololuwar tashi, babu abinda take gani a idanunta sai fuskarshi... ✍️


Ummin fasihu 🧚🏻‍♀�
8/2/21, 9:39 PM - Buhainat😝: *🙍🏻‍♂️DEEN 🙍🏻‍♂�*


*057*


*DEEN 😱*


Tun daga nesa Aymaan ya hangi batool ita kadai zaune inda yabarsu.

Qarasawa yayi cikin zuciyarshi yana wondering ina Zainab


"hey" yafada yana zama gefenta

Juyowa batool tayi ta kalleshi sai tayi murmushi

"laa harka dawo?"


"eh, ina Zainab din kuma?"

"wlh wai burger takeso tagani a playground din yara dazu dazamu shigo shine taje saye"


"Amma meyasa bata gayaminba? Da nataho mata dashi ai"

Daga kafadu batool tayi alamun oho?

Shima dan daga kafadun yayi sannan ya miqa n
Mata nata robar ice cream din shima ya bude nashi suka shiga sha suna fira jefi jefi.


Sun kusan minti ashirin ahakan amma har lokacin babu alamun dawowarta

"wai tun yaushe ta tafi ne? Shirun yafara yawa ga ice cream dinta yafara narkewa" inji Aymaan


"wlh Akhie nima naji Shirun Yayi yawa, tun fa baka dade da tafiya ba ta tafi"

"kema meyasa zaki barta ta tafi ita kadai? Ita da ba yar gari ba? Maimakon kisa ta jirani indawo in saimata kokuma kuje tare"

"wlh nace mata tabari kadawo ka siyamata amma ta qiya tace ai kafin ka dawoma zata dawo"


Shiru Aymaan yayi sai kuma ya miqe tsaye

"bari naje naduba"


Itama batool miqewa tayi
"nima zan bika"


Be amsa mata ba yayi gaba itama ta ta take mashi baya


Wajen playground din yaran suka fara zuwa Saidai ko mai kama da ita basu gani ba hakan yasa suka nufi wajen balaraben dake siyar da burger din

Cikin harshen larabci Aymaan ya gaida mutumin sannan ya tambayeshi wata tazo nan siyan burger yanzu?


Cewa yayi ai masu sayen dayawa bazai iya riqe wadanda suka zo ba

Kwatancen zee din Aymaan yashiga yima mutumin da kayan dake jikinta nan take mutumin ya gane ta

Yace eh tazo ta siya amma fa Tundazu, tana kuma siya ta tafi.


Godiya Aymaan yayi mashi sannan yace ma batool su koma inda suka fito qila sa6a hanya sukayi


Saidai ko da suka koma still batanan.


Wasa wasa tun suna nemanta batareda sun kawo komai aransu ba har hankalinsu yafara tashi don babu inda basu zagaya ba a fadin pack din amma ko me kama daita Basu ganiba.


Hankalinsu ne ya tashi suna tsoron kar ace 6acewa tayi

Nanfa Aymaan ya rufe batool da fada yana cewa duk laifinta ne data barta ta tafi ita kadai yanzu ga irinta nan


Itadai batool batada ta cewa, fatan ta dai kawai aganta din.


Dole sukaje wajen securities din wajen sukayi masu magana

Jin Hakan yasa suma suka gayawa manajojin wajen nan take aka ce a aika su Aymaan din can wajensu.


Tareda jagorancin wasu securities din biyu suka tafi can babban ofishin masu managing wajen.


Shiga dasu akayi recording room kamar yadda suka saba idan wani ya 6ace a wajen nan aka shiga tambayarsu tun yaushe ta tafi


Batool ce ta fada masu lokacin dakuma inda taje

Nan take aka Maida cctv din wajen playground din zuwa daidai lokacin da batool ta bada


Tsayawa dik sukayi suna kallon masu shige da ficen wajen ta cikin majigin ga mai burgern nan shima yanata harkar gabanshi


Can kawai sukaga shigowar zee wajen

"yauwa gatanan, wannan ce" inji Aymaan yana nuna masu zee data nufi mai burger din


Duk nutsuwa suka sakeyi suna kallon yadda take magana da mai burgern da lokacin daya samata a leda yabata da lokacin data Fiddo kudi tabashi yabata chanji


Sai tajuyo tana saka kudin a purse, kawai sukaga tayi kan wani dake tahowa sukayi karo ledar hannunta ta watse a qasa.

Mutumin be tsaya ba ya cigaba da tafiyarshi sai sukaga ta bi mutumin da kallo sai kuma ta duqa tafara tsintar burger dinta dasuka watse qasa


Sai sukaga ta tsaya Cak da abinda takeyi kamar an tsaida ta da remote Saikuma tayi saurin miqewa tana waige waige.


Can tabar wajen da sauri tanata ratsa mutane har tabar playground din.


Hankalin su Aymaan yasake tashi

Shugaban Wurin yaba mai operating din computer umarnin duk ya maido daukar koina na pack din zuwa daidai lokacin da zee tafita daga playground din


Haka kau yayi ya maido daukar daidai lokacin yayi playing record din


Duk nutsuwa sukayi suna baza idanu a kashi kashin recording din dake gaban majigin

"gatacan!" inji Aymaan yana nuna zee datayi hanyar fita

Zooming Wurin akayi akaga har lokacin tafiya takeyi tana waige waige harta fita daga gate.

Shiru sukayi duk kansu akulle, can kuma sukaga tasake Shigowa pack din wannan karon ta nufi zoo.


Zooming din mai dauka zoo sukayi sukaga nan ma neme neme take tana magana kamar ma bata a hayyacinta

Can kuma ta dauki hanyar restaurant nan ma taci nemanta sannan ta dawo ainahin playground din ta cigaba da tafiya tana waige waige kamar marar hankali.


Shiru duk sukayi suna kallonta ta majigin duk inda tashiga sai ayi Zooming wajen har akazo daidai wannan lokacin sukaga ta zauna kan wata kujerar yara mai zagaye ta kife kanta bisa qarfen kujerar

"gatanan, muje kai kuma ka cigaba da monitoring dinta data tashi ka sanar dani" Managern ya gayama mai operating din computer

Da Managern da Aymaan da batool suka fito suka nufi inda suka ganta ta cikin majigin cikin sauri


Cikin lokaci qanqani suka isa wajen kuma suka hango ta tun daga nesa a position dasuka ganta a majigin kanta Hade da qarfen kujerar haryanzu


Saurin ida qarasawa wajenta sukayi


Batool ce ta zauna kusada ita tareda dafata Hakan yasata saurin dagowa


Yadda batool taga idanunta sunyi jajur yasa gabanta faduwa

"meya faru ukhtie? Menene?"


Shiru tayi batace komai ba Saima kafeta da jajjayen idanunta datayi


"talk to me sister, what happened?" taqara fada Saidai nan ma shiru

Hakan yasa shima Aymaan matsowa kusa

"Zee, meya faru? Meyasa kike kuka?"

Wasu hawayen ne suka qara gangaro mata

Sosai Hakan yaqara tada hankalinsu Hakan yasa batool riqo hannunta gam cikin nata tana cewa "Kiyi magana don Allah zee, what happened?"


Saurin fadawa jikin batool din tayi ta rungumeta gamm tana kuka sosai


Sosai Hakan yasake hargiza tunaninsu Hakan yasa nan da nan itama batool tafara hawaye

"sister.. Don Allah ki fadamin" inji batool cikin muryar kuka itama


"na ganshi batool, naganshi.. Wlh"


Dagota batool tayi daga jikinta tana kallonta

"kinga wa?"


"DEEN dina, na ganshi da idanuna wlh.. A playgroud, wlh shine.. Deen dina"

Cikin mammaki Aymaan da batool suka hada baki Suna cewa
"Deen?"


Cikin sauri zee da duk jikinta ke rawa ta kadamasu kai sannan tace
"eh.. Eh wlh, naganshi. Naga Deen dina.. A playground, ya bangajeni.. Ya zubarmin da burger yatafi, nasan be ganni bane, bega fuskata ba, be ganeni ba Amma ni na ganshi, naganshi wlh. My Deen is back batool I can't believe it" tafada cikin kuka sosai

Rungumota batool tayi ganin yadda jikinta ke rawa kamar mazari itama tana hawaye

"waye Deen batool?" inji Aymaan da duk yakasa gane kan maganarta


Share hawayenta batool tayi still zee na jikinta tana shesheka


"her boyfriend" inji batool ahankali


Wani abu Aymaan yaji ya soki zuciyarshi nan take

"boyfriend?" injishi yana kallon batool cikin wani yanayi

Kada kai tayi tace
"wannan wanda ya tafi ya barta"

Maida kallonshi yayi akan zee dake shesheka haryanzu kanta kife a jikin batool

"but Zainab ba yana Nigeria ba?"

Dagowa tayi ta kalleshi wasu hawayen na sake gangaromata
"na ganshi, dazu.. Da idanuna"


Hadiye abinda ya tsaya mashi a wuya yayi cikin tausasa Murya yace
"Zainab, calm down please.. Wataqila wani kika gani kikayi mistaken dinshi dashi, wataqila ko yanayi yayi dashi amma ai wancan Nigeria yake kuma he's gone, mezai kawoshi nan?"


"bansaniba, bansan abinda ya kawoshi nan ba, all I know is shine"


"to idan shine ina yake? Wataqila gizo yayi maki"


"ba gizo yayi min ba Aymaan, na ganshi da idanuna, I took a glimpse of him and before I could turn back again to confirm he's gone"

"that's means definitely gizon yayi miki, kince kafin ki sake juyowa he's gone, bakya ganin dama babu shi din kawai imagination din idanunki ne? Idan shine zaki ganshi immediately you turned back, Koda ba a kusa ba zaki hangeshi"

"meyasa zaimin gizo yanzu? Meyasa tun baya be yimin gizo din ba sai yanzu? Am telling you shi nagani, shi nagani, you guys have to believe me, nasan shi, bazan iya mistaken dinshi da wani ba, nasanshi fiyeda shi kanshi, why zaku maidani mahaukaciya" ta qarashe cikin dan daga murya


Ajiyar zuciya Aymaan yayi yace
"shikenan, yanzu ya kike son ayi?"

"mu nemeshi please, tayiwu ni yake nema shima, tayiwu yaje gidane akace na dawo nan shiyasa shima ya biyo ni, please ku tayani nemanshi" tafada tana Hade hannuwa cikin kuka


Sosai zuciyar Aymaan ke zafi, who on earth is this guy? Is he this heartless? Ji yadda ya maida yar mutane zarrariyar qarfi da yaji.

Maida lower lip dinshi yayi ciki ya cije yana imagining haduwarsu da gayen and how he'll make him pay for all he did

Kallon zee yasake yi yana jin kukan nata har cikin zuciyarshi

"muje" yafada yana kallonta

Dagowa tayi saurin yi ta kalleshi

"Akhie, kaima ka yarda shi din tagani?" inji batool


Kauda kai yayi
"idan muka duba din zamuyi comfirming ko shi dinne ko bashi ba" yafada yana miqewa tsaye

Gabadaya mood dinshi ya chanza, gabadaya wannan al'amarin yayi ruining day dinshi


Itama zee tashi tayi cikin sauri tana share hawayenta

"inane kika ganshi?" inji Aymaan trying so hard to control himself


"A playground wajen mai burger" tafada cikin sauri

"ok muje" yafada saikuma ya juya wajen mutanen dasuka taho dasu nemanta wadanda duk basu fahimci me suke cewa ba kasancewar hausa sukeyi


Abinda ya faru ya gayamasu briefly sannan yayi musu Godiya yace karsu damu zasuyi handling din kingin

Da haka suka rabu Aymaan yayima zee nuni da hanya ta shiga gaba don kaisu inda taganshi din


Playground din suka sake komawa ta gwada masu inda sukaci karo din sannan ta nuna masu hanyar dayabi ya tafi, sai suka bi hanyar suma suka shiga nemanshi


Babu inda basu shiga ba a park din ba, Saida suka duba every nook and cranny din park din, wani Wurin ba basusan dashi ba Amma ko mai kama dashi basu gani ba


Saidai dukda Hakan zee bata haqura ba sai qara jansu take suna komawa wuraren dasuka wuto don sake dubawa.


Sosai Batool ta gaji da yawon Saidai taga su ko ajikinsu, ga Aymaan daya biyemata duk inda tayi Binta yake batareda nuna any single sign na gajiya ba

Hakan yasa itama daurewa kawai ta cigaba da binsu amma harga allah ta gaji sosai da yawon


Haka sukaita zagaye park din har zee din ta gaji don kanta ta haqura ta zame ta zauna bisa grass carpet din wajen ta Hade kai da gwiwa

Hawaye ta cigaba dayi tana sobbing ahankali tana jin raunin zuciyarta daya fara qamewa tadawo sabo kamar yanzu tajishi


Kallonta Aymaan da batool suka tsaya yi Babu mai cewa komai sai ma tausayinta daya qara samun muhalli a zuqatansu.


Ahankali Aymaan ya duqa gabanta ya tsaya yana kallonta kawai

Lumshe idanu yayi ya bude, shi kadai yasan abinda yakeji a zuciyarshi

"Zainab.." ya kira sunanta gently

Bata amsa ba kuma bata dago ba

"kibar kukan nan haka Zainab,please.

Wanda kike zubdama hawayen nan be cancancesu ba"


Dagowa tayi fuska sha6e2 da hawaye ta kalleshi tace
"ban damu da ya cancancesu ko be cancancesu ba, abinda nasani shine na cancanci in zubdasu akan abubbuwan dake faruwa dani"


"Zainab hawaye bazasuyi miki maganin komai ba, da sunayi da sunyimiki tuntuni, abinda zaifi miki shine haquri, Kiyi hqr kikuma rungumi qaddararki, and pray hard to move on, but not wasting your tears ga wanda beyi worthing dinsu ba" yafada zuciyarshi na zafi sosai


"Tears are not a sign of weakness Aymaan, but of courage. Hiding your emotions is self destructive and will never allow you to heal"


"No guy is worth your tears Zainab and when you find one that is, he won’t make you cry" inji Aymaan cikin qunar zuciya


Banza kawai tayi dashi ta kyaleshi don bazai ta6a ganewa ba.

Yanzu idan akwai abinda tafi buqata shine kukan, shine kawai zai sata jin sauqin abinda takeji.

A yan kwanakinnan tayi tunanin she has moved on, tayi tunanin tariga ta maida past dinta behind her ta cigaba

Amma ganin Deen yau ya maido ta at the very beginning, yajawota zuwa level 0 datayi tunanin tuni ta wuce wajen.


Shiru wajen ya dauka na wani lokaci sannan batool ta qaraso itama wajensu ta tsugunna ta kalli zee da haryanzu kanta ke kife da gwiwa saikuma ta maido kallonta ga Aymaan dake kallon zee din shima

Dafa kafadarta batool tayi tace
"it ok sister, Kiyi hqr ki tashi mutafi kinga dare nayi, idan ma shine zaku qara haduwa insha allah, idan allah ya qaddara zaki sake ganinshi zaki ganshi, put that faith in your mind, let's go home."


💙💙💙💙💙💙💙💙💙💙


Haka sukayi tafiyar komawa gida silently, motar tayi shiru kowanne da abinda ke kai kawo a ranshi, sai gashi suda suka fita outing don samun nishadi sun dawo rai a dagule.


Koda sukayi parking zee ce farkon fita daga motar ta nufi cikin gida.


Duk binta sukayi da kallo harta shige.


Ajiyar zuciya batool ta sauke sannan itama ta sauka zata wuce Aymaan ya dakatar daita da

"karki sake ki tadomata maganar, just behave kamar babu abinda yafaru, ok?"


Kada mashi kai kawai tayi sannan ta wuce


Binta itama yayi da kallo harta shige sannan ya maida kanshi a kujera ya lumshe idanu.


Ya jima ahakan sannan ya fito ba don ya shirya ba sai don kiraye kirayen sallar magrib da aka fara


Haka suka qarasa ranar ransu a jagule musanmman zee da Aymaan


Ko wajen dinner Aymaan na lure da zee kuma kallo daya yayimata ya gane tayi kuka ba Dan kadan ba hakan yasashi jin ranshi ya ida dagulewa, idan ya tuna cewa yanzu haka wanda yasakata a wannan halin yana can hankalinshi a Kwance sai yaji ranshi ya qara 6aci, sai yaji inama zai ganshi face-to-face da saiya tabbatar ya hadamashi jini da majina, saiya mashi illan da bazai qara moruwa ba


Batool kau kamar yadda Aymaan ya fada mata haka tayi, kwata2 nunawa tayima kamar ta mance da abinda yafaru, haka taita harkokinta tana kuma sako zee data koma kamar ba ita ba Cikin shirmenta


Da daddare kasa barcin kirki zee tayi, banda juyi babu abinda takeyi, daga baya dataga barcin ya gagara saita miqe taje tayi alwalla tafara nafilfillu

Ta dade tana addu'a akan idan har dagaske Deen ne tagani a pack yau allah yasake bayyana mata shi, idan kuma ba shi bane allah ya sassauta mata abinda takeji a zuciyarta


Sai can cikin dare tasamu barcin ya sadado yayi awon gaba daita.


*WASHEGARI*


Yau asabar kuma weekend so yau ranar hutu ce ga mutane da dama musanmman ma'aikata

Ciki harda Aymaan da dama ranakkun weekend ne kawai yake samun hutawa sosai.


Koda ya sauko yin breakfast qasa sai ya tarar su harsunyi abinsu sun koma sama, Hakan yasa ya zauna shikadai yayi serving kanshi yafara ci


_Deen dina_
Maganar zee ta jiya ta fado mashi a rai a karo na ba adadi


Ya rasa dalilin dayasa yakasa cire wannan kalmar a ranshi kuma duk lokacin daya tunata sai yaji kamar ana gasa mashi zuciya


Jiya shima beyi isashen barci ba, da tunanin abinda yafaru ya kwana, he can't believe duk abinda gayen nan yayima zee zata iya koda yimashi kallon tsiya ne bare na arziqi

A tunaninshi koda tururuwa akayi tayi ana Shigowa ana cewa tafito gashi can waje ko kallo masu kiran bazasu isheta ba, a tunaninshi ta tsaneshi tsanar da bata misaltuwa amma sai yaga sa6anin Hakan

Daga yimata gizo ta gigice ta rikice, wannan da dagaske ne fa to?

Dama haka soyayya take? Mutum yayi maka laifi, ya cuceka amma ka kasa haqura dashi, ka kasa zuciya dashi, dama haka soyayya take koko tata ce Hakan?


Da wannan tunane tunanen yagama cin abincin sannan yakoma sama yashige dakinshi yasake kwanciya ya qure a.c ya kwanta rigingine ya lumshe idanunshi abubbuwa dadama na kaikawo a qwalwarshi


Besan sadda barci ya daukeshi ba sai jiyayi ana bubbuga kofarshi cikin barci


Juyi yayi zuwa dayan gefen gadon yana qara tattare jikinshi wuri guda saboda sanyin a.c din dakin daya fara mashi yawa


Jiyayi an cigaba da bubbuga dakin, wannan karon da dan qarfi


Duk yadda yaso ignoring bubbugawar kasawa yayi don bugun kofar akeyi non-stop Hakan yasashi tashi Dakyar ya miqe zaune.


Agogon bangon dakin ya duba yaga 1 saura


Tsaki yaja yana jin wani irin haushi ya mammaye zuciyarshi


Jin an sake bubbuga kofar yasa ya tashi a fusace ya nufi kofar

Murda handle din yayi ya bude kofar da qarfi wanda Hakan yasata dan ja baya a tsorace


Ganinta yasa nan take expression din dake fuskarshi na fushi yayi saurin chanzawa yafara murmushin yaqe

"ukhtie? Kece ashe?" yafada yana fadada murmushinshi

Sauke idanuwanta tayi qasa kawai tayi sakamakon arba datayi da broad chest dinshi da packs dinshi ta cikin singlet dinshi don dama daga shi sai dogon wando sai singlet

"erm.. You need something?"


Girgiza kai tayi ahankali batareda ta dago ta kalleshi ba


Ganin uneasiness dinta yasashi gane abinda yasata yin Hakan sai yace
"ok, you want to talk to me right? Ina zuwa, just a minute" da haka saiya koma ciki


Ko seconds talatin beyi ba yasake bude kofar wannan karon sanye da jallabiya ash ta maza

Fitowa yayi daga dakin ya jingina da kofar sannan ya kalleta yana murmushi

"ya yau?"

Still bata dago ta kalleshi ba tace
"alhamdullilah"


Shiru yadan ratsa wajen, jin Hakan yasata dagowa sai taga shima ita yake kallo sai tayi saurin sauke idanunta qasa


"tell me, menene?" yafada tenderly

Sake dagowa tayi ta kalleshi sai kuma ta saukar da kanta qasa ahankali kamar mai ciwon baki tace

"park din da mukaje jiya"

Dan shiru Aymaan yayi saikuma yace
"yes? What about that?"


"sunanshi.. Nakeson ka gayamin" tafada still idanunta a qasa


Tsayawa yayi yana kallonta for some moments


Jin shiru yasa ta qara Dagowa ta kalleshi da shining eyes dinta dake glittering saboda dan ruwan daya taru aciki

"please" tafada ahankali tana kallonshi


"meyasa kike son sanin sunan?" inji Aymaan still yana kallonta kamar mai son karantar wani abu a fuskarta

"babu, just tell me"


"zan gayamiki amma saikin fadamin dalili" yafada still idanunshi akanta

"please.." tafada ahankali sai kuma ta sauke idanunta wanda yayi daidai da digar hawayenta qasa


Cigaba da kallonta yakeyi yana jin zuciyarshi kamar ana melting dinta


"ki fadamin me zakiyi da sunan and I'll tell you" yasake fada

"babu ruwanka, just tell me" tafada cikin cracking voice, a inda yake tsaye yana hango diddigar hawayenta

"da ruwana saboda ke sister ta ce, idan batool ce tazo ta tambayeni itama haka zan cemata, ke da batool daya ne a wajena"


Ba don bata iya zuciya ba da babu abinda zai qara tsaidata a gabanshi, Hakan yasata cewa
"inason.. Naje ne"


"Wani abu kikeso? Ki fadamin koma menene zanje nasiyo miki" inji Aymaan din


"babu abinda zan siyo, nidai ka fadamin.. Don Allah" Sai kuma ta rufe fuskarta da taffukan hannayenta ta shiga sobbing ahankali


Lumshe idanu Aymaan yayi cikin quncin zuciya sannan yasake budesu suna kadawa ya kalleta dasu

"Me zakiyi acan?" yasake tambaya Muryarshi na chanzawa


Cikin kuka zee tafara magana
"I know I may sound ridiculous ko ayimin kallon mahaukaciya, I don’t care.

Zuwa zanyi nemanshi, bazan iya jure abinda zuciyata keyimin ba, I can't


Zuciyata na gayamin yana can, yana nemana, Inason inqi zuwa amma bazan iya ba, bazan iya cigaba da jure azabar datake minba, nayi qoqarin jurewa daga jiya zuwa yau but not anymore.

Ka fadamin sunan wajen, ko cab ne sai yayi dropping dina

Idan kuma bazaka fadamin ba zan tafi, zan tafi naita nema harna gane"


Tunda tafara maganar Aymaan ke kallonta batareda yayi qoqarin katse mata hanzari ba har Saida takai aya.


Dan murmushi yayi wannan yafi kama da mai ciwo sannan yace
"to meye na kukan? Why the tears? Da Alamu dai beneath that eyes akwai qoramun ruwa shiyasa abu kadan sai sharr hawaye.

Meye aciki to? Ni bakiyi sounding ridiculous to me ba, thats what your heart wants and so be it.

Jeki shirya na kaiki"


Dagowa tayi ta kalleshi da wet eyes dinta

Kada mata kai yayi
"yes, ki shirya zan kaiki basai kin hau cab ba"

Girgiza kai tayi tace
"A'a nidai kawai ka fadamin sunan, thats all"

Shima girgiza kai yayi yace
"naqi din, go and dress up bari nima na shirya saimu tafi"


Be bata damar qara magana ba ya bude kofar dakin nashi ya shige ya rufo


Bïñ kofar tayi da kallo sai kuma ta share hawayenta ta juya ta koma daki tana jiran fitowarshi don ita dama a shirye take.


Kujerar dake facing din gadonshi ya samu ya zauna akai tareda dafe goshinshi


Shi kadai yasan abinda yakeji a zuciyarshi, musaltashi kuma 6ata lokaci ne don bazai misaltu ba


Ya kusan Mintuna goma ahakan sannan ya miqe ya zare jallabiyar jikinshi sannan ya nufi toilet.


Zaune take kan stool din gaban mirror tana daga kai tana kallon agogon dakin akai akai


Tunda tashigo ko gefen batool bata sake kallo ba don haryanzu haushinta takeji na qin gayamata sunan Wurin datayi wanda Hakan ma yasa taje tasamu Aymaan din


Itakau batool bata damu ba sai cigaba da harkan gabanta da itama tayi batareda ta kulata ba.


Suna Hakan zee tajiyo budewar kofar dakin Aymaan

Jitayi kamar ta miqe ta fita amma tasamu ta danyi controlling kanta kadan ta cigaba da jira


Kwankwasa kofa yayi Hakan yasa tayi zumbur ta miqe tsaye ta nufi kofar

Dakatar da abinda takeyi batool tayi tana kallon kofar don ganin wa ke bubbuga kofar


Bude kofar zee tayi sai sai idanunta sukaci karo da Aymaan da ya chanza shiga zuwa manyan kaya irin namu na hausawa farare sunyi bala'in amsarshi


Murmushi yayi mata
"sorry na tsaidaki ko?"

Batace komai ba sai sauke kai qasa datayi

"oya muje" yafada yana kaucemata a hanya

Dama abinda takeson ji kenan Hakan yasa ta ida fitowa tafara tafiya shikuma ya biyo bayanta

"Akhie!!" muryar batool ta tsaidasu dga tafiyar dasuka fara

Juyowa sukayi suna kallonta Yayinda itakuma ta qaraso bakin kofa tana ma Aymaan kallon mammaki

"Akhie, badai wajen nan zaku ba?" ta tambaya a mammakince

"eh can ne ko kinada saqo?" inji Aymaan

"but Akhie.."


"baki dashi kenan, sai mun dawo" yayi gaba abunshi


Zee ta sauke sigh of relieve sannan itama ta bi bayanshi batareda tabi takan batool dake binsu da kallo cikeda mammaki ba


A parking space ta tarar dashi harya budemata Front seat kamar yadda yasaba

Zuwa tayi ta shiga sannan ya maida kofar ya rufe ahankali sannan ya zagaya yashige shima ya rufo kofar sannan ya tada motar yayi reverse sukazo suka fice daga gidan.


Tafiya suke silently babu mai cewa komai acikinsu har suka qarasa park din jiya.


Fitowa sukayi gabadaya suka rurrufe kofar sannan suka fara tafiya, Aymaan a gaba zee a bayanshi


Saida suka fara sayen ticket sannan suka shiga ciki


Kamar dai jiya yau ma wajen acike yake da mutane sunata kai kawo

Zee ce agaba yanzu Aymaan a bayanta suka shiga bin ko ina suna dubawa kamar dai jiya.

Duk namijin da zasu hadu dashi sai zee ta kalli fuskarshi Koda baya ya juyamata saita san yadda zata shawo gabanshi taga fuskarshi

Haka sukaita zagayen park din kamar dai jiya


Gajiya iya gajiya sunyi amma Aymaan ko kadan be nuna ba Binta kawai yakeyi yadda takeso


Saida taji daga kafa na neman gagararta sannan ta nemi wani kujerar swing ta zauna yana sauke numfashi ahankali

Cikin kulawa Aymaan ya dan duqo yana kallonta

"Are you ok?" yafada ahankali

Kada mashi kai tayi sai kuma ta share hawayen daya sulalo mata
"don Allah mu jirashi, nasan qila bekai da zuwa bane, Inaji ajikina zaizo don Allah mu zauna mu jirashi, kaji Yaya Aymaan?"


Murmushi ya su6uce mashi, wai yaya Aymaan, dama yaushe tafara kiranshi yaya?


"haba karki damu sister, mu jirashi din nima Inaji ajikina zaizo, no p kinji?" yafada still yana murmushi

Dadi taji ya kamata, dama haka gayen nan keda sauqin kai?


Shima zama yayi a kujerar dake kusada ita yayi folding hannu a qirjinshi yana kallon masu kai kawo kamar yadda takeyi itama


This is crazy! Anya kau wannan yarinyar soyayya bata haukatata ba?

Tayaya zata sa su tsaya jiran gawon shanu? Mutumin da batada ma tabbacin ta ganshi din

Amma dayake Aymaan mutum ne matuqar haquri da kuma saukin kai plus yadda yake jinta a zuciyarshi sosai yasa yaqi nuna komai suka cigaba da jira.


Wasa wasa sune har bayan asr zaune suna jira sallah kawai ke tadasu, a inda suke suna iya hango gate so duk masu shige da fice a kan idonsu


Dukda Aymaan be duba wayarshi ba yasan akwai tarin missed calls dayawa dama Saida ya maidata silent tun a gida don kar kira yayi distracting dinshi

Ya riga yasa a ranshi yadda ita tasa suka zo nan to komawar ma saita nemi sukoma din zasu koma don shi mutum ne me bama mutum damar gano bullewar hanyar daya dauko da kansa kamar yadda yanzu yake son tagano haukanta da kanta


Maida kanta tayi kan gwiyagunta jin anfara kiraye kirayen sallar magrib

Sosai zuciyarta ke mata suya kamar ana soyata a tafasashen mai

Ta dan jima ahakan sannan ta dago batareda ta kalli Aymaan ba tace
"mutafi"


Yi yayi kamar bejita ba hakan yasata qara cewa
"ka maidani gida"


Sai a lokacin ya dago ya kalleta
"tun yanzu?" yafada yana kallonta


Miqewa tsaye tayi ahankali tana Rataya jakkarta

"eh mutafi"

"ok, mufara sallah tukkuna" yafada yana miqewa tsaye shima


Saida suka wuce masjid akayi sallar dasu sannan suka fito daga wajen suka hau mota suka kama hanyar gida.


Kamar yadda suka zo yanzu ma silently suka koma babu mai cewa komai kowa da abinda yake sakawa a zuciyarshi


Yana iya ganin yadda take dauke hawayenta akai akai ta gefen idonshi, Ajiyar zuciya ya dan sauke yana dan girgiza kanshi ranshi a mugun jagule.


Koda suka isa gida sai suka tararda su ummy tsaitsaye hankula a tashe


Zee dai tana zuwa tayi sama dagudu cikin kumshe kukan dake neman kufcemata


Hakan yasa suka maida hankalinsu akan Aymaan


Fada sosai suka shiga yimashi akan meyasa zai biyemata sutafi suyi wannan zaman bayan yasan ba lallai bane ace da gaske shi din tagani ba, mezai kawoshi dubai mutumin dake Nigeria


Beyi mammakin yadda akayi suka san da zancen ba don yasan batool ce zata gayamasu Hakan yasa yayi shiru suka qaraci fadansu suka gama ya basu haquri sannan ya wuce sama yashige dakinshi shima.


A ranar babu wanda yafito dinner da zee da Aymaan din


Kowannensu is in a very sad mood Saidai za'a iya cewa na Aymaan yafi don zee ita ke wahalar amma yafita jin zafin abin, jiyake kamar yayi me don takaici.


Ranar dai da daddare barci Saidai sukayi rabi da rabi shima marar dadi


Washegari ma haka suka tashi so moody don dukkansu ransu a cinkushe yake musanmman zee, shi Aymaan ma yana gama abinda zaiyi a gidan ya fice ya wuce gidansu abokinshi Ahmad Junaid


A bangaren zee kuma haka ta wuni cikin rashin walwala, duk yadda batool taso sata feeling better Saidai ta haqura ta kyaleta itama.


Ahankali Zainab takoma gidan jiya, always moody, magana inba takama dole ba batayi, Dariya kuma rabonta dayi tun ranar kafin abin yafaru


Sosai wannan chanjin ya damu su ummy dasuka fara murnar warwarewarta da farko.


Wani sa'in haka zasu zaunar daita suyita yimata nasiha da rarrashinta amma a banza, kwata2 takasa komawa normal self dinta kuma


Aymaan kau shima yana cikin damuwa tunda abin yafaru musanmman daya lura da halin datake aciki yanzu amma dayake gwanin iya 6oye damuwa ne babu wanda yasan abinda yake ciki don Kodayaushe idan ka kalli fuskarnan zaka ganta da qayattacen murmushi akai.


*AFTER TWO WEEKS*


Haryanzu zee bata ida komawa daidai ba Saidai tarage moodiness dinta sosai

Yanzu takan zauna ayi fira daita amma ba mai tsayi ba don haryanzu bata ida healing daga famin datayi ba na raunin zuciyarta


Yau saturday, babu aiki don haka a gida Aymaan ya wuni


Batool bata gida taje ganin wata classmate dinta da batada lafiya

Babu yadda batayi da zee akan ta rakata ba taqiya dole ta tafi ita kadai.

Suna zaune falo da ummy da zee suna dan fira Aymaan ya sauko daga sama cikin shirin shi na fita


Qarasowa yayi falon cikin fara'arshi ya zauna suka dan qara labarin dashi sannan ya miqe yana cewa ummy zaije wajen aikin Abbu amso saqo, shi ya kirashi yaje


Adawo lfy ummy tayimashi itakuma zee takama kallonshi kamar tace zata bishi don itama zaman gidan yafara isarta don jitake wama yace taqi bin batool

Ganin kallon datake mashi yasashi yimata tayin ko zata rakashi?

Da sauri ta Kada kai kamar dama jira take sai kuma ta kalli ummy ta sadda kai


Murmushi ummy tayi tace to ta tashi su shirya sutafi ko babu komai taga gari zata kuma ga ma'aikatarsu Abbu.


Cikin zumudi ta tashi ta haye sama don chanzawa suka bita da kallo fuska dauke da murmushi


Cigaba da firarsu su ummy sukayi harta sake saukowa cikin shirin ta.


Ganin Hakan yasa Aymaan tashi daga zaunen dayake sukayi sallama yayi gaba zee tabishi a baya


Motar Aymaan suka shiga shi a mazaunin driver ita a gefen shi suka fice daga gidan.


Ma'aikatar su Abbu din suka shiga, Aymaan yafita yabarta a motar yashige ciki


Be dade ba sai gashi sun fito tareda Abbu

Qarasowa sukayi wajen motar Hakan yasa zee fitowa suka gaisa da abbu yana tsokanarta kamar yadda yasaba.


Saida suka dan jima ahakan sannan sukayi sallama da juna, Abbu yakoma ciki sukuma suka Kamo hanyar dawowa


Tafiya suke cikin shiru babu mai magana sai waqar dake tashi a background din motar ahankali


Can sai Aymaan yadan juyo ya kalleta sai kuma ya maida kallonshi akan titi
"muje shopping?"


Juyowa itama tayi ta kalleshi

Daga mata girarenshi yayi sannan yayi murmushi yana sake maida hankalinshi akan titi

"No" tafada ahankali

"why? Bazamu dade ba ai, kawai zamu siya some stuffs ne saimu juya, ni akwai abubbuwan danake buqata ne nasan kema bazaki rasa ba"


Shiru tayi kawai bata ce komai ba


"I'll take your silent for yes" yafada tareda karya kan motar ya dauki corner da zata kaishi supermarket na kusa kusa.


Parking yayi a parking space din supermarket din sannan ya fito ya zagayo ya bude mata itama ta fito


Rufe motar yayi sannan suka nufi cikin shopping mall din atare.


Zuwa yayi inda ake daukan shopping basket ya dauki biyu ya bata daya shima ya riqe dayan

"zan shiga session din maza, idan kin rigani gamawa ki jirani anan" inji Aymaan


Kada kai tayi kawai Hakan yasashi Juyawa ya wuce ya barta nan


Ta dan jima a tsaye saikuma ta sauke Ajiyar zuciya sannan itama ta wuce session din mata


Yan sayayya tayi wanda bata kai ta kawo ba wanda mostly turarrika ne masu kyau da tsada sai yan kayan maqulashe da ba'a rasaba.


Ta rigashi gamawa shiyasa tazo ta tsaya inda yace din riqe da basket dinta tana jiran shi


Wayarta dake jakkarta ta dauki ruri Hakan yasa ta ajiye basket din agabanta ta bude jakkar ta fiddo wayar


_*sis batool* taga na yawo a screen din.

Dan murmushi tayi sannan ta daga ta kara a kunne


Dagowar da zatayi sai ta sauke idanunta akanshi


Zuciyarta tayi wata muguwar wuntsilawa

Wara manyan idanunta tayi sosai a kanshi kamar zasu fado daga socket dinsu

"hello.. Hello" taji anayi a kunnenta amma ina? Batama san meye kare a kunnen nata ba, hankalinta ya tafi, ya tafi gabadaya

Ahankali ta rintse idanunta ta bude amma still yana nan, tsaye hannunshi daya zube a aljihun wando daya riqe da waya yana daddanata wani na yimashi magana


Kafeshi tayi da idanu kamar wata hallita take gani daban ba mutum ba irin ta


Sanye yake da black american suit idanunshi toshe cikin da baqin shade, lallausar baqar sumarshi s gyare sai salqi take


Ahankali taga yafara motsa bakinshi yana magana still kanshi hankalinshi akan wayar hannunshi saikuma ya dago ya kalli mutumin dake gefenshi yanata Kada kai cikin girmamawa ga dik abinda yace


Wata maganar yasakeyi sannan ya amshi wata takarda a hannun mutumin ya duba ya miqa hannu baya, wani dake bayanshi shima sanye da suit yayi saurin bashi pen

Dan rubutu yayi a takardar mai kama da file sannan ya rufe ya miqama mutumin

Cikin russunawa mutumin ya amsa yanata washe baki yana qara russuna mashi yana magana wanda bazata iya jin abinda yake cewa ba daga inda take


Sai gani tayi ya juya batareda yabi takan mutumin ba ya nufi hanyar waje cikin wani taku


Hakan yasata dawowa firgigit daga duniyar kallonshi data lula

Sakin wayar da haryanzu ke kare a kunnenta tayi batareda ta saniba


"DEEN!!!" tafada da qarfi tana nufar shi da sauri


"Zainab!" inji Aymaan da yakusan qarasowa inda take amma ina bataji ba hartayi gaba


Saurin ida Qarasowa inda ta jefar da wayar yayi ya dauka saikuma shima yayo hanyar waje


Fitowa zee tayi a gigice tafara waige waige cikin fitar hayyaci can ta hangeshi sun nufi wata mota waya kare a kunnenshi


"DEEN!!!" ta qara qwalamashi kira sannan tayi wajen da sauri sauri gudu gudu.


Bude mashi kofar baya akayi still yana making call

Ahankali ya duqa zai shiga yaji an kamo mashi gefen suit dinshi da qarfi


Dakatawa yayi daga yunqurin shigar dayayi batareda ya juyo ba

Itama zee data damqo gefen rigar kallonshi take tana sauke numfashi mai nauyi

Guards din wajen kau shock ya hanasu ta6uka komai sai tsayawa dasukayi suna kallonta baki bude

"Deen??" tafada cikin wata iriyar karyayar murya


Ahankali kamar wanda ake controlling da remote yashiga juyowa harya qarasa juyowa ya fuskanceta


Kallon kallo suka shiga yima juna dukda shi nashi idanun na lullu6e da shade

"Deen.." tasake fada cikin sarqewar murya tana jin numfashinta na qara yimata nauyi... ✍️


Ummin fasihu 🧚🏻‍♀�
8/2/21, 9:40 PM - Buhainat😝: *🙍🏻‍♂️DEEN 🙍🏻‍♂�*


*058*


*WHO IS WHO�*


Ahankali yasa hannu ya cire shade din dake manne da idanunshi, oily eyes dinshi suka bayyana.


Sauke idanunshi yayi kan hannunta dake riqeda gefen suit dinshi haryanzu sannan yasake Dagowa yana Binta da wani irin kallo


Sosai kallon dayake binta dashi ya sake hautsina mata ciki hakan yasa batasan sadda tasaki rigar ba

"Deen? Baka ganeni ba?" tafada tana kallonshi babu kyaftawa


Kafin ya ko motsa Guards dinshi sukayo gaba zasu taso mata


Daga masu hannu yayi, still idanunshi akan zee da itama takasa dauke nata akanshi, ba komai yasa Hakan ba sai irin kallon dayake binta dashi wanda bata ta6a sanin Deen dinta dashi ba

Duk tsayawa sukayi Cak sanadin dakatar dasu da yayi


Ahankali ya shiga zame suit dinshi na sama a qyamace still idanunshi cikin nata, ganin Hakan yasa wani guard dinshi Qarasowa bayanshi yana taimaka mashi har suka sa6ula rigar


Batayi aune ba taji saukar rigar a fuskarta

Wani masculine qamshi dake jikin rigar ya bugi hancinta Hakan yasa ta lumshe idanunta ta bude sannan tasa hannu ta Janye rigar daga fuskarta Ahankali

Gani tayi ya juya yana niyyar shiga motar again Hakan yasa ta cafki hannunshi tana tsaida shi daga yunqurin shiga again


"Deen.." tasake fada muryarta na rawa sosai


Wani qololon abu ya tsaya mashi a wuya.

How dare her! How dare her zata ta6ashi da wannan dirty hannun nata

Juyowa yayi again yana mata kallon da yasata jin kamar ta narke don tsoro amma dukda Hakan taqi Sakin hannun

"Deen? Meyasa kake min wannan kallon? Nice fa, zee.. Your Zainab" tafada cikin rawar murya sosai


Cikin quluwa ya fizge hannunshi daga riqonta wanda Hakan yasa tadanyi loosing balance tayi kamar zata fadi Saidai bata fadin ba


Sudai Guards dinshi nasu ido don tunda ya dakatar dasu dazu idan bashi yabasu umarnin yin wani abu ba bazasu yi gigin yin wani abin ba


Juyawa yasakeyi zai shiga taqara Kamo hannunshi ido rufe

"No Deen, please don't do this, don’t reject me for the second time, I can't take it, i'll die" tafada cikin kuka sosai hankalinta a matuqar tashe


A matuqar fusace ya sake juyowa, beyi wata wata ba ya daga hannu da niyyar shararawa fuskar mari sai yaji an cafe hannun a iska da qarfi


Zee data tamke idanunta gamm tana sauraron saukar marin taji shiru Hakan yasa ta bude idanun ahankali


Aymaan tagani tsaye gefenta riqe da hannun Deen a iska suna bin juna da fierce kallon kallo

Saurin qarasawa wajen Aymaan tayi
"Aymaan ka kyaleshi, Deen ne fa, shine. Please ka sakeshi kar yayi fushi" tafada tana riqo hannun Aymaan daya riqe hannun Deen dashi


Juyowa yayi ya kalleta cikin matuqar quluwa

"zaki saki hannuna kosai na fasamaki baki?!" Yafada cikin qaraji, fuskarshi na bayyana tsantsar 6acin ran dayake ciki


Sosai zee ta girgiza da yanayin Aymaan wanda bata ta6a saninshi dashi ba Amma so ya riga ya rufe mata ido Hakan yasa taqi saki

"naji, ka fasamin kai ma idan ka tashi just leave him, ina ruwanka da rayuwata!!" itama tafada cikin daga murya


Idanunshi dasukayi mugun kadawa ya kafeta dasu saikuma ya saki hannun Deen din ahankali


Ganin Hakan yasata qara saurin nufar Deen din

"Deen am sorry, besan ko waye kai ba, am very sorry" tafada tana niyyar sake kama hannunshi Hakan yasashi Janye hannun sannan ya turata baya a fusace

Baya baya tasakeyi tana gasping don tasan wannan karon dole takai qasa kuma idan takai qasa saitaji jiki


Jitayi an tareta ta baya an tsaidata daga faduwar


A tsorace tasake bude idanun sai tayi arba da fuskar Aymaan dake kallonta da rinnanun idanunshi

Bata iya cewa komai ba sai kallonshi itama datake numfashinta na qara yin nauyi

Miqar da ita yayi tsaye sannan ya saketa yayi wajen Deen dake tsaye fuskarshi tayi jaa don fushi

Guards ne sukayi saurin tareshi suna kakkama hannunshi


Zuciyarshi ce ta qara harzuqa Hakan yasa ya wuntsilar dasu da iya qarfinshi duk suka sakeshi batareda sun shirya ba sukayi baya baya

"you dog!" Yafada yana shaqo kwalar Deen qirjinshi sai sama da qasa yakeyi alamun zuciyar yan mazan ta tashi


Bïñ hannun da Aymaan ya shaqi kwalarshi Deen yayi da kallo suprisingly sannan ya dago yana kallonshi shima jijjiyoyin jikinshi na tashi

Cikin harshen larabci Aymaan yafara magana
"waye kai?! Waye kai da zaka dora hannu akanta?!!"

Afusace Deen yasa hannu ya kwa6ar da hannun Aymaan daga qwalar rigar tashi, kafin Aymaan yayi recovering daga haka yaji saukar naushi a gefen kumatunshi


Qara Zee tasa tana kiran sunan Aymaan

Baya baya Aymaan yayi saikuma ya dakatar da kanshi daga faduwar dayaso yi


Hannu yasa ya taba gefen bakinshi ya duba sai yaga jini

Sake kallon Deen dake huci yayi sai yayi kukan kura ya nufeshi

Saidai tun kafin ya qarasa gunshi guards dinshi suka tareshi, basuyi wata wata ba suka tarar mashi suka shiga jibga.


Qara Zee tasake saki tana rufe baki hankali a mugun tashe, kuka takeyi kamar zata shide jikinta na wani mugun 6ari


Gaskiyar hausawa dasuka ce sarkin yawa yafi sarkin qarfi don tun Aymaan na iya maida martanin har yakoma kare kanshi har daga baya ma yakasa kare kanshi din.


Ganin Hakan yasa zee nufar Deen dake tsaye yana kallonsu ta Kamo hannunshi

"Deen na roqeqa, kace subari zasu kasheshi"


Wani irin fizge hannunshi yayi wanda har Saida takai qasa

Juyawa yayi zai wuce wajen motar shi tayi saurin rarumo qafarshi daya

"Deen! No! Karka tafi zan mutu!" tafada tana rungume qafar da dukkan qarfinta


A matuqar hasale ya fizge kafar itama yana ja baya yana kallonta da bloodshot idanunta sannan yana nuna ta da yatsarshi datake karkarwa saboda yadda jikinshi ke tsuma don 6acin rai


Sai kuma ya juya ya bude kofar baya na motar ya bude wani akwati ido rufe ya fiffido wrappers din kudinsu nacan ya farka wrappers din yashiga watsamata kudadden ajiki, tsayawa tayi Cak da kukan tana kallon yadda yake warwatsa nata kudadden akai, da wani yaqare Sai ya farka wani har Saida ya qarar da wrappers biyar akanta

"Go away, you brat!!" Yafada cikin hargowa sannan ya juya ya shige motar ya rufo da qarfi.


Ganin Hakan yasa guards din kyale Aymaan da suka yima lilis suka rugo wajen mottocin suka shishiga suka tayar suka bar wajen a 360 suna badesu da qura


Ahankali Aymaan ya bude idanunshi dasukayi mashi mugun nauyi yabi motocin dasuka fita a harabar wajen da kallo sannan ya maido kallonshi akan zee dake zaune har lokacin bata ko motsi


Maida idanunshi yayi ya lumshe cikin azaba yana kiran sunan allah under his breath.


Saida yayi yunqurin tashi sau biyu ya kasa, ana uku yasamu ya tashi zaune Dakyar yana cije lip dinshi na qasa


Koina na jikinshi ciwo yakeyi kamar ana dandaqarsu ga bruises a jikinshi sunyi jaa abinka da fatar hutu dama

Ahankali yasake bude ido ya sake kallon zee dake a sitting position dinta har lokacin


Bude bakinshi yayi Dakyar yafara magana
"kin gani.. Ko? Kinga.. Abinda kika jawo ko?"

Shiru

Shaqar numfashi yayi sannan ya fesar yafara yunqurin tashi, sosai jikinshi yayi laqwas don babu qarya ya jibgu don shi tunda yayi wayau bazai iya recalling lokacin da aka ta6a yimashi irin wannan dukan ba


Ganin bazai iya tashin ba yasa ya qara Dagowa ya kalleta yaga still wuri guda take kallo sai jiyayi ranshi ya kuma 6aci

"ki tashi mutafi" yafada yana kallonta but still bata motsa ba

"Zainab! Am talking"

Nanma shiru


Shima shiru yayi ya tsaya yana kallonta yana qoqarin gano wani abu


Abinka da medical doctor nan take ya gano


Wara idanunshi dasuka tattaso yayi sannan yayi saurin rarrafawa gabanta

"Zainab" yakira sunanta yana waving a gaban fuskarta amma bata ko kyafta idoba

"zee?" yafada yana dan ta6ata kawai sai yaga tayi baya baya

Ba don yayi saurin tarota ba da tasha qasa

"Zainab! Zainab!!" Yafada yana jijjigata amma shiru

Tara yatsarshi yayi a hancinta sannan ya dora kunnen shi daidai zuciyarta yana feeling heartbeat dinta


A rikice ya dago ya karkata ya zaro wayar shi dake aljihunshi still tana jikinshi


Lalubo number Ahmad yayi ya danna mashi kira


Saida takusan katsewa sannan aka daga

"hey!" inji Ahmad daga wancan bangaren

"Ahmed kana ina?"

"lafiya?" inji Ahmad jin muryar Aymaan wani iri

"answer the damn question!" inji Aymaan yana qara jijjiga zee dake sheme ajikinshi

"ina gida, meya faru naji voice dinka wani iri?"


"kazo Ni'ima shopping mall, urgently please"

Daga Hakan ya katse kiran ya maida hankalinshi kanta


"Zainab! Zainab!! Wake up zee!" Yafada yana dan marin fuskarta amma shiru


Waige waige yafara, kasancewar babu mutane sosai a wajen ga kuma motoci dayawa dasuka kakkaresu shiyasa tunma lokacin dasu Deen ke nan ba'a gansu ba.


Ahankali ya maida ta ya kwantar daita sannan ya tashi Dakyar yafara dangyasawa ya fito fili


Waige waige yafara can ya hangi securities, daya na bude gate daya na a zaune

Da dingishi ya qarasa wajensu, tun daga nesa dasuka hangoshi suka fara kallonshi harya qaraso gabansu Dakyar


I.D card dinshi yafara nunamasu, Ganin ko waye yasasu saurin tashi suna tambayarshi lfy suka ganshi haka

Briefly yayi musu bayanin he's attacked By some thugs shi da sister shi dake can unconscious sannan ya gayamasu abinda yake buqata don yimata taimakon gaggawa.


Cikin sa'a aka samu most abubbuwan daya lissafo suka koma wajen zee dake sheme har lokacin

Dukda yadda yakejin kamar kanshi zai rabe gida biyu don sarawa haka ya daure yafara bata taimakon gaggawa


Suna haka Ahmad ya iso supermarket din.


Kasancewar Aymaan dama yariga ya fadamasu wani nanan tafe wajensu yasa yana isowa aka rakoshi wajensu


Sosai hankalin Ahmad ya tashi ganin halin dayaga Aymaan dama zee dake unconscious har lokacin


Cikin qarfin hali Aymaan yace ma Ahmad ya kaisu hospital


Da taimakon Ahmad aka saka zee back seat sannan sukuma suka dawo gaban seat, Ahmad ya tada motar yayi reverse suka fice daga supermarket din.


Asibitin da Aymaan ke aiki suka zarce.

Tun kafin su iso Aymaan ya bugama wani colleague dinshi waya ya sanar dashi Zuwansu shiyasa Koda suka isa akayi saurin kar6ar zee aka shige daita


Da farko Aymaan qin yarda yayi ayi treating ciwukkanshi har Saida ya tabbatar da sun ceto rayuwar Zainab from danger sannan Dakyar su Ahmad suka samu suka lalla6ashi ya yarda.


***


Kwance yake bayan angama treating dinshi idanunshi a lumshe kamar mai barci amma ba barcin ba yake


Shi kadai ne dakin don tunda nurse tagama treating dinshi suka fita suka bashi wuri don ya huta sosai


Qarar bude kofa yaji amma Hakan besa ya bude lumssasun idanunshi ba

"bismillah ummy" yaji Ahmad na cewa Hakan, Hakan yasashi bude idanun babu shiri ya juyo yana kallon saitin kofar


Ummy yagani agaba sai batool a bayanta sai Abbu a bayansu


Yunqurin tashi zaune yafara sai ummy tayi saurin Qarasowa tana taimaka mashi ya ida tashi zaune ta karamashi pillow a baya

Dagowa yayi yana kallonsu sai yaga suma shi suke kallo cikin tausayawa

"sannu Akhie" inji batool kamar zatayi kuka


Dan murmushi yayi mata sannan ya kalli su ummy

"ummy, waya gayamaku?"

"Ahmad ne habiby, muna can hankalinmu Kwance ashe babu lafiya"


Dagowa yayi ya watsama Ahmad mugun kallo shikuma yayi murmushi yana daga kafadarshi


"sannu son, allah ya kyauta gaba amma nayi mammaki ace thugs a supermarket, how come?"

Shiru Aymaan yadanyi sai kuma ya sauke Ajiyar zuciya


"Abbu nidai bansan ya Hakan yafaru ba, kawai nagama siyayya ta nafuto saina hangeta inda nace ta jirani

Amma kafin na qaraso sai naji qarar faduwar abu daga hannunta sai kuma naga tayi wajensu dagudu

Na kwalamata kira amma bata saurareni ba shiyasa nima na qaraso wajen da sauri sai naga ashe wayarta ce ta saki


Saina dauketa na tashi nabita lokacin harta fita waje

Nima saina bita Saidai Koda nafita ban ganta ba don har titi saina nakai amma banga wulginta ba


Dawowa nasake yi da niyyar komawa ciki again sainaji kamar magana a ta parking space din wajen

Saina zagaya, kawai saina hangeta daidai wani ya tureta

I thought faduwa zatayi amma sainaga bata fadi ba, sai nayi saurin nufar wajen

Ina qarasawa wajen ya daga hannu zai mareta saina dakatar dashi..."


Duk tsit mutanen dakin sukayi ya cigaba da basu labarin har kawo yanzu dasuke asibitin nan


Duk salati suka shiga yi cikin tsantsar mammaki da alhini

"innallilahi waina ilaihi rajiun, to shi mutumin waye? Kawai daga ganin mutum sai tace shine Deen? Haka fa tayi muku a park rannan ko?"

Ajiyar zuciya kawai Aymaan ya sauke don shi kadai yasan abinda yakeji a zuciyarshi


"to Gaskiya ya kamata nakira yaya na fadamashi, idan aka tafi Hakan akwai matsala, ace duk wanda tagani tace Deen ne, idan ta qara gamuwa da muggai kamar na yau fa babu wani dazai iya taimakonta a kusa fa?"


"A'a, be kamata a kirasu ba, hankalinsu ne zai tashi sosai, kawai mu nemo mafita da kanmu" inji Abbu


"nima Gaskiya am scared Abbu, gwara asan yadda za'ayi don nima abubbuwan datake yi sunfara bani tsoro, haka fa rannan ta dage akan ita dole shi tagani tasamu mukaita zagaye a banza" inji batool


"kai, amma dai yaron nan ya cuceta wlh, cutar da dole sai allah ya sakamata, daga wannan sai wannan? Sai abu yayi kamar yafara warwarewa sai kuma yaqara ta6ar6arewa, kullum abu beci baya sai gaba?" inji ummy hawaye na taruwa a idanunta

"Addu'a yakamata mu dinga tayata dashi Abbu, allah ya kawo mata rangwame a halin datake ciki" inji Ahmad da Tundazu bece komai ba

Kada kai kawai duk sukayi cikin amincewa da Maganarshi

Shidai Aymaan bece komai ba sai kafe waje guda dayayi da ido kawai, allah kadai yasan meke kai kawo a qwalwarshi


Ranar aka sallamesu suka koma gida


Zee ta farfado and she's ok physically amma karka bincika zuciyarta


Zuciyar tata data samu ta lilliqeta da gum tun bayan rarratsata da Deen yayi tasake Fashewa, fasuwar da mawuyacine taqara iya yimata paci kamar yadda tayimata da farko


Tun daga ranar ta chanza, chanzawar da tafi duk na baya


Bata cin abinci sai an tsareta an tilasta mata to anan zataci kadan

Kuma ko zaka yini kanta kana magana bazata cemaka komai ba har ka gaji don kanka ka kyaleta


Daga baya kuma saita fara zazza6i, irin zazza6innan mai zafi sosai


Dr Aymaan ne kullum mai treating dinta, yana iya qoqarin shi na ganin ya bata dukkanin kulawar datake buqata amma a banza, kullum cikin ciwo take ga wani bushewa datakeyi a tsaye


Sosai wannan ahalin suka sake shiga damuwa mai tsanani


Suna son su sanar dasu daddy na Nigeria amma Aymaan ya hana yana cewa it's not proper gwara suyi iya qoqarinsu akanta basai sun sanar dasu halin da ake ciki ba.


Haka Aymaan dama sauran ahalin gidan sukaita iya bakin kokarinsu akanta


Duk safiya bayan sallar asuba zasu shigo dakinsu zee din su zauna tilawar alqur'ani kowa da nashi a hannu itama a bata nata tana dubawa while su suna karantawa


Sosai Hakan yayi tasiri sosai akanta don duk lokacin da suke wannan karatun takan tsinci kanta cikin nutsuwa, zuciyarta ta ragemata zugin data keyi


Da rana kau wuni suke garden da batool wanda zataita iya qoqarinta wajen sanyata nishadi


Da daddare kuma Aymaan zaizo ya fara karanta mata littatafai masu dadi masu sanya nishadi


Haka sukaita iyakar bakin qoqarinsu akanta suna kuma hada mata da addu'a don tabbas lamarinnan sai an hada da addu'a


Wata rana jikinta yasake tashi, zazza6i mai mugun zafi ya rufe ta.


Ranar kowa na gidan beyi barcin kirki ba Haka suka tare wajenta Aymaan na iya bakin qoqarinshi akanta a matsayinshi na qwararren likita


Dakyar suka samu jikin ya lafa tasamu barci drip maqale da hannunta


Su ummy da batool sai dauke hawaye sukeyi akai akai shikuma Aymaan idanunshi sun Kada sosai, jiyake da shima zai iya kuka da yayi mata


Haka yafita dakin ya barta dasu ummy da anan zasu kwana wajenta


A ranar besamu rintsawa ba, haka ya zauna ya kafe waje guda da ido


Tunanuka kala2 ke kai kawo akanshi

Ko yatafi Nigeria neman Deen?

Ko yaje a chanza mashi fuska irinta Deen?

Me zaiyi? Me zaiyi dazai dauke ma zee abinda takeji?


Shi da yasan yadda zai dauke mata abinda takeji a zuciya shiya dinga ji da yayi Hakan, daya jure kowanne irin wahalar da zaisha muddin zai dauke mata wahalar


Yadda yaga rana haka yaga dare, asuba nayi ya miqe ya fice massalaci


Koda ya dawo dakinsu yafara shiga ya tarar da har lokacin barci take


Sake dubata yayi sannan ya cire mata qarin ruwan don yaqare sannan yafita


A gaggauce yayi shirin asibiti ya fita don dama kwana biyu be cika zaman asibitin ba saboda tattara hankalinshi dayayi akan zee

Yauma wani emergency aka kawo wanda lallai ana buqatarshi a aikin shiyasa ya shirya a gaggauce yayi sallama da mutanen gidan yatafi


Bashi ya fito daga asibitin ba sai wajajen 3pm Hakan yasa ya wuce gida kawai don duk hankalinshi yayi gida kuma yanason yaje yaga wane hali zee din ke ciki


Koda ya shigo gidan parking space yashiga yayi parking sannan ya fito

Kamar kullum yau ma lapcoat dinshi riqe take a hannunshi ya fito ya rufe qofar sannan ya fito daga parking space din


Hangen batool yayi ta fito daga garden tayi hanyar cikin gida batareda ta lura dashi ba

Ganin Hakan ya tabbatar mashi cewa zee tana garden din itama don Mafi yawancin lokaci irin wannan can suke zama don sudan debe kewa.


Hakan yasa ya chanza akalar tafiyar tashi zuwa garden din don dama babu wanda yakeson gani kamar ita yanzu


Cikin takunshi ta nutsuwa ya taka zuwa garden din


Tun daga nesa ya hangota zaune bisa wata yar doguwar kujerar garden din ta juya mashi baya so be ganin fuskarta itama kuma batasan da shigowarshi ba garden din


Wasu yan moli moli take kallo dake tsaye a kan wani reshen bishiya suna dan tsuwarsu suna ra6ar juna

_*look*_
Ta tuna abinda Deen yace wancan ranar da suka gansu a school

_*A Good example of us, ko?*_


Lumshe idanu tayi akansu ta bude sannan ahankali tafara waqa


_the word around town.._

_is that you're back in town_

_and I tried not to think about you_

_I tried_


_but it's been so long.._

_and I thought I moved on.._

_but now I really doubt it_

_I do_


_I wonder why you even come_

_it's almost like you're having fun with me_

_and though if I set my eyes on you, it's on avoidable_

_how come oh boy?_

_I thought you've gone for good_


_so how do you!.._


_have to pull me back!"


_I thought you said, you won't be coming back_


_then why did you?!_

_this is really bad!_


_I thought you said you're gone for Good_


Dakatawa Aymaan yayi daga tafiyar dayakeyi yana kallonta cikin wani irin yanayi

_what you did is wrong_

_cos you know all along am doing ok without you_

_you don't want me to.._

_try to move on.. Try oh_

_the heart is too strong_

_can't be with you and can't be without you_


_the truth is that I.._

_wonder why you even come_


_is almost that you're having fun with me_


_and though if I set my eyes on you, it's unavoidable_


_how come oh boy?_


_I thought you've gone for good_


_so why did you?!_


_have to pull me back?!_


_I thought you said, you won't be coming back_


_then why did you?_

_this is really bad!_


_I thought you said you're gone for Good_


Ahankali yafara takawa da baya baya still idanunshi akanta making sure be ankarar daita dashi ba


Saida yayi nisa sannan ya juya yayi saurin barin garden din


Saboda rufewar idanunshi baya ma ganin gabanshi clearly wanda Hakan yasa yaci karo da batool a bakin kofar shiga falo

Daga mata hannu kawai yayi ya wuce don ga yadda yakeji dinnan yasan ko yayi maganar bazata fito ba


Binshi da kallon mammaki batool tayi, kamar ta bishi sai kuma tafasa don wataqila 6ata mashi rai akayi kuma tasanshi idan yana cikin 6acin rai beson kowa ya ra6eshi, Hakan yasata juyowa kawai ta koma garden din.


A daddafe Aymaan yasamu ya haye saman ya qarasa dakinshi ya bude yashiga ya maido ya rufe


Jingina yayi da kofar ya saki lapcoat din hannunshi qasa yana sauke wani irin numfashi mai nauyi idanunshi a lumshe


Kamar da wasa sai jiyayi wani abu na silalowa daga idanunshi zuwa kan kumatunshi

Ahankali ya bude idanunshi sannan ya kai hannu ya dangwalo ya duba


Hawaye?


Kuka yake?


Sake maida idanun yayi ya lumshe wasu nasake gangarowa.

Jingina kanshi yayi da kofar yana maida lower lip dinshi aciki ya datse da haqora


Besan iya lokacin daya dauka ba ahakan Saida yagaji da tsayuwar sannan ya dago daga kan kofar ya wuce wajen gadonshi ya zauna gefenshi ya dafe kanshi da hannaye bibbiyu yana kallon qasa


Ya jima ahakan yanata saqa da warwara sannan ya Janye hannayen daga dafe kan dayayi ya karkata ya zaro farin hanki dinshi a aljihunshi na wando yashiga wiping fuskarshi


Qara cije lip dinshi na qasa yayi yana kafe waje guda da idanunshi dasukayi ja sai kuma yasake karkatawa ya ciro wayar shi ya kunna ya lalubo number batool ya bugamata


Ringing biyu aka daga


"Akhie?" yaji tafada a can bangaren


"ki riqe wayarki a hannunki zanyi miki sms, it's privacy"

Be jira cewarta ba ya tsinke kiran


Batool acan gefen jin ya katse mata hanzari ta hanyar kashe wayar ta sauke wayar cikin mammaki tana kallonta, itakau zee hankalinta ma ba kanta yake ba, tayi nisa as usual


Ko minti biyu ba'ayi ba text message yashigo wayar tata


Saurin budewa tayi sai taga yasa

_*kisan yadda zakiyi ki dauki phone din Zainab ki kawomin yanzu, it's urgent*_


Shiru tayi tana qara karanta text din

Me zaiyi da wayar zee kuma?

Dagowa tayi ta kalli zee dake zaune har lokacin ta kafe waje guda da ido batama san me takeyi ba.


Ba'ayi Mintuna uku ba yaji an kwankwasa mashi kofa Hakan yasashi saurin tashi kamar dama kan qaya yake ya nufi kofar


Budewa yayi sai ga batool ta bayyana


"yauwa, bani" yafada yana miqomata hannu

"Akhie? Meya sameka?" tafada tana kallon yadda idanunshi sukayi jajur


Be amsa mata ba sai jan hannunta dayayi suka shiga dakin ya rufo kofa

"the phone" yafada cikin kosawa

Dagota tayi ta gwadamashi


Amsa yayi da sauri ya kunna yayi sliding sai yaga ta bude


Direct contact yashiga yayi searching 'Deen' amma babu result saiya tuna ashe wannan sabon layine ma ashe don dama tunda tazo nan ta chanza layi irin na qasar


Shiru yadanyi kamar mai tunani, Itadai batool Binshi kawai take da idanu


Dagowa yasake yi ya kalleta

"ta ta6a nuna miki hotonshi?"

"wa?"


"wannan mayaudarin" yafada kai tsaye


Tasan wanda yake nufi don haka sai tace
"eh, folder daya gareshi ma sunkutukum"


Miqa mata phone din yayi

"gwadamin shi"


Amsa tayi ta shiga inda tashiga rannan nan da nan ta shiga cikin hotunan

Daya tafara shiga sannan ta miqama Aymaan din dake kallonta hannaye rungume da qirji


Amsa yayi ya juyo wayar sannan ya sauke idanunshi akan photon


Idanunshi ne suka fara warawa akan hoton yana kallonshi a mammakince


Ganin yana kallon hoton hankali a tashe yasa itama batool tazama so curious

"Akhie, menene?"


Dagowa yayi ya kalleta
"Are you sure wannan gayen ne Deen?" yafada yana qara nunomata hoton

Sake dubawa tayi itama sai ta Kada kai tace
"eh Akhie, kaga nan a library din school dinsu ne.."

Saita wuce ga wani hoton
"wannan kuma ma a school ne.. Wannan kuma a garinsu mamansu zee din lokacin daurin auren nan na sister din mummyn, to shima yaje daurin auren, nan zaune suke dashi ta daukeshi"


Aymaan sai baza idanu yake da kunnuwa yana sauraron batool

Qara kallon hoton yake, ba fuskar kowa yake gani ba sai fuskar wannan gayen na supermarket


Kenan ba haukan zee bane? Kenan dagaske wannan gayen Deen ne? Kenan ba gizo fuskarshi yake mata ba kamar yadda suka zata?
Kenan Deen ne wannan gayen da yakusan marin zee?

"unbelievable!!" Yafada in total shock

"yaya wai menene? Ka sanshi ne?" inji confused batool


Dagowa yayi ya kalleta saikuma yasake kallon hoton

"shine" yafada yana kallon smiling face din Deen na cikin wayar


"shine wa?" inji batool cikin rashin fahimta


"shine gayen da muka gani a supermarket" yafada yana kallonta

Wara idanu batool tayi in out most shock

"mene?"

"shine, kenan dagaske shine? Tabbas wannan fuskar ce, bazan ta6a mancewa ba. Kenan dama Deen ne wannan gayen?"


"Are you kidding me Akhie? Kana nufin wannan gayen na cikin wayar nan kuka gani?" tafada zuciyarta na bugu sosai

"shine batool, tabbas shine, ya sallam!" Yafada yana dafe goshi in confusion

To kodai shima yafara zaucewan ne? Kodai shima idanunshi sun fara gayamashi qarya ne kamar dai zee?


"but Akhie meya kawo Deen dubai?" inji batool cikin confusion

Shiru yayi yana kafe hoton da idanu hoping zaiga fuskar ta chanza zuwa wani, hoping idanunshi ne ke mashi qarya


"zanje na gayawa ummy, I can't believe this!" inji batool tayi hanyar waje


Saurin dakatar daita yayi ta hanyar riqo hannunta

Juyowa tayi ta kalleshi

Girgiza mata kai yayi sai kuma ya sauke Ajiyar zuciya

"No, ba yanzu ba. Karki sake ki fadawa kowa, zanyi confirming, kibari mu tabbatar sannan"


Batool bataso Hakan ba Amma ya ta iya


Wayarshi dake kan bedside locker ya dauko yashiga xender ya tura pics din Deen din biyu daga wayar zee din zuwa tashi sannan ya miqama batool din wayar

"jeki, zanyi confirming and also karki bari kowa yaji wannan zancen kinji?"


Kada mashi kai tayi sannan ta fita jiki a sanyaye


Komawa yayi ya zauna yana tunani, be ta6a kawowa ranshi ya bincika ko dagaske wannan gayen Deen ne don shi duk a tunaninshi kawai haukace irin ta soyayya, to amma abin da kulle kai, Tunawa yayi da yadda ya daga hannu zai kifamata mari wanda da badon yayi saurin qarasawa wajen ba da babu abinda zai hanashi marin ta din, Tunawa yayi da kallon kyamar da yake Binta dashi, kamar ma beta6a sanin ta ba a duniyar nan

Abin Tambayar anan shine dama can soyayya sukeyi koko dai ita ke sonshi tana liqemashi don shidai bega alamun so ko sannaya ba a qwayar idon wannan gayen ba

Idan ma shine yaushe yazo dubai?

Yaushe yayi kudi?

Mutumin da ummy tace koko da kosai sukeyi for living, yaushe yayi kudi haka harda bodyguards?


Hannu yasa yana scratching kanshi in confusion, kanshi a mugun kulle


Batool ma dai kasa komawa daidai tayi tunda tafito daga dakin Aymaan

She can't believe Deen din zee ne dagaske suka gani anan

Daba Aymaan yafada ba da ta qaryata, meke faruwa to?


Haka Itama ta qarashe wunin cikin tunanin wannan rudaden al'amarin.


Aymaan da shirinshi yafito sallar isha'i


Saida yafara biyawa dakinsu batool inda ya tadda zee zaune kan sallaya da alamun itama jiran afara kiran isha'i take tayi, batool kuma na linke wasu kayan su data Fiddo

Jin batool na yiwa Aymaan sannu da zuwa yasa zee Dagowa


Tsaye taganshi idanunshi akanta


Sanye yake cikin lallausan milk din yadi mai kyau anyi kayan aikin dark brown

A dan zaman nan datayi dasu ta lura Aymaan masoyin manyan kayane don yana sasu sosai kuma suna mashi kyau sosai suna sake fito da cikar kamalarshi


Sauke idanunta tayi daga kanshi ta maida kan sallayar gabanta

Ahankali ya qaraso wajenta ya tsugunna

"patient" yafada yana kallonta yana murmushi

Dagowa tayi ta kalleshi batareda tace komai ba

"ya jiki?" yafada ahankali

Kadamashi kai kawai tayi ahankali sai ta maida kanta qasa

Binta da kallo ya cigaba dayi yana imagining pain dinta

Na farko wanda take bala'in so ya karya mata zuciya ta hanyar gujemata batareda wani dalili ba

Na biyu ta sake ganinshi amma kuma bata gabanshi sam

Na uku mutanen daya kamata su fuskanceta wanda a wajensu zata dan ji sanyi sanyi suna mata kallon zautatta, basa yarda da duk abinda take cewa sai suyita mata kallon mahaukaciya wacce so ya haukata

How painful is that?

_very painful_


Ajiyar zuciya ya sauke yana maida lower lip dinshi aciki ya danne

Tabbas shikuma yayi alqawarin kawo farinciki a rayuwarta, zai sake maido mata lost murmushinta a fuska, zaiyi koma menene don wanzar da farinciki a rayuwarta, saiya maida mata komai tarihi insha allah


Dagowa yayi ya kalli batool yaga itama shi take kallo

Dan murmushin gefen baki yayi saiya miqe tsaye

"Allah ya sawwaqe, batool make sure tasha magani data ci abinci, zan fita"

"insha allah Akhie allah ya tsare" inji batool

Qara duqawa yayi wajen zee din

"natafi dear" yafada ahankali


Dagowa tayi ta kalleshi jin abinda ya kirata

_Dear?_


Kada mashi kai tayi sannan ta bude baki ahankali tace
"Allah ya kiyaye"

Murmushi yayi mata
"Amin dear" yafada sannan ya miqe tsaye yajuya ya fita


Duk Binshi da kallo sukayi atare harya fice.


Saida yayi sallama da ummy sannan yafice cikin motarshi


Saida ya tsaya yafara yin sallar isha'i sannan ya wuce gidansu Ahmad don dama sunyi waya yace mashi yana gida


Gidansu Ahmad shima babba ne don yafi nasu Aymaan ma don sunfisu kudi dama.


Parking yayi sannan ya fito yana dan wurwura keys dinshi


Saida yafara shiga suka gaisa da maman Ahmad din sannan ya fito yawuce part din Ahmad din don dama shi part dinshi daban a gidan


Cikin fara'a suka gaisa

"Dr! Dr!! Ganinka yanzu sai an cika form" inji Ahmad cikin tsokana


Harararshi Aymaan yayi ya wuce wajen dan fridge din dakin ya bude ya ciro ruwan faro yakoma ya zauna yana cewa
"lallai ma, har business man nada bakin yima doctor gori?"

"ai wlh gwara mu daku, kufa har tsakar dare aiki kuke idan ta kama, mu fa?"

"muma ai sai ta kama, kuma ai ba kodayaushe bane"

"dukda Hakan dai kunfimu, haka matarka zataita fama, nidai batool dina ta huta don tun 6 na marece idan nadawo na rufe fita Saidai ko qila fita sallah"

Pillon kujerar kusadashi Aymaan ya jefeshi dashi yana cewa
"ko kunyata bakaji?"


Karewa Ahmad yayi yana Dariya

Kwafa kawai yayi ya chanza cigaba da shan ruwan hannunshi

Saida yagama ya ajiye sannan yakoma jikin kujera yayi balancing


"ya? Miye labari?" inji Ahmad dake qoqarin kunna t.v


Dan shiru Aymaan yayi sai kuma ya dan karkata ya ciro Wayarshi ya shiga gallery yashiga hotunan Deen daya tura dazu saiya miqa mashi


Amsa Ahmad yayi ya koma ya zauna ya kalla


Wara idanu yaga yayi yana kallon hoton

"ya dai?" inji Aymaan
Kallonshi Ahmad yayi
"dama gayen nan yasan kalmar murmushi? Unbelievable"


Cikin rashin fahimta Aymaan yace
"ban gane ba"

"A'a mammaki nake kawai, ban ta6a sanin gayen nan yasan yadda ake murmushi ba, amma kalli nan ma Dariya yake, ina kasamu pics dinnan?"

Cikin mammaki Aymaan yace
"ka sanshi ne?"


Wani kallon uku saura kwabo Ahmad yayi mashi
"mene? Are you kidding me? Waye besan gayen nan ba? Kaima kasanshi Saidai ko kaqi saninshi a fuska amma ina ne sunanshi beyi trending ba?"


Kan Aymaan yasake kullewa
"waye shi din?"


Gyara zama Ahmad yayi
"kasan *NURUL HAQQ PLAZA*, *NURUL HAQQ PARK*, *NURUL HAQQ INVESTMENT*, *GIDAJEN MAN NURUL HAQQ*, *MAKARANTUN NURUL HAQQ* da asibitoci?"


Kada kai Aymaan yayi don babu mahalukin dazai ce be sansu ba duk fadin Abu dhabi kai dubai din ma gabadaya, ko yaro ka tambaya yasani.


Nuna Deen din cikin waya Ahmad yayi yace
"to kaga mai su nan"


Wani irin zaro idanu Aymaan yayi
"what!!" Yafada shocked


"Ca6! Wlh shine, idan kaji ana cewa _*MUSADDIQ AL-HASSAN*_ to wannan gayen ne"

Qara zabura Aymaan yayi
"what!!! Wannan din?!"


Dariya Ahmad yayi ganin yadda ya rude yace
"dole kayi mammaki ai, shi mutum ne da bakowa yasanshi ba saboda bai cika bayyana kanshi ba sai ire irenmu business man.

Kana ganinshi haka business tycoon ne, qwaro a harkar business

Sau daya na ta6a ganinshi face - face shima ranar Saida na raina kaina

Ya wuce duk tunaninka wannan gayen, baya Dariya ko kadan, ni namayi mammakin ganin Dariyar shi anan don wlh cewa akeyi baya ko murmushi ashe yana yi mune bamu saniba"


Zufa ne sosai ke keto ma Aymaan a goshi ya kafe Ahmad da kallo yanata zuba kamar kanya


Saida yakai aya sannan yace
"yanzu kana nufin park din NURUL HAQQ na wannan gayen ne?"


"sosai ma, kaga duk zurfinshi da fadinshi dinnan shine mammalakinshi, Ca6! Multi-billionaire nefa wannan gayen, ya wuce duk tunaninka"


Shiru Aymaan yayi yana kallonshi in shock

Kenan park din dasuka je na wannan ne? Park din da zee tace taga Deen?


Waye wannan gayen? Waye shi?

Ahmad da duk be lura da halin da Aymaan ya shiga ba yace
"amma kai ina kasamu pics dinnan, wlh sunyi kyau, dole natura na gwadama colleague dina nace masu to _*MUSADDIQ AL-HASSAN*_ dai na murmushi harda Dariya ma" yafada yana jawo Wayarshi zai tura


"a wayar zee na tura" inji Aymaan yana kallonshi


"really? Yo ita dataxo daga baya baya ina tasamu irin wannan pics din nashi?" inji Ahmad cikin mammaki

"ita ta daukeshi" inji Aymaan

Wani irin waro idanu Ahmad yayi
"mene? Ita ta daukeshi? A ina?"

"A Nigeria"

Sake qwalalo idanu yayi
"Nigeria?"

"eh.. Wannan shine Deen dinta, her boyfriend"


Wani irin zabura Ahmad yayi ya miqe tsaye
"what!!"


Shima Aymaan tashi tsayen yayi
"yes, boyfriend dinta ne, wanda ya tafi ya barta a can Nigeria"

"what!!!" Ahmad yasake fada in outmost shock... ✍️


Ummin fasihu 🧚🏻‍♀�
8/2/21, 9:40 PM - Buhainat😝: *🙍🏻‍♂️DEEN 🙍🏻‍♂�*


*059*


*WHO IS WHO � 2*


"I don’t get you" inji Ahmad yana kallon Aymaan unbelievably


Ajiyar zuciya Aymaan shima ya sauke yakoma ya zauna yana cewa
"nima am confused wlh"


Dawowa Ahmad yayi ya zauna kusada shi yace
"ina kasamu pics din?"

"a wayar ta"


"kuma saita cemaka shine Deen din?"


"yes, batool ta gwadamawa itakuma ta gwadamin"


"this is crazy! Yaushe sir Musaddiq yazama Deen?" inji Ahmad a mammakince


Shiru Aymaan yayi duk kanshi ya kulle

"idan da cewa kayi ta ganshi a Nigeria zan yarda don business babu inda bekai mutum amma batun shine Deen kwata2 qarya ce, babu yadda za'ayi Musaddiq yazama Deen"

"kuma fa ummy cewa tayi koko da qosai sukayi for living a can Nigeria"


Wara idanu Ahmad yayi sai kuma ya fashe da Dariya

"kutt! Wlh you're very funny" yafada yana Dariya sosai don shi kawai hango sir Musaddiq yayi yana dama koko

"mtcheew, kaifa wani sa'in banza ne, what's funny here?" inji Aymaan a qule


"meye ma ba funny ba, sir Musaddiq dayin koko da qosai for living, hhhh idan ka bibiya ma besan meye kokon ba, kuma ya kamata kubar yarda da duk abinda yarinyar nan tace, she's heartbroken, tana iya ganin fuskar saurayin nata a fuskar kowa ma, ba Haka tayi ba a supermarket rannan? Tajamaka dukan tsiya"


Cikin quluwa Aymaan yace
"ai yanzu ma ba ita na tambaya ba, prove ne nagani a wayarta kuma gayen dakake cewa mun Hade a supermarket din ai shi dinne"

"shi wa?"


"na cikin wayar hannunka" ya amsa mashi kai tsaye

"ban gane ba" inji Ahmad yana kallon Aymaan babu kyaftawa

"mtcheew! Kar allah yasa ka gane mana, ai abinda yasa na yarda da zancen Zainab din kenan don the same guy na cikin wayar hannunka muka hadu dashi a supermarket din, Saidai abinda yafi kulle kai shine wannan da alamu he's rich don harda wasu kartin bodyguards"


Qara qwalalo idanu Ahmad yayi
"kana nufin dashi kukayi wannan fadan?"


"yes?" yafada yana eyeing dinshi

"Omg! Badai da sir Musaddiq kukayi fada ba" yafada in shock


"look I don’t care koma sir wanene, all I knew shine yayi crossing limit dina kuma ni bana barin Hakan"


Sakin baki Ahmad yayi ya cigaba da kallonshi in shock

"wai meye Haka?"inji Aymaan da yaga kallon yayi yawa

"you're unbelievable" inji Ahmad

"so?" inji Aymaan yana daga kafadarshi in an I don’t care manner


"wlh kabar daukar abin wasa, Musaddiq ya wuce duk tunaninka, I wonder ma yadda ya kyaleka a ranar be kulleka ba"


Wani mugun kallo Aymaan ya antaya mashi
"ya kulle wa? Ai wargi ma wuri gareshi, shi kanshi yasan ba sa'ar yina bane shi, nafi qarfinshi wlh"


Ahmad tsayawa yayi yana kallon Aymaan cikin mammaki
"Aymaan you're crazy, very crazy! Kai ban ta6a ganin crazy being ba irinka"


"Sai yanzu kasani? Look let's drop that man's topic don tun gani na farko da nayi mashi naji na tsaneshi, let's get back to business" inji Aymaan wanda kallo daya zakayi mashi kagane he mean what he's saying


Ajiyar zuciya Ahmad ya sauke yace
"alright, ina jinka"

Ajiyar zuciya Aymaan ya sauke
"Deen.. Huhh! Inaji ana cewa sai mutum na zaman zamanshi cikin kwanciyar hankali.. boom!! sai problem din wani yataso yayi maka kane kane a rayuwa

Da farko ban yarda da Hakan ba sai yanzu, yanzu banida wata matsalar data wuce ta zee, I don’t know but na tsani ganinta a yanayin datake aciki, na tsani gani pain a idanunta, ina kwadayin ganin farincikinta, ina kwadayin ganin fara'arta, I want her to live freely and happily kamar kowa amma Hakan ya gagara, kuma babu mai mata katanga da Hakan sai wannan gayen"


Ajiyar zuciya Ahmad yayi yana qara kallon hoton Deen na cikin wayar

"yanzu me kake so?" inji Ahmad

"nima ban sani ba, bansan me zanyi ba, bansan ta yadda zan 6illowa komai ba, shiyasa nazo gurinka don neman shawara, gashi komai na neman qara cha6ewa"


Qara kallon hoton Ahmad yayi sai yace
"Allah mai iko, wallahil azeem haryanzu nakasa yarda wannan musaddiq bane, this is so confusing"


"nima abin ya mugun dauremin kai, don wanda muka hadu dashi supermarket din is freaking rich, kaga kayan jikinshi? Kaga motocinshi? Lokacin datace shine Deen I thought she's out of her sense sai yau danaga pics dinnan sannan"


"kai Aymaan, anya ba editing pics dinnan akayi ba, saifa kaga musaddiq din kodayake ka ganshi ai, ni sai naga akwai inda akasamu mistake"

Amsar wayar Aymaan yayi ya qurawa pics din idanu shima

"Ahmad this is real, duba kagani, dukda a pics ne kana ganin surrounding dinnan kasan ba qasarnan bace, bayan haka dubi kayan jikinshi, very cheap clothes, this is real"

Shiru confused Ahmad yayi
"to idan wannan ba musaddiq bane wanene? Meye alaqarshi da musaddiq har yayi mugun kama dashi?"

"abinda yafi daure kai kenan Ahmad"


Shiru Ahmad yayi kamar mai nazari can kuma yace
"shi wannan waye iyayenshi?"


"nima bansaniba, abu daya nasani shine talakawane kuma Nigerians ne, that's all"


Shiru Ahmad ya sakeyi yana kallon pics din Deen daya kasa dauke idanunshi akai

Yace
"Gaskiya akwai rudani a wannan al'amarin, Indai dagaske mutanen nan biyu ne to akwai wani qullalen al'amari a tsakaninsu, haba kammanin yayi yawa, dole akwai wani abin da bamu sani ba"


"nima haka nake tunani Ahmad, abin da matuqar kulle kai"


Shiru yasake ratsa dakin kafin Ahmad ya dafa kafadar Aymaan

"you know what? Abinda ya kamata muyi anan shine kowannensu mu binciko asalinsu da komai gameda rayuwarsu sai muyi comparing dinsu mugani"


Kada kai Aymaan yayi
"perfect, nima ina ganin Hakan zaifi"


"yes, yanzu kai kaje kasamu zee din ta gayamaka komai gameda shi wannan din, nikuma zan samo mana komai gameda mussadiq"


"perfect! Insha allah Hakan za'ayi, zan qoqarta nasamu dukkan bayaninshi a wajenta"


Haka suka cigaba da shawarwarunsu har Saida Aymaan yaga dare nasonyi sosai sannan ya tashi suka fito sukayi sallama akan sai sun hadu, sannan yabar gidan


Da wannan firar tasu Aymaan ya kwana a rai


Haka maganar nan taita cinshi a rai a kingin kwanakin dasuka biyo baya, kodayaushe cikin son tunkarar zee da maganar yake amma be samun damar Hakan

Ana haka har watarana yasamu opportunity din ganawar daita lokacin ya sauko qasa ne daga stairs ya taddata ita kadai zaune a dining


Cikin jindadin Hakan ya tunkari dining room din yana jujjuya maganar dazai mata din.


"aslm alaiki ya ukhtie" yafada yana jan kujera ya zauna


Dagowa tayi daga abincin gabanta sai tadanyi yaqe

"wlsm" tafada a taqaice


"Me akeci ne babu ko tayi?" yafada yana dan leqa plate din


Murmushi tasakeyi sannan ta tura mashi plate din tana cewa
"bismillah"


Turo mata plate din yayi shima yana cewa
"alhamdullilah, am joking, kici ki qoshi ko kin qara qiba don naga Alamu batool wani Gani gani take mana kwanan nan, baki ga shiyasa nima na dage da cin abinci ba? Wannan yarinyar idan ta rainaka ka banu gwara kema ki dau mataki tun wuri"


Murmushi tasakeyi kawai tana jinjina barkwanci irin na wannan ahalin, kusan dik haka suke, zaiyi wuya ka xauna dasu basu saka Dariya ba


Shima dadi yaji, Ganin irin wannan murmushin a fuskarta ba qaramin sanyashi nishadi yake ba


Cigaba da cin abincinta tayi slowly tana jin idanunshi akanta, bata dago ba Bata kuma nuna tasan yana yi ba har Saida tadan qaraci da dan yawa sannan ta tura plate din gefe ta dauki cup din ruwa tadanyi sipping ruwan sannan ta ajiye


Dagowa tayi ta kamashi yana kallonta kamar yadda tayi zato

Daga mata girarenshi yayi dan murmushi a lip dinshi


Kauda kai tayi itama tana dan murmushi sannan taja kujerar ta baya tana niyyar tashi

"badai har kin qoshi ba?"

Kada mashi kai tayi tana ida tashi

"erm.. Please sit, magana zamuyi.. Idan babu damuwa" yafada yana kallonta


Dan Jimm tayi saikuma ta koma ta zauna tayi still tana saurarenshi


Furzar da iska yayi ahankali daga bakinshi sannan ya gyara zamanshi looking very serious

"Deen..."


Dagowa tayi tana kallonshi yanayinta na chanzawa

"I want to know everything about him" yafada yana kafeta da idanu kamar yadda itama ta kafeshi da nata

Qara jan kujerarta tayi baya ta miqe tsaye Hakan yasa shima ya miqe

"please Zainab, ki tsaya muyi wannan maganar tanada matuqar muhinmmanci"

"agareka ba? Ni aguna batada, please spare me" tafada tana niyyar tafiya

"Zainab Hakan nada matuqar muhinmmanci, shi zaisa abubbuwa da dama su warware mana, ciki harda asalin Deen"


"ni nasan waye shi don haka bana buqatar sanin komai gameda shi again, for me Deen is as Good as dead" tafada cikin qunar zuciya


"why? Meyasa zaki yanke wannan hukunci"


"I don’t own anyone any explanation, banason labarinshi, kai ko sunanshi banason naji an ambata, labarinshi dana sani dinma da nasan yadda zan goge shi a qwalwata da tuni nayi Hakan" tafara yunqurin barin wurin


"Koda kuwa ace bashi kika ganiba a supermarket?" maganar Aymaan ta dakatar da ita


Dan murmushin takaici tayi sannan ta juyo ta kalleshi

"dama ai ku baku ta6a yarda shi nake gani ba, kallon zauttaciya kuke min"


Ahankali Aymaan ya tako har yazo gabanta

"eh ada kallon zauttaciya nake maki, mai ganin fuskar saurayinta a fuskar kowa amma yanzu na fahimta, tabbas Deen ne kika gani, a park da supermarket Saidai bashi bane, kammaninsu ne daya amma bashi bane"


Kallon rashin fahimta tayimashi
"ban gane ba"


"meyasa baki tambayi kanki tayaya Deen yazo dubai ba? Tayaya yazama mai kudi a lokaci guda? Baki lura da motarshi ba? Harda bodyguards? Tayaya yazama haka a lokaci daya?"


Shiru tayi kawai tana kallonshi don ya soso mata inda ke mata kaikayi ne, wadannan Tambayoyin dasu take kwana take tashi a ranta.


"wannan ba Deen bane, sunanshi MUSADDIQ AL HASSAN"


"MUSADDIQ AL HASSAN?" inji zee cikin rashin fahimta

Kada kai Aymaan yayi
"yes, mu zauna na fadamaki komai" yafada yana nuna mata kujera


Kamar bazata yi yadda yace din ba, saikuma ta tafi tajawo kujerar ta zauna tareda sunkuyar da kai abin tausayi


Shima komawa yayi yaja kujerar daya zauna akai dazu ya zauna

"Zainab, Deen qaddararki ne.."

"nasani, mummunar qaddarata, am cursing the day I met him" ta katse shi da Hakan cikin muryar kuka


Ajiyar zuciya Aymaan ya sauke cikin quncin rai shima yace
"shiyasa nayi qoqarin taimaka miki da abinda zan iya don replacing Koda ba duka ba na farinciki dakika rasa a dalilinshi, nasan bazaki ta6a mantawa dashi ba so no need of making you forget him shiyasa nayi tunanin gano waye wannan Deen din dakuma nemoshi duk inda yake dukda ni kaina bansan abinda zanyi mashi ba ko abinda zai yimun.


Sai nasa batool ta satomin wayarki don samun wani hint ko kadan ne akanshi Saidai Koda na duba babu number wayar shi a wayarki saima na tuna bada layin Nigeria kike amfani ba don haka saina chanza akalar binciken nawa zuwa ga Hotuna sai naji inason sanin kammanin wannan mutumin da sunanshi kawai nakeji har lokacin

Abin mammaki da girgizarwa shine lokacin da nayi arba da fuskar mutumin da muka Hade a supermarket

Honestly kafin lokacin kallon zauttaciya kawai nake miki ganin a park kin nuna kinga Deen a supermarket ma daga ganin mutum kince shine, ko ba niba ko wani ne haka zaiyi tunani don kowa yasan wanda ake magana akai a Nigeria yake, yaushe yazo dubai kuma karki manta duk bamusan kammaninshi ba"


"Amma ganin wannan na cikin wayarki yasa kaina ya kulle, nace muddin wannan shine Deen to shine muka gani a supermarket

Hakan yasa kaina yasake kullewa, meya kawo Deen dubai?

Ganin kwalwata nason bursting saboda tunani saina yanke shawarar samun aboki kuma aminina da muka saba zama mu warware matsalolinmu atare wato Ahmad

Saidai me? Ina gwadamashi pics din Deen saiya fara wata maganar daban mai matuqar rikita qwalwa..."


Nan yashiga bata labarin yadda sukayi da Ahmad ranar be 6oyemata komai ba har kawo shawarar dasuka yanke don 6illowa matsalar


Tunda yafara magana zee ta kafeshi da idanu tama kasa ko blinking Yayinda kwalwarta duk ta rikice itama

"kana nufin ba Deen bane muka gani ba a supermarket, kana nufin bayan Deen akwai wani mai sak kammaninshi?"

Ajiyar zuciya Aymaan ya sauke
"bazan iya concluding ba yanzu sainaji waye Deen don tabbatar da hasashena... Zainab waye Deen? Su waye iyayenshi?"


Girgiza kai zee tayi
"bayada iyaye" tafada ahankali

"kamar yaya?" inji Aymaan cikin rashin fahimta

Goge hawayenta tayi da bayan hannu sannan tace
"according to him wai duk sun rasu a hadarin mota, shi bema sansu ba don yana qarami a lokacin, kakarshi kawai ya bude ido yasani"


Shiru Aymaan yayi yana lissafa magangganunta a qwalwarshi

"to iyayen nashi wadanne tribe ne?"

"wai hausawa ne" inji zee

"ok, su kingin danginshi suna ina?"

"kamar yadda nafada maka besan kowa nashi ba sai wannan kakar tashi, besan kowa ba sai ita"

Cikin mammaki Aymaan yace
"but how come? Tayaya za'ayi yaqi sanin danginshi? Ina yan uwan mahaifiyarshi da mahaifinshi?"


"nima Hakan ya dade yana kulle min kai, koni nasha mammakin Hakan, kwata2 besan danginshi ba, daga shi sai kakar tashi ke rayuwarsu"


Shiru Aymaan yayi yana kallonta na wani lokaci sai kuma ya sauke Ajiyar zuciya yana sauke idanunshi

"then cikin dayan biyu ne"

Maida hankalinta zee tayi sosai kanshi don jin abinda zaice

"ko dai wannan kakar tashi na 6oyemashi wani abu gameda shi ne ko kuma shi ke 6oyemaki wani abu gameda shi"


Cikin rashin fahimta tace
"kamar yaya?"

Dan cizon lower lip dinshi yayi yana kallon table din gabanshi sai kuma ya saki lip din ya kalleta yace
"kodai kakarshi tana 6oyemashi wani abu na asalinshi ne ko kuma kawai yayi framing up story ne gareki"

Gaban zee yafadi
"kamar..ya?" tafada cikin rawar murya

"tayiwu they are all fake, tayiwu ba kakarshi bace shima ba Deen din bane, tayiwu kawai framing story sukayi don Shigowa rayuwarki ya wargaza ya tafi.

Cikin dayan biyu, ko dai dagaske bayan mussadiq al-hassan akwai Deen ko kuma mussadiq al-hassan shine Deen, yashigo rayuwarki ne da manufa yakuma fita bayan cikar burin shi"

Saurin dafe zuciyarta zee tayi dataji kamar zata buga saboda wani mugun bugu datayi

"No.. This can't be" tafada hankali a tashe

Ganin yadda hankalinta ya tashi yasashi realizing mistake dinshi na fadamata Hakan kai tsaye bayan ga halin datake aciki

"look zee, ni bance hakane ba, kawai hasashe ne kuma insha allah ba Haka bane"

"kenan he did that purposely? Me nayi mashi dana cancanci Hakan" tafada cikin fitan hayyaci


To fa, abu kadan ya girmama, duk inda hankalin Aymaan yakai Saida ya tashi ganin yadda zee ta burkuce lokaci guda, kuka kawai take cikin fitar hayyaci tana fadin metayi ma Deen dazai sakamata da Hakan.

Nan take kingin mutanen gidan da basusan abinda ke faruwa ba suka sani, Aymaan yayi mugun danasanin fadin wannan maganar don besan zatayi affecting dinta haka ba don shi kawai hasashe yayi

Koda su Abbu sukaji abinda ke faruwa sunyi mammaki sosai sunkuma dorawa Aymaan laifin tada mata hankali da furucinshi suna cewa be yakai shi fadin Hakan bayan yasan halin da dama take ciki

Shidai kasa cewa komai yayi sai tarin nadamar data sauko mashi, da kyar dai aka samu aka kwantar mata da hankali akan tabari suji ta bakin Ahmad kafin su yanke hukunci


Dakyar suka samu suka shawo kanta ta dan kwantar da hankalinta


Hakan yasa Aymaan takurawa Ahmad da har lokacin be gama tara bayyanan Mussadiq al-hassan ba, kasancewar shi babban mutum kuma mai murdadden hali na rashin bayyana kanshi ko sirrinshi yasa tattara bayananshi yayi wahala don shi mutum ne da idan ba saninshi kayi ba baka ta6a sanin shine mai amsa sunan don be yarda da baza sirrinshi ba irin yadda sannanu keyi shiyasa wani lokacin harya shiga wuri yafita baza'a ta6a sanin dashi ba, gashi he's not a social media fan, baya komai sai whatsapp shima ba sosai ba don yana iya wata beyi ba, gashi baya pics ya watsa, idan kaga pics dinshi to daukarshi akayi bada saninshi ba don bayaso kwata2


Dakyar dai Ahmad yasamu ya tattara bayanai akanshi ya kira Aymaan ya sanar dashi


Ranar da Ahmad zaizo gidansu Aymaan din da bayanan kowa Saida jininshi yazo kan akaifa musanmman Aymaan da oganniya zee

Ita zee fargabar ta shine kar ace hasashen Aymaan yazamo Gaskiya shikuma fargabar shi tashin hankalin zee


Sai bayan la'asar Ahmad ya diro gidan

Ganinshi yasa gaban mutane da dama acikinsu faduwa


A falo duk suka zauna aka gaisa sama kowa hankalinshi ba akwance ba


Murmushi Ahmad yayi ganin Hakan saiya bude briefcase dinshi daya zo dashi ya Fiddo wani file ya dagoshi

"to alhamdullilah, wannan file din yana qunshe ne da komai na Mussadiq al-hassan"

Tsit falon yasake dauka kowa na kallon file din

Hakan yasa ya bude shi yafara zazzaro takardun ciki ya barbaxasu a centre table din da aka maido gabansu


Ahmad yafara da
"sunan babanshi *AL-HASSAN* haifafen garin madina a qasar saudiya. Su biyar ne a family dinsu kamar yadda bayanin yazo yanada yayye biyu sai shi da twin dinshi *AL-HUSSAIN* Sai gambonsu wanda itace auta, duk ba'a kawo sunansu ba and I think it doesn't matter.

Sunan mahaifiyarshi *ZAINAB BINT ABUBAKAR* haifaffiyar qasar Misra (egypt).

Sunyi aure ne a shekarar 1***
Tareda AL-HUSSAIN shima da matarshi yar madina itama

Ga hotunan su nan... Wannan shine Al-hassan.. Ga dan uwanshi Hussaini" yafada yana nuna masu hotunan

"wannan kuma matar Al-hassan ce wato Zainab wannan kuma matar Al-hussain"

Nan ma bin Hotunan sukayi da kallo inda nan take zee ta hango tsantsar kammanin Deen da matar Al-hassan wato Zainab bint Abubakar.


"bayan shekaru biyar sa auren sai Zainab matar Al-hassan ta haihu, lokacin matar hussain haihuwarta biyu ma


A lokacin ne Zainab ta haifo yan biyunta kyawawa, gasunan"

Ya gwadamasu pics din jarirrai biyu cikin kayan sanyi dukda hoton yayi dishi dishi sosai

"Ranar suna aka radawa yaran suna *MUSADDIQ* da *MUJAHEED*"

"bayan haihuwarsu da shekara kusan hudu kuma sai aka haifi gambonsu mai suna *AYSHATUL HUMAIRA* a lokacin ma Al-hassan wato mahaifinsu Mussadiq be dade da rasuwa ba, itama ga hotonta nan datake yarinya dakuma yanzu data girma" yafada yana nunamusu hotuna biyu, daya na yar yarinya da batafi 3yrs ba na biyu kuma budurwa kamar dai sa'ar batool

"Al-hassan dama dan kasuwane kuma babu laifi yanada arziqi bakin gwargwado, bayan rasuwarshi ne al-hussain ya riqe masu mussadiq dukiyarsu har mussadiq ya girma yayi karatu yakai munzalin amsar dukiyarsu sannan ya amsa yafara kasuwanci kamar dai babanshi, cikin ikon allah sai gashi allah yasama abin albarka har suka baro madina suka dawo nan dubai ya cigaba da kasuwancinshi har allah yakai shi a matakin dayake aciki yanzu"


Tsit falon yayi bakajin qarar komai don tsab idan alura tafadi a wajen aji qararta kan kowannensu ya kulle gamm

"to kunji gajeran labarin Mussadiq Al-hassan" inji Ahmad yana kallonsu

Shiru dakin ya dauka sai can Aymaan yace
"to twin din mussadiq fa? Mujaheed kace ko me? Ina yake? Ya akayi daga baya baka sanyo Maganarshi ba a labarin?"

Duk Kada kai sukayi kingin mutanen dakin da alamun abinda ke ransu ya fada

"ya rasu!"

Qwalalo idanu dik sukayi suna kallonshi

"ya rasu???" Duk suka hada baki wajen fadin Hakan

Kada kai Ahmad yayi
"eh, shekararsu uku uku, Mujaheed al-hassan ya rasu babu jimawa mahaifinsu wato al-hassan yabishi lokacin Zainab bint Abubakar nada matashin cikin Ayshatul Humaira"


Kowa sai yakoma dumbfounded, kansu yaqara kullewa

"ta..yaya ya mutu" inji zee cikin rawar murya

Kallon zee Ahmad yayi yace
"wannan ne haryanzu bamu saniba, nayi nayi nasamu information ko kadan ne akai amma babu duk hanyar danabi a toshe take, kawai dai ansan Mujaheed ya rasu amma ba'asan sila ma"

Hankalin mutanen dakin yasake tashi

Cikin rawar murya batool tace
"k..kenan? D..Deen shine.. Mujaheed?"


Kowa kallon Ahmad yake zuciyoyinsu na bugawa da qarfi

Ahankali Ahmad ya kada kai
"Tabbas! *DEEN* shine *MUJAHEED*".... ✍️


Ummin fasihu 🧚🏻‍♀�
8/2/21, 9:40 PM - Buhainat😝: *🙍🏻‍♂️DEEN 🙍🏻‍♂�*


*060*


*IN TROUBLE*


_jiya bansamu posting ba don bansamu typing ba saboda baqin da nayi, kamar yadda nayi tunani kuna nan kuna cigiya sai naga cigiyar ma tafi yadda nayi tunani, wasu suna Deeeeen 🗣️🗣️🗣� wasu zeeeeeeee 🗣️🗣️🗣️🗣️ wasu Aymaaaaan 🗣️🗣️🗣️🗣️ amma anrasa mai cewa Ashaaaaanty 🗣️🗣️🗣️🗣️😕, babu komai nasan matsayina a wajenku 😞_


Dukkansu mutuwar zaune sukayi jin abinda Ahmad yace

"yes, idan mukayi duba da tarihinsu inda Deen yatashi beda kowa besan kowa nashi ba sai wannan wanda yake kira kakarshi Hakan ya isa ya tabbatar da hasashenmu, tabbas Deen twin din mussadiq ne, shine wanda akace ya mutu lokacin da basu wuce shekaru uku uku ba, Saidai silar mutuwar da yadda akayi yaje Nigeria shine abu Mafi daure kai aciki, Tambayar anan itace wacece kaka? Meye alaqarta dashi? Tabbas ita kadai zatafi warware mana wannan qullin"

"innallilahi waina ilaihi rajiun" Zainab tafada ahankali tana dafa goshi.

She can't believe this, Deen.. Deen ashe ba Dan Nigeria bane? Deen ashe yanada uwa a duniya? Deen ashe yanada yan uwa? Deen twins ne?


Nan da nan hawaye suka shiga sintiri a kumatunta abinka da ruwa ruwa dama

_*banida kowa sai kaka, itama batada kowa sai ni. Nice duniyarta itace tawa*_
Wasu sabbin hawayen suka sake gangaromata tuna wannan maganar ta Deen datayi


Itama batool hawayen take, abin dai kamar al'mara kamar a shirin film, wani irin tausayin Deen taji ya kamata, she's just imagining kanta ace tarabu da Ummy tun batasan kanta ba takuma rayu a wani wuri tareda wacce basuda alaqa kwata2 daita, a rabata da ummy, Abbu, dan uwanta dama family dinsu gabadaya, akaita wata duniya daban inda batasan kowa ba sai mai riqonta.

This is touching, so touching.


Shima Aymaan jikinshi yayi laqwass yayi sanyi, shi kanshi tausayin Deen ke dawainiya dashi, tunaninshi a yanzu shine ina yake? Ina kaka tasake kaishi?


"Tabbas hakane, kaka kawai zata iya warware mana komai, amma ina take? Ina zamu nemeta a duniyar nan? Ni jikina na bani ita ta gudu dashi, wataqila gani tayi asirinta zai tonu wajen introduction din tunda basuda kowa kuma za'ayi bincike kuma taga Gaskiya na iya fitowa shiyasa ta gudu dashi" inji Abbu


"nima haka nake tunani Abbu, tabbas akwai abinda kaka ke 6oyewa, wataqila saceshi tayi ta gudu dashi Nigeria, yanzu kuma ganin asirinta zai tonu saita qara guduwa" inji ummy


"to amma abin daure kai anan ummy shine, meyasa akace mutuwa yayi? Meyasa ba'ace saceshi ba akayi? There's something fishy here" inji Aymaan


"yes, nima ina wannan tunanin Aymaan, meyasa aka rufe details din mutuwar? Ya za'ayi mutum ya mutu shekara da shekaru kuma a ganshi a wata qasar? Definitely akwai wani qullalen al'amari tattare da wannan abin" inji Ahmad


Shiru dakin ya sakeyi kowa yayi zurfi a tunani, kan kowa ya kulle tamau


Can dai Ahmad yace
"yanzu meye mafita?" yafada yana kallon dukkan mutanen dakin


Dakin ya dauka sannan Abbu yace
"kamar yadda kafada dazu dole mu nemo kaka, kaka ce kawai zata iya warware mana wannan chakwakiyar"


"to amma Abbu ina zamu fara nemanta? Babu mammaki ma yanzu ta chanza qasa, qila bata Nigeria kwata2" inji ummy

Duk Kada kai sukayi cikin gamsuwa da maganarta


"ni a ganina kawai muje mu samesu, mufada musu cewa mujaheed be mutu ba yana Nigeria tareda wata, wataqila Hakan zai taimaka, suna iya ma taimakawa wajen ganota" inji batool


Girgiza kai Ahmad yayi
"idan baka iya kama 6arawo ba barawo saiya kamaka, tayaya zamu tunkaresu haka kai tsaye batareda wata hujjaba qwaqwara? Na farko babu Deen din kuma bamusan inda yake ba, Nabiyu babu kaka itama we can't tell inda take, gashi dama bamusan silar barin Deen din gidan ba, aiki kawai zamu 6allowa kanmu don karkiyi mammaki idan abin yajuye kanmu aka fara zarginmu akan komai"


Kada kai duk sukayi cikin amuncewa da maganarshi shima

Shiru dakin yasake dauka sannan can Aymaan yace
"A ganina task biyu ke agabanmu yanzu
Nafarko sanin Gaskiyar abinda yafaru da Deen koko nace mujaheed a wancan lokacin

Nabiyu kuma nemansu kaka.

Sanin ainahin abinda yafaru da Deen a wancan lokacin zai iya sauqaqa mana ko kuma yabamu haske akan abubbuwa da dama dake lullu6e agaremu, tunkararsu family din mussadiq a yanzu kamar yadda Ahmad yafada gangancine sosai, so samu musamu every proof and evidence kafin Hakan, amma Tambayar anan shine tayaya? Tayaya zamu iya samo information akan mutuwar tashi?"


"da kamar wuya Aymaan, wadannan information din ma don bakusan baqar wuyar da akasha ba kafin asamosu, kwata2 gayen baya barin any space na bayyanar sirrinshi wanda ya shafeshi ko wanda yashafe rayuwar ahalinsu, wadannan ma mafi yawancinsu ta hanyar Aysha muka samesu, kaga abu ne mai matuqar wuya"

Shiru dakin yasake dauka

Zee ce ta dago ta kalli Ahmad, akaro na farko tun fara muhawararsu tace

"kafada mana komai akan Aysha"


Dan daga kafadu Ahmad yayi yace
"well, kamar yadda nafada maku dazu Aysha itace gambonsu kuma autarsu, a halin yanzu tana gab da cika shekara 21, tana karatu ne a jami'ar ANNUR ISLAMIC UNIVERSITY inda zata shiga 300level bana, bayan Hakan kuma tanada bakeries da yayanta ya bude mata da sunanta inda take siyar da kayan snacks kala kala, I think that's all" inji Ahmad


Shiru duk sukayi suna kallon zee da ga dukkan Alamu tayi zurfi a wani tunani nata ne

"ANNUR ISLAMIC UNIVERSITY! Can nakeso ayi register dina" tafada tana kallonsu


Dik kallon rashin fahimta sukayi mata

"meyasa? Ba makarantarsu batool zaki shiga ba?" inji ummy

"eh ummy, yanzu nafasa, zanje ANNUR din, anan zanyi accomplish din first mission dinmu na gano ainahin meya faru da Deen a shekarun baya ta hanyar shigema Aysha inda zan zama friend dinta if possible ma nazama aminiyarta, da Hakan zan samu na shiga jikinta sosai har nasamo mana information din da muke buqata"


"No way! Tayaya zakiyi Hakan? What if suka ganoki? No Gaskiya bazai yiwuba" inji Aymaan


Kallon Aymaan din tayi
"haba Aymaan, it gonna be easy, kawai zanyi duk yadda zanyi ne nazama qawarta daga nan saina san yadda zanyi nasan komai, that's all, I will be very careful"


"bazai yiwuba Zainab! Wannan abin yanada sauqin fada ne abaki amma wuya a aikace so kima bar maganar nan" inji Aymaan firmly

"but..."


"No but malama, that's final!" inji Aymaan cikin hade fuska


Gani tayi yayi mata wani mugun kwarjini daya Hade fuskar Hakan yasa ta sauke idanunta hawaye na kawomata

Ganin Hakan yasa ummy cewa
"Amma Aymaan..."

"ummy please, kema kinsan abinda take shirin yi is very dangerous, zamu samu wata hanyar mu cika mission dinmu but not this, please"


Shiru duk suka sake yi

Ahankali Zainab ta share hawayen dasuka digo mata sai ta tashi batareda ta kalli kowa ba

"excuse me please" tafada sannan ta wuce


Duk Binta da kallo sukayi harta haye sama

Ajiyar zuciya duk suka sauke

"Aymaan, meyasa kake son hanata bayan bamuda wani idea na 6illowa wannan al'amarin bayan nata?"

"Ahmad this is very dangerous, tayaya xa'ayi muyi risking dinta akan wannan al'amarin?"


"do we have any option other than that? Maganar risking kuma kamar yadda tace, we'll be very careful kuma allah yaga zuciyarmu yaga niyyar mu, bamuda niyyar cutar kowa saima taimako, ko don haka zai qaremu."

Shiru Aymaan yayi da alamu maganar Ahmad tafara shigarshi Hakan yasa ya cigaba da cewa
"bayan wannan hanyar ni bansan wane hanya zamubi ba Cikin sauqi mu cimma burinmu.

Aysha itace the easiest way to our mission

Bayan ita bansan wata hanyar ba don mussadiq kamar yadda nasha fadamaka ya wuce tunanin mai tunanin

He's a very smart guy wanda yake amfani da qwalwa kuma qwalwarshi na ja sosai
Ya wuce duk yadda zanyi maka bayani don haka bi ta hanyar shi is out of question don tsaf zai gano komai kafin muyi nisa

So Aysha dinnan dai itace last hope dinmu kuma da ita zamuyi amfani muyi accomplish mission dinmu kuma babu ta sigar daya kamata aje mata kamar na wanda zee tafada, wannan is the easiest kuma ba za'ayi saurin zargin komai ba.

Idan lafiyarta kakeji ka kwantar da hankalinka, inada mutane a school din don da taimakonsu nasamu wadannan informations din ma

Zasu kulamana daita muma zamu kula daita, insha allah babu abinda zai faru sai alhairi" inji Ahmad in affirmation


Shiru falon ya sakeyi kowa idonshi akan Aymaan dake jujjuya magangganun Ahmad a zuciya

"Akhie don Allah ka yarda, mutumin nan yasha wuya, imagine shekaru 20 plus baka tareda ainahin iyayenka, baka tareda kowa naka, bakama sansu ba, how will you feel?

Don Allah ka yarda Akhie, insha allah everything will go smoothly"


Har lokacin Aymaan be dago ba kuma bece komai ba hakan yasa ummy itama saka baki

"Aymaan Ahmad nada Gaskiya, we have no other way na cimma wannan burin namu na sada lost son da family dinshi sai wannan, kawai mu tayata da addu'a dakuma fatan nasara"

Kada kai Abbu yayi
"hakane Aymaan, let's give it a try, idan muka ga Hakan zai jawo wata matsala sai muyi quitting dinshi mu nemi wata hanyar"


Shiru dakin yasake dauka kowa na kallon Aymaan din


Jiyayi dik sun daureshi da jijiyoyyin jikinshi, yes yasan wannan hanyar itace the most easiest way na cimma burinsu amma ya rasa dalilin da yasa Hakan yaqi kwanta mashi, haka kawai yaji baya son taje school din


Ajiyar zuciya ya sauke
"alright, amma fa dole ne musaka mata ido kar mubarta ita Kadai don wannan abin is very risky, dole ne mu dinga bibiyar halin datake aciki don karta fada danger batareda saninmu ba"

"yes, insha allah ai we're into this together, babu yadda za'ayi mubarta ita Kadai babu tsaro" inji Ahmad

Kada kai sannan ahankali kamar beso yace
"shikenan"

Dadi duk suka ji, batool harda yar qarar murna

"yauwa alhamdullilah, to allah ya bamu ikon gama komai sucessfully, Ya kamata a kira yan Nigeria a gayamasu ko?" inji ummy


Saurin girgiza kai Aymaan yayi
"A'a ummy, ni sai naga da kawai mun barsu for now har sai munfara shawo kan abin ko yaya kuka gani?" yafada yana kallonsu Ahmad

Kada kai sukayi Ahmad yace
"Gaskiya kam, kawai a kyalesu tunda ko afadamasu dai babu abinda zasuyi daga can kawai a kyalesu har mushawo kan al'amarin tukkuna"

Duk Kada kai suka sakeyi, nan suka cigaba da yan shawarce shawarcensu atsakaninsu


*ZEE*


Tunda tashigo dakin ta haye kan gado ruff da ciki ta jawo pillow ta cusa kanta aciki tana cigaba da hawayenta


Abin mammaki wai yau ita mutum kamar Aymaan ya hana abu kuma takasa musawa

Abin yayi matuqar bata mammaki ne saboda sanin halinta datayi na idan taso abu babu mai taka mata burki ko ya hanata cikin sauqi

Tunawa tayi yadda ada mummy kadai ke iya hanata ta hanu itama sai tasha wuya

Yes don chanzawa tasan ta chanza amma batayi tunanin chanji harya kai mutum kamar Aymaan, mai irin shekarunshi wanda tsaf ta iya gayawa magana son ranta wai ya hanata abinda ranta keso kuma takasa musawa

Meyasa? Meyasa takasa musawa? Meyasa takejin batason 6atamashi rai ta hanyar jan maganar dashi? Meyasa yana hada fuska takasa cewa komai kuma?

_Respect_

Ta bawa kanta amsa

Yes, Respect din datake mashi ne ya hanata Hakan

Tun lokacin data fuskanceshi na yadda yakeda matuqar sauqin kai agareta, taga baya jin wuyar yin abu Domin faranta mata, kuma baya qaunar tashin hankalinta, tun lokacin taji yanada wani qima a idonta.


Bayan haka a dalilinshi tasake ganin Deen kuma ta dalilinshi asalin Deen ya bayyana saboda yadda ya dauki problem dinta fiyeda yadda take jinshi, wannan kadai ya isa ta dinga ganin girmanshi har abada.

Kuma tana iya haqura da komai itama ko don ta faranta mashi itama kamar yadda shima yasha sadaukar da abubbuwa don farincikinta


Jitayi an bude kofar dakin ahankali an shigo


Bata damu ta juyo ba don tayi tunanin batool ce amma jin dakin ya chanza da scent din turarenshi yasata saurin dagowa daga Kwancen datake ta juyo


Ganinshi tayi jingine da kofa ya harde hannayenshi a qirji yana kallonta


Hakan yasata kauda kai tana share hawayenta stylishly


Dagowa yayi daga jinginen dayayi ya qaraso ahankali har gabanta


Sauke idanunta tayi qasa tana kallon zoben yatsarta tana jujjuyashi ahankali

Duqawa yayi ahankali gabanta making sure ya dan basu tazara a tsakaninsu sannan ya kafeta da idanu


"Are you angry?" yafada ahankali


Dagowa tayi ta kalleshi saikuma ta sauke idanunta qasa tana girgiza kai

"you are" yafada still akanshi

Qara girgiza kai tayi sannan ta dago ta kalleshi

"am not, why will I?"

"saboda na hanaki abinda kike so" yabata amsa

Sake girgiza kai tayi tace
"nasan wataqila Hakan ba alhairi bane agaremu shiyasa ka hana, don haka fushin me zanyi?"

Murmushi yadanyi
"amma ai fuskarki ta nuna fushin kikeyi, ga idanunki so wet alamun kinyi kuka"


Sake saurin sa bayan hannunta tayi tana goge fuskarta tana cewa
"Allah A'a, ni ba kuka ba nake"

Murmushi yasake yi
"ki gayawa wanda be sanki ba, cry cry baby kawai"


Dan turo bakinta tayi tana Hade girarenta sannan ta kauda kai


Murmushi yasake yi ganin Hakan sannan yace
"I think zan bari kije din, allah yasa Hakan shiyafi alhairi"


Saurin juyowa tayi ta kalleshi tana wara idanu saikuma ta kwa6e fuska

"meyasa? Nidai A'a tunda bakaso nima banaso, allah ba fushi nake ba"

Qara murmusawa yayi ganin sigar datayi maganar dashi a shagwa6e

"nima ba don kinyi fushi ba yasa na amince, kawai nayi nazari ne naga Hakan zaifi"

Dan Wara mashi idanu tayi
"dagaske?"


Kada mata kai yayi ahankali yana mata murmushi still

"dagaske"


Dadi taji Hakan kuma ya bayyana sosai a fuskarta

"thank you so much" tafada cikin washe baki

Dariya shima yayi ganin yadda take murna, haka kawai yaji he's proud of himself By making her happy

"amma da sharadi" yafada yana kallonta

Dan daga girarenta tayi saikuma tace
"miye sharadin?"


"da sharadin you'll have to be very careful kuma karki yi rushing abin By approaching her desperately, kawai kibi komai ahankali and muma zamu dinga kulawa iyakar yinmu"

Dadi taqara ji

"insha allah Akhie, zanyi yadda kace" tafada cikin jindadi

Dan tsayawa yayi yana kallonta har tadan tsargu ta sauke idanunta qasa

"Me kika kirani yanzu?" taji ya tambaya

Kunya ce ta kamata Hakan yasa ta rufe fuskarta da taffukan hannunta

"Allah saikin maimaita kokuma ni kadai nasan abinda zan miki"

Turo bakinta tayi ta cikin taffukan hannun datasa ta rufe fuskarta

"cewa nayi insha allah zanyi yadda kace"

"nasan wannan ai, sunan da kika kirani nakeso ki maimaita"

Qara tura baki tayi ta cikin taffukan
"ba kaji ba?"

"banji ba sosai ai"

Qara Hade gira tayi sai kuma ahankali tace
"Akhie.." saita qara rufe fuskarta


Dariya yashiga yi sosai wanda Hakan yasa taqara jin kunya saita hada kanta da gwiwa ta cusa fuskarta a cinyarta


Saida yayi mai isarshi sannan yace
"very nice, yanzu na ida tabbatarwa inada qanne biyu, da alamu anyi accepting dina as yaya kenan, Happy me"

Murmushi tayi fuskarta still a cinyarta

"Good, bari natafi tunda tsabar ba'ason ganina har rufe fuska ake"


Nan ma batace komai ba sai murmushin data sakeyi


Tana jinshi ya miqe yayi mata sallama sannan yafita, sau a sannan ta dago kai tabi kofar daya rufo da kallo

Dan ihun murna tayi takoma ta kwanta ta rungume pillow gamn cikin jindadi, ko babu komai zata samu kusanci da daya daga cikin yan uwan Deen wanda shi besamu damar yin Hakan ba

Takuma quduri cewa insha allah, zatayi iyakar bakin qoqarinta na taimaka mashi wajen ida bayyanar asalinshi dukda he doesn't really deserve that, amma ta quduri anuyar rama sharri da alhairi ko don darajar soyayyar datake mashi wanda haryanzu batayi Koda gezau bane a Zuciyarta


Gadan Gadan suka shiga aiwatar da shirinsu cikin tsari

Dayake dama lokacin registration ne sai suka shiga nema mata admission a school din

Da taimakon Ahmad da wadanda yasani a school din tasamu admission din dukda Saida sukaci kwakwa kuma sun kashe kudade sosai don ba qarya makarantar ta manya ne don sai dan wane da wane ke iya zuwanta


Basuji komai ba wajen narkar da kudinsu a wajen samamata admission din ba Haka suka saki aljihu har suka samu sukayi clearing komai


Nan fa aka shiga shiri gadan Gadan na resuming school, sosai sukeyin sayayya na school din musanmman kayan sakawa na fita school


Batool kau wani sa'in har mita takeyi wai itama da ana transfer daga wata makarantar zuwa wata makarantar batareda an dawo baya a karatu ba da wlh sai anyi mata transfer, wai itama wlh Annur takeso

Itadai zee Saidai tayimata Dariyar shaqiyanci tana cemata bakin alqallami ya bushe sai ta rungumi sorry


Yayinda suke shurye shiryen resuming school din a gefe guda kuma sai qara bata hints ake akan Aysha ana fadamata abubbuwa dazasu amfaneta a tarrayarsu gameda ita dakuma shawarwaru na yadda zata 6illomata cikin sauqi


Haka rannaku sukaita tafiya suna cigaba da shirye shiryensu na resuming school din ga Aymaan ya sakarmata aljihu sai siyayya take na school yadda taga dama a gefe daya kuma she's very eager sufara zuwa school din


Yau ma sun fito zasuje shopping mall suje su ida sayayyarsu ta fama wanda da alamu be qarewa

Dakyar ummy tabarsu suka fito don taga alamun siyayyarnan bata qarewa

Saida sukayi ta gamata da allah suna cewa daga yau shikenan kafin ta kyalesu, suma abinda yasa suka fita din wata latest jakkace tafito mai mugun kyau sukaji idan basu yita ba hankalinsu bazai ta6a kwanciya ba shiyasa suka takura zasuje din don latest design ce bata dade da Shigowa ba.

Haka suka fito cikin jindadin barinsu da akayi, batool tashiga mazaunin driver zee tashiga gefenta don har lokacin bata iya tuqiba, suka tada motar sukaja suka bar gidan


Cikin harabar wani qayattacen mall sukayi parking.


Bubbude koffofin motar sukayi sannan suka fito atare


Rurrufewa sukayi batool ta dannama motar remote sannan ta zagayo ta bangaren zee suka nufi hanyar kofar mall din suna tafe suna firarsu


Koda suka shiga ciki dan qaramin basket suka dauka sannan suka nufi 6angaren bags and shoes.


Layi layin bags din suke bi don neman irin design din dasuke so Saidai babu ita gashi kuma a magazine the shopping mall din sukaga jakkar harta burgesu


Sake dawowa baya sukayi suna bin jakkukunan daya bayan daya da kallo wai ko qila dazu sun wuceta basu saniba saidai har suka gama babu ita


Riqe qugu batool tayi
"to? Sunsan basuda ita sukasa hoton a magazine? Wannan ai wulaqanci ne"


"hmm I wonder too sister, gashi dai duk munbi layikan jakkukunan babu mai kama daita"


"kutt! Aikau bazamuyi fitowar banza ba, bari naje nayi masu magana" inji batool

"kice masu me?"

"gwadamasu hoton jakkar zanyi ai gashi nan allah yaso da magazine din nazo, sai nace ita nakeso wataqila akwai basu fiddota bane"

Kada kai zee tayi tana ta6e baki
"to saikin dawo"


Har batool zata tafi wayarta tafara ringing.

Dakatawa tayi ta zaro wayar ta duba

"wayyo" tafada ahankali

"menene?" inji zee

"kirana ake wlh, please ukhtie ko zakije kiyi musu complain din ni nasamu na daga wayar?"

Wani kallon uku saura kwabo zee tayi mata

"ki mutu baki Daga ba" tafada tana kauda kai

"haba ukhtie, please please 👏 kinga kirana akeyi ki taimaka"

"shi mai kiran naki bazai iya jiraba kigama abinda kikeyi ba? Just tell him you're busy or better still kigama wayar saiki tafi, nikam babu inda zani"

Cigaba da roqonta tayi akan ta taimaka taje har Saida tasamu dakyar ta yarda don batool idan ta nacema abu to saita samu

Fizge magazine din hannun batool din tayi ta gallamata harara sannan tawuce

Dariya batool tayi tana cewa
"eh babu komai" sannan ta maida hankalinta a wayar hannunta


Cikin jin haushi zee ta taho wajen inda ake biyan kudin kaya idan ka siya


Complain tayi cikin harshen turanci akan sunzo sayan jakka amma babu irin wanda suka gani a magazine din

Dubawa mutumin yayi saikuma ya dauki telephone yayi kira

Batasan me yake Cewa ba don da larabci suke maganar

Saida yagama sannan ya ajiye wayar yajuyo gareta

Farawa yayi da bata haquri akan Hakan sannan yace tana iya zuwa sama tayima Manager magana yace akwai jakkar saukota ne ba'akai dayi ba

Kwatancen hanyar dazatabi yayi mata tayi mashi Godiya tabar wajen.


Inda yace zatabi tabi tana tafiya ahankali


Shopping mall din babbane mai hanyoyi daban daban wanda Indai kai baqon wajen ne nan da nan zaka 6ace

Hakan take ga zee, sai gashi tayi missing Kwatancen dayayi mata tabi wata hanyar daban

Haka taita tafiya tun batasan ta 6ace ba harta gane ta sa6a hanya.

Dawowa tayi ta inda ta biyo don ganin ko zata gane Saidai idan tabi wani passage da inda zai 6illa daita, sai ta zama very confused tama kasa gano hanyar komawa inda tafito

Wayarta ce tazaro ta lalubo number batool ta danna mata kira amma wai busy

Haushi taji taja wani gajeren tsaki ta cigaba da tafiyar amma still takasa gano hanyar

Sake dannama batool kira tayi yanzu ma busy sai taji ranta ya 6aci sosai

Wannan wane irin wulaqanci ne? Dukda she's busy ai tasan dole taga kiran nata meyasa bazata daga ba atleast taji ko me zata fada?

Maida wayar tayi cikin jakka ta cigaba da tafiya ranta na suya taga wani passage kamar ta wuce saikuma tabi ta passage din tana addu'ar allah yasa ta gane ita Koda waje ne hanyar ta fiddata


Wurin is so silent and she wonder why

Ahankali tashiga bin passage din tana dan waiwaigawa har tazo tawuce wata kofa

Cak ta dakata daga tafiyar data keyi tadawo ahankali kamar mai sanda daidai wajen kofar

Kofar normal koface amma akwai glass siriri daga tsakiyarta inda ana iya hangen na ciki tanan

Ahankali ta la6e ta inda ba glass bane sannan ta sunkuyo ta leqo ta glass din

Tsaye yake amma yajuyama kofar baya waya kare da kunnenshi

Kallon bayanshi take tana wondering wanene?

Sai wata zuciyar tabata shawarar ta bubbuga mashi tagayamashi 6acewa yayi qila ya iya fiddata

Da wannan shawarar tazo miqewa daga leqen datake yimashi shikuma daidai ya juyo fuskarshi yana facing din kofar


Wara manyan idanunta tayi akan fuskarshi sai tayi saurin rufe bakinta don hana ihun datayi niyyar yi fitowa

Shine!

Deen!

No, Mussadiq!


Rufe bakinta tayi gamm takoma gefe tana sauke numfashi, Tabbas mussadiq ne, me yakeyi anan?


Ahankali tasake duqowa don ta leqa saita hango ya nufo kofar Hakan yasata saurin tashi tashige yar kusurwar dake kusada ita ta mannema bangon wajen jiki na 6ari

Jitayi an bude kofar an fito an maida an rufe

Riqe numfashinta tayi tana jin yadda zuciyarta ke bugawa kamar zata faso qirjinta

Luckily maimakon yayo bangarenta sai yayi wancan 6angaren yashiga tafiya don barin wajen yana cigaba da wayarshi

Jin takunshi yadanyi nisa daita yasa tadan leqo saita hangi bayanshi yayi nisa sai Maganarshi datakeji faintly


Batasan yaya akayi ba sai kawai ta tsinci kanta da Binshi a baya cikin sand'a da bin bango

Da taga alamun zai juyo saita la6e a jikin bango kuma gashi tabashi tazara sosai babu yadda za'ayi ya lura daita


Wata kwana yasha ganin Hakan yasa tayi saurin Qarasowa daidai kwanar don karya 6ace mata, tana kawowa ta hangeshi yana qoqarin shan wata guntuwar kwanar

Takalminta ta cire ta riqe a hannu saboda tsaro don suna dan making sound idan tana tafiya.


Haka taita Binshi a baya cikin sand'a, duk inda yayi saitabi tana making extra sure be lura daita ba.

abin mammaki saigashi duk kwanonin dasuke sha har lokacin ba sukai inda zaya ba, sunsha kwana tafi goma don tun tana qilga harta manta da qilgar

Wata kwana yasha itama tabishi cikin sand'a feeling exhausted

Tanashan kwanar itama ta nemeshi ta rasa

Hanhangawa tayi amma bata ga ko wulginshi ba ga passage din da mugun tsawo be isa ya shanyeta ba

A tsorace tafara biyo passage din tana waige waigen inda zata hangoshi


Daidai tazo tsakiyar passage din babu zato taji an chafki hannunta From nowhere an jata wani lungu

A mugun gigice ta bude baki zata fasa qara taji an dademata baki an kuma mannamata wani abu a gefen ciki

"if you move, I'll shoot" taji anfada cikin husky voice ana qara mannamata abinda yanzu tagane bindiga ce a gefen ciki... ✍️


Ummin fasihu 🧚🏻‍♀�
8/2/21, 9:40 PM - Buhainat😝: *🙍🏻‍♂️DEEN 🙍🏻‍♂�*


*061*


*MUSSADIQ AL-HASSAN*


_Godiya agareku yan Deen fans group ❤️_

_nagode qwarai da addu'o'inku, allah ya saka da alhairi ya bar zuminci 🤲🏻_

_Manage this, da babu gwara babu yawa_


Still tayi tana jin numfashinta na neman daukewa


Mutumin na bayanta hannunshi daya still dade da bakinta dayan kuma riqe da bindigar daya saita mata a gefen ciki


Wani masculine qamshi ke fita daga soft hannunshi dake dade da bakinta yana dakarmata koffofin hanci


Rarraba idanu takeyi babu damar ihu

The thought of wai bindiga ce a gefen cikinta kadai yasata jin tanason suma amma suman yaqi zuwa, sai yanzu tagane ashe idan aka suma tashin hankalin bekai tashin hankali ba


"who are you?" taji cool husky voice din directly a kunnenta kasancewar dama bakinshi nada kusanci da kunnen


Kasa amsawa tayi saboda dademata baki dayayi Hakan yasata cigaba da raba idanu zuciyarta na qara racing

"Speak!!" Yafada da qarfi at the same time yana qara turamata bakin bindigar a kwarin ciki


Jikinta yaqara daukar kyarma tanajin kamar tasaki fitsari a tsaye

Mumbling tafara yi cikin tafin hannun dake dade da bakinta hawaye na kawo mata

"Your hands up, up!!"


Babu shiri ta daga hannayenta sama jiki na 6ari

"if you move, I'll shoot" yaqara fada in a very serious tone

Tamke idanunta tayi gam tanajin wane tsotsai ma yasata fita yau?

Ahankali taji yafara dauke hannunshi a bakinta takuma ji yafara raba jikinshi da nata Hakan yasata bude idanunta

"I repeat, if you move, I'll burst your brain, try me" yafada daringly

Daga jin tone dinshi tasa zai aikata shima shiyasa ta maida idanun ta rufe tayi still harya ida Sakinta yayi saurin zagayowa gabanta yana aiming dinta da qaramar bindigar hannunta

Kallonta ya tsaya yi still bindigar na nunata

"Open your eyes!" Yafada da qarfi Hakan yasa tayi saurin bude idanunta dasuka kawo ruwa ta kalleshi


Zuciyarta ce ta buga sosai sanadin arba datayi da fuskarshi

Deen

No mussadiq

A zahiri ba Deen bane amma agareta kamar Deen ne a gabanta


Komai da komai irin na Deen dinta, oily idanun, pointed nose din, pink lips din, komai

Kamar harta 6aci kawai banbancin shine tunda take da Deen bata ta6a ganin yasha kunu kamar yadda na gabanta keyi ba yanzu, kodayaushe fuskarshi a washe take Koda ba murmushi ba yake, haka allah yayishi da very friendly face

"who are you?" yafada murya a kausashe still yana nunata da bindigar


Bude baki tayi tana son yin magana amma maganar taqi fitowa


"speak! Man anti??!" Yafada cikin tsawa again yana Binta da wani mugun kallo mai tsoratarwa

"D.. Dan allah kayi hqr, ni..."

"shut up! Use English language or Arab, speak!" Yafada again yana kai dan yatsarshi wajen kunamar bindigar


Cikin harshen turanci tashiga cewa
"Am sorry, 6atan hanya nayi, am sorry"


Shima cikin turanci yace
"yimin shiru! Ke yar leqen asiri ce ko? Waya aikoki? Zakiyi magana ko saina tarwatsa kanki da wannan bindigar?!" Yafada yana sake yi kamar zai danna kunamar

Wara idanu zee tayi jin ya kirata da yar leqen asiri

"No, wlh tlh 6atan hanya nayi, cashier ne yayi directing dina nan yace na nazo office din Manager saina 6ace, wlh am not a spy" tafada tana jin kamar ta narke don tsoro

"shut up! Kin 6ace shine kike leqen mutane ta kofa? Kuma nafito kike bina a baya kamar 6arauniya, da 6acewa kikayi fitowa Zakiyi ki tambayeni na nuna miki hanya amma sai kikaita bina idan nayi kamar zan juyo sai kiyi saurin la6ewa, gayamin wacce ta 6ace haka ya kamata tayi!!"

Wara idanu tayi kawai da dropped jaw tana kallonshi

Dama duk yana sane da ita tun lokacin datake leqen shi? Shikenan takawo kanta


"zaki fadamin wadanda suka aikoki din ko saina tsiyayar miki da kwalwa din?!" yasake dakamata tsawa

Baki na rawa tafara motsashi zatayi magana saiya katseta da

"ni kamar ma nasan fuskar nan" yafada yana qure ta da oily eyes dinshi

Jitayi cikin ta ya Murda, shikenan dama ajalinta ya kawota nan

"fadamin, ina na ta6a ganinki?" yafada yana qara saita ta da bindigar

Saurin girgiza kai tayi a rude
"babu.. Babu"


Shiru yadanyi yana kallonta kamar mai son tunano wani abu can kuma saiya daga cikkaken girarshi daya

"yes, the beggar"

Itama kallon rashin fahimta tayi mashi fuska sha6e2 da hawayen da tuntuni tafarasu
"the beggar?" itama tafada cikin rashin fahimta

"yes, kece almajirar dakikayi attacking dina keda wani mahaukaci a supermarket ko? Tun lokacin ya kamata nasan ke yar leqen asiri ce"


"ni ba almajira bace kuma ba yar leqen asiri bace" tafada cikin qunar zuciya

"Zakiyi min shiru kosaina alburusheki!" Yafada yana qara saitata

"speak up, wa kike ma aiki"

Wasu hawayen suka sake zubomata, tunda take bata ta6a ganin an saita wani da bindiga ba bare ita, jitake kamar ta sume musanmman idan ta kalli dan yatsarshi dake bisa kunamar bindigar, mistake daya idan akayi ya Latsa kunamar Saidai wata ba ita ba

"don Allah kabar nunani da bindigar, ni bansan komai ba"

Kamar cewa tayi ya qara nunata da bindigar saiya qara saitata yace
"ba nunaki da bindiga ba, har harsashe saina sa na huda kanki idan bakiyi co-operating ba"

"ni na fadamaka bakin Gaskiya ta, ni ba yar leqen asiri bace, 6acewa nayi" tafada cikin kuka

"then?" yafada yana mata kallon tama rainashi

"then saina ganka... Saina... Saina..."

"Sai kika yanke shawarar bina a baya cikin sanda har na fiddaki ko?" yafada yana mata kallon sheqeqe

Saurin Kada kai tayi
"Eh.. Eh hakane"

"saiki bari saikin samu gara sannan Kiyi mashi irin wannan karatun, wadanda suka turoki basu gayamaki ko ni wanene ba? Kodayake ba lallai bane idan su kansu sun sanni bare susan hadari na, da kinsan hadarina da tun farko baki yarda kin amshi wannan aikin na bibbiyata ba, dakuma kinsan hadari na da nan take zaki fadamin wadanda suka aikoki batareda gargada ba, amma tunda Kin za6i kiyi taurin kai, fine.

Now say goodbye to the world" yafada yana sake dora yatsarshi bisa kunamar bindigar


Ahankali zee ta rufe idanunta tana numfashi sama sama, shikenan dama ashe yau zata mutu, ashe dama ajalinta ke kiranta


Ringing din da wayarta ta dauka yasata sake tamke idanu don tayi tunanin qarar bindigar ce, jin ba taji komai ba yasa ta bude idanu ahankali ta kalleshi taga jakkar kafadarta yake kallo

"Don't move!" Yafada a tsawace saikuma ya sa hannu ya fizge jakkar daga kafadarta


With one hand still aiming at her yasa dayan hannun ya zuge zip din jakkar ya zazzageta a qasa

Lokacin har kiran ya tsinke

Still aiming at her ya duqa yana sa dayan free hannun yana barbaza kayan daya watsar qasa don son samun abu Koda daya ne dazai samu glue akan cewa bibiyarshi din take

Besamu ba don banda kudadden dake ciki sai waya

Sake kira akayi Hakan yasashi daukar wayar ya miqe tsaye still pointing the gun at her

Duba screen din yayi yaga ansa *B sis*

Juya screen din yayi a fuskarta yadda zata gani sannan yace
"who?"

Ganin sunan Batool a screen din wayar yasata jin dadi, atleast qila ta ceceta daga wannan beast din, Is he a beast? Yes, a handsome arab beast

"who!!" yasake fada wannan karon a tsawace

"Batool.. She's my sister tare mukazo nan" tafada da sauri
Duk maganar dasuke da turanci ne don mussadiq bayajin hausa, turancin ma nashi mai irin slang din larabawa ne

Daga kiran yayi yasa hands free


"oh my lovely ukhtie don Allah Kiyi hqr, wlh naga kiranki amma lokacin muna tsakiya da magana mai muhinmmancine,Kiyi hqr.
yanzu kina ina nazo wajen cashier yace Tundazu yayi directing dinki wajen manager naje kuma bakya nan, badai tafiya kikayi ba?"

Shiru zee tayi takasa amsawa sai rarraba idanun datake tsakanin wayar da mussadiq daya kasa kunne yana sauraron batool attentively kamar yasan abinda take cewa

"hello? Hello zee? Kinaji?"

Dagowa mussadiq yayi ya kalleta sannan ya katse kiran

"wacece?" yafada yana kallonta

"my sister, tare mukazo, nemana take"

"tare kukazo leqen asirin?"

Qara dan wara idanu tayi
"A'a, bakaji tace tanata nemana ba har wajen cashier?"

"banji ba, banajin jagwalgwalon yarenku so ban yarda ba, sai nayi confirming" yafada yana saka hannunshi a aljihu dayan hannun har lokacin yana sai tata da bindigar

Yan danne danne yayi a wayar ya kara a kunne ya dago yana kallonta

Daga wayar akayi daga can 6angaren

Bataji me akace ba sai jitayi yafara magana cikin harshen larabci wanda itama bata ganewa saboda dan larabcin data iya bekai ya kawo ba dukda duk tadan qara sanin wasu a zaman datayi a dubai din


Magana yake da nakan wayar amma idanunshi na akanta yana yawo dasu a fuskarta kamar mai neman wani abu

Saitaji ta takura da kallon taji kamar idanun nashi na piercing cikin hudojjin fuskarta

Hakan yasa ta sauke nata idanun tana sauraron maganar dayakeyi

"meye sunanki?" taji ya fada cikin muryar da sak ta Deen, banbancin kawai wannan tanada dan kaushi ta Deen kuma tafi taushi


"Zainab" tafada ahankali


Jimm yayi yana kallonta jin sunan data ambata sai kuma ya cigaba da magana a wayar taji ya sako sunanta cikin Maganarshi

Saida suka qara exchanging few words a wayar sannan ya katse kiran sannan to her outmost relieve taga ya sauke bindigar hannunshi daga nunata daita dayakeyi

Wata iriyar nannauyar Ajiyar zuciya ta sauke har tana lumshe idanu ganin at last yabar nunata da bindigar

"hands down" yafada still yana kallonta

Ahankali ta sauke hannunta da dama sunfara sagemata

"pack these" yafada yana nuna mata kayanta daya watsar

Babu musu ta duqa tafara tattare kudaddenta ta cusa su a jakkar sannan ta zuge ta miqe tsaye

Wayarta ya miqomata batareda ya kalleta ba

Amsa tayi itama ta sakata cikin jakkar

"you're lucky today, karki qara barin tsautsayi yasa ki qara shiga hanyata"

Yana rufe baki taji muryar batool tana qwalamata kira

Saurin juyowa tayi sai taga batool dince tareda wasu mutane uku sun taho

Sake juyowa tayi gareshi taga hankalinshi yanzu yana kan wayar hannunshi Yayinda bindigar hannunshi kuma batanan yanzu


"Zainab ina kika shig..." maganarta ta maqale lokacin da idanunta sukayi arba da mussadiq wanda shima Dagowa yayi a daidai lokacin jin ana kiramashi sunan uwa gatse gatse


Saurin Janye idanunta batool tayi gabanta na faduwa

Wayyo allah, itama tagani, taga mai kama da Deen!

Magana mutanen dasuka zo tareda batool wadanda cashier dinne da Manager din wajen suka shiga yimashi wanda tafi kama da ban hqr da rarrashi.


Be tanka musu ba har suka gama hasalima hankalinshi nakan wayar hannunshi ne

Suma ganin Hakan yasa sukayi shiru suka nutsu suna jiran yaga damar tankamasu

Saida yagama danne dannenshi sannan ya dago oily eyes dinshi be sauke su akoina ba sai acikin large eyes dinta don itama shi take kallo

Atare suka Janye idanun daga na juna sannan ya kalli cashier din da manajan, magana yadan yimasu da larabci yana saka wayar shi a aljihu

Duk magana daya idan yayi sai sun Kada kai da sauri cikin girmamawa suna dan russunawa

Koda ya gama Saida ya qara juyowa ya kalleta itama daidai ta kalleshi suka sake hada ido

Wani kallo mai wuyar fassara yayi mata sannan yajuya yafara tafiya manajan na saurin take mashi baya

Binshi da kallo daga zee har batool sukayi suna kallon yadda yake tafiya majestically

Sai tafiyarshi ta tuna mata da ta Deen

Shima irin wannan tafiyar yakeyi Saidai shi nashi akwai sanyi tattare daita, shi wannan yana yine da kuzari


"am so sorry ma'am, I should have ask someone to escort you, am sorry please" inji cashier din cikin ban hqr

Janye idanunta tayi daga kan su mussadiq dasukayi nisa ta maido kan cashier din sannan ta daga mashi kai kawai

Hanya ya nuna masu alamun suje, yayi gaba suka take mashi baya suma


Tunda suka fito daga supermarket din batool keta zuba kamar ru6a66iyar radio kuma duk akan mussadiq

Ta Wani koma zarrariyar qarfi da yaji, wai ita wlh duk fadin kamanninsu da akeyi bata ta6a sanin ya kai haka ba, sak mutumin data gani a wayar zee


Itadai zee jinta kawai take abinda ya dameta ya dameta, ita wai data ga Deen kenan a pics, ita datayi rayuwa dashi fa? Tace me?

Sai taji ranta ya jagule, ina Deen? Me yakeyi yanzu? Yana cikin farinciki ko akasinshi? Me sukeyi yanzu su samu abinci? Ga yan uwanshi nan cikin daula suna birkida aciki shi yana can allah kadai yasan wane hali yake ciki


Wani irin feelings ke tasomata a zuciya wanda takeyi duk lokacin da ta tuna shi, wani irin tausayinshi takeji a kowanne kusurwar zuciyarta

Yes, yatafi ya barta a lokacin datafi buqatar shi, ya karya alqawurran dayayi mata, ya badamata qasa a idanu, yayi breaking din zuciyarta

Amma Hakan be rage ko kaso 00.001 na soyayyarshi dake cikin zuciyarta ba, saima hauhawa datakeyi ga kuma qarin tausayinshi dake dawainiya da ita tun lokacin data gano asalinshi.


Da gaskiyar batool datace wataqila akwai dalilin rabuwarsu, akwai abinda allah ya tsara masu shiyasa ya hadasu a lokacin da basu shirya ba yakuma rabasu a lokacin da basuyi tsanmmani ba

Qaddarar so ta kawota dubai, gashi yanzu ta hadata da mutane Mafi muhinmmaci a rayuwar masoyinta

Me kuma zai faru nan gaba?
Bata saniba, time will tell, komai dama tsararre ne a wajen allah mune kawai muke haukanmu

Fatan ta dai allah yabasu ikon kammala abinda suka fara lafiya, allah ya gwadamata ranar da Deen zai sadu da lost family dinshi.

Share hawayen dasuka gangaromata tayi da sauri kafin wancan akun ta lura

Komawa tayi jikin kujerar motar ta lafe ta lumshe idanunta

Insha allah zata jajirce, zatayi trying all her best wajen ganin tasamu abinda takeso a wajen Aysha, insha allah sai komai ya warware very soon


Amma matsalar ta anan shine Mussadiq

Yasanta, yasan fuskarta and kuma ya zargeta da yar leqen asiri

Idan yaganta da Aysha anya komai bazai kwa6e ba?


Hakan na nufin she have to be extra careful da duk move da zatayi har tasamu ta cimma burinta


Batasan sun iso gidaba Saida taji sunyi parking

Saurin Kamo hannun batool dake kyarmar fita tayi Hakan yasata dakatawa ta juyo ta kalleta

"batool please karki gayawa kowa munga Mussadiq"

Zumudin fuskar batool ya rage don dama abinda take kyarmar taje tayi kenan

"meyasa?"


"Hakan na iya 6ata komai, musanmman idan yaya Aymaan yaji, yana iya yiwa abin wata fassara daban kokuma ya hanani zuwa school din don dama shawarar bawai kwanta mashi a rai tayi ba, please let this be between me and you"


Shiru batool tadanyi cikin naxari saikuma ta Kada kai

"ok, insha allah"

"yauwa, thanks" tafada tana sakin hannunta sai suka fito tare suka rurrufe koffofin motar suka shige ciki tare


Kingin rannakun sunzo very fast suka wuce, har yau ranar da zata fara zuwa school.


Tunda wuri ta shirya don tare zasu fita da Aymaan don shi zaiyi dropping dinta


Ahankali take saukowa daga stairs din cikin shigarta na atamfa riga da skirt mai pattern fari sai manyan zanen flawowi ja akai

Saita dora jar afterdress asama ta yane kanta da gyalen afterdress din.


A dining ta iske Aymaan dashima ke cikin shirinshi na asibiti Saidai kamar kullum be dora lapcoat din ba, tana gefen table din


Shi kadai ne a dining din riqe da mug din shayinshi daketa tururi


Tunda ya hangota daga nesa ya kafeta da idanu harta qaraso dining din

"sabahal khair Akhie" tafada tanayi kamar bata lura da kallon dayake mata ba

"sabahan-nurr ya ukhtie, kaifa naumiki?" yafada cikin kulawa

"alhamdullilah" tafada a taqaice tana jan kujera itama ta zauna

Shirin daukar mug take itama ta hada nata shayin saiya rigata

Hakan yasa ta fasa takoma ta zauna tana kallon yadda yake hada mata

Saida ya hada mata sannan ya turamata a gabanta

"shukran" tafada tana murmushi

Shima murmushin kawai yayi ya cigaba da shan shayinshi

Itama daukar nata tayi suka cigaba da sha cikin shiru


Basu jima ba duk suka gama suka tashi

Shiga kitchen zee tayi da mugs din ta daurayesu sannan ta ajiyesu ma'ajinsu tafito

Koda tafito saita tardashi tsaye hannunshi daya rataye da jakkarta dayan kuma riqe da briefcase dinshi sai rigar likitocin shi dake bisa kafadarshi


Ganinshi rataye da jakkarta ya tunamata da Deen dinta hakan yasa ta danyi murmushi

Duk yadda taso yabata jakkarta qiyawa yayi itakuma tana jin kunyar amsar nashi briefcase din

Haka dai ba don taso ba suka fita zuwa wajen mota

Shiya bude mata tashiga sannan ya miqo mata jakkarta ta amsa sannan ya rufe kofar shima ya zagaya nashi side din yashiga ya rufo kofar


Reverse yayi da motar suka fito daga parking space din sannan suka nufi gate wanda aka riga aka wangale masu, suka zo suka wuce suka fice daga gidan... ✍️


Ummin fasihu 🧚🏻‍♀�
8/2/21, 9:41 PM - Buhainat😝: *🙍🏻‍♂️DEEN 🙍🏻‍♂�*


*062*


*AYSHA AL-HASSAN*


Tun shigarsu gate din farko take bin school din da kallo har suka ida shiga cikin qatuwar qayattaciyar makarantar

Bïñ harabar school din ta cigaba dayi cikin sha'awa, she can't help but got fascinate with the school

Kallo daya tayima yanayin school din taji ta kamu da sonta

Har Aymaan yayi parking yafita bata saniba sai jitayi an bude kofar gefenta wanda Hakan ya dawo daita daga duniyar kallon school din


Dagowa tayi ta kalleshi sai taga shima ita yake kallo fuskarshi na fidda siririn murmushi

Sauke idanunta tayi sannan ahankali tafara yunqurin saukowa

Ganin Hakan yasashi matsawa gefe don bata damar fitowar

Ahankali ta ida fitowa sannan ta daga kai tana qara samun clear view din harabar makarantar inda mutane keta kai kawo aciki akai akai


Tayi nisa wajen kalle kallenta taji muryashi akusa daita yana cewa
"did you love it?"

Saurin juyowa tayi ta kalleshi saikuma tayi murmushin kunya sannan ta daga kanta ahankali

"Good, dama it's a unique school for unique people like you"

Sake Dagowa tayi ta kalleshi

"muje, ko sai kingama kallon?"


Sakeyin murmushi kunya tayi sannan ta gyara zaman jakkarta alamun she's ready Hakan yasa Aymaan nunamata hanya

Babu yadda ta iya haka tayi gaba shima yazo ya jera daita suka fara tafiya cikin nutsuwa


Tafiya suke suna gamuwa da mutane kala kala, mostly Arabs ne sai few qabilu


The more suke nitsawa cikin school din the more take qara jin shauqinta

This is her dream school, ta dade tana burin fita karatu qasar waje a irin wadannan qayattatun school din, sai gashi allah ya cika mata burin ta a lokacin da batayi tsanmmani ba


Haka sukaita ratsa wajen suna qara shiga ciki


An riga an kammala duk wani registration nata kawai saura tafara attending lecture


Signboard suka wuce tareda Aymaan inda anan ma sun tarar da mutane ba laifi mostly suna jotting out timetable dinsu


Shima Aymaan fiddo wani dan memo yayi daga aljihunshi da pen yashiga yima zee jotting din nata


Kallon yadda yake daga kai ya hango abinda ke rubuce yakuma maida hankalinshi akan memo ya rubuta takeyi

Sai yatuna mata da Deen, ya tuna mata memories dinta da Deen sunje kwafe timetable dinsu


Wai yaushe komai zai bar tuna mata da Deen ne? Duk abinda zai faru baya zama new thing to her Saidai yazamo kamar tuni agareta

Hakan na nufin duk abinda mutum zaiyi mata bazai zama saboba Saidai yazamo kamar tuni agareta? Meyasa?


"Here" taji anfada Hakan yasata dagowa ta kalli Aymaan dake miqa mata memo din

Kallon memo din tayi sannan tasa hannu ta amsa ahankali

"gashinan, komai na rubuce anan, Hakan zai sauqaqa miki, all you have to do shine ki duba zakiga duk lokacin dakukeda lecture"

Murmushi tayi tana Kada kai
"thanks so much"


Shima murmushin yayi mata
"my pleasure"


"yanzu kinga nan da 30mins kunada lecture, ya kamata kishiga class tun yanzu"

Sake Kada mashi kai tayi batace komai ba

"muje na rakaki" yafada yana nuna mata hanya

Babu musu ta wuce suka nufi department dinta


Har class Saida ya rakata ya samarmata Wurin zama daga farko farkon ajin

Akwai few mutane a ajin Saidai kowa harkar gabanshi yake babu wanda ma ya lura dasu


Saida ta zauna sannan ta ajiye jakkarta akan desk din sannan yafara yimata sallama

"zan tafi, please take care, idan akwai wata matsala call me" yafada cikin kulawa, dama tanada numbershi don tuni sukayi exchanging digits

"insha allah" tafada tana murmushi

"Good, yanzu bari natafi, zan dawo around 3pm na daukeki ai naga 2:30pm kuke gama duk lectures din yau ko?"


Kada kai tayi tana kallon memo din hannunta

"Good zan dawo, insha allah zan nema miki driver dazai dinga kawoki yana maidoki kafin na koyamiki tuqi"


Slight murmushi kawai tayi batace komai ba

"to natafi" yafada yana gyara zaman tie dinshi

"Allah ya tsare" tafada ahankali

"Amin ya rabb habibty" yafada cikin jindadi sannan ya juya yafara tafiya

Binshi da kallo tayi harya kai bakin kofar fita sannan ya juyo shima ya kalleta sai suka hada idanu

Murmushi yayi mata mai kyau itama ta maida mashi martani

Daga mata hannu yayi alamun bye itakuma saita qara fadada murmushinta tana kada mashi kai


Tana kallonshi harya ida ficewa ya wuce, sauke numfashi tayi sannan ta koma ta jingina da kujerar datake akai

Bïñ class din da kallo take da mutanen ciki, duk yawanci new comers ne Suma don mostly mutum shikadai zaka gani zaune yana raba idanu cikin baqunta kafin nan da few days lokacin da sabo zai shiga tsakanin juna kowa yayi aboki amma ita ta qudura a zuciyarta cewa bazata ta6a yin qawa ko daya ba kuma a school

Su Deeya sun koyamata hankali, sun nunamata ba duk mai washe maka baki bane masoyinka

Saita tsinci kanta da tunanin ko a wanne hali suke ciki yanzu?

Yanzu dai sun kusa yin shekara a garqame wanda Hakan ke nufin sun kusa rabin zaman dazasuyi a jail, sai taji tausayinsu kamar yadda takeji duk lokacin da suka fadomata arai

Tunawa tayi dasu master, wadanda ma bama sufara sa sanwar zama gidan yarin ba don a zaman dazasuyi a gidan ko kaso daya acikin 100 basuyi ba

Suma fatan shiriya tayi musu da fatan allah yasa Hakan yazama silar shiryuwarsu


Tunaninta ya katse ne lokacin da lecturer yashigo class din

Sai a lokacin ta lura da yadda class din yaqara cika

Tashi sukayi gabadaya suka gaidashi ya amsa yabasu izinin zama sannan duk suka koma suka zauna


Nan take lecture din yafara Saidai ba lesson din suka shiga ba gadan Gadan, introduction kawai ne kamar yadda most lecturers keyiwa sabbin shiga


40mins sukayi a class din kafin lecturer din yafito

Bayan fitarshi suma students din suka fara fita daga class din

Tashi itama zee tayi ta dauki handbag dinta ta rataye sannan tafito daga class din itama


Binging wayarta tayi Hakan yasa ta dagota daman tana hannunta ta duba

Text message ne Hakan yasa tayi sliding wayar tashiga saqon


_*In milk silky Abaya, in the cafeteria*_
Haka aka rubuta a text din


Ajiyar zuciya ta sauke bayan ta karanta sannan ta dago daga kallon wayar tana qara bin harabar school din da kallo

_inane cafeteria din?_
Tambayar datayiwa kanta kenan

Ajiyar zuciya tasake saukewa sannan tafara tafiya tana barin gaban class din


Bata sha wahala wajen locating din cafeteria din ba don ba'a yishi inda mutum zaisha wahala kafin ya gano ba


Cikin cafeteria din tashiga wanda yayi mugun shan banban da cafeteria dinsu na UMYU


Wannan ya hadu iya haduwa, ga varieties din abubbuwan da zaka buqata ko wane iri ne, ga wajen very clean and quiet


Ahankali take taka tiled floor din wajen tana dan wurwurga idanunta ta cikin shade din data saka ma idanunta kafin ta shigo wajen tana son ganota

Bata sha wahala ba wajen ganinta ba don kwatancen kayan jikinta da akayi mata ya taimaka wajen spotting dinta da wuri

Tana gaban wani glass da apples ke jere aciki da alama saye take

Kasancewar ta juyamata baya yasa zee bata ga fuskarta

Hakan yasata wucewa inda drinks ke jere inda tanan tana iya hango duk wani motsin ta


Yitayi kamar tana son za6ar drink din dazaiyi mata Yayinda a zahiri idanunta na kanta Saidai shade din idanunta bazai ba mutane damar gane Hakan ba


Ta inda take tana iya hangenta harta gama selecting apples din da sukayi mata sannan ta hada ruwan gora daya sannan ta wuce inda ake biyan kudin ta bude tsadaddiyar side bag dinta mai kalar kayan jikinta ta Fiddo A.t.m sannan ta miqa ma mai amsar kudin


Ganin Hakan yasa zee maida hankalinta akan abinda takeyi tayi taza6i drink biyu sannan itama ta juya ta nufi inda ake biya lokacin har an cire kudin Aysha daga A.t.m din an maido mata

Zee na isa wajen Aysha na Juyawa zata bar wajen, da wutsiyar ido zee tabita da kallo harta wuce sannan itama ta maida hankalinta kan cashier din


Babu 6ata lokaci ta biya yayi mata packaging din kayan yabata tayi saurin fita don karta 6ace mata

Cikin sa'a kau tana fitowa itakuma Aysha daidai zata sha wata corner

Hakan yasata bin bayanta itama


Koda itama ta shawo corner sai taganta zata shiga kofar wani office

Saida ta qaraso wajen sannan ta lura ashe library ne


Saida tadan ja lokaci sannan itama tashiga library din

Tana shiga ta hangeta can row na biyu a gefen haggu na library din tana duba wani Littafi data bude a gabanta tana gutsirar apple din hannunta


Janye idanunta zee tayi ta qarasa Shigowa ta nufi can bayan library din ta samarma kanta mazauni ta zauna


Few people ke library din shiyasa wajen ya dauki shiru fiyeda yadda library dinsu na UMYU keyi


Zama tayi ta zaro Littafi itama tana kallo sama sama Yayinda hankalinta ke kan Aysha da batama san daita ba


Tayi deciding ba yanzu zata fara tunkarar Aysha ba har saita gama lura da duk moves dinta

Batason sanyo gaggawa acikin aikinta don she believe duk abinda aka sanya gaggawa aciki baya lasting, Hakan yasa ta yanke shawarar cigaba da monitoring dinta har lokacin dataga its the perfect time ta tunkareta


Tana nan zaune still monitoring her tana son ganin lokacin da zata tashi amma har lokacin second lecture dinsu yayi bata tashi ba, kuma batada alamun tashi don da alamu tayi nisa a naxarin littafin datake


Hakan yasa zee maida littafin ta a jakka ta tashi ta nufi hanyar fita daga library din


Second lecture din ma kamar na farkon ne, shima just introduction wanda Hakan kamar revision ne ga zee don tuni ta wuce wannan Wurin back in Nigeria amma dukda Hakan saita nutsu har akayi aka gama

Sa6anin dazu yanzu ta lura yawancin wadanda suke zaune alone a lecture din farko yanzu suna tare da partner wataqila har sunfara sabawa wanda nan gaba sabon zai juye yakoma abota

Ta6e bakinta tayi don ba wannan ke gabanta ba, idan ma abota zatayi to da mutum daya zatayi wato AYSHA AL-HASSAN itama din da dalilin yin Hakan, Hakan yasa taqi Sakin fuskarta a class din har suka gama abinda suke a class din ta biyo ayarin masu fitowa daga class din ta fito itama


Library din ta nufa dukda tasan ba lallai bane ta isketa ba

Illai kuwa bata ciki hakan yasa tajuyo kawai ta nemi wani quiet shady wuri ta zauna ita kadai har lokacin wani lecture din yayi


Shima Saida suka dauki 30mins suna yi sannan suka fito

Agogon hannunta ta kalla taga 2:40pm

Tasan Aymaan nakan hanyar dawowa daukarta yanzu tunda yace 3pm zai zo

Ganin akwai sauran free 20mins yasa ta yanke shawarar sake ganinta kafin ta tafi


Number data turo mata text dazu ta turama guntun text kamar haka

_*where?*_

Bayan minti daya saqo yashigo mata

_*gone*_


Ajiyar zuciya ta sauke bayan taga reply din saita maida wayar a jakka takoma library don jiran isowar Aymaan


Babu jimawa wayarta tafara ringing

Cirota tayi ta duba

Aymaan ne kamar yadda tayi tsanmmani

Dagawa tayi ta kara a kunne tana sallama

Acan bangaren taji ance
"wslm student, hope kin gama komai"


Kada kai tayi sannan tace
"yes"

"ok ina wajen danayi parking dazu"

"ok ganinan zuwa"

"to a iso lfy"


Katse kiran tayi sannan ta miqe ta dauki jakkarta ta Rataya ta fito


Inda yace mata din ta taddashi, yafito ya jingina da motar kanshi sunkuye yana danne danne a waya


Besan isowarta ba Saida yaji motsin ta

Dagowa yayi daga wayar ya kalleta sai ya sakarmata murmushi

Itama dan murmusawa tayi tana Janye idanunta akanshi

"Good afternoon" tafada ahankali

"how are you? Ya makarantar?"

"very nice" ta amsa tana dan kare goshinta da hannunta saboda hasken ranar dake dallota

Ganin Hakan yasashi cewa
"ok muje"


Bude kofar tayi shima ya bude ta gefen shi suka shiga atare sannan suka maido koffofin suka rufe


Tada motar Aymaan yayi ya jata suka dauki hanyar fita daga school din


Suna kan hanya bayan sunyi nisa daga school din Aymaan yadan kalleta sannan ya maida hankalinshi akan titi yace
"so ya kikaga school din?"


"tayi sosai, every thing in order" ta amsa

"lecturers fa? Is anyone hard on you?"

Dan murmushi tayi sannan ta girgiza kai tace
"not at all"


Kada kai yayi
"Good, karki dai manta, idan kikaga ko sign din matsala ne let me know please, kinji?" yafada cikin kulawa

"insha allah" tafada a gajarce idanunta akan gashi gashin jikin jakkarta datake wasa dashi

"kin ganta?"

Kallonshi tayi sannan ta Kada kai
"eh na ganta?"

"wow! Kunyi magana?"

"A'a, nayi deciding ba yanzu ba, be kamata nayi jumping to her ba batareda nasan komai gameda ita ba, kawai ina monitoring dinta ne yanzu kafin opportunity din Magana ya hada mu"

Kada kai Aymaan yayi cikin gamsuwa
"Good, Saidai dukda Hakan ki kula please da kinga something is going wrong ki sanar dani, banason wani abu ya sameki"

Yadda yayi magana yasata dan sunkuyar da kanta tana dan murmushi

Sai taji yaqara cewa
"kinsan ko meyasa?"


Dagowa tayi ahankali ta kalleshi saikuma ta girgiza kai alamun A'a

Shima daga kafadu yayi
"nima haka, amma zanyi qoqarin gano dalilin"


Kauda kai kawai tayi batace komai ba

Ta rasa dalilin da yasa haryanzu takasa sakewa dashi, ba Haka take ba, tanada saurin sabo amma a case dinshi abin ya chanza

Gwara idan tare suke da batool tafi sakewa amma idan daga ita sai shi ne sai taita jinta wani iri, taji ta qagara tabar wajen kamar yadda yanzu ma ta qagara su isa gida ta samu ta sulale


Haka suka cigaba da firar jefi jefi inda duk Aymaan keyin rabi da kwatan ta don zee tana amsawa ne where necessary wani wuri kuma tayi murmushi kawai


Koda suka isa gida ma da Tambayar taga Aysha duk suka tarbeta


Kamar yadda taba Aymaan amsa haka suma tabasu kuma sukayi na'am suma da shawarar tata.


Washegari ma haka zee tayi, daga nesa nesa take lura da Aysha tana kuma monitoring moves dinta kuma batasha wahalar ganota ba don wanda yabata information jiya yabata yau ma wanda duk aikin Ahmad ne don shi yayi assigning wadanda zasu dinga lurarmashi da Aysha din yakuma basu number zee akan su dinga sanar daita akai akai

Hakan ba qaramin sauqaqawa zee yayi ba don nan da nan take ganota duk inda take saboda information dinsu


Ahaka suka cinye satin farko har aka shiga na biyu shima

Acikin kwanakin nan zee ta samu abubbuwa da dama gameda Aysha

Kama daga mutanen da take mu'amala dasu, yanayin mu'amalarta da mutane, wuraren datafi zama ddss


Ranar wata juma'a Zee ta yanke shawarar tunkarar Aysha


Cafteria tashiga bayan ta tabbatar da shigar Aysha aciki


Hangenta tayi usual spot dinta wato wajen apples tana selecting wadanda takeso

Itakuma zee tawuce wajen kayan snacks wadanda ke opposite din inda Aysha take itama tana za6ar wadanda sukayi mata


Ganin Aysha ta juyo zata taho yasa itama juyowa riqe da abubbuwan data dauka


Tahowa sukayi suna fuskantar juna Yayinda zee ke targeting din yadda zata aiwatar da plan dinta

Suna kawowa tsakiya sukaci karo da juna wanda Hakan yasa kayan hannunsu watsewa

"ya Ilahi!" inji Aysha cikin daddadar muryarta

"ya sallam!" inji zee itama tana Wara idanu akan kayyayakinsu dasuka watse a wajen

Atare suka duqa suka shiga tsintsintosu sannan suka miqe

"am very sorry, ban kula bane" inji zee cikin harshen turanci tana kallonta cikin yanayin ban haquri

karo na farko dazasuyi face - face kuma taga fuskarta tarr ba kamar yadda tasaba hangenta daga nesa a yan kwanakinnan ba


Aysha batayi irin kamar nan ba da mussadiq da Deen sukayi, ita kammaninta daban, tafi kama da babbansu amma kallo daya zaka mata kasan jininsu ce don ko babu kama ta fuska akwai ta jini


Itama farace irin fatt dinnan, yanayin fatarta na shige da fatar kajin turawa, tanada yar madaidaiciyar round face mai dauke da dara daran idanu sai dan siririn hanci da madaidaicin baki

She's beautiful in her own way kuma kallo daya zaka mata ka hango tarin nutsuwar dake tattare daita

"oh, never mind, ai karo mukaci, it's not intentional" inji Aysha cikin turanci itama mai karin larabawa irin dai na mussadiq


Murmushi zee tayi tana miqoma ta daya daga cikin apples dinta data tsinto mata

"thanks for your understanding"


Itama murmushin tayi mata tana amsar apple din
"thanks too"


Wani abu yayi knocking kan zee, wani abu Aysha tayi yanzu takoma mata sak Deen Saidai abin yazo ya wuce in a flash that takasa pointing finger akai


"here" inji Aysha tana miqamata sausage roll dinta da itama ta tsinto mata

Amsa tayi tana murmushin yaqe tana kallonta don son ganin abinda tagani dazu

"thanks" zee taqara fadi ahankali

"yeah, take care" tafada tana sake sakarmata murmushi sannan tayi gaba

And then sai lokacin zee ta gano abinda tagani dazu


Murmushinta

A'a ba Murmushinta ba

Abinda yafito ta sanadin murmushin

Dimple

Dimple din tsakiyar gemu


Lumshe idanu tayi ta bude su cikin shauqi

Bata ta6a sanin tayi missing din murmushin Deen ba sai yanzu

Bata ta6a sanin tayi kewar Dimple dinshi ba sai Yanzu

Ajiyar zuciya ta sauke mai nauyi tana maida lower lip dinta ciki tareda cijewa

Tadan jima ahakan kafin itama ta fara yunqurin barin wajen amma abinda witsuyar idanunta ya hango mata ya hanata wucewa din

Kafe wajen da idanu tayi sannan ahankali ta qarasa wajen ta duqa ta dauki abin


Gabanta ne ya fadi

Dago abin tayi a hannu tana jujjuyawa tana ganin kammaninshi sak da wanda tasaba gani


Bracelet ne

Irin wanda take ganin Deen dashi kullum a hannunshi, wanda wani lokacin har tunanin amfanin me yake mashi take ganin kullum yana maqale a hannunshi

Bracelet din da shi ya hadata da Deen ta hanyar sarqahoshi datayi da gyallenta


Tashi tayi tsaye tana cigaba da jujjuyawashi a hannu abubbuwa da dama na yawo a zuciyarta... ✍️


Ummin fasihu 🧚🏻‍♀�
8/2/21, 9:41 PM - Buhainat😝: *🙍🏻‍♂️DEEN 🙍🏻‍♂�*


*063*


_sorry for the late post, yanzu Dakyar nake samun typing, bear, bear, bear with me👏_


Damqe Bracelet din tayi a hannunta sannan itama ta bar wajen da niyyar zuwa maida ma Aysha


Saidai Koda tafito bata nan

Wajen cashier ta wuce ta biya kudin abinda ta siya sannan ta fito waje

Nan ma ta hanhanga bata ganta ba


Tasan wuraren da zata iya ganinta a daidai wannan lokacin Hakan yasa ta dauki hanyar inda takeda tabbacin tana wajen yanzu


Harta fara tafiya wata idea tayi stucking qwalwarta


Sake kallon Bracelet din tayi

Duk yadda akayi wannan abin mai matuqar muhinmmanci ne ga wadannan ahalin

Idan ta fuskanci ya 6ata hankalinta zai tashi kuma zata shiga nemanshi


Yanzu batada tabbacin tama san da faduwarshi so idan takaimata ba zatayi wani murna ba

Kamata yayi tabari ta nemeshi ta jigatu a nemanshi har tafara fidda rai da ganinshi a sannan itakuma ta bata, Hakan zai sata murna sosai kuma qila daga nan abinda take burin ya qullu a tsakaninsu ya qullu


Ajiyar zuciya ta sauke, yes this makes sense, bazata bataba yanzu, sai monday.


Da wannan shawarar ta bude jakkarta ta jefa Bracelet din aciki ta juya ta dauki hanyar class dinsu


Ba lokacin lecture bane amma haka ta shige class din ta zauna

Jitayi duk babu abinda ke mata dadi, she's very lonely gashi babu abokin fira


Buga tagumi tayi da hannu daya datayi supporting da desk dinta tana kallon masu shige da fice a class din


Tunawa tayi da Good old days dinta inda kullum burinta gari ya waye ta shirya ta tafi school ba don komai ba sai don haduwa dashi


Tunawa tayi da yadda suke zama a either library ko wurin zamansu suna karatu

Tunawa tayi da yadda yake haquri daita akan calculations yaita fahimtar daita har saita dauka, idan kuma bata dauka ba bazaiyi gaba ba dole sai yayi ensuring ta iya wannan sannan duk kuwa tsawon lokacin da Hakan zai daukesu


Tunawa tayi da yadda suke fira, firar da haryanzu takasa samun mai mata mai dadi irin nashi kuma haryanzu takasa samun wanda zata saki jiki sosai suyi fira da Dariya kamar shi

Tunawa tayi yadda takeyi kamar zata makeshi da littafi idan yayimata laifi ko yafadi wani abu da bemata ba, Tunawa tayi da yadda yake curewa wuri guda idan tayi Hakan ko yayi baya yana Dariya


Tunawa tayi da yadda yake Hade cikkakun girarenshi idan yana fushi da yadda yake kumbura cute face dinshi


Batasan murmushi take ba, shes lost in his thoughts as always


Lokacin datayi realizing Hakan sai taga few students ma kallonta suke, tasan tunani zasu dinga yi ko wancan lfy?


Bude jakkarta tayi ta ciro wani plain sheet da pen ta ajiye a gabanta ta qara buga tagumi da hannu guda, dayan kuma tafara rubutu


_I heard someone whisper your name, but when I turned around to see who it was, I was alone. Then I realized that it was my heart telling me that I miss you._


_Sometimes, I sit and think of all the memories I’ve made and smile. Then I smile even more at the thought of memories yet to be made._


_I still miss him, I miss him, I’m missing him._


_I miss the old days,the old you, the old us.._


Kasa cigaba da rubutun tayi saboda yadda hannunta yakasa riqe pen din sosai saboda rawa rawar dayake


Kafe rubutun tayi da idanunta tana ganinsu biji biji sanadiyar hawayen dasuka taru a idanunta


Ahankali ta dauke takardar ta cukwikwiyeta ta Runtse ta a hannu


Yaushe Deen zai bar zuciyarta ta huta?

Yaushe zata yini ta kwana batayi tunaninshi ba?

Yaushe zata yini ta kwana bata zubda kwala ba akanshi?

When will all these end?


****


Weekend yazo ya tafi very fast inda zee ke qagare monday tayi don sake fuskantar Aysha

Tasan izuwa yanzu taci nema harta gaji, tasan izuwa yanzu tana cikin damuwar rashin shi kuma samunshi a wannan lokacin ba qaramin dadi zaiyi mata


Haka hassashen zee yake don a bangaren Aysha bata lura da babu Bracelet din a hannunta ba sai lokacin tafiyarta gida


Hankalinta yatashi sosai dataga baya daure a tsintsiyar hannunta, Hakan yasa tashiga nemanshi


Duk inda taje ranar Saida ta koma ta dudduba amma babu shi

Har cafeteria din Saida taje ta dudduba har inda suka ci karo da zee amma babu abu mai kama da Bracelet dinta


Kamar bazata tafi ba ranar amma haka ta haqura tabi driver suka koma gida tana jin kamar taita kuka


Koda ta isa gida haka ta tisa umminta gaba da maganar 6acewar Bracelet din

Sosai ta damu kanta akan Hakan ganin Hakan yasa umminsu lallashinta tana assuring dinta zata ganshi insha allah


Da Hakan ta dan kwantar da hankalinta itama tana looking forward to monday don qara komawa school ta duba ko zataci sa'ar ganinshi ko kuma cleaners din school din sun tsintar mata


*MONDAY*


Tunda wuri ta shirya suka sauko tareda batool da itama tayi shirin zuwa makaranta


Suna zaune kan dining suna karyawa Aymaan shima ya sauko cikin shirinshi na fita asibiti


Shima babu 6ata lokaci yayi joining dinsu suka karya tare sannan suka tashi suka fito gabadaya suna musun wa zee zatabi

Shi Aymaan yace shi zatabi yayi dropping dinta itakuma batool tace bata yarda ba don atare ai yazo ya iskesu qasa Indai yanason tabishi Saidai idan su biyu zaiyi dropping

Shikuma yace bazata shigar mashi mota ba shi zee kawai zai dauka


Itadai zee tana gefe tana kallon dramarsu

Wani sa'in idan suna wannan chaftar tasu kamar ba wa da qanwa ba, ta lura akwai wasa sosai a tsakaninsu ba kamar wasu siblings din ba da zakaga babu yan wasa tsakaninsu


Ganin abin nasu bana qarewa bane kuma lokaci wucewa yake yasa ta dakatar dasu ta hanyar cewa to bari ayi yar chankal duk wanda abin ya fada mawa to shi zatabi


Qin yarda Aymaan yayi yace shi be yarda ba tana iya cheating Saidai idan coin za'a jefa


Haka kau akayi, Aymaan ya Fiddo wani kwandala ya nuna ma batool akan ta za6i side daya

Saida tagama ruwan ido sannan ta za6i side din da zanen mutum ke ajiki shikuma Aymaan aka barshi da plain side din


Zaya jefa batool tace bata yarda ba Saidai aba zee ta jefa


Zee na Dariya ta amshi kwandalar ta jujjuyata a hannu sannan ta jefata sama tayi tumbulan sau uku asama kafin ta fado qasa


Duk tahowa sukayi don ganin wayaci, sai gani sukayi side mai zanen ke sama


Ihun murna batool tayi ta kama hannun zee tajata zuwa motarta suna yiwa Aymaan daya tsaya Hannu riqeda qugu yana binsu da kallo Dariya


Bude mata passenger seat tayi ta shiga sannan itama ta zagaya seat din driver tana cigaba da yimashi Dariyar mugunta

Saida tayimashi gwalo sannan tayi saurin shigewa ta rufo kofar ganin yayi kamar zai nufosu

Saurin tada motar tayi tajata aguje suka fice daga gidan suna cigaba da dariyarsu


Kwafa Aymaan yayi sannan shima ya nufi motarshi murmushi a fuskarshi yashiga ya tada shima yabar gidan


Har cikin school din batool ta kaita tayi parking suka fito tare


Yau zee taji dadin ride din zuwa school din don firarsu sukaitayi suna Dariya har suka iso bata saniba sa6anin idan tareda Aymaan take don jitake ta qagara su iso don she always feels nervous around him kuma tarasa dalili

Aymaan nada fara'a ga wasa da Dariya amma tarasa meyasa take jin kunyar shi, kwata2 bata iya sakewa freely idan suna atare, tarasa dalili


Tareda batool suka wuce cikin school din don cewa tayi sai taga class dinta


Babu musu zee tayi leading dinta har class din inda duk inda suka gitta sai batool tayi santi tana jin dama school dinsu ne


Daga baya ma saita fara fushi wai kishi take da zee don school dinsu yafi nasu kyau

Itadai zee Saidai tayimata Dariya tana mata gwalo don qara tunzurata

Ahakan ta rakota inda tayi parking motar ta tashiga ta tadata sannan sukayi sallama taja motar tayi gaba


Ganin Hakan yasa zee Juyawa takoma class don lokacin first lecture dinsu yakusa


Bayan 40mins zee tafito daga class kamar yadda kingin students din ke fitowa


Wayarta ta fiddo tashiga number dake bata information akan Aysha


*_where?_*
Ta turawa number


Bayan wani lokaci akayi reply da

*_cafeteria_*


Maida wayar tayi cikin jakkarta sannan ta nufi hanyar cafeteria din


Daga nesa ta hango ta tafito daga cafeteria din ta dauki hanyar komawa department dinsu


Sanye take cikin wata tsadaddiyar blue Arabian gown mai kwalliya a gaba tayi rolling gyallenta yadda larabawa keyi, side bag bisa kafadarta mai matching din kayan jikinta

Tunda ta hangota tasan babu lafiya don fuskarta dauke take da yanayin damuwa wanda bata raba dayan biyu rashin abin hannunta yajawo Hakan

Gyara nutsuwarta zee tayi ta nufi hanyar cafeteria itama Saida taje gab da kofa sannan tajuya ta kalli Aysha da har tayi nisa

Cikin dan daga murya zee tace
"hey!"


Bataji ba don tayi nisa a tunanin datake gashi da dan tazara a tsakaninsu Hakan yasa zee biyo bayanta

"hey! Sister! Ukhtie!"


Cikin tunani Aysha taji kamar ana mata magana saita dan dakata sannan ta juya ahankali

Zee ta hango tana daga mata hannu tana nufota murmushi a fuskarta


Tsayawa tayi tana kallonta harta iso tana qoqarin son tuno inda tasan face dinta


Qarasowa zee tayi tana dan panting saboda dan saurin datayi

Murmushi Aysha tadanyi mata tana cewa
"Aslm alaiki"

Ajiyar zuciya zee tayi sannan tace
"wslm warahmatullah, tun dazu nake miki magana bakiji ba" tafada cikin turanci


Dan dafa goshi Aysha tayi
"oh Afuwan, banji bane"


Murmushi zee tayi tace
"nice wannan wanda mukayi clashing a cafeteria ranar juma'a?" tafada cikin sigar son tuna mata


Kada kai Aysha tayi tana murmushin da yasa dimple dinta lotsawa tace

"na tuna, ya kike? Ya yau?"


Da lfy lau zee ta amsa saikuma ta fara qoqarin bude jakkarta tana cewa
"ranar bayan tafiyarki naga wani abu, bansaniba ko nakine" tafada tana laluben jakkar


Zubama jakkar idanu itama Aysha tayi tana jin bugun zuciyarta na qaruwa, fatanta dai ace abinda take nema ne


Bayan yan lalube lalubenta ta Ciro Bracelet din ta nunama Aysha din tana cewa
"naki ne?


Rufe bakinta Aysha tayi cikin tsananin murna sannan tayi saurin amsa tana jujjuyawa a hannu


"ya rahman! Nawane, ina kika ganshi?" tafada cikin tsananin murna


Murmushi zee tayi mata
"a cafeteria bayan kin tafi, qila faduwa yayi"


"kai amma nagode qwarai yar uwa, you have no idea yadda na damu da banganshi ba"


Murmushi zee tayi tana Kada kai
"babu komai yar uwa"


Sake jujjuya shi tayi kamar mai son ganin ko shi dinne Yayinda zuciyarta ta washe tayi wasai tana jin wani irin farinciki a zuciyarta


Sake Dagowa tayi ta kalleta cikin farinciki tana cewa
"shukran aidaan ukhtie, naji dadi sosai, jazakillah bil-jannah"

Murmushi zee tayi don ita banda murmushinta babu abinda take kallo

"ohh babu komai, just take care next time" tafada tana mata murmushi


Kada kai Aysha tayi tana sake damqe Bracelet din a hannunta tana cewa "insha allah sweet ukhtie"


Yar Dariya zee tayi tace
"Zainab, ki kirani da Zainab"


Dan Wara idanu Aysha tayi
"Ashe ummie ce? Zan dai kiraki da ummie saboda sunan Umminmu gareki"


Dan Wara idanu itama zee tayi cikin mammaki
"wow, kice ni Umminki ce" tafada cikin tsokana


Dariya Aysha tayi tana Kada kai
"Na'am, ke Umminmu ce kinga dole daga yau mu dinga biyayya"


Itama dariyar tayi tace
"kefa, ya sunanki?"


"Aysha.. Aysha Hassan"


"wow! Nice name"


"thanks ummie"


Murmushi zee tayi cikin jindadin nasarar da tasamu tace
"zan tafi, kafin lokacin lecture yayi, see you"


"yeah, see you" tafada itama tana daga mata hannu


Saida taga wucewarta sannan ta maida hankalinta kan Bracelet din hannunta tadanyi ihun murna tasake rintseshi a hannu sannan itama ta wuce department dinsu


Da farinciki zee ta qarashe Wunin ranar ganin yadda plans dinta ke working out successfully, saikuma tafara planning what's next don Batason tayi fuck up ko yaya ne a wannan mission din nata


Washegari Zee bata yarda suka sake haduwa da Aysha ba sai washegari

Ranar ma Saida tayi timing lokacin shigarta library sai ta rigata shiga ta zauna daga tsakiyar library din yadda data shigo zata hangota


Tana zaune pretending kamar karatu take Aysha tashigo library din


Da farko bata lura da zee ba Saida ta ida Shigowa library din


Dan Wara manyan idanunta tayi tana cewa
"Ummie!"


Zee jitayi kamar ta dago nan take Saidai ta cije taqi Dagowa Hakan yasa Aysha qarasawa wajenta

"Ummie" taqara fada tana dafata


Saurin dagowa zee tayi da alamun tsorata a fuskarta ta kalli Aysha


Dariya Aysha tafara tana rufe bakinta
"sorry, na baki tsoro"


Ajiyar zuciya zee ta sauke tana dafe saitin zuciya
"Gaskiya kam, kin bani tsoro"


"sorry, I was calling you amma hankalin na can" tafada tana nuna littafin gaban zee


Murmushi zee tayi
"wlh kau, hankalin yatafi, please have a seat" tafada tana matsa mata


Babu musu ta zauna tana murmushi tareda daukar littafin gaban zee tana cewa
"Me kikeyi?"


Daga kafadu zee tadanyi tana cewa
"just going through abubbuwan damukayi a class"


"wow, that's Good, wane level kike?" tafada tana maida mata littafin


"100level" inji zee tana jawo littafin


Dan Wara idanu Aysha tayi
"wow, kice kina cikin sabbin zuwan school dinnan kenan"


Kada kai zee tayi tana murmushi

"ok you better be really ready don akwai aiki agabanku sosai"

Dariya zee tayi tace
"yes ma'am"


Dariya suka sakeyi atare


"shekaranjiya naba Umminmu labarin ki, she's so happy itama, tace na miqa miki saqon godiyarta"


Zuciyarta tadanyi skipping beat, mahaifiyar Deen fa kenan.


Sai tadan daga gira daya
"Godiyar me?"


"Bracelet dina dakika ganomin"


Yar Dariya zee tayi tace
"haba don gano Bracelet kawai?"


"agareki ne kawai amma gareni babban abu kikayimun don I can give anything to get back my Bracelet"


Dan Wara idanu zee tayi
"is it that important?"

Kada kai Aysha tayi
"fiyeda tunaninki, its something very special" tafada tana shafa Bracelet din dake maqale da hannunta


"really? Tell me about it" inji zee cikin zaquwa


Dan murmushi Aysha tayi sannan tace
"never mind, what matters shine an ganoshi"


Zainab Bataji dadi ba Amma bata nuna ba, wataqila tafara zaqewa ne, ya kamata tabi ahankali karta lallatama kanta aiki, be kamata ta fiye shishigi ba, duka yaushe suka fara magana ma da zata so jin wani abu gameda ita, she really needs to be careful kar ta fita kan Aysha


Da wannan tunanin ta dauki burger da ba'a fasa ba Cikin wadanda tasiya ta tura gaban Aysha cikin friendly smile tace
"bismillah"


Girgiza kai Aysha tayi tana cewa alhamdullilah

Dan 6ata rai zee tayi tace
"why?"


Dariya Aysha tadanyi ganin yadda ta 6ata fuska tace
"am not a fan of burger, baya min dadi"


Kada kai kawai tayi bata qara matsa mata ba ta maida kanta akan littafin gabanta


Itama Aysha saita fiddo wani Littafi daga jakkarta tana cewa
"nima bari naduba wasu sums, suna bani wuya, na rasa yadda zanyi dasu, I hate calculations"


Dagowa zee tayi daga littafin ta ta kalleta tana mata Dariya tace
"really? Is it that hard?"


"very hard, ni dama ba fan din calculations bane, I hate it, Dakyar nake coping a class" tafada cikin yanayin mita


Cikin karambani da neman gindin zama zee tasa hannu ta dauki takardar tana cewa
"mugani, maybe I can help"


Wani kallo Aysha tayi mata sai kuma ta fashe da Dariya tana cewa
"really? Kinsan wane level nake? 300level. Tayaya 100 level student zai koyar da 300level?"


Wani murmushi ya kufcewa zee ganin abinda ke cikin littafin Aysha din


Tasan calculations dinnan, sunyishi back then in Nigeria Hakan yasa ta dago ta kalli Aysha tace
"well, let's see"


Wata takardar zee ta fiddo ta ajiye sannan ta tambayi Aysha ina ne kebata matsala

Cikin son qureta Aysha ta nunamata wani question tana son ganin ta ina zata fara


Ahankali zee ta kwafe question din cikin takardar data fiddo sannan ta kauda Littatafan Aysha Agefe sannan tafara solving din question din tana explaining cikin qwarewa.


Tunda tafara Aysha ta kafe takardar da idanu tana kallon yadda take solving question din cikin qwarewa kamar wata expert mathematician


Saida tagama sannan ta dago ta kalleta tace
"Are you clear now?"


Daukar takardar Aysha tayi tana kallo cikin mammaki don dama question din data sani ne ta gwada mata don ganin ko zata iya saigashi tayi solving dinshi expertly


"wow! Tayaya kikayi Hakan?" tafada tana bin takardar da kallon mammaki


Murmushi kawai zee tayi batace komai ba

"ya ilahi! Wlh kinyi shi daidai, but how come kika iya solving sum din 300level while you're just in 100 level?"


Murmushi zee tasake yi
"you know, mathematics is all about calculations and using of formular(s), akwai wadanda muddin zasusan formular din abu to zasu iya solving dinshi ko an koyamusu ko ba'a koyamusu ba, what you need to know about mathematics is how to use formulars and steps you should take" tafada tana copying magangganun Deen back then


Tafi Aysha tafara impressively

"wow, am impressed, ashe ina tareda mathematician"

Wara idanu zee tayi tana Dariya
"No! Nima duka me na iya?"

Murmushi Aysha tayi tace
"Allah kin iya, tunda har kika iya solving wannan question din, haka shima yayana yake tun yana qarami allah yabashi qwalwa, lokacin yana secondary school shike topping kowa a mathematics, har takai seniors dinshi ma na zuwa yayi musu solving, nima shi kemin don dai yanzu ma bayanan shiyasa nake shan wahala"


Dan Wara idanu zee tayi
"wow, kinada yaya?"


"yes, inada yaya daya sunanshi yaya mussadiq, he's a mathematician too amma Koda yaushe he's busy beda lokacin nunamani wani lokacin sainayi Dakyar nake samun ya gwadamin, to yanzu yamayi tafiya, am left all alone with my problems" tafada tana 6ata fuska


Dariya zee tayi mata cikin zuciyarta kuma tana jindadin jin cewa mussadiq yayi tafiya, yes! Seems yatafi yabata space don tayi bincikenta hankali kwance


"amma yanzu tunda gaki ai shikenan" inji Aysha cikin jindadi


Dan Wara idanu zee tayi tace
"nima fa ba sosai na iyaba, just the little my brain could take"


"yes, atleast your brain could take something, nifa?

Yanzu let's solve another one" inji Aysha tana maido littafinta gabansu tana sake matsowa kusada zee

Gwada mata wani question din tayi wanda shima zee ta iya shi, nan take suka hau solving dinshi shima


Wasa wasa Saida sukayi solving question biyar duk masu matuqar wuya a zaman dasukayi, sosai karatun da zee keyi da Deen yayimata rana yau don sosai tayi impressing din Aysha kuma ta burgeta

A bangaren Aysha kau jitayi kamar ta goya zee don dadi


Dama tun shekaranjiya da zee ta maido mata Bracelet dinta taji ta kwanta mata arai, gashi tanada wani stylish way of life dataji ya burgeta plus suna mai girma dake gareta wato sunan dear mahaifiyarsu, tun a lokacin taji tayimata


Washegarin ranar data maido mata Bracelet dinta ta nemeta don haka kawai taji tana son qara ganinta kota sake mata Godiya amma bata ganta ba kuma gashi batasan department dinta ba, haka ba don taso ba ta haqura

Sai gashi yau batareda tayi tsanmmani ba tasake haduwa daita anan


Haka kawai taji tanajin kanta very free around her abinda bata saba yi ba don ko qawaye batadasu sai wadanda za'a hadu a gaisa kawai

Amma lokaci guda taji tanason qulla abota da wannan kyakyawar cool lady din mai burgewa


Bata ida burgeta ba Saida tayi realizing baiwarta na iya lissafi

Lissafi na matuqar ba Aysha wuya don dama can bata sonshi Saidai course din datake yi dole Saidashi shiyasa take matuqar wahala

Kasancewar tana ganin subject din a matsayin subject mai matuqar wahala Hakan yasa duk wanda ya iyashi yakuma qware akai yake matuqar burgeta don gani take their brain is so special


Hakan yasa Zainab ta ida tafiya daita, takuma ji ajikinta tayi qawa, ko babu komai zata dinga qaruwa ta wannan fannin daita


Suna ahaka har lokacin shiga next lecture dinsu zee yayi


Haka ta tashi ba don sun gaji da karatun ba tayi mata sallama


Tambayarta Aysha tayi yaushe zata fito tace mata 2:30pm kuma daga nan gida zata tunda last lecture ne

Hakan na nufin bazasu sake haduwa ba don lokacin dazata fito ita tana class


"here" Aysha ta miqa mata wayarta

Amsa zee tayi tana kallon wayar saikuma ta dago ta kalleta da alamun tambaya

"Your digits please, so that gobe basai nasha wahalar nemanki ba kuma zamu dinga Gaisawa idan muna gida"


Murmushi zee tayi, ko ba'a fadaba tasan tarkonta ya kama, Aysha na sonta da abota


Loda mata numberta tayi acikin wayar sannan tabata

Amsa tayi tayi flashing dinta saigashi kiran yashigo

"save it please, zan kiraki anjima inji ko kin isa gida lfy"


Murmushi zee tayi mata tace
"ok, thanks, bari natafi kar lokaci ya wuce"

"ok bye"

"bye"


Da haka ta fito daga library din zuciyarta fess.

Gashi tasamu shiga awajen Aysha ga tasamu information din mussadiq bayanan, very big opportunity.

Fatanta dai allah yabata ikon kammala komai kafin dawowarshi... ✍️


Ummin fasihu 🧚🏻‍♀�
8/2/21, 9:41 PM - Buhainat😝: *🙍🏻‍♂️DEEN 🙍🏻‍♂�*


*064*


*ONE-SIDED LOVE*


"Hmm Aymaan kenan, ni aganina riqe kashi a ciki baya maganin yunwa, 6oye abinda ke zuciyarka is not a Good idea, aganina fidda abinda ke zuciyarka zaifi kabarshi yana weighing dinka down" inji Ahmad yana kallon Aymaan dake zaune kan office kujerarshi mai jujjuyawa ya maida kanshi can baya yana kallon ceiling


Ahankali ya dago daga jinginen dayake ya zauna dakyau yana fuskantar Ahmad

"Ahmad kenan, karka manta anason duk abinda zakayi ka lura da lokacin daya kamata kayishi kakuma lura da moment din daya cancanci yin abin, am waiting for the right time, dude"


"waiting? Har yaushe zaka cigaba da jira? You want it then reveal it, karka manta abari ya huce shike kawo rabon wani"


"kaima kuma karka manta rabon mutum baya ta6a wuceshi, idan rabota ce zan mallaketa Ahmad

Nima kaina inason rabuwa da wannan nauyin dake kan qirjina, nafika son furta abinda ke raina don ni yake hanawa sukuni dare da tana ba kai ba

But not now, haryanzu zuciyarta batayi healing ba, banaso na dagula mata lissafi

Nasamu kwanan nan tana dan walwala, tana farinciki, banason abinda zai zo yasake dagula mata shi"


Ajiyar zuciya Ahmad yayi yace
"kai komai sai kace farinciki farinciki, what if farincikin nata baya nufin naka farincikin fa?"

"then saina haqura da nawa ita tasamu saboda farincikinta on it own yana sani farinciki"


Furzar da iska Ahmad yayi sannan ya qara matsowa jikin table din gabanshi yace
"Aymaan kana sonta ko baka sonta?"


Dan murmushi Aymaan yayi ya koma jikin kujera ya jingina
"meyasa kake tambayar da kasan amsarta?"

"Don't answer my question with a question dude!" inji Ahmad a dan fusace


Murmushi Aymaan yasakeyi sannan ya sake Dagowa daga jingina da kujerar dayayi ya matso jikin table din daya raba tsakiyar su

"yes, I love her. With all my heart, all.

Tun lokacin dana fara ganinta nafara jin wani abu a zuciyata gameda ita

Lokacin da Ummy tabani labarin ta kuma sainaji tausayinta yasamu matsugunni a zuciyata

Sainaji inajin pain dinta a zuciyata, sainaji kamar ni akayiwa abinda akayi mata, kamar na dauke mata abinda takeji a zuciyarta na maido tawa

Saikuma naji duk duniya babu abinda nakeso kamar walwalarta da farincikinta, every single smile of her means alot to me and also every single drop of her tears means to me too.

I love her so much, so very much" yafada emotionally

"why then baxaka gayamata ba Aymaan? Kafison kayita Ajiyar abin a zuciyarka har abin yazama maka something else?

Look at you Aymaan, you're no more yourself"


Murmushi Aymaan yasake yi
"zai wuce, komai zai daidaita"

"when? Yanzu fa haka kai kadai ke haukanka, ita batasan ma kanayi ba, tell me yaushe zai wuce?"

"Ahmad its not as easy as you think, Zainab's heart is already injured and still yet to heal, why zan kuma zan qara dagula mata lissafi?"

"yaushe zatayi healing? Haryanzu fa tana sonshi, it's first love we're talking about Aymaan, bakasan first love ba ko? Jiranta tayi healing kamar jiran gawon shanu ne, heal her with your love"

Kallo Aymaan ya kafe Ahmad dashi na wani lokaci sannan yace
"yes, nima inason yin haka amma nakasa"

"why?"


Shiru Aymaan yaqara yi yana kafe desk din gabanshi da kallo
"maybe am scared"

"scared? Scared of what?"


Ajiyar zuciya Aymaan yayi yace
"baxaka gane ba, wani abin da ka fadeshi kaji amsar da zai bugar maka zuciya gwara kabarshi a zuciyar ka jure duk illar da zaiyi ma zuciyarka.

Yes inason na fadamata amma ina tsoron amsar dazata bani, baki yasan abinda zai furta besan abinda za'a mayar mashi ba.

Zan jira, zan jira har sai naga perfect time din daya kamata na furta mata feeling dina

Zan cigaba da supporting wish dinta harta cimma burinta, wataqila Hakan zaisa nayi earning soyayyarta..."


❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️


Kamar yadda Aysha tace sai gashi ta kira zee can marece likis

Lokacin suna tareda batool a daki

Basu dade suna gaisawa ba sukayi sallama akan sai sun hadu gobe idan allah ya kaisu

Sosai Batool da zee sukayi ta murna akan nasarar dasuka samu suka kuma zauna suna qara planning abubbuwan daya kamata suyi nan gaba


A 6angaren Aysha kau Koda taje gida ranar da labarin zee ta tusa umminsu gaba tanata bata labarin ta da yanayin turancinta don slang din turancinsu ba daya bane Hakan yasa yanayin na zee ke burgeta ga uwa uba maths data iya


Agaban Ummin ma takira zee suka gaisa tana mata fatan takoma gida lafiya

Basu dade kan wayar na sukayi sallama

Haka kawai itama umminsu Aysha taji yarinyar ta kwanta mata arai itama dukda ko ganinta bata ta6a yi ba


Haka dai Aysha ta kwana da doqin wayewar gari don sake haduwa da new friend dinta


Ahankali ahankali abota tashiga tsakanin zee da Aysha irin sosai dinnan

Koda yaushe suna tare inhar ba class daya daga cikinsu yake ba


Sosai yarda da shaquwa tashiga tsakaninsu inda ta Hakan duk zee tasan tarihin rayuwarsu

Saidai kamar yadda Ahmad yasamo information din Hakan itama tasamu, bata samu abinda takeso ba don da alamu ma ita kanta Ayshar batasan meye silar 6acewar Deen ba, abinda tasani kawai shine ya rasu


Sosai Hakan yaqara dagulawa zee lissafi, tarasa yadda zata 6illowa lamarin

Bata saniba ko dagaske Aysha din batasan komai akai bane koko tasani kawai it's their secret shiyasa bata fadamata ba


Abu na biyu data fuskanta gameda Aysha shine tana soyayya, soyayya mai matuqar wahala


Da farko kafin tasan komai tana lurada kullum idan suna tare wani na bugowa Aysha waya

Idan tazaro wayar taga shine sai alamun tsoro ya bayyana a fuskarta, saita daga kiran cikin rawar jiki tana magana cikin kame kame

Kuma duk sadda suka gama waya sai taga wani expression marar dadi a fuskarta


Da farko tayi tunanin da Mussadiq ne suke wayar don dama taga alamun ba mutunci ba ya isheshi sai daga baya ta fuskanci ashe saurayi ne


Soyayya take da saurayin datake matuqar tsoro kuma abin daure kai aciki shine tana sonshi sosai amma kuma tana tsoronshi don ko waya ya kirata sai taita jawo addu'o'i kafin ta daga


Abin na matuqar daure wa zee kai don ita tunda take bata ta6a ganin irin haka ba Amma sai tayi ignoring tayi kamar batasan me take ciki ba don batason shishiginta ya cika yawa don haryanzu she's not done with her mission don tasa a ranta ko tayaya ne saita samu information akan mutuwa ko 6acewar Deen


Tun zee na kauda kai akan Hakan har wata rana tayimata magana
"Aysha, wai meke tsakaninki da wanda kuke waya ne? Abin da daure kai, kullum idan yabugo sai inga kinshiga fargaba"


Ajiyar zuciya Aysha ta sauke sannan tace
"Saurayi na ne ummie"


"saurayinki? Saurayinki kike tsoro?"

Dan murmushi tayi
"ba tsoronshi ba nake, masifarshi ce banaso"

"masifa yake miki?"


"kusan Hakan, he like complaining alot, komai sai yayi complaining, dana complaining da wanda bekai ayi complaining ba, wlh har tsoron ganin kiranshi ya shigo wayata nake" ta qarashe tana dafe goshinta


"complaining? Wani abu kike masa da bayaso?"


"not at all, kawai shidai akwai shi da neman dalili dik yadda zakayi kaffa kaffa akan karkayi wani laifi bazaka tsira ba, gashi beda hqr ga kishi

Yanzu jiya don ya kirani ban daga da wuri ba ya hau fushi, kira uku yaimin nikuma lokacin ina wajen Umminmu wayata kuma nabarta daki

Shine fa daga baya danagani na kirashi, yama tsaya ya saurari uzuri na yaqi yahau yimin masifa daga baya ma ya katse kiran, nayi ta bugawa yaqi dagawa daga baya ma ya kashe wayar, jiya ko barcin kirki banyi ba, kwana nayi ina tura mashi load and loads of messages din ban haquri amma haryanzu yaqi saurarena, kinga yanzu na kira yashiga naci sa'a ya daga amma still be sauka ba" ta qarashe maganar cikin damuwa


Tunda tafara maganar zee ke kallonta cikin mammaki, meye Hakan? Dama akwai irin wannan soyayyar?


"ban gane yaqi sauka ba, laifin me kikayi masa? Daga ya kira baki daga ba? Ko babu dalili kinada right din qin daga wayar shi bare da dalili"


"hmm, baki sanshi bane, ya wuce duk tunaninki abu kadan ke fusatashi"

"so?" zee tafada cikin qunar rai

"don abu kadan yake fusatashi sai yace zai sauke kwandon bala'i akanki? Kefa budurwarshi ce ba mata ko baiwa ba"


Ganin kamar zee ta fusata yasata dafa kafadarta tana cewa
"haba ummie, bafa yadda kike tunani bane, ni nasan duk soyayyar dayake yimin ce tajawo Hakan, shifa idan ya kirani ban daga da wuri ba sai yayi tunanin ko ina tareda wani ne ballantana yaji line busy, ranar mai rabamu sai allah.

Tsananin sona yasamashi tsananin kishina shiyasa beson yaji koda labarine wai anganni da wani bare kallo ko magana tashiga tsakaninmu dashi.

He's the jealous type don ko wani wuri natafi be saniba sai yaita kawo zargi a ranshi"


"what? Kuma shine kike kiran haka da so? Idan babu zancen igiya meya kawo igiya? Definitely yana yin abinda yake zarginki dashi kenan"


Cikin rashin fahimta Aysha tace
"ban gane ba"


"idan har zai dinga zargin kina tareda wani ko zaki yaudareshi to Definitely shima yaudararki yake shiyasa shima yake ganin kamar yaudararshi kike"


Shiru Aysha tadanyi saikuma ta girgiza tana murmushi
"A'a ummie, kece dai baki fahimceshi ba, idan kinga irin haka to namiji na tsananin kishinki ne kuma soyayya ke kawo kishi"


"idan haka ne shima sai ya dinga gayamiki me yake ciki da kuma ina da ina zaya tunda kema kina sonshi ai kuma kina kishinshi.

Wannan ai be dace ba a matsayinki na budurwarshi yana zarginki yana miki wadannan abubbuwan inaga kunyi aure?"


"idan mukayi aure wadannan abubbuwan duk tarihi zasu zama, kinga hankalinshi zai kwanta tunda ya riga ya mallakeni"


"bazai daina ba Aysha, śaboda shi mutum mai yawan zargi kome zakayi komin taka tsantsanka saiyaji zarginki a zuciyarshi ko yaya ne, kuma irinsu sai kiga basu cika Gaskiya ba shiyasa suke ganin kowa marar gaskiya"


"kibar cewa haka Ummie, ni nasan Umar nakuma yarda da soyayyar dayake min, insha allah da munyi aure komai zai wuce"


"Hmm, banga alama ba Aysha, mutumin dayake miki masifa kamar 'yarshi kafin ya mallakeki Kiyi tunanin me zai dinga yi nan gaba idan ya mallakekin, Gaskiya wannan ba mijin aure bane"


"ummie kibar fadin haka, ke bakisan soyayya bane shiyasa" tafada convincingly

Dan murmushin takaici zee tayi
"wannan ba soyayya bace Aysha, wannan wahala ce, Umar ko mema sunanshi ba sonki ba yake"

"you know what? Mubar maganar nan don Allah, bazaki ta6a ganewa ba, wanda be ta6a soyayya ba bazai gane yadda take ba, so Mubar maganar watarana idan kika fara zaki gane abinda nake nufi"


Shiru zee tayi tana kallonta ganin tama raina mata hankali, wai batasan soyayya ba, lallai ma.


Kyaleta tayi kawai ta fita harkar soyayyarta Saidai kullum da 6acin ran abinda ke faruwa a wannan wahallaliyar soyayyar take kwana


Abin ma gaba gaba yakeyi don kusan Koda yaushe saiya saiya 6ata mata rai, abin dai gwanin haushi wani sa'in zee Saitaji kamar taita marin Aysha don takaici

Kwata2 bata iya ganin laifin Umar duk abinda zaiyi mata, gata very timid daya fara yimata masifa sai tayi shiru ko wani lokacin ma taita hawaye


Sosai Hakan ke qonama zee rai musanmman idan taga kwata2 Aysha takasa daukan haske akan cewa abinda Umar keyimata ba soyayya bane, soyayya tariga ta rufe mata idanu gani take duk abubbuwan dayake mata duk cikin so ne
(wannan labarin ya faru a real life, I just feel like sakoshi a labarin nan ne, akwai masu irin wannan wahallaliyar soyayyar, yar uwa duk mai treating dinki irin Umar ba masoyinki bane

Duk wanda zai kira wayar ki kiji faduwar gaba ko tsoro maimakon kiji sanyi a ranki to ba masoyinki bane

Duk wanda magana mai dadi bata shiga tsakaninku a matsayinku na masoya sai akasin haka to baya sonki.

Ki taimakawa rayuwarki ki rabu dashi, karki yaudari kanki akan idan kukayi aure zai chanza ko zaki iya chanzashi

Aure yasha banban da hangen da Mafi yawan yanmata ke mashi, wata rayuwa ce mai zurfi wanda bazaka santa ba saika shige ta

Masu qaunar juna da nuna tsantsar kulawa da juna kamar zasu hadiye juna ya suka qare bare ire irensu Aysha da Umar.

Wanda Hakan tafaru daita nacan yanzu tana regretting, a lokacin an nunamata Gaskiya an gwadamata amma so ya rufe mata ido taqi ganewa gashi yanzu tana ganewa in a hard way

Duk namijin da baya regarding feelings dinki baya kuma gudun 6acin ranki tun kina gidanku to ba mijin aure bane yar uwa, ki roqi allah ya chanza miki da Mafi alhairi, idan kina sonshi dayawa ki roqi allah ya sassauta miki don wlh wahala zakisha, Allah yasa mu dace🤲🏻)


Tun zee na jin takaicin Aysha har tafara bata tausayi don ta lura soyayya ke dawainiya daita, so ya riga ya rufe mata ido bata ganewa

Hakan yasa tafara Binta da lallami tana qoqarin fahimtar daita don harga allah tanajin Aysha har can qarshen zuciyarta, tana jinta kamar yar uwarta ta jini amma ina? Wanda yayi nisa bayajin kira

Wani irin makahon so take yima Umar wanda fuskantar Hakan dayayi yasa yake mata abinda yaga dama don yasan babu abinda zata iya saboda tana tsananin sonshi (wannan ma na daya daga cikin illolin nunama namiji so dayawa, bawai karki nuna mashi soyayya ba A'a karki nunamishi irin zurfin da kikayi acikinta, Kiyi saisa saisa karki bari ya fahimci yayi miki mugun kamu don idan soyayyar mace ta fito fili harta dara ta namiji to soyayyar zata zama very boring to him, zaki ficemashi a kai dukda kau shima yana sonki din, haka maza suke, da alamu ma sunfi son masu garasu sosai, maza mutanen mu😆)


Watarana suna zaune as usual suna labari cikin nishadi kira yashigo wayar Aysha


Ganin yadda ta waro idanunta cikin tashin hankali kawai yaba zee amsar wake kiranta

Kauda kai tayi gefe tana jin ranta na 6aci

Tana jin sadda Aysha ta daga wayar tayi sallama cikin low calm voice har wata nutsuwa ta musanmman takeyi idan suna waya

Batasan me suke cewa ba don da larabci suke magana har tagama wayar.

Tayi mammakin gama wayarsu da wuri don ba Haka yasaba ba, suna dan dadewa suna waya kamar abin arziqi nan kau shegen masifarshi yake zazzagemata ta waya


Jin Aysha ta kamo hannunta yasata dagowa ta kalleshi

Ganinta tayi Duk a burkuce yanayin tsoro a tattare daita Hakan yasata cewa
"meya faru ne?"

Hadiye wasu yawu Aysha tayi sannan tace
"Ummie, wai cewa yayi nafito gashi can harabar school, am scared, bansan dame yazo ba, muryarshi doesn't sound good"


Tsayawa zee tayi tana kallonta, wai saurayi yakawo mata ziyara take haka kamar wanda zata inda za'a yankata


Rufe Littatafan gabanta zee tayi sannan ta miqe tsaye


"muje" tafada tana kallonta

"ina?" inji Aysha tana kallonta itama fuskarta pale with fargaba

"rakaki zanyi" tabata Amsa


Sauke wata nannauyar Ajiyar zuciya Aysha tayi sannan itama Saurin tashi ta dauki jakkarta ta Rataya tace
"muje"


Tana lura da yadda Aysha ke sauri a tafiyarta har tana dan hardewa da alamun kila batason su jima basu isa Wurin ba yaji haushin sun shanyashi

Yitayi kamar bata gane nufinta ba ta cigaba da normal tafiyarta, sai jitayi tana son ganin wanda beautiful rich mace kamar Aysha keyiwa rawar qafa haka


Daga nesa suka hangeshi zaune bisa booth din arniyar motarshi da alamu shima dan masu shi ne kamar dai Aysha


Har suka qarasa wajen tana kallon bayanshi don baya yabasu

Sallamar Aysha ce yasashi Dagowa daga danne dannen dayake a waya ya juyo garesu


Kallo daya zakayimashi kasan shima balarabe ne don the same skin colour gareshi da Aysha Saidai baida kyau sosai, farinne kawai saikuma kyan fatarshi wanda da alamu harda hutun dayake ciki yabata gudunmawar glowing


Dama da murtukaken fuskarshi ya juyo amma ganin zee yasa yadanyi jimm yana kallonta cikin yanayin rashin fahimta sannan ya kalli Aysha cikin son qarin bayani


Cikin fara'a Aysha tafara gabatar da zee da itama ta Hade rai cikin larabci sannan ta juyo ta kalli zee tace
"Ummie meet Umar, my love"


Jitayi kamar ta kwadeta don haushi ganin yadda take wani rawar kafa wajen introducing din amma saita daure ta dago kai ta kalli wanda aka kira Umar na 2secs sannan ta kauda kai tana dan ta6e baki tayimashi sallama


Kamar bazai amsaba shima saiya amsa sama sama sannan ya maida hankalinshi kan Aysha kamar dama jira yake yafara yimata magana da larabci cikin fada fada


Tsayawa zee tayi tana kallon ikon allah don yamaqi tsayawa yaba Aysha din dake son yin magana damar yin maganar data fara saiya katseta yanayi yana watsa hannuwa kamar wani ubanta Hakan ba qaramin 6ata ran zee yayi ba dukda batasan me suke magana akai ba Amma ko don ita datake baquwa acikinsu kuma baquwar budurwar shi yaci ace yaji kunyar masifeta a gabanta Hakan yasata taka mashi burki a fusace

"Hey mr man! Meye haka? Zaka tusa mutane gaba kana masu ihu?" tafada cikin harshen turanci rai a 6ace


Dakatawa yayi ya tsaya yana kallonta kamar a mammakince sai shima a harshen turanci yace
"Me kika ce?"

"cewa nayi meyasa zaka tisa mutane a gaba da ihu? Waye diyarka anan, Is this also in your manners of speech"

Riqo hannunta zee taji anyi ta juyo taga Aysha ce idanunta fall hawaye

Haushi yaqara kamata ta fizge hannunta daga riqonta tana cewa
"dalla kyaleni, waye diyarshi? Waya haifa anan dazai tisamu agaba da ihu?!"

"who are you?" yafada yana jin zuciyarshi na qara 6aci

"kai ka cancanci wannan Tambayar, waye kai daxaka tisamu gaba da haushi!"

"Ummie!" inji Aysha da dan qarfi hawayenta na gangarowa

Matsawa baya tayi ganin tana niyyar riqomata hannu cikin 6acin rai tana cewa
"dalla karki ta6ani, kai waye dazaka tisata gaba kana mata masifa kamar ubanta? Haihuwarta kayi? Ko baiwarka ce? Zaka kwaso jiki kazo har school kasameta kacimata mutunci, did you even have conscience?"


Afusace yajuya kan Aysha yafara magana cikin larabci

Katseshi zee tayi da
"look, ba ita tayimaka ba ni nayi maka, ni zaka kalla kayiwa magana da yaren dazan gane ba ita ba!"

Juyowar yayi ya kalleta cikin turanci shima yace
"kinsan ko meke tsakaninmu zaki shiga tsakaninmu? Kinsan ko wanene ni?"


"waye kai banda wanda besan darajar mace ba, wanda be darajja soyayyar da akemishi, babu abinda ke tsakaninka daita sai mugunta kuma baka cancanci soyayyarta ba!"


"Zainab!" inji Aysha saikuma ta fashe da kuka


Cikin tsananin 6acin rai Umar yake nuna kanshi da yatsa

"ni.. Ni kike cewa haka?"

"eh kai, sai me?"


Juyawa yayi ya kalli Aysha dake kuka har lokacin yace
"infact, it's over!"


Ya juya Afusace zai bar wajen

"Umar!" Aysha tafada da qarfi tana yunqurin Binshi


Riqo hannunta zee tayi tana cewa
"let him go Aysha, so what?"

Fizge hannunta Aysha tayi daga riqonta itama a fusace tana cewa
"leave me alone!"

Sannan tajuya ta nufi Umar dahar yashiga mota ya rufo kofar


Kwankwasa glass din gefen shi Aysha take tana cewa ya bude mata cikin kuka amma ko kallonta beyi ba ya tada motar yaja da qarfi ba don zee ta fizgo Aysha ba da saiya bigeta


"Umar!!" tasake kiran sunanshi tana kallon motarshi data nufi gate aguje

Binshi tasoyi sai taji takasa yin gaba saboda an riqeta

Juyowa tayi taga zee ce riqe da ita Hakan yasa ta fizge jikinta daga riqonta

"take your hands off me!"

Qara matsowa zee tayi tana qoqarin yimata magana saita daga mata hannu
"stay away From me!"

Saita juya ta nufi hanyar fita daga school din itama


Binta da kallo zee tayi tana jin zuciyarta na suya


And on her very eyes her only link to Deen's problem is gone... ✍️


Ummin fasihu 🧚🏻‍♀�
8/2/21, 9:41 PM - Buhainat😝: *🙍🏻‍♂️DEEN 🙍🏻‍♂�*


*065*


*THE GIRL*


Iya dagulewa ran zee ya dagule, tsayawa tayi tana kallon hanyar da Aysha tabi ta fita cikin dacin rai


Juyowa tayi taga har few mutane sundan taru suna kallon abinda yafaru

Janye idanunta tayi daga kansu ta wuce cikin school din feeling very bitter


Har aka tashi daga school din ranar ran zee na a dagule gashi bata qara ganin ko wulgin Aysha ba a school din


Drivern da Aymaan ya samomata yazo wanda shi ke maidota gida don mostly Aymaan dama ke kawota school din


Shiga motar tayi suka bar school din cike da dacin rai.


****


"wow, this is crazy! Kodai asiri yayi mata?" inji batool tana kallon zee da haryanzu fuskarta ke a dagule


"ba asiri bane, kawai tsantsar soyayya ce, tana sonshi ne over"


"kutt... Wallahi ba'ayi namijin dazai juyani tun ina gidanmu ba, wannan ai idan tashiga gidanshi tashiga uku, tun yanzu yana mata iko kamar ubanta ina ga tashiga gidan nashi yasan ya mallaketa?"


"abinda nake gwadamata kenan taqi fahimta, you have to see yadda yakeyi mata, ko babu komai ai kasancewata a wajen yakamata ya ragamata amma kinga yadda yake mata? Not minding who and who is watching?"


"irinsu ne zakiga ko bayan auren ne basajin komai su duzgata agaban mutane, sai kiga mutunci ya zube hatta abokanshi ma sunsan batada wata daraja awajen shi"


Ajiyar zuciya zee kawai tayi batace komai ba

Tunani take ace misali Deen ne Hakan, Deen ne keyimata Hakan, zata iya jurewa, kai da kamar wuya, duk son datake mashi bazata iya jurar wulaqanci daga wajenshi ba Saidai son ya kasheta


"yanzu meye mafita? Gashi kince ta tafi cikin fushi, idan tayi deciding ta rabu dake fa? Ya kenan?"


Shiru zee tayi bata amsa ba sai kafe waje daya datayi da idanu


"kema da kin kyaleta kawai, gashi yanzu Hakan na neman ta6a friendship dinku wanda wargazewar abotarku daidai yake da wargazewar shirinmu, gashi dama bamu samu abinda mukeso ba har yanzu"


"ni ba damuwa ta wargazewar abotar mu ba, damuwata halin dazata tsinci kanta aciki, yanzu da nan gaba

Batool, yes nafara abota da Aysha saboda wani dalili nawa na kaina amma yanzu ina jinta a raina fiyeda yadda ya kamata na jita

Bana regretting abinda nayi don shine daidai

Koda abotar tamu zata watse bazan damuba kamar yadda zan damu idan Aysha tayi ending up da Umar a matsayin miji


Kwata2 they dont make a match

Aisha is very cool, kamar Deen.

Batada hayaniya, very jovial and timid.
While Umar masiffafene na gidan gaba gashi he doesn't have regard to her feelings, yanzu yana mata Haka yana mata masifa kamar zai rufeta da duka wa keda tabbacin idan sukayi aure bazai dinga dukanta ba? Kwata2 Aysha ba match din Umar bane"


Ajiyar zuciya batool tayi tace
"to ya zakiyi? Idan allah ya qaddara shine mijinta fa? Ya zakiyi? Ya zatayi?"


"insha allah bashi bane ba ma, insha allah mijinta na nan tafe, very nice and kind person wanda zai sata farinciki akoda yaushe, insha allah..."


Har dare Aysha na maqale a ran zee, tunani takeyi ko a wanne hali take ciki yanzu

Qila ma tana can tanata kiran wayar shi baya dagawa kokuma tana mashi text upon text kamar yadda tace tana mashi idan suka 6ata


Wayarta tajawo tashiga number Aysha din tashiga rubuta mata short text message


_*wani lokacin abinda zuciya keso baya zama alhairi ga mutum.. Wani sa'in you have to let go what your heart crave for saboda ba alhairi bane a gareta*_

_*No guy is worth your tears and when you find one that is, he won’t make you cry*_

_*ki roqi allah yayimiki za6i na alhairi, karki roqeshi akan lallai sai za6inki zai mallaka miki*_

Turamata tayi sannan ta tura wayarta qarqashin pillow ta kwanta ta lumshe idanunta trying to catch some sleep

Ta jima tana saqa da warwara sannan barcin yayi nasarar dauketa.


Washegari haka zee taje school da yaqinin ganin Aysha suyi magana Saidai har suka tashi daga school din bataga ko mai kama daita ba, takira number ta ma bata shiga, haka ta haqura tana jin ranta babu dadi


Wasa wasa Saida sukayi kwana uku basu hadu da juna ba tun zee na damuwa tana kiran wayarta da bata shiga always harta haqura ta qyaleta kawai


A cikon kwana biyar da yin abin watarana zee na zaune cikin class tana duba wani Littafi taji an dafata a kafada

Ga mammakinta tana Dagowa sai idanunta sukaci karo da Aysha


Tsayawa tayi tana Binta da kallon mammaki don bata ta6a expecting itace ba


Harara Aysha ta gallamata sannan tace
"Wurin zaman ma baza'a bani ba?"


Dan murmushi zee tayi saita matsamata cikin tsokana tana cewa
"Wata sabon gani, yan yaji an dawo"


Hararar wasa Aysha tayimata tana zama tace
"kuda kukaqi zuwa biko"

Dariya zee tayi tace
"biko na nawa, a school dinnan babu inda ban shiga ba da sunan nemanki, shikenan daga samun dan misunderstanding kinyi cutting off dani ko wayarki bana samu"


Murmushi Aysha tayi tace
"ba Haka bane, dubeni kiga, bakiga na chanza ba?"

Sai a lokacin zee ta tsaya ta kalleta dakyau sai taga tadan rame tayi pale

"ya sallam, meya sameki? Naga kamar kin rame"

Murmushi Aysha tayi tace
"ba kama bane, na rame. Yanzu haka ma da sauqi. Tun ranar da muka rabu nake rashin lfy"


Wara idanu zee tayi saikuma tayi alamun fuskar tausayi
"meya sameki? Kuma shine ko Kiyi informing dina?"


Murmushi Aysha tadan sakeyi sannan tace
"ni tun washegarin ranar ban qara sanin inda wayata ba take sai jiya, tayaya zanyi informing dinki to?"


"to meya sameki?"


Murmushi kawai Aysha tayi


Dan Wara idanu zee tayi tace
"badai saboda abinda yafaru ba?"


Dan murmushi tasakeyi tace
"it doesn't worth it, right?"

"tell me its not because of it" inji zee tana kallonta


Wani murmushin taqara yi sannan tace
"sadly, it is"

Shiru zee tayi tana kallonta not knowing what to say

"Zainab, in gayamaki wani abu?"


Kada mata kai tayi still looking at her

"tunda nake ban ta6a yarda da wata ba ko inji mutum ya mugun kwantamin kamar ke ba, saina dinga jin kamar na dade da sanin ki, sai na dinga jin kamar akwai wani bond daya hadamu tare da daddewa tunma kafin haduwarmu"


Shiru zee tayi still looking at her batareda tace komai ba

"shiyasa naji bana iya rabuwa dake dukda abinda kika yimin yakai na rabu dake din don da wata ce I won't have anything to do with her anymore, a dalilin abinda kikayi nayi rashin lafiyar kwana uku"


Zee dai har lokacin bata ce komai ba kuma bata daina kallonta ba


"Zainab kowa da irin jarabtar da allah yayimishi, ni tawa kenan.

Kowa sai yace Umar baya sona while ni nasan yana sona

Everyone was against soyayyarmu, yayana, ummie na dukda dai bata nunawa fili but itama batason relationship dinmu and now you.


Hakan yaci ace na haqura ko?
Amma nakasa, I love Umar fiyeda tunanin kowa, nima bansan yaya akayi ba kawai I know I can't live without him kuma na gasgata Hakan a kwanan nan

Can you believe don Umar yace it's over na kwanta rashin lafiya harda qarin ruwa?

Wannan yaci ya nuna muku ba laifina bane, it's my heart's"


"Aysha, nasani. It's hard to forget someone you love musanmman first love

Nima I was once in your shoe, infact am still there

Amma mine is totally different From yours

Nawa yana sona, a zuciya akuma aikace

Yana gudun 6acin raina, yana son farincikina, baya iya fushi dani, baya iya hurting feelings dina amma naki fa? Ke kanki kinsan wannan abinda kukeyi ba soyayya bace, ke kanki kinsan ke kadai ke sonshi shi baya sonki"

"yana sona ummie, nina sani, kawai baya gwadawa ne"


"to meye amfanin soyayyar da ba'a gwadawa? Haka zakuyi ta yafiya Aysha, bazaki ta6a sanin dadin soyayya ba idan kuka cigaba da tafiya a Hakan, kuma juma'a mai kyau tun daga laraba ake ganeta, your marriage life depends on your love foundation"


Kada kai Aysha tayi sannan tace
"ki tayani da addu'a, naga message dinki na rannan and I decided zanyi yadda kikace, zan dinga addu'a allah ya za6amin mafi alhairi ko Umar ne ko bashi ba sa6anin da danake addu'ar allah ya mallakamin shi"


"Good, idan ma bashi bane ki roqi allah ya sassauta ko ya ciremaki sonshi gabadaya daga zuciyarki, komai mai yuwuwane a wajen allah, sai kiga abin yazama tarihi"


Kada kai Aysha tayi tana murmushi
"thanks, zanyi Hakan insha allah, nima bada son raina nake wasu abubbuwan ba Amma insha allah zan dage da addu'a, kema ki tayani"


Itama zee saita kadamata kai
"insha allah, ukhtie"


Murmushi sukayi atare

Buga tagumi Aysha tayi da hannu daya
"bani labari"


"labari? Labarin me?" inji zee


"labarin soyayyarki, daji zaiyi dadi naji kince he loves you so much beson ganin 6acin ranki"


Dan murmushi mai ciwo zee tayi ta maida hankalinta kan littafin gabanta

Dauke littafin Aysha tayi tace
"saifa kin gayamin, I love hearing love stories musanmman wanda akwai kulawa sosai aciki, tell me, waye very Lucky guy daya samu mallake zuciyarki"

Dariya zee tayi tace
"hmm is he really Lucky?"

"sosai ma, keta daban ce nasan shima nasan na daban ne, special people always spiced up"

Dariya zee tayi afili a zuciyarta kuma tana cewa
'yeah, he's special kamar yadda kowa na ahalinshi yake including you'


"inaji" inji Aysha tana qara buga tagumi

"to ni ta ina zan fara?"


"ki fara kota ina ne" tabata Amsa


"ok, bari nafara ta ranar damuka fara haduwa"

Gyara zama Aysha tayi cikin son jin labari fuskarta beaming with smile


"Ranar wata juma'a ce...."


Nan tashiga bata labarin soyayyarsu da Deen.

Komai ta gayamata babu abinda ta rage mata har takawo daidai ranar introduction dinsu saita tsaida labarin iya nan

"wow! So so romantic! Mutumin harya shiga raina, very cool guy dama ana samun irinsu a duniya?"


"why not? Gaki? Komai naku na hallaya iri daya, you're also cool kamar shi, inajin shi kika biyo" inji zee


Dariya Aysha tayi tace
"ta yaya xa'ayi na biyoshi? Mutumin dabamu hada komai dashi ba? Honestly speaking soyayyarku ta burgeni, dama mune Hakan"


Murmushi kawai zee tayi mata

"yanzu ankusa engaging din naku?"


Girgiza kai zee tayi ahankali

"ba'ayi ba? Wait ma, meyasa yanzu kike Dubai shikuma yana Nigeria?"


"Destiny" tafada ahankali tana kallon Aysha

Jikin Aysha ya danyi sanyi ganin yanayin datayi maganar

"bangane ba, where is he?"


"I don’t know either" tafada tana jin komai na dawomata sabo


"I don’t get you" inji Aysha cikin rashin fahimta


"he's.. Gone" tafada cikin murya mai sanyi

"on our introduction day... Ya tafi.. Wai maybe forever wai maybe not, Hakan ya rubuta a takardar daya bar min"


"Zainab are you crying?" inji Aysha ahankali


"nasaba, I do that everyday" tafada tana tsane fuskarta

"ina yatafi? Meyasa ya tafi?"


"I don’t know" tafada tana kallonta trying to control her emotion

"tell me, gayamin komai"


Shiru zee tadanyi sannan tace
"Ranar na wayi gari da matsanancin farinciki, I can't believe ranar family din Deen zasu zo suga nawa kuma mainly akan maganarmu, wannan tunanin nasani shiga shauqi marar misaltuwa

Ranar nayi wanka na zauna ina cancada kwalliyata ina humming best waqa ta ina tunanin izuwa lokacin suna can suna tattaunawa akanmu, kwatsam sai aka bubbugo kofata mummy tashigo rai a jagule..."


Nan tashiga bata kingin labarin da bata bata ba daga qin zuwan mutanen Deen har zirga zirgar da akayi tayi gidansu ana taddawa rufe, har zuwan ta da kanta, har bata wasiqarshi daya ajiye mata da akayi har collapsing datayi lokacin data gama karanta ta har farkawarta bayan kwanaki biyar, har rayuwar quncin data cigaba dayi daga lokacin har zuwan qanwar daddynta Nigeria da shawarar tahowa daita nan datayi har kawo yanzu (Saidai ta 6oyemata gano asalin Deen dasukayi dakuma dalilinta na zuwa school dinnan datayi)


Sosai labarin zee ya ta6a Aysha sai gashi itama tana hawayen

"why? Meyasa ya tafi?" tafada cikin hawaye

"I don’t know" itama zee ta bata amsa cikin hawaye

"yanzu dama kina cikin wannan yanayin? Bakiyi kama da mai wata matsala ba"

"yes, ba lallai bane nayi kama dame matsala ba physically amma idan kika ga zuciyata you'll cry for me, its still broken"


"sorry" Aysha tafada cikin tausayawa

Kada kai zee tayi batace komai ba sai tsane hawayenta data cigaba dayi

"kowa da irin qaddararshi, wataqila kema ba alhairi ne ba agunki"

"wataqila.." inji zee itama

"kinada pics dinshi? Inason ganinshi"


Gabanta yafadi, wai meyasa duk wanda taba labarin shi sai yace yana son ganinshi? Lallai akau ganinshi agareta bamai yiwuwa bane, not now.


"banida, duk na gogesu, babu abinda zanyi dasu kuma, hotonshi na cikin zuciyata ya isheni"

Kada kai tayi tace
"hakane, amma karki dora mashi laifi ummie, karki tsaneshi, allah kadai yasan dalilin tafiyarshi, don’t judge him please"

Murmushi kawai zee tayi sai tace
"I won't, dafarko naso yin Hakan amma daga baya da nasan wasu abubbuwa gameda shi sai nafara tunanin qila it's not his fault din"


"Me kika sani gameda shi?" inji Aysha

Murmushi zee tayi tace lakaci hancin Aysha cikin wasa

"zan gayamaki.. But not now, muje mu nemo wani abu dazamu sama cikinmu, am hungry" tafada tana shafa cikinta


Murmushi Aysha tayi tana tashi tsaye
"muje, nima kina fadin haka naji nima cikina yayi min warning alarm"

Dariya sukayi atare suka fita daga class din suna tafe suna fira cikin annushuwa


Daga ranar suka sake qullewa kamar da kai harma fiyeda da don sau da dama Aysha na bugowa ta hada zee da umminsu su gaisa, ranar farko da zee ta gaisa da Umminsu Saida taci kuka kamar zata shide

Ba mahaifiyarta bace amma taji wani iri sosai a zuciyarta kamar itace din bata ta6a jin muryar mahaifiyarta ba shekara da shekaru, muryar Ummin sak muryar Deen, very cool.

Aysha tasha tambayarta yaushe zatazo gidansu amma Saidai tayita yimata kwana kwana kullum da excuse din dazata bata harta haqura ta qyaleta


A bangaren soyayyar Aysha da Umar kau bata qara sanin yaya suke ciki ba don Aysha tabar waya dashi a gabanta, takuma bar bata labarinshi amma tasan confirm suna tare.


Watarana zee na zaune library da Aysha suna fira littatafai a gabanta da alamu ma karatu sukeyi suka zarce firar.


Wayar Aysha tayi beeping

Dauka tayi ta duba sai gani zee tayi fuskarta ta washe

Yar qarar murna tayi sannan ta jefa wayar cikin jakka ta miqe tsaye

"hey, meya faru?" inji zee

"zomuje zaki gani, I have a very huge suprise for you" tafada tana damqo hannunta

Tashi zee tayi tana bin Aysha dake janta
"wait, littatafanmu fa"

Sai a lokacin itama ta tuna, saurin tattarasu tayi ta jefa a jakka taqara Kamo hannunta
"muje"

"wai ina zaki kaini? Inji dai ba siyar dani zakiyi ba" inji zee cikin Dariya tana bin Aysha dake janta har lokacin

"eh mana, siyar dake zanyi kowama ya huta" Aysha tabata Amsa tana cigaba da janta

Dariya zee tayi tace
"ko duniyar nan aka tara basu sayena yarinya"

"kima godewa allah idan kika samu aka tayaki Riyadh 100" Aysha tabata Amsa suna nufar harabar school din

"kutt... Nafi qarfin haka yarinya kema kin sani"

"ok just wait and see, zakisha mammaki"


Cigaba da jan hannunta tayi suna tafe suna fira suna Dariya har suka qaraso parking space din


"Akhie!!!" Aysha tafada da qarfi cikin yar muryarta tasaki hannun zee data ja burki babu shiri tanufeshi da sauri


Juyowa yayi daga basu bayan dayayi yana waya daidai lokacin da Aysha ta fado ajikinshi

Cak komai nata ya tsaya dasukayi ido hudu dashi kamar yadda shima a 6angaren shi komai nashi ya tsaya Cak a sanadin ido hudun dasukayi da wanda be ta6a tsanmmanin gani ba


_the girl_... ✍️


Ummin fasihu 🧚🏻‍♀�
8/2/21, 9:41 PM - Buhainat😝: *🙍🏻‍♂️DEEN 🙍🏻‍♂�*


*066*


*THE GIRL 2*


Jitayi kamar Kaffafuwanta na narkewa ahankali, sotake ta juya da sauri tabar wajen amma kaffafunta sunqi bata hadin kai


"Akhie, ashe dagaske zakazo? Banyi tunanin dagaske kake ba da kace zakazo, am very happy wlh" inji Aysha cikin tsananin jindadi

Ganin kamar hankalinshi ma ba akanta ba yake yasa ta juya tana kallon inda yake kallo


Dan buda idanu tayi saikuma tayi Dariya

"Akhie, gatanan, itace wanda naketa baka labari, my bestie... Ummie meet my brother"


Kasa cewa komai zee tayi saima sauke idanunta datayi aqasa jin yadda nashi ke yawo akanta Dukda idanuwan nashi toshe suke da shade as usual

"oho? Wannan ce bestie din taki da kike bani labari?" inji Mussadiq yana daga gira daya sama

"eh yaya, itace" inji Aysha cikin jindadi


"wow, tanan kenan ta 6illo, taga wancan hanyar babu riba shine ta biyo tanan" inji Mussadiq yana mata wani kallo


Zee da gabanta keta faduwa ta dago ta kalleshi, tama rasa abinda zatayi ko zatace


"I don’t get you Akhie" inji Aysha cikin rashin fahimta


"ita ai ta gane.. So miss spy tanan kika 6illo kuma?" yafada yana maida akalar Tambayar ga zee


Kasa cewa komai tayi still sai kallonshi datake tanason lalubo abinda zata fada amma it seems kwalwarta ma ta daina aiki na wucen gadi


"Yaya wai yaya kake wasu magangganune da bama fahimta?"

"kece bakya fahimta my dear little sis, ita karr take. Dafarko kinzo min a suffar almajira kinzo kinamin kuka kina min yaren da bana ganewa a tunaninki am so dumb da zan fada tarkonki, da Hakan beyiwu ba sai kika chanza dabara kika biyoni wancan supermarket din kina min la6el, shima da kika ga babu riba sai kika biyo ta innocent sister dita ko?"


Tunda yafara magana zee ke girgiza kanta hankali tashe Saidai still bakinta yakasa buduwa bare tayi qoqarin kare kanta


Cire shade din idanunshi yayi ya matso dab da ita

"for the last time who are you?" yafada cikin low but dangerous voice


Matsawa baya zee tayi tana kallonshi shima a idanu jikinta na rawa

"I said who are you!" Yafada da tsawa tsawa


"Akhie?" inji Aysha datayi saurin shiga tsakiyarsu

"meye haka yaya? Dama ka santa ne?"

"ita zaki tambaya, wai Aysha why are you too dumb, I warned you akan yin abokai, didn't I?" yafada a fusace


"you do, amma nima ai bana abokai, wannan kadai ce.."

"shut up kafin na wankeki da mari! Cewa nayi never make a friend bance Kiyi ko daya ba, saboda I knew you're too dumb to know who your enemies are"


"yaya wannan fa babu ruwanta, bama yar qasar nan bace, she's From Nigeria, sunan Umminmu gareta, itace ta tsintar min Bracelet dina, da ita muke maths lesson har nake gane wasu abubbuwan, she's very nice kuma she's there for me akan komai"


"oh? Kema sunan Ummin tace maki sunanta?"


Saikuma ya nufi zee daketa raba idanu Tundazu a fusace

"who are you?!" Yafada yana Kamo wrist din hannunta

Fara qoqarin kwacewa tayi amma takasa

"of all lies dakikeyi babu wanda yafi 6ata min rai kamar liqama kanki pure sunan mahaifiyarmu dakikeyi don kisamu shiga awajen mu, who the hell are you?!"


"let go of my hand!" zee tafada tana qwace hannunta Dakyar daga riqonshi, idanunta har sun duri ruwa


"yar Nigeria? Dama Nigeria is full of corrupt people, Saidai albishirinki, acan ne zakayi abu kaci bulus ba anan ba! Anan din ma ba irina ake ta6awa ba atafi scot-free! Da alama wadanda ke turoki sunsan ko ni wanene kece baki sani ba shiyasa su suka kasa zuwa wajena Saidai su turoki, amma kema zan tabbatar kinsan ko ni wanene!"


"ni babu wanda ya turoni, nafada maka Hakan can baya, yanzu ma na fadi Hakan kuma ko gobe muka sake haduwa Hakan zan fadamaka!"

"ni kike ma tsawa?!" Yafada yana charging towards her Aysha tayi saurin shigewa tsakiyarsu again


Dayake ruwa ruwa ce itama har idanunta sun duri ruwa

"Akhie wai meye haka? Ummie dama kinsanshi ne?" tafada tana maida akalar tambayar ga zee


Girgiza kai tayi sai kuma ta shiga Kada kai, duk ta rude

"look Aysha, n.. Na ta6a ganinshi a wani supermarket, I.. I mistook him for someone, nayi tunanin wani ne dana sani shiyasa nayi mashi magana.."


"a lokacin idanuwan ki sun daina aiki ne? Koko kwalwarki tasamu matsala ne dahar zanyi miki kama da wani, Hakan yasa har kika zube a qasa kika kama kaffafuna?"


Runtse idanunta tayi gam tanajin zuciyarta na wani irin zafi kamar ana gasamata ita a oven

Wasu zafaffan hawaye suka silalo ta qasan ruffafun idanunta

"Are you crying? Save that crocodile tears, kibari sai kin ganki behind bars sannan" yafada yana watsamata wani mugun glare


Bude idanunta tayi akanshi dasukayi jajur sannan ahankali cikin qunar rai tace
"yes, a lokacin na zube a qasa nakuma kama kaffafunka but had it been nasan kaine ko kallo bazaka isheni ba"

Daga cikakkiyar girarshi daya yayi cikin yimata kallon raini hankali

"really? To kinsa wanene da? Kuma dukda kin gane bani bane din kika biyoni wancan supermarket din kika yimin la6el, can you also explain that?"

Izuwa lokacin zuciyar zee ta harzuqa matuqa, ita macece da bata qaunar wulaqanci ko yaya ne gashi ta lura wannan gayen ya matuqar qwarewa a wannan fannin

"speak!" Yafada da qarfi yana yi kamar zai qara matsowa inda take cikin barazana


Kallonshi tayi cikin fushi tace
"you know what? Go to hell! I owe no one any explanation! Idan guntun qwalwarka tabaka kai nake bibiya so be it!"

"what! Ni kike cewa I should go to hell?!" Yafada cikin tsananin 6acin rai don fuskarshi tafara ja ja ja ja din 6acin rai

"Akhie please... Ummie Kiyi shiru please" inji Aysha da duk suka rudata

Batayi shirun ba sai cewa da tayi
"Go to hell nace? That's not what I mean, I mean go to hell and burn to ashes!"


"what!" Yasake fada cikin qurewar 6acin rai

"albasa batayi halin ruwa ba! Kai ke kama dashi ba shike kama dakai ba, kuma kamar ta fuskace don shi yanada pure heart ba kamar naka black coal heart ba!"

Saurin Runtse idanu tayi ganin ya daga hannu zai kawo mata mari

Itama Aysha ganin Hakan yasa tadanyi qara ta Runtse idanunta gamm


Shiru sukaji Hakan yasa suka shiga bude idanun ahankali har suka budesu tarr a kansu


Mussadiq ne tsaye Hannunshi maqale a iske wanda ya daga da niyyar kashe zee da mari

Kallon wanda ya riqe hannun a iska sukayi wanda shima mussadiq yake kallo idanunshi na chanza launi

"yaya Aymaan!" zee tafada cikin kuka tana rugawa bayanshi ta kama dayan hannunshi dayake free ta kifa kanta akan kafadarshi tana kuka mai cin rai


Yarfar da hannunshi Aymaan yayi yana Binshi da wani kallon tsana da kishi

"kasan wake daga hannu akan mace da niyyar duka? DABBA!" Yafada cikin tsananin 6acin rai


Shima Mussadiq kallonshi yake cikin tsananin 6acin rai wanda har kana ganin yadda broad chest dinshi ke sama ke qasa ta spotless white shirt dinshi

"Did you just call me an animal? Did you just insult me?!" ya tambaya yana kallonshi eye-in-eye

"I don’t insult people, I just describe them" inji Aymaan shima yana kallonshi cikin ido

"you brat!" inji mussadiq yana tunkaroshi mugun hasale

"who do you think you are?!" Yafada yana kai mashi blow Saidai this time around Aymaan was too quick wajen tarewa

"karka soma, wancan karon kaci bulus saboda wadannan kartin banzan dake zagaye dakai, yanzu kuma your empty brain yakamata ya sanar dakai kai kadai ne"


Fizge hannunshi yayi a fusace yasa hannu ya tura qirjinshi wanda Hakan yasa yadanyi baya

Shima rai a 6ace ya nufoshi shima ya tura qirjinshi da qarfi wanda Hakan yasa shima yin baya

Saurin riqo hannunshi Aysha tayi tana kiran sunanshi itama zee ta riqo hannun Aymaan dake niyyar tunkararshi again


"please Aymaan mutafi, ka kyaleshi" tafada tana qara qanqame hannunshi ganin yadda yake qoqarin kwacewa


Itama Aysha kama hannun mussadiq dake son zuwa wajen Aymaan tayi ta qanqame idanunta taff hawaye tana cewa
"Akhie ka kyaleshi, don Allah"


A daidai nan wasu mutane hudu cikin mufti suka iso wajen


I.D card din dasuka nunama su Aymaan yasa suka gane jami'an tsaro ne

Hankalin zee yasake tashi

"you're under arrest" inji daya daga cikinsu yana kallon Aymaan

Fizge hannunshi yayi daga riqon zee a fusace yace
"saboda me? Me nayi?"

"idan munje station zakaji dalili, a shawararce zaifi kyau kayi shiru ka Adana duk abinda zakace har saimunje station don duk abinda kace yanzu will be use against you in the station"


Hankali a tashe zee tace
"sir, ba laifinshi bane, you guys should listen"

"sorry ma'am, aikinmu mukeyi"

Sannan suka maida kallonsu akan Aymaan da yakejin wani abu mai wuyan wucewa ya tokaremashi wuya

"shall we?" suka fada suna nuna mashi hanya

Hannu yasa a aljihunshi ya zaro I.D card dinshi shima yace
"Dr Aymaan, gynaecologist a As-shifa'u specialist hospital.

Zan biyoku amma a motata"

"No.."

Sukaji ance a bayansu

Juyawa sukayi sukaga mussadiq ne da haryanzu fuskarshi ke jajur

Zuwa yayi gaban Aymaan yana kallonshi eye-in-eye

"bazaka tafi a motarka ba, su zakabi"

"nafison idan ina magana da masu hankali kar mai empty kwalwa yayi min trespassing, na tsani shiga muhallin daba na mutum ba" inji Aymaan shima yana kallon cikin idonshi


"zan nuna maka, zan nuna maka ni cikkaken marar hankalinne.. Arrest him!" Yafada authoritively


Zee ce ta matso gaba
"kaga, dani kakeda case bada shi ba, idanma arresting dinne ni za'ayi arresting"

"in that case... A hada da ita" yafada yana maida shade dinshi a idanu sannan ya juya


"Akhie!" inji Aysha cikin tashin hankali amma ko tsayawa beyi ba bare ya kalleta

"let's go please" inji daya daga cikin jami'an yana nuna musu hanya


Juyawa sukayi babu musu suka shiga binsu suna a tsakiyar su


"ummie!" inji Aysha dake kuka sosai saikuma ta ruga wajen mussadiq daya shiga motarshi

Saurin kama murfin motar tayi
"Akhie please ka tsaidasu, gasucan zasu tafi da..."

Kallon daya watsamata yasata kasa cigaba da maganar sai rufe bakinta datayi da taffukan hannu tana cigaba da hawaye

"get in" yafada in a low but angry voice

Bata motsa ba sai kukan data cigaba dayi

"I Said get in!!" Yafada cikin qaraji wanda yayi mugun firgitata

Batasan sadda ta zagaya ba ta bude dayan murfin tashiga ta zauna tana sobbing


"ki yimin shiru kafin na karkaryaki!"

Babu shiri tayi tsitt sai hawayen dasuka kasa tsaiduwa


A fusace ya tada motar yaja a 360


Ta glass din gaba Aysha ta hangi su zee na shiga motar dasu jami'an sukazo daita


Fitt sukazo suka wucesu sanadiyar gudun da sukeyi suka fice daga makarantar

Itama motar dasu zee ke ciki ta maramasu baya suma suka fice daga makarantar


Aysha ta baya take Juyawa tana kallon motar dasu zee suke ciki, suna kaiwa wani junction sai taga Motarsu zee ta kama wata hanya daban da wanda suke akai sun wuce


Juyowa tayi ido taff hawaye da niyyar yima mussadiq magana Saidai yanayin fuskarshi yasa takasa cewa komai sai hadiye yawun datayi ta koma ta lafe a kujera tana matsar hawaye


Basu dade ba suka shigo unguwarsu kasancewar ba qaramin gudu yake falfalawa ba akan titin don Hakan na daya daga cikin dalilin da yasa ummie bata barin yayi tuqi da kanshi dole saita hadashi da mai tuqashi don kwata2 be iya tafiya ahankali, on normal days dayake cikin Good mood ma ya aka kaya bare yanzu da ranshi ke a 6ace


Kallo daya zaka yima unguwarsu kasan ta shahararrun masu kudi ne don ko street din wajen ka kalla shikadai saiya baka amsa


A kofar wani tangamemen gate mussadiq ya taka burki wanda Saida sukayi gaba ba don seatbelt dake jikinsu ba da sai sun daki gaban motar


Horn ya danna mai irin mugun tsawon nan don tunda ya danne be daga hannu ba har Saida aka wage tangamemen gate din don ko ba'a fadama securities din ba sunsan shine don dama sun haddace salonshi

Dagudu wasu securities din suka nufo motar da har lokacin bata shiga ba dukda anriga da an bude gate din

Juyowa yayi ya kalli Aysha dataci kukanta ta qoshi sannan cikin Hade fuska yace
"ukhrujj!"

Dan kallonshi tayi sai tadan share hawayenta da bayan hannu ta sa hannu ta bude kofar tafita

Wining glass din wajenshi yayi Hakan yasa securities din qara matsowa suna kwasan gaisuwa

"karku bari tasake fita!" Yafada cikin bada umarni

Cikin sarawa suke amsawa da angama

Be qara sauraronsu ba yafara dage glass din

Daya daga cikin securities din yayi qarfin halin cewa
"erm.. Yalla6ai ko nashigo na tuqaqa naga kamar ka gaji"


Ko kallo be isheshi ba ya ida dage glass din yayi reverse da qarfi yaci taya sannan ya wuce da mugun gudu


Duk bin motar securities din sukayi da kallo cikin zullumi don tabbas sunga ranshi a 6ace yake kuma tuqi a gareshi a wannan yanayin ba abu mai kyau bane, haka suka juya suka shige cikin gidan suma don dama Aysha tana sauka tashige gidan Dagudu tabarsu nan.


Maimakon akaisu police station sai aka kaisu headquarter ta c.i.d bisa umarnin Sir mussadiq


Saida aka amshe wayoyinsu sannan aka shiga dasu wani daki mai kama da office Saidai it's empty dai wani dogon desk da kujeru dake kewaye dashi


Dafarko cewa akayi su zauna aka tafi aka barsu nan, zee banda hawaye babu abinda takeyi, shikau Aymaan kawai zama yayi ya jingina da kujera yayi folding hannayenshi a qirji yana karkada kafaffu shikadai yasan abinda yakeji a zuciyarshi ga sniffing da zee keyi akai akai dake qara dagula mashi lissafi, gashi yakasa rarrashinta don bayajin ko magana yana iya yi a wannan lokacin


Suna ahakan wasu ma'aikata biyu suka shigo suma cikin kayan gida suka zauna a kujerun dake facing dinsu

Gyaran murya daya daga cikinsu yayi sannan yace
"zamu iya sanin sunanka?" yafada yana kallon Aymaan da ko kallo mutumin be isheshi ba

"magana muke" mutumin yaqara fada

I.D card dinshi na dazu yasake Ciro wa ya turamashi a gabanshi


Dauka mutumin yayi ya duba suka kalli juna da dayan mutumin sannan mutumin ya maida kallonshi kan zee

"kefa? Zamu iya sanin sunanki?"

Qara sniffing tayi sannan tace
"Zainab"


"to malama Zainab da mallam Aymaan kunsan akan me ake tuhumarku?"


Shiru sukayi

"akan spying, mai girma sir mussadiq yana zarginku da bibiyarshi wanda yana alaqanta Hakan da leqen asiri ko mugun nufi da aka saba yiwa manyan yan kasuwa irinshi, me zakuce gameda Hakan?"


Nan ma shiru

"munaji" inji dayan mutumin

Aymaan ne ya kallesu for the first time tunda suka shigo

Kamar bazaiyi magana ba sai ya motsa baki Dakyar yace
"zakuyi magana da lawyer na"


Kallon juna mutanen biyu sukayi sai suka sake kallonshi

"munsan da lawyern naka ai, yanzu kai muke tambaya tunda ku abin ya shafa ba lawyern ba" inji dayan, kana iya jiyo 6acin rai kadan a muryar

"zakuyi magana da lawyer na, that's it" yasake fada firmly batareda ya kallesu ba

Kallon juna suka sakeyi, ba don sir mussadiq yace kar ata6asu da babu abinda zai hana daya daga cikinsu fallamashi mari, babu abinda yafi basu haushi kamar yadda yake masu magana a gadarance

Kada kai na farkon yayi sannan ya kalli dayan cikin harshen larabci yace mashi sutafi sai suka tashi suka fita daga wajen suka qara barinsu alone


*AYSHA*


Dagudu tashiga cikin qaton gidan, harabar gidan ba dai girma ba gashi qasan shimfide yake da kwalta ga flowers of different types shufke a gefe gefen titin


Tayi tafiya mai nisa koko ince gudu mai nisa kafin ta isa maid entrance din gidan

Saida kofar tayi scanning face dinta sannan ta bude tashige ciki

"Ummie!" tafada cikin daga murya tana shiga makeken falon daya qawatu da kayan alatu ga tattausan carpet da duk takawa daya zakaji kamar zaka nutse aciki don taushi da laushi


Sama tanufa tafara hawa stairs din da shima kanshi abin kallo ne da gudu

Kasancewar stairs din mai lanqwasar maciji ne Saida ta dauki lokaci kafin ta qarasa saman

Wani qaton falon taqara cin karo dashi shima mai mugun kyau ta wuceshi sannan tashiga passage din dazai sadata da dakin Ummie


Koda ta qarasa kofar dakin ummie banda haki babu abinda takeyi don tasha gudu ba qarya

Bubbuga kofar dakin tahau yi da qarfi qarfi

Can aka bude kofar wata maid ta bayyana

Russunawa tayi tana gaidata Saidai har tayi gaba tashige cikin dakin


Wata mata dattijuwa na hanga zaune bisa tattausan carpet gefe kuma irin pillow dinnan ne masu kyau zagayayyu irin wanda akafi gani mostly a gidajen sarauta ta kishingida akai, plate a gabanta cike da yankakkun fruits wanda take dauka da daddaya tana ci


"Ummie!" Aysha ta qara kiran sunanta tana nufota

Saurin dagowa matar tayi ta kalli saitin Ayshar

_Tsarki ya tabbata ga ubangiji mai hallitu_ (abinda nafada kenan a raina don sak fuskar Deen nake kallo a gabana, kawai banbancin shine wannan mace ce kuma tadan manyanta)

Qarasowa zee tayi ta fada jikin Ummie taqara Fashewa da wani sabon kukan

"subhanallilah! Ya bunatie, meya faru?" tafada a rude tana tashi daga kishingiden datake

Cigaba da kukanta Aysha tayi tana qara qanqame Ummin

A rude Ummie ta cigaba da Tambayar Aysha meya faru cikin harshen larabci hankalinta duk ya tashi, tuni maids din dakin suka shiga sulalewa daya bayan daya suna fita


Dakyar Aysha ta samu ta tsagaita kukanta, cikin larabci tashiga cewa
"Ummie, yaya ne"

"yaya? Meya faru dashi?" ta tambaya hankali tashe

Girgiza kai Aysha tayi tace
"kawai daga zuwa saiyasa aka kama bestie ta da ita da yayanta akaje aka kulle" tafada cikin kuka


"aka kulle? Bangane ba"


"Ummie, wannan qawar tawa danake baki labarinta? Itace yau yaya yazo school don ya ganta don kodayaushe cikin matsa mashi nakeyi yazo ya ganta shine yau yazo amma daga zuwa sai suka kama fada wai spy ce tana spying dinshi ne wai don ya ganta wasu wuraren kafin nan, shine ita tace ba spy bace shine yaji haushi zai mareta sai yayanta yazo From nowhere ya tare sai fadan yakoma kanshi sai yasa aka kamasu aka kulle"


Tunda tafara maganar ummie bata fahimci ko kalma daya nata ba din a dunqule take bata labarin Hakan yasata zama so confused

"look Aysha, ki nutsu. Ki fadamin komai cikin kwanciyar hankali yadda zan gane"

Kada kai Aysha tayi tana share hawayenta da bayan hannu

"to ina jinki yanzu, wace qawarki kike cewa?"

"wannan wanda nake baki ku gaisa?mai sunanki"

Kada kai ummie tayi cikin gamsuwa
"eh nagane, takwarata? To meya faru?"


Cikin nutsuwa Aysha tashiga bata labarin abinda yafaru From A-z


Ajiyar zuciya ummie ta sauke tana dan dafe kai

"ya sallam, yanzu shikenan duk wanda ya ra6eka yazama abokin gabanka? Wannan wane irin hali ne ga bunnaya?" tafada cikin rashin jin dadin abinda yafaru

Qara share hawayenta Aysha tayi tace
"ummie nayi qoqarin fahimtar dashi itama tayi qoqarin fahimtar dashi amma yaqi ya saurari ko daya daga cikinmu, ita batama san shine Mussadiq al-hassan ba, batasan status dinmu ba don ban ta6a gayamata ba kawai nadai bata labarin mu ne in a simple way bance nice qanwar mussadiq al-hassan mai companies din Nurul-haqq ba, tayaya to zatayi mashi leqen asiri mutumin da batama sani ba, ni babu abinda yafi dagamin hankali kamar idan na tuna yanzu haka suna can kulle" tafada cikin kuka


"kiramin shi a waya, wannan abin nashi yafara wuce gona da iri, shikenan kowa saiya dora mashi alamar zargi? Soyake ya hana kowa mu'amalla da kowa kamar yadda ya hana kanshi? Kiramin shi"


"ummie kinsan bazai daga ba, ki kirashi da wayarki zaifi saurin dagawa"

"miqo min ita gatacan bisa cushion, wai ina ma yake shi?"

Aysha data tashi da sauri zata dauko ta amsa da
"ya dai ajiye ni yatafi"

"badai gudu yake ba kamar yadda yasaba, ya tafi da driver?"

"bana tunanin Hakan, can dai shikadai yazo"


Amsar wayar ummie tayi daga hannunta tayi dialing din number ta kara a kunne


Ringing daya biyu aka daga

Daga can 6angaren sukaji muryar mussadiq yana cewa
"Aslm alaiki ya ummie"

Dan Hade fuska ummie tayi wanda yayi mugun yimata kyau kamar dai yadda Deen keyi
"wslm, ina kake?"

"ina wani aiki ne ummie"

"wane aiki? Aikin kama mutane da basuji ba basu gani ba?"

"Ummie waya..."

"kazo kasameni gida yanzu yanzunnan, fatan kajini" tafada in warning

Cikin amsar umarni yace
"to Ummie"

Katse kiran ummie tayi sannan ta cigaba da kwantar ma autar tata hankali akan ta kwantar da hankalinta komai zai warware


Sai gashi ko minti tallatin ba'ayi ba ya iso gidan

"bunnaya, me kake so kazama ne? Shikenan kowa ma abokin gabarka ne? Shikenan kowa ma bazai ra6eka ko ya ra6i wani naka ba? Wannan wane irin aqida ne?"


"ummie mutane ba abin yarda bane, maqiyi bazai fito da pasta manne da goshi na rubutun shi maqiyinka ne, kowa na iya zama maqiyinka"

"kai shikenan baka kyautatawa kanka zato? Kalleka.. Bakada aboki ko daya saboda rashin yarda, yan uwanka ma baka zuminci dasu yadda ya kamata, kowa.. Kana iya yiwa kowa kallon maqiyi.
A dalilin Hakan yasa baka bayyana kanka, anfi sanin sunanka fiyeda kai kanka, yan tsiraru kawai suka sanka, kana iya zuwa wuri kayi hidimarka kafita ba'asan dakai ba Amma dukda Hakan zargin kowa kake, anya wannan hanyar daka dauko mai 6ullewa ce?"

Shiru yayi

"Nan gaba waya sani qila har muma zargin mu zaka dinga yi, a dalilin wannan halin naka ko budurwa baka ta6a yi ba, ga yanmata nan masu sonka a cikin families dama abokan arziqi amma kai bama ta aure kake ba, mussadiq nima inason ganin jikana, inason ganin jininka dana Aysha kafin na mutu dukda ita mutuwa bata ga babba bata ga yaro saita dauki yaro tabar tsoho amma ai ko babu komai anfi sama babban ran fara tafiyar, mussadiq Koda banga 'ya'yanku ba zanso ganin auren ku"

Jikin mussadiq yayi sanyi, dama haka yake kuma ummie tasan lagonshi data ambaci mutuwa sai komai nashi ya sure, ya tsani ummie takira ma kanta mutuwa sai yaji kamar da gaske din tafiya zatayi ta barshi kamar yadda mahaifinsu da dan uwanshi sukayi

Dagowa yayi ya kalli ummie
"ummie kibar fadin haka don Allah"

"to ai Gaskiya ce bunnaya, kowanne mai rai saiya dandani mutuwa, kuma ita wannan yarinyar ni kaina na santa don muna Gaisawa da ita ta waya, da ba alhairi bace ba agareku da naji Hakan a jikina, tun magana ta daita ta farko ta kwanta mun, be kamata kome yazo kanka ka yanke hukunci dashi ba"

"ummie sau uku kenan nake haduwa daita..."
Nan ya fayyace musu yadda duk haduwarsu ta kasance

"bunnaya, akwai coincidence, bayan Hakan wata haduwar ta allah ce kuma alhairi ce, ta yiwu allah keta hadaku wataqila yanada wata manufa akanku amma kayi bincike, abinda ya kamata kayi kenan tun farko bawai kaita zargi ba"

"nafara, yanzu haka school din nakoma nasa an daukomin file dinta, muna tsaka da Hakan kuka kirani"

"yauwa, bincike ya kamata kayi saika kamata dumu2 da hujjoji sannan zaka yanke hukunci bawai ka yanke hukunci akan zargi ba
Yanzu kasa a sallamesu ka kuma basu haquri inyaso sai ka cigaba da binciken ka akansu

Insha allah babu wani mugu dazai ra6eku, kodayaushe kuna cikin addu'o'ina dare da rana, kuma zaku cigaba da kasancewa cikin addu'o'ina, insha allah babu mugun dazai ra6eku"


Kada kai mussadiq yayi cikin gamsuwa


Cigaba dayi musu nasiha tayi mai ratsa jiki kamar yadda tasaba yimasu sannan ta sallami mussadiq akan yaje yasa asake su.


***


A can gidansu Aymaan kau hankalinsu duk ba a kwance ba, driver yaje daukar zee Saidai batanan, duk inda ake saka ran ganinta a fadin makarantar ba'a ganta ba

Ga shima Aymaan wayarshi bata shiga kamar dai ta zee

Kuma sun kira Ahmad sun sanar dashi yaje asibitin ance shima ya dade da fita

Haka dai Ahmad yaita yawon nemansu musanmman ma zee da ba koina tasani ba a garin, ga numbobinsu basa shiga Hakan yaqara dagula masu lissafi.


*AYMAAN/ZEE*


Suna zaune Jigum Tundazu abin duniya ya ishesu musanmman zee take jinta a matuqar takure

She can't believe wai yau ita aka rufe a custody dukda ba irin wannan rufewar bace ta wulaqanci

Tunda nan Wajene mai tsafta ga fili ga fresh air don akwai fankoki masu bada iska sosai aciki ga abinci mai kyau da aka basu Tundazu wanda haryanzu babu wanda ya kalleshi gashi babu duka babu zagi don tunda mutanen nan suka fita banda wanda yakawo musu abinci babu wanda yaqara Shigowa

Saidai kullewa kullewa ce Koda a cikin gidan aljannar duniya aka kulleka, dole wannan right of movement din da aka tauyemaka ya dameka


A 6angaren Aymaan kau abin yafi 6ata mashi rai, shi ba kulleshi din ba yafi 6ata mashi rai wanda yasa aka kulleshi dinne

Gani yake bekai wannan matsayin ba, gani yake qasqanci ne Hakan mutum kamar mussadiq yasa a tsareshi dukda kau yasan ya isa yasa ayimashi fiyeda Hakan ma kuma ayi din babu yadda ya iya

Amma ya rasa meyasa tun haduwarsu ta farko yaji baya son gayen, yana jin haushinshi fiyeda tunani shiyasa yake ganin tsareshi da akayi ta dalilin shi ba qaramin qasqanci bane a gareshi


Suna ahaka sukaji ana bude kofa


Babu wanda ya dago acikinsu bare ya kalli mai shigowar


"kuna iya fitowa" inji wanda yashigo din

Dagowa sukayi atare suka kalli mutumin sai kuma suka kalli juna da alamun tambaya

"you're free, zaku iya fitowa"


Wata nannauyar Ajiyar zuciya zee ta sauke tana jin sanyi a zuciyarta shikuma Aymaan yadan ta6e baki alamun ko ajikinshi


Atare suka tashi suka fito

Ce masu yayi su biyo bayanshi sukayi yadda yace harya kaisu wani office daban

Ce masu yayi su shiga suka shiga shikuma yafito ya rufo kofar yayi tafiyarshi


A tsaye yake jikin window yana kallon waje ta window din hannayenshi zube a aljihunshi


Wani qululun baqinciki ya sake tokare Aymaan, da yasan shi zasu gani a office dinnan da babu abinda zai sashi Shigowa


Ahankali mussadiq ya juyo yana kallonsu still hannayenshi zube a aljihu


Shiru ya ratsa dakin na wasu daqiqu babu mai uhm bare uhm uhm


Can saiya tako ya dawo kusada wani table din office din yadan jingina dashi yana dora hannu daya akan desk din


"seems yau ma is a Lucky day for you guys, Saidai rana 99 na 6arawo rana daya kuma na meshi, ku tafi amma idan kere na yawo zabo na yawo zasu hadu Saidai ku kuji haduwarmu ta gama don it gonna be worst"


Atare suka ta6e baki kamar hadin baki

Aymaan na shirin magana zee ta rigashi

"a juri zuwa rafi dai, kuma am assuring you wannan tsaremu dakasa akayi na few hours saikayi regretting dinshi, saiyasa watarana ka kasa hada idanu damu

Mutum darajja gareshi kowanne mutum da baiwar da allah yabashi wanda sai an taqa zai gane Hakan

Kayi amfani da matsayinka ka tsaremu, to kajira ranar da kai kanka kunyar kanka zaisa ka kasa daga idanu ka kallemu straight in the eyes kamar yadda kayi yanzu

A lokacin zaka gane arziqi is nothing don arziqin besa kasamu abinda wadanda ka wulaqanta suka samo maka ba, a lokacin zaka gane kowama da ranarsa kuma gamewar bazata amfaneka da komai ba don it's like crying over a split milk"


Aymaan ne yadanyi murmushi
"haba lil sis, meyasa kike 6ata yawun bakinki har haka? Magana ta hankali mai hankali ake yimawa don shi zaifi ganewa, it's better Kiyi saving din yawunki mai daraja for something more valuable"


Takowa mussadiq yayi gabansu ya tsaya yace
"kamar yadda nafada dazu, you guys are very Lucky, shiyasa har kukeda damar maida yadda akayi yanzu, amma ku guji ranar da Luck din xaibar side dinku cos you'll regret it. Kuna iya tafiya tun kafin Luck din ya fece yabarku tun yanzu"


"kai kalmar Lucky ta cancanta don albarkacin wani kakeci da nasa akowanne daqiqa ka dinga tuna ni cikin qunar rai amma unfortunately bazan iya ba saboda darajar shi dama mai daraja akecin darajar shi" inji zee


"out.. Kun isheni da hayaniya and this is not market, so out!" Yafada yana nuna kofa

"ko baka fadaba, amma ka tuna zuru batacin zuru" inji Aymaan sai ya kama hannun zee suka juya suka fita daga office din suna maido mashi kofar da qarfi


Bïñ kofar yayi da kallo sannan ya sauke Ajiyar zuciya yakoma ya zauna bisa kujerar Wurin mai jujjuyawa yafara jujjuyawa


_the girl_


Meyasa presence din yarinyar kesashi jin wani iri, absence dinta ke dada jefashi wani hali

Meyasa yakasa mancewa da ita tun haduwarsu ta farko

Meyasa yakasa mance fuskarta tun a gani na farko?


Shi ba mutum bane mai yawan maida kai ga kammanin wani musanmman mace amma sai gashi ita tun a ganin farko kwalwarshi tayi capturing face dinta

A haduwa ta farko bayan ya warwatsa mata kudade ajiki yayi tafiyarshi yaji wani yanayi marar dadi kamar yasa ajuya ya koma wajenta


A haduwarsu na biyu ma bayan yatafi yabarsu da cashier gab da zasu sha kwana ya juyo yana kallonta Daga nesa suna barin wajen, nan ma Wannan feeling din yaji kamar ya tsaidata kamar yakoma wajenta


Yanzu ma basu ida fita ba yaji kamar ya dakatar da ita inda Koda dakatar da itan yayi besan me zaice mata ba


Menene Hakan to?

Meye ma'anar Hakan?... ✍️


Ummin fasihu 🧚🏻‍♀�
8/2/21, 9:41 PM - Buhainat😝: *🙍🏻‍♂️DEEN 🙍🏻‍♂�*


*067*


*THE UNVEIL*


Fitowa sukayi harabar wajen suka nufi hanyar gate


Aymaan kanshi na kan wayarshi da aka maido masu abinsu dazasu fita yana kunnata

Babu dadewa ta kunnu yashiga contact ya lalubo number Ahmad yayi dialing


Ringing daya biyu aka daga

"ya sallam Aymaan ina ka shiga? Na nemeka kamar zan zauce.." abinda Ahmad yafara dashi kenan yama manta da sallamar


"hmm, ai gashi yanzu kajini ko? Kana ina?"


"ganinan nadawo gidanku daga yawon nemanku, kasan kau zee ta 6ata?"


Dan murmushi Aymaan yayi ya dan kalli zee dake kallonshi shima saita Janye nata idanun


"gamunan tare, kazo ka dauke mu"


Jin sallalamin su ummy da ihun murnar batool yasa yadan Janye wayar daga kunnenshi kadan


"dagaske? Amma kai dan air ne, ina kuka shiga munata neman ku harda hadawa da police station?"


"kazo c.i.d headquarter ka daukemu" be jira amsarshi ba ya katse kiran


Sake kallon zee yayi yaga bashi take kallo ba Amma ta kare goshinta da hannunta saboda hasken rana


Juyawa yayi yaga wasu kujeru qasan wani tent saiya kalli zee yace
"muje can mu zauna mu jirashi"


Kallonshi tayi kamar zatayi magana saikuma tafasa suka wuce inda yace din suka zauna


Shiru wajen ya dauka na wani lokaci

Can zee tadan muskuta wanda Hakan yasa Aymaan Dagowa yana kallonta

Batareda tabari sun hada idanu ba ta fara cewa
"Am sorry.."


Shiru yayi yana kallonta Hakan yasa ta dago idanunta itama ta kalleshi

"for what?" ya tambaya yana kallonta cikin ido


Sauke nata idanun tayi sannan ahankali tace
"I caused it all, duk ni naja komai"


Murmushi yayi mai kyau yace
"bake ya kamata kibada haquri ba.. Nine.

Am sorry nakasa hanaki zama a tsare for some hours"

Dagowa tayi tasake kallonshi cikin wani yanayi sai ta girgiza kai

"nice najamana, naja maka tsarewa na wani lokaci"

Murmushi yayi ya kalli gate daga inda yake zaune

"I can do more than that... For you." ya qarashe yana maido kallonshi akanta

"kawai baqincikina shine kasa kareki danayi daga zaman tsarewar, dani kadai ne ko shekara nawa zanyi bazan damu ba Amma the thought of ke a tsare shiyafi komai dagula min rai... Am sorry"


Sunkuyar dakai kawai tayi batace komai ba sai wasa data cigaba dayi da zoben hannunta


Shima be sake cewa komai ba sai maida hankali dayayi yana hango gate ta inda suke zaune


Babu dadewa motar Ahmad ta iso wajen

Ajiyar zuciya Aymaan ya sauke

"ya iso... Muje" yafada yana tashi tsaye

Itama Dagowa tayi ta hango motar sannan ta tashi tabi Aymaan daya fara tafiya

Har Ahmad ya fito saiya hangosu Hakan yasashi tsayawa


Kofar baya Aymaan ya budewa zee ta shiga ya rufo sannan ya bude ta kusada driver yashiga shima Ahmad ya shiga suka rurrufo kofar, tada motar Ahmad yayi yaja suka bar wajen.


Tafiya sukeyi ahankali cikin normal speed babu mai cewa komai


Can Ahmad ya juyo ya kalli Aymaan da idanunshi ke kan titi


"Aymaan, wai meya faru ne? Meya kawoku wancan Wurin?" yafada yana maida kallonshi a titin

"muje gida sannan" Aymaan ya amsa a taqaice

Ajiyar zuciya Ahmad yayi ya cigaba da tuqinshi


Zee na Jinsu amma batace komai ba sai kallon waje datake ta window din motar


Koda suka isa gida duk su dama ake jira, nan take akayi musu caa akan meya faru, ina sukaje


Saida suka zauna sannan Aymaan yafada masu komai daga inda yaje school din da niyyar daukota har hangosu dayayi a parking space din kamar suna hayaniya da mutumin har Qarasowarshi wajen da yadda fadan yakoma kanshi


Sai aka maida akalar Tambayar ga zee akan me ya hadasu

Nan zee ta gayamasu yadda komai yafaru takuma gayamasu haduwarsu da mussadiq din a supermarket lokacin da suka fita da batool siyo jakka Saidai ta 6oyemasu cewa la6el tayimashi ta dinga binshi abaya, kawai cewa tayi tayi 6atan hanya ne sai suka hade dashi shikuma sai yace shi take bibiya


Kowa mammaki ya cika shi da kuma jimami akan abinda yafaru, cikin masu mammakin harda Ahmad da abin yafi kowa kadashi, lallai ba qaramin tsallake rijiya da baya sukayi ba

Mussadiq? Mussadiq al-hassan yasa akamasu kuma ya sakesu da wuri haka?


Nan su Abbu suka yanke shawarar fidda zee daga makarantar saboda tsaro tunda zuwa makarantar na neman zama barazana agareta, kawai gwara a maida ta school dinsu batool tunda ba'ayi nisa a semester din ba qila a kar6eta


Sosai Batool taji dadin Hakan don Hakan na nufin tare zasu dinga zuwa school kenan kuma zasu dinga yini tare

Cikin wadanda sukaji dadin Hakan harda Aymaan don shima abinda ke ranshi kenan kawai sun rigashi furtawa ne kuma yaji dadin da bashi ya furta din ba


A 6angaren zee kau ba taji dadin haka ba sam, Saidai bata nuna ba, that means tabar makarantar annur kenan? Tabar Aysha?


***


Kwance take idanunta akan cieling din dakin tana kallon design dinshi wanda a zahiri bashi take kallo ba tayi nisa ne a tunaninta


"zee nasan bakiji dadin hukuncin dasu ummy suka yanke ba Amma that's the best solution, tunda mutumin nan ya dora ayar tambaya akanki bazai barki ba, zaita bibiyar ki ne har saikin fada tarkonshi so maganin kar ayi kar asoma gwara kibar musu school din"


Ajiyar zuciya zee ta sauke still idanunta akan ceiling din

"ni ba barin school dinne matsala ta ba, rushewar hanyar cikar mission dina yafi damuna, gashi na shaqu da Aysha, zanyi kewarta"

"hakane amma abinda zaki duba anan shine wannan hukuncin is for your own Good, Ahmad yana yawan bani labarin how dangerous that guy is, yana iya yin komai kuma yaci bulus don yanada both matsayi da kudi da connections, ja dashi ba qaramin kasada bane, batun mission dinki kuma allah zai kawo mana mafita ta hanyar da bama zato kawai mu cigaba da addu'a"


Qara sauke Ajiyar zuciya zee tayi tace
"to allah yasa Hakan shiyafi alhairi"


"Amin summa amin" batool ta amsa


Wayar zee ce tayi Ring


Tashi tayi ahankali zaune sannan ta jawo wayar dake kusada ita kan bedside locker


Dan Wara idanu tayi ganin sunan dake yawo a screen din

Ganin Hakan yasa batool cewa
"waye?"

"Aysha" zee ta amsa tana picking call din


"bestie" inji zee cikin fara'a


Wani irin wawan Ajiyar zuciya zee taji Aysha ta sauke sannan cikin murya Kamar zatayi kuka tace
"ummie na"

"na'am sahibatie"


"wayyo ummie na, nayi tunanin bazaki daga kirana ba Tundazu nake son kira amma fargaba ta hanani"

Murmushi zee tayi tace
"inqi dagawa kuma mezai hanani dagawa?"

"komai ma ummie, am sorry, am very very sorry for what happen dazu, da nasan abinda zai faru kenan da ban fara gayyatarshi ba"


Murmushi zee tasake yi
"Don't be, misunderstanding ne kawai"


"wlh bakiji yadda naji ba a lokacin, laifi na ma ne, nasan halin yaya sarai amma banyi tunanin abin zakai Hakan ba da ko sunanki bazan ta6a ambata mashi ba"

"kinga babu komai, kibar damun kanki, komai ya wuce insha allah" inji zee

"nagode qwarai ummie da fahimtarki, fatan dai komai lafiya, ba'ayi muku komai ba ko?"


"babu abinda akayimana, komai lfy lau"

"yayanki fa? Shima is ok ko?"

"kowa lfy lau, na gayamaki babu abinda sukayimana"


"masha allah, naji dadin jin Hakan... Ga ummie ku gaisa"


Wara idanu zee tayi saita kalli batool da itama ta Wara nata idanun don wayar a handsfree take duk tana sauraron su


"Assalamu alaiki habibty" muryar Ummie mai cike da kwarjini ta daki dodon kunnenta


Hadiye wasu yawu tayi sannan cikin nutsuwa itama ta amsa sallamar ta dora da gaisheta, duk maganar dasuke a harshen turanci suke yinta

"lfy lau habibty, ya gida ya mutanen gida"

"alhamdullilah, ummie" inji zee cikin nutsuwa

"masha allah, ina mai baku haquri akan abinda yafaru tsakanin ku da hussain, Gaskiya banji dadi ba kwata2, abin ya 6ata min rai sosai kuma zan dauki mataki akai kuyi hqr kinji"


"haba ummie komai ya wuce insha allah, dama rashin fahimta ce kawai"


"babu wata rashin fahimta, haka yake. Narasa inda yasamo wannan baqar aqidar, shikenan mutum beda yarda kona misqala zarratin? Ai dazu Saida nayi mashi fada sosai nakuma ya sakeku kuma saina dauki mataki akai"

Murmushi zee tayi cikin jin qaunar matar, da wata ce ko ajikinta bare har tayi tunanin kira ta bada haquri

"babu komai ummie, allah yaqara lafiya"


"Amin, ina Ummin naki?"


"tana dakinta"

"kai mata mu gaisa don Allah"

"to ummie, hold on" tafada tana tashi tsaye ta nufi kofa batool ma ta sauko daga gadon ta maramata baya


A daki suka iske Ummu batool tafito daga bayi da alamu ma wanka tayi


Kaimata wayar tayi

Daga gira Ummu batool tayi alamun waye, cikin rada zee tace mata umminsu Aysha ne

Kara wayar Ummu batool tayi a kunne tayi sallama ummie ta amsa ta dayan bangaren


Gaisawa suka farayi cikin mutunci sannan ummie tayi introducing kanta takuma shiga bata hqr akan abinda yafaru

Cikin fara'a Ummu batool ke nuna babu komai ai komai ya wuce insha allah

Sundan jima suna wayar sannan sukayi sallama ummie ta maido ma zee wayarta

Koda ta maida a kunne sai taji muryar Aysha

Nan take gayamata gobe insha allah zatazo

Da farko zee taso hanata zuwa amma saita nace akan saitazo Hakan sukayi sallama bayan tace zee ta turo mata address dinsu


Kallon Ummu batool zee tayi tana Tambayar ta tura mata din

Cewa tayi ta tura mata din tunda zuminci zatazo babu komai taga alamun suna da kirki sosai kuma kamar basuda matsala

Da Hakan ta turama Aysha address din suka koma dakinsu da ita da batool suna cigaba da firar kirkin ummie da Aysha


Sai gashi washegarin kamar yadda tace zatazo tazo din bayan sallar la'asar


Sosai zee tayi murnar ganinta kuma akayimata tarbar mutunci


Sosai suka gaisa da Ummu batool sannan suka wuce daita sama dakinsu zee

Batool tunda taga Aysha taji itama ta kwanta mata a rai lokaci guda don ko ba'afada ba kallo daya zakayi mata kasan tanada nutsuwa sosai

Anan zee tayi introducing din batool agareta suka kuma gaisa cikin mutuntawa sannan zee tafito ta sauko qasa don samarwa qawar tata abin ta6awa.


Lokacin da ta dawo saita tarar firarsu ma sukeyi abunsu saita ajiye masu abin data kawo tana musu bismillah


Tare duk suka sauko qasa kan dan carpet din data shinfida masu suka shiga cin abincin suna fira


"uhmm, abincin nan yayi dadi, daga ji nasan ummie na ta girka" inji Aysha tana lumshe idanunta alamun abincin na kaimata karo

"to ni na dafa, wannan dakike ganinta babu abinda ta iya sai a girka ta shaqe plate taci, duk abincin dazaki shigo gidan nan kici ko agaba ne ni na girka shi" inji batool


Dariya duk sukayi

"kai nidai ban yarda ba, ummie ta tafi kama da wanda ta girka abincin nan"

Dariya suka sakeyi batool tace
"wato har kammani ke akwai kenan na wanda ya girka abinci?"

"qwarai kuwa, da kin kalli abincin kika kalli wanda ya girka sai kiga sunyi matching"

Dariya suka sake sawa

Haka sukaita firarsu har suka gama cin abincin aka kauda abubbuwan dasuka 6ata suka koma kan gado aka shiga fira

"ummie, wlh jiya dake na kwana arai, tsabar yadda nasa abin a raina sai gashi harda su mafarki wai yaya yaqara sawa an kamaki"

Dariya sukayi

"kincika sa abu arai wlh" inji zee tana Dariya

Itama dariyar tayi tace
"wlh, ai haka nake. Gashi dama halin yayan nawa nasani, haka yake bayada yarda kona diss, haka yake tun yana qaramin shi.
Can you believe ko aboki qwara daya baya dashi?
Ummie tace yafara wannan halin ne tun bayan rasuwar dan uwanshi"

Dan Wara idanu zee da batool sukayi cikin hadin baki sukace
"tun rasuwar dan uwanshi?"


Murmushi Aysha tadanyi

"ummie, ban gayamaki mu asalin wayeba, na baki tarihina just briefly batareda na fadamaki wasu abubbuwa ba

Kinsan ko waye yaya na?

Kinsan companies din nurul haqq masu rassa daban daban?"

Batool tayi saurin amsawa
"waye besan nurul haqq ba? Saidai idan ba a dubai yake ba, itama kanta zee datazo jiya jiyan nan tasan wasu wuraren, sis wannan park din damukaje ranan? To shima na nurul haqq ne" tafada tana kallon zee

Zee data dauki hasken abinda batool ke nufi saita Kada kai cikin mammaki tace
"natuna, koba wannan mai girman ba? Mai Hade da zoo"


"shi... Na yayana ne" inji Aysha


Duk Wara idanu sukayi sosai cikin mammaki dukda sunsan komai pretending ne kawai


"yayana ne mammalakin duk wani company na nurul haqq, mussadiq al-hassan"


"ya sallam! Kina nufin ke qanwar mai wadannan wuraren ce?" inji batool cikin kaduwa, yadda take acting din yayi mugun hawa kamar dama yau tafara sani


Murmushi Aysha tayi tace
"eh, duk wadannan wuraren mallakin yaya mussadiq ne, Saidai baya bayyana identity dinshi kamar yadda muma yake hanamu bayyana namu duk don maqiya wai.

Yanada saurin zargi da rashin yarda shiyasa shi kanshi idan ba saninshi kayi ba baka gane babban dan kasuwa ne kuma shi keda wadannan wuraren.

Na ta6a baki labarin cewa twins ne ko?" tafada tana kallon zee dake kallonta Tundazu babu kyaftawa

Kada kai zee tayi saurin yi
"eh kika ce dayan ya rasu ko?"

Kada kai itama Aysha tayi
"eh haka nace amma a zahirin Gaskiya ba mutuwa yayi ba"

Ji zee tayi kamar an kwada mata guduma akai

"b..be mutu ba?" tafada cikin rawar murya itakau batool tama kasa cewa komai sai kallon Ayshar datakeyi

"to ya mutun za'ace amma ba mutuwar allah da annabi ba.. Ina nufin kasheshi akayi"

Wannan karon tashin hankalin zee qarara yafito a fuskarta

"kasheshi akai? Waya kasheshi?"

Da Aysha mai lura ce data lura da yadda zee ta tashi hankalinta fiyeda yadda ya kamata data dora ayar tambaya akan Hakan

"eh, saceshi akayi daga baya aka kasheshi"


"innallilahi waina ilaihi rajiun" zee da batool suka fada atare hankalinsu a tashe


"nima ummie ke bani labari don a lokacin ko haihuwata ba'ayi ba akwai dai qaramin cikina wanda ba'ama san dashi ba.


Mujaheed shine Hassan mussadiq kuma Hussaini, yan biyu ne masu tsananin kama da juna don ummie ma kanta takan kasa banbancesu wani lokacin

Saida suka dan fara girma aka fara samun signs da ake banbancesu dashi

Nafarko shine dimple dinsu.
Mujaheed nada dimple a tsakiyar gemu kamar dai nawa don ance shi na biyo while mussadiq nashi a kumatun haggu yake

Na biyu kuma yanayin qiriniyarsu.
Mussadiq yafi Mujaheed qiriniya nesa ba kusa ba don Saida mussadiq yariga mujaheed fara rarrafe harma tafiya ma

Kamar ummie ke cewa mujaheed yanada sanyi sosai sa6anin mussadiq dake da qiriniya don Mafi yawancin lokuta inda ta ajiye mujaheed nan zatazo ta dauke shi shikau mussadiq daka ajiye shi zai qara gaba yaje yaita 6ana

Haka ma yara basa qwarar mussadiq don shi ba'a sashi kuka Saidai yasa Yayinda shikuma mujaheed babu ruwanshi sai yara suyita bugunshi baya ramawa

Saidai kuma mujaheed yafi mussadiq juriya da haquri don da wuya yayi kuka don cewa tayi ko rashin lafiya yake baya irin rigimar da mussadiq keyi Idan shine bashi da lafiya, Saidai shirunshi da sanyinshi suqara yawa, ko cikin yara yashiga masu qiriniya suna qwararshi baya kuka duk abinda zasuyi mashi idan kaga yayi kuka to abin yakai qurewa

Shiyasa ko a soyayyar dasuke masu ta mujaheed tafi don shi bayan soyayya harda tausayi don yaro mai sanyi dama yafi soyuwa a zuqatan iyaye ko don tausayawa yanayinshi


Abin yafaru ne ranar washegarin wata babbar sallah, lokacin suna saudiya don dama can ne asalinmu daga baya muka dawo nan


Kamar yadda al'adar wannan ahalin take dik washegarin sallah walau babba ko qarama ana haduwa a babban family house dinmu inda anan kowa da kowa na dangi, qwansu da kwarkwatan su saisun hallarta harda wadanda ba garin suke ba

Ana haduwa agidan don taya murnar sallah da sada zuminci


To suma haka suka shirya ranar tunda safe Abbanmu yakai ummie da twins dinta

Lokacin Abbanmu dan kasuwa ne wanda yayi suna sosai a madina a harkar kasuwancinshi kuma a lokacin shima ana iya sashi a sahun masu kudin family dinmu


Kamar yadda ummie ta gayamin tace tunda sukaje gidan Hassan wato mujaheed ya liqemata duk inda yayi yana maqale gashi ranar sanyinshi yaqara yawa fiyeda yadda yake da

Sai tayi tunanin ko bayada lafiya ne dukda jikinshi babu zafi

Saita sa6eshi ta goyashi ta cigaba da aikinta dashi a baya

Haka taita yawo dashi abaya har bayan zuhr don Koda zatayi sallah ma Saidai ta ajiye shi kusada ita yana kallonta har tagama sannan ya rarrafo yadawo kusada ita ya sake lafewa ajikinta


Ganin wannan lauye lauyen nashi yafara yawa yasa tasa aka siyomashi maganin ciwon kai don aganinta qila bejin dadi ne

Tabashi yasha ta maida shi baya ta goya har yayi barci ma

Be farka ba sai wajajen la'asar, tabashi abinci yaci sannan cikin gwarancinshi ya nuna wa ummie zaije wajen mussadiq da tunda suka shigo gidan yake cikin yara suna wasa

Sawa tayi akaishi wajensu din dukda bata cika son yana shiga yaraba saboda qwararshi da akeyi saikuma tayi tunanin ai gwara ya saba qila da haka da haka shima zai iya ramawa idan akayi mashi

Nan ta cigaba da hidimarta cikin dangi anata kai kawo cikin annushuwa da nishadi

Can wajajen bayan la'asar kadan aka fara jin hayaniya a tsakar gidan

Tun suna ji sama sama har abin yafara yawa Hakan yasasu fitowa ciki harda ummie

Abinda ummie tagani yayi matuqar girgizata don Saida jiri yakusan kadata ba don anyi saurin tareta ba

Mussadiq tagani jina jina jikinshi duk ciwo ga kayanshi sunyi futu futu harda yagewa a wasu wuraren

Da gudu suka nufeshi cikin tashin hankali don anason riqeshi amma sai fizge fizge yakeyi

Da gudu ummie ta qarasa gabanshi ta jayoshi ajikinta tana kiran sunanshi cikin kuka

Jin muryar ummie yasa yabar fizge fizgen saiya dago ya kalleta saikuma luuu yafada ajikinta asume.


Kwatanta tashin hankalin da aka shiga a lokacin 6ata baki ne

Nan take aka shiga kiran iyayen maza dasuka fita ta waya cikin qanqanin lokaci saigasu sun duro gidan ciki harda Abbanmu


Lokacin gidan banda koke2 babu abinda akeyi

Cikin gaggawa aka wuce dashi asibiti cikin masu zuwa harda Umminmu


Nan take likitoci suka kar6eshi aka shiga bashi taimakon gaggawa


Saida aka kusan awa sannan akasamu aka shawo kan mussadiq numfashinshi yadawo normal yakuma samu barci sanadiyar allurar barci da akayi mashi

Sai a lokacin likitocin suka fito wajensu ummie da suka kasa tsaye suka kasa zaune nan suka kwantar masu da hankali akan komai ya daidaita yama samu barci

Nan kowanne ya sauke Ajiyar zuciya na jindadin Hakan Saidai ashe zaune bata qareba

Tafiyar su likitocin keda wuya sai ummie da sai a lokacin tasamu zama taqara zabura ta miqe tsaye kamar wanda aka tsikara

Duk sai aka kalleta ana Tambayar lafiya

'mujaheed... Ina mujaheed?'

Nan kowa ya tuna dashi don tashin hankali yasa anma manta dashi

Tofa nan aiki sabo yafara don duk inda aka duba inda akasan za'a ganshi dama inda bazai iya shiga ba Amma babu shi

Babu inda ba'a duba ba a fadin gidan lungu da saqo amma babu mujaheed babu alamunshi


Nanfa hankali ya tashi ba ko kadan ba, tsakanin ummie da Abba aka rasa wanda yafi wani rikicewa

Duk fadin unguwar dama wajenta babu inda ba'a duba ba Amma babu mujaheed

Ummie har qaramin hauka saida tayi suma kau tayishi babu iyaka


Wasa wasa har dare babu mujaheed

Izuwa lokacin an yada cigiya gidajen t.v da radio amma shiru

Daren ranar babu wanda ya runtsa a familynmu, ranar murna ta chanza lokaci guda zuwa ta baqinciki, abu goma da ashirin, ga mussadiq a asibiti ga mujaheed ya 6ata.


Washegari ma dasa neman da akeyi akayi inda aka baza jami'an tsaro sosai wajen nemanshi

Ummie a lokacin bata ganuwa don itama dole qarshe aka bata gado a lokacin ma aka san da cikina.


Wasa wasa kwana daya yakoma biyu yakoma uku amma still babu mujaheed, Izuwa lokacin ummie da Abba sunzama abin tausayi ba kamar ummie don ita abin yafi ta6ata, babu abinda take Tunawa sai maqale mata dayaitayi tun safe, datasanin barinshi fitar datayi yafi cikin kwando Saidai komai muqaddari ne Daga allah, dole allah ya rubuta Hakan zai faru"


Dakatawa tayi ta dago ta kalli su zee da izuwa lokacin fuskarsu sunyi sha6e2 da hawaye sai a lokacin itama taji dumi dumin nata a fuskarta Hakan yasa tasa bayan hannu ta sharesu dukda Hakan ba yana nufin wasu bazasu sake zubowa ba

"A kwana na hudu aka bugo ma Abba waya da number da akayi hiding dinta.

Yana ganinta jikinshi yabashi kiran yashafi mujaheed dinshi

Hannu na rawa ya daga yana jin zuciyarshi kamar zata faso qirji

Kamar yadda yayi tunani Hakan ne don wadanda suka sace mujaheed ne suka bugo suna buqatar kudin fansa inhar suna son a sakomasu dansu.

Da farko Abba qin yarda yayi yace dole saiya ji muryar danshi yakuma tabbatar shine sannan

Aikau sai suka bashi saiga muryar mujaheed radam yana kiran Abba da ummie cikin kuka

Sosai hankalin Abba yayi mugun tashi nan take shima hawaye suka kawo mashi a idanu

Nan take yashiga magiyar don Allah suyi hqr karsu cutar mashi da danshi zai basu duk abinda sukeso

Jin Hakan yasa suka ce zasu sake shi amma sai sun bada kudin fansa

Nan suka yankama Abba kudin dazai bayar na fitar hankali

Abba yaso neman ragi amma firr suka qiya sukace ya za6a ko kudi ko mujaheed
Nan kuma suka jamashi kunne akan karya saki yasako jami'an tsaro aciki don sakosu aciki daidai yake da mutuwar mujaheed, suka kuma ce zasu sake kira don gayamasu inda zasu kai kudin.


Sosai hankalin ahalinmu yasake tashi

Inda duk wanda yaji adadin kudin dasuka nema saiya girgiza

Saidai Abba a shirye yake ya bada dukkan abinda ya mallaka don dawowar danshi Mafi soyuwa a gareshi

A lokacin mussadiq ya dade da farfadowa Saidai wata irin rashin lafiya yake mai zafin gaske ga ciwukkanshi da basu ida warkewa ba kullum cikin kukan ina mujaheed yake abinci ma Dakyar yake ci.

Ummie kuwa tafi kowa zama abin tausayi kodayaushe ciki kuka take duk tabi takoma kamar ba ita ba ga tashin hankali ga ciki.


Wasu daga cikin family dinmu suka bada shawarar sanyo jami'an tsaro acikin case din amma firr Abba yaqi yarda don babu abinda zaisa yayi tempering da rayuwar danshi.

Haka ya hada kudin nan cass family dinsu suma duk sun kawo gudunmawa aka hada kudadden ana jiran suqara bugowa don dole saisun bugo tunda da hidden number suka bugo wancan karon

Sai bayan kwana biyu suka bugo suna Tambayar an hada kudin, baki na rawa Abba ya amsa da eh sai suka fadamashi inda xa'akai

Roqonsu yashigayi cikin magiya kan suqara bashi mujaheed yaji Muryarshi

Babu musu aka bashi

'Abba' mujaheed yafada cikin mugun sanyi

'Abba... Ummie'

Kasa controlling kanshi Abba yayi Saida yayi hawaye

'mujaheed bunnaya, kana lafiya?' yafada cikin rawar murya

'Abba?' mujaheed yasake fada

'kayi hqr zaka dawo kaji? Abba zaizo ya daukeka' inji Abba hawaye na gudu sosai a kumatunshi

'muccadik' mujaheed yaqara fada cikin sanyin murya


'mussadiq nanan lfy, shima zaizo kaji? Kaji dana'

Daga Hakan sai yaji muryar daya daga cikin 6arayin na cewa ya isa haka nan tunda sunyi maganar

Nan yasake gayamasu inda zasu kai kudin da lokacin dazasu kai dakuma qara yimasu gargadi akan karsu sake su sako jami'an tsaro aciki idan ba Haka ba a bakin ran dansu.

Nan aka shirya komai Abba da kanshi yaje bada kudin

Kuma ya ajiyesu inda suka ce sannan yatafi


Saidai shiru shiru basu bugo ba sukace ga inda zasuje su dauki yaron ba

Tun suna jira har hankalinsu yafara tashi da jin yadda shirun yayi yawa

Sai a kwana na biyu da bada kudin sannan aka bugamashi waya, a lokacin saura qiris ya zauce

Nan aka gayamashi inda zaije ya dauki mujaheed cikin wata ash din mota, zasu bar motar a bude dayaje kawai ya bude ya fiddashi ya tafi dashi

Cikin jindadi Abba yayi shirin tafiya, jikinshi har rawa yakeyi don har jiri jiri yakeji na neman dibanshi

Dashi da Hussaininshi suka tafi dauko shi inda akace din


Wuri ne da sai anfara fita daga gari ma, babu gidaje a wajen sai busassun ciyayi don lokacin rani ne

Tun daga nesa suka hango motar ash colour din da akace gefen titi.

Parking Abba yasa Hussaininshi yi tun kafin su qarasa suka fito da sauri suka nufi kofar

Saidai suna kaiwa inda tsakaninsu da motar baya wuce taqi ashirin sukayi mugun ganin da basu ta6a irinshi ba


Motar da akace masu mujaheed na ciki ta tashi da wuta🔥 a gaban idanunsu.."✍️


Ummin fasihu 🧚🏻‍♀�
8/2/21, 9:42 PM - Buhainat😝: *🙍🏻‍♂️DEEN 🙍🏻‍♂�*


*068*


*THE UNVEIL 2*


_🙈ni yau ido rufe zanma yi typing saboda kunyar wasu nakeji 🙈🙈_


Toshe baki zee tayi idanunta awaje tana kallon Aysha da kuka yafara cin qarfinta


"a..agaban idanunsu motar taita ci da wuta... Abbanmu ahakan yaso qarasawa ga motar amma Hussaininshi da tsirarun mutanen da wutar tajawo hankalinsu suka hanashi ta hanyar rirriqeshi.

And..and before his very eyes, beloved son dinshi ya qone qurmus dashi da mot..."


Kasa idawa tayi saboda kukan dayaci qarfinta.


Kamar hadin baki da zee da batool suka rarrafa wajenta suka rungumeta suka hada kai waje guda suna kuka kamar ransu zai fita


Sun dauki tsawon lokaci ahakan anrasa wanda zai rarrashi wani

Can Aysha ta dago da jajjayen idanunta tana kallon su zee da har lokacin kukan sukeyi

"ba acikin hayyacinshi ba aka maido Abbanmu gida, daga nan akayi asibiti dashi.

Itama ummie najin abinda yafaru ta yanke jiki ta fadi, kan kace me jini ya 6allemata

Itama kamar abba sai aka kwasheta sai asibiti.

Kamar hadin baki shima mussadiq jikinshi ya rikice yashiga convulsing, numfashi ma Dakyar yake fizgoshi daga huhunshi.


Iya tashin hankali wannan ahalin sun shigeshi a lokacin.

Nima don Allah yayi zanzo duniyar shiyasa cikin ikon allah aka shawo kan bleeding din da ummie keyi


Lokaci guda happy family dinmu ya tashi daga happy family zuwa akasinshi


Abba tunda ya kwanta gadon asibiti be qara tashi ba

Saida yayi wata daya a kwance sannan watarana yatafi cikin barcinshi.


Yatafi yabi danshi yabar matarshi abar qaunarshi da cikin dake jikinta dakuma danshi da har lokacin beda cikkaken lafiya.


Haka ummie tayi takabarshi, ga ciki ga ciwo don tun lokacin da ta yanke jiki ta fadi lokacin da aka dawomata da labarin mutuwar mujaheed ta hadu da ciwon hawan jini.


Haka tayi takabarshi tagama ta cigaba da zama gidanmu tareda mussadiq da shima izuwa lokacin ya warware sosai Saidai kwata2 ya chanza daga mussadiq din da aka sani.


Mussadiq mai qiriniya mai surutu yakoma so silent.

Yana iya yini batareda ya furta ko kalma daya ba, ga wata rashin yarda da ya bijiro daita lokaci guda.

Baya yarda wani ya ra6eshi ko kadan Duk yadda kau kake dashi.

Ko baqi ummie tayi walau family dinmu ko wasu daban baya yarda yabar jikin ummie duk inda zata yana maqale daita.

Idan baqin zasu shekara suna mashi magana ko kallo bazasu isheshi ba

Idan kuma sukace zasu daukeshi da tsiya sai ya fasa ihu kamar wanda ake yankawa Hakan yasa duk masu qulafucin daukarshi suka haqura Saidai gani daga nesa wato ajikin ummie


Da farko ummie tayi tunanin yarinta ne kuma qila harda abinda yagani ranar da abin yafaru tunda tana kyautata zaton kome yafaru a ranar mussadiq yagani tunda da alamu ma kamar shi kuftowa yayi Saidai a lokacin ko an tambayeshi bazai iya bada amsa ba don qarami ne sosai magana ma bata gama nuna a bakinshi ba

Hakan yasa take yimashi addu'o'i sosai da rubutun sha duk na dangana wanda zai kuma taimaka mashi wajen manta abinda ya faru din


Saidai abin yafara bata tsoro ne ganin harya fara girma bai bar wannan sabon halin nashi ba


A lokacin baya zuwa ya lafe jikin ummie Saidai duk tsiyarka daga nesa nesa zaku gaisa dashi ya maida fuskar ya
dinke tsaf idan zaka shekara yimashi magana bazai amsa ba


A lokacin an haifeni sai ya kasance bayan ni da ummie babu wanda yake kuma yarda dashi.


Anyi maganin anyi gwajin both physically and mentally amma result din ya nuna babu abinda ke damunshi, he's normal Saidai a kowacce rana abin nashi qara gaba gaba yakeyi


Har takai ni kaina yafara hanani kula mutane, ko zuwa yayi ya ganni da yara muna wasa saiya fizgoni daga cikinsu ya hanasu zuwa wajena kuma gashi a lokacin mugun tsoronshi yara sukeyi saboda rashin warginshi shiyasa wani lokacin da sun ganshi sai su gudu ko susha Jinin jikinsu, lokacin fa bazai wuce shekaru goma sha biyu ba Saidai rashin warginshi yasa ko manya saisu kasa tsawatar mashi saboda kwarjinin dayake masu


Wannan abin ba qaramin cima ummie tuwo a qwarya yake ba don da dama can haka yake da da sauqi amma sanin cewa daga baya ya bijiro da wannan halin yasa abin ke damunta sosai

Ko shiryamu tayi muje gidajen danginmu baya zuwa Saidai yaita yawo dani mudawo gida, idan tagane Hakan saita tisa shi gaba da fada shikuma data fara sai yaita kuka kamar ranshi zai fita


Tasha zaunar dashi ta tambayeshi meyasa yake abinda yakeyi ko wasu sukeson yimashi wani abu ne? Sai ya girgiza kai kawai yace
'ummie banason kowa sai ke da ukhtie'


Haka rayuwa taita tafiya tun ummie nasa abin a rai harta fawwalawa allah komai ta cigaba da Binshi da addu'a

Mussadiq ko a makaranta be ta6a yin aboki ba nima ya hanani yin qawa ko daya, kasancewar shi kadai ne yaya na kuma abin koyi na tunda mostly sai kiga a kowanne gida qarami yafi saurin koyi da wa ko yayanshi bisa ga yadda zasuyi koyi da iyaye saboda kusanci dake tsakaninsu, sai ya kasance nima bana Sakin jiki da mutane ko a family dinmu ne don ko ummie ta tilasta mana zuwa gidajen su bama shige masu, daga gaisuwa shikenan, gwara ni fuskata kodayaushe asake take kuma idan akayi min magana zan amsa asake shikau yaya a kodayaushe fuskarnan tashi na dinke tsaf ko magana akayi mashi cikin cin magani zai amsa.
sai ya kasance bamuda wata qawa sai Umminmu

Haka zamu zauna mu ukunmu muyita nishadi wanda mostly dama a lokacin ake ganin Dariyar yaya mussadiq

Familynmu kau tun suna surutu wai ummie takasa controlling dinmu tasanya mana aqidar qin jininmu a zuciyarmu har suka gaji suka qyaleta suma suka yanke mu'amala daita suka bar aiko yaransu gidanmu wanda Hakan ba qaramin dadi yayi wa yaya ba

Saidai dukda Hakan ummie bata fasa turamu zuminci gidajen su ba dukda ba wani kulamu suke ba idan munje ita acewarta ta fita haqqin zuminci


Kawu Hussaini da iyalanshi ne kawai wanda basu juya mana baya Ba, kuma 'yayanshi na zuwa gidanmu shima kanshi yana zagayowa akai akai yana duba lafiyar mu kuma ko sau daya be ta6a nuna 6acin ranshi akan halayen mussadiq ba, yana matuqar haquri akan Hakan don shi mutum ne mai matuqar haquri da kawaici.


Ahaka har yaya mussadiq yagama karatunshi ya mallaki hankalin kanshi to a lokacin Kawu hussain ya damqa mashi gadonmu dake hannunshi tun rasuwar Abbanmu


Kasancewar fannin kasuwanci yaya mussadiq ya karanta saiya zuba kudadden a business yafara jujjuyasu


A lokacin kawunnan mu da danginmu maza sunyo caa wajen bama mussadiq shawarar yadda zaiyi da kudin Saidai duk ya watsa masu qasa a idanu ta hanyar yin watsi da dukkanin shawarwarunsu yayi amfani da nashi


Cikin ikon allah sai gashi allah yasama abin albarka kasuwancinshi yafara girma

Nan kuma danginmu suka tuso ummie gaba da maganar aure, wai ya kamata mussadiq yayi aure tunda ya isa kuma ko a dangine yana iya za6ar wacce yakeso tunda akwai yanmata kala kala a dangin.

Firr mussadiq yaqi yarda yana cewa shi yanzu ba aure ke agabanshi ba kuma Koda auren zaiyi sai wacce yakeso basai an kawo mashi tallar yanmatan dangi ba


Wannan abin ba qaramin rikici yakawo a danginmu ba, nan kowa ya dora laifin akan Umminmu wai ita keson rabamu da dangin mahaifinmu, sosai abin ya damu Umminmu a lokacin takuma so fahimtar dasu akan bazata iya yiwa mussadiq dole ba akan ya auri wata ba amma sukaqi sauraronta saima suka dauki gaba da ita da muma gabadaya


Ashe tun farkon rikicin yaya mussadiq ke tattara dukkanin harkokinshi yana maido su nan dubai

Kwatsam watarana yazo ma ummie da maganar komawarmu dubai


Da farko ummie qin yarda tayi tana cewa babu abinda zai fiddata daga saudiya Hakan kamar tabbatar da magangganun dangin Abbanmu ne na tanason rabamu da danginmu ne


Dakyar mussadiq yashawo kan ummie inda Saida yabi gidajen dangin namu da daddaya yana fadamasu kasuwancinshi zai kaimu can ba wani abu ba kuma zamu ware lokaci muna zuwa saudiya ziyara

Abin mammaki sai aka rasa wanda zai qalubalanceshi akan hakan, hayaniya da cecekucen da ummie tayi tunanin zasuyi sai taji tsit basuce komai ba

Hakan yasa muka tattaro namu ya namu muka dawo nan dubai da zama


Cikin ikon allah cikin qanqanin lokaci business din yaya ya ha6aka yayi albarka, budi yaita shigo mashi takoina, kowa na kwadayin samun share a company dinshi kasancewarshi jajirtacce a aikinshi ga riqon Gaskiya don yaya mussadiq ba duk rintsi baya cutar mutum kuma baya bari a cuceshi shiyasa bada kowa yake aiki ba saiya yarda dakai dakuma qwarewarka a aiki dakuma yanayin riqon amanarka


Har lokacin dabi'arshi ta rashin yarda na nan, baya barin wani space komin qarantarshi wanda xa'a iya yaudararshi, yana yin komai nashi cikin taku shiyasa Koda yafara bude wurare irinsu parks, malls da makarantu be sanya sunanshi ko sunan daya daga cikinmu ba saiya za6i yasanya wani sunan daban wanda duk qwaqwar mai qwaqwa bazai san mai su ba sai idan dama can ya sanshi.

Gwara gwara gidajen marayun dayake dasu wanda ya bude su da sunan Abbanmu da dan uwanshi mujaheed wanda yatara marayu aciki yana kula dasu da saran ladar Hakan allah yakaima su Abba har cikin qabarinsu.


Danginmu na kawo mana ziyara jifa jifa muma muna zuwa qaranci sau biyu a shekara mostly qaramar sallah da babbar sallah.

Tunda muka dawo nan qasar ban ta6a yin qawa ba sai akanki, bansan meyasa ba tun aganin farko naji kin kwanta min arai, naji kamar akwai wani connection tsakanina dake.

Dan zaman da mukayi dake farko farkon abotarmu kuma yasa kika ida shiga zuciyata naji komai naki na burgeni, a lokacin na bawa Umminmu labarin ki kuma na hadaku a waya inda itama nan take kika kwanta mata takuma bani go ahead akan abotarmu

A lokacin yayana bayanan yana switzerland business trip kamar yadda yasaba tafiye tafiyenshi na business

Tun yana can nake bashi labarin ki, dafarko ya nuna 6acin ranshi akan Hakan yana cewa ba ya hanani yin abokai ba? Amma saiya haqura lokacin da ummie tayimashi magana tace itama tasanki ke mutuniyar kirki ce, babu yadda ya iya saiya kyaleni kawai amma yayi min gargadi akan na dinga kulawa


Jiya kwanan shi biyu da dawowa kuma tunda yadawo nake addabarshi akan yazo ya ganki Saidai yace he's busy amma idan yasamu lokaci zaizo

Shine fa kwatsam jiya muna zaune dake a library yayi min text akan gashi nan yazo ganin bestie din tawa dana addabeshi da batunta shiyasa kikaga na Kamo hannunki cikin jindadin wannan bazatar dayayi mana, ashe halinshi zai saida nan saniba"


Ajiyar zuciya duk sukayi kowannensu idanu jajur a dalilin kukan dasuka sha na labarin mujaheed.


"wataqila ba laifinshi bane shima... Tabbas mun ta6a haduwa dashi sau biyu kafin ranar

Ranar farko yayi min kama da wani dana sani a Nigeria shiyasa naje na sameshi, am so desperate that banyi saurin gane bashi bane ba sai daga baya, daga bayan ma bayan yatafi.

Haduwarmu ta biyu kuma a wani supermarket ne, nida batool munje siyayya sai bamu samu abinda mukaje nema ba kuma munga abin a magazine dinsu shiyasa ma mukazo shopping din

Sai naje wajen cashier nayi complaining akan Hakan saiya bani haquri yakuma kira akace ya turoni na amsa sama wajen Manager

To wajen zuwa office din Managern na 6ace

Naita shige shigen hanyoyi amma nakasa gane hanya kuma narasa hanyar dazanibi nadawo inda nafito.

To anan muka sake clashing dashi inda nan take yayi concluding Binshi nake, I was shocked and scared jin yana tuhumata da bibiyarshi, Dakyar nasamu su cashier sukazo suka ceceni a wajenshi

To kinga after all these, ganina kwatsam a matsayin qawarki dolene ya tabbatar mashi da zarginshi, I know shiyasa yayi concluding akan tabbas ni yar leqen asirinshi ce bayan bemasan ita kanta kalmar spy din ba qaramin kadamun hanji yake ba idan aka ambaceta"


Dariya duk sukayi

"that's yaya mussadiq for you, komai saiya dora mashi ayar tambaya. Jiya ran ummie ya 6aci sosai dajin abinda ya aikata shiyasa nan take tasashi Sakinku" inji Aysha


"Allah sarki, ai bayada laifi, duniyar ce ta zama abin tsoro, mutane ba abin yarda bane... Nikau sai naga kamar mussadiq baya rasa sanin wani abu gameda sace mujaheed, as in why lokaci daya zai chanza yabar yarda da mutane bayan da ba Haka yake ba?" inji batool

"abinda yake daurewa kowa kai kenan, tabbas qila yaga wani abin wanda ya firgitashi amma kuma yakamata ya manta tunda lokacin da abin yafaru yanada qarancin shekaru tunda lokacin shekarun su uku uku da yan kai"


"nikuma nafi zargin cikin familynku, anya babu wanda mussadiq ke zargi acikinsu duba da yadda be yarda dasu ba kwata2?" inji zee


"hmm I don’t think so ummie saboda kamar yadda nafada dazu lokacin da abin yafaru yanada qarancin shekaru bazai iya recalling komai ba kuma da ace zai iya da nasan zai fadane right away, kawai ni nafi tunanin razanar abinda yafaru aranar ne taqi sakinshi haryanzu, a lokacin brain dinshi is so fragile wajen daukar irin wannan shock din shiyasa abin yayi affecting dinshi sosai ya zauna ajikinshi har girmanshi batareda shi kanshi yasan meyake damunshi, wataqila Hakan yasa mashi tsoron mutane da rashin yarda dasu har zuwa wannan lokacin don so da dama idan ummie ta tsareshi da Tambayar meyasa yake saurin zargin mutane kuma baya saurin yarda da mutum sai yace shima besaniba kawai yana ji ajikinshi kowa ma na iya zama maqiyinshi shiyasa yakasa yarda da kowa"


Duk Kada kai sukayi cikin alhini, tabbas akwai lauje cikin nadi a wannan al'amarin, dagaske ne mussadiq besan komai ba kawai Hakan nan ne yake jin baya iya yarda da mutum ko yanada dalilin yin Hakan? Allah kadai yasan Gaskiya dashi mussadiq din


Ajiyar zuciya batool ta sauke
"to allah ya bashi mafita akan abinda ke damunshi, allah yajiqansu Abba"

Da ameen duk suka amsa Saidai deep down batool da zee sunsan wannan addu'ar ta Abba ce kadai don mujaheed nanan da ranshi


Cigaba da firarsu sukayi wanda duk ta deen ce, Aysha nabasu labarin yarintarshi wanda itama ummie ke bata su don sosai Aysha ke kaunar deen dukda bata zo ta tardashi ba, da kingata zaune da ummie to labarin deen suke har wani dadi takeji idan ummie na fadin abubbuwan data biyo nashi musanmman a hallaya sai tajita cikin shauqi na musanmman.


Sai gab da magrib drivern gidansu Aysha yazo


Saida suka rakata wajen ummu batool sukayi bankwana inda tabata kyautar turarruka takuma bata saqon gaisuwa ga umminsu sannan tacewa batool ta dauki rubber dambun naman datayimata dazu a kitchen idan sun sauka tabata, godiya sosai Aysha tayimata sannan suka fito


Atare su ukun suka sauko qasa suna tafe suna fira cikin raha

Wucewa batool tayi don yin yadda ummu batool tace sukuma suka nufi kofa.


Wayar Aysha ce tayi ringing daidai sun kusa isa bakin kofar

Dubawa tayi saikuma ta dago ta kalli zee


Harara zee ta gallamata cikin wasa ta kauda kai don ko ba'a fadaba tasan wannan umar dinne


Dan murmushi Aysha tayi sai kuma tayi saurin yin gaba don amsa kiran kafin ta tsinke


Dayake sauri take kuma hankalinta na kan waya bata lura da bude kofar da aka rigata yiba tasa kai sai quuuum! Taji taci karo da abu


Yar qara tasaki taja baya tana sosa goshinta cikin yanayin jin zafi

"ya sallam! Are you ok?" Taji muryar zee dake qarasowa na fada a bayanta


Daga kai tayi taga mai ya qumeta sai taganshi shima tsaye yana murza goshinshi cikin yanayin jin zafi

Sanye yake da farar spotless shirt da baqin wando sai lapcoat dinshi rataye a kafada

Dagowa yayi shima ya kalleta sai suka hada ido

Ganin yadda ya 6ata fuska yana kallonta yasata Dan buda idanu tace
"oh! Sorry"

Bece komai ba Sai duqawa dayayi yana tsintar Wayar data fadi qasa

Binshi da kallo tayi sai taga ashe Wayar hannunta ne ta fadi

Kafin tayi wani abu harya miqe ya miqomata

"oh, thanks.. So much" tafada tana amsar Wayar

Kada kai yayi
"always be careful kuma ki dinga kallon gabanki don next time bazaki sa'ar karo da abu mai taushi kamar goshina ba, sai abu mai mugun tauri kamar garuu"


Dariya zee da batool data fito yanzu sukayi yayinda Aysha ta 6ata fuska

"wayace maka goshin naka da taushi? Dafarko nayi tunanin da dutsin marmara(rock) naci karo"


Wani kallo yayimata yace
"koba dutsin marmara ba" ya cigaba da tafiyarshi

"gayamashi dai ukhtie, kedai idan kika koma gida ki tabbatar ummie takaiki kinga mai duba qashin kai, kar ace wani wuri ya tsage baki sani ba" inji batool

Dariya Aysha da zee sukasa yayinda aymaan ya dakata Daga tafiyarshi ya juyo ya kalleta sai kuma ya cije lip ya girgiza kai

"kinci sa'a agajiye nake yanzu amma ki kiyayi haduwarmu"

Dariya suka sake sawa shikuma ya cigaba da tafiyarshi ya nufi stairs


"ammm... Akhie?"


Jin Hakan yasashi dakatawa daga hawan stairs din dazai fara saiya juyo


Fuska dauke da murmushi tadan qara matsowa gabanshi

"erm.. Dama akan abinda yafaru jiyane... Am sorry on my behalf, my brother's and my mum. Am sorry about that and that won't happen again insha allah"


Sai a lokacin yama shaidata, kamar wanda yagani tareda wannan marar mutuncin jiya

Kallon zee yayi sai itama tadan tako tana cewa
"Aysha... Sunanta Aysha, qanwar mussadiq, tazo bayar da haquri ne on his behalf"


Sake maida kallonshi yayi akan Aysha da tadan sha jinin jikinta Ganin yadda yanayin fuskarshi ta chanza


Dan ta6e baki yayi yace
"oh? Thanks then" saiya juya ya cigaba da tafiyarshi harya haye sama


Bataji dadin Hakan ba don sai taga kamar shi be haqura ba

Zee ce tadan yi Dariya tace
"Dayake yanzu yadawo kuma ya kwaso gajiya, don't worry Hakan yake idan yana gajiye" inji zee duk don Aysha taji Dama dama


"saikace wani ya aikeshi ba" inji batool tana qarasowa itama

Murmushi Aysha tayi tace
"ai dole, aikin hospital akwai wahala"


Da Hakan suka juya suka fita daga falon sukayi mata rakiya har mota.

Shiga tayi gidan baya duk suka miqamata kayayyakinta sannan ta rufo kofar suka Shiga daga ma juna hannu


"sai monday ko?" inji Aysha


Murmushi zee tayi saita kadamata kai

"to allah ya kaimu, zamuyi waya... Ukhtie sai munyi waya" ta maida akalar maganar ga batool


Ansawa sukayi da to shikenan sannan suka cigaba da dagama juna hannu har suka fita daga gidan

Juyowa sukayi xasu koma ciki

"meyasa baki gayamata kinfita daga school din ba"


"let her find out herself" zee ta amsa suna shigewa cikin gidan


****


A satin zee zaman fita gida tayi don anacan ana mata cukucukun Shiga school dinsu batool


Cikin satin aka gama komai saiya kasance monday mai zuwa xatafara zuwa school din, murna wajen batool ba'a magana


A bangaren Aysha kuma ganin zee bata zuwa school ta addabeta da kira tana tambayar lafiya tabar zuwa school


Daga baya dai zee tafito ta gayamata Gaskiya cewa an chanxa mata school ne

Aysha bataji dadi ba kwata2 sai tayi tunanin ko dama basu huceba kawai pretending sukayi komai ya wuce

Zee tace mata wlh komai ya wuce ita kanta batasan da barin makarantar ba sai daga baya kuma ai Hakan baxai shafi abotarsu ba tunda ga waya

Haka dai sukayi sallama rai babu dadi musanmman zee datakejin duk bata kyautawa Aysha ba, amma ya ta iya?


Sosai komai yafara dawowa normal, zee tafara zuwa school kuma babu laifi tana jin dadin school din dukda basu kamo kafar school dinsu Aysha a karatu ba

Koda yaushe tare suke da batool sai idan dayansu na class kuma kullum tare suke zuwa suna dawowa a motar batool Koda kuwa mutum daya keda lecture ranar.


A 6angaren aymaan kuwa Sosai hankalinshi ya kwanta da Hakan don shi dama hankalinshi be kwanta da wancan makarantar kawai amincewa yayi don babu yadda ya iya amma yanzu hankalinshi ya kwanta tunda kullum suna tare da batool.


Yau wednesday.


Tafe zee take tareda batool zasu nufi parking space don tafiya gida

Suna tafe suna firarsu

"nikuma wlh sai inga gwara mubari sai komai ya lafa sannan, kinga fa ga exam nan around the corner, yanzu lokacin karatu ne Sosai" inji batool

"au sai yanzu za'ayi karatun sosai kenan. Matsalata da to irinku kenan bakwa fuskantar abu dawuri sai wuri ya fara qurewa, ni ko yanzu akace kule cass zance" inji zee tana juya idanu

Kya6e baki batool tayi tana mata kallon sheqeqe
"sannu, to waye yace miki shi be shirya ba? Nima ko yanzu akace min kule cass zance"

"A'a wlh, akace miki kule yanzu zubawa aguje zakiyi kaffafu na ta6o qeya"


"kutt.. Amma kin qoshi saura juice" inji batool tana kwafa


Dariya zee tayi tace
"juice dinma nariga na kora dash...."


Kasa qarasa maganarta tayi, lokaci guda ta damqi hannun batool da qarfi

Saurin kallonta batool tayi sai gani tayi wani wuri take kallo Hakan yasa itama kallon wajen


Itama wara idanu tayi cikin tsantsar mammaki


_Mussadiq?!_.... ✍️


Ummin fasihu 🧚🏻‍♀�
8/2/21, 9:42 PM - Buhainat😝: *🙍🏻‍♂️DEEN 🙍🏻‍♂�*


*069*


*RIVALRY*


Zaune yake kan booth din wata danqareriyar baqar motar mai salqi


Sanye yake cikin tsaddadun qanannun kaya farin wando da farar t-shirt mai guntun hannu wanda ya taimaka wajen bayyana damtsen hannunshi ya dora baqar guntuwar jacket akai

Gyarariyar sumar kanshi tayi luff sai sheqin gyara datake

Idanunshi dade da shade as usual kanshi a duqe yana dandanna faskekiyar wayar hannunshi


Kallon juna zee da batool sukayi sai kuma suka maida kallonsu akanshi


Tsayawa sukayi suna kallonshi, bawai don yamasu kyau ba ko wani abu sai don yanayin dayayi parking din motarshi da yadda yayi blocking Motarsu zee yadda bazata iya fita ba saiya janye tashi


Qara kallon juna sukayi cikin rashin sanin abinyi gashi ko sau daya be dago ba da alamu ma besan da wanzuwarsu ba awajen


Batool ce tayi qarfin halin qarasawa wajen mottocin sannan cikin sakin fuska tayimashi sallama

Ahankali ya dago ya dora idanunshi dake cikin shade akanta

Badon taga motsin la66anshi ba da bazata san ya amsa sallamar ba

"amm... Excuse me, I think you have to adjust your car, you've blocked ours" tafada tana nuna nasu motar


Kallon motar data nuna yayi saiya yatsuna fuska kamar yaga abin kyama ya maida hankalinshi akan wayarshi again


Daga girarenta batool tayi cikin mammakin abinda yayi saita juyo ta kalli zee dake baya tana kallonsu with unreadable expression


Sake maido kallonta tayi kanshi sannan a karo na biyu tasake mashi magana Saidai wannan karon cikin larabci

"nace ka tare mana hanya, ka gyara parking motarka fita zamuyi da motar mu"


Sake Dagowa yayi ya kalleta a yatsine cikin gadara kamar mai ciwon baki yace
"Me kike buqata wai?"

"motarmu nace, ka taremu ka gyara parking" tafada patiently


Qara kallon motar yayi a yatsine sannan yace
"kijira nayi abinda yakawoni nagama sannan"

Kallon mammaki tashiga yimashi

"mujira kagama abinda ya kawoka? How?"


Karkatawa yayi ya zaro bundle din kudi ya ajiye daga qarshen booth din inda batool take
"take and go"
Yafada yana maida hankalinshi akan wayarshi


"And what was that for??" yaji muryar da Tundazu ita yake son ji na fadin Hakan

Sake Dagowa yayi ya kalleta, fuskar da kwadayin ganinta ya hanashi sukuni a yan kwanakinnan


Zee ce data qaraso wajen itama tsaye Hannu daya riqeda kugu fuskarnan a tsuke

Kallon up and down yayimata sannan yasake Karkatawa yasa hannu a aljihu ya zaro wani bundle din ya dora akan dayan ya sake maida hankalinshi akan abinda yakeyi


Ran zee yasake 6aci

"seems you're deaf, cewa tayi ka gyara motarka zata fidda tata"


"shiyasa nabaku wannan kuje kusha coffee kafin nagama abinda nake na dauke"


"waye anan yayi maka kama da mayunwacin coffee ko almajira?"


"almajira? A ganina kowa anan yasan wacece" yafada yana mata wani kallo


Wani abu yasake tsayamata a wuya


"look, ko ka dauke wannan kwasgwamar motar ka ko mukira maka security yanzunnan" tafada cikin quluwa


Besan lokacin da wani murmushi ya su6uce mashi ba wanda Hakan ya bayyana dimple dinshi na gefen haggu


Ahankali ya zare shade din idanunshi ya zuba mata oily eyes dinshi da kallonsu ke tsundumata cikin wani yanayi

"Go ahead mhiz" yafada ahankali gefen bakinshi dauke da smirk


Afusace tajuya zata bar wajen batool tayi saurin Kamo hannunta itakuma ta fizge ta cigaba da tafiyarta


Binta da kallo su biyu suke wani murmushin na qara kufcewa Mussadiq.
Wai shi zatakai qara wajen security, lallai yarinyar nan get mind

"please ka gyara motar ka mutafi mu bama neman rigima" inji batool


Kallo daya yayimata ya dauke kanshi ya maida a wayarshi Hakan yasa tayi shiru ta tsaya Kallon ikon allah

Lallai sai yau ta ida yarda da zancen zee na mutumin nan bayada mutunci ko diss


Suna ahaka saiga zee ta taho biye da wani security a bayanta


Sosai Hakan yaba mussadiq Dariya ganin yadda ta taho rai a Hade wani sololon security biyeda ita wai nan shi ta kiramawa

Qarfin halinta ba qaramin Dariya yake bashi ba saiya fuske yayi kamar besan dasuba har suka qaraso


"yauwa, gashi nan" inji zee tana nunashi

Security din ya kalli gayen yace
""kai dagaske ne kayi blocking din Motarsu kuma kaqi kaucewa su fita?" yafada cikin cin serious


Dagowa mussadiq yayi ya kalli security din da ya Hade fuskarnan alamun babu wasa

Sa hannu yayi ahankali ya zare shade din idanunshi ya zuba mashi su sannan ahankali yace
"Wani abu nakeyi, idan nagama zan Janye"


Wani mugun kwarjini mussadiq yayima security din Hakan yasashi fara kame kame

"am.. To..to ka kusan gamawa?"


"eh" ya amsa a gajarce yana sake maida hankalinshi kan wayarshi

Juyowa security din yayi ya kalli zee

"to, ko kubari zuwa anjima idan kuka fito daga lectur..."


"kamar yaya mubari sai anjima? Wane lecture zamu gama bayan wanda muka riga muka gama, yanzu gida zamu to. What the hell is he doing da dole saiya gama zai Janye mu wuce?" inji zee dakeji kamar tayi bindiga


"to yanzu yaya kike son ayi bayan yace..."


"kaga kyaleta, dauki wannan kayi tafiyarka komai zaiyi daidai" mussadiq ya katseshi da fadin Hakan yana turamashi kudadden daya Fiddo dasu


Saurin dauka security din yayi yana washe baki yana zuba Godiya Yayinda ko kallonshi mussadiq be qara yiba

Zuwa security din yayi ya wuce su zee dasuka saki baki Suna kallonshi batareda yako sake kallonsu ba


Ran zee ya qara 6aci

"you know what? Am a king everywhere I go, I was born to rule and my instructions are made just to be followed, don haka kowa zaki kira babu abinda zasu iyayi, I mean har shugaban makarantar nan, so is better kujira din harna tashi tafiya"


Cikin huci zee tace
"you're born to rule the morons not someone like me, am a Queen myself. I rule also and giving instructions is also my role, I'll never follow instructions From someone like you, never!"


Fizgo hannun batool da Tundazu tazama yar kallo tayi suka nufi gate

Dan murmushi mussadiq yayi yana Kada kai
"we shall see" yafada under his breath


Bata saki hannunta ba har Saida suka fita daga school din

"meye haka to zee? Da kika fiddomu nan me zamuyi?"

"cab zamu samu muhau yakaimu gida"

"motar fa?"


"ya cinye ya kora da ruwa" ta amsa still tana huci

"hmm, zee kenan. Nifa banga abin tada jijiyar wuya anan ba, kinsan kowaye wannan mutumin basai an fadamaki ba, sai inga gwara mubishi ahankali ya bari mu Fiddo motar"

"ke kije to kibishi ahankalin, ni allah yasani bazan iyaba. The guy is so rude, wai mema ya kawoshi nan?"

"hmm who knows"

"to nidai da naje yaimin wulaqancin da zanyi sati inajin ciwonshi gwara na haqura nahau cab"

"to idan muka koma gida akace ina motar fa?"

"Sai muce ta lallace ne tana school gobe zamuje da mechanic ya gyara"


Kada kai batool tayi
"to shikenan, amma gayen nan beda mutunci sam"

"fadi 6ata baki, kwata2 halinshi yasha banban dasu, wani mummuna dashi"


Dariya batool tayi
"idan mummuna ne to shima Deen mummuna ne tunda kamar su daya"

"whatever" inji zee tana juya idanu


Haka suka tsaya suna jiran cab dazai kaisu gida

Saidai duk wacce tazo wucewa idan suka tsaidata bata tsayawa bare ma akaiga a daidaita


Wasa wasa suna nan tsaye har tsawon Mintuna talatin, ga Cab din na wucewa amma yadda kasan basa ganinsu don ko alamun tsayawa babu wacce tayi wajensu

Abin mammaki kuma wasu cab din saisu wucesu suje su tsaya agaban wasu dasuma suke jiran abin hawan, sai gashi dik wadanda suka taddasu can sai tafiya suke


Abin sosai yabasu mammaki don duk tsaidawar dasukema cab basa tsayawa yadda kasan they are invisible, ahaka har sukayi awa daya tsaye bakin titi.

Izuwa lokacin duk sun gaji ga rana daketa kwalarsu

Suna tsaye motarshi tafito daga makarantar tazo taja burki a gabansu


Sauke glass din gefenshi yayi yana kallonsu fuskarshi dauke da smirk


"na gayamaki, am a king, I rule. Tunda nace saina gama abinda nakeyi na tafi sannan zaku tafi, qaramar qwalwarki yakamata ta gayamaki Hakan za'ayi.

Ko zaku shekara anan babu wanda zai tsaya bare yaji ina zaku ya kaiku.

Yanzu kunada za6i biyu, Is either kuje ku dauki motar ku kutafi ko kuma kuje gida qasa, have a nice day"
Yana kaiwa nan ya wana glass din motar sama ya ja motarshi yawuce yabarsu anan.


Bin motar sukayi da kallo har tayi nisa

"kutt... Wlh gayen nan kwahi yaimana" inji batool saikuma ta fashe da Dariya

Wani qululun baqinciki ya tokarema zee wuya

"kwahi? Aikau Saidai yau mukoma gida qasa, allah bazan shiga motar nan ba" inji zee cikin kunar rai tanajin kamar tayi kuka

Wata Dariyar batool ta fashe daita tace
"ana nan dai, ai two option yabada is either mutafi mu dauko motar ko mutafi a qasa, kinga idan ma kika tafi a qasan duk cikin option dinshi ne, gwara muyi fuska muje mu dauko motar kawai"

Haushi zee taji yaqara qumeta

"nikuma baxanyi ko daya daga ciki ba, bari kigani" tafada tana zaro wayarta daga cikin jakka

Number Aymaan ta lalubo ta buga Saidai akace a kashe take, sake bugawa tayi nan ma haka

"ki bugama Ahmad yazo ya daukemu number Aymaan bata shiga"

Wayarta batool ta zaro don yin yadda tace din Saidai shima bata shiga

Number Aysha zee ta lalubo tsabar dai tanason proving dinshi wrong Saidai itama tata bata shiga

"omg! Wlh gayen nan dagaske yake, Ato tun wuri bari kiga muyi yadda yace" inji batool tana Dariya sosai wanda ita zee Dariyar ke qara tunzurata don ita bataga abin Dariya ba anan


Anan batool tabarta tsaye tana ta lalube laluben numbobi tawuce cikin school din don dauko motar.

Harta dauko tadawo zee nanan inda take tanata jaraba kira amma still basa shiga gashi taqi haqura

Parking kusada ita tayi ta leqo tace
"zee wlh kitaho mutafi, tunda yace Hakan Hakan za'ayi, bakisan kwahin yan biyu ba ko?"

Ko kallonta zee bata yiba

"haba sis kitaho mutafi kiyi hqr, ko babu komai in-law dinki ne, qila wasan qanen miji yafara yimaki tun yanzu"

"batool, wlh tlh ki kiyayeni, tom" inji zee cikin quluwa


Dariya batool ta fashe dashi tana rufe baki

"to kiyi hqr nabari, yanzu dai don Allah kishigo mutafi"


Saida batool taita roqonta tareda rarrashi sannan Dakyar ta yarda ta shigo motar sai kumburi take itakau batool banda qumshe Dariya babu abinda takeyi, taja motar suka halba titi suka dauki hanyar gida


Ranar da 6acin ran abinda mussadiq yayimata ta kwana ga haushin batool dake mata Dariya every now and then


Washegari Zee na zaune a aji tana ida wani rubutu kafin ta tashi ta fita wani student yazo wajenta yayimata sallama

Dagowa tayi ta kalleshi ta amsa tana mashi kallo mai alamar tambaya


"you're called in bio-chem lab"

"bio-chem lab? Ni?"

"eh, koba kece Zainab Farouq ba?"

Kada kai tayi
"eh nice"

"to you're called"

"ok thanks"

Binshi da kallo tayi harya fita tana Tambayar kanta neman me akeyi mata to?

Kasa ida abinda takeyi tayi ta tattarasu ta zuba cikin jakka ta tashi ta fita


Direct laboratory din tanufa

Kofar arufe take Hakan yasa ta bubbuga

Izinin shigowar da aka bata yasata tura kofar tashiga ciki


Qarasawa tayi ciki da sallama Saidai kingin sallamar sun maqale ne lokacin da sukayi ido hudu da juna


Tsayawa tayi tana kallonshi cikin mammakin ganinshi anan sai kuma takama waigen lab din don ganin wanda yasa a kirata amma babu kowa ciki sai shi kadai

"ni nasa akiraki" yafada yana dan ta6e baki

Maido kallonta tayi akanshi tana jin wani qululun haushi na tasomata

"sit, kin tsaya kina kallona da wadannan idanun, I don’t like them"

_O'O! I don’t like them_
Maganarshi ta yanzu ta tunomata da maganar Deen


Juyawa tayi zata koma ta inda tafito

"ba cewa nayi kifita ba"

"Sai kace? I did what I want at the time I want to"


"kuma shine nasa kizo nan kika zo din?"

"that's because bansan kaine ba and now that I know am doing the right thing" tafada tana nufar kofa

Batasan ya akayi ba sai kawai taji ansha gabanta, it's so sudden har Saida tadan ja baya a tsorace

"bakiyi abinda ya kawo ki ba zaki tafi? You must be joking"


"look mallam get out of my way, meye zaka wani taremin hanya?"

"saboda ban gama dake ba kike niyyar tafiya, kibari nabaki izinin yin Hakan tukkuna"

"waxaka ba izini? You must be joking"


Nufota yayi cikin majestical takunshi yana matsowa daf daita
"Did I look like a comedian to you?"

Dan takawa baya tayi ganin kusancin na neman yin yawa tana kallonshi shima ya tako, with every takunta baya shikuma takushi ne towards her

"wai meye Hakan ne? Get out of my way" tafada tana kallonshi gabanta na dan faduwa

"banyi abinda yasa nakiraki ba"

"meyasa ka kirani din? I thought kace nabar bibiyarka yanzu cikin ni dakai wake bibiyar wani?"

"ke lokacin dakika bibiyeni na hanaki Hakan?, nima yanzu its my turn so is better ki saurareni ko in saki saurarona don dole"


Yanayin dayayi maganar yana qara matsowa gabanta yasata danjin tsoro

"naji dakata... Ina Jinka, Menene?" tafada cikin quluwa

"sit first"

"sauri nake, basai na zauna ba, fadi abinda zaka fadi naqara gaba"


"tun jiya ya kamata kisan duk abinda nace ba'a yimin gardama, ki zauna konasaki zaman kwana uku batareda kin iya ko yunqurin tashi ba"


Besan sadda murmushi ya kufce mashi ba ganin tayi saurin neman wuri ta zauna tun kafin ma ya ida


"Good for you" yafada yana qara murmushin shi na gefen baki

"kaga inada abinyi, Menene?" inji zee dake jin kamar taita ihu, gashi sotake ta tashi amma tsoro takeji yace zai zaunar daita takasa tashi na kwana uku, kenan kwahi zai sake yimata?

Haye dogon desk dake gefe yayi ya zauna sannan ya kalleta yace
"magana zamuyi"

Shiru tayi batace komai ba kuma bata kalleshi ba

"meyasa kikabar Annur?"

"saboda naga dama" ta amsa a qulle


"wannan ba amsa bace, I repeat meyasa kika bar Annur?"

"bansaniba, look mallam inada abubbuwan yi dayawa, danasan kaine tun farko baxakaga qeyata anan ba"

"da kinsani kikace, idan kinji ance danasani to abin yariga yafaru babu yadda aka iya akai don haka kiyi shiru kibani amsata" yafada commandingly

"kai kasani a school din Da zakazo ka tsareni kana tambayata meyasa nafita, nina shiga saboda ina ra'ayin Hakan kuma nafito a lokacin danake so"

"Ko ya fiddaki ba"

"waye?"

"kin fini sani. tell me, meye hadinki dashi?"

"shi wa?" ta tambaya tana mashi wani kallon haushi

"wannan mahaukacin dake binki akoina waiting for opportunity don nuna gwaninta, bayan duk kuri ne" yafada yana yatsina fuska

"oh? Kana nufin wanda yasan darajar mace kuma yake kishin ganin anci zarafinta?"

"A'a, ina nufin wanda burinshi yasamu dama koyaya ne na nuna gwanintarshi ta bogi ga mace"

"kuma saigashi gwanintar tashi ta bogin ta qayyatar don sau dubu yafi mai daga hannu da niyyar dukan mace"


Dan murmushi yayi sannan ahankali ya zare shade din idanunshi

"waya koyamiki baqar magana?"

"idan ka gama zan tafi inada abubbuwan yi" tafada tana kauda kai gefe

"riqeqi nayi dama? Kawai dai kisani da kin tashi batareda nagama ba tau zaki kasance a tsaye har gobe warhaka or better still kiyita tafiya har gobe warhaka"


Jitayi ranta ya qara 6aci

"Me kake nufi da Hakan? Kwahi zakayimin?" tafada a fusace

Wannan karon he can't help but chuckle

"kwahi? Meye Hakan?"

"kafini sani, cemaka akayi don jiya kayi min shizaisa naji tsoron ka?!"

Yanzu ma murmushi ya kufce mashi mai sauti wanda Hakan yaqara lo6ar da dimple dinshi

"kinga, am here for something different gashi kina samu muna wata maganar daban, you're wasting my precious time"


Kasa magana tayi saboda haushi, wai ita kema 6atamashi lokaci


"nasan shi ya fiddaki a school din saboda wani banzan dalilinshi na kareki, abinda besaniba shine am limitless, ina keta duk inda naga dama a lokacin da naga dama, the guy is so full of himself bayan babu abinda yasani sai hauka, maybe shiyasa tun farkon haduwata dashi naji beyimin ba, it's better ki bashi shawara tunda kunfi kusa akan yasan dawa dawa zaija da don sahun giwa ya take na raqumi, yayi kadan yaja dani, daga mashi kafa nake and I don’t think zan cigaba da daga mashi Ita"

Dakatawa yayi yaji ko xatace wani abu saiyaga batada niyyar cewa komai don bama shi take kallo ba

Hakan yasashi cigaba
"secondly, maganar dakika fadamin ranar a office is still stocked in my brain, bansan ma'anarta ba Amma I bet you zan sani, zan gano Saidai ina baki shawarar don’t try to play cunny plays with me don am a turtle itself, slow but cunny. Kifita daga harkata for your own Good"

Qara Dakatawa yayi yaji me zatace Saidai still tayi mashi shiru Hakan yasa yasan maidashi fool tayi wanda dama best answer dinshi shine shiru, Saidai Hakan be dameshi ba tunda dai taji duk abinda yace kuma dama ba wadannan magangganun kadai suka kawoshi ba harda wani dalili nashi daban so be damu ba.


Tashi yayi tsaye yana maida shade din hannunshi a idanu

"fatan kin fahimci dukkan magangganuna kuma zakiyi amfani dasu.. For your own Good... Have a wonderful day" Yana kaiwa nan ya juya yabar lab din in his usual majestical steps


Ajiyar zuciya zee ta sauke, lallai mutumin nan ya cika dan rainin hankali, ita duk acikin magangganunshi babu wanda tayi mata ma'ana

"mtcheew, aikin banza kawai" tafada tana miqewa tsaye itama ta fita daga lab din


Daga ranar kuma bata sake ganin ko mai kama dashi ba a school din.


Everything keep going smoothly har kwatsam watarana ta tashi da text din Aysha a wayarta


*_Am sick, ki tayani da addu'a, I don’t know if I can survive it_*


Sosai hankalin zee ya tashi lokacin dataga text din.

Sukan kwana biyu yanzu basuyi waya ba don sun rage waya ba kamar da ba kuma zee na kyautata zaton har lokacin fushi take saboda tabar Annur don tun a lokacin tadan ja baya kadan da ita, suna yin waya amma not very often kamar da


Babu 6ata lokaci ta kira number tata Saidai bata shiga Hakan yasa hankalinta qara tashi


Koda tagayama batool saita bata shawarar su gwadawa ummie suji ya zatace


Koda suka gwadawa ummie itama ummie ta nuna damuwar ta akai sosai sai tace ya kamata suje su dubota

Jin Hakan yasa zee qwalalo idanu

Da farko taso qin yarda amma sai Ummu batool ta nunamata muhinmmancin yin Hakan kuma bayan Hakan Aysha nada kirki sosai ta yaba da hankalinta kuma tunda har ta iya yimata text tana a halin ciwo be kamata tayi watsi daita ba

Da Hakan zee ta yarda da zuwan amma deep down a tsorace take, babu wanda take fargabar haduwa daita kamar ummie don ko muryarta taji ta waya sai tajita wani iri bare ace taganta a zahiri.


Ahakan suka yanke shawarar gobe insha allah zasuje don dama zee tasan address dinsu don Aysha ta dade da bata complimentary card dinta.


Washegari daya kama saturday suka shirya wajajen bayan la'asar suka fita suka hau cab don motar batool tasamu matsala tana wajen gyara ga Aymaan tunda safe yafita don kwanan nan he's always busy.


Cab suka tsaida suna fadamashi unguwar dazasu yace su shigo don unguwar sannaniyar unguwa ce a garin.

Shiga sukayi sannan yaja motar suka shilla


Tunda suka shigo unguwar suke kalle kalle ta window, unguwar is so silent ga street din very smooth ga gidaje masu shegen kyau sunata wucewa

Ahaka har sukaji Motarsu ta tsaya

Kallon kofar tangamemen gidan dasuka tsaya sukayi sannan suka kalli juna

Batool ce tafara bude murfin kofar tafita sannan itama zee ta fito

Tsayawa sukayi kallon kofar gidan cikin shagaltuwa

Saida mai cab yayi masu horn sannan suka tuna basu sallameshi ba

Zee ce ta zuge jakkarta ta sallameshi sannan ta dawo wajen batool suna cigaba da kallon tangamemen gate din gidan

Su tunaninsu ma ta ina zasu fara bubbuga gate din


Qarasawa sukayi bakin qaramar kofar dake maqale da gate din batool tashiga kwankwasawa


Basu dade suna kwankwasawa ba aka bude wani dan taga dake daga saman qaramar kofar gate din ana leqosu

"yes? Kusu wanene?" inji mai leqen

Kasancewar da larabci yayi magana batool ce ta amsa

"mu qawayen Aysha ce, munzo ganinta fatan nan ne gidansu"


Shiru yayi yana kallonsu, can yace

"bari nakira na sanar, suwaye za'ace?"

"kace da Zainab da batool ne"

Be sake amsawa ba ya maida Wurin ya rufe

Kallon juna sukayi

"kaji manya" inji batool tana chuckling

Dan ta6e baki zee tayi batace komai ba


Suna ahaka sukaji alamun za'a bude kofar Hakan yasa suka maida hankali kanta


Kofar gabadaya aka bude yanzu mutumin dazu yasake bayyana

"bismillah, kushigo ciki"

Batool ce tayi gaba zee na biye daita suka shiga gidan

Dan Wara idanu sukayi ganin tafkeken qayattacen gidan dasuka tsinci kansu aciki

"muje" inji wani daban mai irin shigar wanda ya bude masu gate

Binshi sukayi abaya suna taka shinfidaddiyar kwalta din wajen suna bin silent street din wajen da kallo da yadda aka qawata koina da furrani.


Sun danyi tafiya sannan suka qarasa main entrance din


Door bell mutumin daya rakosu ya danna, can bayan some seconds aka bude kofar wata maid ta bayyana

Sannu da zuwa tayimasu sannan ta kauce tayimasu iso ciki


Yanzu ma batool ce tafara shiga zee na bayanta gabanta banda faduwa babu abinda yakeyi.


Wow! Kowanne yayi gasping a zuciyarshi ganin irin haduwa da tsaruwar da falon yayi.

Fadar irin qayatuwar da falon yayi 6ata baki ne Saidai mai karatu ya hasaso ma kanshi


Iso maid din tayimasu tana wucewa Wurin stairs

Cigaba da binta sukayi suna yi suna yan kalle kalle a falon


Hawan stairs din suka shiga yi wanda shima kanshi abin kallo ne suka cigaba da bin maid din har suka isa sama


Wani falon suka sake iskewa sama wanda tsakaninshi dana qasa sun rasa wane yafi kyau, abu daya kawai suka sani, wancan na qasan yafi girma.


Cikin girmamawa maid din ta nuna masu wajen zama duk suka yima kansu matsugguni a kan dakkakun kujerun falon


Kan kace me? Har anfara cika masu gabansu da kayan motsa baki sannan aka tafi aka barsu bayan angayamasu suyi making kansu comfortable


Kasa ta6a ko daya daga cikin abubbuwan da aka ajiyemusu agaba sukayi sai kalle kallen dasuka cigaba dayi suna jinjina dukiyar da aka narkar wajen qera wannan qerarren gidan


Ahaka sukaji sallamar ummie cikin cool muryarta, muryar data sanya gaban zee faduwa


Amsawa duk sukayi suna Dagowa.

Gaban zee yasake yankewa ya fadi

Wasu irin emotions ne suka shiga building up a zuciyarta still idanunta akan matar da take Deen sak ajikinta


Harta qaraso ta zauna idanunta na kanta

Gani tayi tana magana fuskarta dauke da murmushi amma batasan me tace ba, hankalinta yayi nisa

Mintsinin da batool tayimata ya maido ta daga duniyar kallon ummie data tafi

Sai a lokacin taga ashe batool ta zamo qasa tana gaidata Hakan yasa itama zamowa qasa tana gaidata cikin rawar murya

Amsawa ummie tayi tana cewa su tashi su koma kan kujera amma sukaqi

Zee najin batool na Tambayarta ya jikin Aysha itakuma tana amsa mata da sauki sosai tana ma daki

Duk maganar dasukeyi zee kanta na qasa tana battling da hawayen dake son kwacemata

"wacece takwarata acikin ku?" inji ummie cikin fara'a

Batool ta nuna zee cikin murmushi

"Zainab.."

Dagowa zee tayi ahankali tasake kallonta

Miqomata hannu ummie tayi alamun tazo

Kamar wanda aka ingiza sai gani tayi ta rarrafa wajenta da sauri ta riqe hannun nata ta damqesu ta dora fuskarta akai hawayen datake riqewa suka 6allemata


Sosai Hakan yaba ummie mammaki don harda sheshekarta

To meya sata kuka? Ko tunani take jikin Aysha yayi tsanani? Tambayar da ummie tayiwa kanta kenan

Hakan yasata dago fuskarta tana share mata hawayenta fuskarta dauke da murmushi

"karki damu diyata, ai Ayshar ma jikin yayi sauqi, kibar kuka"

Wasu sabbin hawayen suka sake gangaromata

Wannan wane marar imani ne? Wane mai qonnaniyar zuciya ne ya raba uwa da danta na tsayin shekaru batareda kowannensu yasan da wanzuwar dayan ba? Wane marar imani yayi Hakan?


Jitayi ta tadota tsaye tana cewa sutaho takaisu su ganta don ita harga allah tayi tunanin ciwon Aysha din takema kuka


Tare suka jera suka tafi har suka isa bakin kofar dakin Aysha

Kwankwasawa ummie tayi sannan ta Murda handle din kofar tashiga hannunta jaye dana Zainab


A zaune Aysha take kofin shayi a hannunta da alamu shi take sha, ga hannun daure da cannular da alamun Saida akayi mata qarin wani abu ajikinta


Sosai Aysha ta wara idanu ganin su zee don bata ta6a zaton zatazo ba

Da sauri ta ajiye cup din hannunta ta Wara mata hannu zee tayi sauri ta qaraso itama suka rungume juna cikin shauqi suna Fashewa da kuka atare, kowanne da ma'anar kukan shi

Zee kukan da bata ida ba na dazu ne itakuma Aysha nata na daban ne.

"Ummie, na rabu dashi... Narabu da Umar.. Finally na rabu dashi" inji Aysha cikin kuka

Jin Hakan yasa zee Saurin dagota tana kallonta da mammaki

"kin rabu dashi?" inji zee cikin mammaki

Kada kai Aysha tayi hawaye nasake gangaromata

"eh, nima na gano Gaskiya ummie, Umar baya sona, Finally zuciyata ta yarda da Hakan. Ni kadai nake hauka na, Finally na gane Gaskiyar dakike son ganar dani, and I decided to let him go, Narabu dashi har abada Koda Hakan na nufin rasa rayuwata"

"bazaki rasa rayuwarki ba Aysha, ba akan wannan mutumin ba.. Don be cancanci Hakan ba, be cancanci Koda digon hawayenki ba, insha allah zakiyi farinciki without him, you'll move on zaki samu wanda nan gaba zaki waiwaya rayuwarki tabaya dashi kiyi murmushi kice gwamma da akayi"


Sake rungumeta Aysha tayi gam tanajin sauqin abinda takeji a zuciyarta a sanadin magangganun zee.


Murmushi ummie tayi sannan tajuya tabar dakin tana qara jin qaunar Zainab har cikin zuciyarta

Batool ce ta qaraso wajensu itama ta zauna ta kamo hannun Aysha Hakan yasa ta dago ta kalleta

"kiyi hqr Aysha, wani abin muna sonshi ne amma ba alhairi bane a garemu, wanda allah ya taqaitama wahala sune suke gane Hakan da wuri, Kiyi hqr kiyita addu'ar allah yasa Hakan shiyafi alhairi kuma ya za6a miki Mafi alhairi"


Haka sukaita bata shawarwaru da kwantar mata da hankali

Sai gashi taji sauqin zuciyarta sosai sanadin qarfin gwiwar dasukayita bata

Sai gashi daga baya ummie tashigo ta iske suna fira cikin nishadi Aysha harda Dariya

Sosai abin yabata mammaki, yarinyar da yau kwana uku kenan ko magana batayi sai hawaye

Dadi sosai ummie taji tafita tasa aka aika musu da abinci

Tare suka ci suna fira wanda Hakan ba qaramin taimaka ma Aysha yayi wajen rage nauyin zuciyarta.


Ganin magrib takusa yasa suka fara haramar tafiya

Duk yadda Aysha taso qara tsaidasu qiyawa sukayi don Saida ummie dama ta bige musu warning kan karsuyi dare.


Tare suka fito da Aysha falon saman suna tafe suna Dariyar firarsu

Qamshin turaren da zee taji yasata dagowa ta kallo falon idanunshi suka gauraya


Zaune yake gaban ummie aqasa yana dan mammatsa mata qafa

Saurin Janye idanunta tayi akanshi suna ida Qarasowa falon

Ganinsu yasa ummie fara washe baki

"tafiya zakuyi tun yanzu?" inji ummie

"wlh kau ummie, ance karmuyi dare ne" inji batool

"Gaskiya kam, Hakan yayi sosai ai mun gode qwarai, zuwanku ya samar da abinda kwana uku kenan muketa fama bamu samu ba, Allah yasaka da alhairi, allah yayimaku albarka"

Cikin jindadin addu'arta suka shiga amsawa da amin

Kallon mussadiq da kanshi ke qasa haryanzu yana cigaba da tausa kafarta ummie tayi tace
"kaga qawayen Aysha ko? Suna zuwa ta warware"


Dagowa yayi yaimasu kallon seconds 2 yace
"oh? Mungode"


"takwara wannan shine yayan Aysha, mussadiq"

Murmushi zee tayi sannan ta dan kalleshi
"Good evening" tafada tana dauke kai

"evening" ya amsa a taqaice batareda ya kalleta ba

"Good evening yaya" inji batool

Dagowa yayi ya kalleta sannan itama ya amsa a taqaice ya cigaba da abinda yakeyi


"bunnaya, ka tashi hakanan kaje ka saukesu gida kaga dare yafara" inji ummie

Atare duk suka kallo ummie cikin dan Wara idanu

"na kaisu? Basuzo da mota ba?"

"bazuso daita ba, ko?" ta maida akalar Tambayar kan zee

"eh.. Amma ai zamu samu cab, babu damuwa" tafada hoping bazata matsa masu yakaisu din ba, she dont want to have any thing to do with him again


"samun abin hawa anan unguwar ba qaramin wahala bane don basu cika Shigowa ba kuma idan kukace sai kunfita daga unguwar dare zakuyi, kubari yakaiku kawai, ai dama shima fita zaiyi yanzu"

"ummie.. Driver yakaisu mana. Ni inada urgent meeting dazanyi yanzu"

"nasan da Drivern nace ka kaisu ai, idan baxaka kaisu ba kafito ka fadamin sai nasan abunyi"

Sunkuyar da kanshi yayi don yasan haushi taji sai yace
"to ummie"

Dan hararar shi tayi sannan ta maida kallonta kan su zee tana cewa
"yauwa 'yayana kubari yakaiku kunji? Ina zuwa"

Daga haka ta tashi ta nufi dakinta

Shima tashi mussadiq yayi bayan wucewarta yanufi hanyar fita yana cewa
"Don't waste my time"


Binshi da kallo sukayi sannan batool da zee suka kalli juna sai zee taga kumshe Dariya ma take Hakan yaqara quleta saita dauke kai cikeda haushi

Ummie ce tasake fitowa riqeda yar shopping bag a hannunta tabasu

Dakyar tasasu amsa suna mata Godiya sannan suka rakosu har qasa har inda mussadiq ke jiransu cikin mota

Batool ce tayi saurin wucewa ta bude back seat tashiga leaving zee da only option din Shiga front seat

Badon taso ba ta bude kofar gaban ahankali tashiga itama

Daga masu hannu ummie da Aysha suka shiga yi suna masu fatan tsari suma suna maida masu martani ta hanyar daga musu hannu

Saida ummie taja mashi kunne akan gudu a titi sannan yaja motar suka bar gidan.


Tunda suka hau kwalta babu mai cewa komai sai motar tayi tsitt kamar babu mutane ciki

Dukda ummie tayi mashi gargadin gudu da mota Saida yayi dukda shi nan ba gudu yake ba Sosai, Saidai su zee a tsorace suke da speed din motar musanmman batool Saidai babu wanda yayi mashi magana allah allah kawai suke sukai gida ya saukesu

Abin mammaki sai gashi batareda sun mashi kwatance ba yabi dasu hanya tiryan tiryan har cikin unguwarsu kuma har kofar gidansu

Abin yabasu mammaki sosai don basu ta6a sanin yasan gidan ba.

Lokacin har duhu duhun magrib yafara

A kofar gidan yaja ya tsaya da motar daidai itama motar Aymaan tana danno kai opposite dinsu

Hango motar yasa gaban zee faduwa tayi saurin fara qoqarin bude kofar Saidai tajita gamm alamun a kulle take

Juyowa tayi ta kalli mussadiq a fusace daidai lokacin da Aymaan ya dallo hasken motarshi saitinsu


Saurin Juyawa tayi tana kallon Aymaan ta cikin motarshi wanda yayi mutuwar zaune yana kallonsu suma... ✍️


Ummin fasihu 🧚🏻‍♀�
8/2/21, 9:42 PM - Buhainat😝: *🙍🏻‍♂️DEEN 🙍🏻‍♂�*


*070*


*RIVALRY*


Komai na Aymaan ne ya tsaya lokacin da idanunshi suka hango mashi su


Ahankali ya Runtse idanunshi yasake budesu hoping zaiga wani abin daban amma still sune.


Zainab da wannan marar mutuncin a mota, a qarqashin rufin mota daya.


Wani abu da besan ko Menene ba yazo ya tokare mashi qirji wanda Hakan yasa yaji numfashinshi na bashi wuya Wurin fizgowa.


A bangaren su zee ma mutuwar zaune both ita da batool dake baya sukayi suna kallonshi


Zuciyarta ce tashiga racing sosai ganin yadda ya kafesu da idanu babu ko kyaftawa fuskarshi expressionless


Saurin sake kai hannu tayi Wurin lock din tana qoqarin budewa Saidai still gamm yake Hakan yasa tajuyo akan mussadiq dayayi balancing a fusace

"mallam meye haka wai? Ka budewa mutane kofa"


Dan kallonta yayi sai yayi murmushi yace
"saboda me?"


"saboda zan fita, am suffocating" tafada tana dan satar kallon Aymaan hoping zai iya jiyo abinda suke cewa kar yayi musu wata fassarar


"motata ce, lock dinane ba yanzu naga damar budewa ba, ai bani nace ku liqemun akan dole saina kawoku ba"

"muma cemaka akayi don son ranmu muka biyoka? Saboda ummie ta fadi Hakan kawai yasa muka biyoka if not ko kallo kasan baka ishemu ba"


"then sai kuyi hqr dani kokuma better still ku 6alle murfin kofar kufita"

Hakan yaqara harzuqa zee Saidai kafin tasake magana taji alamun tashin mota Hakan yasa ta waiga taga motar Aymaan ne tazo tawuce gate tayi horn

Ba'a dade ba aka bude mashi kofa ya danna kan motar ciki yashige.


Maida idanun zee tayi ta lumshe cikin wani yanayi Yayinda shikuma mussadiq yadanyi murmushin gefen baki


Qarar cire lock taji wanda ke nufin ya bude kenan


"out" yafada yana hada rai

Jin sautin bude kofa sukaji abaya batool ta fita

"Are you deaf?" mussadiq yaqara fada

Sotake tajuyo ta gaggayamashi magangganu amma qululun daya tokaremata qirji ya hana Hakan yasa kawai tasa hannu ta bude murfin motar tafita tabar mashi ita abude tawuce


Binta da kallo yayi harta shige don batool dama tana sauka taqara gaba don itama ta tsorata da yanayin Aymaan


Bude kofar nashi side din yayi shima yafito daga motar riqeda ledar da ummie tabasu wanda 6acin rai yasa zee mance ta


Gate din gidan yanufa inda maigadi ke qoqarin rufe qaramar kofar gate din


Miqamashi ledar yayi mai gadin ya amsa fuskarshi dauke da alamun tambaya

"na yanmatan dasuka shigo ne" Yana gama fadin Hakan ya juya ya nufi motarshi yashige ya tadata yajanyeta yabar kofar gidan yana jin wani nishadi a zuciyarshi


Zee data kusan kaiwa kofar main entrance taji kamar maigadi na qwalamata kira Hakan yasa ta dakata daga tafiyarta tajuyo tana kallonshi harya qaraso

Ledar hannunshi ya miqo mata yana cewa gashi inji wanda ya saukesu

Kallon ledar tayi taga wanda ummie tabasu ne, kamar karta amsa taji amma sai kuma ta amsa tayimashi Godiya sannan ta juyo da niyyar tafiya


Wani irin bugawa zuciyarta tasakeyi lokacin da sukayi ido hudu da Aymaan dake tsaye bakin kofa yana kallonta


Jitayi kamar ta saki ledar don rikicewa don sosai kallon dayake binta dashi ya rikitata

Ahankali ya dauke idanunshi akanta ya cigaba da warware hannun longsleeve din shirt dinshi wanda ya nannade wajen alwalla sannan yazo ya ra6ata ya wuce.


Sake tamke idanunta tayi cikin wani yanayi tanajin yadda zuciyarta ke bugawa har lokacin


Innallilahi, what's all these?

Ta dade sosai anan din batareda ta iya sake motsawa ba sai kuma tunanin kar yadawo ya taddata wajen yasa ta cira kafarta Dakyar ta wuce ciki


Tana shiga daki batool na fitowa daga bayi

Tsayawa sukayi suna kallon juna

Can batool ta qaraso ciki tana cewa
"Sai yanzu yabarki kika taho?"


Ajiyar zuciya zee ta sauke ta qaraso batareda ta amsa ba ta zauna gefen gado

"ya akayi kuma?" inji batool

"batool, yaya Aymaan fa ya ganmu" tafada tana kallonta

"nagani nima, am scared like hell, tunda nasamu nashigo ban ganshi ba na hauro sama da gudu, wlh haryanzu gabana faduwa yake" inji batool

"hmm naki mai sauqi ne batool, yanzu muka Hade dashi aqasa.. Kai damn this guy!" tafada tana dafe kai

"Menene kuma?" inji batool tana kallonta


"ashe mance ledar da ummie tabamu nayi a motar don 6acin rai, shine yazo yaba maigadi yakawo min, daidai na amsa ina juyowa muka sake ido hudu da yaya Aymaan kuma na tabbata yaji lokacin da maigadi ke cewa gashi inji wannan mutumin"


Wara idanu batool tayi
"what if yayi tunanin shiya baki?"


"abinda nake gudu kenan, dama tun farko banso zuwa gidan nan ba yanzu ga irinta, yanzu da wane ido zan sake kallonshi? Mutumin dayasa aka tsaremu dani dashi few weeks ago yagani taredani a mota harda saqon leda, kai" tafada cikin takaici

"Gaskiya kam abin beyi ba yanzu yaya zamuyi?" inji batool

Saurin juyowa zee tayi tana facing dinta
"don Allah idan yadawo kije ki fadamashi duk abinda yafaru, ki gayamashi muma bada son ranmu muka shiga motar ba, I just can't bear it idan ya cigaba da yimin wannan kallon"


Wara idanu batool tayi
"wa? Ni? Ca6 bakisan yaya Aymaan ba, Kodan kinga Koda yaushe yana washe baki? To wlh idan bude miki dayan shafinshi bayada kyau, ko giyar wake nasha bazan fara tunkararshi ba yanzu don qaramin aikinshi ne ya hurgadoni waje"

Sake dafe kai zee tayi, ita ba komai tafi jiba sai kar ya yimata wata fassarar kar girmanta dayake gani ya zube"


"amma karki damu, ta inda aka hau tanan za'a sauka kawai ummy zamu gayamawa ta gayamashi, nasan zai fahimta" inji batool

Dagowa tayi ta kalleshi
"dagaske?"

"sosai ma, zata fahimtar dashi"


Dukda Hakan ba taji dadi ba, kawai tuna irin kallon dayayi mata dazu takeyi ranta na qara jagulewa


Ranar kasa fitowa ayi dinner da ita tayi Duk kuwa yadda batool tayi tayi daita ta fito

Kawai jitake bazata iya sake hada ido da Aymaan ba, kunyarshi takeji sosai.


Kamar yadda batool tace ma zee Hakan akayi, Ummu batool suka samu sukayi ma bayanin komai harda ganinsu da mussadiq da Aymaan yayi suka kuma roqeta ta sanar dashi


Dariya Kawai ummy tayi tace shikenan zata gayamashi


Basu saniba ko ta gayamashi din don Aymaan beyi musu maganar ba kwata2, tun zee na noqe noqenta harta ware itama don wanda takeyi don shi bema damuba harkar gabanshi kawai yake kuma ko a fuska be ta6a nunamasu ba Saima cigaba da mu'amalantarsu dayayi kamar yadda yasaba.


Saidai a bangaren Aymaan abin na nan a ranshi tun lokacin daya faru.


Shi kanshi be iya musalta yadda yaji ranar da yaga zee agaban mota tareda wani, wanin ma mussadiq

Dakyar ya iya shiga da motarshi yayi parking yafito ya wuce cikin gida yana jin kamar zuciyarshi zatayi exploding at any moment


Babu tunanin da zuciyarshi bata kawo mashi ba akan ganinsu dayah

Be ta6a sanin yanada kishi har haka ba sai ranar


Dakyar yasamu yayi alwalla yafito don lokacin sai kiraye kirayen sallar magrib akeyi


Saukowa yayi daga stairs din ahankali still yana jin yadda zuciyarshi tayi mashi jingim

Saidai me? Yana bude kofa yasakai zai fito yaga maigadi yana bata shopping bag wai gashi abata inji wannan gayen

Ga mammakinshi kuma saita amsa tana Godiya

Jiyayi kamar an makamashi guduma akai a lokacin

Jiyayi kamar zuciyarshi zata fashe a lokacin

Cikin qarfin hali yazo ya ra6ata ya wuce batareda yasake kallonta ba yana jin kamar akan gajimare yake tafiya ba qasa ba


Be dawo ba sai bayan isha'i, kuma Koda ya haye sama yashige dakinshi Be qara saukowa ba don baya buqatar sake ganinta a lokacin don shikadai yasan yadda zuciyarshi ke mashi


Washegari ne bayan yadawo daga aiki ummy ta iskeshi har daki inda anan ta gayamashi duk abinda yafaru

Yaji dadi jin zarginshi be tabbata ba Amma dukda Hakan abin bebar yimashi zafi ba, duk lokacin daya tuna Da image din zee da mussadiq agaban mota sai ranshi ya 6aci, he can't help but notice yadda sukayi matching dajuna sosai.


*BAYAN KWANA UKU*


Tafe suke suna hira jefi jefi kowanne da littafi kare a goshin shi saboda ranar da ake qwalawa

"kai wlh garinnan badai zafi ba, ina ganin weather din Nigeria is harsh ashe tanan tafi?" inji zee

"hmm kema kya gani shiyasa idan zafi yashigo har wani baqi na musanmman kakeyi, fararen sukoma baqaqe baqaqen kuma su qara extra runewa" inji batool


"Ca6 amma kuna qoqari, yanzu idan azumi yazo fa ya zakuyi?"

"ji wata tambaya, daga azumin zamuyi saboda ana zafi? Dole muyi ko muci ubanmu"


Dariya zee tayi tace
"wa zaici ubanku?"

"Yana can yana jira da sanda, gwara ka taimaki kanka duk wuya kayi" inji batool

"hmm Gaskiya bana jin ina iya azumi a qasar nan, kutt! Yanzu fa zafin yafara Shigowa ina ga cikin azumi lokacin ana tsakiyar zafi?"

"aikau wlh babu inda zaki, sai kin dandana kema, kutt! Aikau wlh karma kifara, azumi sai kin yishi anan kiji ingayamiki"

"Sai ki hanani tafiya to idan kina iyawa" inji zee tana Harararta

"tsaf ko, allah ya kaimu lokacin kiga ikon allah"


Da haka suka qarasa food canteen din school din suka shiga

Akwai yan mutane ciki inda Mafi yawanci abin sakawa aciki yazo nema wasu kuma fekewa sukayi ma hot ranar waje

A cikin wajen akwai tebura da kujerun zama

Kowanne table zagaye yake da kujeru uku.


Batool ce ta nufi wani table dake daga gefe taje taja daya daga cikin kujerun dake zagaye dashi ta zauna


Yayinda itakuma zee tawuce siyomasu abinda sukeso


Ruwa da drinks masu sanyi ta siyo masu tareda peanuts


Dawowa tayi ta iske batool na waya

"ok ganinan, nima yanzu nashigo canteen, ok ganinan zuwa"

Zama zee tayi
"keda wa?"

"nida farhana, wai inzo anfara submitting wannan assignment din"

"amma saimun gama sannan ko?" inji zee

"Sai mun gama me? Dole naje nabada yanzu ga lecturern ba mutunci ya isheshi ba" tafada tana tashi tsaye

"to yanzu zaki dawo ko?"

"eh mana, kawai badawa zanyi indawo" tafada tana wucewa

Maida hankalinta tayi kan abubbuwan gabanta ta bude ruwa ta zuba a dan kofin robar da ake siyarwa tareda ruwan, ta zuba aciki takai baki tafara sipping tana lumshe idanu jin sanyin ruwan na ratsa mata bushashen maqoshinta.

Bata ajiye kofin ba Saida taga bayan ruwan sannan ta sauke cup din tana Ajiyar zuciya


Jitayi kamar ana kallonta Hakan yasata bude idanunta dake lumshe tunda tafara shan ruwan


Jada baya tayi babu shiri cikin tsoro a sanadin abinda idanunta sukaci karo dashi

Razanar datayi yasa kingin ruwan da basu ida wucewa ba kwareta tashiga tari babu kakkautawa


Dago idanunshi dake cikin spec sa6anin shade daya saba qwamawa yayi ya kalleta

Ganin dagaske take tarin yasashi saukar da qafar dayayi crossing yana kallonta

"hey, are you ok?"

Cigaba da tarin tayi hannunta dade da baki idanunta har sunyi ja

Hakan yasashi saurin sake daukar kofin gabanta ya zuba wasu ruwan yakai mata saitin baki


Kasancewar a lokacin babu abinda take buqata kamar abinda zai tsayar mata da tarin yasa babu musu itama ta matso jikin table din daya raba tsakiyarsu ya kafamata kofin a baki tashiga shan ruwan


Saida tadan sha dayawa sannan ta kauda kai Hakan yasashi shima Janye kofin daga bakinta


Ahankali take sauke numfashin tarin datayi

Hanki fari qall taga ya miqo mata, batace komai ba ta amsa tashiga goge gefe da gefen bakinta daya 6aci da ruwa

Tana cikin gogewa kamar ance ta kalli bakin kofar Shigowa Wurin, sai idanunta sukayi mata mummunan gani.


Dammm qirjinta ya buga lokacin ta hangi Aymaan tareda batool tsaye bakin kofar sun kafamata idanu


Batasan lokacin da ta saki hanki din hannunta ba Cikin tsananin kidima


Ganin yanayinta dakuma kafe waje guda da idon dayayi yasa shima mussadiq kallon inda nan shima idanunshi suka gano mashi Aymaan da haryanzu ke tsaye kamar statue a inda yake idanunshi sunyi wani irin mugun kadawa

Dan daga girarenshi mussadiq yayi ya ta6e baki sannan yakoma yasake balancing a kujera


Ahankali Aymaan yashiga Takowa wajensu still idanunshi akansu babu ko kyaftawa


Zee jitayi kamar tajita ta 6ace daga wajen, sosai yanayin Aymaan ya razanata don tunda tasanshi bata ta6a ganinshi cikin irin wannan yanayin ba.


Qarasowa wajen yayi ahankali shima yaja dayar kujerar data rage ya zauna


Sauke idanunta zee tayi tana jin yadda jikinta ke rawa innerly


Jawo peanuts din gaban zee yayi batareda ya kalleta ba ya bude seal din yashiga dauka da daddaya yana sakawa a baki yana tauna ahankali

. Wurin ne yayi shiru, very tensed ga zee data kasa Dagowa har lokacin Yayinda mussadiq ko ajikinshi danna wayarshi ma yake hankali kwance


Can ya dago daga danna wayar dayake ya kalli zee directly wanda idanunta ke a qasa har lokacin

"so what did you say baby? Wancan din yayi miki ko a chanza wani?"


Dagowa zee tayi a mammakince tana kallon mussadiq dake kallonta shima

Baby? Wacece baby?

"bakice komai ba dear" yafada softly yana mata wani kallon qasan ido irinna masu jin barci


Cikin tsananin mammaki take kallonshi sai kuma ta kalli Aymaan dake taunar peanuts din bakinshi

Shima mussadiq kallon Aymaan din yayi saiya daga gira data

"oh! Nagane.. Nagane. Shikenan zamuyi waya, I'll take my leave yafada yana maida wayarshi a aljihu ignoring kallon shock din da zee ke mashi yafara qoqarin tashi


"ina zaka bayan baka gama ba?" inji Aymaan batareda ya kalleshi ba

Dakatawa mussadiq yayi daga tashin dayayi niyyar yi don dama abinda yake so kenan, ya tanka


Maida kallonshi Aymaan yayi akan zee da har lokacin takasa ko motsi


"ki bashi amsar shi mana _*baby*" yafada yana kallonta, kallon dake dada Kada yan cikin ta


Girgiza kai tafara tana qoqarin lalubo voice dinta dataji tarasa nan take mussadiq ya katse ta

"karka damu, maganar tsakanina da ita ne, zamu qarashe a waya"

Dagowa Aymaan yayi a karo na farko tunda ya zauna ya kalleshi straight in the eye

"who are you? How dare you?" yafada in a low dangerous voice


Murmushin gefen baki mussadiq yayi yace
"wanne kake son na amsa daga ciki?"

"kanada wani irin qarfin hali, an ta6a fadamaka Hakan?" inji Aymaan yana kallonshi eye-in-eye

Qara Sakin shegen smirk dinshi yayi
"kanada abin ban Dariya, an ta6a fadamaka Hakan?" yafada shima yana kallonshi eye-in-eye


Murmushin dayafi kama dana takaici Aymaan yayi yace
"A'a, amma ba abin mammaki bane idan ka fadi Hakan don abinda zaiba mahaukaci Dariya ba lallai bane yaba kingin normal people ba"


"Careful now, don’t let your brains go to your head�"

Katse shi Aymaan yayi da
" Brains aren’t everything. In fact, in your case they’re nothing"


Dan murmushi mussadiq yayi yace
"you know what? Nasha wannan tunanin, I don’t know what makes you so stupid, but it really works"


" I’d explain it to you, but your brain would explode" inji Aymaan

Sunkuyowa mussadiq yayi gaban Aymaan wanda Hakan yaqara basu kusanci
"you know what? Anyone who told you to be yourself simply couldn't have given you worse advice.. So be yourself" ya miqe tsaye

Shima miqewa Aymaan yayi
"I do heed to advice, but if I Said advice.. I mean advice given By a sane being"

"sane or insane.. I don’t care, all I know is am advising you to stop sticking your nose into my business.. For your own Good"


Zai wuce Aymaan ya sha gabanshi

"and where did you think you're going? Am not done with you yet" inji Aymaan da kallo daya zakamashi kasan bala'i ke cin zuciyarshi

"yaya Aymaan..." batool data qaraso Tundazu tafara fadi Saidai kallon daya watsa mata yasata kasa idawa

Maida kallonshi yayi akan mussadiq dake kallonshi sheqeqe

"ba'a taka ko baki bakin gonata, meya kaika ra6arta?" inji Aymaan yana kallon mussadiq da bloodshot eyes dinshi, kallo daya zakamashi kasan baya cikin hayyacinshi, fushi ya fiddashi daga hayyacinshi kamar yadda yasaba yima masu haquri da aka kai bango

Yar Dariya mussadiq yayi
"yaushe ka chanza sana'a? Koma yaushe ne am sorry to say anci baya Sosai, From Likita to manomi"

"abin bazai ida baka mammaki ba sai na chanza daga manomin zuwa mafed'i"

"Yaya Aymaan, don Allah ka saurareni.. Please" inji zee da duk take a tsorace da yanayin kowannensu


Be kalleta ba ya cigaba da cewa
"answer me, wani tsautsayi yasaka ra6ar gonata?!" Yafada cikin qaraji

"yaya Aymaan please.. Look kallonmu akeyi" inji batool cikin tsananin tsoro

"ra6a? To ka jira, nan bada dadewa ba zan shige cikinta tsamo tsam.."

Naushin da Aymaan yakai mashi ya katse shi yayi saurin tarewa da hannu

Girgiza mashi kai mussadiq yashiga yi yana murmushi
"karka soma.."

Bangajeshi Aymaan yayi da dukkan qarfinshi wanda Hakan yasa yayi taga taga zaya fadi sai kuma yaci nasarar tsaida kanshi

Dagowa yayi ya kalleshi a fusace

"alright.. You'll get it"

Nufoshi yayi shima Aymaan ya Nufoshi suka cakumi juna


Kan kace me fada ya kaure aka shiga musayar blows🤜🏻🤛🏻


Wajen ne ya rikice don dama tunda suka fara hankalin kowa yadawo kansu.


Bugun juna sukeyi with all their strength kowanne na qoqarin huce haushin dan uwanshi daya dade danqare a zuciyarshi


Sosai jikin zee ke rawa, hannayenta rufe da baki hawaye na rige rigen gangarowa a fuskarta.


Dakyar mazan food canteen din suka samu suka 6an6aresu daga jikin juna kowannensu da irin ciwon dayaji a wajen dan uwanshi


Aymaan dayafi zuciya aka shiga qoqarin fitar dashi daga canteen din yana fizgewa yana zagin mussadiq da shima ake riqe dashi cikin canteen din

Dakyar aka samu aka fiddashi daga canteen din su zee na biye dashi suna hawaye

Fizgewa yayi daga riqonsu a fusace yana dakamasu tsawa akan su sakeshi

Sakinshi sukayi suna son ganin ko komawa zaiyi saiya juya ya nufi motarshi hannunshi daya dafe da kai


Saurin maramashi baya zee tayi

"yaya.. Yaya Aymaan please listen to me"

Ko kallonta beyi ba ya cigaba da tafiyarshi harya kai Wurin motarshi ya bude kofar

Riqe kofar itama tayi cikin kuka

"Aymaan ka saurareni mana.. You're going nowhere in this condition!"

Juyowa yayi ya kalleta da rinnanun idanunshi
"as if you care " yafada ahankali


" whatever yaya, just listen, I..."

Katseta yayi ta hanyar daga mata hannu sannan kuma ya Hade taffukanshi waje guda 👏

"spare me that.. Please"

Ya ida bude kofar yashige

"Akhie.." batool tafara

Jawo murfin kofar yayi ya rufe da qarfi sannan yaja motar da mugun qarfi yabar wajen


Bïñ motar sukayi da kallo devastated.


***


Tunda ya hau titi yake tsula wani uban gudu kamar mai gasar tsere, babu ruwanshi da bin dokokin hanya kawai kutsawa yake yana driving yadda yaga dama


Saida yayi nisa sosai sannan yasamu wuri ya gangara gefen titi yayi parking ya dora kanshi bisa sterring yana sauke numfashi ahankali


Ya dade ahakan sannan ya dago kanshi ya jingina da kujerar bayanshi


Tunawa yayi da yadda komai yafaru.

Hanya ce ta biyo dashi hanyar school dinsu, sai yaji babu abinda yakeson gani kamar ita saiya yanke shawarar shiga school din


Yana parking a inda ake parking yafito ya shiga makarantar

Harya fara shawarar ta ina zai fara nemansu sai kamar wasa ya hango batool tana ta sauri

Sunanta yakira da qarfi Hakan yasa ta tsaya tajuyo ta kalleshi

Wara idanunta tayi saita Nufoshi shima ya nufeta suka Hade a hanya

"ina zaki?" injishi

"Wani assignment zanyi sauri nabada"

"ina Zainab?"

"Tana food canteen, tarema muke assignment kawai zan bada nakoma"


"ok muje na rakaki sai Mukuma canteen din"


Tare suka je department din nasu tayi submitting sannan suka juyo suka dawo suka kama hanyar canteen din


Qarasawa bakin kofar wajen sukayi suka shiga

Idanunshi ne ya sauka a kansu suka yimashi mugun gani

Wannan marar mutuncin ne ya sunkuyo yana bata ruwa abaki tana sha

Saida tagama sha sannan ya ciro hanki yabata tana goge bakinta dashi

Mutuwar tsaye yayi Yayinda yaji komai na kwance mashi, zuciyarshi ta tasomishi har wuya yanajin kamar zata biyo ta baki ta fito waje and daga nan yayi loosing control har duk abinda yafaru yafaru


Haryanzu kuma be daina jin radadin da zuciyarshi ke mashi ba

Lumshe idanunshi yayi yafara ambaton allah a zuciyarshi har yasamu tadan yimashi sauki


Bude rinnanun idanunshi yayi yana furzar da huci sannan ya sunkuya ya dauki gorar ruwa wanda yasaba ajiyewa a gaban mota ya 6alle murfin ya kafa kai dukda ba wani sanyi garesu ba ya ida tuttula sauran a kanshi sannan ya qara Sakin nannauyan Ajiyar zuciya


Lalubo wayarshi yayi cikin aljihu ya Fiddota

Number Ahmad yashiga nema Saidai kafin ya ganota kira ya shigo wayar

*Ahmad* yaga yana yawo a screen din wayar

Wani numfashin yasake saukewa sannan ya daga kiran ya kara a kunne

"kana ina?" inji Ahmad ta cikin wayar

"ina nan" Aymaan ya amsa a taqaice

"to kayi maza kazo Aymaan I have a huge surprise for you please"

"Menene?" inji Aymaan moody


"kawai kazo please, its urgent, ina office idan kuma baxaka iya zuwa ba ka fadamin inda kake zanzo"

Jin seriousness din Muryarshi yasashi fara wondering meke faruwa

"ok, ganinan" yafada yana katse kiranshi

Ajiyar zuciya ya sauke sannan ya sake tada motar yahau kan titi yaja wannan karon cikin normal speed


A parking space yayima motarshi matsugguni sannan ya fito daga cikinta ya rufe

Kallon harabar kamfanin su Ahmad din yayi sannan ya sake furzar da huci yafara tafiya yanufi ciki not minding yadda kayan jikinshi sukayi squeesing sukayi kaca kaca ga ruwan daya sheqawa kanshi dazu a mota, yadai koma gashinan dai kamar sabon kamu


Direct elevator yashiga ya danna floor din da office din Ahmad yake, cikin qanqanin lokaci ya isa wajen

Fitowa yayi daga cikin elevator din ya wuce office dinshi Direct


Kwankwasawa biyu yayi aka bashi izinin Shigowa

Murda handle din yayi ya tura kofar yashiga

Dagowa Ahmad yayi daga laptop din gabanshi, Ganin Aymaan ne yasashi saurin tashi tsaye yana cewa

"omg! Tun dazu sai yanzu ka iso?" Sai kuma ya lura da yanayin Aymaan da shigarshi


"Are you ok? Meya samu kayan ka? And your face, ya naga duk bruises?"

Zama Aymaan yayi a opposite dinshi ya harde hannayenshi a qirji
"inajinka" yafada a taqaice

"meya sameka wai Aymaan?"

"idan bakada abin fada zan tafi" inji Aymaan yana eyeing dinshi

"A'a nikau keda abin fada, bari kagani" yafada shima yana zama har wani kyarma yakeyi Wurin zaman


"inada wani mugun surprise for you" yafada yana kallon Aymaan

"uhun?" inji Aymaan yana kallonshi

"bari na faro maka daga farko

Kaga valentine is approaching, kowa yanzu shirye shiryen abubbuwan da zaiyi ya burge masoyiyarshi yake, shine nima nafara tunanin me ya kamata nayi na burge *B-baby* na"


Tunda yafara magana Aymaan ke Binshi da wani matsiyacin kallon haushi

Be lura ba hakan yasashi cigaba da cewa
"saina fara tunanin me ya kamata nayi saina yanke shawarar hada sunana da nata inyi creating video dinsu insamu waqa mai dadi ta soyayya inyi amfani daita..."

"Are you crazy? Wannan ne banzan surprise din daka dameni nazo nagani?" inji Aymaan a fusace

"Kash! Matsalata dakai rashin haquri"

"gudawa ne ni" inji Aymaan a qule


"koma dai Menene kabari nakai aya mana, na yarda idan nakai aya babu abinda yayi making sense aciki kayimin dik abinda kaga dama"


Shiru Aymaan yayi be tanka ba hakan yasa ya cigaba da cewa

"Hakan yasa na yanke shawarar nemo mana waqa mai dadi wanda zata hau da love mood din kuma inason tazamo ta hausa mai ratsa zuciya

Shine na dauki laptop nahau website nafara browsing waqoqin hausa na soyayya masu tashe.


Nasamu guda goma duk na kunnasu nafara sauraronsu daya bayan daya harna saurari duka.

Acikinsu daya tafi kwanta min kuma tahau da abinda nakeson hada mana
Sunanta *kalmar so*


Saboda dadinta na saurareta yafi sau goma, sai daga baya naji inason ganin video din waqar sai nayi downloading din videon.

Bari ka gani" yafada yana sungumo laptop din ya zagayo wajen Aymaan dake kallonshi Tundazu cike da takaici

Jawo wata kujera yayi ya zauna kusada shi ya shiga lalubo waqar cikin sauri

Dan Tsaki Aymaan yaja ya kauda kai yana jin wama yasashi zuwa tun farko gashi yana qara mashi akan abinda yakeji a zuciyarshi

Kida yaji yafara tashi acikin laptop din alamun harya kunna sannan aka fara waqar


_kalmar so tana nufin abinda zuciya tasoo_


_amma anawa 6angaren rai ne da rayuwa_

_so ne lagwan mutane biyu inda shaquwa_

_mai kama dan Adam da aljan da deguwa_

_Domin mu gane so, sai mun qara nutsuwa_

_don dole dole so shike kaimu koguwa_


Juyowa Aymaan yayi ahankali don kallon videon don waqar ta shigeshi shima dukda he's not in the mood, amma waqar ta ta6ashi a zuciya


Wani wawan jada baya yayi da kujerar lokacin dayaci karo da abinda ke kan screen din laptop din

Tashi yayi tsaye yana kallon screen din idanu awaje kamar zasu fado

_so sam beda tausayiii_

_so sam beda tausayii_

_inyai ta6argaza amsar saita bada nayi_

_ba tsoro yake ba shima_

_sannan be gudun husuma_

_zai iya tada yan Adam duk tsaye don yanada girma_

Qara jada baya Aymaan yayi yana kallon fuskar kan screen din

Fuskar da be dade dagani ba yanzu

Fuskar da ya nannausa yan Mintuna dasuka wuce

Mutumin da dazu dazun nan aka 6an6areshi Dakyar daga jikinshi

_mussadiq?_

Girgiza kai yayi

Mussadiq bayajin hausa, ko zo na yankaka da hausa bayaji

_Deen?_

Kanshi ne yayi wani mugun sarawa har Saida yayi saurin dafewa

Kallon smiling face din mutumin dake cikin screen din yayi yana cigaba da waqar guitar a rataye a wuyanshi yana kadawa


Baki na rawa yace
_*"DEEN"*_✍️


alhamdullilah! 💃💃 Anan zan dakatar da Deen mutafi hutun ramadan 💃💃 inda zamu cigaba insha allah bayan sallah idan allah yakai ranmu


Masu Deen! Deen!! To Deen is back!!! Yadawo da wani salo mai ban mammaki, ya dawo muku da bazata kala kala, kudai ku biyoni zuwa bayan sallah muji yadda chakwakiyar zata kaya.

Qaqa qara qaqa! Ga Aymaan ga mussadiq, ga kuma Deen ya fado From nowhere. Yanzu wasan zai fara, ku kasance da Ashaaaaanty dinku Domin jin yadda xa'a qarqare chakwakiyar nan


Allah kabamu ikon yin ibadunmu lafiya, Allah kasadamu da alhairan wannan watan mai albarka (amin summa amin)

Ina mai neman gafarar duk wanda na 6atamawa da sani na ko bada sanina ba, nima na yafewa kowa.


Ma'asallam! Sai mun hadu bayan sallah 😘😘😘


Ummin fasihu 🧚🏻‍♀️🧚🏻‍♀️🧚🏻‍♀️🧚🏻‍♀�
8/2/21, 9:42 PM - Buhainat😝: *🙍🏻‍♂️DEEN🙍🏻‍♂�*


*071*


*THE MUSICIAN🎼*


*barkanmu da dawowa daga hutun azumi, fatan kowa yayi ibadunshi cikin qoshin lafiya, allah yasa dukkanin ibadunmu kar6a66u ne, yakuma maimaita mana🤲🏻*


Qara qurawa gayen kan laptop din idanu Aymaan yayi zuciyarshi na bugu sosai


Tabbas inhar wannan gayen ba mussadiq bane to tabbas DEEN ne


Tashi Ahmad yayi shima ya qaraso inda Aymaan ke tsaye haryanzu kamar statue


"kaima kaga abinda nagani ko?" inji ahmad


sai alokacin aymaan ya iya motsawa ta hanyar juyowa ya kalleshi saidai yakasa cewa komai don yawun bakinshi ma sun kafe gabadaya


dakyar ya kalato wasu bussasun yawu ya hadiye sannan yace
"who is this?"


Dan buda idanu ahmad yayi
"haryanzu tambaya kake?"


girgiza kai aymaan yafara
"karka cemin wannan shine...Deen"


"masu irin wannan fuskar biyu ne duk fadin duniyarnan
Mussadiq da Deen.
kenan wannan is either Mussadiq ko Deen, kuma ni dakai munsan wannan ba mussadiq bane"


"but.. this can't just be, how... I mean yaushe Deen yaxama mawaqi?" inji aymaan confused


"watanni biyar dasuka gabata" Ahmad yabashi amsa


cikin rashin fahimta aymaan yace
"wata biyar? ban ganeba"


Ajiyar zuciya Ahmad ya sauke sannan ya gwadamashi kujera yace
"mufara zama tukun"


Dan jimm aymaan yayi kamar bazai zauna din ba saikuma yaja kujerar ya zauna yana jin yadda zuciyarshi tayimashi jingim


shima Ahmad jan kujera yayi ya maidota kusadashi ya zauna ya dago ya kalli aymaan dake kallonshi shima


"nima nashiga rudani fiyeda yadda kashiga lokacin danayi tozali da wannan fuskar.

abun kamar al'mara, kallo daya nayimashi kwanyata ta burkuce, fuskar Sir Mussadiq sak nake gani a screen din saidai yaren dayake sam ba nashi bane, hakan yasa wani abu ya gifta kwalwata.

domin kore tantama ta sai na jawo laptop din hannu na rawa nashiga searching din sunanshi and this appear..."


sake jawo laptop din Ahmad yayi ya juyota gabanshi yashiga danne2, shidai aymaan kallonshi Kawai yakeyi bece komaiba har yagama ya sake juyomashi laptop din gabanshi


janye idanunshi aymaan yayi daga kanshi yamaida kan laptop din.


kafe sunan dake qasan hoton mai fuskar Mussadiq din yayi nawasu daqiqu sannan ahankali ya bude baki yace" *BALARABE?*"


"yes, balarabe. wannan sunan yasameshi ne a wajen abokanshi da fans dinshi wanda hakan yayi sanaddiyar 6acewar ainahin sunanshi, don dayawa basusan real name dinshi ba, sunfi saninshi da wannan sabon sunan wato *BALARABE*.

Bari kaga full name dinshi..."
yafada yana scrolling laptop din


*KAMALDEEN MUHAMMAD a.k.a BALARABE*


Abinda ya bayyana kenan a screen din


kafe sunan aymaan yayi da idanunshi babu ko kyaftawa


cigaba da scrolling Ahmad yayi yana karanto mashi content din kamar haka


"KAMALDEEN MUHAMMAD,also known as BALARABE shahararren mawaqi ne mai zamani wanda yayi fice a fagen waqoqin nanaye wanda duk suka ta'alaqa ne akan soyayya.


BALARABE yayi fice kuma yayi suna a wannan harkar cikin dan qanqanin lokaci da baigaza wattani biyar ba, abinda ba'a ta6a samu ba a record din wani mawaqi ba.


Abin mammakin bewuce yadda wannan mawaqin yasamu kar6uwa tun awaqarshi tafarko mai taken *KECE* Waqar datayi nasarar bayyanashi ga duniya inda har takaishi ga matsayin dayake ayanzu.


BALARABE yasamu nasarar xama fittace ba iya Arewa ko Nigeria kadai ba hatta wasu qasashen na qetare sunsan da zamanshi


A kuma binciken da akayi BALARABE yana daya daga cikin sannanun Celebrities na Arewa inda yakeda tarin mabiya a shafukanshi na sada zumunta.."


Dan dakatawa Ahmad yayi daga karatun dayakeyi yawaigo yakalli aymaan dake bin karatun shima tundazu.


"Bari kaga nashiga shafinshi na Instagram"


shiga yayi din sannan yaqara karkato da fuskar laptop din gun aymaan wanda haryanzu besake furta komaiba


Gasping Ahmad yayi
"kalla.. over 4million followers! OMG! wlh mutuminnan is famous.. ji pics dinshi... see likes.. kalli millions of comments! cewa akayi idan yayi posting abu koda ordinary picture dinshi ne baya samun likes qasa da million


kalli shows dinshi, duk jiya nayi downloading dinsu..."

Kunna mashi daya daga cikin videos din shows din yayi


Deen ne tsaye cikin wasu tsaddadun fararen qanannun kaya, wuyanshi rataye da guitar yana kadawa ahankali


Abinda zaifi daukar hankalinka a wajen shine tarin mutanen wajen, yadda kasan tururuwa sai ihu suke da whistling yayinda shikuma ke rero waqarshi cikin cool voice dinshi cikeda nutsuwa


kafeshi da idanu Aymaan yayi yana kallon kamillaliyar fuskarnan tashi ma'abociyar fara'a, dakuma yadda dimple dinshi ke lo6awa gwanin sha'awa


waqa yake cikeda qwarewa yayinda sautin waqar ba iya kunne take shiga ba direct cikin zuciya take wucewa tana wanzar da shauqi acikinta.


lumshe idanu Aymaan yayi ahankali yana sauke numfashi ahankali


Ganin hakan yasa Ahmad dannama vidiyon pause ya kalleshi

"ya kagani? Deen is Back!" yafada cikin jindadi


bude idanunshi Aymaan yayi ahankali ya kalleshi

"And what's good about that?" inji Aymaan yana mashi wani kallo


Dan wara idanu Ahmad yayi
"kamar yaya what's good about that? watanni nawa muna nemanshi? yanzu mun sameshi kana fadin haka?"


Maida kanshi aymaan yayi ya jinginar da kujera yasake maida idanu ya lumshe sannan ya bude

"eh, haka nace. what's good about ganinshi? dubi fuskarshi, yayi kama da mai wata damuwa? nace yayi kama da mai wata damuwa!" ya qarashe maganar a fusace


"haba aymaan..."


"yayinda ya jefa wata a tasku, yayi sanaddiyar qauracewar farinciki a rayuwarta, shi yanacan cikin jindadi da walwala yana cin duniyarshi da tsinke! how cruel?" ya katse Ahmad cikin zafin rai


"Aymaan, karka yanke hukunci akan abinda baka.."


"karna yanke hukunci akan abinda ban sani ba? gayamin meye ban sani ba.
akan wannan mutumin rayuwar mutane da dama suka dagule ciki harda tawa!
ya yaudari diyar mutane wanda tasoshi da dukkan zuciyarta ta kuma kafe kai da fata akan sai shi batareda tayi la'akari cewa shi ba kowa bane! taso bijirewa mahaifinta duk don shi! qarshe me yayi? bad'a mata qasa yayi a idanu ya tafi ya barta lokacin datafi buqatarshi

hakan dayayi ya chanza komai a zuciyarta? ya ta6a soyayyar datake mashi? A'a saima qara haukacewa datayi akanshi inda ta dauki dukkan lamuranshi tayi uwa maqar6iya inda kullum da tunanin yadda zata inganta rayuwarshi take kwana take tashi, batada buri sai ganin rayuwarshi ta dawo daidai kamar ta kowa, ta sadaukar da abubbuwa da dama kuma tana kan sadaukarwa duk saboda shi, duk saboda wannan butulun da yanzu nasan ko sunanta baya iya tunawa"
yadda yake maganar Kawai ta isa kagane ranshi a matuqar 6ace yake don har jijiyoyin wuyanshi tashi sukeyi don masifa, he can't believe mutumin dasuke hauka akanshi yana can hankalinshi kwance bayada wata damuwa


"haba Aymaan, meyasa zaka yanke hukunci akan abinda bakada tabbaci akai? dama ana judging book by it's cover ne? don kaga mutum yafito daidai hakan na nufin har cikinshi daidai yake? yayinda wasu murmushi kezama ado agaresu wasu malullu6i ne, mallulu6i na lullu6e ainahin halin dasuke aciki.

Zainab was heartbroken and always in pain, hakan ya hanata murmushi ko dariya ko wasu harkokin na gabanta?

wasu suna fara'a ne domin 6oye ainahin halin dasuke aciki, wasu suna murmushi ne don sunga kowa nayi bawai don hakan na zuwa daga can qasan zuciya ba.

yadda zee ke kwana tana tashi dashi arai shima hakan take a wajenshi

Zainab na maqale a zuciyar Deen kuma zan gwadamaka hujja"


Yana kaiwa nan yasake jawo laptop din yayi yan danne2nshi sannan ya juyoma Aymaan yana cewa
"wannan wata firace da akayi dashi a gidan wani television ko wata daya ba'ayi ba"


danna play botton yayi wanda hakan yaba vidiyon damar farawa


Deen ne zaune kan kujera yana facing presenter din gidan t.v din

sanye yake cikin wata dakkakiyar sky blue shadda wacce tayi mugun hawanshi takuma qara fiddo mashi qwarjininshi da haiba

kanshi babu hula sai lallausan gashinshi dayayi trimming dake kwance luff luff gwanin sha'awa

yaqara haske da kyau ga cute lips dinshi dasukaqara yin pink fiyeda da


kallon presenter din yakeyi dake yimashi tambaya fuskarshi asake

"Mallam balarabe zaka iya gabatar ma masu saurare kanka?"


murmushi Deen yadanyi sannan yace
"insha allah, sunana KAMALDEEN MUHAMMAD amma anfi sanina da BALARABE yayinda wasu kuma ke kirana Deen"


"masha allah, Mallam balarabe zamuso sanin yadda akayi kasamu wannan sunan na BALARABE, koko dama kai balaraben ne Don ana yada jita jitan qila ka hada jini da larabawa duba da yadda kayo ruwansu"


murmushi Deen yayi
"ban hada komai da larabawa ba kamar yadda ake hassashe, ni cikkaken bahaushe ne, sunan BALARABE kuma na sameshi ne awajen abokai na, nickname ne Kuma sai yabini" yafada cikin cool voice dinshi


"masha allah, to Mallam balarabe meye yaja ra'ayinka har kafara wannan harka ta waqa?" inji presenter din


"eh to, dafarko nafara waqa ne ba don nasan inada talent din ba, Kawai ina yine don yaxama Abin debemin kewa duk lokacin da nakejina so boring, sai daga baya aka fahimtar dani talent dina akan waqa sannan aka kwadaitamin bayyana wannan talent din nawa ta hanyar shiga harkar waqar"

"masha allah, yanzu tun lokacin daka fara waqa zuwa yanzu aqalla kayi guda nawa? kana iya qayyadesu"

dan murmushi deen yayi
"waqoqin danayi kuma suka fito adadinsu 27 yayinda akwai wadanda nake aiki akai kuma suna gab da fitowa suma insha allah"


"to masha allah, mallam balarabe zaka iya fadamana nasarorin daka samu sanaddiyar waqa?"


"Alhamdullilah, babu abinda zance a wannan ga6ar sai godiya ga Allah (s.w.t) don nasarori kam na samesu sosai a wannan harkar ta waqa, ciki harda famousity, a sanaddiyar waqa sunana ya zaga wuraren da qila har inmutu bazanje wajen ba, takuma sa ansan dani Kuma nima nasan mutanen da ban ta6a mafarkin zan sansu su sanni ba
bayan hakan kuma tazama garkuwa gareni inda take a.matsayin sana'a agareni wanda nake samun rufin asiri sosai acikinta, Alhamdullilah"


"to Mallam balarabe qalubale fa? kasan duk nasara tana tareda qalubale, wadanne irin qalubale ka fuskanta a wannan harkar ta waqa?"


kada kai Deen yayi
"gaskiya ne, kowanne nasara yana tattare da qalubale.
gaskiya qalubalen dana fuskanta bawata mai yawa bace, a lokacin da nayanke shawarar fara waqa nakuma tuntu6i kakata akan hakan taso hanani don a ganinta babu Abinda yake cikin harkar sai tarin shiririta da shirme amma da taimakon uban gidana muka samu muka shawo kanta har ta amince takuma sanyamana albarka akai wanda inada tabbaci albarkar ke bibbiyarmu haryanzu" ya qarashe murmushi a fuskarshi


shima presenter din murmushi yayi
"ka ambaci ubangida, zaka iya fadamana waye ubangidanka ko jagoranka wato role model dinka a wannan harkar?"


jimm Deen yadanyi saikuma yadanyi slight murmushi

"eh... inada role models biyu... da wanda da taimakonshi nashiga wannan harkar sai wadda tasani nayi realising talent dina.."

saikuma yayi shiru staring in space


Ganin hakan yasa presenter dan muskutawa sannan yace
"wacce tasaka realizing talent dinka? wacece?"


nanma shiru yadanyi still staring blankly at space saikuma yayi wani guntun murmushi yana sauke idanunshi qasa

Ahankali yaqara dagowa ya kalli presenter din still murmushin bebar fuskarshi ba

"wata ce... wata" yafada ahankali yana kallon fuskar presenter din saidai a zahiri ba fuskarshi yake gani ba,.wata fuskar yake gani daban


"Idan aka ambaci kalmar *waqa*.. ita ke fara zuwa raina. Idan nashiga studio da niyyar yin waqa inajin presence dinta ajikina, dana lumshe idanu na don nafara ita nake gani tana min rad'ar waqar daxanyi nikuma nashiga binta ahankali.

itace dalilin komai na career dina, itace dalilin nasarata a duniya, itace dalilin zuwana matsayin danake aciki yanzu, itace nasarata.


*waqa tana zuwa ne daga zuciya, duk waqar datazo directly daga zuciya zakaga tafi wadda za'a zauna a tsara*
wannan kallaman nata sune sukeyin guiding dina a kodayaushe"

"dafarko na dauki hakan kamar abu marar yiwuwa yayinda nasha qoqarin qirqirarta da abinda yake a zuciyata amma daga baya sai nayi realizing gaskiyar maganarta lokacin da nake rero abinda ke zuciyata batareda sanina ba.


Duk waqar dazanyi tana zuwa ne daga can qasan zuciyata kuma kowacce is reffering to her..."

dan murmushi yasake yi absentmindedly sannan in a whisper yace
"my role model"


shiru ya ratsa wajen na wasu daqiqu, can presenter din yace
"to Mallam balarabe, zaka iya fadamana ko wacece wannan role model din taka? dakuma matsayinta a wajen ka"


Nan ma saida yadanyi shiru sannan yadanyi guntun murmushi

"she's an angel, angel of light and beauty, duk inda ta gifta tana barin walwalin haskenta awajen, hasken daxai cigaba da haskaka wadanda tabari awajen.

she's innocent, straightforward, mean, honest, stylish and fun to be with.

tanada baiwar da duk inda taje komin qanqantar zamanta awajen sai tabar memories, sweet brainsticking memories"

presenter din dake enjoying moment din cikin doqi yace
"wacece agareka? girlfriend?"


dagowa Deen yayi yakalleshi na wani lokaci wanda expression din fuskarshi yasa murnar presenter din fara komawa ciki

sauke idanunshi yayi a qasa sannan ya girgiza kai

"A'a..." sai kuma yayi shiru

can kuma ya dago yaqara kallon presenter din
"Actually.. a halin yanzu kowanne na rayuwa ne a wata duniyar tashi daban... and... mun haramta ga juna.. ta haramta gareni"
sauke kanshi yaqara yi qasa yana lumshe oily eyes dinshi

shiru wajen ya dauka, shi kanshi presenter din jikinshi yayi sanyi

be daddara ba yasake cewa
"ta haramta agareka kamar yaya?"


Ajiyar zuciya Deen ya sauke sannan ya dago yakalli presenter din yana murmushin qarfin hali

"I'll be glad Idan mukayi dropping wannan topic din, it's something personal, I dont want to discuss it" yafada politely


jin hakan yasa shima,presenter din dropping topic,din ya cigaba da yimashi wasu tambayoyin daban.


Ajiyar zuciya Aymaan ya sauke ya maida kanshi ya jinginar da kujera tareda lumshe Hazel eyes dinshi


jiyake kamar kanshi zai rabe gida biyu ga wani abu dake tasomashi a qasan zuciya mai dacin gaske


shima Ahmad bece komaiba sai kallonshi dayake yana jiran jin me zaice kuma


Jan kujerar dayake akai Aymaan yayi baya sannan ya miqe tsaye

binshi dakallo Ahmad yayi ga mammakinshi sai gani yayi ya juya ya nufi kofa


sakin baki Ahmad yayi yana kallonshi har yakai bakin kofa sannan cikin qarfin hali ya kira sunanshi

dakatawa Aymaan yayi daidai lokacin daya kai hannu kan handle batareda ya juyoba


tashi tsaye Ahmad yayi
"ya zaka tafi just like that?"


batareda ya juyo ba yace
"what again? akwai wani abu bayan wannan ne?"


qara wara idanu ahmad yayi cikin mammaki
"bangane ba, aren't we suppose to discuss about this?"


sai a sannan Aymaan yajuyo

"discuss about what? there is nothing to discuss about"

"amma..."


"baka jishi ba? he said sun haramta da juna, ni wanene dazan halarta haram?" Aymaan ya katseshi da hakan


kasa cewa komai Ahmad yayi sai bin Aymaan dayake da kallo baki sake


juyawa Aymaan yayi ya murda kofar ya bude yafita tareda maidota da qarfi leaving Aymaan still standing mouth agape


Besan yadda ya fito a daga company din ba saidai.Kawai yaganshi a jikin motarshi yana kiciniyar budeta


ya dade yana kiciniyar budeta kafin ya gane ashe ba makullin motar bane yake amfani dashi


lalubo makullin motar yayi sannan ya bude ya shiga yarufo murfin

kai key din yayi jikin motar yana son kunnata saidai yakasa daidaita key din da inda ake zurashi saboda rawar da hannunshi yake


ganin hakan yasashi sakin key din kawai ya hada kanshi da sterring yana sauke numfashi ahankali


kanshi sarawa yake, mugun sara, jiyake kamar ya cireshi ya jefar ko zai huta


why?

meyasa abbubuwa suka taru suka cakudemashi yau?

meyasa abubbuwan dayake kasa jura ke faruwa dashi yau

first is Mussadiq, yanzu kuma Deen?


meyasa sai yanzu Deen zai bayyana? meyasa ya bayyana tun yanzu?

bude rinnanun idanunshi yayi ahankali

kenan dama duk wannan abin da ake bayaso Deen ya bayyana?

yayi tunanin zaifi kowa farinciki Idan Deen ya bayyana tunda hakan na nufin farincikin zee itama

amma sai yaga sa6anin haka, Abinda yakeji kwata2.beyi kama da farinciki ba, mutumin da suka dade suna nema ya bayyana amma baya murna.

so strange!


ya dade cikin motar ahakan kafin yasamu yadan dawo normal, atleast yasan zai iya lalla6awa yakai kanshi gida


wayarshi dake gaban motar ya dauka ya Kunna


missed calls yagani rututu, daga ummy, abbu, batool da...


qurawa sunanta dake rubuce a screen din wayar idanu yayi


itace tafi qarancin kira acikinsu amma itace kiranta yafi tasiri agareshi


Ajiyar zuciya ya sauke sannan ya ajiye wayar batareda ya.maida kowa cikinsu kira ba, ya duqa ya dauki key din daya saki daxu ya zura a keypoint din ya tada motar ya jata ahankali yabar company din.....✍�


*manage please, nima managing nayi nayimuku post din, keep praying for me, heart you all💗*


Ummin fasihu🧚🏻‍♀�
8/2/21, 9:42 PM - Buhainat😝: *🙍🏻‍♂️DEEN🙍🏻‍♂�*


*072*


*THE MUSICIAN 2*


Qarar bude kofa taji amma hakan besata dagowa ba ko janye ido daga inda ta kafe da kallo ba


ahankali batool ta qaraso wajenta ta zauna gefenta tana kallonta


shiru yadan ratsa dakin kafin batool ta sauke Ajiyar zuciya

"zee.."


bata motsa ba kuma bata juyo ta kalleta ba


"zee ya kamata kisaki ranki hakanan, all is well insha allah" tafada cikin son kwantar mata da hankali


shiru dakin yasake dauka kamar baxata ce komai ba can kuma tace
"meyasa?... meyasa wadannan abubbuwan ke faruwa dani?"


kasa amsawa batool tayi sai kallonta datake emotionally

"daga wannan sai wannan? when will I have peace of mind?" tafada wasu hawayen na kawo mata


jawota batool tayi ta rungumeta ta gefe tana dan jijjiga kafadarta alamun rarrashi

"Zainab, all will be well insha allah"


"when? yaushe komai din zai daidaita? am fed up, nagaji" tafada hawaye na gangaromata a kumatu


"yanzu ina Aymaan, ni dake munsan yanayin daya bar school daxu kuma gashi haryanzu be dawo gida ba and baya picking calls, allah kadai yasan halin dayake ciki kuma kowanne hali yake ciki nice sila"


"shhhh... kibar fadin haka, insha allah yana nan lfy lau kuma zai dawo, kibar dorama kanki laifi da damuwa"


shiru zee tayi tana sauraronta, wani iri take ji a zuciyarta, komai baya mata dadi.

tunda take da Aymaan bata ta6a ganinshi a irin yanayin data ganshi yau ba

gabadaya ya burkuce kamar ba gentle Aymaan data sani ba, ya burkuce ya koma wani daban kuma duk itace sila

and she don't blame him, dole ya fusata a yanayin daya gansu


ganinsu fa yayi yana bata ruwa a baki, mutumin da yasha attempting marinta yana tare mata har takai da an tsareshi na wani lokaci wanda hakan ba qaramin cin fuska bane agareshi duba da matsayinshi da reputation dinshi amma shi zai gani yana bata ruwa abaki


dole koma waye hakan yafaru dashi yaji zafin abun

da farko ya ganta a motarshi yanzu kuma yaganta taredashi yana bata ruwa looking more like lovers, Idan ya yarda wancan karon bada son ranta tashiga motarshi ba yanzu fa? ai ba dura ya iske yana mata ba.


wani irin haushin Mussadiq taji tana ji, bata ida tabbatar da Mussadiq is soo annoying ba sai yau, tarasa dalilin dayasa tun farkon haduwarsu dashi suke samun matsala dashi, kwata2 rayuwar dasukayi da Deen beyi kama data Mussadiq ba ko kadan, rayuwar dasukayi da Deen is opposite data Mussadiq don duk lokacin dasuka hadu basa rabuwa ta dadi kuma tarasa dalili


Jin tsayuwar motar awaje yasata dan qame jikinta waje daya kamar yadda batool itama tayi

kallon juna sukayi sannan suka tashi atare suka nufi window inda suke iya hangen harabar gidan tanan


ganin motar Aymaan na parking yasa suka wara idanu suka kalli juna cikin murna


"he's back!"


tare suka nufi kofa da sauri har suna rige2


fitowa sukayi suka fara saukowa saman stairs din cikin sauri


cak zee ta tsaya tsakiyar benen takasa qarasa sauka saboda tozalin datayi dashi


tsayawa tayi tana kallonshi kamar yau tafara ganinshi

ya koma kamar bashi ba, Aymaan data sani tsaftsaf always looking neat and tidy shine tsaye agabanta cikin squeezed and dirty shirt harda yaga awasu wuraren ga fuskarshi duk bruises daya samu wajen fadan dasukayi dazu, he looked more like a thug

ganinshi a wannan yanayin yasata kasa qarasawa sai tsayawa datayi tana kallonshi


"Akhie!" inji batool tana fadawa jikinshi


hannu yasa ya taro bayanta batareda ya janye idanunshi akan zee daya fara kallo tun shigowarshi


*she's an angel, angel of light and beauty*
tunawa yayi da kalaman Deen


*duk inda ta gifta tana barin walwalin haskenta awajen,hasken dazai cigaba da haskaka wadanda tabari awajen*


How true his words are


"Aymaan..."
muryar ummy ta katseshi


janye idanunshi yayi daga kan zee ya maida kan ummy data qaraso itama gabanshi

Dan murmushi yasakarmata yana kallon worried face dinta

"Aymaan ina kashiga? anata kiran wayarka baka picking shima Ahmad ba'a samunshi, yanzu haka Abbu yafita nemanka" tafada tana kallonshi


dry murmushi yasake qirqira yana sakin batool sannan yamatso gaban ummy yariqo hannunta

"kuyi hqr, ina tareda Ahmad ne kuma nabar wayata a mota"


ganin ummy na bin jikinshi da kallo yasa shima kallon jikinshi

ganin abinda ummy ke kallo yasashi dan murmushi yace
"ummy Bari nashiga nadan watsa"

kada mashi kai ummy Kawai tayi tana kallonshi

juyawa yayi ya nufo stairs din su ummy na binshi da kallo


tunda yataho bugun zuciyarta ya qara gudu, cigaba da kallonshi tayi zuciyarta na cigaba da bugawa tana kallon yadda yake qara kusantota

sotake ta bar wajen amma takasa ko motsawa kamar yadda takasa janye idanunta akanshi

shikuma a nashi bangaren ba ita yake kallo ba, idanunshi na qasa harya fara taka stairs din

ahankali yake taka stairs din harya qaraso inda take tsaye

ahankali ya dago hazel idanunshi ya kalleta

hada idanu sukayi wanda hakan yasa Zainab saurin janye nata idanun ta saukesu qasa zuciyarta na cigaba da bugawa

ahankali taji wucewarshi ta gefenta ya cigaba da haura stairs


hawaye ne suka taru a idanunta dake kallon qasa tana jin wani sense of guilt a qasan zuciyarta

saida taji qarar rufewar kofar dakinshi sannan itama tajuya tayi saman da sauri ta bude kofarsu tashige


Ajiyar zuciya ummy da batool dake kallonsu tundazu sukayi, ummy tajuya tana lalubo number abbu don sanardashi dawowar Aymaan itakuma batool tabi zee sama.


💖💖💖💖💖💖💖💖💖


*ABUJA, NIGERIA🇳🇬*


Tafiya take tana dan bin harabar wajen da kallo.

mutanen dake harabar wajen basuda yawa, don yan tsirarun mutane ne jifa jifa awajen

cigaba tayi da tafiyarta tana scanning wajen kamar mai neman wani


"ranki shi dade!"
taji wata familiar murya namata magana a bayanta


tsayawa tayi daga tafiyar datake sannan ta juyo ahankali

qarasowa saurayin yayi wajenta yana washe baki ganin hakan yasata itama murmusawa


"ranki ya dade, kune yau a ma'aikatar mu?" inji saurayin bayan ya qaraso

"aikaudai Mallam Habeeb, ya aiki?" tafada tana gyara zaman sidebag dinta

"Alhamdullilah, gashinan munata fama, ya zafi2 ya school?"

"Alhamdullilah, daga can ma nake nayi tunanin dropping nan nayi checking abokinka, meya samu wayarshi?"

"bata shiga?"


"baya dagawa dai"


"ayyah, yana cikin studio ne, nasan yanzu haka silent take"

kada kai tayi tana dan ta6e baki
"nima nayi tunanin hakan"


"muje, nasan yanzu ma yakusan gamawa" inji saurayin

"ok, muje"


tare suka jero suna tafe suna dan labari jifa jifa har suka shige wani building


wani passage suka bi suna cigaba da firarsu Idan suka hadu da wasu a hanya su gaisa har suka qaraso inda zasu

tun kafin su shiga tafara jin cool voice dinshi na tashi in a cool rymth


lumshe idanunta tayi ta bude ahankali sannan tashiga ta kofar da Habeeb ya budemata


akwai mutane a studio din as usual amma basuda yawa, kowa hankalinshi da imaninshi ya tattara ya koma akanshi don dayawa basusan da shigowarsu Habeeb ba


daga idanu tayi ta kalleshi tacikin glass din dayake ciki

kanshi sanye da headphones sai mic dake girke a gabanshi mai dauke da abin tace murya


jitayi zuciyarta na melting lokacin data sauke idanunta akan fuskarshi, fuskar da duk duniya bataga mai kyawunta ba, fuskar da ke narkar da zuciyarta daga kallo daya


_Duba kigaa yadda sonki yayi dani.. dukda nasan kina sane_


_ki kalli cikin idanuwanaaa.. nasan xasu zayyane_


_wannan al'ajab na sone da qauna.. baki na kiranki neee_


_dana fada kiji_


_kibani agaji_

_indaina rangaji_

_kidanyi tsokaci_

_kibani ma'aji_

_ba zancen na gaji_

_ki kauda fuu da ji_

_a so baya ji_

_labarin zuciya_


_ni zaki tambaya_


_Abinda nakaji_

_ya zarce duniyaa_


_Idan na waiwaya_


_koko na sunkuya_

_amsar guda nakeji.._

_kinzaman habibiya_...


Kafe pink moving lips dinshi tayi da idanunta tana jin yadda sautin muryar tashi ke sinking har qasan zuciyarta


ahankali ta janye idanunta daga kan bakinshi tafara yawo dasu a fuskarshi


idanunshi a lumshe suke wanda hakan yaba zarazaran lashes dinshi damar hadewa, tarasa yaushe yafi kyau, Idan idanunshi na a lumshe ko Idan suna a bude.


kallon cikkakun girarenshi tayi ganin yadda suke motsawa ahankali, gangaro da idanun nata tayi kan pointed nose dinshi daya dace da fuskarshi, ahankali tasake maida idanun kan bakinshi dake motsawa haryanzu.


lumshe idanu tasakeyi ta bude tanajin wani abu na tasowa daga qasan zuciyarta


anya a duniya akwai wanda zai so gayen nan kamar yadda take sonshi? she doubt it, ajikinta tana jin duk wani mai son Deen to saidai yabi bayanta don soyayyar datake mashi batada iyaka


Deen on the other hand besan tana yi ba, yayi nisa, nisa daga wannan duniyar tamu, yana wata.duniyar daban, wanda yasaba shiga duk lokacin dayake waqa

idanunshi na alumshe amma yana gani clearly saidai ba abinda wadanda kecikin studio din ke gani yake gani ba

he has wander into his dreamland kamar yadda yasaba

acikin lumssasun idanunshi wani beautiful scene yake gani

fuskar da kullum ke zuwa mashi tana mashi gizo dare da rana, fuskar da sai idan yana ganinta yake iya rairo abinda ke zuciyarshi, fuskar da tazame mashi kamar abincin dayake ci ko iskar dayake shaqa


_ya za'ai na burge wacce nakeso da qauna? ya za'ai?_


_kalamaina sun kadan ta fahimceni sannan... ba hanya_


_kalamaina sun kadan ta fahimceni sannan ba hanya!!_


_inaso tasoni ne ba guruu babu laya_

_babu dad'i babu qarya.. ni banison riya_

_badon kwalliyaba kuma badon dukiya ba_


_badon zantuka ba kullum taimun maraba_


_ina sonki.. ina sonki.. inaa sonki_


_ina sonki so na gaskiya ba yaudara ba_


_ina sonki.. ina sonki.. ina sonki ni.._


_ina sonki so na gaskiya ba yaudara ba_

_ina sonki so na gaskiya ba yaudara baaaaa_


ihu studio din ya dauka da tafi wasu harda fito.

sosai mutanen cikin studio din ke nuna jindadinsu afili sai kirari suke mashi


bude lumsassun idanunshi yayi ahankali yana bin mutanen cikin studio din da kallo murmushi a fuskarshi


ahaka oily idanunshi suka sauka a kanta inda take tsaye tayi crossing hannayenta a qirji itama tana kallonshi


kafe juna da kallo sukayi na wani lokaci sannan ahankali deen ya sakarmata kyakyawan murmushinshi

jitayi wani farinciki ya mamaye zuciyarta nan take, ahankali itama ta sakarmashi nata murmushin mai kyau.


***


"ya school?" yafada cikin cool voice dinshi


"Alhamdullilah, ya naka aikin?" ta tambaya itama suna cigaba da tafiya side by side


"Alhamdullilah also, yasu mamy?"

"su mamy na nan lfy lau, tace ka kyauta daka maidasu gefe guda"

Dan murmushi yayi yana cusa yatsunshi cikin saisayayen sumarshi wadda bata kai ta da cika ba

"hmmm ba haka bane" yafada cikin murmushi

"to yane? kwata2 ka daina zuwa, ganinka yanzu sai an cika form, aita kiran wayarka ma ba'a samu" she complained

"am sorry, I've been busy ne a kwanakinnan amma zanzo, kiba mamy hqr"


Dan wara idanu tayi tace
"A'a, kabari duk ranar dakaje kabata, ni babu ruwana"

murmushi kawai yayi bece komai ba

ganin hakan yasa itama bata qara cewa komai ba suka cigaba da tafiya silently, tafiya gefe da gefe taredashi ba qaramin dadi yake mata ba musanmman Idan ta lura da yadda ake binsu da kallo inda mostly mata ne ke kallon nasu kowanne fuska dauke da kishi don sun lura Deen baya kula kowacce mace sai ita hakan yasa basasonta ko kadan.


parking space suka isa Deen yashiga waige2


"ina motarki?"


Dan daga kafadu tayi
"tadan samu matsala tana wajen mechanic"

"to da me kikazo?"


"adaidaita, yanzu ma dashi zan koma"


"amma kinsan adaidaita na wuya a arear nan ko?"

Dan 6ata fuska tayi
"I'll wait, no p"


Ajiyar zuciya ya sauke
"ina zuwa"

yana fadin hakan ya juya


Dan murmushi tayi

seems tarkonta ya danu, dama da gangan tasa drivernta dropping dinta tace yatafi kawai


ko minti biyu ba'ayi ba wata blue din mota ta qaraso wajenta ta tsaya


Deen ke ciki

"get in, let me drop you" yafada bayan ya sauke glasses din qasa


Dan sunkuyowa tayi tana kallonshi
"aren't you busy? kabarshi kawai xan samu adaidaita"


bece komai ba sai matsowa dayayi ya bude mata kofar

Ajiyar zuciya ta sauke sannan ta ida bude murfin tashiga ta maido ta rufe


tada motar yayi sannan yajata suka fita daga wajen.


Tafiya suke babu mai cewa komai acikinsu sai qira'ar Qur'an dake tashi cikin motar


Deen hankalinshi na kan titi yana driving at normal speed while itakuma tana lafe a kujerar mai zaman banza tana shaqar qamshinshi daya hadu da sanyin a.c din motar yabada wani sanyayar yanayi.


Babu jimawa suka isa kofar gidansu, batasan sun iso ba saida taji tsayuwar motar, sai.taga sunyi saurin zuwa, bata gaji da shaqar qamshinshi ba


"here we are" inji Deen


tashi tayi zaune sosai

"Bazaka shiga ba?"


Dan wara oily eyes dinshi yayi
"zan dai shigo soon insha allah"


"hmm to saina gayamata" tafada tana qoqarin fita

"me zaki gayamata?" yafada yana kallonta

"kazo amma you choose to turn around and go back"

"bazaki fadamata nazo ba" yafada fuskarshi da slight murmushi

"saina fada" tafada tana ida fita


"I dare you" yafada daringly fuskarshi da slight murmushi

kada kai tayi tana kwafa
"zaka gani kau" tafada tana rufo mashi kofar motar


dagama juna hannu sukayi sannan tajuya tanufi tangamemen gate din gidansu shikuma yaja motarshi yaqara gaba.


*10:15pm*


"Shikenan Kaka, allah yakaimu goben lfy" yafada ahankali


murmushi Kaka tayi ta shafa mashi kai
"Amin kyakyawana, yanzu kaje ka kwanta dare yayi nima barci nakeji"


"to Kaka, saida safe"


"Allah ya tashemu lfy, karka manta kayi alwalla kuma kayi addu'a"


kada kai yayi cikin murmushi sannan ya tashi ya kashemata fitilun dakin yabarmata na bedlamp kadai sannan yayimata sallama yafita.


ahankali yake takawa kasancewar dare yayi hakan yasa anajin faint sautin takunshi, ahaka harya isa dakinshi.


dakin is so big and neat, yasha kayan furnitures na zamani ga haske takoina.


direct gefen makeken gadonshi that is neatly spread ya nufa yafara rage kayan jikinshi

jefa wadanda yacire yayi a wani dogon bin inda dama yake saka kayanshi masu datti kafin laundrier yazo ya dauke washegari


toilet yashige don freshen up.


ya dade sosai a toilet din sannan yafito daure da towel a kugu sai wani a hannunshi yana tsane jikinshi


chanzawa yayi cikin kayan barci farare sannan ya shinfida sallaya ya gabatar da shafa'i da witr sannan ya rufe da addu'o'i


nade sallayar yayi ya maida ma'ajinta sannan ya miqe tsaye.


maimakon ya nufi gadonshi ya kwanta saiya nufi wani side din na daki


ahankali ya bude wata qofa wanda ta sadashi da balcony din gidan


stepping yayi cikin balcony din yana kallon waje yana feeling yadda iskan daren ke kadawa


koina yayi shiru sai kukan tsintsaye da zaka dinga jiyowa daga nesa dana qanannun qwari


garin yayi duhu sai hasken wata dake haskawa faintly

ahankali ya zura hannayenshi cikin aljihunnan wandonshi yana bin wurin da kallo


yaushe zaibar jinshi so empty?

yaushe wawakeken gurbin dake zuciyarshi zai cike?

yaushe duhu zai yaye?


yaushe haske zai qara ziyartar rayuwarshi?

yaushe farinciki zai sake ziyartar rayuwarshi?

yaushe?


ahankali ya daga kanshi ya kalli sama yana hango wata daya fara disashewa alamun soyake shima yashige cikin gajimare

bin yan mitsi mitsin taurarin dake saman yayi da kallo trying to count them amma sunyi yawa daya fara saiya 6ata a lissafin.

haqura yayi ya sauke idanunshi qasa yana qara observing din garin

hasken watan dake dan haska garin sai qara disashewa yake hakan yasa garin ke qara duhu, duhun da ga wasu na dan qanqanin lokaci ne don da gari ya waye zasuga haske, amma agareshi ba haka abin yake ba, koda gari ya waye wa kowa baxai waye mashi ba

ya dade cikin duhu kuma besan iya lokacin daxai sake dauka acikinshi ba.


maybe forever


maybe not...✍�


Ummin fasihu🧚🏻‍♀�*🙍🏻‍♂️DEEN🙍🏻‍♂�*


*072*


*THE MUSICIAN 2*


Qarar bude kofa taji amma hakan besata dagowa ba ko janye ido daga inda ta kafe da kallo ba


ahankali batool ta qaraso wajenta ta zauna gefenta tana kallonta


shiru yadan ratsa dakin kafin batool ta sauke Ajiyar zuciya

"zee.."


bata motsa ba kuma bata juyo ta kalleta ba


"zee ya kamata kisaki ranki hakanan, all is well insha allah" tafada cikin son kwantar mata da hankali


shiru dakin yasake dauka kamar baxata ce komai ba can kuma tace
"meyasa?... meyasa wadannan abubbuwan ke faruwa dani?"


kasa amsawa batool tayi sai kallonta datake emotionally

"daga wannan sai wannan? when will I have peace of mind?" tafada wasu hawayen na kawo mata


jawota batool tayi ta rungumeta ta gefe tana dan jijjiga kafadarta alamun rarrashi

"Zainab, all will be well insha allah"


"when? yaushe komai din zai daidaita? am fed up, nagaji" tafada hawaye na gangaromata a kumatu


"yanzu ina Aymaan, ni dake munsan yanayin daya bar school daxu kuma gashi haryanzu be dawo gida ba and baya picking calls, allah kadai yasan halin dayake ciki kuma kowanne hali yake ciki nice sila"


"shhhh... kibar fadin haka, insha allah yana nan lfy lau kuma zai dawo, kibar dorama kanki laifi da damuwa"


shiru zee tayi tana sauraronta, wani iri take ji a zuciyarta, komai baya mata dadi.

tunda take da Aymaan bata ta6a ganinshi a irin yanayin data ganshi yau ba

gabadaya ya burkuce kamar ba gentle Aymaan data sani ba, ya burkuce ya koma wani daban kuma duk itace sila

and she don't blame him, dole ya fusata a yanayin daya gansu


ganinsu fa yayi yana bata ruwa a baki, mutumin da yasha attempting marinta yana tare mata har takai da an tsareshi na wani lokaci wanda hakan ba qaramin cin fuska bane agareshi duba da matsayinshi da reputation dinshi amma shi zai gani yana bata ruwa abaki


dole koma waye hakan yafaru dashi yaji zafin abun

da farko ya ganta a motarshi yanzu kuma yaganta taredashi yana bata ruwa looking more like lovers, Idan ya yarda wancan karon bada son ranta tashiga motarshi ba yanzu fa? ai ba dura ya iske yana mata ba.


wani irin haushin Mussadiq taji tana ji, bata ida tabbatar da Mussadiq is soo annoying ba sai yau, tarasa dalilin dayasa tun farkon haduwarsu dashi suke samun matsala dashi, kwata2 rayuwar dasukayi da Deen beyi kama data Mussadiq ba ko kadan, rayuwar dasukayi da Deen is opposite data Mussadiq don duk lokacin dasuka hadu basa rabuwa ta dadi kuma tarasa dalili


Jin tsayuwar motar awaje yasata dan qame jikinta waje daya kamar yadda batool itama tayi

kallon juna sukayi sannan suka tashi atare suka nufi window inda suke iya hangen harabar gidan tanan


ganin motar Aymaan na parking yasa suka wara idanu suka kalli juna cikin murna


"he's back!"


tare suka nufi kofa da sauri har suna rige2


fitowa sukayi suka fara saukowa saman stairs din cikin sauri


cak zee ta tsaya tsakiyar benen takasa qarasa sauka saboda tozalin datayi dashi


tsayawa tayi tana kallonshi kamar yau tafara ganinshi

ya koma kamar bashi ba, Aymaan data sani tsaftsaf always looking neat and tidy shine tsaye agabanta cikin squeezed and dirty shirt harda yaga awasu wuraren ga fuskarshi duk bruises daya samu wajen fadan dasukayi dazu, he looked more like a thug

ganinshi a wannan yanayin yasata kasa qarasawa sai tsayawa datayi tana kallonshi


"Akhie!" inji batool tana fadawa jikinshi


hannu yasa ya taro bayanta batareda ya janye idanunshi akan zee daya fara kallo tun shigowarshi


*she's an angel, angel of light and beauty*
tunawa yayi da kalaman Deen


*duk inda ta gifta tana barin walwalin haskenta awajen,hasken dazai cigaba da haskaka wadanda tabari awajen*


How true his words are


"Aymaan..."
muryar ummy ta katseshi


janye idanunshi yayi daga kan zee ya maida kan ummy data qaraso itama gabanshi

Dan murmushi yasakarmata yana kallon worried face dinta

"Aymaan ina kashiga? anata kiran wayarka baka picking shima Ahmad ba'a samunshi, yanzu haka Abbu yafita nemanka" tafada tana kallonshi


dry murmushi yasake qirqira yana sakin batool sannan yamatso gaban ummy yariqo hannunta

"kuyi hqr, ina tareda Ahmad ne kuma nabar wayata a mota"


ganin ummy na bin jikinshi da kallo yasa shima kallon jikinshi

ganin abinda ummy ke kallo yasashi dan murmushi yace
"ummy Bari nashiga nadan watsa"

kada mashi kai ummy Kawai tayi tana kallonshi

juyawa yayi ya nufo stairs din su ummy na binshi da kallo


tunda yataho bugun zuciyarta ya qara gudu, cigaba da kallonshi tayi zuciyarta na cigaba da bugawa tana kallon yadda yake qara kusantota

sotake ta bar wajen amma takasa ko motsawa kamar yadda takasa janye idanunta akanshi

shikuma a nashi bangaren ba ita yake kallo ba, idanunshi na qasa harya fara taka stairs din

ahankali yake taka stairs din harya qaraso inda take tsaye

ahankali ya dago hazel idanunshi ya kalleta

hada idanu sukayi wanda hakan yasa Zainab saurin janye nata idanun ta saukesu qasa zuciyarta na cigaba da bugawa

ahankali taji wucewarshi ta gefenta ya cigaba da haura stairs


hawaye ne suka taru a idanunta dake kallon qasa tana jin wani sense of guilt a qasan zuciyarta

saida taji qarar rufewar kofar dakinshi sannan itama tajuya tayi saman da sauri ta bude kofarsu tashige


Ajiyar zuciya ummy da batool dake kallonsu tundazu sukayi, ummy tajuya tana lalubo number abbu don sanardashi dawowar Aymaan itakuma batool tabi zee sama.


💖💖💖💖💖💖💖💖💖


*ABUJA, NIGERIA🇳🇬*


Tafiya take tana dan bin harabar wajen da kallo.

mutanen dake harabar wajen basuda yawa, don yan tsirarun mutane ne jifa jifa awajen

cigaba tayi da tafiyarta tana scanning wajen kamar mai neman wani


"ranki shi dade!"
taji wata familiar murya namata magana a bayanta


tsayawa tayi daga tafiyar datake sannan ta juyo ahankali

qarasowa saurayin yayi wajenta yana washe baki ganin hakan yasata itama murmusawa


"ranki ya dade, kune yau a ma'aikatar mu?" inji saurayin bayan ya qaraso

"aikaudai Mallam Habeeb, ya aiki?" tafada tana gyara zaman sidebag dinta

"Alhamdullilah, gashinan munata fama, ya zafi2 ya school?"

"Alhamdullilah, daga can ma nake nayi tunanin dropping nan nayi checking abokinka, meya samu wayarshi?"

"bata shiga?"


"baya dagawa dai"


"ayyah, yana cikin studio ne, nasan yanzu haka silent take"

kada kai tayi tana dan ta6e baki
"nima nayi tunanin hakan"


"muje, nasan yanzu ma yakusan gamawa" inji saurayin

"ok, muje"


tare suka jero suna tafe suna dan labari jifa jifa har suka shige wani building


wani passage suka bi suna cigaba da firarsu Idan suka hadu da wasu a hanya su gaisa har suka qaraso inda zasu

tun kafin su shiga tafara jin cool voice dinshi na tashi in a cool rymth


lumshe idanunta tayi ta bude ahankali sannan tashiga ta kofar da Habeeb ya budemata


akwai mutane a studio din as usual amma basuda yawa, kowa hankalinshi da imaninshi ya tattara ya koma akanshi don dayawa basusan da shigowarsu Habeeb ba


daga idanu tayi ta kalleshi tacikin glass din dayake ciki

kanshi sanye da headphones sai mic dake girke a gabanshi mai dauke da abin tace murya


jitayi zuciyarta na melting lokacin data sauke idanunta akan fuskarshi, fuskar da duk duniya bataga mai kyawunta ba, fuskar da ke narkar da zuciyarta daga kallo daya


_Duba kigaa yadda sonki yayi dani.. dukda nasan kina sane_


_ki kalli cikin idanuwanaaa.. nasan xasu zayyane_


_wannan al'ajab na sone da qauna.. baki na kiranki neee_


_dana fada kiji_


_kibani agaji_

_indaina rangaji_

_kidanyi tsokaci_

_kibani ma'aji_

_ba zancen na gaji_

_ki kauda fuu da ji_

_a so baya ji_

_labarin zuciya_


_ni zaki tambaya_


_Abinda nakaji_

_ya zarce duniyaa_


_Idan na waiwaya_


_koko na sunkuya_

_amsar guda nakeji.._

_kinzaman habibiya_...


Kafe pink moving lips dinshi tayi da idanunta tana jin yadda sautin muryar tashi ke sinking har qasan zuciyarta


ahankali ta janye idanunta daga kan bakinshi tafara yawo dasu a fuskarshi


idanunshi a lumshe suke wanda hakan yaba zarazaran lashes dinshi damar hadewa, tarasa yaushe yafi kyau, Idan idanunshi na a lumshe ko Idan suna a bude.


kallon cikkakun girarenshi tayi ganin yadda suke motsawa ahankali, gangaro da idanun nata tayi kan pointed nose dinshi daya dace da fuskarshi, ahankali tasake maida idanun kan bakinshi dake motsawa haryanzu.


lumshe idanu tasakeyi ta bude tanajin wani abu na tasowa daga qasan zuciyarta


anya a duniya akwai wanda zai so gayen nan kamar yadda take sonshi? she doubt it, ajikinta tana jin duk wani mai son Deen to saidai yabi bayanta don soyayyar datake mashi batada iyaka


Deen on the other hand besan tana yi ba, yayi nisa, nisa daga wannan duniyar tamu, yana wata.duniyar daban, wanda yasaba shiga duk lokacin dayake waqa

idanunshi na alumshe amma yana gani clearly saidai ba abinda wadanda kecikin studio din ke gani yake gani ba

he has wander into his dreamland kamar yadda yasaba

acikin lumssasun idanunshi wani beautiful scene yake gani

fuskar da kullum ke zuwa mashi tana mashi gizo dare da rana, fuskar da sai idan yana ganinta yake iya rairo abinda ke zuciyarshi, fuskar da tazame mashi kamar abincin dayake ci ko iskar dayake shaqa


_ya za'ai na burge wacce nakeso da qauna? ya za'ai?_


_kalamaina sun kadan ta fahimceni sannan... ba hanya_


_kalamaina sun kadan ta fahimceni sannan ba hanya!!_


_inaso tasoni ne ba guruu babu laya_

_babu dad'i babu qarya.. ni banison riya_

_badon kwalliyaba kuma badon dukiya ba_


_badon zantuka ba kullum taimun maraba_


_ina sonki.. ina sonki.. inaa sonki_


_ina sonki so na gaskiya ba yaudara ba_


_ina sonki.. ina sonki.. ina sonki ni.._


_ina sonki so na gaskiya ba yaudara ba_

_ina sonki so na gaskiya ba yaudara baaaaa_


ihu studio din ya dauka da tafi wasu harda fito.

sosai mutanen cikin studio din ke nuna jindadinsu afili sai kirari suke mashi


bude lumsassun idanunshi yayi ahankali yana bin mutanen cikin studio din da kallo murmushi a fuskarshi


ahaka oily idanunshi suka sauka a kanta inda take tsaye tayi crossing hannayenta a qirji itama tana kallonshi


kafe juna da kallo sukayi na wani lokaci sannan ahankali deen ya sakarmata kyakyawan murmushinshi

jitayi wani farinciki ya mamaye zuciyarta nan take, ahankali itama ta sakarmashi nata murmushin mai kyau.


***


"ya school?" yafada cikin cool voice dinshi


"Alhamdullilah, ya naka aikin?" ta tambaya itama suna cigaba da tafiya side by side


"Alhamdullilah also, yasu mamy?"

"su mamy na nan lfy lau, tace ka kyauta daka maidasu gefe guda"

Dan murmushi yayi yana cusa yatsunshi cikin saisayayen sumarshi wadda bata kai ta da cika ba

"hmmm ba haka bane" yafada cikin murmushi

"to yane? kwata2 ka daina zuwa, ganinka yanzu sai an cika form, aita kiran wayarka ma ba'a samu" she complained

"am sorry, I've been busy ne a kwanakinnan amma zanzo, kiba mamy hqr"


Dan wara idanu tayi tace
"A'a, kabari duk ranar dakaje kabata, ni babu ruwana"

murmushi kawai yayi bece komai ba

ganin hakan yasa itama bata qara cewa komai ba suka cigaba da tafiya silently, tafiya gefe da gefe taredashi ba qaramin dadi yake mata ba musanmman Idan ta lura da yadda ake binsu da kallo inda mostly mata ne ke kallon nasu kowanne fuska dauke da kishi don sun lura Deen baya kula kowacce mace sai ita hakan yasa basasonta ko kadan.


parking space suka isa Deen yashiga waige2


"ina motarki?"


Dan daga kafadu tayi
"tadan samu matsala tana wajen mechanic"

"to da me kikazo?"


"adaidaita, yanzu ma dashi zan koma"


"amma kinsan adaidaita na wuya a arear nan ko?"

Dan 6ata fuska tayi
"I'll wait, no p"


Ajiyar zuciya ya sauke
"ina zuwa"

yana fadin hakan ya juya


Dan murmushi tayi

seems tarkonta ya danu, dama da gangan tasa drivernta dropping dinta tace yatafi kawai


ko minti biyu ba'ayi ba wata blue din mota ta qaraso wajenta ta tsaya


Deen ke ciki

"get in, let me drop you" yafada bayan ya sauke glasses din qasa


Dan sunkuyowa tayi tana kallonshi
"aren't you busy? kabarshi kawai xan samu adaidaita"


bece komai ba sai matsowa dayayi ya bude mata kofar

Ajiyar zuciya ta sauke sannan ta ida bude murfin tashiga ta maido ta rufe


tada motar yayi sannan yajata suka fita daga wajen.


Tafiya suke babu mai cewa komai acikinsu sai qira'ar Qur'an dake tashi cikin motar


Deen hankalinshi na kan titi yana driving at normal speed while itakuma tana lafe a kujerar mai zaman banza tana shaqar qamshinshi daya hadu da sanyin a.c din motar yabada wani sanyayar yanayi.


Babu jimawa suka isa kofar gidansu, batasan sun iso ba saida taji tsayuwar motar, sai.taga sunyi saurin zuwa, bata gaji da shaqar qamshinshi ba


"here we are" inji Deen


tashi tayi zaune sosai

"Bazaka shiga ba?"


Dan wara oily eyes dinshi yayi
"zan dai shigo soon insha allah"


"hmm to saina gayamata" tafada tana qoqarin fita

"me zaki gayamata?" yafada yana kallonta

"kazo amma you choose to turn around and go back"

"bazaki fadamata nazo ba" yafada fuskarshi da slight murmushi

"saina fada" tafada tana ida fita


"I dare you" yafada daringly fuskarshi da slight murmushi

kada kai tayi tana kwafa
"zaka gani kau" tafada tana rufo mashi kofar motar


dagama juna hannu sukayi sannan tajuya tanufi tangamemen gate din gidansu shikuma yaja motarshi yaqara gaba.


*10:15pm*


"Shikenan Kaka, allah yakaimu goben lfy" yafada ahankali


murmushi Kaka tayi ta shafa mashi kai
"Amin kyakyawana, yanzu kaje ka kwanta dare yayi nima barci nakeji"


"to Kaka, saida safe"


"Allah ya tashemu lfy, karka manta kayi alwalla kuma kayi addu'a"


kada kai yayi cikin murmushi sannan ya tashi ya kashemata fitilun dakin yabarmata na bedlamp kadai sannan yayimata sallama yafita.


ahankali yake takawa kasancewar dare yayi hakan yasa anajin faint sautin takunshi, ahaka harya isa dakinshi.


dakin is so big and neat, yasha kayan furnitures na zamani ga haske takoina.


direct gefen makeken gadonshi that is neatly spread ya nufa yafara rage kayan jikinshi

jefa wadanda yacire yayi a wani dogon bin inda dama yake saka kayanshi masu datti kafin laundrier yazo ya dauke washegari


toilet yashige don freshen up.


ya dade sosai a toilet din sannan yafito daure da towel a kugu sai wani a hannunshi yana tsane jikinshi


chanzawa yayi cikin kayan barci farare sannan ya shinfida sallaya ya gabatar da shafa'i da witr sannan ya rufe da addu'o'i


nade sallayar yayi ya maida ma'ajinta sannan ya miqe tsaye.


maimakon ya nufi gadonshi ya kwanta saiya nufi wani side din na daki


ahankali ya bude wata qofa wanda ta sadashi da balcony din gidan


stepping yayi cikin balcony din yana kallon waje yana feeling yadda iskan daren ke kadawa


koina yayi shiru sai kukan tsintsaye da zaka dinga jiyowa daga nesa dana qanannun qwari


garin yayi duhu sai hasken wata dake haskawa faintly

ahankali ya zura hannayenshi cikin aljihunnan wandonshi yana bin wurin da kallo


yaushe zaibar jinshi so empty?

yaushe wawakeken gurbin dake zuciyarshi zai cike?

yaushe duhu zai yaye?


yaushe haske zai qara ziyartar rayuwarshi?

yaushe farinciki zai sake ziyartar rayuwarshi?

yaushe?


ahankali ya daga kanshi ya kalli sama yana hango wata daya fara disashewa alamun soyake shima yashige cikin gajimare

bin yan mitsi mitsin taurarin dake saman yayi da kallo trying to count them amma sunyi yawa daya fara saiya 6ata a lissafin.

haqura yayi ya sauke idanunshi qasa yana qara observing din garin

hasken watan dake dan haska garin sai qara disashewa yake hakan yasa garin ke qara duhu, duhun da ga wasu na dan qanqanin lokaci ne don da gari ya waye zasuga haske, amma agareshi ba haka abin yake ba, koda gari ya waye wa kowa baxai waye mashi ba

ya dade cikin duhu kuma besan iya lokacin daxai sake dauka acikinshi ba.


maybe forever


maybe not...✍�


Ummin fasihu🧚🏻‍♀�
8/2/21, 9:43 PM - Buhainat😝: *🙍🏻‍♂️DEEN🙍🏻‍♂�*


*073*


*THE HARD DECISION*


*Aslm fans, ya kuke😊 sorry for jina shiru kwana biyu, bear with me bear with me, insha allah andawo kenan🥰, masu kira da masu cigiya dama masu sakamu addu'a duk ina Godiya, Godiya marar adadi. Allah yabar zumunci Amin🤲🏻*


Ringing din da wayarta keyi akaro na uku yasata jan dogon tsaki tareda jawo wayar afusace


shin me kiran baya ganewa ne? tunda taqi dagawa tun farko ya kamata ya gane batason takura ya kyaleta hakanan.


da niyyarta da kashe wayar amma ganin unknown number yasata dakatawa.

ba wai rashin sanin mai kiran yasata dakatawa ba sai,yadda taga number, very special number da kallo daya zaka mata ka haddaceta

katsewa kiran yayi

cigaba da riqe wayar tayi,taga ko za'a qara kira amma shiru hakan yasa ta juyazata maida wayar inda ta daukota

kafin ta gama ajiye wayar wayar tasake daukar ruri hakan yasa tafasa ajiyewar tasake dagota

number ce dai, wannan ko maye ne sai haka

saida kiran yakusan tsinkewa sannan ta daga takara a kunne batareda tace komai ba


can ma shiru akayi ba'a ce komai

Dan yamutse fuskarta tayi ta dago wayar taduba taga kiran na counting

to meyasa ba'a magana?

maidawa tayi a kunne again taji shiru hakan yasa taji ranta ya 6aci sai kawai ta tsinke kiran tana jan tsaki


ko seconds biyar ba'a qara ba wani kiran yasake shigowa na number

qin dagawa tayi kuma hakan besa aka fasa qara kira ba

a kira na uku ta daga a fusace ta kara a kunne da niyyar zazzagawa koma waye bala'i


kwanannan she's not in a.good mood, abu kadan ke fusatata amma seems basa ganewa most especially wannan annoying caller din


bude baki tayi da niyyar fara masifa saidai kafin tafara aka katseta da

"How dare you?" cikin wata muryar da kanaji kasan mammalakinta a wuya yake


sakin baki tayi in confusion, waye wannan? the voice...


"I said how dare you! ni nakiraki awaya ki tsinke? kinsan koni waye!" yafada cikin tsawa2 da alamu hakan ba qaramin 6ata mashi rai yayi ba


wani murmushin takaici yazo mata, hmmm dama takawo hakan, the annoying fringe won't just leave her alone

cikin son qara quleshi tace
"and who are you?"

cije lower lip dinshi yayi daga dayan 6angaren, yadda tayi maganar cikin izgili ba qaramin qara qonamashi rai yayi ba

"just don't let me show you the real me baby, I bet you you'll be sorry" yafada tsakankanin haqora

"really?" tafada in a mockery sound sai tadanyi dariya sannan tace

"well am sorry bana daga wayar zarraru, lokacina qayyadadene kuma ina amfani dashi ne wajen yin abu mai amfani, zarraru number doctor ya kamata su kira. zasu fi gane yarensu. have a nice day"

saita fara qoqarin cire wayar daga kunnenta don tsinke kiran amma annoying muryarshi tasake katseta

"KARKI SOMA! karki fara tunanin katsemin waya or else.." sai kuma taji shiru

jitayi fargaba tadan ziyarci zuciyarta

"or else?" ta tambaya cikin dakewa

"you'll be sorry" yafada cikin low but dangerous voice


taji d'arr a yanayin yadda yayi maganar, mexeyi mata? kwahi? dama ana kwahi ta waya? wane irin kwahi zaiyi mata, wadannan tunanin sunsata jin fargaba don tasan yana iya yin komai don ba mutunci gareshi ba.

amma Idan taqi katse kiran me hakan ke nufi? hakan hanya ce ta nunamashi cewa tsoronshi takeji, wanda hakan ke nufin qarin raini akan wanda yayi mata, no way!


"then.. make me be" tafada daringly sannan batareda tabashi damar maida numfashi ba ta katse kiran tamayi blocking number gabadaya


Tilla wayar tayi gefen gado cikin fushi da fargaba

"do your worst!" tafada cikin son kawar da fargabar tunanin abinda zaiyi mata, no matter what bazata gwadamashi tana tsoronshi ba, that's it.


A bangarenshi kau sakin baki yayi yakuma kasa sauke wayar daga kunnenshi

he can't believe ta katse mashi kira a karo nabiyu, shi? Mussadiq Al-hassan? shine yau ake katsewa kira? bayan hakan kuma takirashi zarrare?


sauke wayar yayi ahankali yana kallon numberta, number daya sato a wayar qanwarshi, duk don yaji ya take yakuma ji ko wannan mahaukacin dan uwan nata beyi something stupid ba

amma ji Abinda tayi mashi, na farko taqi daga kiran harya jeramata uku abinda be ta6a ba sannan bayan ta daga ta katse mashi kira, abinda duk duniya ya tsana, qarin gishiri a ciwo ta kirashi zararre.


lallai ma!


qara maida lower lip dinshi yayi ciki yana tauna ahankali

he'll make her be sorry

that's a promise!


A bangaren zee kau komawa tayi ta jingina da frame din gado zuciyarta babu dadi, sosai damuwa ta mamaye zuciyarta.


yau kwana biyu kenan da faruwar wannan al'amarin sai taga kamar Aymaan avoiding dinta yake

kwata2 baya bari su hadu Idan ma sun hadun baya bari ko magana ta hadasu zaya bar wajen

wasa wasa har sukayi kwana biyar ahakan, ko kwakwarar magana daya bata shiga tsakaninsu ba, koda yana zaune awuri datazo wajen zai wayance ya kara waya a kunne ya tashi yabar wajen


hakan ba qaramin dagulawa zee lissafi yake ba, duk jikinta yayi sanyi tana jinta so guilty.

duk yadda takeso magana ta hadasu koda gaisuwace yaqi bata damar hakan, don kwata2 ya toshe duk hanyar dazasu mu'amallanci juna ya sauya mata daga Aymaan din data sani zuwa wani Aymaan din daban.


***


Zaune yake yana kallon yadda Aymaan ke attending wata patient yana mata bayanai.


yafi minti goma yana mata bayanin sannan ya rubuta mata magungguna ya bata takardar yana fada mata ranar dazata sake dawowa for checkup.


Godiya sosai matar wanda da alamu taji dadin ganawarta da Dr Aymaan din tayi sannan ta tashi tafita shikuma yajawo wani file gabanshi yana yan rubuce rubuce


Ajiyar zuciya Ahmad ya sauke sannan yace
"wani lokacin kamar mutum y rufeka da duka don takaici"

Dan murmushi ne ya kufcema Aymaan saidai bece komai ba

"yanzu da zuwana patients nawa kayi attending agabana? ka shanyani kamar kayan wanki, tsabar bana gabanka dukda patients din sun qare Bazaka saurareni ba?"


sai a lokacin Aymaan ya dago ya kalleshi sannan ya dan ta6e baki
"I thought zuwa kayi ka kalli yadda ake attending patients"


"dole kace haka tunda ni ai nataso nazo wajenka, dole kayimin wulaqanci son ranka tunda ni nakawo kaina" inji Ahmad yana fuming fuska

murmushi kawai aymaan yayi bece komai ba saima cigaba da aikin gabanshi dayayi


"to maganar dai da bakaso ne, maganar dakaita avoiding dina akanta itace takawoni, Aymaan kabani mammaki, ban ta6a tunanin zaka sare a daidai wannan stage din ba, ban ta6a tsanmmanin haka agareka ba"


Aymaan be dago daga Abinda yake ba ya kalleshi amma hakan bazai hana mutum hango yadda mood din fuskarshi ta chanza ba

"Aymaan, Idan mutum zaiyi taimako yayi da zuciya daya haka Idan bazaiyi ba yaqiyi da zuciya daya"


sai a lokacin Aymaan ya dago daga rubutun dayake ya kalli Ahmad, ya tsaida idanunshi akanshi na wani lokaci kafin yace
"me kake nufi?"


"kafini sanin Abinda nake nufi Aymaan, da gaske ne so sone amma sonkai yafi, saidai inason kasani duk inda akasa sonkai gaba ana aikata kuskure,kuskuren dake jawo tarin danasani"


Aymaan da ranshi yafara 6aci yace
"go straight to the point Mallam, I hate kwana kwana"


"Batun Deen nake maka, zancen dakake qoqarin watsarwa saboda son kanka"

ran aymaan yasake 6aci
"then? meye nayi na sonkai aciki? are you trying to blame me for everything? koko ka kuramce lokacin dayace sun haramta ga juna?" yafada cikin 6acin rai


"ba maganar hallarci ko haramcin dake tsakaninshi da zee ke gabanmu ba, hallalci dake tsakaninshi da iyayenshi da danginshi shine gabanmu, haba Aymaan? you've been helping tunfarko, ka sadaukar da abubbuwa dayawa tun daga farkon wannan abin, ka jajirce kayi tsayin daka akan wannan al'amarin, sai yanzu da komai yazo gangara zaka cire hannunka akai, haba aymaan, you need to think twice"


kallonshi Aymaan keyi tunda yafara maganar harya kai aya, saiya sauke Ajiyar zuciya

"yanzu me kake tuhumana dashi? kana tuhumana ne akan rashin bayyanarshi ga iyayenshi ne ko me?"


"ina tuhumarka ne akan qin taimakawa d'an uwanka musulmi saboda wani dalili naka na daban, Aymaan ka ta6a tambayar kanka meyasa warwarewar komai ke biyowa ta wajenka? kaine silar sanin asalin Deen, kaine silar warwarewar cunkussashen matsala dake cunkushe shekara da shekaru, ain't you proud of that?


Aymaan nasan kana son Zainab kuma duk abubbuwannan dakakeyi kanayi ne don tsoron rasata, kana gudun kar bayyanar Deen tazama rugujewar mafarkinka nason mallakar zee saidai karka manta matar mutum kabarinsa, babu mai auren matar wani, Idan zee matarkace babu wanda ya isa ya aureta saikai haka zalika Idan ba matarka bace duk dubararka duk wayonka baxaka ta6a mallakarta ba"


Dan murmushin takaici Aymaan yayi
"wannan fatanka ne agareni ko?"

girgiza kai Ahmad yayi yana Dan murmushi
"meyasa zanmaka wannan fatan? Aymaan ni kaina zanfi kowa jindadi Idan ka mallaki Zainab, saidai mu musulmaine, munada imani kuma imanin mutum bazai ta6a cikaba sai ya yarda da qaddara walau mai kyau ko akasinta.


Idan Zainab matarkace zaka aureta aymaan Idan Kuma ba ita bace ka roqi Allah ya musanya maka da mafi alhairi, Aymaan ba dukkan Abinda bawa keso yake zaman mashi alhairi ba, kullum Abinda akeso da bawa shine ya roqama kanshi Abinda yafi alhairi ta hakan kawai zai cigaba da ganin haske a rayuwarshi

bayan haka ya kamata ka tausayawa Deen, Aymaan kata6a saka kanka a matsayinshi ko sau daya? mutuminnan na rayuwarshi ne acikin duhu, haryanzu lalube yake don shi kanshi besan koshi waye ba.

ace kanada iyaye kanada dangi amma baka ta6a saninsu ba? ace kanada uwa amma baka ta6a sanin dadinta ba? ko dan wannan yaci ace ka tausayamashi ka taimaka mashi, bakasan dalilin dayasa kafi kowa shiga case dinnan ba, bakasan dalilin dayasa kodayaushe kaine sanadin warwarar wannan matsalar, bakasan inda zaka tsinci sakammakon wannan taimakon naka ba"


qara matsawa jikin table din daya raba tsakaninsu Ahmad yayi ya kamo hannun Aymaan dake kallonshi tundazu da hannu bibbiyu yace

"Aymaan I know this is a very hard decision for you amma ka kalli abin da idon basira, kayi tunani akai, ka kwatanta misalta kanka dashi sannan ka yanke abinda kake ganin yafi dacewa, kayi tunani Aymaan"


***


kashe motar yayi sannan yacire seatbelt din dake jikinshi ya bude kofar motar yafito ahankali


Dan lumshe oily eyes dinshi yayi yana dan qanqantar dasu sanadin rays din rana daya dallemashi fuska


rufe kofar yayi sannan yadanna mata remote sannan yajuya yafara takawa cikin tafiyarshi mai cikeda nutsuwa


mutanen dake harabar wajen keta gaisheshi inda matan kowacce ke gaisheshi cikeda kicihi da iyayi shidai iyakarshi slight murmushi kawai


ahaka harya shiga cikin building din.


Da manager dinshi suka cikaro shima yana shirin fitowa

washe fuska Habeeb yayi yana qarasowa

"Dan halaq kai nafito nema dama, kayi baqi"

"baqi? suna ina?" inji Deen yana cigaba da tafiya

"suna reception suna jira.. kuma da alamu manya ne sosai don kallo daya zakamasu kagane da alamu dai akwai babban kamu" ya qarashe cikin rad'a yana kashe mashi ido daya


Dan harararshi Deen yayi bece komai ba sai cigaba da tafiyarshi dayake


duk inda suka iske mutane sai an gaidasu musanmman Deen da suke bama wani extra girmamawa


ahakan suka qarasa reception din inda baqin nashi ke zaune suna jiranshi


su biyun idanu suka zubamashi kamar zasu hadiyeshi ko kyaftawa basason yi yayinda Deen ya qaraso gabansu da friendly face dinshi


sallama yayi musu wanda saida sukaji saukarta.har qasan zuciyarsu

cikeda sanabe suka amsa suna wani kwanainaya duk wai don su burgeshi

"kune baqin namu?" ya tambaya still wearing the friendly face

daya daga cikinsu datasha matsasun qanannun kaya ta.langwa6e kai tace
"eh, tundazu muna nan muna jira duk mun gaji da zama"

"ayyah,afuwan. ai yanzu jira yaqare.. shall we?" yafada yana nunamasu alamun su biyoshi

cikin jindadin yadda yasake musu suka tashi yayi gaba suka bishi abaya har suka isa office dinshi


office din dan madaidaici ne saidai it's very neat and tidy

saida ya nunamasu wurin zama suka zauna sannan shima yawuce kujerarshi ya zauna yana facing dinsu, ana haka shima manager dinshi yashigo shima riqeda dan tray mai dauke da two table water da glass cups ya ajiye.gaban yanmatan shima fuskarshi awashe saiya koma gefen Deen ya tsaya

"yeah, how may I help you miss(s)" inji Deen yana maida hankalinshi akansu fuska asake

duk blushing sukayi suna jin kansu untop don samun kansu gaban wannan shahararren mutumin yana basu full attention ba qaramin fasa masu kai yake ba

cikin karya murya wadda tayi magana dazu tace
"ni sunana halimatu amma anacemin hally baby diya ga minister of finance wannan kuma qawatace jamcy diyar comissioner of education, dama ba komai ya kawomu ba illa munaso kayimana waqa ne na birthday kasancewar insha allah next week Friday qawata jamcy keyin birthday, zamuso kayimata waqa inso samune ka hallarta kayimana show" ta qarashe tana wani jujjuya idanu

kada kai Deen yayi sannan ya maida kallonshi ga wadda takira jamcy din wadda itama ta tsuke cikin English wears anci makeup sai qyalli ake, Dan murmushi yayi mata yace
"congratulations and happy birthday in advance"

wani dadi yaqara qumesu hakan yasa tayi murmushi broadly itama cikin narke murya tace
"thanks so much"

"saidai am very sorry domin bazan samu damar yimuku aikin nan ba kasancewar ranar dakuke magana baninan inada aiki aranar a kebbi state, I sincerely apologize for this" yafada cikin nuna rashin jindadin yadda baxai samu yimasu aikin ba


suma kallo daya zaka masu kasan murnarsu takoma ciki

"kanada aiki ranar?" inji hally cikin rashin jindadi

"yes, zanje wani daurin aurene nayimasu waqa a dinner, sunriga sunyi schedule din ranar tun watan daya gabata, am very sorry" yafada apologizingly

"but.. yanzu babu yadda za'ayi kayi cancelling wancan schedule din? zan biya koma nawa ne" inji jamcy


murmushi Deen yadanyi
"am sorry miss, amma baxan iya cancelling schedule dinba, it's almost a month dasuka kama ranar sai yanzu kawai one week da bikin na chanza magana? kema kinsan hakan beyi daidai ba, hakan karya alqawarine and a promise is a debt, nasan ku kanku baxakuso nayi hakanba, your conscience will bother you too I know"


shiru sukayi saidai kwata2 ba haka sukaso ba

"to yanzu Mr balarabe ya kake ganin za'ayi? please karka cemin hakan bazai yiwuba, nariga nagama sanar da dukkan friends dina kai xakazo ranar, please do something"
yadda take shagwa6ewa sai.kayi tunanin wata yar shekara uku ce sai wani mar mar take da idanu ga wani langwa6e wuya datake tana 6ata fuska kamar zatayi kuka


Ajiyar zuciya Deen daduk ya qagara sutafi yayi yadan cije lower pink lip dinshi cikin naxari can yace
"gaskiya nima banji dadiba, Am sorry for the dissapointment, gashi duk ranakunnan dazasu zo I'll be busy, da wuya asamu ranar da zan kasance free, saboda irin hakan yasa masu son aiki kezuwa dawuri sosai don kama rana da lokaci saboda irin wannan dissapointment din, amma... babu komai zanyi qoqari nayi squeezing time nasamu ko waqar ce kadai nayimuku kinga koda banzoba nidin dai nayi waqar"

hakan yadan yimasu dadi

"oh! we're very grateful, da babu gwara babu dadi, ko?" inji hally tana kallon jamcy

kada kai jamcy tayi still fuska a kwa6e tace
"hakane mungode, dukda naso kaidin kazo amma still duk lokacin dakake less busy kazo don kaima ka tayani murna, ga i.v din dakuma complimentary card dina, number na naciki, feel free to come anytime youre less busy" tafada tana doramashi cards din asaman table din


murmushi yayi ya dauki cards din yace
"oh.. thanks so much, insha allah xanzo duk.lokacin danake less busy, Habeeb.."


Habeeb dake tsaye yana sauraronsu tundazu yadan sunkuyo yana cewa
"yes sir"


"take their names, Idan kuma akwai sunayen datakeso asaka a waqar kayi listing dinsu"

"ok Sir" inji Habeeb yana dawowa kusada yanmatan don yin yadda yace

cikin qanqanin lokaci suka gama komai suka kumayi ciniki sannan suka fara shirin Tafiya

turamashi faskekiyar wayarta jamcy tayi agabanshi

kallon wayar yayi saikuma yadago ya kalleta

kashe mashi ido daya tayi cikin salo tace
"your digits..please" tafada tana wani narke murya

Dan murmushi yayi zaiyi magana tayi saurin katseshi da
"pleeease" tana narke fuska


dauke idanunshi yayi daga kanta yana ta6e baki cikin zuciyarshi don wannan ba karo na farko bane da mata ke mashi irin wannan shirmen ba

babu musu yadauki wayar yashiga lodamata phone number dinshi daya saba ba ire irensu wanda ko sau daya baya picking call dinsu sannan ya turamata agabanta


cikin jindadi ta dauki wayar tayi dialing number sai gashi daya daga cikin wayoyinshi tafara Ringing

"save it, zamu dinga gaisawa" tafada cikin lullumshe idanu

"alright, insha allah" yafada yana kada kai

nan tazaro kudin aikin dasukayi ciniki ta dora a table suma, Habeeb ya dauka ya qilga yaga suncika sannan suka tashi suna bankwana inda sai ranar daren birthday din zasu dawo su amshi aikinsu.


bankwana suka sakeyi kamar basuson tafiya sannan suka wuce Habeeb na take musu baya don rakasu waje


Ajiyar zuciya Deen ya sauke bayan fitarsu sannan yakoma jikin kujera yadan kishingida

guntun tsaki yaja, shifa shiyasa beson aikin mata, ya lura duk yawancinsu ba hankali ya ishesu ba, kullum burinsu su burgeshi shikau haryanzu yakasa ganin wacce ta burgeshi koda daidai da kwayar zarra ce, he found them so annoying and suffocating


yana haka aka sake bude kofar office din

dagowa yayi ya kalli kofar yaga ashe Habeeb ne sai washe baki yake

bebi takanshi ba yajawo wata takarda yana dubawa

"yayi mai farinjini! gaskiya aiki a matsayin manager dinka ba qaramin alhairi bane agareni, kai allah yaqara nisan kwana" Habeeb ya qarashe yana fifitama Deen yana dari biyar biyar miqaqqu dake hannunshi

ta6e baki Deen yayi ya maida hankalinshi kan Abinda yakeyi don kobe tambaya ba yasan kudin menene hannunshi

"ai dama ina ganinsu nasan fa yau kakata ta yanke saqa, da ganinsu kaga 'ya'yan manya, wannan mai kamada zabuwar tabani wai na shigar daita, wahallaliya" ya qarashe yana fashewa da dariya harda xama kan kujera


qara ta6e baki Deen yayi don yasaba da hakan, hakan yasha faruwa, yanmata suyita tulama malohon kudi wai a sunan kamun kafa shi yarasa meke damun qwalwar wasu matan

"gaskiya aikinnan akwai samu, bayan albashi ga allowances wajen yanmata, kai allah dai yaja zamani ai balarabe nidakai mutu karaba takalmin kaza, donma kacika kwafsawa? da kana bada hadin kai da nafi haka samu, narasa sadda zaka waye?"


"zakaci ubanka ne Idan na koreka daga aikin kwata2, now get out" inji Deen yana hade cikkakun girarenshi


yar dariya Habeeb yayi yace
"haba oga, ai bama za'ayi haka ba. insha muna jone kodayaushe babu mai rabamu sokake nakoma wajen oga Audu mai sallamar #500 arana? ga aiki ga wahala amma anyi gudun tsiya kasamu #500 arana? nan kau hmmm abin ba'acewa komai dai"

"aikau ka kusan komawa wajenshi tunda naga alamun ba nutsuwa zakayi ba"


"haba balarabe, wace nutsuwa bayan wannan danayi? ai duk wanda yaganni yanzu yasan na nutsu, haba ai da da da yanzu ba daya ba wlh.

Don ma kanamin black stomach, kwata2 baka bani hadin kai. ni narasa wane irin.mutum ne kai da kwata2 baka wayewa.

ji yadda mata ke binka kana.gudunsu, a xamaninnan wlh mata inba mahaukatan kudi suka ganka dasu basu binka kaiko mata ba kudinka ba sukeso kai sukeso, wasu ma suna iya 6atar da ko nawane akanka amma kai ko ajikinka, mtcheew allah dai na ragewa aya zaginta, wlh danine kai? hmmm" ya qarashe yana.kada kai yana cije lower lip dinshi


yar dariya Deen yayi yana cewa
"Dan Air.. dakaine ni mezakayi"

"hmmm ai fadi ma 6atawa, ace ni mata ke rubibi haka ai ina? zanyi zamanina yadda ya kamata inci duniyata da picking stick, ai ina ganin nima dai waqarnan zan koya nafara qila adace nima azo ana rubibi na, ca6! da kaga abu, tsala tsalan yanmata zan dinga sawa a vidiyoyina ba irin naka ba da babu wani armashi ko qayatarwa, saidai.kayima mutane tsaye gandadar kana waqa ko irin yanmatan nan da akesawa a vidiyo baka sawa kuma ahaka ake rubibin kallon vidiyon,mtcheew.

Don qauyanci ko amshi bakaso mace tayi maka, kafiso kayima kanka komai, haba abin ko armashi babu, wlh koyaya kasanyo mace ciki abin saiya fi armashi amma kai baka ganewa

babu inda kafi afki sai share yanmata, wai kaga mata tsala tsala suna binshi amma batasu yake ba kamar wani marar lafiya, gaskiya ya kamata ka binciki kanka wlh, kar ace bakada lafiya ne baka saniba

ni duk duniya babu wacce na ta6a ganin ka kula ko kake kulawa sai ko *Lailah*, ita kadai naga kuna dan shiri daita, itama kuma nasan saboda babanta shiyasa kake kulata har kuka dan shaqu don nasan da babanta ba ubangidanka bane itama ba kulata ba zakayi...."


barin sauraronshi Deen yayi ya cigaba da Abinda yakeyi don yasan halin Habeeb, Idan yafara zuba yadda kasan ru6a66iyar radio hakan yasa wani lokacin yake bude kwandon shara ya jefashi ya rufe ya cigaba da harkar gabanshi

shi yanzu soyayya ma bata burgeshi, kai ba soyayya bama matan gabadaya basa burgeshi, so dayane yariga ya daukeshi dungurungum yaba wata, wacce duk duniya ita kadai ke iya burgeshi, saidai kash! tayimashi nisa, nisan da ko hangenta bazai iya yiba...✍�


Ummin fasihu🧚🏻‍♀�
8/2/21, 9:43 PM - Buhainat😝: *🙍🏻‍♂️DEEN🙍🏻‍♂�*


*074*


*THE HARD DECISION 2*


Horn biyu yayi sannan yaga alamun gate din yafara motsi alamun za'a bude

komawa yayi ya jinginar da kanshi da kujerar ya lumshe gajiyyayun idanunshi

yana jin lokacin da aka wangale gate din amma ko motsawa beyiba, can yaji ana kwankwasa glass din motar

ahankali ya bude idanun nashi dasukayi ciki ya kalli mai kwankwasar sannan ahankali yasauke glass din motar

cikin girmamawa da fara'a maigadin yafara yimashi sannu dazuwa

Dan murmushi kawai yayi mashi yana daga mashi hannu, ganin hakan yasa maigadin yasan yau ba lau

ganin ya sake tada motar yasa maigadin dan jada baya yabi motar da kallo harta shige cikin gidan sannan shima yashiga cikin zuciyarshi yanajin babu dadi ganinshi a wannan yanayin dabe saba ganinshi ba.


Parking yayi a parking space sannan yakashe motar saidai maimakon yabude kofa yafita saiya maida kanshi ya dora akan sterring tareda sake lumshe idanunshi


this is the toughest time of his life, komai ya jagule mashi, kanshi ya dauki chaji yarasa ma wane tunani ya kamata yayi, he was feeling very very exhausted, komai ya daina tafiya mashi daidai.


ya dade sosai a wannan yanayin sannan can yasamu ya dago yasa hannu ya bude kofar cikin mutuwar jiki yafito.

jawo briefcase dinshi da lapcoat dinshi yayi sannan ya rufe kofar

hannu yasa yadan sassauta necktie din wuyanshi sannan yafara takawa ahankali cikin mutuwar jiki yanufi cikin gida.


Jin alamun za'a bude kofar datayi yasata saurin waigawa daga kallon datake ta kalli kofar

dama ba kallon take ba don idanunta kawai ke kan t.v din amma hankalinta kwata2 baya akai

qurawa kofar idanu tayi har ta ida budewa mai shigowarya shigo


wani Ajiyar zuciya da batasan dashiba tayi tana jin dan relief a zuciyarta

cigaba da binshi da kallo tayi tana kallon yadda yake komai akasalance

gani tayi ya maida kofar ya rufe sannan yajuyo yanufi hanyar wucewa sama yana qara sassauta daurin necktie din dake damunshi

ganin kamar bema lura daita a falon ba yasata miqewa tsaye tana kallon yadda yake tafiyar tashi cikin jan kafa, kallo daya zakamashi kasan amatuqar gajiye yake kuma yana buqatar hutu saidai batajin tana iya kyaleshi don tundazu take nan xaune duk don taga dawowarshi

tagaji da sharetan dayake, tagaji da nuna halin ko in kula dayake nuna mata, tanaso su shirya, tanaso su koma kamar da

dukda dama can bawai tasake irin sosai dinnan dashi bane bare ace tayi missing company dinshi, kawai dai sotake tabashi hqr takuma tabatarda baya riqe daita arai ko babu komai hakan zai bata sallamar zuciya

"Akhie?.." tafada daidai lokacin daxai fara taka stairs


cak ya tsaya daga yunqurin hawan stairs din dayayi fara kamar wanda aka tsaida da remote


ganin ya tsaya kuma be juyoba yasata fara takowa ahankali wajenshi tana jujjuya magangannu a zuciyarta tana son gano wacce kalma zayafi dacewa tayi amfani daita


saita tazarar tsakaninsu yarage kadan sannan ta tsaya tana kallon bayanshi dake kallonta haryanzu

Dan qaqalo murmushi tayi tana dan wasa da yatsunta nervously tace
"Akhie kadawo? sannu da dawowa"


"yauwa"

taji ya amsa mata ataqaice sannan yafara taka stairs din zai wuce

ganin hakan yasata saurin sake dakatar dashi da cewa

"Akhie, inason muyi magana please"


be dakata daga tafiyar dayake ba yace
"later, yanzu am tired"


"nasani, amma maganar bamai tsayi bace please ka saurareni" tasake fada itama tana haurowa saman ganin yafara yimata nisa, tasan Idan tabari yatafi ita dasake sashi a ido sai Allah yayi


dakatawa yayi daga tafiyar amma bai jiyoba hakan yasa zee tasake matsowa kusa.tana cewa
"please, koda 2mins ne"


Ajiyar zuciya aymaan ya sauke ahankali sannan yajuyo ahankali ya fuskanceta ya zubamata Hazel idanunshi


sauke idanunta tayi tana cigaba da fidgeting yatsunta tama rasa ta ina zata fara

jin shirun zaiyi yawa yasa Aymaan cewa
"2mins dinfa na Tafiya"


dago large eyes dinta tayi ta kalleshi idanun na kyallin ruwan hawayen dasuka fara taruwa aciki

kallonshi tayi taga shima kallonta yake babu ko kyaftawa

ahankali tasake sauke idanun sannan cikin sanyayar murya tace
"kayi haquri.."


"Don Allah.." tasake fada tana dagowa tana sake kallonshi


shima kallonta yake bece komai ba kuma bayada alamun cewa komai din

hakan yasa tasake sauke idanunta qasa hawayen dake maqale a idanun suka digo qasa

"Am so sorry... I... nasan komai zanfada maka bazan ta6a iya wanke kaina agurinka ba, am sorry, kayi hqr kadaina fushi dani... am so sorry" ta qarashe muryarta na breaking saboda kukan dake shirin kufcemata


saurin rufe fuskarta tayi da taffukan hannayenta tana kukan marar sauti


Lumshe idanu Aymaan yayi ya bude cikin wani yanayi yana jin ranshi na qara dagulewa

kallonta a wannan yanayin ba qaramin sake burkita mashi lissafi yayi ba yayinda yakejin sheshekarta har cikin zuciyarshi

"shhhh... wayace ina fushi dake? ni ba fushi nake dake ba Zainab" yafada cikin tattausar murya


dagowa fuskarta datayi.sha6e2 da hawaye tayi daga cikin taffukanta ta kalleshi tace
"ba wani, ni nasan fushi kake dani, babu ruwanka dani, you no longer speak to me, ko kallona bakayi, Idan nazo wuri saika tashi, Idan nayimaka magana baka amasawa, you're totally ignoring me" tafada cikin shesheka


murmushi ya kufcemashi ganin yadda take magana cikin shesheka kamar wata qaramar yarinya, ahankali yashafa saisayayar sumarshi sannan yace
"ayyah, am sorry. ni ba ignoring dinki nake ba kawai am busy ne a kwanakinnan amma am sorry Idan hakan ya 6atamiki rai"


dago wet eyes dinta tayi ta kalleshi tanajin wani sanyi sanyi a zuciyarta, girgiza kai tayi tace

"ni zance maka sorry, nice nayimaka laifi amma wlh ba yadda kayi tunani bane, ni bansani ba, bansan shine ba.. bama shiri ma kwata2 dashi, shine keta zuwa school din yana tarana.. and kodayaushe saimunyi fada dashi.. ranar ma bansan yadda akayi yazo wajen ba, Kawai saidai naga..."


"shhhh..." Aymaan ya dakatar daita daga bayanin datake son yimashi


murmushi yayi yana kallon cute fuskarta, Dan matsowa yayi kusada ita yana kallon fuskarta still fuskarshi dauke da murmushi yace

"I know Zainab, no need to explain. Actually ni banji haushinki ba saboda nasan koke wacece, I know yayi hakan ne don inji haushi.. kuma naji.

shiyasa nayi taking out haushin akanshi, so kibar damun kanki unnecessary kinji? nasan babu komai atsakaninku, koda akwai banida hurumin dakatar dake ko hanaki, don haka kibar damuwa kinji"


kada kai tayi tanajin kamar anyi lifting dutsi mai nauyi daga kan qirjinta

"kanada hurumi akan haka Akhie, kanada hurumi akan komai saboda kai yayana ne, kafini sanin what's best for me, kafini sanin Abinda zai cutar dani kuma ka isa kasani abu nayi ka hanani kuma na hanu"


murmushi sosai Aymaan yayi yana jin sanyi na ratsa cunkussashiyar zuciyarshi sanadin kalamanta

"hakane, nagode qanwata. sorry for making you cry, now wipe those.tears kar wancan.uwar gulmar tafito taganki haka taga wallenki"


murmushi ya kufcemata ta sauke kanta tana goge fuskarta da bayan hannu akunyace tanajin dadin yadda yayi maganar yanzu cikin barkwanci kamar yadda yasaba, kobabu komai hakan sign ne na ya daina fushi daita

"good, yanzu Bari natafi, your 2mins yazama almost 10mins, Bari natafi karna fadi don nafara ganin double double"

sake murmushi tayi kawai batace komai ba hakan yasa yajuya kawai yashiga qarasa.haurawa saman

binshi da kallo tayi harya ida haurawa saman sannan ta danyi ihun murna qasa qasa sannan tajuyo tasauko daga stairs din takoma falon tanajin wani irin dadi a zuciyarta, atleast tasan sun shirya dashi kuma zaibar riqeta a zuciya, hakan yasa taji zuciyarta tayi wasai tanajin wani dadi a zuciyarta.


****


Dagowa tayi daga kallon wayar hannunta datake ta juyo ta kalli Lailah dake kwance rigingine dan qaramin pillow rungume a qirjinta idanunta a lumshe


"kai gaskiya bestie, dole ma ki rikice akan wannan gayen, ya hadu over, soo masha allah" injita


murmushi kawai Lailah tayi batareda ta bude idanun ba

gyara zama budurwar tayi tace
"gaskiya zakuyi making perfect match Idan har kuka jone, just look at him so handsome and geogous"


"hey! watch out, banfa cika son ana yabamin taurarona ba, karki ja labari ya chanza yazunnan" inji Lailah tana dan hade face


dariya budurwar tafashe dashi sannan cikin sigar tsokana tace
"iyee? su kishi manya. yo labarin ya chanza mana. ke nifa inajin nakusa chanzawa daga supporter zuwa rival, muddin na cigaba da kallon wannan fuskar tsab zaki hangoni cikin yan takararki"


tashi Lailah tayi kamar wadda aka mitsina ta kwace wayar hannun budurwar tana cewa
"to narabaki dasake kallonshi Idan kuma kika qara ko bayan idanuna ne ban yafeba"


dariya tasakeyi tana riqe ha6a
"Idan baki yafeba sai akace mai zai sameni?"

"tsab zaki watse don tsab zan dagamiki nono bari ganin ina washe miki 36" inji Lailah tana komawa tasake kwanciya

dariya sosai budurwar tasake yi sannan tace
"sannu uwata, aikau dole na kiyaye inba sonake na watse ba, kika dagamin nono aina kade"


"har ganyenki kau" Lailah dake danne dannenta a wayar tabata amsa

tasowa budurwar tayi daga kan stool din datake tadawo saman gadon itama kusada Lailah ta zauna

"Babe gaskiya mutumin nan yayi akowane siga, ina baki qwarin gwiwar kicigaba da jajircewa wajen winning heart dinshi, wlh Idan kika mallaki balarabe kin more"


sauke wayar datake dannawa tayi ta kalleta sannan ta tashi zaune itama tana facing yarinyar

"Meenah, Abinda kike fada is easy wajen fada amma da matuqar wuya wajen aikatawa.

tun lokacin dana fara dora idanuna akan balarabe yagama da zuciyata, tun ranar daya fara zuwa gidannan nakamu da mahaukacin soyayyarshi.

ada inajin ana love at first sight, this and that duk bana daukar hakan serious saida hakan yafaru akaina, Meenah I love this guy, fiyeda tunaninki, fiyeda tunanina ma"


"then fight for your love Lailah, kinada komai, komai da kowacce mace zatayi taqama dashi.

kinada kyau Lailah, Idan kinso kina iya contesting gasar kyau kuma ki cinye saboda allah yayimiki baiwar kyau both facial da na diri, gaki diyar maishi babu Abinda kika nema kikarasa ga ilimi both Islamic and western ga wayewa, kin mallaki komai Lailah don haka wannan ma zaki mallakeshi insha allah"


Dan murmushi Lailah tayi tadan kada kai
"hakane, amma kinsan ita soyayya babu ruwanta da Abinda da Abinda ka mallaka, sai kiga ke mai taqamar kin mallaki komai kinanan zaune wata dako kamo kafarki batayi ba tazo tayimiki zarra, misali ni yanzu.. na mallaki komai amma nakasa mallakar zuciyarshi, yayinda nikuma tawa zuciyar ke begenshi shi tashi wata take bege"


"Lailah, kar wannan ya sanyayar miki gwiwa, wancan ex dinshi ce, kinsan meye ex? short time din EXPIRE kenan"


Dan murmushi Lailah tayi tace
"expire.. amma ba agunshi ba, nidake munsan yadda haryanzu zuciyarshi ke bugawa daita acikinta, Meenah haryanzu balarabe yana sonta.. har gobe.

And.. wannan shiyafi komai yimin ciwo. kinsan zafin ka dinga kallon wanda kake bege yana begen wani? kinsan zafin kafada soyayyar wanda kakeda tabbacin bakama gabanshi sam?"

"Lailah kibar cewa bakya gabanshi, ke kanki kinsan kina gaban balarabe, ko babu komai yana treating dinki with respect yana kuma kulaki"


komawa Lailah tayi ta jingina da frame din gado tana dan murmushi mai ciwo tace
"yana treating dina da respect? dama waye balarabe baya treating da respect? kema kinsan wulaqanci ba halinsa bane ba, haka yakewa kowa"

"ba kowa ba, kema kinsan baya kula mata dik yadda zasu shigemashi, he always try to avoid them in a polite way though"

"wayasani ko nima yana qoqarin avoiding dinane? wayasani ko yana kulani ne don dole? ni nasan nike cusa kaina agareshi, be damu daniba"


"Lailah..."


"kinga Meenah nagane, nagane bakyason gwiyaguna su sare ne shiyasa kike encouraging dina haka, amma a fidda sonkai Meenah kema kinsan nikeson balarabe not the other way round.

Da farko nazaci abin zaizomin da matuqar sauqi, ganin simpliness dinshi da yadda yakeda sauqin sha'ani

can kuma ganin nafara gaining attention dinshi saina fara jindadi ina tunanin shima ya fara sona ne duba da yadda yake treating dina yana kuma kulani, ashe nice ban fahimci abin ba, ashe yana treating dinane yadda yake treating kowa, Idan ma akwai banbanci Dan kadan ne kuma shima saboda alaqar dake tsakaninshi da abbana ne.


kwatsam nagano ashe duk Abinda nake tunani duk imagination dinane, banice gabanshi ba, yanada wadda yakeso, wacce tariga ta mamaye mashi zuciya.

ada Idan ina sauraron waqarshi sai naita ganin qila
duk kalamanshi dayakeyi ni yakemawa ashe ba haka bane, ashe yana expressing kanshi ne ga wata, wata can" ta qarashe tana girgiza kai ahankali tana iya qoqari wajen controlling emotion dinta

tarasa dalilin dayasa duk lokacin data tuna da akwai wata wadda wanda take so ke haukar sonta takejin zafi, zafi marar misaltuwa a.zuciyarta"


dafata Meenah tayi a kafada tace
"kar hakan ya sanyayar miki gwiwa Lailah, bakisan dalilin dayasa Allah yarabashi da wancan din ba, bakisan dalilin da Allah ya hadaku ba, wataqila dama they didn't deserve each other, wataqila dama kece perfect match dinshi, maybe he's the ONE and you're also the ONE.
wataqila qaddara ce ta rabasu da wancan don ke ta hadaku"


Ajiyar zuciya Lailah ta sauke ahankali tace
"I hope so, Meenah Idan narasa balarabe..."


"bazaki rasashi ba insha Allah, kisamu wannan yaqinin kikuma dage da addu'a dakuma qoqarin mantar dashi wancan ki kafa taki rumfar a zuciyarshi"


"it's not easy..."


"it is insha Allah, it will be.,kawai kidage da du'a, I'll help too"


kallonta Lailah tayi tadanyi murmushi

"thanks Meenah, thanks for always been there for me"


murmushi itama Meenah tayi tana dan bige kafadarta tace
"shut up, what are amminai for? insha Allah saimun 6arar da gwamnatinta, sai munkoma mune da mulkin!"


dariya Lailah tayi ganin yanayin datayi maganar tana jin wani qwarin gwiwa itama a qasan zuciyarta.


***


kwance yake kan neatly spread gadonshi, yayi matashin kai da pillow yana kallon sama, sanye yake da singlet sai short nicker, dakin yayi shiru babu Abinda kake ji sai qarar a.c da aka qure adakin.


*_bakasan dalilin dayasa kafi kowa shiga case dinnanba_*


*_bakasan dalilin dayasa kodayaushe kaine sanadin warwarar wannan matsalar ba_*


*_bakasan inda zaka tsinci sakammakon wannan taimakon naka ba_*


lumshe idanunshi Aymaan yayi yana dafe goshinshi da hannu daya


*_kaine silar sanin asalin Deen, kaine silar warwarewar cunkussashen matsalar dake cunkushe shekara da shekaru, aint you proud of that?_*


*_I know this is a very hard decision for you Aymaan amma ka kwatanta misalta kanka dashi sannan ka yanke abinda kake ganin yafi dacewa_*


bude idanun yayi ahankali ya zubama p.o.p din dakin ya qureshi da kallo


kallo daya zakamashi kagane yana cikin tsantsar damuwa, yarasa tunanin dazaiyi yarasa me zai yanke.

ga qoshi ga kwanan yunwa.

bayyanar Deen zai samo abin farinciki ga kowa amma baya tunanin harda shi.

yayinda bayyanarshi xaizama hanyar warwarewar matsalolin wasu shi zai zama silar toshewar nashi.


what should he do?


what decision should he make?


ya zaiyi?


Ummin fasihu🧚🏻‍♀�
8/2/21, 9:43 PM - Buhainat😝: *🙍🏻‍♂️DEEN🙍🏻‍♂�*


*075*


Tunda zee da Aymaan suka shirya zee hankalinta yasake kwantawa don sosai shariyarshi ya hanata nutsuwa don tana matuqar girmamashi kuma yanada qima sosai a idanunta, baxataso abinda zai lallata kyakyawar alaqar dake tsakaninsu ba.


tuni ta cigaba da harkokin gabanta lafiya lau takuma dauki tunanin duk abubbuwan dasuka faru ta watsar gefe ta cigaba da harkokinta.


kasancewa exam is at the corner yasa ta maida hankalinta sosai a karatunta dukda dai bawai exam din ya matso kusa sosai dinnan bane.


yanzu tafi zama library a duk lokacin da batada lecture kasancewa batool ba gwanar zaman library bace yasa kusan kodayaushe ita kadai ke tafiyarta library din tayi karatu sai Idan zasu gida ko Idan zasu shiga cafteria suke haduwa.


Yau ma kamar kullum tana zaune a kusurwar library din inda nan ta maida mazauninta duk lokacin da tazo library din


littatafai ne gabanta sai pen a hannunta tana rubuce rubuce

sosai hankalinta yatafi akan abinda takeyi har ya kasance batasan abinda ke wakana ba a kewayenta.


tadade tana jin wani qamshi qamshi wanda kamar ta saba jinshi saidai bata maida hankali akai ba don sosai kanta ya dauki zafi da abinda take ko qwaqwaran motsi batason yi.


ahankali wani siririn zufa ya gangaro daga gefen kanta ya silalo gefen fuskarta

Ajiyar zuciya ta sauke ahankali tana dan dakatawa da rubutun datake

ajiye pen din hannunta tayi da niyyar dauko hanki a jakka don share zufar saidai kafin tayi hakan taga an miqomata wani hanki fari qall

babu musu ta amsa tafara tsane gumin dashi

can kamar wadda aka tsayar da remote ta qame qamm

kasa cigaba da tsane gumin tayi haka kuma takasa dagowa


bugun zuciyarta ne yafara qaruwa yayinda kwakwalwarta tafara lissafa mata Abinda ke faruwa

ta dan dade a wannan position din kamar wanda aka dasa kafin can tafara dago idanunta cikin qarfin hali


bisa kyakyawar fuskarshi ta sauke idanunta wanda hakan yayi daidai da faduwar gabanta

ahankali tadan jabaya tana kallonshi a bit shocked and surprised


a bangarenshi kau zaune yake kan kujerar dake facing dinta yayi balancing yayi crossing kaffafunshi

as usual idanunshi toshe suke cikin black shade fuskarnan atamke

hankalinshi na kan wayar hannunshi dayake daddanawa hankali kwance

ahankali zee ta hadiye yawu still zuciyarta na racing

rabonta dashi tun ranar dasukayi fada da aymaan a canteen, sai gani tayi kamar an sauyashi ne don yaqara mata wani qwarjini bisa wanda yakedashi

tunawa tayi da qarshen haduwarsu ta waya hakan Kuma yaqara mata gudun bugun zuciyarta, tasan yauma baxasu wanye lafiya ba


qoqarin daidaita yanayin fuskarta tayi tana cin serious itama sannan ta jefa hankin hannunta a dan waste basket din dake gefen kujerarta.

daukar pen din data ajiye tayi ta maida hankalinta akan littatafan gabanta tana qoqarin ida daidaita nutsuwarta

cigaba da pretending din yin aikin gabanta tayi saidai samm bawani gane abinda takeyi take ba hankalinta duk yana kanshi tana jiran jin mezai biyo baya


ahankali tadan wurga idanunta a fakaice tana duba library din sai taga almost kowa yafita saura mutum daya kawai dake daga farko farkon library din

sake maida idanunta tayi kan littatafan gabanta tana saqe saqen abinda ya kamata tayi, ta tashi ne? kota bari taga ikon Allah?

batason tabashi slight chance din dazai gane tana tsoronshi don hakan bazai taimaka ba kwata2 saima damar dazai bashi na cigaba da takura mata saidai dukda hakan tana fargaba don ta lura samm mutumin nan bayada mutunci ko digo, ita abinda yafi daure mata kai ma shine dalilin dayasa yake bibiyarta, meyasa bazai sakarmata mara ba hakanan? a lokacin,da ita ke bibiyarshi shike bayaso amma yanzu data fita harkarshi shi yanzu ya bude nashi shafin na takuramata.

me ya kamata tayi don getting rid of him daga rayuwarta? meya kamata tayi? koko takai qararshi wajen school authority?

tunawa tayi da kallamanshi na rannan dayace ko shugaban school din be isa ya hanashi ba, shin hakan gaskiya ne? koko kawai cika bakine kawai?


motsin dataji daga gaban library din ya katsemata guntun tunaninta

kallon wajen tayi taga wannan saurayin dayayi saura ne ke shirin fita daga library din

Dan bude idanunta tayi tana kallonshi harya ida ficewarshi daga library din


ahankali ta sauke idanunta ta maida kan littafin gabanta zuciyarta fall saqe saqe, ahankali tasake dagowa tadan saci kallonshi qasa qasa sai taga haryanzu hankalinshi nakan wayar hannunshi

shawara tafara yi da zuciyarta kan meya kamata tayi

ita kadai dashi a wannan quiet wurin beyi making sense ba, Idan yayimata wani abin fa? wait.. Idan wani yashigo ya taddasu haka fa? Idan batool tashigo fa? Idan akasake coincidence tashigo tareda Aymaan fa?

gabanta taji yafadi sanaddiyar wannan tunanin dayaxo mata.

no, bazata sake bari irin abinda yafaru abaya yasake faruwa ba, no way!

dagowa tayi sai gani tayi wannan karon wayarce kare a kunnenshi yana magana qasa qasa cikin larabci cikin gadara kamar wanda akaiwa dole.

ganin hakan yasata yanke shawarar yin amfani da wannan damar wajen fecewa


rurrufe littatafan tashigayi da sauri ta cuccusasu a jakka sannan ta miqe tana gyara nadin veil dinta

rataye jakkar tayi tazo ta giftashi zata wuce


cakk ta tsaya lokacin dataji an cafki tsintsiyar hannunta

wara manyan idanunta tayi saboda yadda abin yazo mata so sudden

saurin Juyowa tayi tana fizge hannun nata da qarfi tana kallonshi da manyan idanunta dake ware haryanzu


ko motsawa beyiba bare ya juyo yadda kasan bashi ya riqo hannun nata ba sai cigaba ma dayayi da wayarshi hankali kwance


motsi bakinta yafarayi kamar zatayi magana saidai tama rasa abinda zatace hakan yasata qara juyawa da sauri zata wuce

qara kamo tsintsiyar hannunta taji anyi, sake Juyowa tayi ta kalleshi in shock sai gani tayi wannan karon shima ita yake kallo

cikkakiyar trimmed girarshi daya ya dagamata ahankali in a naughty way

kafin tayi wani tunanin taji an fizgota da qarfi and the next thing data gani shine fuskarshi daff da tata wanda tazarar dake tsakanin tsinin hancinta da nashi befi 1 inch ba


💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖


qara kallon kanta tayi a mirror din a karo na babu adadi, sotake taga inda beyiba cikin kwalliyarta ta gyara.

ita kanta tasan qarshen kyau tayishi saidai tarasa meyasa takejin kamar haryanzu beyiba, tundazu take gaban mirror din tana kwalliyar amma haryanzu takasa gamsuwa da ita.

ahankali ta buga tagumi tana kallon kanta cikin mirror din

tarasa yaushe tazama haka, wai yau ita ke tsaye gaban mirror for almost an hour don kawai ta burge wani, just to impress wanda batajin zaima tsaya kallonta bare ya tantance irin kwalliyar tata

she can't believe itace wannan dai classic Lailah din wadda maza basa gabanta, wadda ta dauki soyayya shirme har take kallon duk wanda yazo wajenta dasunan soyayyar mashirmanci, yanzu itace tsundum tayi nitso cikin kogin soyayyar, soyayyar ma mai wahalar wa.

Tunawa tayi da ranar data fara ganinshi wanda baxata ta6a mantawa ba don ranar na maqale a qwalwarta tana iya tunawa very vividly


tunawa tayi da lokacin data fara ganinshi a kofar main entrance dinsu lokacin tadawo daga school

tunawa tayi da yadda taganshi jingine da daya daga pillar wajen yana dan daddana qaramar wayarshi


tunawa tayi da yadda ya dago oily idanunshi ya saukesu cikin nata wanda tundaga eye contact dinnan komai nata ya chanza, rayuwarta ta sauya ta chanza daga Lailahrta tada takoma wata sabuwar Lailah din

daga kallo daya komai nata ya chanza, labarin rayuwarta ya sauya takoma wannan lailahr, Lailah datasha banban da wancan.


shigowar wata qaramar yarinya tana tsallen murna ya katseta daga guntun tunaninta tajuyo tana kallonta


qarasowa yarinyar tayi wajenta cikin tsallen murna tana kalkadama Lailah ledojin chocolates din hannunta

ko bata tambaya ba tasan inda ta samosu amma still tace
"tofa? kekuma daga ina haka? who gave you chocolates?"

cikin washe baki yarinyar tace
"uncle mana kuma harda Icecream ma babba mami tace naba Jamila tasamin a fridge"

Dan wara idanu Lailah tayi tace
"wow! yanzu ina uncle din?"


"yana falo tareda mami, mami tace kizo ku gaisa" tafada tana qoqarin bude daya daga cikin pack din chocolates din


shiru Lailah tayi tana sauraron yadda bugun zuciyarta ya chanza, dukda dama tasan da zuwanshi kuma tundaxu shi take jira don tun jiya dataji abbanta na waya dashi akan yau zaizo takasa nutsuwa tanata jin kamar tajawo lokacin amma gashi yanzu yazo din amma kuma tanajin kamar bazata iya zuwa dinba dukda yadda zuciyarta ke kwadayin ganinshi din.


Ajiyar zuciya ta sauke tasake kallon kanta a mirror din, sanin cewa Idan ta cigaba da lagudar fuskar tana iya 6ata kwalliyar ma takoma wani abin daban hakan yasa ta miqe tsaye tana gyara rolling din veil dinta ta dauki turare taqara dan fesawa sannan ta kwashi wayoyinta tanufi hanyar fita tana qoqarin ganin ta saita bugun zuciyarta


***


qara wara manyan idanunta tayi in outmost shock zuciyarta na mugun bugu


kusanci sosai ke tsakaninsu don hannayenta data dafa qirjinshi dasu ya hana jikinsu hadewa waje daya

huramata iskar bakinshi mai qamshin mint yayi yana qara daga mata gira daya

"da ina zaki?" yafada cikin muryar rad'a


qoqarin tashi tafarayi tanajin yadda inner jikinta ke rawa

hanata tashin yayi ta hanyar zagaya hannunshi ta bayanta ya ruqota wanda hakan ba qaramin jan lantarkin jikinta yayi ba

agigice zee tace
"innalillahi, wh..what are you doing" tafada tana qoqarin tashi again


"am showing you how crazy I am, you called me psycho, don't you?" yafada still cikin rad'a yana kusanto fuskarshi ga tata


jabaya tayi tana qara tareshi da taffukan hannayenta dake kan qirjinshi

"m..mussadiq stop, wai meye haka? a..are you in your right sense?" tafada cikin rawar murya zuciyarta kamar zata faso qirjinta tafito

"no.. ni zarrare ne, koba haka kikace ba?"


"Mussadiq.."


"kince number Dr ya kamata na nema don mu gana shine nazo kibani"


"Mussadiq zanmaka ihu, I swear" tafada muryarta na rawa, sosai tsoro ya bayyana a fuskarta


wani guntun murmushi ya su6ucemashi sannan yaqara matso da fuskarshi dab da tata

"hakan ma zaifi qayyatarwa, azo aganmu ahaka" yafada still cikin rad'a qamshin bakinshi sai shigarmata hanci yake saboda kusancinsu


hankalin zee ne yaqara tashi, iya rudewa ta rude, ga yadda tunanin wani yazo yagansu ahakan yaqara hautsinamata yan ciki

dama haka Mussadiq yake, she know he's crazy amma batasan Abin nashi yakai har hakaba

"Mussadiq let me go.. this is wrong, you know it" tafada cikin muryarta data kasa daidaitawa


tunda take bata ta6a samun irin wannan kusancin da namiji ba

dukda ba bisashi tafado ba saidai suna daff sosai don taffukan hannunta data tare qirjinshi dasu ya hanata ida fadawa kanshi wanda shine kadai contact din jikinta da nashi sai kuma hannunshi dayasa ya tareta abaya don hanata tashi

ganin beda niyyar yin yadda tace din yasata dan rintse idanunta ta bude sannan cikin ahankali tace
"please.."


nanma shiru yayi sai kallo daya kafe fuskarta dashi

"you're not my muhharam Mussadiq, this is totally wrong, please let me go" tasake fada tanajin kamar ta fizge kanta saidai tasan any slight struggle zaisa taqare ajikinshi abinda Kuma bataso kenan


"sai kin maimaita Abinda kika fada ranar"

"Mussadiq.."


"nine zarrare ko?"


saurin girgiza kai tayi

"ni kika katsewa kira?"


"no, I.."


"maimaita Abinda kika fada aqarshe, mema kikace?"


"m..mussadiq wannan duk ya wuce.. I... kabarni natashi tukkuna please"


"yadda zaki gudu ko? answer me, ni kika katsewa kira? kinsan hakan meyake nufi agareni?"

tunda yafara magana take girgiza kai, ita kadai tasan yadda takeji


qara matso da fuskarshi daff tata yayi yana cewa
"speak, are you a lizard?"

qara girgiza kai tayi tana maida kanta baya

"m..mussadiq..."


"yes?"


"stop moving closer.. please"


"why?" yasake fada still moving closer


"al..alright, am.. am sorry" tafadi kalmar datasan ita kadai zata ceceta


ganin still bebar matso fuskar ba yasata sake cewa

"am sorry, ba gashi nafadi ba? please stop"


"you're sorry for what?" yafada still moving closer

"sorry for hanging up your call"


"and?"


"and.. and for calling you a psycho" tafada tana qara jabaya


"and?"


"and.. and for... for daring you"


"and?"

Dan squeezing fuskarta tayi cikin rashin fahimta

"I.. I think that's all"


"really? you thought so?" yafada yana daga gira daya

"am sorry for everything then, please let me go, this is totally wrong" tafada kamar zatayi kuka


shiru yayi yana sake kafeta da idanunshi dake lullu6e cikin glass din idonshi

itama sai samun kanta tayi da kafeshi da idanu kamar yau tafara ganinshi

sun dan jima ahakan idanunsu kafe da juna

motsa baki Mussadiq yayi zaiyi magana saidai kafin yayi zee ta rigasa


"Deen.." tafada ahankali cikin murya mai kama da rad'a


kallonta ya cigaba dayi bece komai ba


hawaye yaga sun taru a idanunta data kafeshi dasu babu kyaftawa

ahankali suka zubo suka gangaro kumatunta

mammaki ne ya kamashi ganin hawayen nata sunqi tsayawa sai gangarowa suke daga cikin idanunta dasuka fara chanza launi


hakan yasa ahankali ya janye hannunshi daya tareta dashi abaya saidai bata motsaba bare ta tashi din tana nan a yadda take still wet idanunta kafe dashi


jiyayi duk badadi don saiyayi tunanin shine silar hawayen nata


"are you ok?" yafada yana kai hannunshi fuskarta ya sharce hawayen kumatun damarta da yatsa

firgigit tayi lokacin da taji contact din yatsar a fuskarta sai kuma tayi saurin kallonshi kamar wadda ta farka daga barci sai kuma tayi saurin tashi tsaye


shima tashin yayi yana kallon yadda take share hawayen fuskarta da bayan hannunta

saurin duqawa tayi ta dauki jakkarta data fadi tun lokacin daya fizgota ta rataya idanunta aqasa

"Z... Ummie" ya kirata yana kallonta

bata kalleshi ba tazo zata wuce still kanta aqasa

shan gabanta yayi, ganin hakan yasa ta chanza hanya nan ma ya tare yana kallonta yanason suhada ido amma taqi dago fuskarta


"Ummie..."


"get out of my way please" ta katseshi cikin muryarta dake rawa sosai


"but why..."

kasa qarasawa yayi saboda dagowa datayi ta kalleshi da idanunta dasuka qarasa rinewa daidai kuma lokacin wani hawayen ya digo

cigaba da kallonshi tayi da idanun nata batareda ta iya fadin abinda takeson fadi ba

jikin Mussadiq ne yayi sanyi, tabbas ya hango wani abu cikin idanunta mai wuyar fassaruwa kuma kallo daya yaimata yagane she's emotionally hurted


ahankali ya kauce mata daga hanya still yana kallonta

bata jira komai ba tawuce dasauri tanufi kofa

juyawa yayi yana binta da kallo yana cire shade din idanunshi a lokaci guda harta fice daga library din.


dasauri tafito daga library din ta juya tabi wata hanya cikin gudu gudu sauri sauri

bata tsaya ba saida takai wani quiet wuri inda babu mutane

dagudu ta qarasa gindin wata bishiya ta durqushe wajen kukan datake riqewa tundaxu ya kufcemata ta toshe bakinta da taffukan hannayenta tacigaba dayi da dukkanin zuciyarta


❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️


tun daga nesa data hangoshi zuciyarta tasake sauya bugu

ahankali shauqi yafara mamaye zuciyarta harya tsuma dukkanin jikinta

ahankali ta cigaba da saukowa daga stairs din idanunta akanshi


zaune yake kan daya daga cikin luntsuma luntsuman kujerun falon

sanye yake cikin wata dakkakiyar dark brown shadda wadda tafiddo farar fatarsh sosai


kanshi na sanye da hula zanna bukar wadda ta shiga da shaddar hannunshi sanye da tsaddadiyar agogon fata brown kaffafunshi kuma sanye suke da baqaqen socks.


zaune yake a kujerar dake facing kujerar mami fuskarshi dauke da qayyataccen murmushinnan nashi mai bayyana beauty point dinshi

agabanshi akwai Dan qaramin table na glass dake cikeda drinks da kayan ciye ciye wanda da alama ko ta6asu beyiba.


shagala tayi da kallonshi harta qaraso falon batasaniba saida muryar mami ta katseta daga lulawar datayi duniyar kallonshi


"kinga baqon August ko?" inji mami tana nuna Deen dake murmushi

murmushi Lailah tayi tace
"lallai kam mami, nima yanzu Afrah taje take gayamin, maraba da baqin August"

dagowa Deen yayi ya kalleta yadan hade girarenshi sai kuma ya sauke kanshi qasa murmushi still a fuskarshi

"shiyasa garin yau ya lumshe kamar za'ayi ruwa ashe dai da dalili" inji mami cikin tsokana

"aikaudai mami, but are you sure nan yazo direct? tayiwu fa 6atan hanya yayi don ni ban yarda wannan ziyarar tamuce ba" inji Lailah data zauna kujerar kusada ta mami

qara dagowa Deen da duk kunya ta hanashi saqat yayi ya kalli Lailah again da expression din 'ke ko?' a fuskarshi, itakuma tayi murmushi tana dan juya idanunta

"lallai kau, babu mammaki. to Mallam balarabe anya ziyarar nan tamuce koko dai gaskiya Lailah ke fada?"


hannu yakai yana dan shafa sumar kanshi cikin jin kunya yace
"mami Lailah kawai sotake ta hadamu"

"babu ruwana mami, ki tambayeshi yaushe rabonshi da gidannan" inji Lailah

"ina ruwanki to? ai nasan ayyukane sukayi mashi yawa shiyasa amma ai kowa yasan son mai son zumunci ne" inji mami cikin kare Deen

kallon juna Lailah da Deen sukayi Deen yayi wani murmushin gefen baki

Dan 6ata fuska Lailah tayi tace
"kai mami shine zaki bani gula?"

dariya mami tayi
"ai gani nayi kina neman yima dana sharri ne"

"d'an da bama wani jidake yake ba?" inji Lailah yana kumburi

"babu komai, ai tsakanin uwa da d'a sai Allah, babu mai shiga tsakaninmu"

qara kumbura fuska Lailah tayi tana kauda kai tace
"aike dama bakyason laifinshi"

yar dariya mami tayi tace
"ai baya laifi"

saikuma ta fuskanceshi

"ya aiki? komai lfy ko?"

Deen da murmushi yaqi barin fuskarshi yace
"Alhamdullilah mami, komai na tafiya daidai"

"masha Allah, Allah ya taimaka ya cigaba da budawa"


"Amin ya Allah mami" ya amsa cikin girmamawa

"ya wajensu Kaka? kwana biyu haduwa tayi wuya"


"suna lfy, tacema a gaidaku"


"muna amsawa, insha allah zan shigo wajenta ma kwanannan"

"to allah ya amince mami"

duk hirar dasuke idanun Lailah na kanshi tana cikeda burgewa tana jin kamar ta hadiyeshi don so


miqewa mami tayi tana cewa
"ina zuwa bari nadubo wancan sarkin 6anar, yanzu haka tanacan tanayi dama Idan kaji shiru babu wulginta to gwara ka bincika"


murmushi kawai Deen yayi


"ayimin magana Idan katashi tafiya"

"to insha Allah, a sauko lfy"


ahaka mami tatafi tabarsu su biyu a falon


sadda kai Lailah tayi tafara wasa da yatsunta nervously

dama Idan suna wuri daya su biyu kadai haka takeji, duk saitaji ta takura

jin shiru yasa tadan dago ta saci kallonshi sai taga hankalinshi ma nakan wayar hannunshi

sauke idanun tayi tanadan murmushi sannan taqara dagowa tace
"bakasha komai ba yaya"


dagowa yayi daga kan wayar ya kalleta sai kuma ya kalli kayan gabanshi yace
"hmmm nasha ruwa ai, wannan tullin kayan ina zani dasu? am full"


tasan gaskiya yake fada don Deen baya yima abinci kawaici Idan yanaso ci yake

"ok, ya aikin? hope yanzu ayyuka sundan lafa" tafada cikin son janshi da fira don tasan Idan tayi shiru saidai suyi zaman kurame don ta,lura kamar he's not good at fira, shirunshi yafi surutunshi

"Alhamdullilah, da sauqi gaskiya sosai. pressure din yarage"

"to Allah ya taimaka, more more grace to your elbow"


murmushi yayi yace
"Amin Amin, kefa? ya school?"


"school Alhamdullilah, munata fama ga exam nata gabatowa"


"to Allah yabada sa'a, adai cigaba da dagewa"


"insha Allah yaya"


haka suka cigaba da firarsu sama sama har suna haka abba yashigo.


sosai abba yaji dadin ganinshi dukda dama yasan da zuwanshi, cikin girmamawa Deen ya gaidashi yana amsar handshake din da abba yake miqomashi a kunyace

inda sabo yaci ace Deen yasaba da hakan don hakan nacikin al'adar abba miqama mutum hannu suyi musabaha duk banbancin shekarunsu kau


abba irin mutanen nan ne masu faran faran ga raha da dariya

nan ya zauna suka shiga labari wanda duk yashafi aikin Deen


a yanayin dasuke firar zaka hango tsantsar qaunar da abba keyima Deen shikuma Deen zaka hango tsantsar girmamawa da biyyaya dayakema abban.

can kuma suka tashi abba da Deen suka fita waje suka bar Lailah a falon


parking space suka nufa inda Abba yanunama Deen sabuwar motarshi daya saya kwana uku daya wuce wadda ke lullu6e cikin rigar motar


da taimakon Deen suka yaye lullu6in motar.

danqareriyar motace yar yayi mai mugun kyau, sosai Deen yayima Abba allah yasanya alhairi sannan yashiga duba mashi lafiyar motar kamar yadda Abba ya buqata don ganin ko tanada wani fault daya kamata agyara kafin afara hawanta


Lailah ce ta tashi daga inda take zaune taqarasa jikin Windows din falon tadan yaye labulen wajen tana leqensu


Deen ne tagani gaban motar ya dage murfin gabanta ya sunkuya yana dubata

tattare hannuwan rigarshi dayayi yaba farar fatar hannunshi bayyana mai cikeda kwanttatun gargasa


lumshe idanu tayi ahankali tasake budewa akanshi, tarasa meyasa komai Deen yayi saiyayi mugun yimashi kyau.

cigaba da kallonsu tayi har yagama yan gyare gyaren dayake, Abba ya zagaya yashiga motar Deen na gaban motar still harya tadata shikuma yaqara sunkuyawa yana duba engine motar


sun dan dade ahakan kafin abban yafito bayan yakashe motar shikuma Deen ya maida murfin gaban motar ya rufe alamun sungama Abinda sukeyi


sake lullu6e motar sukayi sannan sukazo suka wuce suka kama hanyar part din abban.


Ajiyar zuciya Lailah tasauke tana sakin labulen, sosai take tausayama kanta na fadawa son maso wanin datayi, fatanta dai Allah yabata mafita akan wannan matsalar tata yakuma sassauta mata.


sai bayan sallar isha'i Abba da Deen suka sake shigowa main house din don Deen yayi bankwana dasu mami.

basu dade ba suka fita da Abba da Deen da Afrah data liqemashi suka rakashi har wajen motarshi


ko anan ma sundan qara dadewa suna fira sannan Deen yashiga motar bayan sunyi sallama ya tada motar yajata.


bin motar da kallo Lailah dake leqensu ta windown dakinta tayi harta fice.


sauke wata nannauyar Ajiyar zuciya tayi sannan tasaki labulen takoma ta jingina da bango tana Lumshe idanunta.


💚💚💚💚💚💚💚💚💚💚


Tun bayan rabuwar zee da Mussadiq bata qara walwala ba, haka ta qarasa ranar cikin qunci da rashin kuzari

sosai batool ta damu da hakan kuma tambayar duniyarnan tayimata akan meke damunta amma taqi gayamata saidai tace mata babu komai

dole ta haqura ta kyaleta saidai tasan akwai abinda ke damunta kuma tafi alaqanta hakan da qila mikin soyayyarta ne yatashi don dama haka take wasu lokacin, duk yadda takeson 6oye damuwarta tayi pretending she's ok wani lokacin kasawa, wani lokacin kawai sai kaga mood dinta yachanza takoma very depressed.


murda handle din kofar akayi tawaje aka turo kofar


batool ce tashigo dakin ta tsaya daga bakin kofar tana kallon zee

haryanzu zaune take inda tabarta rungume da pillow ta kafe wuri guda da ido


Ajiyar zuciya batool ta sauke sannan ta qarasa shigowa cikin tana sakin murmushi cikin son wartsakar daita


fadawa tayi kan gadon itama gefen zee tana dariya wanda hakan yadawo da zee daga duniyar tunanin data shiga tajuyo tana kallonta


"albishirinki" inji batool happily


dauke kanta xee tayi daga kallonta don kwata2 bata cikin mood din wasa, kamar bazatayi magana ba can kuma tace
"goro"


murmushi batool tayi tace
"to yarinya Akhie tafiya zaiyi, guess where?"

Dan kallonta zee tayi saikuma tasake kauda kai, da batool tasan yadda batason ko magana ce dabatazo tana takura mata ba amma sanin wacece batool din yasata sanin amsamata din kawai shine kwanciyar hankalinta


"where?" ta tambaya tana dan yatsine fuska cikin qosawa


"Nigeria!" batool tabata amsa cikin murna

saurin juyowa Zainab tayi ta kalli batool din


"Nigeria?.."✍�


Ummin fasihu🧚🏻‍♀�
8/2/21, 9:43 PM - Buhainat😝: *🙍🏻‍♂️DEEN🙍🏻‍♂�*


*076*


*THE TRIP*


"Are you serious?" inji zee tana kallon batool cikin mammaki


"wlh yanzu naji suna labarin da ummy, gobe ma zasu tafi zasubi flight din 12noon"

shiru zee tayi tana kallonta, kawai saita tsinci kanta dajin wani irin kewar kasar tata.

bata ta6a tunanin zatayi missing Nigeria nan kusa ba amma yanzu dataji wannan zancen saitaji tayi missing dinta sosai, tayi missing qasarta da mutanen ciki, jitayi dama daita za'ayi tafiyar amma kuma anya zuwan bazai famamata tsohon mikinta na zuciya ba? kodayake anan dinma ba tsira tayiba, tagudo nan don mance past dinta tayi moving on amma seems it's not easy don kullum past dinta cikin hunting dinta yake

kauda kanta tayi daga kallon batool din tace
"me zaije yi acan to?"


"asalin tafiyar batashi bace, Ahmad wani business trip zaikaishi can shine shima yace zayaje don yarabu dazuwa gashi dama kwanannan he's less busy"


"kenan tareda Ahmad zasu tafi?"

"yeah... did you want to go too?" inji batool tana quramata idanu


wani kallo zee tayi mata sai ta kauda kai
"never!" tafada tana hade fuska

murmushi batool tayi
"nayi tunanin kina kewan can ne"

"banayi" tabata amsa tana komawa ta jingina da frame din gadon


murmushi tasake yi tace
"A'a dole kiyi missing Nigeria, gida gidane ko don mahaifanki dake can"

"ai yanzun ma kamar tare muke don kullum muna waya kuma Idan naso ganinsu ma zan gansu ta video call so bana wani missing dinta"


murmushi kawai batool tayi bata qara cewa komai ba saidai talura da yadda mood din zee yaqara chanzawa wanda ta tabbata harda zancen tafiyar tasake dagulamata mood din


A daren ranar barci rabi da rabi zee tayi, sosai tunanin tafiyarsu Aymaan ya tsayamata arai yakuma tadomata tsumin kewar qasarta da mutanen cikinta.


washegari sukuku ta tashi, jiki babu kwari tahau daily chores dinsu da shirin makaranta.

suna zaune a dining suna breakfast Aymaan ya sauko daga sama shima yayi joining dinsu.


gaidashi batool da zee sukayi ya amsa cikin kulawa da barkwanci kamar yadda yasaba sannan shima ya gaida ummy


batool ce tayi serving dinshi sannan ta koma ta zauna tacigaba dacin abincinta

jawo abincin yayi gabanshi yafara ci saidai rabin hankalinshi nakan zee daketa tsakurar abincin sama sama

Dan murmushi yayi sannan yadauki mug din shayinshi dake tururi yadan kur6a ya ajiye yasake kallon zee

"ke yar Nigeria, hope kinsan yau zankaiwa qasarku ziyara?"

dagowa zee tayi ta kalleshi sai tadanyi murmushi
"hmmm jiya nakejin labari, Allah ya tsare hanya"

Dan daga gira daya yayi yace
"hakama zakice? nayi tunanin liqewa zakiyi kice kema kina zuwa"

Dan ta6e baki tayi tace
"saidai nace Allah yakiyaye hanya"

dariya batool tayi tace
"hmmm haka zakice ai, yarinya tazo qasar turai taji dadi ta manta da qauyenshi" taqara fashewa da dariya Aymaan na tayata

"kekau kullum tana cin dajaja🍗ta larabawa tana shan ni'imttaciyar weather mu ba dole ta manta ba?" inji Aymaan

kumbura fuska zee tayi tana makamasu wani kallo

"wane ni'imttaciyar weather? ai wlh Nigeria tafi nan weather mai ni'ima. kuda nan da rana tsabar zafi kamar ana gasa mutum a oven? a qasarnan Idan kayi walwala da zirga zirga cikin kwanciyar hankali to darene, ahakan kuma kukeda weather mai kyau?" tafada tana harararsu

"ahaka kuma kike qara haske kina fresh, dakike can kauyen naku ko rabin kyan yanzu baki kaiba dukda ni'imttaciyar weather taku" inji batool


"wake haske? ai kuma kunsan nafi kyau danake qasarmu, anan banda tsabar rana da zafi me akeyi, badon ina kaffa kaffa da kaina ba da yanzu nazama duna qila sai an haska da touchlight za'a dinga ganin fuskata dakyau"


dariya duk sukayi harda ummy dake aikin sauraronsu

"aimu ranarmu fari takesawa ba baqi ba ko kin ta6a ganin balarabe baqi? koma akwaisu yan kadanne, mafi yawancinmu fararene" inji Aymaan

"Allah mai iko, yanzu nan kuma jinku kuke ku larabawa ne ko?" inji ummy da sai yanzu tasa baki

dariya zee tayi
"karfin hali kenan, dadai ba'a san asalin balbela ba"

kumbura fuska batool tayi tace
"yo Idan ba larabawa bane ba su wanene?"

"ato, tayani tambaya" inji Aymaan

"cikkakun larabawa nemu" inji batool

"fararen ma kuwa" Aymaan yabata amsa


dariya sosai zee keyi don sosai suka bata dariya

"A'a gwarama kayi shiru da bakinka Aymaan, Idan ana maganar farare kabar zazzaqewa don.kunya zakasha" inji ummy dake taya zee dariya


Dan 6ata rai Aymaan yayi yace
"to ni ba farin bane? wai batool ni ba fari bane?"

Dan kallonshi batool tayi saikuma tafashe da dariya
"wlh tlh Akhie kai baqine"
ta qarashe tana saurin miqewa daga kan kujerarta don dama kusadashi take

sakin bakinshi Aymaan yayi yana kallonta itakuma takoma bayansu ummy dake dariya tana dariyar itama

"kutt... nizakiba kunya muna team daya? lallai kin qoshi" yafada yana kwafa ya sake daukar mug din shayinshi

"yo ai gaskiya ne Akhie, kasan ni bana qarya" inji batool tana dariya

kada kai kawai Aymaan yayi bece mata komai ba ya cigaba dacin abincinshi


kujerar kusada ummy batool taja ta zauna taqi komawa kusadashi suka cigaba da breakfast din nasu cikin walwala, wannan karon murmushi kwance a fuskar zee dakejin duk wata damuwarta data tashi daita ta yaye

ganin hakan yasa Aymaan Dan murmusawa don dama burinshi kenan, kullum burinshi farincikinta, ya tsani ya ganta cikin damuwa ko yayane.


ahaka suka gama breakfast din su zee suka tashi don wucewa school

"ukhtie baki gayamin tsarabar dazanyi miki ba Idan zan dawo" inji aymaan yana kallon zee

kafin zee tayi magana batool tayi saurin ca6ewa da
"ka siyamin komai nacan dangin maqulashe na gargajiya irinsu magarya, goruba, taura, jawuwa, jan madam, kanya..."

"wa ake tambaya wake bada amsa? kinji na ambaci sunanki ne?" Aymaan ya katseta yana mata kallon up & down

kumbura fuska tayi tana kallon ummy

"nida kika kira baqi nikuma kikeso nayimiki tsaraba?lallai bakida hankali" yafada yana binta da mugun kallo

qara kumbura fuska tayi kamar zatayi kuka

"yauwa ukhtie inajinki" ya maida hankalinshi kan zee dake qumshe dariyarta

"nidai babu komai yaya, kawai fatana Allah yakaiku lafiya ya maidoku lafiya akuma gaidamun su mummy sosai ace nayi kewarsu sosai"

"kenan bakison tsarabar komai?"

girgiza kai tayi kawai

"to ni Idan nayimiki don karan kaina fa?"

murmushi zee tayi
"it ok, xanji dadi sosai"


murmushi shima aymaan yayi yadan kauda kai saikuma yasake kallonta
"to Shikenan, zan miki tsaraba, wadda bazaki ta6a mantawa ba"

Dan daga gira daya tayi
"dagaske?"

kadamata kai yayi alamun eh

"shukran so much"

kada mata kai kawai yayi ya kauda kai yacigaba da cin abincinshi dabe cinye ba

juyawa zee tayi tayima ummy sallama sannan tasake yima Aymaan bankwana tanufi kofa

batool daketa kumbure kumburenta itama tayima ummy sallama sannan ta kalli Aymaan da hankalinshi kekan abincinshi tace
"to nima Akhie Allah yakiyaye yakaiku lfy amma karka manta harda atamfofi irin nacan da shaddoji da kayan kad'i irinsu kuka, ku6ewa, ya6do, daddawa..."

duqewa tayi saboda jifanta dayayi da spoon din hannunshi tana dariya

"wlh yarinyar nan ta rainani nizakiba sautun daddawa da kuka?"


gwalo tayimashi sannan tanufi kofa tana cigaba dayimashi dariya suka fice itada zee.


binsu da kallo Aymaan da ummy din sukayi harsuka fice daga falon sannan kowanne ya janye idanunshi yana sauke Ajiyar zuciya

ummy ce tadago takalli Aymaan tace
"kana ganin komai zaitafi smoothly?"

qurawa plate din gabanshi idanu aymaan yayi sannan yadan sauke Ajiyar zuciya sannan yadago yakalli Ummin

"insha Allah ummy, just pray for us"

"to Allah yabada sa'a yakuma taimaka"

"Amin ya rabb"


haka suka cigaba da karinsu suna labari jefi jefi duk akan tafiyar.


sai wajajen 11am Ahmad yaduro gidan cikin shirinshi na tafiya

saida suka gaisa da ummy sannan ya haura sama dakin Aymaan


sai wajajen 11:30am suka sauko kowanne cikin shirin tafiya kowanne goye da jakkar goyawa wanda ke daukeda duk abubbuwansu na amfani.


saida sukayi bankwana sosai da ummy tayimusu addu'o'in tsari sannan suka bar gidan cikin motar da Ahmad yazo daita wanda drivern gidansu ke jansu.


lokacin dasuka isa airport din saura mintuna shabiyar jirginsu yatashi

nan suka shiga yin duk wani tantancewar daya kamata suyi kafin lokacin tashin jirgin.


cikin qanqanin lokaci suka gama all neccesary things dazasuyi suka bi ayarin passengers masu shiga jirgi suma suka shiga suka zazzauna a seats dinsu dake.kusada juna.


cikin qanqanin lokaci aka fara sanarwar tashin jirgin nan kowa duk ya daddaura belt din cikin few minutes jirgin ya daga ya lula sararin samaniya


***


Wunin ranar a school cikin walwala zee tayishi, bata yarda ko kadan taba tunani damar yin tasiri a zuciyarta ba.

yau bataje library ba kamar yadda tasaba saboda gudun sake haduwa da Mussadiq dukda tasan ba qaramin aikinshi bane ba yabiyota har class din dayake Idan yaga dama.


sai bayan asr sannan suka fito daga school din da ita da batool suka nufi motarsu suka shiga suka fice daga school din.


fitarsu keda wuya shima yaba drivernshi umarnin sutafi, drivern yataka motar yaja suma suka fice daga school din.


💙💙💙💙💙💙💙💙💙💙


sai da marece liss jirginsu Aymaan ya sauka a babban filin jirgin sama na babbar birnin tarrayar Nigeria wato Abuja.


cikin qanqanin lokaci suka fito suka gama clearing din komai sannan suka kamo hanya suka nufi hanyar fita daga airport din


ganin ba'a dade da gama magrib ba yasasu fara tsayawa a massalacin dasuka fara cin karo dashi sukayi sallah sannan suka fito neman abin hawa.


basu wani jimaba suka samu adaidaita sahu suka hau suna gayamashi hotel din daxai kaisu


tafiyar mintuna shabiyar sukayi suka isa hotel din suka sauko suka biya mai adaidaitan haqqinshi sannan suka shige cikin hotel din.


cikin qanqanin lokaci suka kama daki suka biya sannan aka rakasu dakin

a lokacin har wasu massalattan sunfara sallar isha'i hakan yasasu sake fitowa sukaje sukayi sallar tasu a massalacin hotel din


sai bayan sun dawo sun nutsu har sunci abinci sannan suka doddora sabbin layyukansu dasuka siya.


nan Ahmad yajawo laptop yafara aikin gabanshi shikuma Aymaan ya shigewarshi toilet.


sai bayan awa daya aka turomusu sms na zasu iya amfani da layyukansu

nan take suka fara ma mutanen Dubai domin sanardasu isowarsu Nigeria lfy

sun dade suna waya dasu inda saida suka farayi da iyayen Ahmad sannan suka kirasu ummy suma daga nan suka maida akalar kiran wajensu Daddy(mahaifan zee) dake katsina don sanardasu isarsu don suma sunsan da tafiyar don dasun gama Abinda yakawosu zasu biya ta katsina din kafin sukoma Dubai


suma sundan jima suna gaisawa dasu sannan sukayi sallama.

daga haka Aymaan yawuce yayi shirin kwanciya yayi kwanciyarshi yabar Ahmad nan daya cigaba da aikin dake gabanshi.

yana jin lokacin daya kira abokin aikinshi nanan Abuja din suna tattaunawa akan abinda yakawosu dakuma fitarsu ta gobe.

maida idanunshi Aymaan yayi ya rufe kamar mai barci amma ba barcin yakeba, banda saqe saqe babu abinda ke kai komo a kwalwarshi.

ahakan har Ahmad yagama duk abinda yake shima yazo ya kwanta

ya dade sosai idonshi biyu kafin yasamu can cikin dare barci ya sadado shima ya daukeshi.


*WASHEGARI*


Sai bayan sallar zuhr suka fita daga hotel din.

dama abokin aikin Ahmad ne yazo daukarsu don haka gabadayansu suka nufi motar da mutumin yazo daita


duk sanye suke cikin qannanun kaya sunyi kyau sosai mussanman aymaan dayayi shigar all white wanda yayi mugun yimashi kyau sosai saidai fuskarnan tashi babu wannan walwalar da fara'ar da aka saba ganinta dashi.

kallo daya zakamashi kasan cewa yau baya cikin good mood kwata2

ko a motama Ahmad da usman (abokin aikinshi) kawai ke labarinsu shikau hankalinshi nakan wayar hannunshi dayake daddanawa tunda suka shiga motar


sunyi tafiyar kusan mintuna 30 sannan suka iso inda zasu.

jin tsayuwar motar yasa Aymaan sanin sun iso

duk fiffitowa sukayi banda Aymaan da saida ya mula yasha iska sannan ya bude kofar 6angarenshi yafito.

Ahmad tun jiya yake lura da take takenshi dakuma yadda yake wani shashan qamshi amma be kulashi ba don yasan abinda ke damunshi kuma yasan qiris yake jira ya burkuce musu shiyasa yake taka tsantsan yana lalla6awa harsuyi abinda ya kawosu sutafi.


maida kofar aymaan yayi ya rufe bayan yafito sannan yafara bin harabar wurin dasuke da kallo

wurin babban industry ne ya hadu daidai misali don koina is neat and well trimmed.

akwai mutane jefi jefi a harabar wasu tsaye wasu kuma na kaiwa da kawowa.

waya usman yazaro yayi kira, bayan yagama yajuyo kansu Ahmad yace suje.

gaba yayi suma suka maramashi baya har suka shiga cikin building din.


suna tafe Ahmad da usman na magana yayinda Aymaan dake bayansu yayi tsit sai bin wurare yake da kallo cikin nazari.

Ahaka har suka qaraso reception din.

anan suka hadu da managern wajen wanda yayi musu tarba mai kyau wanda da alamu akwai sannaya a tsakaninshi da usman

anan usman ya gabatar mashi da Ahmad da Aymaan suka gaisa inda har lokacin babu walwala tareda Aymaan.

iso managern yayi musu zuwa wani qayyataccen waiting room yakuma sa aka kawomasu abu mai sanyi sannan ya sanardasu sudanyi haquri ogan na studio yanzu amma insha Allah yakusan fitowa.

da hakan yafito yabarsu wajen don jiran isowar ogan.

tunda suka zauna Aymaan ya jingina da jikin kujera ya rungume hannayenshi a qirji ya sauke idanunshi qasa.

ko kallon kayan drinks din gabansu beyi ba bare yayi marmarin ta6a daya daga ciki kawai dai zaune yake yana kalkada kaffafunshi yana saqe saqen da shikadai yasansu.


sunyi 20mins ahakan sannan suka farajin alamun ana tunkaro dakin dasuke

su Ahmad daketa labarinsu daya shafi business tuni suka nutsu suka maida dukkan hankalinsu ga kofar shigowa wajen yayinda Aymaan ko motsawa beyiba daga position dayake ba.

qarar budewar kofar yaji sannan yaji sallamar manager din daya kawosu nan din, can saiya sake jin sallamar cikin wata very cool calm voice.

bugun zuciyarshi ce tafara sauya salo lokacin da wannan muryar ta dira kunnuwanshi.

su Ahmad ne suka samu damar amsa sallamar yayinda shikuma ahankali yafara dago idanunshi daga qasan dasuke kallo


cikin two pair of oily eyes dinshi ya saukesu wanda yaqara yin daidai da motsawar zuciya...✍�


Ummin fasihu🧚🏻‍♀�
8/2/21, 9:43 PM - Buhainat😝: *🙍🏻‍♂️DEEN🙍🏻‍♂�*


*077*


Kafeshi yayi da kallo shima Deen din ya tsinci kanshi da tsareshi da nashi idanun.


"bismillah, gasunan tundaxu suke zaman jiranka" maganar Habeeb ta dawo da Deen daga duniyar kallon Aymaan

janye idanunshi yayi akanshi ya kalli kingin mutanen dakin yana sakarmasu kyakyawan murmushinshi yana ida qarasowa dakin.

Ahmad tunda ya dora idanunshi shima akan Deen yayi suman zaune, be ta6a sanin kammanin nasu yakai hakaba, ba don yasani ba da yana iya rantsewa cewa wannan Mussadiq ne.

"barkanku da warhaka, sorry for keeping you waiting" yafada calmly cikin friendly tone yana miqamusu hannu don suyi musabaha

da usman dake farko suka fara musabahar sai Ahmad dayayi iya bakin qoqarinshi wajen daidaita nutsuwarshi yana murmushin yaqe sannan ya miqama Aymaan da har lokacin idanunshi bebar fuskar Deen ba


ganin be amshi hannun ba saima kallonshi daya tsaya yanayi yasa shima Deen cigaba da kallonshi trying to read his expression don shima tun kallon farko dayayiwa mutumin yakejin kamar akwai wani abu attatare dashi.

harya fara fidda rai da zai amshi hannun yafara shawarar saukewa Aymaan ya dago nashi hannun yabashi sukayi musabahar wanda ko second daya basuyi ba kowanne ya janye nashi hannun

iso Deen yayi musu akan sutaso sutafi office dinshi yadda zasu tattauna dakyau.

duk miqewa sukayi yayi gaba batareda ya qara kallon gefen aymaan da ko motsawa daga zaunen dayake beyiba yayi hanyar fita daga dakin.

Ahmad ne ya dafa kafadar Aymaan ganin beda alamun tashi din

dagowa Aymaan yayi yana kallon Ahmad da wani irin expression a idanunshi, fuskar roqo Ahmad yayimashi yana mashi nuni daya taso please.

dakyar yasamu yataso din yana cije lip dinshi na qasa.

suma hanyar fita sukayi Don kingin harsun fita.

basuyi wata doguwar Tafiya ba suka qarasa office din Deen din

duk yimasu iso managern yayi ya gwagwadamasu wurin zama duk suka zauna a kujerun dake facing table din daya raba tsakaninsu da Deen dake zaune yana facing dinsu ta dayan 6angaren.


tunda Aymaan ya zauna yayi crossing kaffafunshi ya sauke kanshi qasa yana danne2 a waya be qara dagowa ba

a bangaren su Deen kuma gaisawa suka sakeyi dasu Ahmad sosai sannan Habeeb yafara magana

"wannan shine wanda nacema zaizo yau dashi da abokanshi, sunanshi usman ya rako abokanshi ne akan wani aiki amma gashi nan ai, waqa abakin mai ita tafi dadi"

duk murmushi sukayi sannan usman ya amsa da
"hakane Mallam Habeeb, ni sunana usman mahmud wadannan abokainane kuma yan uwana da Ahmad da Aymaan, su yan Nigeria ne amma suna zaune ne a Dubai yanzu hakan ma aiki ne yakawosu nan din, wannan Ahmad din shi yayimin magana tun kafin suzo akan zasu shigo 9ja kuma xaiso haduwa da shahararren mawaqinnan balarabe don fan dinka ne sosai dukda yanacan amma yana yinka kuma yana sauraron waqoqinka sosai, kasan shahara babu abinda bata kawowa, kai kananan zaune waje daya amma bakasan iyakar inda ka zaga ba.
ganin yadda yake kwadayin ganinka yasa nikuma nace insha allah zanyi qoqari na hadaku... to Mallam Ahmad yau dai gaka ga balarabe face-to-face" yaqarashe yana kallon Ahmad daketa murmushi tunda yafara maganar

"aikaudai Dan uwa, yau gani ga wanda nadade ina mafarkin gani a zahiri.

gaskiya naji dadi sosai don I never thought ganinka will be this easy for me, ban ta6a tunanin zanganka anan kusa ba koda daga nesa ne bare ace har nasamu damar magana dakai, gaskiya am very happy today and ina farincikin gayamaka cewa.muna yinka sosai, more more basira insha Allah"


Deen dake murmushi sosai yace
"Thanks so much bro, am glad and happy I can statify your expectations without my knowledge, Allah praise be to Allah dayabani damar gamsar daku da guntun baiwar dayabani, allah yasaka da alhairi yakuma cigaba dabani ikon cigaba da gamsardaku da aikina"


"Amin ya allah, ai Mr balarabe sunanka yayi trending inda kwata2 baka tunani kuma bakomai yaja hakan ba sai irin yadda kake captivating zuciyar mutane da salon waqarka, ga sanya nutsuwa ga sanya shauqi don duk daskarewar zuciyar mutum dayaji waqarka saita motsa wlh, allah dai yaqara basira yasa afi haka" inji usman


"Amin amin, Allah yaqara daukaka yaqara zaqin murya da kaifin kwalwa.."

tashin da Aymaan yayi yasa Ahmad Dan yin shiru

wayace kare a kunnenshi hannu daya a aljihu

"hello..." daga haka yawuce hanyar kofar office din yafice


Duk binshi da kallo sukayi harda Deen harya ida ficewa daga office din

maido dubansu sukayi kan Deen da haryanzu idanunshi nakan kofar office din

yar dariya Ahmad yayi yace
"workaholic kenan, haka yake kodayaushe cikin aiki mutum kamar agogo"

duk dariya sukayi banda Deen dayayi murmushi kawai


"yes as I was saying Idan babu damuwa nima zanso adan yimin waqa ace yau gani da waqar actor na kuma ni akaiwa, gaskiya I'll be very happy Idan akayi granting wannan wish din nawa"

murmushi Deen yayi yace
"babu damuwa insha allah, hakan bazai gagara ba saidai wane iri kakeso? just waqar koko harda performing?"

dan wara idanu ahmad yayi
"wow performing? sounds nice. wane procedure akebi to Idan mutum nason ayimashi performing din?"


"gaskiya Idan performing ne ana sanarwane dawuri misali a month to the date yadda za'a riga akamamaka ranar"


"hakan yayi, insha Allah zamu dawo don performing din very soon amma yanzu kasancewar zuwa mukayi kuma ba dadewa zamuyi ba inajin waqar kadai ta wadatar"

"alright to wace iri kakeso?"


"waqar mahaifiya, umma ta nakeso ka waqe" yafada yana washe baki

duk murmushi mai sauti sukayi

"masha Allah, Shikenan insha allah yanzu Habeeb kar6i bayyanan komai da komai, yaushe kukeson waqar?"

"eto, kaga bawani dadewa zamuyi anan dinba kawai wani aiki ne yakawomu zamuyi mu juya, insha allah jibi mukeson juyawa Idan Allah yakaimu"

"alright, jibi da yaushe zaku tafi?"

"jirgin marece zamubi insha Allah"

"to kuna iya dawowa jibin dasafe insha Allah everything will be ready"

cikin jindadi Ahmad yace
"kai masha allah, mungode kwarai allah ya qara daukaka"

da Amin ya amsa yana murmushi sannan Habeeb yashiga yin abinda Deen din yasashi.


cikin qanqanin lokaci suka gama clearing komai suka dan qara ta6a fira cikin raha da barkwanci inda anan saida Ahmad yayi ya dauki hoton Deen shikadai sannan kuma yabada akayimusu taredashi.

lokacin da zasu tafi har waje saida Deen da Habeeb suka rakosu saboda dan sabo daya shiga tsakaninsu adan wannan lokacin suna tafe suna fira.

tundaga nesa suka hango Aymaan zaune kan wani benci dake karkashin wata bishiya dake parking space din kanshi sadde yana latse latsenshi a waya.

har suka qaraso dan nesa da wajen be dagoba don bema nuna alamun yasan dasuba dukda tun fitowarsu yagansu

tsayawa sukayi adan nesa da wurin sukayi bankwana cikin aminci sannan Deen ya juya batareda shima ya kalli gefen da Aymaan yakeba yatafi Habeeb na takemashi baya.


saida sukaga wucewarsu sannan suka nufi inda Aymaan yake

"haba aymaan, meye hakan dakayi? you just walk out without even excusing yourself, hakan dakayi is not proper" inji Ahmad

dagowa yayi ya makamashi wani kallo sannan ya tashi yana pocketing wayarshi

"kunga muje, abinda yasa kuka iskeni anan ma don babu car key a hannuna ne" yafada yana wucesu

"aida kabi adaidaita tunda garin ba baqonka bane bare ka 6ace" Ahmad yabashi amsa

"I thought as much saidai earliness dinku na minti biyar ya hana hakan, dakun qara minti biyar aciki da yadda kace din za'ayi" Aymaan yabashi amsa

Ahmad zai sake magana usman yadan dafa kafadarshi yana murmushi sannan yajuya wajen Aymaan dake qoqarin chanza akalar tafiyarshi daga motar zuwa hanyar waje yace
"kyaleshi dude, muje please wani lokacin sai ya dinga abu gadaiyanan"

da hakan yabude motar ya budewa Aymaan din dake cika yana batsewa backseat din.

kamar karya shiga saikuma yashiga don bazaiso qara saida halinba mussanmman ga usman dayake baqo awajenshi sannan suma duk suka shiga gidan gaba usman ya tada motar suka fice daga industry din


***


yauma sai wajajen bayan asr suka fito daga school din suna tafe suna firarsu suka nufi parking space inda sukayi parking din motarsu


tundaga nesa suka hangeshi zaune bisa booth din danqareriyar motarshi baqa

sanye yake cikin shigar suit dinshi as usual saidai babu coat din sama acikinshi sai farar spotless shirt da guntuwar jacket dinta dake sama.

idanunshi sanye da shade as usual ya sunkuyar dakai yana danne danne a wayar hannunshi.

kallon juna batool da zee sukayi sannan suka sake kallonshi don yau ma kamar kwanaki parking yayi yadda yaga dama don yauma yaga taremusu motarsu dole saiya janye tashi sannan zasu samu damar fiddo tasu.

rolling idanu zee tayi cikin qosawa, meyasa wannan mutumin baxai fita rayuwarsu ba hakanan?

"ai shikenan, sai kije ki fiddomana motar" tafada ma batool tana juyar da kai gefe guda

"wa? ai wannan aikinki ne tunda naga kunfi kusa" batool tabata amsa

"ai shikenan saimu nemi abin hawa mutafi don yau babu wanda zai 6atamin rai abanza" inji zee tana juyawa zata nufi hanyar gate

yar dariya batool tayi tace
"good idea, ashe kema yanzu kingane fada da aljani babu riba" tafada tana binta

harara zee ta gallamata ta gefen ido suka cigaba da tafiyarsu batareda sunqara bi takan parking space din ba


"Ummie!!" sukaji an kwalamasu kira daga bayansu


"Ummie! sis batool!"


atare suka juyo saikuma suka wara idanunsu atare

"Aysha!!" sukayi exclaiming atare sannan suma suka nufeta cikin sauri da murna


a tsakiyar hanya suka hadu su ukun suka rungume juna suna tsuwar murna


saida suka gama haukarsu sannan suka saki juna suna dariya

"yau kece a school dinmu?" inji zee tana riqe ha6a

harara Aysha ta gallamata tace
"aike kin manta da mutane ko kiran mutane bakiyi yanzu bare akaiga kin nemi ganinsu"


dariya zee tayi tace
"haba daughter, wlh kina raina"


"banga alama ba ai, yanzu ma badon na takurama Akhie yakawoniba da haka za'aita Tafiya"


"ai haka take wannan matar batason zumunci ko kadan" inj batool

"ai harda ke, kema yaushe rabon da ki kirani?" inji Aysha tana harararta itama


gwalo zee tayima batool data turo baki tana cewa
"hhh yarinya wayace ana shiga tsakanin uwa da 'ya?"

"yasu Ummie? ya school?" inji zee tana kallon Aysha

"school babu dadi, haryanzu nakasa sabawa da rashinki" tafada tana Dan kwa6e fuska

itama zee kwa6e fuska tayi tace
"ayyah same here"

"bawani same here keda baki damu da mutane ba?"

"haba Ayush dita? nina isa"

Aysha zatayi magana wayarta tayi Ringing

zaro wayar tayi taduba saikuma tajuya takalli saitin parking space

suma bin inda tabi da kallo sukayi sukaga Mussadiq ne wanda haryanzu ko dagowa beyiba daga danne dannen dayake

Juyowa Aysha tayi ta kallesu tace
"bari kuga natafi, yaya yafara min warning dama dakyar nasamu yakawoni don saida Ummie ma tasa baki, naji dadin ganinku sosai"


"muma haka dear, ki gaidamin Ummie insha allah muma zamu shigo" inji zee

Dan harararta tayi tace
"kamar gaske"

dariya sukayi zee tace
"allah dagaske"

"to Allah yasa, a gaidamin kowa da kowa please"

"insha Allah saimunyi waya"


Juyawa tayi dasauri tanufi motar don har Mussadiq duro daga booth din motar.

wucewa yayi gefen driver ya bude ya shige itakuma Aysha ta zagaya dagudu

bude dayan 6angaren tayi itama tashiga wanda yayi daidai da tashin motar

ganin hakan yasa zee kauda kai daga kallon wajen tana kallon gefe

zuwa motar tayi ta wucesu aguje tana barmasu qura

bin motar sukayi da kallo harta fice daga school din suka ta6e baki atare

"Dan wahala" inji batool

"na bugawa a news" zee ta amsa


Juyawa sukayi suka koma parking space din suka shiga motarsu suma suka fice daga school din.


***


Aymaan qarasa wunin ranar yayi yana hidindimunshi shikadai duk yadda Ahmad yaso yasaki ranshi qiyawa yayi dole ya qyaleshi

yasan meke damunshi kuma beyi mammakin yadda yayi reacting ba don koshine hakan zaiyi

kwata2 Deen yazomusu a yadda basuyi tunani ba, ganinshi a zahiri yafi jinshi don kama kawai suke da Mussadiq amma Aura dinsu yasha banban

duk yadda yake ganin Mussadiq da qwarjini Deen yafishi, yafishi komai kama daga qwarjini, haiba da wata iriyar baiwa tashiga rai farat daya.


a kallo daya yagane dalilin dayasa zee ta haukace a soyayyarshi don he worth being crazy for.


kwanansu biyu agarin a cikon na uku wato ranar dazasu tafi suka koma industry din saidai wannan karon Aymaan be bisuba daga Ahmad sai usman.

anan suka tadda har an kammala masu aikinsu kamar yadda aka alqawartamusu kuma aikin yayimusu sosai har hakan yasa Ahmad yakasa 6oye farincikinshi.

anan Ahmad kecemashi insha Allah zaiso yayimusu performing watarana shikuma Deen yace Allah yakaisu lokacin

saida Ahmad duk yatura latest waqoqinshi da videos dinshi sannan sukayi bankwana suka tafi.


Qarfe 5:30pm taimasu a airport inda zasu hau jirgin katsina wanda zai tashi 6:00pm


cikin qanqanin lokaci suka gama komai suka shiga jirgin 6 dot jirgin yadaga zuwa garin katsina ta dikko dakin kara


*KATSINA*


Lokacin da suka sauka a filin jirgin sama dake katsina har duhu yafara don ba'a dade da gama sallar magrib ba.


lokacin har drivern da daddy yaturo don daukarsu ya dade da isowa.

basusha wahala ba wajen ganin juna nan ya tayasu zuba kayansu a booth suka shiga motar yaja suka fice daga airport din.


Tarba sosai Mummy da Daddy sukayi musu don rasa inda zasu sasu sukayi don murna.

saida suka fita sukayo sallah tareda Daddy sannan suka dawo

cikin qanqanin lokaci aka cikamasu gaba da girke girke kala kala.


nan suka zauna suna kwasan girkin suna firar yaushe gamo Mummy nama Aymaan tsiya akan Allah yayi yau shine a 9ja.


saida suka gama cin abincin sannan sukasa aka kaisu part dinsu da aka riga aka gyareshi tsaff sai zuba qamshi yake.


dayake duk agajiye suke cikin qanqanin lokaci sukayi shirin barci kowanne yabi lafiyar gado.


*WASHEGARI*


Yau takama Saturday weekend shiyasa Daddy befita ba hakan yabashi damar zama dasu Aymaan sosai suna firar dabasu idaba ajiya.


suna cikin haka Mummy itama tazo tayi joining dinsu suka cigaba da firarsu gwanin sha'awa.

acikin firar ne aka kama topic din zee inda aka zarce zuwa rabuwarsu da Deen wanda yayi sanaddiyar barinta qasar.

Daddy ne kebada labarin yana fadin yadda tunfarko yaqi yarda da soyayyarsu saboda irin haka amma suka nace da ita da Mummy harya haqura sai gashi Abinda yake gudu yafaru


Aymaan ne ya gyara zama yana kallon Daddy yace
"to amma Daddy kai aganinka meyasa yatafi din? wannan tafiyar tashi kwatsam batareda wata hujja ba akwai alamun tambaya, gashi ance shima yana sonta"

Mummy ce tace
"nima haryanzu abinda ke dauremin kai kenan, dole akwai dalili wanda shine duk bamusaniba"

"wane dalili kuke nema bayan wanda yanuna na bayasonta? wayasani ko dama yaudararta yake ba ita yakeso ba dukiyarta yakeso shiyasa dayaga alamun bazaici ribaba ya yanke shawarar rabuwa daita don yaga a take takena bazan ta6a bari ya cutar da shalele ba"

jinjina kai Ahmad da Aymaan sukayi cikin nazari can Ahmad yace
"amma ni aganina Idan saboda yaudararta kawai yake baya sonta yana iya fitomata a mutum yace bayayi su rabu basai abin yakai ga barin gari ba, kufa duba kugani ace kawai don yasan bazaiyi nasara ba wurin yaudararta yaci kudinta saiya tattara yabar gari? yabar mazauninshi yabar karatunshi? yadda naji ance wai yana level na qarshe a school anya hakan yakai dalilin dazaisa yayi watsi da shekarun daya 6ata yana karatu saboda wannan dalilin? gaskiya akwai wani abin bayan wannan"

Mummy tace
"nima abinda nake tunani kenan, ace ka 6ata tsawon shekaru da tsabar kudade bayan ba wani hali ke garesu ba ace yabar karatun saboda dalilin da baikai yakawo ba?"


"To ku aganinku mezaija hakan?" inji Daddy yana rungume hannu a qirji

"ba kunce sai ranar introduction yabar garin ba? anya dalilin bayada alaqa da introduction din?"

"how?" inji Mummy


"meyasa saida maganar introduction tatashi sannan yagudu? ko baya sonta din yana iya Bari ayi introduction din tunda introduction din ba daurin aure bane kosa biki? then meyasa akan hakan kawai zai yanke wannan hukuncin?"

shiru dakin duk ya dauka kowa da alamun yayi zurfi a tunani

"waye mahaifinshi?" Aymaan ya jefo masu tambayar daga sama


"cewa akayi daga mahaifinshi har mahaifiyarshi rasuwa sukayi tun yana qarami" inji Mummy

"waye mahaifinshi yasha banban da mahaifinshi na raye ko amace? koda mahaifinshi ya mutu ai yakamata asan kowaye shi ko, meye sunanshi? waye danginshi kuma ina yake zaune kafin ya rasu din hakama mahaifiyarshi"

"to nidai duk lokacin dana tambaya haka Zainab kecemin don itama Idan ta tambayeshi haka yake fadamata wai shi kanshi besansu ba kawai wannan kakar tashi ya bude ido yasani, kaga da sunzo introduction din daduk ansan wadannan abubbuwan"


"good, yanzu munfara kamo bakin zaren dalilin dayasa yagudu din, tayiwu akwai Abinda suke 6oyewa gameda asalinshi ne ko kuma bayada wadanda zasu zone kwata2"

duk kada kai sukayi cikin gamsuwa Daddy yace
"no wonder, koda mukaje gidansu bayan tafiyarsu babu wanda yasan kowa nasu, wani neighbour dinsu ma cewa yayi tunda suka dawo unguwar almost 12years babu wani Dan uwa nasu daya ta6a zuwa wajensu" inji Daddy

"good, wannan yayi daidai da dalilin barinsu garin wato rashin asali, yanzu tambayar anan shine waye DEEN?" inji Ahmad


shiru dakin yayi Mummy da Daddy sai kada kai suke cikin mammakin wannan al'amari, tunda suke basu ta6a kawoma ransu wannan tunanin ba

"no wonder, shiyasa tunfarko naji hadin beyimin ba ashe bayada asali? kinga irinta ko maimuna? har abada duk Abinda babba ya hango qaramin kome zai hau bazai hangoshi ba, kinga irinta ko?" inji Daddy


itadai Mummy batace komai ba sai tunane tunanen datake

Deen bashida asali? anya? haka kawai taji bata yarda cewa Deen beda asali ba, beyi kama da marar asali ba.


"Allah ma ya taimaka nakawo shawarar yin introduction din da ahaka za'a tafi yaita yaudararmu bayan beda asali daga qarshe yayimana abinda yai niyya ya gudu don yasan bashida kowa bare ayi tracing dinshi"

haka Daddy yaita banbamin fada shikadai yana qara aibata Deen yana qara dorawa Mummy laifi data goyi bayanshi a lokacin


itadai mummy batace komai ba sai tagumi data buga tayi shiru abubbuwa da dama na kai kawo a kwalwalwarta

suma Aymaan da Ahmad basuce komai ba sai kallon daddyn suke har saida ya gaji don kanshi yayi shiru.

sai a sannan Aymaan ya kalli Ahmad yayimishi ido akan ya fiddo.


wayarshi Ahmad yafiddo yadanyi yan shafe shafenshi sannan yajuyo da screen din saitin Daddy yace
"Daddy kasan wannan?"

amsar wayar Daddy yayi yana qurawa wayar ido saikuma ya wara idanu yace
"ai shine wannan, kalli kobashi bane?" yafada yana gwadawa Mummy

itama wara idanu tayi don hoton Deen ne jikin screen din zaune cikin shigar suit sai baqin glass a idanunshi yadan sunkuyar dakai yana rubutu kan wata takarda

"shine wlh, ina kuka sanshi?" inji Mummy

"shine wa Mummy?" inji Ahmad

"kamal mana, tabbas wannan kamal ne"

"to wannan fa?" inji Ahmad din yana miqomasu wata wayar daban

atare suka leqa wayar nan ma the same person suka gani saidai wannan yana sanye ne cikin manyan kaya na hausawa ga kuma murmushi a fuskarshi sa6anin wancan

"wannan ai duk hotunan mutum daya ne, ina kuka samu wadannan pics din?" inji Daddy


"Daddy a matsayinka na businessman wanda ke harkoki na qasa dana waje nasan kasan wani Dan kasuwa mai suna Mussadiq Al-hassan ko?"

"Mussadiq Al-hassan?"


"Eh the young multi-millionaire na qasar Dubai mai companies din NURUL-HAQQ masu rassa qasashe daban daban?"

"oh, wai Sir Mussadiq Al-hassan? waneDan kasuwa ne besanshi ba duk fadin duniyarnan? nasanshi sosai"


"kenan ka ta6a ganinshi? kasan kammaninshi?"

"A'a gaskiya bansan kammaninshi ba don he's always hideous, kasan manyan yan kasuwa sunansu yafi fuskarsu sanuwa don most of them basu cika bayyana kansu ba, ban ta6a ganinshi ba amma ina fatan watarana naganshi din don inada burin haduwa dashi koda badon muyi business ba Kawai don naganshi nima nasa hakan a record dina...amma meya kawo wannan zancen muna wani Batun daban?" inji Daddy


Dan murmushi Ahmad yayi yace
"saboda wannan shine Mussadiq Al-hassan" yafada yana nuna wayar hannun daddyn


kallon wayar daddy yayi saikuma ya kalleshi
"bangane ba"


shine Aymaan be qara cewa komai ba sai rungume hannu dayayi a qirji yana binsu da ido

"ina nufin wannan shine the famous Sir Mussadiq Al-hassan dakake burin ganin"

qara kallon hoton hannunshi yayi in confusion
"Mussadiq Al-hassan kuma? wannan ai Deen ne"

"A'a, ga Deen can hannun Mummy" yafada yana nuna wayar hannun Mummy

kallon wayar hannun Mummy din sukayi saikuma suka kalli juna

Mummy ce tayi magana wannan karon
"kamar yaya? wannan ai duk mutum dayane"

"A'a wadannan mutane biyu ne living in their different world, wannan shine Mussadiq Al-hassan wanda ahalin yanzu yana can Dubai..wannan kuma Kamaldeen Muhammad wanda maganar damuke yanzu yana nan Nigeria a garin Abuja"

"bangane me kakeson cewa ba, kana nufin wadannan hotunan ba mutum daya bane?" inji Daddy very confused

"yes, mutane biyu ne Daddy"

""but how on earth mutane biyu zasuyi kammanni guda? saidai ko..ko.." kasa idawa Daddy yayi lokacin da wani tunani ya gifta kwalwarshi

"saidai.. ko twins ne?" Mummy ta qarasawa Daddy maganarshi cikin rawar baki

Dan murmushi Ahmad yayi
"yes, ta hakan kawai za'a samu irin haka mummy"

cikin rawar baki Daddy yace
"kenan..kenan Deen twin ne"

"yes Daddy, Deen twin ne, twin din the famous Sir Mussadiq Al-hassan"...✍�


Ummin fasihu🧚🏻‍♀�
8/2/21, 9:43 PM - Buhainat😝: *🙍🏻‍♂️DEEN🙍🏻‍♂�*


*078*


Tsitt falon ya dauka sai kallon kallon da ake bakin Mummy da Daddy sunqirufuwa don mammaki.

can Daddy yayi qarfin halin fizgo muryarshi datayi qaura na wucen gadi

"I..still dont get you, kayimana bayyani yadda yakamata. what are you trying to say?"


Ajiyar zuciya Ahmad ya sauke yadan gyara zama sannan yace
"maganar gaskiya dole kuma abin ya rudaku don muma saida muka shiga rudani a farkon bayyanar wannan al'amari.

Bayan rabuwar Deen da Zainab kun turota tabiyo ummy Dubai don tasamu tayi moving on ta manta da past dinta amma mutum na nashi Allah na nashi, maimakon past din yawuce sai yacigaba daga inda ya tsaya.

dafarko zee tafara recovering daga past dinta saidai ba'a kai koina ba ya dawo mata alokacin da ta hadu dawani Deen din acan..."


Tiryan tiryan Ahmad yashiga basu labarin abubbuwan dasuka faru tundaga haduwar zee da Mussadiq Al-hassan na farko a park zuwa haduwarsu nabiyu a supermarket ya gangaro zuwa lokacin da suka gane masu fuskar Deen din biyu ne zuwa lokacin dasuka samo information akan Mussadiq Al-hassan har suka gane su yan biyu ne, ya gangaro zuwa admitting din zee da akayi school din Aysha Al-hassan don samun information akan 6acewar Deen zuwa yadda Aysha ta warwaremasu yadda Deen din ya 6ace, ya kuma gangaro zuwa bayyanar Deen din wanda yanzu haka shahararren mawaqi ne anan Nigeria, yakuma gayamasu dalilin wannan tafiyar tasu wanda sunyita ne don su hadu da Deen dinne face-to-face ya gangaro da labarin har zuwa yanzu dasuke zaune.


shiru falon ya dauka bayan qarewar wannan rikittacen labarin dayayi kama da tatsuniya

daga Mummy har Daddy babu wanda ya iya motsin kirki don haryanzu shock din labarin begama sakinsu ba.


Ahmad ya cigaba dacewa
"kuyi hqr bamu sanardaku tun farkon faruwar al'amarin ne don kar hankalinku yatashi a lokacin kuma alokacin bamu ida tabbatar da komai ba. yanzu haka munzo Nigeria ne don muyi confirming koshi dinne mukuma san inda yake zaune kuma munada burin sadashi da iyayenshi da yan uwanshi insha Allah"


Mummy batasan sadda tayi bursting in tears ba
"innalillahi waina ilaihi rajiun, wannan wane irin rashin imanine? wane irin rashin tausayine zaisa araba mutum da danginshi tun yana qarami a nisantasu a kawoshi wata uwa duniya? kai Dan Adam abin tsoro ne" tafada tana hawaye sosai

shidai Daddy yakasa cewa komai saidai shima kallo daya zakayi mashi kasan abin ya ta6ashi sosai.

"to meyasa kuka baroshi acan? meyasa baku taho dashi ba kuka maidashi wajen dangin nashi?" inji mummyn still hawaye a idanunta


Dan murmushi Ahmad yayi
"ai Mummy its not that easy, tayaya kawai zamu tunkareshi da wannan maganar off hand? kallon mahaukata ma zai mana, kawai ahankali zamubi komai.

maimakon mutsaya yimusu bayani kawai hadasu ya kamata mufara yi sai bayanin ya biyo baya"


"ta yaya to zaku hadasun?" inj Mummy

"shine muke shawara son yi, hadasu abune mai wuya saboda ba a wuri daya suke ba, dole saidai daya ya tadda daya, ko na Nigeria ya tadda na Dubai din ko na Dubai din yazo Nigeria, amma tayaya? shine babban abinda kecimana tuwo a qwarya"


hanki Mummy tasa tashare fuskarta tana qara jin abin a ranta sannan ta dago ta kallesu

"Zainab tasan da bayyanar Deen din?"

kallon juna Ahmad da Aymaan dayazama kamar baya wajen saboda rashin maganarshi sukayi sannan Ahmad ya maida kallonshi ga Mummyn

"A'a, dama somuke muyi confirming sannan mu sanar daita"

shiru falon yasake dauka kowa da abinda ke kai komo a zuciyarshi

dagowa Daddy yayi for the first time tun bayan bada labarin Ahmad

"yaushe zaku koma Dubai?"

"gobe insha Allah"


tashi tsaye Daddy yayi

"kubari sai jibi yadda muma zamu samu damar hada visar mu"


duk dagowa sukayi suna kallonshi

"yes, muma zamuje Dubai din, tare zamu koma" yana kaiwa nan yawuce


binshi da kallo sukayi harya wuce, sosai farinciki yakama Mummy don dama can tana burin zuwa Dubai din bare yanzu da wannan abin yafaru, she can't wait taga wannan mai kama da Deen din.


Washegari shirye shiryen tafiyarsu suka yini sunayi inda Mummy keta shiko Daddy baka gane yanayinshi don gadai yanan, sosai Mummy ta lura da restlessness dinshi don ko jiya daddare taji yadda yaketa juyi yakasa barci.

saida suka shirya komai tsaff aranar ya kasance wayewar gari kawai suke jira suyita tafiya.


Washegari Qarfe 1 tayimusu a airport kasancewar jirgin Qarfe 2 zasubi.


saida suka gama clearing din komai sukayi sallar zuhr sannan suka shiga jirgin.

cikin Dan qanqanin lokacin aka gama duk abinda ya kamata jirgi ya daga sai Dubai✈️✈️✈️


****


Yau ma kamar kingin yan kwanakinnan ganinshi sukayi zaune bisa booth din motarshi.

yawan zuwanshi a school din yaja mutane dayawa sanin dashi.

kullum Idan sunfito zasu tafi gida saisun ganshi a parking space bisa booth din motarshi yana danne dannen waya saidai tun ranar dayazo da Aysha beqara taremusu mota ba hasalima nesa da motarsu yake parking yanzu.

haka zasuzo sushige motar tasu sufice batareda yako dago ba bare ya kalli gefensu kuma suna fita daga school din shima zai diro daga booth din shima yashige motar yabar school din.


zirga zirganshi a school din yasa yasamu tarin crushes batareda yasaniba don dayazo yanmata zasu fara parade agabanshi suna kai komo saidai shi ko sau daya be ta6a lura da hakan ba shidai kawai dayayi abinda yakawoshi yake ficewa.


yauma ko gefenshi bata kallaba ta zagaya passenger seat tabude tashiga itakuma batool tashiga mazaunin driver don haryanzu zee bata iya mota ba.

tada motar tayi tajata suka fice daga school din.

suna fita school din tasa speed sosai har suka iso wata corner ta yanka suka shiga ciki

dagowa zee tayi ta kalleta cikin ayar tambaya
"meye haka?"

"shii.." inji batool tana tsaida motar sannan tafito ta xagaya ta budewa zee daketa binta da kallo har lokacin.

fitowa zee tayi babu musu batool taja hannunta suka koma farkon corner suka la6e suna leqen waje


"wai meye haka ne?" inji zee again

"shiii kibari idanunki su gayamaki, ki cigaba da kallon gate din school amsarki na can" inji batool tana qara leqawa

itama zee leqawa tayi don ganin Abinda batool din keson tagani daidai nan motar Mussadiq tafito daga school din ta halba kan titi.

saurin maido zee dake leqe haryanzu batool tayi suka maqale a garu har motar tazo tawuce dagudun tsiya

Ajiyar zuciya batool ta sauke tana dafe zuciyarta

"mtcheew, wai menene to? ni banga komai ba" inji zee

"bakiga komai ba? bakiga motarshi datazo tawuce ba?"


"motar wa?"

"Mussadiq mana, dummy" tabata amsa tana wucewa wurin motar tasu

"so? meye a wucewar motar?" inji zee tana dan wara hannuwa

"gwadamaki nayi saboda ke Mussadiq kezuwa tunda gashi kingani muna fitowa ya fito" inji batool data bude kofar mazauninta

tsaki zee taja tana qarasowa itama
"shiyasa zaki wani tsaidamu anan? mtcheew wlh wani lokacin Idan kikayi abu kamar aita jibgarki"

dariya batool tayi tace
"ato, Idan nagayamaki ba yarda zakiyi ba shiyasa na gwadamaki, to wlh is better kinyi warning dinshi yabar zuwa don alamu sun nuna zuwan nan nashi zai iya jawo carryover din mutane dayawa, wlh saikinga yadda yanmata ke crushing akanshi, class dinmu dakinga group of yanmata maganarshi akeyi, yawani zo ya janye hankalin yanmata daga karatu bayan ga exam nata gabatowa da wannan cunkussashiyar fuskarshi"

tsaki zee dahar tashiga motar tasake ja tace
"nidai don Allah muje, kinwani tsaida mutane akan unnecessary thing bayan kinji tundaxu nakecewa yunwa nakeji, mtcheew nima dai zuciya zanyi na iya motarnnan hakanan"

dariya batool tayi tace
"dadai yafi don nima na gaji da janki kiwani tilewa mutane babu amfani"

harararta zee kawai tayi bata tanka mata ba itakuma ta tada motar suka fito daga corner suka halba titi suma.


🤍🤍🤍🤍🤍🤍🤍🤍🤍


Lokacin dasuka dawo gida sai suka tadda ummy nata aiki kamar mai shirin taryar baqi

hakan yasa suka tambayeta tabasu amsa cewa su Aymaan ne ke kan hanya

nan da nan batool ta turo baki gaba

"ya haka? bakya murna da dawowarsu ne?" inji ummy

"dama nasan kinfi sonshi akaina, kawai don yatafi na yan kwanaki ji yadda kike shirye shirye kamar zakiyi tarban wasu sarakuna, dakuma nice nasan bazakiyi wannan zumudin ba" tafada tana qara huro kumatu


kallon up & down ummy tayimata tace
"yo ke dama zumudin dawowar me zanyi miki bayan tafiyar taki hutune agareni da jan maganarki, dalla kauce min ahanya jare" tafada tana wucewa

qara 6ata fuska batool tayi tajuyo ta kalli zee

gwalo zee tayimata tana gwalemata idanu sannan tayi hanyar sama tana dariya


tana jinta tafashe da kukan shagwa6a tayi wucewarta tana murmushi


kaya tafara ragewa tashige toilet ta watsa saboda zafin da akeyi sannan tafito

tunanin dawowarsu Aymaan kawai takeyi, tunda suka tafi sau daya sukayi waya lokacin data kirashi tayimashi ya hanya a washegarin tafiyarsu daga ranar basu qara waya ba sai taji kamar bata kyautaba takamata taqara kiranshi ko sau daya ne

daga kafadu kawai tayi don aikin gama ya gama tunda harsun taho ma

kaya ta chanza tana tunanin wane tsaraba yayi mata, yace zaimata tsarabar dabazata manta ba, to meye shi? nan ma daga kafadu tayi koma menene ai zata.gani Idan sun iso.


saida tagama shiryawar sannan tafito daga dakin tayi joining ummy a kitchen

itama tayi mammakin ganin girke girken data tadda tanayi, lallai ummy naji da Aymaan, wadannan duk na tarbonshi ne?

saida tafara zuba abincin ranarta taja kujera agefe ta zauna tana ci tana taya ummy da fira, saida tagama sannan itama tazo tayi joining Ummin suka cigaba da shirya girkin tana cewa dole batool tayi kishi wannan irin gara da ake shiryawa Aymaan?

murmushi kawai ummy tayi batace komai ba don batason zee tasan da zuwansu Daddy tafison abin yazomata as surprise.


Sai wajajen magrib suka gama dukkan shirye shiryen nasu suka gyagyara koina gida yaqara extra kyalli, harda batool aka kama wajen aikin bayan tagama kumbure kumburenta saidai every now and then saitayi complaining akan irin uban shirin da akeyi na tarbon Aymaan din.


saida suka gama komai sannan suka haura sama don lokacin har anfara kiraye kirayen sallah


sai wajajen 8 Abbu yafita da mota don zuwa taryarsu a airport, tun a lokacin batool tafara kokwanto anya Aymaan dinne kadai don bataga dalilin dazaisa Abbu yaje tarbonshi ba a airport kamar wani baqo, shiru tayi kawai ta cigaba da zuba ido tana jiran dawowarsu.


suna falo suna kallo suna fira motar Abbu tadawo, ummy ce farkon miqewa kamar wadda aka tsikara tayi waje tana lale lale marhabin


nan take suma su zee suka tashi suka takemata baya don ganin kwam


lokacin dasuka fito har motar tayi parking mutanen ciki sunfara fitowa

kamar a mafarki zee ta hango Mummy tafito daga motar

wara manyan idanunta tayi cikin tsananin mammaki tana bude baki lokacin dataga shima Daddy ya zagayo daga dayan 6aren motar

wani irin ihu tasaki sannan taruga dagudu saitinsu

direct Daddy tanufa tana zuwa ta qaleshi ta maqalqaleshi tana cigaba da ihun murnarta.


dariya sosai kowa nawajen keyi ganin yadda take ihu tana tsalle tsalle kamar yar yarinya


raba jikinsu tayi taqara kallon Daddy kamar mai son tantance eh shi dinne saikuma taqara rungumeshi tana cigaba da ihun murna tana kiran sunanshi

sosai farinciki ya mamaye zuciyar Daddy da bakinshi yaqi rufuwa, ganin diyar tashi yake kamar ba ita ba taqara mashi girma kodon sun jima basu hadu bane?

hango Mummy datayi tareda ummy yasata sakin Daddy taruga wajenta itama ta rungumeta tana kiran sunanta cikin tsananin murna


murmushi kawai Mummy tayi tana Dan shafa bayanta don ba qarya itama tayi missing dinta sosai

suna ahaka batool tazo ta ture zee daga jikin Mummy tana cewa
"dalla ya isa hakanan, kinwani bi kin maqalqaleta saikace mummyn takice ke kadai" tafada itama tana rungume mummyn


harararta zee tayi takoma wajen Daddy

"Daddy shine baka gayamin zakuzo ba?"

murmushi Daddy yayi
"ai gashi yanzu kinganmu daga sama ko?"

"i miss you soo much Daddy!"


"miss you more shalele"


"to ya isa hakanan, mushiga ciki, sun kwaso gajiya zaku qaramasu wata gajiyar" inji ummy

gabadaya suka dunguma suka nufi ciki Zainab still a maqale jikin Daddy

binsu da kallo Aymaan da babu wanda yayi ta tashi yayi saiya girgiza kai yanufi booth yafara sauko kayan ciki

muryar batool ce ta katseshi daga abinda yakeyi

"oyoyo Akhie! ashe harda kai aka dawo? wlh nama manta dakai akayi tafiyar sai yanzu dana hangoka"


wata lafiyayyar harara ya makamata ya cigaba da fiddo kayan

"da fatan dai kayomin tsarabobi na don ina ganinka naji babu Abinda nake kwadayi kamar goruba"

daukar jakka daya yayi ya rataya yajawo dayan trolley din yanufota

juyawa tayi saurin yi tanufi cikin gidan dagudu don tasan Idan ya kamata saita gane kurenta

a tsaitsaye a falo batool ta taddasu hakan yasa ta qaraso da sauri jim kadan saiga Aymaan shima yashigo

bude baki ummy tayi sannan tace
"Allah sarki, wlh na manta dakai"

6ata fuska Aymaan yayi yaqaraso dakin yana cewa
"ai dama nasan ba'aji dani"

dariya duk sukayi daidai lokacin zee ta dago suka hada ido da Aymaan

wani kyakyawan murmushi tasakar mashi wanda yakusan melting zuciyarshi, hakanan tayi hasashen qila wannan shine tsarabar dayace zaiyi mata wato ya kawomata su Daddy

shima mayarmata martanin murmushinta yayi yana jin wani sanyin farinciki na ratsa zuciyarshi sannan yayi hanyar sama yana cewa
"to nidai na haye kafin gajiya ta kadani"


Jin hakan yasa Abbu cewa suma su Mummy arakasu masaukinsu su Dan huta kafin sufito cin abinci

su zee suka rakasu har masaukin nasu dayasha gyara sai qamshi yake

badon zee tasoba suka juyo suka barsu don sudanyi freshning up


basu dade ba suka sake dawowa main falo din inda suka dunguma gabadaya sukayi dining inda aka baje kolin girke girken da akayimusu kowa yashiga kwasa

fira ce sosai ta 6arke a tsakanin wadannan families din biyu, hira suke cikin raha da barkwanci, zee haryanzu tana maqale kusada daddynta murmushi yaqi barin fuskarta shima aymaan sosai ake firar dashi don nan take fara'arshi da surutunshi yadawo kamar bashine yakoma wani dunkum ba a Nigeria

sun raba dare sosai atare suna maida yadda akayi saida sukaga barci yafara cin qarfinsu sannan suka haqura kowa yaje ya kwanta.


*WASHEGARI*


Ranar fashin school sukayi sukaqi zuwa sai sukayi qaryar basuda lecture ranar

Haka sukayi zamansu suna aikin bude tsarabobin dasu Mummy sukayi musu suna hira cikin nishadi

Mummy kau dik inda zee ta gifta saita bita da kallocikin sha'awa don taga zee taqara hankali sosai kamar ba itaba ga kuma tausayinta datakeji a qasan zuciyarta don sosai taji dadin yadda ta taimakama Deen batareda tayi la'akari da Abinda yayi mata ba, that's shows tanada good heart.


sai bayan asr Ahmad shima yaduro gidan.

dama jiya tun a airport suka rabu shi yawuce gida kasancewar dare yayi lokacin kuma dama yayimusu alqawarin zai dawo yau don akwai zaman da Daddy keso suyi ayau din.


bayan sun gama gaigaisawa cikin mutunci shima ya zauna aka dasa firar daga inda ta tsaya.


can Daddy yayi gyaran murya wanda ya tattaro hankalin kowa zuwa wajenshi suka zubamashi ido cikin son jin mai zaice

"to Alhamdullilah, muna godewa Allah daya hadamu cikin aminci da qoshin lfy muna kuma roqonshi ya cigaba da wanzarda farinciki da hadin kai atsakaninmu"

"wannan zaman namu yanada.dalili koko ince zuwanmu qasarnan ma gabadaya, wasu acikinku sunsan dalilin wasu kuma basu saniba ammazasu sani very soon inshaAllah.

amma dafarko zanfara nuna jinjina da yabawa ga jajircewar wadannan samarin biyu wajen qoqarinsu na aikin qwarai dasuka sanyo gaba, haqiqa kun cancanci yabo akan jarumta da nargartattun halaye naku kuma muna fatan Allah yabiyaku yasaka maku da alhairinsa"

duk da Amin aka ansa wasu kuma kamar irinsu zee da batool basusan inda zancen yadosa ba haryanzu

"Aymaan da Ahmad sunje Nigeria akan wani aiki, aikin da babu mai iya biyansu sai Allah, kuma muna fatan Allah yabamu nasara yakawo mamu warwarewar wannan al'amari.

sunyi mana bayani, bayanin da nasan kowa anan yasanshi kuma mun gamsu hakan yasama muma muka shirya mukazo nan don ida warware matsalar dukda badamu aka faraba"

zee dai kallon Daddy take very confused don haryanzu takasa gane inda ya dosa

kamar ance ta dago kai sai sukayi ido hudu da Aymaan dake kallonta tundazu

wani guntun murmushi yaimata kawai ya dauke kai

"ga wadanda suka sani dakuma wadanda basu saniba ina farincikin sanardaku bayyanar KAMALDEEN MUHAMMAD wato DEEN"


wani irin bugawa zuciyar zee tayi har saida ta dafe saitin zuciyar tana miqewa tsaye batareda tasaniba

gasping batool tayi tana wara idanu kamar zasu fado cikin tsananin shock


murmushi Daddy yayi yana kallon zee dake tsaye haryanzu hannunta a saitin zuciyarta idanunta a ware tana kallonshi

"yes daughter, Deen is back. Deen yadawo, yana Nigeria. can su Aymaan sukaje kuma sun ganshi sunyi magana dashi"

girgiza kai zee take unbelievabling tanajin komai a mafarki tanason yin magana amma takasa

"eh Zainab, Deen ya bayyana, munsan inda yake. yana Abuja yazama mawaqi, munso mugayamaki tunda wuri amma muka yanke shawarar fara confirming.komai sannan, Deen ya bayyana, na ganshi Aymaan ma ya ganshi, munyi magana dashi"

cigaba da girgiza kai zee tayi don sam zee bata yarda ba, dole wani suka gani, wani mai kamadashi kokuma Mussadiq, yes qila Mussadiq suka gani sukayi tunanin Deen ne

"m..mussadiq ne" tafada cikin wata murya mai rawa sosai

"A'a Zainab, ba Mussadiq bane, Deen ne. look.. duba dakanki kigani" yafada yana fiddo wata laptop yabude

duk zubamashi idanu sukayi in curiosity harya gama yan danne dannenshi ya juyomasu ya ajiye akan stool din kusadashi yayinda image din laptop din yafito tarr kowa na falon nagani


waqa ce ta video


da sajenshi tafara tozali kasancewar gefen fuskarshi akafara haskowa


bugun zuciyarta ne ya ninku lokacin da aka hasko pink lips dinshi wadanda bazata ta6a qin ganesu ba daidai lokacin lips din suka fara motsawa cikin salon waqa


_karki barni.. sahibata_


_karki qini... ki fahimta_


_sai dakee... zani huta_


_zuciyata ga kece ta lalla6o_


_ta amince ki maidata yar dako_


_kinga qaunarki taimun riqon la6o_


_wani reshe ya kama ya jijjigo_


zee batasan sadda takoma kan kujerar data tashi ba jagwab lokacin datayi tozali da full face din Deen din.


_kingani ban iyawa da So haka_


_magani zaki ban don na waraka_


_kinga ya maidani wani sa d'aka_


_yafi qarfina sai yaita ha66aka_


_tunda nabaki raina da zuciyaa!_


_me kikeso nayimiki zan iyaa!_


_yau dake gobe na shaida tunjiyaa_


_kinga nazam kamar marar lafiyaa_


_zuciyata ❤️ tanaimun bugun tara💗_


_gashi nikuma naqi na haqura_

_dukda nasha wuya bani daddara_

_kai bala'i na So🤍 nada takura😭_


_wai ina kika jene masoyiyaa!_


_nayi nemanki naqara tambaya!!_


_har wadansu sunaimini dariya😔_


_ni bazan daina sonki ba kinjiya_

_dukda yasani ban jiyo Dan kira_


_tallafa min kissamini lafiya🙏🏻😭_
(sai dake � hamisu breaker)


Ummin fasihu🧚🏻‍♀�
8/2/21, 9:43 PM - Buhainat😝: *🙍🏻‍♂️DEEN🙍🏻‍♂�*


*079*


*wannan page din nakine takwara, nagode da ziyarar jiya fatan kun koma gida lafiya🥰*


Rufe baki batool tayi da hannunta dake dan 6ari idanunta cikeda kwalla, she's shocked Idan akwai kalmar datafi shock ma tayishi.

she can't believe Deen ne wannan, she can't believe Deen is back!

dauke idanunta tayi daga screen din laptop din takalli saitin zee

haryanzu zaune take inda take motionless, idanunta dasuka sauya launi kafe a screen din babu ko kyaftawa

haka suka cigaba da kallo har waqar taqare

kowa Juyowa yayi yana kallon zee don ganin reaction dinta amma haryanzu tana a yadda take yadda kasan statue

"munfara ganinshi ne ta media, mawaqine sosai wanda ke zamani. yana xaune a Abuja kuma acan yake gudanar da rayuwarshi, wannan tafiyar ma damukayi duk don muganshi ne kuma muga inda yake yadda komai zaizo mana da sauqi" inji Ahmad yana kallon zee

Aymaan kau hannunshi ne rungume a qirji ya sadda kai qasa bakama ganin fuskarshi bare kasan halin dayake ciki.

kuka ne ya kufcema batool tayi saurin rungume zee dake gefenta tanayi ahankali
"Zee Deen is back"tafada cikin rawar murya tana qara qanqame zee dahar yanzu batayi motsiba

ganin batace komai ba yasa batool dan sakinta ta dago ta kalleta ganin still idanunta na saitin laptop saita sa hannu tajuyo fuskar saitinta

"kinji zee, Deen is back, say something. abun farinciki ne right? abun farinciki ne" inji batool tana hawaye sosai

kallonta zee kawai keyi batace komai ba sai gangarowa da hawayen dake maqale a idanunta sukayi

ahankali tasa hannu ta janye hannayen batool daga riqon datayiwa fuskarta ta miqe ahankali

kowa dagowa yayi yana kallonta harda Aymaan da shima idanunshi sun chanza launi sosai


ahankali tafara takawa ta wuce ta nufi stairs

ahankali Aymaan daya lura da yanayin tafiyarta ya miqe idanunshi akanta

takai bakin stairs ta daga kafa kenan zata fara taka stairs din wani wawan jiri ya dibeta tayi baya baya

Aymaan da dama kamar yasan da hakan yayi wuff cikin zafin nama ya qarasa kafin takai qasa ya tarota tafado jikinshi har yana durqushewa akan gwiwa daya

farr farr idanunta keyi kamar mai qoqarin budesu yayinda sukuma suke rufewa

kafe fuskarta Aymaan yayi na kallo yana jin yadda jijjiyoyin kanshi ke tashi rudu rudu

"Zainab.." yafada ahankali kamar a rad'a

"Deen..." itama tafada ahankali daidai lokacin da idanunta suka ida rufewa ruff


tsayawa yayi yana kallon fuskarta kawai batareda ya iya ko motsawaba


kingin yan dakin ne suka qaraso wajen a gigice kowa na kiran sunanta.


dagudu batool tadawo hannunta riqeda bottle water ummy ta amsa aka bude murfin aka shashafamata ruwan a fuska amma shiru

qara yayyafamata sukayi nanma ko motsi batayi ba

ganin hakan yasa Aymaan dake jin kanshi kamar zai rabe gida biyu don sara yunqurawa ya tashi daita a hannunshi

hanyar fita falo yanufa hakan yasa Ahmad saurin ficewa yanufi parking space.


kafin Aymaan ya isa harya bude mashi back seat Aymaan ya sunkuya ya sakata ciki sannan ya nufi gaban motar yana barma su ummy kofar bayan bude don su shiga.


ummy da Mummy ne suka shiga bayan while Aymaan da Ahmad ke gaba sukuma Daddy suka hau dayar motar tareda batool daketa qoqarin dakatar da hawayenta

cikin qanqanin lokaci suka fice daga gidan suka nufi hospital din da Aymaan ke aiki.


babu 6ata lokaci aka kar6eta aka kuma shiga bata taimakon gaggawa

Aymaan baya cikin likitocin dake dubata don suna kaita dakin da aka kwantar daita yafice daga asibitin

su ummy sune suka zauna waje jugum kowa abin duniya ya dameshi

ba'a dade ba akafara kiraye kirayen sallar magrib hakan yasa duk mazan suka wuce massalaci suka bar matan anan.

dawowarsu daga massalacin yayi daidai da fitowar likitocin daga dakin da aka kwantar da zee


saurin qarasawa sukayi suna tambayar yadda ake ciki

ataqaice suka amsamasu yanzu komai yayi daidai amma zasuso ganin mahaifanta personally a office


Abbu da Daddy suka bisu suka wuce office din.


bayani marar dadi likitocin suka basu na hawan jinin zee daya qara tashi ya hau sosai

sunkuma sanar dasu damuwa tayimata yawa har abin na neman ta6amata zuciya

shawarwari suka basu na yadda yakamata su bar barinta tana shiga damuwa domin hakan ba qaramin illa bane agareta yanzu

sannan sukace zasu daurata akan magani wanda zai taimaka mata sosai akan halin datake ciki.


sosai jikinsu yayi sanyi sunajin badadi sosai

Abbu ne yayi qarfin halin tambayarsu halin datake ciki yanzu sukace yanzu sun shawo kan komai don yanzu haka barci take sanaddiyar allurai da akayimata.

sosai suka qara yimasu bayanai akan ciwon zee din da shawarwaru sannan suka shaidamusu mutum daya kawai za'abari yayi jinyarta kingin saidai sukoma gida.

Tare da likitocin suka sake fitowa daga office din suka nufa ward din da aka kwantar da zee din gabadaya

a kwance suka taddata tana sauke numfashin barci ahankali hannunta daure da drip

babu wanda be tausayamata ba a wannan halin don she looks so pale kamar wadda tayi wata tana jinya.

basu dade ba aciki suka fito waje inda anan suka hau shawarar wadda za'a bari wajenta tunda sunce mutum daya suke buqata.

daga qarshe dai ummy aka bari daita kingin duk suka fito zasu gida batool sai 6atarai take don ita da so samune ta zauna.


haka suka bar asibitin cikin nauyin zuciya da jimami kowanne tausayinta danqare a zuciyarshi.


koda suka isa gida kowa shigewa yayi part dinshi kasancewar dare yayi hakan yasa kowa shigewa sashenshi with heavy heart.


batool na zaune bisa sallaya bayan tagama sallolinta wayatafara Ringing

waigawa tayi taga wayar zee dake kan mirror ke Ringing din

tashi tayi ta dauka da niyyar kasheta amma ganin mai kiran yasata dakatawa

kallon wayar ta cigaba dayi tana shawarar ta daga ne koko

ganin zata tsinke yasata saurin dagawa ta kara a kunne

"Aslm Ummie na" inji Aysha daga dayan bangaren

"wslm Ayush" inji batool cikin son daidaita yanayinta

"laa sis batool, ya kike"

"lfy lau, ya kike yasu Ummie?"

"duk lfy, ina mutuniyar?"

Dan shiru batool tayi saikuma tace
"oh tayi barci"

"barci yanzu? this is just to 9"

"ai... qila agajiye takene shiyasa" tafada adan daburce don dama batool bata iya qarya ba


Dan shiru Aysha tayi can tace
"this is not true, gayamin meke faruwa? ina Ummie?"

"ai...ai gaskiya nake.."

"no sis batool kada muyi haka dake, kifadamin gaskiya please, tsakaninki da Allah ina Ummie?"

rolling idanu batool tayi, batajin tana iyayin qarya kuma bayan ta hadata da Allah

Ajiyar zuciya ta sauke
"tana hospital"

"what!!"

"erm... look da sauki sosai kawai dan zazza6ine bawani abu ba"

"innalillahi waina ilaihi rajiun, wane hospital? meya sameta?" tafada hankali tashe

"zazza6ine kawai kuma nace miki dasauqi"

"wane hospital take?"

"A-shifa'u hospital amma nama san gobe za'a sallame... hello? hello?"
ina har an katse kiran

sauke wayar tayi daga kunnenta tana sauke Ajiyar zuciya ahankali.


***


ahankali ya murda handle din kofar ya turo ahankali batareda tayi qara ba sannan yashigo shima

hango ummy yayi saman dayan gadon wanda dama na masu jinya ne tana barci

ida qarasowa yayi dakin idanunshi akanta har saida yazo gabb da gadonta

kafe fuskarta datayi fayau yayi da idanunshi dasukayi ciki ciki

ya dade sosai ahakan kafin ya motsa yabar wajen yanufi yar locker kusada gadonta ya dauki file din dake kai ya bude yashiga going through dinshi

saida yagama sannan ya maida ya ajiye ya gyaramata tafiyar ruwan drip din sannan yajuya yafice daga dakin as quietly as he entered


*WASHEGARI*


Da wuri mutanen gidansu batool suka bar gidan suka nufi hospital don dama jinsu suke kamar akan qaya, saida suka hadama yan asibitin breakfast sannan suka fito suka hade dasu Daddy suka kamo hanya.


lokacin dasuka isa har lokacin zee bata farka ba amma likitocin sun tabbatar musu komai is normal kawai alluran ne basu gama sakinta ba.


haka suka zauna don ana barin zama a ward din suna fira wanda duk ta Deen ce da zee.


suna ahakan har wajajen 11am lokacin harda su Daddy cikin ward din aka kwankwaso kofa

izinin shigowa sukabada don sunyi tunanin Ahmad ne ko Aymaan dukda Aymaan din be dade da fita ba

murda kofar akayi aka turo

Dan wara idanu batool tayi ganin mai shigowar

Aysha ce sanye cikin milk abaya tayi irin shigarsu ta larabawa saidai fuskarnan dauke take da alamar damuwa

mammaki ne yakama batool don ita tama manta dawata wayar dasukayi daita jiya

mammaki be ida kasheta ba saida Aysha tashigo na bayanta ya bayyana

sakin baki tayi cikin tsananin mammaki bama ita kadai ba harda dukkan mutanen dakin

zuciyar Daddy da Mummy sukayi wata iriyar faduwa lokacin da idanunsu sukayi tozali dashi


sanye yake cikin simple qanannun kaya sa6anin suit da aka saba ganinshi dasu saidai wannan baqin tabarau din nashi na gado nanan maqale da idanunshi


kowa na dakin idanunshi nakanshi yayinda shikuma idanunshi ke kanta ya kafeta dasu babu kyaftawa.

gaisuwar Aysha ta dawo dasu daga duniyar kallon Mussadiq duk suka maido hankalinsu kanta

yan dakin suka shiga amsa gaisuwar tata banda Mummy data kafe Aysha itama da kallo tana ganin wasu qanannun qanannun kammaninsu da Deen kama daga coolness din muryarta da dimple dinta na tsakiyar gemu mai lotsawa koda magana take.

kasa janye idanu Mummy tayi akanta tanajin zuciyarta na melting ahankali cikin shauqi, tabbas wadannan jinin Deen ne ko makaho tashafa saiya gane.

cikin damuwa Aysha tawuce gefen zee dake kwance takama hannunta ahankali tana tambayarsu yamai jiki asanyaye kamar mai shirin kuka

cikin sigar kwantar da hankali su ummy ke amsamata cewa da sauqi sosai yanzu ma barci take.

shiru Aysha tayi tana kallon fuskar zee kamar zatayi kuka don ganinta a wannan condition din ba qaramin ta6ata yayi ba.


ahankali shima Mussadiq dake bakin kofa har lokacin qarasowa dakin idanunshi dake lullu6e da tabarau akan sleeping zee

Daddy har wani dauke numfashi yayi saboda Juyowa dayayi ya kalleshi

cikin alamun girmamawa yadan russunar dakai yace
"good morning" ataqaice


dafarko kasa amsawa Daddy yayi saboda rikicewa saikuma yasamu ya fizgo muryarshi dakyar yace
"y..yes, g..good morning"

be qara bi takanshi ba yawuce wajenda su ummy ke zaune suma yashiga gaidasu cikin turancinshi mai slant din Arab

ganin hakan yasa Daddy saurin juyawa daga dakin ya bude kofa yafita duk arikice.


amsawa su ummy da Mummy data kasa janye idanu akanshi sukayi, gani take kamar batun wannan na gabansu ba Deen bane ba qaryane don itadai idanunta Deen yake gwadamata

tambayarsu yayi jikin mai jiki suka amsamashi cikin fara'a

daga nan yaja bakinshi yayi shiru.

batool ce ta dago tadan saci kallonshi sannan ta gaidashi

beko kalli gefenta ba ya amsa ahankali ya cigaba da tsayuwarshi yana kallon zee dake barcinta ahankali


"Aysha meet Mummy, maman zee" inji batool tana nuna Mummy

tare suka kalli Mummy da Aysha da Mussadiq

wara idanu Aysha tayi cikin mammaki
"really?"

kada mata kai batool tayi hakan yasa Aysha wucewa wajen Mummy dasauri tayimata side hug cikin jindadi tana dariya

wani farinciki ya kama Mummy itama tanata murmushi suka shiga sabuwar gaisawa Aysha na tambayarta ya Nigeria kuma yaushe sukaxo Mummy na amsa mata.

ummy ce tadago ta kalli Mussadiq dake tsaye daga nesa dasu kamar wani saqago cikin larabci tace mashi
"ko ka iya cire drip kunga yaqare gashi basu shigo ba"


kallonta yayi saikuma yakalli drip din sannan ahankali ya qarasa wajen batareda yace komai ba

duk binshi da kallo sukayi harya qaraso yafara cire drip din daga cannula din hannun zee

yana cikin hakan idanun zee suka fara motsi arufen dasuke

shidai Mussadiq belura ba don hankalinshi nakan Abinda yakeyi

ahankali tafara bude idanunta dake ganin biji biji harsuka ida budewa tangaram


again wannan fuskar ita taqara yin arba dashi


kafe gefen fuskar tashi tayi da ido babu ko kyaftawa harya gama yajuyo shima ya kalleta suka hada ido.


Shima kasa dauke idanunshi yayi akanta suka kafe juna da idanu na wani lokaci

tunawa dayayi akwai mutane a dakin yasashi saurin janye idanunshi daga kanta yajuya zai wuce

caraff yaji an cafko hannunshi wanda hakan yasashi tsaya cak daga tafiyarshi


Dan shiru yayi sai kuma yafara Juyowa ahankali harya ida Juyowa ya sauke idanunshi cikin nata dake qyallin hawaye

tsayawa yayi yana kallonta kawai batareda ya iya amsar hannunshi daga nata ba.

"Deen..." tafada in whisper...✍�


*kuyi hqr, haryanzu jikin sai a slow, acigaba dasani a du'a🙏🏻*


Ummin fasihu🧚🏻‍♀�
8/2/21, 9:43 PM - Buhainat😝: *🙍🏻‍♂️DEEN🙍🏻‍♂�*


*080*


ahankali yasa hannu yaxare glasses din idanunshi yana kafeta da oily eyes


kamar wadda idanun suka tunama wani abu saitafara releasing hannun nashi ahankali still idanunsu acikin najuna


dukkan mutanen dakin idanunsu na kansu not moving

"waye shi?" yafada ahankali idanunshi anata


kowa wara idanu yayi yana kallonshi in outmost shock

"who is Deen?" yaqara tambaya yana kallon tsakiyar idanunta


bazai manta ba farkon haduwarshi daita Abinda takirashi kenan, wancan haduwar tasu a library ma ta kirashi da hakan and know? waye mai wannan sunan? meyasa Idan ta ambaci sunan saitayi hawaye?

su ummy ko kallonsu suke hankali a mugun tashe kowa yakasa motsi


"tell me, who the hell is he!" yafada da Dan qarfi idanunshi na dan sauya launi


"hey Mr, incase ka manta this is hospital ba filin kasuwanciba"

Juyowa duk sukayi suna kallon Aymaan dake tsaye bakin kofar ward din hannunshi zube a aljihu

wani qololon baqinciki ya tsayawa Mussadiq awuya daga ganinshi hakan yasashi jan guntun tsaki yajuya ya cigaba da kallon zee data maida idanunta ta lumshe

"Ummie..."

"muna buqatar kowa yafita don zamu dubata" yaqara jin muryar Aymaan na katseshi da hakan

su ummy dai kasa cewa komai sukayi sai binsu da kallo dasuke da daddaya

ignoring dinshi Mussadiq yayi ya cigaba da kallon zee
"are you ok?"

"wannan likitan ta zai iya gane hakan wanda hakan zai yiwuwu ne Idan kuka bashi wuri ya dubata, don't ask her if she's ok cos you can only get the answer from her doctor.. that is Me" inji Aymaan yana qarasowa gaban gadon shima


Juyowa Mussadiq yayi yana kallonshi in the eye sternfully shima Aymaan na maida martanin irin kallon yadda kasan zakaru biyu masu shirin afkawa juna


kingin mutanen dakin kallonsu kawai suke sunkasa cewa komai kowa da Abinda ke jeka kadawo a zuciyarshi

Mummy ce tayi qarfin halin tankawa ta hanyar cewa
"it ok, Bari mufita dama tunda ta tashi kamata yayi adubata, batool, daughter kutaso mukoma waje" tafada reffering to Aysha da batool

kamar jira sukayi duk sai suka tashi harda ummy sukayi waje

har lokacin da Aymaan da Mussadiq basu Bar jifan juna da mugun kallon dasukeyi ba can ahankali Mussadiq ya maida shade dinshi yana cije lower lip dinshi sannan shima yajuya yafice daga ward din kamar zai tashi sama


da kallo Aymaan da zee suka bishi harya fita.

Dan tsaki Aymaan yaja sannan yajuyo ya kalli zee, sauke idanunta zee tayi kawai batareda tace komai ba

qarasowa gefen gadon yayi yana kallonta

"ya jikin?" yafada yana zura hannu daya a aljihu idanunshi kanta

kadamashi kai kawai tayi batareda tace komai ba

shima batareda yasake cewa komai ba yashiga dubata

saida yagama sannan yadanja baya yana sauke abin kunnenshi qasa ya dauki file dinta ya ciro pen yafara rubutu

"I hope kinsan condition din heart dinki"

dagowa tayi takalleshi taga hankalinshi ma na kan rubutun dayake

"Idan ta cigaba da samun attack irin wannan am sorry to say komai na iya faruwa... ciki harda bugawarta"

sauke idanunta tayi batace komai ba

"the heart is the strongest organ of the body and at the same time the most fragile organ, ya danganta da yanayin datake ciki at the particular time, saidai akowanne yanayi take yakamata mai ita yasan cewa it's the most important organ that without it no other organcan perform it's function"

daidai nan yadago ya kalleta yaga itama shi take kallo

"without out heart there will be no life, tana bugawane tareda rayuwa, tana tsayawa rayuwa ma zata tsaya.. cak kamar tsayuwar agogo"

still idanunsu nacikin najuna

"mutuwa abuce data zama dole, mutuwa ta sanaddiyar bugawar zuciya is very normal don mutuwa daya ce amma silolinta nada yawa kuma bugawar zuciya na daya daga cikinsu Don haka don zuciyar mutum tabuga yamutu abune da bazai zama na alhini ba... saidai Idan zuciyar tabuga a dalilin Abinda be cancanci bugawar zuciyar ba ko akan wanda be cancanta ba.. za'a kira hakan ne bada tsautsayi ba saidai ganganci"

kallonshi take sosai lokaci guda kuma hawaye suka fara taruwa a large eyes dinta

"zaya mutu ne akan wanda be cancanci hakan ba yabar wadanda suka cancanci hakan, wadanda kullum burinsu farincikinshi, walwala da nishadi. wadanda suke iya sadaukar da komai akanshi tunkafin yazo duniya har yashigo duniyar har wannan lokacin dayake qoqarin wancakalar da rayuwarshi akan wani abin daban.. har abada"

"zaya tafi yabarsu suna baqinciki, baqincikin da wanda yatafi dominshi bazaiyi rabin rabinshi ba saboda shi bashida asara ko yanada ita yar kadan ce batakai ta wadannan mutanen ba... kuma ba kowa bane wadannan mutanen face IYAYE"

"Iyayenka ne zasu iya xama dakai akowane irin yanayi, suyi sharing kowane feeling dakai, farinciki? baqinciki? qunci? damuwa? komai.
kuma duk lalacewarka bazasu ta6a rabuwa dakaiba duk wahalar dakake basu bazasu ta6a yin watsi dakai ba.. duk runtsi"

"wadannan mutanen?.. su ya kamata mutum yafara sawa agabanshi, yafara duba wane hali zasu shiga Idan har ya aikata wani abin bawai mu rufe zuciyarmu ba mu makance qarshe muzo muyi Abinda zaiyi hurting our beloved ones na har abada"


Dan shiru yayi yana kallon yadda hawayenta yaqi tsayawa

Dan murmushi yayi yana sauke idanunshi kan file din dake kan locker haryanzu

"hawaye... wani lokacin rahamane domin yana gangarowane tareda kaso mafi yawa na damuwa amma Idan yayi yawa harya rikida yakoma jini yana zama babban illa.. ga zuciya da gangar jiki gabadaya"


sake dora pen yayi kan file din yasake yan rubuce rubuce sannan ya maida yarufe

dagowa yayi batareda yasake kallonta ba yace
"za'a doraki akan magani, please endeavor to take them at the right time ko don beloved ones dake damuwa da damuwarki"

yana kaiwa nan yajuya yanufi kofa.


binshi da kallo tayi da rinnanun idanunta harya fice

fashewa tayi da wani kuka mai tsuma zuciya tajawo pillon kusada ita ta cusa fuskarta aciki tana cigaba dayi.


***

A bangaren Mussadiq kuwa yana fitowa beko kalli kowa ba yanufi hanyar fita daga wajen.

sosai ranshi ke a 6ace don ba qaramin qonamashi rai Abinda Aymaan yayimashi yayi ba.

harshi zai mashi taqama da matsayinshi? harshi zai koro waje don kawai taqamarshi shi likita?


a stairs suka kusa cin karo da Daddy dake tareda Abbu suma sun karyo kwana

saurin sake dauke numfashi Daddy yayi ganin kamar ya kalloshi ya kauda kai har Mussadiq da 6acin rai bemasa yawani tantancesu ba yayi wucewarshi


sauke numfashi yayi nannauya yana bin bayanshi da kallo sannan yajuyo gun Abbu dake kallonshi

"lafiya daiko?" inji Abbu


"lfy... kawai Idan nadora idanuna akanshi.. sainaga kamar Deen ne" inji Daddy yana qara bin inda Mussadiq yabi da kallo


murmushi Abbu yayi yace
"ai ikon Allahn kenan, wani abin saisun hadu su biyun ankasa tantancesu, Allah dai ya nunamana ranar"

"Amin" inji Daddy sannan suka wuce saman


Direct parking space din asibitin Mussadiq yanufa ya nufi motarshi ya bude yashige ya maido ya rufe

yadda yake abubbuwa da qarfi zaisa kagane har lokacin afusace yake

saida yashiga motar sannan yatuna ashe tare suke da Aysha

dogon tsaki yaja sannan yazaro wayarshi ya lalubo numberta yayi dialing


Ringing biyu aka daga

cikin larabci yafara yimata bala'i kamar zai jawota ta wayar ya daka (nidai bansan meyake cewa ba🙁)

can ya katse kiran yana sake jan wani tsakin yakoma jikin kujerar motar ya rungume hannayenshi a qirji

Idan akwai wanda kebashi haushi duniya to saidai yabiyo bayan Aymaan, yarasa dalilin da tun a haduwarsu nafarko yaji bemashi ba, he just hate him for no reason.


*Deen?*


waye Deen? meyasa zee ke yawan ambatar wannan sunan? meyasa take kuka duk lokacin datake ambatar sunan?

dole yagano kowaye? dole yagano dalilin kukanta akodayaushe akanshi.

rungume hannayenshi yayi yana saqa da warwara shikadai.


sauke wayar tayi daga kunnenta jiki asanyaye sannan ta kalli su Mummy

"erm... I think I have to go" tafada asanyaye

"tun yanzu?" inji batool tana matsowa kusada ita

ahankali ta kada kai cikin damuwa

"Akhie ne... yace nafito.. qila akwai inda zashi" tafada asanyaye


murmushi Mummy tayimata tace
"ayyah, ai mungode qwarai ma. kiyi sauri to karku tsaidashi, batool ki rakata"

da to batool ta amsa tana gyara mayafinta


ajiye ledar hannunta Aysha tayi tace
"Allah ya sawwaqe, insha Allah zan dawo"

"to mungode qwarai ki gaida Ummie qwarai kinji?" inji ummy cikin kulawa

kada kai tayi tana murmushi sannan suka juya tareda batool suka wuce


Tafiya suke basu cewa komai saidai batool ta lura kamar Aysha tana cikin damuwa


"yadai?" inji batool tana kallonta

Dan murmushi kawai Aysha tayi batace komai ba

"karfa kidamu, insha Allah taji sauqi, trust her she's strong, danasan hakan zaki damu da ban gayamaki ba tunfarko"


murmushi Aysha tayi tace
"I want to see her before I leave, kinga fa tafarka yakamata naganta kafin natafi"

Dan shiru batool tayi kamar mai tunani sai can tace
"in that case muje mugani nasan yaya bazai hanaba iyaka yayimana warning yace karmuyi hayaniya"


cikin jindadi Aysha tace
"yes! let's go please"


ida qarasawa bakin ward din zee din sukayi, saboda zumudi Aysha ce agaba

murda handle din tayi tatura tasawo kai daidai lokacin da shima yasawo nashi sai jikake quuum! sun qume.


saurin jabaya tayi tana dafe goshi cikin jin zafi kamar yadda shima yayi

alokaci daya suka dago suka kalli juna

"ya sallam! sannu, bigewa kukayi?" inji batool data qaraso wajen

ahankali yanayin Aymaan ya chanza lokacin daya gane ko wacece Aysha saiya hade rai yana qarasa fitowa yajawo kofar


Aysha data lura da sudden chanjin fuskar saitayi tunanin ko laifinta ne dasuka qumen hakan yasata cewa
"sorry"


"same" ya amsa sama sama batareda yasake kallonta ba


ganin zai wuce yasa batool saurin cewa
"amm.. yaya wai da ganin zee zatayi kafin tatafi, tafiya zatayi"

Dan Juyowa yayi yadan kallesu sannan yace
"saidai wani lokacin amma yanzu ba'a yarda wani yashiga ba"

daga hakan yajuya yawuce suka bishi da kallo

cikin rashin jindadi batool takalli Aysha

"sorry"


Dan murmushi Aysha tayi tace
"babu komai ai zan dawo, muje Akhie najira"


Juyawa sukayi suka nufi hanyar ficewa daga asibitin


lokacin dasuka isa parking space Mussadiq yakusan bindiga, tun daga nesa yake jifansu dawani mugun kallo

ganin hakan yasa batool dakatawa tun kafin su qarasa sukayi bankwana

qarasawa Aysha tayi ta zagaya tashige motar yaja kamar dama shigowarta yake jira suka fice a tamanin

ta6e baki batool tayi tajuya itama tanufi cikin gida...✍�


*ya hqr dani🙁 adai cigaba da wanke hannu ana tayamu du'ai wlh aljannun typing dina sunfara kawo gardama😆 anemo masu ruqiya🤣🤣*


Ummin fasihu🧚🏻‍♀�
8/2/21, 9:44 PM - Buhainat😝: *🙍🏻‍♂️DEEN🙍🏻‍♂�*


*081*


Inda su mummy suke aymaan yanufa ya taddasu zazzaune hardasu daddy dabasu dade da isa wajen ba

duk dagowa sukayi daga firar dasuke suna kallonshi shikuma yaqaraso yana murmushi

"likita bokan turai, fatan dai diyar tawa tana lfy" inji abbu

murmushi yasakeyi
"eh komai normal, yanzu abinda xataci za'a samarmata taci saitasha magani"

masha allah duk suka fada cikin jindadi daddy yadora da
"sannu da qoqari d'ana, allah yayi albarka wa rayuwa"

duk da amin suka amsa banda aymaan dayayi murmushi Kawai

"to yanzu muna iya shiga ko? dazu kawani koromu waje ko yar kararnan babu" inji ummy tana harararshi

dariya duk sukayi daddy yace
"ato ai gwara hakan idan kuna ciki ba lallai bane kubari yayi aikinshi yadda ya kamata ba"

shidai murmushi aymaan yayi bece komai ba

tashi duk sukayi zasu wuce ward din daidai nan batool data dawo daga rakiyar aysha tayi joining dinsu

"ina zaku mummy?"

"wajen zainab, we can see her now"

kallon aymaan tayi cikin mammaki, ba yanzu yace ba'a buqatar kowa cikiba?

mugun kallon daya watsamata yasata kauda kai tana dan turo baki sannan tajuya tabisu mummy da har sun wuce


Jin alamun za'a bude kofar yasa zee saurin share fuskarta ta maida idanunta ta rufe


Jin muryoyinsu mummy adakin yasata bude idanun dasukayi ja tana kallonsu harsuka qaraso wajenta

duk sannu suka shiga yimata kowa namata kallon tausayi kowanne damuwa qarara a fuskarshi

ahankali take kada masu kai tana dan murmushi

cikin dan qanqanin lokaci aka hadamata kakkauran shayi aka bata don tasha

babu musu ta amsa tana sha tana kallon yadda kowa ke qoqarin kyautata mata don sata farinciki


*sune zasu iya zama dakai akowane irin yanayi, suyi sharing kowane feeling dakai, farinciki? baqinciki? qunci? damuwa? komai.*
maganar aymaan tadazu tadawo mata a kwalwa


*wadannan mutanen?.. su ya kamata mutum yafara sawa agaba, yafara duba wane hali zasu shiga idan ya aikata wani abin bawai mu rufe zuciyarmu ba mu makance qarshe muzo muyi abinda zaiyi hurting our beloved ones na har abada*


Dan lumshe idanu tayi tasake budesu.

tabbas aymaan yayi gaskiya, meyasa kullum takeyin abinda daga qarshe beloved ones dinta ke finta shan wahala?
meyasa kodayaushe take saka beloved ones dinta cikin damuwa?

meyasa take sakasu a wahala bayan wanda takeyi donshi bemasan tanayi ba?

imagine? he's a musician, famous musician while ita tananan tanason kashe kanta awofi

tunawa tayi tun bayan barowarta Nigeria wanda yanzu almost 1year ne babu wani abin kirkin data ta6uka illa 6ata lokacinta, tunaninta da tsaddadun hawayenta ga wanda qila yanzu bayama iya recalling sunanta

ita tananan tana hauka akanshi tana 6ata lokacinta akanshi while shi yanacan yayi moving on harya zama wani abin acan

how foolish is she?


jitayi ma ta tsani komai ma, ta tsani asibitin ma, idan ta tuna saboda shi take kwance akan gadon datake akai saitaji wani baqinciki yaqara mamaye zuciyarta


maganinta akabata ta kar6a ta shanye sannan takoma jikin pillon da aka taramata abaya ta jingina

"are you ok now ko kina buqatar wani abin?" inji ummy cikin kulawa

kallon ummy zee tayi saita kada kai sannan ahankali tace
"inaso mukoma gida"


duk kallonta sukayi

"mukoma gida? why? keda bakida lfy?" inji abbu

Dan murmushi da iya fatar le6e ya tsaya tayi tace
"naji sauqi ai, Kuma banason scent din hospital dinne yana tadamin zuciya" taqarashe zancen tana yatsine fuska

"ikon allah, to ai sai abari likitocin suzo muji ta bakinsu tunda suke bada sallamar idan sunga lafiya lau ana iya sallamarki saisu bada, zaman asibiti dama sai don dole bayada wani dadi" inji ummy


daidai nan aka bubbugo kofar ward din

saida akabada izinin shigowa sannan aka murdo kofar saiga Ahmad yashigo tareda ummanshi da aymaan cikin yin sallama

cikin fara'a mutanen dakin suka amsa sallamar sunama umman Ahmad maraba

umman Ahmad mai yawan fara'a ta qarasa ciki suka shiga gaisawa cikin fara'a da girmama juna tana tambayar jikin mai jiki

batool tunda umma tashigo takasa sakewa Kuma

akunyace ta gaidata ta amsa warmly cikin kulawa daga haka ba'a qarajin bakinta ba

zee ma cikin girmamawa ta gaida umman wadda ta amsa cikin kulawa tana tambayarta ya jiki ta amsa da dasauqi itakuma umman tashiga kwararamata addu'o'in samun afuwa

gaisawa sukayi da Ahmad shima yana tambayarta yajiki shima ta amsa da da sauqi

fira ce ta kaure adakin atsakanin ahalin cikin fara'a da nishadi Inda manyan ke firarsu sukuma qananun na sauraronsu daga bayama Ahmad da aymaan suka fice daga ward din


sai wajajen 12 noon suka sake dawowa dakin Inda anan su ummy sukayima aymaan zancen sallamar da zee tace tanaso

qara dubata yayi sannan yace za'a sallameta bayan zuhr don taji sauqi sosai Kuma zata ida warwarewa muddin zata cigaba dashan maganinta on time


umman Ahmad na taredasu har lokacin sallamar aka sallamesu suka fito tare Inda Ahmad yawuce da ummanshi gida suma aymaan sukayo gida suma.


Acikin kwanakin dasuka biyo baya zee tayi iyakar bakin qoqarinta naganin taragewa kanta damuwa

kodayaushe cikin making kanta busy take don kar ma tabama tarin tunannikan dake qunshe aranta damar tasiri azuciyarta.

kodayaushe cikin walwala take Kuma cikin mutane don bata yarda ta kadaice ko yaya ne.

sosai take fighting da zuciyarta wajen ganin ta yakice tunaninshi kwata2 daga zuciyarta


A bangarensu ummy kau wannan sabon halin na zee sosai yabasu mammaki don zee ta tashi daga zee din dasuka sani tana neman komawa her real lively zee

Abinda yafi dauremusu kai shine watsi da maganar Deen datayi don tun ranarda aka gwadamata shi bata sake tada maganarshi ba Kuma dataji alamun za'a dauko topic dinshi zata tashi tsam tabar wajen.

abin nabasu mammaki sosai don ga yadda abaya tanuna son bayyanar deen basuyi tunanin xata shashantar da maganar ba dawuri haka.

ganin bata ko qaunar atada maganarshi don kosun tada barin wajen take yasa suka bar tadamata zancen nashi suka koma can atsakaninsu suna cigaba da qulla plan dinsu na yadda zasu hada Deen da ainahin ahalinshi.


*2 WEEKS LATER*


"Kaka kinyi shiru" yafada yana kallonta da oily eyes dinshi

Ajiyar zuciya ta sauke sannan tadago ta kalleshi
"kyakyawana me zance?"

"Kaka kifadi Abinda ke ranki, kinsan koma menene kika fada ya zauna ni Kawai izininki nake nema idan kuma baki bani ba zan haqura"


"kyakyawana, bawai hanaka nakesonyi ba, kasan yadda banason kanayin nesa dani koyayane, kodayaushe nafison najika kusadani"

"nima Kaka, kullum burina mu kasance atare amma kema kinsan yanayin aikina yanzu, tafiye2 naciki don hakan na daya daga alamomin nasarar aikin"

"amma baka ganin wannan yasha banban da dukkan tafiye tafiyen dakake? kamal bafa garin zaka bari ba, qasar zaka bari gabadaya. wakasani acan? tayiwu masu satan mutane nema sukeson yaudararka da sunan aiki"


Deen kasa dakatar da dariyar data kufcemashi yayi hakan yasashi darawa ganin hakan yasa Kaka Dan hade rai

"au, wato dariya ma nabaka"

"to Kaka saceni fa kikace za'ayi, kamar wani toy?"

"koma dai menene, ai baka girmi sacewa ba indai wurin wadannan marassa imanin yan kidnafin ne? yo su ina ruwansu da yaro da babba? ai sunma fison babba"

murmushi Deen yayi
"Kaka anan Nigeria ke akwai kidnappers nikuma barin qasar zanyi gabadaya, Kuma wannan tafiyar ba daka zan tafi ba, Alhaji Bashir yasan komai akan tafiyar nan Kuma yabada goyon baya Kuma beyi hakan ba saida yayi bincike sosai sannan kuma shi ainahin wanda zanje wurinshi nasanshi, Dan Nigeria ne amma acan yake dazama shida iyayenshi wadanda sai daga baya nasan cewa ashe sunsan juna da Alhaji Bashir don mahaifin yaron tsohon abokin Alhaji Bashir ne tun yarinta"

"shi mahaifin yaron ne abokin Alhaji Bashir?" inji Kaka

"eh, nima sai daga baya Alhajin ke gayamin bayan namashi magana yasa an bincika, Kuma yaron yanada kirki sosai dukda sau biyu muka ta6a haduwa dashi lokacin sunzo Nigeria harnayi ma mahaifiyarshi waqa kuma dukda yakoma can din zumuncinmu be yanke ba don kodayaushe muna ta6o juna via media"

buga tagumi Kaka Kawai tayi tana kallonshi batace komai ba, tarasa dalilin dayasa kwata2 tafiyarnan bata kwanta mata arai ba

"amma Kaka idan bakyason tafiyar babu komai saina fasa nabasu hqr dama bawai amsa nabasu ba tsayayya"

"A'a niba wai tafiyar ce banaso ba Kawai tunanin kewarka dazanyi nake"

"Kaka kwana uku Kawai zanyi fa, kuma zamu dinga waya ga Lailah ma nan nasan zata dinga zuwa tana debemiki kewa tunda dama tasaba zuwa bare yanzu datasan bananan"

"hakane.. to allah yasa hakan shiyafi alhairi. ai tunda Alhaji ya yarda nasan baza'a samu matsala ba insha allah amma fa ka kula kuma dakaga Abinda beyimaka ba kajuyo gida"

murmushi Deen yayi cikin jindadi
"insha allah Kaka, babu Abinda zai faru sai alhairi insha allah"

"allah ya yarda, dakai da habibun zaku?"

"eh dashi zamu insha allah"

"to allah ya tabbatar da alhairi" inji Kaka

"amin summa amin kakata" yafada yana Dan jawo kaffafunta data miqar saman tutu yana Dan tattausa mata suna cigaba da firarsu wanda yashafi tafiyar tashi


A daren ranar Deen yaba Ahmad tsayyayar amsa akan samun hallartar taron daya gayyaceshi don yayi musu performing.

sosai Ahmad yayi farinciki yakuma bayyanama Deen irin farincikin daya shiga abin haryaso yayi yawa

Nan suka tattauna sosai akan Abinda yashafi tafiyar Inda firr Deen yaqi yarda da zancen Ahmad na ya sauka gidansu ya nace akan shidai zaiyi lodging a hotel

babu yadda Ahmad ya iya haka ya haqura suka cigaba da tattaunawar.


Shirye shiryen tafiyar Deen yashiga yi Inda da taimakon Alhaji Bashir wato mahaifin Lailah akayi musu visa dashi da manager kuma abokinshi Habeeb

cikin qanqanin lokaci komai nasu na tafiya ya kammala ya kasance ranar kawai ake jira

A bangaren Kaka har lokacin bawai tafiyar ta kwanta mata bane kawai dai hakanan take pretending kamar ta yarda amma deep down batason tafiyar jitake kamar idan yatafi ya tafi kenan, sau dayawa saitaji kamar tacemashi afasa tafiyar amma ganin kamar shi yanason tafiyar yasa take hqr badon taso ba.


Acikin wadanda basason tafiyar harda Lailah, tasan zatayi kewarshi sosai dukda koda yananan ba kullum take sanyashi a ido ba amma the thought of zai tafi wata qasar yanasa jin wani iri, kamar zatayi loosing dinshi ko wani abu makamancin haka.

ahaka dai akaita rarrafawa har ranar daren dazasuyi tafiyar

ranar da daddare kasa isashen barci Kaka tayi, juyi kawai taitayi har gari yawaye.

washegari kuma duk tayi wani iri har hakan ya daga hankalin Deen

tambayar duniyar nan yayimata akan meke damunta amma taqi sanardashi, ganin hakan yasa da farko cewa zaiyi cancelling din tafiyar indai tafiyar ce bataso don bazai iya tafiya against her wish ba

dafarko tayi tunanin dawasa yake fadin hakan amma ganin ya tubure akan yafasa yasata komawa lalla6ashi don lokacin har 10am gashi 12pm jirginsu zai tashi


ganin yaqi yarda din yasa Kaka yima Alhaji Bashir waya Inda ta zayyanemashi komai

babu shiri shima alhajin ya iso gidan Inda anan suka hadu dakyar suka shawo kanshi ya yarda da tafiyar don shima a lokacin zuciyarshi tafara bashi akwai wani baqon al'amari dake shirin faruwa dashi


Har airport suka rakasu Inda nan ma da taimakon Alhaji sukayi settling komai don yafisu sanin takan komai awajen tunda daga Deen din har Habeeb wannan ne fitarsu qasar waje nafarko.


cikin qanqanin lokaci akafara sanarwa Inda ake buqatar passengers sufara boarding jirgin

Sosai jikin Kaka yayi lakwas lokacin dasuke bankwana amma ganin yadda Deen ke kallonta keenly yasa taqi bayyana hakan don shima da alamu asanyayen yake

addu'o'in tsari suka yimasu sosai sannan sukayi sallama Deen namasu alqawarin dasun sauka zai chanza layi yakirasu

ahaka suka rabu Inda suka wuce sukabi ayarin passengers dake boarding jirgin

wasu hawaye ne suka zoma Kaka lokacin da Deen ya 6acemata yayinda wani feeling na emptiness ya mamaye zuciyarta

a bangaren su Deen kau shigewa jirgin sukayi Inda duk suka nemi seat number dinsu suka zauna.

shiru Deen yayi ya jinginar da kanshi jikin kujerar dayake akai yana sauraron 6a66atun Habeeb dayaqi qarewa

haka kawai yakejin wani feeling azuciyarshi wanda bazai iya pointing finger akai ba

ahaka akafara sanar da tashin jirgi and in few minutes jirgin ya tashi ya lula sararin samaniya✈️


Ummin Fasihu🧚🏻‍♀�
8/2/21, 9:44 PM - Buhainat😝: *🙍🏻‍♂️DEEN🙍🏻‍♂�*


*081*


*jiya nasha kira😆 am sorry naso nayimuku jiya amma page dinne banason gutsira muku, Ku ma nasan zakufi son long page, to yaudai ga long page💃🏻*


Qarfe 8:00pm daidai jirginsu Deen yayi landing a babban filin jirgin sama na babban birnin Abu dhabi

fara saukowa passengers din jirgin sukayi aciki hardasu Deen dasukayi matuqar gajiya due to the long journey

kasancewar darene yasa koina yake tarr da haske yadda kasan ba dare ba gashi sai hada hada akeyi gwanin sha'awa

saida suka gama clearing din komai suka amshi luggages dinsu sannan suka fito suna tafe suna qarewa wajen kallo Acikin zuciyarsu suna yaba kyau da tsarin qasar.


basu sha wahala ba suka samu cab wanda zata kaisu hotel din da Ahmad yariga ya kamamasu tunkafin zuwansu suka shige suka kama hanya


A gaban qayyataccen hotel din aka saukesu suka shiga bayan sun sallami mai cab din


basu sha wahalar locating masaukinsu ba don dama Ahmad yariga yayi settling komai kuma yaturomasu information about komai don haka Kawai zuwa sukayi aka tantancesu sannan aka rakasu dakinsu.

kasancewar agajiye suke sosai yasasu yin wanka Kawai suka rama sallolin da'ake binsu sannan kowanne yabi lafiyar gado.


*WASHEGARI*


Tunda safe Deen yafita ya chanzo masu layi don babu Abinda yakeson ji a lokacin kamar muryar kakarshi

he missed her so much don jiyake kamar yayi wata daya baya tareda ita ne


setting komai yayi sannan ya zauna zaman jiran lokacin da aka dibarma SIM din kafin yafara aiki

to whine away time saiya ciro laptop dinshi yafara yan dube dube aciki, duk Abinda yakeyi habeeb nacan nade kan gado don shi dama tun bayan sallar asuba yakoma ya kwanta bemasan lokacin da Deen yafita nemo layi ba.


yana zaune yana aikinshi a laptop yana sipping tea dayasa aka kawomashi wayarshi tayi beeping

ajiye mug din hannunshi yayi ya dauki wayar yaduba, gani yayi sms ne na companyn SIM card din alamun yana iya amfani dashi yanzu

gyara zama yayi yafara saka number wayar Kaka cikin zumudi yanajin wani dadi a zuciyarshi.


ko kwakwarar ringing biyu batayiba aka daga kiran kamar dama ita akejira

"kyakyawana?.." yaji muryar Kaka daga dayan bangaren

wani sanyi yaji ya ratsa zuciyarshi lokacin da muryarta ta doki kunnenshi hakan yasashi sakin kyakyawan murmushinshi

"Kaka ta"

"kyakyawana, kasan tun yaushe nake jiran kiranka? meyasa baka kirani ba sai yanzu?" yaji tafada muryarta.na dan breaking

"Kaka sai yanzu layin yafara aiki, nima naqosa nakiraki naji muryarki, nayi kewarki"

"nima kyakyawana, ni sai yanzu nake danasanin barinka yin tafiyar nan. ina kewanka sosai ga mafarkai da naitayi jiya... yanzu dai yaushe zaka dawo?" tafada cikin muryarda kanaji kasan tana cikin damuwa sosai

"mafarkai? mafarkan me Kaka?"

"babu komai, insha allah alhairi ne. yanzu dai yaushe zaku dawo?"


murmushi Deen yayi
"Kaka duka yaushe mukazo? jiya fa mukazo"

"nidai na qagara kadawo ne"

"zamu dawo kaka insha allah, kinga saima fa gobe ake taron, yau dai zamu hadu da mutumin muyi shirye shiryen daya kamata, gobe muje muyi masa aikinsa jibi mu juyo insha allah"


Ajiyar zuciya Kaka tasauke ahankali sannan tace
"to allah ya yarda ya bada sa'a yakuma maidoku lfy"

"amin kakata, kinga bamu gaisa bama ko? fatan jiya kinyi barci lfy kinkuma tashi lfy"

"hmm ai jiya barci rabi da rabi nayi, kwata2 gidan babu dadi idan babu kai aciki"

"nikuma jiya barci harda minshari, dakyar nasamu sallar asuba ma" yafada cikin sigar tsokana

"ja'iri, dama nasan bawani sona kake ba, wato ni inanan nakasa barcin kirki saboda kai kaikuma kana can kana barcinka hankali kwance"

dariya Deen yayi
"to Kaka me yafi raina, wai kinga qaton dakin damuke kuwa? ga a.c ai dole na shari barci na" yafada cikin dariya cikin son lighting up mood din Kaka

"ah lallai, gwara kau kashari barcinka.. ina habeebun ko batare kuke ba?"

dagowa Deen yayi yakalli habeeb dake nade cikin bargo har lokacin yadan ta6e baki yace
"gayacan nade yanata sharar barci"

"barcin lafiya yanzu Qarfe tara koko ku nan dare ne?"

"A'a, to mu nan Qarfe goma ma, Kawai lallaci ne tunda muka dawo sallar asuba yabaje ko motsi bayayi"

"to kodai a.cn nasu na daban ne shiyasa idan mutum ya kwanta beson tashi? kaima fa cewa kayi saida ka makara da asuba"

dariya Deen yayi cikin tsokana yace
"yo dama tayaya zaki hada a.c din turai dana Nigeria? sanyinshi ma na dabanne har wani feshi feshi ruwa masu qamshi yake"

"A.cn?!!" inji Kaka tana kwalalo idanu

dariyar da Deen yafashe daita ne yasata gane ashe shaqiyanci Kawai yake mata

"zakaci qaniyarka ne, badai ka maidani kakarka ba?" tafada tana kwafa

"to dama mecece?" yafada cikin dariya


ahaka suka shiririce sunata kwasar fira yadda kasan ba kudinsu suke qonewa ba

saida suka jima suna wayar sannan sukayi sallama kowanne farinciki fall zuciyarshi

yana gama wayar da Kaka yakira Alhaji Bashir Inda shima ya sanardashi isarsu

suma sundan dade suna waya sannan sukayi sallama

daga shi sai ya juya akalar kiran zuwa ga Ahmad

ya sanarda Ahmad isowarsu tun jiya anan Ahmad kecewa yana kan hanya ma don shima tun jiya yake baza idanun ganin kiranshi shiru, Jin hakan yasa Deen cewa to saiya shigo din sukayi sallama ya katse kiran

sake kallon Inda habeeb yake kwance yayi ya girgiza kai yamiqe yanufi gadon

yaye bargon dayayi rufa dashi Deen yayi wanda hakan yasashi bude idanu babu shiri

"kasan allah? zan fita nayimaka booking flight kakoma Nigeria tunda barci yakawoka nan din" inji Deen yana hade cikkakun giranshi


murza idanu habeeb yashigayi yana qoqarin tashi zaune

"wannan ne kuma bazai yiwuba, idan kaga nabar qasarnan saina gama zagaye koina lungu da saqo nacikinta sannan, ca6! inzo qasar waje jiya inkoma yau? wasama kenan"

sakin bargon Deen yayi yana kwafa yanufi toilet yana cewa
"wasa kake gani, zaka gane ne"

da haka yashige toilet don freshen up.


Babu jimawa Ahmad ya qaraso, direct dakinsu yanufo don dama shi ya kamamasu dakin, lokacin har sunyi wanka duk sun shirya

cikin farinciki Ahmad ya tarbesu yanamasu sannu dazuwa

yadda Ahmad yanuna farincikin zuwansu har mammaki yaba Deen don shidai yana mammakin irin wannan soyayyar da wannan gayen kemashi.

anan suka zauna suka shiga tattaunawa akan event din gobe


sosai suka baje suna fira don daga Ahmad har habeeb ba'asan gwani ba a surutu gwara gwara ma Deen din don ko rabin d'iminsu bayadashi


saida sukaji anfara kiraye kirayen sallar zuhr sannan dik suka tashi suka fita masjid din hotel din sukayi sallah suka dawo

anan Ahmad yayi suggesting idan sunaso saiya dan zaga dasu gari to whine time away

da Deen yace A'a amma da habeeb yanace akan don allah sutafi din ya haqura ba don yasoba don shi becika son saurin shishigewa mutum ba yafison ya tsaya matsayinshi

shiryawa sukayi suka chanza kaya sannan suka fito

amotar da Ahmad yashigo daita suka shiga Inda Ahmad ne ke tuqin, suka fice daga hotel din.


***

A bangaren zee kau tafara adapting da wannan sabon halin nata data tsiro dashi

yanzu batada wani buri daya wuce ta tsaida hankalinta waje guda itama tayi wani abin kirki koda guda ne

ta dade tana 6atama kanta lokaci batareda tasani ba yanzu batason wasting any single second abanza Kuma

ita sai yanzu dawowarta Dubai kebata haushi, akan wani banzan dalili tabar qasarta ta nisanci iyayenta takuma datse karatunta

idan tatuna da bata baro Nigeria ba da wannan shekarar zatayi graduating saitaji wani baqinciki ya mamaye zuciyarta

akanshi tabar makarantarta lokacin da takusan gamawa kuma anan din ma saboda shi taita canje canjen school while shi yanacan yana gina rayuwarshi hankali kwance, idan ta tuna hakan ba qaramin zafi takeji a zuciyarta ba

shiyasa yanzu ta zage damtse bata barin komai yayi distracting dinta komai qanqantarshi, sotake itama tazama wani abu, she want to made it also, she want to move on.

hakan yasa yanzu ta tattara hankalinta kacokam ta maida ga karatunta, bata wasa dashi ko kadan, ta maida dukkan attention dinta akai shiyasa wani lokacin bata cika sanin Abinda ke wakana a gidan ba.


yau ma kamar kullum tana zaune cikin dakinsu a tsakiyar gadonsu littatafai takoina tana aiki

tsabar yadda hankalinta ya dauku ko sanin shigowar batool batayiba sai jitayi an fige pen din hannunta


saurin dagowa tayi adan tsorace, ganin batool ce sai tadanyi tsaki tana girgiza kai

hayewa kan gadon batool tayi tana cewa
"bookworm, ke shikenan idan kika samu littafi bakyaji bakya gani, dama haka kikeda tsoron exams? is better kiragewa kanki don munan bamada tsaurin exams kamar can qasarku dazakiyita abu guda kamar cin qwan makafi"

harararta zee tayi
"wake tsoron exams?"

"ke mana, tunda exam ya gabato kinwani addabi kanki da karatu kullum abu daya ko gajiya babu, gwara ki sassautawa.kanki don kanki bursting zaiyi abanza ingayamaki"

ta6e baki zee tayi tace
"to naji bani pen dina Kuma ni ba don exams nake karatu ba don exams be ta6a tsoratani,ba saboda akodayaushe ashirye nake ba kamar kuba dakuke bari sai yazo gab sannan kuyita tsalle tsalle" ta qarashe tana fige pen dinta daga hannunta taduqa tana cigaba da rubutunta

ta6e baki tayi tace
"kyaji dashi... wai kinsan wani abu?"

batareda ta kalleta ba ta girgiza kai

"dazu mukayi waya da habiby" tafada tana farr da idanunta

mere baki zeetayi tace
"iyee? shagali"


"yacemin he's very busy yau don yanzu haka yana tareda wani babban baqo ne" inji batool tana kallon zee dake sauraronta absent-mindedly


"allah sarki" inji zee tana cigaba da Abinda take

"Kuma kinsan wani abu?" batool tasake tambaya


rolling idanu zee tayi cikin qosawa sannan tadago ta kalleta

"don allah don annabi batool spare me, wai bakiga abinda nake ba ne? don allah ki kyaleni hakanan sai distracting dina kike da labarai marassa ma'ana" tafada cikin qosawa


riqe ha6a batool tayi tana kallonta harta gama sannan ta kada kai Kawai ta miqe batareda tace mata komai ba tafice daga dakin fuuu

binta da kallo zee tayi tadanyi shiru na wani lokaci saikuma ta daga kafadu tajuya ta maida hankalinta akan abinda takeyi


***


sunyi yawo sosai agarin Inda Ahmad ya shiga dasu wurare daban daban qayattatu na garin.

sosai sukaji dadin wannan fitar don sun kashe kwarkwatan idanunsu ba dan kadan ba

daga qarshe saida Ahmad yabiya dasu gidansu Inda sukaje suka gaida su umma

sosai sukayi musu tarba na musanmman don harda baban Ahmad suka tadda gidan

anan suka qarashe wunin sai gab da magrib sannan suka kamo hanyar hotel din

wannan yar fitar dasukayi ba qaramin sabo yajawo ba tsakanin gayun uku don lokacin dasuka dawo ma sun dade suna fira kafin Ahmad yatafi akan sai goben idan sun hade wajen event din


Bayan tafiyar Ahmad Deen yasake bude laptop dinshi yana qara shiri na aikinsu na gobe

sosai mutuncin ahalin Ahmad ya burgeshi shiyasa shima yaji yanason yimasu aiki na burgewa

haka yakusan raba dare yana aiki Inda habeeb uban rakad'i tun yana damunshi da 6a66atunshi na santin zaga garin dasukayi har barci yaci qarfinshi ya bugas yabarshi anan

shima saida barcin yafara cin qarfinshi sannan ya haqura ya kwanta zuciyarshi cikeda tunanin event din na gobe


*WASHEGARI*


Kasancewar yau Saturday yasa bayan sallar asuba duk komawa barci sukayi musanmman zee data kusan raba dare jiya tana karatu don da asuba ma dakyar batool ta iya tadata tayi sallah takoma tasake bin lafiyar gado


ahankali tafara motsi da idanunta dake arufe saboda hasken rays din rana dayayi reflecting fuskarta

Dan yamutsa fuskar tayi tana yin juyi agadon tana lallube involuntaryly

Jin bata ta6o komai ba yasata qara miqa hannu tana lallubawa nan ma wayam hakan yasata fara bude idanunta dabasu gaji da barcin ba ahankali

waiwaigawa tayi taga dagaske ita kadai din ce adakin hakan yasata miqewa zaune tana miqa agajiye

ahankali take bin dakin dake wani qamshin dadi da kallo ganin yadda yake fess fess tana wondering yaushe aka gyarashi, kardai ace ranan barci tayi sosai

duba yar qaramar agogon dake kan bedside locker tayi taga duka Qarfe tara ne da yan mintuna Kuma a irin wannan ranakun na weekend suna kaiwa har 10 kwance

lallai yau batool yan aikin ke bisa kai tunda harta tashi dawuri haka hardasu gyaran daki.

sauko qaffafunta tayi daga kan gadon tana qara miqar da gajiyayyun ga6o6in jikinta sannan ta tashi tawuce hanyar toilet

brush tafarayi sannan tayi wanka sannan tafito cikin bathing robe

Dan dakatawa tayi daga bakin qofar toilet din ganin gadon data tashi tabari ayamutse yakoma tsaff tsaff kamar ba'a ta6a kwanciya akai ba gawani qamshi da dakin yaqara dauka

da mammaki tabi koina na dakin da kallo taga bakowa hakan yasata ida qarasowa dakin walking slowly

to waya shigo yagyara gadon daga shigarta wanka? tambayar datayiwa kanta kenan

ganin Babu mai bata amsa yasata wucewa closet dinsu tazaro wata light silky gown kalar yellow ta shirya acikinta a gurguje sannan tadan shafa roll on mai sanyin qamshi tazura takalmin soso ta bude kofar tafice


ahankali take saukowa a stairs din tana qarewa gidan kallo saboda wani extra kyallin dayake

gidan yasaba zama cikin gyara da qamshi amma nayau yasha banban dana kullum don sosai gidan yaqara daukan extra kyalli ga wani qamshi dayake na musanmman


Babu abinda yafi bata mammaki irin extra silent da gidan ya dauka yadda kasan babu kowa adakin

"batool?.." tafada tana qarasowa cikin falon tana waige2

"batool!" tasake kiranta tana yin hanyar kitchen saidai sauke idanunta datayi a dining area yasata jan burki daga tafiyar datake

Dan wara idanunta tayi tana tana kallon yadda aka qawata dining area din wurin sai bada different colours of dim lights yake

"wow!" tafada ahankali tana yin wajen

tundaga nesa ta hangi dining table din wanda da alamu abubbuwan ciye ciye aka jejjera akai saidai bata iya hango ko meye saboda rufeshi da akayi da white spotless sheet

qarasawa tayi bakin table din tana kallonshi kafin ahankali tasa hannu ta yaye farin qyallen nasama

"HURRAY!!!" taji wajen ya dauki ihu nan take wanda hakan yasa harta tsorata

saurin waigawa tayi nan taga dukkan ahalin gidan ne duk sun fito from nowhere suna tafi suna waqar


_Happy birthday to you_

_Happy birthday to you_

_Happy birthday.._

_Happy birthday_

_Happy birthday to you!!_

Hangame baki zee tayi in outmost shock

wait.. wai dama yau ne birthday dinta?


Nan take wajen yadauki kidan ryhmth din waqar Happy birthday mai dadin gaske su ummy na bin waqar

"ya sallam!" zee tafada cikin wani irin shauqi taruga wajensu ta rungumesu gamm tana tsallen murna


dariyar farinciki wajen ya dauka

raba jikinta tayi dasu tana kallonsu

"tayaya kukasan yau ne birthday dina? ni kaina na manta" tafada cikin tsananin farinciki

"mu ai bamu manta ba" inji daddy da sai alokacin ma ta lura dashi


wara idanu tayi taruga wajenshi
"daddy! yaushe kadawo?" tafada tana rungumeshi

"jiya" yabata amsa

"shine ban saniba?"

"it's a surprise!"

sakin daddyn tayi tanufi ummy ma ta rungume kai da gani dadin ne yaimata yawa

"kai amma kun shammaceni, this is the best surprise ever! thank you" tafada cikin murna bakinta yaqi rufuwa don farinciki

"you deserve it dear, Happy birthday" inji abbu yana miqamata wani dan box dake lullu6e da ledar gifts irin.mai qyallin nan

"wow! thank you abbu" tafada cikin jindadi tana amsar box din

"Happy birthday sweet daughter" inji ummy itama tana bata wrapped gift dinta

"ohh! thanks so much sweet ummy" tafada tana rungume ummy kafin ta amsa

"Happy birthday shalele" inji daddy yana miqamata guntun box shima wrapped cikin ledar gift

Dan ihun murna tayi sannan ta amsa

"thank you daddy"

"Happy birthday ukhtie, wullnp" inji aymaan shima yana bata nashi gift din dake cikin dan madaidaicin flat box

"wow! shukran akhie" tafada tana amsa cikin murna

"Happy birthday rude sis" inji batool tana miqamata wani siririn abu nannade a ledar gift

"thank you silly girl.. meye wannan abin kamar kara?" tafada tana jujjuyashi ahannu

kashe mata ido daya batool tayi tace
"karki damu, zakiji dadinshi sosai saboda nasan duk sai.kinfi jindadin gift dina.bisaga na kowa"

harararta zee Kawai tayi ta ajiyeshi shima Inda duk ta ajiye kingin gift din

Nan duk kallo yakoma kan mummy

ganin hakan yasa mummy kauda kai

"mummy kefa? ina gift dina?" tafada ashagwa6e

wata harara mummy ta gallamata hakan yasa ta tur6une fuska tana turo baki

"dama nasaba baki birthday gift ne? wannan sai wadanda sukaji zasu iya"

dariya duk yan dakin suka dauka ummy tajawo zee jikinta tace
"kyaleta daughter ai dadin abun kinada iyaye dayawa"

"aikaudai, gasunan tili tili duk masu sonki" inji abbu

itadai mummy ta6e baki Kawai tayi batace komai ba


"To yanzu yaushe za'a fara cin abincin? nidai cikina yafara kiran ciroma" inji batool tana yatsine fuska

aymaan dake kusada ita yayi kamar zai tandaremata qeya tayi saurin duqewa

"ffo Kawai" yafada yana harararta

"A'a da gaskiyarta, daughter taho muje mufara mu nima dai dauriya Kawai nake" inji mummy tana kamo hannun batool

dariya wajen yasake dauka suma suka bisu dining din dayake shaqe da kayan ciye ciye kala2

"wow! dik yaushe kukayi wannan?" inji zee tana zama tana qarewa table din kallo

"kina can kina wannan barcin asarar mana, to don ma kisani nima ga nawa birthday din saikin ramamin yarinya don ba akyauta nayi miki wahalar yau ba" inji batool

wani kallon uku saura kwabo zee tayi mata ta watsar

addu'a suka farayi sannan akace birthday girl zata fara ta6a abincin kafin kowa yaci

tsayawa zee tayi tana qarewa abubbuwan kan table din kallo sannan tayi murmushi ta miqa hannunta ga wani plate dake cikeda favorite snack dinta wato burger tana cewa
"zanfara da gift din mummy"

dariya duk mutanen wajen sukayi don dagaske mummyn ce tayi burger din Kuma tayishi exactly yadda takesonshi

gutsira tayi tafara tauna ahankali tana lumshe idanu saikuma ta bude ta kalli mummy
"thank you sweetest mummy!"

yadda tayi maganar yasa mutanen wajen qara sa dariya itakau mummy murmushi Kawai tayi tana girgiza kai

bismillah akayi kowa yafara cin Abinda yakeso a table din

sosai zee takejin dadin moment din, rabon da taji irin farincikin datakeji ayau harta manta

tunda take bata ta6a celebrating birthday dayasata farinciki kamar na wannan

dama ita bawani celebrating birthday dinta takeyi sosai ba, yawanci duk tareda tsoffin qawayenta (sumy) take celebrating dinshi Inda zata kwashesu sutafi outing Inda zasuje susamu wani grand restaurant suci su qoshi sukuma yi shopping wanda duk ita zata biya

saikuma daddy da duk ranar birthday dinta saiya bata wani abu a matsayin gift itakau mummy ba'a ma maganarta don bawani shiri sukeba alokacin bare akaiga maganar gift

rabonta da celebrating birthday shekara biyu kenan don wancan har yaxo ya wuce batasaniba don alokacin suke cikin chakwakiyar su master lokacin Deen na kwance asibiti

sai wannan wanda busy yasa tama manta shaff dawani birthday don da basuyimata bama da sai daga baya zata tuna


tayi mammaki Kuma taji dadin wannan bazatan sosai don tunda take bata ta6a birthday mai armashin wannan ba

firace ta kaure a dining din suna fira mai cikeda barkwanci da tsokana ga dan kidan dake tashi har lokacin ta bayan fage

sosai kasancewarta cikin wannan Happy family din yaqara sanyayamata rai tana Jin kamar su dawwama ahaka

"wow! gaskiya bazan gaji da godemuku ba.,you guys made my day. wannan birthday din is the best birthday of my life, I heart you millions times" tafada farinciki fall zuciyarta

"wani abin ma sai anjima" inji batool saikuma tayi saurin toshe baki alamun tayi su6ul da baka

ganin duk mutanen wajen,sun harari batool yasata sanin tabbas akwai Abinda suke 6oyewa

"anjima? wayyo allah me Kuma zai faru anjima? karku kasheni da dadi" tafada tana dan tsalle a kujerarta kamar wata qaramar yarinya

"mtcheew mai bakin parrot beyi ba" inji aymaan yana gallama batool harara sannan ya maida kanshi kan abincinshi

"nidai don allah ku gayamin, pleeease" inji zee tana marairaicewa

"dont mind them daughter, Kawai yar qaramar liyafa zamuyi na birthday dinki anjima, that's all" inji ummy

"really? amma ai meyasa? wannan ma ya wadatar" inji zee don itafa dama can tara mutane ana celebrating birthday becika burgeta ba tafison tayishi in a small way

"bawai wani taro bane, Kawai iya mune zamu dan zauna muyi celebrating in a small way kingane ai, a garden ma za'ayi, Kawai daga mu sai mu" ummy tabata amsa

"Kuma munason yin hakane don yazama memory da kowa zai riqe koda watarana bama tare irin hakan mu dinga tunawa munajin dadi" inji abbu

kada kai zee tayi cikin gamsuwa tace
"allah yakaimu, can't wait"


cigaba dacin abincin sukayi, itadai batool bata qara cewa komai ba don karta sake wani su6utar bakin

ahaka suka gama karyawar cikin jindadi

saida suka sake dadewa a zaune suna fira kafin afara watsewa

zee da batool sukayi clearing table din komai yakoma daidai sannan da taimakon batool zee ta kwashi gifts dinta suka haye sama cikin zumudin budewa suga abubbuwan dake ciki...✍�


*banso datse page dinnan ba amma ya na iya? 🤦🏻‍♀� banason rushing dinshi don haka kuyi hqr _reunion_ sai next page insha allah*


Ummin Fasihu🧚🏻‍♀�
8/2/21, 9:44 PM - Buhainat😝: *🙍🏻‍♂️DEEN🙍🏻‍♂�*


*083*


*last page nayi mistake wurin numbering, 82 ne instead of 81*


Akan gado suka baje gifts din suka shiga budewa da daddaya

kwalin Abbu mai dan girma suka fara budewa nan sukaci karo dawata tsadaddiyar Abaya kalar sky blue mai hula irin ta alkyabba tasha stones masu walainiya atakoina na jikinta sai daga gefe takalmine kalar kayan masu shegen kyau da yar guntuwar purse

wani ihu suka saki atare cikin tsananin murna suna qanqame juna

fadin farincikin dasuke 6ata lokaci da baki ne

sakin juna sukayi batool tazaro rigar tana dagata sama don su ganta dakyau


"OMG! wayoo allah na, zee don girman allah kibani idan baki baniba zan mutu" inji batool tana rungume rigar qaqam ajikinta

fizge rigar zee tayi tana cewa
"allah yajiqanki ya gafartamiki, idan kin mutu zanyi volunteering gero musha gumba"

"muguwa, kede wlh mutuncinki qalilan ne" inji batool tana harararta

gwalo Kawai zee tayimata tana maida rigar carefully cikin kwalin ta rufe ta maida gefe sannan suka dauko gift nagaba

dan madaidaicin box din ummy suka bude Inda anan sukaci karo da tsadaddun yan kunnenshi da sarqa da bangles dinsu duk iri daya sai daukar ido suke

nan ma ihun murna sukayi suna santin kyawun jewelry din

gift din daddy shine nagaba Inda anan sukaci karo da wata faskekiyar waya ta yayi mai daukar ido

anan ma ihun suka saka kamar qanannun yara suna tsallen murna

next sai gift din aymaan dake cikin flat box

ahankali suke yage ledar da akayi wrapping kwalin dashi har suka raba kwalin da ledar

Jan kwali sukaci karo dashi mai dan fadi

daga murfin kwalin sukayi nan take abubbuwan ciki suka bayyana

wara idanu duk sukayi bakinsu na forming 'O' shape suna kallon kayan cikin kwalin speechless


Acikin kwalin wani dan kwali ne mai shape din heart dauke da qananun qananun candies of various colours suma masu shape din heart, Kasancewar abin da aka rufe kwalin transparent ne yasa suke iya hango mouth-watering candies din dake ciki

agefe kuma wata yar kwalbar turare ce wadda kallo daya zakamata kasan tsaddadiyace sai dan birthday card mai design din red roses ajiki.

sun dade suna kallon abubbuwan batareda sun iya cewa komai ba

batool ce tafara iya magantuwa

"wow! wow!! wow!!" tafada kamar wata jiniyar mota tana bude transparent covering din candies din

ahankali ta dauko guda daya aciki takai bakinta ta gutsira tafara tauna tana yin luum da idanu

"wayyo ummy na, wlh tunda nake ban ta6acin candy mai dadin wannan ba, don allah ci kiji" inji batool tana kaima zee da haryanzu takasa magana candy din abaki

ahankali itama zee da duk jikinta yayi sanyi ta gutsira tafara tauna tana jin yadda gardin candy din ya gaurayemata baki

"how was that?" inji batool cikin zumudi

ganin batayi magana ba kuma har lokacin bata bar kallon candies dinba yasa batool kallonta murnarta na dan komawa ciki


"zee lfy?" tafada ahankali tana kallonta

sai a lokacin zee tajuyo ta kalleta itama

Dan kirkirar murmushi zee tayi wanda iyakarshi fatar baki

"am.. am ok, Kawai gift dinne yayi mugun burgeni" tafada tana daukar card din tana jujjuyawa

azahiri ba gaskiya bane Abinda tace ba don ganin wadannan candies dinne suka sata a wannan yanayin

sai suka tunomata da candies dinsu na ranar Valentine wanda da ita da Deen sukaci suna celebrating soyayyarsu, sak wadannan irin wadancan ne banbancin kawai colour don na wancan na chocolate ne wannan kuma kaloline daban daban kowanne kuma da taste dinshi


Bude card din tayi Inda anan taci karo da yar farar linkakkiyar takarda wanda ke tsakiyar card din

cirota tayi ta warwareta tafara karantawa


*_To a Special Princess_*

_*Today marks a Special day to a Special person*_

_*Happy birthday to the cutest and unique being i've ever came across*_

_*may this day mark the beginning of your indefinite happiness and joy*_

*_may allah continue to brighten the way for you and may your unique smile stayed plastered to your face forever (Ameen)_*

*_Enjoy your day PRINCESS👸🏻_*


saida tagama karantawa sannan talura ashe tare suke karantawa da batool don tunda tabude itama ta leqo kanta tana karantawa itama

"woow! ashe haka akhie iya tsara kalamai! mugani.." inji batool tana neman amsar takardar daga hannun zee

6oye takardar zee tayi abayanta tana harararta dukda yadda takejin zuciyarta na rawa rawa

"yo saboda me? amebo you better face your business" tafada tana ninke takardar saidai har lokacin zuciyarta batabar rawa ba

dukda rubutun aymaan gajere ne ba qaramin tasiri yayi a zuciyarta ba

wani tunani yakeson bijiromata a zuciya amma takama iyakar bakin qoqarinta don kaudashi don bata fatan hakan ta kasance ko a mafarki

domin kawar da tunanin saita janyo gift din batool wanda duk ciki shine qaraminsu

"nidai wannan abu bansan ko meyeba, abu kamar icce kamar kara" tafada tana qoqarin warwarewa

dariya batool tafashe dashi tace
"kedai duba, am telling you babu gift din dazakiji dadinshi irin nawa"

"ahakan? to allah yasa"

ida warwarewa tayi nan Abinda batayi expecting ba ya bayyana

qara fashewa da wata yar iskar dariya batool tayi ganin yadda zee tasaki baki tana kallon gift din

ba komai bane illa pen saidai pen din nada kyau kuma jikinshi transparent ne Inda taciki tana iya hango yar takardar da batool ta cusa ciki ajikin takardar tarubuta

*_Happy birthday bookworm_*


"kutt.. amma kinyi mugun raina min hankali, dama wannan ne gift din?"

cikin dariya sosai batool tace
"ai naga kamar zakifi jindadin gift dina bisaga na kowa yadda kwana biyun nan kika maqalewa littafi"

jifanta zee tayi da pillow tana cewa
"silly girl"


atare suka tattare kayayyakin suka adana banda candies din wanda batool tabude ciki sai zaqa take

zama sukayi suna cigaba da firarsu suna cikin haka wayar zee tayi beeping

dauka tayi taduba saitaga birthday message ne daga Aysha

Dan wara idanu tayi tace
"waya gayama Aysha?"

daga yatsa batool tayi kamar irin tana cikin aji dinnan

makamata pillow zee tayi tace
"waya aikeki?"

dariya batool tayi tana sosa Inda ta bugamata pillon tace
"har sai an aikeni? kema kinsan tasake taji labari daga baya cewa kinyi birthday ba'a gayamata ba kaina zata huce, ya akayi lokacin da aka sallameki asibiti ba'a gayamata ba har taje ta iske wayam? ba nan tazo tahauni da masifa ba kema harda tayata?"

"mtcheew, kede kikasani mai bakin parrot Kawai"

"eh din, don haka kima shirya nasan tana nan tafe anjima wurin taron nan"

sakin baki zee tayi tana kallonta
"gayamata kikayi?"

juya idanu batool tayi
"sosai ma, tun yaushe nakai mata i.v? kece fa bakisan da wannan abin ba sai yau, kinacan kun daura aure da littafi dama ya za'ayi kisani? to na gayyaceta bama ita kadai ba harda yayanta"

kwalalo idanu zee tayi
"Mussadiq?!!"

"yes? wlh harda shi saidai yakawo mana kwafsi wai bayanan yana wani business trip tun last week injita" inji batool tana ta6e baki alamun ko ajikinta

sakin baki zee tayi tana kallon batool

lallai batool batada hankali, tarasa wanda zata gayyatomata sai wannan mutumin? bayan tasan yadda basa shiri dashi ga gabar dasukeyi da aymaan?

to waima meye alaqarsu dazata wani gayyaceshi? haka Kawai saita gayyaceshi bayan tasan bawani maganar arziqi sukeyi ba?


Tunawa tayi da karonsu na qarshe a school

lokacin ba'a dade da sallamarta ba a wannan kwanciyar datayi asibiti

a lokacin ta quduri aniyar tattara komai daya shafi Deen ta watsar don sotake tayi moving on for real

saidai har lokacin Mussadiq bebar bibiyarta ba a school

abin nashi harya kai duk Inda tayi saita ganshi hatta sabon wurin data chanza tana ke6ewa don tayi karatu

saidai abinda yafi daure mata kai shine duk lokacin data ganshi baya nuna yama san da ita awurin don ko kallon banza bata isheshi ba bare na arziqi, yi yake kamar besan da wanzuwarta ba awajen hartayi Abinda zatayi tabar wajen

tasha hasashen kodai ba.ita din yake bibiya ba hakan kesata chanza wurin zama kodayaushe Kuma sai taga duk Inda taje saiyaje hakan yasata tabbatar da eh ita din yake bibiya

ganin hakan yasata yanke shawarar samunshi tayi warning dinshi yafita harkarta don ahalin yanzu bata buqatar taqara hada wani abu da Abinda yashafi Deen don shi dinma sotake ta gogeshi a kwalwarta ta huta hakanan

hakan yasa watarana taje tasameshi yana zauna daga nesa da Inda take as usual

nan tacemashi yabar bibiyarta hakanan kota hadashi da hukumar makarantar don bataga dalilin daxai dinga bibiyarta ba haka Kawai

a ranar ta tabbatar da Mussadiq dan air ne na gaske don gabadaya saiya juye abun kanta ya nuna ita har wacece dazai bibiyeta kuma mema zaisa ya bibiyeta ko taga yazo wajenta ne ko yayimata magana

cikin shaqiyanci yace Kawai sotake tayi making kanta noticeable ne awajenshi amma shi samm ko sanin da ita bayayi

yadda ya juyar da maganar yana mata shaqiyanci shiyafi 6atamata rai gashi ya iya gayama mutum magana yadda zakaji kamar kaita kurma ihu

saida sukayima juna tass sannan tawuce tabarshi yana mata dariyar shaqiyanci wanda ke qara qonamata zuciya, sai taji wama yace tunfarko taje tasameshi gashi ya 6atamata rai a banza


tun daga lokacin bata qara kulashi ba kuma shima be fasa bibiyarta ba saidai ko kallo baya isanta don itama ta quduri aniyar watsar dashi tayi pretending batasan dashi ba


kullum tana ganinshi amma bata kulashi saikuma taga daga baya tabar ganinshi kusan kwana hudu kenan, ashe tafiya yayi? kenan da yana nan din haka zata gayyaceshi? wannan ai zubar da mutunci ne

girgiza kai tayi sannan ta miqe tsaye tana kallon batool on a serious note tace
"batool mu ajiye batun wasa, karki qara yimin haka, idan ina abuna karki qara sakoman wannan mutumin aciki"

"to amma..."

"nadai gayamaki" zee ta katseta sannan tanufi hanyar toilet tashige tana maido qofar da qarfi


ta6e baki batool tayi tadaga kafadu ta cigaba da cin candy dinta hankali kwance


***


Dago kai aymaan yasake yi ya kalli Ahmad dake kai kawo a dakin looking very restless saiya mere baki yasake maida hankalinshi akan wayar hannunshi

"what should we do now?" inji Ahmad dabe bar safa da marwan ba har lokacin

qara ta6e baki aymaan yayi batareda ya Dago daga danne dannen dayakeyi ba

dakatawa daga zirga zirgan Ahmad yayi ya kallo aymaan

"wato kai ko ajikinka, mutane,nacikin damuwa kai kawani harde kana danne danne ko a kwalar rigarka ko?" yafada a little angry

qara ta6e baki aymaan yayi yana dagowa ya kalleshi
"su mutanen su sukaso sa kansu a damuwar, ni banga abin damuwa ba anan"

"dama tayaya za'ayi kagani? ni ai nagama lura bawai son wannan al'amarin ba kake Kawai kana following ne shiyasa ko ajikinka"

"to da fa? kaima kasan dalilin dayasa haryanzu nake cikin case dinnan, Kawai don nacikama zee burinta na sadashi da ahalinshi Kawai yasa kaga ina biye ba don hakan ba..." saiya daga kafadu

tsaki Ahmad yaja Kawai yajuya yabar kallonshi

"yanzu haka za'ayi abinnan Babu Mussadiq? ni nafison sufara haduwa dashi haduwa zaifi tsari wlh"

ta6e baki yayi yace
"saikaje can Australia din kasameshi kataho dashi yadda abin zaifi tsari"

sake juyowa Ahmad yayi ya gallamashi wata muguwar harara hakan yasa aymaan murmusawa

kwafa Ahmad yayi yajuya

"kaga wannan duk fa ba abin 6acin bane, idan shi Mussadiq din bayanan ai qanwarshi nanan, banaji batool tace zatazo ba?"

"dukda hakan, idan Mussadiq yazo komai zaifi armashi"

"hmm koba armashi ba, wataqila ma gwara da bayanan don wannan mahaukacin Babu Abinda ke kanshi sai hauka, banda hauka me zaizo yaiwa mutane?"

"ai dama kai ba sonshi ba kake"

"ni ai naga yana sona, Kawai.ku manta dashi kuyi proceeding plan dinku, wayasani ma ko hakan zaifi"

Ajiyar zuciya Ahmad yayi saidai still fuskarshi na nuna alamun rashin jindadi

furzar da huci yayi sannan yace
"ok, bari na lalubo Deen din"

daga kafadu Kawai aymaan yayi yacigaba da danne dannenshi shikuma Ahmad yazaro waya zai lalubo Deen din


***


Kamar yadda batool tayi hasashe tun bayan asr Aysha ta diro gidan

sosai sukayi murnar ganin juna nan suka rungume juna suna murna

bayan sungama suka baje adakinsu batool suna fira Inda anan itama Aysha din tabata birthday gift din data kawomata Inda xee tanuna jindadinta sosai takuma yimata godiya


adakin sukayi zamansu sunata firarsu Inda acan waje Kuma ake decorating garden din daza'ayi dan taron daza'ayi anjima.


*8:00pm*


Ahankali take nada mata veil din cikin qwarewa irin nadinsu na larabawa

saida tagama sannan tadauko turaren dake kan mirror din (aymaan's gift) tashiga feffesamata shi ajiki, nan take dakin yadauki wani qamshi mai sanyin dadi

"wow! gaskiya turarenan yayi, I love the scent" inji Aysha tana ida gyagyaramata Inda beyiba

murmushi Kawai zee tayi

kaucewa Aysha tayi yadda zee zata samu damar ganin kanta a jikin mirron

"now, here you go" Aysha tafada tana murmushi

dagowa zee tayi ta kalli kanta ajikin qaton madubin nan take tawara idanu tana kallon kanta without blinking

dariya Aysha tayi ganin yadda zee ke kallon kanta ta mirror Babu ko kyaftawa sai tace
"to ya?"

cikin wara idanu zee tace
"wai.. dagaske nice anan?"

dariya Aysha tasakeyi tana xagayawa bayanta ta dafa kafadunta ta sunkuyo yadda zasu dinga kallon kansu ta mirror tace
"ga zahiri?"

"wow! this is...amazing! tayaya kikayi transforming dina haka?" inji zee cikin murna

"bani nayi transforming dinki ba, dama ke kyakyawace gakuma kyawawan kaya dole ki chanza... now time for selfie" inji Aysha tana zaro wayarta sukayi posing ta daukesu

daidai nan aka bude kofa batool tashigo

"wai wannan wane irin shiriritane? kunsan lokaci yayi amma kuntsaya kuna..." maqalewa a iska kingin maganarta tayi datayi tozali da zee

wara idanu tayi cikin mammaki tana kallon zee baki bude

"who is this?" inji batool idanunta still akan zee

harararta zee tayi ta kauda kai tana murmushi

"wow! wow! wow!!" tafada tana qarasowa wajensu itadai Aysha banda murmushi Babu Abinda takeyi

"zankad'aziya kenan, wai zee kin ganki kuwa?" tafada tana bin koina na jikin zee da kallo

fari zee tayi da idanu tana tsuke baki
"ya nakoma?"

"kai aradu dafarko nakasa.ganeki, kinga wai yadda rigar tayi maki? kai dole mukashe selfie, tashi tashi" tafada tana zaro wayarta

Nan fa suka samu abin yi sukaita daukar kansu selfie dukkansu suna styles kala2

ahaka har aka sake bude kofar

"wai wannan shirun na lafiya ne? kufa kadai ake jira" inji ummy data leqo

idanunta ne suka sauka kan zee

"kai kai kai masha allah, diyar tawa takoma haka?" inji ummy tana qarasa shigowa dakin

murmushin kunya zee tayi

"kai masha allah, gaskiya kinyi kyau daughter, allah yayi albarka yaqaro shekaru lodi lodi masu albarka"

duk da amin suka amsa harda Aysha Kasancewar duk da turanci suke maganar

"yanzu kuyi sauri inajin ai kungama ko? ku kadai ake jira"

"eh mungama ummy" inji Aysha

"to mutafi, kowa ya hallara ku kadai ake jira"

"ummy baqin sun iso" inji batool cikin zumudin

"idan kika kin gani" inji mummy tana doroma zee hular Abayar bisa kai wanda keda jela jelar zarruruwa wadanda suka dan karemata fuska

kama hannunta ummy tayi sukayi waje su Aysha na maramasu baya


koina tarr yake da haske dukda Kasancewar dare ne, daukar hanyar garden din sukayi suna tafe Aysha na gyarama zee rigarta dake dan jan qasa abaya

Garden din shima tarr yake da haske dake haskowa daga both kwayaye masu haske da masu kaloli

anyi decorating garden din gwanin sha'awa ga fararen plastic kujerun da mutanen da aka gayyata duk suka zazzauna akai

daga gaban mutanen Kuma wata royal blue kujera ce mai kyau sosai sai dan qaramin glass table daga gabanta wanda ke dauke da dan madaidaicin cake dake dauke da burning candles masu kaloli akai.

mutanen wajen basuda wani yawa

daga su Abbu sai su mummy sai su aymaan da Ahmad dakuma iyayen Ahmad din

Ahankali suka qaraso garden din suna tafe fuskokinsu dauke da murmushi

sosai kallo yadawo kan zee wadda taxama kamar tauraruwa acikinsu

Ahankali take tafiya hannunta cikin na ummy dake janta fuskarta dauke da murmushi

dukda bata ganin mutanen wajen sosai saboda baza bazan hularta dasuka dan karemata gani taga alamun mutanen dai nada dan yawa

sautin 'masha allah' keta tashi daga bakunan mutanen wajen cikin yaba irin kyawun datayi wanda hakan kesata murmushin kunya tana qara sinne kai

acan na hango aymaan dake sanye cikin wani danyen tsaddaden yadi kalar madara yaci gayunshi Inda yayi shigar milk and brown

tun lokacin dasuka shigo garden din idanunshi ke kanta ya kafeta dasu babu kyaftawa

dukda baduka fuskar tata yake gani ba yana hango karan hancinta da guntun bakinta dake shining saboda lipgloss datasa, yana ganin yadda yake curving beautifully idan tana murmushi


da kallo yarakasu har ummy ta qarasa daita wajen da aka tanada mata don zama

koda suka isa wajen bata zauna ba sai qarasowa da mutanen wajen sukayi wajenta suka fara gaisawa

akunyace zee keta gaidasu don duk saitaji kanta yayi girma ganin itace centre of attraction din wajen


aymaan dai yakasa ko kyafta idanu akanta duk motsinta saiyabishi da Hazel eyes dinshi

jiyayi an zungureshi hakan yasashi waigowa yana dawowa daga duniyar kallonta

"kallatu ance mutaso mu yanka cake" inji Ahmad cikin tsokana

harararshi aymaan yayi sannan ya tashi suka qarasa wajen mutanen daduk sun koma gaban wajen ana shirin yanka cake din

hada idanu Aysha tayi da aymaan yawani hade rai tareda kauda kai

binshi da kallo tayi saikuma ta ta6e baki itama ta kauda kai

waqar birthday suka shiga yimata suna tafi sannan da taimakon mutanen wajen ta yanka cake din


tafi wajen yadauka sosai ana dariyar farinciki

anan zee tashiga ciyar da makusantanta suna ramawa suma

ciro wani guntun tayi tanufi bakin Aysha dake kusada ita tanata murmushi

cikin murmushi Aysha ta bude bakinta tasaka mata nan ma aka dau tafi

itama Aysha guntun ta dauke ta bata tana lakuta mata sauran akumatu

dariya duk aka dauka ganin Abinda tayi

kamar ance Aysha tadago sai suka qara hada idanu da aymaan

wani mugun kallo ta jefeshi dashi ta kauda kai

Dan buda idanu aymaan yayi yana kallonta saikuma ya kauda kai yana kwafa acikin zuciyarshi


bayan sungama kowa yakoma mazauninshi ya zauna Inda akabar zee kadai gaban wajen zaune a maxauninta

anan ne Ahmad daya ari aikin m.c yafara gabatar da mawaqin dazai danyi entertaining dinsu

be ambaci suna ba Kawai dai gabatarwa yayi mashi yakuma buqaci atafa mashi

tafi din kau aka dauka wanda yayi daidai da shigowar mawaqin filin

sanye yake cikin wani ratsatsen suit fari Inda yayi shigar mai combination din fari da jaa

farin wando sai jar shirt yadora coat fari asama, wuyanshi sanye da jan necktie guntu, kaffafunshi sanye da fararen half cover, yar saisayyayar sumar kanshi sai shining take

abayanshi kuma managern shine kuma mai sakarmashi kida shima cikin shigar suit saidai nashi baqaqe ne

da wannan kyakyawan murmushin yaqarasa shigowa wajen yana kallon mutanen wajen dake tafamashi kowa idanunshi akanshi

ahankali yadanyi bowing alamun godiya still murmushi afuskarshi

habeeb kau tuni yanufi wurin setting dinsu Inda zai dinga sakarmasu kida

musabaha Deen yayi da Ahmad dake gaban stage din sai washe baki yake

mic din hannunshi Ahmad yabashi ya amsa yana godiya sannan yajuyo yana kallon audience din

tun shigowarshi bugun zuciyoyin mutane biyu suka chanza, zee da Aysha

Aysha binshi Kawai takeyi da kallo cikin mammaki da bugawan zuciya

mammaki take yaushe yayanta yadawo daga tafiyar harya zo nan din, saidai kuma sai take ganin kamar bashi ba duba da wasu dabi'u dayakeyi wanda kamar banashi ba, ga sumarshi yar kadan sa6anin ta yayanta dakeda yawa kuma a kwance luff

zee kau bata ganshi ba don yana daga can gefe ne kuma yana facing mutane saidai zuciyarta wani irin bugu take kamar zata faso qirjinta, sosai takejinta awani yanayin da bazata iya musaltashi

ahankali Deen yayi gyaran murya sannan cikin harshen turanci ya gaida mutanen wajen yakuma gabatar da kanshi ta hanyar amfani dasunan da akafi sani dashi wato *Balarabe*

sannan yatayasu murnar wannan taron dasuke na zagayowar ranar haihuwar diyarsu yana kuma yin fatan allah ya maimaita

Tunda yafara magana zee taqame a kujerar datake zaune

kwalwarta ke birgita mata cikin kai tana jin kamar bamaa duniyar ba take

wannan muryar...

waye mai wannan muryar?


ahankali Deen yayima habeeb alamun suje zuwa, nan take habeeb yashiga aikinshi Inda ya sakarmasu wani cool kida mai dadin gaske


lumshe idanunshi Deen cikin son daidaita nutsuwarshi daya rasa Inda ta fece

tun shigowarshi wannan wurin yanemi duk wata nutsuwarshi yarasa, Abinda besaba faruwa dashi ba

yasaba hallarta taron daya linka wannan jama'a linki ba linki amma beta6a tsintar kanshi a irin wannan yanayin ba sai wannan karon, meyasa?


Ajiyar zuciya yasauke ahankali yana iyakar bakin qoqarinshi wurin cooling down

humming yafarayi cikin cool voice dinshi yana lumshe idanunshi


ahankali yafara rero waqar birthday dayayi composing saboda taron


sosai waqar ke tafiya cikin wata iriyar salo mai narka zuciya

tsit wajen ya dauka kowa hankalinshi akanshi suna sauraron yadda yake rairo baitukan waqar cikin qwarewa da salo na daban

kasa ko kyafta idanu Aysha tayi akan Deen, kallonshi Kawai take kamar tana kallon wani hallita daban

yaushe akhie yazama mawaqi?


Tunda yafara waqar zee tarasa awane duniyar take ciki, komai ya burkuce mata, zuciyarta, kwalwarta, ruhinta suka shiga harmutsawa takasa gane takaimaiman Abinda ke faruwa akewayenta Kawai Abinda take iya ji shine wannan muryar

Deen kau a bangarenshi shima bugawar da zuciyarshi keyi yafara affecting waqarshi don sai sarqewa yakeyi akai akai duk iyakar bakin qoqarinshi naganin ya daidaita nutsuwarshi abin ya faskara, jiyake kamar zuciyarshi zata tsinke saboda gudu

habeeb dake gefe yana playing piano yana lura da yanayin Deen dukda bakowa zaiyi saurin fahimtar uneasiness din nashi ba amma shi yagane don yasan Deen yasan yadda yake aikinshi, dole akwai Abinda yake damunshi


dukda Deen nadan kallon gefen zee saidai baya wani tsayawa kallonta don shi kanshi ba Acikin nutsuwa yake ba bare har yatsaya kallon wani abin

aymaan duk Abinda ake idanunshi nakan zee yana lura da halin data shiga

ahankali yaga tamiqe tsaye daga kujerarta tana kallon Deen daya juya mata baya

shima Deen sai akayi daidaitoni ya juyo side dinta cikin waqar yana ambaton birthday girl

sauke idanunshi yayi kanta tana atsaye tana kallonshi shima

wani irin bugu zuciyoyinsu sukayi lokaci guda dukda basu tantance juna ba don zee bata hangenshi sosai saboda hular kanta shima bega fuskarta ba sosai saboda boye rabin fuskar da hular tayi

ahankali ya cigaba da waqar yana kallonta zuciyarshi na lugude


_Happy Happy birthday... to... you..._

yaqarashe baitin da daddaya lokacin da zee tasa hannu tazame hular kanta tafada baya


cak numfashin su biyu ya dauke na wucin gadi

kallon juna suke kamar idanunsu zasu fado Babu mai iya kwakwarar motsi acikinsu

tsit wajen ya dauka kowa idanunshi akansu

jikin Deen ne yafara rawa yadago hannu yana nuna zee da yatsarshi dake rawa lips dinshi ma na rawa as well

"Z... Zainab?.." yafada cikin wata iriyar murya


ko motsi zee batayi ba Kuma ko kyaftawa idanunta dake kanshi basayi

ahankali yafara kusantota still yana nunata jikinshi na rawa har lokacin

"Zainab.."

ahankali kowa yafara tashi daga saman seat dinshi kowanne idanunshi akansu harda habeeb shima da besan meke faruwa ba


ahankali zee tafara takawa tanayin baya baya ganin yana kusantota

kallo daya zakayiwa su biyun kasan babu wanda kecikin hayyacinshi

"Zainab.. stop, please" yafada ganin tana qara nisantarshi

"stop!" yafada yana nufota da sauri kamar mahaukaci

saurin juyawa tayi kamar wanda abin tsoro yabiyo tana tattare rigarta tayi hanyar barin garden

"No! Zainab!" inji Deen yana maramata baya

"Balarabe!" inji habeeb yana takema Deen baya shima


------


saukowa yayi daga cikin motar ya maida kofar yarufe

hannu yasa ya gyara red guntun necktie dinshi sannan ya zagayo ta dayar 6aren motar

bude back seat yayi yadan zira jikinshi ciki can saigashi yafito riqeda abu ahannunshi

maida kofar yayi yarufe yama kulle motar gabadaya sannan yajuyo

dago abin hannunshi yayi yana kallo

qaton bunch of flowers ne mai glass vase daga qasa wajen mariqinshi

misalta kyawun flowern 6ata bakine saidai masu karatu suyi hasashe da kansu saidai kallo daya xakayi mata kasan tsaddadiyace ta qarshe

murmushinshi na gefen baki ya su6ucemashi lokacin dayakai hancinshi jikin flower din ya sinsina

qara riqeta yayi dakyau sannan yafara takawa cikin takunshi ta qasaita ya nufi Inda yake kyautata zaton nan ake taron

tafe yake yana saqe saqen yadda zata kaya tsakaninsu don yasan akwai chakwakiya agaba

yana cikin saqe saqenshi yaji kamar hayaniya na kusantoshi

dagowa yayi wanda yayi daidai da bangajeshi da akayi

baya baya yayi cikin ikon allah kuma yasamu ya tsayar da kanshi

saurin juyawa yayi yabi figure din daya wuce dagudu da kallo

dukda wulgin mutum Kawai yagani amma yagane itace

juyowa yayi yaga meya biyota saidai kafin yayi hakan yaji anqara bangajeshi again wanda hakan yayi sanadiyar su6ucewar flowern hannunshi ta fadi aqasa jikake tassss! tayi qarar fashewa

cikin zafin nama ya damqi gefen rigar wanda ya bangajeshin ya maidoshi baya daqarfi daga yunqurin yin gaba dayakeyi


dagowa sukayi atare suka kalli juna lokaci guda oily eyes dinsu na sarqewa ana juna....✍�


*please masu kirana ina typing kuna maidomin aiki baya, koyaya nadaga kafin nagama wayar Abinda narubuta ya fece shiyasa ma bana dagawa, please ku dinga yin haquri tunda ku ma kunsan inamuku iya qoqarina*


Ummin Fasihu🧚🏻‍♀�
8/2/21, 9:44 PM - Buhainat😝: *🙍🏻‍♂️DEEN🙍🏻‍♂�*


*084*


*THE REUNION*


wani irin jada baya su biyun sukayi kamar wadanda aka tura da force mai qarfi


alokaci daya suka sake wara oily eyes dinsu akan juna suna kallon juna kamar suna ganin wata hallita daban ne ba mutum ba

wani irin rawa inner part dinsu ya dauka zuciyoyinsu na wata iriyar halbawa kamar zata faso qirjinsu


habeeb ne yafara qarasowa wajen saidai babu shiri yaja wani irin mugun burki lokacin dayayi tozali da Deen guda biyu suna kallon juna


dauke numfashinshi yayi yana wani irin kwalalo idanu waje kamar zasu fado daga socket dinsu

daidai nan kingin jama'ar suka qaraso wajen Inda suma sukaci karo da the same scene

suma anan suka taka burki suna kallonsu kowanne speechless

wani irin gasping Aysha tayi mai sauti tana yin baya baya

aymaan dake bayanta yayi saurin tarota daga faduwar datayi niyyar yi tafado jikinshi

"Hey.." inji aymaan yana kallon yadda take farfar da idanu

mummy ce data lura dasu tayi saurin qarasowa wajensu itama takama Aysha din da kejin kanta na juyamata

ganin hakan yasa itama umman Ahmad matsowa sai aymaan ya sakarmasu ita


ahankali Mussadiq yaqara jabaya still idanunshi dasuka fara sauya launi akan Deen, komai na jikinshi rawa yake ga jijjiyoyin kanshi dasuka fito rad'o rad'o


cikin kidima da fitar hayyaci yasa hannu yazaro wata qaramar pistol from nowhere ya nuna Deen da haryanzu yakasa motsi daita


yadda jikinshi ke rawa haka hannunshi dake riqeda bindigar keyi don saima yitake kamar zata silale dukda iyakar qoqarin dayakeyi na riqeta sosai


"w..who are you?" yafada cikin wata iriyar murya dake rawa sosai

duk buda idanu mutanen wajen sukayi suna kallonsu cikin kidima

"speak or I shoot!" inji Mussadiq cikin qaraji jikinshi na rawa sosai yana qara nuna Deen da bindigar, kallo daya zakamashi kasan baya cikin hayyacinshi don ko cewa akayi ya danna kunamar bindigar baya iyawa saboda rawan da ilahirin jikinshi keyi

shikau har lokacin Deen kasa ko kwakwarar motsi yayi Kawai yana tsaye ne yana kallonshi kamar gunki

rolling idanu aymaan yayi cikin zuciyarshi yana cewa
'ai dama nace wannan mutumin mahaukaci ne'


"mu..Mussadiq"

"speak!" Mussadiq ya katse Ahmad daya fara magana

"Mussadiq calm down.."

"go away!" yafada yana maida akalar bindigar kan Ahmad

"listen son.."

"who are you? kusu wanene!"
yaqara fada yana pointing dinsu duka yana jabaya, sosai alamun gigita ta bayyana ajikinshi


ahankali bindigar ta su6uce a hannunshi dake karkarwa ya cigaba da kallon Deen yana haki

"calm down son.. calm down, this is your twin.. Mujaheed" inji Abbu dake qoqarin calming dinshi down

dago rinnanun idanunshi yayi ya kalli abbu

"yes, Mujaheed.. your lost brother"

"No.." inji Mussadiq cikin muryar mai kama da rad'a

"yes.."

"he's dead" yaqara fada

"he's alive"

"No"

"calm down"

"No.. No!" yafada yana dafe kai

"Mussadiq.." inji Abbu again yana qoqarin kusantoshi

"No, don't come closer.. don't" yafada yana jada baya

duk tsayawa sukayi suna kallonshi

saurin juyawa yayi cikin sassarfa zai bar wajen sai gani sukayi timm yafadi aqasa


gasping mutanen wajen sukayi sukayi saurin nufarshi

dagoshi sukayi sukaga kamar ma baya motsi

"aymaan quick kawo mota" inji Abbu

juyawa aymaan da be motsa daga Inda yakeba tundazu yayi yanufi parking space Ahmad kuma yanufi Deen dahar lokacin baya motsi kamar wanda aka dasa

"Deen" yafada yana ta6a kafadarshi saidai beko dago bayan bare ya kalleshi, idanunshi nanan kyar akan Mussadiq

habeeb ma yana daga baya kusan shima suman tsayen yayi don yakasa motsawa daga Inda yake saidai ya kalli wannan ya kalli wannan atsakanin Deen da Mussadiq


aymaan ne ya qaraso da motar wajen yafito da taimakonshi aka daga Mussadiq aka sakashi abayan mota tareda Aysha da itama tuni tasuma

aymaan yashiga front seat dashi da Abbu

yayinda Ahmad yaja hannun Deen suka nufi motarshi shima yasakashi a front seat habeeb yayi saurin binsu yashiga backseat shikuma Ahmad yazagaya mazaunin driver

ganin hakan yasa su kingin suka shiga wata motar Inda akabar ummy datace zata tsaya tareda zee agidan

ajere motocin suka fita daga gidan suka halba titi


***


dagudu zee tayi hanyar stairs tana hayewa da bibbiyu bibbiyu

ba don allah ya tsareba data sha qasa yadda rigar keta tadeta tana kawo mata tirjiya a gudun nata

bata ja burki akoina ba sai dakinsu Inda tashiga ta maido kofar tarufe ta danna sakata sannan tanufi toilet dagudu shima tabude tashige tarufo harda murza makulli.


komawa tayi ta jingina da kofar tana maida numfashin gudun datayi

_Deen_

_Deen dinta tagani_

_Deen dinta_

hannu bibbiyu tasa ta toshe bakinta dasu tareda silalewa qasan tiles

wani irin kuka yazo mata mai tsuma zuciya tashigayi hannunta toshe da baki dukkan ilahirin jikinta na gab gab


kuka take da dukkanin zuciyarta jikinta na rawa sosai, she can't believe yau idanuwanta Deen suka gani, Deen dinta, her timid, silly boyfriend. wanda ta yanke qauna dasake sakashi a ido.

zuciyarta takasa yarda, kwakwalwarta takasa dauka.

bugun kofar dataji ne yasata dan tsagaitawa daga kukan datake

kofar dakin ake bubbugawa ana kiran sunanta

data saurara saitaji muryar ummy ce

sosai take bubbuga kofar tana kiranta tazo ta bude

maida kanta zee tayi jikin kofar ta lumshe idanu wasu hawaye nasake gangaro mata

tanajin ummy nata haukan bubbuga kofar da kiran sunanta amma takasa koda motsi ne bare ta iya tashi ta budemata


***


tsaye yake yana kallon Mussadiq dake kwance bisa gado ta glass kofar dakin a gefe guda kuma yana sauraron Dr dakemusu bayyanin cewa yanzu komai normal dama shock ne kuma lokacin dazai farka zai sakeshi komai zai koma daidai

haka ya tsaya yana kallon photocopy dinshi dake kwance ko kyaftawa babu kwakwalwarshi ta hargitse ta yamitse yarasa wane tunani ma zaiyi

"Balarabe" muryar habeeb tadawo dashi daga duniyar kallon Mussadiq

dagowa yayi ya kalleshi saikuma ya maida kallonshi akan mutanen wajen yana binsu da kallo one after the other

mutane biyu Kawai ya iya shaidawa acikinsu, daddy da mummy

yarasa meke faruwa, meyasa yake gane gane, wane irin mafarki ne wannan harmutsatse?

dafarko yaga Zainab, macen da yasan qila harya mutu bazai qara ganinta ba

yazo kuma yaga wani mai irin kammaninshi sak yadda kasan kanshi yake kallo a madubi

yanzu kuma mummy da daddy wadanda shidai a Nigeria yasansu, to meke faruwa ne? wannan wane irin birkittacen mafarki ne mai dogon zango? yaushe zai farka? yakamata mafarkinnan yaqare hakanan tunkafin kwalwarshi tayi bursting

suma shi suke kallo cikin tausayawa halin dayake aciki don kallo daya zaka mashi kasan tsabar taurin rai ne Kawai yakeyi

mammaki ma suke yadda shi ya iya jurewa be suma ba, idanma sumar ne aishi ya cancanci yayita tunda shi kwata2 besan komai ba, everything just came at sudden ne, besan yanada yan uwa ba, besan shi twin bane, besan yanada iyaye bayan wadanda yasan sun rasu ba sa6anin su Mussadiq dasuka san dashi

maida kallonshi akan habeeb dake kallonshi

yasan mafarki be dakatuwa harsai yaqare amma bazai iya dauka ba kuma soyake ya farka ko ya bar wannan page din na mafarkin

ahankali ya matsa kusada habeeb yakama hannunshi yariqe gamm yana kallonshi

"habeeb ka fiddani daga nan, ka kaini wajen kaka"
shike maganar amma saiyaji kamar bashi ke motsa bakin ba, ganin komai yake amafarki

shiru habeeb yayi yana kallonshi yama rasa Abinda zaice mashi

"habeeb wani irin mafarki nakeyi, don allah ka tasheni ko ka fiddani daga nan" tasake fada yana Jin kanshi soo empty

wani irin tausayinshi ya tsirgama mutanen wajen suna kallonshi cikeda tausayawa

"nima mafarkin nake Balarabe, wai ka rabe gida biyu" inji habeeb cikin yin qasa da murya, kallo daya zakamasu kasan they're totally confused


"nima, nima naganni agabana, gani tsaye gakuma wani nidin agabana, kuma.. kuma naga Zainab.. Zainab dita, mubar nan habeeb... kwalwata zata fashe"


"Kamal" muryar mummy ta katseshi

juyowa sukayi suna kallonta babu ko kyaftawa harta qaraso gabansu

idanunta sun duri ruwa sosai tausayinshi ke tsuma zuciyarta

"Kamal ba mafarki ba kake, this is real"tafada tenderly


kallonta yakeyi Babu ko kyaftawa

"mummy?" yafada ahankali kamar maison jingina dagaske ita dince

kada mashi kai tayi hawayenta na gangarowa

"eh son, mummy ce. mummyn Zainab. it's real...taho taho ka zauna" tafada tana jan hannunshi tanufi kujera

binta yashigayi kamar rakumi da akala har ta zaunar dashi sai binta da ido yake

"Kamal this is real, ba mafarki bane, nice.. mummyn Zainab, wancan kuma daddy, ka tuna? kuma dagaske kaga Zainab kuma dagaske ku biyu ne masu irin kammaninka, kai tagwaye ne"

kafeta yayi Kawai da idanunshi yana kallonta confused

"iyayenka basu rasu ba, mahaifinka ne Kawai yarasu amma mahaifiyarka nanan, tana nan da ranta, wancan kuma twin dinka ne, kaine Hassan shine Hussain, bayanshi kuma kanada qanwa Aysha duk suna nan Dubai ne, kaima saceka akayi tun kana qarami aka kaika Nigeria amma kai ba dan Nigeria bane, kai Balarabe ne, Dan saudia, mahaifinka mutumin saudiya ne mahaifiyarka kuma yar misra, Kaka ba kakarka bace bakada alaqa daita, ga danginka nan suna nan, saceka akayi.."

kuka ne yaci qarfin mummy tashigayi da dukkanin zuciyarta

bama ita kadai ba babu wanda babu kwalla a idanunshi idan ka cire Deen daketa kallon bakin mummy tunda tafara magana

cikin kuka mummy tace
"Deen ba sunanka Kamaldeen ba sunanka Mujaheed.. Mujaheed Al-hassan shikuma twin dinka Mussadiq Al-hassan, kai Balarabe cikkaken Balarabe ne Kamal"


batool datakasa jurewa ta rungume umman Ahmad dake kusada ita batareda tasani ba ta cigaba da rusa kukanta kamar ranta zai fita

"eh Deen, kai asalinka Balaraben saudiya ne, duk acan mahaifanka suke, acan aka haifeka dakai da Dan uwanka Mussadiq saidai shekararka uku aka saceka aka kasheka ashe baka mutu ba, qila Kawai wucewa dakai akayi aka nuna an kasheka saigashi ankaika Nigeria. mahaifinka yarasu amma mahaifiyarka nanan tana cikin garin nan yanzu haka" inji Abbu shima cikin kwantar da murya

bin Abbu shima Deen yake da ido Kawai becewa komai Kawai kallon motsin bakinshi yakeyi

"daga baya muka gane hakan, wannan dalilin yasa muka quduri aniyar hadaka da danginka, shine ma dalilin zuwanmu Nigeria lokacin daka fara ganinmu, babu wani aikin daya kaimu, kai ka kaimu Deen kuma bawai saboda aiki yasa muka gayyatoka nan ba mun gayyatoka ne don hadaka da ahalinka da bakasan dasu ba" inji Ahmad da shima idanunshi suka rine

aymaan sai kallon Deen yake shima da jajjayen idanunshi yakasa cewa komai

saida Deen yagama sauraronsu tsab sannan ya maida kallonshi kan mummy da har lokacin hawayen idanunta sukaqi tsayawa

"Kaka..." yafada ahankali kamar mai rad'a

"ku kaini wajen Kaka don allah" yafada yana kallonsu cikin wani yanayi

hawayen mutanen yakasa tsayawa ganin yadda yake magana so confused kamar dan shekara biyun daya 6ata tsakiyar hanya yana gantali

Abbu zaiyi magana aymaan ya katseshi

"No Abbu.. zaku fasamashi kwalwa, don't stress his brain futher, yana buqatar hutu, idan kuka takura za'a samu matsala"

saikuma ya kalli Deen

"kanason zuwa wajen Kaka?"

saurin kadamashi kai Deen yayi kamar qaramin yaro

"taso to, taso nakaika" yafada yana miqamashi hannu

Dan tsayawa yayi yana kallonshi saikuma ya miqamashi hannu ya tadashi aymaan yayi gaba jaye da hannunshi suka fice daga wajen

wani kukan batool taqara rushewa dashi, bama ita kadai ba harda sauran matan dakin, mazan nema masu dan tauri taurin rai iyakarsu hawaye kowa jikinshi yayi sanyi lakwas

jikin daddy yafi nakowa yin sanyi, ganin Deen a irin wannan yanayin ba qaramin sanyayamashi jiki yayi ba, yarasa Inda zai tsoma ranshi yaji sanyi


habeeb dai haryanzu bece komai ba saidai alamu sun nuna shi ya gamsu da bayyanansu don they make sense to him don shima yadade yana zargin Deen ba bahaushe bane, komai nashi sak na larabawa dukda hasken fatarshi ba irin fauu dinnan bane irin na kajin jikin kajin turawa amma dai daka ganshi kaga ruwan Arab


haka suka zauna jigum har aymaan yadawo

duk dagowa sukayi suka kalleshi

"anyi mishi allurar barci to settle his brain" Abinda Kawai ya iya fadamasu kenan

duk Ajiyar zuciya suka sauke kowa najin zuciyarshi da ruhinshi badadi


daga baya ne suka yanke shawarar yakamata wasu sukoma gida wajensu ummy


Abbu da umman Ahmad da abban Ahmad suka tafi sukabar mummy, daddy, batool data maqale sai aymaan da Ahmad suka kwana a asibitin.


💜💜💜💜💜💜💜💜💜💜💜💜


ahankali yafara bude idanunshi dasukayi mashi mugun nauyi

dafarko biji biji yafara gani kafin daga baya ganinshi yafara yin clear


ahankali yake bin dakin da kallo cikin son tuna inane wajen

shikadai ne kwance adakin, ganin yanayin dakin yasashi gane a asibiti yake

ahankali yakai hannu yadafa kanshi dake mishi ciwo

ahaka yasamu ya lalla6a yamiqe zaune

cigaba da bin dakin yake da kallo cikin son tuno Abinda yafaru

ahankali abubbuwan dasuka faru jiya suka shiga dawomashi tiryan2

shiru yayi confused, abin tambaya anan shine dukkan wadannan abubbuwan mafarkine ko dagaske yafaru, idan mafarkine meya kawoshi asibiti harya kwanta?


yana cikin wannan saqe saqen aka bude kofa aka shigo

dagowa yayi ya kalli kofar sai suka hada idanu da mummy

wani sanyayyan murmushi ta sakarmashi tana qarasowa ciki nan kingin mutanen suka ida shigowa

da daddaya yake binsu da kallo yaga duk mutanen jiya ne, kenan hakan na nufin ba mafarki ba yake?

"sannu.. ya jikin?" inji mummy tana masa murmushi tenderly

shima murmushinshi yayimata asanyaye sannan ahankali yace
"alhamdulillah"

aymaan ne yashigo Ahmad biye dashi sai habeeb abayansu

duk da idanu yabisu yana tuna every bit of conversation dinsu na jiya

saurin qarasowa wajenshi habeeb yayi cikin murnar ganin ya farka

"Balarabe" yafada yana kallonshi

Dan murmushi Deen yayimashi shima yana kallonshi

"ya jikin?" ya tambaya

"alhamdulillah" ya amsa mashi shima asanyaye


qarasowa aymaan yayi wajenshi shima

"sannu..akwai Abinda ke damunka ko kemaka ciwo"

ahankali ya girgiza kai
"No, just a slight headache"

"sannu.. zai daina insha allah..mummy adan bashi wani abu" inji aymaan


da to mummy ta amsa nan da tashiga hadamashi tea

duk shi suke kallo kamar t.v harta gama hadawa tabashi

amsa yayi yana godiya sannan yafara sha

yasha sosai sannan ya ajiye, nan ya buqaci yin sallah

habeeb ya rakashi bakin toilet yayi alwala yafito sannan yahau sallayar da har an shimfidamashi ya rama sallar asuba don lokacin har gari yawaye don takwas ma tawuce


duk fita sukayi lokacin dazaiyi sallar yarage saura habeeb Kawai da Ahmad

yana nan zaune ya idar da sallar aka bude kofar

atare duk suka dago suka kalli kofar don ganin mai shigowa

Aysha ce tsaye abakin kofar batool abayanta

hada idanu sukayi da Deen dake kan sallaya har lokacin

kafe juna sukayi da idanu yayinda bugun zuciyoyinsu ya tsananta

ahankali hawaye suka taru a kumburrarun idanun Aysha tana kallon yayan nata dasu

shima dai Deen kallonta Kawai yakeyi yana Jin wani feeling na alaqa mai qarfi gameda ita a zuciya da gangan jikinshi


"come in Aysha, come in and say hi to your brother" inji Ahmad dake kallonsu

dagowa tayi ta kalli Ahmad saikuma tasake kallon Deen dashima ita yake kallo har lokacin

dafa mata kafada batool tayi cikin qarfafa gwiwa hakan yasa Aysha fara takawa kamar wadda kwai ya fashemawa aciki ta nufi Inda Deen yake tana kallonshi

saida ta qaraso gabanshi ta tsaya suna kallon juna saikuma tayi qasa ta durqusa cikin daidaita tsayinsu tana kallonshi still

sake kafe juna da idanu sukayi na wani lokaci

ahankali Deen yasakarmata guntun murmushi

bin dimple din tsakiyar gemunshi Aysha tayi da kallo babu kyaftawa

"what's your name?" yafada ahankali

dagowa tayi tana kallon eyeball dinshi

"A..Aysha" tafada cikin rawar murya hawayen idanunta na gangarowa

"meyasa kike kuka?" ya tambayeta da harshen turanci

saurin goge hawayen tayi tana girgiza kai
"n..na daina" tafada cikin muryarta dake a disashe

murmushi yayi shima idanunshi na chanza launi

miqomata hannu yayi

kallon hannun tayi saikuma ta dago hannunta ahankali tasaka acikin nashi ya riqe gamm wani feeling na jini na yawo ajikinsu

"dagaske ke qanwata ce?" ya tambaya ahankali yana kallonta

wasu hawayen suka gangaromata tana kadamashi kai dasauri

"dagaske ni twin ne kuma... kuma inada Mama?"

fadawa jikinshi tayi cikin kasa jurewa tafashe da kuka mai ta6a zuciya

"eh yaya.. kanada Mama..mai sonka, tana sonka sosai yaya..muma muna sonka yaya.. bamu ta6a mantaka ba daidai da second daya ba tun tafiyarka, meyasa katafi kabarmu?.. meyasa kabarmu da kewarka yaya? karka qara tafiya yaya.. karka qara barinmu.. muna sonka yaya"

kuka take sosai koina na ilahirin jikinta banda rawa babu Abinda takeyi, ta qanqameshi sai sheshekar kuka takeyi

ahankali Deen yasa hannu ya zagayo bayanta ya rungumeta shima batareda ya iya cewa komai ba sai sauraron bugun zuciyoyinsu

abin haryanzu bebar yimashi kama da mafarki ba, wai shikeda family, shikeda qanwa, shikeda mahaifiya

lumshe idanu yayi yana sauraron sautin kukan Aysha yana Jin yadda kukan ke ta6amashi zuciya

ahankali yaqara bude baki yace
"stop crying.. please"

kamar cewa yayi taqara saita qara rushewa da kuka tana qara cusa fuskarta a qirjinshi

Ajiyar zuciya ya sauke sannan yabude jajjayen idanunshi ahankali

"am here now, I promise bazan sake tafiya ba" ya tsinci kanshi da fadin haka

qara fashewa da kuka Aysha tayi tana qara qanqameshi kamar zata shige jikinshi

shima qara rungumeta yayi zuciyarshi na melting

babu wanda zuciyarshi bata motsa ba don masu saurin kuka irinsu batool harsun bude shafi

kamar ance yadago sai suka hada idanu da Mussadiq dake tsaye bakin kofa yana kallonsu

kafe juna da kallo sukayi kamar sunsamu t.v

shima Mussadiq idanunshi sunyi jajur sun dan kumbura harda lips dinshi

yanzu babu coat ajikinshi sai t-shirt din ciki kamar dai Deen

ahankali Deen yadaga Aysha daga jikinshi idanunshi still akan Mussadiq

komawa gefe Aysha tayi tana kallon yayyen nata biyu tana hawaye

cigaba da kallon juna sukeyi babu mai ko kyaftawa

ahankali Deen ya dago hannunshi ya miqoma Mussadiq

binshi da kallo Mussadiq ya cigaba dayi batareda ya motsa ba

kowa na dakin shi yake kallo yaga me zaiyi

Deen be sauke hannunshi ba kuma be janye idanunshi daga kanshi ba

ahankali Mussadiq yashiga takowa yana tunkaro Deen harya qaraso gabanshi

kallon hannun da Deen ke miqomashi yayi yana tuna kalamansu daddy

*Mujaheed be mutu ba, yana raye kuma yadawo gareku*


maida kallonshi yayi akan fuskar Deen yana kallo sannan ahankali kamar wanda ake controlling da remote yadago hannunshi ya dora akan na Deen

wani irin electric feeling ya tsirgamasu gabadaya ilahirin jikinsu

zubewa Mussadiq yayi on his knees the next minute sai gani mutanen dakin sukayi sun qanqame juna cikin wata iriyar wawiyar runguma


"Mujaheed.." Mussadiq yafada cikin wata iriyar murya kamar ba tashi ba


"Mussadiq.." inji Deen shima cikin rawar murya

wasu hawaye masu zafin gaske suka gangaromasu alokaci daya suna qara qanqame juna


"Mujaheed..😭"


"Mussadiq😭"...✍�


Ummin Fasihu🧚🏻‍♀�
8/2/21, 9:44 PM - Buhainat😝: *🙍🏻‍♂️DEEN🙍🏻‍♂�*


*085*


*THE REUNION*


sun jima ahakan rungume dajuna kamar zasu shige jikin juna, feeling dasukeji yana tasomasu daga zuciya zuwa ilahirin jikinsu is unexplainable


ahankali suka raba jikinsu dana juna suka hade goshinsu waje guda kowanne na mayar da numfashi

dago wet eyes dinsu sukayi atare suna kallon juna batareda sun iya cewa komai ba

"I thought you're gone..forever" inji Mussadiq cikin muryar rad'a daidai wasu hawayen naqara gangarowa daga idanunshi

kasa cewa komai Deen yayi sai hannu daya daga yayi cupping fuskarshi

"the memory is still fresh Mujaheed.. nakasa mantawa..lokacin..,lokacin dasuka sakaka amota suka tafi, nan kadai nake iya riqewa.. nasan ya isa na manta saboda dadewa da shudewar shekaru.. amma nakasa.. nakasa
kullum sai wannan scene din yazomin a mafarki.. kullum sainayi mafarkinka da yadda aka rabamu..." in between kuka Mussadiq ke wannan maganar

"ashe zaka dawo? ashe zanqara ganinka?.. kasan yadda rabuwarmu tayi affecting dina? kasan yadda rayuwata ta chanza bayan tafiyarka?"

shidai Deen kallon yadda yake kuka sosai yake shima hawayenshi naqin tsayawa, besan meyake magana akai ba don shi betuna komai ba amma kalamanshi ba qaramin ta6amashi zuciya suke ba bare yadda yaga yana kuka sosai kukan da kallo daya zakayimashi kasan daga qasan zuciya yake tahowa

shima Mussadiq grabbing fuskar Deen yayi

"ina kashiga all these years? meyasa katafi kabarmu? karka qara wannan gangancin kaji? if you do I'll kill you" yafada yana riqe fuskar Deen sosai

murmushi suka saki atare suka sake rungume juna

"I won't, I promise" inji Deen yana qara rungume Mussadiq

Aysha dake gefe itama ta rarrafo wajensu ta rungumo bayansu

atare suka dago suka kalleta da wet eyes dinsu sai suka sakarmata murmushi suka sake rungume juna su ukun suka hade kansu waje guda


kowa na dakin share hawayen farinciki yake kowa murmushi a fuskarshi mai nuna farinciki dasuke ta
ya wadannan bayin allahn


sun dade ahakan sannan suka saki juna kowanne murmushi afuskarshi

sai a lokacin suka lurada yadda mutanen dakin suka qara yawa don harda su mummy adakin

da kallo duk suka bisu suna kallon yadda suke masu murmushi kowanne farincikinshi yakasa 6oyuwa

suma murmushin suka maida masu atare fuskarsu na nuna how grateful they are

kafin wani yayi magana acikinsu wani Dr yashigo dakin riqeda waya

sallama yayi sannan yace
"wannan wayar tunjiya ake kiranta, a dayan dakin muka tsinceta"

duk kallon wayar sukayi

"akhie, your phone" inji Aysha

Jin hakan yasa Mussadiq miqa hannunshi Dr din yabashi, saida yayimashi alamun thank you da ido sannan ya maida hankalinshi akan wayar, lokacin harta tsinke

wani murmushi yayi sannan yadago yakalli Deen dake kallonshi

"it's ummie" yafada yana nunamashi screen din wayar

gaban Deen yafadi saidai bece komai ba sai cigaba da binshi da kallo dayayi ganin yana re-dialing number

handsfree yasa shiyasa kowa na dakin kejin sautin ringing din alamun tashiga

bugu uku tayi aka daga

cikin wata kamillaliyar murya mai sirki da yanayin damuwa akayi sallama ta dayan bangaren

gaban Deen yasake yankewa lokacin da muryar tadaki kunnenshi sai kallon wayar yakeyi kamar yana hango mai maganar ta cikinta

amsa sallamar Mussadiq yayi cikin wata murya mai cikeda annushuwa yana gaidata da harshen larabci

bema ida gaisuwarba ta katseshi itama cikin harshen larabci da
"Mussadiq ina kake? dama kabaro Australia? nayita kiran numberka tacan bana samu, yaushe kadawo? kuma kasan jiya Aysha bata dawo ba? gidan wannan qawar tata taje birthday dinta tun yamma amma haryanzu bata dawoba gashi wayarta bata shiga, ina cikin damuwa sosai Mussadiq gashi kaima naita kiranka baka dagawa"

tun sadda tafara magana Mussadiq keta murmushi yana kallon yanayin fuskar Deen dayayi kasaqe yana sauraron yaren da ummie keyi, yasan larabci ne amma besan metake cewa ba don bayaji kwata2 sai dan wanda ba'a rasaba wanda suke dan tsinta a islamiyya

kallon wayar Kawai yakeyi yabata dukkan hankalinshi yana sauraron muryar da akecewa ta uwarshi ce

dafa kafadarshi Mussadiq yayi still yana murmushi sannan ya amsa ma ummie

"ummie muna tare daita" yafada yana kallon Aysha dake sauraronsu itama

"kuna tare? yaushe kadawo harkuka hade?" inji ummie adayan 6angaren a mammakince

"jiya.. karki damu gamunan zamu taho yanzu and guess what" yafada yana kallon Deen

"what" inji ummie

"zamu tahomaki da wani Abinda bazaki ta6a mantawa ba" yafada yana kallon Deen yana murmushi

"menene abin?" inji ummie

"sai munzo Kawai, gamunan"
daga haka saiya katse kiran

dagowa yayi ya kalli Deen daya maidashi t.v tundazu

murmushi yayi mashi
"are you ready to see your ummie?" yafada yana mashi murmushi

gaban Deen ne yaqara faduwa

"I..don't know" yafada ahankali

murmushi duka yan dakin sukayi

"c'mon akhie, just calm down, we'll be there for you and you'll like her I assure you" inji Aysha

kada kai Kawai Deen yayi saidai he's very nervous

zaije ganin wata kuma wai mahaifiyarshi, shida ya girma da tunanin baida mahaifa amma yanzu wai mahaifiyarshi zaije gani, wannan tunanin nasashi Jin wani iri.


tashi Mussadiq yayi yaqarasa gabansu Abbu yana murmushin da ke nuna tsantsar godiya da hallarcin dasukayi masu

cikin turanci yafara magana
"bansan ta ina xanfara ba amma inaso kusani ko za'a tara dukkan kalaman duniyar nan babu wadda zatayi daidai da bayyana maku irin godiyar damuke muku, allah kadai zai iya sakamaku Abinda kukayi mana"

duk murmushi sukayi abbu yace
"mu godewa allah son, allah shine yanufi hakan zai faru, allah shine abin godiya"

dik kada kai kingin sukayi

atare kuma suka furta alhamdulillah cikin tsantsar nuna godiyarsu ga allah subhanahu wata'ala


"zamuje gida, inaso kubiyomu don allah" inji Mussadiq din

yadda yazage yana magana cikin Kasa dakai da fara'a zai baka mammaki kamar ba wannan proud Mussadiq dinba mai ego


"eh to, bazamu ce A'a ba saidai ba dukkanmu zamuje ba, as you can see anan ma bamuda yawa don su daddy sun koma gida dazu saboda wata yar matsalar data taso, so muma munason zuwa can ne amma aymaan da Ahmad suna iya binku, muma lalurace zata hana hakan" inji Abbu

basuji dadin hakan ba amma basuce komai ba

"Ahmad ina aymaan?"

"yana office I guess" inji Ahmad

"to kayimashi magana kace yabiku injini"

"to shikenan Abbu"

"abbu don allah batool tabimu? pleeease?" inji Aysha cikin marairaicewa

kallonta Abbu yayi saikuma ya kalli batool itama ta shagwa6e fuska

"alright then" inji Abbu

dadi sukaji wanda hakan.ya bayyana a fuskarsu

"yanzu bari mu mutafi"

da addu'ar tsari suka bisu suka fice suka bar daga Deen sai Mussadiq, Aysha, batool, Ahmad da habeeb

anan Ahmad yafita don nemo aymaan shikuma Mussadiq yafiddo wayarshi yayi kira

a office dinshi yasameshi tareda Abbu

yanayin dayaga fuskar aymaan yasa yasan maganar me Abbu kemashi

"kajini ko?"

"to Abbu" inji aymaan fuskarshi na bayyana rashin jindadin shi

"to saikun dawo mu muntafi" inji Abbu yana yin hanyar fita

da addu'ar tsari suka bishi harya fita sannan Ahmad yajuyo kan aymaan da ranshi ke a6ace

"meye fa'idar binsu din?" inji aymaan afusace

"su suka buqaci hakan"

"su wa?"

"Mussadiq"

"mtcheew, idan mukaje me xamuyi musu? ni wlh banason irin wannan tunda anyi mai wuyar ba shikenan ba?"

ta6e baki Ahmad yayi yace
"wannan Abbu ya kamata ka fadamawa mallam, saida yatafi sannan zakaita.tada jijiyoyin wuya, wannan ai ihu bayan hari ne"


wata uwar harara aymaan ya makamashi yakoma ya zauna cikeda takaici

dariya Ahmad yayi yace
"saika shirya don't keep us waiting" yana kaiwa nan yafice

tsaki aymaan yaja cikeda takaici, sosai yaji haushin binsu dazaiyi don shi yanzu haka shirin tafiya gida yake don ganin wane hali zee take don tun jiya take ranshi daita ya kwana gashi ankawo mashi kwafsi

shi bega dalilin binsu ba, is not as if basusan hanyar gida bane, kwata2 bega amfanin binsu ba.

haka yaita dacin rai shikadai a office din yanajin kamar yayi bindiga


acan ward dinsu Deen kuwa Deen keta kallon Mussadiq daketa waya yana bada order daban daban

azahiri kallon Mussadiq yake amma a badini hankalinshi ma ba akanshi yake ba, tunaninshi yayi nisa daga duniyar dasuke ciki

jiyayi anja hannunshi hakan yasashi dawowa daga duniyar tunanin daya lula yakalli mai kama mashi hannu yaga Aysha ce tana mashi wannan cool murmushin nata irin nashi

shima murmushin ya maida mata yana damqe hannunta itama sukayi interlocking yatsunsu

ko mintuna shabiyar basu qaraba ordern da Mussadiq yabada suka iso

sabbin qannanun kaya ne kala biyu iri daya

kala daya ya dauka yaba Deen daya don shima ya chanza don duk kayan jikinsu sunyi squeezing

cikin dan qanqanin lokaci suka chanza suka fito

sakin baki mutanen dakin sukayi lokacin dasukayi arba dasu biyun ganin yadda suka fito a ainahin identical twins din

komai nasu daya baka ta6a banbancewa, Abinda ma yasa yan dakin suka iya babancesu shine sumar kansu Inda na Mussadiq yafi na Deen yawa, baya ga wannan Babu wani banbanci.

cikin qanqanin lokaci suka gama shirinsu sukayi shirin tafiya bayan wani Dr ya rubuta masu sallama.

atare duk suka fito Inda saida Ahmad yayi excusing kanshi don zuwa tahowa da aymaan.

saida aymaan ya6atama Ahmad rai da shiririta kafin yafito suma suka nufi parking space din

wata shegiyar danqareriyar mota qirar Lamborghini suka gani awajen Inda ganin habeeb agabanta yasasu sanin aciki zasu

dafarko aymaan yaso qin binsu cikin motar yace zai biyo bayansu Acikin tashi amma daga baya ya haqura saboda yadda Ahmad yaita lalla6ashi

duk sunyi wannan abin ne kafin su qarasa wajen motar

koda suka isa exchanging pleasantries sukayi tsakanin juna babu yabo babu fallasa suka shishiga motar Inda ta kwashesu duka saboda girmanta

koda wasa aymaan be kalli gefen Mussadiq ba kamar yadda shima hakan take a 6angarenshi

saima dai Aysha da idanunsu ke yawan hadewa Inda da hakan yafaru kowa zaiyi saurin kawar dakai


haka sukayi wannan tafiyar in silent for fifteen minutes kafin su isa unguwarsu Mussadiq.


tun a farko farkon unguwar zaka fahimci kashigo unguwar manyan mutane sakamakon manya manyan gidajen dasuketa wutowa

ahaka har motar ta tsaya a bakin wani tangamemen gate

basuyi one minute da tsayuwa ba aka wangale musu qaton gate din motar ta danna kai ciki.

tafiya sosai sukayi yadda kasan ba gidan suka shigo ba sannan motar ta tsaya.

guards ne takoina suka rurrugo suka tsaya agaban motar

acikinsu wani yabude musu kofar duk suka dare suna basu hanya don saukowa

da daddaya suka fara saukowa daga motar har suka gama fitowa

sosai mammaki ya bayyana afuskokin guards din lokacin dasukayi arba da Mussadiq da Deen

sai kallonsu suke dasun kalli wannan saisu kalli wannan saidai babu damar magana

"welcome home akhie" inji Aysha tana ma Deen daketa bin harabar gidan murmushi

Jin kalmar 'HOME' yasa Deen jin wani iri a zuciyarshi ga yadda bugun zuciyarshi ke qara tsananta at every passing minute

"shall we?" inji Mussadiq yana kama hannun Deen


daidai entrance aka kawosu so basai sunsha wahalar yin wannan uwar tafiyar ba don daga gate zuwa ainahin gidan akwai tafiya sosai

hakan yasa nan da nan suka isa bakin kofar shiga

doorbell Mussadiq ya danna sau biyu sannan yaqara juyowa yana kallon Deen da kejin wani uneasiness ajikinshi ga wasu gumin dasuka fara tsatsafomashi a saman goshi, tunda yake beta6a shiga halin nervousness irin na yau ba

murmushin qarfafa gwiwa Mussadiq yayi mashi yana dan bugun shoulder dinshi daidai nan aka bude kofar.

ganin Mussadiq yasa maid din data bude kofar saurin jabaya tana russunawa cikin girmamawa tana musu sannu dazuwa

shigewa yayi still riqeda hannun Deen suka shiga qayyataccen falon

daya bayan daya kingin ma suka shiga Inda aymaan ne qarshen shigowa

duk sannu dazuwa maid din dake cikin uniform takemusu cikin girmamawa har suka gama shigowa sannan tayi saurin qarasowa falon tana nunamasu wurin zama duk suka zazzauna and within a twinkle of an eye anfara shigomasu da kayan ciye ana diddirewa

Aysha taso yin sama dagudu tun shigowarsu amma Mussadiq ya hanata saidai ya tabbatar kowa ya zazzauna sannan yayi excusing kanshi ya haye sama domin iske ummie can.

tun bayan tafiyar ummie falon yadauki shiru, Deen dai a zaune yake amma baya cikin nutsuwarshi kwata2 don ko a yanayin yadda yaketa gyara zama zaka gane hakan

zuciyarshi bugu take kamar ganga jiyake kamar zai mutu saboda nervousness

ahankali yaturahannayenshi biyu tsakiyar cinyoyinshi dake amiqe ta takure yana kallon qasa


sunkusa mintuna biyar ahakan kafin sufara Jin tafiya natahowa daga saman stairs

bugun zuciyar Deen yaqara speed nan take gumi suka fara tsatsafomashi takoina

be dago ba amma yana jin yadda sautin tafiyar keqara kusanto falon ga faint voices dayakeji suna tunkarosu


duk daga kai mutanen falon dasuka qagara suga ummie sukayi banda Deen suna kallon su ummie dasuke saukowa daga stairs din

kallo daya wadanda basu ta6a ganinta ba sai yau sukayi mata suka san cewa tabbas itace ummie, ko mahaukaci ya laluba zai tabbatar saboda mugun kammanin dake tsakaninsu kamar tayi kaki

tundaga nesa tafara sakamasu murmushi tana saukowa Mussadiq abayanta

dukda bata shaida kowa ba acikinsu hakan be hanata tarbarsu da fafadan murmushinta ba har suka ida saukowa stairs din

cikin larabci tafara musu lale marhaban cikin sanyayyar muryarta datadan manyanta

tunda muryarta ta daki dodon kunnen Deen kanshi yaqara kwancewa, inner jikinshi yafara rawa ahankali

qara cusa hannayenshi yayi tsakankanin kaffafunshi yana matsesu cikin rikicewa.

ida qarasowa cikin dakin sukayi Inda Mussadiq yayiwa ummie masauki a kujerar dake facing dinsu

cikin larabci tashiga sake yimasu sannu dazuwa fuskarta fall fara'a

sosai tayimasu kwarjini hakan yasa duk suka sunkuyar dakai suna murmushi

dan rad'a Mussadiq yayimata akunne hakan yasata yin Dan dariya sannan cikin harshen turanci tasake yimasu sannu dazuwa tana tambayarsu sun iso lfy?

duk amsa mata suka shigayi cikin girmamawa suna gaidata daya bayan daya tana amsawa tana kallonsu

idanunta ne ya sauka kan Deen da har lokacin kanshi ke akasa ya makure wuri guda kamar maijin sanyi

Dan tsiramashi ido tayi sannan takalli Mussadiq dake kusada ita

cikin tsokana a harshen turanci don Mussadiq ya gayamata akwai wadanda basajin larabci tace
"shikuma wancan d'an nawa fa? tsoron mutane yake?"

yar dariya duk sukayi sai Mussadiq yace
"da alama"

shidai Deen bedago ba saima lumshe idanun dayayi yana sauraron bugun zuciyarshi

"d'ana? wai dagaske tsoron.mutane kake?" inji ummie tana kallonshi keenly tana lura da yanayi da dama dake kamanceceniya dana wani wanda tasani

haka Kawai taji itama zuciyarta na halbawa tun lokacin data dora idanu akanshi

soyake ya dago amma yakasa, tsoro yakeji yakuma rasa na menene

"ummie da alamu dai tsoronki yakeji" inji Mussadiq yana murmushi

"ni?" inji ummie a mammakince

"ga alama nan" yafada yana kallon Deen fuskarshi fall murmushi

sake kallon Deen da ina part dinshi kerawa sosai tace
"d'ana dago ka kalleni kaji?"


zuciyarshi ce tabada damm! lokacin dayaji ta kirashi da d'anta

ahankali yashiga dago kanshi kamar mai tsoro cikin bin umarninta harya ida dagowa

idanunsu ne suka sarqe dana juna wanda yayi daidai da bugawar zuciyarsu alokaci guda


kafe juna sukayi da idanu Inda Deen ke kallon fuskar mahaifiyarshi for the first time in his life yayinda ummie afarko kallonshi take blankly kamar wanda hankalinta yagudu na wucin gadi saikuma ahankali tadawo daidai

ahankali idanunta suka shiga warawa akanshi kamar kuma wanda aka tsikara tayi saurin juyowa ta kalli Mussadiq da har lokacin ke kusada ita


maida kallonta tayi akan Deen dahar lokacin kallonta yake babu kyaftawa atsorace saikuma taqara kallon Mussadiq

qara kallon Deen tayi dasauri sannan taqara kallon Mussadiq kamar wata zarrariya

ahankali tafara qoqarin tashi jikinta na rawa, ganin hakan yasa Aysha saurin qarasawa wajen tana riqota

juyowa tayi atsorace ta kalli Aysha din saikuma taqara kallon Deen ta kalli Mussadiq

"Aysha.. idanuna gane gane sukemin, gani nayi yayanki yakoma biyu" tafada cikin rawar murya tana qoqarin tashi

qoqarin maidata zaune Aysha tashiga yi tana cewa
"ki kwantar da hankalinki ummie..."

"yayanki biyu fa nake gani, ko idanuna sunfara lallacewa ne? kalla kigani ga wani can ga wani nan" tafada tana qara binsu da kallo kamar ta66a6iya

"eh ummie su biyu ne, nima nagani"

wani irin wara idanu ummie tayi

"kema kingani? kinga su biyun"

kada kai Aysha tayi tana qoqarin danne hawayenta
"eh ummie, aidama su biyu ne, dama su biyu kika haifa"

shiru ummie tayi tana kallonta saikuma tace
"eh subiyu na haifa amma ai yanzu daya ke akwai, wancan ya... ya..." saikuma takasa idawa sai juyawa datayi tana kallon Deen dake kallonta har lokacin zuciyarta na wata iriyar bugawa

kusada ita Mussadiq yazo ya duqa
"beyi komai ba ummie, beyi komai ba... gashi nan yadawo gareki"


kallon Mussadiq tayi shock all over her face

kada mata kai yayi
"yes ummie, Mujaheed dinmu beyi komai ba, gashinan yadawo, gashinan agabanki, yadawo garemu"

girgiza kai ummie tashigayi unbelievable jikinta na rawa sosai

"No" tafada unbelievable

"yes ummie Mujaheed is alive"...✍�


*I can't go futher, kuyi manage please banajin well🤒*


Ummin Fasihu🧚🏻‍♀�
8/2/21, 9:44 PM - Buhainat😝: *🙍🏻‍♂️DEEN🙍🏻‍♂�*


*086*


girgiza kai ummie tashigayi cikin rashin yarda, tayaya za'ace Mujaheed na raye bayan an tabbatar agaban idanun mutane ya qone cikin mota

"he was kidnapped ummie not killed, dama nasan Dan uwana bazai mutu hakanan ba, nasha ji ajikina akwai wani sashe na jikina a wani wuri, nasha jina incomplete, ashe shine kuma gashi cikin yarda allah yadawo, yadawo garemu ummie dawowa ta har abada" duk wannan maganar da Mussadiq keyi idanunshi nakan Deen dake kallon ummie still

itama ummie idanunta na kanshi tana Jin wani irin feeling mai qarfi na yawo a ilahirin jikinta

tashi Mussadiq yayi yaqarasa wajen Deen dake makure waje guda har lokacin yariqo hannunshi ya tadoshi tsaye sannan yanufo ummie

duk da kallo mutanen falon sukabisu dashi harsuka qarasa wajenta

jan Deen Mussadiq yayi qasa ya kasance sun duqa agaban mahaifiyar tasu

"Mujaheed ga ummie, ummie ga Mujaheed, rabonku da juna shekaru ashirin da uku kenan amma na tabbata koda bayan shekaru dubu ne kuka hadu bazaku kasa gane juna ba"

hawaye sosai kezuba a idanun ummie data kafe Deen dasu

shima Deen hawayen yakeyi involuntary yana bin fuskarta da kallo


hannu ummie tadaga ahankali tadora afuskarshi kamar mai tsoro, ahankali tashiga tatta6a fuskar

"Mujaheed?" tafada tana cigaba da tatta6a fuskarshi

"ummie.." Deen shima yafada ahankali

"Mujaheed"

"ummie na"

"Mujaheed na!" tafada daqarfi tana jawoshi ajikinta lokaci daya cikin fashewa dawani matsanancin kuka

wani irin warmness yaji lokacin data sakashi ajikinta, warmness din dabazai iya misaltawa ba

yasha samun warmness ajikin Kaka idan ta rungumeshi amma wannan na daban ne don sai jiyayi kamar yanarke su cigaba daxama ahakan saboda wani unexplainable sense of comfort dayakeji a jikinta

dama wannan ake kira da mother embrace?

kuka sosai ummie keyi tana magana at the same time cikin larabci, tariqeshi gagam kamar zata sakashi ajikinta

shima dai jiyake kamar yashige cikin jikin natan ne don shima gagam ya rungumeta

bayajin Abinda take cewa amma ga duk kalma daya dazatayi saiya amsa da kalmar 'ummie na'

kuka suke sosai su biyun kowanne uncontrollable

ahakan wani irin tari ya sarqe ummie tashigayi babu kakkautawa

Jin hakan yasa Deen raba jikinsu yadago yana kallonta sai yaga she's coughing blood, tana tari jini nafita abakinta

arude ya riqota ahannunshi jikinshi na rawa sosai

"ummie! no..No, ummie No!" yafada cikin ihun kuka yana dan jijjigata

da gudu kingin yan dakin suka qaraso wajensu cikin tashin hankali

"ummie kar kiyimin haka please! please stop am scared!" yafada cikin kuka sosai yana mannata ajikinshi not minding yadda jinin ya 6atamashi kaya

har lokacin tarin ummie keyi amma a mugun galabaice

Mussadiq kau tuni yatashi arude yakoma gefe yafara qoqarin lalubo number family Dr dinsu

aymaan ne yaqaraso gaban Deen yana qoqarin amsar ummie ahannunshi amma Deen ya matsa baya yana qara qanqameta

"No! go away!... ummie na" yafada cikin fitar hayyaci yana qara qanqame ummie din

"calm down ok? she's gonna be ok, kabari nadubata" inji aymaan ahankali

"No!" Deen yaqara fada cikin kuka sosai gani yake kamar sake rabasu za'ayi

"idan baka bari nadubata ba zamu iya rasata, ka duba kagani she's in a very critical situation, tama suma zamu iya rasata"

sai a lokacin Deen yafara dawowa hankalinshi saidai be saketan ba sai maida numfashin dayakeyi

"kabari a dubata before it's late, kun dade ba atare ba nasan yanzu bazakaso kuyi rabuwar har abada ba" inji aymaan again cikin persuading voice

maganar aymaan tashigeshi hakan yasa yafara nutsuwa

qara matsowa aymaan yayi kusada ita yana neman kama ummie din

"kawota na kaita saman kujera"

maimakon yabashi din saiya qara qanqameta yafara qoqarin tashi daita

"easy" inji aymaan yana dan tarosu ganin zasu fadi

da taimakonshi Deen yakaita kan dagowar kujerar ya kwantar saidai yaqi matsawa ko inch daga kusada ita saima bake wajen dayayi


"alright, kadan matsa nadubata" yafada gently

ahankali Deen ya matsa din amma hannunshi na riqe da nata gamm kamar wanda za'a kwacemawa

babu 6ata lokaci aymaan yafara dubata

ruwa da tissue yafara buqata

dagudu Aysha dake tsaye tareda batool sunci kuka sun godewa allah taruga ta dauko tabashi


amsa yayi yafara bata ba ummie taimakon gaggawa cikin qwarewa

Mussadiq daketa safa da marwa shima tsayawa yayi yana kallon aymaan don har lokacin Dr din daya kirawo be isoba


cikin qwarewa aymaan yashiga ceto rayuwar ummie


🤍🤍🤍🤍🤍🤍🤍🤍🤍🤍


zaune take takafe waje da kallo ta glass window dake kusada ita

kofin shayi ke hannunta wanda tuni yahuce ma don tunda aka bata kur6a biyu tayimashi takuma fita babinshi


idanunta na kafe akan window daya kasance glass ne don ana iya hango waje tarr ta wajen

kallo daya zakayi mata kasan bata awannan duniyar tamu kwata2


bude kofar dakin akayi ahankali aka shigo

Inda ta barta nan tazo ta sake taddata

girgiza kai Kawai tayi sannan tanufeta

zee batama san da shigowarta ba saida taji an dafata

saurin dagowa tayi daga duniyar tunanin data lula

ganin ummy ce yasa tadanyi murmushi tana kai kofin shayin da har yayi sanyi baki

murmushin itama ummy tayi mata taja kujera ta kawo kusada ita ta zauna

"daughter" takirata ahankali

dagowa zee tasake yi ta kalleta

"haryanzu baki shanye shayin ba?"

qara kai kofin zee tayi abaki ta kur6a dukda rashin dadin dayake mata gashi yayi sanyi

"gashinan ina sha ummy"

murmushi ummy tayi

"ai yama huce ko? mugani kinasonshi ahakan ko ahada wani mai zafin?"

saurin bata zee tayi cikin marairaice fuska tace
"ni nama qoshi ummy kalla kigani nasha dayawa"

kallon shayin da ba'asha ko kwata ba tayi tayi murmushi tace
"to shikenan yanzu tashi ki chanza daddy na qasa yana jiranki kutafi yawo"

nan take fuskarta tayi brightening

"dagaske?" tafada cikin zumudi

"dagaske, maza yi sauri kar yaita jira"

da sauri ta tashi cikin jindadi

dama tagaji da wannan zaman loneliness din tasan koyaya suka fita koda kaso kadan ne zai rage daga cikin damuwarta


wucewa bathroom din dakin tayi ummy tabita da ido cikeda tausayawa saikuma tadan girgiza kai sannan ta tashi tafita riqeda kofin shayin zee din


***


Ahankali tafara bude idanunta dasuka yimata nauyi

da farko biji biji tafara gani sai ahankali ahankali ganinta yafara dawowa

akan fuskarshi tafara sauke idanunta yana kallonta itama affectionately

lumshe idanu tayi akanshi tasake budewa and he's still there

hakan ya tabbatar mata ba mafarki bane kamar yadda tayi tunani

"ummie na" yafada ahankali yana qara damqe hannunta dake cikin nashi

idanunta ne suka fara qyallin hawayen dasuka fara taruwa a kwarin idanunta

girgiza mata kai yayi yana kai hannunta dake hannunshi saitin bakinshi ya sumbata yace
"don't ummie, you're sick, please no more tears.. am here"

ahankali takai hannun nata tashafi gefen fuskarshi daidai nan hawayen suka gangaro

dora nashi hannun yayi saman nata dake bisa kumatunshi yasa dayan hannun yana share mata hawayen


"ina katafi kabarmu?" tafada in tears

"bazan qara barinku ba" ya amsa mata

riqo fuskarshi tayi
"karka qara nisantarmu kaji? karmu sake haka dakai"

"har abada ummie.. har abada"


rungumeshi tayi cikin shauqin qaunar d'an nata mafi soyuwa a zuciyarta

shima rungumeta yayi yanajin kamar su dawwama ahakan

ahankali Aysha ma ta matso tayi joining dinsu ganin hakan yasa shima Mussadiq qarasawa suka rungume juna dukkansu in a big family hug

kowa na dakin murmushi ne afuskarshi na farinciki da taya murna na wannan family reunion din


saida komai ya lafa sannan su aymaan suka nemi tafiya

anan ummie taso riqesu wai ba yanzu ba su tsaya suci abinci inyaso idan sun tashi tafiya saisu tafi tare don sotake suje suyima su Abbu godiya don they own them much


cikin girmamawa sukayi turning request dinta down Inda suka nuna gwara dai su tafin kuma ai batada lafiya tafiya bazata yiwuba agareta yanzu

ba don taso ba tabari suka tafi Inda tasa aka kaisu bayan goma ta arziqi data hadosu dashi wanda saida tayimasu tilas sannan suka amsa


bayan tafiyar su aymaan ummie tasa aka kirawo dukkan ma'aikatan gidan Inda anan tayi musu introducing Deen amatsayin d'ayan d'anta kuma twin din Mussadiq

sosai ma'aikatan sukayi mashi maraba cikin girmamawa a qasan zuciyarsu kuma suna mammaki to ina yashiga tuntuni don sudai basu ta6a ganinshi ba ko sanin dashi

anan ummie tabada order ashirya abinci Inda nan take tasa akayo hiring kuku wadda ta iya abincin Africans

agefe kuma kaya sosai tasa aka fitar domin yin sadaka ga mabuqata amatsayin nuna godiya ga allah daya bayyana mata d'anta

da farko taso sanarda yan saudiya saidai Mussadiq ya hana yace ai zasuje subari Kawai sai sunje


shidai Deen dan kallo yazama shida habeeb da aka barsu tare suna kallon irin rawar kafar da akeyimasu kowa burinshi ya faranta mashi.

Daga baya wani haddaden part aka kaisu don suyi wanka su shirya Inda part din ma abin kallo ne don ya qayattu iya qayatuwa


har lokacin Deen bebar Jin komai kamar a mafarki ba, Kawai gani yakeyi soon za'a tasheshi ya farka yaga komai mafarki ne


koda suka gama shiryawa sukayi Acikin wasu tsaddadun kaya wanda tuni akayi musu order su

saida suka shirya tsaf sannan suka dawo main falo din Inda anan akayi leading dinsu zuwa dining area wanda izuwa lokacin shake yake kalolin abinci daban daban

akusada ita ummie tasashi zama tashiga serving dinshi da kanta, kallo daya zaka mata kasan tana cikin tsananin farinciki

shikau Deen maidata t.v Kawai yayi dama gashi akwai asirin kallo ya iya kafe abu da kallo babu ko gajiya


duk Abinda tanuna mashi akan yanaso zai kada mata kai Kawai idanunshi akanta, kwata2 baya qaunar Abinda zai janye mashi hankali daga kallon wannan kamillaliyar fuskar tata

itama ta lura da kallon dayake mata saidai bata damuba don tasan ba laifinshi bane koda yayi fiyeda hakan don itama tana iya kwana tana kallonshi batareda gajiyawa ba

da kanta ta dinga feeding dinshi Inda shikuma yabuda ciki yana amsa

Aysha tashiga tsokanarshi wai daga zuwanshi ya kwacemata matsayin autanci

dariya duk sukayi ummie na cemata sai hqr don ita yanzu tabar yayenta kuma

hira sosai ta kaure atsakaninsu cikin yaren turanci Inda shima habeeb,ba'a barshi abaya ba don 'A' ne a surutu

daga bayama komawa yayi basu labarin Nigeria Inda kowa ya kasa kunne suna sauraronshi shikuma yana cigaba da zuba kamar Radio

a bangaren Deen kau baya cewa komai sai amsar abincin da ummie ke feeding dinshi yana kallonta affectionately kamar wanda aka hallita don haka

hakan wadannan ahalin suka kasance cikin farincikin da basu ta6a Kasancewa ba.


***


ahankali take dibar Icecream din da dan qaramin cokalin Icecream din tana kaiwa baki


sosai taji dadin wannan fitar don ta ragemata kaso kadan daga cikin damuwarta


cigaba dashan Icecream din tayi gefe guda kuma tana sauraron hirar daddy dayake mata duk don yasata nishadi

bata cewa komai sai aikin sauraro Kawai saikuma idan akayi abin dariya tadan murmusa


daga jiya zuwa yau duk ta chanza, yar jarumtar datakeyi a yan kwanakinnan duk ta fece, she looks so sad dukda yadda take qoqarin 6oyewa


tun tana sauraron daddy har hankalinta yabar wajenshi

kallon titi take ta front glass yayinda hankalinta yayi nisa da Inda suke

lura da daddy yayi cewa hankalinta sam baya taredashi yasashi dan sakin Ajiyar zuciya

shima kallo daya zakamashi kasan he's very disturbed as well

ahankali ya dora hannunshi guda bisa hannunta dake kan cinyarta wanda hakan yasata juyowa ta kalleshi

ganin yana kallonta keenly yasata sakarmashi dry murmushi sannan taqara kai spoon din Icecream din abaki tanasha tace
"inajinka daddy"

"bakya jina shalele, tunanin me kikeyi?"

Dan buda idanu tayi saikuma ta girgiza kai tana qara murmushi

"inafa Ji daddy, babu tunanin danake"

murmushi daddy yayi yace
"tunaninshi kikeyi?"

juyowa tayi ta kalleshi saikuma ta kauda kai

"wa?"

"Deen" yabata amsa yana kallonta

qara kauda kai tayi tana hadiye abu mai d'aci

"A'a, me zaisa nayi tunaninshi?"

"you still love him right?" inji daddy yana maida idanunshi kan titi


shiru zee tayi tana Jin yadda kalmar 'LOVE' din tayi tasiri a zuciyarta

"No.." tafada ahankali

"na tsani soyayya" taqara fada cikin tone dayake bayyana iya gaskiyarta

"meyasa? saboda Deen yatafi yabarki? what if... what if ba laifinshi bane?" yafada yana qara kallonta

kauda kai tasake yi tana qoqarin maida hawayen dasuke neman tararmata

"I don't care daddy, Kawai na tsani soyayya ne daduk wanda zaimin, ko kalmarta banason jin an ambata akusadani"

"shalele, Deen..."

"daddy please, dakasan yadda maganar nan ke affecting dina da ka daina, banason wata magana datayi alaqa dashi ko soyayya, am fed up, nagaji"

yanayin datayi maganar yasa daddy sauke Ajiyar zuciya cikeda tausayinta

yasan a halin datake ciki be kamata ya dinga tadamata irin wannan maganar ba, amma ya zaiyi? sosai yakejin guiltiness a zuciyarshi, sosai abin ke damunshi, soyake ya furta koshima zaiji sallamar ruhi.


kingin tafiyar sun qarasata ne in silent babu wanda yasake cewa komai har suka iso gida saidai zuqatan kowannensu cike take da saqe saqe daban daban.


koda suka qaraso gida su aymaan sunriga da sun iso tuni


afalo suka taddasu suna firar Abinda yafaru acan gidansu Mussadiq din

zee tunda tashigo suka dan gaisa da mutanen falon tayi sama Kawai abinta don sosai mood dinta ya chanza dalilin maganar da daddy ya tadomata


aymaan da shima yana falon binta Kawai yayi da kallo harta haye saman yanajin badadi sosai a zuciyarshi.


a daren ranar batool ta tisa zee agaba tana bata labarin yadda haduwar Deen da family dinshi ya kasance

babu abunda yafi tsayawa batool kamar yadda taga wannan uban yan girman kan ke kuka kamar yaro don sai nanatawa takeyi tana cewa wlh bata ta6a tunanin ko kowa zaiyi kuka Mussadiq zaiyi ba gwara gwara Deen don shi yanada dakiya babu laifi don weakness dinshi be bayyana ba sosai saida suka hade da ummie.

itadai zee aikinta sauraro Kawai don duk surutun da takeyi idanunta a lumshe suke bata cemata ci kanki ba saidai hankalinta na kanta tana sauraronta ga mammakinta kuma tana jin dadin labarin don har jitake dama tana wurin komai yafaru

ko babu komai tayi farincikin haduwar Deen da ahalinshi wanda hakan babban burine nata data dade tanason cikashi, dukda babu wata alaqa atsakaninsu yanzu kuma har abada babu alaqar dazata qara shiga tsakaninsu tana tayashi murna, tana taya shi da familyn nashi murnan sake saduwa, tana kuma yimasu fatan alhairi.


*10:00pm*


zaune suke a wani dan balcony su biyu suna fira kowanne da mug din shayi ahannunshi

sanye Deen yake da fararen kayan barci dasukayi mugun haskashi while Mussadiq daga shi sai baqin trouser da farar singlet


habeeb kau tuni yabi lafiyar gado don dama shi baya wasa da barci gashi jiya a asibiti ba wani barcin kirki yayi ba

hakan yaba su Deen damar samun lokacin fira sosai Inda duk yawancin rabi da kwatan firar Mussadiq keyi Deen kuma yafi yin aikin saurare.

Dan shiru sukayi kowanne na kur6ar tea dinshi ahankali

kallon Deen Mussadiq yayi yaga he was staring into space da alamu hankalinshi yatafi

Dan murmusawa yayi sannan yace
"a coin for your thought"

kallonshi Deen yayi sai yadanyi murmushi
"ba tunani nake ba"

"really?" inji Mussadiq yana dariya

"yadda kake kafe waje daya da kallo kana sauke Ajiyar zuciya akai akai zaka cemin ba tunani ba kake? tell me, meke saka cikin damuwa bayan gamu?" inji Mussadiq seriously

murmushi Deen yasakeyi
"babu komai.. I think I'm exhausted"

murmushin gefen baki Mussadiq yayi yace
"sure, you're exhausted, tunaninta ai ya isa yayi exhausting dinka"

kallonshi Deen yayi cikin rashin fahimta

"wa?"

kashe mashi ido daya yayi yace
"kafini sani ai, ummie mana"

"ummie?"

"yes...I mean your Zainab"

Dan wara idanu Deen yayi saikuma ya kauda kai
"no, that's not true"

"yes, it is. tundazu ai kallonka Kawai nake nasan me kake ciki ai"

saikuma yadaga kafadu

"anyway banga laifinka ba ai,she worth it, she worth more.,Zainab macece mai kyakyawar zuciya"

Deen dake kallonshi yace
"kasanta ko kaima?"

murmushi Mussadiq yayi
"sosai ma, abokiyar fada ta ce amma yanzu nasan idan nahadu da ita dakyar kunya zata bari na iya kallonta" yaqarashe yana qara sipping tea dinshi

"abokiyar fada as how?" inji Deen

murmushi Mussadiq yasakeyi
"tun farkon haduwarmu har zuwa yanzu da fada muke rabuwa.. dafarko fadan gaske ne don alokacin I don't like her don ni gani nake ma batada gaskiya amma daga baya fadan saiyazo yanamin dadi hartakai dakaina nake tsokanota don haka Kawai sainaji ina missing tsiwarta"

murmushi yasakeyi

"dafarko na dauka bibiyata take da sharri hakan yasa nayi mata rashin mutunci karo da dama ashe da alhairi take bibiyata"

Deen dayayi kasaqe yana sauraronshi ya gyara zama yace
"tell me, kabani labarin komai please"

murmushi Mussadiq yayi yaqara kur6ar shayinshi sannan yace
"mun fara haduwa ne awani supermarket Inda naje don haduwa da wani colleague dina...."

from A-Z Mussadiq yabashi labarinsu da fadan dasukeyi, aqarshe ya ida da

"saiyanzu nagane magangganunta na ranar danasa aka tsaresu kuma maganarta nakan hanya, zaiyi wuya na iya hada idanu daita after all these"

shiru Deen yayi cikin sanyin jiki yana Jin babu dadi sosai, sanin cewa duk shine silan wulaqancin da Mussadiq yayimata yasashi jin babu dadi sosai har hakan ya bayyana a fuskarshi

"am sorry, nasan bazakaji dadi ba, nima yanzu haka nakeji, jinake kamar na,maido hannun agogo baya nayi deleting wuraren" inji Mussadiq in a serious tone

Ajiyar zuciya Deen yayi yace
"babu komai Mussadiq, ai rashin sanine, kuma rashin sani akace yafi dare duhu.
Kawai inajin babu dadi ne Mussadiq.

i've caused her pain upon pain, na cutatamata fiyeda tunanina... nasan bazata ta6a yafemin ba domin ban cancanci yafiyarba"

"amma Mujaheed meke tsakaninku daita? farkon haduwarmu daita da sunanka takirani *DEEN* sannan akwai lokuta da dama idan muna tare saita quramin idanu sai takirani da sunanka tana hawaye, dukda su abbu sunyimin bayani briefly Inda suka nuna tasanka basu fadamin alaqarku ba Kawai nunamin sukayi tasanka acan takuma zonan taganni shiyasa suka nemi hadamu"


shiru Deen yadanyi sannan ya dan hadiye yawu mai d'aci sannan yace
"she's my.. ex girlfriend"


wara idanu sosai Mussadiq yayi yana kallonshi

"as in?" yafada yana kallonshi cikin mammaki


kada mashi kai Deen yayi
"mu masoya ne.. ada. she's my first love"

shiru Mussadiq yayi shocked for a moment sannan yace
"and then? yanzu fa? ya akayi kuka rabu?"

ahankali Deen ya lumshe idanu ya bude, kaida ganinshi kasan yanajin ciwon abin

"yaudararta nayi" yafada ahankali

sake wara idanu Mussadiq yayi
"what?"

"yes, I betrayed her trust.. na yaudareta na gujeta alokacin da tagama sakankancewa tabani ragamar zuciyarta, am a bad man ko? ofcourse nasan am a bad man, tun a wancan lokacin"

"to amma meyasa? dama baka sonta?" inji Mussadiq confused

shiru Deen yayi saikuma yayi saikuma yace
"har yanzu my heart beats for her and it will continue... forever"

shiru shima Mussadiq yayi yana kallonshi sannan yasake cewa
"tell me, kabani labarinku from A-Z please"


"labarinmu bayada dadi Mussadiq, farkon keda dadi amma qarshen yafi mad'aci d'aci"

"dukda hakan kabani Mujaheed, inason sanin komai please"


Ajiyar zuciya Deen ya sauke sannan ya ajiye mug din hannunshi yatashi ahankali yataka zuwa bakin balcony din yana kallon harabar gidan dake fayau da haske ga securities takoina

"munfara haduwa ne a ranar wata juma'a, ina sauri zan tafi class daukar wani lecture...."


and kamar yadda Mussadiq ya buqata tiryan2 yabashi labarin soyyayarsu from A-Z

lokacin daya gama bashi labarin sosai jikin Mussadiq yayi lakwas don dafarko ma he's speechless

shikau Deen tsohon mikinshi ne yafamo don tuni zuciyarshi tashiga zugi da radadi idanunshi sun kada sosai

"to amma meyasa katafi all of the sudden Mujaheed?"


Dan murmushi Deen yayi yace
"qaddara Mussadiq... qaddarata"

"Kuma nayi regreting tunkafin nayi nisa, na azabtu kuma ina kan azabtuwa Mussadiq Kuma zan cigaba da azabtuwa har qarshen rayuwata.. I deserve it anyway"


"amma meyasa dakayi regreting baka dawo ba Mujaheed? meyasa kaza6i kayita zama kana cutuwa kana kuma cutar daita" inji Mussadiq


"nadawo Mussadiq,nadawo... amma a qurarren lokaci don lokacin tariga tayimin nisan dabazan iya ko hangenta ba"


"kamar yaya? lokacin tadawo nan Dubai?"


"nima bansani ba, amma da ace lokacin nasan Kawai dawowa tayi nan zan iyayin,komai domin nabiyota, saidai kamar yadda nagayamaka tayimin nisa, nisan nisan da ko muna wuri daya baxan iya mallakarta ba"


kallonshi Mussadiq keyi confused
"bangane ba? bazaka iya mallakarta ba kamar yaya?"


sai a lokacin Deen yajuyo ya fuskanceshi yace
"eh mana, batayi aure ba? tayaya zan bibiyi matar aure"


wara idanu Mussadiq yayi yana kallonshi
"aure? wacece tayi aure?"


"Zainab mana, tun bayan nayi breaking heart dinta tayi auren huce takaici which I don't blame her, kai dama bakasan tanada aure ba?"

wani irin kallo Mussadiq keyima Deen in confusion, aure? waye yayi auren? badai zee ba

"tayaya kasan tayi aure? waye yafada maka?" inji Mussadiq confused

"wanda bazaimin qarya ba akanta kuma nagani da idona"

"waye bazai maka qarya ba?"


"her Daddy"....✍�


Ummin Fasihu🧚🏻‍♀�
8/2/21, 9:44 PM - Buhainat😝: *🙍🏻‍♂️DEEN🙍🏻‍♂�*


*087*


"her dad? but... when? I mean yaushe tayi auren kuma waye mijinta?" inji confused Mussadiq


"tayaya za'ayi insani Mussadiq? all I know shine tayi aure don har i.v card dinta saida nagani da idanuna" inji Deen

shiru Mussadiq yayi still confused, dama Zainab matar aure ce? towaye mijin?

wani tunani yazo mashi arai, dasauri ya kawar dashi

ina? impossible!

sake kallon Deen yayi yace
"yaushe daddyn nata yagayamaka hakan?"

"three weeks bayan tafiyata?"

"ina kuka hadu?"

"nine nadawo... nakasa jurewa ne... nakasa walwala kuma na nemi dukkan farincikina narasa, alokacin nagani rayuwa batareda itaba is meaningless shiyasa na yanke shawarar dawowa nayi facing koma menene but... it's too late"

kallonshi Mussadiq yake tunda yafara magana haryakai aya, Dan shiru yayi kamar mai tunani saikuma yace
"dakaje saiyace maka tayi aure?"

"eh, haka yacemin kuma yabani evidence kuma ya tabbatar min cewa a lokacin ma bata qasar sun fice honeymoon daita da angonta"

"i.v kadai be isa shaida ba Deen"

"har hoton bikin saida nagani Mussadiq, tunda kaga na yarda hujjar dayabani takai na yarda din ne"

kan Mussadiq yaqara kullewa, kenan dagaske aure yakawo zee nan?

"nakasa yarda" inji Mussadiq


Dan murmushi Deen yayi mai ciwo yace
"nima haka, dafarko nakasa yarda amma daga baya dole na haqura na rungumi qaddarata"

"amma be kamata tayi aure ba Kawai don kayi breaking heart dinta, there will never be smoke without fire, ya kamata tayi tunanin dole ne akwai dalilinka nayin hakan... wait, tell me. meye dalilinka na barinta at the first place?" inji Mussadiq yana kallonshi

murmushi Deen yayi ya kauda kai Kawai

juyo dashi Mussadiq yayi ta hanyar dan dakar kafadarshi

"Hey magana fa nake maka" yafada yana mashi wani kallo

"baka cemin kanada saurin fushi ba? meye abin fushi anan?"

"look ka amsamin tambayata kana qara kuleni" inji Mussadiq da kanshi yadau zafi sosai

"meyasa kabarta bayan kana sonta? bayan nasan idan itace kome zai faru bazatayi hakan ba duba da yadda ta jajirce akan soyyayarku dukda rashin amincewar mahaifinta"

"saboda ni banida wannan jajircewar? am a coward"

shiru Mussadiq yayi yana kallonshi

Dan budamashi idanu Deen yayi yace
"yes, dafarko naso sarewa a soyayyarta saboda tunanin status dinmu ba daya ba, ita mai kudi ni talaka ina ganin kamar hakan bazai yiwuba... maimakon na gwada sa'ata nagani saina yanke shawarar sarewa wanda ba don da taimakonta ba da soyyayarmu bazata ma samu asali ba

na biyu kuma naso sarewa.lokacin da na fahimci kwata2 daddy baya ra'ayina.. maimakon nayi fighting for our love sai naso haqura.. still ba don qarfafa gwiwarta ba agareni da alokacin soyyayarmu ta datse

and lastly daga qarshe bayan duk gwagwarmayar damukasha kokuma nace datasha I still back down... wanda hakan ke nuna ni lusari ne... coward"


shiru Mussadiq yayi Kawai yana kallonshi yakasa cewa komai


janye idanunshi Deen yayi daga kanshi yana kallon harabar gidan absent-mindely

"am weak Mussadiq... inada rauni takoina, wannan shike qwarata"

sake kallon Mussadiq yayi da dan murmushi a fuskarshi
"be kamata na kasance haka ba ko a matsayina na namiji?"


"meye rauninka na qarshe? meye dalilinka na qarshe?" inji Mussadiq yana kallonshi in the eyeball

kauda kai Deen yayi Kawai bece komai ba

"nafarko kanada hujja Mujaheed, abu ne mai wuya mai kudi da talaka suyi soyyaya, yana faruwa but it's rare musanmman da macen itace mai kudin

nabiyu kuma mahaifinta bayaso, wannan ma hujja ce don aure batareda yarda daya daga iyaye ba babbar matsala ce, konine ina iya sarewa a wannan ga6ar

to amma na qarshen fa? meye dalili? bayan kasamu,amincewar yarinyar da iyayenta har suka baka damar turowa, meye dalilinka na janyewa har ka za6i ka datse karatunka mai matuqar muhinmmanci daka samu dakyar? meye dalili?" inji Mussadiq yana kallonshi sosai

kallonshi shima Deen yayi for some seconds da idanunshi dasuka chanza launi sannan ya kauda kai yana kallon gabanshi

"Kaka.." yafada ahankali

cikin rashin fahimta Mussadiq yace
"mene?"

"my grandmum" yafada ta yadda zai gane

Dan shiru Mussadiq yayi kamar mai tunani saikuma ya kalleshi

"wannan matar? wanda ta saceka?"

wani kallo Deen yayimashi
"babu wanda yasaceni, karka sake fadamata haka, kakata ce, my grandmum"

Ajiyar zuciya Mussadiq yayi yana rolling idanu sannan yace
"to naji, ita kakar taka ita tasaka guduwa?"

"eh" inji Deen ataqaice

"akan wane dalili?"

"saboda ta isa" inji Deen yana daukar hanyar barin balcony din don kwata2 firar ta ficemashi arai

"to amma..."

"am tired and sleepy Mussadiq, mubar firarnan please. good night"

yana kaiwa nan yashige yabar Mussadiq nan tsaye cikin saqe saqen zuci.


a daren ranar kasa barci Deen yayi don sosai wannan firar tasu tafama mashi tsohon mikin zuciyarshi, haka ya kwana yana juyi

shima Mussadiq be iya barcin kirki ba don shima sosai abin ya tsayamashi arai sai hada magangganunsu yakeyi yana rarrabasu cikin son samoma kanshi amsoshin tambayoyinshi.


*WASHEGARI*


suku suku Deen yar tashi, dafarko yaso manta a Inda suke sai daga baya yatuna.

har lokacin jikinshi da zuciyarshi asanyaye suke, yanayin komai ne cikin sanyi gashi dama yanada sanyi sai sanyin nashi yaqaru.


atare sukayi breakfast da dukkan family din Inda har lokacin ummie ke nan nan dashi don ko alokacin ita tayi feeding dinshi

ganin tadamu sosai da suku sukunshi yasashi yin qarfin hali wajen dan gyagijewa yana pretending komai lau

Mussadiq kau duk motsinshi idanunshi nakanshi yana kuma lura da yanayinshi, ahakan har suka gama suka koma sama

Deen ne gaban mirror yana bottoning din boturan rigarshi

besan shigowar Mussadiq ba sai Jin muryarshi yayi daga sama


"kakarka tasa kun gudune saboda batada wanda zata nuna kokuma tasa suje wannan introduction din amatsayin yan uwanka kuma tana tsoron don kar ta silar hakan asirinta ya tonu na cewa batada wata alaqa dakai ta jini, right?"

dakatar da Abinda yakeyi Deen yayi ya daga kai yana kallon Mussadiq dake jingine da kofa hannayenshi harde a qirji ta mirror din gabanshi

tashi Mussadiq yayi daga kofar yashiga tunkaro Deen

"hakan yasata sakaku guduwa Inda ba'asankuba bare asirinta yatonu... shikuma daddy saboda haushin yaudarar dakayiwa diyarshi yasashi yimaka qaryar tayi aure don nesantar dakai ga ita har abada"

sai a lokacin Deen yajuyo ya fuskanceshi

"mene? tayaya kasan qarya yayi?" inji Deen yana kallonshi

"to da me kake tunani? cikin sauqi zaisake baka ita bayan ka gudu ka 6ata damarka tafarko? plus dama abin be kwanta mashi ba tunfarko tunda tunfarko yayi zargin zaka yaudareta, guduwarka kuma ta tabbatar da hakan so dole yanemi hanyar rabaka daita na har abada kota halin qaqa"

shiru Deen yayi for sometimes sannan yace
"to meye tabbacinka akan batayi aure ba?"

"Aysha"

"Aysha?"

"eh... ita qawarta ce sosai, naje nasameta na tambayeta tace gaskiya batada aure dukda bansani ba ko itace,bata bayyana mata hakan ba don abotar tasu ma asalinta shirine, qila dagasken batada auren kokuma tanadashi bata dai bayyana mata bane"

hope din da Deen yafara samu da farko farkon maganar Mussadiq yakoma ciki jin Abinda yafada daga qarshe

yes it's possible ace tanada auren bata dai bari Aysha tasani bane, amma idan dagaske batadashi fa?


wani irin yanayi Deen yashiga, ada yasare kwata2 akan Deen amma wannan dan hope din da Mussadiq yabashi yasa yanajin wani irin yaqini na tasomashi from nowhere


"ka shirya zamu gidansu" muryar Mussadiq ta katse mashi tunaninshi

"gidansu wa?" inji Deen yana dagowa

"zee din mana" Mussadiq yabashi amsa yana nufar bathroom

"mezamuyi acan din?" inji Deen again zuciyarshi na bugawa

"wannan ne bansani ba" yafada yana fadawa toilet din


bin rufaffiyar qofar Deen yayi da kallo batareda ya iya motsawa daga Inda yake ba kuma.


***


Tunda ta tashi yau tagama duk Abinda takeyi ta koma ta nade akan gado

yau Monday Kuma sunada lectures amma haka Kawai taji bata iya zuwa school din don tasan kotaje babu Abinda zata dauka

ganin hakan yasa itama batool yin zamanta don jitayi bata iya zuwa itakadai

yanzu haka tana qasa tareda su ummy don bata iya wannan zaman saman irinna zee


wajajen bayan la'asar su ummie suka duro gidan
dafarko sunso zuwa dasafe amma sanin cewa ba lallai bane su iske mazajen gidan ba yasa suka daga tafiyar zuwa marece


alokacin daga mummy da ummy sai batool ke falon zaune suna fira, su Abbu da daddy na part din Abbu, aymaan kuma bedawo daga asibiti ba


suna zaune afalo suna fira sukaji qarar doorbell

batool ce ta tashi taje domin dubo waye

bude kofar tayi nan taci karo da fuskokin dabatayi tsanmmaniba

wara idanu tayi cikin mammaki tana cewa
"ummie! sannunku dazuwa.. ku shigo" tafada cikin murna tana kaucewa don basu damar shigowa

ummie dake murmushi tace
"fara dai gayama masu gidan abamu izini tukunna"

dasauri batool tajuya takoma falon ta sanardasu mummy

suma sunyi mammaki nan suka cemata tashigo dasu kowacce na qoqarin yafa mayafinta

da sallama ummie dake gaba tashigo Aysha abayanta

rungume juna sukayi da batool da Aysha cikin murnar ganin juna

ganin su Mussadiq na qoqarin shigowa yasa batool dan nutsuwa

kallonsu tayi, su biyun sanye da kaya iri daya baka ko iya banbancesu itama batool ta sumar kansu ta iya gane Deen aciki

kallo daya tayimashi tasan he's so nervous dubada yadda beson ko dago kai

habeeb ne ke bayansu wanda shima sanye yake cikin qananun kayanshi masu kyau

gabadaya ta gaidasu tana jan Aysha gefe don subasu wurin wucewa

amsawa sukayi saidai har lokacin Deen be dago ba ahaka suka shige falon


ganin hakan yasa suma shigowa Aysha nama batool rad'an ina zee itama tana bata amsa acikin rad'a cewa tana sama.


koda suka shigo falon sai suka iske duk sun zazzauna anata gaisawa hakan yasasu suma qarasowa suka zauna Aysha tashiga gaidasu ummy.


saida batool ta gaida ummie tasake gaidasu Deen sannan ta tashi tayi kitchen domin kawomasu abin motsa baki


Akan stool din kowacce kujera ta ajiye musu sannan takoma ta zauna kusada Aysha

cikin mutuntawa sosai da fara'a su ummy ke gaisawa Inda suma su Mussadiq suka gaishesu cikin girmamawa

shidai Deen duk Abinda akeyi yakasa sakin jiki kwata2 don ko dagowa beson yi, sosai yakejinshi atakure musanmman idan yanajin muryar mummy

tunanin cewa zee na cikin gidan nan ya hanashi sukuni ko kadan.


ummy takira Abbu Inda take sanardashi zuwan baqin nasu

ba'a jima ba kau saigasu Abbu da daddy suma sun shigo falon.

nan aka shiga sabuwar gaisuwa cikin farinciki da walwala

suma yan samarin suka shiga gaidasu cikin girmamawa sukuma suna amsawa cikin kulawa suna masu barka dasake saduwa

duk wannan abin da akeyi har lokacin Deen yakasa dagowa yayinda shikuma daddy yakasa janye idanunshi akanshi kwata2


anan ummie tashiga yimasu godiya sosai akan Kasancewarsu silar sake haduwarsu da Mujaheed dasuka dade da fidda rai dashi

anan tashiga basu labarin yadda rabuwarsu ta kasance cikin hawaye da yadda hakan yayi silar mahaifinsu kuma mijinta

kowa saida ya tausaya mata don sosai labarin ya ta6asu dukda sun sanshi dama

godiya taita yimusu har abin yaso yin yawa tana nuna tsantsar godiyarta agaresu hawaye a fuskarta

dakyar suka samu tayi shiru sunata rarrashinta da yimata,nuni da ta godewa allah donshi ya tsara komai a yadda yafaru dinnan suma ba wayonsu bane ko dabararsu

anan Kuma aka shiga fira wanda duk ta Kaka ce kowanne nakawo ra'ayinshi akanta Inda suka kasa tsayar da matsaya akan ko ita ta saceshi din kokuma tanada alaqa da 6acewarshi

anan aka buqaci Deen yabasu labarin iya zamansu daita

dukda halin dayake ciki na uneasiness haka yabasu labarin rayuwarshi tun tasowarshi daya bude idanu yasan Kaka

babu komai a labarin sai tsantsar kulawa da qauna da Kaka keyimashi

nan kansu yaqara kullewa suka rasa a wane matsayi zasusa Kaka

dole idan sunason wannan chakwakiyar ta warware su samo Kaka don ita kadai zata iya warware masu wannan sarqaqiyar

nan suka shiga shawarar yadda zasu samu Kaka

dafarko akace sukoma Nigeria suje su isketa amma firr ummie taqi yarda tace bazata ta6a barin Deen yaqara nesa daita ba saidai sutafi tare

haka sukaita shawarwari har daga baya suka samu mafita Inda Deen yabasu tabbacin Kaka zatazo nan Dubai dakanta

dasuka tambayi tayaya sai yace abar komai a hannunshi yasan yadda zaiyi.

ahaka suka cigaba da tattaunawar har zuwa wani lokaci

anan ummie tashiga tambayar ina zee

nan akace tana sama, sai ummy tasa su batool suje sutaho daita halan batasan da zuwansu bane.


tunda aka ambaci sunan zee Deen yaqara rasa yar nutsuwarshi

bugun zuciyarshi ce ta sauya yayinda wani feeling mai tsuma jiki ya mamayeshi

sauke kanshi yayi qasa ya cigaba da sauraron firar dasu ummie keyi sama sama yayinda duk hankalinshi da nutsuwarshi suka tattara sukayi hanyar dayaga su batool sukayi, dukda ba kallon wajen yake ba amma gabadaya hankalinshi na wajen.

ahankali bugun zuciyarshi tafara sauyawa tana yin doubling

ahankali yashiga murza taffukan hannunshi together kamar mai son yin maganin sanyin nan


sosai tsigar jikinshi ke tashi yanajin kamar ya dago amma yakasa dagowar

ahakan ya tsinkayi muryar da kunnuwanshi suka jima suna bege da marari, muryar da sai yanzu yasan iya adadin kewar dayaimata

"Ummie" yaji tafada cikin zazzaqar muryar da har yanzu beji mai irinta ba

cigaba dazuwa mashi muryar tayi cikin gaisawar dasuke da ummie

kasa riqe kanshi yayi daga qin dagowa

ahankali yafara dago oily eyes din nashi kamar wanda ake controlling da remote

daidai nan itama ta kallo wajen kamar tasani

caraff oily eyes dinshi ya sarqe da nata large pure white eyes din...✍�


*ga post din dare😆 nasan wasu harsun fidda rai🙁*


Ummin Fasihu🧚🏻‍♀�
8/2/21, 9:44 PM - Buhainat😝: *🙍🏻‍♂️DEEN🙍🏻‍♂�*


*088*


Qirjinsu yabada damm lokacin da idanun nasu suka gauraya dajuna

ko seconds biyu batayi ba tana kallonshi ta janye idanunta ta maidasu akan ummie dake mata magana

murmushi tayi tadan sunkuyar dakai Jin yadda ummie keta mata godiya itama

cikin murmushi zee kecewa babu komai ai allah shine abin godiya

kasa janye idanu Deen yayi akan zee, gani yake kamar mafarkan daya sabayine kamar ba dagaske ita yake gani ba


komai nata nanan

her geogous smile, her melodious voice, her breathtaking beauty

sanye take cikin wata doguwar hijab harqasa milk colour, fuskarta babu makeup sosai amma she looks so cute

ahankali yakejin yadda zuciyarshi ke melting in emotions ga yadda zuciyarshi ke bugu sosai linkin yadda takeyi ada

A bangaren Mussadiq ma ita yake kallo dan murmushi na forming agefen bakinshi wanda duk kwakwarka baka iya gane yanayi saishi dakeyin abinshi


yadda zee ta basar ta hanyar avoiding qara kallon gefensu yabashi dariya, irin wannan dabi'un nata na Jin kai da class yasa tunfarko tafara burgeshi

ahankali yayi gyaran murya sannan yace
"hyy good afternoon"

ko bata juyo ba ta gane mai muryar kuma tasan daita yake amma saitayi kamar bata saniba don saima kallon Aysha tayi cikin murmushi tana mata magana

"yaya namiki magana ummie" inji Aysha tana nuna Mussadiq

da qarfi tayi maganar so kowa yaji hakan yasa zee juyawa ta kalli saitin data nuna

maimakon idanunta sufada akan Mussadiq din saisuka sake sauka Acikin na Deen da haryanzu ita yake kallo

saurin sake janye idanun tayi tana jin yadda zuciyarta taqara bugawa da qarfi

"hmm hyy" tafada ahankali batareda taqara kallon gefensu ba

"thanks so much for your effort, words can't express our gratitude to you, jazakillah biljannah" inji Mussadiq yana kallonta

"amin, thanks too" ta amsa batareda tasake kallon gefensu ba

saikuma ta tashi tsaye kamar wadda ke kan allura ta riqo hannun Aysha

"let's go upstairs" tafada tana janta

"gulma zakuje yi ko?" inji ummy cikin tsokana

dariya Kawai sukayi suka tashi su ukun sukayi hanyar sama suka haye.


ta qasan ido Deen yabisu da kallo harsuka haye saman

wani sad feeling yaji ya mamaye zuciyarshi

ahankali ya lumshe idanunshi ya bude yana jin wani daci daci a maqoshinshi


sama sama ya cigaba da sauraron firar su ummie jiyake kamar yatashi yafita ko yadanji sauqin Abinda yakeji a zuciyarshi idan yashaqi iskar waje


kamar Mussadiq yasan meke ranshi sai ji Deen yayi yana excusing kansu akan cewa zasu dan fita waje

jin sun amince yasa Deen saurin miqewa kamar dama akan qaya yake sauran ma suka miqe suka fice wajen atare


wajen qarafunan da aka qawata entrance din yanufa yana dafawa yayi inhaling iskar dake kad'awa mai sanyi sannan yafesar

qarasowa Mussadiq da habeeb dake bayanshi sukayi suma

shiru wajen ya dauka yayinda Deen yakafe harabar wajen da kallo da idanunshi dasuka sauya launi

abun da matuqar ciwo ace kuna under roof daya da wadda kake matuqar so da bege amma ko kalma daya takasa shiga tsakaninku

ga yadda yaga tanayi ma kamar batama ganeshi ba don ko kallon kirki batayi mashi ba, she looks so okay and calm kamar ma ganinshin be tunamata da komai ba

kodai dagasken tayi aure ta manta dashi?

tayiwu nan din gidansu mijinta ne, tayiwu Abbu da ummy iyayen mijinta ne, then waye mijin?

daidai nan sukaji anyi horn abakin gate

atare duk suka kalli saitin gate din daidai lokacin da shima maigadi yaruga don zuwa budewa

cigaba da kallon wajen sukayi har aka bude gate din

wata ash colour mota ta danno kai tashigo ciki

direct parking space tanufa tayi parking

kauda kai Mussadiq yayi yana dan ta6e baki don ko ba'a fada ba yasan ko waye

bude kofar akayi a bangaren driver aka fito sannan aka maida aka rufe

da kallo Deen yabi aymaan daya zagayo ta dayan side din motar ya bude backseat ya fiddo briefcase dinshi

maida kofar yayi yarufe ya kulle motar sannan yajuyo hannunshi daya riqeda briefcase dayan kuma rataye da farar lapcoat dinshi

hada idanu sukayi da Deen dake kallonshi har lokacin

Dan dakatawa aymaan yayi da tafiyar don beyi expecting ganinsu ba saikuma ya cigaba da tahowa yana janye idanunshi daga na Deen

Deen dai cigaba da kallonshi yayi har ya qaraso, babu irin tunanin dabaizo mashi ba arai akan aymaan

ganin ya kusan qarasowa yasashi dan janye idanu shima yana dan lumshesu yana Jin yadda zuciyarshi kemashi wani irin zafi

da sallama aymaan ya qaraso wajen yana Dan kallonsu

atare duk suka amsa suna dagowa suna kallonshi banda Mussadiq daya juyar dakai ma dukda shima ya amsa sallamar

"likita bokan turai" inji habeeb cikin washe baki

murmushi aymaan yayi yace
"kune agidan namu?"

"eh wlh barka da dawowa" inji habeeb yana Bashi hannu

musabaha sukayi aymaan na amsawa da barka dai

shima Deen danne zuciyarshi yayi yadanyi forming murmushi yabashi hannu
"welcome" yafada ahankali

"welcome too" aymaan yafada sunayin musabahan

"why are you here?" inji aymaan batareda yako kalli gefen Mussadiq ba bare su gaisa

"yanzu muka fito ai" inji Deen

kafin susake magana sukaji muryoyin su ummy zasu fito


duk atare suka juya daidai lokacin dasu ummie suka fito harda su zee suna fira cikin wasa da dariya

"A'a Dr, andawo?" inji ummie don ta shaidashi

murmushi yasaki sannan yadan matso yana gaidata cikin girmamawa

amsawa tayi cikin kulawa tana tambayarshi ya aiki

da alhamdulillah ya amsa yana tambayarta ya qarfin jiki

amsa mashi tayi da da sauqi sosai ko bega alama ba

cikin dariya yace eh yaga alamu ma ba alama bama kadai

duk dariya sukayi banda Deen da Mussadiq da abin bewani basu dariya ba

shidai Deen sai kallon aymaan yake akaikaice yakasa janye idanu akanshi

Kasancewar idanunshi na akanshi yasa yaga lokacin da aymaan ya dagawa zee gira daya itakuma tayi murmushi shyly tana kauda kai

shima murmushin yayi yana binta da wani kallo

sauke idanunshi Deen daga kansu yana jin zuciyarshi na yin jingim, jiyake kamar an doramashi qaton dutse akai

itadai Aysha bata ma yarda suka hada idanu da aymaan ba don sai kauda kai takeyi

tunda talura da yadda yake wani shasha mata qamshi yana hade haden rai idan yaganta ta yanke shawarar fita sabgarshi itama


sallama ummie tashiga yimasu bayan ta amshi address dinsu Ahmad akan suma zataje hargida tayimasu godiya, dama kuma already sunyi exchanging number akan zasu dinga kiran juna akai akai akan maganar Kaka

har wajen motarsu suka rakasu Inda anan ummie tasa su Mussadiq suka fiffidomasu kayan dasuka zomasu dasu

dafarko sunso qin amsa suna cewa yayi yawa gashi dama sun hado su aymaan da tilin kaya jiya

nacewar da ummie tayi yasa akan dole suka amsa suna masu godiya sosai

Nan sukayi sallama cikin aminci da fara'a kamar wadanda suka dade dasanin juna

itadai zee tuni takoma ciki don tunda suka tsaya jayayya akan kaya ta silale ta fece

suna nan har motar tasu ta tashi maigadi yabude masu gate suka fice

da taimakon su aymaan suka kwashi kayan dasu ummie suka kawo suma suka koma ciki


***


cigaba da kai kawo yake waya kare a kunnenshi, kallo daya zakamashi kasan cewa yana cikin damuwa sosai don sosai hakan ya bayyana a fuskarshi


haryanzu amsa daya ake bashi, lambobin dayake kira kwata2 basa shiga


Ajiyar zuciya ya sauke yana sauke wayar daga kunnenshi sannan yajuyo ya kalleta

tana nan Inda take buga uban tagumi, idanunta harsun gaji da zubar da hawaye

"innalillahi waina ilaihi rajiun.. meke faruwa ne haka? wlh haryanzu babu wayar kodaya acikinsu datake shiga" inji Alhaji Bashir cikin tsantsar damuwa


"innalillahi waina ilaihi rajiun, allahuma arjini fi musibati, wannan wane irin abu ne? kuma harda number abokin naka dayaje wajenshi din bata shiga?" inji mami dake zaune kusada Kaka cikin damuwa

"wlh harda ita, I don't know what's going on. dukkansu nambobinsu bata shiga" inji Alhaji cikin damuwa


qara fashewa da kuka Kaka tayi cikin dakussashiyar muryarta wadda tagaji da kuka
"dama saida raina yabani, saida naji banason tafiyar nan saida naji ajikina tafiyar nan ba alhairi bace, yanzu gashi ta tabbata

innalillahi waina ilaihi rajiun, yanzu ina zansakaina ni ma'u? ya zanyi da rayuwata? wlh bazan iya rayuwa babu kyakyawana akusadani ba, wlh mutuwa zanyi" saikuma tafashe da matsanancin kuka

Lailah dake kusada ita da damqe hannunta itama tana hawaye

tun shekaran jiya wancan suke cikin tashin hankali

kwata2 number Deen dana habeeb sunbar shiga gashi shekaran jiya yakamata sudawo amma haryanzu shiru

babu su babu alamunsu ga numbersu bata shiga

jawo Kaka mami tayi ajikinta tashiga bata baki tana kwantar mata da hankali amma yadda kasan qara zugata takeyi

"banida kowa saishi, shima beda kowa saini. tunda ya bude idanu duniya ni kadai yasani nashi, bayan ni besan kowa ba

bayada hayaniya, babu ruwanshi da kowa meyasa ake bibiyarshi da sharri?

dama ni ban yarda da wannan abokin nashi dayace zaima aiki ba, aiki ace harsai kabar qasarka kaje Inda bakasan uban kowa ba? ai daji ba alhairi bane

gashi beda lafiya, akasi kadan za'a samu ciwonshi na namonia (pneumonia) yatashi kuma idan yatashi dakyar yake sha kamar bazaiyi rai ba haka yakeyi

abu goma da ashirin duk suntaru sun hau kanshi ya akeson yayi da rayuwarshi?

yanzu haka muggai ne azzalumai sunsa yafito yazo qasarsu Inda babu yadda zaiyi dasu, yanzu yazanyi idan wani abu yasamu Kamal? yazanyi da rayuwata?"
duk cikin kuka sosai take wannan xancen, tsabar kukan datasha muryarta ma bata fita sosai don tun shekaran jiya take abu guda ko abinci bata iyaci saboda tashin hankali

"kiyi hqr Kaka insha allah babu Abinda zai faru dasu, ki kyautata masu zato na tabbata wani akasi akasamu qila amma insha allah zasu dawo cikin qoshin lafiya
Kuma karki manta baban yaron abokinane, tsohon abokinane damukayi primary da secondary dashi daga baya kuma aka rarrabu insha allah mundin yana taredashi babu Abinda zai faru dashi na cutarwa" inji Alhaji cikin son kwantar mata da hankali

"tsohon abokinka? tsohon aboki fa kace, waya san meya zama bayan rabuwarku? Kawai daga kunyi firamari da sakandiri atare shikenan saika yarda dashi kusani tura jikana wajenshi? wayasan meya zama bayan rabuwarku? ai muggayen mutane.sai daga baya suke zama mugaye bawai la'akari za'ayi da yarintarsu ba"

"yanzu dai insha allah daga nan zuwa gobe xan tabbatar nasamo mana information.ko yaya ne akansu, don allah ki.kwantar da hankalinki Kaka, jifa yadda kika koma ko abinci fa bakya ci sai aikin kuka. Balarabe yanzu babu Abinda yafi buqata wanda yafi addu'a, ki kwantar da hankalinki Kaka" inji Alhajin cikin rarrashi

"kiyi hqr Kaka mu cigaba da kyautata musu zato.insha allah zasu dawo garemu cikin qoshin lafiya, mu cigaba dayimasu addu'a insha allah zasu dawo garemu cikin aminci" inji mami


haka dai suka taru sunata rarrashin Kaka da kwantar mata da hankali

Lailah kau na gefe itama damuwa ce rubuce koina a fuskarta, bata jin tana iya jurewa idan wani abu yasamu Balaraben ta, fatanta allah ya kareshi aduk Inda yake ya maido masu shi lafiya.


***


Washegari su ummie sukaje gidansu Ahmad Inda su shigar dare ma sukayi musu don saida suka ma kirasu saboda dama sun amshi contact dinsu awajen su abbu

sosai su iyayen Ahmad sukaji dadin zuwan nasu Inda anan sukayiwa juna tarbar mutunci

godiya sosai ummie tashiga yimusu suma tana samasu albarka musanmman ma Ahmad

sosai suma suka nuna babu komai ai d'a nakowa ne suna kuma tayasu murnar sake saduwa

Ahmad kau fita dasu Deen yayi waje Inda suka samu wani tent sukayi zamansu suna fira

abin mammaki saigashi tasu tayi saurin zuwa daya da Mussadiq don nan da nan suka jiki da juna

kan kace me sunyi nisa a firarsu wanda mostly ta Abinda yashafi aikinsu ne wato Business


shidai Deen becika sakamasu baki ba don mostly besan akan me suke magana akai ba daga baya ma tashi yayi ya koma gefe ya tsaya yana bin harabar gidan da kallo yana feeling daddadan iskan dare dake kadawa


gabadaya daga jiya zuwa yau duk ya chanza yakoma kamar bashi ba

sosai damuwa ta bayyana a tattare dashi dukda iya bakin qoqarin dayakeyi na 6oyewa

yakasa mantawa da image din Zainab, zuciyarshi taqi bashi sukuni dukda yana tunanin da aure akanta kuma auren wannan likitan

yasan indai har tanada auren what he's doing was wrong don it's very wrong kadinga tunanin matar wani

saidai yarasa dalilin dayasa yakasa tankwara zuciyarshi akan haka don with every passing minute tunaninta qara addabarshi yake soyyayarta kuma qara qaruwa takeyi

hakan yasa duk yabi ya susuce yarasa Abinda kemashi dadi


ahakan har lokacin tafiyarsu tayi suka kamo hanyar gida

a hanya ummie taita tambayarshi meke damunshi don duk yadda yake qoqarin 6oye damuwarshi musanmman ma agabanta saida tagane yana cikin damuwa

murmushi Kawai yakeyi yace babu komai yagaji ne Kawai

haka ummie ta kyaleshi ba don ta yarda gajiyar bace saidai bata takura mashi ba suna isa gida ta kadasu part dinsu wai suje su kwanta tunda duk agajiye suke musanmman ma Deen din


koda suka shiga part din nasu duk shirin barci sukayi kowa yanemi lafiyar gado ya kwanta bayan sun.kashe wuta


Deen dai dama ba barci yakeji ba don haka kwance yake Kawai staring to dark space


ya dade sosai ahakan don dare yayi ma sosai don koina yayi tsit, kamar.daga sama yaji muryar Mussadiq nacewa

"she's not married"

shiru ya ratsa dakin nawani lokacin kafin wutar bedside lamp yakawo sanadiyar kunnawa da Deen yayi

"bakayi barci ba?" inji Deen yana kallon side din Mussadiq Kasancewar kowa dama da bed dinshi

sai alokacin Mussadiq yajuyo daga juyamashi bayan dayayi

"kaima ai bakayi ba" yabashi amsa

"me kace yanzu?" inji Deen

"nace batayi aure ba" Mussadiq yabashi amsa


shiru Deen yayi yakura mashi ido for sometimes sannan yace
"tayaya akayi kasani?"

"Ahmad ya gayamin, she's not married amma she will be soon idan kayi sake" yafada yana gyara kwanciyarshi

shiru Deen yasakeyi na wani lokaci

dagaske batada aure? kenan he still has another chance? amma meyasa yace zatayi soon idan yayi sake?

"meyasa kace hakan?" inji Deen

"saboda akwai masu harinta" Mussadiq yabashi amsa

"masu harinta? su waye?" inji Deen yana kallonshi beson ko dauke ido akanshi

"kai yanzu baka gane wannan annoying likitan sonta yake ba?"

"ni dafarko nayi tunanin shine mijin nata ai"

kya6e baki Mussadiq yayi
"Zaidai zama idan kayi sake, sonta yake na dade dasanin hakan kuma he can do anything to win her heart don haka kanada babban aiki agabanka"


shiru Deen yayi yana tunani

yes it's possible ace aymaan son zee yake, bazai manta da kallon dayayi mata ba rannan, the look is something else, gashi the guy is perfect atakoina, ga kyau ga ilimi ga gayu he can easily win any girl's heart

saiya tsinci kanshi da comparing kanshi dashi

da me da me yafishi? shima aymaan din dame dame yafishi

saidai beyi nisa a comparison dinba zuciyarshi ta tuna mashi da matsayinshi awajen zee yanzu


zee yanzu ba kallon wancan Deen din nata take mashi ba, yasan kallon mayaudari take mashi, maqaryaci maci amana

tunawa yayi da yadda tanuna halin ko in kula dashi ranar nan

yitayi ma kamar batasan da wanzuwarshi ba awajen

wataqila ma ta tsaneshi ko ganinshi batason yi, gashi shikanshi kunyarta yakeyi, tayaya ma zai iya sake tunkararta? me zaice mata? dawane ido zai kalleta

"kayi shiru" inji Mussadiq jin shirun yayi yawa

"Mussadiq banajin inada wata dama kuma, banajin zee zata sake saurarata bare tasake bani wata dama, tunkararta da niyyar sake samun yardarta is just a lost battle, bazanci nasara ba"

Dan dagowa Mussadiq yayi yana kallon Deen a mammakince
"wait.. wai kana nufin harka sare kafinma ka gwada sa'arka?"

girgiza kai Deen yayi
"meye amfanin gwada sa'ar da kasan baxakayi nasara ba? nasan zee bazata ta6a qara yarda dani ba, nasan yanzu haka ma ta tsaneni"


shiru Mussadiq yayi yana kallonshi har lokacin da unknown expression a fuskarshi

can yadan saki murmushi yakoma ya kwanta yana cewa
"good... kace yanzu nadawo cikin game din kenan"

kallonshi Deen yayi
"kamar yaya kadawo game?"


murmushi Mussadiq yayi
"dama ina cikin game din ai, bayyanarka dakuma jin cewa kaima kana ciki yaso sani janyewa amma yanzu no need, am still in"


kallonshi Deen yake cikin rashin fahimta can yace
"meaning?"


juyowa Mussadiq yayi yadda zasu fuskanci juna sosai yace
"meaning ina sonta and zan cigaba da trying wajen winning heart dinta"


wara manyan oily eyes dinshi Deen yayi

"what?"...✍�


Ummin Fasihu🧚🏻‍♀�
8/2/21, 9:45 PM - Buhainat😝: *🙍🏻‍♂️DEEN🙍🏻‍♂�*


*089*


Dan murmushi Mussadiq yayi ganin irin kallon da Deen kemashi

"yes, you know what? Abinda bakasaniba shine a rayuwar nan idan bakayi kau ban wuri akeyi, idan kai kana iya wasa da opportunity dinka wasu irina baxasu iya bada even the slighest chance wajen su6ucewar damarsu ba,
what you don't know is kafin zuwanka nafara developing feelings akanta, banace inamata mahaukacin so ba irin wanda bazan iya rabuwa daita ba ko idan narasata zan shiga wani hali, I just like her, attitude dinta na burgeni sosai and idan so samune zanso mallakarta

amma zuwanka dakuma jin labarinku yasani jin cewa babu wanda ya cancanceta sama dakai and na yanke shawarar barmaka ita amma tunda you can't do it ina tunanin gwara nadawo cikin game din don bazan iya haqura wannan Dr din yasameta ba just like that"

yana kaiwa nan yajuya ya gyara kwanciyarshi yarufe entire jikinshi da bargo


kasa dauke idanu Deen yayi akanshi still

cigaba yayi da kallonshi yanajin yadda zuciyarshi tayi wani irin jingim

wait, is Mussadiq serious? this is crazy!

kenan yana nufin yana iya soyayya da wadda yakeso?


saiya tsinci kanshi da kishin Mussadiq fiyeda aymaan

sai jiyayi yana iya haqura da zee yabarwa aymaan amma badai Mussadiq ba


maimakon firar dasukayi yasashi jin sauqin Abinda yake damunshi sai abin yaqara worsen

daren ranar be runtsa ba yadda yaga rana haka yaga dare.


Washegari Deen yatashi yarasa Abinda kemashi dadi aduniyar nan

da zancensu da Mussadiq ya kwana kuma haryanzu zancen yaqi sakinshi

shidai gani yake kamar wasa yakeyi, ai da kunya ma yaso wadda yakeso saidai kuma bega alamun da wasa Mussadiq yake ba, what if dagaske yake?

ga mammakinshi sai yaji yafi kishin Kasancewar zee da Mussadiq bisa ga aymaan

ina? bazai yiwuba, bazai ta6a barin hakan ya yiwuba.


Mussadiq kau hankali kwance yake hidindimun gabanshi

yana lura da Deen amma yayi kamar besan yana yiba yayinda deep down yake mashi dariya

lallai mutum ga kishi ga tsoro, zai koyamashi hankali ne


ahaka akayi kwana biyu

cikin kwanaki biyun nan Deen ba qaramin shiga damuwa yayi ba


he so much crave to see Zainab don wani lokacin saiyaji kamar yayi tsuntsuwa yaganshi agabanta yaga fuskarta koda na second daya ne

sosai kewanta da begenta ke nuqurqusarshi

agefe guda kuma haryanzu hankalinshi yaqi kwanciya adalilin maganar dasukayi da Mussadiq


cikin kwanaki biyun nan babu wanda yasake tada ma Dan uwanshi maganar amma Deen yakasa sukuni don harwani sanyama Mussadiq ido yayi yana studying movement dinshi


A bangare guda kuma kewar Kaka ke addabarshi, he missed her so very much, yanaso yaji muryarta koda sau dayane amma ya haqura yaqi kiranta ko bude wayarshi don gani yake it's not yet time.


sosai shaquwa da sabo yashiga tsakanin Deen da sabon family dinshi don kowa jidashi yakeyi most especially ummie don ko motsi yayi saita tambayi akwai damuwa?

yadda ummie take nuna tsantsar damuwarta da qaunarta akanshi yasa yake iya qoqarinshi wajen 6oyemata halin dayake ciki na damuwa


Aysha ma sosai jininsu ya hadu da Deen don sunfi shiri ma dashi busaga Mussadiq

she's very fond of him don muddin tana nan to kodayaushe suna tare tana mashi fira kokuma kagansu tana koya mashi larabci


shima he's very fond with her don kusan dabi'unsu daya daita

habeeb kau anzama dan gida, shi yana waya da mutanenshi na 9ja dukda baya yawan barin wayar akunne gudun kiran Alhaji Bashir

shi sosai qasar tayimashi don kusan kodayaushe saiyasa Mussadiq ya hadashi da driver ya dan yawata dashi yaga gari

ko kadan qasar bata isheshi ba bare yaji yagaji da zamanta, he's living happily Acikin familyn Deen din.


fitowa Deen yayi yana dan strolling yana qarewa gidan kallo

haryanzu mammakin irin girman gidan yake don yadda kasan unguwa guda ce

tsari da kyawun gidan baya misaltuwa don shi tunda yake beta6a gani ko yataka gida mai irin kyawunshi ba

ahankali yake tafiya hannayenshi zube a aljihu

sosai Deen yaqara chanzawa cikin yan kwanakinnan, yaqara wani irin kyau da fresh ga kwarjininshi daya sake fitowa sosai.


habeeb bayanan as usual, yafita yawon zaga gari dinshi shikuma Mussadiq yana garden yana wasu yan ayyuka a laptop, Aysha kuma tana school.


gajiya dayayi dazama shikadai yasashi fitowa shima don yadan sha iska


yana tafe ma'aikatan gidan na gaidashi yana amsamasu da dan murmushi harya qaraso garden din


garden din ya hadu ga trimmed grass carpet tun daga farkon garden din har qarshe

ga wani dan swimming pool daga can kusurwar garden din mai kyan gaske ga shufke shufken kayan itatuwa daya qara qawata garden din yakuma bada shades ga garden din


wani iska mai sanyin dadi ke kadawa a garden din, garden din is very quiet sai dan kukan tsuntsaye da akeji akai akai


ahankali yanufi Inda Mussadiq yake zaune ya duqufa akan aikin gabanshi


Mussadiq besan da shigowarshi ba garden din ba saida yaji motsi akusada shi

dagowa yayi daidai lokacin da Deen kejan kujerar dake facing dinshi ya zauna

murmushi Mussadiq yayi mashi shima ya maida mashi martani

"sannu workaholic"

qara murmusawa Mussadiq yayi yace
"yauwa ai kaima ka kusan zama hakan, lokacin kadan yarage yanzu haka chanza komai nakeyi yadda zai dawo da sunanmu mu biyu"

kalloshi Deen yayi
"ban gane ba"

"yes, lokaci yayi da zamuyi running komai mu biyu" inji Mussadiq

wani kallo Deen yayi mashi
"cemaka akayi na iya business? karma kasoma don banada ra'ayin business kwata2"

"hmm ai aikin gama ya gama mallam, nufinka ni,zan cigaba da running komai bayan gaka? impossible"

"look seriously nifa banida ra'ayin business sam, is better ka cigaba da running abinka yadda kafara don ni bama shi na karanta ba"


"me ka karanta?"


"engineering"


"wow! still ba'a makara ba ai sai ka karanci business din ai shima"

"A'a bana ra'ayinshi kwata2 ne, koda xanyi wani abu to engineering zan cigaba dayi"

"wane irin engineering ka karanta?"

"constructional engineering amma yanzu mechanical engineering nakeso nasake karanta nayi zurfi akai"

"why?"

"saboda nadan fara aikin mechanic ne kwanakin baya and I love it, zanso na cigaba"

"yaushe kayi aikin mechanic?"

"bayan rabuwarmu da zee"


shiru Mussadiq yayi saikuma yadan kada kai

"not bad but still komai saiya koma da sunanmu mu biyu afterall dukiyar ai batawa bace ni kadai tamuce all, aikina Kawai juyamana ita"


"nidai A'a, continue the way it is please, karka chanza komai"

Dan ta6e baki Kawai Mussadiq yayi ya cigaba da Abinda yakeyi besake tanka mashi ba


shiru yadan ratsa wajen


"kenan ka iya gyaran motoci?" Mussadiq yayi breaking silent din

murmushi Deen yayi
"ko kanada wadda za'a gyara maka ne?"

murmushi shima Mussadiq yayi
"yanzu kam babu amma za'a samu soon, amma you're talented kuma kace da kana carpentry?"

kada kai Kawai Deen yayi bece komai ba

"wow! ga carpentry ga mechanic ga singing, duk kai kadai?"

murmushi Kawai Deen yayi

"wane kafiso ciki?"

shiru Deen yadanyi can yace
"gaskiya mechanic"

"why?"

"hakanan Kawai aikin gives me joy"


Dan shiru Mussadiq yayi cikin tunani sai yace
"what of ka koma school ka karanci mechanical engineering din kaga saika bude wani forum kafara displaying dinshi, waya sani ko nan gaba kama dinka qirqirar motocin dakanka?"

dan wara idanu Deen yayi
"really?"

"yes, wannan aikin is very talented something, kaga tunda.kace it gives you joy allah kadai yasan Abinda zaka iya creating if you put it to work"

"wow Ka kawo shawara, Kawai haka za'ayi" inji Deen cikin jindadi

"but waqarka fa?"

"nifa inayin waqa don nishadi ne, banma ta6a tunanin zanci abinci daita ba"

dariya Mussadiq yayi
"ikon allah kenan ai, amma twinnie kanada basirori wlh, idan babu wannan akwai wannan idan babu wannan akwai wannan duk Inda tafadi shaa nikau daga business sai business, dull me"

murmushi Deen yayi yace
"business din ma,ai aikin qwalwa ce da basira, babu aikin datafi chaza qwalwa da kai kamar business, you're talented too"

murmushi Kawai Mussadiq yayi ya cigaba da danne dannenshi

"ya kamata nafara zazzagawa dakai companies.dinmu" inji Mussadiq hankalinshi akan screen din laptop din

dan ta6e baki Deen yayi don wannan bashi ne damuwarshi ba asali ma Abinda yakawoshi wajenshi daban


shiru wajen yadauka nawani lokaci kafin Deen yace
"kaje wajenta?"

tsaida Abinda yakeyi Mussadiq yayi for a moment sannan ya dago ya kalleshi cikin rashin fahimta

kauda kai Deen yayi, he know he sound stupid amma yakasa jurewa ne

"wa?"

"kafini sani ai" inji Deen yana harararshi

Dan murmushi Mussadiq yayi
"tayaya za'ayi insani baka gayamin ba"

"gidansu zee" yafada yana kauda kai

sake yin Murmushi yayi yana maida hankalinshi akan system

"oh! mezai hana? ai da zafi zafi ake dukan qarfe kuma abari ya huce shike kawo rabon wani, ko jiya naje, yauma xanje"

wani mugun kallo Deen ke binshi dashi tunda yafara harya kai aya

"to karka qara zuwa" yafada yana hade cikkakun girarenshi

"saboda?"

"saboda she's mine ok? karka qara zuwa kaji na gayamaka" yafada yana fuming don dagaske ranshi ya 6aci

dariya Mussadiq ya fashe daita

"yaushe tazama taka?" ya tambaya cikin shaqiyanci

"dama can tawace kuma a tawan zata cigaba da Kasancewa, so back off!" yafada yana eyeing dinshi

"to? kaida ke tsoron tunkararta? cewa fa kayi baka iya facing dinta"

"babu ruwanka, that was then amma yanzu I'll fight, I'll fight everyone akanta including you" yafada yana watsamashi harara

dariya Mussadiq yasake fashewa daita harda tafi

"wow! wayaga fighter, tofa duk wannan courage din daga ina? rannan fa kace kayi backing off"

"yanzu kuma nace am IN😬" yafada tsakankanin haqora

cikin dariya Mussadiq yace
"Alright Alright, aini banida matsala da hakan, ina iya backing off ai idan ka matsa saidai fa zan dora ne idan naga kana neman gazawa"

harararshi Kawai Deen yayi ya kauda kai

chuckling Mussadiq yayi ya cigaba da aikinshi cikin zuciyarshi yana cewa
'baban kishi'


shiru wajen yadan sake dauka sannan deen yace
"inane unguwarsu? inason zuwa gidansu"

"wajen zee din zaka ko wani daban?"

"Ina ruwanka?" inji Deen yana eyeing dinshi😠

dariya Mussadiq yayi yace
"ok ok da alamu dai awuya kake, Kawai shawara nakeson baka ne, idan wajenta zaka kaje school dinsu instead zakafi samun damar yimata magana amma idan gidan kaje ba lallai bane kasamu ganinta bama"

shiru Deen dake huci haryanzu yayi can yace
"really?"

"sure"


"to inane school din?"

"zan kaika"


***


Fitowa sukayi daga cafeteria din suna tafe suna fira suna dariya

both of them sanye suke cikin abaya saidai kowacce da kalar tata

hannayen kowacce rungume da books dayan kuma riqe da yar polythene nylon dake dauke da abubbuwan dasuka siyo a cafeteria din

tafiya suke suna fira kamar sauran daliban dake wucewa jefi jefi kamar daga sama sukaji ance

"Zainab..."

cak zee ta tsaya daga tafiyar datake zuciyarta na bugawa lokaci guda


batool ce tajuya saitaga Deen yana takowa wajensu

kafin tayi komai taji zee dabata juyo ba ta damqi hannunta tafara janta zasu wuce

"Zainab.. Zainab please wait" yafada yana binsu da sauri ganin suna wucewa

cigaba dajan batool dake biye daita tayi bata tsaya din ba saima qarama tafiyarta sauri datayi

ganin hakan yasa shima qara pace dukda be iya sauri ba harya samu yasha gabansu

"Z...Zainab, please listen" yafada yana dan sauke numfashin saurin dayayi

wani kallo ta watsa mashi wanda yasa gabanshi faduwa hakan yasashi saurin sauke nashi idanun

juyawa tayi zatabi wata hanyar yayi saurin qara shan gabanta

"Zainab please" yasake fada pleadingly

"wai mallam lafiyarka kuwa?!" tafada atsawace tana jifanshi dawani kallo

Dan jabaya yayi sanadiyar ihun datayi mashi don sosai tsawar tashigeshi (ya tsani tsawa remember?)

"lafiya zaka zo kana tarewa mutane gaba, who are you?" tafada afusace

"kiyi hqr please, am sorry idan kinji haushi"

tsaki taja tazo zata wuce don sosai jikinta ke rawa innerly

sake tareta Deen yayi

"please kibani 5mins muyi magana idan babu damuwa..."

"akwai damuwa, banida lokacin 6atawa" tafada bluntly

"please Zainab, atleast listen to me, nasan ayanzu babu Abinda kikafi tsanar gani kamar fuskata..."

"then meyasa kake gwadamin ita bayan kasan haka" tafada a masifance

shiru Deen yayi yama rasa abinda zai sake cewa

"Ka matsar mana ahanya mallam zamu wuce"

"please Zainab, ki saurareni, kibani dama nayi explaining kaina" yafada cikin magiya

"did you owe anyone any explanation?"

"yes, I owe you zee, please let me explain"

"na yafe explanation din, I don't know you and I don't wanna see ever again"

taja hannun batool daqarfi suka wuce

"Zainab! Zainab!..."


tana jin yadda yake qwala mata kira amma bata juyoba saima saurin datakeyi

batool dai na biyeda ita tanayi tana waigen Deen harya 6acemasu


wani empty class zee tajasu suka shiga saita saki hannun batool tawuce ta zauna kan wata chair tadafe goshinta

binta da kallo batool tayi nawani lokaci sannan ta qaraso wajenta

"haba zee, what have you done? dubi yadda kikayima mutuminnan"

wani kallo zee tadago tana mata
"me nayimashi?"

"wannan abin dakikayi mashi wulaqancine be kamata..."

"Hey look mallama spare me that ok? babu ruwanki ok? wannan abin be shafeki ba in any way so stick your nose out of my business" tafada cikin fushi idanunta na durar qwalla

sakin baki batool tayi tana kallonta saikuma ta kada kai tajuya tafice daga classroom din

sake dafe goshi zee tayi dayan hannun kuma ta dafe saitin zuciyarta dashi tana sauke Ajiyar zuciya ahankali

lumshe idanunta tayi tana cigaba da sauke numfashi ahankali.


Deen ya dade a Inda suka barshi tsaye

daga baya ne daya gaji da tsayuwar yajuya yakoma ta Inda yafito


tun daga nesa Mussadiq ya hangoshi, Dan murmushi yayi ganin yanayin yadda yake tafiya kamar wanda kwai yafashemawa aciki

qarasowa Deen yayi yasa hannu yabude motar yashiga ya zauna kusada Mussadiq dayasha shade dinshi a ido yana sauke Ajiyar zuciya

"harka dawo?" inji Mussadiq

kadamashi kai Kawai ya iya yi don sosai jikinshi yaqara sanyaya

"are you ok?" inji Mussadiq again yana kallonshi

furzar da huci yayi sannan yace
"yeah"

"to ya? mutafi ne?"

shiru Deen yadanyi

"No katafi, idan natashi dawowa zan kiraka saika turo ko driver kokuma kagayamin yadda zancewa mai cab saiya kawoni"

"first option din yayi zan turo driver" inji Mussadiq

bude kofar Deen yayi zai fita saiyaji Mussadiq yace
"3:00pm suke tashi yau"

juyowa Deen yayi ya kalleshi
"akwai masjid ai anan ko?"

"eh akwai akwai signboards daxaiyi directing dinka"

"ok thanks"inji Deen yana rufo kofar

"bye saika dawo" inji Mussadiq yana wining glasses din motar

yana tsaye motar ta fice daga school din

Ajiyar zuciya ya sauke

dama yasan this is going to be tough amma ya quduri aniyar jajircewa, wannan karon bazaiyi wasa da any slight chance dinshi ba, yayi determine cewa zaiyi fighting for his love no matter what....✍�


Ummin Fasihu🧚🏻‍♀�
8/2/21, 9:45 PM - Buhainat😝: *🙍🏻‍♂️DEEN🙍🏻‍♂�*


*090*


Ajiyar zuciya Deen ya sauke sannan yajuya yakoma cikin school din


wani tent yasamu yayi zamanshi aciki ya harde hannayenshi a qirji ya zubama harabar school din ido


haka Deen yaita zama har lokacin zuhr yayi

tashi yayi yafito daga tent din yafara dube duben Inda zaigano hanyar masjid

kamar yadda Mussadiq yafada akwai signboards masu directing mutum duk Inda yake son zuwa a school din

da taimakon signboards din yagano hanyar masjid din yawuce ciki

bayan sallar ne yafito yana tafe yana kalle kallen mutanen dake zirga2 amma harya koma wurin tent din bega mai kama daita ba

komawa mazauninshi yayi ya zauna yasake harde hannayenshi a qirji yana cigaba da jiran tsanmmani


Tunda Qarfe uku ta buga yaketa baza idanun ganin ta Inda zee zata 6illo

mutane da dama dasuka gama lectures din ranar sai fita suke yayinda wasu sai lokacin ma suke gyara zaman tsayawa school din Kasancewar sunada kingin lectures din gaba

tun yana hange hangenshi daga zaune harya kai ga ya tashi yafito daga tent din yana bin masu wucewa da kallo

qara kai duba yayi ga wristwatch dinshi saiyaga har uku da rabi hakan yasashi fara tunanin kodai suntafi batareda ya lura ba


harya fara fidda tsanmmani da ganinta can kamar ance ya waiga sai yaganta tafe da ita da batool

wani irin nannauyan numfashi yasauke yana murmushin jindadi

beyi wata wata ba yanufesu fuskarshi still dauke da murmushi


Tundaga nesa batool ta hango Deen tafe yana sakin cool murmushinshi

Dan satar kallon zee tayi dake gefenta saitaga fuskarnan nata amugun tsuke take wanda hakan ya tabbatar mata cewa itama ta ganshi

dan ta6e baki batool tayi ta kauda kai

daidai nan Deen ya qaraso

"Aslm alaikum" yafada still smiling

batool kadai ce ta amsa itakau zee ko kallon gefenshi batayi ba taqara gaba

ganin hakan yasa itama batool binta

maramasu baya yayi

"erm... Zainab" yakira sunanta amma ko nuna alamun taji batayi ba


"Zainab please listen to me, please"


cigaba da tafiyarta tayi yadda kasan he's invisible

"Zainab please ki saurareni, just this once please" yafada yana cigaba da binsu


haka yaita binsu yana mata magana amma yadda kasan batasan da wanzuwarshi ba har suka qarasa motarsu

bude seat dinta tayi tashiga tarufo tana danna lock

"Zainab please" yafada yana leqota da glass din motar dake rufe saidai ana iya hangenta Kasancewar ba tinted bane

ko kallonshi batayi ba saima wayarta data zaro tana daddanawa

haka ya sunkuyo yana mata magana wanda batama iya ji Kasancewar glass din asama yake

batool dake kallon komai ta bude mazaunin driver ta shiga itama tana Jin duk badadi ganin yadda zee ke ignoring dinshi

tadan tsaya taga kozai janye daga jikin motar amma taga beda niyya hakan yasata tada motar sannan tayimashi horn

ahankali yatashi daga jikin motar yana kallon zee dake kallon wayarta har lokacin cikin damuwa

matsawa baya yayi don ba motar space and yanaji yana gani motar ta tashi ta wuceshi


da kallo yabita harta fice daga school din gabadaya


Ajiyar zuciya ya sauke yana jin zuciyarshi cikin qunci


yasan dama ba lallai bane zee ta saurareshi ba, ya riga ya tafka kuskuren dazai dade yana danasani, he deserve this and more tunda shi yaja komai, duk Abinda yafaru shine sila


yanzun ma saida yagaji da tsayuwa sannan yawuce wurin tent din daya zauna dazu yaciro waya don kiran Mussadiq.


------


shiru motar ta dauka kamar babu kowa ciki

tunda suka kamo hanya babu wanda yace uffan acikinsu

can batool ta sauke Ajiyar zuciya tadan saci kallon zee dake kallon waje ta window sannan tasake maida kallonta ga titi

"gaskiya Zainab Abinda kika yima gayen nan baki kyauta ba" inji batool


banza zee tayi ta kyaleta

"ko babu komai shi musulmi ne, yayi miki sallama kobazaki yimashi magana ba,atleast answer the salaam amma yayimiki,sallama ko kallonshi bakiyi ba"

Ajiyar zuciya zee tayi tana rolling idanunta
"wai batool meye damuwanki ne? ina ruwanki dana amsa sallamarshi ko ban amsa ba? what if na amsa acikin zuciyata? please batool kibar shiga wannan maganar idan ba sokike mu sa6a ba"

"Zainab ni gaskiya nake fadamiki, kome mutumin nan yayi miki be kamata kiyimashi wulaqanci ba, agaban fa mutane kikayi ignoring dinshi yana binki yana begging dinki amma ko kallo, haba?"

"ni nace ya tareni agaban mutane? duk Abinda nayimashi shiyaja, he even have guts dahar zai tareni, mema zai gayamin idan na saurareshi?"

"ki saurareshi tukunna mana, bakisan me yazo dashi ba, bakisan me zaice maki ba"

"kuma banason sani ok? please and please kifita harkata akan wannan batun batool, banason musamu misunderstanding akan hakan"


Ajiyar zuciya batool ta sauke ta cigaba da tuqinta batareda tasake tankawa zee ba


itama zee maida hankalinta tayi akan window ahaka har suka isa gida.


Washegari ma kamar jiya tana fitowa daga class bayan daukar wani lecture sai cin karo tayi dashi daga dan nesa da class dinsu


dauke kai tayi kamar bata ganshi ba tanufi hanyar fita daga wajen

binta shima yashiga yi yana mata magana da magiyar ta saurareshi not minding who and who is watching


kamar jiya ko kulashi batayi ba ta cigaba da tafiya tama rasa inda zata nufa


daga qarshe tayi hanyar class dinsu batool luckily anata suna ajin ana jiran lecturer yashigo hakan yasa itama fadawa class din tawuce wurin zaman batool ta xauna kusada ita

"kekuma fa? daga ina?"

Ajiyar zuciya zee tadan sauke
"class" ta amsa ataqaice

"to dakika shigo nan bakiga lecture zamuyi ba"

"babu damuwa, I'll take part too"


batool zatayi magana lecturer yashigo hakan yasa suka nutsu


lecture din ya daukesu almost an hour kafin sugama Inda duk Abinda akeyi hankalin zee ba wajen yake ba yayi nisa


bayan lecturer yafita students suma suka fara fita

tattare books dinta batool tayi tajuyo ta kalli zee taga hankalinta ma baya kusa kwata2

girgiza kafadarta tayi wanda hakan yasata yin firgigit ta kalleta

"lafiyar ki kuwa? tunanin me kike?"

Ajiyar zuciya zee tasauke sannan tahau waige waigen class din

"wai har angama lecture din?"

"A'a ke za'a jira, nidai tashi am hungry nasama ma cikina wani abu" inji batool tana miqewa


tashi itama tayi aqasan zuciyarta tana fatan karsu ga Deen idan sunfita

kallon agogonta tayi

awa daya kenan tasan yagaji yatafi ma

da wannan tunanin tafita


saidai me tana fita ta hangoshi qarqashin wata bishiya dake daga opposite din class din jingine ya zubama kofar ido


ganinta yasashi miqewa daga jinginar da yayi yana sakarmata murmushi


saurin kauda kai tayi ta sake rungume books dinta tawani hada rai tazo tawuce


nufota yayi hakan yasa tayi hanyar fita wajen da sauri

"Zainab... wait" yafada yana binta shima da Dan sauri


binsu da kallo batool tayi harsuka fita daga wajen sannan ta girgiza kai itama tafito tayi hanyar cafteria


cigaba da bin zee Deen yayi yana mata magana amma ko kallonshi batayi ba

tarasa Inda zata dosa kuma don zai iya binta duk Inda taje gashi suda wani lecture sai nan da 30mins


data gaji da bin dayake mata saita juyo afusace tana makamashi wani mugun kallo


ganin hakan yasa shima dakatawa yana kallonta

"meye damuwanka danine? wai who are you ma?" tafada afusace

"Zainab..."

"tambayarka nayi waye kai?"

"Kamal ne.. Kamal dinki"

wani kallo tayimashi

"Kamal din wa? as far as am concern banta6a sanin mai irin sunan nan ba"

"Zainab nasan kina tsananin fushi dani amma don allah ki saurareni even if sau daya ne please... nasan nasaki a qunci dayawa..."


"qunci? dawa dawa kasa a qunci? look at me up and down nayimaka kama damai wata damuwa?"


rasa Abinda zaice yayi don kwata2 she's not helping matters

"Zainab..."

"am Happy bakaga haka ba? ko bakaga alama ba? banada wata damuwa daidai da qwayar zarra, quncin me kake magana akai to?"


"Zainab..."

"look sunana yafita daga bakinka don ba'ayishi don kazo kana cikamun kunnena dashi ba, as far as am concern I don't know you, ban ta6a ganinka ba so please kabar bina kamar wadda kabaiwa Ajiyar kidney dinka, I have nothing to do with you ok? spare me please"

tana kaiwa nan ta juya

"Zainab! Zainab!!"


ina harta wuce


furzar da zazzafan huci yayi yana riqe waist dinshi

"this is serious" yafada ahankali


Ataqaice haka Deen yaita bibiyar zee a school cikin son ganin ta tausaya ko sau dayane ta saurareshi amma a banza don kwata2 qara botsarewa takeyi every passing minute


wani lokacin haka zaita binta yana mata magana taqi tankamashi yadda kasan da gini yake wani lokacin kuma tafada mashi baqa


saidai duk Abinda take mashi baya sarewa haka yake lallashin zuciyarshi yana cigaba da binta yana baiwa kanshi kwarin gwiwar cewa watarana zata saurareshi


kullum haka zaizo ya wuni a school din yana binta batareda gajiyawa ba

kwata2 baya damuwa da irin wulaqancin da zee kemashi don yasan he deserve it tunda shine sila

wannan karon yayi determine bazai sareba kamar yadda yasaba abaya, he's determine to show zee how far he can fight for her love


batool dai abin bayamata dadi kwata2

ita Deen bala'in tausayi yake bata musanmman idan taga yabiyo zee tana ignoring dinshi

akwai lokacin da taje tasameshi tace mashi ya kyaleta tunda bata saurararshi yabata space atleast qila tasauko amma saiyace mata karta damu shi Abinda takemashi baya damunshi cos he know he deserve it

haka dai ta kyalesu dole ta zubamasu ido

Mussadiq ma a 6angarenshi yana sane da duk Abinda ke faruwa saidai ya kyaleshi yana son gani how far he can go and he was amazed as how Deen yaqiyin ko gexau daga qudurinshi na shawo kan zee


Deen fa yakoma zee's chewing gum, duk Inda tayi yana biye saidai idan tana a class

tun tana mashi masifa harta kyaleshi takoma bata tankamashi ko shekara zaiyi yana zuba

sosai wannan taurin kan na Deen yabata mammaki

tasanshi very timid da saurin sarewa but this time around labarin na neman chanzawa

abubbuwan datake mashi ya isa ya haqura ya kyaleta koda itace autar mata amma ita gani tayima ko ajikinshi kamar ma bashi take mawa ba

haryanzu taqi bashi damar explaining kanshi shima kuma haryanzu beda niyyar haqura

wani lokacin cikin mutane zaita binta babu Abinda ya dameshi saidai ita taitajin kamar ta nutse

tagaji, tagaji sosai da wannan nacin na Deen hakan yasa watarana daya biyota yana mata magana tayi wata hanya

binta yayi yana cigaba dayimata magana har sukaxo wani wuri da babu mutane

juyowa tayi tana kallonshi hannaye riqeda kugu hakan yasa shima tsayawa yana kallonta


shiru yabiyo bayan haka suna kallon kallo

"gayamin me kakeso, mezanyi maka kabar bina kamar snail and it's shell?" ta tambaya a qule

murmushi keson kufcema Deen amma yayi saurin hadiyewa

"inason ki saurareni ne please"

"ok ina sauraronka meya faru?" tafada cikin qosawa

rasa ta ina zaifara yayi

"you have 2mins" tafada tana kallonshi

"Zainab it's about Abinda yafaru atsakaninmu ne, Don allah kiyi hqr ki gafarceni, nasan ban cancanci yafiyarki ba amma Don allah ki yafemin..."

"na yafemaka, shikenan?" ta katseshi da hakan


Dan buda idanunshi yayi

"d..dagaske?"

"dagaske, yanzu zan iya tafiya?"


cikin jindadin yafiyar datayi mashi yace
"oh thank you, nagode nagode sosai Zainab"

"it ok, now I'll get.going karka qara bibiyata kuma" tafada zata wuce


saurin tare gabanta yayi yace
"No please Zainab"

"meye kuma?!" tafada afusace

"O'O! please don't shout" yafada pleadingly


harara ta gallamashi jin ya ambaci sararshi

"Zainab I know Abinda zance yana iya 6ata miki rai amma kiyi hqr, please mukoma kamar da please, Zainab I still love you, wlh haryanzu my heart beats for you please.."

"how dare you?" tafada ahankali idanuwanta na kadawa

shiru yayi ganin reaction dinta

"how dare you say that to me?"

"Zainab am sorry but.. that's the pure truth, I love you Zainab, ban ta6a daina sonki ba kullum soyayyarki banda qara hauhawa babu Abinda takeyi a zuciyata"

"qarfin halinka ashe yawuce yadda na musalta?" tafada tana kallonshi sosai kamar da mammaki

"kiyi hqr zee, amma this is the truth... I love you... I still love you, I never stop loving you and I'll never stop"


Dan murmushi zee tayi
"wane irin love kake magana akai don ya kasu kashi kashi"

"true love zee, inamaki soyayya ta gaskiya"


"soyayya ta gaskiya, irin wanda kesa agudu abar heart breaking letter?"

lumshe idanu Deen yayi zuciyarshi na zafi

"Zainab..."

"ko irin wanda kesa a karya alqawari?"


"Zainab kiyi hqr"

"ni tambayarka nayi bacewa nayi kabani haquri ba" tafada hawaye na taruwa a idanunta

"wacce daga ciki kake nufi?"

"Zainab... nasan na yaudareki nakuma ci amanarki amma..." saikuma yarasa Abinda zaice


"yes? amma me?" tafada tana kallonshi hawayen idanunta na barazanar zuba


to her greatest surprise saitaga yafara yin qasa before she knew it yana kan knees dinshi

wara idanu tayi tareda kyafkyaftasu akanshi

"amma kiyi hqr zee, kiyi hqr... banida hujjar dazan kare kaina kona wanke kaina illa nabaki hqr"

"Deen meye haka kakeyi?" tafada tana dan jabaya

"kiyi hqr zee"


"ka tashi" tafada hawayenta nazubowa

"No zee, I can lay for you ma, nidai Kawai ki yafemin"

ganin zaiyi laying din yasata cikin tsawa tace
"stop!"

ganin be saurareta yasata qarasowa gabanshi dasauri itama ta zube a gwiwowinta tana tareshi

"I said stop!" tafada tana turashi baya

"nacemaka kayimin kneeling ko kayimin laying ne?" tafada cikin kuka

"I don't know what to do again Zainab" yafada idanunshi na kadawa sosai

"ni nace kaimin wani abu? you always make me cry, Ka qware wajen sani kuka, kanajin dadi kaga ina kuka ko?" tafada cikin kuka sosai

girgiza kai Deen yayi yana matsowa kusada ita

"A'a wlh, Zainab aduk duniya,babu Abinda na tsana sama da kukanki, I hate seeing you cry"

"amma kuma kake sani? duk wadancan daka sakani be isheka ba saika qara sani?" tafada cikin kuka sosai dama qiris take jira

"Zainab kiyi hqr, please forgive me, bansan yadda akayi nima nake saki kuka ba, I swear it's again my wish"

"against your wish? katafi kabarni Deen, shima against your wish ne?"

sunkuyar dakanshi yayi daidai da digar hawayenshi

"nasoka da dukkan zuciyata Deen, nabaka amana na yarda dakai na damqamaka amanar zuciyata as a whole amma kai mekayi? you broke it into pieces and throw it back at me!"

runtse idanunshi Deen yayi gam zuciyarshi na mugun zafi

"katafi kabarni Deen alokacin danafi buqatarka, ka kunyatani, you betrayed my trust for you!"

"am..sorry" yafada cikin rawar murya sosai


"katafi without even looking back for once, katafi kabarni without caring wane hali zan shiga... sau daya ko,sau daya,baka ta6a waiwayena ba"

rufe fuskarshi Deen yayi da taffukanshi zuciyarshi na wani irin zafi

"kuma shine yanzu zakace kana sona kuma? are you this cruel?" tafada tana kallonshi da jajjayen wet eyes dinshi

ahankali Deen ya janye taffukanshi daga fuskarshi datayi ja ga hawaye a cheeks dinshi

"Zainab nasan nasaki a qunci da baqinciki, nasan nayi breaking heart dinki amma wlh bada son raina bane nayi hakan kuma nima na azabtu don tun bayan rabuwarmu dake ban qara farinciki ba.."

"shiyasa har kayi moving on harka zama wani a duniya? while nikuma inanan nakasa gaba nakasa baya"

Dan lumshe idanu Deen yayi yabude yace
"Zainab duk Abinda nazama aduniya kece sila, kece silar sanina a duniyar nan da'akayi"

"katafi kabarni Deen batareda tunanin kadawo kaga halin daka barni,acikiba ko sau daya"

"Zainab nadawo, wlh nadawo... nakasa jure zama babu ke wlh adaddafe nayi three weeks nadawo amma...amma aka tareni da mummunan labarin daya girgiza zuciyata akace min wai...wai kinyi aure kinbar qasar"

dagowa zee tayi tana kallonshi da rinnanun idanunta

"ni?" tafada ahankali

"eh zee, fadin halin dana shiga aciki a lokacin baxai misaltuba, kusan haukacewa nayi, zee nayi kuka, nayi nadama nayi danasani kuma ina kanyi, wlh tun bayan rabuwarmu basake farinciki ba rayuwata bata sake tafiya daidai ba"

shiru Kawai Zainab tayi tana kallon yadda yake magana yana hawaye kallo daya zakamashi kasan da dukkan gaskiyarshi yake magana

"Zainab ki saurareni yau zan fadamiki komai, zan fadamiki silar komai"


shiru zee tayi tana kallonshi nawani lokaci sannan tace
"ina sauraronka"....✍�


*naso mugama Deen kafin babban sallah amma allah be yarda ba, anyimana haihuwa najiki sosai so baxan dinga samun damar posting ba don haka anan zan tsaya harsai bayan sallah idan allah yakai ranmu, allah yanunamana wucewarta lafiya🤲🏻*


Ummin Fasihu🧚🏻‍♀�
8/2/21, 9:45 PM - Buhainat😝: *🙍🏻‍♂️DEEN🙍🏻‍♂�*


*091*


*Barka da sallah to you all, fatan anyi sallah cikin qoshin lfy, allah ya maimaita mana🤲🏻*


"it all started ranar damuke waya dake daddy dinki yayi banging in

naji komai.. naji duk fadan da daddy yayimiki da kalamanshi akan soyayyarmu..."


_*FLASHBACK*_


_"wato ke bakyajin magana ko? duk abinda nake gayamaki ta kunnen dama yake shiga yafita ta haggu ko? dama bakida hankali bansaniba?"_

_"ina nunamiki hanya kina rufe ido! kinje kina biyewa wancan dan iskan yaron ya huremaki kunne ya bushe maki idanu bakya ganin kowa da mutunci ko? eh!!"_

_"kullum kinacan banda qara liqemashi babu abinda kikeyi ko? and itama good for nothing uwarki babu abinda takeyi sai goyon bayanki ko?"_


cikin kuka sosai yajiyo muryar zee nacewa

_"don allah daddy kayi hqr wlh ina sonsh..."_


cikin ihu sosai yaji daddy ya katseta da

_"will you shut that your dirty mouth up! are you stupid! ina yimaki magana kina min zancen banza zancen wofi?!"_

_"harni zaki fadawa soyayya? ni zaki fadawa kina sonshi! soyayyar banza soyayyar wofi! soyayyar dakike mashi yakai wacce nakemaki koko soyayyar dayake miki takai wacce nakemaki? wato ni kuka maida shashasha ashe? ni inacan ina haukana ku kunacan kuna abinda kukaga dama babu abinda ya dameku.. am disappointed in you Zainab, very disappointed"_


kitt... Deen ya katse kiran don jiyayi bazai iya cigaba da saurare ba


sosai jikinshi yayi sanyi musanmman idan yatuno sautin kukan zee dayake jiyowa qasa qasa

tashi yayi daga kishingiden dayake kan katifarshi ya zauna ya jingina da bango


sosai zuciyarshi ta quntata ga wani d'aci d'acin dayakeji a maqoshinshi

haka ya zauna shiru na wani lokaci ya kafe wuri guda da ido


besan iya lokacin daya dauka ba ahakan sai jiyayi haske ya dallomashi fuska sanadin yaye labulen dakinshi da akayi

dagowa yayi ya kalli kofar yaga kakace

"wai kyakyawana kwana biyun nan meke 6oyeka a daki? saikazo kashige kayi shiru kamar wata amaryar qauye, badai bakajin dadi bane kake 6oyemin?" inji kaka tana qarasowa

gyara zamanshi yayi yana kokarin gyara yanayin fuskarshi

"A'a kaka Kawai nagaji ne shiyasa nashigo nadan kwanta"

"Ka kwanta? kwanciyar lafiya yanzu bayan la'asar? maza tashi to kaje can shagon Abba ka qaromana barkono don naga wancan be isa kaga zaka dan warware ma idan kadanyi tafiya amma idan ka kwanta yanzu ai kasan abinda zaka jawowa kanka" tafada tana kwance ha6ar zanenta

"to" ya fada yana qoqarin tashi


kudin tabashi tana fadamashi abubbuwan dazai siyo sannan tarakoshi har tsakar gida saida taga fitarshi sannan takoma


ahankali yake tafiya a layin nasu hannayenshi zube a aljihunshi kanshi asunkuye

idan ka kalleshi saikayi tunanin tafiyar qasaita yakeyi yayinda kwata2 ba haka bane damuwar dake ranshi ma ta isheshi


shagon Abba din yaje inda ya iske jira sosai hakan yasa yanemi wuri a dan bencin dake waje ya zauna don jiran jama'ar su rage


harde hannayenshi yayi a qirji ya kafe waje guda da ido ya lula duniyar tunani


besan adadin lokacin daya dauka ba ahakan sai jiyayi an dan girgizamashi kafada

saurin dagowa yayi ya kalli mai girgizamashi kafadar sai yaga ashe Abban ne

"yadai kyakyawan kaka? kaxo ka zauna nan shiru tundazu sai magana nakemaka bakaji, halan dai ba magana kaje ka janyowa kaka ba" inji Abba cikin tsokana don shima tsarar Deen ne don ko zai girmeshi baxai bashi shekaru masu yawa ba


murmushi Kawai Deen yayi yace
"siyayya nazoyi naga shagon acike shiyasa nace bari najira"

"waya gayamaka ana komawa gefe azauna ajira shago yarage? sai kaga wadanda suka zo daga bayanka ma,sun rigaka tafiya, irin haka ai magana zakayi saina baka ma batareda kajira ba tunda duk yarane masu sayayyar amma kazo ka zauna anan salan kaja kaka taji shiru tafito ta tattaro yan unguwa zuwa shagona nemanka" ya qarashe cikin tsokana

murmushi Deen yasakeyi sannan yace
"barkono zaka bani da maggi"


"na nawa?" inji Abba yana,komawa shagon da yanzu babu kowa ciki Deen na biye dashi


saida Deen yagama siyayyarshi tsaf sannan yabiya yajuyo yakamo hanyar gida


daga nesa ya hangi wata dalleliyar mota kofar gidansu

ahankali yake tafiya idanunshi akan motar yana wondering ta wanene

be gama zancen zucinshi ba yaga anfito daga gidansu

gabanshi ne yafadi lokacin da sukayi ido hudu da daddy

wani matsiyacin kallo daddyn ya jefeshi dashi sannan yayi gaba fuuu mutumin dake taredashi na maramashi baya yana yi yana waigen Deen dayayi tsaye yakasa qarasowa


wannan motar yaga sun nufa sun bubbude kofoffin gidan gaba sun shiga sannan aka tada motar suka bar wajen atsiyace


bin motar Deen yayi da kallo harta bar layin

gabanshi ne yacigaba da faduwa

meya kawo daddy gidansu?

tunawa yayi da magangganunshi na dazu dayaji ta waya hakan yasa zuciyarshi taqara tsinkewa

koma me yakawoshi ya tabbata ba alhairi bane duba da matsiyacin kallon daya jefeshi dashi

ahankali kamar marar lakka yaja qafaffunshi yanufi kofar gidan nasu cikin fargabar abinda zai tarar aciki


da sallama yashiga ciki amma shiru hakan yasashi ida qarasawa cikin gidan inda ya hango kaka zaune kan sabuwar tabarmarta ta buga tagumi kanta a sunkuye


ahankali yasakeyin sallama yana qarasowa yana kallon kakar tashi wadda harlokacin bata dagoba bare ta amsa sallamar tashi

saida ya qara kusantota sannan ya lura da dami damin kudadden dake gabanta yan dari biyar biyar sunkai wajen wrapper biyar hakan yasashi dan wara idanu yana kallonsu shima

"kaka?" yafada yana qarasowa

"kaka meye wadannan?" yafada yana kallon kudadden

sai a lokacin kaka tadago ta kalleshi

"idanuwanka sunfara ciwone? kudaddene, kudadden daka siyar da mutuncinmu akai"

kallon rashin fahimta Deen yayimata
"bangane ba kaka"

"tayaya za'ayi kagane Kamal? tayaya? bayan baka dauki maganata abakin komai ba baka yarda da,hangen danake maka ba" tafada cikin qunar zuciya

"kaka..."

"Tunfarko saida nagayamaka yarinyarnan ba sa'arka bace, tafi qarfinka amma ka nunamin kafini sanin abinda duniya keciki, to gashinan... gashinan ubanta yazo har gida ya taddani har nan yayimin wankin babban bargo babu abinda ya manta be gayaminba, ga Kuma kudi nan ya ajiye yace akyalemashi yarshi yariga yayimata miji, yanzu Kamal abinda zakamin kenan? ina zaman zamana? ina rayuwata cikin rufin asiri da kwanciyar hankali zakaje kasiyomin tashin hankali da kudinka? da mutunci na da komai wadannan mutanen sukazo sukayimin tass suka zubemin wadannan tsinnanun kudadden niga matsiyaciya? yayi maka kyau" ta qarashe tana miqewa tsaye tana share hawayenta


tunda tafara yaji kamar an zaremashi dukkanin lakka ajiki yakasa koda kwakwarar motsi

nuna kudadden kaka tayi cikin muryar kuka tace
"gasunan ka kwashesu don dama kai suka kawomawa, sunce dama abinda kakeso,kenan ba diyarsu ba Kuma idan basu isheka ba kayi magana su qaromaka don suna iya baka ko nawa ne don ka kyalemasu diyarsu"

tana kaiwa nan tajuya tashige daki tarufo tana hawaye

kasa ko kwakwarar motsi Deen yayi awajen

sosai zuciyarshi taqara dagulewa yarasa abinda kemashi dadi

yana nan tsaye aka fara kiraye kirayen magrib

cikin mutuwar jiki yajuya yanufi kitchen dinsu ya ajiye siyayyar dayayi sannan yafito yawuce wajen bokitan ruwansu batareda yako kalli gefen kudadden dake kan tabarma har lokacin

ciccika butocinsu yayi daruwa yayi alwalla sannan yadawo kofar dakin kaka

turawa yayi yaji gamm hakan yasashi sanin rufewa rtayi daga ciki


cikin kwantar da murya yace
"kaka don allah kiyi hqr kitaso kiyi alwalla lokacin sallah yayi"

banza tayi dashi ta kyale

"kinji kaka?"

nanma shiru

jiyayi an kabbara sallah hakan yasashi cewa
"kaka zantafi masallaci don allah kifito kiyi alwallar ga ruwan can nazuba"

banza tayi nan ma ta kyaleshi hakan yasashi juyawa Kawai yatafi zuciyarshi a quntacce


koda yadawo daga sallar sai yaga alamun tafito tayi alwalla din don butarta ma babu ruwa hakan yasashi sake nufar kofarta saidai har lokacin a kulle take


haka yatsaya yayta bubbuga yana bata haquri akan tabude amma tayi banza dashi har lokacin isha'i tayi

dole ya haqura yaje ya chanzo alwalla yasake fita sallah

koda yadawo ma,bata budeba haka yasha bubbugarshi yagaji ya haqura yaje ya kwashe kudadden dasu daddy suka bari zuciyarshi na quna yashiga dakinshi

daidai nan yaji wayarshi dake gefen katifa na ringing

saida yafara adana kudadden sannan yazo ya dauki wayar yaduba lokacin harta tsinke

ganin sunan zee yayi Kuma har 3missed calls

sauke ajiyar zuciya yayi sannan yakashe wayar gabadaya ya ajiyeta


ranar sosai kaka tayi fushi dashi don qin bude dakinta tayi tana jinshi yana didimarshi shikadai a tsakar gidan taqi fitowa

shi yayi tatar qullin koko ranar ya daka barkonon duk tana jinshi taqi fitowa dukda yadda takejin kamar tafito ta tayashi din don tasan dole aikin yayimashi yawa


aranar dai haka kowannensu ya kwanta rai babu dadi


Washegari tunda yadawo daga sallar asuba yashiga kiciniyar dora koko


saida yafara hura wuta ya dora ruwa sannan yaje yafara surfen waken qosai

kaka na daki tana jinshi amma bata fito ba don har lokacin tana cikeda baqincikin abinda su daddy sukazo sukayimata jiya

tana jinshi harya gama yazo bakin dakinta ya kwankwasa

shiru tayi batace komai ba saiya sake kwankwasawa yace
"ina kwana kaka"

nan ma shiru

yasan tana jinshi hakan yasashi cewa
"kaka zantafi kai markade"

nan ma shiru

hakan yasashi tashi zai juya yaji muryarta qasa qasa tana cewa
"kasa rigar sanyinka"

kallon kofar yayi yadanyi murmushi sannan yace
"to kaka"

komawa yayi daki yasanyo rigar sanyin dukda bawani iska akeyiba yadawo yasake mata sallama sannan yatafi


be dade ba sosai yadawo da markaden lokacin har gari yafara haske

ganin kaka agaban murhu tana hura wutar kosai yasashi jindadi sosai


zuwa yayi ya ajiye markaden yazo zai tayata hura wutar saita tashi tabar mashi murhun fuska atamke tawuce tadauki markaden

be damuba ya cigaba da hura wutar itakuma tashiga hada kullin kosan


haka sukaita aiki ba uhm ba uhm uhm kamar kurame

da taimakon Deen suka sheqa kokon lokacin har yan saye sunfara shigowa


ahaka suka shiga sallaman customers dinsu inda kaka ke gaban kaskon qosai shikuma Deen ke sallaman masu saye


zuwa 10 saura sungama tsaff sun gyara gidan, har lokacin kaka taqi sakarmashi fuska

ahaka suma sukayi kalaci sukayi wanka

ganin Deen beda niyyar shiryawa yatafi school yasata kallonshi fuska adaure tace
"Makarantar fa?"

"kaka yau bazani ba"

"dalili?"

turo baki yayi
"nidai bazan iya fita kina fushi daniba"

harara ta gallamashi

"zakaje ka shirya ka wuce koko?"

qara narkewa yayi yace
"kaka wlh konaje bazan iya komai ba, don allah kiyi hqr kibar fushi dani"

"ni fushi nace inayi dakai? Kawai kaje kaitayi tunda nidai baka ganina da mutunci kaje kayi duk abinda kakeso, babu ruwana"

"haba kaka, wlh bakiji yadda nakejiba idan kina fadin haka, duk duniya wa nakedashi bayan ke? ke kadai zaki sani nayi ki hanani nabari don allah kibar fadin haka" yafada kamar zaiyi kuka

"Kuma shine nace ka rabu daita kaqiya? duk abinda nake gudanmana kenan ai, don yimin yarinyarnan tayimin don alamu sun nuna tanada hankali amma ai ba anan take ba, yanayinmu dasu ba daya bane kuma bazai ta6a zama daya ba, mu dasu mabanbantan mutanene masu mabanbantan rayuwa wanda hadawarmu abune mai matuqar wuya"

"kiyi hqr kaka, wlh nima bansan abin yakai haka ba amma insha allah zan kiyaye"

kauda kai Kawai tayi batace komai ba

"kinji don allah kaka?" yafada cikin marairaicewa

"to indai kanason mu shirya dakai kafita harkar wannan yarinyar, iyayenta ba mutanen arziqi bane ka kyalemasu diyarsu suyita kaya allah zai baka wacce tafita, kadai jini ko?"

"to kaka"

"bawai to a iya fatar baki Kawai, a aikace nakeso don ko a Makaranta ban yarda ku haduba"

"to kaka, insha allah hakan za'ayi" inji Deen in,affirmation dukda yasan wannan abun abune mai matuqar wahala


"kudaddensu fa ya kayi dasu?" inji kaka


"na adana, zan maidamasu kayansu"

"dadai yafi" inji kaka tana ta6e baki


"yanzu katashi kashirya kawuce Makarantar don bawai bari zanyi kayi qalula ba"

murmushi Kawai Deen yayi yatashi yashige dakinshi tabishi da kallo cikeda qauna da tausayawa


Ranar dayaje school be ganta ba Kuma yasan hakan be rasa nasaba da daddy don yasan tsaff ya hanata zuwa kodon karsu hadu


haka ya yini a school din ranar cikin rashin kuzari, babu abinda yake mararin ji kamar muryarta, idan yatuna da sautin kukanta najiya saiyaji ranshi yaqara dagulewa


gashi ya manta wayarshi agida da babu abinda zai hanashi kiranta

yasan yayima kaka alqawarin fita harkarta amma shi kanshi yasan abune marar yiwuwa

bazai iya rabuwa da zee ba, bazai iya datse soyayyarsu ba don rabuwa daita daidai yake da rabuwa da farincikinshi gabadaya


haka yawuni a school din ranar batareda ya iya ta6uka komai ba har lokacin tafiya gida yayi yakoma gida rai duk badadi


koda yadawo gida da doqinshi yafada dakinshi don daukar wayarshi yakirata saidai yaga wayam be ganta ba

neman duniyar nan yayimata be ga ko abu mai kama daita ba


yana cikin haka ne kaka tashigo ta taddashi yana bincike bincikenshi hakan yasata hade rai tace

"wai meye haka kawani burkita daki kamar dakin mahaukata?"

yana dan yarfe gumin dayayi na neman dayake yace
"kaka wayata nake nema wlh, naduba koina,ban ganta ba"


"wayar allurace dazata 6ace harka burkita daki haka don nemanta? to tana wajena"

dagowa yayi ya kalleta yaga tawani qara hade rai tana kallonshi

"tana wajenki?"

"eh" tabashi amsa kai tsaye

"to.. amfani kike daita?"

"A'a Kawai daga yanzu nahanaka riqeta tunda ba dole bane riqe wayar" tafada tana cika tana batsewa


"amma.. meyasa" yafada ahankali

"shine nace saboda ba dole bace, aidai duk cikin masu kiranka nice mai muhinmmanci ko? to zan haqura koma menene saimun hadu sai nafadamaka amma yanzu dai bakai ba waya"


shiru Deen yayi rai babu dadi

"menene kawani sunkuyar dakai kamar wanda akayiwa rasuwa?"

ahankali ya girgiza kai
"A'a babu komai"

"to maza muje kaci abinci yau abinda kafiso nayimaka" tafada tana mashi murmushi don lightening dinshi

"to" yafada Kawai yayi hanyar waje rai babu dadi


a tabarmar dake waje ya zauna ya jinginar da kanshi yanajin zuciyarshi na d'aci

ahaka kaka takawo mashi abincin ta tusashi gaba tana bashi abaki tana mashi fira duk don farantamashi


shidai amsan abincin Kawai yake yana tauna yana hadiyewa badon dadi ba don gabadaya bemada appetite

sosai zuciyarshi ta dagule, yasan saboda zee kaka tadauke wayar wanda hakan ke nufin bazai qarajin muryarta ba

saidai wani bangaren zuciyarshi ta tausheshi kan yayi hqr idan tahanashi waya daita ai bazata hanashi haduwa daita a school ba

hakan yasashi jin dan sauki sauki yadan saki ranshi yana jin kamar yajawo gobe don doqin ganin zee


Washegari tunda wuri yaje school din

dukda bayada lecture ko daya haka yabuga safkon zuwa duk don yaganta saidai shiru

haka yaita gararanba cikin school din amma babu zee babu alamunta


shine har bayan la'asar school din amma ko mai kama daita be ganiba class dinsu kuwa yaje sau babu adadi amma babu ita, dole daga baya yaja qafaffunshi yabar school din rai adagule


wasa wasa saida sukayi sati batareda sun haduba ko sunyi waya

izuwa lokacin yagane tabar zuwa school ne don kullum haka zaije yaci zamanshi a school amma babu ita babu alamunta

ga kaka har lokacin taqi bashi wayarshi yakuma nema adakinta beganiba don ba qaramin 6oyo tayimata ba


cikin satin nan guda duk ya chanza kamar bashi ba, kallo daya zakamashi kasan yana cikin tsananin damuwa

kaka ma na lure da yanayinshi dukda qoqarin 6oyemata dayakeyi saidai babu yadda ta iya don ita aganinta hakan yafi gwara yarabu daita tun wuri kafin komai ya lallace, haka yasa taita iyakar qoqarinta wajen ganin tana yayemashi damuwa ta hanyar yimashi abubbuwan datasan yanaso saidai ko kadan hakan be taimakama yanayinshi ba don zuciyarshi tariga tayi nisa, batajin kira.


Ana haka watarana Deen yadawo daga school ya tadda gidan a kulle

ganin hakan yasashi wucewa gidan maqocinsu Mallam Nasiru don mafi yawanci idan zata fita nan take barin makulli

yaro yasa yashiga ya tambayomashi ko an bar makulli

can saiga matar Mallam Nasirun tafito dakanta tabashi makullin tace ai haihuwa kaka taje amsa qasan layinsu batama dade da tafiya ba


amsar makullin yayi yaimata godiya sannan yawuce yabude gida yashiga


direct dakinshi yashiga ya ajiye littatafanshi sannan yafada kan yar katifarshi


shiru yayi ya qurawa ceiling idanu can kamar wanda aka tsikara yamiqe zaune yana zare zaren idanu sai kuma yamiqe dasauri yafita yanufi dakin kaka.


bincike yafarayi adakin yana duba every possible place da kaka zata 6oyemashi waya


haka yaita bincike yana yi yana kallon kofa harwani hada zufa yakeyi, can dakyar yaganota can qasan kwallarta ta daddaneta da kaya

ajiyar zuciya ya sauke yana fiddota

qara kallon kofar yayi sannan yasamu wuri ya zauna gefen gadonta yana kunna wayar don akashe take


cikin sa'a kau takama dukda battery dinta yayi low sosai


shiga yayi call log yaga number ta ce asama don dama itace tayi kiran qarshe


qurawa number ido yayi nawani lokaci sannan yakai hannu da niyyar dannamata kira saidai kafin yayi hakan kiranta yashigo


tsayawa yayi yana kallon kiran yakasa dagawa harta katse

can saiga wani kiran

lumshe idanu yayi yanajin sanyi a zuciyarshi, dama yasani duk inda take tana cikin damuwa kamar shi kuma tana missing dinshi itama

akira na uku ya daga yakara a kunne

shiru yaji ba'ace komai ba hakan yasashi cewa
"Zainab.."


nan ma shiru

"hello Zainab?"


nanma shiru


"Zainab is this you? please say something" yafada cikin damuwa


"Deen..." yaji tafada cikin rawar murya saikuma sheshekar kukanta yabiyo baya


"Zainab are you crying? please kibari kinji kar zuciyata tabuga, am ok kinji?" yafada yanajin kamar shima yayi kukan


"Deen ina kashiga? nakusan mutuwa saboda fargaba, meya samu wayarka?" yaji tasake fada cikin kuka


"am ok zee, babu abinda yasameta Kawai babu charge ne" yafada cikin son kwantar mata da hankali

"no Deen you are not ok, gayamin meya faru? me daddy yayimaka?" tafada cikin kuka


"babu komai Zainab, babu abinda yayimin. I love you and I'll never back off, no.matter w..."


fittt... yaji anfige wayar hakan yasashi juyowa arazane


wara idanu yayi cikin faduwar gaba ganin kaka tsaye agabanshi da wayar hannunta

zaiyi magana yaga takara wayar a kunne yaci ta cigaba dacewa

"eh yana jinki, Mallama mekuma kike nema da jikana? mekuma yasaki nemanshi?"

shiru tayi saikuma tace
"eh nice, kaka ce nagodema allah dayasa kika gane hakan, meye kuma kike nemanshi bayan abinda kukaimashi eh?" tafada amasifance

"to ahir dinki wlh, karki qara kiran yarona wlh don shima yariga yagama dake, dama ai qarfin haline irin nashi banda haka ai ke ba kalar matar dazai aura bace"

"kaka.." inji Deen daya sandare atsaye tunda tafara


"menene? menene kake hanani magana? kabari nayimata wonin

kina jina? wlh kifita harkar jikana kina jina ko? muba,kowan kowa,bane,bamuda wadanda zasu tsayamana idan kika jefamu a chakwakiya. muna zaman zamanmu ne cikin rufin asiri da wadatar zuciya, muna zamanmu cikin farinciki don allah karki tarwatsa mana shi.don allah ki kyalemin yaro kije kema allah yahadaki da daidai ku masu kudi muma haka
mungode daduk dawainiyar dakukayi mana da qaunar dakuka gwadamana amma don allah karki sake nemanmu, ba don muba don allah"

daga haka ta katse wayar kitt tayi jifa daita kan gadonta

juyowa tayi afusace tana kallon Deen dake kallonta shima kamar wanda ruwa ya cinye ga idanunshi sunyi jajir

nunashi tayi da yatsa

"wato bakajin magana ta ko? ban isa nasaka kayi ba ko kuma ban isa na hanakaba ko? to shikenan ga wayar nan kadau abinka amma kasani kasake ka qara kiranta ko takiraka ka daga ban yafe ba kuma ban yafe ba idan kaje kuka hadu bare harka bude baki kayimata magana, kai ko ita tazo wajenka tayimaka magana ka amsa ban yafeba, shashasha Kawai!"

daga haka ta juya ta hankada labule tafice daga dakin afusace


binta da kallo yayi harta fice sannan yazame yazauna bisa gadonta ya dafe kanshi dake mugun saramashi da hannu bibbiyu....✍�


Ummin fasihu🧚🏻‍♀�
8/2/21, 9:45 PM - Buhainat😝: *🙍🏻‍♂️DEEN🙍🏻‍♂�*


*092*


Aranar Deen kasa walwala yayi kwata2, tunaninshi bewuce wane hali zee zata shiga ba bayan wayar dasukayi, haka Kawai yakejin duk inda take ba lfy.


haka ya qarashe wunin cikin tsananin damuwa

a bangaren kaka kau shareshi tayi dukda lura da halin dayake ciki datayi saidai batajin tana iya barin wannan al'amarin yacigaba da tafiya ahakan don tunfarkon kawo zancen zee taji abin be kwanta mata ba don bata qaunar abinda zai tarwatsa dan farincikinsu har yakai ga tonuwar babban sirrinta na shekara da shekaru


a daren ranar kasa barcin kirki yayi, washegari kuma tunda wuri yafice school ko yadanji sauqin abinda yakeji dukda yanzu school din yabar yimashi dadi saboda rashin zee acikinta

sosai yakejin kewarta kamar sunyi shekaru basu hadu ba

ranar haka ya yini a school din batareda yama fahimci lectures din daya dauka ba


bedawo gida ba sai bayan asr inda yauma kamar rannan ya tadda wata galleliyar mota a kofar gidansu


tsayawa yayi yana kallon motar abubbuwa da dama na kai kawo a zuciyarshi


can sai yanufi hanyar shiga gidan zuciyarshi fall saqe saqe


da sallama yashiga yana bin mutanen tsakar gidan da kallo kamar yaddasuma suka dago suna kallonshi


kaka ce zaune kan tabarma tana facing daddy da wannan mutumin dasuka zo tare rannan


amsa sallama duk sukayi suna kallonshi hakan yasashi qarasawa yana karantar yanayin fuskokinsu

gani yayi su daddy suna mashi kallon dayasha banban dana rannan don har murmushi yaga kamar daddyn namashi itakau kaka fuskarta babu yabo babu fallasa


qarasawa yayi gabansu ya russuna ya gaidasu cikin girmamawa suma suka amsa cikin kulawa

ganin zai tashi yasa daddy cewa
"A'a d'ana zauna ai dama maganar takace"

babu musu ya zauna yana satar kallon kaka dataqi kallonshi tundazu

wanda ke tare da daddy yace
"nasan kana mammakin meya dawo damu yau don nasan kaji labarin abinda yakawomu rannan ko?"


shiru Deen yayi kanshi aqasa hakan yasashi cigaba dacewa
"munzo bada hqr ne akan abinda yafaru rannan, agaskiya muma mun gane abinda mukayi samm be kyautu ba, munyi nazari munga sam bamu kyauta ba shiyasa mukazo baku hqr don muma ba ason ranmu mukayi hakan ba.
kunsan dai yadda duniyar ta lallace yanzu, masu gaskiya yan qalillan ne, yanzu a duniya saika rasa wanda zaka yarda dashi don gur6atattun suke 6ata nagarin shiyasa duk ake tsoron tsoro

abinda yasa daddy be yarda da zancenku ba kenan don yawanci mutane basuda gaskiya saisu nuna suna sonka don allah while a zuciyarsu ba haka bane. ba,komai alhaji ke gudu ba sai yaudara shiyasa Tunfarko beyi na'am da zancenku ba don Zainab itace diyarshi daya tilo bazaiso abinda zai cutar daita ba shiyasa Tunfarko yaqi amincewa amma yanzu yagano gaskiya, ya bincika yaga dagaske bazaka yaudareta ba shiyasa yajawoni muka sake dawowa don mubaku hqr akan abinda yafaru wancan karon, kuyi hqr sharrin zuciya ne kuma insha allah tunda yanzu ansamu fahimtar juna hakan bazai sake faruwa ba, don allah d'ana katayamu ba Baaba haquri"


tunda suka fara magana kan Deen naqasa yana sauraronsu bece komai ba harsuka kai aya

daddy ya dora da
"hakane son dik abinda yafada hakane, insha allah,yanzu komai ya daidaita tunda ansamu fahimtar juna, idanuna yaso yarufe nayi abinda zaijawo tarin danasani nan gaba amma alhamdulillah tunda yanzu komai ya daidaita nakuma fuskanci soyayyar gaskiya kukewa juna, fatanmu anan dai allah yasa kun huce yakuma sa hakan yafi alhairi"

nan ma kasa cewa komai Deen yayi don besan me zaice ba, ba zato yaji muryar kaka nacewa
"amin amin, shikenan komai yawuce allah ya kyauta gaba"

dagowa Deen yayi ya kalli kaka with surprise saiyaga har lokacin taqi kallon 6arinshi hakan yasashi sunkuyar dakai yanajin wani sanyi na ratsa qasan zuciyarshi, kenan kaka ta yarda daddy ma ya yarda, this is unbelievable!


cikin jindadi suma su daddy suka shiga amsawa da amin

nan suka sanardasu Deen halinda zee keciki cewar yanzu haka tana kwance asibiti

sosai hankalin Deen yatashi dajin wannan labarin har hakan ya bayyana a fuskarshi

nan suka nemi alfarmar Deen yabisu asibitin qila zuwan nashi ya taimakama yanayinta


Deen yayi tunanin kaka zata hana sai gani yayi ta amince da hakan hakan yasa yashiga farinciki sosai saidai saida suka maidamasu kudaddensu wanda suka kawo rannan wanda dafarko su daddy sunso qin amsa amma ganin sun nace yasa suka amsa badon sunso ba

babu 6ata lokaci Deen ya kimtsa suka wuce taredasu daddy asibitin da aka kwantar daita


anan sukaje asibitin har komai yakoma daidai har takai ga tasamu sauqi an sallameta har daga baya daddy ya bijiro da maganar Introduction (all in book 1)


Sosai batun Introduction din yaba deen mammaki don beyi expecting hakan ba a lokacin

a tunaninshi sai sungama school sannan za'a fara maganar amma sadda zee tayimashi bayanin wai so ake atsaida maganar ne kawai bawai auren za'ayi ba yasa hankalinshi yadan kwanta don soyake ya kasance kafin lokacin koyaya ne yasamu abinda zai iya riqe kanshi da zee


lokacin da zancen Introduction din ya iso ga kaka duk saita rasa kwanciyar hankali

dukda bata nunawa Deen komai ba amma deep down abin na cinta


nan take ta gano manufar su daddy akan wannan Introduction din dasuka qirqira wanda bata raba dayan biyu suna sane sukayi hakan

dama wannan zuwan nasu da amincewarsu lokaci daya bawai shiganta yayi ba, tasan duk yadda za'ayi akwai maqalqashiya gameda hakan

jin batun Introduction din ya tabbatar da zarginta yakuma darsa fargabar tonuwar sirrinta data dade tana rufewa


sosai kaka tashiga damuwa komai ya kwance mata, kullum da tunani take kwana take tashi

bata fatan sirrinta ya fallasa a wannan lokacin, bata fatan abinda zai maidamata hannun agogo baya


duk halin datake ciki bata bari Deen yasani ba don batason kwata2 yasan da damuwarta yayinda a gefe guda tashiga nemama kanta mafita akan wannan hargitsatsen al'amarin dake shirin tunkarota


A bangaren Deen kau besan kaka nayi ba, shi duniya cema tadawo mashi sabuwa inda suke shan soyayyarsu da zee kamar zasu hadiyewa juna, kodayaushe suna maqale awaya don har lokacin batayi resuming school ba don bata,ida warwarewa ba

lokacin Introduction sai qara matsowa yake inda Deen kejin kamar yajawo ranar don doqi

dukda bawai auren za'a daura ba bakuma saka rana za'ayi ba hakan besashi doqin ranar ba don gani yake wannan Introduction din sharen fage ne na mallakar zee tunda koba komai za'a tsaida magana ne akansu yadda koma wani yazo daga baya yana sonta akwai maganarshi akanta


sosai cikin yan kwanakinnan Deen yadage da buga buga duk don yasamu yatara kudin daza'akai Introduction din hakan yasa shima yabar zuwa school din akan da anyi Introduction din saisuyi resuming school din gabadaya dashi da zee

besan ya tsarin abin yakeba amma yasan ba'a zuwa hannu biyu neman aure

wannan busyn daya shiga yasa beda lokacin lurada halin da kaka tashiga ciki


*TWO DAYS TO THE INTRODUCTION*


Zaune kaka take tsakar gida kan tabarma ta miqe kaffafunta ta hardesu tana kalkadawa ahankali

kallo daya zakamata kasan cewa she's very disturbed

kafe hanyar shigowa gidan tayi da ido kamar mai jiran 6illowar wani yayinda saqe saqe da dama keta kai kawo a kwanyarta


da sallama Deen yashigo gidan wanda hakan yayi daidai da saukewar naunauyan ajiyar zuciya daga kaka

murmushi yasakar mata lokacin daya hangota yaqaraso ciki hannunshi riqeda yar baqar leda


cigaba da kallonshi kaka tayi batareda ya motsa ba harya qaraso ya zauna gefenta yana washh yana yatsine fuska alamun gajiya

"wlh kaka nagaji, jikina ciwo" yafada yana qara yatsine.fuska

jin shiru yasa yadago ya kalleta yaga itama shi take kallo

"kaka?" yafada ahankali yana kallonta

hakan yasata kauda kai wadda hakan yaba kwallar idanunta damar digowa

ganin digar hawayen yasa hankalin Deen tashi nan take yanemi gajiyar tashi yarasa

"subhanllilah, kaka menene? meya faru" yafada yana kamo hannunta zai juyo fuskarta don tabbatar da abinda yagani amma taqi bari

"kaka don allah menene?" yafada yana qara qoqarin leqa fuskarta

fizge hannunta dake cikin nashi tayi tarufe fuskarta da tafukkan hannu tareda fashewa da wani irin kuka mai tsuma zuciya

gaban Deen yayi mummunan faduwa ganin dagaske kuka take hakan yasashi saurin rarrafowa gabanta ya kama hannayenta zai janye daga fuskarta amma taqi bari

"innalillahi, kaka wai meya faru? don allah kiyi magana" yafada cikin tashin hankali

qin maganar tayi saima qara volume din kukanta datayi wanda hakan ba qaramin daga hankalin Deen yayi ba don jiyayi kamar shima yasa kukan


"kaka don girman allah ki gayamin meke faruwa, don allah kiyi shiru ki gayamin, don allah" yafada kamar zaiyi kuka don har idanunshi sunfara chanza launi

nan ma batace komai ba sai kukan data cigaba dayi wanda yakeji har cikin ranshi

"kaka don allah ki gayamin, don allah kibar kukan nan zuciyata zata buga" yafada muryarshi na dan rawa rawa

sai a lokacin tadago ta kalleshi fuska sha6e sha6e da hawaye

"Kamal nima zuciyata zata buga, zasu rabamu, xan rasa raina. zamu rabu na har abada"

"innalillahi waina ilahi rajiun, rabuwa kuma? haba kaka meyasa kike fadin wannan mummunan kalmar? don allah kibar fadin haka"

"Kamal kaine komai nawa, baxan iya rayuwa babu kai ba baxan juri nisa dakai ba, mutuwa zanyi" taqarashe cikin fashewa da kuka sosai

hawayene suka taru a idanunshi shima
"kaka don allah kibar fadin haka, babu wanda zai rabamu, nima bazan iya rayuwa babu ke ba..."

"to idan hakane mu gudu Kamal.. mubar nan wajen, mubar garinnan don allah" ta katseshi dasauri kamar zautatta


tsayawa Deen yayi yana kallonta for a moment kafin yace
"mugudu? kamar ya mugudu?"


"mubar nan Kamal, nidai hankalina be kwanta da nan ba kuma, ina tsoron kar arabamu ina tsoro Kamal" tafada cikin yanayin tsoron

"wazai rabamu kaka? waye zai rabamu" inji Deen in confusion


"nidai mubar nan Kawai... tashi kagani, taso" tafada tana miqewa tsaye tana jan hannun Deen da kanshi yayi mugun kullewa

tashi shima yayi tajashi har dakinta yana biye daita suka shiga

"kagani? na tattara komai tafiya Kawai yarage, Kawai mutafi don allah"


tsayawa yayi yana bin jakunkunan kayansu dake tsakiyar dakin da kallo Speechless, yama rasa meke faruwa

"da daddare saimu tafi Kawai yadda babu wanda zai ganmu ko?" inji kaka da hawayenta yaqi tsayawa ga jikinta har lokacin rawa rawa yakeyi

dakyar Deen ya iya tattaro yawun bakinshi ya hadiye.sannan yace
"kaka.. wai meke faruwa ne? ina zamu?"

"koina ma,.Kawai muyi nisa danan"

"amma akan wane dalili kaka? Kawai saimu bar gari haka Kawai? haka Kawai saimu gudu mubar gari kamar 6arayi" yafada totally confused

"Kamal, bazaka ganeba amma ni nasan abinda na hango, wlh inaji ajikina idan muka cigaba dazama anan sai an rabamu, inajin hakan ajikina" tafada wasu hawayen nasake saukomata

"wazai rabamu kaka?"

"nima bansaniba Kawai mubar nan"

"amma kaka shikenan saimu bar gari? ina zamuje? wa mukedashi? wani wurin garemu bayan nan?"


"Kamal zamu samu wurin zuwa, nan ma ai sdaga wani wuri mukazo kuma muka samu nan din har muka zauna mukayi tsawon shekarunnan, mutafi insha allah zamu samu wurin zuwa allah na taredamu"

"amma kaka karatuna fa? bama wannan ba kin manta jibi za'aje tsayar da maganarmu da Zainab? duk ahakan zamu bar gari?" inji Deen dake cikin confusion sosai, kwata2 magangganun kaka doesnt make sense to him

"duk ina sane da hakan Kamal, duk wadannan basuda muhinmmanci yanzu"

"basuda muhinmmanci?" ya tambaya cikin tsananin mammaki

"eh Kamal, abinda yafi muhinmmanci shine mucigaba da rayuwa da juna..atare"


shiru Deen yayi yana kallonta kamar yau yafara ganinta saikuma ya girgiza kai yakama kafadun kaka da hannun bibbiyu ya zaunar daita gefen gadonta

"kaka meya faru? don allah ki gayamin meye silar dukkan wadannan abubbuwan"

"babu komai Kawai sonake mubar garinnan, hankalina be kwanta da zama anan ba kuma"

"meyasa hankalinki be kwanta da zamanmu anan ba din?"

"Kawai hakanan, Kawai mutafi"

tsayawa yayi again yana kallonta kamar yau yafara ganinta

"intafi inbar karatuna bayan befi shekara ba zan qarqare gabadaya?"

"wanda kayi allah yasamashi albarka, dama meye amfanin karatun don dai mutum ya iya rubuta da karantawa ne bayan hakan ko ka gama aibakada tabbacin cin abinci dashi tunda mutane nawa suke gararanba atiti da kwalinsu aiki ya gagaresu, idan mukaje inda mukaje saika samu aikin hannu mu cigaba da rufawa juna asiri"


sake sakin baki Deen yayi yana kallonta cikin tsantsar mammakin abinda take cewa can kuma yace

"maganata da Zainab fa?"

tsaki taja

"itama sai a haqura, aiba ita kadai ce mace aduniya ba ko?"

cikin tsananin mammaki yace
"a haqura?"

"eh, allah zai hadaka da wacce ta fita"

"haba kaka? jibi fa za'a tura..."

"babu inda za'a tura, kai nifa dama can bason abinnan nakeba shima munafikin uban nata baso yakeba, na me zanbari a tarwatsamin farinciki a banxa a wofi? kama cire wannan maganar aranka don yanzu kam babu ita"

jin magangganunta yayi kamar saukar guduma atsakiyar kanshi


kallonta Kawai yake totally Speechless

"kayi shiru kana kallona" tafada ganin kallon yayi yawa

"amma dai,wasa kike ko kaka?"

tsuke fuska tayi

"alamun wasan kagani a fuskata"

"to kaka idan ba wasa ba meye zamu kira wannan to?"

"kai yayi maka kama dawasa amma babu ko alamun wasa a magana ta, batunka da wannan yarinyar babu shi!"

"meyasa?" yafada ahankali yana kallon kaka da idanunshi dasuka kada sosai

"saboda nace babu shi don haka kama manta da batwwannan yarinyar don ba alhairi bace agaremu"

sosai zuciyar Deen take zafi jiyake kamar ana gasamashi ita

"amma kaka kinsan inason Zainab ko?" yafada yana kallonta da idanunshi dasukayi jajir

"zaka daina sonta ne ahankali"

ahankali yashiga girgiza kai
"kaka baxan ta6a daina sonta ba, babu ranar dazan daina sonta, kada allah ya gwadamin ranar kaka"


"Kamal ni kake fadawa haka?"

"kiyi hqr kaka, amma Zainab itace komai tawa, itace farincikina itace komai tawa bazan iya rabuwa daita ba"

hawayene suka saukomata
"itace komai taka Kamal, wato tafini matsayi agurunka?"

girgiza kai yayi yace
"ko daya kaka, kowanne da matsayinshi aguna kaka, bazata ta6a finki matsayi ba amma kamar yadda ban iya rayuwa babu ke haka itama bani iya rayuwa babu ita"

kuka sosai kaka ta fashe dashi

"ni kake fadawa bazaka iya rayuwa babu itaba Kamal? duka yaushe kasanta? kenan tafini muhinmmanci agurunka"

"kaka ba haka bane, nina rasa dalilin dayasa baki sonta bayan ita tana sonki" yafada kamar zaiyi kuka

"ni ba itace banisoba, bani daison munafikin babanta ya cutar damu ne"

"me babanta zaiyi mana? yafa amince da maganarmu kuma harnan yaxo yabaki hqr akan abubbuwan dayayi amma dukda haka bazaki sama abin albarka ba? ni yanzu meye hujjata ta janye wannan maganar? mahaifinta ya yarda har yasa aturo to menene kuma ya rage?"

"munafikine mahaifin nata, Kawai yanuna ya yarda ne amma hakan bekai zuciyarshi ba, turowan ma dayace ayi duk na manufa ne" tafada cikin kuka sosai

"manufar me kaka? meye manufarshi akai?"

"yasan bamuda kowa kamal shiyasa yace aturo, soyake ya titsiyemu"

"meye don bamuda kowa? ai ba daga sama muka fadoba, saimu fadamasu komai gameda mu, kuma koda bamuda kowa wadanda zasu tsayamana bazasu gagaremu ba, ga Mallam Nasiru da sauran mutanen arziqin unguwarnan nasan zasu tsayamana"


murmushin takaici kaka tayi
"hmmm yaro yarone, bazaka gane komai ba Kamal, bazaka gane ba"

"meye bazan ganeba kaka? kifadamin babu abinda bazan ganeba, idan akwai wani abu bayan wannan ki gayamin"

"nidai nace babu maganarka da wannan yarinyar kuma gari dolene mubarshi, kaji na gayamaka" tafada tana daure fuska don tasan duk abinda zatace mashi bazai ganeba

Tashi Deen yayi tsaye yana kallonta
"kiyi hqr kaka amma baxan iya ba, baxan iya barin Zainab ba, ina sonta"

daga haka yajuya yabar dakin


binshi da kallo tayi baki sake harya fice daga dakin

tunda suke bata ta6a sashi abu yaqiya ba sai yau

fashewa tasakeyi dawani kukan mai tsuma zuciya cikin rasa abinyi kuma....✍�


*manage please*


Ummin fasihu🧚🏻‍♀�
8/2/21, 9:45 PM - Buhainat😝: *🙍🏻‍♂️DEEN🙍🏻‍♂�*


*093*


Tunda Deen yake beta6a shiga halin damuwa da confusion irin ranar ba


koda yafita ma rasa inda zaya yayi Kawai saiyaita yawo batareda yasan inda zaya ba

sosai damuwa tayimashi katutu arai, yarasa meya samu kaka data burkucemashi lokaci daya ta bijiro da wannan buqatar tata marar yiwuwa


nan take yamanta dawani batun shirye shiryen Introduction, damuwa ta maye gurbin doqin dayakeyi


aranar sai bayan isha'i yashigo gidan yana addu'ar allah yasa kaka tadawo hayyacinta tabar wancan maganar marar ma'ana

saidai me? yana zuwa yatarar da wani tashin hankalin inda kaka ta tsaya akan bakanta na barin garin, qarshe ma tace idan shi bazai bita ba ita zata tafi ita kadai duk yadda allah yayi daita daidai ne


sosai Deen yashiga tashin hankali ganin dagaske fa kaka take

babu roqon da baiyi mata ba da magiya harda kukanshi amma firr kaka taqiya, takoma kamar wata zautatta bataji bata gani


ganin dagaske tafiyar zatayi tabarshi yasashi shima amincewa da binta din don baxai iya rayuwa batareda itaba, itace yabudi ido yasani duk duniyar nan bayada kamarta, itace uwarshi itace ubanshi itace komai nashi


xai iya rayuwa batareda zee ba dukda rayuwar bamai dadi ba don rasata yana daidai da rasa farincikinshi amma bazai iya rayuwa batareda kaka ba, bama zai iya misalta rayuwa batareda ita ba.


haka ya amince ba don yasoba amma ya roqeta akan tabari sai gobe sai sutafi din

kamar bazata yarda ba saikuma ta amince akan gobe tafiya babu fashi ko dashi ko babu shi tafiyarta zatayi


ranar yadda Deen yaga rana haka yaga dare

ganin komai yake kamar a mafarki, jiyake dama mafarki ne da babu wanda zaikaishi murna a duniyar nan


kwata2 he never saw these coming, abin yaxomashi ne Kawai daga sama, yakasa yarda cewa zaiyi nisa da zee, nisa na har abada, yakasa ma imagine din hakan aranshi Kawai gani abin yake kamar a mafarki


Washegari ko kofar gida be leqa ba, yana cikin daki idan kuma yafito to lokacin sallah ne yayi saiyayi alwalla yakoma dakin yayi abinshi

abinci ma kasa ci yayi haka kaka ke kawo abinta tana daukewa

itama kakar kallo daya zakamata kasan she's down sosai, she looks so pale and disturbed, komai na duniya bayayi mata dadi

ganin Deen a halin dayake ciki baqaramin qara dagulamata lissafi yake ba saidai takasa yin komai akai, takasa koda consoling dinshi

haka suka qarashe wuninsu agidan cikin wani irin yanayi marar dadi wanda basu ta6ayin irinshi ba tunda suke don kowa na qunqume a dakinshi babu mai fitowa saida dalili, magana ma kanta bata hadasuba sosai kowa nafama da zuciyarshi


sai a lokacin isha'i Deen yafita daga gidan yaje masallaci don yin sallah

sai bayan sunfito yahadu da wani dan unguwar nasu mai suna Salman wanda yakasance kamar aboki ne gareshi yabashi wani envelope tareda cemashi wata zatazo sunanta Zainab don allah idan tazo yabata saqon nada muhinmmanci


tsokanarshi Salman yashigayi akan saqon menene, badai na soyayya bace shidai dan murmushi kawai yayi yayimashi sallama akan zaishiga gida don samm he's not in the mood for any joke


koda yakoma gidan awaje ya tadda kaka tabuga tagumi very worried

be tankamata ba yashige dakinshi don shima kanshi nashi damuwar ta isheshi kaya


komawa dakin yayi ya raku6e wuri guda staring at space

har lokacin yakasa yarda da abinda yake faruwa, he can't imagine wane hali zee zata shiga idan taji labarin tafiyarshi

hakan yasashi lalubo wayarshi dake kashe tun jiya ya lalubo numberta ya bugamata


jin muryarta yasa wasu emotional feelings tasomashi, she sound so innocent and cool

nan take saiyaji tausayinta ya mamayemashi zuciya

bata cancanci abinda yake shirin yimata ba, bata cancanci yayi breaking heart dinta ba bayan tasoshi da dukkanin zuciyarta, tasoshi a yadda yake batareda tayi la'akari da tarin difference dake tsakaninsu ba

nan take yaji wani irin guiltiness a zuciyarshi, ya zaiyi? ya zaiyi da rayuwarshi?


haka sukayi wayar yana iyakar bakin qoqarinshi wajen controlling muryarshi don wayar yake yana hawaye, tunanin cewa qila muryarta yakeji na qarshe yasa yakasa tsaida hawayenshi


itama taso tagane kamar ba daidai yake ba don taji a yanayin muryarshi kamar he's not ok ganin hakan yasa yaimata qaryar mura yake.


kalaman dayake mata amfani dasu da ace mai saurin ganewa ce data gane ba lafiya amma dayake bata kawo hakan aranta ba yasa batabi takansu ba sosai

wannan innocence din nata kuma ba qaramin qara tsuma zuciyarshi yayi ba har hakan yasa daga baya yakasa cigaba da wayar daita sukayi sallama akan beda charge


bayan gama wayar ya kasheta gabadaya ya zare sim card din ya karya yana hawaye sosai


sannan yatashi ya tattara important stuffs dinshi ciki harda takardunshi, sannan ya dauko wannan band din da zee tabashi ranar Valentine wanda tun ranar ya adanashi cikin wani box yafiddoshi ya daura a hannu


komawa yayi kan katifarshi ya takure waje guda staring into space idanunshi jawur.


saida dare yayi sosai kafa dik ta dauke sannan suka fito daga gidan daga su sai kayansu wanda kecikin madaidaiciyar ghana must go sai qatuwar jakar goyo dake goye abayan Deen


kulle gidan sukayi da katon kwado sannan suka nufi hanyar barin layin

tafiya suke babu mai cewa kowa komai don duk yau maganar dasuka yiwa juna qididdigagga ce


babu dadewa suka isa titi don dama basuda nisa da titi

basu tsaya ba suka cigaba da tafiya gefen titin dake kwal don motoci ma sai jefi jefi suke wucewa saboda yadda dare yayi

sunyi tafiya sosai kafin susamu wata adaidaita data tsaya gabansu don jin ko tafiya ce

kaka ce tayima mai adaidaitan magana cewa tasha zasu

saida yaqaremasu kallo sannan yafadamasu kudin dazasu bada

kaka bata musaba tace suje dukda yasa kudi dayawa itadai burinta subar unguwar kwata2

ita tafara shiga sannan aka saka ghana must go din atsakiya inda akesa kaffafu sannan Deen da saikayi zaton kurmane saboda rashin maganarshi yashiga yana rufo yar kofar adaidaitan

babu 6ata lokaci mai adaidaitan yaja sukabar wajen


tafiyarsu zuwa tashar sunyishi ne silently don babu mai cewa komai cikinsu

sosai halin da Deen keciki ke damun kaka amma batasan mezata yimashi ba, batada kalmar dazata fadamashi dazaisashi jin sanyi hakan yasa tayi shiru tana hoping cewa komai zai wuce very fast insha allah

harga allah itama tasan wannan decision din yayi tsauri sosai musanmman ma ga Deen amma ya ta iya? hakan take ganin yafi musu alhairi don aganinta gwara wannan tashin hankalin da wanda take hangomasu nan gaba


tafiyar 30mins yakaisu tashar inda sa6anin koina wajen akwai mutane sosai ga fitilu takoina yadda kasan ba tsakar dare bane

biyan mai adaidaitan sukayi suka sauka da loads dinsu


ciki suka shiga inda yawanci duk travellers ne dazasu kwana a tashar da drivers din motoci


qarasawa ciki sukayi Deen biyeda kaka dake agaba yana sauraron yadda take tambayar inane wasu daga motocin zasu tafi


shidai haryanzu ko uffan bece ba sai binta dayake everywhere she go har daga qarshe tasamo masu motar dazasu shiga wacce zata Abuja itama ta za6eta ne don taga takusan cika kuma zatayi saurin dagawa


kayansu aka sakamasu a baya sannan suka kama seat suka shiga suka zauna saboda yadda iskan daren ke kadawa sosai

akwai few mutane ma acikin motar inda wasu ma barci suke wasu kuma idanunsu biyu, cikinsu kaka ta tambayi wani time akace mata yanxu uku da rabi na dare hakan yasata sauke ajiyar zuciya takoma ta jingina jikin kujerar


dagowa tayi ta kalli Deen dake zaune silently yana kallon yatsun hannunshi saitaji yayi mugun bata tausayi

ahankali ta kama hannunshi tadan matsa tana kallonshi

be dagoba bare ya kalleta sai cigaba da kallon hannayen nasu dayayi

"kayi hqr Kamal... insha allah hakan shiyafi alhairi" tafada ahankali tana kallonshi da idanunta dasuka duri ruwa


dan murmushi yayi wanda dagani kasan na qarfin haline Kawai ya kadamata kai batareda ya kalleta ba

"yanxu gayamin meke damunka? kana buqatar wani abu?" tafada tana kallonshi cikin kulawa

"inajin sanyi" yafada ahankali

kallonshi tayi cikin tausayawa sai tajawoshi jikinta yadora kanshi a cinyarta tashiga shafa mashi kai

"sannu, ai gari yakusan wayewa harda sanyin dare" tafada tana gyaramashi hular sanyin kanshi yadda zai rufemashi kunnuwa sosai don dama shigar sanyi yayi saboda yanayinshi

ahankali Deen ya lumshe idanunshi yana sauraron bugun zuciyarshi dake bugawa abnormally


ahaka har asuba tayi

duk fitowa sukayi sukai sallah sannan suka koma cikin motar da gab take da cika don saura mutane biyu

cikin qanqanin lokaci ta ida cika aka shishiga motar akayi duk abinda ya kamata sannan driver yahau ya tada motar yaja suka fice daga tashar


Tunda Deen yake beta6a long and boring tafiya ba irin wannan


tunda motar tafara tafiya ya maida kanshi ga window yana kallon waje yanajin cewa wai yau shi zaibar garinsu Katsina bawai bari na dawowa ba A'a na har abada


dukda shekaru sunja sosai amma yana iya tuna lokacin da suka shigota sama sama, lokacin yanada shekaru goma aduniya

tunawa yayi da fadi tashin dasukayi tayi da kaka kafin susamu wurin zama inda yazaman masu gida kusan na tsawon shekaru sha takwas

dukda yasan Katsina ba garinsu bane amma hakan be hanashi jin kamar yana barin bane don duk cikin garurruwan dasuka zauna babu wanda sukafi dadewa suka kuma yi rayuwa comfortably kamarta gashi yayi achieving abubbuwa dadama acikinta marassa goguwa a memory


lokacin dasuka fita kofar Welcome to Katsina wani feeling na emptiness ya ziyarci zuciyarshi

shikenan, shikenan yatafi, yatafi yabar abubbuwa masu matuqar muhinmmanci a rayuwarshi batareda sanin lokacin sake waiwayarsu ba

sai jiyayi kamar zuciyarshi tayi dropping daidai kofar yabarta abaya yayinda yanzu gangar jikin kecikin motar ana tafiya daita


ahankali ya lumshe idanunshi, imagining yafarayi me zee keyi adaidai wannan lokacin

wataqila tanacan cikin farincikin kasancewar yau zai turo magabatanshi, wataqila takirashi, wataqila sunacan sunata shirye shiryen Introduction din

ya Zainab zataji? ya zataji idan dagabaya tagane abinda yayi, ya zataji idan tagano he yayi betraying trust dinta


_*please don't leave me, no matter what*_
muryar zee tadawo mashi


_*never... I will never*_
yasake tuna amsar dayabata lokacin


sake maida idanunshi yayi ya lumshe yanajin wani irin zazza6i na tasomashi


yasan shi da farinciki kuma har abada, yasan wannan new chapter din daya bude na rayuwarshi is the worst chapter


lokacin dasuka tsaya sallar zuhr jikin Deen yayi ringis da zazza6i

sosai hankalin kaka yatashi ganin hakan

ahaka yayi qarfin halin saukowa shima cikin motar da niyyar yin alwalla yayi sallar saidai inda ya tsugunna yana alwallar yahau kwarara amai

sosai hankalin kaka yaqara tashi duk ta gigice tana kuka ganin yadda yake zazzaga aman kamar zai amayar da yan cikinshi gabadaya

da taimakon wasu daga mutanen motar yasamu ya tsaftace jikinshi ya daura alwalla yadawo wata yar rumfa dake wajen inda duk nan pasinjojin sukayi sallah

sosai mutanen suka tausaya mashi don kallo daya zakamashi kasan yana jin jiki sosai

adaddafe yayi sallar lokacin har ansiyomashi maganin masassara a wani dan chemist dake wajen kaka kuma ta siyamashi fura inda tabashi yasha kafin yasha maganin

ko rabin furar besha ba yashiga kwara wani aman kamar zai zazzago yan cikinshi

sosai kaka takuma rudewa, kuka take bilhaqi da gaskiya cikin tashin hankali tana ataimaka mata karya mutu shikadai gareshi

sosai mutanen wajen suke bakin qoqarinsu wajen taimakawa don sosai Deen kejin jiki, yayi laqwas ga wani irin zafi da jikinshi yadauka

kasancewar a inda suka tsaya qauye ne yasa babu wani clinic kusa gashi dan chemist dinma irin dan shagonnan ne da ake saide2 bawani abu suka saniba gameda lfy Kawai suna saida irin paracetamol ko maganin ciwon jiki saboda ire iren pasinjojin dakan tsaya a wajen idan suna buqata

ganin halin da Deen keciki yasa mutanen wajen ba kaka shawarar gaskiya idan suka cigaba da tafiyar nan ahaka jikin Deen ida rikicewa zaiyi Kawai susamu cab dazai shiga cikin gari dake kusa takaishi clinic ko babban chemist inda za'a dubashi abashi right meditation


hakan kau akayi, nan aka saukomasu kayansu dayake wurin kamar yar karamar tasha ce nan da nan suka samu mota Golf mai shiga cikin gari

ahaka suka shiga kaka nata dauke hawaye

babu 6ata lokaci motar tasu ta tashi tafita daga tashar

tafiyar awa daya sukayi suka qaraso cikin gari inda drivern yakaisu wata yar qaramar clinic ta gwamnati

lokacin Deen ko bude idanu be iyawa sosai

tareda drivern suka shiga ciki ganin yadda Deen kejin jiki ga kaka tsohuwace bata iya handling komai ita kadai hakan yasa yatsaya ya taimaka wajen yin zirga zirgan komai har suka samu nasarar ganin likita

anan aka dubashi aka rubuta mashi magungunnan daya kamata

drivern nanan har saida yaga ansiyo magani inda dakyar suka samu Deen yasashi bayan yasha wani dan shayin da aka siyomashi wajen clinic din sannan yatafi yabarsu anan yakama gabanshi shima


kasancewar basuda wurin zuwa yasa suka tsaya cikin asibitin don ga halin da Deen keciki tafiya bata yiwuwa agaresu


ataqaice dai cikin asibitin suka kwana, Washegari kuma suka sake daukar hanya ba don ya warware ba amma da dan sauqi


ataqaice dai sai wajajen 3pm suka isa garin Abuja a wurwurce har wani ramar dole kowannensu yayi

suna isa Abuja suka qara danganawa da asibiti don a lokacin sosai jikin Deen yasake rikicewa

wannan karon ganin yanayin da Deen keciki yasa aka basu gado


saida sukayi kwana uku a asibitin kafin yadanji sauqi aka sallamesu


a lokacin duk sun kashe yan kudaddensu wadanda suka rage basu wani taka kara suka karya ba gashi basuda mazauni dama acikin kwanakinnan asibitin ne yazama kamar gida agaresu


duk kaka takoma wani iri ta fiffige saboda damuwa, bata ta6a kawowa haka tafiyar zata juyemasu ba

gani take komai zaizo masu smoothly kasancewar lokacin dasuka fito sunada enough kudinsu wanda zasuyi tafiyar harsuzo susamu haya sukama inda zasu zauna amma wannan rashin lafiyar ta Deen dukta cinye kudin wajen hidindimun magungunna dana abinci


ganin halin da kaka tashiga na zullumin inda zasu koma lokacin da aka rubuta musu sallama yasa Deen dahar lokacin bawai ya warke garau bane ya dauki jakar dayayi parking important stuffs dinshi yazaro wayarshi wanda zee tabashi

anan yace ma kaka bari yaje ya siyar susamu ko kudin kama daki daya ne

dafarko kaka taso hanashi saboda batason yashiga gantsareriyar ranar da akeyi ya maidoma kanshi ciwo baya amma kuma saita haqura sanin cewa basuda wani option tunda ita ba iya zuwa zatayi ba


ahakan Deen yafita inda da tambaya yasamu shagon siyar da wayoyi yashiga don siyarda ita

jin tayin wulaqancin da akamashi a shagon farko yasashi fitowa yanufi wani inda nan ma kanwar ja ce

sosai abun yabashi mammaki ganin yadda suke mashi siyen wulaqanci bayan wayar babbace kuma mai tsada

kamar ya haqura da siyar da wayar amma ganin itakadai ce hope dinsu yasashi hqra inda yasamu ya saidata wani shago wanda yafi sauran siyenta da kudi

anan ya tambayi mai shagon inda zaisamu gida haya ko daki daya ne cikin sa'a saigashi mutumin ya hadashi dawani dilali da dama irin aikinsu kenan

hadashi yayi da dilalin inda dilalin yatafi dashi ya nunnuna mashi gidajen dakeda vacant na hiring


aciki Deen ya za6i daya inda yakama masu daki daya inda dakyar yasamu mai gidan ya yarda zai amshi kudin wata shidda daga baya sucika mashi sauran


gidan dakuna uku ne sai kitchen da bayi

akwai wasu occupant din aciki inda duk magidanta ne da iyalansu kowa da daki daya inda dakin da Deen yakama shine na qarshe


saida yabiya kudin hayan aka bashi makullin dakin sannan yafito yatari adaidaita don komawa asibitin


alokacin har jiyake kamar kanshi zai rabe gida biyu saboda sarawa haka dai yaita daurewa har suka iso asibitin ya sauka yabiya mai adaidaitan yashiga ciki


A reception ya tadda kaka don lokacin har an maye gurbinshi dawani patient a gadonshi hakanyasa dole tadawo reception din ta zauna

tana ganinshi tayi saurin miqewa tsaye don dama tundazu kamar a qaya take baxa idanu Kawai take taga ta inda zai 6illo


tararshi tayi tanamashi sannu don he looks so weak qarfin hali Kawai yakeyi

anan yafada mata yasamo masu mazauni amma daki daya

albarka taita shimashi tana jeramashi sannu tana tambayar yanzu me yakeji

cewa yayi babu komai Kawai ta tashi sutafi

anan suka tattara yan kayansu suka fito daga asibitin suka tari adaidaita yafada mashi inda zaikaisu


unguwar unguwar talakawa ce don ga yanayin unguwar Kawai zaka gane hakan


har kofar gidan adaidaitan ta saukesu suka sassauke kayansu suka biya sannan suka shiga


a lokacin har anfara kiraye kirayen la'asar

saida suka gaigaisa da occupant din gidan sannan suka qarasa dakinsu

anan Deen yake tambayarta yayi? hakan yasa tayi murmushi tana cewa yayi sosai allah yayi mashi albarka

da amin ta amsa sannan yace bari yaje yadawo

bejira cewarta ba yasake fita inda da kingin kudin hannunshi yayimasu sayayyar yan kayan daxasu buqata kama daga tabarma, bokiti, buta, yan plate biyu da cups sai tsintsiya kingin kudin kuma yasiyomasu kayan abinci wanda zasu dan fara dashi


sosai farinciki ya lullu6e kaka lokacin daya dawo da kayayyakin hakan yasa taita samashi albarka

tare suka tsaftace dakin suka shinfida tabarmar suka kuma ajiye kayansu da kingin kayayyakin da Deen yasiyo a wani Corner na dakin


sosai dakin yayi fili don bawasu kayan kirki aciki

sai a lokacin dik suka samu damar yin sallar la'asar din sannan kaka ta jiqamasu garin kwaki cikin wanda Deen yasiyo cikin kayan abincin suka sha Deen yasha maganinshi yakoma ya kwanta dukda babu kyau kwanciyar marece amma haka kaka ta kyaleshi don tasan yagaji sosai cos he looked so exhausted

haka Deen yaita kwanciya idanunshi alumshe dukda ba barci yake ba

tunanin zee Kawai ne dankare a zuciyarshi, yasan izuwa yanzu tagano komai kuma tasan ya yaudareta, yasan yanzu tana cikin wani hali don yaudara agun wanda kabama dukkan yarda ba qaramin ciwo gareshi ba


haka yaita kwance har wajajen magrib sannan yafito yayi alwallar magrib inda ya tadda kaka waje suna dan fira da matan gidan

alwallar yayi yafita inda bedawo ba sai bayan isha'i

yana dawowa yashige ya kwanta ya rufa da qaton bargonsu yana rawar d'ari sanadiyar sanyin dayakeji nakaimashi har cikin qashi

kan kace me har wani zazza6in yasake lullu6eshi inda kaka tashiga kuladashi cikin tsananin tausayawa jikan nata


ataqaice dai haka Deen yaita fama cikin kwanakin dasuka biyo baya, yau lafiya gobe sauqi

sosai rayuwa tayimusu wuya, ga ciwo ga babu kudi haka sukaita fama inda dan abincin da Deen ya siyamasu yaketa qasa every passing day


ganin hakan yasa Deen fara fita nema ganin kwanciyar bayi bace

haka yake fita ya yini waje yana yan buga buga qarshe yadawo da abinda be taka kara ya karya ba

abu ya hademashi goma da ishirin, ga ciwon dayake tsaitsaiye ga fita nema ga tarin damuwa dake danqare a zuciyarshi

gashi kaka bawata sana'a take ba bare itama ta taimaka don sana'a saida jari sukau ahalin yanzu ta cinsu ma Kawai suke, gashi rayuwa tafi tsada a Abuja bisa ga Katsina


haka sukaita rarrakawa Deen yana iyakar kokarinshi na ganin basu rasa ciba ko yayane

ahaka yasamu wani qaton shago a kasuwa na lemuna kala kala inda anan yake zuwa yatayasu safko carton cartons din juices ko ruwa daga manyan trailoli dake kawowa zuwa cikin shagon


shima dakyar yasamu aikin ashagon kasancewar akwai masu irin aikin sosai awajen

haka zasuyita zirga zirgan jigilar kayan daga motocin zuwa qaton store din shagon wasu masu barrow cikinsu kuma har dako sukema masu zuwa saye a shagon


kasancewar shagon babban shagone yasa kodayaushe cikin busy yake, kodayaushe cikin sauke kaya da siyarwa suke hakan yasa masu dakon wajen ke jigatuwa sosai musanmman ma ire iren su Deen dabasuda barrow saidai a tittilamasu akai


farko farkon fara aikin a shagon ba qaramar wahala Deen yasha ba don yana jigatuwa sosai at the end of the day inda kullum saiya kwana da zazza6i da ciwon jiki saboda wahala daga baya yaji ashe hayar barrow akeyi wanda hakan yasashi shima fara quma safko yaje don amsar hayar barrow inda hakan yadan sauqaqa mashi wahala


haka rayuwa ta cigaba da tafiya inda Deen ya cigaba da aiki wannan shagon inda yake samu ba laifi don ci da sha lafiya lau yake dauke masu harda yan buqatun yau da kullum saidai fa kullum lafiyarshi bawata cikkaka bace don da ana sabo da ciwo daya saba dashi saboda har lokacin bawata cikkakiyar lafiya gareshi ba Kawai qarfin haline irin nashi


cikin sati biyu Deen ya chanza kamar bashi ba, ya rame ya rage haske, gashi yaqaro sanyi bisa wanda yake dashi

kallo daya zakamashi idan kasanshi sosai kasan akwai abinda kecimashi zuciya, bayada walwala ko kadan, rayuwa ta daina yimashi dadi


sosai kaka ke tausaya mashi don wani lokacin har kuka take 6oyewa tayi don sosai ta hango tarin damuwar da Deen keciki

kwata2 farinciki yayi qaura a rayuwarshi Kawai rayuwa yakeyi badon yanajin dadinta ba


haka ranaku sukaita wucewa tun Deen na iya controlling emotions dinshi harya kai gejin dayakejin be iya haqura, he missed zee so very much don idan akwai abinda idanuwanshi sukafi kwaidatuwa da gani a lokacin zee ce


ganin yakasa cigaba da daurewa yasashi fara tara kudi secretly acikin kudin dayake samu don zuwa ganinta

be damu da abinda zatayi mashi ba ko korar kare zata mashi kotasa a kulleshi wannan ba damuwarshi bane, damuwarshi Kawai yaganta yasata a idanunshi koda na seconds biyu ne ko zaiji sauqin abinda yakeji a zuciyarshi


haka yatara kudinshi watarana tunda safe yafita azuwan zashi aiki ya zarce tasha inda anan direct yayi boarding motar Katsina...✍�


*🤦🏻‍♀️wannan flashback yaqi qarewa ni ashaanty*

*na yarda aski idan yaxo gaban goshi yafi zafi, I want to end it but it's not ending😩😩*


Ummin fasihu🤧🤧
8/3/21, 8:01 PM - Buhainat😝: *🙍🏻‍♂️DEEN🙍🏻‍♂�*


*084*


*masu complain ba'a posting kullum kuyi hqr, am trying my best, da danakeyi a kullum dama yabada hakan yanzu dakukaga sa6anin hakan yakamata kuyimin uzuri, dama kebada komai*


Sai wajajen 5pm motarsu Deen tashiga garin Katsina, garin da yaga ya chanza mashi daga yin yan kwanaki ba acikinshi ba


saukowa yayi daga cikin motar kamar yadda kingin pasinjojin keyi yana sake bin wajen da kallo

shaqar iska yayi ya fesar yanajin wani irin feeling a zuciyarshi marar misaltuwa

ahankali yafara tafiya yana dan waiwaigawa don samun abin hawa

ba jimawa wata adaidaita tazo ta paka gabanshi mai adaidaitan na tambayar tafiya ce

amsamashi Deen yayi da eh sannan yafada mashi inda zashi

fadamashi kudin dazai biya mai adaidaitan yayi shikuma Deen yashiga batareda yasake cewa komai ba


tafiyar kusan mintuna shabiyar sukayi kafin adaidaitan taja ta tsaya alamun an iso


ta cikin adaidaitan Deen yajuyo yana kallon tangamemen gate din gidansu zee kasancewar a opposite din gidan adaidaitan tayi parking

kafe kofar gidan yayi da kallo bugun zuciyarshi na qaruwa

"ko ba nan bane?" inji mai adaidaitan jin shiru yaqi sauka

sai a lokacin Deen ya janye idanunshi daga kallon gidan yajuyo ya kalleshi yace
"eh nan ne"

saukowa yayi daga adaidaitan sannan yazura hannu a aljihu don fiddomashi kudinshi daidai nan wata baqar motar tashigo layin

ciro kudin Deen yayi ya sallami mai adaidaitan daidai motar ta tsaya kofar gidansu zee

jin an danna horn yasashi dan juyowa daga mai adaidaitan dake bashi chanji

gabanshi ne yafadi ganin mota a qofar gidan

amsar chanji yayi sannan yajuyo sosai yana kallon motar da baya iya hango mutanen ciki saboda duhun glass dinta


zuciyarshi ce tashiga racing yana wondering waye acikin motar


bude gate din gidan akayi amma maimakon motar tashiga saitacigaba da tsayuwa a wajen

kafe motar Deen yayi da ido daga dayan bangaren yana ji ajikinshi cewa shima kallonshi naciki keyi

_was it Zainab?_
tambayar da zuciyarshi tayimashi kenan

wannan tunanin yasa bugun zuciyarshi qara qaruwa


ahankali yaga anbude seat din driver hakan yasashi kafe wajen da ido don ganin mai fitowa

bala yaga yafito daga ciki yana kallonshi kamar idanuwan zasuyi magana


shima Deen kallonshi yake batareda ya motsa inda yake ba

gani yayi bala yanufi baya da sauri yabude mazaunin bayan

binshi da ido Deen yayi yana kallon ta inda naciki zai fito

sosai zuciyarshi ke wani irin bugu, yau dai gashi a kofar gidansu zee wanda wannan shine zuwanshi gidansu na farko

sosai zuciyarshi tabashi zee ce bayan motar ganin bala agaba hakan yasa bugun zuciyarshi qin daidaita, burinshi tafito yaganta ko yaji salama


na cikine yafito ahankali tun baya hangenshi sosai saboda bala daya kareshi harya bayyana agareshi sosai


daddy ne tsaye staring keenly at Deen kamar yadda shima Deen din ke kallonshi

ji Deen yayi kamar an sagemashi gwiwa, tsabar sanyin da jikinshi yayi jiyake kamar kaffafunshi bazu iya daukarshi

kallo daddy ke binshi dashi na tsagwaron mammaki don hakan yanuna qarara a fuskarshi hakan yasa Deen sauke idanunshi qasa yanajin wani irin kunyar daddy ta lullu6eshi

"Kamaldeen?" daddy yafada cikin mammaki wanda hakan yasa Deen dagowa yasake kallon daddy

"Deen.. is that you?" daddy yaqara cewa yana,binshi da kallo


saurin kada kai Deen yayi saikuma ya tsallako cikin sauri yana zuwa ya tsugunna yana gaida daddy idanunshi aqasa

"me kakeyi anan?" inji,daddy batareda ya amsa gaisuwarshi ba

dagowa Deen yayi ya kalleshi saikuma yafara motsi da baki amma maganar taqi fitowa

"kaga Mallam tashi kabude baki kayimin magana, meya kawoka gidana uhm?" yafada cikin fada fada

tashi Deen yayi yanajin kamar ya nitse ya huta

"d..daddy..."

"am not your daddy, tambayarka nayi kuma amsa,kadai nake buqata awajenka" daddy ya katseshi da hakan

"meya kawoka gidana?" yasake tambayar meanly


"daddy kuyi hqr...please, am so sorr..."

"haryanzu baka bani amsata ba" daddy yaqara katseshi

"na..nazo nabaku hqr ne..."

"haqurin me? wani abu yafaru?" inji daddy yanamashi kallon raini


Deen dakejin kamar zuciyarshi zata katse don tsalle ya hadiye yawu dakyar sannan yace
"daddy kuyi hqr don allah, nima bada son raina komai yafaru ba"

"kanajina? kayi maza kabar kofar gidannan kafin kafara regretting zuwanka" inji daddy meanly

"please daddy don allah" yafada pleadingly

"nace kabar nan" inji daddy


tsugunnawa Deen zaiyi yana cewa
"please dadd..."

"nace kabar nan!!" daddy ya katseshi atsawace wanda hakan ya hanashi ida kaiwa qasa saima jada bayan dayayi jin tsawar har tsakiyar kwalwarshi

"you have guts dama zaka,kwaso kaffafunka kazomin kofar gida? who do you think you are? to wlh kabarmin kofar gida tunkafin nayimaka abinda zaisaka danasanin sanina"

"daddy don allah kayi haquri"

"bakaji ba kenan?"
saiya fiddo waya yafara shafe shafe

"don allah daddy kayi hqr, nasan ban kyauta ba nasan bamu nuna hallarci ba, kuyi hqr ku gafarcemu amma wlh bada son raina hakan yafaru ba wlh inason Zainab.. komai yafaru ne bisa qaddara"

dakatawa da shafe shafen da yake daddy yayi yayimashi wani kallo

"wannan kalmar tafita daga bakinka mayaudarin banza, wane irin so kake mata dahar zaka gujeta alokacin datafi buqatarta, you broke her heart and you still have the guts to say you love her? how dare you?"

"daddy wlh qaddara ce, I love her so very much Kawai..."

"you never loved her.. baka ta6a sonta ba, yaudararta dama kakeyi kuma ni tuni nasan da hakan, itace dai,batasan da hakan ba har saida kanuna true colour dinka... well wannan kuma kai yashafa yanzu don daughter ta tariga tayi moving on, ta cikwikwiye babinka ta yar a dustbin yanzu haka,tayimaka nisan da ko hangenta bazakayi ba don haka kariqe haqurinka kabarmin kofar gida kafin na sassa6amaka"


tunda yafara magana Deen ke sauke ajiyar zuciya ahankali, jin magangganunshi yake kamar ana watsamashi garwashi, dakyar ya iya bude baki yace

"I know daddy.. I know nariga na 6ata damana, nayi ruining chance dina kuma ba lallai bane nasake samun wata ba amma don allah kuyi hqr ku yafemin duk abinda yafaru asanadina"

ta6e baki daddy yayi yace
"babu abinda yafaru ma sai alhairi, so no need of neman yafiya don munan jimukai ma gwamma da akayi"


rintse idanu Deen yayi cikin jin zafin abinda daddy yafada, zuciyarshi zafi take mashi kamar a oven

"you can go now" inji daddy cikin rashin damuwa da halin daya shiga

ahankali Deen yabude idanunshi dasukayi jajur ya kalli daddy sannan cikin rawar murya yace
"I'll go daddy, amma don allah kabari naga Zainab please"

wani kallo daddy yayimashi
"kaga Zainab kayimata me?"

"please daddy.. don allah kabari naganta please" yafada pleadingly muryarshi na rawa sosai idanunshi jajur

"don kasake huremata kunne? to bazaka ganta ba, now get going"

"don allah daddy.. ba huremata kunne zanyi ba, hqr itama zanbata akan halin dana jefata"


"wane hali ka jefata? babu halin daka jefata don kamar yadda nafada dazu wannan abin jimukai gwamma da akai so no need to bother yourself"

"daddy don allah kabarni naganta please...please" yafada yana dafe saitin zuciyarshi saiga hawaye

"bazaka ganta ba nace, bakaji abinda nace ba? nace,tayimaka nisa nisan da ko hangenta bazakayi ba so karka qara 6atamin lokaci get lost!"

tsugunnawa Deen dake hawaye sosai yayi don duk dauriyarshi yakasa riqesu
"don girman allah daddy kabari naganta, don allah. idan ban ganta ba zan iya mutuwa please"

"to allah yajiqanka don idan hakane mutuwa tazama ma dole don Zainab batanan ko tananan bazan bari kaganta ba don kallon fuskarkama na iya tadomata wani ciwon, so go Zainab batanan, bata garinnan, bata qasarnan koma tananan babu abinda zatayi maka saboda she belongs to someone else now, kotananan bakada hurumin ganinta because she's now someone's wife...she's married"


dagowa yayi ya kalleshi saikuma yadanyi murmushi yana girgiza kai

"daddy I understand bakason komai yasake hadamu da zee, I know abinda kakeyi shine abinda kowanne mahaifi da akayima abu irin wanda nayimaka zaiyi, nasan bakason naganta ne don karna huremata kunne or something like that, please daddy koda agabanka ne ka kirata please hqr Kawai zanbata na nemi yafiyarta"

dan murmushin takaici daddy
"wato ga maqaryaci ko? you think kowa maqaryaci ne kamar kai? believe it or not Zainab is someone else wife dama cemaka akayi tarasa manemane data nace sai kai? mtcheew bala muje" yafada yana qoqarin komawa cikin motar

saikuma yasake juyowa kan Deen dake kallonshi still kamar statue yana qoqarin fassara me daddy kecewa

"for the last time kabarmin kofar gidana for your own good amma"

yana kaiwa nan yashige motar dama bala yashiga suka shiga ciki leaving Deen standing like a tree


kasa gane me daddy ke nufi yayi, jiyayi kamar wani yare yayimashi dabaya fahimta

Zainab? Zainab is married? haba impossible

Kawai daddy beson yaganta ne shiyasa yace hakan amma babu yadda za'ayi ace Zainab tayi aure

da wannan tunanin Deen yadanji zuciyarshi tayi sanyi

qara daga kai yayi ya kalli gate din gidan dakeda tsayi sosai yana tunanin behind this gate akwai muradin ranshi aciki, baxai iya tafiya ba dukda warning dinda daddy yayimashi, he has come this far don Kawai yaganta kozaiji sauqin abinda zuciyarshi kemashi so duk yadda za'ayi duk tsawon lokacin dazai jira saiya jira don baxai zo abanza ba


haka yakoma gefe yasamu dakali ya zauna yana kallon gate din kamar za'a iya budemashi at any moment

haka yaita zama under the scorching sun yana jiran tsanmmani ga wata iriyar yunwa dake kwakularshi don dik yau beci wani abin kirki ba


yana lura da yadda every now and then maigadi ke dan bude qaramin kofar gate din ya leqoshi saikuma yakoma

bece komai ba bekuma tashi ba saima hoping dayake allah yasa daddy yaji tausayinshi ya yarda yaga zee din


ahaka yana zaune marece yayi sosai don har rana tafara alamun faduwa wata mota ta qaraso kofar gidan

dagowa yayi yana bin motar da kallo batareda ya motsq daga inda yake ba

wasu maza biyu cikin shigar shirt and trouser suka sauko daga motar suka nufoshi

har lokacin be motsa ba har suka qaraso wajenshi suna bin juna da kallo

batareda sunce mashi komai ba daya daga cikinsu yakara wayar hannunshi kunne yana cigaba da kallon Deen

"eh alhaji.. gashi nan mun iso... eh mun taddashi.. ok to shikenan" saiya katse wayar sannan yaqara fuskantarshi

"young man meyasa kakeson proving stubborn? mai gidan nan ya buqaci kabarmashi kofar gida amma you stubbornly remain there, did you know what you're getting yourself into?" inji mutumin


Deen dai bece komai ba sai cigaba da kallonshi dayake daga zaune

dayan yazaro ID card yanuna mashi yace
"mu yan sanda ne alhaji yakiramu nan ne don muyi getting rid of you from his house, so for your own good katashi katafi batareda mun tilastaka ba"

sai a lokacin Deen ya bude baki ahankali yace
"zan tafi, amma please kubari naganta... saboda naganta Kawai nataho daga inda nake mai nisa,.I promised idan naganta zan tafi koda bazaku bari nayimata magana ba"

"bakaji yace tayi aure ba? she's married kuma batama qasar kwata2 bare kaganta so is better you leave" inji nafarkon

"tana ciki sir, I know tana ciki Kawai bayaso naganta ne..."

daidai nan aka bude qaramar qofar gate daddy yafito wanda kallo daya zakamashi kasan ranshi a matuqar 6ace yake

"meye kuke jira haka baku tafi dashi ba? eh?"

"alhaji abinda muke niyyar yi kenan, muna qoqarin fahimtar dashi yarinyar bata gidan ne" inji daya daga cikin yansandan

"harsai kun fahimtar dashi? wazai maka qarya anan? wayai maka kama da qaramin mutum anan? who did you think you are da Zainab bazata auri wani ba bayan kai? gani kake don tanasonka bazata iya rayuwa,babu kai ba? inma haka kake gani you're totally wrong, she proved you wrong tunda gashi tayi exactly abinda kake ganin bazata iya ba, tayi moving on tayi aure tana abroad living happily, nobody needs you now so disappear"

Deen dake hawaye tunda daddy yafara magana ya girgiza kai ahankali

"daddy I know I hurt you guys and you're trying to hurt me back too, daddy ko iya nan ka tsaya naji kwatankwaci ko fin abinda nasaku ji, don allah ka sassautamin hakanan, kayi hqr kabari naganta nasan tana nan, Zainab bazata auri wani ba.. kada allah yasa hakan yafaru"

sakin baki daddy yayi yana kallonshi tunda yafara saikuma ya kada kai yace
"saidai atari gaba don hakan yariga yafaru, Zainab saidai wata ba 'yata ba don tayimaka nisa and if you think am lying ga wadannan..." yafada yana watsamashi wasu yan cards

"check and see, fatan hakan zaibaka amsar ka"

bin cards din qasan Deen yayi da kallo saikuma ya tsugunna yayi picking dinsu yatashi yana dubasu


kanshi yayi wani mummunan sarawa lokacin dayayi arba da invitation cards wanda sunan zee ke rubuce 6aro 6aro ajiki amatsayin bride under it kuma sunan namiji ne wanda tashin hankali besa ya iya riqewa ba


"yanzu ai zaka yarda ko tunda kagani da idonka, Zainab is married..happily don haka ka kama gabanka allah ya hadaka da rabonka"

"impossible.." Deen yafada in whisper yana cigaba kallon cards din hannunshi da gajiyayyun idanunshi

"but it is, it's possible don gashi ma kagani.. please officers send him away banason ganinshi anywhere near here"

sakin cards din Deen yayi yanufo daddy dasauri

"no.. daddy please don't do this to me, please" yafada da muryarshi datafi kama da rad'a yana nufo daddy saidai kafin ya iso officers din sun tareshi ganin zai turesu yawuce yasa suka rirrikeshi

"ku sakeni! get your hands off me!" yafada cikin daga murya yana fizgewa da qarfi saidai sun riqeshi gamm

"don't do this to me daddy... please" yasake fada cikin very cracked voice

"kubarmin kofar gida dashi" inji daddy da ko kadan halin da Deen keciki be ta6ashi ba illa wani farinciki da satisfaction dayakeji na ya ramama zee abinda yayi mata

"NO.. Zainab! Zainab!! Zainab please come out am here!!"
yafada cikin daga murya sosai yana qoqarin wucewa gate din gidan amma mutanen sun rirrikeshi

"take him away" inji daddy


"don't do this to me..." yafada qirjinshi na heaving


haka suka janye Deen dake maimaita 'don't do this to me' cikin muryarshi dake fita dakyar suka sashi a motarsu qarama ba irinta yan sanda ba

maimakon ya cigaba da struggling kamar yadda suka zata saigani sukayi ya kife fuskarshi akan.front seat yadafe saitin zuciyarshi da hannu bibbiyu yana sauke numfashi masu nauyi hakan yasa dayan dan sandan saurin zagayawa yashiga mazaunin driver dayan kuma na taredashi abaya riqeda bindiga suka ja motar suka wuce


ajiyar zuciya daddy ya sauke bayan tafiyarsu sannan yajuya yakoma ciki yana fatan yatafi kenan don idan yadawo he won't take it likely with him

saida yaqara bigema su bala da masu gadi warning cewa kada maganar dawowar Deen yasake yayi leak har yaje kunnen mummy sannan yawuce ciki don dama dalilin dayasa bebi da hayaniya ba kenan don beson yajawo hankalin mummy tasan meke faruwa don tsaf zata ruguzamashi shiri


a bangaren Deen kau tunda yakifa kanshi a tafukkan hannunshi be dagoba har suka iso idan suka ja suka tsaya

bubbude kofoffin sukayi suka fita sannan mutumin baya ya fiddoshi ya watsar gefen titi

"go away for your own good, idan kasake komawa we'll make sure you rot in jail" inji dayan sternly

komawa sukayi cikin motar suka ja suka barshi nan


kasa koda motsi yayi a inda yake yashe azaune, misalta abinda zuciyarshi ke going through lokacin abune mai matuqar wuya

jiyake he's world is turning upside down

sai lokacin yasan ashe kuka ma rahama ne don kasayi yayi sai ajiyar zuciya dayake saukewa kawai, tsakanin zuciyarshi da maqoshinshi yarasa wane yafimashi yaji yajin ciwo

har akayi magrib akayi isha'i yana nan zaune inda suka barshi gefen titi

yakasa ko motsawa hannayenshi still dafe dake zuciyarshi dayakejin tanamashi wani bala'in zafi


daga baya ne yasamu yatashi dakyar yafara tafiya,cikin jan qafaffu

tafiya yake batareda sanin inda zashi ba


***


A bangaren kaka kau tunda marece take jiran dawowar Deen amma shiru

wasa wasa har magrib tayi har akayi isha'i shiru hakan yasa hankalinta ida tashi

babu shiri tafito daga gidan don nemanshi ita da daya daga cikin mazan gidan nasu

sosai hankalinta yatashi dukda kwantar mata da hankali da mutumin keyi, gashi babu waya a hannun Deen bare akira aji

abinda yafi dagamasu hankali shine sanin dasukayi kasuwar dayake aikin ana rufeta ne shidda da rabin marece kuma daga nan beda wurin zuwa sai gida don saima yadawo yake sake fita sallar magrib

ganin lallashin da mutanen gidan keyima kaka da kwantar mata da hankalin beyi yasa suka fito din tareda wannan mutumin don cigitawa don suna zaman mutunci sosai da sabbin maqoftansu


gidansu wani saurayi dake qasan layinsu sukaje wanda shima yana zuwa aiki akasuwa saidai ba aikinsu daya da Deen ba

cikin sa'a suka taddashi be dade da dawowa sallar isha'i ba

anan suka tareshi suka gaisa sannan suka tambayeshi don allah ko duk yau yaga Deen akasuwa

amsamasu yayi da shidai gaskiya duk yau bega Deen ba kuma ba laifi ya bibbi ta shagonsu

nan suka sake tambayarshi ko yasan wani daga cikin wadanda suke aiki a shagonsu Deen

saida yadanyi tunani sannan yace eh yasan wani amma ba nan unguwar yake ba

nan suka roqeshi yakaisu ko yaimasu kwatance saiyace to bari yashiga gida yafito saiya rakasu

haka kau akayi babu dadewa saurayin yafito suka hau abin hawa sukaje unguwar dukda bawani nisa ke akwai ba cikin sa'a suka iske wanda sukaje nema a rumfar wani mai shayi

saurayin daya kawosu yaje yakirashi suka dawo wajensu kaka suka gaisa sannan suka tambayeshi yaga Deen yau

amsamasu yayi cewa gaskiya duk yau besa Deen a ido ba don bemazo aiki ba don har jajenshi saida akayi awurin kasancewar basu saba ganin yayi fashin zuwa aiki ba


nanfa hankalin kaka yaqara dugunzuma, kan kace me harta fara kuka tana cewa ina Deen zai shiga cikin garinnan da duka duka ko wata basuyiba acikinshi? ina zata fara nemanshi?


ataqaice dai haka suka koma gida cikin damuwa suka gayawa mutanen gidan nan suma hankalinsu yatashi, duk inda suke tunanin zasu ganshi sunje amma shiru babu shi

qarshe dai nearest police station sukaje suka bada report din 6atanshi inda akayi musu alqawarin bincikashi sannan suka koma gida


ranar yadda kaka taga rana haka taga dare kuka kau tun tanayi har muryarta yabar fita


Washegari ma haka suka tashi da heavy heart, mutanen gidan dayake sunada kirki sosai su sukaita tausar kaka da har wani hiri hiri tayi saboda tashin hankali

ranar ma haka suka dasa neman Deen amma shiru har police station din suka koma suma ba labari


haka suka wuni cikin jimami mutane nadan shigowa sunama kaka jaje, daga baya ma har sanarwa sukakai gidan radio da taimakon su mazajen gidan


sai wajajen isha'i kowa na waje an zazzauna kan tabarma matan gidan sunsa kaka atsakiya sunata qoqari wajen kwantar mata da hankali sukaji sallamar wasu maza daga bakin kofa

amsawa duk sukayi suna bada izinin shigowa wasu maza suka shigo suna cewa ga wannan yaron da ake nema can waje asume


kafin kowa yatashi kaka ta tashi don tunkafin su ida maganar tayi zumbur tamiqe tanufi waje agigice mutanen na maramata baya

daga qarshen dakalin kofar gidan nasu tahangi tarin mutane hakan yasa tanufi wajen tana kuka sosai


ratsa mutanen tayitayi harta qaraso gaban wurin inda taga Deen kwance daya daga cikin mazajen gidan na shafamashi ruwa a fuska

agigice kaka tazube gabanshi tajawoshi ajikinshi tana rusa kuka kamar ranta zai fita

ganin dik shafa ruwan da akayimashi be farkaba yasa mazajen wajen shawarar akaishi asibiti Kawai

haka kau akayi cikin qanqanin lokaci aka samu abin hawa suka saka Deen da har lokacin ke unconscious aciki sai kaka da daya daga cikin mazajen gidan hayansu suka kama hanyar asibiti


suna isa babu 6ata lokaci aka amshesu saboda ganin yanayin dasuka kawo Deen, nan da nan aka hau bashi taimakon gaggawa

tun kaka na kuka har hawayen idanun suka kafe haka sukaita jira waje cikin tashin hankali suna jiran tsanmmani


saida likitoci sukafi awa akanshi sannan suka fito inda suka nemi ganin iyayen yaron

kaka da mutumin sukabi likitan har office dinshi inda anan yake gayamasu halin da Deen yake ciki cewa jininshi yahau sosai ga ciwon zuciya dake barazanar kamashi

sosai hankalin su kaka yasake tashi inda ganin hakan ne yasa likitan kwantar masu da hankali cewa insha komai zaiyi daidai sannan ya rubuta masu magungunna da injections dasuke buqata

haka suka fito daga office din likitan kaka still takasa daina kuka gani take kamar zata rasa Deen ne

lokacin har dayan mijin matan gidan hayansu yaqaraso shima inda da taimakonsu aka siya duk abubbuwan da aka buqata don kaka bawani kudi gareta ba

anan kaka ta kwana tareda Deen wanda da alamu allurar barci sukayi mashi, fuskarshi tayi fayau tafada sosai gwanin tausayi


be farka ba sai Washegari wajajen taran safe

yana tozali da fuskar kaka da tunda yabude ido tayi wajenshi tana kiran sunanshi yafashe da kukan daya kasayi tun a Katsina

kuka yake sosai yana fadin yarasa zee shikenan yarasa zee har abada

ganin yadda yake kukan yasa hankalin kaka sake tashi babu shiri tayi waje don kiran likita


koda suka dawo ma kukan suka tadda yanayi yana shikenan yarasa zee, dakyar Dr yashawo kanshi yaqara yimashi wani allurar barcin wanda yasashi komawa to slumber nan take


sosai kaka tadinga kuka tana kallon Deen daya dawo abin tausayi duk saitaji wani feeling na guiltiness zuciyarta tayimata mugun nauyi sanin cewa kowanne hali Deen yashiga itace sila


lokacin da Deen yasake farkawa beyi kuka ba wannan karon saidai kallo daya zakamashi kasan he's really in pain

he looks so sad and down

and that day mark the beginning of his sorrowful life


kwanansu biyar aka sallamesu saidai kwata2 Deen ya chanza yakoma kamar bashi ba

he's no more the cool and happy Deen, farinciki yayi qaura a rayuwarshi Kawai rayuwa yakeyi batareda yasan dadinta ba

baya murmushi, shirunshi ya ninka nada yakoma wani iri gashinan dai

baya fita saida dalili wanda mostly zuwa masjid ne ko shiga toilet amma daga ba haka ba kodayaushe yana qunqume cikin daki kamar matar kulle

wannan sabon sauyin na Deen ba qaramin sake dagulama kaka lissafi yayiba, wani irin tausayinshi takeji tana kuma rashin kyautawarta na hukuncin data yanke tunfarko, tasan ko mai yafaru itace sila hakan yasa takejin guiltiness sosai

kaka fara jaraba sana'a tayi da yan kudin hannunta don tunda Deen yadawo beqara fita da sunan zuwa kasuwa ba gashi komai nasu qasa yakeyi hakan yasa kaka tattara yan kudinta tafara sana'ar toya fanke dasafe

cikin ikon allah saigashi allah yasama abin albarka don kaka koyaya tayi abu dasunan sana'a sai allah ya albarkaci abin ya buda mata

tun tanayi mutanen cikin gidan kawai na siye har yan waje suma suka gane suna shigowa saye

cikin ikon allah saigashi suna samu suna rufawa kansu asiri da sana'ar


saida Deen yafi wata a yanayin dayake ciki sannan yafara dan samuwa

da taimakon addu'o'i da kaka ke sashi aciki kullum dakuma rubutun dangana datake bashi yaji sauqin abinda yakeji yakuma yi deciding yayi moving on dukda abu ne mai matuqar wuya agareshi

yakasa mantawa da memories din rayuwarshi da zee abaya, jiyake da ana tariya daya tariyo rayuwarshi ta baya sun dawwama acikinta amma hakan be yiwuwa


ganin wahala da fadi tashin da kaka kemasu itakadai don rufama kansu asiri yasa Deen yake shawarar cigaba da fita nema don he can't watch her struggling all alone


ranar daya shirya zaya koma kasuwa farinciki awurin kaka baya misaltuwa don jitake kamar taita rawa don murnar yaronta yafara dawowa

haka taita samashi albarka ta rakashi har waje tana qara godewa allah azuciyarta tana addu'ar allah yasa qarshen wahalar kenan, sosai tayini cikin farinciki don tasan koba komai dan fitan nan dazai dinga yi zai taimaka wajen ragemashi damuwarshi sosai


sosai co-workers dinshi na kasuwan sukayi murnar dawowarshi don babu laifi sundan saba dashi kuma duk sunji abinda yasameshi hakan yasa sukaita mashi ya qarfin jiki yana amsamusu da faint smile dinshi dayanzu yazama shade to his sorrowful state

babu 6ata lokaci yakoma aikinshi kamar da saidai kwata2 yanzu bayajin dadin aikin kamar farko kawai yiyake maganin zaman banza amma har a zuciyarshi aikin bemashi ba bawai don ba'a samu ba Kawai dai yafison yayi wani aikin daya kasance dole akwai experience yakasance aikin hannu daxaka koya ka iya ba wannan da qarfi Kawai yake buqata ba yana son aikin dake buqatar basira kamar dai wancan na capentary dayakeyi a Katsina

hakan yasashi fara neman workshop workshop na capentary don komawa irin aikinshi nada amma duk inda yaje babu vacancy

haka ya cigaba da aikin dakonshi a gefe yana neman aikin capentary amma tsit kakeji

watarana yazo wucewa zaitafi kasuwa yabi tawata gareji daya saba bi idan zai tafi kasuwa, saiya tsinci kanshi da tsayawa ya qurawa wurin ido yana kallon kanikawan dake buge.bugen karafuna

haka Kawai yaji aikin nasu yashiga ranshi farat daya hakan yasa ya qarasa wajen yana kallon mutanen wajen

sallama yayima mutanen wajen wanda hakan ya maido hankalinsu akanshi

amsamashi sukayi suna binshi da kallo hakan yasashi dan sakarmasu murmushi

"erm...dan allah ina ogan garejin nan? nima garejin nakeson fara zuwa idan akwai vacancy, inason fara irin aikinku ne"

kallon juna mutanen da duk samarine sukayi sai daya yace
"kutt... wlh nayi tunanin balarabe ne dafarko, nan jira kawai nake yafara cemana *Hal anta majnunun*"

dariya kingin suka kwashe daita sannan daya yace
"majnunu fa mahaukacine Dogo, kodai anyi asarar kudin laraba ne"

daya yace
"Yo ai dama mahaukacinne, dama kajen haquri yayi da beyi magana ba dasai balaraben ya tambayeshi koshi majnunun ne don akallo daya akegane hakan"

"kai wlh qaryane don ubanka, dani dakai wayafi ruwan mahaukata?" inji nafarkon

haka suka cigaba da caftar mai cikeda ban dariya sukama manta da Deen dake tsaye yana kallonsu

ganin hakan yafara shawarar koya tafine? saikuma yace bari dai yasake masu magana hakan yasashi sake cewa

"don allah.. yana nan ne ogan?"

sai a lokacin suka sake dagowa

"eh to yanzu dai bayanan amma ko yananan dakyar zai daukeka muma kanmu complain yake munyi yawa" inji wani

"sannu.. ina ruwanka da yanke hukunci akaran kanka,kabari yaga ogan mana yagayamashi idan ma munmashi yawan, bansan iyayi... kai balarabe kaje kadawo anjima idan yadawo saika sameshi" inji dayan

"to da yaushe kenan?" inji Deen dake kallonsu

"anjima kadan bayan azahar kadawo nasan yana nan",inji saurayin

"to amma kai karasa aikin daya burgeka sai kanikanci kana fari tass dinka? ca6 wlh da nikeda farinka babu abinda zaisani kanikanci wlh saidai aikin office" inji Dogo


"kaji marar kishin kai yana kushemana sana'a to wlh kamar kayi a kunnen oga"

"yo ai gaskiya ne, kanikanci banda kwalliya da baqin mai me ake aciki, dubeni fa da haske na nazo garejin nan amma yanzu nazama dawanau"

dariya suka fashe daita

"a gidan ubanwa kaxo da haske? dama a dunan ka kazo sai uban qasusuwa banda ma rashin godiyar allah ai kaima kasan kamori kanikanci tunda gashinan kayi 6ul6ul dakau banda uban kai me kake dashi?"

"tubarkallah bismillah" inji mutumin da akema tsiya din

Deen be tsaya qarasa jin caftar su ba yawuce yana addu'ar allah yasa ogan ya daukeshi aikin don haka Kawai yaji aikin yashiga ranshi lokaci daya

da wannan tunanin ya qarasa wajen aikinshi inda yashiga yin aikinshi

yana fitowa daga sallar zuhr yawuce direct garejin yana addu'ar allah yasa ya tadda ogan

cikin sa'a kau ya taddashi inda yaga mutumin magidanci ne don zaikai irin shekara arba'in dawani Abu dinnan


saida suka gaisa sannan ya gabatar mashi da buqatarshi nason fara zuwa garejin

da farko kamar baxai yarda ba don acewarshi yara sunmashi yawa saikuma yace yaje yadawo gobe idan allah yakaisu zai duba

godiya Deen yayimashi sannan yatafi cikeda saran samun aikin

Washegari kau tunda wuri yaje don harwani doqin zuwa yakeyi inda anan ogan yace ya daukeshi aikin yakuma gayamashi sharuddan garejin tareda gabatar mashi da sauran yaran garejin su biyar Dogo, Sule, Habeeb, Nura da Yusuf

yakuma gayamashi a matsayinshi na junior dole yabi wadanda ya tadda koda ya girmeshi don yanzu shine junior dinsu kwata2 kuma akwai banbanci a sallama don anayine according to seniority

duk Deen ya amince da hakan sannan ogan yace yana iya tsayawa yau din kokuma yaje yabari sai gobe yafara zuwa

cewa Deen yayi zaifara yau din hakan yasa ogan ya hadashi da daya daga cikin yaran (Habeeb) akan yatafi dashi cikinsu

ranar Deen yaqara sanin yadda yan garejin suke don shaqiyai ne na gidan gaba

zolaya babu wanda besha ba wurinsu inda suka rad'amashi balarabe da qarfi da yaji don babu wanda ya tsaya bi takan sunanshi kawai sun rad'a mashi nasu wato balarabe

ranar saidai yazama dan aike, dauko wancan spanner miqo wancan haka sukaita aikenshi idan be ganeba suyimashi bayani, at the end of the day aka sallamesu inda nashi sallamar duk yafi na sauran qanqanta

be damuba ya amsa yai tahowarshi gida yanajin dadi don sosai yaji dadin yininshi daya a garejin don mutanen garejin badai ban dariya ba, suna aiki suna shaqiyancinsu hakan yasa koyaya kaje zauna wajen saisun saka nishadi

saida yakoma gida yagayama kaka sabon aikin dayasamu yakuma bata sallamarshi

kaka bataji dadi ba don sallamar batakai abinda yake samu a kasuwa ba gashi tana ganin aikin aikin qarfi ne zaifi na kasuwar wahala amma ganin yadda Deen yanuna yanason aikin yasa bata hanashi ba saima fatan alhairi datayi mashi

to daga wannan lokacin Deen yazama bakanike shima yazamana kullum yana gareji

Atashin farko Deen yayi popular a garejin, bayada surutu ko kadan saidai rashin kyashi dinshi yasa yaran garejin ke sonshi sosai don saidai kaji ana balarabe miqo kaza, balarabe yi kaza kuma nan take zaiyi yana haddace me akeyi

dayake yana son aikin sosai hakan yasa yake saurin dauke komai batareda anyimashi maimaici ba, ga tambaya don duk abinda yashige mashi baya jinkirtawa wajen tambaya

kaifin kwalwarshi da karsashinshi a aiki yasa cikin qanqanin lokaci yayi suna a garejin inda ogansu keji dashi sosai saboda tsantsar biyayyarshi da kaifin kwalwarshi


duk cikin yan garejin Deen yafi sabawa da Habeeb don jininsu yafi haduwa dukda Habeeb nada surutu sosai sa6anin Deen

shaquwarsu yasa Deen fara kwana shagon da Habeeb ke kwana kasancewar unguwarsu daya

kullum tare suke zuwa gareji sukoma tare lokacin kwanciya kuma su hade a shago, wannan yasa abotarsu taqara qarfi sosai


cikin yan watanni Deen yayi suna a garejin na ban mammaki, sosai customomi keson aikinshi don dayawa saisuka dawo idan sun kawo aiki basusan kowa ya ta6amasu mota sai Deen

gaskiyarshi da rashin ha'inci irin na wasu daga cikin yaran garejin yasa customomi sukafi sonshi ga uwa uba sanyinshi da biyayyarshi dake matuqar burge mutane sosai

hakan yasa nan da nan ya kwacema sauran customomi inda duk cikin yaran garejin yafi kowa customers dukda shine junior dinsu


gashi ogansu ya yarda dashi sosai yana kuma yawan dorashi akan abubbuwa da dama saboda yarda dayayi dashi kasancewar ogan ba a iya kanikanci Kawai ya tsaya ba harda kasuwanci irin nasu na yan gwangwani

daga baya ma saima ya miqa kusan ragamar kasuwancin hannun Deen don saiya zama kamar wani assistant dinshi don duk cikin yaran garejin babu mai makullin shagon kasuwancin ogan sai Deen


wannan cigaban daya samu sosai saiya tsonewa wasu daga yaran garejin ido musanmman wadanda ke ganin sundade sosai a garejin tayaya wannan daga zuwanshi a dinga fifitashi akansu a matsayinshi na junior dinsu

hakan yasa suka fara yimashi hassada suna ganin be cancanci matsayin dayake akai ba


tun suna iya 6oye hassadar dasuke mashi harsuka kasa don dagabaya qarara suka fito suna nunamashi qiyayya, Habeeb ne Kawai mai kaunarshi tsakani da allah

dayake hassada ga mai rabo taki take zama hakan yasa kodayaushe Deen cigaba Kawai yake samu takoina wanda hakan yasa yan garejin hada kai don qullamashi sharrin daxai dusashe tauraruwarshi

ranar ranace da Deen bazai ta6a mantawa ba inda aka nemi wasu kayan engine akarasa a shagon wanda kudinsu ba dan kadan bane

abin ya tadawa kowa na garejin hankali musanmman Deen don bayan ogansu shikadai keda key din shagon hakan yasa kullum shine qarshen tafiya gida

tun ana daukar 6atan kayan wasa har akaga dagaske sun 6ata din inda babu wata wata aka dora ayar tambaya akan Deen

dayake ogan irin mutanen nan ne dabasu yarda da qaddara ba ko asara nan take ya manta da tsantsar amanar Deen da gaskiyarshi yahau tuhumarshi acewarshi dole yasan wani abu gameda 6atan kayan

nanfa hayaniya ta tashi ogan ya murje ido akan sai Deen yabiyashi kayanshi

sosai hankalin Deen yatashi don tunda yake ba'a ta6a yimashi qazafi irin haka ba, duk yadda yaso wanke kanshi qin yarda dashi ogan yayi inda sauran yan garejin keta qara zugashi akan karya yarda

mutane biyu Kawai suka goyi bayan Deen da Habeeb dawani maqocinsu a garejin mai saida tayoyi

ganin hakan yasa Deen cewa zai biya amma allah yasani bashi yadauka ba, be ta6a sata ba kuma insha allah bazai ta6a yiba


haka yadawo gida zuciya a quntacce yaba kaka labari inda itama ta tayashi jimami sosai tana tayashi jin zafin qazafin da akayimashi

haka Deen ya tattaro yan kudaddenshi dayake tarawa kaka tacikamashi yabiya ogan daga ranar kuma ya daina zuwa garejin


sosai rayuwa tasake juyema Deen inda yasake komawa halin qunci na da

dama wannan aikin dayakeyi ke dan debemashi kewa hakan yasa yanzu yaqara komawa gidan jiya na halin damuwa


komawa yayi tsohon shagonsu na kasuwa ya cigaba da aikin dako badon yanason aikin ba saidon baison zama hakanan

sosai yayi missing gareji da kanikanci don yanason aikin sosai saboda aikin ma kanshi nasashi nishadi na musanmman

har lokacin alaqarsu da Habeeb nanan don dafarko shima Habeeb yaso barin garejin Deen ya hanashi hakan yasa anytime he's free yake leqo Deen acikin kasuwa

haka rayuwa ta cigaba da kasancewa har watarana Deen a hanyarshi tadawowa daga kasuwa lokacin har magrib takusa yagamu dawani mutum yana fama da motarshi

harya wuce saikuma yadawo ya qarasa wajen mutumin yana mishi sallama

amsawa mutumin yayi yana dagowa yana kalleshi hakan yasa Deen cewa

"motar taqi tashi ne?"

kamar wanda dama ke akan qaya yace
"eh wlh dan saurayi, kaganta nan narasa meke damunta gashi sauri nake zani wani wuri gashi duk garejijika sun kulle na rasa yadda zanyi" yafada da alamun damuwa a fuskarshi

"bari mugani..." inji Deen yana sunkuyawa gaban motar yana dubawa

haka kawai yaji kwadayin kanikancin na tasomashi, rabonshi da ta6a mota da niyyar gyara tun lokacin dayabar garejinsu

mutumin dai tsayawa yayi yana kallon Deen don kwata2 bemashi kamada bakanike ba, hakan yasashi tsayawa kallon ikon allah

saida Deen yadan dauki lokaci a sunkuye sannan yacema mutumin yashiga motar ya tada yaji

hakan kau mutumin yayi yashiga yatada Deen ya sake sunkuyawa yana gyaran

cikin qanqanin lokaci motar ta tashi

sosai farinciki ya lullu6e mutumin wanda hakan yakasa 6oyuwa a fuskarshi hakan yasa yafito yanata mashi godiya yana tambayar dama shi bakanike ne?

murmushi kawai Deen yayi bece komai ba

kudi mutumin yabashi amma firr Deen yaqi amsa, dik yadda mutumin yaso ya amsa qiyawa Deen yayi hakan yasashi haqura

nan mutumin ya tambayeshi inane garejinsu, kamar Deen zaice bayada gareji saikuma yayi mashi kwatancen tsohuwar garejinsu kawai

godiya mutumin yasake mashi suka rabu


Bayan kwana biyu mutumin yaje garejin da Deen yaimashi kwatance don sosai Deen ya kwanta mashi yakuma shiga ranshi farat daya gakuma tunda yake bada gyaran mota ba'a ta6a yimashi gyaran dayaji dadinshi ba irin wannan

saidai koda yaje bega Deen ba yakuma tambaya inda yana musu kwatancenshi suka gane Deen ne

abinne yasosama yaran garejin rai don tun barin Deen garejin ba ranar banza da baza'a zo nemanshi ba, wasu ma har barin kawo aiki sukayi garejin

hakan yasasu cewa su basu sanshi ba qila ba daidai yaimashi kwatancen ba

daidai nan Habeeb yazo wurin jin abinda ake tattaunawa yasashi yin caraff yace kodai balarabe yake nema

dasauri mutumin ya kadamashi kai yace eh yana kama da balarabe

caraff daya daga cikin yaran garejin yace inda balarabe ne toya andade da korarshi daga garejin saboda sace sacen dayakeyi

ran Habeeb ya6aci da kalamanshi nan yashiga maidamashi cewa saidai insune 6arayin amma Deen ba 6arawo bane kuma zakaran da allah yanufa dacara ko ana muzuru ana shawo saiyayi sannan yajuyo kan mutumin yace aiki ya kawo ko balaraben yake nema?

mutumin daketa kallonsu tundazu yace balaraben yake nema hakan yasa Habeeb yace yataho yakaishi wajenshi

sosai hakan ya 6ata ran yaran garejin don ba haka sukaso ba, dukda sun raba Deen da garejin sunkasa rabashi da masoyanshi don hatta ogansu shima yanzu danasanin abinda yafaru yakeyi don barin Deen garejin nashi ba qaramin cibaya yajamashi ba


Cikin motar mutumin suka tafi neman Deen inda akan hanya Habeeb ke labartama mutumin duk abinda yafaru da barin Deen din garejin hakan yasa Alhajin tausayawa Deen yakuma ji yaqara shiga ranshi fiyeda da


koda suka isa shagon basu iske Deen ba don acewar co-workers dinsu be dade da tafiya gidaba don wani lokacin yana komawa gida cin abincin rana

Alhajin be gajiba yace suje gidan nasu shidai yanason ganinshi

babu musu Habeeb yakaishi har gidan nasu inda anan suka hade da Deen da fitowarshi kenan da niyyar komawa kasuwar

sosai Alhajin yaji dadin ganin Deen nan suka gaisa cikeda mutuntawa inda saida Alhajin ya tunama Deen inda suka fara haduwa don shi harya manta

nan Alhajin ya buqaci zai dinga kiranshi duk lokacin dayakeda gyara yazo yayimashi

babu musu Deen ya amince mutumin yabashi card dinshi mai dauke da address dinshi da number waya shima Deen yabashi number wayarshi

haka kau akayi don duk lokacin da Alhaji Shamsu kamar yadda sunanshi yake ya buqaci gyaran mota zai latso Deen yazo yayimashi wani lokacin har hanya yakemashi yayima wasu don sosai yakeson aikin Deen saboda qwarewarshi

shima Deen sosai yakejin dadin aikin Alhajin don mutumin akwai sanin darajar mutane, dukda shi mai kudine amma hakan besa ya qyamaceshi ba, yana nunamashi qauna sosai

ahaka ne suka hadu da diyar Alhajin mai suna Lailah agidan Alhajin wanda tun a farkon haduwarsu ta afka soyayyarshi kuma haryanzu tana sonshi batareda yama san tanayi ba don shi banda gaisuwar mutunci babu abinda ke hadasu daita


Alhaji Shamsu yanada mata daya sai 'ya'ya shidda duk mata, hudu daga cikinsu duk sunyi aure sai Lailah dake karatunta haryanzu sai yar qanwarta kuma autarsu Afrah

Alhaji bayada d'a namiji kodaya kuma tunda yake beta6a jin qaunar mutum kamar yadda yakejin yadda yakeji gameda Deen ba hakan yasa ya daukeshi kamar danshi yana nunamashi qauna ta tsakani da allah


ana haka watarana yabashi aiki inda yayimashi text din address din inda zaije yasamu motar don lallacewa tayi ahanya yabarta yahau wata yadawo

sashi yayi yafara aikin gashinan zuwa

haka kau akayi inda Deen yaje wajen yafara aikin motar

can yana tsaka da aikin tunanin zee yafadomashi kamar yads tunaninta ke yawan kawomashi ziyara akodayaushe

dukda yasan yanzu zee tayimashi nisa hakan besa yadaina tunaninta ba

akodayaushe cikin tunaninta da begenta yakeyi


fuskarta tayimashi gizo a idanunshi smiling like an angel hakan yasashi shima sakin guntun murmushi ahankali

_old good memories of you.._

_never want to fade in my brain_

_you're stick to my brain like a magnetic glue_

_never wanting to shift for a bit_


_an angel.._

_the angel... that I never saw someone like her that exist_


_an angel..._

_the angel that will always never exist_


cikin cool voice dinshi yacigaba da waqar wanda anan take yake composing dinta

dama yanzu haka yake, haka kawai yana zaune shikadai saiya fara waqa wanda mostly tana zuwa ne duk lokacin dayayi nisa cikin tunanin zee dinshi

shikanshi besanin sadda yake farawa saidai yaji kawai yanayi kuma waqar nazuwa ne from the bottom of his heart don abinda yakejine yake furtawa directly a sigar waqar

haka yaitayi yana aikinshi yana waqarshi, dayayi wannan yayi wannan, wasu da hausa wasu da turanci

nan da nan yagama aikin ko harda waqar datayi making dinshi busy yasa yaga saurin aikin oho?

yana gamawa ya maida gaban motar yarufe yadago yana share gumi

tozali da Alhaji dayayi agabanshi yasashi dakatar da abinda yakeyi yana dan wara idanu

"Alhaji yaushe kazo?" yafada da mammaki

"tun lokacin daka fara waqarka" yabashi amsa

kunyace takama Deen hakan yasashi sunkuyar dakai yana sosa gefen wuya

"ashe ka iya waqa? gaskiya tunda nake banta6a jin muryar datayi captivating dina irin wannan ba"

kunya Deen yaqaraji hakan yasashi cewa
"to ko ka gwada motar kotayi?"

murmushi Alhajin yayi yashiga motar yatada yajita tayi daidai hakan yasashi fitowa yana cewa tayi sosai

murmushi Kawai Deen yayi

Alhaji yasake cewa
"kanada ra'ayin yin waqa? yadda naji muryarka dinnan awaqa nasan baqaramin mawaqi za'ayi anan ba"

sunkuyar dakai Deen yaqara yi cikin jin kunya don dayasan Alhaji na wajen babu ma abinda zaisashi yi don yanajin kunyarshi sosai

"kayi shiru?"

"Alhaji bafa wani iyawa nayi ba"

"wani ba iyawa kayi ba? wai kajika kuwa? gaskiya zan kwadaitamaka jaraba waqar muji don gaskiya inaji ajikina voice dinka zai mayar dakai wani, idan kanada ra'ayi kayimin magana zan tsayamaka insha allah, ai waqa ma babbar sana'a ce kuma baiwace babba, kayi tunani Akai"

da to kawai Deen ya amsa badan yadauki maganar serious ba

cemashi yayi yakai motar gida shi yanzu wani wurin zashi sannan yashige motar yawuce

tun Deen na daukar maganar Alhaji wasa harya ga dagaske fa yakeyi don kodayaushe cikin yimashi maganar Alhajin yake

tun yana zillewa beso haryaji shima sha'awar gwadawa din inda a gwajin farko ya burge mutane dayawa

ahankali ahankali da taimakon Alhaji dakuma qarfafa gwiwarshi Deen yacigaba da waqar inda ahankali waqoqinshi suka fara samun kar6uwa acikin al'umma

kan kace me? cikin ikon allah cikin qanqanin lokaci Deen yayi fice yakuma yi suna acikin mawaqan zamani

sosai Alhaji yayi farinciki da hakan yakuma ginamashi studio inda zai dinga gudanar da harkar waqarshi


sosai waqar ta kar6eshi don cikin qanqanin lokaci yayi suna yana kuma samu sosai acikinta wanda hakan yajawo chanjin rayuwa agaresu har suka mallaki gidan kansu


ahaka ya nemi Habeeb abokinshi qwallin qwal yamaidoshi wajenshi yazama manager dinshi inda suke gudanar da harkar waqar tare

ahankali Deen ya chanza daga poor timid guy zuwa rich handsome guy wanda harda kyawunshi ke qara mashi farinjinin jama'a yakuma zama abinda yazama yanzu....✍�


Ummin fasihu🧚🏻‍♀�
8/5/21, 8:17 AM - Buhainat😝: *🙍🏻‍♂️DEEN🙍🏻‍♂�*


*095*


"duk abinda nazama na zama hakan ne ta dalilinki Zainab, am sorry for going away just like that, nayi danasanin tafiya nabarki, nayi danasanin rashin tsayawa kai da kafa wa soyayyarmu, natafi nabarki batareda tunanin ya zakiji bayan kingane na gujeki, I should have stay.. I should have tell you komai alokacin qila mu iya shawo kan matsalar atare, saigashi sanadin stupidity dina nayi wata irin rayuwa marar armashi kwata2, I guess that's what I deserve... and the amazing thing is yadda kikayi connecting dina da wadanda kwata2 banma san dasuba duk tsawon rayuwata... namaki sharri kinsakamin da alhairi, be kamata na iya hada idanu dake ba, bansan ta ina zanfara ba, bansan da wadanne kalamai zanyi amfani dasu ba wajen godemiki, all I know is samin masu golden heart irinki a duniyar nan zaiyi matuqar wuya"


lumshe idanunta dasuka gaji da zubda hawaye zee tayi tasake budesu ahankali jikinta duk yayi sanyi dajin labarin Deen, he went through alot hakan yasa taji wani irin tausayinshi ya lullu6eta, mutum da gatanshi da family dinshi amma yasha wahalar duniya

bata tunanin tunda mussadiq yake yasan wani abu wai aikin qarfi, kallo daya zakamashi kasan cewa shi real ajebo ne, besan komai ba sai hutu, yana nan cikin hutu da jindadi while twin dinshi nacan yanashan wahalar duniya, such is life

"Zainab please forgive me, let's forget our past and start afresh.. ina sonki Zainab son da bazan iya misaltawa ba, ada naji kamar na hqra dake jin cewa ke matar wanice amma yanzu bazan iya ba... ki hukuntani takowace hanya amma banda ta hanyar juyamin baya..idan kikayi hakan zan zauce... zan mutu ...please" yaqarashe ahankali yana kallonta in the eye da oily eyes dinshi dake jiqe sanadin hawayen dayayi

itama shi take kallo takasa janye idanu akanshi ganin yadda yawani marairaice mata

komai nada ne yashiga flowing back a qwalwarta, tunawa tayi da farkon haduwarsu, tunawa tayi da yadda dafarko basa shiri takuma tuna yadda akayi suka shirya

sosai memories din ke flooding qwalwarta inda take tuno rayuwar dasukayi a school inda suka zama kamar wasu besties, tunawa tayi da incident dinsu master da yadda yakusan rasa rayuwarshi akanta, tunawa tayi da soyayyarsu, yadda yake treating dinta like a queen, beson 6acin ranta ko kadan, yadda yake nunamata tsantsar so da qauna...

"Zainab please give me another chance...kisake bani dama na nunamiki yadda nakesonki a zuciyata, kisake bani dama na nunamiki haryanzu wutar qaunarki na ruruwa a zuciyata, bata ta6a mutuwa ba kuma baxata ta6a mutuwa ba har abada... please kisake bani wata damar" yafada softly but romanticly


"Zainab!.."

atare suka dago daga Deen har Zainab din suka kalli saitin inda aka aka kirata


Aymaan ne suka gani daga dan nesa dasu yana kallonshi shima fuskarshi expressionless

"Akhie?" zee tafada ahankali tana tashi tsaye don daman har lokacin a kneeling position suke

sai a lokacin tama lura da yadda marece yayi sosai, mammaki yakamata don ita harta manta dama cikin school suke

ahankali Aymaan yafara takowa yana kusantosu hakan yasa shima Deen miqewa yana kallonshi batareda wani yanayi yanuna a fuskarshi ba


saida ya qaraso gabansu sannan ya dakata idanunshi akan Deen dashima nashi ke kanshi saiya dan sakarmashi guntun murmushi yabashi hannu

"aslm alaika"

amsar hannun Deen yayi shima yana danyin murmushin da iyakarshi lips

"wa'alaika sallam warahmatullah"

daga haka kowa yajanye hannunshi Aymaan ya maida kallonshi kan zee

"mutafi if you're through" yafada yana kallonta

sauke idanunta tayi daga kallonshi saboda wani kwarjini dayaimata

batace komai ba tazo tawuce tayi gaba Deen yabita da kallo


ahankali ya maida kallonshi kan Aymaan dake kallonshi haryanzu

dan murmushi Aymaan yasake yimashi sannan ahankali yace
"bansaniba ko awajenku it's proper amma anan kokuma ince a musulunce bedace namiji yatare mace daba muharramarshi ba ahanya harya tsaidata tsawon lokaci haka, the proper way shine zuwa gidansu yanemi izinin magabatanta kafin yayi hakan... fatan za'a gyara"

daga haka shima yajuya yabi bayan zee dahar tayi nisa


binshi da kallo Deen yayi cikin tafarfasar zuciya

idan yace be 6atamashi rai ba yayi qarya, he just appear from nowhere ya 6atamashi moment kuma har yanada gut din fadamashi baqar magana?


furzar da huci yayi ahankali yakai hannunshi akan sumarshi yana scratching dinta


***


tafiya suke babu mai cewa kowa komai, motar tawani dauki shiru kamar babu kowa ciki

Aymaan hankalinshi nakan tuqinshi itakuma idanunta nakan kwalta bata yarda ta janyesu akai ba


tafiya yake slowly don kwata2 motar bata gudu don gani zee take qila da aqafa take dasai tafi motar sauri saidai batace komai ba don ko hada ido bata yarda sunyiba don wani iri takeji sosai, jitake kamar ta 6ace daga motar ta huta, hakanan takejin rashin jindadin taddasu dayayi da Deen akuma yanayin daya taddasu, sosai takejin wani iri akan hakan, shi wonder me tunaninshi zaibashi akan hakan


jitake taqara su isa gida tafita daga motar saboda yadda takejin kanta amatuqar takure amma saiwani tafiya yake slowly kamar snail

ahankali taga ya gangara gefen titi hakan yasata dagowa tana kallon inda suka shiga


akaro nafarko tunda suka taho tajuyo ta kalleshi lokacin yana neman wurin parking

sake kallon wajen tayi sannan tasake juyowa ta kalleshi daidai shima yajuyo ya kalleta


murmushi yasakarmata hakan yasata janye idanunta kanshi Kawai takasa cewa komai

"want some ice cream?" yafada ahankali cikin romantic voice

dagowa tayi ta kalleshi saikuma tayi saurin kauda kai ganin irin kallon dayake mata namasu jin barci

girgiza kai tayi alamun A'a

murmushi Kawai yayi bece komai ba ya bude motar yafito ya zagayo ya budemata

dagowa tayi ta kalleshi

"get down dear" yafada ahankali

qara girgiza mashi kai tayi tace
"banason ice cream..."

"get down kona fiddoki dakaina" ya katseta da hakan

tsayawa tayi tana kallonshi kamar da mammaki sai gani tayi ya sunkuyo kamar zai daukota hakan yasata saurin yin baya tana cewa

"wait.. zan..zan fito" tafada tana zaro large eyes dinta

wani qayattacen murmushi yasaki yaja baya yana cewa
"better"

ahankali ta sauko tana sissine kai cikin kunya

murmushi Kawai yasakeyi yarufe kofar sannan ya nunamata hanya alamun suje

babu musu tafara tafiya suka nufi Icecream joint din


"which flavour kikeso?" inji Aymaan yana zaro wallet dinshi

"vanilla" ta amsa ahankali

juyawa yayi kan attendant din yayi mashi bayanin abunda sukeso

babu 6ata lokaci akayimusu packaging din Icecream din da snacks acikin yar babba babbar leda aka basu Aymaan ya amsa yabiya sannan suka juya

motarsu suka koma suka shiga Aymaan ya tada motar sukabar wajen


yanzu ma a slow speed suke tafiya motar tayi shiru

ahankali Aymaan ya waigo yadan kalli zee dake wasa da yatsunta ledar siyayyarsu akan cinyarta

maida kallonshi yayi kan titi yadanyi murmushi

"you still love him right?" ta tsinci muryarshi da fadin hakan

dagowa tayi ta kalleshi saikuma ta janyesu dasauri ganin shima yajuyo xai kalleta

"hmmm, am sorry na katsemuku moment dinku nasan I shouldnt interrupt you guys, sorry" yafada yana flashing dinta da murmushi

girgiza kai zee tayi dasauri tace
"ba yadda kayi tunani bane"

"koma dai yayane be kamata kidinga ke6ewa da namiji daba muharraminki ba, batool fa saidai takoma gida ita kadai wai ta nemeki bata ganki ba gashi anata kiran wayarki bakya picking... Zainab you're matured enough dazaki banbance daidai da akasinsa, bawai cewa nake karki kulashi ba ko karku ke6e kuyi magana ba but do that in a proper way... Makaranta fa yabiyoki yakuma jaki inda babu mutane, mezamu kira wannan?"

zee da tunda yafara magana takejin zuciyarta na bugawa sosai tadago ta kalleshi da idanunta dasuka fara durar ruwa
"it's.. it's not what you think" tafada ahankali

"waya gayamiki am thinking of something? am thinking of nothing Zainab.. I trust you kuma nasan hakan ba laifinki bane.. abinda Kawai nakeso na fahimtar dake shine try to do things in proper ways ok? ina baki shawara ne amatsayina na dan uwanki kuma yaya agareki, wannan dadewar dakikayi da dawowar da batool tayi babu ke bakisan iya tashin hankalin dazai iya jefamu aciki ba.. mu family dinki ne... we care about every slight thing about you... aduk abinda zakiyi kifara sa family dinki agaba kafin wani abin... shawara ce amma" ya qarashe da murmushi a fuskarshi saidai deepdown shikadai yasan abinda yakeji

ganinsu dayayi tareda Deen ba qaramin dokarmashi zuciya yayi ba kuma haryanzu zuciyarshi bata bar hucin zafi ba Kawai daurewa yake yana iyakar qoqarinshi wajen controlling kanshi

zee da jikinta yayi sanyi sosai da magangganunshi ta sauke idanunta qasa ahankali

"am sorry" tafada ahankali

murmushi yasakeyi
"don't be, Kawai dai ki kiyaye"

"insha allah" ta amsa asanyaye

murmushi yasakeyi
"now fiddo Icecream dinki kisha kar yayi melting"

"zansha idan muka isa gida"

"no kisha yanzu, idan ba hakan ba zan maki wata fassarar"

kallonshi tayi, kamar zatayi magana saikuma tafasa ta bude ledar ta fiddo daya daga cikin robobin Icecream din ta bude tasa dan spoon din ta diba takai baki saita dago idanunta suka hada ido

murmushi yayi mata itama tadan maida mashi tana sauke idanun qasa

babu wanda yaqara magana acikinsu harsuka qarasa gida


parking yayi a parking space sannan suka fito atare


atare suka shiga cikin gidan zee agaba Aymaan abaya

murda handle din kofar tayi tashiga da sallama hannunta riqeda da ledar snacks din

ummie da batool dake falon suka dago suna amsa sallamar

qarasowa zee tayi cikin falon tana dan murmushi azuciyarta tana tunanin mezata gayawa ummie idan tace ina ta tsaya

"A'a? harkun dawo? kungama practical din" inji ummie tana kallon zee

"p..practical?"

"eh sungama.. koda najema gab da zasu gamane don ko 10mins banyiba dazuwa suka fito" inji Aymaan dashima yashigo dakin

kallon Aymaan tayi suka hada ido ya kauda kai

"ayyah, sannu" inji ummie tana maida hankalinta kan t.v tana cigaba da kallon program din datake kallo

"bari nahau sama" inji Aymaan yana wucewa zee tabishi da kallo qasa qasa

"inyee meye wannan din?" taji muryar batool data taso tadawo kusada ita nacewa hakan tana fizge ledar hannunta

hade rai zee tayi tfara qoqarin amsa hakan yasa batool miqewa tayi hanyar sama

miqewa itama tayi tabita tana saita bata ledarta

murmushi Kawai ummie tayi tana girgiza kai tacigaba da kallonta


asama kau bayan sungama guje2nsu suka zube agado kowa na maida numfashi

batool ce tajuyo tana kallon
zee dake kallon sama har lokacin tana maida numfashi

"ina kika tsaya ne zee? babu inda ban nemeki ba amma banganki ba kuma inata kiran numberki bakya picking"

juyowa itama zee tayi tana kallonta

shiru tadanyi sannan tace
"wane practical,ummie ke magana akai?"

harara batool ta gallamata
"na tambayeki kina amsamin tambaya da tambaya?"

ajiyar zuciya zee tayi tamaida kallonta sama tace
"ina tareda Deen ne"


"Deen?" batool tafada cikin mammaki

"yes"

"kamar yaya kuna tareda Deen? doing what? yaushe ma kika fara saurararshi?" inji batool tana kallonta sosai


qara sauke wata ajiyar zuciyar tayi sannan tace
"yau... yau na tsaya na saurareshi, he told me everything" tafada batareda tabar kallon sama dakin ba

"what did he told you?"

"labarin da tsayi" zee ta amsa

"to amma yafada.miki dalilin tafiyarshi?"

"yes... kaka tasa suka gudu saboda gudun kar asirinta yatonu cewar batada wata alaqa da Deen, taji ajikinta sirrinta zai bayyana shiyasa ta yanke wannan hukuncin shikuma Deen bayada option dole yabita saboda tayi threaten zata tafi ita kadai lokacin dayaso kawomata gardama, shikuma baya iya rabuwa daita kasancewar itace komai nashi, ita kadai,yabude ido yagani a duniya amatsayin danginshi shiyasa yabita suka gudun"


shiru batool tayi tunda tafara maganar harta kai aya
"that makes sense amma duk wayonta gashi sirrin ya bayyana, waya gayamata anama allah wayau?" inji batool

ajiyar zuciya zee tasake saukewa sannan ahankali tace
"kuma... kuma wai ashe yadawo 3weeks bayan tafiyarshi, can you imagine wai daddy saiya cemashi nayi aure yakuma yimishi koran kare? banta6a tunanin daddy zaiyi haka ba"

"daddyn yayi hakan?" inji batool cikin mammaki

"yes.. nima nayi mammaki sosai, meyasa daddy zaiyi hakan? koda yayi hakan ne don yarama ai bekamata yace nayi aure ba, tunda harya dawo dakanshi ai yakamata ya tsaya ya saurareshi idan ma hukunci zai yanke mashi saiya yanke mashi wanda bekai wannan tsauri ba don wannan ba Deen kadai yayimawa ba harda ni, 3weeks da tafiyarshi lokacin ina cikin halin desperation, imagine da lokacin yasanar dani dawowarshi da bansha duk wahalar danasha ba"


ajiyar zuciya batool ta sauke
"gaskiya kamar daddy be kyauta ba amma saidai bamusan dalilin dayasa yayi hakan ba.. anyway komai yawuce ai gashi yadawo kamar ba'ayi ba"

lumshe ido Kawai zee tayi batace komai ba

"yanzu wane matsayi yake agareki"

bude idanu tayi tajuyo tadan kalleta
"kamar ya?"

"ina nufin ya matsayin soyayyarku?"

"wai he want another chance"

"zaki bashi?"

shiru tadanyi saikuma tace
"I don't know"


shiru yadan ratsa dakin kafin can zee tasake katse shirun da
"wane practical ummie ke magana akai dazu?"

dan ta6e baki batool tayi tace
"well, wannan duk shirin Akhie ne, lokaci daya muka dawo dashi ganin nikadai nadawo babu ke yasashi tambayata nagayamashi komai saiyace to bari yakoma school din yaduboki wai idan nashigo aka tambayeki ince kin tsaya wani practical ne ganin zaki dade yasa kikace intaho zaki kira yaya Aymaan yadawo dake..shikenan saiya juya ko shigowa beyiba yakoma school din"


shiru zee dake kallonta tunda tafara magana tayi saikuma ta sauke ajiyar zuciya ta maida idanunta ta lumshe tunani kala kala na kai kawo a kwalwarta


***


tsaye yake agaban balcony inda yazama favorite wurinshi yana kallon harabar gidan dake tarr da haske kamar ba dare ba

mussadiq ne yashigo wajen waya kare a kunnenshi ya qaraso wurin kujeru yaja guda ya zauna yana cigaba da wayarshi yana kallon bayan Deen

saida yagama wayar sannan yadanyi murmushi yana ajiye wayar kan table

"eh gaskiya ka afka dayawa..love is suffering someone here" yafada cikin sigar tsokana

Deen beko juyoba bare ya tanka mashi

"you know what yakamata karage tunani, don taqi sauraronka saika tsangwami kanka haka? dama nasan wannan stubborn girl din bazata saukoba so easily, kabi komai ahankali komai zai warware"

juyowa Deen yayi ya 6allamashi harara
"karka qara kiranta stubborn"

yar dariya mussadiq yayi yace
"but she is.. wannan yarinyar? uhmm nikadai nasan halinta"

"baka kaini sanin halinta ba Mallam"

ta6e baki mussadiq yayi
"whatever Kawai dai nidai shawara zanbaka karage saka kanka damuwa don taqi sauraronka"

"waya gayamaka taqi saurarona? ta saurareni nakuma gayamata komai"

"wow, yaushe?"

qarasowa Deen yayi wajenshi shima yazauna kan kujera daya
"yau, I told her everything"

"wow, sai tace me?"

"bata kaiga magana ba wannan gayen yazo?"

"who?"

"wannan doctor din"

yatsine fuska mussadiq yayi saikuma yata6e baki
"that annoying fringe"

"kabar cemashi hakan"

"why? I don't like him from the beginning"

"amma yanada kirki"

"hmmm koba kirki ba"

"seriously mussadiq yakamata kabar gaba dashi saboda mutumin kirki ne, harda shifa wajen taimaka mana mukayi re-uniting ga yadda yakula da ummy lokacin datayi collapsing, the man has a good heart"

ta6e baki mussadiq yayi ya cigaba da danne dannenshi Kawai

"saidai nalura kamar yanason zee"

"fidda kamar, sonta yakeyi kuma shi taqama yake cousin dinta ne shiyasa yake wani jijji dakai yana nuna isa akanta, abinda yafi 6atamin rai gameda shi kenan" inji mussadiq

ajiyar zuciya Deen ya sauke yace
"koma menene nata zee tawace.. insha allah, insha allah zee matata ce"

"allah yasa"

"amin ya rabb"

"kunyi waya da master din naka?" inji mussadiq

"yes.. munyi magana nagayamashi komai though briefly, nasan very soon zasu duro Dubai"

"kace nakusan ganin your so called kaka" inji mussadiq yana dan ta6e baki

wani kallo deen yayimashi
"kardai kafadi wani abu akan kakata"

"to mai kaka" mussadiq yafada yana ta6e baki sannan yamaida hankalinshi kan wayar hannunshi shikuma Deen ya jingina da kujera ya harde hannayenshi a qirji yana kallon sararin samaniya....✍�


Ummin fasihu🧚🏻‍♀�
8/7/21, 4:46 PM - Buhainat😝: *🙍🏻‍♂️DEEN🙍🏻‍♂�*


*096*


*NIGERIA*


Sosai Alhaji Shamsu ke mammakin wannan al'amari

kiran wayar Deen ba qaramin sashi a rud'ani yayi ba, ga wasu magangganu daya gayamashi masu birkita kwalwa


dukda sama sama Deen yabashi labarin kasancewar labarin bana waya bane amma yagane abinda Deen keson gayamashi

idan ba kunnuwanshi suka ji ba daidaiba yana nufin yahadu dawasu dayake ikirarin familynshi ne

tayaya hakan zaya faru bayan tunfarko yabashi labarinshi inda yacemashi bayada sai kaka kuma shi bahaushe ne, ya kwatsam kuma zaice yahadu dawasu kuma family dinshi ne? kuma bama a qasarnan ba a Dubai?


sosai kan Alhajin ya kulle yakasa samun amsoshin tambayoyin daketa kai kawo a kwalwarshi


kenan Deen nacikin qoshin lafiya duk kwanakinnan? fadin tashin hankalin dasuka shiga a yan kwanakinnan 6ata bakine don kowa hankalinshi atashe yake dajin su Deen shiru musanmman kaka dahar wata rama tayi saboda tashin hankali da damuwa


tunawa yayi da maganar Deen nacewa don allah yasama musu visa sutaho harda kaka Dubai akwai qullallen al'amarin da dole kaka zata iya warwarewa


dama kuma Alhajin yayi niyyar zuwa Dubai din duk saboda jinshi shiru da akayi don harya gama komai na tafiyarshi inda zaibi jirgin dazai tashi jibi

tattaunawarsu da Deen yasashi fara cuku cukun nema masu kakan visa suma inda tafiyar zata hada dashi da hajiya da kaka sai subar su Lailah da Afrah gidan qanin Alhajin

koda labari yaje ga Lailah na tafiyar tasu saita burkuce ta dinga kuka ita don allah aje daita

sosai ta tada hankalinta akan hakan don dama bayan kaka babu wanda yakaita shiga damuwar rashin Deen don kusan kodayaushe cikin kuka take duk tayi fayau daita don damuwa


izuwa yanzu su mamy duksun gano son Deen take hakan yasa take basu tausayi

ganin cewa idan ba'a tafi daita dinba zata qara shiga damuwa yasa Alhajin hadawa daita a tafiyar gashi dama anci sa'a suna cikin hutun Makaranta

nan da nan Alhajin yayi cuku cukun tafiyarsu inda adaren ranar tafiyar yagama settling komai inda Washegari zasubi jirgin qarfe goman safe mai zuwa Dubai


ranar ko barcin kirki kaka kasayi tayi, dukda Alhajin be gayamata sunyi magana da Deen ba don ita gani take Alhajin ya yarda ne sutafi nemanshi tare don tunfarko dama tanace zata bishi Alhajin ne be yarda ba

haka takusan kwanan zaune zuciyarta fall addu'ar bayyanar Deen, danasanin barinshi wannan tafiyar kau tayishi yafi cikin kwando


Washegari tunda safe suka fara shirye shiryen tafiya don jirgin nasu dawuri zai tashi

qarfe tara tayimasu cikin airport inda cikin qanqanin lokaci suka gama settling komai qarfe goma nayi dota jirginsu ya lula sararin samaniya yadauki hanyar dubai


***


ahankali Aymaan ke jujjuya dan qaramin puzzle box din hannunshi yana arranging din puzzle din, daya kumayi arranging dinsu sai yayi scattering dinsu saikuma yasake arranging dinsu


dagowa Ahmad yayi karo na ba adadi ya kalleshi saikuma yadan girgiza kai


"Aymaan"


dan dakatar da abinda yakeyi yayi batareda ya dago ya kalleshi ba kuma bece komai ba


gyara zama Ahmad yayi yana kallonshi sosai

"Aymaan wai meke damunka ne kwanannan? yaushe muka fara 6oyewa juna damuwar juna? Aymaan you're not ok these days kuma you don't want to share your problem with anyone, aganinka barin damuwa aranka shine mafita?" yafada yana kallon Aymaan daya cigaba da jujjuya abin hannunshi kamar badashi yake ba


ganin beda niyyar amsa mashi kuma baxai amsa mashin ba yasa ya yunkura yaqwace puzzle box din daga hannunshi yana cewa
"am talking to you idiot!"


komawa jikin cushion din Kawai Aymaan yayi ya lumshe ido yana sauke nannauyan numfashi

"Aymaan... listen Aymaan barin kashi aciki baya maganin yunwa, kana cikin damuwa why not kayi sharing dinta dani? ko babu komai zakaji sauqi na kayi sharing din damuwarka dawani kuma ina iya samamana shawara dazata taimaka, ba haka muke dakai ba kaima kasani we're like brothers muna sharing damuwarmu mukuma zauna mu samama kanmu mafita atare, banajin dadin ganinka a wannan yanayin kwata2" yafada cikin kwantar da murya yana kallon Aymaan da har lokacin idanunshi ke a lumshe

"Ka gayamin damuwarka please, I can help"


"you can't help" Aymaan yafada ahankali still idanunshi a lumshe

"meyasa? just tell me, we can't say" inji Ahmad

sai a lokacin Aymaan yabude idanunshi wadanda suka kada sosai ya kalli Ahmad

"you can't Ahmad, baxaka iya taimakamin ahalin danake ciki ba, I... am broken" yaqarashe cikin raunin murya

ganin hakan yasa Ahmad saurin dawowa kusadashi yana kama hannunshi daya

"meyasa nafara son abinda tunfarko ba nawa bane? why? meyasa nafara son wacce bazata ta6a mayarmin da so ba? why?"


"Aymaan..."


"kasan ciwon dake tattare dason wanda baya sonka kuma baxai ta6a sonka ba? kasan zafin dake tattare da ganin wanda kakeso yana son wani? ni haka tawa qaddarar so zatazomin? ada soyayya stuffs duk shirme na daukesu ina ganin Kawai rashin aikin yine amma jibeni yanzu.. crying over love while wacce nakeyi domin ta ma batasan inayi ba, what did i do to deserve this Ahmad? meye narasa na d'a namiji da xaisa bazata soni ba nima? meye Deen yafini? me Deen yafini dashi? meyasa ko sau dayane bazata waiwayeni ba? at least tanuna tasan inayi, tanuna tasan dani, what did I do to deserve all these pain?"


sosai hankalin Ahmad yatashi ganin yadda Aymaan ke hawaye sosai, kana kallonshi zakasan he's really in pain

"Aymaan please... kabar kukan nan haba kamar ba namiji ba"

"tears are not sign of weakness, but of courage. hiding your emotions is self destructive and will never allow you to heal... haka Zainab ta ta6a gayamin kuma yanzu nagane hakan, babu abinda kecikin maganarta sai gaskiya, my heart is hurting ahmad, it's hurting terribly" yafada wasu hawayen nasake saukomashi


Ahmad da jikinshi yayi sanyi sosai yajawo Aymaan jikinshi cikin sigar rarrashi yana cewa
"Aymaan ba kome mutum keso yake zama alhairi agareshi, wani abin kanasonshi amma ba alhairi bane agareka shiyasa allah ke hanaka, allah shine mafi sanin daidai kuma ya tsara komai na rayuwarmu da dadewa, kayi hqr Aymaan kadage da addu'a, idan zee ce mafi alhairi agareka allah ya karkato da hankalinta kanka idan ba ita bace allah yaxa6a maka mafi alhairi, ka daina ganin laifin Deen ko zee, kadage da addu'a Kawai, wani baya ta6a auran matar wani"


haka Ahmad yayita kwantarma Aymaan hankali da kalaman rarrashi harsaida Aymaan yaji sassaucin zugin da zuciyarshi kemashi


***


A babban filin jirgin garin Abu dhabi jirginsu yasauka inda cikin qanqanin lokaci pasinjojin jirgin suka shiga saukowa daga jirgin


can na hango su Alhaji Shamsu cikin masu saukowa tareda su kaka suna saukowa suma

cikin qanqanin lokaci suka sauko sukayi clearing komai suka amshi kayansu

dukda damuwar dasuke ciki hakan be hanasu ganin haduwar qasar ba wacce tahada jinsin mutane qabilu daban daban


ahankali suke takawa suna nufar hanyar barin airport din dake dauke da mutane sosai sai kai komo suke

kaka sai bin mutane masu wucewa take da kallo kamar don ganin ko zataga mai fuskar Deen, duk tawani yi yaushi kamar ba itama

fitowa sukayi daga entrance din airport din inda adaidai lokacin idanun Lailah suka sauka akanshi


still tayi da numfashinta tana sake wara ido tana kallonshi sannan tasake kyafkyafta idanunta cikin son gasgata abinda tagani

hannun kaka dake gefenta ta damqe cikin sauri tana cewa
"gashi can kaka, ga yaya balaraben can kalla kigani!" tafada da qarfi tana nuna Deen din dake tsaye jikin budaddiyar kofar motarshi yana kallonsu tacikin baqin shade din idanunshi

bata tsaya bi takan kaka data sandare atsaye ba tayi wurinshi aguje tana kwala kiran sunanshi cikin kuka

tana zuwa batayi wata wata ba tafada jikinshi tana kuka sosai

qamewa yayi a tsayen dayake don ita kanta Lailah saida taji sanda ya dauke numfashi don be ta6a expecting hakan ba, hakan yasa itama saurin dawowa hayyacinta ta sakeshi tana dan ja baya

"y..yaya, am sorry amma nakasa yarda kaine" tafada muryarta nadan rawa saikuma tajuya ta kalli su Abba dake can tsaye basu qaraso ba sannan tajuyo ta kalli Deen dahar lokacin beyi motsi ba

"yaya kalli kaka.. ga kaka can, tareda ita mukazo.. kullum saitayi kuka saboda rashinka zoka gani" tafada tana jan hannunshi suka qarasa gabansu kaka Deen nabinta kamar sakarai

"kaka ga yaya! kingani ko dama nace yana lafiya" tafada cikin tsananin murna batama lura da tashin hankalin dake fuskokinsu Abba ba


"kaka..." taji anfada ahankali cikin raunin murya

juyawa Lailah tayi ta kalli Deen din kusada ita don tabbas muryarshi taji amma kamar ba daga kusada ita ba gashi Deen din akusada ita yake

kallon Deen din da Kamar bashi yayi maganar ba tayi kafin tace komai taji ansake cewa
"kakata"


still tayi jin muryar abayanta gakuma Deen agabanta da baiko motsa bakinshi ba

wara idanu tayi gabanta na faduwa hakan yasa mussadiq dake gabanta dan sakin murmushinnan nashi nagefen baki yana kallonta tacikin glass din idanunshi

saurin juyawa tayi daidai lokacin da Deen na ainahin ya rungume kaka dake tsaye kamar an dasata yana qara kiran sunanta yanajin wani irin kewarta na tasomashi daga qasan zuciya kamar sunyi shekaru basu hadu ba

sosai Lailah ta girgiza ganin Deen biyu agabanta, bama ita kadai ba kowama na wajen saida ya girgiza don ko Alhajin Deen be gayamashi batun twin dinshi ba


hakan yasa duk sukayi still kamar wanda aka dasa suna binsu da kallo inshock sunma kasa magana

Habeeb dake tareda su Deen murmushi Kawai yakeyi don yasan za'a rina, that's the same shock he recieve lokacin dayaga Deen da mussadiq at the same time

"kaka nayi kewarki.. nayi kewarki kakata" inji Deen yana cupping fuskar kaka data qurawa mussadiq din bayan Deen idanubabu kyaftawa

"ky..kyakyawana.. k..kalli bayanka, nashiga uku.. kalli bayanka" tafada cikin rawar murya tana riqe hannayen Deen dake fuskarta gamm idanunta har lokacin akan mussadiq

juyawa deen yayi yakalli mussadiq saikuma yajuyo ya kalli kaka yana murmushi

"eh nagani kaka"

"w...wani ne mai kama dakai" tafada har lokacin muryarta na rawa

"eh kaka dan uwana ne" yafada ahankali yana murmushi

"d..dan uwanka?"

"kaka muje gida muzauna saina fadamaku komai.. karki damu kinji?"

itadai batace komai ba sai riqe hannunshi datayi gamm tana kallon mussadiq kamar a tsorace, jikinta sai rawa rawa.yake

sai a lokacin yajuya kansu Abba da Habeeb ke gefensu yanata murmushi ya tsugunna yana gaidasu suka amsa suna kallonshi saikuma su kalli mussadiq wanda hakan yasa shima mussadiq qarasowa ya cire glass din idanunshi yana yimasu sallama

duk amsawa sukayi dakyar suna kallonshi don dukkansu arude suke they can't understand what's going on

ganin dai haryanzu kamar suna cikin shock yasa Deen yimasu iso zuwa mota wanda girmanta yasa zata iya kwashesu tsaf

duk wucewa sukayi wurin motar Habeeb na budemasu duk suka shiga

"Lailah come and get in" inji Deen ganin taqi motsawa a inda take

saida ta kalli Deen sannan ta kalli mussadiq daya daga gira daya yana mata wani kallon qasa qasa hakan yasata saurin kauda kai tawuce tanajin kamar zata harde kafaffu

duk shishiga sukayi cikin motar inda mussadiq yashiga mazaunin driver yatada suka fice daga wajen


------


A gidansu mussadiq suka taka sauka


tunda akafara tafiyar babu mai magana acikinsu kowa tunanin dake zuciyarshi ya isheshi


jin motar ta tsaya ankuma bubbude kofofi yasa suka fara yunkurawa suna saukowa


kowannensu sake wara idanu yayi yana kallon kantamemen gidan da aka kawosu

sai bin koina da kallo suke cikin mammaki kansu na dad'a kullewa

"Abba bismillah mushiga daga ciki" inji Deen da farinciki yakasa 6oyuwa a fuskarshi, he was just extra happy na ganin kaka ayau, jiyake kamar ya goyata don murna, he can't wait ya gwadama kaka umminshi datake yawan gayamashi tarasu


kasancewar daidai entrance motar takawosu yasa basusha wahalar fallo hanya don ba laifi ko daga parking space akwai tafiya kafin azo entrance


bisa jagorancin Deen da fuskarshi ke washe kamar gonar auduga suka shiga entrance din yabude masu kofar yashiga yana musu iso

sudai binshi Kawai suke babu mai iya magana saboda yadda kansu yayi mugun qullewa


wani katafaren qayattacen falo suka tsinci kansu aciki wanda tunda suke basu ta6a ganin mai irin haduwarshi ba

daga can cikin falon suka hango wata mata fara qall mai mugun kama dasu Deen tayi shigarta cikin shigar larabawa daya qara fiddo kwarjininta da haiba

"ummie! ummie! gasu Abba! ga kakata!" inji Deen cikin dan larabcin dayake ji yana jayeda hannun kaka da tunda taga ummie jikinta yadau rawa sosai

ummie datun shigowarsu tamiqe ta karaso gabansu cikin murna da fara'a tana masu lale marhabin cikin harshen larabci Aysha kuma na wucewa wurin kaka da Deen ke riqeda hannunta har lokacin tana kallonta fuskarta fall murmushi


iso ummie keta yimasutana cewa su zazzauna inda dakyar mutanen suka iya yin yadda tace don banda kallonta babu abinda sukeyi kamar sunsamu t.v


kan kace me? maids sunfara kai kawo inda cikin qanqanin lokaci aka cikamasu gaba da abubbuwa iri iri


babu wanda ya iya ta6a komai aciki dukkansu sai kallon ummie da Aysha daketa qara yimasu marhabin suke kansu na qara mugun kullewa

Gaisawa suka farayi inda duk cikinsu Abba ne mai dan tauri taurin dayake amsawa lafiya lau, hajiya kaka kau jikinta banda rawa babu abinda yakeyi

nan ummie take tambayarsu sunzo lafiya? duk suka amsa cikin qarfin halil banda kak da ha lokacin bata dawo nutsuwarta ba


Aysha ummie ta kalla tace taje ta gwadama su mamy da kaka masaukinsu su huta sai tawuce da Lailah dakinta shikuma Deen yakaisu Abba suma masauki

haka kau akayi, Deen yawuce dasu Abba Aysha tawuce dasu mamy da har lokacin zuciyarsu cinkushe take da tambayoyi kala kala


adakin da Deen yakai Abba Abba yahau fadan wai duk meke faruwa ne, yazai kawosu wuri without any explanation yasa sukoma kamar wasu sakarkaru


ganin kamar Abba yadan hau yasa Deen yashiga bashi haquri yana cewa ai zaiyi musu bayani

"waye wancan matar balarabe? kaga yadda.kuke kama kuwa?"

murmushi Deen yayi
"Abba ummie na ce"

"umminka? ba cewa kayi umminka da abbanka basa raye ba?"

"nima haka nayi tunani amma a wannan tafiyar allah ya bayyana minsu, allah ya hadani da ainahin family dina"

cikin mammaki sosai Abba yace
"yanzu dagaske wannan ce ta haifeka? but how come? ya akayi kaka tace bakada iyaye? wacece kaka?"

"wannan amsar kaka ce Kawai zata iya badata, itace Kawai zata warware mana komai"

"hasbunallahu wani'imal waqeel, allah mai iko, wannan fa me kama dakai din?"

murmushi Deen yayi
"he's my twin brother"

"you're a twin?" inji Abba cikin tsantsar mammaki

murmushi Deen yayi yana kadamashi kai


sosai Alhaji Shamsu yaita mammakin wannan al'amari inda abin yaqara kullemashi kai, miliyoyin tambayoyine ke kai kawo akanshi amma shima yasan babu mai bada amsarsu sai kaka


ahaka Deen yafita yakoma bangaren da aka sauke su kaka inda yaje ya tadda kaka nata kuka kamar ranta zai fita su mamy suna zagayeta suna rarrashi amma taqi shiru

cikin tashin hankali Deen ya qarasa wajensu yana tambayar kaka lafiya

ganin Deen yasa kaka tashi tafada jikin Deen da qarfi ta rungumeshi qaqam kamar za'a kwacemata shi tacigaba da kuka sosai

sosai Deen yarude jin irin kukan datakeyi hakan yasa yahau rarrashinta shima kamar zaiyi kukan

"ka gafarceni Kamal, ka gafarceni" tafada cikin kuka sosai


"kaka don allah kibar wannan kukan, don allah kibari"


"dole nayi kuka Deen dolene nayi, na rabaka da kowa naka na tsawon shekaru, naita guje guje duk don kar arabamu dakai ashe dai zamu rabu din, nayimaka qaryar komai ma, nasa kayi tunanin bakada kowa gashi duk dubarata da wayau na yau sirrina ya tonu, Ka gafarceni Deen don allah"

"kaka don allah kiyi shiru kibar fadin haka, ni haryanzu kece komai tawa kuma babu mai rabamu insha allah"

"wlh nasan rabamu zasuyi Kamal, shikenan baxan qara ganinka ba, shikenan narasa Ka dama kai kadai nake gani naji dadi, kai kadai nake iya kira nawa, shikenan banida kowa kuma"

haka kaka tadinga kuka tana surutai wanda dole tabaka tausayi gashi taqi sakin Deen don gani take rabasu za'ayi

kowa na dakin saida jikinshi yayi sanyi Aysha kau dabatasan me suke cewa ba saboda hausar dasuke sai kallonsu take tana hawaye don sosai tsohuwar tabata tausayi


dakyar Deen yasamu ya rarrashi kaka har tadan kwantar da hankalinta inda yasa Aysha ta hadamasu ruwan wanka sudanyi freshen up


dakyar kaka tabar Deen yafita daga dakin mamy na cigaba da kwantar ma kaka hankali


*RANAR WANKA....*


Zaune suke a babban falon kowa idanunshi akan kaka dake hawaye har lokacin


qarewa yan falon kallo nayi naga hardasu mummy da daddy da ummy da abbu agefe daya kuma babban Ahmad da ummanshi duk zazzaune akan kujerun falon


aqasa kan carpet kuma zee ce Zaune jikin qafaffun ummy sai batool akusada ita sai Aysha sai Lailah adayan bangaren kuma Deen ne kusada kafar kaka dake kan kujera itama sai mussadiq kusadashi sai Habeeb sai Ahmad daga qarshe kuma Aymaan


kowannensu kansu aqasa suna sauraron kaka da dakyar ta iya bude bakinta tafara magana....✍�


Ummin fasihu🧚🏻‍♀�
8/10/21, 8:09 AM - Buhainat😝: *🙍🏻‍♂️DEEN🙍🏻‍♂�*


*097*


*WAIWAYE*


"Asalin sunana Asma'u Mamman, ni marainiyace banida uwa banida uba don agidan marayu natashi na tsinci kaina a garin komasi dake qasar ghana.


Acikin gidan marayu natashi kamar sauran yan uwana marayu damuke rayuwa a cikin gidan

baza'a kira rayuwarmu da ingantacciyar rayuwa ba don gaskiya bama samun kulawa yadda ya kamata, abinci ma kanshi bama samun ingantacce saidai kame2


ga rashin ilimi daga na bokon har na arabi bama samu (gwara gwara na arabin tunda munsan wasu abubbuwan kamar yadda akeyin sallah da yan gajerun surori) ga rashin suturun kirki


gidan marayun kasancewar anyi yawa sosai aciki yasa babu kulawa sosai gashi da dan tallafin da gomnati ke badawa duk wata aka dogara saidai idan allah ya taimakemu yajefo mana taimako daga ire iren mutane masu sadaka dasuke tunawa da yara marayu irinmu


zama gidan marayunmu zama ne marar dadi don kowa burinshi allah ya rabashi da gidan ko ta hanyar adoption (daukar yara don rainonsu) kokuma aikatau

don har taya wadanda xasu bar gidan murna mukeyi munaji dama mu


Haka nataso nima kamar sauran yaran babu ilimin arabi ba na boko sai qwarewa a iya aikace aikace da rainon yara don yawanci marayun dasuka tasa suke komawa masu kula da qanannu qanannun cikinsu


haka muka tashi cikin wata irin rayuwa marar alqibla, kullum a aiki da raino muke qarewa bamu fita daga gidan ko nan da wajen gidan, duk wanda kaga ta fita to ko ansamu masu daukarta ne ko tasamu aikin aikatau kokuma tayi aure don babu laifi akwai masu zuwa neman aurenmu agidan wani lokacin kuma marayu yan uwanmu maza ke auranmu


haka natashi agidan kullum inama kaina fatan fita daga gidan watarana nima nasamu ingantacciyar rayuwa koyaya ne

rayuwa awajen gidan na matuqar bani sha'awa musanmman idan ina ganin mutanen dakan shigo gidan marayun namu don daukarmu sai inji sunbani sha'awa ina kuma qara jin kwadayin son fita daga gidan inason jin yadda wajen yake


saboda kwadayin son fita daga gidan yasa duk lokacin da akazo dauka har addu'a nake aza6eni nima, bandamu ba ko aikatau xanje inyi burina Kawai nafita daga gidan

duk lokacin da akazo akayi dauka ba'a daukeni ba kwana nakeyi kuka bama ni kadai ba harda wasu acikinmu saboda yadda zaman gidan ya ishemu, burinmu Kawai mufita aganinmu rayuwarmu awaje saitafi tacikin gidan inganci


ahaka harna girma naxama budurwa, ina shekara 20 wani mutum yazo neman aure na agidan


da gudun tsiya na amince dashi batareda duba yanayin shekarunshi ba don babbane sosai don a haife ya haifeni gashi yanada mata biyu da 'ya'ya kusan goma sha

ban damu da duk wannan ba alokacin na amince nan da nan aka daura aurenmu bayan anyi dan bincike dasukeyi na sanin mazaunin mutum da sana'arshi inda aka gano sana'arshi qera tukane na qasa da tulu dadai sauran kayan qerawa na qasa


bayan daurin aurenmu aka damqani ahannun mijina daga ni sai yan kayana sai dan ihsani da manyan gidan suka hadamin wanda betaka kara ya karya ba nabi mijina bakina har kunne don tsabar murna muka bar gidan da tun haihuwata banta6a fitowa ba


abin hawa muka hau dani da mijina har gidanshi wanda yakasance na qasa ne duk ya tsufa ya zaizaye

gidan zagaye yake da yar gajeriyar katanga ta qasa inda idan kashiga ciki saika fara cinkaro da wani washeshen fili mai girma sosai inda daga nesa xaga hangi yan qanannu qanannun dakunnan dake gidan


dakuna hudu ne gidan masu yan qanannun taga (window) daga can sama

daki nafarko na maigidan ne sai biyu na kowanne matarshi daya kuma na yara inda na qarshen wanda da alamu saida akayimashi kwaskwarima saboda qamshin sabon shafen qasan dayakeyi nawane ni amarya

babu kitchen gidan don a tsakar filin gidan suke girki sai makewayi dake daga can qarshen gidan.


ahaka nashiga gidan ina kalle kalle inda yarane sosai tsakar gidan duk yan kuya kuya kusan duk kai daya kowa na,binmu da na mujiya, daga tagar dakunnan matan gidan kuma ina iya hango kawunnan mutane ana leqomu

ahaka muka shiga dakina wanda yasha gyara ga tabarmi anbaza takoina sai dan tulu dake daga can kusurwar dakin

ataqaice nan yazama dakina kuma ranar nazama cikkakiyar mace ta hanyar raya sunnar aure da mukayi da mijina


da farko farkon zamana gidan komai na tafiya min lafiya lau don sosai.mijina kesona don yamafi fifitani akan kingin matan

baya yarda inyi wahala don ko girkin gidan da sai andora qatuwar tukunya baya bari nayi kullum abinci na shi ke kawomin wanda duk yawanci kayan dadi ne

hakan yaqara sani jindadin auren don ina samun kulawa sosai fiyeda wanda nake samu agidan marayunmu hakan yasa kan kace me nayi 6ul 6ul naqara kyau


haka naita rayuwa mai dadi agidan mijina inda nalura kamar mijina bayason kingin matanshi saboda yadda baya shiga harkansu don becika shiga dakunnansu ba kuma maganar arziqi bata hadasu kullum sai fada ga yaranshi suma banga yana wani kula dasuba don suma rayuwarsu suke kara zube


ina mammakin abubbuwan dake faruwa agidan dakuma yadda yake watsar da sauran iyalenshi saidai ganin ni bayamin haka yasa Kawai nashare na cigaba da more rayuwata


acikin wata na hudu dayin aurenmu nasamu ciki

inda sai anan nagane waye ainahin mijina

tun lokacin dayaji batun cikina ya chanzamin kwata2 inda yafara tsiromin da wulaqanci iri iri inda tun bangane dalilin hakan ba harna gane ashe haihuwace bayaso

lokacin nasha wahala sosai saboda cikin yazomin irin mai shegen laulayinnan ne gashi mijina yajuyamin baya abinci kanshi yabar bani sai alokacin nagane ashe matan gidan suke ciyar da kansu ma

gashi matan gidan dama duk haushina sukeji saboda yadda mijinmu ke nuna kulawa agareni abaya hakan yasa alokacin babu mai tausayamin saima allah qara dasuke yimin da qannanun habaice habaice


ahaka naita kashe yan kudadden hannuna a lokacin inasamu inci abinci don ko shekara zanyi banci abinci ba babu wanda zai damu da hakan agidan

haka naita wahala ga laulayi ga rashin kula har na qulla wata biyu sai alokacin na yanke shawarar fara sana'a ganin idan nazauna hakanan yunwa zata kasheni ne abanza gashi duk na cinye yan kudaddena

ahaka nafara aikin wankau dukda yadda banida lafiya haka nake daurewa nayi wanki don samun abinda zansaka aciki

ahaka har cikina yayi wata biyar inda lokacin muka wayi gari mukaga ana tada daki daya a gidan

cikin qanqanin lokaci aka gama ginin yaji shafen qasa kamar nawa inda sai anan nakejin labarin ashe aure zaiyi


naji baqinciki sosai a lokacin don sai a lokacin nakejin ashe mutum ne shi daya saba da aure2

cikin sati biyu aka daura aurenshi dawata ta tare inda itama yakoma yimata duk abubbuwa na kyautata dayake yimin abaya

ahaka naita rainon cikina nikadai yau fari gobe baqi inda har lokacin babu wani jituwa atsakaninmu da matan gidan don kowaharkar gabanta takeyi, kowa kanshi yasani da 'yayanshi

ahaka naita rainon cikina da tun kafin na haifeshi allah ya dasamin qaunarshi sosai a zuciyata don koyaya nake cikin baqinciki na dan cikina ya motsa sainaji sauqi sauqi, kullum burina na haifeshi lafiya nima inga wanda zan kira nawa

cikina na shiga wata takwas mijinmu ya6ata da amaryarshi kasancewar itama ta dauki ciki

wulaqanci yafara mata itama kala kala hardamu ma yana cewa bamu iya komai ba sai haihuwa

ahaka ya watsar daita itama tafara dandana abinda muke dandanawa

ana hakan watarana yashigo dakina daya rabu dazuwa don har saida nayi mammakin ganinshi don rabonda yashigo dakina tun ina amarya

ashe shigowar ma bata alhairi bace don yana shigowa babu cass bare ass ya sakeni saki irinna jahilci wato uku gabadaya yakuma ce na tattara nafitarmashi agida aure zai qara


sosai naji ciwon abin sosai don abin nashi babu ko tausayawa, ga tsohon ciki ga saki sakin ma na wulaqanci

ahaka nabaro gidan bayan kwana biyu saboda budemin wutar dayayi na nabarmashi gidanshi

sanin babu inda zani don babu wanda nasani yasa ban zarce koina ba sai gidan marayunmu

koda naje nafadama manyan wajen yadda komai yafaru sai Kawai suka bani hqr don dama sunsaba irin wannan case din don yawanci ana sako wadanda sukai aure sukuma dawo gidan marayun su cigaba da rayuwa

haka nakoma cikin gidan da rayuwa har lokacin da allah ya saukeni na haihu lafiya inda na haifi d'a namiji saidai ko kwana beyiba yakoma


sosai naji rashin d'ana don na kwallafa rai akanshi sosai kuma inasonshi sosai tunma kafin na haifeshi

hakan yasa har ciwo saida na kwanta kafin daga baya na hqr na cigaba da rayuwata dukda har lokacin d'ana na maqale a zuciyata


haka na cigaba da rayuwa a gidan har tsawon shekaru takwas inda ana tara nasamu wata tazo daukar yan aikatau aka hada dani

matar munsanta sosai don tana yawan zuwa dibar yara agidan inda take rarrabawa aikatau kamar dai wata dillaliyace ta masu kudi mai kaimasu yan aiki

kasancewar angaji dani a gidan yasa aka hada dani dukda na girma don lokacin shekaruna talatin aka samu akatafi dani don dama yawanci abinda yasa suke badamu aikatau don susamu sauqin yawanmu ne don bawani iya riqemu sukeyi ba

nima dai naji dadin daukata da akayi agidan don nima nagaji da zaman gidan

ahaka aka tafi damu inda aka rarrabamu wa masu kudi inda ni dawasu guda biyar ne za'a tura saudiya aikatau don matar har qasashe take tutturawa mutane yan aiki


sosai naji dadi jin zanbar qasar gabadaya naje qasar da kullum nake burin ganinta koda a mafarki ne hakan yasa naita doqin tafiyar don har hangoni nakeyi acan ina shiga da fita da cud'anya cikin larabawa


cikin qanqanin lokaci akayimana shirye shiryen tafiyar inda mukabi jirgin ruwa (6arauniyar hanya) har muka samu muka shiga qasar


tunda nake ban ta6a ganin haddaden waje mai kyawun gaske irin na qasar. haka aka tafi damu munata zuba qauyanci har muka isa masaukinmu

anan muka kwana Washegari kuma aka rarrabamu a gidajen dazamuyi aiki

ni gidan wani attajiri aka kaini don kai koda ganin gidan kasan gidan masu dashi ne saboda haduwa, anan aka hadamu nida wadansu da suma aka kawo aikatau da matar gidan mai tsananin wulaqanci

kwata2 mutan gidan basa qaunar baqar fata don afili suke nuna qyamarmu ahaka aka rarrabawa kowa aikinshi dakuma fadamana kudin albashinmu

rayuwa agidan amatsayin yar aiki rayuwace ta wahala da qasqanci don kwata2 basa qaunarmu kamar ma ba kallon mutane suke mana ba don kuskure kadan idan kayi saika yabawa aya zaqinta

ahaka muke wannan qasqanttaciyar rayuwar wanda saida na gwammaci zamana a qasarmu akanta don abin nasu ba iya kyama da hantara ya tsaya ba, abin haryakai harda cin mutuncinmu na 'ya mace inda mazajensu keyimana kallon dabbobin dazasu iya zuwa sujuye qazanttaciyar buqatarsu akai suyi tafiyarsu


hakan dana gani yasa hankalina tashi ainun don abin abin tashin hankaline inda nan take nafara danasanin zuwana qasar


haka naita lalla6awa kullum cikin roqon allah ya kareni daga sharrin mutanen don naga yadda sukeyima kingin yan uwana masu aiki inda suke maidasu kamar karuwansu idan kuma baki yarda ba a laqamaki wani sharrin da za'ayi miki hukuncin dazakiji inama tunfarko kin yarda da buqatunsu (hakan nafaruwa a real wlh, mutane yan Africa masu zuwa wasu qasashen don aikatau dadai sauransu ba qaramin tashin hankali suke fuskanta ba acan saboda tsananin qabilanci da ake nunawa acan inda yawanci ake maidasu sex machine don yawanci sunfison Africans don acewarsu sunfi satisfying dinsu, allah ya kyauta)

ahaka nayi wata uku agidan ina kaff kaff dakaina ina addu'ar allah ya ku6utar dani saidai ba'a dauki lokaci ba wani d'an gidan yafara kawomun hari

sosai hankalina yatashi da ganin hakan, hakan yasa naita kakaucemashi ina addu'ar allah ya ku6utar dani daga sharrinshi

alokacin sosai zaman qasar ya gundureni don da nasan yadda za'ayi nagudu danayi gashi wacce takawomu tun ranar data kawomu bansake sata a idoba

ahaka har watarana saurayin yaso raping dina

lokacin babu kowa gidan don saida yayi yan dabarunshi na yadda zaisameni yaci karenshi babu babbaka


ranar naga tashin hankali don da tsiya yaso afkamin saidai allah yabani ikon makeshi da vase din tangarau mai nauyi akai inda nan take ya silale yasume jini nabin kanshi

ganin hakan yasa na rude don nasan shikenan tawa,ta qare don muddin akadawo aka taddamu haka shikenan nagama shaqar numfashi

hakan yasani fitowa agigice don ni duk tunanina mutuwa yayi, cikin sa'a kau ban tadda mai gadi a gate ba hakan yasa na afka waje nafara gudu irin gudun fanfalaki burina Kawai intsira da rayuwata


haka naita gudu shiga nan fita can batareda nasan inda na nufaba, kuka kau tun inayi harna kasa saboda muryata databar fita ahaka dare yayimin nasamu qarqashin wata gada na ra6a saboda yan kame dake kame da daddare na raku6e ina kyarmar sanyi ina addu'ar allah ya kawomin dauki


ahaka har dare yayi sosai koina yadauki shiru, motoci nawucewa jefi jefi asaman gadar dana 6uya

ahaka tun ban iya barci saboda sanyi da cizon sauro har wani barci marar dadi ya figeni

can cikin barci naji motsi sama2

abinka da dama atsorace nake sainayi firgigit na tashi ina zare idanu

ganin yadda hasken fitilu keta walainiya awajen yasani qara la6ewa ajikin bangon gadar ina toshe bakina don duk tunanina mutanen gidan danake aiki suka biyoni suna nemana kokuma yan kame

daga saman gadar suke haskowa da fitilarsu mai mugun haske kamar masu neman wani abu

nidai qamewa nayi wuri guda inata hawaye ina kyarma

bayan kusan minti daya da haske hasken naji qarar abu tsindum sunjefo cikin ruwan gadar dake gudana yana tafiya

atsorace nasake maqalewa ajikin bangon gadar ina qara toshe baki don atunanina su suka duro ciki

can sainaga nabar ganin hasken can kuma naji tashin mota tasaman gadar aka tafi

dukda antafi hakan besa na iya komawa barcin ba haka naita zaxzare ido cikin duhu ina kyarma saboda sanyin da akeyi gashi ina qarqashin gada

ahaka har haske hasken alfijir yafara ketowa inda anan na yanke shawarar barin wajen don nagaji da cizon da,sauro keyimin hakan yasa na lalla6a ina qoqarin fita daga gadar

kamar ance in kalli gabana saina hangi wani box mai dan girma daga nesa da inda nake

kasancewar akwai tazara,da inda nake yasa nakasa hango ko menene sosai

harzan wuce saina tuna da mutanen dasuka zo jiya suka jefo abu acikin gadar hakan yasa naji inason ganin koma menene


ahankali nake bin gefe gefen gadar ina tattaka dutsinan ciki gudun karna afka cikin ruwan

ahaka harna iso wurin kwalin daya jiqe jagab shima don dutsi ya tokareshi ne da,tuni yabi ruwa

tsayawa nayi ina kallon kwalin cikin dan hasken safiya daya farayi ina saqe saqe

zuciyata nabani qila sharace aciki suka jefar saidai kuma dukda hakan sainaji inason budewa inga me keciki


ahankali nasa hannuna dake kyarma kyarmar sanyin danake ji nabude kwalin inda ganin abinda yake ciki yasa numfashina daukewa cakk na wucin gadi


wani farin yaro nagani aciki hannayenshi da qafaffunshi a quqqule da igiyoyi bakinshi toshe da tsumma an daureshi tamau idanunshi alumshe babu alamun numfashi ko kadan attatare dashi....✍�


*manage banida charge, qila gobe inyi*


Ummin fasihu🧚🏻‍♀�
8/11/21, 2:03 AM - Buhainat😝: *🙍🏻‍♂️DEEN🙍🏻‍♂�*


*cigaban 097*


ja baya nayi amugun tsorace don ban ta6a tsanmmanin abinda zan gani kenan

nan take jikina yahau rawa nafara yin baya baya hannu toshe da baki

atsorace najuya nabar wajen dagudu ina bi ta duwatsun cikin ruwan harna samu na koma hanyar danabi nashigo qarqashin gadar nasamu nafita

daga saman gadar na tsaya ina kallon kwalin danake hange daga nesa har lokacin zuciyata banda bugawa babu abinda takeyi


sonike intafi amma kuma nakasa sai kallon kwalin nake batareda na iya motsawa daga inda nakeba

kamar wanda aka jawo saina tsinci kaina da komawa cikin gadar kuma ina tafiya ahankali nasake nufar kwalin


jiki na rawa nasake leqawa naga abinda nagani daxu

yaro ne da bazai wuce shekaru uku ba, farine dukda ba irin tass dinnan ba na larabawa don nashi irin farin nanne mai jajaja, gashin kanshi ajiqe kamar yadda sauran jikinshi yake ya kwanto yarufe rabin fuskarshi

nafi minti biyu atsaye ina kallonshi zuciyata na bugawa kafin cikin qarfin hali dasa hannu nadan ta6ashi

ko motsawa beyiba hakan yasa naqara ta6ashi duk atsorace

ganin be motsa ba yasa cikin qarfin halin na hau kekketa kwalin har ya ida fitowa fili sannan najuyoshi nasa hannu ina qunce mugun daurin da akayima bakinshi

saida nasha wahala sannan na kwance na zazzaro tsummunan da aka cuccusamashi cikin baki ina kuka sosai don an daure mashi bakinne cikeda mugunta ga bakin da kumatunshi sunyi jajur alamun kwanciyar jini

bayan nagama kunce bakin nakoma kan hannayenshi da qafaffunshi dake daddaure nahau quncewa, suma saida nashi wahala sosai kafin na samu kuncewa

saikuma narasa abinda zanyi mashi daganan gashi gari yawaye don haske yayi sosai

ganin hakan yasa nafara qoqarin daukarshi saidai yayimin nauyi sosai hakan yasa nadan kwantar dashi kan dutsin wajen nahau daddana mashi cikinshi daya dan yo sama

akau saigashi ruwa sunshiga fitowa ta hanci ta baki, haka naita dannawa har suka daina fitowa saidai har lokacin ko motsawa beyiba hakan yasa na cije na cicci6eshi dukda lokacin yadan rage nauyi nasamu dakyar nadorashi abaya na don har inayi ina faduwa sannan nashiga takowa ahankali don barin cikin gadar dashi

koda nafito rasa inda nanufa nayi gashi har lokacin ina tsoron kar ace yan gidan danake aiki nacan na nemana gashi nasan shima wannan yaron wadanda suka jefashi a gada sunyi hakan ne don son ganin bayanshi hakan na nufin daga ni har shi muna cikin hadari

hakan yasa maimakon nayi titi nashiga cikin mutane saina yanki daji kawai batareda nasan inda muka nufaba burina Kawai na tseratar da rayuwarmu dukda har lokacin banida tabbacin ba gawace goye abaya na ba


ahaka harna samu nayi nisa sosai harsaida naji ban iya tafiya sannan na haqura muka zube awajen ina sauke numfarfashi

dagowa nayi ina kallon yaron wanda farat daya yashiga zuciyata ina jinshi fiyeda nakejin d'ana dana haifa yakoma

bansan ko yana rayeba ko ya mutu don kwata2 baya motsi kuma natara yatsuna a hancinshi nidai banji yana numfashi ba

kunnena nasa a saitin zuciyarshi ina sauraro ko zanji bugun zuciyarshi saidai shima shiru saida na dade ina sauraro sannan naji bugun zuciyar can qasa qasa


sosai nayi murnar hakan don dafarko harna fara sadaqarwa dacewar yamutu

tashi nayi ina kallonshi batareda nasan wani taimakon dazanyi mashi ba, nasan asibiti yakamata na nema na kaishi amma zuciyata taqi bani hadin kai don gani nake kaishi asibitin daidai yake da jefashi cikin hadarin daya fito don qilan hakan yazamo silar dazaisa mutanen dasuka so ganin bayanshi dafarko susake dawowa


haka mukaita zama awurin cikin rashin sanin abinyi ga yunwa ga sanyi don daga ni har shi kayanmu ajiqe suke


haka mukaita zama har rana tafara fitowa inda anan nasamu nacire mashi jiqaqiyar rigarshi ko yadanji sauqin sanyin


haka natusashi gaba nabuga uban tagumi ina kallonshi batareda nasan abinda zanyi ba ahaka har rana ta take sosai


ganin hakan yasa nasake miqewa na daukeshi nasake goyashi nacigaba da tafiya acikin dajin


ranar naci baqar wahala don haka nawuni ina tafiya babu ci gwara gwara ruwa idan nahadu da matattarar ruwa ina dan kwalfa in jiqa maqoshina ahaka harna qarasa wani qauye qauye

anan qarfina yaqare bansan ya akayi ba kawai sainaji lumm idanuna na rufewa dakansu kaina na juyamin nazube awajen dani da d'an dake bayana


bansan iya adadin lokacin dana dauka ba asume saidai Kawai nafarka naganni cikin wani daki mai dan duhu duhu

firgigit nayi na miqe zaune ina waige waige anan nagane kamar ma cikin bukka nike

agarin waige waigena na hangi wannan yaron shima kwance daga dayan gefen dakin

bansan sadda naqarasa wurin ba da rarrafe nayi saurin tattaroshi ajikina na rungume

ga mammaki na sainaji yayi motsi yana yatsuna fuska saboda motsashi danayi saikuma yafara tari ahankali cikin wata iriyar dakussashiyar murya dabata fita sosai

farinciki ne ya lullu6eni ganin ya motsa hakan yasani sake rungumeshi ina jin wani irin sonshi har qasan zuciyata sai kallon kyakyawar fuskarshi nakeyi babu ko kyaftawa kamar nasamu madubi

ahaka wasu mutane suka shigo bukkar

jin motsinsu yasani dawowa daga duniyar kallon yaron naja dabaya atsorace ina binsu da kallo kamar yadda suma sukemin

suma larabawa ne saidai dagani yan qauye ne duba da yanayinsu

mace ce da namiji duk sun manyanta sun tsaya daga bakin kofa sun zubamana idanu


nima dai kallonsu nake amma atsorace sai qara rungume yaron jikina nakeyi qamm a qirjina yadda kasan za'a kwaceminshi

kallon juna naga sunyi sunyi murmushi sannan suka qaraso ciki suna kallon yadda nake qara jabaya ina mannewa da jikin bukkar

ganin yadda na tsorata yasa suka bar nufomu inda anan matar cikin murmushi don kwantar min da hankali tafara cemin na kwantar da hankalina babu abinda zasuyimin cikin larabci

dukda banajin larabcin sosai amma nagane abinda take nufi saboda gwadawar datakeyi da hannu hakan yasa hankalina dan kwantawa

miqomin hannu tayi akan nabata d'an nikuma saina qara matseshi jikina ina jada baya alamun ban badawa, murmushi sukayi sai mutumin cikin harshen larabci yake tambayata d'ana ne?

dan zaman danayi agidan danake aiki yasani dan sanin wasu guntayen larabci hakan yasa nagane abinda yace min hakan yasa na kada kaina cikin sauri

murmushi suka sakeyi nan suka hau nunamin baxasu cutar damuba taimaka mana zasuyi

dakyar dai suka samu suka lalla6ani na yarda dasu nabasu shi suka mayar dashi shinfidarshi suka kwantar dashi inda anan naga sun cigaba dayimashi wani hayaqi wanda yaita sashi tari da shaqaqiyar muryarshi

nidai ina gefe ina kallonsu harsuka gama yimashi duk maganin dasuke mashi suka kyaleshi yanata barcinshi

abinci suka bani wanda kamar jira nake na amsa hannu narawa nashiga ci saboda tsananin yunwar da dama nakeji

saida naci na qoshi sannan nadawo nutsuwata inda anan sukaso sanin wacece ni mekuma yakawomu qauyensu

dayake duk bajin yaren juna muke ba yasa maganar kurame (demonstration) duk tafi yawa a maganarmu inda anan nake kwantantamasu cewa gudowa mukayi za'a kamamu mu ba yan qasar bane nakuma nuna masu sonike mubar qasar

shiru sukayi suna kallona hakan yasa gabana cigaba da faduwa don duk a tunanina sungano yaron ba nawa bane don shi farine nikuma gaskiya baqa ce dukda ba irin qirin dinnan ba amma dai kwata2 bamuyi kama da yaron ba kuma gashi shi sak balarabe dukda jikinshi ba irin farinnan tass ba yake kamar na jikin kajin turawa amma farine irin mai jajaja wanda anasamun daidaikun masu irin fatar a Africa

tambayata sukayi wacce qasa nake nace Ghana a Africa

sai suka sake tambayata ina uban yaron

cikin qwarin gwiwa nabasu amsar yamutu nima nan aikatau yakawoni saboda tsananin rayuwa saina tsinci kaina da gayamasu duk abinda yafaru a tsohon gidan danake aiki da silar gudowata, abu daya ne ban gayamasu ba shine yaron tsintarshi nayi

sundade suna jujjuya maganata kamar dai basu yarda dani ba don saidai su kalli yaron su kalleni

can sukace karna damu zasu taimaka min nakoma qasarmu can Africa amma sai yaron ya farfado tukunna yasamu lafiya


ba haka nasoba amma babu yadda na iya haka na haqura ina addu'ar allah yarufamin asiri mubar qasar lafiya


saida muka kwana uku agidan kafin yaron ya farka

kuma abin mammaki yana farkawa yafara waige waige yana kiran ummie cikin muryar dabata fita munayin ido hudu dashi ya rarrafo wajena dasauri ya maqalqaleni

sosai na sauke ajiyar zuciya ganin yadda yaron yayi don da yaqi yarda dani da qila mutanen sun zargeni

duk yadda mutanen sukaso ta6ashi qiyawa yayi ya lafe ajikina yayi lamo kamar dagaske ni mamarshi ce

ahaka muka qara kwanaki biyu inda na matsa ni sonike nakoma qasarmu don har lokacin hankalina be kwanta da zamanmu qasar ba

izuwa lokacin sungama gamsuwa cewa d'ana ne saboda yadda yake liqemin kodayaushe yana maqale dani

duk yadda sukaso muqara zama ko don jikinshi dabe ida warwarewa ba qiyawa nayi nace idan naje can zankaishi ayimashi magani


ahaka suka haqura ranarda muka cika sati daya awurinsu namijin ya rakamu mukayi tafiya sosai bisa raqumma har mukazo wani qauye shima

anan ya hadamu dawani wanda aikinsu fitarda mutanen qasar ta 6arauniyar hanya

anan yabarmu bayan yadan bamu dan guzurin tafiya nikau naita godiya kamar zan ari baki

anan aka hadamu da wasu mutanen dasuma qasar za'a fita dasu rabi da kwatansu duk yan Africa ne inda aka lodamu awani qaton jirgin ruwa cikin dare muka daga


daren ranar ko rintsawa banyiba ina qanqame da KAMALDEEN kamar yadda nasamashi suna

hankalina be kwanta ba saida naga mun qetare iyakar saudiya sai lokacin naji sanyi sanyi araina

alokacin nakuma lura duk yawanci mutanen cikin jirgin yan Nigeria ne sannaniyar qasarnan datayi suna duk fadin Africa dama duniya bakidaya hakan yasa nima jin hankalina karkata acan

ataqaice dai saida mukayi kwana uku muna tafiya sannan muka iso Nigeria aka jibgemu garin lagos


lokacin jikin Kamal yaqara rikicewa saboda yanayin tafiyar tamu ga sanyin daya bibbigemu hakan yasa muna sauka na dangana da asibiti wanda dakyar dagano ta hanyar kwatance

ganin mawuyacin halin dayake ciki yasa aka kar6eshi cikin gaggawa inda anan likitoci suka shiga bashi taimakon nikau nakasa zaune nakasa tsaye saboda yadda jinina ke kan akaifa jinake kamar zan rasashi

ahaka likitocin suka fito daya daga ciki yanemi tattaunawa dani inda anan yake sanar dani yaron yakamu ne da ciwon nimonia (Pneumonia) saboda sanyin dayayi mashi mugun kamu (wannan ne Asalin ciwon Deen)

sannan ya rubuta min abbubuwan dasuke buqata tareda magungunna

koda naje wurin sayen sai akayi min lissafin kudadde masu yawa dukda ga lokacin bansan sunada yawaba don bansan kan kudin Nigeria ba sosai

tambaya nayi inda xa'a chanzamin yan kudaddena dana taho dasu daga Nigeria aka nunamin naje na chanzo inda anan na fahimci ko rabin kudin maganin banidasu

komawa nayi asibitin wurin likitan nayimashi bayani akan cewa kudaddena kenan ya taimaka ya dubamin shi banida komai bayansu

cewa yayi babu abinda zai iya yimin indai ina buqatar lafiyar yarona inje inkawo abubbuwan dasuka buqata

haka nasake fita hankalina amatuqar tashe gashi bansan kowaba bare na nufeshi ya taimakamin

haka naita yawo inda daga qarshe nayi abinda banta6ayiba wato bara

haka naita tare duk wanda nagamu dashi akan ya taimaka min inda qalilan ke saurarona har sudan bani wani abu wasu kau ko kallo ban ishesu ba

ahaka nasamu nadan tattara yan kudadden nakoma wajen likitan nazube mashi su da wanda nasamo da wanda dama nake dasu nace yaduba yaga ko sun kai

gani nayi yabi kudadden da kallo wanda hakan ya sanyaya jikina saikuma ya sa hannu yafara tattarasu ya hadesu ya kirga

yana gama kirgawa yadanyi murmushi yana girgiza kai wanda hakan yaqara sanyaya min gwiwa don da alamu dai basu kai ba

nurse yakira yabata wasu kudin banda nawa da takardar maganin yace taje tasiyo sannan yaturomin kudaddena yace na ajiye Kawai

godiya naita yimashi harda kukana don da be taimaka min ba bansan inda zankuma je insamu taimako ba

ahaka nurse din tadawo da abubbuwan daya aiketa saye nan da nan yatashi yafita yakoma inda aka kwantar da kyakyawana.."

dan shiru tayi ta dago tana kallon mutanen dakin daduk suka maidata t.v, daidaiku ne babu hawaye a idanunsu kowa idanunshi yayi jajir jikinsu duk yayi sanyi kamar wadanda akayima shegen duka

kallon Deen tayi da fuskarshi tayi jajir idanunshi sunyi jajir sungaji da zubda hawaye sai kallon kaka yake kamar yau yafara ganinta

ahankali takamo hannunshi tariqe tareda matsewa anata tana dan murmushi sannan tacigaba dacewa


"ataqaice dai saida muka kusan sati asibitin inda likitan duk ya daukemana komai nakula da lafiyar shi sai abinci Kawai nake siye da yan kudadden hannuna


acikin wannan yan kwanakin Kamal yasamu sauki sosai ya warware inda wata shaquwa tashiga tsakaninmu, yadda yake liqemin sai kayi tunanin dama can yasanni ko mun hada wani abu dashi kuma ba haka yakema kowaba don nalura yanada qiwuya don ko likitan baya yarda dashi amma ni yadda kasan uwarshi.


ahaka har aka bamu sallama inda likitan yaita gayamin abubbuwan daxan kiyaye saboda gudun tashin ciwonshi sannan yabamu kingin magungunnanshi yayimana fatan alhairi.


sosai nagodewa mutumin da bazan ta6a mantawa da alhairinshi ba, ahaka nafito dashi abayana don nalura yanada bala'in son jiki gashi dama yanzu yake samun sauqi bazanso yayi tafiya ya wahala ba

ahaka muka fito batareda munsan inda muka dosaba ga garin babu ruwan kowa da kowa, kowa harkar gabanshi yake


karnaja xancen da tsayi, iya wahala mun wahala don saida mukayi kwana uku batareda masauki ba inda darana muke yawo ina dan yimana barar abinda zamuci idan dare yayi muzo tasha mukwana.

sosai nagaji da barar danake don bara wata iriyar qasqanttaciyar sana'a ce wanda batada dadi kwata2, na gwammaci aikin wahala abiyani da yinta gashi kuma banaso na cigaba ahaka har kyakyawana yatashi ahaka shima don sosai naci buri akanshi naji inason koyaya ne yasamu rayuwa ingantacciya


ahaka nafara neman abinyi inda daga baya nasamu aiki acikin tashar wajen wata bayerabiya mai saida abinci, dafarko wanke wanke nakemata da share share tana bani abinci safe da rana kafin daga baya yazamana har girkin nake tayata inda anan nadan koyamata wasu abincicikanmu na ghana wadanda suka samu kar6uwa sosai awajen customominta hakan yasa bayan abinci tafara biyana kudi wadanda nake adanasu don burina lokacin insamu inkama mana ko daki dayane mubar kwana tasha don kwata2 banason kwana tashar damukeyi don yawanci yan iska sunfi yawa aciki haka zasu kwana suna shaye shaye da bushe bushensu da kayan hayaqi nikuma banison kyakyawana yatashi cikin irin wannan environment din


ahaka nasamu dakyar dahada kudin kama daki daya na rabin shekara muka koma can inda daganan muke zuwa aikin kullum nida kyakyawana wanda ke maqale dani duk inda nayi baya yarda da kowa saini

sosai kyakyawana keda shiga ran mutane don mutane dayawa sunsanshi suna kuma sonshi don mutane sunsha bashi kyautar abubbuwa don yana matuqar burgesu saboda kyawunshi (kunsan yare dason kyawawa)


ataqaice dai saida mukafi shekara agarin kafin na tattara muka bar garin muka koma garin minna inda anan nasa kyakyawana Makarantar primary da islamiya nikuma nakama sana'a ina kula damu

nabaro lagos ne badon komai ba saidon dama ni garin beyimin ba, banaso kyakyawana yatashi acikinta bare yatashi da al'adunsu don sai ahankali hakan yasa ina tara isassun kudadden danaga zai ishemu natattaro muka barota

sosai na jajirce akan ilimin kyakyawana, komai dazanyi duk saboda shi ne, nayi sana'o'i kala2 wadanda nikaina bansan iyakarsu ba nidai burina na inganta rayuwar kyakyawana wanda shikadai nake iya kira nawa kuma shikadai nake kallo inji dadi


ataqaice dai munyi zaman garruruwa daban2 nayi sana'o'i daban daban dik don riqe kaina da kyakyawana wanda nake mashi kallon duniyata

ina qaunar Kamal qaunar dabaxan iya misaltawa ba don da ata6amin shi gwara ni ata6ani sau dubu

Kamal yataso yaro mai matuqar sanyi da rashin hayaniya, bayada hayaniya kwata2 ga tsantsar biyayya ga nagaba, gashi allah yabashi kwalwar daukar karatu don tun yana primary yake ciwo kyaututuka na hazaqar karatu both islamiya da boko hakan yake qara qarfafamin gwiwa wajen qara zagewa don tallafawa karatunshi


shaquwar dake tsakanina da Kamal bata misaltuwa, nice komai nashi kamar yadda shine komai nawa, Kamal yakasance yarone mai tsananin tausayawa da jin qai, bayada qiwuya ko kadan don duk yawancin sana'o'i na tare dashi mukeyi yana matuqar taimakamin sosai


ahaka harya girma yagama primary yakuma yi saukarshi tafarko inda alokacin ne muka sake tattarawa muka bar garin muka koma Katsina lokacin yanada shekaru goma sha biyu

zan iya cewa duk tafiye tafiyanmu da zama garurruwan damukayi babu wanda naji dadinshi kamar na Katsina

cikin ikon allah na tsayar da sana'a datayi matuqar amsata na saida Koko da qosai inda da ita muka samu muka,cigaba da rufama kanmu asiri

anan nasamoma kyakyawana Makarantar secondary ta gomnati ya cigaba da zuwa inda anan ma yayi fice saboda hazaqarshi ahaka harya kammala yakuma fito da sakamako mai kyau

inada burin kyakyawana yayi karatu mai zurfi kodan inganta rayuwarshi gashi nalura shima yanason karatun sosai hakan yasa naji inason ya cigaba da Makarantar gaba da secondary

kasancewar babu kudin shiga Makarantar alokacin hakan,yasashi zaman gidan shekara daya inda anan maqocinmu wanda yazama kamar dan uwanmu yasama mashi wani shagon kafinta ya dinga zuwa, acikin shekara guda din nayita tari don babu laifi inasamu sosai da sana'ar nan,tawa ta Koko da qosai gashi Kamal shima yana dan samo wani abu andcan shagon nasu

ahaka muka hada mukaita tarawa har shekara tazagayo muka samu yashiga Makarantar gaba da secondary din wanda dik shine burinmu


zan iya cewa nafishi farinciki da fara zuwa Makarantar dayayi don harwani alfahari nakeji araina idan na kalleshi naga wannan yaron nawane rainonane.


Deen yarone mai,matuqar sanyi hakan yasa wasu ke amfani da sanyinshi wajen cutardashi hakan yasa yake matuqar bani tausayi kuma nake tsayamashi tsayin daka bana kyale duk wanda ya ta6amin shi, kowama yasan irin yadda nakeji dashi kuma banison komai ya ta6ashi shiyasa ake shakkar yimashi wani abin don akanshi banajin nauyi ko kunyar kowa


haka muka cigaba da rayuwa har zuwa lokacin da Zainab tashigo rayuwar Kamal..."


cigaba tayi dabada labarin yadda akayi case din incident dinsu master inda anan tafara saninsu Zainab da yadda Deen ya kwanta asibiti harwani da zumuncin dasukayi da ahalin Zainab bayan lokacin saita gangaro kan soyayyarsu dakuma yadda soyayyar tasu bata kwanta mata ba tunfarko saboda dama tunfarko tahangomasu matsala a soyayyar

nan ta gangaro kan yadda su daddy sukazo dashi da abokinshi Alhaji Abubakar(baban asaad) sukazo suka nuna rashin son dangantakar dake tsakanin Deen da zee dakuma cewa tajamashi kunne yafita harkar yarsu harzuwa lokacin dasuka dawo kuma dakansu daga baya suka bada haquri akan abinda sukayi suka kuma yarda da soyayyarsu wanda itama dole ta amince saboda yadda talura Deen nason zee din

saikuma tagangaro zuwa maganar data tadamata hankali na batun Introduction dinsu wanda dafarko bata tashi hankalinta ba sai lokacin da wannan abokin daddyn yazo gidan shikadai lokacin Deen bayanan yana Makaranta yafadamata batun Introduction din yana kuma cewa dangin Deen suke buqatar gani najini don gaskiya bazasu wani yarda da bayada kowa ba sai ita don ba'a ta6a yin hakaba tunda ita kakarshi ce dole dai ace yanada dangi bayan ita babu yadda za'ace ita kadai ce danginshi saidai idan akwai wata qullaliya don haka su bazasu lamunci rainin wayau ba don bincike zasuyi na sosai da sosai bazasu aurama diyarsu marar asaliba

tofa abinda yatashi hankalin kaka kenan alokacin komai ya dagulemata taga kamarma sunsan babu abinda tahada da Deen

hankalinta yatashi sosai don saitaga kamarma sosuke su rabata da Deen din gabadaya

hakan yasa alokacin ta tashi hankalinta ta burkuce ma Deen akan dole subar garin don saitaji garinma yaficemata akai gabadaya

hakan shine dalilin barin garin nasu har suka koma Abuja

nanma tabada labarin irin rayuwar tsukun dasuka shiga a Abujan kafin allah ya dafamasu suka hadu da Alhaji Shamsu wanda ta silarshi Deen yazama abinda yazama yanzu, ahaka harta gangaro kan wannan tafiyar dayayi dakuma yadda ranta be kwanta da tafiyar ba don jitayi ajikinta kamar zata rasashi ne ashe kaddarace ta kirashi.. kaddarar haduwa da ainahin ahalinshi...✍�


*insha allah page 100 littafin zai qare, so start saying byebye to DEEN👐🏻*


Ummin fasihu🧚🏻‍♀�
8/19/21, 6:39 PM - Buhainat😝: ahaka suke firar inda jefi jefi zee da Lailah kesamusu baki Aysha da batool nema masu surutun

sallama sukaji anyimusu daga bayansu hakan ya katsesu daga firarsu duk suka dago suna amsawa

"barka" yafada cikin murmushi

suma martanin murmushin suka maida mashi suna amsawa banda zee da tunda tadago suka hada ido ta kauda kai

"please kudan bani aronta for a few minutes..please" yafada yana nuna zee

kallon juna batool da Aysha sukayi sukayi murmushi

"oh.. sure" inji batool sai takama hannun Lailah tana cewa

"kinga mukoma daga can sis"

suka wuce sukabar daga zee sai Deen awajen

qarasowa Deen yayi ya tsaya yana fuskantar zee dahar lokacin bata qara kallonshi ba

harde hannayenshi yayi a qirji yana kallonta fuskarshi dauke da murmushi


jin shirun yafara yawa yasa zee dagowa sai taganshi a yadda yake yawani kafeta da ido

hade fuska tadanyi taqara kauda face

ahankali cikin muryar rad'a taji yace
"angry bird"

dagowa tayi ta kalleshi

dan budamata idanu yayi yace
"yes, my cute angry bird"

harararshi tayi Kawai tafara qoqarin ra6ashi tawuce

"you know what?" ya dakatar daita da hakan

tsayawa tayi batareda tajuyoba

"banta6a ganin hallita mai kwatankwacin kyawunki ba aduk duniyar nan"

qarasowa yayi gabanta yana kallonta
"tell me.. what did you do to me?"

dagowa tasake yi ta gallamashi harara ta kauda kai
"zan wuce" tafada ciki ciki

kaucewa yayi daga kan hanyar yana dan bowing
"as you wish ma'am"

kauda kai taqara yi cikin qoqarin 6oye murmushin dake neman su6ucemata tazo tasake ra6ashi tawuce

"please kibani digits dinki idan babu damuwa" yafada daidai tawuceshi

batareda tajuyo ba ko ta dakata daga tafiyarta tace
"akwai damuwa"

"ok please ki taimaka ki daga idan nabugo" yasake fada da d'an qarfi don tafara yimashi nisa

banza tayi dashi ta cigaba da tafiyarta


"i'll take your silent as yes" yaqara yafada yana kallonta

dan murmushi Kawai zee tayi tana cigaba da tafiyarta, Deen won't change, her silly timid guy


agefe kuma bayan su batool sunbasu wuri suka samu wani wurin suka koma suka tsaya suna fira suna cigaba da jiran fitowarsu abbu

Lailah kasa concentrating tayi a firar tasu don hankalinta gabadaya yana gasu Deen data baro, she can't help but feel jealous, wani irin kishi taji tanaji ganin wanda take mugun crushing tsaye da wata

duk yadda taso maida hankalinta akan firarsu batool kasawa tayi don banda satar kallon inda suke tsaye babu abinda takeyi


ahaka har zee tabaro Deen tadawo wajensu inda hakan yayi daidai da fitowarsu abbu da kingin daga cikin gidan suna fira suna dariya

anan hankalinsu yadawo kansu gabadaya

wata sabuwar sallamar aka sakeyi tsakanin juna kafin su rakosu har wajen motocinsu

zee zata nufi motarsu ummy Aymaan yabude mata kofar tashi motar yana cewa tashiga fuskarshi da murmushi

dan maida mashi murmushin tayi taqaraso tashige motar batareda ta yarda tajuya takalli saitin inda takeji ana kallonta ba

maida kofar Aymaan yayi yarufe yajuyo zai wuce suka kusan karo da Aysha data gama bankwana da batool data shiga bayan motarshi

saurin jabaya Aysha tayi tana cewa
"oh..sorry"

rolling idanu Aymaan yadanyi yazo zai wuceta ciki ciki yace
"clumsy gal"

binshi da kallo tayi don tajishi harya zagaya seat dinshi

kamar ance yadago sai suka hada ido don har lokacin shi take kallo

kamar dama shi take jira yadago ya kalleta saita gallamashi mugun harara tareda murgudamashi baki sannan tajuya tawuce wajensu ummie dake dagama su ummy hannu

dan murmushi yayi yana dan girgiza kai Kawai sannan yashige motar

shishigewa motocin kowa yayi suka rurrufo sannan suka tada

har lokacin ummie bata daina dagamasu hannu ba fuskarta dauke da murmushi shikau Deen yakasa dauke ido akan zee dake cikin motar Aymaan

Ahaka motocin suka jera suka bar gidan

anan kingin suka juya suka koma ciki

dayake dare yayi sosai yasa Kawai su mamy dasu kaka suka wuce masaukinsu shima Alhaji haka inda Lailah zata kwana tareda Aysha duk sukayima juna bankwana suka shishige


adaren ranar Lailah kasa barci tayi, jitayi komai ya dagulemata

ganin Deen nason wata ba qaramin jagulemata lissafi yayiba hakan yasa ranar banda juye2 babu abinda takeyi don barcin yaqi zuwa

a bangaren Aymaan ma haka, zuciyarshi takasa sukuni, yakasa hqr da tunanin zee dukda yanajin qamshi qamshin rabuwa daita, ganin barcin ya gagara yasashi miqewa daga baya yayo alwalla yafara nafilfilu inda daga qarshe yaita addu'ar za6in alhairi yana addu'ar allah ya sassautamashi soyayyar zee a zuciyarshi yakuma bashi haqurin da juriyar rabuwa daita idan batashi bace....✍�


*manage🙏🏻*


Ummin fasihu🧚🏻‍♀�


*🙍🏻�
8/19/21, 6:43 PM - Buhainat😝: *🙍🏻‍♂️DEEN🙍🏻‍♂�*


*099*


*SEMI-FINAL*


*TWO DAYS LATER*


Acikin kwanaki biyunnan sosai su kaka dasu ummie suka zama kamar family

zama suke yadda kasan sun dade dasanin juna don sosai zumunci yaqullu atsakaninsu wanda ga dukkan alamu zaiyi qarfi sosai don juma'a mai kyau tundaga laraba ake ganeta


kaka tazama kamar wata kakarsu ta gaskiya don yanzu ba iya Deen ba hatta mussadiq da Aysha sunyi wani irin shaquwa da kaka, musanmman ma Aysha don tazama kamar wata kaka's pet kullum tana sashenta fira inda tadage wai tana koyon hausa awajen kaka


mussadiq ma babu laifi yana yawan zuwa sashen kaka saidai be faye surutu ba Kawai dai zaije ne yayi zaune yana kallon firarsu da Aysha sannan yasha furar kaka wanda tunda tabashi yafara sha sau daya yaji duk duniya babu abinda yata6a yimashi dadi irin furar hakan yasa kullum yake lalla6owa yazo part din ya zauna baya fita saiyasha furar, itama kaka lura datayi da hakan yasa kodayaushe take tanadarmashi furar don ta lura masoyinta ne sosai

abu nabiyu dake kaishi part din kaka kuma Lailah ce, yarinyar da tunda yafara dora idanunshi akanta a airport yakejinshi ba daidai ba


haka Kawai yake samun kanshi dason tsareta yaita kallo batareda shima kanshi yasan amfanin kallon ba agareshi, Kawai dai burinshi kullum ya sameta ya kafamata wadannan idanun nashi yana kallo

saidai ya lura yarinyar kamar bata magana don dafarko yayi tunanin she's the silent type sai daga baya daya tattara hankalinshi akanta yana studying dinta yagano damuwace ta maidata hakan don akodayaushe haka zaka ganta so moody bata magana saita kama, mostly yafi ganinta tana danne dannen wayarta with unknown expression a fuskarta


yau ma kamar kullum part din kaka yashiga

sanye yake da kayan gida don bedade da fitowa wanka ba bayan sundawo daga Yawon zagayen companies dinsu dayayi da Deen

he's too tired shiyasa suna dawowa yashige toilet yayi freshen up sannan yafito ya shirya cikin qanannun kaya yafita yabar Deen dake jibge a kujera tunda suka dawo waya kare a kunnenshi yana magana qasa qasa sai zabga murmushi yake kamar wanda akewa wani babban albishir


direct part din kaka yanufa don alokacin saiyaji babu abinda yakeso kamar furar kaka


da sallama yashiga part din inda as usual ya iskesu a qayattacen falon nata daita da Aysha data daddage tana koyon hausa sai mamy daga gefe tana gyara wasu kaya don gobe zasu koma 9ja


atare duk suka dago suna amsa sallamarshi ya qaraso cikin falon

"sannu.. dai zuwa" Aysha tafada cikin yanayin hausarta data fara koya tana kallon mussadiq fuska washe

harara ya gallamata yana zama kusada kaka cikin larabci yace
"idan na wanka maki mari ko?"

6ata fuska Aysha tayi tana kallon kaka

dariya Kawai kaka tayi tana cewa
"kyaleshi kishi yake don kinfara iyawa shi be iyaba"

dukda Aysha batasan me tace ba amma tasan rarrashi ne hakan yasa tadan tura baki tana sake komawa gefen kaka tana dan murmushi

shima mussadiq murmushin yadanyi sannan yashiga gaidasu kaka da mamy suna amsawa cikin fara'a, kaka sai tsokanarshi takeyi shikau saidai ya sunkuyar dakai yana murmushi don besan me take cewa ba

ba jimawa kaka ta tashi ta tafi wurin fridge din dakin tabude taciromashi furarshi data dama donshi tazo ta ajiye mashi nan take fuskarshi ta washe babu ko kunya yaqara jawo furar yabude yafara aikata don shi kanshi har mammakin yadda yakeson furar nan yake, gani yake da za'a bar bashi komai naci acigaba da bashi fura as abinci tsaff zai iya rayuwa yana shanta ita kadai

haka yaita shan furarshi yana sauraron su kaka dasuka dasa darasinsu inda mamy ce yar fassara don idan Aysha tayi tambaya da turanci mamy ke fassarawa kaka itakuma saita bata amsa

yana cikin sha yafara yawo da idanunshi a falon

something is missing, akwai abinda babu a falon

_Lailah_


dan dakatar da shan furar yayi yana tunani

gobe su Lailah zasu bar Dubai sukoma Nigeria and har lokacin magana bata ta6a hadasu ba saiko gaisuwa sama sama irin hyy hello.

ya lura idan yazo waje taganshi saita fara quramashi idanu kamar Maison tantance wani abu, daga bisani kuma saita janye idanunta akanshi baxata qara yarda ta kalleshi ba


shima most time yanason yimata magana amma saiya fasa saboda yanayin damuwar dayake hangowa qarara afuskarta hakan yasa saiya zubamata idanu instead yaita kallo kamar t.v


saida yasha fin rabi sannan yarufe kingin furar yatashi ya maida a fridge din

dagowa kaka tayi ta kalleshi bayan yadawo yazauna tace
"harka qoshi?"

yanayin yadda tayimashi nuni yasashi gane metace hakan yasashi yin dan murmushi yana kada kai

"na'am shukran laki, jazakillah" yafada ahankali


murmushi itama kaka tayi sannan tajuya kan Aysha daketa maimaita wata kalmar hausa cikin son riqewa


yadan qara zaman yan mintuna sannan yatashi yayi musu sallama yafita, he was wondering ina tashiga don a irin wannan lokacin batada wurin zama sai part din kaka

main house din yashiga inda ya tarar babu kowa dama kuma ummie batanan hakan yasashi fita waje

haka Kawai zuciyarshi tabashi yaje garden din gidan wanda hakan yasashi nufar wajen hannayenshi zube a aljihu yana takawa ahankali cikin tafiyarshi


tundaga nesa ya hangota zaune kan kujera ta kafe waje guda da ido glass cup mai daukeda fresh milk ahannunta

tsayawa yayi yana kallonta kamar mai karantar wani abu tattare daita sannan yafara takowa ya nufota


saboda zurfin datayi a tunaninta yasa batasan sadda yazo wajen ba sai jitayi an zare glass cup din hannunta

adan firgice ta juyo sai taganshi zaune a kujerar dake facing dinta yakai kofin abaki yana sipping ahankali

quramashi idanu tayi kamar mai son tantance wani abu kamar yadda tasaba kullum insun hadu can saikuma ta janye idanunta ta maidasu qasa

ajiye cup din yayi yana gyara zamanshi yace
"yes bashi bane.. ba wanda kike tunani bane, mussadiq ne" yafada da turanci

dagowa tayi ta kalleshi

"muna kama sosai ko? kamar da saikin dauki mintuna kina kallona kafin ki iya tantance waye agabanki, aganina da dagaske abinda kike tunani hakane da bazaki dauki lokaci kafin ki iya tantancemu ba don a kallo daya zuciyarki zata baki ko waye agabanki"

kallon rashin fahimta take mashi don duk takasa gane kan maganarshi

"you're confused gal... so confused, you're confusing your brain and mind, yakamata kiyi realizing gaskiya izuwa yanzu"

"gaskiya? as in?" inji Lailah tana kallonshi still confused


komawa yayi ya jingina da kujerar yana kallonta qasa qasa yace
"as in abinda kike tunani bashi bane, abinda kwalwarki ke tunani yasha banban da abinda zuciyarki ke tunani"

yanayin yadda tayi da fuska yasashi sanin yasake kullemata kai hakan yasashi yin guntun murmushi yace
"you think you love him? No, kisake bincikar zuciyarki"

wannan karon kallonshi take sosai
"what did you mean?"

"I mean you two don't really deserve each other, there's someone who deserve you most, zuciyarki tagane hakan amma haryanzu kwalwarki takasa gane hakan"

shiru tayi tana kallonshi nawani lokaci, wai akan me yake magana ne? badai akan Deen ba, idan ma akanshi ne tayaya yasani? shi kanshi Deen din bata tunanin yasan tana sonshi bare ya gayamashi


"look, wani lokacin zuciyarmu tafi kwalwarmu saurin gano abu, so goes yours don haryanzu zuciyarki bata iya gane mere presence din wanda kwalwarki take ikirarin kinaso, meyasa akallo daya zuciyarki bazata baki cewa eh shidin ko bashi bane? meyasa saikin dauki lokaci kafin ki iya tantance hakan... because your heart doesnt really beats for him, you're decieving yourself ne Kawai"

jitayi ranta ya6aci, who is he dazaiyi judging dinta haka? zuciyarshi ce ko tata? tayaya zai fita sanin abinda takeso?

daukar wayarta dake kan table din tayi tafara qoqarin tashi don iya abinda zata iyayi kenan yanzu, tabarmashi wurin don taga alamun abin ma harda rainin wayau

d'an murmushi mussadiq yayi yasake jingina da kujerar yana harde hannayenshi a qirjinshi yace
"you might be angry but that's it, zuciyarki ba wa Deen take bugawa ba, idan ma tana bugamashi ada yanzu tadaina, da alamu tafiki hangen nesa saboda tuni ta hangomiki wanda yafi cancanta dake"


tunda yafara maganar ta tsaya daga qoqarin tafiyar datake tana sauraronshi batareda tajuyo ba

tashi shima yayi yatako har kusada ita

"stop wasting your time on someone who's not even aware of your feelings maimakon hakan kiba wanda yafi cancanta dake dama, damar wanke dukkanin damuwar dake a zuciyarki.. mai kwadayin ganin murmushinki wanda kuma zai iya komai don dawwamar da murmushin akan fuskarki"

daga hakan yazo ya ra6ata yawuce walking in his usual majestical steps


binshi da kallo tayi daga inda take tsaye kamar mutum mutumi, takasa koda motsi don komai ya tsaya mata cakk sai magangganunshi dake mata kai komo a kwalwa.


part din kaka yakoma inda nan ya tadda dukkan mutanen gidan harda Deen dashima izuwa lokacin ya chanza shiga da ummie da bata dade da dawowa ba

fira suke gwanin sha'awa don dama haka sukeyi sutaru dakin kaka suyita fira

zama yayi gefen Habeeb yana maida mashi martanin barka dayake mashi

nan ya cigaba da sauraron firarsu wanda duk na komawar su Abba Nigeria ne don gobe zasuyi tafiyar tareda su daddy da mummy

agogon hannunshi ya kalla sai yadago ya kalli Aysha dake kusada kaka

da harshen turanci yace
"Aysha anjima bayan isha'i kushirya keda Lailah nakaiku shopping"

wara idanu Aysha tayi cikin murna
"dagaske Akhie?"

harararta yayi
"dawasa"

dariya mutanen falon sukayi

ummie tace
"wai nikam tana inane lailan? duk yau banganta ba"

kafin kowa yayi magana mussadiq ya amsa da
"tana garden"

duk kallonshi sukayi harda Deen dake danna wayarshi saida yadago ya kalleshi

tashi yayi yafara shirin fita not minding kallon da mutanen falon keyimashi yace
"karku sani jira ok?" yafada reffering to Aysha sannan yafita

kallon juna mutanen dakin sukayi saikuma sukayi murmushi sannan suka dora da firarsu kowanne da tunanin dake zuciyarshi


BAYAN ISHA'I


kallonshi yake harya gama shiryawarshi ya feffesa jikinshi da turarrukanshi sannan yajuyo suka hada ido

daga gira daya yayi
"what?"

murmushi Deen yayi
"babu komai Kawai am smelling something fishy ne"

"to? akan me kenan?"

tashi zaune Deen yayi sosai sannan yace
"is there something you're hiding to me about Lailah?"

wani kallo yayi mashi
"as in?"

"dazu kace tana garden, ya akayi kasan tana can?"

"saboda tare muke acan" yafada yana dan ta6e baki

wara idanu Deen yayi cikin murna
"as I thought! kenan you two are dating! wow!"

harararshi mussadiq yayi
"ni nafada maka hakan?"

"saika fada? wow amma natayaka murna don Lailah mace ce mai hankali sosai"

"ina ruwanka ko mahaukaciya ce? bansan sa ido" yafada yana harararshi

riqe baki Deen yayi yace
"to? abin yar haka ce"

"eh din, ka tsaya kasamu kaji da wancan mai taurin kan taka karka qara shiga sabgata banaso" yafada yana gallamashi hararar wasa

nan da nan Deen ya hade fuska jin anta6omashi jewel dinshi

"I've warned you times without number karka sake kushemin mata"

kallon dage mussadiq yayimashi
"da wa yabaka? ji qarfin hali, kama samu tafara kulaka" yafada yana mashi dariyar shaqiyanci

"waya cemaka bata kulani? ina ruwanka ma.idan bata kulani? bana hanaka shiga sabgata daita ba?" inji Deen cikin hade girare

"bakaso nashiga taka kashiga tawa?"

"to karka qara shiga tawa nima babu ruwana da taka"

"better" inji mussadiq yana kwama shade dinshi yafita yana dariya

kwafa Kawai Deen yayi yakoma ya kwanta jawo wayarshi don dama jira Kawai yake yafita yabashi wuri yasamu yin wayarshi hankali kwance don dama Habeeb na can part din kaka


cikin kwana biyunnan yafara samu zee na kulashi sama sama saboda nacin dayake mata

kusan kodayaushe saiya kirata ga lots of romantic SMS dake turamata akai akai

yanzu ba laifi relationship dinsu yafara farfadowa don abin ba yabo ba fallasa dukda bekai nada ba amma yana hango cewa zasu koma kamar da koma wucenan very soon


a bangaren su mussadiq kuwa tare suka fice gidan dashi da Lailah da Aysha

Lailah tayi mammakin jin zasu shopping din datayi, dafarko taso qi saida mamy ta tilasta mata sannan tashirya badon tasoba

har lokacin kwalwarta a birkice take akan magangganun mussadiq, takasa kaudasu daga kwalwarta sai sake bitarsu take tanason fahimtar every single word dayace

koda suka fito ta hangoshi a jikin motar saida gabanta yafadi don sosai yayi wani irin kyau cikin shigarshi ta larabawa sak

hakan yasata sauke kanta qasa bata qara yarda ta kalleshi ba saboda yadda zuciyarta ta chanza bugu adalilin ganinshi

back seat taso ta zauna amma Aysha tarigata hakan yasata bude front seat badon tasoba tashiga ta zauna ta maido kofar tarufe


tunda tashigo daddaden qamshin turarenshi ya ziryarci hancinta wanda ya saukar mata da nutsuwa nan take

komawa tayi jikin kujerarta ta lumshe ido ta cigaba da shaqar qamshin nashi, ahaka yaja motar suka bar gidan


babban shopping mall yakaisu, dukda yanadasu dayawa hakan besa yaje daya daga cikin nashi ba don shi dama haka yake he hates attention don yasan idan yaje cikin nashi dole a dakatar da siye da siyarwa har saiya gama yatafi hakan yasa ko shopping din takama zaiyi bayayi cikin nashi dukda da wuya ma yafita shopping komai order yake badawa akawomashi har gida

shopping sukayi sosai inda dafarko Aysha kadai keyi ganin hakan tayima Lailah dataqi daukar komai magana akan ta dauki abinda takeso mana

batajin shopping din don ita dukma atakure take saboda komawa gefen da mussadiq yayi ya rungume hannu yazubamata ido

talura mutumin nan ya iya kallo sosai babu ko irin basarwa dinnan don ko juyowa tayi takamashi yana kallonta baya janye ido

ahaka tadan tsinci abubbuwa yan kadan ganin hakan yasa mussadiq qarasowa dakanshi yafara za6armata abubbuwan dasukayi mashi

sosai mammaki ya kasheta ganin yadda yazage yana zazza6omata kaya yana lodamata a basket dinta hakan yasa tama kasa motsi a inda take

Aysha kau dama tana ganin hakan tayi saurin wucewa da nata basket din zuwa wani bangaren tana murmushi

kaya yake xa6armata masu mugun kyau kowanne hade da set din handbag da shoes dinsu har mammakin yadda,ya iya za6e take don ko ita albarka

saida yagama lodamata iya son ranshi sannan yayi gaba

binshi da kallo tayi batareda ta ko motsa ba shikau jin kamar bata biyoshi ba yasashi dakatawa ya juyo

hada ido sukayi tayi saurin janye nata

"c'mmon let's go" yafada yana kafeta da idanunshi

kasa musa mashi tayi hakan yasa tafara takowa batareda ta taho da basket din ba

ganin hakan yasashi dawowa ya jawo basket din yafara turawa sukayi bangaren turarruka

nan ma cewa yayi ta za6a saita dauki biyu batareda tama tsaya tantancesu ba tajefa cikin basket din hakan yasashi girgiza kai sannan yadawo gaba yafara za6armata yana tilamata su ciki, itadai kasa cewa komai tayi sai kallon bayanshi datake, she was wondering wannan besan zafin kudi bane? don daukar kayan yake yadda kasan ba biya zaiyi ba


ataqaice dai haka sukayi shopping din inda duk mussadiq yayimata, saida suka gama tsaff sannan suka wuce wurin cashier yabada a.t.m dinshi suka zare kudinsu

daga nan kuma suka nufi Icecream joint inda yasiyo masu snacks da Icecream sannan suka juyo gida

koda suka isa gida saida kowa yayi mammakin siyayyar daya yiwa Lailah,don sunyi over hakan yasa kowa qara gasgata tunaninshi akansu


Lailah ma ranar kasa janye tunanin fitarsu tayi, kwata2 tunanin gayen yaqi barin kwalwarta don tadade batayi barci ba tanata juyi zuciyarta fall tunanin mussadiq sa6anin na Deen datakeyi kullum.


WASHEGARI


kasancewar jirgin qarfe shabiyu zasubi yasa suka isa airport din tun 11 da yan mintuna

anan suka hade da family din zee ma dasuka rakosu daddy da mummy suma


sosai hira ta 6arke atsakaninsu don wuri daya suka zauna suna jiran agama every necessary thing dayakamata kafin lokacin tashin jirgin yayi


masu tafiyar acikinsu sune daddy, mummy, Abba, mamy, Habeeb da Lailah

kaka kau ba yanzu ba don da ita za'a daga saudiya😜


iya manyan Kawai ke firarsu while su qannanun suna zaune shiru sai exchanging kallo dasuke tsakanin juna


zee na zaune kusada Umminsu Aysha don tunda sukaxo ummie tajawota tazaunar daita kusada ita wanda hakan yasa takasa ko dago kai don sosai takejin kunyar ummie


a inda take zaunen tana jin hasken idanunshi akanta amma taqi dagowa tana kuma jin yadda wayarta ke beeping kai da kai na shigowar saquna taqi dubawa don tasan ko ba'a fada shine

a bangaren mussadiq ma ya tusa diyar mutane da kallo inda itama ta takura sosai da kallon qurillarshi

a bangaren batool kau tana gefe suna chatting da Ahmad da baisamu zuwa rakiyar ba saboda wata tafiyar dayayi tun shekaran jiya, shagala datayi da chatting din taqi bin Aysha data tashi zataje siyen ruwa mai sanyi saboda qishin datakeji

Aysha kadai tatafi tasiyo ruwanta bayan ta fadawasu ummie

saida tagama siyayyarta tajuyo zata taho sukaci karo dawani gorar ruwan ta sun6ule tafadi

"oh.. sorry" mutumin dasukayi karon yace yana sunkuyawa ya daukomata ruwan nata yatashi yana miqamata

ganin Aymaan ne yasata dan buda ido saikuma tasa hannu ta kwace gorar adan masife tana harararshi

"kuma ka iya kiran wani clumsy while you're clumsy yourself" tafada tana qara gallamashi harara tazo wucewa

riko hannunta yayi wanda hakan yasata saurin juyowa tana zaro idanu

"waye clumsy din?" yafada cikin hade

"let go of my hand" tafada adan tsorace tana qoqarin kwace hannun

"nine clumsy din?" yafada yana eyeing dinta batareda yasaki hannun ba

6ata fuska tayi kamar zatayi kuka har lokacin tana kicininyar kwace hannunta cikin rawar murya tace
"ni..ni kasake min hannu"

ganin dai da alamu kukan zatayi don har manyan idanunta sun duri ruwa yasa ya saketa yana cewa
"kika qara bin hanyar danabi saina tsonemiki wadannan idanun"

fashewa tayi da kuka tana saurin toshe bakinta sannan tabar wurin dasauri

sakin baki yayi yabita da kallo donshi bega abin kuka ba anan, saida tayi nisa sosai sannan tajuyo ta gallamashi harara da wet idanunta ta murgudamashi baki sannan tajuya,tabar wurin dasauri kamar wadda aka biyo

kasa daurewa yayi saida yasaki dariya marar sauti, lallai ashe dai wannan yarinyar matsoraciya ce? kwafa yayi Kawai yajuya ya qarasa wurin don siyen abinda zai siya don dama shima yabaro can ne don yin sayayya, izuwa yanzu yarage jin yadda yakeji towards zee wataqila allah ne ya qar6i addu'arshi don sosai wutar soyayyar zee tarage azuciyarshi kuma izuwa yanzu yagane cewa zee ta Deen ce kuma ya rage jin wannan zafin dayakeji duk lokacin daya gansu atare


siyayyarshi yayi yakoma can wajensu inda sai shirye shiryen tafiya su daddy keyi don jirgin yakusan tashi

tunda Aysha taga dawowarshi takoma bayan mussadiq don ya kareta don batason ma ganinshi kuma data dan leqo sai sun hada ido yayimata kallon zamu hadune saitayi saurin sake la6ewa abayan mussadiq

shidai mussadiq besan sunayi ba hankalinshi nacan kan Lailah

ahaka suka shiga bankwana inda zee kamar tayi kuka don sai jitayi tafara missing dinsu daddy tunma kafin sutafi

ahaka suka tafi suna dagawa juna hannu cikin mixed feeling suna binsu da addu'ar safe journey

Lailah duk yadda takejin idanun mussadiq akanta qin kallonshi tayi tajuya suka wuce

saida takai daidai kofar dazata shiga sannan tajuyo idanunta suka fada cikin nashi

murmushi ya sakarmata ahankali itakuma tayi saurin juyawa tashige.


ahaka suna tsaye har jirgin nasu yadaga ya lula sama


*AGURGUJE*


kingin ranakun sunzo suntafi very fast inda su Deen keta shirye shiryen tafiyarsu zuwa saudiya


sosai Deen ke doqin tafiyar don he can't wait yataka qasarshi ta haihuwa

a bangaren soyayyarsu da zee kuwa kullum qara cigaba ake samu don da alamu zee tagaji dajan ajin tafara bada kai sosai suke shan soyayyarsu tawaya saidai idan yajene bata cika sakin jiki dashi sosai ba kamar dai da


ranar daren tafiyar tasu sukaje gidansu Aymaan din don suyi bankwana

inda suna zuwa Deen yasamu ya ke6e da zee a garden suna zance sukuma Aysha sukayi sama tareda batool

sundan jima agidan kafin sufito zasu tafi inda su Aysha sukayi gaba ita da batool zasu fita suna gulmarsu zee wai suna can suna soyewa suga love birds

abakin kofa sukaci karo da Aymaan da dawowarshi kenan daga asibiti inda ganinshi kamar daga sama yasa Aysha fasa qara takoma falon aguje

da mammaki duk akabita da kallo harta qarasa wajen kaka ta la6e bayanta

girgiza kai Aymaan yayi Kawai yashiga don qararta ma firgitashi tasoyi, yawuce yabar batool dake tsaye cikeda mammaki abakin kofar

sadda yashiga ciki ya tadda anata tambayarta meye takema ihu

ganinshi yasata qara la6ewa bayan kaka Kawai tana turo baki

shidai bece komai ba yaqaraso yana gaidasu Ummie da murmushi

anan yaji ashe gobe zasu wuce saudiya

fatan sauka lafiya yayi masu sannan yawuce sama yana hararar Aysha dake la6e still abayan kaka ta gefen idanu


har parking space suka rakosu suna masu fatan isa lafiya


saida suka shiga motar suka ja suka tafi sannan suma suka juya ciki batool nata tsokanar zee


*SAUDI ARABIA*


lafiya lau suka sauka garin saudiya, fatherland din Deen inda yana taka qasar shima yaji eh wannan fatherland dinshi ne

farincikin daya tsinci zuciyarshi aciki baya misaltuwa don ganin abin yake Kawai kamar amafarki


twin din Abbansu Deen wato Al-hussain Kawai yasan da zuwansu kuma shi yaje tarbonsu a airport

saidai ganin mussadiq biyu ba qaramin burkitamashi kwalwa yayiba don shima kwata2 besan da bayyanar Deen ba

saida sukaje gida sannan sukayi mashi bayani dalla dalla inda fadin farincikin daya shiga ma 6ata lokaci ne sai godiya da kirari yake kwararawa allah mai yin yadda yaso maikuma maida abu marar yiwuwa abu mai yiwuwa

kaka kau tasha godiya da addu'o'i awajenshi kamar ya ari baki

haka suka kwana batareda sanin kowa a family dinba don Al-hussain yace kar agayawa kowa shida kanshi zai qirqiri family meeting gobe inda anan za'a bayyana Deen


haka kau akayi don nan take aka sanar da gobe akwai family meeting wanda dama abune da akeyi duk in wani abu yataso


Washegari a family meeting din inda babu wanda be hallara ba aka gabatar da Deen inda suka shigo shi da mussadiq cikin shiga iri daya


fadin hautsinewar da wurin yayi 6ata lokaci ne don nan take wurin ya rude

inda sai bayan Al-hussain ya gabatar da Deen amtsayin mujaheed daya 6ace awajen asiri yafara tonuwa inda matar Al-hussain ta tashi tana ihu tana bori wai qaryane mujaheed ya mutu saida aka tabbatar mata da hakan, wannan ba mujaheed bane mujaheed yamutu

nan hankali yadawo kanta don sosai mutanen wajen suka cika da mammakin ganin yadda take ihu tana sambatu inda acikin sambatun ta tonawa kanta asiri

asali dama matar Al-hussain bata qaunar Zainab matar al-hassan kwata2, wannan tsanar tasamo asaline tun lokacin dasuke amare kasancewar dama atare al-hassan da Al-hussain sukayi aure inda Zainab matar al-hassan tafi matar Al-hussain farinjini

sosai danginsu Al-hussain sukafi sonta saboda saurin shiga ranta da kirkinta

Duk abinda za'ayi itace kan gaba hakan yasa matar Al-hussain fara yimata hassada tana ganin duk ta saye soyayyar dangin mazajensu


matar Al-hussain tariga Zainab haihuwa don saida tayi haihuwa biyu kafin Zainab ta haihu saidai ga haihuwar Zainab anfi murna yadda kasan ba'a ta6a haihuwar jika a dangin ba hakan yaqara tunzura matar Al-hussain

abin be ida kasheta ba saida taga irin soyayyar da ake nunamasu mussadiq saboda wani irin jidasu akeyi a family din kamar su kadai ne jikoki kowa burinshi ya daukesu ga kyaututuka dasuke samu kota ina akai akai gashi kuma dama Al-hassan yafi Al-hussain wadata alokacin sai abin yataru yayimata yawa

ganin bazata iya cigaba da qunsar baqincikin bane yasata Kawai shirya tagayyara family din Al-hassan din inda da zugar wata qawarta suka sa akayi kidnapping dinsu inda basu samu nasarar daukarsu su biyun ba don allah ya ku6uto da mussadiq sai sukayi garkuwa da mujaheed (Deen)

duk tashin hankalin dasuka shiga alokacin matar Al-hussain jitake kamar ta taka rawa, sosai taji dadin ganin burinta na tarwatsa ahalin Al-hassan yafaru hakan yasa tama yanke shawarar salwantar da Deen a 6addashi daga doron qasa don su dawwama a baqinciki don sun lura sosai sukeson Deen


saida tasa aka amshi kudadde dayawa wajen Al-hassan sannan tasa a qone Deen acikin motar da xasu sashi ciki agaban idon Al-Hassan

hakan kau yafaru saidai abinda bata saniba shine alokacin jisukayi bazasu.iya qone Deen Acikin motar ba don he's way too innocent aganinsu be kamata yayi irin wannan mutuwarba hakan yasa Kawai suka jefashi aruwa aganinsu wannan mutuwar zatafi sauki


tofa! sosai hankalin family din yatashi jin sambatun matar Al-hussain

babu 6ata lokaci Al-hussain dayafi kowa rudewa alerting jami'an tsaro inda babu 6ata lokaci akazo akayi ramm daita aka wuce daita

sosai family din suka shiga tashin hankali sai koke koke akeyi, shikanshi Al-hussain kasa tsaida hawayenshi yayi don sai alokacin komai kedawo mashi fresh, wannan wace iriyar matace yake zaune daita tsawon shekaru? sosai kowa ke mammakin abinda ta aikata don koda wasa batayi kama da wadda ke iya aikata rabin abinda ta aikata ba

shima Deen sosai jikinshi ya mutu musanmman yadda yaga kowa nata rungumarshi ana kuka, kakarsu wato ainahin mamansu babansu babu wanda yakaita kuka tabi ta rungume Deen qamm kamar za'a kwace mata shi tanata sambatu cikin larabci


saida hankali yadan kwanta sannan suka nemi jin yadda Deen ya bayyana inda anan akayi musu bayanin komai

zokuga yadda akema kaka godiya kamar zasuyimata sujjada, addu'o'i kau aranar tashasu don acewarsu ba qaramin jihadi tayiba kuma sakamakonta na gun allah don dik abinda zasuyi mata bazasu iya biyanta ba...✍�


Ummin fasihu🧚🏻‍♀�
8/19/21, 6:46 PM - Buhainat😝: *🙍🏻‍♂️DEEN🙍🏻‍♂�*


*100*


*FINAL🤸🏻‍♀�*


Satinsu Deen biyu a saudiya inda acikin wannan sati biyun babu inda basu shiga ba domin zagayen dangi sai alokacin Deen yasan cewa ashe shi d'an dangi ne domin yanadasu ba adadi gashi sai nunamashi wani irin soyayya sukeyi suna jidashi suna riritashi kamar kwai


idan yajuya yatuna da rayuwarshi tabaya yayi comparing dinshi data yanzu saiya godewa allah bisa ni'imomin dayayi mashi, abin har mammaki yake bashi wai shi da tun tasowarshi beda kowa beda wanda zai kalla ya kira nashi bayan kaka amma yanzu jibeshi xagaye tsamo tsamo cikin dangi dangin ma masu tsananin qaunarshi, dole ya godewa allah


kaka ma abangarenta tasamu babban matsayi a wannan dangin don sosai suke qaunarta suke kuma girmamata, tuni suka qulle da ainahin kakarsu Deen suka xama kamar wasu aminnan juna

a bangaren matar Al-hussain kau tanacan anmakata kotu da ita da qawarta dasukayi qulle qullensu tare bayan Al-hussain ya yanke igiya daya ta aurenshi dake kanta


Satinsu biyu a saudiya suka daga zuwa misra garinsu ummie inda anan Deen yaqara ganin tsantsar qauna da tarairaya

kowa soyake ya kasance taredashi kowa soyake yanuna yadda yake qaunarshi hakan yasashi zama kamar wani cele acikinsu


Satinsu daya a qasar suka barota suka dawo Dubai inda dama Deen allah allah yake yadawo don sosai yayi missing *jewel* dinshi kamar yadda yasamata suna yanzu dukda kullum suna maqale awaya


a bangaren zee ma sosai take missing baby boo din nata, rabonta dashi tun daren dazasu tafi saudiya gashi ba video call sukeyi ba bare su dinga ganin juna hakan yasa tayi wani irin missing dinshi, kullum idan suna waya saita dinga damunshi kan yaushe xai dawo saidai yace mata very soon insha allah


relationship dinsu yanzu yayi improving sosai don har yana neman fin na da don sosai suke zuba soyayya mai tsayawa a qwalwa


shaquwarsu tada tadawo tama ninka nada don wani lokacin ma idan suna jin yan shiriritarsu haka zasu dinga musayar kalaman soyayya ta sigar waqa atsakaninsu ta waya

yanzu zee ita kanta tasan bazata gwadama Deen komai ba akan waqa don har mammaki yake bata idan yazaro mata wani baitin

daya daga cikin dream dinta na neman tabbata don aduniya tanason waqa tana kuma dreaming tasamu wanda ra'ayinsu zaizo daya suyita tisa kansu agaba suna zubama juna baitika


Yau tunda ta tashi takejin kanta cikin wani irin happy mood don Kawai tsintar kanta tayi dawani irin nishadi ayau din

kowa ma na gidan ya shaida haka don qarara hakan ya bayyana a fuskarta da ayyukanta don tariga kowa nagidan tashi saidai suka tashi sukaga tama kusan gama aikace aikacen gidan

haka tawuni cikin nishadi don abu kadan saita fashe da dariya dana dariya da wanda bana dariya ba har batool na tsokanarta kodai she needs psychiatric doctor ne? itadai Kawai saidai tayi dariya tace yau Kawai tana cikin nishadi ne without knowing why


da daddare bayan isha'i suna zaune cikin dakinsu suna kallon wani series film cikin laptop din batool wayar zee tayi ringing

ringing dinne yan dawo dasu daga duniyar kallon dasuka bada dukkan hankalinsu akai

"mtcheew don allah shut that phone up tana distracting dina" inji batool idanunta akan laptop din batason ko janyesu daga kan screen din

harararta zee tayi tasa hannu ta danna ma film din pause wanda hakan yasa batool tashi zaune azabure

"haba meye haka?" tafada a little upset


"saina gama wayar zamu cigaba" tafada tana jawo wayar dake gab da tsinkewa

danna play batool tazo zatayi zee ta suri laptop din ta miqe tsaye tana mata gwalo

itama miqewar tsaye tayi tafara kiciniyar kwace laptop din da zee ta6oye abayanta zee na zillewa tana dariya

ahaka har kiran ya tsinke bata saniba wani yaqara shigowa

dira zee tayi daga kan gadon still laptop din abayanta tana son rugama batool dake qoqarin kamota

dago wayar hannunta tayi da niyyar kasheta ma gabadaya don taji dadin rigimar dasukeyi da batool don dama sun saba saidai number data gani na yawo akan screen din yasata yin still tana waro idanu

batool dabata lura da yanayinta ba tasamu ta kwace laptop din tana
dariya tana cewa
"got yah!"


"OMG!" inji zee tana kallon wayar idanu abude

"meye?" inji batool tana matsowa

bata amsa mata ba sai daga wayar datayi takara akunne ahankali

sallamarshi dataji cikin cool voice dinshi ya ida tabbatar da zarginta, Deen is back!


sauke wayar tayi saurin yi ta katse kiran sannan ta wawuro batool dake gabanta tawani irin rungumeta tana ihun murna

"he's back! he's back! OMG!"

saurin qwace kanta batool tayi tana cewa
"wai meye haka? who is back?"

cikin tsananin murna tace
"my boo mana! kalla da number nan yakirani, wayyo! what a surprise!" tafada tana juyi

tsaki Kawai batool taja takoma kan gadon tana bude laptop din

saita kanta zee tayi kafin taqara daga kiran daya sake shigowa

"hello?"


taji anfada daga dayan bangaren

"hello... is this for real?" tafada ahankali cikin yanayin mammaki

sautin murmushinshi tajiyo sannan yace
"kifito and see for yourself"

"infito ina?" tafada tana dan wara idanu

yar dariya yayi sannan yace
"waje, ganinan a parking space kizo kiyimin iso"

"are.. you serious?"

yar dariya Kawai yayi yace
"saikin zo" daga haka ya,katse kiran

dungule hannayenta tayi tana ihun murna sannan tayi wani juyi tafada kan batool dake kallon ta

"wai meye haka?" inji batool tana tureta daga jikinta

"wai yana waje, what a huge surprise!" tafada cikin tsananin murna

harararta batool tayi tace
"ji gulma, kamar irin batasan dazuwanshi ba dinnan. ashe ba banza ba duk wunin yau baki yaqi rufuwa ashe kinsan abinda kika taka"

"ji banza, wlh bansan da zuwanshi ba"

ta6e baki batool tayi tana maida hankalinta akan laptop din gabanta tana cewa
"saikiyi"

dunguremata qeya zee tayi tana cewa
"banza joy killer Kawai" ta tashi tanufi closet dinsu tabude


cikin qanqanin lokaci tashirya cikin wata baqar abaya ta yafa gyallenta in a simple way tadan gyara fuskarta sannan ta feshe jikinta da turare

zuwa tayi taqara dungure ma batool kai tana cewa natafi sannan tajuya tawuce dasauri

kwafa batool data dago tana kallonta tayi sannan ta maida hankalinta kan abinda takeyi


fitowa tayi daga falon sannan tafara takowa ahankali ta entrance din tanufi parking space hoping badai tsokanarta yakeyi ba bezo ba


wata baquwar ash colour motar data gani pake a parking space din yasata jin wani irin sanyi na ratsa zuciyarta

ahankali take takawa tana nufar wajen inda ko rabin kaiwa batayi ba aka bude murfin kofar daga bangaren driver yafito


tsayawa tayi daga tafiyar datake tana kallonshi yana zagayowa dayan side din motar

bata ta6a sanin har haka tayi missing dinshi ba sai yanzu, jitake kamar sun shekara basu hadu ba gashi yawani chanza yaqara yin fresh dashi


shima bangaren Deen hakan take don shima sosai yaji yayi kewarta kuma ta chanza mashi sosai cikin dan lokacin dasukayi basuga juna ba


ahankali ya sakarmata wannan cool murmushin nashi itama saita tsinci kanta da mayar mashi da martani

ahankali yashiga takowa zuwa ina take tsaye hakan yasa ta cigaba da kallonshi abubbuwa dayawa nakai kawo azuciyarta

komai nashi na daban ne hatta tafiyarshi, komai nashi cikin nutsuwa yakeyi, kai she love this guy!

saida yaqaraso gabanta ya tsaya yana dan bada tazara atsakaninsu

kallonta yakeyi da oily eyes dinshi fuskarshi dauke da murmushi, kasa cigaba da jurar kallon tayi hakan yasata sauke nata idanun qasa tana d'an murmushi

"wow! you're welcome, dama yau zaka dawo baka fadamin ba? kai amma am very happy and surprise altogether, I missed you so much" inji Deen yana kallonta

dagowa tayi ta kalleshi tana dan daga gira

shima daga gira daya yayi yace
"koba haka kikeda niyyar cewa ba?"

harararshi tayi
"to ba haka nayi niyyar cewa ba, besides fushi ma nake dakai, ashe yau zaku dawo amma shine baka gayamin ba kuma har waya munyi dasafe?"

yar dariya yayi yace
"it's a surprise, yanzu da kika ganin kamar daga sama ba kinfi jindadi ba?"

kauda kai tayi tace
"ni banwani jindadi ba"

"ai bake zaki fadi jindadinki ko rashin jindadinki ba, fuskarki zata bayyana kuma tariga ta tonamiki asiri"

harararshi tasakeyi sannan tajuya
"muje"

"to ranki shi dade"

murmushi Kawai tayi suka jera atare suka nufi cikin gida


zee tafara shiga falon sannan tayima Deen iso shima yashigo ciki bayan ya cire takalminshi saura baqaqen socks akafarshi bakinshi dauke da sallama


falon babu kowa sai qamshin dake tashi afalon

nunamashi wurin zama tayi ya qaraso ya zauna ahankali ita kuma tawuce kitchen

ba dadewa tadawo da dan tray mai dauke da ruwa da drinks tazo ta ajiye akan stool din dake kusada kujerarshi

dagowa tayi ta kalleshi saitaga shima ita yake kallo ya sakarmata murmushi

kauda kai tayi itama tana murmushin tace
"bari nakira ummy"

"nabari" yafada yana kallonta

juyawa tayi tawuce sama tanajin idanunshi kanta


saida tahaye sama sannan ya daina kallon stairs din sannan yakoma ya jingina da kujera yana murmushi kai da ganinshi kasan yana cikin farinciki sosai


ba'a jima ba yaji motsin saukowarsu hakan yasashi dagowa yaga ummy agaba zee biyeda ita

cikin murmushin kunya ya miqe tsaye ya dan sinne kai har suka qaraso falon

"A'a? maraba da mutanen saudiya, saukar yaushe?" tafada tana qarasawa ta xauna

russunawa Deen yayi yana gaisheta cikin sinnar dakai

amsawa tayi cikin kulawa tana cewa ya zauna

maimakon yakoma ya zauna kan kujerar daya taso saiya zauna nan qasan carpet din

"A'a? ka koma sama mana" inji ummy

"A'a nanma yayi ummy" yafada akunyace

"to ya hanya? ya mutanen saudiyan?"

"alhamdulillah ummy duk suna gaidaku"

"muna amsawa, yasu kaka?"

"kaka na gida tana gaisheku itama"

"muna amsawa, fatan kundawo lfy"

"lfy qalau ummy"

"to madallah... daughter kawomashi abinci kinji"

dasauri yace
"A'a alhamdulillah ummy"

"to bari nahau sama, let me know idan zaitafi Zainab"

"to ummy" Zainab dake tsaye bayan kujerar ummy tundazu ta amsa

ummy ta tashi tawuce sama

ajiyar zuciya Deen yasauke bayan hayewarta sannan yadago ya kalli zee

dariya tadanyi
"kamar na allah" tafada tana dariya

dan wara idanu yayi
"to da na wanene?" yafada yana tashi yakoma kan kujera

itama dawowa tayi gaban kujerar da ummy ta tashi ta zauna

"wow! I missed this girl so much, kinsan daga saukarmu wanka Kawai nayi na chanza nayonan? I just can't wait to set my eyes on you"

murmushi zee tayi
"miss you too"

"A'a banga alama ba, naga nikadai ma ke doqi na"

"haka dai kace"

"hakane ma"

"to ya hanya? hope kun iso lfy"

"lfy lau wlh, hope munsameku lfy"

"lfy lau, so how's saudi?"

"alhamdulillah, duk lfy.. kinsan wani abu?"

girgiza kai zee tayi

"banta6a sanin haka mutum kejiba idan yana cikin family dinshi ba saida muke saudiya... wai nine tsamo tsamo cikin mutane kuma wai family dina, wlh ko amafarki banta6a hangowa kaina haka ba, jinike kamar ba gaske ba..I was just so overwhelmed.. banta6a sanin haka family keda dadi ba.. ranakuna a saudi da misra are one of my best moment ever"


Zainab kasa daina murmushi tayi tunda yafara magana, kallo daya zakayimashi kasan he mean duk abinda yake cewa, sosai farinciki ke bayyane afuskarshi, sosai taji tana tayashi murna da hakan don wannan abin abin atayashi murna ne

"congratulations, aidama family nada dadi bazaka gane hakan ba sai kana cikinsu, gaskiya ina tayaka murna, am very happy for you"

murmushi Deen yayi sannan ya kalleta
"and all these happened because of you, har duniya ta nade bazan ta6a mantawa da mutane biyu ba arayuwarta, dake da kaka. kun taka rawar gani arayuwata sosai

kaka ta ku6utar dani takuma raineni cikeda so da qauna batareda tasan koni waye ba, takuma zamemun kowa alokacin dabanida kowa kekuma kinyi silar dawomin da komai dana rasa arayuwata, kindawomin da asalina kin dawomin da kowa nawa... tayaya za'ayi namanta daku Zainab?"

sauke idanunta zee tayi tana murmushi don kallonta yake directly in the eye, maganarshi yasata jinta very emotional har tanajin kamar ta zubda mashi kwalla

ahankali tace
"you know.. komai muqaddari ne daga allah,allah yariga ya qaddara baxaka tashi cikin danginka ba yakuma qaddara xakayi rayuwa nesa dasu sannan ya qaddara cewa a irin wannan lokacin zaka dawo garesu, daga ni har kaka Kawai kamar tools ne na gudanar da abinda allah ya tsaramaka..allah yariga ya qaddara kaka ce silar raboka da danginka dakuma qasarka while nikuma ya qaddara nice silar hadaka dasu bayan shekaru masu yawa, so muma ba wayonmu bane Kawai hakan is destined don haka allah yakamata ka dinga godemawa domin ba qaramar ni'ima yayimaka ba, akwai mutane da dama irinka basu rayu dakowa nasuba kuma harsu koma ga allah,basu ta6a komawa ga nasu saidai ko a lahira saboda basuda rabon ganawa a duniyar kaiko kanada rabon sake ganawa da danginka aduniya, kanada rabon ganin mahaifiyarka wanda tun tashinka baka Santa ba, meyakai wannan? so ka cigaba da godewa allah domin ba qaramar ni'ima yayima ba"

sosai magangganun zee suka sanyaya jikin Deen, hakane yanada rabon sake ganawa dasu ne shiyasa komai yafaru a yadda yafaru, da beda rabon ganawa dasu da qila be hadu da zee ba bare har ta silarta yasan asalinshi da ahaka zai qare rayuwarshi besan yanada mahaifiya ba a duniya, babu komai a maganar zee sai tsantsar gaskiya don yanada gashi dayake beda rabon haduwa da abbanshi saigashi shi bayanan, yatafi. qila shikuma sai acan, yana kuma fatan allah ya hada fuskokinsu a aljanna

"alhamdulillah.. alhamdulillah rabbil a'alamin... alhamdulillah bi ni'imatika alayya" yafada ahankali saikuma yadago ya kalli zee da idanunshi dasuka kada sosai

"marry me please... don allah kibari na mallakeki"

wara idanu zee tayi saidai kafin tayi magana haryakai kan knees dinshi
"please marry me"

qara wara manyan idanunta tayi in shock

"Deen.."

"am proposing the second,time, will you marry me?"

"Deen get up"

"saikin amsa min"

"Deen.."

"I mean it"

"ok..ok" tafada stana furzar da huci

"YES"

wani irin wara idanu Deen yayi
"dagaske!"

saiya tashi yadawo kan kujerar datake hakan yasata dan ja baya

"dagaske?"

"eh..eh" tafada tana qara jabaya

"yaushe? gobe? jibi? inkoma ingayama ummie ta,turo gobe ayi komai?"

tashi tayi tana kallonshi idanu aware

"aturo ina? are you serious?"

"anan mana, look barima natafi yanzunnan" yafada yana tashi

saurin shan gabanshi tayi
"ina zaka?"

"wurin ummie mana dole nafadamata yau asan yadda za'ayi agama komai on time"

"mene? are you alright? ina kata6a jin anyi hakan? Kawai daga cewa yes shikenan?"

"to me zamu jira?" inji Deen kamar zaiyi kuka

"bakaga karatu nake ba? saina gama ko ana tada wata magana"

tsayawa yayi yana kallonta kamar wanda ake fadawa mugun abu

"ka..me? Zainab sokike ki kasheni?"

"na kasheka kamar yaya?"

"Zainab bakiji abinda kikace ba? wai saikin gama karatu lokacin na sheqa kenan, haba wasane ma wannan"

"kaike daukarshi wasa but am damn serious" tafada da iya gaskiyarta


tsayawa yayi yana kallonta for some seconds saikuma yayi murmushi yace
"to ai shikenan, we shall see.. ki yima ummie magana nizan tafi"

"kamar ya we shall see? me kake nufi da hakan?"

"time will tell, yanzu dai kiyiwa ummy magana bari nashigo muku da tsarabarku" yafada yana juyawa yafice daga falon fuskarshi dauke dawani murmushi dashi kadai yasan ma'anar kayanshi

tadan jima bayan fitarshi atsaye cikin jujjuya maganar Deen sannan ta girgiza kai tahau sama don kiran ummy

tareda ummy da batool suka dawo inda tundaga sama suke hango akwatinan biyun da Deen ya ajiye atsakar falon

wara idanu duk sukayi suna ida saukowa ummy na tambayarshi wadannan kayan fa

murmushi Kawai yayi yace
"tsarabarku ce ummy, ayi hqr"

mita ummy tafara akan kayan sunyi yawa daga baya kuma takoma godiya

sai alokacin suka gaisa da batool itama tana mashi godiyar tsarabar

anan sukayi sallama ummy taba zee ledar data sauko daita tace tabashi yaba kaka


Deen yayi godiya yajuya yafita zee na bayanshi don yimashi rakiya

saida suka isa parking space sannan yajuyo yana kallon zee itakuma ta miqamashi ledar da ummy tabata tana mashi godiyar tsarabar

murmushi Kawai yayi daidai xaiyi magana mota tashigo gidan


tsayawa sukayi suna kallon motar harta qaraso wajen parking din ta parka

Aymaan da abbu ne suka fito daga motar

sunyi mammakin ganin Deen sosai don basusan da dawowarsu ba

har qasa ya tsugunna ya gaida abbu cikin girmamawa sannan sukayi musabaha da Aymaan

nan suke tambayarshi saukar yaushe yace yau

sudan dauki lokaci suna dan ta6a fira kafin suyi sallama su shige ciki

bankwana suka sakeyi da zee sannan yashige motar yatada

zee na nan tsaye haryaja yafice daga gidan sannan tajuya takoma ciki

koda takoma ciki iskewa tayi duk suna falon sunata duba kayan da Deen yakawo

akwatina biyune da qarami da babba, kallo daya zakayiwa kayan qaramun akwatin kasan na zee ne inda dayan kuma yayima kingin yan gidan

sosai suke yaba kyawun kayan harda Aymaan wanda yanzu alhamdulillah bayajin komai gameda relationship din zee da Deen don sosai allah ya sassautamashi yakuma sa yayi facing din gaskiya cewa zee fa ta Deen ce. cikin ikon allah yarage jin yadda yakeji sosai akan zee don yanzu yama fara hasasowa kanshi wata, tunaninta ya addabeshi a yan kwanakinnan kullum bayada aiki sai tunaninta, saidai yasan abune dakamar wuya ta amince mashi but he'll try his best


Bayan kwanaki uku da dawowarsu daga saudiya Deen da mussadiq suka daga zuwa Nigeria inda Deen zaije ne don waiwayar masana'antarshi shikuma mussadiq yajene da sunan rakiya amma abinda yakaishi daban


agidan Deen suka sauka inda saida suka huta sosai sannan suka nufi gidansu Lailah bisa matsawar mussadiq


sosai akayimasu tarbar mutunci inda ahalin sukayi matuqar farinciki da ziyarar tasu ta bazata

ganin mussadiq da Lailah tayi aranar yaqara tabbatar mata da abubbuwan data dade tana hasashe

tun bayan dawowarsu daga Dubai takasa nutsuwa, zuciyarta takasa samun sallama inda tunanin twin din Deen yabi yayi mata bake2 yayimata katutu azuciya

kullum idan ta zauna kalamanshi Kawai kemata yawo a kwalwa, yanayin maganarshi, salonshi, komai nashi is different

dukda kammaninsu daya da Deen saidai hallayarsu da yanayinsu ya banbanta, yayinda Deen keda sanyi sosai shi mussadiq talura is way too classic gashi kallo daya zakamashi ka iya jerashi a layin miskilai, haka Kawai takejin hallayar mussadiq yafi burgeta bisaga na Deen.


koda ta sauko don su gaisa kasa looking directly at him tayi, abin mammaki saigashi maganarshi ta tabbata don yau akallo daya taganeshi dukda shigar da sukayi iri daya.

fira sosai sukesha a tsakaninsu most especially Deen da Abba don mussadiq be cika magana sai shegen kallon daya kafe Lailah dashi babu ko kunyar su Abba

ganin abin na neman yin yawa yasa Lailah excusing kanta ta haye sama donta lura mussadiq be iya takaittacen kallo ba

saida zasu tafi sannan mamy takirata ta sauko don suyi bankwana inda anan suka d'an samu damar magana lokacin Deen da Abba are busy suna maganar aikin Deen

dagowa tayi ta kalleshi taga ita din shima yake kallo, ahankali yasakar mata guntun murmushinshi

itama d'an murmushin tayi ta sauke idanunta

"your phone?" yafada yana miqamata hannunshi

kallonshi tayi saikuma ta,miqamashi wayar hannunta

amsa yayi yay dialing sabon layin dayayi na Nigeria kiran yashigo wayarshi sannan ya katse kiran ya maida mata

"will call you later" yafada ahankali

kada kai Kawai tayi daidai nan su Deen suka qaraso wajen sukayi bankwana suka tafi.

kamar yadda yace din saigashi yakirata da daddare inda sukasha firarsu inda anan taqara sanin wasu daga cikin hallayenshi

babu abinda yafi burgeta gamedashi kamar yanayin maganarshi, idan zaiyi magana adunqule yake yinta ko abaibai wanda dole saika nutsu sosai zaka gane ma'anarta. he just know how to deal with words.

ga slang dinshi na Arab turanci yake mata amma da karin larabci saitaji turancin wani iri amma kuma ga mammakinta tamafison irin nashi din.


sati daya sukayi a Nigeria inda cikin satin Deen yashiga busy sosai saboda aikin dasuka tararmashi yayinda shikuma mussadiq ya 6ata satin wajen yad'a manufarshi awajen Lailah

Acikin satin ya bayyanama Lailah son dayake mata kuma yasamu kar6uwa don alokacin yariga yagama daita yatafi da imaninta

a kwanansu na goma suka juyo Dubai lokacin hatta yan gidansu Lailah sunsan da soyayyar dake tsakaninta da mussadiq, Deen yafi kowa kowa farinciki da hakan don aganinshi sunyi mugun dacewa dajuna


a bangaren Aymaan kuwa tunda yaga Deen agidansu lokacin dasuka dawo daga saudiya yafara neman hanyar yad'a manufarshi ga Aysha.

at last ya tsaida wata shawarar dayaga ta hakan zaisamu kusanci daita

nan yafara bibiyar Aysha a school dinsu

yalura yarinyar is so timidshiyasa yake amfani da hakan wajen tsokanarta don sosai yake samun nishadi da hakan

tun suna fada idan suka hadu har wata iriyar shaquwa tashiga tsakaninsu wadda cikin qanqanin lokaci ta rikide takoma soyayya

anan Aysha tasan ainahin menene so saboda Aymaan ba baya ba afagen love da nuna kulawa

sai alokacin taga ashe soyayyar datayi da umar abaya ba soyayya bace wahala ce don batasan haka soyayya keda dadiba sai akan Aymaan

tofa atsakanin Deen da zee dakuma mussadiq da Lailah da Aymaan da Aysha sai narasa wadanda sukafi iya buga love, kowannensu ba daga baya ba don soyayyar kowanne abin burgewa ne

Deen ne yafara yunqurowa a maganar tasu donfa shi dagaske yake bayada burin daya wuce na mallakar zee

ganin hakan yasa mussadiq shima bijiro datashi maganar inda ummie taji kamar tazuba ruwa tasha don murna

hakan yasa tayima yan uwanta da mutanen saudiya magana inda suma sukayi farinciki sosai da hakan babu 6ata lokaci suka fara shirye shiryen garzayowa Dubai domin qara maganar gaba

kamar hadin baki adaidai lokacin shima Aymaan ya gabatarma su ummy maganarshi da Aysha

sosai suma ahalin sukayi farinciki da za6inshi musanmman ma zee dataga mugun dacewarsu da Aysha don Aysha yarinyace dakowa zaiso hada jini daita

abu kamar wasa cikin dan qanqanin lokaci mutanen su Deen suka garzaya wajensu abbu wanda daddy ya damqa komai ahannunshi don acewarshi shima ubanta ne inda anan sukaje neman auren zee inda nan aka tada maganar su Aymaan wanda hakan yayima kowa nawajen dadi, wato zasu bayar kuma za'a basu nan aka tsaida magana inda mutanen Deen suka nuna sunason ayi komai dawuri inda anan aka tsaida lokaci inda bayan wannan hutun nasu na wannan semester din za'asha biki

sosai zee tashiga rudu lokacin dataji labari nan tafara kuka wai yayi kusa dayawa ita sotake tagama karatu batool kau mexatayimata banda dariyar qeta

saigashi kwana biyu dasa ranar su Deen shima Ahmad yaturo magabatanshi akan maganarshi da batool inda shima qarshe aka jona danasu Deen da Aymaan, nanfa itama batool ta sire don kwata2 she didn't saw that coming saigashi zee ita takoma yima batool dariyar qeta

asatin daya biyo baya kuma mutanen su Deen suka garzaya Nigeria don nemawa mussadiq Lailah inda shima.ataqaice aka jona danasu Deen ya kasance daurin aure hudu alokaci guda

zokuga murna awadannan ahalin musanmman ahalin su Deen, ummie rasa inda zatasa ranta tayi don farinciki wai itace zata aurar da dukkan 'yayanta alokaci guda, wannan abin yakai abin farinciki

suma ahalinsu batool ma hakan take dasu daddy, baxaka ma iya tantance wanda yafi wani farinciki ba.


a bangaren su Lailah ma haka, sunyi farinciki sosai na hada zuri'a dazasuyi da ahalin su Deen gashi lokacin zaikama daidai lokacin da Lailah ke qarasa karatunta abindai ba'a cewa komai

ahankali lokaci yaita tafiya inda ake shirye shirye takowane bangaren

sosai kan amaren yadau zafi kasancewar ga jarabawa daketa gabatowa gakuma shirye shiryen biki haka sukaita fama har lokacin jarabawar yayi suka zana.

alokacin saura duka yan satittika da bikin

suna gama jarabawar kowacce tadawo gida basu qara zuwa school dinba aka hau yimasu gyare gyaren amare

sosai iyayen amaren takowane bangaren suka zage wajen gyare 'ya'yansu wanda cikin qanqanin lokaci suka sauya suka fito a ainahin amaren

biki na saura sati daya dangi suka fara bararowa takowane bangare

gidansu batool sauran sati daya amma yadda kasan gobe ne bikin

tuni su mummy suka iso Dubai don anan za'a daura auren both zee da batool

biki saura kwana hudu su dangin su mummy suma suka fara durowa ciki harda aunty feenah wadda keda diya kyakyawa mai kama daita sosai tareda su cousins dinsu zee

nanfa gida yaqara hargitsewa yakoma ainahin gidan biki

abangaren su Deen ma hakan take don tuni gida yacika da larabawa kala2

tun biki saura kwana biyar gidan ya harmitse koda yaushe kaje banda tashin mandiri babu abinda kakeji

biki saura kwana hudu duk aka kawo kayan lefe agidansu amare, kaya nagani nafada don fadin haduwar kayayyakin 6ata bakine

itama Lailah Washegari aka tura nata lefen Nigeria kowa sai san barka akeyi

bikin babu wata bidi'a daza'ayi illah dinner daxa'ayi ranar daurin auren

haka ranakun sukaita wucewa kowa kanshi yadau xafi akan hidimar


*RANA BATA QARYA...*


Yau ranar juma'a takama ranar da kowa yake jira

ranar da zata chanza labarin wasu

auren mussadiq aka fara zuwa Nigeria aka dauro inda suka aka taho da amarya ta private jet akadawo Dubai

dama sanin cewa most events anan Dubai za'a yishi yasa duk yawanci family dinsu Lailah sunriga sun iso Dubai din tun daren ranar

suna isowa aka zarce massalacinda za'a daura kingin auren aka daura auren KAMALDEEN(MUJAHEED) da ZAINAB sai AYMAAN(ABUBAKAR) da AYSHA sai AHMAD da BATOOL(FATIMA)

sosai garin Abu dhabi ya rude don babu wanda besan da wadannan daurin auren ba

Deen tunda aka daura auren jinshi Kawai yakeyi kamar yana yawo kan iska

komai sai yake mashi kama da mafarki, wai yau shine aka daura aurenshi da zee, yau zee tazama mallakinshi

sujjudu shukur yayishi yafi a qilga fadin farincikin dayake ciki baya misaltuwa don shi kanshi baxai iya fasalta yadda yakeji ba

abangaren kaka ma haka ana kawo mata labarin daurin auren tahau sujjadar godiya ga allah saikuma kuka, kuka takeyi kamar ranta zaifita, she can't believe yau ita keganin daurin auren Deen abinda tadade tana mafarki

itama ummie saida ta tayata kukan don itama kasa riqe hawayen farincikin tayi itama jitake babu wanda yakaita farinciki aduniya aranar


Washegari takama dinner inda wadda za'ayi da daddare daga nan kuma kowa ya dau matarshu yaqara gaba

tunda safe kowanne gida ya hargitse da shirye shirye, kowanne gida babu matsaka tsinke

shirye shiryen dinner sukeyi sosai sunason ya kasance one of the best dinner ever


sai bayan isha'i sannan motoci sukaita zuwa daukar mutane zuwa dinner inda amaren motar angwayen kezuwa daukarsu


idan kaga amaren lokacin idan ba farin saniba kayimusu bazakayi saurin ganesu ba

sun chanza sunyi wani fresh sai glowing suke

kowacce taci kwalliyarta acikin fararen wedding gown masu kyan gaske sukuma angwayen anci kwalabo Acikin baqaqen suit kowanne yayi wani irin breathtaking kyau fuskarsu sai glowing na angwanci sukeyi

Deen kasa daina kallon zee yayi lokacin da aka shigo daita amota

rabonshi da sata a ido tun lokacin dasuka gama exams suka rufe fita lokacin kusan saura sati uku ga bikin

gani yayi kamar anchanzamashi itane kamar ba ita ba

haka yatusata gaba da kallo harsuka isa wajen event din babu ko kyaftawa


atare amaren da angwayen suka shiga hall din kowanne da amaryarshi agefenshi

fadin haduwar dasukayi ma 6ata bakine don sun hadu over

bayyanarsu yasa hall din kaurewa da tafi da whistle gawani waqa mai shegen dadi da aka saki ta background

ahaka aka rakasu har zuwa maxauninsu sannan akafara event din

taro yayi taro inda hall din ke dauke da manyan manyan mutane, businessmen, mawaqa yan uwan Deen dasukayi mashi kara, likitoci abokan Aymaan, fararen fata, baqaqe da larabawa dik an gwamutse a hall din anata chasu

can nahango yan *DEEN FANS GROUP* tsamo tsamo cikin yan dinner, kowacce taci uban dauri sunsha ango sai bidiri akeyi


iya qawatuwa dinner din ya qawatu inda aka gudanar dashi cikin salo mai matuqar burgewa

basu suka tashi ba sai qarfe shadaya saura inda kowanne ango yadauki amaryarshi yayi gaba daita (dama kuma tunkafin sufito daga gidansu akayiwa kowacce nasiharta)


a gida daya mussadiq da Deen zasu zauna don tare sukayi gini tun lokacin da akasa bikin saidai kowa da part dinshi, gidan dai awajene amtsayin gida daya amma aciki gidaje biyune komai iri daya kowanne danashi

gidane daya hadu yakuma qawatu don fadin haduwarshi ma 6ata bakine

anan kowa yashige da amaryarshi part dinshi inda daga nan nikuma naja bandararrun kafaffuwana najuyo gida don agajiye nake matuqa don baqaramin raqashewa mukayi ba nida yan Deen group a dinner.


*TWO WEEKS LATER*


sai alokacin daqara waiwayar amaren da angwayen inda kowanne gida naje abin gwanin sha'awa don kowannensu cin amarcinsu suke da picking stick

gidan Deen ne qarshen zuwana inda na tadda zee a kitchen sanye cikin wasu hot English wears wadanda sukayi bala'in yimata kyau tana gaban cooker gas dinta tana soya musu egg omellete


shikuma Deen na zaune daga bayanta kan wata kujera guitar ahannunshi yana kadawa cikin wani cool romantic tone, sanye yake cikin dogon baqin wando sai baqar singlet wanda suka fiddo farin complexion dinshi sosai

zee da sautin guitar kemata dadi sosai sai kada kai take ahankali tana rausaya kugu tana humming ahankali tana cigaba da abinda takeyi

dagowa daga kallon guitar dayakeyi Deen yayi ya kalli bayan zee ya quramata ido yana cigaba da kada guitar sannan yatashi ahankali yanufeta yana chanza salon kidan guitar din

zuwa yayi ta bayanta gab daita sosai kafin tajuyo ya zagayo da hannunshi dake riqeda guitar ta gabanta daidai cikinta yacigaba da kadawa

murmushi tayi tana cigaba da rolling kwai din

ahankali ya sunkuyo da kanshi daidai wuyanta ya hura mata iska wanda hakan yasata dan shivering tana murmushi

kai bakinshi yayi yadan ciji earlobe dinta sannan ahankali kamar arada cikin sigar waqa datayi daidai da sautin da guitarshi kebadawa yafara rairomata waqa ahankali kusada kunnenta jikinshi still manne daita

*Deen*: _If I could do it all over_
_baby i'll do it different_

_maybe I wouldn't be here_

_in this..position_


murmushi zee tayi itama ta amsa

*Zee*: _I found you then I lost you_

_looking back is torture_

_and it hurt to know that I let you go_

_you live right around the Corner_

Juyo daita yayi suna fuskantar juna fuskarsu dab dana juna hancinsu na gogar najuna suka cigaba da cewa

*Deen & zee👩‍❤️‍�*: _And I could've had it all, could've had it all_

_true love❤️ I know I had it_

_true love❤️ it's so hard to find!!_

_true love❤️ If I could get it back_

_i'll never let it go this timeee💕_


*Deen*: _true love_

*zee*: _it's an inspiration🥰_

*Deen*: _true love_

*zee*: _it's was mine, all mine_

*Deen*: _true love_

*zee*: _yeah_

*Deen*: _I'll never let it go_

*zee*: _I'll never let it go.._

*Deen & zee*: _I'll never let it goooo💞💞💞💞💞💞_

hade bakinsu sukayi lokaci guda suka shiga bama juna hot French kiss kamar zasu cire le66en juna

ganin hakan yasani saurin juyawa saikuma natuna da abinda take soyawa wanda da alamu ma sunmanta dashi nadawo nakashe gas din na wafci rabin kwan nayi waje ina cusawa abaki....✍�


THE END💃🏻


alhamdulillah!

alhamdulillah!!

alhamdulillah rabbil a'alamin!!!


allah na godemaka dakabani ikon gama novel dinnan lafiya, kurakuren dake cikinshi allah ka yafemin🤲🏻


ina yan amana? mutanen group dina masu haquri da uzuri🥰

ina miqa dunbin godiya ta agareku don kun nunamin qauna iya qauna, kunkuma yimin uzuri kunata bina da addu'o'i alokacin nake buqata yayinda wasu kuma suka kasayin hakan kullum sai complain yadda kasan biyanka albashi sukeyi.

allah dai yabar qauna sweet sisters don qaunarku pure ce nima na shaida, allah yabar tare yakuma sake hadamu awani book din nagaba


thanks soo much, Ashaanty heart you soo much💞💞💞💞💞
Chapter 4 · 0% Book details