Sashe 2
Dauke Dai Dai Duniyar Shaidanu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Fitowa sukayi Suna nufar dajin datake Wayoyinsu da Computer suka d'auke komai ya daina Halbawa,
Cikin mamaki Samir Yace"kunga Computer tadaina Aiki hakan Yana Nuna muna cewa Cewa inda zamu shiga ba Network duk wani Sadarwa baya Aiki wurin,"
"Yaya zamuyi kenan tinda kusan computer itace d'auke da Abun komawar my dama zuwan namu," Cewar Sam
Taj Yace"Saidai mu d'auke duk wani Abu da zamu iya, Sai kuma muyi Amfani da Taswirar takarda, Yanzu Aikinka zai fara Emanuel"
Cikin Isa da hura Hanci Yafito tsakiyar su Yace, Kowa Yacika wannan cakar da makaman domin kariya wa kansa tinda motar Bata shiga ciki, sannan wannan zagaye nane so dole kumin biyayya," Yana gama Fad'ar Hakan Yafara lodar nasa makaman A jaka, ganin haka yasa kowa Yafara d'iba,
Tsaki Sam tayi Tace"dube shi kamar wani Birin har yake Fad'in Dole A masa biyayya Mtssswwww"
"Rabuda banza dama ni haushi yake ban wallahi," Cewar jidda
Murmushi Samir yayi"Kunga ku manta dashi kawai muje mud'iba Muma,"
Kowa ya d'auke Abunda zai iya Koda na lek'a motar Naga sun kwashe makaman dukan ko wanne d'auke da k'atuwar jaka A bayansa Hannuwansu kuwa d'auke da manyan bindigoginsu Suka nausa cikin dajin, Emanuel ne gaba sai Samir, Taj, Sam, jidda sai sauran tawagar tasu ko wanne rik'e da bindiga Kuma A shirye Koda wani Abu zai taso musu,
Sunyi nisa sosai domin sunshiga tsakar dajin ba Abunda Suka gani, bakajin komai sai sautin kukan wasu tsuntsaye Yan tsiraru, ga manya manyan itace dogaye Wad'an da suka ma dajin k'awanya,
Kwatsam sukaji wani irin gurnani na fitowa ta gefensu Yana nufosu,
Cikin tsorata Suka tsaya can bisa d'aga hannu da Emanuel yayi yana wurwurga idanuwa Dan ganin meke Shirin kawo musu far maki,.
Kamar daga sama saiga wani gabjejen Zaki Ya fito, Wanda Sam baida shawar kallo, sau d'aya zaka kalleshi kasan lalle bawai iya zakin gaske wanda Suka sani bane, Dole wannan SHAID'ANIN ALJANINE Yadawo zaki,
Tsaye yayi yana k'ura musu idanuwansa wad'an da jajir suke hak'uransa Zara Zara masu tsinin gaske, Wani irin Gurnani yayi Wanda Saida dajin Ya Ansa gaba d'aya, kansu Ankara Wasu shirga shirgan zakuna kamar sa suka bayyana bayansa,
Tsorata Iya tsorata sun tsorata domin wasu har sun ja baya,
Cikin rawar muryar Sam tace"Bana tinanin bindiga zata iya Kub'utar da rayukan mu dole mu k'ara da takubba,"
Maida bindigar Samir da Sam sukayi zuwa Taj jidda kuwa iya bindigar kawai zata iya rik'awa,
Ganin hakan yasa SHAID'ANUN ZAKUNAN suka fad'a musu da mugun nufi.......................
Wai koya zata kasance??
Kubiyoni next page Masoyana....
*BASEERATA ITACE ARZIKINA😍*
WhatsApp number 07064904617 or 07031012948
*D'AUKE D'AI D'AI DUNIYAR SHAID'ANU🧟♀️☠️☠️💀💀*
_PAID BOOK #300 ONLY_
_RUBUTA LABARI DA TSARAWA MUJAHEEDAH MATAR MLM AMMYN KHAUSAR 🤱..._
```MARUBUCIYAR... (1)Fahat hot-luv Free book, (2) Barrister khalee Free book, (3) Zuciyar namiji Free book, (4)Saina kashe mijina Free book, (5) Akan pre-wedding pictures free book, (6)Shagala Free book, (7) Silar d'a namiji Free book, (8) Maizaman kanta paid book, (9) Abbakar sarakeey paid book, (10) doctor Heesham paid book, (11) jinin Mulki paid book, (12) Bak'in kishi paid book, (13) Raunin macce baya hana d'aukar fansa free book. (14) ZAYYAN 💞 ZEEYAT PAID BOOK. (15) MAKARANTAR KWANA FREE BOOK. (16) SHAGALA FREE BOOK,, (17) SO SIRIRIN ZUCIYA..... And Other's BUT NOW (18) SAURAYINA.. (19)D.S.P ANNUR PAID BOOK....(20) SAKACINA PAID BOOK.... (21) SO!!! FREE BOOK... (22) FATALWAR ☠️ BUDURWAR MIJINA PAID BOOK... (23) D'AUKE D'AI D'AI DUNIYAR SHAID'ANU PAID BOOK
loading..... Dika na Mujaheedah Matar Mlm Ammyn khausar 🤱 QUEEN OF WRITER 📝```
_Alhamdulillah godiya ta tabbata ga Allah mad'aukakin sarki Mai bayarda baiwa gawanda yaso Kuma sanda yaso Ina godiya ga Allah Allah daya sake bani dama had'ida baseerar sake kawomuku sabon littafina maitaken_ *D'AUKE D'AI D'AI DUNIYAR SHAID'ANU🧟♀️☠️☠️💀💀👹👹 PAID BOOK #300 ONLY*
_Ina fatan yabada darussuka dama ilmantarwa Kamar dai yarda sauran littafaina suka bayar....._
*Free 🅿️ 11 to 15*
..........Cikin A zama Suka soma yima zakunan Ruwan wuta da bindigoginsu Amma Har suka iso nufosu ba wanda yasami nasarar samun Koda Zaki d'aya,
Suna Isowa Sukayi sufa Kan dakarun Sojojin take suka soma Hallaka duk wanda Sukayi nasarar fad'awa, Sojojin Ihun Wuya A zaba kawai suke zabgawa domin zakunan cikin zafin nama suke kaimusu Hari da Tsinin farantansu zuwa Hak'oran su, duk wanda suka Yaga da K'afar su kuwa tamkar Ansa Wuka Antsaga nama saidai kaga jini ya tsartu wanda Suka Sara ya zabga Ihu ya Fad'i k'asa, Idan kuwa Suka kaima mutum cizo to saidai ya zube matacce domin basu saki Saida wani sassan jikinsa Kuma su had'iye,
Samir kuwa fad'a yake da zakunan da tako binsa amma ko Rauni ya kasa musu Domin zafin Naman zakunan yawuce tinaninka Mai karatu, Sam kuwa Gajiya tafara saidai takare harin da zasu kawo Mata Amma takasa maida martani, jidda kuwa duk'e take k'asa kawai tana jiran mutuwar ta Domin tagama Sadaukarwa Akan yau mutuwa zatayi,
Emanuel kuwa ya dage sai har binsu Yake Yana ja baya Amma ya kasa nasarar Koda kashe d'aya domin Bak'in zafin nama ga zakunan tamkar takarda hake suke yawo Kan iska,
Kafin cikar Rabin sa'a take suka soma yima Sojojin b'arna Domin sunkashe Ak'alla 10 guda 20 kuwa Raunika sosai suka musu,
Wani Zakin ya nufo Jidda cikin son ya galgala namanta dawani irin gurnani, Koda taji sautin gurnanin Yana nufota tad'ago, Aikuwa sukayi Arba da idanuwan Zakin da saura kad'an ya cinmata Yana daf da samunta Yayi tsalle da niyar rabata da kanta Baki d'aya, ta rafka uban Ihu, hakan Yajanyo Hankalin Taj wurin ta, Cikin Bak'in A zababben gudu Wanda baisan Yana dashi ba ya falfala zuwa gareta tareda zabtarar wani icce, Zaki Yana sauka daniyar sauke mata Kai k'asa Taj ya isa gareta Ya d'aga Icce Ya zabgawa Zakin Aka,
Wani Firgitaccen ihu Zakin yasaki wanda ya janyo Hankalin kowa zuwa Nan hatta su kansu sauran zakunan Saida suka tsaya cak suna kallon irin kashin walak'ancin da Taj yayiwa Uban gayyar nasu, Zakin ya Fad'i k'asa kansa Ya tarwatse jini Yanata malama Ak'asan, Jidda kuwa tsabar mamaki dama kasada irin wadda Taj ya d'auka saboda ita yasa ta zuba masa ido bako kyaftawa,
Shikuwa baima lura da yanayin nataba Cikin d'aga murya Yace"Kansu shine lagonsu Ku Hanzarta halbin kawunansu da kukansu Aka," Yana rufe Baki kuwa sauran zakunan suka musu rufduku Aka sake kacamewa Da Bakin Artabo Wanda wannan karon zakunan ne ke bajewa kasa matattu,
D'ayan Zakin yasamu nasarar laftawa Emanuel Tsinin K'afarsa A hannu take wurin ya dare sai jini Emanuel ya sandara Ihu da Kiran Jesus, Ya Fad'i k'asa, Aikuwa Zakin ya hayesa daniyar sake cizonsa, Amma Cikin sauri Sam ta d'auke Kan Zakin da halbi da wata k'atuwar bindiga, Yasa Kan Emanuel mattace,
Shima Samir Yasami damar d'auke Kan Zakin da takobinsa gangar jikin Zakin ta Fad'i sai jini kawai dake tartsatsi,
Ganin An Hallaka Rabin SHAID'ANU ZAKUNAN Yasa sauran ja da baya suka gudu,
Zama sukayi gurin suna maida numfashi bama kamar Taj Domin ya kashe zakunan da yawa, Ruwa Jidda ta d'auka ta Aje masa gefensa tana Fad'in"nagode sosai da kaceci rayuwa ta,"
Baiyi magana ba murmushi kawai yamata tareda d'aukar Ruwan yasha,
Emanuel kuwa saida Aka d'auke masa gawar Zakin Sannan yasami iya mik'ewa, da taimakon sauran mutanen Suka masa d'inkin raunin,
Kallon Sam yayi Wadda take kusa da jidda suna Magana k'asa k'asa,
Yace"kinceci Rayuwata Mai kyau, Ina godiya sosai Amma Kamar bashi ne Zan Rama miki,"
Cikin Rashin sonyin Magana tace"Mu musulmai idan mukayi taimako badan A Rama Mana muke ba Dan Allah muke Domin shike bamu Lada, kuma shine yabani ikon taimakon ka, Kuma ni Sunana Samarai Dan gajarce sunan kace sam kawai,"
Murmushi kawai yayi domin dama yajima da k'aunar Sam cikin zuciyar shi Amma Yakasa fad'a mata Domin lokuta da dama Samir Yakan gifta masa ta Hanyar sata wani Aikin ko bata dokar kada tafita, shiyasa ya kejin haushin samir sosai,
Wad'an da basu mutu ba suka farfad'o inda wad'anda sukaji Rauni Aka musu dressing Suka D'an matsa daga inda gawarwakin zakunan suke, sannan Suka sake kafa tanti Suka Kwana Anan, Amma cikin zulmi kada ragowar zakunan sudawo,,
Har safiya ta waye babu Abunda ya faru, Anan sukayi jinyar kwana 7 suka warke Sannan sukaci gaba da tafiyar, Wannan karon Samir ne gaba sannan Emanuel,
Sunyi tafiya sosai suna tsayawa basu had'u da komai ba har tsawon kwana 7, Suka iso wata Hanya, Wadda guda 2 ce rak d'ayar tayi cikin wani kogo Mai zurfin gaske, d'ayar kuma Ruwa ce ke kwarara sosai k'orama ce wurin, Amma manyan kadoji ne ciki suna ta Kai komo A ruwan,
Tsayawa sukayi suna kallon kallon domin ko wacce Hanya dole tanada nata Hatsari,
Samir Yajuyo yace"Ina Shawara ta Ina kukaga Ya kamata mubi? Domin basai na fad'a muku ba ko wacce hanya da gani tanada nata Hatsarin , kuduba wad'annan kadojin sam bazamu iya fad'a dasu ba, to amma bansan Kuma meye cikin kogon ba, Ina kuke ganin ya kamata mubi,"?
"Anya Wai samir bamu b'ata ba? Muna kan hanya kuwa,"? Cewar Jidda cikin d'an tsoro
"Eh muna Hanyar Domin ga Taswirar Hannuna munkusa zuwa ai in Sha Allah,"
"Ya kamata kicirewa ranki tsoro da karaya Jidda kinriga kinzo ba Hanyar komawa ki dogara ga Allah kawai Jidda," Cewar Taj,
Gyad'a kata tayi cikin Alamar k'arb'ar zancensa,.
Sam tace"Ko Alama bazamu iya fad'a da wad'annan kadojin ba kawai Anawa ganin mushiga kogon kawai"
Caraf shima Emanuel ya K'arb'e zancen da cewa"Eh mushiga ciki"
Anan kowa ya Aminta Abita kogon,
Saidai kuma Anrasa d'aya Wanda zaishiga gaba,
Ganin Anata b'ata Lokaci yasa Sam gyara Rik'on takobinta tanufe k'ofar kogon tana Mai Addu'a,
"A'a kina hauka bayan kina macce Zaki Shiga gaba Kuma idan wani Abu Ya sameki fa,"?
Da mamaki ta kalleshi domin karon farko dataga kulawarsa gareta,
Ganin kallon da take masa yasa, Yasa kansa kawai Cikin kogon Yana Addu'a taj yabi bayansa da wasu Sojojin masu manyan bindigogi guda 20 suka wuce sannan Sam da Jidda, Wannan karon jidda Cikin k'arfin guwa take sannan suran Suka shiga,
Sunyi nisa sosai cikin tafiyar har sundaina ganin bayansu,