← Book details Deen Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
CHAPTER 3 OF 4

Part din Umma takoma ta tarda tana sallar asr da aketa kira

Deen Part 1 Complete Hausa Novel · about 169 min read

Itama wucewa toilet tayi tai alwalla sannan tazo kusada ita ta gabatar da tata

Daga nan suka shiga fira inda yawanci fadan jika da kaka ne

Anan ta shiririce har magrib, dama bala tun bayan asr yayi sallama dasu ya juya

A dakin Feenah takoma tayi magrib Da isha'i sannan tafito riqeda tsarabar Umma takai mata nan ma da fada aka rabu sannan tafito daga part din ta shi shiga part din kawunanta don su gaisa kasancewar sun dawo

Anan duk ta shiririce sai can wajajen 9pm takoma part din Umma

Dakin Feenah takoma inda ta tarar daita lafe kan gado rungume da pillow tana waya cikin muryar da ba'aji bare ka tantance me take cewa

Kallonta tayi taga sai wani lumshe idanu take murmushi yaqi barin fuskarta

Tayi mammaki sosai da Hakan don Aunty Feenah ba ma'abociyar murmushi bace da wuya ka ganta tana fara'a don koda yaushe a wuya take jira take qiris ka ta6ota ta sauke maka kwandon bala'i batada haquri sam yadda kasan zawo

Qarasowa tayi ciki ta bude closet ta ciri towel ta rage kayan jikinta ta daura sannan tawuce toilet

Tadan jima sannan tafito tana makyarkyatar sanyi don garin yau da iska sosai gashi dama su cikin damuna ana yawan yimasu ruwa ba kamar cikin katsina ba shiyasa weather dinsu yafi nacan sanyi

Saida tagama shafe2nta sannan ta saka thick night gown ta hawo gadon ta kwanta


Har a lokacin waya Feenah keyi cikin qasa qasa da murya sai sakin siririyar Dariya take every now and then

Deen ne yafadomata arai, dama kuma yana ranta don yau ma wuni tayi dashi arai don ba taqi ba zuciyarta damar tsayawa tunaninshi shiyasa taqi zama bata nan bata can don da tadan nutsu zai fadomata arai

Qara qudundunewa tayi cikin bargon tanajin kewarshi na dawo mata sabuwa, babu abinda ya chanza a abinda take ji game dashi saima abinda ya qaru

Tana ahaka har Feenah tagama wayar ta ta gyara kwanciya ta kwanta

Shiru koina ya dauka don dare yayi sosai Saidai ko alamun barci babu a idanun zee, wannan dai tunanin nashi ya addabi kwalwarta kamar yadda yasabayi duk dare

Ta dade ahakan jin bazata iya jurewa ba yasata kiran sunan Feenah

Shiru, tasake kira hoping batayi barci ba

Juyowa Feenah tayi tana fuskantarta tana kallonta da idanunta dasuka fara jin barci

"ya akayi ne? Dama bakiyi barci ba?"

"eh Aunty, please magana zamuyi" tafada not sure idan ya kamata ta gayawa wani amma ai taji ana cewa problem shared is problem solved wata qila zata bata haske akan yadda zatayi ta rabu da abinda ke damunta

Kallonta Feenah ta tsaya yi na wani lokaci sannan ta muskuta ta tashi zaune ta jingina da jikin gado ta harde hannayenta a qirji tace
"yes? Inaji"

Itama tashi tayi ta zauna tana fuskantarta amma takasa cewa komai

"idan bazaki iya magana ba inkoma in kwanta banson wulaqanci" inji Feenah tana hade rai

Ajiyar zuciya zee ta sauke sannan tace
"dama Aunty, tambayarki zaniyi. Dan allah idan mutum ya kasance koda yaushe yana tunanin abu duk motsinshi saiya tuna da abin har ya hana shi barci wani sa'in, me Hakan ke nufi kuma tayaya mutum zai iya yakice tunanin a ranshi?"


Shiru Feenah dake sauraronta Tundazu tayi tana Kallonta irin kallon tuhuma sannan itama ta sauke Ajiyar zuciya itama tace
"Wani abu, shi abin menene? Mutum ne koko?"

Shiru zee tadanyi sannan tace
"eh asa mutum dinne"

Harararta Feenah tayi tace
"munafuka, gwara kifito kimin gwari2 yadda zan gane, mutum dan tatsitsi dashi sai gulma, mtcheew"

6ata fuska zee tayi tace
"kai Aunty, munafurcin me nayi?"

"kin fini sani ai, to bari kiji koma menene abin sonshi kikeyi, koma waye mutumin you're in love with him kuma babu yadda za'ayi ki yakiceshi a zuciyarki, the more kike qoqarin yakiceshi the more zai qara liqewa don haka the best solution is Kiyi accepting soyyayarshi"

Tunda Feenah tafara magana taja dabaya tana Kallonta baki bude

"w.. What?" tafada unbelievably

"yes, sonshi kike koma wanene, that's one of the symptoms of love, you're in love Zainab"

Qara jada baya tayi tana girgiza kai
"no.. No.. It can't be"... ✍️


Juma'at mubaraq in advance � 🌜


Ummin fasihu 🧚🏻‍♀�
8/2/21, 9:35 PM - Buhainat😝: *🙍🏻‍♂️DEEN 🙍🏻‍♂�*


*033*


"No, it can't be. Haba Aunty ya zakice haka? So fa? This is totally impossible" tafada cikin qaryata zancen

Tayaya xa'ace tana son Deen? Deen fa, of all people ta rasa abin so sai Deen? Impossible!


Tsayawa Feenah tayi tana kallonta sannan tace
"bari kiji, nothing is impossible indai love is involve, shi so babu ruwanshi da wanda ya cancanta da wanda be cancanta ba kawai daya tashi kama mutum kama shi yake batareda duba cancanta ba, zee you're in love ko kinqi ko kinso don gayanan rubuce
vividly a idanunki so zaifi maki kidawo hayyacinki tunda wuri kibar yaudarar kanki"

"Aunty Feenah, baki san fa wa muke magana akai ba, da kinsani da kema kin qaryata Hakan da kanki, how on earth zan fada soyyayar Deen? Kinsan shi kuwa? Kwata2 beyi matching qualities danake nema a namijin da zanso qarasa rayuwata dashi ba, that annoying being? That timid mouse? How? When? Why?"

Dariya Feenah tayi tace
"kalli yadda kika firgice akan wannan yar maganar"

"har haukacewa ina iya yi akanta Aunty, kinsan ko dawa kike dangantani kuwa?"

"ban saniba kuma banson sani, abinda nasani shine you're in love with koma waye mutumin, gashinan rubuce 6aro2 a fuskarki kuma abubbuwan da kika fadamin early na daya daga cikin alamomin fadawa soyyaya, bari kiji kadan daga alamomin


Soyyaya tana zuwa ma mutum ta siga daban2

Na farko if you're in love with someone koda yaushe zai kasance maqale a cikin zuciyarki, idan wani abu kike zaki dinga wondering shi me yakeyi, kiji kamar a hasko maki shi ki ganshi, abin nufi anan koda yaushe yana maqale da zuciyarki dashi zaki dinga kwana kina tashi


Na biyu kunya, wasu yana zuwa masu da kunya, kiji bazaki iya hada idanu dashi ba and if you do bazaki iya jurar kallonshi eye-eye na tsawon lokaci ba


Zai kasance duk lokacin da kuke tare zakiji kamar ku kadai kuka rage a duniyar babu sauran wasu inma akwai kin manta da wanzuwarsu haka zalika idan bakwa tare zakijiki so empty kamar kin rasa wani muhinmmin abu na sashenki


Zakiji kina tausayamashi fiyeda qima, bakya qaunar wani abu ya sameshi idan kuma ya sameshi kiji kamar ke abin yasama koma kifishi jin radadin abin kiji kamar ki cire abin daga jikinshi ki maido naki

Akwai changing of heartbeat ma, idan akwai soyayya duk lokacin da kuka kusanci juna ko kuke tare sai bugun zuciyarki ta chanza

Duk damuwar da kike ciki arba dashi batareda ma kunyi magana ba zakiji kamar bakida sauran damuwa a duniyar nan

Komai nashi burgeki zaiyi koda ba abin burgewa bane

Shaquwa ta sosai da sosai zata shiga tsakaninku inda rabuwa a lokacin will hurt you both physically and emotionally...

Ke signs din soyayya are so much to be mention, so very much don idan natsaya lissafa miki sai mu kwana a zaune ni kuma barci nakeji'


Zee data maidata t.v Tundazu takasa magantuwa don kamar mai duba, maganganunta sunyi matching da abinda takeji sosai amma still this is impossible

Tayaya za'ayi ace tana son Deen? Classic girl kamar ta ta bige da son Deen

Deen beda qualities din datake bid'a tattare da namiji

Zata iya cewa daya kawai yake dashi cikin siffofin namijin datake fatan aura shine KYAU

Yes yanada kyau, a wannan ga6ar bazata ja ba don duk kushen mai kushe bazai iya kushe kyawunshi ba

Yana da kyau mai sanyi da tafiya da zuciya farat daya

Tana son namiji mai kyau amma ba kyawun kadai ba

Tana son namiji mai jida kyau da naira, jarumi mai jida kanshi, very Classic handsome guy abin nuni ga kowa

Yadda take Classic dinnan itama tana son Classic guy irin ta dan kwalisa mai ji da gayu da qasaita

Acikin abubbuwan data lissafo abu daya Deen ke dashi wato kyau amma duk kingin bedasu then how on earth za'ace tana sonshi

"Aunty Feenah, wataqila kinyiwa abin bahaguwar fahimta ne, Yes ni dashi friends ne kuma akwai Shaquwa sosai a tsakaninmu wataqila shiyasa nake missing dinshi amma tayaya Hakan zai zamo soyayya? Beda qualities din my dream man kwata2 so kima bar kawo batun soyayya aciki"

Tunda tafara Feenah ke mata kallon up and down fuska a yatsine sannan taja tsaki tace
"banda ke shashasha ce ina kika ta6a ganin an qulla abota tsakanin namiji da mace an wanye lfy? Babu wata alaqa dake tsakanin namiji da mace da babu soyayya aciki muddin ba muharraman juna bane

Kosu duka basu kamu da son juna ba daya zai kamu kamar yadda nake zargin ke kadai kika kamu a naku alaqar

Bari kiji duk namijin dakika gani yana abota da mace to ki bincika is either suna son juna ko daya na son daya aciki don a jadawalin alaqa dake tsakanin namiji da mace babu abota, ba yadda za'ayi ayi abota zalla tsakanin mace da namiji that's impossible

Dan haka ki nutsu Kiyi tunani dakyau ki banbancema kanki abinda kike ji a zuciyarki don the earlier the better, soyyaya muguwar abu ce wanda idan ta juyamaka other side dinta sai kayi nadamar zuwanka duniyar baki daya, ina magana ne akan experience bawai kara zube ba, nasan soyayya ciki da bai, na dandani kowanne side dinta, da mai dadin da mai dacin

Fatana dai ace shima yaso ki, karkiyi son maso wani don wannan sashen yafi kowanne daci a soyyaya"
Tana kaiwa nan ta juya ta kwanta tareda lullu6e jikinta har saman kai ta qudundune

Da kallo zee tabita na mammaki don tana iya rantsewa taga kyallin hawaye a idanun Feenah

Hakan ba qaramin qara sanyaya mata jiki yayi ba, sai gashi ita dake ganin zata samu mafita abin ya qara dagule mata

Komawa tayi ta jingina da frame din gadon ta rungume hannuwa a qirjinta

Rasa tunanin da zatayi tayi Hakan yasa ta lumshe idanu tana sauke numfashi ahankali tana dauko magangganun Aunty Feenah da daddaya tana warwaresu tana masu fashin baqi daidai fahimtarta.


*WASHEGARI*


Sukuku ta tashi yau, idanunta sunyi ja sunyi nauyi saboda rashin isashen barcin jiya

Sallar asuba kawai tayi ta koma kan gado wani barcin yasake yin gaba daita


Bata farka ba sai wajajen 10am shima Feenah ce ta tadata don kar breakfast dinta yayi sanyi

Dakyar ta tashi tashiga bayi tayi freshen up tafito

Haryanzu maggungunan dasukayi da Feenah daren jiya keta kai kawo a kwalwarta, maggungunan dasuka liqema kwalwarta suka hanata sukuni

Daga ita har Feenahr babu wanda ya tadama juna maganar jiya don daga baya ma Feenah barin gidan tayi ta tafi unguwa


Sama2 tayi break din ta fita

Parts din kawunnanta tashishiga suka gaisa sannan ta dawo dakin Umma

Tunda suka gaisa ta haye bisa gadonta na qarfe ta lumshe idanu

Duk zazzage zazzagen da Umma keyi mata akan ta sauko mata daga gado bata tanka ba hasalima ko bude idanu batayi ba bare ta nuna alamun tasan abinda take

Gajiya Umma tayi ta kyaleta ta fice daga dakin ma gabadaya

Sai a lokacin zee ta samu damar tunanin nata dakyau

Meyasa kowa ke danganta alaqarta da Deen a matsayin soyayya?
Haka su Nurr ma sukayi gashi Feenah itama tabi sahu, meyasa?

Da gaske ne babu wata alaqa tsakanin mace da namiji da baza'a rasa soyayya ba?

Idan Gaskiya ne to cikin shi da ita wa keson wani?

Waya damu da wani?

Wake kewar wani?

_ni?_

_no, never! Insha allah ba so bane.. Insha allah_

_kai bama so bane, tayaya zanso Deen? He's just a friend shima ada, yanzu he's no more, abotanmu ta yanke tun ranar da ya maidomin wayata, Hakan ya nuna be daukeni yadda na daukeshi ba, it's over and over and over!_


Haka ta wuni ranar daga kwanciya sai kwanciya

Idan kaga ta tashi to abinci zataci ko sallah, dakuma tagama zata koma ta nade

Tun Umma na mita har tafara xargin ko batajin dadi ne

Hakan yasa ta tsareta da tambaya dole tayi qaryan kanta ke ciwo

Tana ji tana gani Umma ta tilasta mata shan maganin da bazai amfaneta da komai ba na ciwonta

Da daddadare ma haka tayita juye juye, ta juya 6angaren dama ta juya haggu amma sam barci yaqi zuwa, haka ta kusan raba dare idanunta biyu sannan allah ya taimaketa barcin ya dauketa can cikin dare


***

Haka ta cigaba da zaman garin amma kwata2 batada walwala


Ita da taje don ragema kanta abinda takeji sai gashi abin yaxama gwara baraa da bana


Haka kawai zaka ganta zaune ta kafe wuri guda da ido tayi shiru

Tun Umma bata dauki abin da muhimmmanci ba har abin yafara damunta

Sai tayi tunanin ko kewar gida take Hakan yasa takira Feenah tasata suje tareda zee su yawata dangi ko zataji dama dama

Feenah da tasan dawon garin ta ta6e baki kawai don tasan babu wanda zaiyi maganin abinda ke damunta sai mutumin


Washegari wanda yayi daidai da kwanakinta hudu a garin suka fara zaga dangi da zee da Feenah dake tuqi dakanta

Babu laifi tadanji dama daman abinda takeji aranta amma still abin yaqi fita ranta ta rasa yadda zatayi

Har suka qaraci yawonsu suka dawo babu wanda ya tadawa dan uwanshi maganar Saidai acan cikin zuciya kowa da abinda yake saqawa


Yau ma da daddare batayi barci ba, tanajin Feenah na waya, har tayi ta qarashe idanunta biyu tanajin sadda Feenahr ta gyara kwanciya ta kwanta ta rufe jikinta

Sai jitayi dama ita, dama ita keda peace of mind din kwanciya haka tayi barci

Tayi nisa a tunaninta taji muryar Feenah kamar daga sama tana cewa
"ba tunani ko takura kai ne mafita ba, mafita shine ki ajiye komai ki fuskanci Gaskiya"

Juyowa tayi ta kalli Feenahr dake lullu6e haryanzu wanda ita tamayi tunanin tayi barci

Kamar bazata amsa ba sai kuma tace
"kamar ya?

Sai a lokacin Feenah ta yaye lulli6in tana kallon ta

"ina nufin ki ajiye duk wani tunaninki na qualities or whatsoever dakike ganin be kai ba na wanda yakamata kiso don shi so babu ruwanshi, so mahaukaci, real mahaukaci don yana iya yin hadi da hadin da kwakwalwa ma bazata dauka ba, muddin dai mutumin kirki ne then kibi abinda zuciyarki keso, karki yaudari kanki"

Tashi zaune zee tayi
"wai Aunty waya gayamiki sonshi nake? Ni idan kina furta kalmar so dinnan bakiji yadda nakeji ba"


Murmushi Feenah tayi sannan ta tashi zaune itama tana kallon zee da hawaye suka taru a idanunta

"to meye na kuka kuma?"

Dauke kai zee tayi hawayen na gangarowa dama mai neman kuka aka jefa da ledar kashi

Murmushi Feenah tasakeyi tace
"ke kanki you're confused zee, kin fada soyayya amma baki yarda kin fadaba to tayaya za'a fara maganar mafita bayan ke kanki baki yarda akwai matsalar ba?

Dole sai idan da matsala ake neman mafita amma ke yanzu kinma qi yarda da matsalar bare akai ga batun neman mafita"

Dafe kanta kawai zee tayi hawayenta na cigaba da diga

Murmushi Feenah tayi ta dafa kafadarta
"Nima na ta6a cikin wannan yanayin zee, nasan yadda kikeji don na shiga yanayin dayafi naki ciwo, ke ki godewa allah abokinki ne nikau babu abinda yahadamu zan iya cewa ma besan da wanzuwata a duniyar nan haryanzu, so is better kidawo hayyacinki ki fuskanci me kike ciki yadda zaki shawo kan matsalar kafin komai ya kwa6e miki"

Tana kaiwa nan ta juya ta gyara kwanciyarta

Dagowa zee tayi tana Binta da kallo da jiqqaqun idanunta zuciyarta na qara dagulewa

A halin yanzu ma ta rasa mema zatayi? Komai sai qara kwa6emata yakeyi ta rasa tunanin da zatayi.


Washegari da ciwon kai ta tashi ga idanunta dasuka kumbura alamun kuka da rashin barci

Sosai hankalin umma ya tashi ta tusata gaba tana tambayar meke damunta, da aka takura mata ma sai tasa kuka don ita kanta idan tace ga abinda ke damunta to tayi qarya

Ganin Hakan yasa hankalin umma ya ida tashi tasa aka kira kawunnanta aka suka zo suka tusata gaba da rarrashi akan tafada masu abinda ke damunta amma ba amsa don batasan abinda zatace masu ba

Duk abinda ake Feenah na gefe tana kallonsu gefe guda kuma tana charting da saurayinta da akayi masu baiko dashi don befi saura wata uku ba auren dama tana shiga final level aka turo neman auren ta akasa bikin gabadaya

Ganin sun dameta yasata cewa ita gida zata koma tana kewar daddy

Ganin dagaske ta tubure gida takeson komawa yasa aka bata hqr tabari zuwa jibi sai ta tafi, Dakyar aka samu ta yarda sai jan zuciya take

Ranar a dakin umma ta kwana don bata buqatar sake jin abinda zai qara dagulamata lissafi


Kingin ranakun kawai idasu tayi a darare burinta kawai tabar garin

Sai a lokacin ma take danasanin zuwa garin, gashi garin neman qiba taje ta kwaso rama

Ranar dazata koma kawu umar dakanshi ya maidata bayan sun cikata da tsarabobi

Dayake tafiyar safe ce basu wani jima ba suka isa


Sosai daddy da mummy suka tarbi kawu umar inda anan daddy ya riqeshi har bayan la'asar sannan ya juya


*STRANGE WORLD💗*


Sosai zee ta chanza cikin yan kwanakinnan, takoma wata silent da ita batada walwala ko kadan, ga saurin kuka abu kadan sai hawaye


Sosai abin ke damun su daddy musanmman ma shi daddyn da damuwarshi tafito qarara

Tambayar duniyar nan yayimata akan tafada mashi meke damunta amma babu amsa sai kuka idan aka matsa mata


Yawan shaqatawa da shopping kullum sai sun fita don dai ta warware amma a banza don babu abinda ya chanza, kodayaushe she's moody batada walwala

Ganin Hakan yasa suka danganta Hakan da missing din school don dama tun farko abinda ta ambata kenan shiyasa sukaita allah allah Ayi resuming qila takoma her normal self


Saura kwana biyu suyi resuming daddy yafita daita shopping din school resumption

Kaya sosai ta loda na zuwa school da kingin tarkacen datake ganin tana buqata


Cikin kwanaki biyun nan sai tarasa me takeji, doqin komawarsu school take ko doqin sake ganinshi


*MONDAY*


Tunda ta tashi da asuba bata koma ba, shirye2 take na resuming school yau

Duk yadda taso qaryata abin dole ta yarda tana doqin komawarsu makaranta, doqin da bata ta6ayi ba duk hutun baya


Sosai tayi shiga ta kece raini kamar yadda tasaba

Sanye take da less 'yan ubansu mai shegen kyau

Lace din kalar baqi sai yarfi yarfin jaa ajiki

Anmata dinkin riga fitted da skirt pieces wanda ya zauna a kugunta d'ass

Tayi daurin dan kwalin zahra buhari sannan ta yafa jan siririn kyalenta a kafada

Kaffafuwanta sanye suke da jajjayen hill shoes sai jar jakkarta mai daukar ido dake hannunta da faskekiyar wayarta a dayan hannun

Kamar koda yaushe fuskarta tasha kwalliya guntun bakinta yaqara yin jajur gwanin sha'awa


Sosai shigar baqi da jaa din suka amsheta tayi wani irin kyau mai tafiya da numfashi

Ahankali take tako stairs din cikin tafiyarta mai kamada ta sarauniyar kyau

A dining tagansu daddy namata murmushi

Itama murmushin ta maida masu ta qaraso wajensu

"wow princess kinyi kyau sosai" inji daddy yayinda mummy ko dagowa batayiba

Dan Kada idanu zee tayi murmushi a fuskarta tace
"thanks dad" tafada tana jan kujerar kusadashi ta zauna


"mummy ina kwana?" tafada tana kallon mummyn dake cin abincinta

"lfy lau" ta amsa a taqaice

"daddy good morning"

"morning dear, wannan fara'a haka ashe daman ciwonki school? Ai gashi nan ankoma mun huta da koke2"

Dariya tayi tana rufe fuska

Abinci tadan zuba shima saboda mummy ba don haka ba da wucewarta zatayi idan taje school tasamu snacks

Bataci dayawa ba ta tayi wiping bakinta tana niyyar tashi

"ba dai har kin qoshi ba" inji daddy

Dan 6ata fuska tayi tana shafa cikinta
"eh daddy zai Fashe"

Murmushi mai sauti daddy yayi yace
"Daga cin abinci sai ciki yafashe? To tashi hakanan ai baxanso yafashe ba"

Tashi tayi tana satar kallon mummy data wani hada rai, daman idan tayi Hakan to dawani abu aqasa

Illai kuwa tana tashi mummy ta dago tana harararta

"idan bazaki iya yafa gyallen ba kije ki sanyo hijab"

Kafin ma takai aya tayi saurin warware gyallen ta yafa don akace tasama kayannan hijab an cuceta

Murmushi daddy yayi kawai sannan ya miqomata hannu

Kama hannun tayi tana yiwa mummy saita dawo mummyn nacewa allah ya tsare


Tare suka fito da daddy hannu cikin hannu

Bala na ganinsu yayi sauri ya taso yana kwasan gaisuwa sannan yawuce motar dazasuyi amfani daita ya bude mata

Saida tagama shagwa6arta daddy na biyemata sannan tashiga motar daddy ya maida ya rufemata

Da sauri Bala ya zagaya dayan bangaren ya bude mazauninshi ya shige ya zauna sannan ya rufo

Ana tada motar daddy yaja da baya yana daga mata hannu itama tana daga mashi Bala yaja motar suka bar gidan


*UMYU*


A parking space Bala shima ya ra6a tashi motar yayi parking sannan ya sakko ya zagayo ya bude mata kofa

Gyara zaman gyallen data maido kafadarta tayi sannan taciro siririn spec fari tasa a idanunta

Ahankali ta ziro qafarta ta fito tana shaqar iskar da tarabu da shaqa na makarantar

Lumshe idanu tayi ta bude tana kallon harabar makarantar abubbuwa da dama na dawomata a qwanya


Daga farkon fara zuwanta makarantar nan zuwa yanzu abubbuwa da dama sun faru amma wancan semester din yafi abubbuwan tunawa abubbuwan da bazata ta6a mantawa dasu ba, abubbuwan da zasu dora daga inda suka tsaya a wannan semester din

Sagale jakkarta tayi a hannu tafara tafiya ahankali tana analysing din makarantar da bata wani cika ba kasancewar yau ne ranar farko na dawowa

Dama masu doqi irin ta ne ke dawowa farko farkon dawowa wadanda suka ci suka gyare kuma sai next week

Cikin tafiyarta take tafiya tana jin yadda daidaikun idanu ke Binta da kallo

Bata damu ba ta cigaba da tafiyarta harta bar harabar ta sha wata corner don wucewa tsohuwar department dinsu


Tunda ta karya corner taji gabanta ya tsinke ya fadi Hakan yasa tafara slowing din tafiyarta

Wani iri tashiga ji, feeling din is familiar, tasaba jinshi, amma a ina?

Kallonta akeyi, yes kallonta akeyi, kuma wannan feeling din tana jinshi ne idan mutum daya na kallonta...


"Zainabbb..."


Cak Kaffafuwanta suka tsaya daga tafiyar dasuke lokacin da wannan cool voice din nashi mai gardi ta ziyarci kunnenta... ✍️


Ummin fasihu 🧚🏻‍♀�
8/2/21, 9:36 PM - Buhainat😝: *🙍🏻‍♂️DEEN 🙍🏻‍♂�*


*034*


"Zainab..." taqara jin an ambata daga bayanta tana jin takunshi na qara kusantota

Runtse idanu tayi ahankali battling with her heartbeat


_*akwai changing of heartbeat ma, idan akwai soyayya duk lokacin da kuka kusanci juna ko kuna tare sai bugun zuciyarki ta chanza*_
Maganar Aunty Feenah ta rannan tashiga dawomata a qwanya


Qarasowarshi dakuma kiran sunanta da datakejin kiran har cikin zuciyarta yasa ta bude idanunta ta saukesu tarr akan fuskarshi
Fuskar da batasan haka tayi missing dinta ba sai yanzu Saidai duk kwadayin zuciyarta nason kallon fuskar to the fullest kasawa tayi saboda haske da kaifin idanunshi bazasu bari ba hakan yasata kauda nata

_*Na biyu kunya, wasu yana zuwa masu da kunya, kiji bazaki iya hada idanu dashi ba and ko kinyi bazaki iya jurar kallonshi eye-eye na tsawon lokaci ba*_
Maganar Feenah tasake dawomata


Deen dake sauke numfashin saurin dayayi ya kalleta yana murmushi, murmushin nan nashi mai tafiya da zuciya

"Zainab, is this you?"

Nan take taji kaso 80% na damuwarta yabi iska, jitayi kamar anyi lifting wani qaton dutse daga qirjinta

_*duk damuwar da kike ciki da kinyi arba dashi batareda ma kunyi magana ba zakiji kamar bakida sauran damuwa a duniyar nan*_

Sake dago idanunta tayi ta zubasu a fuskarshi


A take zuciyarta ta amince mata da maganar Feenah

Wata murya acikin kanta tafara cemata

_*you're in love Zainab!*_
_*you're in love Zainab!!*_
_*you're in love Zainab!!!*_

Saurin toshe kunnuwanta tayi da hannuwanta biyu tana runtse idanunta gamm


Deen dake magana ya dakata ganin reaction dinta

Kallonta ya tsaya yi da oily eyes dinshi cikeda ayar tambaya

"Zainab are you ok?"

Shiru kuma bata bude idanunta ba

"Zainab.." dakatawa yayi ganin ta bude idanunta ahankali tana kallonshi kallon daya sanyaya jikinshi nan take


Batareda tace komai yaga tazo tabi ta gefenshi ta zagayeshi ta wuce

Juyawa yayi yana kallonta da mammaki sai kuma yayi saurin Binta abaya

"Zainab.."

"Zainab!"

Jin muryar shi da takunshi a bayanta yasata sanin biyota yayi Hakan yasata qara pace

Ganin Hakan yasa shima qara sauri don sosai hankalinshi ya tashi ganinta a yanayin da be ta6a ganinta ba nan take duk sai murna da doqin ganinta suka koma ciki

Dakyar yasamu ya taddota daidai wata kwana yayi saurin shan gabanta

Yin gefe tayi zata wuce shima yayi saurin yin gefen ya tare tasake yin wani gefen nanma ya tare

"Zainab listen to me, are you ok?"

Dakyar ta iya bude bakinta datake jinshi a kafe tace
"ka bani hanya"

Beyi yadda tace ba sai qara matsowa dayayi gabanta yana cewa
"Zainab.."

"ka bani hanya nace!!!" tafada a mugun tsawace wanda yasashi ja baya atsorace

Dagowa tayi ta sauke idanunta cikin nashi dasuke kallonta a mammakince

"I Said go away can't you get it?! I don’t want to see you, I don’t want to talk to you, just go.. Go!"

Yadda tayi maganar yaqara kayarmashi da gaba don kwata2 kamar bata a hayyacinta

Dan qara matsowa yayi yace
"Zainab, please.."


Dafe kai tayi ta juya tabi hanyar data fito da sauri

Binta da kallo yayi harta sha kwana sannan shima yayi saurin bin bayanta zuciyarshi na rayamashi duk yadda akayi ba lafiya ba, bazai ce be ta6a ganinta a wannan yanayin ba Amma ya dade rabon da yaganta a irin wannan yanayin, tun lokacin da case din assignment dinta ya hadasu, Hakan yasashi zargin duk yadda akayi yauma ba lafiya

Koda yashawo kwanar harta kusan kaiwa gate Hakan yasa ya qara sauri dukda be iya tafiyar sauri ba, yana kallon sadda ta fita gate Hakan yasashi qara sauri dukda he's exhausted already


Yana isowa bakin gate yaga wucewar wata adaidaita

Be bi takanta ba yashiga waige waigen inda zai ganta amma babu ita babu alamunta, nan take kwakwalwarshi tabashi tana cikin adaidaitan nan

Juyawa yayi yabi adaidaitan data fara 6acemashi agani da kallo yana jin zuciyarshi na wani irin daci da nauyi


💖 💖 💖 💖 💖 💖 💖 💖 💖 💖


Mai adaidaitan yaqara juyowa karo na biyu yace
"baiwar allah nace ina zan kaiki?"

Dagowa tayi ahankali da idanunta dasuka fara chanza launi ta kalleshi sai kuma tadanyi jimm na tunanin ina zatace akaita

"any closest restaurant"

"Na'am?" inji mai adaidaitan da alamu be gane turancin nata ba

"nace gidan abincin dake kusa kusa da nan"

"oh to" yafada yana cigaba da jan napep din ita kuma ta maida idanunta ta lumshe


Tana jin yadda napep din ke slowing down harta tsaya amma bata bude idanun ba

"hajiya mun qaraso"

Sai a lokacin ta bude idanunta ahankali tana dan leqa inda suke

Jakkarta ta sagala sannan ta sauko daga napep din tayi zipping din jakkar

#500 taciro tabashi ya amsa yana shirin bude dan abin dasuke ajiye kudi don ciromata chanji yaga taqara gaba

Dan leqowa yayi yana
"hajiya chanjin fa?!... Hajiya!"

Ko nuna alamun ta jishi batayi ba tashige restaurant din

Daga kafadu mai adaidaitan yayi sannan yaima napep din key yaja shima yaqara gaba.


Cikin restaurant din is very quiet don daidaiku ne customers din wajen sai ma'aikatan dake kai kawo jefi jefi sai cool music dake tashi ta background din wajen


Wani table dake a dan kusurwa ta nufa taja daya daga cikin kujerun dake kewaye dashi ta zauna tana dora jakkarta kan
cinyarta sannan tayi interlocking yatsun hannayenta bisa table din ta dora fuskarta akai


Bata dade ahaka ba taji muryar wata waiter na yimata sannu da zuwa

Dago fuskarta tayi ta kalli yarinyar da bazata wuce sa'arta ba Amma kallo daya zakamata kasan ba bahausa bace duba da yanayin shigarta da gashin kanta

Kada mata kai kawai ta iya yi tana sauke idanunta daga kanta

"me kike so akawo miki?" tafada a cikin hausarta da bata ida zama abakinta ba

Shiru tadanyi sai kuma tadan yamutsa fuska tace
"something chill, maybe softdrink"

"wane iri ma'am"

Dan dafe kanta zee tayi don idan akwai abinda bataso yanzu to magana ne

"something milky haka"

"ok ma'am" inji yarinyar tana Juyawa

Bata dade da tafiya ba ta dawo dauke da tray dake dauke da hollandia yoghurt sai glass cups biyu a gefe

Ajiyewa tayi ganin batace komai ba saita juya ta tafiya

Ganin ta tafi yasata dan gyara zama ta jawo kwalin hollandia din ta bude murfin ta zuba a daya daga cikin glass cups din ta maida ta rufe ta ajiye sannan ta dauki na kofin takai baki tafara kur6a ahankali

_*A jadawalin alaqa dake tsakanin mace da namiji babu abota, babu yadda za'ayi ayi abota zalla tsakanin mace da namiji batareda so yashiga ciki ba, is either suso junansu ko daya yaso daya*_
Maganar Feenah tasake dawomata


_*So mahaukaci ne, real mahaukaci don yana iya hadin da kwakwalwa ma bazata dauka ba*_

_*is better kidawo hayyacinki ki fuskanci me kike ciki yadda zaki shawo kan matsalar kafin komai ya kwa6e miki*_


Lumshe idanunta kawai tayi tana nanata innallilahi waina ilaihi rajiun a ranta


Yaushe wannan abin yafaru? Tayaya? Yaushe? Meyasa?

Meyasa zuciyarta zataso Deen? Yaushe tafara sonshi ma? Tayaya tafara sonshi


Wani irin abu zuciyarta keyimata wanda bazata iya musaltawa ba hakan yasa taqara interlocking hannunta ta dora fuskarta akai tana sauraron cool music din dake tashi a background din restaurant din mai taken _did you believe in love ❤️_


*DEEN*


Ya dade nan tsaye yana bin inda suka bi da kallo kamar mai sa ran ganin sun sake 6illowa


Da yafara gajiya da tsayuwar ne saiya juya ahankali jiki a sanyaye yakoma cikin school din

Tambayoyi dayawa ne keta battling a zuciyarshi

_meya faru kuma?_

_meyasa ta fusata?_

_dama batayi missing dinshi ba?_

_yayi tunanin tayi kewarshi kwatankwacin yadda yayi mata, amma alamu ma sun nuna bama ta tashi ba take_

Tunawa yayi yadda tun saura kwana uku Ayi resuming yake ta doqin zuwan ranar badon komai ba sai don ya ganta

Yayi kewarta, kewa ta haqiqa don a tsawon rayuwarshi be ta6a yin aboki ko qawa ba sai akanta, bayan kaka babu wanda yakeji aranshi kamar ita wannan hutun ma hakanan yayi shi a darare kullum lissafin kwanakin dasuka rage suyi resuming yake ba don komai ba sai don ya ganta

A tunaninshi itama tana can tana doqin ganinshi

A tunaninshi zasu yi farinciki marar musaltawa na ganin juna bayan kusan wata daya rabon da suga juna ko suji muryar juna

Amma sai yaga akasin haka, abinda be ta6a kawo ma ranshi zai faru ba


Samun wuri yayi ya zauna kan dakalin wani office inda yake iya hango gate daga nan idanunshi akan gate din hoping zaiga 6illowarta akoda yaushe amma shiru

Tunani yafara yi a zuciyarshi akan reaction dinta

Meyayi zafi haka?
Waya fusatata?
Meyasa takoma bayan yanzu tazo?
Ina ta tafi?
Wane hali take ciki yanzu?

Tambayoyin da yaita yima kanshi kenan wanda babu mai bashi amsarsu


*ZEE*


Batasan iya adadin lokacin data dauka ahaka ba Amma tasan ta dade sosai

Hollandian data zuba a cup din ma ko rabi bata sha ba


Tunani kau tayi shi har tafara jin kwalwarta na neman fashewa amma har lokacin abu daya ta iya tsayawa akanshi shine tabbas tana son Deen

How? When and why? Shine bata saniba

Dama ana soyayya batareda wani dalili ba?

Tambayar data kasa samun amsarta kenan


Jin ta gaji da zaman yasata duba agogon wayarta

01:15pm ta gani Hakan yasa ta sauke Ajiyar zuciya tayi swiping din screen din wayar ta lalubo number bala ta dannamashi kira

Ce mashi tayi yazo ya dauketa sannan ta fadamashi inda take ta katse wayar takoma jikin kujerar ta jingina ta kafe wuri guda da kallo tayi shiru.


Ba'ayi 30mins ba saiga kiranshi wanda yabata tabbacin zuwanshi, bata daga ba ta tashi tareda daukar jakkarta ta rataya tawuce wurin biyan bill tabiya sannan tafito


Tana fitowa ta hangi motar daga can gefen titi Hakan yasa itama ta nufi wurin tana tafiya kamar wanda kwai ya Fashemawa aciki

Bude back seat din tayi ta shiga ta rufo sannan takoma cikin kujerar motar ta lafe tana lumshe gajiyayyun idanunta tana cigaba da sauraron yadda zuciyarta ke tsira takoina.


*DEEN*


Ganin lokacin zuhr yayi yasashi tashi daga bisa dakalin dayake akai Tundazu

Ahankali yafara takawa zuwa hanyar dazata sadashi masjid din school din don gabatar da sallar

Koda aka gama sake dawowa inda yatashi yayi don duk a tunaninshi zata dawo tunda dole nan drivernta zaizo daukarta

Amma shiru har lokacin asr yayi, tashi yasakeyi yanufi masjid ya sauke farali sannan ya fito

He has no option than yatafi shima Hakan yasa yanufo gate din cikin sanyi yanajin zuciyarshi na qara jagulewa


Koda yafito ma tsayawa yayi a gefen hanya ya kafe titi da idanu yayi shiru tunanika kala2 na kai kawo a zuciyarshi

Ya dan jima sannan wata adaidaita ta gitta ya tsaidata

Cikin sa'a yana gayamashi inda zaya yace yashigo suka bar wajen.


***


Yinin ranar haka suka qarasheshi cikin rashin walwala musanmman zee

Sanin cewa ta kamu da sonshi ba qaramin daga mata hankali yake ba gashi da alamu dai kamar yadda Aunty Feenah ta fada qila ita kadai ke haukanta

Meyasa to? Meyasa zuciyarta zata yimata haka? Ya zatayi da son nashi? Tadai san ko mutuwa takeyi tana dawowa bazata iya bayyanamashi halin da zuciyarta ke ciki gameda shi ba, yama zatayi wajen yin Hakan? Sam bazata iyaba

Sosai zuciyarta ta shiga damuwa, damuwar makomarta don tasan idan zataso abu bata iya sonshi ba kamar yadda bata iya qin abu ba

Idan taso abu da dukkan zuciyarta take sonshi haka ba idan ta tsani abu ta tsaneshi kenan ko me za'ayi abin baya ta6a burgeta

Dole ne, dole ne tayi gaggawar takawa zuciyarta burki, ta yakiceshi daga ciki da qarfin tsiya Koda Hakan zai illatata

Saidai ta yaya? Yanzu haka idan da abinda take son gani to shine

Sau biyu ta kalleshi dazun amma sai gizo fuskarshi ke mata

Kunnuwanta babu abinda suke son ji kamar muryarshi

Babu abinda takeso yanzu sai kasancewa tare dashi, to tayaya zata iya abinda ta quduri yi?


*WASHEGARI*


Sa6anin jiya, yau sukuku ta tashi tana jin idanunta na mata wani nauyi2 sanadiyar barcin da be ishesu ba


Da farko tayi niyyar yin zamanta agida kawai basai taje school ba Saidai kuma sanin cewa zaman bazai wani amfaneta da komai ba inbanda qarin damuwa ba yasa ta fasa

Bayan haka kuma zuciyarta na son ganinshi itace ma ke ingizata akan taje din koba komai zata ganshi wanda Hakan zai sanyaya mata rai ko yayane

Dama tasani, Dakyar zata iya controlling zuciyarta a wannan ga6ar don zuciyarta is very fragile and sticky, idan ta damqi abu Dakyar take iya saki musanmman ma a wannan ga6ar da takejin abinda bata ta6a ji ba akan abu

Bazata iya musaltawa yadda takeji ba Saidai kawai tasan shine maganin matsalar ta, ganinshi zai yayemata damuwarta, murmushin shi zai sanyaya mata zuciya, muryarshi kuma zata sakata a shauqi sosai


Dayake komai yinshi takeyi kamar lakka Hakan yasa taita jan jiki har 9 tawuce sannan ta fito

Wajen motar dazasu fita dasu ta wuce tana tafiya a hankali

Koda tazo dama bala yariga ya bude mata kofa Hakan yasata shigewa kawai

Zagayawa bala yayi shima ya bude mazauninshi ya shige sannan suka fice daga gidan


*UMYU*


Jin qarar budewar kofa yasata bude idanunta data lumshe tunda suka Kamo hanyar tahowa

Sotake ta taso ta fito amma takasa Hakan yasa ta maida idanunta taqara lumshewa

Takusan mintuna biyu ahakan sannan tasake bude idanunta ta yunqura dakyar tafara niyyar fitowa

Qara matsawa baya bala dake tsaye Tundazu yayi ta fito sannan ya sunkuya ya dauko mata jakkarta da tabaro aciki ya miqamata

Saida tagama gyara yafin gyallenta sannan ta amshi jakkar tana ratayeta kasancewar side bag ne

Bata qara bi takanshi ba ta juya tafara tafiya ahankali


Yau ta lura makarantar tafi jiya cika

Ba abin mammaki bane don dama da kadan kadan za'aita dawowa har zuwa next week da makarantar zata cike


Wannan karon sabon department dinsu ta nufa Saidai Koda taje Wurin daidaikun mutane tagani kuma duk maza Hakan yasa tayi kwana ta koma inda tafito

Tsaki taja a zuciyarta tana jin qunci da kadaici sosai tama rasa inda zata nufa kuma

Zuciyarta ce ta yanke mata ta wuce tsohon mazauninsu inda suke zama dasu sumee

Can din tanufa tana jin kanta na mata nauyi saboda rashin isashen barci

Akwai qura sosai akan bench din dasuke zama amma kasancewarta agajiye yasa tasa hanki dinta ta kakka6e inda zata zauna kawai ta zauna tana maido jakkar akan cinyarta sannan jingina kanta da bishiyar bayanta ta lumshe idanu


Ta dan jima a wajen a Hakan idanunta still a rufe sai jitayi zuciyarta tafara chanza bugu


Wannan feeling din datake ji duk lokacin da yake kallonta ya biyo baya

Zuciyarta ce tayi motsi da qarfi wanda Hakan yasa ta bude idanunta ta dago bashiri bata saukesu a koina ba sai akan kamillaliyar fuskarshi


Batasan ko ya akayi ba sai jitayi takasa Janye idanunta akanshi duk yadda taso Janyewa kuwa yadda kasan anyi magnetting din idanunta akan fuskarshi

Zuciyarta tashiga narkewa ahankali cikin shauqin ganinshi


Shima Deen dake jingine da bishiyar dake facing dinta Tundazu ita yake kallo yana son karantar abubbuwa da dama a fuskarta amma it's blank baya iya hango komai

Dagowa yayi daga jinginen dayayi da bishiyar yafara takowa ahankali batareda ya bar kallonta ba harya kawo gabanta yana dan basu tazara a tsakaninsu


Ahankali ya rage tsawo ya daidaita tsawonsu ta hanyar duqawa wanda Hakan yasa itama tabiyoshi qasa da idanunta

Cigaba da kallon juna sukayi aka rasa wanda zai magantu


Lumshe idanu tayi akan fuskarshi tasake budewa tana jin yadda emotions ke building up a kowacce kusurwa ta zuciyarta Hakan yasa hawaye suka fara taruwa a idanunta

"Zainab.."

Maida idanun tayi ta lumshe tana kallon gefe

Ita kadai tasan yanayin da muryarshi ta jefa ta, jitake kamar tana yawo a gajimare

"Zainab meke faruwa? Meke damunki?"

Qara tamke idanunta tayi trying so hard wajen controlling emotion dinta

"Zainab.."

Saurin miqewa tayi tsaye tayi wanda yayi daidai da miqewarshi tsaye shima

Juyawa zatayi ta tafi yayi saurin shan gabanta

6ata fuska yayi yadda yasaba yana cewa
"O'O! Please say something Zainab"

Sake kauda kai tayi tana jin yadda shagwa6ar tashi tayi tasiri akanta sosai

"please Zainab kiyi magana, am so worried, jiya ma haka kika tafi naita jiranki baki dawo ba kuma yanzu zaki sake tafiya, don Allah ki fadamin, are you angry with me? Wani laifi nayimiki? Please tell me and I promise to apologize, zan baki haquri"

Jin hawayen datake ta maqalewa na neman sakkomata yasa tayi saurin kauda kai ta chanza hanya zata bi

Ganin Hakan yasashi saurin tarewa again

Bata kulashi ba ta chanza wani yasake bi ya tareta Hakan yasata dagowa a fusace tace
"wai menene haka?! I said leave me alone can't you get that?!"


Dan jada baya yayi yana kallonta cikin rashin sanin abinda zaice ganin Hakan yasa ta ra6a gefe zata wuce don jitake kamar zuciyarta zata Fashe saboda bugun datakeyi

"Zainab, saboda kyautar da na maido miki kike fushi?" Tambayarshi ta dakatar daita daga tafiyar data fara


Ganin ta tsaya yasashi dan takowa yadan rage tazarar dake tsakaninsu

"am sorry amma ni bada wata manufarba nayi Hakan, na lura tun ranar ranki ya 6aci akan Hakan amma ni banyi Hakan da nufin 6ata miki rai ba, am sorry babu kyau gaba"


Hawayen ne suka silalo mata ahankali Hakan yasata cigaba da tafiyarta da sauri don bata buqatar yagansu

Binta da kallo yayi jiki a sanyaye batareda yasake yunqurin binta ba, yana ganin kamar ba Zainab din daya sani bace, kamar an sauyota... ✍️


Love in the air💃


Wannan labarin is all about love ❤️ a very emotional love story wanda zai antaya ma karanta da dama cikin shauqi har yakawo qwalla a idanun masu raunin cikinsu

It's all about true love, sadaukarwa da heartbreak.

stay tuned insha allah wannan book din zai zama one of your favourite book ever 🧚🏻‍♀�


Ashaanty love 💖
8/2/21, 9:36 PM - Buhainat😝: *🙍🏻‍♂️DEEN 🙍🏻‍♂�*


*035*


*2 DAYS AFTER*


Kwance take a tsakiyar gadonta ruff da ciki ta cusa fuskarta a pillow qaffafunta a sama tana ta dan wuwullawa


Yau kwana biyu kenan rabonta da school

Tun ranar da ta tafi tabar Deen tsaye a inda yasameta

Daga ranar bata qara zuwa school ba saboda gudun haduwarsu don bata fatan sake jin abubbuwan dataji gameda shi ranar shiyasa ta yanke shawarar qin zuwa school din duk don tasamu sauqi ashe Hakan ba sauqi bane ba

Bata gane Hakan ba sai cikin kwanakinnan biyu


Halin data shiga a cikin kwanakinnan biyu ya sake tabbatar mata cewa ba qaramin nutso tayi ba a kogin soyayyar Deen ba kuma ya tabbatar mata cewa qaurace mashi ba mafita bace agareta ba don a cikin kwanaki biyun nan tashiga halin da taji gwara ta dinga ganinshi din ko babu komai zataji sanyi a zuciya

A cikin kwanakinnan ta gano cewa rayuwa batareda Deen ba kamar rashin gishiri ne a abinci, bazakayi saurin lura da kasantuwarshi ba bare alfanunshi sai idan babu shi

Taji kuma ta gane cewa rayuwa bataredashi ba rayuwa ce mai cike da qunci da azabtuwar ruhi

Batasan sadda tafara sonshi ba kuma bata tunanin akwai lokacin da zata daina don a cikin kwanakinnan ta gano abubbuwa da dama gameda yadda takeji gamedashi

Da farko gani take nisantarshi zai zamemata mafita yadda zata manta dashi gradually amma a cikin yan kwanakinnan ta qaryata Hakan don tun kafin akai koina tafara wahala

Takoma gatanan dai kullum soo moody komai baya mata dadi a duniyar nan


A cikin kwanakin is either kaganta zaune shiru tayi nisa cikin duniyar tunani, ko kuma kaji tafara rairo wani baiti wanda yayi daidai da abinda take ji a lokacin

Ko wanne mutum da irin baiwar da allah yabashi, both ta 6oye data bayyane

Wasu har su koma ga mahallicinsu basu gane baiwar da allah yayi musu

Wasu suna ganewa amma basa ta6a amfani da baiwar a aikace

Daidaiku ne masu bayyana baiwar su ga jama'a suyi amfani daita ta kuma zama garkuwa agaresu


Zee nada baiwa guda wanda bata san dashi ba, ko tasani to bata maida kai akanshi ba

*WAQA*

Allah ya yimata baiwar iya tsara baiti a nan take kuma kaji yahau yayi dadi kamar wanda aka zauna akayi nazari sosai aka tsarashi

Tun tana qaramarta takeda habit din qirqirar waqa datayi daidai da yanayin datake ciki walau farinciki ko akasin haka


Saidai ko kadan bata ta6a maida hankali akan haka ba don abin kawai yazama kamar cikin jininta yake bata ganinshi a matsayin wani abu daban daya kamata ta fiddoshi fili ba mutane su sani harma tayi tunanin zama wani abu da Hakan


Ahankali ta dago fuskarta daga ciki filon ta dora ha6arta akan hannuwanta dake bisa juna kan pillon suma ta kafe mirrornta da idanu


_my heart beats_

_echoes into the cold streets_

_where nightmares and darkness.._

_begin to meet!!_

_how?_

_how did I fell in?_

_how did I fall for.._

_the cold hand of LOVE_

_I have always been so afraid_

_of losing people I love_

_but sometimes I keep asking myself_

_is there anyone out there_

_anyone out there_

_who’s afraid of losing me too_

_sometimes one hello_

_makes you never want to say goodbye_

_SO_

_dadin fada a baki ne dashi_

_amma a zuciya in yayo dashe ..._

_zance ya lalace!_

_yaushe ne nafara?_

_yaushe zani gama?_

_yaushe zanji rahma?_

_rahama da sallamar ruhi_

_I want to push you_

_push you out of my heart_

_but every breath I take_

_proves I can't live without you_


Saukar abu mai dumi dataji a kumatunta yasata tasan kuka take again

Kukan da ba yanzu tafara shiba kuma ba yanzu zata gama shiba

_I wish_

_I wish_

_I wish... Am wishing_

_and wishing_

_but I don’t know what to wish_

_to have you or to leave_

_cos when my brain said NO.._

_my heart says YES!_


Lumshe idanu tayi wasu hawayen suka sake gangaromata

_Ina ma.. Ina ma_

_zuciya idan tasamu rauni_

_za'a iya yanke daidai raunin_

_ina ma.. Ina ma_

_za'a iya numfashi ba zuciya... da na bada nau kyauta_

_ina ma.. Ina ma_


_za'a iya maida hannun agogo baya... Dana tsallake haduwarmu dakai_

_ina ma_

_ina ma..._


Saita kasa idawa ta maida kanta ta cusa cikin pillow tana shesheqa ahankali

Ita kadai tasan abinda takeji babu kuma wanda zai san abinda takeji sai wanda ya tsinci kanshi acikin irin wannan yanayin

Ace ka kamu da soyayyar wanda har abada bakajin kana iya furta Hakan gareshi

Ba soyayyar bace illah, barinta a zuciyar tafi komai illah

Domin fitowarta tafi linketa a zuciya

Amma tayaya zata bayyanata?

Tayaya?

Allah ya hallici mace da kunya da kawaici wanda Hakan tamkar ado ne agareta

Duk macen da batada su to ta tashi daga mace ta koma wani abin daban

Yaya zatayi?

Cigaba zatayi da qumshe abinda takeji a zuciya?

Koko ajiye wannan adon nata a matsayin ta na mace zatayi ta fitar da abinda ke ranta?

Yaya zatayi?

She's damn confused.


_*it's better kidawo hayyacinki, ki fuskanci me kike ciki yadda zaki shawo kan matsalar kafin komai ya kwa6e miki*_
Maganar Aunty Feenah ta rannan tadawo mata a kwanya

Yanzu ta fuskanta, meye mafitar

Wani abu yayi clinging a brain dinta hakan yasata saurin tashi zaune ta jawo wayarta dake kan bedside locker tashiga contact ta lalubo number Aunty Feenah

Har zata danna dail botton sai kuma takasa

Yanzu idan ma ta kirata me zata cemata? Ta ina zata fara?

Hakan yasata chanza shawara tafita daga contact din ta kunna data connection dinta ta shiga whatsapp app dinta


Messages suka fara Shigowa Hakan yasa ta tsaya har Saida suka gama Shigowa sannan tashiga contact ta lalubo number Aunty Feenah

Gani tayi batafi awa da sauka ba hakan yasa tashiga keyboard tafara typing kamar haka

_*Barka da wuni Aunty, ya mutanen Ruma? Yasu umma?*_

_*Please Aunty I need your help.. Na fuskanci matsalar, meye mafitar?*_


Saida ta tsaya taqara karantawa sannan ta danna send botton ya shiga

Shiru tayi tana kallon message din data tura hoping Aunty Feenah zata samarmata mafitar dazata sauqaqa mata abinda takeji

Saida ta gaji don kanta sannan ta rufe datarta ta sauka hoping lokacin dazata sake hawa zata tararda amsar mafitar ta


💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖


"wai haryanzu baka gamaba kyakyawa na?" inji kaka data leqo dakin nashi a karo na uku

Dagowa yayi daga zagaye abincin dayake da cokali ya kalli kaka dake bakin kofa tana kallonshi shima

"Kaka nidai allah na qoshi" yafada yana 6ata fuska

Sakin labulen tayi tana ida Qarasowa ciki

"bangane ka qoshi ba? Abincin da kafi so fane, ka duba da kyau, ko wani abu ne beji ba?" tafada tana amsar cokalin hannunshi tayi tasting taji komai daidai

"Kaka komai yaji kuma yayi dadi sosai kawai na qoshi ne"

"kyakyawa na, ko wani abu na damunka ne? Nina kasa gane kanka tun shekaranjiya wacan, ka koma wani iri gakanan abinci ma kanshi baka ci, sokake qwalsa ta kamaka mushiga uku?"

Murmushi Deen yayi ganin yadda take maganar cikin damuwa

"Kaka ulcer ce ba qwalsa ba"

Tallabe mashi qeya tayi tace
"kajimin ja'iri ana maganar qwarai yana sanyo wasa aciki, ina ruwana da koma mecece? Tunda dai ka gane ba shikenan ba?"

Shafa qeyarshi yake yana kumbura fuska alamun yaji zafi

Tsaki taja tace
"yanzu zaka fadamin abinda ke damunka din ko kuwa?"

Zamewa yayi ya dora kanshi bisa cinyarta ya lumshe idanu
"Kaka banajin dadi, kaina na ciwo kuma bakina babu taste"


Nan take kaka ta rude
"dagaske? Tun yaushe? Meyasa baka gayaminba?
Maza tashi indauko maka paracetamol kasha, waya gayamaka ana zama da ciwo?"

Sai a lokacin qaryar dayayi ta dawo mashi, cewa yayi beda lfy ko?
Innallilahi! Meyasa yace haka? Yanzu shan magani farilla.
Dama Dakyar yasamu tabar bashi wadancan don ko bayan warwarewarshi tilasta mashi take saiya sha Dakyar yasamu ta yarda ta kyaleshi gashi yasake jama kanshi


Saurin tashi yayi daga kan cinyarta yace
"Kaka dama shekaranjiya kan ke ciwo kuma nasha magani tun a school, tun ranar ma na warke yanzu lafiya lau nake, Allah" yafada yana 6ata fuska ganin kallon datake binshi dashi

"hmm daga baya kenan, magani ne sai kasha, ashe dama bakajin dadi ne shine daka fadi gwara kaita zama da ciwon saboda rashin son magani? To allah ya matsi bakinka kuma babu abinda zai hanaka sha don bazan zuba maka idanu kayi ta zama da ciwo ba" Tana kaiwa nan ta tashi ta nufi kofar fita tanata sababi ita kadai

Binta da kallo yayi harta fita sannan ya dafe kai tareda lumshe idanu cikin rashin sanin abin yi


Babu abinda yafi tsaya mashi arai kamar zee, yakasa sukuni kwata2 akanta

Jiya da yau haka yakusan wuni a makaranta cikin saka ran ganin ta amma ko mai kama daita be gani ba

Sosai abin ya dameshi don haka kawai yaji beson loosing dinta a matsayin qawa ko don be ta6ayin abokin da sukayi shaquwa kwatankwacin wanda sukayi da ita?

Yana nan zaune kaka tadawo da sachet din magani da ruwa a kofi

Ganin yadda ta tamke fuska yasa yasan ko me zayayi sai yasha Hakan yasa be ba shara'a wahala ba ya amsa sadda ta miqomashi yanajin kamar yayi saboda warin maganin daya bugi hancinshi

Kamar dai yadda yasaba wannan ma Dakyar ya hadiyesu sannan yakoma ya kwanta yana maida numfashi kaka nata jeramashi sannu

Tattare abincin da beciba tayi ta fita dasu sannan tadawo ta rufeshi da bargo har iya wuya sannan ta shafa sumarshi tana cewa yayi barci qila kafin yatashi ciwon kan ya lafa

Kada mata kai kawai yayi ya maida idanun ya rufe yana sauke Ajiyar zuciya ahankali

Ta dade tana qaremashi kallo tanajin wani irin tausayinshi na ratsa mata zuciya

Addu'a tayi mashi ta tofeshi dashi sannan ta tashi ta fita tana share hawaye ta jamashi kofa

Ahankali ya bude idanunshi bayan fitarta yayi juyi a gadon yana qara qudundunewa a bargon yasake lumshe idanu yayi luff kamar mai barci amma ba barcin ba yake


❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️


Sake hawa tayi a karo na uku, still babu amsa amma ga alamun an karanta nan yafito amsar ce dai ba'a bada ba

To me Hakan ke nufi? Tambayar data yiwa kanta kenan

Dubawa tayi taga she's still online kawai batayi niyyar tankamata bane

Haushi taji amma ya ta iya? Ita ke nema dole tayi haquri

Sake typing tayi
_*Aunty Feenah baki bani amsa ba, am waiting please*_
Tasake sandawa

Saida aka kusan mintuna biyu da turawa sannan taga alamun an karanta Saidai tajira har tsawon mintuna goma shiru ba amsa babu kuma alamun typing ake

Ranta ne yaqara 6aci, tasan wulaqanci kawai Aunty Feenah keyimata don gashi nan sarai ta gani kawai amsarce batayi niyyar badawa ba

Hakan yasa ta kirata video call ta whatsapp din

Saida takusan katsewa sannan aka daga, nan take Feenah ta bayyana kwance akan gado kanta sanye da hular net ta barci

"ya?" inji Feenah cikin halin ko in kula da so6are so6aren da zee keyi

"haba Aunty, nayi maki magana kin shareni alhalin kin gani, haba Aunty" tafada kamar zatayi kuka

"a ina kikayi Magana?" inji Feenah

"anan mana, kuma kin karanta kikayi ignoring dina"

"a ina wai, sai wani anan kike, ina ne nan din?" tafada cikin masifa daya riga ya zamemata jiki

Turo baki zee tayi kamar zata fasa kuka tace
"ba texting dinki nayi ba via whatsapp? Kuma ai kingani"

"naga me? Naga waiting dai, waiting for the message yasa ni banga komai ba"

Dan murmushi zee tayi don tasan tabbas ta gani kawai rainin hankali ne irin nata

"to bari nasake turomiki.."

"kinga idan bazaki fada min yanzu ba karki kuskura ki sake damuna, yanzu bakinki ciwo yakeyi da bazaki fadaba sai na tsaya jira kinyi typing? If you're not serious zan kashe wayata yar rainin hankali kai"


Zee data turo baki tun sadda tafara ta qara 6ata fuska, dama tasani tagani sarai kawai sotake ta furta da bakinta

"dama.. Dama maganar rannan ce.. Shine nace na gano matsalar meye mafitar?"

Dariya sosai taba Feenah a dayan 6angaren Saidai ta dake taqiyi a cikin zuciyarta tana cewa 'yaro man kaza"

A zahiri kuma tace
"matsala? Matsalar me kuma ana zaman lfy?"

Kukan shagwa6a zee ta fashe dashi tana cewa
"kai Aunty Feenah, kinfa san komai kawai pretending kike"

Tsaki Feenah taja tace
"bakida aikin yi" tana shirin katse kiran Hakan yasata saurin cewa

"maganar Deen din damukayi Aunty wanda kika ce am in love with him na qaryata shine nace na gano matsalar ki fadamin mafitar" Tafada kamar tayi kuka

"meye matsalar to?"

Fashewa da wani kukan shagwa6ar tayi tace
"kai Aunty, kinfa sani, ina sonshi mana"

Sai a lokacin Feenah tashiga yin dariyar da taketa dannewa Tundazu harda kyakyatawa, iya cika zee ta cika famm sai kumburi takeyi

"shashasha! Dama nace ina nan ke da kanki zaki nemeni ba ke yar rainin sense ba? Ana so ana kaiwa market? Kadan kika gani yarinya" tafada tana yin kwafa

"nidai yanzu tunda kinsani fada a taimaka min abani mafitar" inji zee tana kwa6e fuska

"yaushe kikayi realising haka?"

"ranar damukayi resuming school, ina dora idanuna akanshi nayi realising na afka" tafada tana rufe face🙈

Dariya Feenah tayi tace
"awwn! Love in the air 😘 sai kikayi yaya? Badai gayamashi kikayi ba"

"kai Aunty, tayaya ma zan fara? Never and ever"

"to yanzu ya ake ciki?"

"Aunty tun lokacin danayi realising Hakan sai naja baya dashi, bana yarda magana ta hadamu amma sai ya cigaba da nacemin duk inda nayi saiya bini Hakan yasa kwana biyu kenan rabona da zuwa school saboda shi duk don incireshi a rai kafin abin yayi nisa amma wani abin mammaki Aunty bakiji yadda naji a kwanaki biyun nan ba, kamar ana sake huramin wutar sonshi, am helpless, na rasa yadda zanyi, yanzu haka babu abinda nakeson gani kamar shi"

Tsaki Feenah taja
"banda ke shashasha ce dama angayamaki yin nesa dashi mafita ce? Da mafita ce da tuni kin shawo kan lamarin tun a hutun ku tunda ba hadewa ba kuke, abinda muke magana a yanzu shine what your heart wants, zuciyarki na sonshi kekuma kina nisantata dashi dama ina za'aga zaman lafiya?"

Zee dake jinta Tundazu tace
"to Aunty meye mafita? Ni gudu nake kar muna tare abin yaita gaba gaba har yakai stage din da bazan iya controlling dinshi ba kuma ba sona yake ba"

"shi yace miki baya sonki? Meyasa zaki yanke cewa baya sonki tun yanzu"

"da yana sona ai da ya nuna min Aunty"

"wawuya, to kika sani ko shima beyi realising yana sonki ba? Duka kema yaushe kikasani? Kika sani ko shima yana sonki sani ne beyi ba? Baki tsaya kikayi tunani ba kika yanke shawarar nisantarshi"

Shiru zee tayi tana calculating din maganar Feenah

"tayiwu shi ma is in love with you besaniba ko kuma yasani amma yakasa samun courage din fadamiki koko kinyi it's very easy to say I Love You? Idan da da sauqi ai da kema kin furta
Wataqila yana can shima yana tunanin ta hanyar dazai fadamiki amma kuma kike neman nesanta kanki dashi wanda Hakan ba komai zaiyi ba sai sagar mashi da gwiwar da zaiyi yakasa furtawa ku biyun ku cigaba da wahala

Kinga ita soyayya idan an shigeta anshigeta ne babu batun backing off don indai ta Gaskiya ce jada bayan bazai amfaneku da komai ba saima qarin wahala dazaku jama kanku, so karki kuskura Kiyi wannan mistake din, stick on ku koma yadda kuke da zai furta maki am assuring you"

Zee datayi tsit Tundazu tana sauraronta cikin gamsuwa ta sauke Ajiyar zuciya tace
"to idan muka koma yadda muke da din shaquwarmu ta linka da daga baya nagane ni kadai ke hauka na fa?"

"think positively zee, insha allah Hakan ma bazata faruba, kina da komai da namiji zai soki dashi, baki rasa komai ba zee, bayan haka akwai hanyoyi da dama da mace zata nuna alamomin soyayyar ta ga namiji ta dasa mashi tata a zuciyarshi batareda ta furta ba

Ciki akwai kyautatawa, zuciya ko wacce iri ce tana son mai kyautata mata kema kin sani
Iya wannan ya isa and am telling you zaki samu zuciyarshi, zaki shige ciki Kiyi bake2 am telling you"

Murmushi zee tadanyi saikuma ta kalli Feenah dake cikin screen din wayar tace
"amma Aunty Feenah naji kince kema kin ta6a tsintar kanki a wannan yanayin, waye mutumin? Yaya Auwal?"

Yanayin Feenah ne yadan chanza sai tace
"A'a na gayamaki wancan ko sanina beyi ba ko kin manta?"

"eh hakane, to waye shi? Kuma ya akayi kema bakiyi amfani da abinda kika cemin ba wajen ganin yasoki"

Shiru Feenah tadanyi sai kuma tadanyi murmushi wanda yafi kama da na takaici tace
"I told you be sanni ba, besan fa wanzuwata ba tayaya zanyi yadda na gayamaki? Wannan sai idan akwai sannaya ko yayane kamar dai naku amma wannan Saidai na ganshi a hanya ko sunan shi ban ta6a sani ba har kawo yanzu

Kuma bazan iya cusa kaina gareshi ba that's not perfect a matsayina na mace dukda kuwa nayi qoqarin lurar dashi yasan dani amma be saniba ko don banje directly ba? Yes nace maki ki kyautata mashi bawai ina nufin kiyita rawar kai ba, maza basason mai rawar kai sunfison mai aji kamar dai ke dinnan, karki chanza mashi in anyway har yagane kina mashi rawar qafa amma ki cigaba da bayyana mashi kyawawan hallayenki a kaikaice da duk abinda zaisa ya dinga ganin mutuncin ki ki kuma dinga burgeshi ciki harda son family dinshi, kowanne namiji yana matuqar alfahari da mai son family dinshi, mai nuna damuwa da kulawa akanshi dama sauransu

So bawai rawar kai zakiyi ba, no, ki cigaba da zama classic girl dinki don class adon mace ce dukda ba'ason yayi yawa, insha allah zakiga komai yazo miki cikin sauqi, insha allah"


Sosai zee ta gamsu da bayyanan Feenah Hakan yasa taji zuciyarta ta rage nauyi ga wani qwarin gwiwa datakeji tasamu sosai Saidai kamar taga yanayin Feenah ya chanza tun lokacin da ta ambato mata wancan mutumin

"bye, am sleepy ki gaidamin yaya da daddy" inji Feenah

Zatayi magana taji qiit an katse wayar

Bïñ wayar tayi da kallo taga tama sauka Hakan yasa itama ta sauka ta ajiye wayar gefe tayi folding din hannunta a qirji tashiga dauko magangganun Aunty Feenah da daddaya tana masu filla filla


*WASHEGARI*


Yau juma'a kuma yau ta tashi da qudurin zuwa school, jiya ta dade idanunta biyu tana nazarin magangganunsu da Feenah takuma yanke shawarar zata gwada tagani Hakan yasa ta yanke shawarar zuwa school yau


Kamar yadda tasaba duk ranar juma'a yau ma bata fito da wuri ba sai bayan sallar juma'a

Sanye take cikin shadda dark purple buba wanda tasha aiki mai kyau daga daman rigar har qasa

Kanta yafe da farin siririn gyale, takalminta farare haka ma jakkarta da agogonta

Motarsu tanufa tana zuge zip din jakkarta data fiddo waya daga ciki

Koda ta qaraso har bala ya budemata kofa Hakan yasa ta shige ya rufo ya zagaya shima ya shige suka fice daga gidan


*UMYU*


Tunda suka shigo harabar makarantar zuciyarta tafara qara gudu

Bata san meyasa ba sai jitayi tana fargaba, fargabar yin amfani da shawarar Feenah nan gaba abu ya kwa6e mata

Batayi nisa a dan guntun tunanin data fara ba taji an budemata kofa Hakan yasa ta lumshe idanu ta bude sannan taja nannauyan numfashi sannan tafara yunqurin saukowa


Iskar dake kadawa ya bugi fuskarta Hakan yasa ta lumshe idanu tasake budewa tana shaqar sanyayar iskar dake kadawa

Rataye jakkarta tayi a hannu tafara tafiya tana dan kallon harabar da daidaikun mutane keta kai kawo


Tasan yau mutane qalilan ne suka zo don dama ko anyi resuming fully mutanen dake zuwa ranar friday basada yawa bare yanzu da ba'a ida resuming ba


Ahankali ta cigaba da takawa a cikin zuciyarta tana tunanin anya kau yau zasu hade da Deen? Tasan ba lallai bane su Hade ba don ba lallai bane yazo yau ba Amma still tana sa ran ganinshi

Tunawa tayi da kalmarshi ta rannan

Wai ko fushi take saboda ya maido mata wayarta? Wato yasan abin da ban haushi kenan, yasani dagangan yayi mata

Saikuma wani tunani ya bijiromata a kwakwalwa

Wane tunani zaizo mashi bayan tafiyar ta a ranar?

Qila ya dinga yimata kallon mai riqo marar saurin yafiya tunda har haquri yabata amma taqi sauraronshi

Tunawa tayi da lokacin da tabashi hqr akan watsamashi coke datayi yakuma haqura nan take batareda ya qullaceta ba

Saita auna abubbuwan biyu a mizani sai taga idan ma qullatar ne shi yafi cancanta ya qullaceta a lokacin ba itaba saboda shi yanada right din amsar abinda yayi mashi yakuma maida abinda beyi mashi ba dukda ba dadi maida kyauta hannun kyauta baya

Yanzu tasan kallon mai riqo da rashin saurin yafiya zai dinga yimata kuma bataga laifin shi ba don kusan haka ne tunda ga lokacin takasa tsayawa ta saurareshi dukda iyakar bakin qoqarin shi dayayi na ganin tayi Hakan


Ahankali bugun zuciyarta yafara qaruwa sannan wannan feeling din data saba ji idan yana kallonta tafara jinshi


Dago kai tayi tafara dan waige waige ahankali don ganin inda zata ganshi

Daga can jikin wani office mai facing dinta ta ganshi jingine da bango hannuwanshi harde a qirjinshi

Ja tayi ta tsaya itama tana kallonshi kamar yadda shima yakeyi

Ganinshi a yanzu yasata samun daya daga cikin Tambayoyin datakewa kanta

Yaushe?

Yaushe tafara sonshi?

Ganinshi datayi yau da shigar dake ajikinshi yabata amsarta

Tafara sonshi ne ranar data fara ganinshi

Rana mai kamar ta yau, sanye da shiga irin ta yau

Ranar da bracelet din hannunshi ya sarqaho mata gyallenta

Sai yanzu tagane ma'anar Hakan, wato Hakan na nufin bond ne tsakaninsu tunma kafin susan juna

Bracelet dinshi ya sarqaho gyallenta ne don akwai alaqa mai qarfi dazai qullu tsakanin mammalakin bracelet din da mammalakiyar gyallen

Haka kwakwalwarta ta bata, hakane!

Kasa dauke ido akan juna sukayi suka cigaba da kallon juna kowanne da irin kibiyar dake fitowa a idon dan uwanshi yana fadawa nashi


A hankali murmushi yafara forming a fuskarta tana cigaba da kallonshi

Dukda bata ganin fuskarta amma tasan this is the sweetest smile ever data ta6a yiwa wani

Gani tayi yayi blinking idanu sau biyu kamar na mai son tabbatar da abinda yake gani can kuma ya miqe daga jinginen dayake da bangon yana cigaba da kallonta kamar mai son tabbatar da wani abu

A hankali shima fuskarshi tafara washewa, murmushi yafara gauraya fuskar, wannan cool murmushin nashi mai tafiya da zuciyarta... ✍️


Ummin fasihu 🧚🏻‍♀�
8/2/21, 9:36 PM - Buhainat😝: *🙍🏻‍♂️DEEN 🙍🏻‍♂�*


*036*


"Am happy kinzo Zainab, jiya da shekaranjiya haka na wuni a school dinnan amma ko sign of you ban ganiba, am damn worried" inji Deen cikin cool voice dinshi fuskarshi dauke da murmushi

Zee dake kallonshi shima tadanyi murmushi ta dora jakkarta akan desk din library din ta dora hannunta kan desk ta buga tagumi

"and why are you worried?" tafada tana kallonshi

Murmushi yasake saki ya dan kauda kai sannan yasake kallonta
"saboda yanayin da muka rabu rannan, it's not normal shiyasa nashiga damuwa"

"damuwa akan me?" tasake Tambayar shi

"damuwa akan halin dazaki shiga"

"meyasa ka damu to?"

"saboda nasan nine sila"

Dan daga gira daya tayi
"really?"

Kada mata kai yayi yace
"yeah, and I begged you amma kinqi saurarena"

Kauda idanunta tayi akanshi tana jinta a wani yanayi jin yace _*i begged you*_

He's so innocent, beda matsala ko kadan, beda girman kai irinna wasu samarin, yayi ta koina.


Jin tayi shiru yadan qara matsowa jikin desk din data raba tsakaninsu yace
"am sorry, qila lokacin banyi explaining kaina ba yadda ya kamata shiyasa kikaji haushi but the truth is banyi haka don kiji haushi ba, Swears"

Murmushi tadanyi, ba na komai ba saina tausayin kanta, soyayyarshi a zuciyarta qara qaruwa take da duk wani kalma tashi

She's confused, tarasa gane wannan abu

Lokacin data qaurace mashi zuciyarta ta azabtu yanzu kuma dasuke tare zuciyar qara dulmiyawa take tana qara yin nisan nisa a sonshi, Tambayar anan itace dama haka so yake? Koko nata yazo da hakan?


"kinyi shiru" inji Deen yana kallonta

Itama kallonshi take, idan yana wani abin kamar shima sonta yakeyi, koko shima sonta yakeyi? Koko da Gaskiyar Aunty Feenah shima yana sonta bedai gano bane? Koko ya gano bazai iya fadi ba? koko hakanan yake wannan abin babu sonta a ranshi? She's confused

Ajiyar zuciya ta sauke sannan tace
"ok duk naji amma ban huceba"

6ata fuska yayi yace
"O'O! Meyasa? Haven't I apologize?"

"you have amma it's not accepted"

Shiru yayi yana kallon na wani lokaci sannan yace
"then tell me what to do"

Gyara zamanta tayi ta kalleshi taga ya buga tagumi shima yana kallonta alamun yana jinta ga murmushin dayaqi barin fuskarshi Tundazu

Itama murmushin tayi sannan tace
"idan kanason in huce saika amsa"

Dan 6ata fuska yayi yace
"O'O! Please mubar maganarta haka nan mana"

Daga kafadu tayi tace
"yes zamu bari, idan ka amsa kenan... Look na bakane ba don komai ba sai don kyautatawa dakuma tunanin danayi mun zama daya, we're friends.. Good friends so banyi tunanin idan nayi maka abu zakayi rejecting ba kamar yadda nima idan kayimin bazanyi rejecting ba, that's what real friends are, amma Hakan dakayi yasani tantama akan Hakan kuma nima bazai bari nazama very free da kai da abinka ba"

Ajiyar zuciya ya sauke batareda yace komai ba

"what did you say?" tafada tana kallonshi ita kanta tarasa dalilin dayasa ta nace ma Hakan akan dole saiya amsa


Ajiyar zuciya ya sake saukewa sannan yace
"Alright... Thank you so very much!"

Wani murmushi da batasan dashi ba ya su6uce mata sai kuma ta jawo jakkarta tashiga zugewa

Tsayawa yayi yana kallonta feeling very happy ganinta itama in a happy mood

Gani yayi ta zaro wayarta ta qara dagowa ta kalleshi sai yaimata murmushi itama ta maida mashi martani sannan tashiga yan danne danne aciki can ta ajiye itama tana sauke Ajiyar zuciya

"me kikayi?" inji Deen

"ina ruwanka?" tafada tana harararshi

Dan Hade gira yayi yace
"I'll tell kaka"

Dan Dariya tayi saikuma ta tuna da maganar Feenah na taso family dinshi takuma dinga nuna damuwa akansu

Saikuma ta tuna abinda ya ta6a cewa a hospital

_*duk duniya banida masoyiya kamar kaka, daga ita sai mai sonta, sai mai son mai sonta sai wadda taso mai son wadda tasota*_


"Allah sarki kakata, please how is she?"

Kallonta yayi sai taga ya saki murmushi
"she's fine amma tawace ba taki ba" ya qarashe yana harararta

Itama harararshi take tace
"inji wa? Kai yanzu tsohon yayene, ni kaka ke yaye yanzu"

"ba wani nan, ni ake yaye kuma ni za'a cigaba da yaye"

"in your wildest dream ba, tambayi kaka kasha labari, nan gaba kaka tarkatoka zatayi ta watso waje ni nakoma ciki inyaso sai katafi wajen mummy kema"

"mummy? Yes I like her, indai wajenta zani babu damuwa atleast zan huta da durar magani da kaka kemini"

Yar Dariya zee tayi, a halin yanzu jinta take wasai kamar bata ta6a shiga damuwa Hakan yakuma qara tabbatar mata cewa farincikinta yana tareda Deen

"har yanzu baka bar tsoron maganin ba?"

"har gobe.. What's Good about magani? I hate it ko warinshi banaso sai inji cikina na rumbling"

Murmushi tayi tace
"aikau kanada aiki don itama mummy ba sauqi gareta ba, bari ganin tana washe maka 36"


Murmushi shima yayi yana jin dadin wannan moment din, kasancewa da ita ahaka ba qaramin nishadi yake sashi ba

"babu komai, dukda Hakan nabarmiki kakan abarmin mummy"

"hmm idan mummy ce gaka ga ita, abu mai sauqi?"

Murmushi sukayi atare sai shiru yadan gitta a tsakaninsu

Jin shirun yasata dan dagowa ta kalleshi taga shima ita yake kallo

Murmushi ya sakarmata yace
"tell me"

Gabanta ne yadan fadi sai ta dake tace
"me?"

Tagumi yasake bugawa yace
"yadda kikayi spending holiday dinki"

Dauke kai tayi tana sauke Ajiyar zuciya, cikin zuciyarta tace 'wannan holiday din ai shine worst holiday dina, duk a burkuce nayishi kuma kaine sila'


A zahiri kuma tace
"well the holiday is so amazing, kaga the first week a hospital nayishi kafin a sallameku sai nasake wani agida doing nothing sai hutawa daga baya kuma nayi tafiya zuwa garinsu mamanmu"


"wow! Interesting, ina ne?"

"Ruma"

"Ruma? State ne?"

"No gari ne a 6atagarawa local government"

"wow! I love travelling" yafada yana murmushi still da tagumi

"yeah travelling yana da dadi sosai, kaga zakaje wani wuri ka xauna da mutanen Wurin for a while, you'll learn something From them therefore adding to your experience"

Kada kai yayi cikin gamsuwa
"nima zanso watarana nayi tafiya wani wuri"

"baka ta6a ba?"

"I don’t think so don da wayauna ban ta6a tafiya ba qila sannan ina qarami"

Shiru tayi saikuma tace
"karka damu ai watarana nasan zakayi, ko wajen dangin mamanku ko wasu naku haka, ko duk cikin garinnan suke?"

Shiru shima yadanyi sannan yace
"maybe"

Itama shiru tayi tana kallonshi, da alamu wani tunani yayi crossing zuciyarshi gameda danginshi

Ita dai tana mammakin yadda za'ayi ace mutum beda wani dangi bayan kakarshi

Koda mamanshi da babanshi sun rasu ina danginsu? Ina dangin uwa? Ina na uban? Ina na kakar itama? Abinda ya dade yana qullemata kai kenan don ko a kwanciyarsu asibiti yan unguwarsu kawai ke zuwa babu danginsu ko daya


Ganin kamar shima yafara nisa a nashi tunanin sai tace
"kaifa? How did you spend yours"

Murmushin daya fara tafiya daga fuskarshi yadawo sannan ya gyara zama shima ita kuma ta buga tagumi kamar yadda yayi dazu yashiga bata labarin yadda ya cinye lokacin hutunsu wanda yawancin wajen aiki yake zuwa ya dawo ya taya kaka aikin sana'arta kamar dai yadda yasaba


Sun jima sosai suna firarsu mai cikeda nishadi har mancewa ma suke da tafiya gida


Suna ahaka kiran wayar bala tashigo wayarta sai a sannan suka farga da tsawon lokacin da suka dauka tare

Daga wayar tayi yafada mata ya iso

Tambayarshi tayi ya amso mata saqo a wajen maid dinsu?

Da eh ya amsa yana cewa gashi nan ma hannunshi


Kwatancen inda zai taddasu tayi mashi tace ya kawo mata sannan ta kashe wayar

Ba'a jima ba kau sai gashi ya qaraso gaban library din

Waya yaqara buga mata ya sanar daita ya iso Hakan yasata tashi tafito

Amsar saqon tayi tace mashi ya jirata yanzu zata fito

Komawa tayi cikin library din tana zuwa ta ajiye ledar agabanshi


Ko be duba ba yasan meke ciki Hakan yasashi yin murmushi yana jin wani iri

Jawo ledar yayi ya dan bude ta ya leqa saikuma ya dago ya kalleta

"thank you so very much, jazakillah khairan"

Lumshe idanu tayi ta bude tareda yimashi murmushi batareda ta amsa ba ta tashi ta dauki handbag dinta ta rataya

"ni zan wuce, he's waiting for me outside"

Shima tashi yayi yace
"ok, sai monday ko?"

"yeah"

"to ki gaidamin mummy na"

Wani dadi ya ratsa zuciyarta jin abinda yace
"insha allah, kai fa? Ba yanzu zaka tafi ba?"

Dan yamutsa gashin kanshi yayi yace
"yes.. Sai anjima kadan, akwai abinda zanyi ne"

Tasan qarya ne kawai beson suyi mashi tayin rage mashi hanya ne amma saita share tace
"ok, see yah"

Ta juya tafara tafiya tana jin idanunshi akanta itama tana jin kamar ta juyo ta sake kallonshi amma ta maze

Har takai bakin kofa zata fita taji ya kira sunanta wanda taji kiran har cikin zuciyarta

Dakatawa tayi sannan ta juyo ahankali tana kallonshi

Shima takowa yashiga yi ahankali harya qaraso gabanta ya tsaya suka shiga kallon kallo

Ahankali ya dago hannunshi ya miqamata

Maida kallonta tayi a hannunshi taga yar qaramar wayarshi ce yake miqomata

Bata amsa ba sai sake maida kallonta datayi a kanshi cikin ayar tambaya

"your digits.. Please"


Dan wara idanunta tayi cikin tsananin mammaki, _finally.. Finally!_


Saurin gyara yanayinta tayi sannan ta dan yamutsa fuska

"ban gane ba"

"number ki zaki samun.. Please"

_OMG! Sai Yanzu? Why are you so slow?_ Abinda tafada a zuciyarta kenan

A zahiri kuma tace
"Why? I thought kanada number mummy"

"yes, yanzu taki nakeso so that zamu dinga gaisawa musanmman on weekends zamu kuma dinga sanar da juna some important stuffs idan sun taso bama tare" yafada calmly

Murmushi tayi cikin zuciyarta, kai mutumin nan yacika gara mutane, sai yanzu yasan duk da wadannan? Tun yaushe take expecting haka amma sai yanzu data gama fidda rai sannan

Jitayi tana son qara jamashi aji amma kuma tana gudun karya tsinke😝 Hakan yasa ta amshi wayar ba yabo ba fallasa amma deep down tsallen murna take

Number ta ta sakamashi sannan ta miqa mashi ta juya tana cewa
"bye.."

"bye!" taji ya amsa mata gab da zata fita

Koda ta fito babu bala Hakan yasa ta nufi parking space tanajin kamar tana tafiya kan iska don dadi, jitake kamar tayi ta tsallen murna tana ihu

Dakyar dai takai kanta bakin motar tashige ciki fuskarta a washe

Komawa tayi cikin kujerar motar ta lafe ta dora hannayenta saitin zuciya tana sauke numfashi ahankali

Ita kadai tasan yadda takeji, farinciki takeji marar musaltawa, farincikin da rabon da taji irin shi harta manta

Lumshe idanunta tayi broad smile shimfide a fuskarta Deen nayi mata gizo a idanu

Tanajin tashin Motarsu dakuma fara tafiyar ta, ahankali ta bude bakinta cikin rada tace
_bye ruhii❤️_


Saida ya tabbatar sun tafi sannan shima ya tashi ya hada tarkacenshi shima yafito


Cikin sa'a yana fitowa wata napep tazo wucewa ya tareta sukayi ciniki ya hau suma suka lula


💝💝💝💝💝💝💝💝💝💝


_first let me tell you_

_I cannot wait to see you 👀_

_you're the treasure� I've been waiting for 💃💃_

_Did you know? Did you know?_

_how much I really need you?_

_I dey pray for the day when_

_I can finally kiss 💋 you 🙈_

_you know say everyday I dey pray 🤲🏻 for you 😭_

_in my heart oh there's a permanent place for you 👉🏻❤️_

_that's why my heart dey beat like.._

_duduke 💓 *du💓* *du 💓* *ke💓*_

_cos na you I choose oh_

_Ayonfemi 👩‍❤️‍💋‍� ayonfe😘_

Waqar datake bi kenan na simi mai taken _Duduke_ tana tsane gashinta kasancewar bata dade da gama wanka ba don wani irin zafi ake garin yau

Da rawar fairy ta isa gaban closet dinta tana cigaba da bin waqar ta bude shi tana duban kayanta tana shawarar wanne ya kamata tasa

Wata blue black armless gown ta ciro marar nauyi da farar hula takuma koma gaban mirrornta da rawar data taho

Kallo daya zakayi mata kasan yau fa take sallah a wajen ta don farincikin datake ciki be 6oyuwa kwata2

Saka kayan tayi sannan taja kujerar gaban dressing mirror din tana busar da gashinta

Saida tagama sannan ta dan shafa powder sama sama tasaka kwalli kadai a idanun sannan tayi amfani da roll on mai sanyin qamshi a duk kusurwar jikinta sannan ta feshe kayanta da turare shima marar hayaniya don dama duk yawancin turarrikanta sai kana gab daita zakaji qamshinsu bata cika son wanda da kaje wuri ba turarenka zai fara tonaka

Kashe disc din dake waqar tayi ta bude kofa ta fice


A dining ta tardasu har sun fara cin abincin

"daddy na!" tafada da yar qara sannan tayi wajenshi tabashi side hug

Dariya daddy yayi yace
"daughter na!" cikin yanayin da tayi magana

Dariya sukayi gabadaya mummy ma tadanyi murmushi tana cigaba da cin abincinta

Ja mata kujerar kusadashi daddy yayi ta zauna fuska fall murmushi sannan ta kalli mummy tace
"mummy ina wuni?"

Dagowa mummy tayi ta harareta saita sunne kai tana sosa kai

Dariya daddy yayi yace
"kyaleta, kishi take don baki fara yimata magana ba, me zakici? Tundazu na aika akiraki shiru"

"daddy wanka nake shiyasa" tafada tana daukar spoon tasaka a plate din daddyn alamun tare zasu ci

"guess yau tsintuwa kikayi, wannan fara'ar haka? To Gaskiya raba daidai za'ayi"

Rufe fuskarta tayi da tafuka tana Dariya tace
"kai daddy"

"eh mana, naga yau farinciki akeyi, kwananan you're so moody amma yau shar"

Murmushi tayi cikin zuciyarta tace
'bazaka ganeba daddy'

Azahiri kuma tace
"mood swing ne daddy"

Cigaba da cin abincin sukayi suna firarsu da daddy mummy na dan samasu baki jefi jefi, kallo daya zaka su burgewa don they are small example of a Happy family


💜💜💜💜💜💜💜💜💜💜


Bude kwalin yayi ya ciro wayar dake kwance carefully yana jujjuyata a hannunshi


Wayar ta hadu iya haduwa, he can't believe shi zai dinga amfani da wannan wayar

Jin alamun za'a bude kofa da muryar kaka yasa yayi saurin ajiye wayar bayanshi Saidai he's too late don taga alamun ya 6oye abu

"hmm me ake 6oyemin?" tafada tana qarasowa

Dan kumbura fuska yayi yace
"ashe kece nayi tunanin 6era ne"

"eh 6era ce mai qaffafu biyu" tafada tana gallamashi harara

Murmushi yayi sannan ya fiddo wayar daga bayanshi ya miqamata yana cewa
"kalla kaka"

Dan wara idanu kaka tayi ta zauna kusadashi ta amshi wayar itama tana jujjuyata

"wannan ba wannan wayar bace?" inji kaka tana qara jujjuyata a hannu

"itace kaka"

"to ba kace ka mayar ba? Ya akayi kuma na ganka daita?"

"itace ta maidomin kuma"

"wa? Mummyn?"

Sai a lokacin ya tuna ashe kaka batasan zee ce mai kyautar ba

"A'a Zainab ta aiko"

Tagumi kaka tayi tace
"ni ma'u, dukda an maida Saida suka maido? Yanzu ya kake ganin za'ayi"

Shiru yadanyi sannan yace
"Kaka mu amsa kawai tunda babu dadi aqara maidawa Saidai bazamu qara abu hannunsu ba, koko?"

"kuma fa, ka kawo shawara kawai mu amsa tunda sun nace ya zamuyi?"

Murmushi yayi yace
"tanada kyau ko kaka?"

Dan yamutse fuska kaka tayi tace
"ni ai kasan ban cika ganin kyan irin wadannan wayoyin ba, dadai irin tamuce"

Murmushi kawai Deen yayi ya ciro tashi qaramar wayar ya budeta yafara zaro sim card da memory card dinshi

"to amma badai riqeta ba zakayi, sayar da ita zakayi ko?"

Dakatawa yayi daga abinda yake yace
"meyasa?"

"tayaya zaka riqe wayar dubu hamsin? Wannan ai almubazzaranci ne, zaifi maka ka Saida kasamu wani abu mai muhinmmanci kayi dasu wannan ta hannunka ta isheka"

Dan jimm yayi sai kuma yace
"kuma fa, insha allah haka xa'ayi"

Cikin jindadi kaka tace
"yauwa kyakyawa na, kaga sai muyi wani abu dashi ko jari yadda zamu dinga samun kudi ta wata hanyar bayaga namu ko?"

Kada mata kai yayi alamun eh yana murmushi amma deep down yasan tatsuniyace don babu abinda zai sashi siyarda wayar, yasan idan zee tasani to daidai yake da yankewar alaqarsu

"yauwa to yanzu maza ka shirya katafi"

"A'a kaka yanzu marece yayi, mubari sai gobe idan ba Haka ba tayin wulaqanci zasuyi mana"

"kuma fa, to shikenan a bari sai goben sai kutafi da salmanu don naga yafika baki idan katafi kai kadai qwararka za'ayi"

Murmushi kawai yayi bece komai ba

Tashi tayi ta nufi kofa tana cewa
"bari naje naduba abinda yake kan wuta karyayi kamu, kai amma mun gode wannan aka bamu kudinta ai mun warware"

Saida ya rakata da kallo harta fita sannan ya sauke Ajiyar zuciya ya maida hankalinshi kan wayar hannunshi yana ida zuramata sim din da t-card sannan ya kunnata


'wow!' yafada under is breath ya shiga daddanata yana shige da fice a wurare dayawa cikin ta yana jin wani irin nishadi a ranshi


💖 💖 💖 💖 💖 💖 💖 💖


Tun dazu waya ke hannunta tana danne danne Saidai a zahiri ba danne dannen take ba, wani abu take jira

Kira take jira, kiranshi amma haryanzu shiru

Tunda tadawo daga school take kasa kunne da baza idanun ganin kiranshi amma shiru wai mallam yaci shirwa

Da tagaji da jira saita kunna datar ta tashiga whatsapp dinta

Gani tayi Aunty Feenah na online Hakan yasa tayi mata sallama

Bayan minti daya ta amsa mata nan suka shiga fira both typing da voice note inda Feenah ke Tambayar ta ya ake ciki ita kuma ta gayamata sun hade yau har sun koma sun jone kamar da tana kuma gayamata yadda yake nuna damuwarshi akanta kamar yana sonta shima din

Qarfin gwiwa Feenah taqara mata na karta sare kuma ta dinga yawaita addu'a dakuma neman za6in allah

Sun dade suna fira Feenah nata bata shawarwari yadda kasan yaya da qanwa sannan daga baya Feenah tace insha allah kwanan nan zata shigo katsinan itama zee tayi ta murna tana cewa allah yakaisu lokacin

Da haka sukayi sallama duk suka sauka

Duba lokaci tayi na saman wayar taga har 12 na dare

Haushi taji ya turnuqe ta

Wannan wane irin slow mutum ne mai ban haushi?

Dama yasan ba kiranta zaiyi ba ya amshi number ta?

Koko duk salon jan rai ne daya saba?

Wannan idan aka tafi a haka ga yadda take ganin alamu Koda sonta yake saita kusan zarewa sannan zai bayyanamata


Kashe wayar tayi cikin jin haushi ta tillar daita can tsakiyar gado taja bargo har kai tana jan tsaki

A ranar ta dade barci bai dauketa ba sai juyin datake tayi, tsaki kau tajashi yafi cikin kwando, daga baya dai tasamu barcin ya sadado ya dauketa


*WASHEGARI*


*02:40pm*


Zaune suke ita da mummy Kadai a dining suna lunch

Bakajin komai a Wurin sai qarar cokali sai kau maganar t.v dake dan kawomusu anan


Zee sai tsatsakurar abincin take don dole don kwata2 batada appetite

Yau haka ta tashi zuciya a cunkushe komai ma bata haushi yake shiyasa batada walwala sosai

Mummy data lura da Hakan taita mammaki don kwanan nan zee takoma kamar wata mai aljannu, yanzu zaka ganta cikin farinciki anjima kuma ka rasa gane kanta

Yanzu dai kamar jiya haka fa tayita washe baki kamar wacce aka biyawa hajji amma yau kwata2 babu wannan fara'ar saima kumbure2 data lura tana yi Tundazu


Ringing din wayar zee ne ya katse shirun Wurin wanda Hakan yayi daidai da dakatar da cokalin da zee tayi niyyar kaiwa a baki


Kallon screen din take ganin sabuwar number ce zuciyarta na qara gudu

Dagowa tayi ta kalli mummy taga itama ita take kallo

"ki daga mana" inji mummy ganin wayar takusan tsinkewa

Kamar dama umarnin mummyn take jira saita dauki wayar ta daga kiran ta karata a kunne batareda tace komai ba


"Assalamu alaiki..."


Luu... Tayi baya baya ta jingina da kujerar datake akai kamar marar lakka tana lumshe idanu ta bude daidai lokacin da muryar tashi ta daki dodon kunnenta... ✍️


Ummin fasihu 🧚🏻‍♀�
8/2/21, 9:36 PM - Buhainat😝: *🙍🏻‍♂️DEEN 🙍🏻‍♂�*


*037*


_jiya nayi mistake, *Ruma* cikin qaramar hukumar *BATSARI* take ba *6atagarawa* ba. Afuwan👏_


"Hello?"

Muryarshi taqara ratsa dodon kunnenta dama zuciyarta baki daya


Ahankali ta bude lumssasun idanunta ta saukesu akan na mummy dake kallonta itama


Saurin zabura tayi zaune don ita harga allah ma manta a inda take zaune

"hello" tafada tana miqewa tsaye

"excuse me mummy" tafada tana wucewa hanyar stairs da sauri

Mummy ba tace komai ba sai Binta datayi da idanu

"hello?" Deen yaqara cewa a karo na uku

"hy" zee ta amsa daidai tashiga daki ta maido kofa ta rufe


Sautin murmushin shi taji wanda ba qaramin tasiri yayi a gareta ba

"aslm alaiki"


Zamewa tayi ta zauna gefen gadonta tana shaqar numfashi ta fesar ahankali tana jin yadda 6acin ran data wuni dashi na fecewa ahankali yana bin iska

"wslm.."

Sai shiru ya biyo baya

Jin shirun na neman yin yawa yasata cewa
"yes? Who’s this?"


Sautin murmushin shi taqara ji sannan taji yace
"Kamal ne"


Itama murmushin tayi amma marar sauti tace
"Kamal?" tafadi sunan cikin wani salo da Saida Deen yakoma ya jingina da bangon dakinshi ya lumshe idanu

Jiyayi tasake cewa
"wane Kamal din?"

Murmushi yayi wanda tajishi sarai yace
"like seriously baki gane muryata ba? Deen ne fa"

Murmushi tayi cikin zuciyarta tace
'ko cikin muryoyi dubu naji muryarka saina tantanceta"

A zahiri kuma tace
"Oops! Deen? Dama naji muryar sounds familiar ashe kaine?"

Murmushi yasakeyi yace
"eh nine, good afternoon"

"afternoon, how you? Ina kakata?"

"lfy lau, kakarki na nan lfy lau ina mummy na?"

"mummy tana dakinta"

Murmushi taji yasake yi sai jitayi dama tana ganinshi taga smiling face din

"just call to say hello"

Murmushi itama tayi mai sauti tace
"thank you so much, how's weekend?"

"weekend alhamdullilah, zaki zo school on monday?"

"why not?" tafada tana jawo pillow tana rungumewa a qirji

"ok saimun hadu monday din" inji Deen a dayan bangaren

Ba haka tasoba don ita nan gyara zaman susha firarsu tayi amma ya ta iya?

"ok allah ya kaimu" tafada ahankali

"bye ki gaida min mummy"

"zataji nima ka gaida kaka"

"ok bye"

"bye"

Kittt... Taji an katse wayar

Lumshe idanu tayi ta Janye wayar daga kunnenta ahankali tana sauke wani nannauyan numfashi


Wani kayattacen murmushi ya su6uce mata tayi wani juyi a kan gadon wanda yakaita tsakiyar gadon ta kwanta rigingine still pillon a qirjinta


Number daya kirata dashi ta shiga kallo fuskarta dauke da murmushi

Latsa wajen adding contact tayi tayi saving din number shi da
_*D❤️*_

Sannan ta maida wayar ta rungume a qirji ta maida manyan idanunta ta rufe.


***


"kyakyawa na! Kyakyawa na!!"

Kiran da kaka keyi mashi yasashi ajiye wayar ya tashi ya fito

"kakata?" yafada yana qarasawa kitchen din datake


"maza ga abincinka nan ka dauka ka cinye ka kawo na qara maka"tafada tana nuna mashi kwanon abincin

Waro idanu yayi yace
"aqara kuma? Kaka wannan ai yayi yawa"

Dan harararshi tayi tace
"kuma saika cinyeshi ba, maza dauka bari na shinfida mana tabarma waje" tafada tana fita daga kitchen din

Tabarma ta fiddo ta shinfida daidai Deen yafito da abincinshi dana kaka

Zama sukayi kowa yaja abincinshi gabanshi sukayi bismillah suka fara ci


Can kaka ta dago tace
"yau za'a Saida wayar nan ko?"

Dago idanu Deen yayi ya kalleta sannan ya kada kai kawai

"yauwa ai gwara ayi a saidata ko mun samu jari, jiya kusan raba dare nayi ina tunanin yadda zamuyi dasu harna samu na yanke shawara

Idan aka samu kudinnan zan qara jarin kokon nan don dama sau dayawa ba isa yake ba kafin takwas ya kare azo kuma aita nema babu, kaga saimu qara yadda zamu dinga samu da dan kwari ko?"

Kada kai Deen dake aikin sauraronta yayi alamun gamsuwa

"Sai kuma wata shawarar dana yanke, mezai hana nafara siyarda dambu?"

Dagowa Deen yayi ya kalleta
"Dambu kuma kaka?"

"eh dambu, kaga da hantsi wajajen 12 haka zuwa azahar zanyi kuma naga babu masu yi anan unguwar sai inga kamar za'a samu alhairi, koko?"

"to kaka muda bamu ga kudin ba tukkuna"

"ai zamu gani ko? Ba yau za'a siyar daita ba?"

"eh"

"to? Ina wannan lissafin ne yadda komai zai qara zo mana da sauqi, kaga yanzu ba aiki kuke samu ba can wajen aikinku sai wannan yar sana'ar tawa ta koko ita ke dan taimaka mana ga kudin makarantarka don ma aski yazo gaban goshi kaga ya kamata mu qara himma ko kuwa?"

Deen dake sauraronta Tundazu ya kada kai ahankali zuciyarshi fall tunani kala2

Yasan tanada Gaskiya don yanzu sunfi raja'a akan abinda ake samu a sana'ar ta na koko da qosai don ba aiki suke samu ba sosai yanzu yawanci yan gyare gyare ne da kudinsu basu taka kara suka karya ba, ga kudin makaranta

Gaskiya so samu a siyarda wayar don zata taimaka sosai amma kuma bejin yana iyawa bawai don yana kwadayin riqeta ba don gayu ko wani abu, A'a kawai jiyake bazai iya siyarda kyautar da akayi mashi ba, kyautar kuma ta zee

"yauwa kayi da jiki ka gama kaga idan ka fita siyan geron gobe sai ku wuce kasuwar tsaitsayen ku sayar"

Da to ya amsa mata ya cigaba da cin abincin cikin sanyi, zuciyarshi fall tunani


Atare suka gama cin abincin ya kwashe kwanikan yakai kitchen din yadawo ya xauna kusada kaka dake qilga kudin dazata bashi yayi sayayyar

Saida tagama sannan ta bashi ya amsa ya tashi ya shiga daki ya dauki wayar yafito yayi mata saiya dawo ita kuma tabishi da adawo lfy


Koda yafito hanyar gidansu salmanu yayi Saidai kafin ya qarasa yaci karo da qannen salmanun nan yake Tambayar shi ina salmanun sai yace bayanan yafita

Hakan yayi ma Deen dadi sosai sai kawai yayi tafiyarshi kasuwa don yiwa kaka sayayya


Koda yadawo da batun wayar ta tareshi nan ya gayamata ai be samu salmanun ba shiyasa basuje ba

Bataji dadi ba Amma saita haqura akan ai akwai gobe, sai aje siyarwa goben

Deen kawai jinta yake amma bayajin zai iya Hakan don he valued the phone kamar yadda yake value mai ita


Da daddare bayan sun fito sallar isha'i Deen ya tari salmanu yayi convincing dinshi akan Koda kaka tayimashi maganar siyarda waya yasan abinda zai gayamata

Dayake salman dan maqocinsu ne kuma sunzo tsararraki da Deen kuma ba laifi suna mutunci sosai Hakan yasa ya amince bayan yagama tsokanarshi akan to ya tanaji kudin dazai biyashi na qaryar da zaiyi don buhari ya hana aikin banza

Shidai Deen Dariya kawai yayi sukayi musabaha ya wuto gida


Washegari ma haka yaita raina ma kaka hankali akan bega salmanu ba can dai taje gidan da kanta tabada sallahun idan salmanu yadawo yazo tana nemanshi


Dayake shima yasan kiran ko na menene be tashi zuwa ba sai bayan isha'i, sanin cewa babu halin zuwa lokacin saita cemashi yatafi yadawo gobe da marece zai raka Deen kasuwa

Da to kawai ya amsa ya tashi yayi tafiyar shi.


A bangaren zee kau yau ma haka taita jiran kiran Deen Saidai bata qwalaffa rai ba irinna shekaranjiya Saidai har dare babu kira babu alamun shi

Bata wani damuba don tasan gobe zasu Hade school Hakan yasata kwanciyarta hankali kwance wani barci mai shegen dadi yayi gaba daita


*MONDAY*


Tafiya take ahankali cikin tafiyarta data zame mata jiki

Bïñ harabar school din take da kallo ganin yadda yacika sosai yau don dama kowa wannan monday din ne harinshi


Qara gyara zaman gyallenta da iska ya saukoshi daga kafada tayi tana cigaba da tafiyarta


"Zainab..."

Taji an kirata daga baya wanda ko bata juyaba tasan mai kiran


Yitayi kamar batajiba ta cigaba da tafiyarta tana murmushi slightly


"Hey! Zainab.." taqara jin muryarshi na qara kusantota

Wani murmushin tasake saki tana dan daga gira daya sama batareda ta tsayaba


"Zainabbb!" taji a kusa kusa da ita da alama yana gab da ita

Sai a lokacin tafara slowing down ta juyo ahankali cikin son ganin wa ke kiranta


Deen din ne, sanye cikin baqin wandon jeans sai farar t-shirt mai zanen baqi a gaba, as usual sumarshi a dan tuje take dan akwai zirin dama ya biyo mashi ta fuska

Ganin shine yasata tsayawa tana kallon yadda yake ida qarasowa yana dan yatsine fuska

"my goodness Zainab, are you deaf?" yafada yana sauke numfashin saurin dayayi

Dan daga gira daya tayi cikin alamun tambaya shikuma daidai ya qaraso

"tun daga bakin gate nake kiranki amma bakiji, are you sure Kunnuwanta lafiya lau suke?"

Harararshi tadanyi suka cigaba da tafiya tace
"kokuma kaine za'ayi ma wannan Tambayar ba? Are you sure maqoshinka lfy lau yake? Dama tayaya zani jika da wannan voice din naka?"


"Allah da qarfi nake kiranki, cewa nake Zainab! Zainab!! But unknown to me ashe kurma ce"

Juyowa tayi tayimashi mugun kallo shikuma yadan matsa gefe yana Dariya

"Allah, gashi energy dina ya qare Wurin shouting"

"dama kanada energy din ne? Lazy bone" tafada tana dan Harararshi

"O'O! Am not lazy"

"O'O! You are" ta kwaikwayeshi

Kafin wani yasake magana a cikinsu sukaji daga bayansu ance

"hey! Ku biyunnan kuzo"

Atare suka juya daidai wanda ya kirasu din shima ya kallesu sai kuma ya dauke kai yana cigaba da Fiddo abubbuwan dayake fiddowa a booth din motarshi daya wuto da ita ciki sosai yadda kayan zasuyi dadin kaiwa office.

Kallon juna Deen da zee sukayi saikuma suka qarasa wajenshi kamar yadda yace


Deen ne cikin ladabi yafara cewa
"Good morning sir"

Amsawa mr ibrahim yayi batareda ya dagoba sai sannan itama zee ta gaidashi itama ya amsa mata batareda ya kalleta ba


Suna nan tsaye a bayanshi har yagama fiddo kwalayen daga booth sannan ya rufe ya juyo ya fuskancesu


"help me with these" yafada yana nuna masu kwalayen

"ok sir" inji Deen yana wucewa don daukar daya

Itama zee wucewa tayi Wurin qaramin cikinsu ta dauka sai jitayi ashe babu nauyi ma da alamu takardune ciki ko littatafai

"ga key, ka bude kushiga dasu ciki saiku dawo mu ida kwashewa" inji mr ibrahim yana miqama Deen key din office din

Amsa yayi sannan suka jera da zee suka wuce don kaiwa


Saida sukayi nisa sannan Deen cikin muryar rada yace
"mutuminki"

Kallonshi tayi tana dan Harararshi tace
"Amebo" itama cikin rada

Murmushi mai sauti yayi yace
"eh din"


Ajiye nashi kwalin yayi bayan sun qarasa ya bude office din zee tashige sannan shima yadawo ya dauki kwalin shima yashiga

Ajiyewa duk sukayi a qasa sannan suka fito yasake rufe kofar sannan sukayo hanyar dawowa


"guess ya haqura" inji Deen yanzu ma cikin rada dukda basuma shawo kwanar da zasu hangi mr ibrahim din ba

Daga kafadu zee tayi tace
"may be, maybe not"

"gashi nan ya kiramu"

"ai besan mune ba, bakaga reaction dinshi ba dayayi realizing nice"

"ni ban gani ba"

"dama ya xa'ayi ka gani da wadannan small small eyes din naka kamar na cinnaka🐜"

Dan 6ata rai yayi yace
"kekuma da naki big big eyes kamar na kwado🐸"


Dan wara idanun tayi
"nidin?"

"exactly"

Yitayi kamar zatazo wajenshi yayi saurin matsawa yana Dariya

Kwafa tayi tana murmushi suka shawo kwanar da zasu dinga hango mr ibrahim suka hangoshi tsaye yana magana da wani lecturern shima


Cikin rada zee tace
"yaushe kake ganin ya kamata na sake samunshi? Now?"

"No not Now, kibari zamuyi magana but not Now" yafada daidai sun qaraso wajensu mr ibrahim din

Gaida dayan lecturern sukayi sannan suka sake daukar kwali guda guda ya rage saura daya sukayo gaba


Kafin ma ya bude kofa sukaga shima mr ibrahim yataho da kwalin qarshe

Kafin ya qaraso har sun shiga sun ajiye yana isowa shima ya shigo ya ajiye yayi masu Godiya sannan ya sallamesu suka fito


"yanzu ina zaki?" inji Deen

"Sabon department dinmu ofcourse"

"kinje copying timetable?"

"No kaifa?"

"nima yanzu zanije"

"ok muje, Hakan ma yakamata nafara ko?"

"nima haka nagani"


Daga nan sai suka sha kwana suka kama hanyar inda ake liqa timetable suna tafe suna fira gwanin sha'awa


Tare sukayi copying din timetable din anan suka ga ashe duk basuda class yanzu

Zee sai 12pm saikuma na 2:30pm shikuma yanada na 1pm shima da 2:30pm.

Ganin Hakan yasa suka wuce library don a lokacin duka qarfe 10 da yan mintuna

Anan sukayi zamansu sunata fira har lokacin shiga lecture din zee yayi ta tashi tabarshi anan


Ganin Hakan yasashi daukar wani Littafi yana karantawa to wine time away, lokacin shigarshi class nayi shima ya tashi ya fice ya nufi sabon department dinsu


Zee tarigashi fitowa Hakan yasa tawuce cafteria ta siyamusu snacks ta dawo library din


Bata dade ba sai gashi shima yayi joining dinta

Tare sukaci abinda ta siyo din suna duba lecture din da suka dauka yau


Sai wajajen 2pm suka tashi suka nufi masjid gabadaya shi yayi bangaren maza ita tayi na mata

Koda suka fito classes dinsu duk suka wuce don duk sunada lecture a daidai lokacin


A kusan tare suka fito inda a lokacin har Motarsu zee ta qaraso

As usual sallama sukayi don Deen cewa yayi akwai abinda zaiyi ba yanzu zai tafi ba

Bata damuba itama sukayi sallama tashige mota bala yaja suka fice tanajin kanta cikin nishadi marar musaltawa


Haka ranaku sukaita tafiya masu, kodayaushe zaka gansu a school atare Saidai idan daya ya shiga class yabar daya, sosai wata iriyar shaquwa datafi tada tasake shiga tsakaninsu Agefe daya kuma wutar soyayyar Deen tana cigaba da balbala a zuciyar zee

Yanzu yana dan kiranta don wani sa'in yana kiranta sau daya a rana wani sa'in kuma sai bayan kwana biyu yake kiranta, itama tana dan kiran shi amma ba sosai ba kuma yasha bata kaka su gaisa ta waya

Duk yadda takejin soyayyar shi a zuciyarta tana iya bakin qoqarinta na dannewa tayi acting normal musanmman ma a gaban shi dukda wani sa'in Dakyar take iya controlling din emotion dinta

Sosai soyayyar shi ke qara hauhawa a duk kowacce daqiqa a zuciyarta abin har tsoro yake bata don wani sa'in har kuka take tana fargabar kar allah ya jarabceta ta wannan fannin don tasan ba qaramar wuya zatasha ba

A gida ma mummy tayi noticing chanji sosai daga gareta

Don yanzu kusan kodayaushe indai tana gida to batada Wurin zama kamar garden, can zataje ta xauna shiru ko ta buga tagumi tana kallon waje guda tana murmushi kamar ta6a66a

Wani sa'in ko a dining suke haka kawai sai takama murmushi tun abin na ba mummy mammaki har abin yafara damunta


A bangaren Deen kau haryanzu be furta soyayyar shi ga zee ba Saidai yana bata kulawar dake sata tantamar anya babu sonta a ranshi kuwa?

Saidai kuma data tuna waye Deen da abinda yake iyawa sai ta bar wannan tunanin don ba qaramin aikinshi bane ace duk kulawar nan babu sonta ko daya a ranshi kawai abota ce


Yanzu haka satinsu uku da komawa school, komai yana tafiya masu daidai a karatunsu musanmman ma zee don sosai Deen ke warware mata abubbuwan dasuka shigemata

Gashi sun shirya da mr ibrahim don taje ta sameshi personally tabashi hqr dukda Saida Deen yasha fama kafin ta yarda taje don sau uku ana saka rana sai ranar tazo taji bata iya zuwa daga qarshe dai Dakyar ya iya convincing dinta taje sai gashi mr ibrahim din ne gwasaleta ba kamar yadda take gudu yayi accepting apology dinta yakuma yimata nasiha

Hakan ba qaramin dadi yayi mata ba don jitayi kamar anyi lifting wani abu mai nauyi daga saman qirjinta


***

Yau friday, dawowarta daga makaranta kenan tashigo falon tana sallama qasa qasa tana jan qaffafu irin a gajiye dinnan Saidai wanda tayi tozali dashi yasata warwarewa nan take

"Aunty Feenah!!!" tafada cikin wara idanu sannan ta nufi Feenah da gudu ta fada jikinta tana dariyar murna

Itama Feenah riqeta tayi cikin Dariya tana cewa
"ji yar rainin hankali zata qaryani, ni abokiyar wasarki ce?"

Mummy dake gefe zaune tace
"hmm ai indan wannan ce kadan ma kika gani"

Dagowa zee tayi still tana Dariya tace
"wai dama yau zakizo shine baki gayamin ba? Gaskiya banji dadi ba" tafada tana so6ara baki

"to idan ma gayamiki wani abu zaki yimin? Kema ba daga sama ba naga kin fado gidanmu ba?"

"oh ramawa kikayi kenan?"

"qwarai kuwa"

Dariya tayi tace
"babu komai ai, tsakanin uwa da 'ya sai allah, ina kayan ki nashigar miki dasu ciki dukda ni ba'a shigarmin da nau ba"

Yi Feenah tayi kamar zata maketa tayi saurin miqewa ta nufi stairs tana Dariya

Kwafa Feenah tayi tana cewa
"zanyi maganinki ai tunda naga kin maisheni kakarki"

"ai kunfi kusa, dama zani ce ta tarda muje don kaff babu abinda tabari a halin ki" inji mummy

"kai yaya, wlh nafi Zainab hankali" inji Feenah tana turo baki

"kindai fita" mummy ta amsa tana Dariya


*10:30pm*


Sake dagowa tayi daga wayarta datake danne danne daita ta sake kallon Aunty Feenah data juya mata baya tana waya cikin yin qasa da murya sosai don ko zee dake kwance kusada ita bata jin abinda take cewa

Sai jitayi ta bata sha'awa har itama tana hasaso kanta tana waya da Deen dinta

Tunawa tayi da yadda suke waya, sunyi gudun tsiya suyi 5mins suna waya amma Tundazu take duban agogo awon Aunty Feenah daya da kusan rabi suna waya
_ko me suke cewa?_ abinda ta tambayi kanta kenan saikuma ta ta6e baki ta cigaba da danne dannenta


Saida Feenah taqara daukar 15mins kafin suyi sallama da saurayin nata ta juyo ta kalli zee datayi nisa a wayarta tana downloading wata waqar hamisu breaker

Fizge wayar Feenah tayi tana cewa
"dawa ake charting?"

Tashi zee tayi zaune da sauri tana cewa
"wayyo Aunty dan allah karki datsemin yakusan Shigowa"

Jada baya Feenah tayi tana Dariya ganin tana qoqarin amsa ta daga wayar sama tana dubawa

"Yadda kunne yaji? Menene wannan?" inji Feenah tana yatsine fuska

"Wata sabuwar waqar hamisu breaker ne, naga gajeriyar video dinta a status dazu sai naji ta burgeni shiyasa nake downloading"

"mtcheew! Ni dalla amsa, namayi tunanin dashi kike charting"

Amsa tayi tana Dariya
"da wa?"

"bansaniba yar rainin sense"

Dariya zee taqara yi
"wai Deen? Bana tunanin yana charting"

"why?"

Daga kafadu zee tayi
"qila ra'ayi"

Ta6e baki Feenah tayi
"to Saidai waya kadai kuke yi?"

"itama ba sosai ba"

"why?"

"hmm kema fa kinsani Aunty, wayar ma duka yaushe muka fara? The guy is so slow in everything qila saina haukace sannan zai bayyana min zuciyarshi" tafada tana maida fuskarta kalar tausayi

Murmushi Feenah tayi tace
"karki damu zee, ana slowing a komai amma banda soyayya, insha allah zai bayyana miki ba kince kina ganin signs ba?"

"sosai ma, amma yaqi furtawa. Kuma ni tsoro nakeji karna sakankance dayawa abin yazo ya juye ba yadda naso ba in shiga uku"

Dariya sosai Feenah tayi ganin yadda ta qarashe maganar

6ata fuska zee tayi tace
"kai Aunty, Dariya ma nabaki?"

"dole kibani Dariya mana, wai ki shiga uku"

"ato Aunty har tara ina iya shiga wlh don bakisan yadda nakeji a zuciyata bane"

Murmushi Feenah tayi tace
"nasan yadda kikeji zee don na fiki dandana dacin soyayya"

Zee tadanyi jimm saikuma tace
"Aunty dan allah kibani labarin wadda kike so din, rannan kince ba yaya auwal bane, to waye?"


Shiru Feenah da mood dinta ya chanza tayi sannan tadanyi murmushi tace
"Wani ne" Sai kuma tasake yin shiru

Zee ba tace daita komai ba Haka ma bata bar kallonta ba


"A france muka hadu... Haduwar da bazata ta6a mancewa ba qila har namutu" Sai kuma tasake yin shiru

Ganin Haka zee tayi kasadar cewa
"a school?"

Nan ma shiru sai kuma taga ta kauda kai gefe ta dauke hawayen dake shirin gangaro mata Hakan yasa jikin zee yayi sanyi qalau

"A'a.. Ba a school ba, a supermarket... Ranar na raka wata course mate dina siyayya, asali ma siyan pad ya fiddamu don lokacin period dinta ya matso don harta fara jin alamu.

Da farko badani za'aje ba don cewa nayi bani zuwa can dai suka lalla6ani harna yarda zan bisu, ashe qaddarar so ke kirana"


Sosai jikin zee yaqara yin laqwas ganin yadda Aunty Feenah of all people take hawaye sosai dukda qoqarin datake na sharewa amma tana sharewa wasu na zubowa Hakan yasa itama taji idanun nata na durar ruwa

"harmun gama siyayyarmu mun fito saina lalluba naga banga bangles dina ba wanda najire wajen gwada wata agogo dana siya

Saina koma don daukota

Koda naje na tarar dashi inda na ajiyeshi saina dauki abuna na juyo ina maidawa kawai sai naji na gwara kaina da abu mai zafi"

Shiru tasakeyi tana hadiyar zuciya itakau zee sai kallonta take tana hawaye

"ashe shine, kallo daya na yimashi nasan tawa ta qare daga nan, kallo daya"

"kallon ma irin briefly dinnan don ko tsayawa ya kalleni ko yaga wanda ya buge beyiba sai dan daga hannu dayayimin alamun sorry ya wuce yana cigaba da amsa wayar dake kare a kunnenshi, kallon danayi mashi befi na daqiqu biyu zuwa uku ba amma kwakwalwata tayi capturing dinshi, ba ita kadai ba.. Harda zuciyata"

Share wasu hawayen dasuka gangaro mata tayi tana sniffing

"bansan iya tsawon lokacin dana dauka tsaye anan ba kamar an dasani Saidai jinayi daya daga cikin qawayena da mukazo tare tana girgiza kafadata, sannan nadawo. Nadawo daga duniyar da bansanta ba"

"Tambayoyi taita jeramin na lfy? Amma ban iya amsa mata ko daya ba na kama hanya kamar wacce bata cikin hayyacinta nafito tabiyoni itama da sauri abaya"

Dagowa tayi ta kalli zee dake hawaye itama cikin muryar kuka tace
"zee, bana fatan ko maqiyina ya tsinci kanshi a irin halin dana shiga a lokacin, na zauce zee, zaucewa na haqiqa.

Kullum... Kullum saina je wajen nan.. Don nasake ganinshi.. Koda brief kallo zan mashi irin na wancan, Koda bekai wancan ba.

Kullum saina je, na tsaya waje ina jiran shi, ina jiran wanda ko sunan shi ban saniba.

Tun qawayena na daukar abin wasa har abin yafara basu tsoro, bana kuka Saidai na xauna shiru, idanuwa jawur ina kallon waje daya, cikin dare bana barcin kirki konayi shi ke addabata a mafarki"

"nazo na daina gane komai a makaranta, hankali na baya jikina, ko attending class ban cika yiba ina can.. Ina can ina jiranshi.. Ina jiran wanda bansaniba, bansan sunan shi ba, bansan addininshi ba... It hurt zee, akwai ciwo sosai, ciwon da bazan iya musalta mikiba, ciwon da babu wanda zai iya ganewa sai wanda ya dandani abinda na dandana"

"haka zan wuni acan, Saidai in dinga chanza position don kar a lura dani afara zargin meke kawoni, haka zan wuni jira amma bazan ganshi ba na Kamo hanya kuma nadawo, idanuwana jajur don ban ta6a kuka ba don duk yadda naso yinshi baya zuwa, Saidai su qawayena suyita yi, suyita yimin kuka.. Ni kuma ina kallonsu ina ji azuciyata inama nice su, nima in iya kukan ko zanji sassaucin abinda nakeji"

Kuka sosai zee takeyi kamar zata shide, Ganin Feenah tana kuka ba qaramin tadamata hankali yayi ba

"Saida nayi kwana sha tara daidai sannan nasake ganinshi... Ganin da shima bazai ta6a gogemin a zuciya da kwakwalwa ba"

"A ranar nayi kukan da nake roqon allah yabani damar yi don inji sassaucin zuciyata, nayi kuka zee kukan da ban ta6a yiba.. Kukan da ya tashi hankalin dukkan yan hostel dinmu, kukan da nasan farkon shi amma bansan qarshen shi ba"

"na ganshi.. Shi da matarshi... Da 'ya'yanshi biyu.. Suna..." kasa idawa tayi saita hada kanta da gwiwa kawai

Saurin rarrafowa zee dake kuka sosai tayi ta rungumeta gamm suka cigaba da rera kukan tare 😭


Ummin fasihu 🧚🏻‍♀�
8/2/21, 9:36 PM - Buhainat😝: *🙍🏻‍♂️DEEN 🙍🏻‍♂�*


*038*


"A lokacin nayi tunanin mutuwa zanyi Zainab... I never thought I will survive it, gashi ni kadai naje ranar. Ina zaune inda nake kamar statue har suka shiga suka fito.

Na kallesu dakyau naga bayyananiyar farinciki da shauqin juna a tare dasu da alamu su basuda wata damuwa a duniyar nan"

"kamar yadda suka shigo a gaban idona haka suka fice a gaban idona"

"bansan tsawon lokacin dana dauka ba a wajen, nadai san kamar qawayena suka dawo dani gida.. Koko ni nadawo? Bana ce ba.. Nadai kawai ganni a dakin mu qawayena zagaye dani suna kuka.. Sama sama naji suna girgizani suna cewa inyi kuka ko zanji sauqi"

"da farko kasawa nayi amma ahankali ahankali sai yafara zuwa.. Sai nayi"

"ganin cewa allah yabani damar kukan yasa banyi wasa da damar ba, naitayi.. Naitayi zee.. Nayi tayi bakin iyawa na duk don in amayar da radadin zuciyata"

"bansan me yasake faruwa daga nan ba na farka a gadon asibiti daga nan sai gida"

"a lokacin kina secondary school, wataqila zaki tuna Da wata rashin lafiyar danayi don har Saida kukazo... A sanadiyar naqara repeating shekara daya a makaranta don a shekarar babu abinda nayi a school."

"na dade ina jinya both physically and emotionally sannan nadan warware nakoma school"


Dagowa tayi daga rungume juna dasukayi Tundazu tana kallon zee da fuskarta yayi jajur saboda kuka da rinnanun idanunta


"tun a lokacin ban qara ganinshi ba, yatafi.. Wataqila har abada.. Ya tafi ya barni da tabon da qila dashi zan mutu"


Sake rungumeta zee tayi tana lumshe ido wasu hawayen na silalowa

"Kiyi hqr Aunty Feenah, am so sorry"

Qara rungumeta Feenah Tayi itama ta lumshe idanu

"Don't be zee, don't be"


Shiru ya ratsa dakin bakajin komai sai qarar naurar a.c


Sun jima a Hakan sannan Aunty Feenah taqara breaking rungumarsu takoma jikin gado ta jingina tana share hawayenta

"amma dukda Hakan na godewa allah daya musanyamin da Auwal, dama abinda kakeso wani sa'in becika zama alhairi a gareka ba, alhamdullilah yanzu na wuce wajen, na samu mai sona.. Auwal"


"amma shima kina sonshi?" inji zee tana kallonta da jiqqaqun idanunta


Dan murmushi tayi
"it doesn't matter"

"kamar yaya?" inji zee cikin alamun tambaya

Dan murmushi Feenah tayi tace
"so dayane zee, kuma nariga na baiwa wancan mutumin"

"to yaya Auwal din fa? Kina nufin bakya sonshi?"

"it doesn't makes sense ko?"

Shiru zee tayi takasa amsawa

"yeah, banace bana sonshi ba kamar yadda bazan ce ina sonshi ba. Amma shi yana sona... Sosai
Kinga banida damuwa"

"kamar yaya?"

"zee, Koda ace nasamu mutumin nan yasan abinda nake ciki gameda shi yayi deciding ya aureni saboda sonshi danake bawai don shima yana sona ba, bazan ta6a auranshi ba"

"meyasa?" inji zee cikin mammaki

Ajiyar zuciya Feenah ta sauke tace
"saboda wahala zansha, kinsan illar auran mijin da baya sonka kuwa? Baki sani ba Amma ni nasani... Babu komai cikin auren da mata tafi son miji bayan azabtarwa da wulaqanci. Da Hakan gwara ki auri mai sonki Koda kuwa bakya sonshi muddin nagarttace ne, zakiji dadin rayuwar aure fiyeda tunaninki"

"Auwal na sona, makauniyar soyayya. farincikina shine nashi Koda kuwa zai cutar dashi, baya qaunar abinda zai 6ata min rai, kullum cikin tattalani da kulawa dani yake kamar kwai, idan na aureshi na more"


"Zainab, da mace ta auri wanda takeso baya sonta ko kuma soyayyar dayake mata bata kai tata ba gwara ta auri mai sonta wlh don rayuwar aure rayuwace mai zurfi da tarin qalubale idan har mijinki na sonki, so na Gaskiya bazaki ta6a wulaqanta ba"

"zan auri Auwal badon soyayya ba saidon nasan zan samu farinciki wanda shine muradin kowacce mace agidan mijinta.. Wataqila.. Wataqila farincikin dazai sani ya goge min wancan araina, wataqila watarana shima nasoshi.. Wataqila"


💖 💖 💖 💖 💖 💖 💖 💖


Da magangganunsu dasukayi jiya da daddare zee ta kwana ta tashi.


Sosai jikinta yayi laqwas matuqa da kalar soyayyar Aunty Feenah

No wonder, shiyasa take mata kallon shashasha lokacin da take denying din soyayyar Deen

Sosai taji tausayin Aunty Feenah dama kanta don itama batasan wace qaddara zata fadamata ba, fatan ta dai kar ya shafi soyayyar Deen don Hakan ba qaramin tashin hankali bane agareta.


Feenah kau tashi tayi garau kamar babu abinda yafaru, yanda take zirga zirganta freely yaba zee mammaki sosai don yadda kasan ba ita kebada labari jiya ba tana kuka

Ganin Hakan yasa itama dan warwarewa, sukayi komai tare sannan suka shirya suka shiga zaga gari kamar yadda Aunty Feenah ta buqata


Sosai yawon nasu ya ragema zee cinkushewar zuciya harda ma Feenah dake qoqarin 6oye nata damuwar

Basu dawo ba sai yamma liqis lode da kayan qwalama da zaqi


Washegari kau shopping suka tafi don ranar monday zata juya dama kwana uku tazo yimasu

Zee bataji dadi ba sam don sosai takejin dadin dan zaman nan da Feenah dukda zafinta, Saidai masu iya magana na cewa idan kasan halin mutum sai kaci maganin zama dashi

Sosai zee ta laqaici halayen Feenah shiyasa tafi kowa sanin yadda zata xauna daita shiyasa ma suke jituwa sosai don duk cikin dangi sunfi jituwa daita


Daddy ne mai daure gindin zuwa shopping din

A.T.M yabasu akan suje su dauki duk abinda sukeso a zara ta atm din


Aikau sunyi siyayya harta hauka inda yawanci duk na mayyuka ne na gyaran fata wanda duk yawanci Feenah ce tasansu don wasu ko ta6a ganin su zee batayi ba

Itama zee batayi wata wata ba tashiga daukar duk wanda taga ta dauka itama wai zata jaraba


A taqaice dai Saida sukayi shopping son ransu sannan suka kamo hanya suka dawo gida

Koda suka iso gida mummy riqe baki tayi ganin uban shopping din dasukayi, zatayi magana daddy yace babu ruwanta ba shi yabasu go ahead ba?


Ranar ma da daddare sunsha fira inda zee taita roqon Feenah idan zasu tafi su biyo school taga Deen

Da farko qin yarda tayi tace ita batason abinda zai jawomata raini wajen mutum, saida zee taita roqonta tana cemata Deen babu ruwanshi, beda matsala ko kadan sannan tasamu dakyar ta yarda.


A bangaren Deen kau tun kaka na maganar siyar da wayar harta haqura don kullum da kalar karatun dasuke kawomata musanmman salmanu don yafi Deen baki

Daga qarshe ma cewa sukayi sunje anyi musu tayin wulaqanci wai dubu 15, wai yanzu babu kudi

Nan suka lalla6ata akan tabari sai anshiga kaka lokacin kudi sun wadata sai a siyar


Babu yadda kaka ta iya haka ta haqura da sharadin da kaka tayi za'a siyar suka ce sun yarda.


*MONDAY*


Zaune take inda suka saba zama duk lokacin da sukayi sha'awar zama waje ba library ba


Memo ne bisa cinyarta sai pen a hannunta tana rubutu tana waqa ahankali


Ita kadai ce zaune don batada class shikuma Deen yana class Tundazu don sunada lecture


Tayi nisa a abinda take har batasan da Qarasowarshi ba

Dan nesa daita ya tsaya ya rungume littatafanshi a qirji yana kallon bayanta


_da rai lafiya take amfanuwa_

_da lafiya ake more rayuwa_

_a rayuwa so na kauda damuwa_

_da damuwa akan rasa rayuwa_

_soyayya ce da ba'a yin kwatance_

_in kayi dace hankalinka kwance_

_idan ta 6aci sai tasa a xauce_

_mafita ce, addu'a a taqaice_

_dakai na dace_

_a soyayya banda yakai_

_har abada dani dakai_

_da'iman! Da'iman!!_


Jin alamun kamar ana kallonta yasata saurin juyowa saita ganshi tsaye bayanta rungume da littatafai yana kallonta

Kunya taji ya kamata sai tayi saurin Juyawa kawai dana dan matse ido

Qarasowa ya ida yi ya xauna daga can gefenta yana murmushi

"wow! Waqar tayi dadi"

Murmushi kawai tayi bata dago daga rubutun da take ba

"dama kina waqa?"

Dan daga kafadu tayi
"Wani sa'in"


"tayi dadi, you have a melodious voice"

Blushing tayi tana kauda kai dadi na lullu6e zuciyarta

"inason waqa" taji yasake fada

Dagowa tayi ta kalleshi tace
"kanason waqa ko kanason ka dinga yin waqa?"

"duka" ya amsa yana ajiye littatafanshi akan cinya

"kuma zaka iya, your voice is sweet idan kayi waqar zatayi dadi" saikuma taji kunya tace Muryarshi nada dadi Hakan yasa ta qara kauda kai ta cigaba da rubutun ta

"really? To amma ni ban iyaba, as in how zan qirqiri waqar da kaina?"

Dagowa tayi daga rubutun datake ta kalleshi tace
"waqa directly daga zuciya take, duk abinda yake zuciyarka kana iya furtashi ta sigar waqa, it's so simple kuma yafi dadi ma saboda you're singing with the whole of your heart, pouring out your mind"

"how? Nayi tunanin koyo akeyi" inji Deen

Gyara zama zee tayi tace
"eh ana koya akwai kuma masu basira ta wanda they can form their song nan take, zasuyi amfani da abinda sukeji at exactly lokacin suyi forming din waqa kuma sai kaji yayi dadi sosai yafi na wadanda suka koya din ma"

"but tayaya Hakan zai yiwu? Kawai daga tunani sai waqa? Kowa ma na iyawa kenan"

Murmushi tayi tace
"kusan Hakan don abin baiwace, idan har ka iya lanqwashe harshenka ka iya juya maganar yadda kasan zatayi dadi to shikenan.. Yanzu misali kai wane abu ke ranka ko yanayin dakake aciki?"


"yanayin danake ciki?" Sai yayi shiru alamun mai tunani can yace
"am happy"

Murmushi tayi
"to kayi kalma da farincikin dakake dakuma abinda yasaka farincikin"

Shiru yasake yi alamun tunani can kuma yace
"sitting beside a friend and feeling the pleasant atmosphere make me happy" ya qarashe yana daga gira alamun yayi

Kada kai tayi tace
"to yanzu bari muyi forming waqa da kalaman"

Sai tadanyi gyaran murya tafara


_Happiness is the best gift of the nature that exist_

_smiling is the cutest gift of the cutest that exist_

_friends are the best thing that happen to human that exist_

_cool weather, the best atmosphere that exist_

_joining them together gives you the best moments that exist_

_the best feeling comes when all these exist_

_the best feeling and moments which made the word HAPPINESS_


Deen daya saki baki Tundazu yana kallonta yayi blinking din idanunshi sau biyu
"OMG!" Sai kuma ya hau tafi

"wlh tayi dadi, soo much!"

Murmushi kawai tayi

"to amma tayaya kika iya yin haka?"

"saboda ina iyawa"

"to wa ya koyamiki?"

"babu, kawai gani nayi na iya"

"wonderful! Kudos"

Murmushi tayi kawai

"to nima na Jaraba?"

"eh jaraba"

"ok kema kiyi wata kalma amma mai sauqi fa"

Murmushi tayi tace
"ok.. I love travelling alot" tafada sanin cewa shi ya ta6a amfani da kalmar kuma daga zuciyarshi take

Gyara zama yayi yana gyarar murya

_l love travelling, because travelling is good. You'll see lot of people and know their culture, therefore adding to your experience and also..._


Dariyar zee ce ta katseshi ya dakata daga zubar da yakeyi

Ganin Dariya take mashi sosai tana nuna shi ya 6ata rai

"O'O! Meyasa kike min Dariya?"

Bata amsa ba saima Dariyar data cigaba dayi, Hakan yaqara kular dashi ya cika yayi famm

"like seriously, wannan waqa ce ko magana?" Sai kuma taqara Fashewa da Dariya

"kafara abu babu full stop babu comma kamar mai rapping ko numfasawa bakayi?"

Deen dake kumburi yace
"kema ai haka kikayi"

"wa? Ni bakaji baiti baiti nake kawowa ba?"

"nima ai baiti baiti zan kawo"

"a ina? Kaida tunda kafara baka tsaya ba"

"ai bankai baitin farko ba ai"

Qara wara idanu tayi sai tasake daukar Dariya
"wato wadannan duk cikin baiti daya ne? Hhhh🤣 wayyo cikina"


Qara cika yayi sai huro hanci yakeyi

"to qarasa baitin" tafada Dariya na cinta

Harararta kawai yayi ya dauke kai

Duqar dakai tayi tayi Dariya marar sauti sannan tasake cewa
"ka cigaba mana"

"don kinga ban iyaba kike yimin Dariya?" yafada yana kauda kai gefe

"ok, ok sorry, ni bansan Dariyar tazo ba ma, yanzu dai sorry, qarasa baitin" tafada tana danne dariyarta

"saboda kiji dadin yimin Dariya ko?"

"A'a bazanyi ba"

"promise?"

"yes"

Sai yakuma gyara zama ya gyara murya sosai

Zee kallonshi kawai take tana iyakar kokarinta na ganin ta riqe dariyarta

_kuma zanga gari naita yawo aciki, ina lura da banbance banbancen al'adarmu, idan sunada yare nima saina koyaaa yadda idan nadawo gida naita yiwa kaka amma bata ganewaaa_


Kallon zee yayi data hada kai da gwiwa Tundazu, dan yamutse fuska yayi cikin ayar tambaya yace
"hey.. Hey!"

Qin dagowa tayi

"hey, are you ok?" yafada yana dan leqo fuskarta ta qasa sai a lokacin ta dago fuskarta idanunta sun duri hawaye

Kafin yayi magana ta fashe da dariyar da Tundazu take yinta a ciki tasake maida kanta bisa gwiwa tana yi Sosai

Tsayawa yayi yana kallonta kawai har tayi ta gaji sannan tasake dagowa ta ciro hanki dinta ta dan tsane hawayenta

Cikin muryar Dariya tace
"tau saura baiti na uku"

Kauda kai kawai yayi bece komai ba


"kaji? Saura na uku"

Juyowa yayi ya Harareta ya kauda kai


Murmushi tayi sannan cikin danne dariyarta tace
"you know what? Matsalar waqarka shine kana jan baitin da tsawo.. Hhh... Kuma kamar ba waqa ba.. Baka fidda karin waqa.. Hhh"

"wannan da a cinema aka daukeka waqa da kafin ka kai baiti daya zaka fara jin ruwan duwatsu😆"

Be tanka mata ba kuma be juyo ya kalleta ba

Saida tagama yimashi shaqiyanci sannan tace
"yanzu bari kaji, idan zakayi waqa, anaso ka taqaita tsawon baitin yadda ba zaiyi sounding boring ba misali

_kuma zanga gari naita yawo aciki_

Kana iya barinshi daidai nan sai kasake wani baitin
Misali

_kuma zanga gari naita yawo aciki_

_na dinga lura da al'adun ciki_

_nakoyi yaren dasuke aciki_

_nai jama'a da mutanen dake ciki_"

"akwai wani abu da ake kira kafiya a waqa, shine ya kasance duk baitin waqarka ya dira lafiya lau, so samu ma ace duki kalmar qarshe tazo daya na wadannan baitikan misali a wadancan baitikan dana kawo kaga duk (ciki) shine kalmar qarshe, yana iya zama (ki) din qarshe ma duk ana iya yin Hakan saboda waqar tatafi a tsari takuma bada taste"

(duk inda nayi kuskure a wajen bayanin waqa acan sama👆🏻 ayimin afuwa.
Qarfin hali ne kawai na marubuci, babu abinda nasani a waqa ☹️ kawai dai hasashe na ne kuma saboda labarin ya ta'alaqa dashi shiyasa na sakoshi ciki, so mawaqa Ayi hqr 👏 na shiga gonar da batawa ba😝 waqar ma Dakyar nake hadata 😆 donma a rubuce na, da na saurarone da babu kanta🏃🏻‍♀️🏃🏻‍♀️🏃🏻‍♀�)


Deen da tunda tafara bayanin ya juyo yana sauraronta harta kai aya ya Kada kai yace
"ok, bari nasake gwadawa"

"ok gwada" inji zee dake readyn cin Dariya

Qara gyaran murya yayi yace

_saina siyawa kaka tsaraba dayaWA_

_ciki harda ku6eWA_

_harda alaWA_

_sai na hau abin haWA_

_nadawo gida ina.._

Shiru yayi ganin baitin bazai qare da WA ba

Saiya sake cewa

_nadawo gida ina riqeda ledar ku6eWAR_


Atare suka shiga yin Dariyar wannan karon don shi kanshi yasan he sounds so funny


Suna cikin haka wayar zee tayi ringing


Zaro wayar tayi ta duba mai kiran taga Aunty Feenah ce

Dan wara idanu tayi don ita shaf tama manta yadda sukayi daita

Daga wayar tayi ta kara a kunne tayi sallama cikin muryar da Dariya bata gama saki ba

"gamunan waje karki 6atamin lokaci" taji Feenah tace daga dayan 6angaren

"to Aunty, gamunan zuwa"

Kittt suka katse wayar Atare

Kallon Deen dake kallonta shima tayi

"kaga na manta ko?"

"menene?"

"Wata Aunty ta ta Ruma tazo tun ranar friday, to a schedule dinta gobe zata koma amma saboda wani abu daya taso cikin gaggawa shine tafiyar tadawo yau, ni kaina ban sani ba don Saida nazo school sannan ta kirani ta gayamin shine nace bazata tafiba sai tazo munyi bankwana, kaga har tazo ma"

"ayyah" yafada a gajarce yana murmushi

"muje muyi mata bankwanan"

Dan wara idanu yayi yace
"ni kuma? No kije zan jiraki"

6ata fuska tayi
"why? Yanzu fa zamu dawo"

"but.."

"shikenan kawai" tafada tana tashi alamun ranta ya 6aci ta dauki jakkarta ta rataya

Ganin Hakan yasashi tashi shima don kwata2 beson 6acin ranta, ko yaya yanayin fuskarta ya chanza sai yashiga damuwa


Dama tasan idan yaga tayi fushi zai taso Hakan yasa ta danyi murmushi a cikin zuciyarta

"ok mutafi a gaisuwa ce ko?"

Kada kai kawai tayi


"ok muje" yafada shima yana rungume littatafanshi a qirji


Tare suka jera suna tafe suna fira gwanin sha'awa kowanne da murmushi a fuskarshi


Saida suka fita wajen gate don motar na waje

Motar suka hanga daga gefen titi na dama, dukda zee tayi mammakin ganin ba tasu bace haka suka nufeta don ganin ko sune.

Tun kafin su qaraso murfin bangaren driver ya bude wani kyakyawan Saurayi yafito daga ciki

Dan wara idanu tayi
"Yaya Auwal?"

Murmushi saurayin yayi yace
"na'am diyarmu?"

Daidai nan itama Feenah ta Fito daga bangaren mai zaman banza

"Ina wuni yaya Auwal"

"lfy qalau lumi yar daughter mu, kin ganni kamar daga sama ko?"

Kada kai tayi tana murmushi


"zuwa mukayi daukar gimbiyar, mun samu Dakyar an sahale mana muzo" inji saurayin wanda ga dukkan alamu yanada faran2 sosai

Dan hararar shi Feenah tayi tana dan 6ata fuska cikin salo

Murmushi zee tayi tace
"aikau dai yaya, kuma dama kun rabu da shigowa k.t kunga har zuminci sai ayi"

"ashe kin gane, yar daughter mu" injishi yana Dariya

"ya karatu?"

"alhamdullilah yaya, ya aiki"

"gashinan munata fama wlh, wannan abokin nawa fa?" yafada yana kallon Deen dake baya yana sauraronsu

Sai a lokacin Deen ya dago fuskarta dauke da murmushi yayi musu sallama

Atare suka amsa suna maida mashi martanin murmushin

"Yaya Auwal, Aunty Feenah meet my course mate Deen, Deen wannan itace Aunty ta sai yayana"

Fuska dauke da murmushi ya gaidasu calmly sukuma suka amsa suma murmushi a fuskarsu sai kallonshi suke

"ya karatu, fatan za'a qara tighting belt"

"insha allah brother" inji Deen

"to allah ya taimaka, daughter mu zamu wuce" inji Auwal yana dan sunkuyawa ya ciro ledar dayayi mata siyayya ya miqo mata

"gashi Ayi manage"

"kai yaya, harda hidima? Thanks so much" inji zee tana amsa

"Don't mention" yafada yana komawa cikin motar

"to sai munyi waya ko?" inji Feenah tana dan kashe mata ido alamun akwai labari

"to Aunty a gaida kowa da kowa, ace nayi missing dinsu"

"eh, tunda ni yar aikenki ce ba?" tafada itama tana shigewa ta zauna

"pleeease" tafada cikin marairaicewa

"ok amma ba don halinki ba" tafada tana harararta

"eh babu komai" inji zee tana maida mata kofar ta rufe

Tada motar Auwal yayi nan suka shiga daga ma juna hannu harda Deen, Auwal yaja motar suka tafi

Ajiyar zuciya zee ta sauke sannan tajuyo ta kalli Deen

"how was that?"

"nice, they're so nice"

Murmushi kawai tayi suka juya suka koma ciki

Sallah duk suka wuce suka farayi sannan dik suka shiga class kasancewar suna da lecture a lokacin

Saida suka fito sannan suka zauna suka ci kayan da Auwal ya ba zee dukda Deen be wani ci sosai ba

Suna haka akazo daukar zee sukayi sallama ta tafi sannan shima ya fito ya samu abin hawa shima ya tafi


***


*10:15pm*


Kwance zee take kan gado wayarta a hannunta tana danne danne sai murmushi take akai akai da alamun abinda takeyi da ita na bata sugar

"hmm Aunty Feenah, wannan rudewa haka?" ta tura

Can sai message yashigo kamar haka

"wlh zee gayen yayi 👌🏻 wai kinga sadda kuka jero? Yadda kikasan romeo and his juliet😍"


"😆😆 dama kin sansu a kammani ashe?"

"baki da labari ashe 🤨"

"banida ☹️"

"to saiki sani tun yau 😏 ashe dai dama da walakin goro a miya 🤔 haba dole ai ki rude ki gigice, taga dan fari kyakyawa 😒"

"kai Aunty, duk kyawunshi ya kaini😟"

"😳wa? Ke? 🤮🤮🤮"

"😩😩😩"

"kyaji dashi 😒, Gaskiya maganar Gaskiya kun dace, ya kamata kuyi ku daidaita junanku hakanan, Ca6 you'll make a perfect match, na so naga 'ya'yanku🥰"

"kai Aunty 🙈🙈🙈"


"munafuka, anaso ana kaiwa market 🙄"

"kai Aunty 😫"

"yanzu dai kuyi ku daidaita junanku musha biki💃💃"

"kai Aunty 😟 nifa yarinya ce haryanzu 😔"

"sannu jaririya 😕 ai naga ko yayeki ba'ayi ba"

"😁😁😁"


"yar rainin sense kawai, ki gaida yaya da daddy, ni zan sauka, barci 🥱"


"tun yanzu 😳 yau babu wayar 👉🏻❤️ ne?"

"ungo nan 🖐🏻😡"


Dariya zee tayi a zahiri ta turamata

"🏃🏻‍♀️🏃🏻‍♀️🏃🏻‍♀"


Sannan ta rufe datarta ta koma ta kwanta rigingine ta jawo pillow ta rungume

Tunawa tayi da dramarsu ta dazu na koyan waqa

Murmushi mai sauti tayi ta murgina tsakiyar gadon ta rungume pillon gamm a jikinta


_*DEEN*_ tafada cikin shauqi da begen mammalakin sunan... ✍️


Ummin fasihu 🧚🏻‍♀�
8/2/21, 9:36 PM - Buhainat😝: *🙍🏻‍♂️DEEN 🙍🏻‍♂�*


*039*


*SIRRIN ZUCIYA ❤️*


Akwana a tashi gashi har su zee sun qulla wata kusan biyu da resuming school


Komai yana tafiya masu daidai kuma sosai suka maida hankalinsu akan karatunsu musanmman ma Deen dake final year

Yana da burika dayawa dayake son cikawa a duniya ciki harda inganta rayuwarsu shi da kaka, most especially ma kaka saboda ita ta tsaya mashi kai da fata wajen karatunshi don kusan dik abinda tasamu nan suke tafiya saboda ta yarda karatu shine gatan mutum kuma ko ba dade ko ba jima zasuci gajiyar shi shiyasa bata wasa da abinda ya shafi karatunshi komai tana iya badawa muddin akan karatunshi ne

Shiyasa shima a nashi bangaren be sanyo wasa ko shiririta a bangaren karatunshi

Yanada burin zama wani abu a duniya ta dalilinshi yadda zai tallafi rayuwar kaka kamar yadda ta tallafi nashi


A 6angaren zee kuwa jiya-i-yau.

Haryanzu tana nan tana dakon soyayyar shi a zuciyarta

Kullum sonshi qara hauhawa yakeyi a zuciyarta kamar yadda kullum shaquwarsu ke qara qarfi


Sosai take azabtuwa da soyayyar shi datayi mata bake bake a zuciya Saidai haryanzu shiru a ta bangaren Deen Saidai akwai signs da symptoms na soyayyarta dayake nunawa amma that wasn't enough, so take ya furta mata, abinda taga bashi da niyyar yi kwata2.


A bangaren Feenah kau biki sai qara gabatowa yake don yanzu bekai wata daya ba, ata kowanne bangare shirye shiryen bikin akeyi musanmman ma bangaren Amaryar kasancewar itace auta shiyasa ata koina ake nuna mata gata.


***


Yau asabar, babu school don haka yini tayi a gida tana hutu

Fitowa tayi daga dakinta dauke da wani dan bowl din tangaran wanda tagama shan fruit salad cikinshi ta fara tako stairs don sauka qasa ta maida


Muryar mummy da daddy taji suna magana da alamu fira sukeyi

Murmushi tayi ta cigaba da saukowa Saidai maganar dataji mummy tayi yasa tafara slowing tafiyarta

"Gaskiya ne, nima dama nayi wannan tunanin, kaga Feenah tun tana makaranta ta tsaida miji, gab da zata gama kuma akasaka rana kaga yanzu duka watanta biyu da gamawa nan da yan satittika asha biki, me yafi wannan? Wlh zaman ba yi bane gwara da angama Ayi auren don shine mutuncin ko wacce 'ya mace dama namiji ma

Kuma idan akace sai an gama karatun sannan za'a samu mijin yaushe za'ayi kenan? Gwara tun yanzu asa sanwar abin bare kai dama ita kenan daya, kowa ya dauko idanu ya zuba maka yaga yadda zakayi

Ni sai inga Hakan shi yafi kawai"

Tsayawa zee tayi takasa qarasowa tana jujjuya maganar mummy cikin son gane inda ta dosa


Daddy taji yana cewa
"nima haka nagani wlh Maimuna, gwara afara tun yanzu. Gashi yaron yanada tarbiyya don nasanshi sosai, muna Yawan hadewa idan naje gidansu ko kuma wasu lokutan idan sunzo tare da baban.

Kuma bayan wannan kinga zumunci zai qara qulluwa, amintarmu da babanshi zai qara qarfi kuma bazanyi fargabar wani abu yasamu diyata ba don ko babu ni a duniya nasan Alhaji Abubakar mai iya riqe amanar iyalaina ne"


Kan zee yaqara kullewa

Tabbas tasan Alhaji Abubakar, babban aminin daddy ne kuma abokin kasuwancinshi.

Sau dayawa shida iyalanshi suna zuwa nan ziyara suma suna zuwa gidanshi Saidai zee bata cika son zuwa ba don yaran gidan mugun yan zafin kai ne, girman kansu yayi over shiyasa basa shiri don kamar yadda suke jinsu su wasu ne haka itama ke jin kanta shiyasa basa shiri sam

"wlh kam, to yanzu yakusan dawowa ne?" inji mummy

"eh, ga yadda muka tattauna dashi Alhaji Abubakar din cewa yayi yagama komai kawai sai yan ide ide, nan da wata daya nasan yadawo, to kinga me ake jira? Aiki dama akwai shi available shi dama yake jira, kinga a lokacin saisu fahimci juna da tashiga level 400 din sai asaka rana tana gamawa sai asha biki, ko yaya kika gani?"

"Gaskiya Hakan yayi Alhaji, kaga zamu sauke dukkan nauyinta akanmu, ga ilimi mun bata kuma mun aurar daita a lokacin daya dace, dama ni na matsu naga anyi Hakan saboda ita 'ya mace ce kuma duk inda hankalin iyayen 'ya mace yake to bazai ta6a kwantawa ba sai sunga sun rabu daita lafiya ta hanyar aurar daita. Allah yasa Hakan shi yafi alhairi kuma allah ya daidaita su kasan diyar taga yar tutsu ce wani sa'in"

Dariya daddy yayi
"ai karki damu, insha allah zaiyi mata 100%, nifa nasan taste din diyata, nasan abinda zataso da abinda bazata so ba kuma am betting you, zaki gani. Da hannu bibbiyu zata amshi tayin bari dai lokacin yayi"

"to allah yasa, ka dai san ba'a shaidar 'ya'yan yanzu, bare wannan diyar taka mai shegen ruwan ido, kana ganin yadda masu neman ta ke zuwa take musu wulaqanci, duk wanda yazo saita nemi makusanshi ta kushe, nayi fadan nayi nasihar a banza"

Dariya daddy yasake yi
"ai jewel din kenan, ita allura ce cikin ruwa, mai rabo ka dauka kuma *Asad* shine mai rabon don dama don shi taqi sauraron kowa, nasan diyata kuma nasan abinda takeso don hakama yasa nasan da Asad zasu dace, kuma zaki gani"

"to allah ya tabbatar da alhairi ai haka akeso" inji mummy cikin farinciki

"hmm kaji su Hajiya Maimuna an kusa zama in-law" inji Alhaji cikin tsokana

Dariya tayi tana juya idanu wanda a wurinta zee ta gado nata

"Ato, kana black stomach ne?"

"A'a, namafi kowa white stomach" yafada shima yana kwaikwayon juya idanun datayi

Dariya duk sukayi mummy na cewa
"to allah dai ya tabbatar mana da alhairi"

"Amin summa amin" inji daddy


Ahankali zee ta juya tafara taka stairs din don komawa batareda tayi motsin dazasu lura daita ba

Bude kofar ta tayi ta shiga sannan ta rufo ta taho ahankali kamar marar lakka ta ajiye bowl din hannunta saman bedside locker ta zauna ahankali gefen gadonta


Shiru tayi tana kallon Kaffafuwanta dake bisa dan carpet din dake gaban gadon kamar anan zataga amsoshin tambayoyin dake tsere a kwalwarta


*kinga a lokacin saisu fahimci juna, da tashiga level 400 sai asaka rana tana gamawa asha biki*
Maganar daddy ce tadawo mata a qwanya


*nasan abinda takeso don hakama yasa nasan da Asad zasu dace*

Wai wa yake magana akai? Waye kuma Asad? Wacece zasu dace dashi?

Hadiye wasu yawu dasuka taru a maqoshinta tayi


Me suke nufi? Tadai san basuda wata 'ya bayan ita kuma taji suna maganar sauke nauyi ta hanyar aurar da 'yar su

_Ni kenan?_


Sai kuma ta girgiza kai

_no this is impossible!_

_it can't be_

Waye wani Asad kuma? Suna ko gishiri babu.

Ca6 dasake wlh, yanzu yanzu ba sai anjima ba zataje tagayawa daddy don karma ya wahalar da d'an mutane wajen zuwa don Hakan bazai ta6a yiwuwa ba don tanada wanda takeso


Zumbur tayi tasake tashi ta nufi kofa

Harta dora hannu akan handle saita kuma dakata

Idan taje me zatace mashi?

"daddy Gaskiya ni banason wannan Asad din, inada wanda nakeso"

Sai yace
"waye?"

Me zatace?

Deen? Deen zata ambata?


Mutumin da har yanzu batasan matsayinta ba a gareshi?

Idan tace Deen din ne yakuma nemi ya ganshi me zatace?

Cewa zatayi ita ke sonshi? Ko cewa zatayi jiranshi take taji matsayinta a wajenshi?


Ahankali ta saki handle din

Tabbas tasan daddy, takuma san idan yayi farinciki to yaga tayi ne

Idan tace mashi bata sonshi bazai gardama mata ba don tasan bazai ta6a yimata dole ba

Amma shi wanda zatayi Hakan akanshi tanada tabbaci akanshi?

Tanada tabbacin yana sonta?


Ahankali takoma da baya2 ta lulubi stool din dressing mirror dinta ta zauna akai


Tasan idan tace bata son wanda suke magana akai zasu nemi sanin wa takeso, idan tace babu bazasu yarda ba musanmman mummy da dama burinta taga tayi aure kuma ga yadda taga ta nuna amincewarta sosai akan wannan maganar da wuya ta barta ta tafi a iska

Idan kuma tace tana da wanda takeso zasu so sanin ko waye, idan ta ambaci Deen zasu so jin ta bakinshi, idan kuma sukaji cewa bema san da maganar ba me kenan?


Hannuwa takai bisa kanta ta cusa yatsunta cikin lallausan gashinta tana maidasu baya sannan tayi interlocking din yatsunta bisa wuya


Anzo wajen!

Anzo ga6ar da take gudu


Lumshe idanuwanta tayi ahankali tana jin baqinciki na mammaye zuciyarta


Har zuwa yaushe? Har zuwa yaushe zata cigaba da jiran shi? Har zuwa yaushe zata cigaba da dakon soyayyarshi? Har zuwa yaushe zata cigaba da wahala


Ranta taji ya 6aci, zuciyarta ta dagule, jitayi kamar taita ihu don takaici.

Dama tasani, wannan slowness din nashi wahala zai bata, dama tasan saita fara zaucewa sannan zai bayyana mata sirrin zuciyarshi.


Haka ta qarashe Wunin ranar rai a matuqar dagule

Baqinciki, 6acin rai, takaici duk sun taru sun tokaremata qirji wanda Hakan yasa taji babu abinda keyimata dadi a duniyar nan


Haka ta qarashe weekend din wannan satin cikin cinkushewar zuciya, sosai takejin haushin Deen har cikin zuciya, jitake kamar ta sameshi taita duka ko zata huce shiyasa Koda yakirata da marece ranar lahadi kamar yadda yasaba sai bata daga ba sai tasa number shi yadda idan ya bugo zaiga line busy


Da daddare ma ta dade batayi barci ba kamar yadda yake a al'adarta indai akwai abu a ranta yakan hanata barcin kirki

Haka taita juyi kafin tasamu dakyar wani barci marar dadi ya dauketa


*WASHEGARI*


Zaune take a library wani qaton textbook a gabanta tana budewa ahankali page by page

A zahiri sai kayi tunanin wani abin kirki takeyi amma maganar Gaskiya ita kanta batasan me take dubawa ba, hankalinta da tunaninta yayi wani wuri daban


Deen ne yashigo library din, waige waige yadan farayi na ganin inda zai ganta sai ya hango ta can qarshen dakin

Murmushi yayi sannan ya nufo inda take cikin tafiyarshi ta nutsuwa

Tunda yashigo ta ganshi amma tayi kamar bata ganshi ba, haushin shi takeji kamar me? Jitake kamar ta tashi taita zazzagamashi abinda ke cin ranta

Tanajin Qarasowarshi amma bata dago ba harya ja kujerar dake facing dinta ya zauna


Sa hannu yayi ya rufe littafin data kafama idanu kamar mai karatun gaske, yana cewa
"hey... Book worm"


Sai a lokacin ta dago ta kalleshi da alamun bazata a fuskarta

"oh! You scared me"


Yar Dariya yayi yace
"ai kece hankalinki na kan Littafi baki jin ko motsin mutane, meye kike karantawa?" yafada yana juyo da littafin gaban shi yadda zai gani

Dan daga kafadu zee tayi tace
"just going through topic da mukayi jiya"

Kada kai yayi yana maida mata littafin shima ya doro nashi littatafan a sama

"good, how's your weekend?"

"Alhamdullilah" ta amsa a gajarce tana sake jawo littafin daya maido mata gabanta tana cigaba da dubawa


"meya samu phone dinki jiya?" yafada shima yana zaro wani littafi a tsakiyar littatafanshi


Zee da maganar nan ma datake yi duk dauriyace don ita tasan me takeji a zuciyarta ta dago ta kalleshi sannan ta daga kafadu
"babu"

"but nayita kira bata Shigowa saima line busy dayaita nunawa"

Qara daga kafadu tayi batareda ta dagoba tace
"qila lokacin waya nake"


"amma fa na dade ina kira tana rubuta Hakan har da daddare ma"

Qara daga kafadu tayi in an I don't care manner tace
"yeah, ina waya ne"

"wow! Da wa? Irin wannan dadewa haka?"

Dagowa tayi tadan yimashi murmushi
"kayi mammaki ne?"

"sosai ma"

Murmushi taqara yimashi tace
"to ka daina"

Shiru yadanyi yana kallonta

"and who is that if I may ask" yafada yana dan bubbude littafin daya ciro


*"my man"*


Cak ya tsaya da bubbude pages din dayake kamar wanda aka tsaida da remote

Saikuma ya dago ahankali ya kalleta yaga ita hankalinta ma na kan textbook din gabanta

"Your man?" yafada yana tsareta da ido


Dagowa tayi itama tana kallonshi and she can swear taga wani abu mai shigen da kishi a idanunshi saikuma taga yayi saurin sauke idanu

Hakan yasata amsawa cikin fara'a
"yes, sorry ban ta6a discussing dinshi da kai ba, he's my cousin, he's very nice insha allah zanyi introducing dinku wa juna watarana"


Tunda tafara maganar ya sake dagowa yana kallonta har takai aya


Wani dry murmushi yayi sannan ya maida kanshi akan littafin gaban shi ya cigaba da budewa

Itama bata qara cewa komai ba ta maida hankalinta kan littafin dake gabanta

Sai wajen ya dauki wani unusual silent da basu saba dashi ba don muddin suna tare babu yadda za'ayi su dauki tsawon lokaci kamar haka batareda sunyi exchanging Koda kalma daya ne


Suna ahaka har lokacin shigar zee class yayi Hakan yasa ta maida littafin ta rufe ta dago ta kalleshi taga idanunshi kafe suke akan littafin gabanshi shima

Tashi tsaye tayi wanda Hakan yasa shima ya dago for the first time bayan maganarsu ta dazu yana kallonta


Maida textbook din tayi a shelve din library din inda ta zaroshi sannan ta dawo ta dauki jakkarta dake kan desk pretending bata lura da kallon dayake binta dashi ba


Rataya jakkar tayi sannan ta kalleshi

"Bari natafi kar na makara Deen, see you" tafada tana dan daga mashi yatsu


Murmushi kawai yayi ya kada mata kai tawuce yabita da kallo harta fice

_*my man*_ kalmar ta ta dazu tadawo mashi a kwanya


Ahankali ya lumshe idanu ya bude yana jan wani nannauyan numfashi


Me Hakan ke nufi? Me take nufi da *her man?*

Koma dai me Hakan yake nufi beyi sounding good to him ba

Haka kawai yaji zuciyarshi ta quntata tayi mashi nauyi ga wani daci daci dayake ji maqoshinshi


Maida littafin gaban shi yayi ya rufe shima ya tashi ya kwashi littafanshi ya rungume ya fice daga library din


Wani quiet wuri yasamu ya zauna don haryanzu akwai kingin lokaci kafin yashiga class

Duk yadda yaso ya maida hankalinshi akan littafin daya kuma zarowa kasawa yayi

Kalmarta kawai take mashi kai kawo a zuciya

*sorry ban ta6a discussing dinshi da kai ba, he's my cousin, he's very nice insha allah zanyi introducing dinku wa juna watarana*


Jiyayi zuciyarshi taqara quntata, yaji ya tsani mutumin tun kafin ma ya ganshi


Haka yaita zama shikadai cikin quncin zuciya har lokacin lecture dinsu yayi ya tashi ya wuce class

Saidai me? A class din ma babu abinda ya fahimta, yadai ga lecturer din nata 6a66atu amma bazai iya riqe kalma daya daya fada ba


Har akayi lecture din aka gama be fahimci komai ba, haka shima ya taso yabiyo ayarin masu fitowa daga class din yafito


Kasancewar anfara kiraye kirayen sallah yasa yawuce masjid din school din don yin sallah

Koda yafito be bi takan inda zasu hadu ba yawuce class ya zauna dukda saura mintuna talatin afara lecture din, haka kawai yaji beson zuwa wajen ta yanzu saboda yadda zuciyarshi kemashi zafi duk in yatuna da kalmarta

Haka ya zauna ya rungume hannayenshi a qirjinshi ya kafe wuri guda da kallo abubbuwa kala2 na kai kawo a qwanyarshi


Ahankali ahankali class din yafara cika har lecturern dazai yimasu darasin shima yashigo

Abin mammaki wannan karon ma babu abinda ya tsinta a abubbuwan da akeyi a class din

Gangar jikinshi ke zaune a class din amma hankalinshi da tunaninshi sunyi nisa, be ankaraba yaga anfara fita daga class din alamun har angama lecture din

Agogon hannunshi ya duba yaga har 4pm saura Hakan yasa shima ya tashi jiki a sanyaye yafito


Koda yazo inda suke zama be ganta ba hakan yasashi wucewa library nan ma babu ita sai ya wuce department dinsu don ganin ko tana can amma canma babu ita don babu ma mutane sosai Wurin Hakan yasashi sanin ta tafiyarta

Sai yaji zuciyarshi taqara quntata, ranshi yaqara dagulewa yaji wani abu ya tokaremashi qirji


Juyowa yayi kawai yanufi hanyar fita school din

Cikin sa'a yana fitowa yaga wata napep ta sauke wadansu sai ya qarasa yayiwa mai napep din magana suka daidaita yashige suka wuce


A bangaren zee kau tun daga reaction dinshi na farko data gani tafara tabbatar da hasashenta

Kamar yadda Deen yayi attending class batareda ya fuskanci komai ba Haka itama tayi

Itama kawai zama tayi a class din amma bata fahimci komai ba, gabadaya hankalinta da tunaninta nakan reaction din Deen na dazu.

Tabbas ta hango wani abu mai shigen kishi a qwayar idanunshi and then sai yarage kuzari, yama qi magana harta taso tabar wajen

Dukda yayi qoqarin 6oye expression din fuskarshi tana iya hango bitterness din fuskar, tabbas maganar ta ta dakeshi don taga alamun Hakan

Cije lip dinta na qasa tayi sosai tana jin yadda zuciyarta ke bugu sosai. Tama rasa tunanin da zatayi.


Koda suka fito lecture din itama masjid ta nufa tayi sallah, tana fitowa kuma ta hangoshi shima ya fito ya nufi hanyar barin wajen, kamar tayimashi magana kuma saita fasa tabi tafiyar dayakeyi a sanyaye da kallo, tabbas muddin ka sanshi sosai kallo daya zakamashi ka gane ba lau


Wani dan murmushi ya su6uce mata tana wani calculating a zuciya sannan ta dan ciji qasan lip dinta itama tafito daga wajen


Koda tafito daga next lecture din nasu bata tsaya jiran shi ba kamar yadda tasaba kawai tashige mota suka fice tana jin wani yaqini a zuciyarta


***


A bangaren Deen haka ya qarasa ranar cikin rashin walwala, ko kaka ma tasan yau ba lau ba

Tambayar duniyar nan tayimashi amma amsar daya ce "babu komai"

Hakan yasa tayi tunanin ko bejin dadi ne shiyasa yake tsoron gayamata saboda shan magani

Hakan yasa taje ta dauko magani tabashi akan yasha

Ga mammakinta sai gani tayi ya amsa babu ko gardama ya watsa a baki ya kora da ruwa ya tamke idanu yana hadiyewa don shima abinda zai sauqaqa mashi abinda yakeji a zuciya yake nema shiyasa beko yimata gardama ba ya amsa yana ganin inhar zai sauqaqa mashi abinda yakeji babu abinda zai sashi yaqi sha

Komawa yayi ya jingina da bangon dakinshi yana maida numfashi

Jiki a sanyaye kaka ke mashi sannu Saidai ko bude idanunshi beyi ba

Ce mashi tayi ya kwanta ya dan rintsa qila kafin ya farka zaiji sauqi

Babu musu ya zame ya kwanta yaqara tamke idanu yana jin yadda zuciyarshi ke tashi kamar zaiyi aman maganin dayasha


Saida yaji fitarta sannan ya bude idanu ahankali ya kalli kofar data rufomashi

Qara maida idanun yayi ya rufe yayi shiru

*my man* muryarta taqara yimashi amsa kuwa a kunnenshi

*he's very nice*


Bude idanun yasakeyi sannan ya miqe zaune ahankali

Wayarshi ya lalubo ya danna power botton takawo haske

Time ya duba yaga 10 saura na dare

Haka kawai sai gani yayi ya shiga contact ya fara scrolling sunayen ciki

Daidai sunanta dayayi saving da *bestie* ya tsaya


Ya dade yana kallon number sannan ahankali kamar mai tsoro ya dannama number kira

_the number you dial is busy with another call, please hold on or try again later_
Abinda yaji baturiyarnan ta m.t.n tafada kenan sannan ta cigaba da ringing

Harta katse bata dagaba Hakan kuma be hana yasake kiraba yanajin zuciyarshi na wani irin zafi kamar a oven

Tambayar dake kai kawo a qwalwarshi itace dawa take wayar? Yayinda zuciyarshi ke hasasomashi qila da so called *man* dinta take wayar

Saida ya jeramata kira uku duk babu wanda ta daga she's busy on another call, qarshe sai tayi sending sms na
_*am busy, please call later*_


Besan ya akayi ba sai gani yayi ya wurgar da wayar ta daki bango ta fado qasa

Be bi takanta ba ya koma ya kwanta kan gadon ya jawo bargo ya rufe jikinshi har kai dukda uban zafin da akeyi

Ya runtse idanunshi Gamm yanajin zuciyarshi na suya kamar a kasko... ✍️


Ummin fasihu 🧚🏻‍♀�
8/2/21, 9:37 PM - Buhainat😝: *🙍🏻‍♂️DEEN 🙍🏻‍♂�*


*040*


*THE CONFESSION💗*


Koda gari ya waye Dakyar kaka ta iya tadashi yafita sallar asuba don dama sai gab da asuban yasamu barcin ya dan daukeshi


Kallo daya zaka yima yanayinshi kayi tunanin beda lfy duba da yadda yaqaro sanyi ya hada da ainahin sanyinshi


Ba'a dade da gama sallar ba yadawo yana jin kamar yayi shigewarshi daki yayi barcinshi amma bazai iya barin kaka da wadannan tulin aikin ba ita kadai


Gaisawa sukayi da kaka kamar yadda suka saba tana Tambayar jikinshi yace mata da sauki ya wuce Domin hura wutar koko


Be wani sha wahala ba takama kasancewar dama ya saba da hurin wutar amma maimakon ya tashi ya dora tukunyar saiya tsaya a tsugunnen dayake ya qurawa jar wutar dakeci ido


Kaka batasan yana yiba har Saida tagama wanke waken data surfa takawomashi don yakai markade sai ta ganshi tsugunne gaban murhun ya qurawa wutar ido kamar mai karantar wani abu jikinta

Magana tayi mashi amma beji ba don yayi nisa sosai Saida ta dan ta6ashi sannan yayi saurin dagowa sai kuma ya kalli wutar yayi saurin tashi yawuce don dauko tukunyar kokon kaka na binshi da kallo


Saida ya dora ruwan sannan ya amshi bokitin waken yafita yo markaden

Kasancewar ya dan makara da zuwa markaden sai ya tararda jira har mijin mai markaden na tsokanarshi wai ko yau ranar barci sukayi

Shidai bayan murmushi babu abinda yake


Waje ya koma don jira yasamu dakalin kofar gidan

Shiru yayi ya kafe santar tasu da ido yana dorawa daga inda ya tsaya a tunaninshi yana kuma tunano mafarkan dayayi nata a yar kwanciyar nan dayayi


Wanda yafi daga mashi hankali cikinsu shine wanda yayi daga baya bayannan wanda yana cikin yinshi ne kaka ta tadashi

Wai a cikin mafarkin yaga zee zaune da so called cousin din nata suna fira dukda be iya ganin fuskar mutumin ba sosai

Fira suke sosai suna Dariya, kawai sai gashi kamar an jefoshi a wajen

Be nufi kowaba sai saurayin yafara yimashi qarajin ya tashi yabar wajen

Qin tashi mutumin yayi kuma yaqi kallonshi hasalima kamar basu masan dashi ba don firarsu suka cigaba dayi cikin nishadi


Haushi yaji saiya ture mutumin daga kujerar dayake akai ya fadi

Jiyayi zee tayi qara kamar ita ya ture sannan ta tashi tana hayyayako mashi akan meyasa ya ture "man" dinta shikuma ambatar man dinnan yaqara qular dashi sai ya juyo kanta yafara magana cikin hayyayakowa shima, Saidai shi kanshi besan abinda yake cewa ba, kamar ma maganar bata fita don jin maqoshinshi yayi tamau kamar an shaqe amma ahaka yake fizgar magangganun yana gayamata, magangganun ma ko sauti babu

Yana cikin haka yaga ta tureshi gefe taje zata tada wancan wanda ke kasa har lokacin sai ya cafko hannunta ya fizgota ta fado jikinshi beyi wata wata ba ya Hade bakinsu Waje daya

Mutsu mutsun qwacewa tashiga yi amma yaqi bata dama saima farma le66unanta dayayi kamar maye yasamu nama, ahaka yaji ana janshi a baya ana jijjigashi, can yaji muryar kaka na cewa
"kyakyawa ka tashi, kyakyawa na! Kyakyawa! Ka tashi karda ka rasa jam'i"

Sai a lokacin yafara bude idanunshi ahankali har suka bude tarr yaga kaka sunkuye akanshi tana cigaba da tadashi, dan Juyawa yayi saiya fuskanci ashe ma kan katifarshi yake, ashe mafarki yake.

Saida ya tabbatar Yana da tsarkin jiki sannan ya lalla6a ya taso yafito jiki a mace


Jin a dan bubbugi kafadarshi yasashi qara yin firgigit ya dago yadawo daga duniyar tunanin daya sake lulawa

Wani yaro yagani tsaye akanshi bokitin markaden Deen a gefe

"yaya Deen wai ance ga markaden" inji yaron

Miqewa Deen din yayi ya lalubi kudi yaba yaron yace yakai sannan ya dauki markaden yayo gida cikin dan sauri sauri ganin yadda gari yayi fau yayi haske yasan ma kaka nacan tana tunanin lafiya


Illai kuwa yana shiga sukaci karo da kaka datake shirin fitowa jin shirun yayi yawa

Tambayar shi tayi ya akayi ya dade haka yace mata jira ke akwai

Suka dawo ciki tare yaga harta sheqa tukunyar farko ta maida wasu


Murhun qosai yanufa yafara hurawa ita kuma kaka tashiga hada kullun qosan


Cikin dan qanqanin lokaci suka gama kaka tafara tuya izuwa lokacin har yara sunfara Shigowa


Haka dai Deen ya daure yayi attending customers din har suka samu yaqare duka

Lokacin har tara da rabi Hakan yasa kawai yafada bandaki yayi wanka sannan ya fito ya hau shirin school


Har daki kaka ta kawomashi nashi kokon don ya karya

Saida tagama sannan ta miqa mashi magani akan yasha taga haryanzu kamar jikin be warware ba

Kamar zaiyi kuka yake cemata shifa ya warke amma bata kulashi ba Saida yashasu yana kakari yana komai

Sannan ta sallameshi yafito daga gidan lokacin har goma ta wuce yasamu aca6a suka daidaita yahau suka lula


*UMYU*


Koda ya iso school din be nemeta ba don yasan tana class kasancewar yau morning lecture gareta sai kawai yayi wucewarshi inda suka saba zama idan basa library yayi zamanshi can ya dora karatun jakinshi daga inda ya tsaya


Students suke ta fita daga class din.

Ida rubuta abinda take rubutawa tayi sannan ta maida littafin ta rufe ta bude jakkarta ta saka aciki

Itama tashi tayi tabi ayarin masu fita itama tafito


Fiddo wayarta tayi ta duba time taga 11:52am Hakan yasa tasan is either yana library ko wurin da suka saba zama don yau lecture din 1pm gareshi, dama duk sunyi cramming lokacin lectures dinsu aka


Library tafara nufa dukda tasan mawuyacine ace yana can duba da zafin da akeyi a garin don yanzu damuna ta wuce ana zafin gasa dawa


Bata tarar dashi ba wurin kamar yadda tayi hasashe saita juya ta nufi inda suke zama din don tasan tabbas yana can


Daga nesa ta hangoshi zaune bisa benci ya sunkuya qasa amma batasan abinda yakeyi ba


Ida qarasowa tayi, jin motsinta yasa Deen saurin sa kafa ya baje rubutun dayakeyi da dan kara a qasa sannan ya dago yana kallonta, looking so beautiful as ever


Harta qaraso wajenshi be Janye idanunshi akanta ba har Saida ta kyafkyafta mashi yatsu a fuska sannan yadanyi blinking sai kuma ya sauke idanunshi qasa

Zama tayi kan dutsen dake facing dinshi tana cewa
"wannan kallon saikaja inyi tuntu6e"

Bece komai ba kuma be dago ba

"Saida naje library na tarda baka nan, how's my kaka?"

Sai a lokacin ya dago ya kalleta sai kuma ya motsa baki kamar mai ciwon baki yace
"she's fine"


Ganin yanayin dayayi mata magana kamar anyi forcing dinshi yasa bata qara ce mashi komai ba ta zaro wani Littafi ta shiga budewa

"I called jiya baki dagaba" yafada yana kafeta da ido

"yes I was on another call kuma I tried to reach you later amma bata shiga" tafada hankali Kwance batareda ta dago daga bude littafin datake ba

"you're busy with another call, da wa?"

Kafin ta bude baki ta amsa ya tari numfashinta da
*"Your man?"*


Dakatar da bude littafin datake tayi ta dago ta kalleshi and for the first time taga a very serious expression a fuskarshi, tunda take bata ta6a ganinshi in seriousness kamar yau ba, babu alamun wasa ko kadan a fuskarshi


Daga kafadu tayi ta maida hankalinta akan littafin hannunta tace
"yeah, ka canka daidai, I was busy with him"


Jin maganar tata yayi kamar saukar mashi a qahon zuciyarshi, bugun zuciyarshi yashiga gudu sosai


Dukda taji yadda hasken idanunshi ke reflecting a fuskarta bata dago ba saima cigaba da bude littafinta take wanda a zahiri tama wuce inda take son budowa


Hadiye wani yawu mai daci Deen yayi sannan ahankali yace
"Zainab.."

Sosai kiran yashigeta don yayishi ne in a very cool manner

Dagowa tayi ta kalleshi batareda tace komai ba sai zuciyarta dake qara gudu

Kamar bazai ce komai ba sai kuma yaqara tattaro wani yawun ya hadiye sannan yace
"please ina neman wata alfarma wajenki"

Shiru tayi takasa cewa komai saboda yadda zuciyarta ta tsananta bugu jitake kamar data bude bakin zuciyarta zata biyo ta wajen ta fito

Ganin batace komai ba kuma bata bar kallonshi ba yasashi cewa
"please, karki qara... Kulashi" ya qarashe yana kallonta da wani expression mai wuyar ganewa a fuskarshi

Batace komai ba sai kallonshi datake still
"please... Don Allah" yasake fada murya a matuqar sanyaye


Cikin danne abinda ke taso mata a zuciya ta yamutsa fuska

"I don’t get you"


Ajiyar zuciya ya sauke yadan ciji lower lip dinshi yasaki sannan yace
"I mean, your... Cousin, please kibar kulashi"

"why?" tafada tana mashi wani kallo

"because... I think... I don’t like him, please just stay away From him kuma kibar picking call dinshi... Please, do this for me... Please" Sai kuma ya dafe kanshi yana jin yadda zuciyarshi ke zillo


"what? Kasan abinda kake fada kuwa? Kasan matsayin wanda kake magana akai aguna, you just Said it, he's my cousin"

Janye hannunshi daya dafa kanshi dashi yayi yace
"am.. Sorry, nasan family dinki ne but... Just let it remain like that, babu qari babu ragi.

Please kibar kiran shi your man kuma kibar waya dashi like that" yafada shi kanshi yasan he sound so stupid

"me? Meye aciki don nayi waya dashi?"

"ba wayan dashi ne matsalar ba, what you guys are discussing ne"

"me muke discussing?" inji zee tana kallonshi kamar yau tafara ganinshi don sosai yakoma kamar bashi ba yawani burkuce

"I don’t know also amma koma menene it doesn't sound good to me, nasan qila kunyi awa kuna wayar.. And also dare ne, kamata yayi ace barci kike a lokacin"


"kamata yayi ace barci nake a lokacin kuma kai ka kira?"

"na kirane don nayi confirming kinyi barcin ne and also Koda kin daga bewuci mu gaisa ba inyi miki good night muyi hanging call amma shifa? Heaven knows what he's saying to you kuma allah kadai yasan lokacin da kuka gama wayar"


Tunda Deen yafara take kallonshi cikin mammaki deep down kuma farincikine kesata jin kamar ta taka rawa

Ganin wanda kake tunanin kai kadai ke haukanka akanshi na kishinka ba qaramin abu bane mai antaya mutum cikin farinciki, wanda ya tsinci kanshi a wannan yanayin kadai zai iya ganewa

"well ni banga abinda zai dameka ba akan haka"

"but am your friend, dole na damu dake"

"and he's my man, my boyfriend.."

"damn it!" yafada yana qara dafe kai cike da takaici


"wai Deen are you sure you're ok?"

Dagowa yasake yi wannan karon idanunshi sun fara chanza launi

"Nace maki kibar kiranshi your man and you're now calling him your boyfriend"

"wai Deen meke damunka ne? Meye matsalarka dashi"


"I don’t know, I just hate him, can't you get that?!" yafada cikin dan daga murya yana jin kamar yaita ihu don takaici

"you hate him? My boy friend?"

"oh my God! For Heaven's sake kibar kiranshi haka?" yafada jijjiyoyin wuyan shi na tashi


Dukda taji tsoron yanayin shi amma bata fasa cewa
"why? He's my boy friend, he loves me who are you to tell me not to love him back" tafada tana miqewa tsaye tana mashi wani kallo


Shima miqewa tsaye yayi
"No! Qarya ne, wlh ba sonki yake ba, yaudararki zaiyi, he never loved you" yafada yana maida numfashi ahankali

"what?" tafada tana dan ja baya

"yes, he doesn't, I swear, kawai he want to play your heart ne, he want to use and dump your heart, ki yarda dani" yafada yana dan matsota

"Deen, are you sure you're ok?" tafada tana qara jada baya ganin kamar ma ba a hayyacinshi ba yake

"yes.. Yes, yes Zainab, am ok, ki yarda dani, he doesn't love you, baya sonki, nike sonki Zainab, nike sonki..."


Tsit wajen yayi


Dafe kai yayi yana jan numfashi ahankali yayinda zee data qame kamar statue takasa Janye idanunta akanshi


Dagowa yasake yi ya kalleta da idanunshi dasukayi ja

"am... Sorry Zainab, am..." saikuma yaqara dafe kanshi, yakoma wani zararren qarfi da yaji lokaci guda


Sake Dagowa yayi
"Don Allah.. Kiyi hqr, bansani bane, bansan sadda nace haka ba... Amma kuma Gaskiya ce

I.. Love..you, Kiyi hqr amma that's it, the truth

Na dade ina ajiye wannan kalmar a zuciyata, na dade ina juriya wajen ganin na barta iya cikina amma not any more, bazan iya ba kuma. Am sorry.. Am sorry" yafada yana Hade hannayenshi


Ahankali zee da haryanzu idanunta ke kafe akanshi tafara takawa da baya baya

Ganin Hakan yasa yafara Binta shima ahankali

"nasani.. Nasan na wuce iyakata amma don Allah Kiyi hqr, wlh nima bansani ba, bansan sadda nafara sonki ba, please don't leave, please"


Haryanzu batace komai ba kuma bata bar kallonshi ba kuma bata bar tafiya da baya baya ba

"please Zainab, stop moving, say something but please don't leave me, nima nasan I was stupid to think of doing that but I swear nima bansani ba, bansan yadda akayi ba nafara ba, I swear ban saniba" yafada still yana Binta


Juyawa tayi da sauri tafara tafiya da sauri sauri don barin Wurin

Ganin Hakan yasa shima Binta da sauri, Ganin Hakan yasata fara gudu shima yasa gudu yabita Saidai cikin tsautsayi yayi tuntu6e da wani dutse a gabanshi yayi saurin duqawa yana kama kafar

Sake Dagowa yayi yaga takusan shanye kwana Hakan yasa shima yacije ya tashi dukda radadin da qafarshi kemashi yabiyota Saida Koda shima ya shawo kwanar babu ita babu alamunta


Cigaba da tafiya yake yana waige waige, yadai san bata isa takai gate ba don akwai tazara sosai da nan wajen dole ya hangota, dole Saidai idan wani Wurin ta 6oye

"Zainab? Zainab!!" yafada yana dudduba Wurin amma babu ita Hakan yasashi qarawa gaba yana nemanta amma ba ita ba labarin ta, Hakan yasa yadawo yanufi department dinsu yaga ko can tayi

Daga inda take la6e ta hangi shigewarshi kwanar da zata sadashi da department dinshi Hakan yasata fitowa tana share hawayenta ta nufi hanyar gate da sauri sauri tana yi tana waige harta samu tafito daga school din

Wasu adaidaita biyu tagani sunzo wucewa tashiga tsaida na farkon Saida tazo gab taga ashe cike take

Saita koma tana tsaida na biyun

Cikin sa'a babu kowa ciki, fadawa ciki kawai tayi tana cema mai adaidaitan sutafi tana leqen gate din school din

Babu musu mai adaidaitan yaja napep din suka bar wajen


Babu inda be duba ba a department dinsu amma babu ita yasake dawowa inda ta 6oye dazu batanan ya wuce library nan ma haka

"ya sallam!"
Yafada yana zama kan daya daga cikin kujerun library din ya dafe kanshi

"my goodness! Tayaya ma nayi wannan su6ul da bakan" yafada yana rufe fuskarshi da taffukan hannunshi yana furzar da huci


Yes he's in love with zee kuma ya dade da sanin haka Saidai bayada courage din tunkararta da Hakan

Tayaya talaka kamar shi wanda bayan allah da annabinsa beda kowa sai kakarshi zai tunkari mace kamar zee, yarinya yar masu kudi, wanda babanta sannane ne a katsina dama nigeria gabadaya? Tayaya?

Bazai iya tunkararta da hakan ba, gani zatayi yama raina ajinta, gani zatayi don yaga tayi strooping tana abota dashi shine yasa zai wuce makadi da rawa wajen cewa yana sonta

Tabbas yasan zee tafi qarfinshi ata koina, asali, arziqi, class, komai ma

Yanayi ne ma da qaddara yasa suka Hade a school dinnan don yasan tafi qarfin zuwa school din

Tun sadda ya fahimci halin da zuciyarshi ke ciki gameda ita yasa yafara kafa kafa da ita wajen barin Hakan iya zuciyarshi batareda ya barshi ya fito ba

Ya gano Hakan ne tun kwanciyarshi a hospital, yaso yayi denying Hakan amma ita zuciya batasan wannan ba, abinda takeso shi takeso ko kai mai zuciyar kaqi ko kaso

Lokacin da aka sallamesu daga hospital he's very sad

Dik majinyaci farinciki yake a lokacin da aka bashi sallama amma shi akasin haka ne a wajenshi don yasan Hakan na nufin yin nisa da juna, dan ganin ta dayakeyi sau biyu a ranar zai zama tarihi

Hakan yasa lokacin dazasu tafi yakasa tafiya ya tsaya yana kallonta yana jin kamar ya hanata tafiya amma haka ya daure yanaji yana gani ta tafi tabarshi feeling very empty kamar ta tafi mashi da abu mai matuqar muhinmmanci kodayake ta tafi din da abin nashi mai muhinmmanci, zuciya ❤️


Tun daga lokacin yake jin tsananin kewarta da begenta, kullum cikin tunaninta yakeyi da mararin ganinta amma yasan ba hali wataqila shida ganinta sai sunyi resuming

Kwatsam sai gata sati daya da sallamarshi

Lokacin daya shigo ya ganta jiyayi kamar a mafarki don be ta6a kawo Hakan a ranshi ba

Murza idanunshi yashiga yi don tabbatar da ita din ce sai yaji kaka na cewa
"qaraso mana, ita din dai ce"

Qarasowa yayi cikin doqin ganinta Saidai me? Saiya lura ita kamar bata doqin ganinshi don kallo daya tayimashi ta sauke idanunta qasa

Hakan yayi matuqar sanyaya mashi jiki amma ya daure yayi mata magana yana tambayarta yasu mummy

Babu yabo ba fallasa ta amsa mashi saikuma ta tashi wai zata tafi

Beji dadi ba sam don ba Haka yaso ba, so yayi tayi zamanta susha firarsu yayita kallonta yana jin dadi

Ganin dagaske tafiyar zatayi harta miqe yasashi shima tashi ya shiga dakin kaka ya dauko wayar data bashi don maida mata

Koda yafito har takai zaure yayi saurin Binta

Kiranta yayi ta tsaya amma bata juyoba


Tambayar ta yayi tafiya zatayi sai ta juyo tace eh ko yanada matsala da Hakan ne?

Beji dadin amsar ba Amma ya amsa da A'a sannan ya maida mata wayarta, da farko be lura da kallon datake mashi ba sai daga baya lokacin daya miqa mata wayar hannunshi don ta samashi number mummy

Kallon datake mashi lokacin yakuma sanyaya jikinshi sai yaji yakasa yimata dayar maganar wato tasamashi numberta su dinga gaisawa


Ganin taqi barin kallonshi yasashi tambayarta lfy kau? Sai yaga ta kauda kai saikuma tasake juyowa ta amsa da lfy ta amshi wayar tayi yan danne danne ta miqomashi

Qin amsa yayi yana kallonta trying to read her expression amma Abu daya ya iya ganewa, tana fushi

Hakan yasa yakasa qara tambayarta number ta sai ya amshi wayar kawai yana cewa
"Are you sure you're ok?"

Sai gani yayi ta juya tana cewa
"more than you are" ta fice


Binta da kallo yayi yana jin ba dadi, tsawon satin dayayi batareda yasata a idanunta yasa yayi missing dinta sosai yayi tunanin itama Hakan yake a wajen ta yayi tunanin duk lokacinda suka sake ganin juna Dakyar zasu rabu

Fitowa yayi ya tsaya bakin kofar gidansu yana kallonta ta cikin mota dukda baya iya hangota saboda tinted glass din motar, yana ji yana gani aka ja motar aka tafi aka barshi nan


Daga lokacin duk sai jikinshi yayi sanyi, ya kasance kodayaushe cikin tunaninta yake

Bayan kwana biyu da tafiyarta ya matsa ma kaka ta bugama mummy tayi mata godiyar datace zata yimata

Haka yaje yasanyo kati na #200 a lokacin ita kenan ma gareshi duk don yaji lfyar zee in so samu ne ma yaji muryarta

Saidai Koda suka gaisa din kaka ta tambayi zee tace ina take tace mata lfy lau tana dakinta, jiyayi kamar yace ma kaka tace a kai mata amma babu dama haka shima ya amshi wayar suka gaisa sukayi sallama da juna ba don yaso ba

Bayan kwana biyu again yasake tusa kaka gaba akan tasake kira, shima wannan lokacin zee batanan tashiga wanka wai, Hakan ba qaramin sake dagulamashi lissafi yayi ba

A kira na uku ne yaji mummy na gayama kaka zee tayi tafiya zuwa garinsu mummyn, Hakan ba qaramin sake dagulamashi lissafi yayi ba don Hakan ya tabbatar mashi cewa shi da ganinta ko jin muryarta kuma sai sunyi resuming

Haka ya hqr don dole ya cigaba da looking forward na resuming dinsu, kullum cikin qirgar ranakun dasuka rage yake

Ranar daren dazasu koma ko isashen barci beyi ba saboda doqi

Ranar dazasu koma kuma safko ya buga saboda doqi, yaci kwalliyarshi ciki kayanshi na qure daka yatafi Saidai me? Wannan karon ma tarbar dabeyi tunani ba tayi mashi

Yana shiga gate din school din yaganta kuma kallo daya yaimata ya gane itace dukda bayanta yagani, Hakan yasa yafara sauri yana kiran sunanta

Saida yakusan taddota sannan yaga ta tsaya alamun tajishi amma bata juyo ba

Da sauri ya qarasa yana maida numfashin saurin dayayi

Zagayowa yayi gabanta yana kallonta cikin so da shauqin ganinta

"Zainab is this you?" yafada cikin tsananin shauqi da jindadin ganinta

Sai gani yayi ta dago ta kalleshi tayi shiru kamar mai karanta wani abu a face dinshi

"Zainab, are you ok?" yafada ganin yadda ta kafe shi da ido

Still babu amsa kuma batabar kallonshi ba

"Zainab..."

Sai yaga tasa hannu ta toshe duka Kunnuwanta ta runtse idanunta gamm

Ganin Hakan yasashi rudewa, qara kiran sunanta yayi sai yaga tayi saurin Zagayeshi ta wuce Hakan yasashi binta ya sha gabanta

Cikin matsanancin damuwa yasake tambayarta lfy amma saita qara ra6awa zata wuce yasake tareta da sauri yana sake kiran sunanta

Tsawa tayi mashi wanda yajishi har cikin ranshi wanda Hakan Saida yasa yadanja baya

"I said leave me alone, can you get that?!" tafada again a tsawace

Dukda tsoron tsawar dayake Hakan be hana yadan qara matsowa ba yasake kiran sunanta, sai ta dafe kai tajuya takoma ta inda ta fito

Da farko kasa Binta yayi saikuma yabita amma yana zuwa yaga wucewar adaidaita ashe itace a ciki


Sosai jikinshi yayi sanyi yaji kamar yaita kuka, ya dade tsaye a wajen harya gaji yakoma

Koda yakoma ma wuri yasamu kan dakalin wani office ya zauna inda zai dinga hango gate yadda data shigo zai ganta

Amma shiru babu ita babu alamunta har lokacin zuhr yayi dole ya tashi yaje yayi sallah yakuma dawo ya dasa jiranta daga inda ya tsaya Saidai har asr bata dawo ba hakan yasa ya tashi yayi sallah yawuce gida zuciyarshi a matuqar sanyaye

Ranar beyi wani barcin kirki ba saboda damuwa

Washegari ma Hakan take don ranar tun Shigowarta ya ganta kasancewar ranar ma dawuri yaje school din

Yana kallonta har tazo ta wuce sannan shima ya lalla6a yabita har inda tasamu ta zauna

Tsayawa yayi jikin wata bishiya mai facing dinta ya rungume hannayenshi a qirji yana kallonta

Abin mammaki Saida yadan jima ahakan kafin ta farga dashi kuma tana ganinshi ta sake kafeshi da ido irin jiya

Qarasowa yayi gabanta ya tsugunna yafara qoqarin yimata magana tăsake tashi zata tafi

Shan gabanta yayi yana mata magiyar ta gayamashi ko fushi take dashi amma taqi sauraronshi saima tsawar datayi mashi, Ganin Hakan yasashi barinta ta wuce, har tayi nisa ya tsaidata ta hanyar tambayarta ko saboda ya maido mata wayarta take fushi, idan ma don hakane tayi hqr shi bada niyyar ya 6ata mata rai ba yayi Hakan

Bata ko juyo ba tawuce ta barshi nan tsaye

Sai yaji zuciyarshi taqara quntata, sai jiyayi duk murnarshi ta Ayi resuming school yaganta duk ta koma ciki, damuwa ta maye gurbinta


Washegari yazo har yatafi bega 6il6ishinta ba, Hakama Washegari nan ma ko mai kama daita be ganiba Hakan kuma ba qaramin qara tsundumashi kogin tunani da damuwa yayi ba


Ranar juma'a kamar bazai ceba saikuma ya shirya jiki a sanyaye yaje don daya zauna gida yaita tunani gwara yaje can Koda bazai ganta ba atleast zai samu damar tunaninta batareda takurawar kaka ba


Usual inda yasaba zama cikin yan kwanakinnan wato dakalin wannan office din inda ake iya hango gate daga nan ya tsaya ya jingina da bango

Be dade ba kamar a mafarki kawai yaga Shigowar motarta

Be motsa ba hakan zalika be kyafta idonta ba akanta har aka bude mata kofa tafito

Sosai tayi mashi kyau cikin shigar shaddar datayi Hakan yasa ya shawara da kallonta

Kawai sai gani yayi tafara waige waige, sai zuciyarshi tabashi ya 6oye kar ganinshi yasa tasake Juyawa ta koma yau ma

Saidai kafin yayi wani yunkuri harta juyo sun hada ido

Gani yayi ta kafeshi da ido shima sai yakasa Janye nashi akanta yana kallonta zuciyarshi nata zallo kamar zata fito waje


Ga mammakinshi sai yaga ta sakarmashi murmushin da be ta6a ganin wanda ya ta6a yimata kyau irinshi ba

Tashi yayi daga jinginen dayayi yana jin nauyin zuciyarshi na raguwa ahankali

Blinking idanu yayi don ganin ko idanunshi ke gayamashi qarya

Sai yaga dagaske ne, zee daice tsaye tana mashi murmushi

Besan sadda shima yafara murmushi ba harda yar Dariya sannan ya qaraso wajenta da sauri

Murmushi tasake yimashi sannan ta wuce shi ta nufi hanyar library ganin Hakan yasa shima yabita da sauri feeling so happy, baqincikin zuciyarshi na yayewa


To a lokacin ne suka shirya, ranar yayi farincikin daya rabu dayi kuma a ranar bebari damarshi taqara su6uce mashi ba ya amshi number ta kuma ya amshi wayarta data mashi kyautarta


Yaso ya kirata tun ranar amma gudun karya takura mata ko taqara botsare mashi yasa yafasa ya haqura har Washegari, da yaso yabari ya haqura har dare amma yakasa sai ya bugamata a lokacin


Yaji dadin samunta dayayi da kuma dagawar datayi a kira na farko don yadda yasanta da ajinnan yayi tunanin bazata daga ba, kuma ajinta na daya daga cikin abubbuwan dayasa ya kware mata sai kyawawan dabi'unta wanda idan ba saninta kayi ba sosai bazaka ta6a sanin tanada su ba, she's classic but simple, very simple and nice


A ranar badan yaso ba yayi mata ban kwana dawuri ba saidon karya takura mata gashi daman lalla6ata yake yi karta qara yin fushi dashi don yasan shi zaisha wahala don bazai iya yin zuciya ya barta ba don zuciyar bazata bada hadin kai ba, gwara dai ya lalla6a


Ahaka har suka kwashe wadannan lokacin kullum da sonta yake kwana yake tashi don jiyake ma kamar qara huramashi wutar sonta a zuciyarshi Hakan kesa wani sa'in har tausayin kanshi yake don yasan abinda bazai yiwubane yake qwallafawa ranshi akai, amma ya ya iya? Shi kanshi da yasan yadda zaiyi ya cire sonta a zuciyarshi da yayi Hakan amma baya iyawa Hakan yasa yabar abinshi a zuciya dukda wani sa'in Dakyar yake controlling emotion dinshi, gudu yake kar Hakan yasa yayi biyu babu ba soyayyar takuma warware abotarsu, gwara ya tsaya da daya, da babu gwara ba dadi


Saidai kalmar ta na *my man* yazo ya ruguje tsarinshi, besan yanada kishi ba sai jiya, jiyayi kamar garwashin wuta ta watsa mashi a lokacin, Ganin idan yace zaiyi magana zai saki layi yasashi hadiye wa Dakyar yayi controlling emotion dinshi amma na yau is so unbearable

Jiyayi kamar yaita hauka lokacin da take kiran wani her man wai harda boy friend, Hakan yasa yakasa controlling kanshi harya furta abinda ya dade yana 6oye wa a zuciyarshi


Shikenan ya rushe komai, ya lallata komai, ya rasata har abada, bazata qara kulashi ba, he can't imagine rayuwa batareda ita ba, yasan shikenan watan wahalarshi ta kama


Sauke taffukanshi daya rufe fuskarshi yayi ya hadesu daidai saman bakinshi yana jin kamar yayi kuka

Shi kenan, shi kenan. Abinda yaita nanatawa a zuciyarshi kenan


Dan karkatawa yayi ya zaro qaramar wayarshi don dama baya fitowa da babbar yayi saurin shiga call log ya lalubo numberta dake sama don dama tun bayan Kiranta dayayi jiya be qara waya ba

Dialing number yayi yana hadiye wasu yawu a bakinshi

Ringing take amma har tayi ta tsinke ba'a daga ba, qara danna wani kiran yayi nan ba babu response be gaji ba yasake danna wani kiran itama harta yanke ba'a daga ba.

Sake kira a karo na hudu yayi amma sai yaji yar baturiyarnan mai ban haushi na cewa
_the number you dial is switch off, please try again later_


Cike da jin haushi yau ma ya jefar da wayar kamar na jiya yasa hannu bibbiyu ya dafe kanshi dake barazanar rabewa gida biyu... ✍️


Ummin fasihu 🧚🏻‍♀�
8/2/21, 9:37 PM - Buhainat😝: *🙍🏻‍♂️DEEN 🙍🏻‍♂�*


*041*


*IS LOVE REALLY BLIND? 🖤*


"madam ina muka nufa?"


Sa bayan hannunta tayi ta goge wasu sabbin hawayen dasuka qara zubomata

"New Layout" ta amsa ahankali


"kudinki #250 ne" inji mai adaidaitan


"muje" tafada tana qara share wasu hawayen dasuka qara gangarowa


Sunqi tsayawa, kuma dama batayi qoqarin dakatar dasuba, bata damuba suyi ta zuba, suyi ta zuba bazata gaji da sharesu ba


Zuciyarta ta cinkushe, a halin yanzu ita kanta batasan a yanayin da take ciki ba

Farinciki ko baqinciki? Dadi? Haushi? Takaici? Batasaniba, batajin komai

She's emotionless, batajin komai, dama ana haka?


Qara share wasu da suka sake gangarowa tayi


*Saboda ni ke sonki Zainab, nike sonki...*


"Ya allah!"
Tafada tana rufe fuskarta da taffukan hannunta tana shesheka


Mai adaidaita yadan waigo ya kalleta jin kamar kuka take don sheshekar nata mai sauti ne

Maida kallonshi yayi ga titi cikin zuciyarshi yana cewa
"aifa! Ita wannan ko me tayi? Idan kaga yanmata na kuka to ta 6aci, sun sufka tsiyar. Allah ya kyauta, dama yan jami'a ai sai ahankali tunda har baraka ta iya haka ai kowama zai iya, allah ya kyauta"


Itadai zee batasan yana yi ba don tayi nisa a kukan datake sai jitayi wayarta na ringing


Bata dago ta duba ba har kiran farko ya katse, sai a kira na biyu ta dago ta duba wayar taga shine


Bata daga ba kuma bata bar kallon wayar ba har ta tsinke

Tana tsinkewa kira na uku yasake shigowa kuma still shine


"madam kamar fa kira ake" inji mai adaidaita


Ko kallonshi batayi ba bare ta nuna tajishi


Kiran na katsewa ta danna power botton ta kashe wayar gabadaya ta jefata a jakka sannan takoma ta jingina da jikin kujerar ta lumshe idanu Tanajin yadda zuciyarta ke qara cinkushewa wuri guda.


Da kwatancenta suka isa qofar tangamemen gate din gidansu


Tsane fuskarta tayi ta ciro google dinta na cikin jakka ta kwama ma fuska sannan ta sauko

#500 ta ciro miqaqa tabashi

Shima kafin yayi yunqurin bata canji har tayi gaba

"hajiya chanjin fa?" inji dan adaidaitan yana leqowa


Hannu kawai ta daga mashi alamun yabarshi batareda ta juyoba ta qarasa gaban gate din tafara knocking


"to angode, Allah yabiya!" inji mai adaidaitan cikin daga murya yadda zataji


Ko nuna alamun taji batayi ba ta cigaba da knocking gate din wannan karon a dan fusace, Ganin bata kulashi ba yasa yaja yar napep dinshi yayi gaba


Qaramar kofar jikin gate aka bude security ya leqo fuska a daure yana readyn yin bala'i amma ganinta yasa yadan wara ido sai yayi saurin ida bude kofar yana mata barka da dawowa


Ko kallonshi batayi ba tazo ta shige

"wai wanene naji kayi shir... " ganin Zainab ya sa bala kasa ida Maganarshi yayi saurin tashi tsaye


"subhanallilah, madam? Sai naji kamar kince sai qarfe uku zanzo" inji bala yana rarraba idanu


Ko iskar data deboshi bata kalla ba ta wucewarta ta nufi cikin gidan tanajin zatayi breaking down at any time, babu abinda takeso kamar ta fada kan gado ta jawo pillow ta rungume ta rintse idanunta gamm


Security ya qaraso wajen bala dake tsaye yana bin zee datayi nisa da kallo


"ya akayi to tadawo dakanta yau?"

"wama yasani, ni wlh 3pm tace nadawo" inji bala


"to qila kawai taga damar tahowa ne, tunda kaga bata cemaka komai ba ai saika share" inji security din yana komawa ya zauna

Shima bala zaman yayi amma kana gani kasan jikinshi a sanyaye yake


Luckily lokacin data shigo babu kowa a falon, dama tasan mawuyaci ne ta tararda mummy don dama tasan zata fita, zataje gidan wata qawarta Hajiya Kubra mai kayan qamshi, zatayiwa Feenah yan siyayya na kayan kamshi


Sama ta haye tayi dakinta direct


Tana shiga ta maido kofar ta rufe sannan tawuce wajen gadon da Tundazu take muradin ganinshi ta fada kanshi tajawo pillow ta rungumeshi qaqaam a qirjinta tana sauke numfashi ahankali


*I.. Love.. You, Kiyi hqr amma that's it.. the truth*

Qara rungume pillon tayi wasu hawayen nasake sauko mata


*Na dade ina ajiye wannan kalmar a zuciyata*

*na dade ina juriya wajen ganin na bar Hakan iya cikina..*

*... But not anymore*

Cusa fuskarta tayi cikin pillow

*Nike sonki Zainab... Nike sonki*


*I.. Love.. You*


Kuka take sosai tanajin kamar ana melting din zuciyarta


Bata ta6a tunanin haka zatayi reacting a irin wannan ranar

A tunaninta duk ranar da Deen ya bude baki yace yana sonta yini zatayi rawar murna

A tunaninta yini zatayi washe baki

Amma saigashi Hakan ya faru, mafarkin data dade datayi ya faru, burin daya dade a zuciyarta ya cika

Amma kuma ta rasa abinda zatayi sai kuka? Kuka?

To kukan menene? Meya sata kuka, dadi?

Dama wannan ake kira kukan dadi?

Inkau shine yaci sunanshi kukan dadi

Don kukan takeyi amma dadi yake mata, bata saniba ko kukan keda dadi ko dadi yasa kukan yayi dadi

Kawai abinda tasani shine tanaso tayi kuka, tayi kuka har yazamo babu sauran hawayen zubarwa.


*DEEN*


Gajiya yayi da zaman library din ya tashi jiki a matuqar sanyaye

Jiyake kamar an zuqe mashi dukkan lakkar dake jikinshi


Inda ya yasar da wayar yaje ya tsinceta don har battery yayi nashi wajen, don ma allah yaso qaramar ce mai ran qarfe da faduwar datayi jiya da yau ya jawo mata matsala don jiya ma da ya wurgata har Saida wani wuri yadan 6alle


Maida batteryn yayi ya rufe murfinta sannan ya kunnata


Saida yabari ta kunnu sannan ya qara shiga call log ya sake danna kiranta Saidai yanzun ma amsar daya ce, switch off


Saka wayar yayi a aljihunshi yafita daga library din


Be nufi koina ba sai inda suka zauna dazu

Littatafanshi daya bari wajen ya tattara ya rungume a qirji sannan ya nufo hanyar fita daga school din gabadaya yama manta dawani lecture dayake dashi


Koda yafito titin qwal yake sai private cars dake wucewa jefi jefi


Tafiya yafarayi ta gefen titi yana jin kanshi na wani irin saramashi


Haka yaita tafiya kai a qasa batareda yaqara Dagowa da niyyar tsaida abin hawa ba dukda yanda suke Wucewa jifa jifa Saidai ko lura dasu beyi don yayi zurfi a tunani


Yaci tafiya sosai sannan yaji ana mashi magana kamar daga sama

Saurin dagowa yayi ya waigo sai yaga ashe dan express(aca6a) ne ke mashi magana

"tafiya ne?"

Sai lokacin ya tuna ashe abin hawa zai hau

Kada mashi kai yayi yace
"eh"

"ok muje, ina ka nufa?"

Zagayowa Deen da yakejin kanshi kamar zai tsage yayi yace
"kofar kwaya bayan A.T.C"


"dari da hamsin" inji dan express din

Bece mashi komai na ya hau sannan yace
"muje"

Tada mashin din dan express din yayi yaja suka wuce


A kofar gidansu aka saukeshi, saka hannu yayi a aljihu ya zaro kudi yaba mai express din #200 yabashi chanjin #50 sannan yaja mashin dinshi yaqara gaba


Ahankali Deen yanufi kofar gidansu feeling very empty


Da sallama yashiga gidan Saidai shiru, sake kutsawa yayi yana sake sallamar nanma babu amsa kuma yasan Hakan baya rasa nasaba da yadda Muryarshi take bare kuma yanzu taqara sanyi

Qarasawa yayi bakin kofar kaka ya sake sallamar batareda ya shiga ba

Kaka dake zaune kan sallaya bata dade da gama sallar zuhr ba ta dago

"wslm, wa nake ji kamar kyakyawa na?"

Bece komai ba sai shiga dakin dayayi looking so weak

Kaka dake yunqurin tashi ta koma ganin ya shigo


"kyakyawa na, kace Saida la'asar zaka dawo" tafada tana kallonshi

Bece komai ba sai Qarasawa dayayi wajen ta ya kwanta ya dora kanshi a kan cinyarta ya lumshe idanu

Gaban kaka yafadi ganin yadda yayi

"Kamal lfy? Meke damunka wai?"

Shiru

"Kamal?"

Bude idanu yadanyi sai kuma ya maida yarufe cikin sanyin murya yace
"Kaka banida lfy, kibani magani"


Hankalin kaka ne ya tashi, yau Deen ke neman magani?


"Innallilahi waina ilaihi rajiun, bakada lfy meya sameka? Tashi muje asibiti, banga tazamaba ni ma'u, tashi tashi"

Sake bude idanunshi dasukayi mashi nauyi yayi sai kuma ya maida ya lumshe yace
"kaina ke ciwo, kibani magani nasha na kwanta zai daina"

"A'a kyakyawa na katashi mutafi asibiti wannan abu bana zama bane, banga ta zama ba"

Yiyayi kamar zaiyi kuka

"nidai kaka kibani bakisan yadda nake ji bane, jinake kamar kan zai tsage"

Jin Hakan yasa ta daga kanshi ta dora carefully akan pillon data jawo daga saman gadon qarfenta

Sannan ta miqe tashiga neman magani acikin wata yar locker

Fiddo maganin tayi sannan tayi sauri tafita ta debo ruwa tadawo wajenshi

Dakyar tasamu ya tashi zaune jikinshi harya fara daukan zafi


Maganin tabashi ya amsa ya watsa a baki yana danne yunqurin aman dake son tasomishi ya amshi kofin hannun kaka da sauri ya kora ruwan yasamu ya hadiye Dakyar


Maida kanshi yayi saman filo yana sauke numfashi ahankali

Kaka keta jeramashi sannu, jitake kamar taita kuka

Dakyar ta lalla6ashi ya tashi ya koma kan gadonta ya kwanta sannan taja abin rufa ta rufeshi tana jin kamar taita kuka don tausayinshi


Lamo yayi kan gadon ya lumshe idanu kamar mai barci amma ba barcin yakeyi ba


Tunannika kala2 kawai ke zarya a kwalwarshi ga saran da kan kemashi yanajin kamar ya cire kan ya yar ya huta


Yana nan Kwance kamar wanda dannau ya danneshi don kwata2 yakasa tashi don wata iriyar kasala ke nuqurqusarshi


Jin kiran sallar la'asar ya fargar dashi zuhr din da beyi ba hakan yasa ya tashi Dakyar feeling so weak


Kaka data shigo daidai lokacin tayi saurin qarasowa wajenshi

"yaya? Me zakayi?"

"sallah" yafada ahankali

"to bari na zubamaka ruwa, kana iyayin alwala da ruwan sanyi ko a zazzafa?"

Girgiza kai yayi sannan yace
"ina iyawa"

"to ka jirani ina zuwa" ficewa tayi don hada mashi ruwan

Can sai gata ta dawo dakin tace yafito yayi alwalar


Tashi ya sakeyi trying very hard to be stronger


Fita yayi wajen yayi alwalar sannan ya shiga dakin kaka ya gabatar da zuhr lokacin har an kabbara asr Hakan yasa yafito ya nufi massalacin wanda ana iya jin sallarsu ma daga gidansu Deen din


Koda ya isa massalacin har sun dago daga ruqu'i na raka'ar farko

Niyyar bin Liman yayi yayi kabbara sannan yayi joining dinsu


Koda suka sallame shi tashi yayi ya kawo nashi raqa'a dayan daya rasa sannan shima ya sallame


Ya dade nan zaune yana addu'o'i sannan ya shafa a fuska


Dan waiwaigawa massalacin yayi mutanen dake ciki yan tsiraru ne


Ja gefe yayi ya jingina da bango yana sauke Ajiyar zuciya

Jin zuciyarshi yake kamar wanda aka dauke wani dutse mai nauyi akanta


Dukda fargabar dayake na rasata gabadaya Hakan be hanashi jin sallamar rabuwa da abinda kullum dashi yake kwana yake tashi dashi ba

Furta mata abinda ya dade cinkushe a zuciyarshi ba qaramin sassauta mashi abinda yakeji a zuciyarshi yayi ba, he feel very relieve dukda acan qasan zuciyarshi tsoron rabuwa da ita yakeyi don yasan rabuwa daita daidai yake da rabuwa da farincikinshi


Karkatawa yadanyi ya zaro wayar shi ya danja gefe ya jingina da bango


Kunnata yayi yashiga call log yatsaya yana kallon number ta


Lumshe idanu yayi ya bude sannan ya danna mata kira badon yasa ran zata shiga ba


Jin tafara ringing yasa yadan wara idanu sannan ya kasa kunne yana jiran a daga

Saidai harta yanke ba'a dagaba, qara bugawa yayi itama harta tsinke ba'a dagaba Hakan yasa ya maida akalar kiran zuwa sms

Typing yafara
*Zainab am so sorry.. Please pick my call.. Please*
Ya tura


Saida yadan jira na yan mintuna sannan yasake bugawa Saidai harta tsinke bata daga ba hakan yasa yasan ko me zaiyi bazata daga ba hakan yasa ya cigaba da text din

*zăinab nasan yanzu haka ranki a 6ace yake kuma nasan ni naja amma please listen to me, I can explain*


*yes abinda nafada dazu is nothing but the truth, Ina sonki zee, na dade ina dakon soyayyarki a zuciyata, na dade ina 6oyonta a zuciyata dukda wahalar dani datake, I know haushi kikeji yanzu haka da kike karantawa amma that's it, that's the truth*

*nasan bankai matsayin inyi soyayya dake ba zee and that's why nake 6oyewa*

*kullum qoqari nake wajen danne zuciyata akanki, kullum qoqarin controlling emotion dina nake akanki, kullum qoqarin pretending am ok nake while am not... Kinsan meyasa?*


"meyasa?" inji zee dake karanta text din acan bangaren ta

Ko minti daya ba'a qaraba wani text din yashigo

*Because I don’t want to loose you*


*banason narasaki a matsayin qawa agareni, banason ki juyamun baya, idan kikayi Hakan zan shiga matsanancin damuwa, it will break my heart more than your expectation*

*please don't leave*

*pretend as if Hakan be faru ba*

*Kiyi pretending kamar ban fadamiki Hakan ba, please*

*muci gaba da abotarmu kamar komai be faruba*

*pleaseeee🙏*


"shashasha aini abinda kafada din nakeso amma saboda kana maloho kaqi ganewa, mtcheew" tafada ita kadai cikin jin haushi

Wai tayi pretending kamar bece komai ba, tayaya? Bayan abinda ta shafe lokaci mai tsawo kenan tana jira, mtcheew


Kashe wayar tasakeyi don yafara bata haushi, wai maimakon ya cigaba da nacewa akan eh sonta yake no matter what amma wai shi burinshi ma ta manta da yafadi Hakan saboda wata banzar abota

"Aboto! Nabi abota da gudu, idiot"

Takoma ta jingina da frame din gado tareda lumshe idanu


Sai kuma ta tuna yadda ya rikicemata jiya don ta ambaci wani da boy friend

*damn it!*

*Oh my God, For heaven's sake kibar kiranshi da haka*


Wani kayattacen murmushi ya su6uce mata ta lumshe idanu ta sake budesu


*I.. Love... You*
Maganarshi tasake dawo mata


Pillon kusada ita ta dauka ta rungume a qirjinta ta dora ha6arta akai tasake Lumshe idanu murmushi a fuskarta

Cikin sanyin murya tafara waqa :


_oh you what you did?_


_what you did to me?_

_it's a feel and it stole my heart away_

_mr deputy oh come to my aid_

_cos I don’t know how I got this way_


Wurgar da pillon tayi ta tashi tsaye kan gadon ta zare ribbon din kanta ta girgiza kanta gashinta duk suka barbaje ta cigaba da waqar tana rawa

_the thing dey do me tininny🤩_

_this kind love is amazing 😍_

_boy you let me feel everyday like am abiding_

_I can't deny am feeling it💃_

_I wanna call you baby🥰_

_baby.. Butterfly🦋🦋_

_boy you give me butterfly🧚🏻‍♀️_


_you be thief.. I know sey you be thief oh💃_

_and you know sey.. You don steal my heart oh❤️_

_you be thief... I know sey you be thief oh💃_

_oh boy you get my.._

_you get my heart away... You be thief💃_
(waqar simi ~you be thief~)


Murnar daya kamata tayi Tundazu takeyi yanzu

Tsalle kawai take kan gadon tana wurwurga gashinta tako ina tana cigaba da waqar

Jin zuciyarta take wasai babu kingin damuwa ko kadan saima farincikin daya maye gurbin damuwar


Murnar datake hasaso ma kanta zatayi a irin wannan ranar saigashi tanayin finshi

Saukowa tayi daga kan gadon tafara stripping kayanta still tana rawar waqar datakeyi

Saida ya rage saura bra da pant sannan ta jawo towel ta daura ta nufi toilet still tana lalauyewa kamar macijiya, gashin kan nan yayi kaca duk sun zubomata a fuska


Tana shiga ta cire towel din ta wurgar ta ida stripping sannan ta tsaya qasan shower ta sakarma kanta ruwa

Runtse idanu tayi tana jin saukar ruwan bisa kanta

Dago kanta tayi ta tara fuskarta a ruwan tana murmushi ruwan na dukkan fuskarta


_*ina sonki zee*_


_*na dade ina dakon soyayyarki soyayyar a zuciyata*_

Qara fadada murmushinta tayi tana zaro halshe ruwan shower din na dukanshi


Farinciki takeji kamar tayi hauka, bazata iya musalta yadda takeji ba don duk yadda zata musalta mai karatu bazai gane ba don gane irin wannan sai wanda ya ta6a tsintar kanshi a halin datake aciki


Yayinda zee a bangarenta take celebrating shikuma Deen a bangarenshi yana can zuciya a cinkushe


Ranar haka ya qarasa Wunin a sanyaye, da daddare ma haka ya kwanta yayi barci rabi da rabi sai yawan farkawa dayake yaga ko gari ya waye sai yaga still darene

Daren ranar yazamo mashi Mafi tsayin dare don bemashi gudu kwata2, sai gab da asuba sannan barci na sosai da sosai ya daukeshi


*WASHEGARI*


Yau safkon zuwa school yayi da 8:00am dukda beda lecture ma kwata2 ranar


Bayada burin daya wuce yaga zee yakuma san matsayinshi a wajen ta yanzu don da Hakan ya wuni jiya ya kwana


Aikau yasha jira don zee bata shigo school din ba sai wajajen 12pm


Yana zaune kan dakalin office dinnan dake facing din gate ya qurawa hanyar Shigowa ido kawai kamar a mafarki yaga shigowar motar ta


Wani dadi ya ziyarci zuciyarshi har yana Sakin wani qayattacen murmushi

Tashi tsaye yayi yana kallon motar data tsaya zuciyarshi na racing


Bala yaga yafito ya zagayo side din da zee take sannan ya bude mata kofa


Kafe ta inda zata fito Deen yayi ko kyaftawa babu

Ahankali ta zuro kafarta dake sanye da farin takalmi mai dan tudu sannan gangar jikin suka biyo baya


Lumshe idanu yayi ya bude akanta yana jin wani sabon shauqin sonta na huhhuda zuciyarshi takoina


Sanye take cikin farar arabian gown mai adon stones masu walwali agaba ta yane kanta irinna larabawan nan, fuskarta tayi fess sai sheqin makeup take

Rataya white side bag dinta tayi sannan ta sallami bala tafara tafiya


Sosai Deen ya shagala da kallonta don sosai shigar fararen kayi ya hauta


Ganin takusan qarasowa ta inda yake yasashi shima tahowa wajenta


"Zainab.."

Dan kallonshi tayi ta kauda kai ta cigaba da tafiyarta

"Zainab please let me explain, please"

"shiyasa nazo ai, but not here" tafada tana qara dan kallonshi sannan tayi gaba shima ya maramata baya


Library ta nufa Hakan yasashi shima Binta kamar raqumi da akala


Koda suka shiga shi yayi saurin jamata kujera don ta zauna

Dan kallonshi tayi sai kuma tadan kauda kai tana dan murmushi sannan ta zauna shima yaja mai facing dinta ya zauna sai Wurin ya dauki shiru


Ganin shirun yafara yawa gashi ita ko ajikinta don danne dannen waya takeyi ma hankalinta Kwance

Hakan yasa ya hadiye wasu yawu sannan ya bude baki yace
"Zainab, please let me explain everything to you"


Sai a sannan ta dago ta kalleshi sai taga yanayin fargaba a tattare da fuskar, fargabar kar ya rasata, irin fargabar datasha shiga a kwanakin baya
Murmushi tayi a zuciyarta tana cewa
_sha kuruminka dan saurayina, ni takace kai kadai_


A zahiri kuma ta ajiye wayar ta koma jikin kujera ta rungume hannuwa a qirji tace
"inaji"


Ajiyar zuciya ya sauke saikuma ya rasa ta inda zai fara

Saida yaqama kame kamenshi sannan ya fara cewa

"Zainab, I don’t know when it started amma inaji ajikina a lokacin da na jefaki a chakwali ne"


"bayan incident din sai mutane sukaita zuwa wajena suna yabona akan jefaki danayi a ta6o dukda kuwa ina gayamasu bada gangan bane amma sai suce su ai Hakan yayi musu daidai sunata maganganu marar dadi akanki"


"da farko ban dauki abin wani serious ba Amma ganin yadda mutane ke tururuwar zuwa ganin wanda ya jefaki a ta6o yabani mammaki kuma duk wanda zaiso kalmar allah kara yake furtawa dakuma bayyana dadin da abin yayi musu


Anan ne nafara tunani, nafara tunanin meyasa haka? Meyasa naga kamar duk basa sonki, kowa da kalar furucin da zaiyi akanki marar dadi, maimakon ayimiki jaje sai allah kara?

Sai naji kin bani tausayi, sai kuma naji ba dadi kasancewar nine silar Hakan

A ranar danaje na gayawa kaka saita cemun idan nazo school washegari nabaki hqr

Da qudurin Hakan nazo school din amma bakizo ba

Washegari ma haka, Washegari ma haka.

Sai naji banji dadi ba da tunanin qila nine silar rashin zuwanki din


Kwatsam ranar monday ina zaune ina karatu naganku kamar daga sama keda qawayenki

Na tashi ina kallonki ganin yadda kike bina dawani irin kallo, duk sai naji badadi don nasan dole kiji haushi na


Naso baki hqr a lokacin sainaga a matuqar fusace kike kuma kinqi bani damar magana sai tsawar da banso kike yimin Hakan yasa nafara gano dalilan dayasa mutane basa sonki, bakida kirki


Qawayenki sunyimin barazanar ko nazama errand boy dinki ko kisa akamani wai kawunki commander sojane uncle dinki kuma commissioner of police


A lokacin na yarda da Hakan ne ba don tsoro ba A'a sai don nabaki damar hucewa"


"qawayenki dama ke kanki kunamin kallon psycho nikuma saina biku ahaka dukdon mu rabu lafiya

A cikin kwanakin dakika maidani errand boy dinki da ida gano dalilan dayasa mutane basa sonki

Ranar da kika watsamin coke kuma ya ida tabbatar min da bakida kirki


Amma kuma saina kasa gayawa kaka ainahin abinda yafaru kawai nabar abin a matsayin tsautsayi nakuma yi alqawarin fita daga hanyarki gabadaya Saidai kuma a qasan zuciyata Koda yaushe kina fadomin a rai in dinga wondering ya kike, banji haushin abinda kika yimin ba a lokacin don ke kallon mahaukaci kikemin tayaya zaki yarda da abinda na rubuta? Saina maida laifin kaina saboda nasan da ban ta6a miki kayaba da duk Hakan be faru ba"


"saina yanke shawarar fita harkarki kwata2 wanda Hakan yasa Koda nadawo school nabar zama mazauni na nafara zaman library, nayi kwana uku da dawowa, Kwatsam sai gaki kin shigo library din kema

Naso intashi inbar wajen amma saina kasa sai naita kallon ki inajin wani feeling da bansan kona menene ba, inajin wata kewa taki wanda bansan dama inayi ba

Sai kema kika dago idanu muka hada ido Hakan yasa gabana yafadi

Sai naga kema kin kafeni da kallo Hakan yasani jin uneasiness saina tashi na fita

Bansan kin biyoni ba sai gani nayi ansha gabana

Gabana yasake faduwa saboda bansan dame kika zo dashi ba kuma a lokacin saboda nariga tayi entitled dinki a matsayin marar kirki

Amma jin kina bani hqr yayi matuqar bani mammaki

Ban ta6a zaton Hakan ba don nayi tunanin wata tijarar zakiyimin sai naga akasin haka, kika bani hqr kuma fuskarki ta nuna you're sorry din har cikin zuciyarki

Sai naji kin burgeni, saina qaryata daya daga cikin magangganun da mutane keyi akanki, Girman kai.

Saina qaryata Hakan don da kinada girman kai bazaki ta6a bani hqr ba

Saina hqr muka zauna muka fara magana, a lokacin kuma saina lura you are so simple don dukda a lokacin bansan ko ke wacece ba na fahimci ke yar manya ce amma kuma kika saki jikinki dani

Anan kika gayamin abinda ke tsakaninku da mr ibrahim

Tun anan Naso na nuna miki kuskurenki na gaba da malami amma kuma saina fasa saboda ba lallai bane ki fahimceni

Sainaji inason taimakonki a subject din don naga kamar kina fargabar faduwa sai nayi maki tayin Hakan kuma kika kar6a hannu bibbiyu, anan kuma naqara tabbatar da rashin girman kanki"

"ahankali ahankali naita fuskantar halayenki wanda sai nakusa dake kawai zai san su saina fuskanci kyawawan halayenki sunfi marasa kyan yawa

Daga baya kuma na fuskanci ashe rashin qawayen kirki yasa kike wasu abubbuwan ganin daga baki shawara akan gabarki da mr ibrahim kika nuna damuwarki kema akai kika kuma nuna kinason ku shirya, Hakan ya tabbatar min cewa eh daga qawayen ne don a dan lokacin damukayi tare naga kamar su babu ruwansu da karatu, they're not serious at all shiyasa nima na kawar da hankalinki daga kansu ta hanyar baki lokacina da gudunmawa gwargwadon ikona don ganin kinyi nasara"


Dakatawa yayi ya dago yana kallonta yaga itama shi take kallo babu ko kyaftawa

"Bansan sadda nafara sonki ba, abinda nasani shine kina burgeni amma bansan sadda Hakan ya rikide zuwa so ba.


Na fuskanci Hakan ne a zamanmu na asibiti, a lokacin nasan na kamu da makauniyar sonki, a lokacin da aka sallamemu Sainaji kamar Kada a sallamemu kamar muyi ta zamanmu a asibitin muddin zaki dinga zuwa sau biyun nan ina ganin ki, ranar da aka sallamemu sosai jikina yayi sanyi, najini so empty kamar wanda kika tafi mashi da wani abu mai matuqar muhinmmanci...."


Cigaba yayi da bata labarin yadda yayi missing dinta kamar yadda nakawo a last page har kawo ranar datazo gidansu da yadda beji dadin yanayin datazo dashi ba da kuma fasa niyyar amsar number ta dayayi, ya gangaro zuwa kiran dayasa kaka taita yiwa mummy don yaji muryarta har zuwa lokacin da akace tayi tafiya har zuwa lokacin resuming dinsu da abinda yafaru har zuwa kawo yanzu dasuke zaune.


Shiru yadanyi saikuma ya saki Ajiyar zuciya

"Zainab, am not begging love From you, nasan bazan ta6a samuba saboda bankai matsayin Hakan ba, Kiyi hqr naci amanar abota, kin riqeni a matsayin aboki nikuma na chanza tawa manufar gareki"

"meyasa kake ganin bakakai matsayin ba?" inji zee karo na farko tunda suka zauna

"saboda ta koina akwai banbanci atsakanina dake"

"meye banbancin?" inji zee again

"zee, ke diyar masu kudi ce, you're born with a sliver spoon in your mouth, nifa?"

Dan murmushi tayi sai ta kada kai tace
"bayan wannan fa?"

Shiru yayi yana tunani saikuma yace
"family, kinada families masu sonki sosai, nifa? Kaka ce kawai"

"kakan ba family bace? Kaka kawai ce? Soyayyar kaka ba soyayya bace?"

Shiru yayi yana kallonta

Ajiyar zuciya ta sauke tace
"tunda muka zauna nan kake fadamin dalilan dayasa kafara sona mun dauki kusan 30mins kana lissafosu dakuma bayyana yadda kakeji aranka game dani amma dakazo akan dalilan da zaisa ka haqura dani sai naga ko minti daya bakayi ba, hasalima duka dalilai ne guda biyu kacal, marassa tushe"

Shiru yayi still yana kallonta batareda ya iya cewa komai ba

"miye banbanci na dakai? Meye banbancin mai kudi da talaka, atsakaninmu mu yan Adam ke akwai banbanci amma a wajen Allah fa?"

Girgiza kai yayi sannan ahankali yace
"babu... Sai wanda yafi tsoron allah"

Murmushi tayi sannan tace
"families kuma, dama kasan wasu families dinane banida labari? A tunanina mummy da daddy kawai ka sani koko don kai bakadasu kake jin kamar bakadasu? Daga sama ka fado? Kaima dole kanada baba da mama kuma sun rasu, ba Haka kaceba?

Yakuma za'ayi kace bakadasu? Ina kaka? Ita ba family bace? Ko bata kai matsayin a kirata da Hakan ba?"

Shiru yayi nan ma yana jin zuciyarshi na wani iri

"soyayya babu ruwanta da mai kudi, marar kudi, mai kyau, marar kyau, yare, qabila, addini... Babu ruwanta

Makauniyace, marar dan jagora duk abinda tasamu kaimashi wafta take ta damqe gamm

Mai so na asali bazaiyi fargaba akan banbancin komai ba tsakaninshi da abinda yake so zai soshi ne yakuma tsaya tsayin daka akan Hakan no matter what

Amma tunda abotarmu ne bakason ya wargaje, fine mu tafi a Hakan, Abokai" tafada tana murmushi

Saita fara yunqurin tashi, saurin rigarta tashi yayi yana cewa

"yes, yes nagane, nagane Hakan Zainab, I was so stupid to think of that, a lokacin babu abinda nake hasasowa idan na tunkareki sai rabuwa, rabuwa na har abada kuma Hakan shine abu na qarshe da zanso yafaru damu because... I LOVE YOU"

Dagowa tayi tana kallonshi

"yes I love you, I love you! I love you!! Please give me a chance, give me a space no matter how tiny it is in your heart, please love me back, give me a chance... Please"


Tunda yafara take kallonshi babu kyaftawa tanajin zuciyarta na kumburi don shauqi

Kallon pleading face dinshi tayi data koma abin tausayi saita miqe ta dauki jakkarta da wayarta ta rataye jakkar

Binta da kallo yayi tayi zuciyarshi na bugawa da qarfin gaske

Dagowa tayi ta kalleshi taga shima ita yake kallo babu kyaftawa

"idan ban baka space ba a zuciyar tawa fa?"

"zan roqi kibani dama nayi jaraba kutsawa har nasamu nasarar yin Hakan watarana" yafada ahankali

"idan nabaka kuma fa?"

"zanfi kowa farinciki a duniya" yafada still yana kallonta zuciyarshi kuma bata bar bugu ba


Wani kayattacen murmushi tayi sannan tace
"Go ahead, kafi kowa farinciki a duniya"

Saita juya ta nufi hanyar fita

Dan yamutsa fuska yayi cikin rashin fahimta

Yafi kowa farinciki kuma?

Wani abu ya gifta mashi a qwalwa

Yace zaifi kowa farinciki a duniya idan ta amince dashi
Kuma tace yafi kowa farincikin

Kenan?

Ta amince?

Dagowa yayi saurin yi saigani yayi harta fice

"OMG! Ta amince! Ta amince!!!"... ✍️


Ummin fasihu 🧚🏻‍♀�
8/2/21, 9:37 PM - Buhainat😝: *🙍🏻‍♂️DEEN 🙍🏻‍♂�*


*042*


*DEEZEEN💞*


Saurin tashi yayi ya fita Saidai ya waiga ta koina babu ita.

Duba agogon hannunshi yayi sai yaga har 1pm ta dan gota kuma dama tanada lecture qarfe 1


Murmushi yayi ya saka hannu yana dan yamutsa gashin kanshi ya nufi hanyar department dinsu.


Tun daga nesa ya hango alamun class din karatu ake amma dukda Hakan be hqr ba ya zagaya ta dayan side din class din yafara bin bango ahankali kamar wani qwararren dan F 😒


Koda yazo wajen window saiya leqo ta gefe ahankali yana scanning din iya inda yake iya hangowa amma be ga ko wulginta ba


Hakan yasashi yin qasa ya rarrafa don kar aganshi ta window yawuce dayan windown sannan ya miqe ahankali ya jingina da bango yasake leqawa ahankali ta gefen windown


Qara bin iya inda zai iya gani da ido amma be ganta ba


Har zai qara gaba sai kuma yaga windown gaba ai na masu zama baya ne kuma ya tabbata Zainab bata zama baya

Hakan yasa yaqara dan leqawa yana dan wurwurga idanu ta koina

Saikau gashi ya ganta a row din tsakiya zaune Littafi kan desk dinta ta buga tagumi da hannu daya tana taunar gindin biron hannunta hankalinta akan lecturer din

Murmushi ne ya su6uce mashi saiya qara gyara tsayuwa yana cigaba da leqenta


Jin wannan feeling din tayi wanda takeji idan yana kallonta Saidai bata wani maida hankali akai ba don tasan bayanan


Tunani tayi ko ya gane hausarta dazu? Sai kuma tayi murmushi tana cigaba da taunar biron hannunta, allah yasani yau tana cikin farinciki, farinciki marar musaltawa


Kamar ance ta waigo ta windown gefen damarta sai taga kamar abu na leqowa yana komawa

Hakan yasa ta kurawa wajen ido

Shikuma ganin ta kallo wajen yasashi dan qara leqowa sosai yadda zata ganshi


Wara idanu tayi ganin shine sai kuma tayi saurin kauda kai tana kallon lecturern dake koyar dasu

Lallai ma Deen, baya tsoron ko aganshi ma?
Tambayar da tayiwa kanta kenan


Haka aka cigaba da lecture din rabin hankalinta akan lecturer rabi kuma akan Deen


Duk lokacin da zata juyo ta kalloshi sai taga yamata murmushi ya daga mata hannu saita kauda kai kuma


Ahaka har lecture din ya qare lecturern ya fita


Ganin Hakan yasashi zagayowa da sauri shima don tarbonta

Zee daketa sauri ta fito itama taci karo dashi a waje

"har kun gama?" yafada yana qarasowa yana mata murmushi

Murmushi kawai itama tayi mashi tana lura da yadda wasu ke kallonsu

"kai zan tambaya, harka gama la6en?" tafada tana nufar hanyar fita

Shima Binta yayi suka jera yana cewa
"eh, amma fa nasha wuya, bayana ciwo" yafada yana 6ata rai

Ta6e baki zee data kasa hada ido dashi tun dazu tayi tace
"dakyau"

"hakama zakice?" yafada yana marairaicewa

Murmushi kawai tayi ta kauda kai, shi bemasan kunyarshi take jiba

Tare suka nufi masjid don har ankusan kabbarawa

Kowa nashi nashen yayi, basu dade da shiga ba aka tada iqama


Kusan tare suka fito don Deen na fitowa itama tana fitowa


Tare sukaje cafteria sukayi siyayyar abinda zasu dan ci kowa daidai aljihunshi sannan suka wuce usual Wurin zamansu idan basa library


Zama sukayi Deen yafara bude masu ledar chips dinshi suka shiga ci tare


Shiru wajen ya dauka na wani lokaci bakajin komai sai sanyayar iska dake kadawa sai kukan tsintsaye dake kai kawo

Deen daga kai yayi yana kallon wasu balbelu dasuka zo suka wuce ta gabansu

"look" yafada yana nuna mata da yatsa

Bïñsu da kallo itama tayi

"suna tayamu murna suma" yafada yana murmushi

Itama saita tsinci kanta da murmusawa

"the birds are also singing, suma suna tayamu murna... Kalli can"

Bïñ inda ya nuna tayi da kallo sai taga yan moli moli ne guda biyu mace da namiji bisa kan wani reshen bishiya

"A good example of us, right?" yafada yana kallonsu yana murmushi

Itama su take kallo fuskarta dauke da murmushi, ahankali tace
"so beautiful"

"yes, love is beautiful and amazing" yafada sannan ya maido kallonshi akanta Hakan itama yasa ta juyo tana kallonshi shima


"Nagode Zainab, Nagode da kika bani damar jan ragamar zuciyarki, I promised you bazaki ta6a danasaniba. Zan jagora agareki, jagora dazai jagoranceki zuwa duniyar farinciki, zan iya sadaukar da komai akanki zee na, komai"

"promise" inji zee ahankali

"promise you'll never let me down, no matter what" tafada tana kallonshi tanajin hawaye na neman taruwa a idanunta

Kama hannunta yayi cikin nashi ya matse
"nayi, nayi alqawari my zee, I'll never let you down insha allah don letting you down is equal to letting myself down, down to grave"

" If I could chose between loving you and breathing I would use my last breathe to say I LOVE YOU." Sai kuma yayi interlocking din yatsunshi da nata ya dago hannun yana kallo

Itama kallonsu tayi dukda tasan be dace ba Amma takasa hanashi

Murmushi yayi ya kalleta, itama shi ta kalla not saying anything

"yanzu nagane dalilin space dake a tsakanin yatsu na da naki

Anyisu ne don yatsunmu su maye gurbinsu, kamar haka" yafada yana dan daga hannayen nasu


Murmushi tayi sosai tanajin wani dadi na ratsa zuciyarta, Gaskiya soyayya dadi gareta musanmman kaso aka soka, wayyo dadi 😍


Zame yatsunta tayi daga nashi ta duqa zata dauki juice din gabanta

Saurin riganta yayi ya dauko mata ya miqamata

"ki dinga fadamin duk abinda kike so idan ina kusa, kibar wahalar da kanki, feel free wajen sakani komai, dama ni errand boy dinki ne"

Murmushi tayi kawai ta amsa ta dan kur6a don harya bude mata


Haka sukaita zama wajen Deen nata tarairayarta, wasu abubbuwan ma har mammaki yake bata don batasan ya sansu ba, a ganin ta babu abinda ya iya a faggen love, batasan yan shiru shiru dinnan akwai iya buga love🥰

Suna ahaka har drivernta yazo

Saida ya rakota har motar, kafin bala yama zagayo shi ya bude mata kofa, babu abinda ya dameshi ko lura da kallon da daidaikun mutane ke masu beyi ba

Shiga zee tayi ya sunkuya ya maida mata yar jelar rigarta da bata ida shigewa ba sannan ya rufo mata kofar ahankali

Bala daya saki baki yana kallon ikon allah ya lalla6a yakoma cikin motar gulma fall ranshi

Sunkuyowa yayi jikin glass din Hakan yasata wining din glass din qasa

Murmushi suka yima juna

"bye.. Ki kulamin da zuciyata"

Murmushi tayi sannan tace
"nima haka"

"kema me?"

Blushing tayi tana dauke kai tace
"yadda kace"

Murmushi yayi
"to shikenan, qila maganar ke miki wuya amma na gane ai, zan kula miki daita sosai and please.. A taimaka a daga wayata yau.. Please"

Kallonshi tayi taga yadda yawani marairaice

Murmushi kawai tayi tafara wining din glass din motar sama tace
"bye"

"bye.. Godiya nake"

Jin an tada motar yasa yadanja da baya yana kallonta dukda baya hangenta amma yasan itama shi take kallo

Ganin xa'aja motar yasashi fara daga mata hannu yana murmushi har motar ta daga ta nufi hanyar gate

Bebar daga hannun ba har Saida suka fita daga school din

Ajiyar zuciya ya sauke yana jin zuciyarshi sakwat kamar an rabashi da wani mai nauyi aka, tabbas ya yarda zee ce farincikinshi kuma idan yana tareda ita zaiji dadi da sallamar zuciya da ruhi.


Ajiyar zuciya itama zee tayi sai takoma jikin kujerar motar ta lafe tana murmushi, murmushin dayaqi barin fuskarta tun jiya


Wani irin dadi takeji marar musaltawa, she can't believe yau ita Deen ke furtawa kalaman soyayya, she can't believe yanzu Deen natane

Dama kenan shima yana sonta tuntuni shine baya gwadawa kwata2? Kai amma ya gama daita, duk wannan sleepless nights din da damuwa ashe wanda takeyi don shi shima tana can a ranshi? Dakau tasan da Hakan da ba zata ta6a damun kanta ba irin haka, amma nevertheless yanzu ma alhamdullilah, ta godewa allah daya kawomata abin da sauqi, dama wannan itace babbar matsalar wato kaso aqi sonka amma muddin soyayyar ta kowacce bangare ce to duk abinda zai biyo baya mai sauqi ne.


Ahankali ta dago hannunta tana kallo

_*yanzu nagane dalilin space dake tsakanin yatsu na da naki*_


_*anyisu ne don yatsunmu su maye gurbinsu, kamar haka*_

Murmushi tayi tareda runtse hannun ta lumshe idanunta cikin jindadi


A bangaren Deen ma bata dade da tafiya ba shima yafito feeling himself on top of the world

Be dade ba yasamu abin hawa suma suka shilla


Koda ya dawo gida kaka tayi mammaki sosai ganin yadda kai kawo cikin nishadi, murmushi yaqi barin fuskarshi sa6anin dasafe daya fita kamar yayi kuka yana komai sumi sumi

Koda ta tambayeshi lfy? Ko tsintuwa yayi? Sai yakama Dariya kawai yana cewa eh tsintuwa yayi, a zuciyarshi kuma yace *Tsintuwar soyayya ba*


Haka wadannan bayin allahn suka qarasa Wunin su cikin nishadi da annushuwa kowanne Saida aka ganemashi a gida don fara'ar yau ta dabance


💖 💖 💖 💖 💖 💖 💖 💖


"wow! Wow!! Wow!! Dole na kwaso shokiii💃💃💃" inji saqon Feenah via whatsapp


Dariya zee tayi afili sannan tayi typing
"kai Aunty, yaushe kika zama motar yansanda?😆"


"har tarakta ma ina iya zama, wayyo dadi 💃 amma na tayaki murna 🥰"


Murmushi zee tayi sannan tace

"thanks Aunty 😍"

"shikenan kuka yaqare ko 😏"


"dama wani ke kuka 🤨"


"qaniyarki, shegiya kin manta lokacin da kike kuka hawaye da majina kina wlh Aunty idan be soni ba mutuwa zanyi😩 yar rainin hankali kawai 😒"


"😳kai Aunty yaushe akayi haka? Wlh adai dinga tsoron allah 😫"


"kyaji dashi... Yanzu shikenan harkin amince? Bawani jan aji ba komai?😒"


"shi ajin wani kalan abinci ne 🙄"


"😦 kinci bashi yarinya 😠"

"babu komai na biya idan muka hadu😜 ina alarrama yaya Auwal?"

"waya bashi muqamin alarramancin 😒"

"ai basai anbashi ba, alarrama ne 😆 alarrama ango ba🤣🤣"

"kutt! Ni tsarar wasanki ce 😬"

"😝😝😝"


"zaki gane bakida wayau ne 😠"


"👏👏tuba nake uwata ta kaina"


"zamu Hade ne zaki fadamin yaushe muka fara wasan jika da kaka dake 😠"


"haba Aunty ta ta kaina, ai babu mai jin kanmu insha allah🥰"


"😒😒ayi kema azo a aurar dake don naga wani tashen balaga kikeji kwanan nan"

"can't wait 😁💃💃"

"😳marar kunya?"


"🙈🙈🙈😄"


"😞Allah ya shirya"


"Amin summa amin Aunty ta 😜"


Kira taga ya shigo wayarta

*D❤️* taga ansa Hakan yasata dan murmusawa

Daidai nan message din Aunty Feenah yasake Shigowa

"ai yanzu tunda hankali ya kwanta dole ki nunama kowa kin qoshi"

Murmushi tayi sannan tayi saurin typing

"eh babu komai😜, Saida safe"

"tun yanzu?"

"shine yakira🙈"

"yar isss lamiya😒"

Dariya tayi ta kashe datarta lokacin har kiran ya tsinke amman nan take wani kiran ya shigo


Murmushi tayi Saida takusan tsinkewa sannan ta daga, saita tsinci kanta da kashe murya wajen yin sallama

Wata nannauyar Ajiyar zuciya Deen ya sauke daga dayan bangaren sannan ya amsa sallamarta sannan ya dora da

"nayi tunanin har kinyi barci wlh"

Murmushi tayi
"kamar kaza?"

"who knows"

Murmushi tayi ta janyo pillow qirjinta ta rungume tace
"ina kaka ta?"

"tayi barci nasan takai kaduna yanzu"

Yar Dariya tayi tace
"bakada kirki, a gaban aminiyar tata kake fadin haka?"

"oh haka ne fa ashe ku aminan juna ne"


"sosai ma" inji zee

Murmushi taji yayi sannan yace

"banida lfy, ko ki kira kiji ya nake" ga yanayin dayayi magana tasan kumbura fuska yayi

Dan wara idanu tayi tace
"bakada lfy? Meke damunka?"

"kewa"

Dan daga gira tayi sannan tace
"kewa? Kewar wa?"

"Kewar wa? Banda ke"

Murmushi tayi
"duka yaushe muka rabu"

"duka yaushe ma zakice? Tunfa 3"

"3 din, duka awa nawa?"

"O'O! Kenan ni bakiyi missing dina ba" yafada a marairaice

Yar siririyar Dariya tayi tace
"nayi amma kadan"

"babu komai, what matters shine kinyi, zan taimaka miki nazo school gobe dawuri don ki ganni kiji sanyi a ranki" yafada cikin sigar tsokana

"wasa ma kenan, dani dakai wa zai ga wani yaji sanyi?"

"dani dake"

Sai sukayi Dariya atare


Hira suka shiga yi mai cikeda nishadi da raha

Sai gashi wasa wasa har sukafi mintuna talatin sai anan kudin Deen suka kare


Bugamashi zee tayi ita kuma don Saida firar ta dauko sugar katinshi ya qare

Sai gashi sune har 12 dare suna fira kwata2 sunma mance a wace duniyar suke kawai basa tunawa da kowa da komai sai kansu


Tun zee na iya qoqarin bude idanunta idan suna rurrufewa alamun barci har barcin ya saceta batareda ta farga ba


Jin saukar numfashinta yasashi sanin tayi barci Saidai kuma yaqi kashe wayar saima ya danna recording yana daukar saukar numfashi a zuciyarshi kuma yana hasasota tana barcin, yasan barci zai mata mugun kyau, zaiso ganinta idanunta Lumshe bata komai sai sauke numfashi ahankali, yasan sosai fuskarta zata qara Fiddo cuteness dinta


Katse kiran yayi ba don ya gaji ba sai don tunawa dayayi kudinta ne ke qonewa a banza


Koda ya katse kiran kasa barcin yayi sai juye juye yakeyi

Firarsu yake sake yin bitarshi a zuciyarshi yana jin wani shauqin sonta na qara fizgar zuciyarshi

Ahaka har shima barcin ya daukeshi batareda ya shirya ba.


❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️


Soyayya sukeyi tsaftattaciya wanda ya kunshi kulawa da tarairaya a kowanne bangare


Zee bata bar soyayyar ta zama boring ba ta hanyar yin dunkum, itama tana nuna mashi kulawa da soyayya tsantsa dukda ba wai rawar kai takeyi ba, komai tana yinshi ne stylishly da kuma class.


A school tun ana zargin soyayya suke har suka tabbatar da Hakan don a relationship dinsu babu batun wani 6oyo ko kunya, don wani lokacin ma zee ce ke dan jin kunya amma shi baya kunyar nuna mata kulawa a koma inane.


Duk inda kaga daya to dayan na wajen except idan daya yashiga class yabar dayan

Idan suna tafiya Deen ne ke Rataya jakkar zee ita kuma ta rungume littatafanshi

Da farko daya fara amsa jakkarta hanawa take don cewa take tayaya zai daukar mata jakka kamar wata mijin Hajiya

Amma nacinshi dakuma cewan dayake dama ai mijin hajiyan zai zama yasata dinga bashi itakuma saita amshi littatafanshi ta rungume


A fannin waya kau ba dama

Bata ta6a tunanin Deen ya iya waya ba sai a dan wannan lokacin don sa6anin da da idan sunyi gudun tsiya suyi wayar five minutes to yanzu wayar awanni suke kuma su rabu bawai don firar ta ishesu ba

Deen ke fara bugowa sai sun cinye katinshi sannan ita ta bugo su ida wayar.

A fannin text messages kau zee har tasan lokutan shigowar text dinshi a wayarta

Idan ta farka da asuba da text dinshi take fara tozali, idan ranar akwai school kafin ta fito sai yayimata na fatan isowa lfy, idan kuma suka rabu daga school saiya daidaici sun isa gida zai mata na fatan sauka lfy, da daddare ma haka


Itama tana yimashi Saidai ba kamar nashi ba barkatai, tana yimashi daya kowacce safiya, sai ranar juma'a kuma tayimashi na barka da juma'a bayan an taso daga sallar juma'a


Zee bata yarda da yin dunkum ba a soyayya kamar yadda Mafi yawan yanmata keyi

Idan be kira ba ita tana kiranshi, idan suna fira tana co-operating itama batayi mashi shiru Daga eh sai A'a sai hmm

Tana Sakin jiki suyi labari na raha Saidai kuma tana matuqar kama kanta sosai wajen ganin bata bar wata 6araka tashigo a soyayyarsu ba


Akwana a tashi saigashi bikin Feenah sai qara matsowa yake, kowanne bangare an shiga hidima ka'in da na'in


Amarya sai shan gyara take ciki da bai taqara fitowa tass fess kamar ka wanke hannu kafin ka ta6ata


Mummy da zee sai biki saura kwana hudu suka wuce Ruma


Anan zee taita santin kyaun da Feenah tayi tana tsokanarta da itama wacce tayi mata gyaran zatamata itakuma saita hau masifar ta rainata ta maidata kakarta


Bikin ba'ayi wani bidi'a ba sai dinner daza'ayi ranar daurin aure da daddare


Washegarin ranar da suka isa zee da qawayen Feenah data shige cikinsu tsamo tsamo dukda duk sun girme mata suka wuce saloon

Idan ka ganta cikinsu sai kayi zaton tsararraki ne don kusan babu mai girman jiki sosai cikinsu gashi ta iya mu'amalla da mutane musanmman yan gayu irinta shiyasa suma suka jiki sosai daita don tun a ganin farko yanayinta da gayunta yayi musu


Daga saloon suka wuce shopping bags da shoes dazasuyi amfani dashi da yan abubbuwan da ba'a rasaba.

Daga nan suka dawo gida

Ranar daren biki kuma masu qunshi sukazo gidan inda aka yini ana yin qunshi, ita amarya dama mai qunshinta ta musanmman ce don ita kadai dama zatayi mawa


Haka aka xauna a garejin gidan kasancewar yanada girma sosai aka baje anama amarya da qawayen amarya qunshi sai fira ake ana shewa na irin wayyayun mata

Qawayen Feenah kau sai tsiya suke mata ganin yadda Auwal ya addabeta da kira, bini bini sai ya kira Hakan yasa wata qawarta ta amshe wayar daya sake bugowa cikin barkwanci tace allah idan yasake damunsu saisu fasa bashi amaryar su riqe abinsu

Dariya yayi yana cewa tuba yake kanshi abisa wuya, idan suka hanashi ita ai Hakan daidai yake da hanashi numfashin shaqa, ya tuba bazai qara ba sannan yace to don Allah abata yaqara jin muryarta yayi alqawarin daga wannan bazai qara takura musu ba

Dariya dik sukayi sannan qawar tata ta karama Feenah da duk ke jinsu wayar a kunne kasancewar hannunta duk qunshi ne

Suka danyi magana wanda babu wanda yaji abinda suke cewa Saidai dariyar datake ahankali sannan sukayi sallama ya katse kiran

Zee daga inda take zaune ana zana mata na qafa jaa take kallon dramarsu cikin burgewa

Sai yanzu taqara gano hikimar Feenah na amincewa da Auwal don ko yanzu ka santa dashi to saika lura da tsananin so da kulawar dayake nunamata kuma tana ji ajikinta insha allah zata soshi don yana kyautata mata kuma zuciya kowacce iri ce tana tsananin qauna da ganin girman mai kyautata mata


Hakan yasa ta tuna da Deen dinta, basu dade da gama waya ba yana complaining shi ta tafi tabar shi cikin kewarta tana mashi Dariya akan cewa ba gobe zaizo ba (dayake ta gayacceshi daurin aure, Aunty Feenah da kanta tabada katin I.v din abashi don tsakani da allah mutumin yayi mata kuma muddin kaji Feenah ta yabi abu to karka bincika abin yayi 💯)
Dakyar tasamu sukayi sallama bayan ta fadamashi qunshi za'ayi mata


Basu suka gama qunshin ba gabadaya sai can da marece liss kowanne sai santin nashi qunshin yake don ba qarya masu qunshin qwararru ne


*WASHEGARI*


Rana bata qarya... 💃

Yau su Hajiya Feenah za'a amarce

Gida ya cika maqil ya cinkushe takoina, duk wanda zaka gani is very busy musanmman su mummy da matan kawunnan zee.


Su Umma ana bedroom dinta an qame bisa gado tasha dakakkiyar shaddarta dataji aiki ajiki ga daurin dan kwalin da zee ta dotsana mata mai kyau, anci gayu ansha lalle tsohuwa ta fada kwata, kukau bikin auta guda? 😆


A bangaren Amarya kau tana dakinta dake cike da qawayenta da yanuwa yanmata


Kowa sai shiri yake don an kusan daura auren

Amarya ana gefen gado taci kwalliyarta itama cikin ankon bikinta, fuskar nan tasha makeup ga wani dauri mai shegen kyau da aka murzamata sai hasketa masu daukarta hotuna keyi da flasher.


Zee ce tashigo dakin cikin hijab iya gwiwa sai daurin gaba datayi da zane aciki wanda ana iya hango zanen ta qasan hijab

Fuskarta da hannayenta duk a jiqe suke da alama daga wanka tafito

"wai ke ina kika shiga Tundazu kinbar waya anata kira?" inji wata cousin dinta

Qarasowa tayi tana yamutsa fuska
"wanka najeyi part din Aunty Raliya I can't use toilet din dakinnan"

Harararta yarinyar tayi tana cewa
"sannu tsafttatu, nidai dalla amshi abinki an wani cika mana kunne da kira"

Itama Harararta tayi sannan ta amsa tana cewa
"waye?"

"saiki duba ai da kanki" inji yarinyar tana kauda kai ta maida gasu Feenah dake can suna dimi bama susan abinda suke ba


*D❤️* tagani


Murmushi tayi sannan ta juya tafita daga dakin saboda hayaniya ta zagaya can bayan gidan inda babu hayaniya sosai tayi dialing number


Ringing biyu aka daga amma sai akayi shiru

"Baiby.." tafada cikin sigar tsokana


"babu wani nan, don't baby me mun 6ata"

Dan wara idanu tayi murmushi a fuskarta

"6atawa? Meyasa?"


"kinsan kira nawa nayimiki?"

"yakai dari?" ta Tambaya cikin sigar jan fada


"Haka ma zakice?"


Dariya kawai tayi

"mun sake 6atawa, hang the phone banason yin wayar dake kuma"

Dariya tasake yi tace
"kai kayi hanging din mana"

"ai ke kika kira ke ya kamata Kiyi hanging up"

"then we die here"

Dariya sukayi gabadaya

"gist me, kun taho?"

"yanzu muka gama Gaisawa da suruki na"

"suruki kuma?"


"yes, ashe zai iya ganeni? Rabonmu da juna tun hospital kafin a sallameni amma tsaf ya ganeni, muka gaisa amma naji kunya 🙈"


"wow! Nufinka har kun qaraso?" tafada cikin doki

"yes? Gashi nanma ana shirin daura aure" injishi


"wow! Ashe dai kakar tabari"

"zauna nan... Bari in katse gashinan za'a fara"

"na bari... Tare zaka biyo su daddy ku dawo nan?"

"tambaya ma kike? Me zan tsaya yi acan?"


"tsayawa Wurin anguna"

"meye kuma anguna? Dama shi ya kawoni? I came to see my missing princess"


Zatayi magana ya sake katseta da
"gashi nan za'a fara, bye.. See you"

Kittt.. Ya katse kiran


Ajiyar zuciya tayi tana rollling manyan idanunta sannan tayi hanyar cikin gidan da sauri don shiryawa


Koda tashigo dakin saita tararda anama Feenah wani daurin dan kwalin don harta chanza kaya zuwa wani royal blue materials

Bata tsaya wani kalle kalle ba tawuce bude wardrobe din Feenah taciro kayanta dake cikin leda tafice daga dakin again
Chapter 3 · 0% Book details