← Book details Ciki Da Gaskiya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 35 OF 41

Sashe 35

Ciki Da Gaskiya Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

_____________________________
Su mama sun isa asibiti itada Anty Mamie domin duba bintu.
Saida doctor d'in dake dubata yafito sannan suka shiga, gwaggo bintu na zaune akan gado, ta jingina da filo, bishirah nabata abinci, sallama dasu mama sukayice tasakata d'ago ido tana kallonsu da amsa sallamar ahankali.
Ganin mama yasaka gwaggo bintu wata zabura, har taune harshe takeyi wajen fad'in fad'ima! Kece?.
Mama ma tace, "bintu! Dama kece mara lafiyar?".
Hawayene suka shiga zarya a kumatun gwaggo bintu alokacin data tsinkayi muryar Anty Mamie na fad'a mata aii itace Baffansu ya aura kwanaki ko, kuma matarsace tunkan ya aureta, jikinta sai rawa yakeyi, tabbas tasan mama tata6a aure kafin ta auri yayansu, kenan Alhaji Abdallah jigawane dama tsohon mijin nata?, nan take zufa tafara ambaliya akowane sashe najikin gwaggo bintu, fad'i take a zuciyarta nashiga uku ni binta, yanzu yazanyi da wannan kulli? Ina zan samoma matarnan 'yarta? Nasan dolene ta tambayi ina Aysha, ni bintu nashiga Tara, nikuma k'arshena yazo kenan, hajia babba kin cuceni keda shaid'anin daya bani k'arfin guywar yarda daku.
Babu Wanda yazargi wani Abu tsakanin Anty Mamie da mama, duk zatonsu ciwon ne yake damunta, dukda mama tana ganin kamar mamaki gwaggo bintu tayi dakasancewarta matar mai gidanta.
Sunkai mintuna 30 a d'akina sannan sukai musu sallama suka fito, amota mama take sanarma Anty Mamie dangan takar dake tsakaninta da gwaggo bintu (wadda suke kira Maman yara), Mamie tayi dariya, tace haba shiyyasa naga ta nuna mamakinta da ganinki, lallai ALLAH kenen mai hikima.
Mama tace aikuwa dai, (bata fad'ama Mamie komaiba dangane da rashin k'aunar da gwaggo bintu take nuna mata, lokacinda tana matar yayanta).
Harda sukazo gida abin na'a zuciyar mama, amma bata damuba, tunda alhamdulillah 'yarta tadawo gareta.
Gobe idan ALLAH ya kaimuma, zatazo Abuja itada fadeelah.

_____________________________

Washe gari Aysha da fadelah sukayi shirin zuwa Abuja, da mortar haya zasu hawo, amma sai kawu bilyamin yabada motarsa akaisu.
Hakan yayma Aysha dad'i, dan dama batason hawa motar hayar.
Kasancewar tafiyar yamma sukayi sai around 6:30 suka iso anguwar ta mai-tama. Gaban Aysha ne yaketa luguden fad'uwa tunda suka shigo anguwar, danta gane anguwar data zaunace kafin barinta k'asar, mamakine ya isheta akan miya kawo mama nan?, batama tsinkeba saida taga mortar tatsaya k'ofar gidan alhaji Abdallah Jigawa tana horn, kallon fadeelah tayi, tace Yaya fadeelah anan mama take aure?.
Eh, nanne Aysha, fadelah tafad'a kanta tsaye.
Shiru Aysha tayi tana had'iyar yawu, aranta tace *Cakwakiya kenan*, lallai nabar *baya da k'ura*, wannanfa shine *Kwai cikin k'aya*.🤥
Abubuwa dayawa sun canjama Aysha, bakamar zuwanta da gwaggo bintu ba, taga ancanja gate d'in gidan, hakama ansamu wasu sauye-sauye, fentin gidanma bawanda tasani baneba.dukda sun isa ana shirin magriba ne hakan bai hana anguwar kasancewa cikin hasken wutar lantarkiba, ko ina farr da haske.
'Dan gwari mai gadi dai haryanzu shine gateman d'in gidan, amma yad'an kara manyanta, bakamar sanda Aysha ta sanshiba.
Aharabar gidan baba bala yayi fakin, kamar ankwashema Aysha jini haka tafito daga motar, handbags nasu kawai suka d'auka, sauran kayan baba bala yace suje za'a shigo dasu, fadeela sai zumud'in Shiga takeyi dantayi kewar mama, amma ga Aysha Sam abin Bahaka baneba, tafiya takeyi kwakwalwarta na tariyo mata baya, jitakeyi kamar yauma tazo gidanne amatsayin boyi-boyi Mara 'yanci.
Rungumetan da akayine yasakata sakin ajiyar zuciya da d'ago kanta, Ashe harsun shigo falon batama saniba, mamace tarungume Aysha cikin matuk'ar kewar 'Yar d'iyar tata, itama Aysha ganin haka saita k'ank'ame Maman tareda sakin wani irin kuka dabasan dalilinsaba.
Fadeelah dai 'Yar kallo takoma.
Babu kowa a falon, Duk sun shige d'akuna Dan gabatar da sallah, 'yan uku ne kawai ke k'iriniyarsu.
6angaren mama suka yanda zango, saboda tsabar farinciki mama tama kasama Aysha magana, sai kallonta takeyi tana zuba murmushi.
Ayshar Ce tagaji tace Mamana nayi kewarki, ina sonki, amma shine kikayi aure bansaniba ko? Tak'are maganar da turo Baki gaba.
Daga fadeelah har mama abin yabasu dariya, Dan haka suka dara abinsu.
Mama tace to Aysha ayima mama afuwa, nasan kina kishin babankune, amma inaso kiyarda da k'addara, haka ALLAH ya hukunta mana, nima bawai da son raina baneba kinji.
Aysha ta jinjina kanta, saitaji tama daina jin haushin mamar, wanka sukayi sukai salloli, mama tayima umma-hanee itama, 'yan uku na nane zasu Aysha, Aysha sai dad'i takeji suma yanzu mama ta haifesu dayawa, gata da k'anne maza, abinda tadad'e tana sha'awa kenan.
Bayan sunci abincin da mama ta shirya musu suka mik'e danzuwa gaida mutan gidan, harsun fara shirin Fita saiga Anty Mamie tashigo, a'a inakuma zakuje?.
Fadeelah tace zamuzo gaishekune Mamie.
A'a fadeelah kuzauna Ku huta, wanan wahalar tafiya aii tayi yawa, da safe sai'a gaisa aii, nima sallah natsaya yi shiyyasa ban lek'oba tunda kuka shigo, Dan 'yan uku sunkaimin labari.
Mama tayi dariya, aii wad'annan 'ya'yan naki bilkesu sune redio mai jini.
Mamie ma dariya tayi, tace a'a a'a, ai abunda suka gani suke fad'a.
Aysha sai kallon Mamie takeyi tanajin k'aunar matar aranta, amma talura bata ganetaba, taji dad'in hakan, Dan dama bata fata kowa yaganeta agidan, hakanne zai bata damar aiwatar da aikinta akan su hajia babba hankali kwance.
Mamie tace d'iyata 'yan turai, ya turai da karatu?.
Murmuahi Aysha tayi, cikin rissinar dakai tace alhmdllh Mamie, munsameku lafiya?.
Lfy lay muke, yagajiyar hanya?.
Alhmdllh.
To masha ALLAH, mamie tafad'a tanama ummu-hanee dake hannunta wasa.
Mamie ce tahanasu zuwa gaida kowa agidan tace su huta, dama baffah bayama k'asar, Ammah kuma tana Jigawa. Daman takanje tayi dogon Hutu a can idan tajuyo mata..............✍🏿

*_I love you all😍😍😍😍😘😘😘😘_*
[8/26, 8:48 PM] Aisha Galadima: *_Typing📲_*

🤰🏻
*_CIKI DA GASKIYA........_*
_{🔪wuk'a bata hudashi🗡}_

*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*

*_NIKA'DAI WRITER ASSO........_*😜

*_Sadaukarwa_*
_My sweet dady_
~(ALLAH ya gafarta maka)~
🤲🏻😭

*_part 1_*
(littafi na d'aya📕)

3⃣6⃣

Washe gari su Aysha basu tashiba sai around 9, wanka sukayi sannan mama takawo musu breakfast sukayi, bayan sun kammala suka fita gaida mutanen gidan.
Da Anty Mamie da umme Amaraya kawai suka gaisa, itama bata fita da wuri baneba, hajia babba kam tafita aiki, samarin gidan kowa yatafi uzurinsa, hakama su Amal, shiru gidan, 'yan ukuma sunfara makaranta shiyyasa gidan yayi tsit.
Sun d'an dad'e a 6angaren Anty Mamie sannan suka dawo d'akin mama.
Mama takallesu cikin soda k'aunar y'ay'an nata, tace, "kutashi Ku shirya baba bala yakaiku shoprite kuyo tsaraba.
To suka fad'a suna mik'ewa, Aysha tasaka wando da Riga sunmata k'yau.
Amma sai mama ta harareta, nifa matsalata da shiga al'adun wasu kenan, duk taka tsantsan d'inka sai yaro yakoyo abinda va tarbiyyarsaba, Aysha cire kayannan kisaka wannan less d'in, mama tayi maganar tana mik'ama Aysha farin less mai k'ananun jajayen fulawoyi.
Kamar Aysha zatayi kuka haka takar6a, itafa kayannan nauyi suke mata yanzu wlhy, amma bazata iya yima mama musuba, itama dai tasan masifar mama darashin d'aukar raini.
ALLAH yasotama siket ne ba zaniba, kayan sunyi masifar mata k'yau, gashi basu kama mata jikiba, bata d'aura d'an kwalinba, Dan bazata iya da wannan kayan nauyinba, siririn Jan gyale tayane katta dashi, gashinta datayi parking a tsakkiya yanata kyalli da k'amshi saiya zauna d'am a gyalen, har ana hango jelar gashin data kwanta a dokin wuyanta kad'an, saboda gyalen shara-shara ne, kasancewar yanda tayi acuci da gashin nata ya zauna sosai sai gyalen yad'an zama kad'an daga gaba, kwantaccen gashin gaban goshinta yayi luf-luf kamar atsaya kaita kallonta dan kyawun datayi.
Ita kanta mama saida tafurta masha ALLAH a zuciyarta, Dan tasan d'iyar tata abar kalloce.
Aysha tad'auki Ummu'hanee akafad'a tafita tana zun6ura baki, ita adole fushi takeyi ansakata saka kaya masu nauyi.
Fadeelah tabiyo bayanta rik'eda 🏧 d'in mama tana dariya.

Tunda suka Isa shoprite d'in k'irjin Aysha ke bugu da sauri-sauri, addu'a tafara karantowa ahankali, basuwani 6ata lokaciba suka fara duba abinda suke buk'ata, Aysha ce rik'eda keken🛒tana za6a tana sakawa bayan tad'an duba bayan, Anty fadelah Na rik'eda Ummu'hanee tana taya ayshar da shawara.

Har sund'an gota shoprite d'in yadakatar da Emmanuel, Ema yataka burki ahankali yana fad'in yes sir.
Kamar bayason magana yace Ku koma baya mushiga shopping zan d'anyi.
OK sir EMA yafad'a a giramame.
Saida Ema yanuna ID cart d'insa aka bud'e musu gate d'in da sauri, motocin uku suka Shiga ajere.
Adams ne yabud'e masa k'ofa yafito, cikin takun Nutsuwarsa kamar kullum yake tafiya, yayinda su Ema ke take masa baya.
Sanye yake cikin Uniform d'in aiiki, amma babu hula a hannunsa, ko gun d'insama a mota yabarta, kallon yaransa yayi yace kowa yad'auki abinda yake buk'ata, baijira amsarsuba yay gaba.
Adams ne kawai yay saurin jawo keken yabi bayansa.
Sukuma sauran sunata Murna, da yabon adalin ogan Nasu, Wanda yasan darajar Na k'asa dashi, bashida bak'inciki ko kad'an, ga k'yautar ban girma, komai nasa abin sone, haka kowa yafara d'aukar za6insa suna zuba masa addu'a azuciyarsu.
Chapter 35 · 0% Book details