← Book details Ciki Da Gaskiya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 41 OF 41

Sashe 41

Ciki Da Gaskiya Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Bak'aramar kid'ima hajia babba tayiba, saboda tana hangen fitar figa da ya khaleel yayi saga gidan ta window d'in d'akinta, gumine yashiga karyo mata.
Hannunta Na rawa takuma kiran number hajia khaltum.
Yanzun kan ta sameta, tana d'agawa tace aminiya k'aryarmu ta k'are.
Kamarya aminiya? Miya kawo maganarnan?.
Ibraheem sun d'anama Barau modibbo tarko, kuma kinsan kamashi tamkar muma an kamamune, Dan bamuda wani sirri Wanda yawuce Barau modibbo.
Bak'aramin wuntsilawa y'an hanjin cikin hajia khaltum sukayiba, tunda taji bayanin Aminiyar tata.
Itama kanta zufar ke keto mata, muryarta Na rawa tace Aminiya mun d'ebo ruwan dafa kanmu, lallai yau naga sharrin d'an kunama.🦂
Bata jira amsar hajia babba ba tayanke wayar, tareda fara Neman layin Barau modibbo.

___________

Aysha Na tsaye inda ya khaleel yabarta tamkar gunki taji wayarta Na wringing, dubawa tayi saitaga mama.
Batareda tad'agaba ta nufi cikin gidan.
A d'aki ta iske mama da yaya fadeelah, mama tana sakama ummuhanee kaya, fadeela kuma Na d'aura d'an kwalinta.
Mama tad'ago tana kallon Aysha data shigo sukuku, ke lfyarki kuwa?.
Babu komai mama, Aysha tafad'a da sauri.
Ido mamar ta tsura mata, kimsan banason k'arya dai.
Kamar Aysha zatayi kuka tace, "mama ya khaleel ne".
Khaleel kuma? Miya faru dashi?.
Babu komaifa, naga ankirashi awayane, ya d'auki bindugu yafita akid'ime, wlhy tausayi yabani, inajin tsoro, tak'arashe maganar da matso kwalla.
Murmushi mama tayi, danta gano wani Abu tartare fa ayshar, tacigaba da sakama ummuhanee kayan tana fad'in to kimasa addu'a, ALLAH ya tsaresa, insha ALLAH babu abinda zai samesa, aikinsane yazo da hakan.
Kai Aysha tad'aga kamar zata rushe da Kuka.
Mama tace jeki shirya zakuje dubiya asibiti.
Da to Aysha ta amsa, tashiga bayi tad'an wanko fuskarta tafito, bak'ar doguwar Riga mama tabata.
Badan taso sakawarba tasaka, Dan Rabin hankalinta yana kan ya khaleel, jitake kamar tayi tsuntsuwa tabisa, komai yafaru a gaban idonta.
Fadeelah takar6i d'an kwalin rigar ta nad'a mata, kaikace wata balarabiya ce, dukda batayi kwalliyaba, farar fauda kawai tashafa kad'an sai kwalli.
Mama tabasu kud'i tace su sayi kayan marmari a hanya, suje ga Ramadan can yana jiransu a waje.
Har zasu fita, Aysha tace mama wai wama zamuje dubawa?.
Kuje mana, aii zaku gani, Ramadan yana jirankufa, zaitafi aikine narok'esa ya ajiyeku tunda asibitin yake, kukuma bakusan asibitinba.
To mama saimun dawo.
Adawo lfy mama tafad'a tana mik'ewa, jikinaba, a cikeda tunanin yanayin Ayshar, afili tace Aysha dama kin fidda khaleel aranki, babu yanda za'ayi gudan jinina yahad'u da gudan jinin hajia laurah, abindama bazai ta6a yuwuwaba kenan, dama cikin y'ay'an Bilkeesu ne tabbas Dana amince miki, amma d'an hajia laurah bazai ta6a Auren y'arda tafito daga tsokar jikinaba🤕 wannan ALWASHI ne👉🏻.

Afalo suka iske ya Ramadan yana jiransu, ganin sun fito yamik'e, yauwa kumuje karna makara ko, yay maganar yana kallon agogon hannunsa.
Fita sukayi har bakin motarsa, fadeelah tashiga baya, dole Aysha tashiga gaba, shima ya zauna a mazauninsa yaja motar suka fice.
Saida yatsaya wajen saida kayan fruits kamar yanda fadeelah tarok'a, dakansa yafita yasayo komai da'ake buk'ata da kud'insa, sannan yadawo suka cigaba da tafiya.

________________
Neman duniya hajia khaltum takasa samun Barau modibbo, takira wani makusancin yaronsama yak'i d'auka, bak'aramin tashin hankali takuma shigaba, sai kai kawo takeyi tsakanin falonta da bedroom, ga zufa dake ketowa adukkan sassan jikinta, tasan wanene Ibraheem Abdallah, takuma San mizai iyayi, wlhy kasancewar mahaifiyarsa a wannan lamarin bazai ta6a d'aga musu k'afaba, tabbas bayyanarsu a wannan harkar itada mahaifiyarsa tamkar bayyanar wani tone-tone ne agaresu, dolene Ayi *Walk'iya* kowama yagansu, wata gudawace taji tazo mata babu shiri, dagudu tanufi bayi.
Tana gudawa tana turama Barau modibbo massage a wayarsa.

______________
Duk yanda youseef kemasa kwatance haka yabi, har ya isa cikin dutsen Alhaji, a can k'arshen gari gidan Na Barau modibbo yake, shikad'ai, tamkar gidan mayu, dagani kasan wannan gidansane Na sirri, babu Wanda yasan dashi.
Rigar makarin bullet Adams yabashi yasaka, yakuma d'urama bindigarsa bullet, saida yacikasu fam sannan suka zagaye gidan, kuwa tafiya yakeyi cikin sand'a, idan and'an tafi sai a tsaya ana sauraren ko akwai Wanda yafito, dahaka har wasunsu suka sami damar shigewa ainahin cikin gidan.
Cikin sand'a ya khaleel yabi tabayan wani mazgegen k'ato dake tsaye da bindiga AK 47 ahannu, bakimsa yay saurin toshewa da hannunsa ya murd'e wuyansa, jikake k'ak'assss!!!!! Ya karya Wuyan, yajefar dashi awajen tim, sannan yakuma rik'e bindigarsa cikeda kula, yana tafiya cikin sand'a.
Wani yakuma hangowa agabansa, yay saurin janyo buhun ledar dake kan wani dirom a tsakar gidan, tafiya yake cikin sand'a yana bin bango, harya kai inda yake, da sauri ya kunshe kamsa acikin buhun ya kulle, buge buge yafara saboda rashin fitar numfashi, ya khaleel yakuma murd'a bakin bukun, bai sakiba saida yaga jikin mutumin yasaki alamar ya mutu sannan ya hankad'ashi ya daki bango.
Wani icce yad'auka ya mazgama Wanda ke tsaye bakin k'ofar a kai, da sauri yazube awajen tareda sakin razananniyar k'ara, wannan ne yasaka su Barau modibbo farga da abinda ke faruwa....

_______________
Su Aysha sun isa asibitin, har d'akin da gwaggo bintu take kwance, da bishirah Aysha tafara cin karo, wata iriyar zabura tayi da zare ido waje, tayi saurin kai dubanta ga gwaggo bintu dake kwance bisa gadon.
Cikin muguwar fad'uwar gaba gwaggo bintu take kallon Aysha, dukda batada tabbacin itad'ince ko ba ita bace, Dan Aysha ta canja sosai...............✍

_to masu karatu, idanfa kere🏑 Na yawo zamo🐇na yawo wataran za'a had'u._

*yau dai ga Aysha ga kuma gwaggo bintu, shin mikuke tunanin zai farune?.*

*ga ya khaleel can zai damk'i ogan su hajia babba, mikuke tsammanin zai biyo baya?.*

*mama Na zargin gwaggo bintu, kuma tanada burin bincikenta akan wanda yafidda Aysha k'asar waje karatu, kunga koda Aysha tayi yunk'urin 6oyewa mamafa zata tono, yakuke ganin za'a kwashe?.*

*ya maganar auren Aleeya da ya khaleel? Kunsan dai ya khaleel ya d'aukama mama alk'awarin amincewa, aganinku babu lauje cikin nad'i akan had'in auren Aleeya da ya khaleel?, kuyi nazari, gakuma baffah yayi wani furuci akan auren ya khaleel d'in, shin shikuma wacece za6insa? Dan nasan ba shirinsu d'aya da hajia babba ba, kuna ganin hajia babba zata yadda?, kokuwa baffah zaiyi hak'uri danasa za6in?, ko za'a had'a masa sune suduka?, towama baffan zai za6ama ya khaleel?.*

*mi Aysha da meerah suke shiryawa su gwaggo bintu?, tabbas akwai 6oyayyen tarko dasuke shirya musu, to amma nami? Kuma zasu sami nasara?.*

*ya maganar soyayyar da Aysha kema ya khaleel?, ga mama ta d'auki alwashi akan hakan, shin burin Aysha zai cika kuwa?.*

_kutttt cakwakiya nacikin *CIKI DA GASKIYA* part 2, karku bari abaku labari, zaizo muku da abubuwan mamaki, soyayya mai k'ayatarwa, k'aryar wasu zata k'are, gad'an Karen tone-tone, za'ayi WALK'IYA fa, kuma zamuga kowa, hardama wad'anda bakuyi tunaniba, akwai abubuwan al'ajabi, mamaki, tsoro, k'ayatarwa, kai hardama naban haushi._

Kudai kawai Ku kasance da Bilkeesa Ibraheem Musa, (bilyn Andull) danjin yanda zata kaya.

Marubuciyar...

_Rashin Sani!!._
_Auren k'addara ko biyyaya?._
_k'anwar uwace ko kishiyar uwa?._
_Ni da aminayata!!_
_Nawaff!!._
_Sabon al'amaree!!_
_Kukan kurciya....!!_
_Ban saketa ba!!_
_Abdul-maleek bobo!!_
_Karayar arzeek'i!!_
_Sanadin bikin sallah!!_
_Ciki da gaskiya...!!_

Wanda bai karantaba yanema akasuwar online🤣😘😜

K'ak'ak'ak'a, wata rikita rikita sai a CIKI DA GASKIYA part 2, yana nan tafe nan kusa kad'an.

*_CIKI DA GAAKIYA!!.... (wuk'a bats hudashi), kashi Na biyu._*

*COMING SOON!!!!!.*

Ngd sosai masoya, ina alfahari daku, ina k'aunarku, inayinku 100%, karku gaji, kukasance dani a part 2❤❤❤❤❤😘😘😘😘😘😘😘😘😘😘😘.

K'aunarku dabance a zuciyar bilyn Abdul😍😍😍😍😍😍😍😍🙋🏻‍♀🙋🏻‍♀🙋🏻‍♀saikun jini.👍🏻👍🏻.
Chapter 41 · 0% Book details