← Book details Budurwar Mijina Book 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 31 OF 32

Sashe 31

Budurwar Mijina Book 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Dagani har shi makara mukayi sallah asuba sai a gida yayi sallah asuba.

Sanin zaije aiki tunda ranar Monday ne yasa ban koma bacci ba na fara k'ok'arin zuwa kitchen na sama Masa abinda zaici.

Sai dai Ina zuwa na gansa a kitchen Yana soya kwai Ido da muka hada dashi yasa ya kanne min Ido Yana "Na hutasheki farin cikina jekiyi kwanciyarki kiyi baccinki"

Ina karya Zan wuce na Kulle Miki gidan idan bazaki iya girkin rana ba Zan siya na Aiko miki dashi"

Hmm kawai nace tare da barin Kitchen din nasan duk Yana hakane dan na manta abinda yamin,nima zanso na manta din amma bansan Mai yasa nakeji kamar bazan iya sakin jikina dashi kamar a baya ba,ban koma d'aki ba na zauna a palo,ya fito daga kitchen din da plate din kwai da kofin shayi.

Ya zauna a gefena yana ci Yana min hira nidai biyesa kawai nake har ya gama ya jawoni ya Kara jagwalgwalani san ransa banda ma naki nasan karawa zaiyi ya shige daki ba dadewa ya fito a shirye Yana kamshin turare ya ajiyemin Dubu biyu a gefena Yana "bari naje kar na makara"

"A dawo lafiya"

Ya sunkuyo yamin kiss zai juya nace "Idan har ka sake cin amanata Allah ya isa ban yafe maka ba idan bana kallonka Allah na kallonka"

Murmushi yayi Yana "Mahfuz bazai ci amanarki ba mahfuz nakine ke kadai ki kwantar da hankalinki a gabanki dai jiya kina kallon irin gargadin da nayi mata"

Yarda daya ce amma ba abinda mahfuz zai cemin yanzu na yarda da Ido na bishi har ya fice daga gidan.

Na Mik'e na koma daki na kwanta bacci ya Kara awon gaba dani.

Mahfuz

Sosai yaji shi cikin farinciki dan a yanzu yasan ya samu ya shawo Kan lubna zaiyi iya kokarinsa wajen gujewa duk wani abu da zai saka su samu sabani.

Take yaji shi cikin b'acin rai daya tuno ganin da yayiwa Hadeeza da wani jiya,tunda yake da ita bai tab'a ganinta da wani ba baisani ba ko hakane yasa jiya yaji ransa ya b'acin da ganinta da wani,Ashe karya take da tace masa bata kula kowa Ashe karya take da tace shi kadai ne saurayinta,a yanzu ya Kara tabbatar da zarginsa akan fuska biyu gareta,dama hanya yake nema da zai yakiceta,dama hanya yake nema da zai ce Mata bazai iya aurenta ba, a yanzu Kuma ya samu hanyar tunda ya ganta da wani jiya.

Sai da ya isa office ya dan kammalla wasu ayyukan kafin ya Nemo lambar Ammi ya kirata dan su gaisa,dan ba mai wanan sabon layin nasa.

Sai dai Ammi na Jin muryarsa ta rufeshi da fada tana "Wulakanci ne yasa ka kashe wayarka tun jiya nake neman layinka a kashe"

'canja layi nayi Ammi shiyasa na kiraki da sabuwar Dan na daina amfani da wancan"

"Sabida me ka canja layin da tun kana Saurayi kake amfani dashi"?

"Haka kawai na canja layin Ammi"

"Karya kake yi kace min matarka ce ta saka ka canja layi sabida Kar mu ringa samun ka a waya mahfuz kasan dai ba ita ta haifamin Kai ba ko"Anya yarinya nan ba asirice ka tayi ba naga alama so take ta rabaka da kowa ta hanaka muamalla da kowa to wlh wanan ne bata Isa ba dan ko dawo da ita da kayi bada yawuna ba,amma tunda ka dage wlh sai ka Kara aure Ina nan akan bakana Kuma kafin na Saba maka ka mayar da layin nan da kowa yasanka dashi,ba ruwana da wanan sabon layin jibi kazo Ina san ganinka"

Kit ta kashe wayar yabi wayar da kallo,ya riga da yasan halin Ammi idan baiyi abinda tace ba kadan da aikinta tace zata maka baki, mayar da layin nan da tace yayi zai iya haddasa Masa matsala da Lubna yasan halin Hadeeza da azababben naci ko yayi blocking dinta sai ta kirashi da wani layin ba Kuma lalai duk bayanin da zai yiwa Lubna akan ita take nace Masa ba ta yarda,zancen Karin Aure Kuma da ta dage sai yayi sam bai shiryawa wani aure ba,Koda zaiyi ba yanzu ba Hadeeza ce dama ta matsa Masa yaji Yana San ya Kara auren,a yanzu Kuma bazai tab'a iya aurenta ba.

Layin ya mayar a karamar wayarsa dan yasa a babbar wayarsa sai Hadeeza ta kusa cika mishi waya da magana ta watsapp.

Yana sakawa ko minti goma baayi ba sai ga Kiran Hadeeza a wayarsa ya riga da ya haddace lambarta a kansa baiyi wata wata ba ya danna Mata blocking sai yake hango ta a idonsa yanda ta dame ko'ina a jikinta wani katon da a haife ya haifeta ya ringa bata ice cream a baki.

Texes ne sukayi ta shigowa da wani lambar zain ko bai bud'e ba yasan itace tayi amfani da wani layin

Duk message din na ban hakuri ne da bayanin ba saurayinta bane wani dan uwansu ne ya bata dama su had'u bata ji dadin wulakanci daya mata ba jiya ko bacci batayi ba,Kar ya manta irin san da take masa,Kar ya manta irin dukan da ta Sha a hannun matarsa bai dace ya Mata haka ba.

Tsaki yayi ya goge duk messages din ya Nemo lambar lubna a waya dan so yake ya goge komai a zuciyarta sai da Kiran ya kusa katsewa kafin yaji ta d'auka hira ya hau janta dashi amma daga yanda take amsa wayar yasan ba so take ba,dariya ma yanzu take bashi ita a lailai fushi take dashi,bayan yasan balain San shi take dannewa kawai take katse wayar yayi ya tutura Mata text ya ajiye wayar.

Kiransa da Hadeeza ke tayi da layin zain din da ta ke ta Masa texes ya danna a block Yana Jan dogon tsaki,har yanzu hangota yake da wanan katon yana bata ice cream ya rasa ma mai yasa yake Jin haushi idan ya tuna.

Wajen karfe daya ya mik'e dan so yake daga massallaci ya biya ta restaurant yayi take away guda biyu ya aikawa lubna daya shima yaci daya.

A bakin k'ofa ya ci Karo da Hadeeza da ta sha bak'ar doguwar Riga har kasa kamshin turare kawai take.

Da sauri yaja da baya cikin mugun hade rai,Yana "Mai ya kawoki office dina ban hanaki zuwa wajen aikina ba Wai Mai yasa bakida hankaline wane kallo kikeso a ringa min ne bana ce miki ki rabu dani ba"

Ba ko alamar fushi a fuskarta ta rufe k'ofar tana "Mahfuz taya zan rabu dakai bayan Ina sanka nasan kaima kana Sona, Mahfuz Ina duk alkawarikan da kayi min,na zaka aureni,duk wahala da na sha da dukan da naci a hannun matarka ya tashi a banza kenan a yanzu zaka ce na rabu da kai,bayan kasan banida kowa Wanda ka gani dashi a jiyan cousin dina ne ba saurayina bane"

"Hadeeza ada ni nace zan aureki a yanzu Kuma na fasa ba Kuma ki isa kimin dole ba,har ni zaki rainawa hankali kicemin wanan katon da na ganki dashi jiya cousin dinki ne?cousin dinki ne yake baki ice cream a baki?wane irin rantsuwa ne bakimin akan bakida saurayi ba ni kadai gareki,nasan irin wayanda kike hulda dasu taya zan aureki kina biye biye wlh Hadeeza Sam ban yarda dake ba na dade Ina zargin badani kawai kike muamalla ba jiya kuwa idona ya gane min dan haka a yanzu ban yarda da ke ba bazan iya aurenki ba ki daina kirana a waya Hadeeza karki hadani fada da lubna inasan matata"

Akan gwiwarta ta zube hawaye na zubo Mata Tana "Wlh mahfuz dakai kawai nake hulda ka yarda dani ba komai tsakanina da wanan da kagani dashi jiya,san da nake ma yasa nake ma duk abinda nakeyi bawai dan halina bane ba Zan iya maka komai dan na faranta maka rai"

Kamar an fusgo maganar daga bakinsa dan ya dade Yana san ya mata tambayar "Hadeeza bani na fara saninki ba wa Kika fara bawa kanki"?

"Fyade aka min a lokacin Ina secondary mahfuz shiyasa kaji haka amma wlh ba na muammalla da kowa"

Tasan ta hanyar da take Kama mahfuz hakan kuwa yasa ta cigaba da kuka cikin kirsa tunda taga yayi shiru ta cigaba da kuka cikin shagwaba taja gwiwar ta zuwa wajen da yake tsaye ta mike tsaye tare da rungumeshi.

Har zai janyeta ta Kara kankame shi.

So take ko Yaya ne ta rinjayeshi tunda ya fara botsare mata hankalinta ya tashi bata da wata hanya da zata samu ya fito ya aureta sai ta wanan hanyar da idan ta samu cikar burinta ya gama zuwa hannunta,so take ta nunawa lubna tayi kad'an bata Isa ta hana aurenta da mahfuz ba,so take ta nunawa lubna iyakarta a jiya ko runtsawa batayi ba burinta kawai mahfuz ya aureta.

Yanda ta fara kunna shi yasa mahfuz janye jikinsa da sauri Yana "Dan Allah ki tafi gida Hadeeza nan karki Manta wajen aikina ne"

"Bazan tafi ba sai ka tabbatar min da zaka zo gidanmu idan ba haka ba wlh haka zan ta zuwa nan"

"Hadeeza Dan Allah ki bari na samu nutsuwa zanzo ki daina kirana a waya bana so ki haddasa min wata fitinar har yanzu ban gama shawo Kan lubna ba Kuma kinsan duk abinda ya faru ke Kika jawo min,kema kinsan bazan samu wani kwanciyar hankali ba har nayi tunanin wani aure idan bana zaman lafiya da lubna"

Kamar ruwan zafi yake watsa mata haka ta ringa ji amma haka ta daure tana "toh idan ban kiraka ba kai zaka kirani"?

"Eee karki sake ki Kara kirana a waya Hadeeza da kaina Zan kiraki Kuma Dan Allah ki daina fesa wanan turaren yanzu lubna tasan kamshin turaren ki idan har kinaso mu cigaba da muamalla ya zama dole ki kiyaye Abubuwan da na fada miki na Kuma gaya Miki gaskiya a yanzu banida halin aure idan har matsuwa kikayi da auren sai dai ki nemi wani idan Kuma Zaki iya jirana toh sai ki bini a hankali"

Murmushi ta sakar Masa tana "Duk yanda kace ayi haka za'ayi Ina kaunarka Mahfuz"

Ta Kara rungumeshi,mahfuz da kyar ya Kai zuciyarsa nesa bai biye mata ba amma har kasan ransa yaji yana san kasancewa da Hadeeza dan wani irin salo take masa dake gigita shi.
Chapter 31 · 0% Book details