← Book details Buzuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 6

Sashe 2

Buzuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Aniyarka ta bika"
Yasir yace "wai meyasa Dan Allah kake yawan yimin mugun bakine to bari kaji ko mata sunkare a duniya mai zanyi da wata MARYAM ita kuma wanan yarinyar ba karamar yar raini hankali bace da kake ganin ta,kaga dai yanzun gashi a gaban idonka kai kadai ta gaisar tai wucewar ta kamar Allah baiyi ina wajan ba saboda tsabagen ta rainani haka take min duk sanda ta ganni ,to a haka mafa
bance Ina son taba dubi abin da takemin in nace ina sonta ai nakade dan wlh ba karamin rainani zataiba ni kuma abin da bazan taba dauka ba kenan yar ficiciyar yarinya ta rainani saboda bansan raini shiyasa kaga koh irin,su bana sha'awar kulawa dan ba karamin jinake da mutunci naba shiyasa rannan da su Yusuf suka zo nace a kawo musu abin dan tabawa gashi yar aikin mommy bata nan little ma batanan mummy tasa takawo daman da kai da Yusuf jirgi daya ya kwasoku zo kaga yanda yake rawar kafa a kanta wani irin bakin cikine yakamani Wanda bansan na menene ba haushin ta zanji koh na Yusuf da badan na taka mishi birki ba wlh da yasa ta gama rai nani dan haka kaima ka daina min maganar su dan in ba hakaba wlh zan fasa rakiyar haba" shiru kawai ABK yayi yana kallon ikon Allah wanda ya tabbata gaba kadan abokin nashi zai gane me yake nafi ABK yace "duk da haka kai tunani sosai a kan maganar nan dan gaba nake jiye maka"
Kallon shi kawai Yasir yayi ya kauda kai dan shi maganar da ABK yakeyi bata masa rai take abune yake fad'a da bazai taba faruwa ba a dai-dai nan sukayi parking waya ABK ya dauko call din Hasina yayi "baby gamu mun karaso muna bakin get" banji metace ba yace "OK ki fitoh lafiya" koh 5 mint basuyi ba sai gata ta fitoh
Yasir yace ai daman nasani ta tsuniyar gizo bata wuce koki Dan Allah dubeta ashe duk daya suke dan wannan bazata girme little ba ABK in ban da murmushi yana kallon,to ba abin da yake'yi wani maganadisun kaunar ta yana taso masa,da sallama Abakin ta karaso wajan amsawa sukai Yasir sai wani dan cin magani yakeyi gaisheshi ta Farayi "barka da zuwa abokin mu" murmushi dole ya kakalo "yace yauwa barka da fitoh wa kina lafiya ya mutanan gidan? " lafiya lau tace sai yau Allah yayi zan ganka ganin ka yafi jinka my love sai cewa yake zai kawo ka aman shiru sai yau Allah yayi gaskiya yau ina da babban bako" murmushi yake yakeyi, a zuciyar shi yace lallai abokina ya ebo parrot dube ta koh kunya bata ji a gabana take cewa my love yar ficiciyar ta da itah bata tafasa ba zata kone.
Muryar ABK ce tadawo dashi daga balaguran tunani da yatafi
Mushiga daga ciki koh kasa Yasir yayi da murya kai Dan rainin wayau ba inda zani ABK yace haba abokina karka min haka mana Dan Allah pls help me kaga in bamuje ba wlh bazata ji dadi ba" tsaki Yasir yaja muje maye karka cinyeni a gobe ma rana ce sai dai ka nemi wani ya rakoka wajan jaririyar nan,baby Muje koh Dan duk maganar da sukayi bataji komai ba gaba tashige sukuma suna binta a bayan har suka karasa palon baki gaskiya tamusu tarba ta musan man Dan ga kayan ciye ciye nan kala kala sai da tagama hada musu komai sanan tace ina zuwa taiciki abinta da Yasir kaman bazai ciba aman da yafara sai da yakusan kau da bin da ta hada musu
Ya kalli ABK wanan da ga gani ba ita tayi ba "wata uwar harara ABK yayi mishi yace aman ka lau da komai bari kaji wanan da kake rainawa ba abin da bata iya ba sanan...sallamar tace yasa ABK shiru Yasir ba yabo ba falasa yace godiya meke sanan yacero bandinr din yan 200 yata yace wa ABK in kagama kasame ni awaje bai jira godiyar da take mishi ba yayi gaba

Muje next page

Yar mutan KD
🌹🌻🌹🌻🌹🌻🌹🌻🌹🌻
🌹🌻🌹🌻🌹🌻🌹🌻🌹🌻

*_BUZUWA_*

🌹🌻🌹🌻🌹🌻🌹🌻🌹🌻
🌹🌻🌹🌻🌹🌻🌹🌻🌹🌻

*_STORY & WRITTEN_*

*_BY_*

*_AUNTY FAUZAH YAR AMANAH_*

*_Editing_*
*_by_*
*_SISIN MAMA_*

*_🌈KAINUWA WRITERS✍ ASSOCIATION_*🤝
```{United we stand and succeed; Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers} ```

https://www.facebook.com/kainuwawritersassociation/

```Wanan page din sadaukar wane ga dauka,cin masoya book din nan ```

🅿3⃣

Yasir bai,fi 7mint ba da fitowa yafara kiran ABK amman yaki dagawa
a dan fusace ya kara kiran shi a ransa yana wannan shine kiran,karshe In kaki fitowa sai dai kazo kaga bananan
yanayi yana kara wayar a kunne ringing biyu ABK
ya daga Yasir bai jira daga gareshi ba yafara fada
"dalla malam ka fitoh in ba haka ba wlh inyi wucewa ta kazo Kabar mutum atiti kai gaka dadi soyayya wlh in baka fitoh ba sai dai kazo kaga bana nan" bai jira tajin bakin da ABK zai fada ba ya yakashe wayar yana harararta saikace wayar ce ABK

2 minutes ba ayiba sai ga ABK ya fitoh yana wani shu'umin murmushi wata uwar harara Yasir ya ruga mishi "saboda kai dan iskane kashige kayi zaman ka lokacin da na fitoh nai mata sallama ai kaima sai ka biyo bayana amman dayake kai dan rainin hankaline kabar ni a waje kowa yana wucewa yana kallo na" ya karasa maganar yana kokarin bude mota murmushi ABK yayi yace abokina wlh bazaka taba gane menene so ba sai rananr daya rikeka barin irinku saban shiga baya muku da kyau bazan Yasir yayi dan shi wanan maganar bata mishi rai ma takeyi
"kaga Malam ya isheni haka haba dan Allah wai kai dan Allah baka gajiya da maganar soyayya ce a rayuwar ka wanan jaririyar naga tanaso ta zautar da kai wlh dubeta fa amman a gabana take cema my love ba kunya
Ko kadan a cikin kwayar idonta" murmushi ABK yasaki "kadan ma kaji ai sunana a wajan ta yafi kalla goma bakasan ma wani abuba wlh In nazo wajan,ta tanamin shagwabar nan tata har rasa inda zan tsoma raina nake yana wani dafe saitin zuciyar shi tare da wani lumshe ido
wani wawan tsaki Yasir yasaki "kaga malam in zaka tada mota mutafi ka tada in kuma zaka cigaba da wanan shirman naka bismillah ABK motar ya tada sai da suka hau kan titi sosai sanan yasaki sautin wakar Umar m Sharif ta Bilkisu duk wajan da za a kira bilkisu sai yace hasina abin ya gama zuwa ma Yasir wuya yace "Abubakar me zai hana ka hada kayan,ka ka koma gidan su hasinan nanne gaskiya ka dameni kuma kacika min kune wlh
Kai kawai ABK ya girgiza abokina bazaka taba ganewa ba a dai dai nan suka kawo bakin get din gidan su Yasir horn ABK yayi get man ya bude suna saka hancin motar su
Yusrah su hango tsaye da wani block beauty gays a tsaye Yasir jiyayi kamar an buga mishi guduma a zuciyar har wani daci-daci yakeji saboda tsabagen bacin rai ABK yaga yanayin da yakoma lokaci daya dafashi yayi ABK yace lafiya kuwa abokina? gaba daga hankalin Yasir baya wajan ya kefe inda Yusrah da wanan saurayin suke da ido
Lafiya kuwa abokina ABK yakara fada lafiya mana Yasir yace mekaga nine naga yanayin ka duk ya chanja ne lokacin daya uhmm Yasir yace duba wacan yarinyar tana kwaso mana tar kacan samari gida dube ta sai wani murmushi take meshi bari kaga naje na koreshi yana kokarin bude koh fa da sauri ABK ya rukoshi haba abokina wanan ba girman ka bane sanan ba taifin,shi bane
Yasir yace ok laifinane kenan koh?a a ABK yace
nama gane laifin wacen kodaddiyar ce nan ma ABK a a yace da sauri Yasir yajiyo wai mekake nufine Abubakar nifa nakasa gane ina kasa gaba ma gaba daya aman ka barni da waccan kodadiyar zanyi maganin ta akan yan jaye jaye da take ma mutane har gida
ABK yace look Yasir wai dan kaganta da wani meye naka a ciki kai kace bakasan ta toh ko me zatayi basai ka zuba ido ba, in zuba ido fa kace wataran sokake zuciyata tatarwatse kamar ya?
ABK ya tambaye shi da sauri Yasir yadago badai maganar ta fitoh fili ba? yake tambayer kanshi.

Dan jin amsar da Yasir zai ba Abubakar muje a next page

By yar mutan KD
🌹🌻🌹🌻🌹🌻🌹🌻🌹🌻
🌹🌻🌹🌻🌹🌻🌹🌻🌹🌻

*_BUZUWA_*

🌹🌻🌹🌻🌹🌻🌹🌻🌹🌻
🌹🌻🌹🌻🌹🌻🌹🌻🌹🌻

*_STORY & WRITTEN_*

*_BY_*
*_AUNTY FAUZAH YAR AMANAH KAINUWA_*

*_🌈KAINUWA WRITERS✍ ASSOCIATION_*🤝
```{United we stand and succeed; Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers} ```

https://www.facebook.com/kainuwawritersassociation/

*SIGOGIN ISTIGHFARI KALA TAKWAS NE.*

*Manzon Allah, tsira da amincin Allah su kara tabbata a gare shi, yace:*

*Na rantse da wanda raina Ya ke hannunSa, Allah! Ina neman gafararSa, kuma ina tuba zuwa gare shi, a kowace rana sama da sau saba'in.*

*Kuma Manzon Allah (SAW) ya ce:*

*Ya ku mutane! Ku tuba zuwa ga Allah. Domin ni ina tuba a kowace rana zuwa gare Shi sau dari.*

*SIGA TA FARKO*

*Shugaban Istighfar gaba daya shine:*
"ﺍﻟﻠﻬﻢ ﺃﻧﺖ ﺭﺑﻲ ﻻ ﺇﻟﻪ ﺇﻻ ﺃﻧﺖ ﺧﻠﻘﺘﻨﻲ ﻭﺃﻧﺎ ﻋﺒﺪﻙ ﻭﺃﻧﺎ ﻋﻠﻰ ﻋﻬﺪﻙ ﻭﻭﻋﺪﻙ ﻣﺎ ﺍﺳﺘﻄﻌﺖ ﺃﻋﻮﺫ ﺑﻚ ﻣﻦ ﺷﺮ ﻣﺎ ﺻﻨﻌﺖ ﺃﺑﻮﺀ ﻟﻚ ﺑﻨﻌﻤﺘﻚ ﻋﻠﻲ ﻭﺃﺑﻮﺀ ﻟﻚ ﺑﺬﻧﺒﻲ ﻓﺎﻏﻔﺮ ﻟﻲ ﻓﺈﻧﻪ ﻻ ﻳﻐﻔﺮ ﺍﻟﺬﻧﻮﺏ ﺇﻻ ﺃﻧﺖ ".
*Allahumma anta rabbee la ilaha illa ant, khalaqtanee wa-ana 'abduk,wa-ana 'ala 'ahdika wawa'adika mas-tata'ata, a'uzu bika min sharri ma sana'atu, abuu-u laka bini imatika alai, wa abuu u bizanbi, faghfir li fa-innahu la yaghfiruz-zunuba illa anta.*

*Manzon Allah (SAW) ya sunnanta mana karanta wannan istighfari sau daya, safe da kuma yamma.*

*Sannan kuma yace:*

*Duk wanda ya karanta shi da safe yana mai imani dashi, idan ya mutu kafin yamma, zai shiga aljanna. Kuma idan ka karantata da yamma kana mai imani da hakan, idan ka mutu kafin safiya zaka shiga aljanna in sha Allah.*
@Sahihul Jami'i.

*SIGA TA BIYU*
ﺍﺳﺘﻐﻔﺮ ﺍﻟﻠﻪ.

*ASTAGH FIRULLAH*

*SIGA TA UKKU*
3-ﺭﺑﻲ ﺍﻏﻔﺮ ﻟﻲ.

*RABBI GHFIRLI*

*SIGA TA HUDU*

4-ﺍﻟﻠﻬﻢ ﺇﻧﻲ ﻇﻠﻤﺖ ﻧﻔﺴﻲ ﻓﺎﻏﻔﺮ ﻟﻲ ، ﻓﺈﻧﻪ ﻻ ﻳﻐﻔﺮ ﺍﻟﺬﻧﻮﺏ ﺇﻻ ﺃﻧﺖ.

*ALLAHUMMA INNI ZALAMTU NAFSI FAGHFIRLI FA INNAHU LAA YAGHFIRUZ ZUNUBA ILLA ANTA.*

*SIGA TA BIYAR.*

5-ﺭﺏ ﺍﻏﻔﺮ ﻟﻲ ﻭﺗﺐ ﻋﻠﻲ،ﺇﻧﻚ ﺃﻧﺖ ﺍﻟﺘﻮﺍﺏ ﺍﻟﻐﻔﻮﺭ.

*RABBI GHFIRLI WA TUB'ALAYYA INNAKA ANTAT TAUWABUL GHAFUR.*

*SIGA TA SHIDA*
Chapter 2 · 0% Book details