Chapter 31: Between Books and Breaths
Beyond The Veil Part 1 Complete Novel · about 525 min read
Rayuwa a India ba kamar Nigeria ba ce. Yare, abinci, yanayi, komai daban. Amma Azrah ta yi ƙoƙari wajen blending in da sabuwar rayuwar da ta samu kanta a ciki. A haka har suka gama first semester suka koma second semester wanda kamar wasa yanzu tana neman shekara a India, amma har yanzu dai, karatu ya zama priority dinta, ba ta da wani lokaci sai karatu, ina kika fito karatu, ina zaki karatu
" kuma cikin wannan ƙanƙanin lokaci sunanta ya gama karade department ɗinsu, daga lecturers har zuwa non-academic staff, babu wanda bai san Azrah ba ko da ba da suna ba, da siffa suke ganeta 'yar Nigeria mai natsuwa da hazaka
A bangaren Nigerian Students Association (NSA) ma, sai da suka nemi ta da kansu suka mata rijista da su, wannan kuwa saboda kullum sai sun ji ana ambatonta ko dai daga wani lecturer, ko wani activity inda aka ga irin tsayuwar da take yi. Har wani daga cikinsu ya ce, "Even if she tries to hide, her brain and discipline will always expose her"
Ba wani taro ko activity da ya shafi entrepreneurship, leadership ko creativity da za'a kira dalibai ba, sai an fara da sunan Azrah, ta riga ta zama alamar wakilci ga Nigeria a wuraren da ba ko'ina ba ne ake samun irin hakan, ko a cikin WhatsApp group na department ɗinsu, in har discussion ya shafi wani abu mai muhimmanci, yawanci sai an ambaci sunanta
Kullum da sassafe tana tashi zata nufa library, daga can ta wuce class, ta dawo tayi assignment, babu wani unnecessary talk babu yawan hira, strict routine kawai. Sai dai idan zata kira gida, musamman su Umma ko Zahra, toh anan ne zaka jita tana magana, ko kuma lokacin da Samira ke lallaba ta ta ci abinci, shine zaka ga ta fara surutu wai tana damunta
A gefe guda kuma, Khalil, wanda ta haɗu da shi a cool-down spot, bai tsaya daga kokarin sa ba, ya mayar da ita kamar wata biological sister ɗin sa, Kullum sai ya nemo inda take karatu duk da yawan canza wajan karatu da take yi, haka zai tsiya abinci ya kai mata duk da yadda sometimes take ki amma inaa baya hakura, kullum yana zuwa kuwa abinda yake fara faɗa shine
"Bari ki huta yauzu pls let ur brain rest, I brought this for you"
Azrah sai dai tayi murmushi wanda ba ya wuce laɓɓanta ta ce
"Na gode, but I have a test next week"
"Wanda kika iya ba guduwa zai yi ba, wanda kuma zaki koya kawai ki fahimta no need ki cigaba da wahalar da kanki" zai faɗa yana gyara zamansa kusa da ita sannan ya zuba mata Idanu wanda kallon Granny ɗinsa yake mata
Azrah har yanzu bata ganin Khalil da wata romantic light, sai dai yadda yake tausayinta yana daɗa birgeta, ba a soyayya ba, amma in silent appreciation, Kamar wani big brother wanda yake tausaya wa ƙanwar sa da take wahala
Amma akwai abu ɗaya da ke damunta "Samira" Duk da suna ɗaki ɗaya, har yanzu ba ta iya gane halin kawarta ba, Yarinya ce mai wayewa sosai, amma kullum cikin hira da samari da kawo su ɗakinsu tana cewa ai "friends" ne kawai, amma Azrah tana kallon abin da ke sama da haka dan ita bata saba ganin haka ba, sai tana tunanin wata kila haka rayuwar masu kuɗi suke
Wata rana Azrah ta gagara daurewa ta tambaye ta
"Samira, ba kya gajiya da chatting da su ne? Yaushe kike karatu? Kuma bakya jin wani iri ne kawo maza har ɗaki ne wai?"
Samira ta yi dariya kawai
"Ai ni in ba nayi socializing ba, I can't even focus, That's how I balance my mind"
Azrah ta girgiza kai
"Allah ya shirya mu baki ɗaya"
***
Kiran gida kuwa ya zama wani sashi na ranarta da ba ta sakaci da shi har ya zama yana cikin daily routine ɗinta, Zata kira Umma, su gaisa da natsuwa cike da annashuwa su yi hira sosai, sannan idan ita da Zahra ne har wani lokaci sai dariya ta cika dakin, Amma da zarar ta kira Bappah inhar baya ɗakin Umma sai ya haɗa ta da Mama Wanda ko ta gasheta ma a dakile take amsawa
Wannan disconnect tsakanin Azrah da mahahaifiyarta na daga cikin abubuwan da suka fi daci a ranta sai dai ta saba, ta ɗauki komai a matsayin ƙaddara
*****
A cikin wannan rayuwa, akwai wata rana da Azrah ta ji kamar duniya ta tsaya mata ne, dan duk sanda taji ance zasu tsiya wanu abu hankalinta tashi yake dan kuɗin da gomnati ke basu dashi ta riƙe kanta kuma take turawa su Umma, Khalil ya kawo mata abinci, ya ce
"I hope you try this Egyptian dish, I made it myself"
Azrah ta kalli food container ɗin da mamaki
"You cooked this? For me?"
Khalil ya ɗan sosa kai
"Don't be shocked, I know a few things in the kitchen"
Bayan ta ci, sai ya kalleta da nutsuwa ya ce
"You know, I admire how focused you are, But don't let the world pass you by while you read about it in books"
Wannan magana ta taɓa zuciyar Azrah, Bata ce komai ba sai dai ta yi shiru, ta lumshe ido
Maybe... just maybe, akwai darasi a ciki
Wata safiya bayan Azrah ta gama karatunta, ta shiga bathroom domin ta watsa ruwa, Bayan ta fito, tana goge jikinta da towel, ta ji wayarta na kara, da sauri ta ɗauka tana tunanin kiran daga gida ne ai kuwa taga video call ne daga Bappah ne dan duk sanda video call zai shigo wayan ta toh shi ɗin ne, shi kaɗai
Ta zauna a bakin gado tana receiving call ɗin, Zahra ce ta bayyana akan screen da fara'a sosai a fuskarta kamar wacca aka mata albishir
"Zahra ke ce? Masha Allah, sai wani shauki kike kamar an ba ki sabuwar waya!" Azrah ta faɗa tana dariya, tana sake hayewa saman gadonta
Zahra ta haɗe girarta da shagwaɓa
"Saboda bani da wata bukata sai ta waya"
Azrah tayi dariya ta ce
"Ai sanin halin ne, ba abinda yanzu kike bukata sai waya, yanzu faɗa min menene ya saka min ke farin ciki"
Zahra tayi dariya ta ce
"Ai da gaske ne! A sabuwar makarantar mu Nice dai da aka fitar da result ɗin term ɗin nan, ni na zo first position!"
Azrah ta tashi zaune ba tare data san tayi hakan ba ma, ta ce
"Subhanallah! Zahraaa! Na miki murna, congratulations! Ni kaina sai na ji kamar ni na ci"
Zahra ta yi ƙara tana dariya jin yadda Azrahn tayi sounding
"Toh ke kuma yaushe za ki dawo? I miss you wallahi"
Azrah ta ce
"Very soon, Muna gama Exams ɗin da zamu fara na second semester zan dawo, Nima nayi missing ɗinku nayi kuka har na gaji"
Suka ci gaba da hira na ƴan mintuna kafin suka yi sallama, Azrah tayi tagumi ta faɗa duniyar tunani da girman nauyin da ke kanta, Zahra ta dogara gareta fiye da yadda take tunani hakan yake kara bata wani motivation speed
***
Washegarin kamar yadda take daga Library sai class, ana cikin lecture, wani lecturer ne a class ɗin ganin kamar basu fahimta kuma basu wani bada hadi kai yasa ya fara tambayoyi, kamar yadda aka saba, Azrah ce ta miƙe tsaye da kwarin gwiwa ta bada amsa mai gamsarwa, har lecturern ya gamsu da murmushi ya ce
"Excellent response as always, Miss Azrah"
A nan ɗalibai suka kalle ta da girmamawa kamar wata scholar
Sai dai kafin lecture ya ƙare, wani lecturer ya shiga cikin hall ɗin da sauri yana daftari a hannu, ya ce
"Hey, Everyone! Please note, new exam timetable has just been pasted outside the department. Check it immediately"
Da sauri ɗalibai suka fara fita da damuwa, zuciyoyinsu na duka uku uku, Azrah kuwa, da ke son ta duba da kanta kafin a saka a WhatsApp group, ta ɗauki littafinta da nutsuwa ta nufi inda aka manna timetable ɗin dake bakin department ɗinsu
Tana cikin tafiya a corridor mai cike da ɗalibai, ta hangi Khalil na tahowa daga nesa, kamar wanda ya shigo da nufin ganinta sai kuma take ayyana cewa dan ita ɗinne ma ya shigo dan shi baya wani damuwa da nasa karatun kamar yadda ya damu da nata karatun
Bayan ya iso inda take da murmushi a fuskarta kafin ta ce uffan, ya miƙa mata folded paper
"Your timetable, I figured you'd want it early"
Azrah ta buɗe baki da mamaki
"Khalil? How did you even know it's out?"
Ya ɗan harare ta da murmushi
"Don't thank me, I don't like all that unnecessary drama"
Ta yi dariya cikin shauki tana jinjina kanta
"Toh shikenan, Nagode kawai in secret"
Buga mata wani littafin hannunsa yayi a kanta ya ce
"Even in secret, I'll still know"
A wannan rana, Azrah ta ƙara fahimtar cewa a duk inda ka ke, akwai mutane da Allah ke turo maka domin rage maka nauyi ba lallai sai danginka ba
Tana tafiya tana duban timetable ɗin, zuciyarta na bugawa da ƙarfin karatu da fargabar jarabawa.
****
Azrah ta zauna tana fuskantar bangon ɗakin, tana kallon exam timetable da Khalil ya kawo mata jiya, wanda ta manna da tape sosai kamar wani important docx Yadda ta kira masa ido dai ka ɗauka tana son ya mata magana ne, Sai ta sake dauko wani blank paper ta fara rubuta tsarin karatun ta rannan da zata maida hankali akan kowanne course, irin abubuwan da take bukatar maimaitawa, da kuma notes da zata koma duba wa, A hankali ta dora pen a akai ta miƙe, ta manna shi a jikin bangon kusa da timetable ɗin.
Samira da ke kwance akan gadonta tana kallonta cike da mamaki ta ce, "Ohh, Nikam naga ta kaina da ke, Kin dawo kamar irin robot ɗin nan ne fah, haba mana ai ko robot ne yana bukatar chargy"
Sai ta kwashe da dariya, ta dafe cikinta tana kallon Azrah, "Just imagine, kina reacting kamar wata mad person! Haba mana Azrah, calm yourself down, yanda kika ci uban karatu yanzu, ko baki sake duba komai ba in exams ya zo, you'll still pass In Shaa Allah"
Azrah ta juyo ta wani harare ta da idonta mai cike da gajiya banda bacci babu abinda kake ganin a idon nata, ta ce da ita,"Ni ki kyale Ni Samira! I can't afford to joke around"
Ta juya zuwa wajan da wayarta ke charging ta cire ta daga charger ta zauna kusa da window, Tana kallon timetable da kuma reading plan ɗinta da ta manna a bango, zuciyarta cike da tsoro da fargaba, Ta buɗe contact list, ta danna lambar Bappah, A zuciyarta, she just wanted to hear Umma's voice koda kuwa zata ce mata "Allah ya bata sa'a" ne, sannan kuma ta faɗa mata already ta tsara schedule ɗinta gaba ɗaya yau
Zuciyarta na ta bugawa da dan karamin tsoro da kuma anticipation, She wanted to do well, She needed to, bayan ya kusa katsewa sai aka yi picking call ɗin, bata san sanda ta sake murmushi ba ganin Umma ce da kanta ta ɗaga kiran, cike da farin cikin ganinta
"Hello Umma" ta faɗa a hankali cikin lumshewar murya
"Azrah... Azrah 'yata, kina lafiya?" muryar Umma cike da ƙauna da kulawa, kana jin muryar nata kasan tayi missing 'yarta
"Lafiya lau Umma naa, ai yau na ce kiran na musamman ne Umma... timetable ɗinmu ya fito" ta ce tana ɗan lumshe ido, tana ƙoƙarin danne damuwar da ke damunta
"Toh Allah ya taimaka Azrah, Allah ya baki sa'a, ko da yaushe ina muku addu'a kuma za'a kara In Shaa Allah, Kin shirya dai ko?" Umma ta tambaya, tana ƙoƙarin sauraron komai daga muryar nata dan nan take fahimtar komai ko da bata furta ba
Azrah ta ɗan numfasa "Nayi iya ƙoƙarina Umma na, Nayi reading plan na ma, Nakan ɗanyi karatu har dare, sometimes ban ma komawa ɗaki da wuri ba idan na tashi daga lectures"
Umma tayi shiru na dan lokaci sai tace da tausayi 'yarta "Allah ya miki Albarka Azrah, ki tabbatar kina hutawa kaɗan-kaɗan, kiyi addu'a Kema sosai, sannan kada ki manta da karatun Al-Qur'ani everyday Kuma kar kiyi overwork kanki fa"
Azrah ta dan yi murmushi mai rauni ta ce
"In shaa Allah Umma, Ina missing dinki sosai"
"Ina missing dinki nima, ga Bappahn ku na kusa
Sai taji muryar Bappah ya ce "Azrah sannu da ƙoƙari, ki kula da kanki, Allah baki sa'a"
Azrah ta dariya cike da jin kunya da tace da Umma tana missing ɗinta, ta ce
"Amin Bappah, Nagode kwarai"
"Toh Allah ya sa mu dace, ki dinga hutawa dan nasan kinda ɓaci"
"Amin Bappah, Thank you"
Bayan ta kashe wayar, ta sauke ajiyar zuciya, ta dan jingina da gado, tana jin kamar ta samu wani abu da ta daɗe tana craving wani nutsuwa ce taji yana shigarta
Samira dake gefe ta ɗago kai, "Anya kuwa wannan kawar tawa ba zata yi distinction ba? You're too focused girl'
Azrah ta juyo da murmushi, ta ce "Distinction kawai fa? In har babu first class, I won't stop'
This book costs 500. Make the payment to Hauwa Jibrin, Wema Bank account 0421255553, and send proof of payment to 08110615256.
Episode 32: The Unfamiliar Voice
Ranar wata Juma'a bayan azahar, Azrah ta dawo ɗaki a matuƙar gajiye, tana shiga ta fara buɗe warmers ɗin ɗakinsu amma bata samu abinci ba, kanta na sarawa kawai taje ta zube a gadonta da hijabinta har sannan a jikinta. Kallon Samira da take dariya ga waya ƙare a kunnenta tayi, taɓe baki tayi dan sana'ar Samira kenan, ji tayi tana cewa
"Baby wallahi ka raina ni" Samira ta faɗa tana dariya sosai
Sai kuma ta juyo tana kallon Azrah ta ce
"Ga Deen ɗina" ta kare maganar tana dariya "ku gaisa mana, ko da yake kina yawan ƙin yarda in baki labarinsa''
Azrah ta ɗan ware ido sosai tana kallonta ta ce "No need…"
"Come on!" Samira ta ce tana miƙa mata wayan nata, "he asked to say hi, Just for a second mn"
Cikin murmushi da rashin kuzari, Azrah ta karɓi wayar, ta kai kunnen ta sannan cikin nutsuwa ta ce
"Hello, sir! good evening''
A can ɗayan bangaren kuwa, muryar saurayin ya amsa da very calm voice ɗinsa ya ce
''Peace be upon you, kawar Samira, Ni dai na gaji da yawan jin sunanki kullum a gun Samira, Finally yau dai, na samu zan gaisa da ke"
Azrah ta tsinkayi zuciyarta ta buga 'dimmm' Muryar… kamar ta ta san sa, tabbas tasan me wannan muryan, tunanin me murya ta fara tana son figure it out ne amma ta kasa, Muryar ba sabuwa bace a kunnenta, itakam har tama manta cewa waya take yi kuma har sannan zuciyar nata bai daina tsinkewa ba, muryansa taji wanda ya dawo da ita daga duniyar tunanin data faɗa, murmushi kawai tayi, tana kokarin ɓoye rikicewarta
Deen ya ci gaba da cewa
"By the way, kina huta wa ko? Samira ta ce min kina stressing kanki sosai, Please, don't do that, You won't help anyone if you break down''
Azrah ta ce a hankali ''Thank you. I'll try''
"But… muryarki tana da daɗi sosai har yafi na kawarki'' Azrah ta juya ta saci sallon Samira dake shirin fara haɗa musu lunch, sai kuma ta ɗauke kai bata san sanda ta kirkiri murmushin ba
Kafin ya ƙara wani abu, Azrah tayi saurin katse shi da ɗan dariya marar kuzari
''No, thank you''
Yayi dariya a can bangaren ya ce
''Ko dai wayar a handsfree take ne? Naga kamar baki son magana sosai''
Sake Satan kallon Samira tayi sannan tayi kasa da murya ta ce
"Please stop, ba zata ji daɗi ba"
Wani murmushin yayi ya ce
"Okay, dole zan zo ko saboda ke Azrah"
Azrah da zuciyarta ke bugawa tayi saurin cewa "No... Thank you" daga haka ta cire wayan daga kunnenta ba tare da taji me zai sake cewa ba ta karasa wajan da Samira take zaune ta miƙa mata ta ce
"Samira, gashi mun gaisa" Samira na Murmushi ta karɓi wayan daga hannun Azrah
Azrah ta zauna bakin gado tayi tagumi ''Where have I heard that voice before?'' Ta fada cikin zuciyarta, tana bin kowane kusurwa na memories dinta da tunanin inda wannan muryar ta shiga rayuwarta a da
Samira kuwa ta cigaba da dariyarta kamar ba ta lura da halin da Azrah ta shiga ba, Amma Azrah… zuciyarta tuni ta dau wani sabon nauyi, Kuma bazata iya bayyana shi ba
Bayan fitar Samira, Azrah ta kwanta. Amma a zuciyarta tana nan 'taɗaɗɗen tunani' tana ƙoƙarin tunawa inda ta tsɓa jin wannan murya... amma ta rasa.
Lumshe idonta tayi, zuciyarta na bugawa da ƙarfin da bata san dalilinsa ba
*****
Wani babban parlour ne mai ɗauke da duk wani kayan more rayuwa ta duniya, yalwa da kuma peace, Fentin bangon cikin parlorn launin cream, sannan gefe guda kuwa wall paper ne, kujeru masu launin fara kal sai wasu kuma Black, da agogon zinariya dake manne a bangon ɗakin, ana hango manyan framed photos na iyalin a bango tun daga bakin kofa, A tsakiyar parlorn kuwa wani dattijo ne zaune a kan wani resting chair, yana sanye da farar jallabiya da hula, yana lumshe ido lokaci zuwa lokaci wanda hakan yasa baka gane wani yanayi yake ciki, hannunsa da yake saka wa lokacin zuwa lokaci yana ɗiban fruit salad daga cikin glass bowl da ke gefensa
A gefe guda kuma matar sa ce wanda ake kira da Ummi, mace mai kamewa da natsuwa, tana zaune a kan sofa tana kallon su cike da kauna. A gaban dattijon kuwa, akwai samari biyu da suke suna zaune a kan carpet, duk da girman su, alamun cewa suna gaban mahaifinsu da girmamawa
Abbah ya gyara zama, muryarsa ya fito da karfi amma cike da kulawa dan hakan ma alamune na ransa ya fara ɓaci ne dan jayayyan da suke son masa
''Ku saurara Ni da kyau, dole ne ku koma makaranta na ce, Ku maza ne, ba za ku zauna da tunanin cewa yanzu komai ya ishe ku ba a rayuwa ba ko baku bukatar komai, A'a, Ilimi ba ya ƙarewa''
Wanda yake zaune kusa da Abba ne ya ɗago kai, yana mai cike da rashin jin daɗi amma yana ƙoƙarin bayyana ra'ayinsa cikin mutunci da kuma girmama Mahaifin nasa, baya so ya buɗe wani door da abokinsa ma zai samu har yayi jayayya da mahaifinsa, ya ce
"I'm sorry to say this Abbah… amma yanzu fa, ba lallai sai mun koma physical school ba, Zamu iya yin online classes, kuma we'll still graduate successfully''
Abbah ya masa wani kallo yana mai harararsa, sannan ya girgiza kai ya ce
"You're very stupid for even thinking like that! Makaranta nace, kuma sai kun koma da ƙafafunku, Ya zaku ce kuna da kamfani da zaku jagoranci amma diploma kawai ke hannunku? Is that what you'll present to the board? Ko dan kuna ganin kuna da gadon dukiya shiyasa baku ganin bukatar ƙarin ilimi, ba certificate kaɗai nake so daga gare ku ba harta ilimin ina so ku samu?"
Sagir wanda tun farko bai ɗago ba ya ɗan gyara zama, sannan da ladabi ya ce
"Toh Abbah… zamu koma, ee understand"
Ummi ta ajiye bowl ɗin hannunta a gefe, ta sauke ajiyar zuciya sannan ta ce cikin natsuwa
"This is for your own good ne Ilimin shine zai sake baki daman shiga cikin manyan masu companies kuna represent mahaifinku, ba zai ɗauke muku matsayi ba sai ma ya kafa muku daraja da kuma karfafa ku a gaban duniya, Hakuri za ku yi, ku je ku kammala karatun ku akan fannin da ya dace da ku sannan ku samu certificate ɗin degree"
ɗayan saurayin ya ce "In Shaa Allah Ummu zamu koma, hakan gaskiya ne kam"
Ummi ta juya tana kallon kofar ɗakin Hajara tana kwala mata kira "Hajara!"
Sai ga wata yarinya mai kimanin shekara 20 ta fito da sauri, tana sanye da apron tana
"Na'am Ummi'
Ummi ta ce "Ashe ma kina kitchen, toh je ki haɗawa 'yayanki lunch, kinji ko?"
"Toh Ummi" ta amsa cikin sauri
Tana wucewa sai saurayin ya tashi yana kallon mahaifinsa da girmamawa ya ce
"Abbah zamu iya tafiya ?" Kai ya gyaɗa musu ya ce "Eh zaku iya"
Ummi ta ce "Ina kuma zaka bayan Hajara zata saka muku abinci" ɗan murmushi yayi yace
"Abu zan karɓa yanzu zan dawo"
kafin ya fice daga parlorn yayin da abokinsa ya biyi bayansa, zuciyarsu cike da tunani… amma sun san wannan shawarar da Abbah ya kawo yayi daidai dan suma jin daɗin rayuwa ne ke mantar da su.
Yayin da kwanaki ke tafiya, test da assignments na ƙaruwa, amma hakan bai hana occasional calm moments tsakanin Azrah da Khalil ba
Kamar kullum har lecture hall ya raka ta sannan ya zauna a cool down dake gaban hall ɗin har sai da suka gama lectures suka fito, Azrah da murmushi ta karasa inda yake zaune ta zauna tana maida numfashi ta ce
''Exams mutum zai fara Monday amma su wani takura sa da lectures ko ya suke so muyi copping"
Sake baki Khalil yayi yana kallonta cike da mugun mamaki sai kuma yayi murmushi bai ce komai ba, duk shiru suka yi suna shan iskan wajan can Khalil ya ce
"You always act like you have 10 children to feed back home''
Azrah bata san sanda ta fashe da dariya ba, ta ce
''I'm feeding more than that dreams, expectations, and fear of failure''
Khalil yayi shiru yana kallon ta, kullum yana son tambayar ta game da tarihinta amma sai ya ƙasa, yanzu ma yaji yana son sanin komai akanta sai kuma yaji ba zai iya tambayarta ba
***
Kwance take a kan gado tana bacci irin na gajiya, dan har zazzaɓi ta fara ji bata ma san sanda baccin ya ɗauke ta ba, sai ƙarar wayarta da ke ta ruri kamar zata fashe ya farkar da ita, ta jayo wayar a hankali, har sannan kuma idonta a lumshe yake, tayi receiving call ɗin Khalil, ta gyara kwanciyar ta tana kokarin maidawa jikinta kuzari kafin ta ce
"Hello" muryarta na nuna alamun daga bacci ta tashi
"Are you okay?" Khalil ya tambaya, muryarsa cike da damuwa
"I'm fine… just tired, still studying'' ta amsa a hankali
''Azrah… you need rest, You've been pushing yourself too hard, Exams ba sa bukatar ki rasa lafiyar ki pls*
Ta ɗan murmusa, da wani ƙarfi da bata san ina ya fito ba ta ce "I'll rest after the exams, I promise''
"You always say that'' ya faɗa ƙasa ƙasa, amma cike da kulawa ''Anyway, I brought some food, I'm coming to the usual spot ki fito ki same Ni a wajanll
Bata ce komai ba, kawai ta sauke ajiyar zuciya. Bayan mintuna kaɗan, ta yaye duvet ɗin sannan ta buɗe idonta cike da karfin hali,
toilet ta wuce ta wasa ruwa sannan ta fito ta sanya Abaya, Studying bag ɗinta ta ɗauka sannan isa inda ya ce mata, ganin baya Nana ta buɗe littafi ta fara karatu, can taga Khalil ya nufo ta da leda a hannu, yana karasowa ya durƙusa a gabanta ya ajiye mata abincin yana mata murmushi meanwhile yana leƙa idonta
"You skipped lunch again, right?"
Ta ɗan yi murmushi ba tare da ta amsa ba, ya ce
"Azrah... please, just eat something"
Da kyar ta ɗauki spoon ta fara ci, tana ci tana duba nots dinta Khalil ya girgiza kai kawai yana kallonta cike da mamaki
*****
Zahra da ta shigo cikin gidan da sallama ta samu Bappah yana alwala anan compound, turo baki tayi dan bata ɗauka ma zata gansa ba tana karasa inda ya ke, ta ce
"Bappah ina wuni" a dakile ya amsa mata da lafiya, babu ya school ko ya hanya nothing more, kuma ya bata amsar ma ba tare da ya kalleta ba, Zahra ta ce
"Bappah ko dai laifi na maka ne da har baka son gani na ballai ka tambaye ni ya school da kuma tests tunda test week muke kuma ka sani" Bappah ya ɗan kalle ta sai kuma ya ɗauke kansa ya ce
"Dan Allah tashi ki wuce ɗaki kina cika min kunne kuma hakan ciwon kai kike saka min" with shock Azrah take kallon Bappah, iya saninta Bappah koda wasa baya ƙaunan ɓacin ranta amma ji abin da yake ce mata
Mama ce ta fito daga ɗakinta tana ɗan wake wake da alama dai ko ta fahimci me ke faruwa ko kuma kawai dai tana son maida magana ne, kallo ɗaya tayi wa Zahra ta ce
"Kema ai Kinsan ba'a shiga gonan mai unguwa ko?" Zahra bata sake kallon direction ɗin Mama ba kawai ta shiga ɗakin Umma bayan sun gaisa ta ce
"Umma Nikam ko Bappah aljanun garesa ne? Umma ta dinga kallon ta da mamaki can ta ce
"Zahra amma tafiyarki kuwa? Toh ai kece ma wanda ya kamata ayi wa wannan tambayar?" Zahra ta ce
"Allah kuwa Umma, Ni abun Bappahn ne yake bani mamaki, wani lokaci Kiga yadda yake damuwa da damu abin ban sha'awa amma tunda Dada ta koma shikenan kuma halinsa na da ya dawo sabo fil fah" Umma ta ce
"Toh bana son na sake jin wani magana daga bakinki kwatankwacin wannan ya fito, kinji?" Zahra ta miƙe tana turo baki ta nufi ɗakin su tabar Umma a ɗakinta
Episode 33: The Wait After The Storm
Kwanaki sun shige, sati na biyu kenan da Azrah ta shiga cikakken yanayin exam pressure, Dan har mantawa take da gida idan ba wai ta zo shiga exams hall bane ta kira gida ta ce a mata addu'a. Ba dare, ba rana, babu komai a gabanta sai books da schedule ɗinta da ta manna a bango. Kullum dare tana karatu har wayewar gari, idan kuma ta fita da rana toh da kyar take komawa ɗaki kafin 11 na dare
A wani yamma, tana zaune a wani kusurwar bayan makaranta, inda take jin iska da nutsuwa duk sanda take karatu a wajan, saboda wajan babu wasu ɗalibai, So wajan very quiet place ne, yau ma kamar sauran ranakun ne ta zauna tana karatun ta, ba zato ba tsammani kawai taji an aje mata food flask a gabanta da sauri ta ɗaga kai dan ganin wanene, sai ta kalli Khalil ne, ya kafe ta da ido, yana mata murmushi
''You haven't eaten all day'' ya ce a hankali, yana matsawa kusa da ita 'You'll break down if you keep this up''
Azrah ta sunkuyar da kai kawai, sai can ta ce
''I'm fine, I just need to finish these chapters'' mamakin yanda yasan tana wajan ta fara
''Toh ni kuma zanyi reminding ɗinki everyday'' ya ce da murmushi sai kuma ya ɗaura
"Even if you ignore me''
Can sai ga Samira ta nufo su, tana isa inda suke zaune tayi musu sallama, ganin books a gaban Azrah yasa ta taɓe baki ta ce
''I just came to pick the room key'' And guess what? I'm tired of begging this girl to rest'' ta karasa maganar tana kallon khalil dake zaune gefen Azrah
Khalil ya bawa Samira duk wani attention ɗinsa yana kallon ta kamar dai ba zai ce komai ba sai kuma yace ''I was just telling her the same thing''
Samira ta girgiza kai
''Wallahi sometimes I feel like I'm talking to a wall, But fine, if she collapses, we'll read the books to her in the hospital.''
Azrah tayi murmushi tana ɗauke kanta daga kansu, ta ce
"Thanks for caring, I'll eat, I promise''
Khalil yayi saurin ya ce
''Good, and next time, if you don't eat, I'll drag you myself'' Duk suka yi dariya...
A cikin wani yanayi na zafin rana da gajiyar karatu, ɗalibai ke tafiya a hankali zuwa cikin examination hall. Murmushin nasara da alamar ƙarshe na wani dogon tafiya ya bayyana a fuskokinsu, musamman Azrah da ke tafe da Samira wanda yau venue ɗinsu ɗaya, hannunta ɗauke da biro, exams card da kuma bottle water ɗinta.
''Wallahi Samira idan aka fito da tutorial Questions ɗin da nake ta karantawa jiya, sai na miki rawa a cikin hall ɗin, dan wlhi calculation ɗin da wahala'' Azrah ta faɗa tana dariya
Samira ta harare ta ''Ke dai muyi sauri kafin muyi latti a hana mu shiga idan ba haka ba sai kiyi rawan a waje''
Suna isa venue ɗin suka samu already har an shiga, suka shiga cikin hall din, suka zauna a seat da aka riga aka manna sunan su da kuma ID no ɗinsu, silence ya fara ɗaukar hall ɗin, yayin da invigilators suka raba question papers, Azrah ta karɓa, ta kalli page ɗin gaba ɗaya tana bin questions ɗin da kallo, sai murmushi ya bayyana a fuskarta ba tare data ma ankara ba 'Exactly what I revised!' zuciyarta ta furta
Ba tare da ɓata lokaci ba ta fara rubutu da sauri kamar wata ‘yar jarida da ke bi da lokaci, ko kuma judge dake ɗaukan statement Lokaci na tafiya, duk da gajjiyar da tayi amma zuciyarta cike da kwarin gwiwa take, Har aka kaɗa ƙararrawar stop aka karɓi papers ɗin daga hannunsu, Azrah ta dafe kirjinta da hannunta biyu tana fitar da wani hucin gajjiya
''Finally... we made it, In shaa Allah" ta faɗa a hankali tana kallon Samira wadda take ɗayan row ɗin, suna haɗa ido ta sakar mata murmushi
Suna shirin fita sai ga wani non academic staff ya shigo hall ɗin nasu, da hannu ya fara musu alamun su zauna suyi shiru ganin yadda suke surutu, ya ce
''Attention please! All students are to remain on campus for seven more days. The final results will be released within this period. Only those without any issues will be cleared to travel afterward''
Wani ''Ahh?'' ya cika gurin kowa ya fara kallon kallo dan wasu already sun shirya tafiya gobe, wasu ɗaliban kuma suka ce, ''Gaskiya we need this rest, at least zasu huta a school kafin su tafi gida'' wasu kuma banda hararan sa babu abinda suke masa, Azrah dai bata ce komai ba duk da yadda take craving tafiya gida, sai lumshe idanu da ta yi tana sauke numfashi, ta san cewa kwanaki bakwai kawai ke tsakanin ta da farin cikin ta fiye da komai, she pray hakan shine mafi Alkhairi kuma Allah yasa ta samu sakamako mai kyau, dan bata damu ta tafi da wuri kuma ace sakamakon bai yi yadda take so ba
Washe gari Azrah tayi wani irin bacci mai cike da kwanciyar hankali, da kyar Samira ta tashe ta sallan asuba a hakan ma wai da wari ta kwanta, tana idarwa dakyar dakyar ta samu ta yi azkar dan wani wawan baccin kuma take sake ji, tana idarwa ta miƙe ta faɗa kan gadon ko hijabi bata cire ba nan da nan wani baccin ya sake kwashewa ta, daga karshe Samira ce ta mike ta gyara mata kwanciyarta tana mita
"Ba dole ba, ai dole kiyi irin wannan baccin, wani ma sai ya ɗauka ai shaye shaye kika fara" amma ina tuni Azrah tayi nisa
Can wajajen karfe 8am sai ga wayan Azrah na ringing, Samira ta miƙe da niyyar mai da mata wayan silent, idan gida ne kuma ta ɗauka mata, ga mamakinta kawai taga Azrah tasa hannu ta ja wajan daga kasan pillow ɗinta ta yar kasan tile sannan ta cigaba da baccinta, Samira ta kwashe da dariya ta ce
"Da kyau, ai dole ki biya bashin baccin da baki yi"
Ba Azrah ta farka ba sai karfe 12pm itama kanta sai data yi mamakin kanta, wanka ta fara yi sannan ta fito ko kallon Samira dake tsokarta bata yi ba, wayan ta dake ringing yasa ta jawo ta ɗauka
Murmushi tayi ta ce
"Umma naa, ɗazu kun kira ai bacci nake yi" Umma ta ce
"Just wanna say congratulations ne, Allah yasa kin rubuta a sa'a" bata kai ga amsawa ba sai ga muryan Zahra
"Ya Azrah.. kin taso ne? Ki cemin kawai kina jirgi" dariyar da bata yi niyya bane tayi ta ce
"I'm sorry Zahra sai nan da 6 Days, sun ce sai mun jira result ɗinmu ya fito, wanda basu da matsala ne za'a sake su tafi gida" Zahra ta taɓe baki ta ce
"Ni gaski na gaji da jira" Umma dake gefenta ta ce
"Kuka yi wajan shekara baku tare shine 7 days ba zaki iya kara mata ba, toh sannu Zahra" Azrah ta ce
"Toh ai shine" Umma ta ce
"Toh Allah sa hakan ya zama alkhairi, Allah baki sa'a" ta amsa da Amin sannan ta miƙawa Samiran wayan suka gaisa da Umman.
Tun daga wannan ranan haka Azrah ta mayar da schedule ɗinta kamar wata princess, daga bacci sai kuma sallah da cin abinci, ko tashi bata son yi, ita kanta har mamaki take yadda take wannan baccin, duk wani ramar da tayi during exams period duk ta mayar da jikinta harda kara wani kiban, dan ko fita bata yi sai idan Khalil ya zo duba ta ne
Kwanaki bakwai sun wuce kamar mintuna, musamman ga Azrah da zuciyarta ke cikin wani irin tseren murna da fargaba bata da buri kamar ta ganta a gida, A ranar da aka ce za a fitar da sakamakon, tun da safe aka fara jin hayaniyan students a cikin hostels hatta makarantar ma sai data ɗauki wani sauti na musamman duk yawancin students dake offK ma duk sun shigo, kowa da sabuwar shelar sa, wasu na fargaba, wasu na fatan alheri, wasu kuwa ba sa cewa komai duk da dai zuciyarsu a ciƙe take da fargaba
Azrah ta farka da wuri fiye da kullum. Ko data yi sallar asuba bata koma bacci ba kamar yadda ta saba, sai ma wanka da tayi, ta ɗaura doguwar rigar cotton mai launin sky blue, ta ɗaura light veil, ta zauna bakin window tana jiran lokacin da za a fitar da result, bakinta kuma bai bar ambaton Allah ba
Kamar da misalin 10:35am ne aka fara tura sakamakon ta online platform ɗin makarantar. Kamar wani mugun abu ya faru a cikin School ɗin, aka fara jin ihun ''I passed!'' daga ɗayan hostel ɗin, Samira ta shigo da gudu tana cewa ''Azrah! Azrah! Check your result please! They've started uploading!''
Azrah ta fara danna wayarta hannunta na rawa. Password ɗin kanta ma sai da ta kusan mantawa, Sai da ta shaki iska sau biyu kafin ta sake shiga portal ɗin tana addu'a ta danna result section...
First Class Honors CGPA 4.88/5.00
Best Student of the year Department of Business Administration
Ji tayi kamar wacca aka datsa ta a wajen, zuciyarta ta tsaya na wani dakika, Sai hawaye suka fara tsintiri suna sauka kan fuskanta, ta toshe bakinta da hannayenta biyu, sai kuma ta fashe da kuka sosai, Kukan da ke tattare da shekara guda na wahala, rashin bacci, tashin hankali, da ƙoƙari amma sai yanzu ya mamaye da abinda take buri, burin samu, wato ta tsinci kanta cikin wani irin yanayi na farin ciki ne, Samira ta rungumeta tana cewa, ''Azrah you did it! Wallahi kin ci ubansun! I'm so proud of you!''
Itama tayi wrapping hannunta a bayan Samira tana sake fashewa da kukan kuma meanwhile tana dariya ta ce
"Samira ki ce min ba mafarki bane, please ki faɗa min Samira, Ya Allah..... Alhamdulillah! Alhamdulillah!! Alhamdulillah!!!"
Kan kace me har neighbors ɗinsu sun fara shiga suna mata murna
Bayan ta samu nutsuwa ta kira Umma, tana ɗaga wayar muryarta na rawa
''Umma… result ɗinmu is out Umma... na fito da first class... I'm the best in my department...''
Umma was speechless at first sai kuma ta ce
"Alhamdulillah ya Allah, Allah mun gode maka... Ma Shaa Allah Azrah, Congratulations, In Shaa Allah kuma da wannan first class din zaki gama makarantar"
Zahra data shigo daga waje ta tsinci reply ɗin Umma hakan yasa ta fahimci me ke faruwa ta saka ihuu ta ce
''Allah ya saka miki Ya Azrah, wallahi baki taɓa bani kunya ba... Dan Allah ki bari sunanki ya zaga cikin India kamar yadda ya zaga anan, Ni kuma nayi ta bragging da sunanki" ta kare maganar tana dariya da karfi
Azrah tayi dariya ta ce
"Nagode Zahra, yanzu ki kwantar da hankalin ki gobe ko jibi zan dawo amma sai na tafi scholarship unit tukun zan san yaushe zan dawo, a haka suka gama wayan cike da farin cikin
Samira dake kallonta ta ce
"Khalil fah? Ki kirasa"
Azrah ta yi screenshoting ta tura masa, immediately taga ya buɗe dan yana online, next thing kawai taga kiran Khalil ya shigo, ta ɗaga ta kai kunne ya ce
"Hey Azrah, wlhi I'm very proud of youuuu, Ma Shaa Allah, Congratulations" Azrah tayi murmushi ta ce
"Thank you" Ji tayi ya katse kiran, ba'a wani ɗauki time ba sai ya sake kira tana ɗauka ya ce ta fito yana bakin hostel, ta ɗauki veil ɗinta ta rufe kanta sannan ta fita ta same sa, tun kafin tayi magana ya ce
"Ai ba zan iya magana ta waya bane, kai I'm super proud of you Azrah, I told you, babe! I told you all the strees will pay off!''
Azrah ta ɗago kanta, tana murmushi mai haɗe da hawaye, ta ce
''I didn't just make it… I conquered''
Khalil ya gyaɗa kai, yana kallon ta kamar bai taɓa ganinta ba, ya ce
''Azrah, kin zarce duk wata expectation da nake da ita akan ki, I'm genuinely proud of you''
A cikin hour guda kacal, department ɗinta ya cika da congratulatory messages, dama su haka suke saboda yadda suke ɗaukan karatu da muhimmanci, Lecturers sun kirata har da wasu da bata tsammanin suna ma kula da ita. Ana yi mata kallon 'model student" Hatta school page ta saka ta a official handle ɗinsu da rubutu ''Student of the Year'' na IG ɗinsu
A daren ranar, Azrah ta koma dakinta. Ta kwanta a saman gado, tana kallon ceiling da murmushi yana yawo saman fuskarta, sai kawai ta ce a ranta
''Every tear, every pain, every sleepless night… it was all worth it''
Zata rufe idonta kenan tana gyara kwanciyarta kawai taji murya Samira ta ce
''Bari na faɗa miki gaskiya wahalan da kika sha? It has paid off completely''
Episode 34: The Final Hours
Washe gari, da dakyar Azrah ta buɗe idonta daga baccin mai nauyin da take yi, ganin hasken daya haska mata fuska yasa ta saka hannu tana tarewa dan windown nasu a buɗe yake, juyawa ta sake yi ta ɗayan side ɗin ya sa ta ɗan lumshe idanunta don cigaba da baccinta sai kuma nan da nan baccin ya sake ɗauke ta, Amma nan take sai ta ga kiran Khalil a waya yana doka mata, buɗe idonta ta sake yi, ta ɗaga kai ta kalli agogon ɗakin dake nuni da karfe 9 na safe, ta miƙe a hankali, tana jin jikin nata kamar ba nata ba saboda gajiya, amma zuciyarta cike take da murna, bin ɗakin tayi da kallo ko ina an gyara shi fesfes kuma Samira bata nan hakan ya nuna mata cewa fita tayi
Azrah ta nufi toilet ta yi wanka, sannan ta fito da fresh feeling, ta ɗauki wayarta ta shiga WhatsApp. Duk da cewa tana jin gajiya, ba za ta iya barin messages ɗin congratulatory daga abokan department ɗinta ba duk da ba wai wani shiri suke ba, bin new messages ɗin tayi da kallo tayi scrolling ganin yawan su
Ta fara reply ɗin kowanne message, tana amfani da dan mix na English da kuma yadda ta koyi godiya da Hindi, ko wani chat ta shiga abin da take typing kenan har keyboard ɗinta ya saba tana fara typing zai fito mata 'Thank you so much, I appreciate it! God bless you too!' har ta gama yawancin replies ɗin kenan
A nan ne Samira ta buɗe kofar ɗakin ta shigo, Azrah ta ɗaga kai tana kallonta ta ce
''Barka da safiya!''
Samira ta yi murmushi ta ce
''Kin samu kin tashi yanzun kenan?''
Azrah tayi frowning face ɗinta ta ɗan ja tsaki ta ce
''Khalil ne ya ɗaga ni da ɗan banzan kiran da ya dinga mi'' Samira ta gyada kai tana murmushi ta ce
''Kee kuwa, wannan ɗan Egyptian ɗin naki, kullum yana tayaki hira ne fah, nothing more''
Jin furucin Samira yasa Azrah ta komar da hankalinta kan wayarta, dan tasan Samira magana ta faɗa mata, yanzu kuma bata da strength ɗin magana
Samira ta dibar musu breakfast a plate, ta kawo musu ta ce 'sauko mu ci' amma Azrah ta ci gaba da chatting ɗinta kamar ma hankalinta baya tare da Samiran ne, har Samira ta gama ci Azrah bata ɗago ba, zuwa tayi ta ɗebo mata a wani plate ta ɗan yi dariya ta ce
''Yanzu kam, kin gama exams, ko cin abincin ma sai an roƙe ki ne ban sani ba?" Ta karasa maganar tana miƙa mata plate ɗin abincin
Azrah ta yi murmushinta mai sanyi ta ce
''Na gode Samira, amma bari na karasa replying abinda nake typing sai ɓaci"
Samira ta ƙwace wayar a hannunta, ta ajiye abincin a kan gado kusa da ita ta ce
''Gashi ki ci, wayan ki kuma sai kin gama zan baki''
Azrah ta yi murmushi ta soma cin abincinta a hankali, tana jin wani irin farin ciki yana lulluɓe zuciyarta cike da solace da tranquility na nasarar da ta samu duk sanda ta tuna
A haka har ta gama cin breakfast, ta ɗaga plate ɗin ta nufi wajen da suke tare kayan wanke wanke ta ajiye, sai ca wayarta ya fara ringing, Samira ta mika mata, Azrah ta karɓa da ɗan mamaki, ganin har sannan Khalil ne
"Madam, sleeping har yanzu? Sbd babu exams ai mun shiga uku da wannan baccin naki kuma'' ya ce da dariya a muryarsa
Azrah ta ɗan yi murmushi
"Ya na iya toh?"*
Ya ce "Toh ki fito gani a bakin hostel ɗinku zaki raka ni''
Kamar zata tambaye sa ina ne, amma ta fasa, ta ajiye wayan a bedside, already tayi wanka kawai ta buɗe sip, ta ɗauki wani maroon abaya, ta saka, tayi rolling veil ɗin sa, ta ɗauki wani fashion designer bag black color, ta saka wayarta a ciki, sannan ta ɗauki flat black shoes ta sanya a fararen kafarta
Tun da take shiryawa, Samira ta tsaya kallonta kamar wata Tv, tagumi tayi tana mamakin yadda ko wani irin shiga ke karɓan Azrah, yanzun ma tayi kyau sosai, harta gama, Azrah data gama shirinta ta ɗan kalli Samira
"Bari zan fita, zan ɗan raka Khalil ne''
Samira ta washe baki ta fara dariya ta ce
"Ahhh, ki ce dai zaku fita on a date ne ko?"
Azrah ta buɗe ido sosai tana kallon ta cike da mamaki ta ce "As how kenan? Rakasa fa kawai zan yi, ko baki ji Meta ce bane"
Samira ta kyalkyale da dariya ta ce
"Irin wannan kyau idan ba fita on a date bane, ina zuwa toh? Sannan ai saiki sa dan mutane ya zuzuce a hanya"
Azrah ta buɗe kofar ta fita, ba tare da ta sake kula da Samira ba, tana fita taga Khalil yana tsaye a bakin hostel ɗinsu, inda ya saba jiranta, Kallonsa ta tsaya na ɗan seconds, saboda ba karamin kyau ya mata ba kafin ta karasa inda yake tsaya
Shima idonsa akanta ne, fuskar sa cike da murmushi, harta karasa ta yi masa sallama, ya amsa da murmushin sa mai kyau ya ce
"Kin yi kyau fiye da ko yaushe Azrah, dama karatu ke biye miki kyau haka?"
Azrah ta murmushi ta ce
''Thank you, kai ma kayi kyau ɗin ai sosai''
Yayi kasa da muryarsa kaɗan ya ce
"Ban kai ki ba, Azrah"
Azrah ta yi dariya sosai, har sai daya mayar da ita TV, ta tsakaita dariyarta ta ce "Ina Nigerian kana Egyptian kace nafi ka kyau?"
Khalil kawai yayi replying din ta da murmushi, daga nan ya ce "Mu je''
Tana kallon sa ta tambaya sa da *
"Ina?"
Ya ce "Raka Ni zakiyi mall"
Da farko ta nuna ba zata je ba, da kyar ya yi convincing dinta, har ta yarda,
Inda yayi parking motar wani abokinsa suka karasa, ya buɗe mata front seat ta shiga, sannan ya zaga ya zauna a driver seat tana jin zuciyarta na bugawa da karfi, ji take kamar za ta kurma ihu amma ta riƙe kanta
Azrah ta kasa zama comfortable a motar, duk da cewa tana jin wani irin natsuwa cikin zuciyarta, wanda ke ɗan sauƙaƙa mata damuwar amma inaa ta gagara zama comfortable, Khalil ya tada motar a hankali sannan yayi reverse suka fita daga makarantar yana mata hira dan yaga yadda ta takure kanta amma duk tambayoyin sa da murmushin sa, Azrah ta gagara amsa masa sai dai tace 'Uhm ko U'um'
Bayan wani lokaci, suk isa wani babban mall, Khalil yayi parking ya buɗe mota ya sauka, Azrah ma ta buɗe ta fita, hannunta ɗan ɗauke da jakka ta, Suka shiga cikin mall ɗin, Khalil ya ɗauki cart, ya miƙa mata ya cs
''C'mon, ɗauka ki taimaka min mn''
Ta tsaya kallon sa kawai, yayi saurin cewa
"Tsaraba zan ma Mami na da kuma kanwata mai 17 yrs fah, Ni kuma wani irin zan ɗauka musu ina namiji pls, ki taimaka min ki zaɓa musu Kinsan ku mata ku fimu iya sanin kaya. Sai kuma ki ɗauki yadda zan iya tafiya da su kar a hanani a airport… but masu tsada pls''
Jin hakan yasa Azrah ta cart ɗin a hannunsa ta fara ɗaukar kaya masu tsada, har da perfumes masu tsada da kayan bacci sai gowns dan tasan su Egyptian zasu so tunda daily dress dinsu knn, Duk sanda ta ɗauka, Khalil zai kalli kayan da ta ɗauka, sai murmushi ya bayyana a fuskar sa, yana tabbatar mata cewa yayi kyau kayan, a haka suka ci gaba har suka gama shopping ɗin, suka biya duk kuɗin, aka ɗauki kayan aka kai booth.
Bayan su ɗan yi tafiya Khalil yayi parking a wani babban eatry y ce
"Mu shiga mu ci abinci dan yunwa na fara ji'' daga haka ya kashe motar ya juya yana kallonta ganin ko attempt ɗin sauka bata yi ba ya sake cewa
''Mu sauka ko?"
Amma Azrah taki, Duk yadda Khalil ya yi mata dan convincing dinta da murmushi da words amma ko kulawa bata yi, daga karshe ya sauka daga mota, ya wuce shi kaɗansa ya shiga ya siya musu takeaway, ice cream da snacks, sannan ya dawo ya tada mota.
A hanya, Azrah ta kasance cikin shiru, kamar dai yadda suka tafi, har suka koma cikin school ɗin, wannan ranan ne na farko data fita daga school zuwa cikin garin india, har bakin hostel ɗinsu yayi parking, Khalil ya sauka ya sauke kayan booth ɗin wanda ta yi shopping da wanda ya siya masa shima, kallon sa kawai ta tsaya yi ganin ya sauke kayan kasa
Ya ce da murmushi
"Please don't say no, ki kaiwa Umma da Zahra tsarabar pls"
Azrah ta girgiza masa kai da sauri tana jin zuciyarta na bugawa, ta ce
"No Khalil, Noo please" amma Khalil bai daina roƙon ta ba, daga baya, kawai ya shige motar ya bar wajan, ya bar ta da kayan a kasa, ba yadda zata yi dan ta kwashe
Ta karasa ta kwashe kayan, ta shiga da su ɗakin su. Samira dake kwance ta mike zaune tana kallon manyan ledojin baki da Azrah ta shigo da su baki buɗe, da sauri ta sauka daga kan gadonta ta buga uban tsalle ta ce
"Yess, nace miki dama date zaku fita amma kina wani ɓoyewa min''
Azrah ta ɗan yi murmushi, amma zuciyarta cike da damuwa ta rasa yadda zata yi da kayan
Samira ta fara bubbuɗe kayan a hankali tana kallon su daya bayan daya, ta ce da muryar mamaki
"Ya Allah.. wallahi expensive kaya ne! Kinga wannan designer ɗin Yaya na ya saka a lefensa" tana nuna jakar da Khalil ya ɗauka da kansa, Sai kuma ta juya ta nuna mata wasu kayan da murmushi har sannan a fuskar ta, tace
"Nima kayan da Deen yake tarawa na lefe in faɗa miki harda wannan''
Ta karasa maganar tana ɗaukan wani jakka mai kyau, tana kallon sa da kyau, sannan ta ɗauki chocolates daga wani laida ɗin ta ajiye a gefe, amma sai mood ɗinta ya baci tunawa da Maman Deen ta ce da muryarta dake nuna takaici
"Da badan shegiyar Maman Deen da bata so na ba ai da tuni anyi auren mu''
Azrah ta ɗan yi murmushi mai sanyi tace
"Ki cigaba da addu'a kawai, idan alkhairi ne, ba yadda zata yi za'a yi auren, idan kuma babu Alkhairi Allah baki wani wanda ya fi shi Samira"
Daga wannan maganar Samira bata kara kulata ba sai ma miƙewa data yi ta jawo kayan Azrah ta fara jera mata kayanta a trolley ɗin da zata koma da shi Nigeria, Azrah ta ɗabar mata chocolates sai kuma wani flat shoe da Abaya, da ƙyar ta karbi chocolates ɗin amma fir taki karɓan sauran
Can yamma suna zaune suna hira sai ga wayan ta ya fara ringing, Azrah ta ɗauka, taga Khalil ne, tana ɗauka tun kafin tayi magana ya ce
"Come on, we need to head to the scholarship unit now, Or are you going to wait here until next semester start? Or you'll wait for me?"
Azrah ta yi dariya tace
"Gani fitowa" sannan ta sauya kaya zuwa riga da skirt na atampa, ta ɗan ɗaura veil a kai ta ɗauki jakkanta, ta saka wayarta cikin jakar, ta fita daga hostel tana jin natsuwa da wani irin excitement a zuciyarta ko dan zata gida ne ohi
Tunda ta fito ya kafe ta da idanu hatta isa ya ce "This your Nigeria attire… it looks amazing on you, You look more beautiful than ever"
Azrah ta ɗan yi dariya, tana jin zuciyarta na bugawa da sauri, daga haka suka fara tafiya, suna hirar cike da kulawa, Khalil na faɗa mata yadda zaiyi missing ɗinta idan ta tafi
Suna isa scholarship unit, Khalil ya taimaka mata wajen clearing, yana ɗaukar duk wasu takardu, tickets da sauran abubuwa. Duk wani abu da zai buƙaci kulawa kafin tafiya ya gama, bayan an gama da su, suka karɓi document ɗin khalil ya tsaya kallon time ɗin da jirgin zai tashi da kuma yaushe zasu tafi, yana kallonta ya furta mata "jirgin ku zata tashi gobe da yamma"
A hanya ta komawa hostel Azrah ta gagara rufe baki saboda murna komawa gida gobe, godiya ta fara masa tana jin dadin yadda yake taimaka mata a abubuwa da dama irin haka, ɓata rai yayi ya ce baya so, tunawa gobe warhaka basu tare ta ji wani ɗan damuwa a zuciyarta game da barinsa da rabuwa na ɗan lokaci
Tunawa da hakan yasa nan da nan mood dinta ya canza, sai dai kuma sabuwar yanayi da yadda zata sake ganin Umma da Zahra yasa ta danyi murmushi, duk da haka, hirar Khalil da kulawarsa na sa ta jin wani irin comfort da assurance cewa komai zai daidaita ko ta koma gida ba rabuwa zasu yi ba
Episode 35: Sunrise and Goodbye
Azrah ta shiga hostel ɗin su cike da farin ciki, taga Samira na girki, dan Samira bata wasa da ciki, Samira ta ɗaga kai tana kallonta, fuskanta cike da mamaki sannan ta fara jero mata tambayoyi lokaci guda
"Har kin dawo? Kun gama kuma? Yaushe ne tafiyar naki suka ce?"
Azrah ta ɗan yi murmushi a hankali ta ce
"Gobe around 4 pm, In Shaa Allah''
Samira ta zaro ido, tana ɗan girgiza kai ta ce
"Azrah kina nufin gobe zaki tafi? Gobe gobe wai? Haba manaa!"
Azrah ta yi dariya ganin reaction ɗin Samira, ta ɗan girgiza kai ta ce
"Da ta nine ma da tun last week na tafi wllh"
Samira ta yi tagumi tana kallonta, fuskar ta cike da ɗan damuwa, ita kuwa Azrah ta karasa cikin ɗakin, ta fara ajiye traveling documents ɗinta cikin jakar hannu, sannan ta cire kayan jikin da suka yi mata nauyi, ta saka wani simple gown mai laushi, ta zauna kan gado, ta fara ƙoƙarin kiran Bappah amma sau biyu take trying bai shiga ba, sai ta ajiye wayar a gefen gadon ta lumshe idonta, ta kwanta tana jin wani excitement a zuciyarta, amma tana tunawa Khalil sai yaji ba daɗi, cikin shiru na ɗan lokaci, zuciyarta na yi mata tunanin ''Gobe zai kasance wani sabon farkawa… Sabuwar rana, sabon gida, sabuwar natsuwa… In Shaa Allah komai zai daidaita'' murmushi tayi ta miƙe zuwa toilet..
Washe gari.... da asuba tun karfe 4am Azrah ta farka, ba kamar kwana biyu da sai dakyar Samira zata ɗaga ta ba, zuciyarta na cike da wani nauyi da excitement a lokaci guda, sauka tayi a kan gadon ta nufi toilet, ta fito bayan tayi alwala, nafila ta fara bayan ta shimfiɗa dadduma, bayan ta idar ta zauna kan sallayan tana jiran a kira asuba, can ta miƙe ta je ta ɗauki Qur'an ɗinta a hankali, sannan ta fara karatun Alkur’ani, da muryarta mai laushi da tsantsan daɗi, ga shi duk wani harafi da lazafinsa ta san yadda take fito da su
Can sai ga Samira ta farka, ta miƙe zaune tana bin ɗakin da kallo, fuskanta cike da mamaki, take kallon Azrah dake zaune kan darduman, murmushi tayi ta ce
"Eh lallai, dake kinsan yau zaki tafi gida, shine harda wani tashi da wuri haka? Sannu Azrah''
Azrah tana karatun Alkur'ani bata san sanda tayi murmushi ba, amma zuciyarta cike take da natsuwa, jin za'a shiga sallah yasa ta miƙe kawai ta fara yi, ta idar da sallar, tana jin ƙwarin gwiwa a jikinta
Sai ga kiran Bappah ya shigo wayarta, da murmushi take kallon wayan ganin Bappah ne
Azrah ta ɗaga wayar, ta kai kunnen da sallama ɗauke a bakinta. Kafin ta gama sallamar sai ga muryar Bappah yana "Hello" A lokaci guda kuma ta ji muryoyin Umma da Zahra suna magana a gefe, alamar sun saka wayar a handsfree ne
"Assalamu alaikum Bappah'' ta ce, tana murmushi.
"Wa alaikum salaam Azrah, ya shirin zuwan naki?" Bappah ya tambaya cikin muryar kulawa
"Alhamdulillah Bappah, Anjima ne ai In Shaa Allah'' Azrah ta amsa
Sai ta ji muryar Zahra "Yaya Azrah, yanzu dare ne ko a wajan ku?"
Azrah ta ɗan yi dariya a hankali ta ce
"Aa, asuba ne, ai mukan nan 12am ne ba?"
Zahra ta ce "Ehh, kenan a wajan mu sai gobe zaki zo, ai shiyasa nace ma Bappah ya gwada kiran ki yanzu kafin mu kwanta''
Ta ɗan yi murmushi ta ce "Toh bawa Umma wayan mana"
Tun kafin tayi magana Umma ta ce
"Assalamu alaikum Azrah''
Azrah ta ce "Ohh Umma, gobe In Shaa Allah warhaka ina tare da ke"
Bayan sun ɗanyi hira da Umma, Zahra ta tambaya
"Me za'a dafa miki?"
"Anything" Azrah ta amsa cikin shauƙi, tana jin farin ciki da natsuwa.
Bayan sun yi sallama, Azrah ta ajiye wayar, ta karasa azkar ɗinta cikin sauri dan bacci sosai take ji kuma, ta miƙe ta cire hijabin jikinta, sannan ta kwanta a gadon, Nan da nan bacci ya sake kwashe ta
Samira bata yi ƙoƙarin daga ta ba, kawai ta ayyana a ranta cewa za ta tashe ta 10am, tunda har jirgin su sai yamma zai tashi.
Da misalin ƙarfe 2:40pm, sai ga Khalil ya iso bakin hostel ɗin su da mota.
Azrah dake zaune suna hira da Samira wayanta yayi ringing, zuciyarta na ɗan buga da sauri tayi picking call ɗin, dama kuma tun da wuri suka shirya, shi ɗin dama suke jira, kawai so take ta ganta a airport ko hankalin ta zai kwanta, ta kai wayan kunnenta da murmushi a fuskarta, Khalil ya ce
''ku fito gani a bakin hostel ɗin ku" ta ce
"Okay gamu fitowa" daga haka ta kashe kiran
Samira ta ɗaga mata jakkanta ita kuma ta rike handbag ɗinta wanda komai na tafiyar ya kasance a ciki yake, Suka fito daga hostel, Khalil dake motar yana yana jiran su suna fitowa ya sauka daga motar
Khalil ya karɓi akwatin hannu Samira, suka gaisa cikin mutuntawa, sannan ya saka jakar a booth na motar Azrah ta bude gaban motar ta shiga, Samira tana ta shiga bayan motar, Khalil ya shiga mazaunin driver, ya tada motar, suka bar makarantar
Tafiyar minti 40 suka isa cikin Indira Gandhi International Airport, New Delhi, bayan Khalil yayi parking duk suka sauka, Khalil ya shiga tare da Azrah har zuwa cikin hall ɗin masu tafiya, Samira na binsu a baya dan ta basu space sosai, ya tsaya sosai wajan ganin komai ya zo mata da sauki, yana rike da jakkanta yayin da suke bi ta check-in counter, Bayan an tara duk takardun tafiyarta, an duba tickets, passports, da boarding pass, Khalil ya tabbatar da cewa baggage ɗinta an karɓa cikin sauƙi, sannan ya miƙa mata boarding pass ɗinta da passport ɗinta cikin hannu.
Bayan haka, suka nufi security check, inda Azrah ta miƙa jakar hannu ta shiga scanner, wayarta da charger sai ear ring ɗjnta an saka a separate tray, sannan ta wuce ta metal detector, Khalil ya tsaya kusa da ita, yana kallonta, yana tabbatar da cewa komai lafiya daidai
Sai suka wuce immigration desk, inda Azrah ta gabatar da passport ɗinta, aka duba visa, an tambaye ta wasu tambayoyi masu sauƙi game da tafiyar, sannan suka buga stamp ɗin fita, Khalil ya murmusa yana kallonta ya ce
"All done, Azrah"
Murmushi tayi daga haka suka nufi departure lounge, inda mutane ke zaune suna jiran flight, Khalil ya raka ta har zuwa gate ɗin boarding, ya tsaya yana kallonta, idanunsa cike da seriousness
"Safe flight Azrah" ya ce
"Thank you so much" ta amsa,
zuciyarta na ɗan bugawa da sauri
"Please, idan kin koma gida, kada ki manta da ni… Ko kuma ki ki daga kira na" ya ƙara murmushi a fuskar sa
Azrah ta yi dariya, ganin seriousness ɗinsa ta ɗan sassauta muryanta ta ce
"Ohh Toh sai na manta" dariya yayi ya kuma cewa
"Idan kin koma gida, akwai wani magana da nake so muyi… pls" ya ce muryarsa cike da ɗan rauni
Azrah ta tsaya kallon sa, zuciyarta ya dinga bugawa da sauri, ta sauke idonta kasa ta ce
"bye-bye, ina sauka zan kira ka" tana hana kanta hawaye, Khalil ya juya ya bar wajan ba tare da ya yarda ya sake kallonta ba
Ta tsaya ta bisa da kallo harya ɓace ma ganinta, ta kuma cigaba da tsayuwa a wajan har na ɗan wani lokaci tana kallon inda ya bari, sannan ta juya ta shiga cikin gate ɗin, zuciyarta cike da wani nauyi na rabuwa
Da ta hau cikin jirgi, ta nufa kujerarta ta zauna kusa da window, tana kallon fasinjojin da suna shiga, Da jirgin ya fara tashi, Azrah ta lumshe idonta, ta ji wani irin ƙuncin a zuciyarta ta rasa kuma meke damunta, a haka har jirgin ta fara daidaita kanta a sama, ji tayi kamar ta bar wani ɓangare ne na jinkinta a wajan
Tana kallon hasken birnin New Delhi daga sama, zuciyarta na haɗuwa da tunanin daya addabeta ga kuma excitement na ganin Umma da Zahra, amma kuma damuwar rabuwa da Khalil ta sanya ta jin wani irin emotional tug da ba zata iya faɗi ba
Da jirgin ya fara tafiya a sama, Azrah dake zaune window seat, hannunta ta ɗaura a kan armrest, idanuwanta na kallon birnin New Delhi daga sama. Rana dake ƙoƙarin faɗi yana bayyana kowane gine-gine da tituna da motoci kamar ƙananan toys, ta ɗan yi numfashi mai karfi sannan ta lumshe idanunta sai bacci...
Flight attendants suka fara zagayawa, suna rarraba snacks da ruwa Azrah ta ɗauki tray ɗinta, ta ɗan ɗanɗana sandwich ɗin sai kuma ta ajiye, ruwa mai sanyi ta ɗan sha amma zuciyarta na cikin wani mood ne, Duk lokacin da ta kalli fuskar jirgin da ke facing ɗinta daga window, tunanin Khalil na sake dawowa mata fil
Bayan tafiya mai tsaho da suka yi, flight attendants suka kawo *
lunch/dinner tray, Azrah ta ɗauki abincin ta fara ci a hankali da nutsuwa, haka kawai taji yanzu kuma babu abun da take son gani sai Umma da Zahra
A cikin jirgin, lokacin da map a monitor ya nuna sun shigo cikin
airspace na Nigeria, flight attendant ya sanar:
"Ladies and gentlemen, we are now entering Nigerian airspace. Estimated time to arrival in Lagos is 1 hour and 15 minutes."
Azrah bata san sanda tayi wani murmushi ba, burinta dama ganin Umma ne, haka kawai taji tama koshi da abinci zata je ta samu na Umma
Flight ɗin ya ɗauki kusan 8 hours daga New Delhi zuwa Lagos sannan internal flight daga Lagos zuwa Katsina ɗin kusan 1 hour 30 minutes ne
Ta ɗan yi murmushi, sannan ta dubi window, tana kallon ƙasar da ke ƙasa kamar yadda take ƙara ganin wasu ƙananan gari da tituna, zuciyarta cike take da murna
Da jirgin ya sauka a Katsina Airport, Azrah ta ji farin cikinta ya ninku, zuciyarta na bugawa da sauri duk da gajiya, kawai so take ta ganta a gida, ta ga Umma da Zahra kuma ba tare da bata lokaci ba ta rungume su duka biyu, sauka ta fara daga jirgin tana shakan iskan garin, gani take kamar mafarki
Bayan ta sauka, ta fara tafiya zuwa inda jakkanta yake, zata ɗauka, amma jiri take ji bata san me ke faruwa da ita ba, tafiya take bata ganin gabanta kawai ta bugi wani mutum, ta yi saurin ja baya ta fara bashi hakuri ba tare da ta kalli wanda ma ta buga ba
Muryarsa yasa ta ɗaga kai tana kallonsa da mugun mamaki
"This is not the only time kike wannan abun ko da yaushe idan kika ganni, sai kinyi wani abu da zaki calling attention ɗina zuwa gareki, Me zanyi da ƙazama jahila irin ki, Ko da kike aiki a gidanmu, kin taɓa ganin na kalli inda kike ne, balle kiyi tunanin har ni zan so ki, ki cire wannan tunanin da Suhaila ta saka miki akai"
Azrah banda Kallonsa babu abinda take yi, zuciyarta ta dinga bugawa da sauri da sauri, ta ji ranta ya mugun ɓaci, kalamansa sun ƙona mata rai, ta ɗan kalli wajan dan ganin ko ana ganinsu, ganin babu wanda yake ta kansu, sai ta juya ta ci gaba da tafiyarta ba ta ji zata iya sake bashi hakuri ba, balle ta tsaya ta yi magana da shi tunda ya zageta, kuka take son yi amma tayi kokarin hana kanta yi
Saif da shock a fuska ya bita da kallo, sannan ya saurin cewa
"And stop acting like this, dan kin samu har kin taho airport tarɓan wanda kike musu aiki, ba shi ke baki daman haɗa kafaɗa da kowa ba, Mind you ko a hanya karki sake kallona!"
Azrah ba ta juya ba, harta isa wajen ɗaukar trolley ɗinta ta fita, ta tara taxi, ta saka akwatin ta a booth, sannan ta shiga bayan motar ta zauna
Sai kuma ta hango Saif yana waya yana nufo inda suke da alama shima akwai wanda yake nema, idanuwansu suka haɗu ta banka masa harara tare da murguɗa masa baki, sannan ta ɗauke kanta daga side ɗinsa, Saif ya ɗan ɗauki lokaci yana kallonta da mugun mamaki, ko wani move ya kasa, kawai ta cigaba da wayarsa, yayin da taxin ta fara tafiya daga airport din
Ga ba ɗaya zaman Azrah a taxi ɗin nan bata san ma ina take ba, ba kaɗan ba ta faɗa duniyar tunani tana kara jin tsanar Saif har can kasan zuciyarta
Har suka shigo unguwarsu bata sani ba, sai da Mai taxi ya tambaye ta ina ne layin kafin ta dawo reality, taxi tana parking a kofar gidan su, yaran da suke wasa a wajan suka taho da mugun gudu ganin ita ce suka fara ihu suna tsalle tsalle
"Azrah! Azrah, Azrah ta dawo daga India, Yeeeee ta taɓa ganin indiyawa"
Azrah ta fara musu dariya, tana amsa gaisuwar su, duk sun cika unguwar da ihuun su har makwabta sun fara lekowa dan gulma, sauke akwatin ta tayi ta bawa mai taxin kuɗin sa, yaran kuma suka ɗauka mata akwatin suka yi cikin gidan da shi
#Jiddatulkyar writes
08110615256
Episode 36: Homecoming and heartstrings
Mama da Siyama suna tsakar gidan, suna girki cikin annashuwa. Siyama na bada labarin faɗan da aka yi a garage ɗin, lokacin da suke je Tallah, tana yi tana demonstrating yadda abun ya faru cike da dariya, Mama ma na biye mata tana dariyan, cigaba tayi da bata labarin amma kafin ta gama, sai yara suka shigo gidan cikin hayaniya suna ihu
"Azrah ta dawo daga India!''
Mama da Siyama suka juya da sauri cike mamaki, idanuwansu na kallon yaran da wani irin expression da ke nuna tsananin mamaki da bakin ciki, Mama ta taɓe baki tana mai da hankali kan tankaɗen garin tuwon da take yi, kamar ba ta ji hayaniyar yaran ba
Zahra wani kara tayi ta fito daga ɗaki a mugun guje kamar wata guguwa, fitowan nata kuwa yayi daidai da shigowan Azrah, tana isa ta faɗa jikinta tana dariya kamar zasu zube ƙasa dan murna da ƙauna, Azrah ta daidaita kanta tana murmushi ta ce
''Ai sai ki kada ni kasa Zahra!''
Zahra ta amsa da dariya mai cike da kaunar 'yar uwarta "Baki san yadda na yi missing ɗinki ba ne"
Azrah ta kalli kofar ɗakin Mama taga suna zaune, ta ɗan tafi kusa da inda suke ta ce cikin muryan murna ta ce
"Mama ina wuni, Barka da gida'' Mama ta ci gaba da tankade tankaɗenta kamar bata ji ba, Zahra na kallon Siyama ta ce
"Ya Siyama Barka da gida'' Siyama ta mata wani banzan kallo sannan ta dauke kanta, Azrah taji wani iri sosai a ranta kamar ba ita bace sometimes suke gaisawa a wayan Bappah
Zahra ta kyalkyale da dariya
"Ai toh kamata yayi ki wuce kije ki huta, amma kina wani abu kamar salalo''
Azrah ta kalle ta irin tayi shiru, Zahra ta ce "Eh mn maganar gaskiya kenan''
Zahra ta kama hannunta ganin duk yadda jikin Azrahn yayi sanyi suka fara nufa hanyar ɗakinsu
Yaran da suka shigo da kayan Azrahn ne suka tsaya Azrah ta kalli Zahra ta ce
"Pls Zahra Idan akwai chanji, ki basu''
Daga haka Azrah ta wuce ɗakin Umma ta shiga zuciyarta yearning to see Umma, tana jin wani nutsuwa yana rasa zuciyarta cike da abubuwa daban-daban farin ciki da kuma ƙauna
Da gudu Azrah ta faɗa kan Umma dake zaune kan sallaya, alamar ta idar da sallar La'asar ne, Umma ta rungume ta a hankali tana jin wani farin cikin ta ce
"Welcome back Azrah"
Azrah ta janye kanta daga jikin Umma tana kallonta cike da shauki ta ce
"Wallahi Umma na yi kewarki fiye da yadda na ake tunani, kai fiye da tunanin mai tunani ma" Sai kuma ta sake mayar da kanta jikin Umma tana dariya cike da annashuwa
Umma ta murmusa ta ce
''Ni ma na yi missing ɗinki, Sai da na ji jikin rashin ki''
Zahra data gama sallamar yaran suka tafi ta shigo ɗakin tana kallon su tayi sauri ta ce cikin dariya
''Toh ai ya isa ko?''
Azrah ta juya tana kallon Zahra ta ce
''Sai ki hana ni toh! Shekara guda ban saka Umma a ido ba, naga ke tare kuke kwana''
Zahra ta ce
"Ohh ni kuma ina ruwa na, kawai dai nayi reminding ɗinki cewa Ni ce dai autar Umma"
Azrah tayi dariya ta ce "Dadin abin ba Umman ki ke kaɗai ba ne''
Duk suka yi dariya
Umma ta ce
''Azrah za ki yi wanka ko kuma ki fara cin abinci?''
Azrah ta miƙe tana cewa
"Bari na yi bacci tukun Umma, Kaina ke min ciwo, harda jirijiri nake ji''
Umma ta amsa da taushin murya "SubhanAllah , sorry toh, ki je ki huta"
Daga haka Azrah ta wuce ɗakinsu, Zahra kuma ta ɗauki akwatin ta ta bita da shi
Meanwhile....Bayan shigansu Azrah ciki, Siyama ta ɗaga kai tana kallon Mama dake tuka tuwon duk mood dinta ya ɓaci ta ce
"Hmm yanzu kuma sai yadda iyayi da rashin kunya da kuma jin tafi kowa ya karu kenan"
Mama ta amsa tana ci gaba da tuka tuwon ta "Ai sai karma ku gwada kun san tana yi ba, Inda take ba karku kalla, bare su ji daɗi, ba Shikenan ba"......
Azrah bata tashi daga bacci ba har sai da aka fara kiraye kirayen Magrib. Umma tana kallon Zahra ta ce
"Zahra Magrib yayi jeki taso Yayarki"
Zahra ta miƙe da sauri, ta shiga ɗakin su, gani tayi ma kamar Azrah ta farka, zata yi magana sai Azrah ta tashi, tana kallon Zahra ta ce cikin sanyin murya
"Bari na yi wanka yanzu kawai, sannan sai na yi sallah"
Zahra ta gƴaɗa mata kai da murmushi a fuskarta ta ce
"Toh bari na saka miki ruwan zafi"
Bayan ta fita, bata ɗauki lokaci ba, sai gata ta dawo, tana kallon Azrahn daga bakin ƙofa ta ce
"Ya Azrah ga ruwan a bakin ƙofa, Bana so na kai miki ban ɗakin ne, sai kin fito, idan ba haka ba kazaman can su bata miki ruwan"
Azrah ta ɗan yi murmushi mai tana kallon Zahra cike da mamakinta ta ce
"Har yanzu dai kina nan da wannan halin naki ko Zahra?"
Zahra ta kyalkyale da dariya ta ce
"Eh mana ai hakan ne mana, wallahi kazamai ne mana" Azrah ta girgiza kanta tana mamakin Zahra dai, Zahra kuma ta juya zata fita kamar ta tuna wani abu sai ta sake dawowa ta ce
"Ai baki san me ba, kafin Dada ta koma ko abincin su bata taɓa ci ba, ta ce ba zata iya cin abincin kazamai ba balle cuta ta kamata ta mutu" ta kare maganar tana mai sake fashewa da dariya sosai
Daga haka Azrah bata kara kulata ba ta juya zuwa wajan kayanta, buɗe akwatin tayi ta ɗauki shower gel, sannan ta fita wankan, Zahra ta kai mata ruwan ban ɗaki ganin ta fito, tana fitowa Azrah ta ce
"Thank you" daga haka ta shiga ban dakin
Bayan ɗan lokaci har an fara Magrib Azrah ta fito daga ban dakin, jikinta ɗan damp da turaren gel, tana kallon Mama, ta ce cikin sanyin murya
"Ina wuni Mama"
Mama bata kulata ba, ta ci gaba da tattare kayan da take kwashewa kamar ba ta ji taba, Azrah kuwa tana ɗan murmushi kawai ta wuce ɗakin su tana jin nutsuwa da jin daɗin dawowa gida, duk da dai rashin kulawar Mama.
Bayan tayi sallah, Azrah ta zauna gefen Umma, idanuwanta na kan fuskar ta cike da ƙauna da jin daɗi, Umma ta lura da kallon da take mata, ta ɗan zato ido ta ce
"Kallon kuma fah?"
Azrah ta yi murmushi mai kara mata kyau, ta ce
"Na ga wani kyau ne kika kara ai Umma, Ga kuma missing ɗinki da nayi cikin ƙwando ƙwando"
Umma ta ware ido sosai tana kallon Azrah ta ce
"Ke kinganki ne? Kinyi kiɓa sosai fah Ma Shaa Allah, kamar dai wadda bata san wahala, ga wani haske da kika kara"
Zahra dake gefen Umma tana kallon su tayi murmushi ta ce
"Ai Umma kin rigani faɗa ne kawai wllhi" amma tun ɗazu sai kallonta nake ganin yadda tayi wani kyau kamar dai an kara mata ne"
Azrah ta ɗan yi dariya tana gyara zamanta ta ce
"Chap! Ai baku ga yadda na rame ba ne? Kawai one week dana kara ne ya wani canza ni fah"
Zahra ta ce "amma Kema kinsan dole dama da zaki canza"
Azrah tayi murmushi bata ce komai ba kawai ta kwanta kan cinyar Umman tana jin wani sabon yanayi da nutsuwa
Umma da Zahra kuwa sai kallon wani sabon confidence data zo dashi daga India suke, ganin yanzu ta cire duk wasu abubuwan da daa take yi
Sun zauna suna hirar su cike da kauna, suna labari da jimamin yadda suka yi shekara ba tare da ganin juna ba, Zahra sai bata labarin abubuwan da suka faru take ita kuwa sai dariya take, Zahra ta tankwashe kafa tace sai dai Azrah ta bata labarin yanzu turn ɗinta ne, haka Azrah ta fara bata duk da agajiye take amma ta daure, suna tsakiyar wannan hira, wayar Azrah dake hannun Zahra ya fara ringing, ganin me kiran yasa Zahra miƙa mata.
Murmushi ya bayyana a fuskar Azrah ganin sunan Khalil a screen, cike da shauki ta ɗaga wayar ta kai kunne kawai, tun kafin ta fara magana, Khalil ya riga ta magana
"Don't you dare tell me you've forgotten me just because you're home"
Azrah ta yi dariya sosai wanda da alama ta manta da su, dan har sai da Umma da Zahra suka tsaya kallonta, tana jin zuciyarta na bugawa da sauri ta ce
"Me? No way! Bana jin daɗi ne shiyasa ina zuwa na kwanta bacci"
Khalil ya ce cikin kulawa
"Oh… how's your body feeling?"
Azrah ta ɗan yi murmushi cike da shauki ta ce
"Stress I guess, but now I feel better after sleeping"
"Ma Shaa Allah, Did you get home safely? How are Umma and Zahra?" Khalil ya ci gaba, muryarsa cike da kulawa.
Azrah ta ce
"They're fine, thank you Everything's okay, Alhamdulillah"
"Rest well Azrah, I'Il call later so I can greet them properly" Khalil ya ƙara cikin muryar sa mai kulawa
Azrah bata so hakan ba, amma ba yanda ta iya sai kawai ta amsa da
"Okay… "
Khalil ya kashe wayar, sai sanna Azrah ta tuna da tsarabar da ya bayar a kawo musu ta miƙe, ta wuce ciki don ɗauko tsaraban
Zahra ganin Azrah ta mike ta bita da kallo, tana ganin ta shiga ɗakin tayi kasa da murya tana murmushi ta ce
"Umma kin yi suruki fa da alama"
Umma ta amsa cikin dariya ta ce
"Ke komai sai kinyi bayani ne? Baki iya shiru bane?"
Fitowar Azrah da akwatin kayan ya sa duk suka yi shiru, sauke akwatin tayi ta ajiye sannan ta zauna
ta fara wawware kayan zuciyarta cike da ɗan excitement, Zahra da Umma kuwa, sai kallonta suke da mamaki
Bayan ta gama ciro kayan daga akwatin, ta ɗauko tsarabar da Khalil ya tsiyo mata wanda shi ya zaba mata ta ajiye a gefe, sauran kuma ta raba gida biyu, ta miƙa ɗayan wa Umma, dayan kuma gaban Zahra, tana cewa cikin murya da ɗan annashuwa
"Tsarabar ku, inji Khalil"
Umma ta dinga kallonta, idanuwanta cike da mamaki but very calm sannan ta ce
"Sai kuma kika karɓa Azrah?"
Azrah ta yi dariya ta ce
"A bakin hostel fah ya barsu ya tafi dana ce masa A'a , shiyasa kawai na ɗauka amma da banyi niyya ba"
Umma ta ce cikin taushin murya
"Dauki kayan bana buƙata nikam"
Azrah ta ɗan tsaya kallon Umma da mamaki tama ga gagara magana, Zahra kuwa sai washe baki take yi tana murmushi ga kuma ihuun da take yi idan taga wanda ya mata kyau, harda tsallenta laidan su chocolates ta buɗe da sauri ta rungume tana wayyo daɗi
Azrah ta ɗan yi tagumi, tana kallon Umma wanda da gaske ko kallon kayan bata yi ba tace bata so, ta ce
"Umma ko za a bawa su Mama ne… I mean Siyama da Hibbah suma tsarabar?"
Zahra ta fara dariya tana tafe hannu cikin mamakin halin irin na Yayarta ta ce
"Eh Lallai Ya Azrah, Yanzu sai ki kai musu? So kike ki kai musu da gaske?"
Azrah ta ɗan yi murmushi ta gyaɗa kai, Zahra ta ce
"Hmmm... Ke da kika tafi karatu, ina ke ina kai musu tsaraba in ba neman wajan zama ba da kuma nema ma kanki magana ace aina kika samu kuɗi"
Zahra ta sake fashewa da dariya mai cike da Mugunta tana kallon Umma ta ce
"Umma imagine, can you here Yaya Azrah"
Azrah kuwa sai harararta take jin yadda take dariyar
Umma ta dinga kallonta, sannan ta ce
"Azrah kanwarki tayi gaskiya"
Muryan Bappah suka ji a tsakar gidan, yana ta masifan waya bar buta a kofar gida, Azrah ta tashi daga zaunen da take, zuciyarta na bugawa da sauri ta juya tana kallon Umma tana cikin murmushi da excitement sai kuma ta miƙe tsaya da sauri ta fita da mugun gudu taje ta rungume shi da ƙarfi
Bappah kuwa ya yi dariya ganin ita ce, yana jin daɗin ganin ƙaunar data ke nuna masa, ta ce
"Bappah na tun ɗazu fah nazo" Bappah yana murmushi ya ce
"Haba? Ai ban sani bane ina can, toh ya hanya? Ya karatun kuma?"
Azrah ta ja numfashi, tana jin farin ciki fal zuciyarta, tana murmushi ta ce
"Alhamdulillah Bappah, komai lafiya, Na yi missing dinka sosai fah Bappah"
Mama ta taɓe baki, ta juya ta wuce ɗakin ta ba tare da ta sake kallon su ba, tana jin zuciyarta na mugun tafasa
Bappah ya ci gaba da murmushi, yana kallon Azrah da farin ciki a fuskar sa ya ce "sannu da zuwa, sannu Azrah"
Azrah ta bita Mama da kallo, sannan tana kallon Bappah cike da nutsuwa ta ce
"Bappah mu shiga ciki ko?"
Bappah ya yi murmushi ya ce
"Je ki, zan shigo nan ba da dadewa ba"
Azrah ta juya ta wuce ɗakinsu, ranta fes da natsuwa, ta samu Zahra tana kan kwashe kayan tana kai wa ciki
Ta ɗaura kanta kan cinyar Umma, ta lumshe ido, nan da nan scene ɗin da ta da Saif a airport ya faɗo mata, hakan yasa mood ɗinta ya canza lokaci guda tana jin tsantsan tsanarsa a ranta
Episode 37: After Her Return
Umma ganin kamar Azrah tayi bacci a cinyarta, yasa a hankali ta kira sunanta, Azrah ta tashi ta zauna tana murmurta idanunta saboda baccin dake cike a idonta, Umma ta ce
"Je ki ciki ki kwanta, kina bukatar hutu yanzu"
Azrah ta mike, kamar zata shiga ɗakin su kuma sai ta tsaya kamar ta tuna wani abu ne, tana kallon Umma ta ce
"Umma, Bappah bai shigo ba ne? Ko ya shigo sanda nake bacci?"
Zahra ta kalle ta da sauri tana dariya ta ce
"Shin da gaske ya ce miki zai shigo ne?" Azrah ta gyada mata kai
Zahra ta ce "Hmmm! Tun bayan tafiyarki Bappah kamar me aljanu ya koma, ba lokacin sai murna muke ya daina abubuwan da yake mana ba? Amma kina tafiya, Dada ma ta koma shikenan Bappah ya bokare wllhi Umma dai na kokari, shiyasa naji kamar na shake Mamar nan dan kamar ba'a banza ba"
Umma ta daka mata tsawa "Zahra ki dena wannan maganar nace miki, bana son na kara jin wannan maganar daga bakin ki" Sai ta juya ta kalli Azrah ta ce
"Azrah kina bukatar hutu yanzu, idan Bappah ya shigo zan faɗa masa kin yi bacci, amma yanzu ki jeki kwanta''
Azrah ta gyada kai daga bisani ta wuce ciki
Zahra taki kallon direction ɗin Umma dan tasan zata iya mata magana da ido ita kuwa bata bukatar hakan, kawai tabi bayan Azrahn tana ma Umma sai da safe
Azrah ta shiga ɗakinsu ta kwanta kan katifarta, Zahra ma data bi bayanta kwanciyar tayi, duk suka yi addu'a suka kashe wutar ɗakin
Azrahn ta rufe ido kawai maganar da Khalil ya fada mata a airport ne ya fado mata a rai, bata ma san sanda ta mike ta zauna ba daga kwanciyar da take ba, lokaci guda taji baccin ya tafi daga idanunta, mamaki ne ya kama ta yadda ta manta da wannan maganar
Ta jawo wayarta, ta shiga WhatsApp ta kunna datan ta sannan ta shiga chats ɗinsu, zura ma chats ɗin ido tayi, sannan ta kalli agogo ganin ƙarfe 9 ne yasa ta san yanzu dare ne sosai a wujensu, kusan asuba ma, typing ta fara sai kuma ta goge abun da tayi typing ta rubuta "Hey" sannan ta tura masa, kawai taga yayi double tick alamun yana online kenan, bata san sannan murmushi yayi escaping lips ɗinta ba, tana jiran reply dinsa amma har kusa 10 mins ko buɗewa bai yi ba balle ta saka ran zai reply dinta
Kawai ta kashe datar, ta koma ta kwanta, bata san dalilin ba, sai kawai ta ji hawaye yana zubo mata, ta share fuskarta cikin sauri, tana mamakin abin daya saka ta zubar da hawayen, ta daɗe kwance bacci yaki ɗaukarta wanda da farko dakyar ma ta karasa cikin dakin zunzurutun bacci, ta kusa sha-biyu idonta biyu daga karshe bacci ɓarawo ya kwashe ta
Washe gari bayan Azrah ta idar da sallar asuba, tana idar da morning azkar ɗinta ta koma bacci sbd ba ta samu isasshen bacci jiya ba, Umma ta hana Zahra tashin ta, tace ta bar ta ta huta dan tana bukatar Hutu, Zahra kuwa ta gama dukkan aikace-aikacen gidan, tayi share, da wanke-wanke, har ta dafa breakfast. Sai suka ɗiba nata a cikin kula, suka kai mata ciki.
Wajen ƙarfe goma Azrah ta farka Ta miƙe zaune tana furta azkar ɗin tashi daga bacci, agogon ɗakin ta kalla taga har goma tayi, miƙewa tsaye tayi tana daure gashinta, ta sanya hula sannan ta ɗauki brush da toothpaste ta fita a ɗakin
Umma da Zahra na zaune suna hira, Azrah ta sake gaishe su
Umma ta amsa cikin fara'a tace "Yaya gajiyar hanya?"
"Alhamdulillah Umma" Azrah ta amsa, Zahra ta ce
"Ashe akwai abin da zai sa ki yi baccin safe haka?" ta karasa tana dariya
Azrah ma tayi dariyar dan itama abin mamaki yake bata yadda yanzu take wannan baccin ta ce
"Toh tunda na gama exams na ke wannan irin bacci kamar an dora min shi" Umma ta ce
"Ai hakan yana da kyau, tunda hutu kike, lokacin semester ai ba bacci kike ba sai karatu"
Azrah ta ce "Na ma isa?!" Umma ta ce "Toh kin gani"
Azrah ta danyi dariya ta ce
"Halan Bappah ya shigo ina bacci ko?"
Umma ta ce "Eh kuwa, ganin kina bacci yace kada a tashe ki"
Azrah ta ce "Ayyah" sannan ta tashi ta fita zuwa compound ɗinsu, tana fita idonta ya sauka kan wata makwabciyarsu, Maman Asabe, Mama, da wata Mata dake tsaye a ƙofar gida suna hira, Mama na tattare gongonin tsana'arta na alale, Azrah ta gaishe su gaba ɗaya, makwabciyarsu ta ce cikin murmushi
"Ki ce dai mutanen India ne! Sannu Azrah, ashe kin dawo"
Azrah ta gyada kai tana murmushi ta ce
"Eh, na dawo"
Mama Asabe kuwa sai kallon ta kawai take yi, ta amsa gaisuwarta a takaice
Azrah ta samu gefe ta fara brush,
Maman Asabe tayi ƙasa da murya ta ce
"An ce karatu da wahala amma kalli yadda yarinyar nan tayi bulbul haka? Tayi kyau sosai wllhi kamar ba karatun take ba"
Mama ta ce "Toh ba dole ta yi kyau ba? Ai ciki ne gareta"
Maman Asabe da makwabciyarsu suka zaro ido suna kallonta mamaki kwance a fuskarsu
Mama ta gyada kai da tabbaci ta ce
"Eh mana, ku yanzu ba ku ga alamun ya bayyana ba?"
Makwabciyar ta ce
"Kai Maman Abdul wannan dai kyau ne kawai, irin na can India, ta ci daɗi ne ba wai ciki ba"
Mama ta ce "Toh mu zuba mu gani, Kwanan nan magana ta zata tabbata"
Bayan Azrah ta gama brush, ta koma cikin ɗakinsu, ta wuce wajen da aka ajiye breakfast ɗinta, ta ɗauko kularta sai kuma ta dawo ta zauna kusa da Umma. Da ta buɗe kukan kawai taga doya da ƙwai ne favorite ɗinta, nan da nan ta ware ido tana kallon Umma ta ce
"Kai Umma! Nagode sosai!"
Umma ta yi murmushi, Zahra kuwa ta ce
"Kinsan fa Umma tana matuƙar ƙaunarki, shi yasa tace a miki favorite ɗinki"
Azrah ta ce "Na sani ai. Na fi ki sanin yadda Umma ke sona. Ni ce zuciyarta in human form"
Duk dariya suka yi baki ɗaya harda Amma dake kallon su cike da sha'awa
Zahra ta ce "Chap! Wannan karyar taki bata da kafaɗa, Umma Ni tafi so idan baki sani ba"
Azrah ta zuba tea a cup dinta, ta zuba some slides na doyan a plate, ta ɗauki fork ta fara ci tana kallon Zahra ta ce
"To ki bar wannan maganar naki sanda bana gida Amma yanzu... ki daina kwatanta kanki dani dan nice kan gaba"
Duk suka sake dariya dukkansu cike da farin ciki da annushuwa,
Wayan Azrah ne ya fara ringing a ɗaki, Zahra ta wuce ɗakin da sauri ta ɗauko mata wayan tana mika mata ta ce
"Wannan Khalil ɗin naki ne"
Azrah ta karɓa wayan daga hannun Zahra sannan ta ɗaga kiran ta kai kunne tana murmushi ta ce
"Hello Khalil"
Khalil ya ce "Hi Azrah, Good morning! Hope you slept well?"
Azrah ta ce "I did, thank you! How about you?"
Khalil ya ce "I'm good! Please, can you pass the phone to Umma? I'd love to greet her"
Azrah ta ce "Okay" tana murmushi ta miƙa wa Umma wayar tana faɗin
"Umma Khalil ne, wai zai gaishe ki"
Umma ta karɓi wayan da fara'a ta ce
"Hello, Khalil! How are you, my son?"
Khalil cike da murna ya ce "I'm doing fine, Alhamdulillah. Good morning Ummu?"
"Umma ta ce "We are all fine, Azrah came back home safely, thank you for the care"
Khalil ya ce "She means a lot to us all, I'm glad she's back safely"
Umma ta yi murmushi sannan ta ce
"Allah ya kara muku Albarka" cike da jin daɗi ya amsa yana ta godiya mata
Azrah fa karɓi wayan ta ce "Here, talk to Zahra too, she's beside me"
Ta miƙa wa Zahra wayar
Zahra ta ce "Yessss Mr. Khalil! Our in-law to be!"
Azrah ta zaro ido tana kallon Zahra da mugun mamaki sai kuma tana girgiza mata kai ta bata wayan, Zahra ta make kafaɗa
"Khalil yayi dariya sosai ya ce "Zahra you'll never change'
Azrah taji kamar ta nitse dan kunya
Zahra ta ce "Never! How's India?"
Khalil ya ce "India is hot as usual, but we're pushing, and I just miss Zahra"
Zahra ta ce "A lot! Especially she too, almost cried yesterday talking about you!" Azrah zata kwace wayan tayi saurin komawa baya
Suka ci gaba da hirarsu cikin raha da dariya har sai da suka yi wajan 15 mins
Daga baya Zahra ta miƙa wayar ga Azrah
Khalil ya ce "I missed talking to you"
Azrah quietly ta ce
"Me too, actually, I wanted to talk to you about something... but maybe later"
Khalil ya ce da muryan damuwa "Is everything okay?"
Azrah ta ce "Yes, yes Everything's fine, I just don't want to say it onow"
Khalil ya ce "Alright then, I'll be waiting when you're ready"
Azrah ta yi shiru na ɗan lokaci, tana murmushi da wani abu a zuciyarta da ita kaɗai ta sani Sannan tace
"Okay, take care of yourself, Khalil"
Khalil ya ce "You too, bye"
Ta kashe wayar tana murmushi, ta ajiye wayar gefenta Zahra na kallonta da murmushi ta ce
"You both are talking like there's a movie scene between you"
Azrah ta ce "Well… maybe our life is the movie"
Duk suka yi dariya
Umma ta ce "Amma ke Azrah, aina kika san saurayin nan Khalil?"
Azrah ta ɗan lumshe ido kafin ta ce
"Kawai lokacin ina karatu ne a wani spot, sai kawai wannan bawan Allahn ya zo yace ina kama da kakarsa, har yadda nake dariya da kuma idona, musamman lokacin da ya ga hotonta a lokacin tana 'yan mata Wai kamar na ɓaci ne"
Zahra tayi dariya sosai har tana riƙe ciki ta ce
"Ya Azrah! Kin yarda ko? Kyaun nan naki yasa ake miki kallon kamar 'yar India ce ke! Ikon Allah, mu da muke 'yan Nigeria"
Umma tayi shiru kamar tana nazari sai can ta ce da
"Kila ɗibi kike da ita kakar tasa… Amma ace har da kama sosai? Mu da ba mu da alaƙa da Indiyawa ko kadan?"
Azrah ta ɗan kalli umma cikin annuri ta ce
"Amma Umma, Khalil ba ɗan India bane fa"
Zahra ta biyo da sauri tana kallon ta ta ce
"Laaa! Ai sai kice mana ɗan Nigeria ne shima!?"
Azrah ta girgiza kai ta ce
"Nope, Masters ya kai shi India shima, Next week ma zasu fara Exams, But he's Egyptian"
Umma ta taji wani tsinkewar zuciyarta, har sai data dafe kirjinta ta zaro ido tana kallon Azrah da mamaki ta ce
"Egyptian kuma!?"
Azrah da Zahra suka haɗa baki ganin reaction ɗin Umma suka ce
"Lafiya Umma?"
Umma ta yi saurin ɗauke kanta kamar tana son gyara al'amarin ta numfasa cikin nutsuwa ta ce
"Eh... babu komai.. Just... ai Egypt nesa ne sosai..."
Azrah ta ce
"To Umma ai duk nisan sa bai kai indian ba fa, kuma ai ba nesa ke hana ƙaddara ba"
Zahra tace da wasa
"Kai, kin ji Ya Azrah da philosophy! Amma gaskiya ne, shiyasa if u'ar meant to be together duk inda kuke sai wani abu ya faru da zaku haɗu"
Umma dai tayi shiru bata sake cewa komai ba, zuciyarta na cike da tambayoyi, amma ta ɓoye komai da murmushi, duk da ba ta kara fahimtar komai ba daga nan, duk maganar da suke hankalints baya kansu sai can ta ce
"Allah ya tabbatar da alkairi"
Suka yi shiru na ɗan lokaci, sannan Azrah ta canja zancen da wata hira daban
Bayan Azrah ta gama cin breakfast ɗinta,Zahra ta fitar da plates ɗin waje, Azrah kuma ta shige ɗakinsu, tana cire kayan jikinta cikin shirin yin wanka don ta ji jikinta na buƙatar freshening up
Zahra ta shigo ɗakin tana kallon Azrah da mamaki ta ce
"Wanka zaki yi yanzu Ya Azrah?"
Azrah ta gyada mata kai ta ce
"Eh mana, na gaji ne kuma bansan meya kawo gajjiyar ba, Kuma ba wani baccin kirki nayi ba Jiya ba"
Zahra ta ce "Okay, toh bari na kai miki ruwa"
Ta fice da sauri zuwa wajen fetcher, ɗeba mata tayi ruwan wanka a babban bokiti, Mama dake zaune a baranda tana gyaran waken alalen gobe ta ɗago kai ta ce da sarkakiya a muryarta
"Ke Zahra, sau nawa zakiyi wanka ne yau? Ku ne ku ke karar mana da ruwa kamar ruwa isanmu yayi har haka bayan dakyar Bappahn ku ke turo mana masu garuwa"
Kafin ta gama fadar maganar Azrah ta fito daga ɗakin ɗaure da towel da hijab ta tsaye a kofa, ta katse Mama da ladabi
"Mama ni ne zan yi wankan ba Zahra ba"
Mama ta taɓe baki kamar bata fahimci me suke nufi ba tana kallon Zahra ta ce
"Ikon Allah, Ita Azrah! Tunda ta dawo daga Indian shikenan, ba zata ci gaba da aiki a gidan bane? Komai sai an mata kenan? Ko ta manta inda ta fito ne? Naga komai yi mata ake yi"
Zahra ta ɗauki bokitin ruwa, ta ɗan kalli Mama kafin tace
"Mama jiya da yamma ta dawo gidan nan fah, Kuma ta dawo tana ciwon kai sosai, ai Kinga ba zata fara aiki ynz ba "
Mama ta tabe baki cike da yarda da rashin yarda. Zahra bata kara kallon ta ba, kawai ta wuce cikin toilet da bokitin ruwan
Bayan ta fito tace da Azrah
"Ki shiga kiyi wankan''
Azrah ta dan yi murmushi tana kallon ‘yar uwarta ta ce
"Thank you Zahra, Allah ya saka da alheri"
Zahra ta ce da wasa
"To ai na saba da aiki, ba kamar wasu ba..."
Duka suka yi dariya, Azrah ta shiga toilet ɗin cikin nutsuwa domin yin wankanta
Episode 38: Returning Echoes
Bayan Azrah ta gama wanka ta fito daga toilet ɗin, tana ƙoƙarin tunkarar ɗakinsu kenan sai suka haɗa ido da Mama wadda ke shirin shiga ɗakinta, Mama ta watsa mata wani irin kallo mai nauyi, wanda yasa Azrah ba shiri ta sauke idonta ƙasa, kuma ta gagara tafiya, ta fara watsa da fingers ɗinta cikin sanyin jiki, kawai ta cigaba da tafiyarta bata ce komai ba har ta shige ɗakinsu, tana jin jikinta babu ƙwari haka kawai taji bata yarda da kallon ba
A ɗaki ta zauna gefen katifanta ta shafa lotion a jikinta cikin nutsuwa, sannan ta saka wani simple gown, mai sauƙin launi da kamala, Bayan ta gama shiryawa, ta tashi ta nufi ɗakin Umma
Zahra ce ta ɗaga kai daga inda take zaune, tana kallon ta cike da yabo ta ce
"TabarakAllah Ya Azrah, kin yi kyau sosai" ta faɗa tana murmushi.
Azrah ta mayar da murmushi ta ce
"Thank you, ke ma kin yi kyau"
Umma na zaune tana kallon su, tana jin daɗin ganin ‘ya’yanta cikin fahimta da soyayyar junansu, Sai kawai wani tunani ya faɗo mata daga nan kuma ta tuna da Khalil, lokaci gudu kuwa taji zuciyarta ya fara bugawa da karfi, ta sauke ajiyar zuciya a hankali tana kallon Azrah zuciyarta na raya mata abubuwa da dama...
Azrah ta kalli Zahra tana murmushi ta ce
"Yau kuma me za mu dafa a gidan nan?"
Zahra ta ɗaga kafada tana buɗe hannayenta alamun bata sani ba itama, ta ce
"Ai yanzu ke za a tambaya, me kike so a dafa? Tunda yanzu ke baƙuwa ce a gidan"
Azrah ta yi dariya tana girgiza kai ta ce
"Ko ba baƙuwa ba, dama kana zama baƙuwa ne a gidan ku ban sani ba"
Duk suka sake dariya, Zahra ta ce
"Toh tashi muje kitchen, ki zaɓa mana abin da za'a dafa"
"Mu je muga me ake da shi" Azrah ta faɗa tana miƙewa
"Kee , we lack nothing fah, komai akwai, Sai dai ki zaɓa me ranki ke so" Zahra ta amsa tana binta a baya
Bayan sun fita suka wuce zuwa store wanda a da kitchen ne aka maida shi store yanzu, sai suna girki a compound ko bakin kitchen ɗin. Bayan sun shiga, Azrah ba wai kallon kayan abinci bane ya fito da ita, a'a, zuciyarta tana cike da damuwa da tambayoyin da ke yawo a kwakwalwarta tun jiya wanda take buƙatar amsar su, ta sauke numfashi ta zauna kan kujerar roba dake cikin store ɗin, ta kalli Zahra da fuskar dake nuni da seriousness ta ce
"Zahra zo ki zauna, magana nake son yi da ke"
Zahra ta tsaya cak, tana kallonta cike da damuwa ta ce
"Allah sa lafiya Yaya Azrah" ta kare maganar tana zama kusa da ita tare da dafe kirjinta
Azrah ta jinjina kai ta ce
"Lafiya lau. Amma jiya kin faɗi wata magana da ta tsaya min a rai ne Zahra"
Zahra ta zaro ido tana tambayar ta
"Wacce magana ce kuma na faɗa Yaya?"
Azrah ta dan langwaɓe kanta tana kallonta kai tsaye ta ce
"Maganar Bappah... yadda kika fara magana jiya cewa bayan tafiyata sai ya koma wani iri, kika ce kamar mai aljanu, har Umma ta ƙwaɓe ki"
Zahra tayi shiru, sai ta sauke ajiyar zuciya tana kallon ƙasa...
Azrah ta ɗan matsa kusa da Zahra, tana kallonta da nutsuwa, ta ce da murya mai taushi
"Ina jinki Zahra… please, don't hide anything from me. Tell me everything pls"
Zahra ta ɗago kai ta kalleta, sannan ta sauke wani dogon numfashi, ta ce
"Maganar gaskiya, Ya Azrah... Umma tana ƙoƙari da Bappah ba kaɗan ba, Wllhi Umma na bani tausayi sosai, Gashi bata da kowa, ko makwabta bata yawan shiga, gwara idan Maman Azizah ce ta zo gidan nan shine zaki ji suna hira"
Azrah ta datse lips dinta tana jinjina kai, sannan tace da murya mai ɗaci
" Ba wannan nake son ji ba Zahra. What exactly is going on Zahra?"
Zahra ta ɗan juyo tana kallon Azrah, sannan ta cigaba da magana cikin sanyi da damuwa ƙarara daya bayyana a fuskarta ta ce
"Tun bayan tafiyarki… da wani bayan sati guda kacal, Dada ta koma garinta, Itama ta bar Umma wanda a lokacin Umma ta ɗan warware, tun daga lokacin ne Bappah ya sauya hali, wlh Ya Azrah total canzawa yayi, Wasu lokuta sai na ganshi kamar wani mutumin daban. Na fi sau uku na kama Umma tana kuka, ko kuma tana magana ita kaɗai, kamar mai rikicewa haka wanda damuwa ce ta mata yawa, Amma duk lokacin da na tambaye ta, sai tace ‘babu komai’ ki san halin Umma ba faɗa zata yi ba...''
Zahra ta gyara zama tana ɗan girgiza kai ta ce
"Kuma kema kin san akwai abubuwan da Umma take ɓoye mana tun ba yau ba..."
Azrah bata bari ta gama ba ta ce da ƙarfi
"Innalillahi wa inna ilayhi raji’un!"
Ta ɗaura hannunta a goshi, tana girgiza kai, idonta ya cika da hawaye ta ce
"Yanzu duk waɗannan abubuwan suna faruwa, ni kuma ban sani ba? Umma... ta wahala haka... ni kuma ina rayuwata can, ban san komai ba hankali na kwance..."
Tana jin wani sabon nauyin damuwa ya sauka a zuciyarta, Hawaye ya zubo a gefen fuskarta, ta share shi a hankali, sannan ta ce da raɗa
"I need to know everything Zahr, I really do''
Azrah ta runtse idonta sosai, tana jin kamar zuciyarta na ƙoƙarin fashewa da wannan nauyin damuwar, Zazzaɓi kamar na kwana biyu ya sauko mata cikin mintuna, zuciyarta na bugawa da sauri da sauri, tayi shiru na ɗan lokaci kafin ta buɗe ido a hankali, tana kallon Zahra da raunanniyar murya ta ce
"Zahra… why didn't you tell me all these since? Har haka abubuwa suka lalace? Kuma Umma bata taɓa faɗa min komai ba… Ni da nake waya da ita every blessing day, kullum da fara'a, da dariya… she was dying slowly and I didn't even notice.. goshh My bad"
Zahra ta kama hannun Azrah, ta ce da tausayi
"I’m sorry Ya Azrah… wlhu bana so ki damu ne sosai dan nasan halinki, Tunda kin zo, sai na ga lokaci yayi da ya kamata ki sani, toh ba gashi yanzun kin sani ba, amma gsky we really need you at home, Babu wanda Umma ke ji da shi kamar ke kuma kinyi mata nisa''
Azrah ta lumshe ido hawaye na saukowa a hankali sannan ta ce
''Zan yi magana da Umma yau dan gsky ba zan iya shiru ba, I need to hear it from her… kuma wallahi idan wannan Mama da saka hannu a cikin komai, zata gane I'm not that small girl she used to know, zata sha mamaki na''
Zahra ta girgiza kai a hankali ta ce
"I trust you Ya Azrah… yanzu kin dawo, abubuwa zasu chanza in shaa Allah ko da kuwa ta ɓangaren Bappah ne, dama Mama kam ai tasan bana ragar mata''
Azrah daga haka ta miƙe ta wuce ɗakin Umma, tana shiga ɗakin ta sameta kwance tana sauraron wa'azi a wayarta, tana ji kamar zuciyarta na bugawa fiye da ko yaushe amma sai ta zauna a bakin katifar Umman tana kallon fuskarta, a hankali ta ce
"Umma... dan Allah zan tambaye ki, amma ki taimaka gskyr amsar tmby ta zaki bani?"
Umma ta ɗaga kai tana kallonta da murmushin meanwhile kuma tana nazarin tmbyr da zata mata ne sannan ta ce
"Yi tmbyrki idan ina da amsar zan faɗa miki In Shaa Allah''
Azrah ta gyara zama, ta ɗan kurawa Umma ido kafin a hankali ta ce
"Zahra ta faɗa min abubuwa dake faruwa tun tafiya ta Umma... Umma maganarta gaskiya ce ko akasin hakan ne?"
Umma ta ɗauke kallonta daga Azrah tana kallon wani direction daban, cike da nutsuwa ta ce
"Bakomai fah Azrah, Zahra dai shirmenta na yaranta ke damunta ne, amma abu wanda bai kai abu ba sai ta ɗora musu nauyi fiye da yadda suke kamar wani laifi haka take'' sai tayi dariyar yaƙe ta ce
"Ko dai kin manta Zahra ne Azrah?"
Azrah ta tsareta da ido hawaye na taruwa a idonta muryanta na rawa ta ce
"Umma kar ki ɓoye min nace fa... Tun jiya da na dawo, banga Bappah ya shigo ba, Ko kafin na tafi ai nasan halinsa''
Sai kawai Azrah ta fashe da kuka ta ce
"Umma kina shan wahala, wallahi baki cancanci haka ba! Banda bakin ciki babu abinda kike kwasa a gidan nan... Umma, dan Allah kiyi adalci ma rayuwarki''
Umma na kallon ta, amma bata ce komai ba dan tasan muddun ta buɗe baki tace zata yi magana she might end of crying too, kawai hannunta ta kama tana murza shi cikin nata
Azrah ta kama hannunta cikin tausayi ta ce
"Umma even if it's once, ki haɗa mu da danginki. Ko ke ki koma cikinsu... Please, ki daina rayuwa irin haka shiyasa daga Bappahn har matarsa suke miki abun da suka ga dama''
Umma bata iya magana ba, dagaske maganar azrah ya bugeta sosai, kawai ta fashe da kuma
Nan da Nan Azrah ta ruɗe kuma ta fara magana
"Ki gafarce ni Umma, ban so in saka ki kuka ba... nasan hawan jini gare ki, ga kuma ciwon da kike fama da shi, ki yafe min ki daina wannan kukan''
Umma ta share hawayenta a hankali, ta juya gefe ba tare da tace komai ba
Azrah kuwa ta sunkuyar da kai cikin nutsuwa, tana sauke ajiyar zuciya, tace a hankali
"In shaa Allah Umma ba zamu ƙara tambayarki game da dangin ki ba, Mun fahimci duk sanda muka yi miki wannan tambayar kamar muna fama miki ciwo ne, kiyi hakuri''
Zahra ce ta shigo ɗakin, ganin haka yasa Azrah ta miƙe ba tare data kara cewa wani abu ba, Zahra ta kura mata ido, Azrah tace da ita cikin ƙasa da murya,
"muje mu ɗaura girki, Zahra'' Fita suka yi suka koma kitchen ɗin, inda Azrah take kallon kayan abinci da mamaki ta ce
"Zahra, waya kawo waɗannan kayan abinci masu yawa haka?" Ta tambaya cikin rashin fahimta
Zahra ta sauke aziyar zuciya ta ce
"Hmm… Wlhi Allah ba zai bar mu mu sha wahala ba ne, tunda kika tafi India, da kuɗin da gwamnati ke biyan ki kike turo mana, muka dinga managing sbd rashin isan mu da baya yi a wata Ya Azrah''
Ta ɗan yi shiru kafin ta cigaba, "Sai kuma Mama ta zuga Bappah wai ya mayar da sadakin Honorable, wai kar wata rana ya zo ya ce ke ɗin nasa ne tunda ai ba'a mayar ba, Duk da cewa lokacin aka kira Honorable, yace baya buƙatar kuɗin, amma Bappah ya mayar da shi."
Azrah ta buɗe baki cikin mamaki, ba ta iya cewa uffan ba
Zahra ta ce
"Wata rana kawai sai ga kiran Honorable a wayan Umma, yana cewa na fita na karɓi sako. Ina fita, sai naga kayan abinci kamar wanda zamu buɗe shago. Na faɗa wa Bappah, yace a mayar da kayan. Na kira Dada, shine tace ‘babu ruwansa’, abincin kuma namu ne''
Zahra ta ɗan juya idanu ta ce "Waccan matar Bappahn kuma ta dinga shela a gari wai da kuɗin da ake amfani da ke a India ne kika mana siyayya''
Azrah ta sauke ajiyar zuciya, zuciyarta cike da damuwa ta ce
"Allah saka wa Honorable'' ta furta a hankali.
"Amin'' Zahra ta amsa. Daga nan Azrah ta mike, suka fara duba abincin da zasu dafa.
Bayan sun gama girki suka kai cikin ɗaki, a babban plate Azrah ta zuba musu duk suka haɗu suka ci tare, harda Umma wanda take avoiding eye contact da su, bayan sun gama ci suka fara hirar su, ba a jima ba, sai suka fara jin sallama daga bakin ƙofa Zahra ta miƙe tace dan jin menene sai kuma ta dawo tana kuntse dariyarta ta ce
"Azrah ga mutanen unguwa sun fara zuwa wai gashe ki zasu yi''
"Toh su shigo" Azrah tace tana tashi daga kan katifar da take zaune
Mutanen unguwar waɗanda da yawansu suke shigowa dan gulma fiye da gaisuwa suka fara shigowa, suna ce wa
"Sannu da dawowa Azrah, ai munji dawowar ki tun jiya!"
Wasun kuma kafin su gaisa zasu fara zuba mata tambayoyi, "Yanzu da gaske kina India kenan? Kina jin harshen su kuwa? Wai zaki yi aure ne ko mene?"
Azrah dai yin murmushi ne kawai aikinta tana amsa musu cikin ladabi. Umma dai sai juyawa take tana danne haushin wasu daga cikin su da already ta san ba wai gaisuwa suka zo ba, gulma ce kawai
Zahra kuwa dariya ma abin yake bata especially yadda Azrah ke behaving daga karshe tace ta wuce ɗakin su duk wanda ya sake shigowa zata ce tayi bacci ko bata nan
Episode 39: Unspoken Truths
Azrah na zaune kusa da Umma, Zahra kuwa banda dariya, babu abin da take yi. Umma tace
"Duk mutanen nan gulma ce ke shigowa da su, dama can suna shigowa ne sai yanzu wai zasu ce sunzo ma Azrah Sannu da zuwa?" Zahra ta ce
"Umma ni Ya Azrah na ban mamaki ai, sai ta gwada basu saba haka da su ba. Amma sai ta wani kirkiri murmushi tana yake musu haƙora ai shiyasa suke ta shigowa ai" Umma ta ce
"Toh ya zata yi Zahra? Ai dole hakan zata yi, tunda ba wulakanci zata musu ba?"
Duk suna zaune sai ga muryan Bappah, da alama yanzu zuwan sa dan faɗa yake, Azrah najin muryansa ta miƙe da sauri tana kallon Umma sai ta karasa jikin kofar ta ɗaga labulen
Sauka Azrah tayi daga kofar ta sauke labulen, sannan ta karasa har cikin compound. Bappah da ya jiyo ya kalleta tana tun tunkaran sa, sai ya tsaya yana kallonta Itama kallonsa take yi cikin natsuwa sannan tace da shi
"Bappah sannu da zuwa"
Bappah ya fara takowa yana nufarta yace
"Sannu Azrah ya gajiyar tafiya? Ina fatan yanzu gajjiyar yabi lafiya ko?"
Azrah ta gyada kai, tana murmushi ta ce
"Babu sauran gajiya Bappah"
Ya gyada kai sai kuma ya juya kenan tayi saurin cewa
"Yauwa Bappah please, ba ka ce zaka shigo jiya ba? Har bacci ya kwashe ni, ban ga ka shigo ba"
Bappah yayi murmushi ya ce
"To mu shiga ciki"
Dakin Umma suka shiga Sai dai Bappah ko da wasa bai kalli Umma ba ko sau daya, wanda hakan ya jawo hankalin Azrah Zama sukayi Azrah tace
"Wlhi Bappah jiya ina ta jiranka har bacci ya kwashe ni baka shigo ba, na tambaye Umma ta ce ka shigo ina bacci'
Bappah ya ɗan lumshe ido, sai sannan ya ɗan saci kallon Umma dake jin wa'azin ta a wayanta ya ce
"Yi hakuri Azrah, nayi dare ne a kasuwa"
Ta gyada kai kawai cikin fahimta
Bappah yace "Toh dama menene?"
Azrah ta saki murmushi kadan sannan ta ce
"A'a Bappah ba wani abu bane fa, Wai dai tunda na daɗe bana gida, at least mu yi hira... ko na baka labari, na faɗa maka irin experiences dina a can, amma babu komai bayan wannan"
Ta ƙarasa maganar tana ɗan sunkuyar da kai kamar wacce ke jin kunyar Bappahn
Bappah ya kallet, da murmushi wanda ba'a gane cikakken ma'anarsa sannan ya ce
"Haka ne In shaa Allah zamu samu lokaci, but not now Azrah"
Azrah ta gyada kai, sai ta lumshe idonta a hankali ta ɗora kanta kan gwiwarta tana jin zuciyarta cike da wani irin ɗaci da kuma kin son sa, a lokaci guda ɗaci saboda yadda Bappah ya nuna halin ko in kula a gareta, kin son sa saboda yadda yake wulakanta Umma kamar ba ta cancanci kallon kirki ba koda a gaban su ai sai yayi ko dan ganin idon su
Bappah ya kalli Azrah cikin wani yanayi ya ce
"To idan babu komai... zan iya tafiya?"
Kafin Azrah ta ce komai, Zahra ta katse shi da cewa
"Bappah... kana da inda zaka je yanzun ne? Na ga yanzu-yanzu ka shigo amma kana sauri har kana son fita? Ko an kira ka ne yanzu a kasuwa ana son ganin ka cikin gaggawa ?"
Bappah ya ɗan juyo yana kallonta ya ce
"Kina da sako ne?"
Zahra ta girgiza kai ta ce
"Aa, kawai dai tambaya nayi"
Bai ce uffan ba, ya cigaba da tafiyarsa har ya fice daga ɗakin
Azrah ta ɗaga kai tabi sa da kallo harya fita, sai kuma ta sunkuyar da kanta, ta dafe goshinta tana jin hawayen da ta daɗe tana ƙoƙarin ɓoyewa ya fara zubowa
Zahra ta sauke numfashi tace,
"Idan wannan ne zai dameki... toh wlhi ƙadan kike gani Ya Azrah"
Umma ta juyo ta ma Zahra wani irin kallo mai cike da gargaɗi, kamar tana ce mata ta rage maganganun ta
Zahra kuwa ta kau da kanta, ta ɗauke kai kamar ba ta ma fahimta ba
Bayan Bappah ya fice daga ɗakin Umma, sai ya nufi ɗakin Mama. Mama na zaune tsakiyar ɗaki, ko'ina cikin ɗakin ya cika da kaya, datti da tarkace kaca kaca Sai dai hakan bai hana Bappah tsallakewa ya shiga a hakan ya zauna ba
Mama ta ajiye yalon da take ci, ta ce da mamaki
"Yanzu fa na ji kamar muryarka da wata kamar Azrah... na laika da sauri, sai ban ga kowa ba, nace lallai yau nayi gamo, Azrah Ita da ke India, me zai sa naji muryanta a nan?"
Bappah ya kalleta cikin nutsuwa ya ce
"Ke baki san tazo bane? Azrah tana gida ai"
Mama ta dafe kirjinta da mamaki,
"Au! Ashe dai ita ce naji ku tare? Yanzu kenan ta dawo? Ashe gsky nake ji..."
Bappah ya ɗan harareta ya ce
"Ya kike magana kamar baki san ta dawo ba, Azrah tazo tun jiya fah, kina nufin baki ganta ba?
Mama ta zaro ido ta ce
"Ko shiyasa dazu a unguwa ake cewa wai Azrah ta dawo... nace musu ai ba zata zo ba, amma naji Bappahn su na cewa ta kusa dawowa, Ashe tuni ma tazo?" Ta karasa maganar tana tagumi
Kallon damuwa ya bayyana a fuskarta, hawaye ya fara sintiri yasa ta ce
"Yanzu saboda ba ni na haifeta ba... shine har zata dawo ba zata shigo ta gaishe ni ba? Ashe har yanzu bani da daraja a idonta Shikenan na gode, dama an riga an nuna musu cewa ban isa da su ba"
Bappah ya ɗan ɓata rai ya ce
"Toh me zai saki kuka kuma yanzu? Ki daina fadar haka, bana son kuna nuna cewa wannan ne 'ya'ya na wannan kuma 'ya'yan kishiya, Zan yi mata magana yanzu"
Ko jiran amsarta bai yi ba, ya miƙe tsaye ya fice daga ɗakin ya nufi ɗakin Umma
Mama kuwa ta share hawayenta da zaninta, tana ɗan murmushi mai cike da zurfin makirci... Dama reaction ɗinsa take son gani sai kuma ta haɗa Azrah da ubanta
A fusace Bappah ya ɗaga labulen ɗakin Umma, kamar wanda zai fasa rufin ɗakin da muryar sa, ya shiga yana huci ya ce
"Yanzu ke dan ubanki Azrah! Har zaki zo tun jiya, ki kasa shiga ki gaishe da Mama saboda ba ita ta haifeki? Ko dan kin san ba uwarki bace Shikenan bata da kima a wajen ki? kin rainata? An riga an datsa miki a rai cewa bata da daraja ko?"
Fuskar Azrah ta cika da mamaki lokaci guda, ta zaro ido tana kallonsa sai hawaye suka fara gangarowa mata, Zahra kuwa ta buɗe baki tana kallonsa cikin tsananin fushi ta ce
"Wani babban munafikin ne! Jahili! Makaryaci! Wanda bai da hankali, sannan wanda ba zai ga Annabin bane yazo ya maka irin wannan karyar da kowa yasan karya ne tunda har makwabta sun san tazo balle wanda muke gida ɗaya, waye ya faɗa maka wannan zancen? Wannan karyan dan Allah Bappah?
Umma na zaune amma ko da wasa bata ɗaga kai ba, sai dai idonta na nuna tana jin komai
Bappah ya ɗago idonsa da mamaki yana kallon Zahra ya ce
"Ni kike tambaya akan maganata Zahra?!"
Azrah ta goge hawayenta da hanci, hawaye na cigaba da zuba. Zahra ta matso, tana kallon Bappah kai tsaye
"Toh Bappah karya aka maka wlh, Jiya fa daga isowar Ya Azrah, kai kanka baka nan amma Mama tana nan! Tare suka shigo gida, Azrah ta gaisheta da mutunci, amma Mama bata amsa ba. Magrib ma, na ɗibo mata ruwan wanka, Mama tace wai Azrahn uban wa ce da zata zo ta yi wanka da ruwa kadan kamar mai ji da kanta?"
Bappah ya tsaya cak yana kallon ta da mamaki, ya ɗan juya ya kalli Zahra, sai ya kalli Azrah wacce ta durƙusa, tana goge hawayen da ba su daina zuba ba.
A wannan lokacin, Bappah ya rasa abin cewa dan yasan halin Azrah da Zahra ce ba zai Musa ba, kalmomin Zahra sun katse hucin da ke cikin zuciyarsa, sake kallon Azrah da har sannan tana kuka yayi sai kuma ya juya ya fita
Bayan Bappah ya fita ɗakinsa direct ya wuce, Umma ta ɗaga kai tana kallon Zahra ta ce
"Ke komai sai kin haɗa da habaici ne Zahra? Can't you just go straight to the point? Ji yadda kike wa Bappahn ku magana kamar ba mahaifinku ba"
Zahra ta ja dogon tsaki kasa kasa ta ce
"To ai da ban faɗa masa gaskiya ba, zai ɗauka da gaske Ya Azrah ce bata da hankali, kiji shima ai haicin yake wai an datsa mana a rai? Wa zai datsa mana a rai inba da ke yake nufi ba?"
Umma ta juyo tana kallon Azrah ta ce da tausayi
"Yanzu me amfanin kuka zai miki Azrah? Tunda kinsan ba laifinki bane, ki share hawayen ki kwantar da hankalinki."
Azrah ta gagara magana kawai ta gyada kai a hankali, sannan ta miƙe cikin shiru ta nufi ɗakinsu
******
Azrah ta nufi dakin Umma, tana kallonta ta ce
"Umma nikam ba zan iya zama haka ba, Gobe in shaa Allah zan tafi kasuwa, dan in sake tsiyayan wasu kayan da zamu cigaba da siyarwa, Ni ba zan iya zama ba sana'a ba''
Umma ta kalleta tana murmushi, ta ce
"Har yanzu baki daina wannan halinki ba kenan?"
Azrah ta kwantar da murya cikin dariya tace
"Haba Umma, ko dai kin manta Business Admin nake karantawa ne?"
Umma ta yi dariya cikin jin daɗi. A daidai lokacin Zahra ta shigo dakin
Azrah ta ce
"Zahra ɗauki ATM ɗina, ki je ki tsiyomin kayan haɗin illoka kinji?"
Zahra ta gyaɗa kai, ta nufi zuwa ɗakinsu. Azrah kuwa ta kwanta a kan cinyar Umma cikin natsuwa
Zahra ta fito sanye da hijabi, ta musu sallama sannan ta fita.
Zahra na tafiya cikin nutsuwa, taji an kira sunanta
"Zahra!"
Da sauri ta juya, jin muryar Fatima
Tsayawa tayi har sai da Fatima ta karaso, sannan suka gaisa
Zahra ta ce
" kawarki fah ta zo''
Fatima ta ɗan ɗaga gira ta ce
"Wacce kawata kike nufi?"
Zahra ta buɗe baki tana kallon ta da mamaki
Fatima ta yi murmushi ta ce
"Kar dai Azrah kike nufi?"
Zahra ta amsa da dariya
"Eh mana, kina da wata friend ɗin ne bayan ita?"
Fatima ta girgiza kai cikin ɗan kaushi tace
"To ai yanzu Azrah I'm not her mate, Ko da zata tafi ma, bata min sallama ba,Sai a gari kawai naji ta tafi''
Zahra taji wani iri a ranta ta ce
"I'm sorry on her behalf. Amma na tabbata abubuwa suka ɗan shige mata ne, shiyasa ta manta, Ba da gangan bane''
Zahra ta koma gida a gajiye, da sallama ta shiga, ta tarar da Azrah na zaune tana wa Umma kitso.
Ta zauna tana fitar da kayan da ta tsiyo daga kasuwa, sannan ta ce
"Ya Azrah, gaskiya baki kyauta wa Fatima kawarki ba, Mun haɗu da ita yanzu da nake dawowa''
Azrah ta sake baki tana kallon ta, sai kuma ta ce
"Wallahi Nima kwanakin baya sai da nayi tunaninta, har da zan tambaye ki amma na manta
Zahra ta ce:
"Harda cewa ai yanzu, you're not her mate amma dai na gaishe ki."
Azrah tayi shiru na ɗan lokaci, sai kuma ta ce
"Gaskiya ban kyauta ba"
Umma da ake wa kitso ta ce
"Ai ke ban san meyasa kike da saurin mantawa da mutane haka ba cikin kankanin lokaci kuma ba daɗi gaskiya''
Azrah ta ce
"Kafin na koma, zan je na ganta in shaa Allah."
Umma ta gyada kai tace
"Haka yayi''
Duk sukayi shiru na lokaci, sai can Umma ta kara cewa
"Yauwa Azrah, ya kamata ki kira Dada ma fa, kada taji haushi ko ranta ya ɓaci''
Da daddare bayan sun gama dinner, har sannan kuma basu ga Bappah ba, Azrah ta wuce ɗaki tana shirin kwanciya ta ɗauki wayarta sai taga missed call ɗin Khalil, ajiye wayan tayi har sai da ta gama shirin bacci, sannan ta kira sa back, da kiran ya fara shiga sai ya cutting call ɗin ya kuma kira ta nan take
Tana ɗagawa a hankali tace,
''Hello, Assalamu Alaikum''
Ya amsa da
''Wa alaikumus salam. You left me here and this school is boring without you''
Tayi dariya ta ce
A'a, at least this way you'll be able to concentrate on your exams''
Ya ce
''But when you were around, I had more motivation to study... Not now''
Tayi shiru. Shima yayi shiru.
Can ta ce
''Uhm, you said you had something important to tell me, and up till now you haven't''
Ya ce
''Yeah, I don't know how to start, It's... complicated''
Ta ce
''Just say it anyhow''
Ya ce
''l'm afraid I might score zero'
Tayi shiru tana nazarin maganarsa da bata fahimta ba
A nan ne Zahra ta shigo dakin da sallama, ta bude baki tace
''Oh, kina waya da in-law dina kenan''
Azrah ta harare ta
Zahra ta ɗaga murya da gangan ta ce
''Mr. Khalil, good day?''
Khalil ya murmusa, yace da Azrah,
''l'll call you after Fajr prayer so we can talk properly''
Azrah ta ce,
''Okay'
Suka yi sallama.
Ta ajiye wayar tana kallon Zahra ta ce
''Ke Zahra, ni da Khalil ba soyayya muke ba, don Allah ki daina sa masa magana haka a baki, karya ɗauka I like him''
Zahra ta kyalkyale da dariya ta ce
''You and Khalil please stop deceiving yourselves''
Azrah bata sake cewa komai ba, ta juya ta gyara kwanciyarta.
Episode 40: The Shout That Shook The House
Washe gari, Gidan yayi ɗan nisa da hayaniya, kowa na harkar gaban sa ne, Zahra na wanke wanke, Azrah kuma tana jefa ɗan wanke, Habiba da Siyama suna can suma suna aikin su, Mama na aikin kwashe alalen siyarwa, sallama suka ji daga bakin kofar gidan duk suka ɗaga kai da mamaki suna Kallonsa, ya shigo gidan kamar wanda aka koro sa, Habibah ta ce
"Laaa Yaya ne ashe" Siyama ta taɓe bakin tana cigaba da aikin da take yi ta ce
"Sai sanda yaga dama yake zuwa kuma banga alamar kuɗi yake zuwa nema ba tunda ko sisin sa ban taɓa ci ba"
Ya shiga gidan har zai karasa part ɗinsu sai kuma ya tsaya yana kallon Azrah dake jefa ɗan wanke, zuba mata ido yayi wanda ita kuwa tana kokarin kaucewa daga ɗaga kai amma ta gagara har sai data ɗaga kai ta kalle sa, Mama da ganin haka yasa ta ce
"Kai Abdul, ko ka manta ɗakin ku ne ban sani ba?" hakan yasa ya juya ya nufe su, yana mita ya ce
"Ai naga kamar basu iya gaisuwa bane" Mama ta ce
"To kai yanzu kaga alamar tarbiyya tattare da su ne?
gaishe da Mama yayi yana kallon kannan sa sannan ya kunduma musu zagi ya ce
"baku iya gaisuwa bane ku ɗin ma?"
Duk suka Gaishe sa a takaice, ko amsa musu bai yi ba ya wuce ciki
Bayan su Azrah sun gama girkin su suka kai ɗaki, suka yi breakfast ɗinsu duk tare, Umma na kallonsu ta ce
"Ina son magana da ku?" Duk suka tsaya da abin da suke suna kallon Umma da mamaki dan sun san ba karamin magana bane tunda har tayi sounding so serious, Azrah ta ce
"Yanzu Umma?" Umma ta ce
"Eh, amma ku kai plates ɗin kitchen sannan" bayan sun yi haka duk suka zo suka zauna a gaban Umma, Umma ta ɗauke idonta akan su tana kallon wani wajan ta ce
"Kuyi hakuri da abubuwan da nake boye muku, nasan baku jin daɗi, nima ko kaɗan bana jin daɗi" duk kallonta suke da mamaki, Umma ta cigaba ta ce
"Tabbas akwai abin dana ke ɓoye muku tun kuna kanana, akwai wani sirrin daya kamata Ku sani, amma bana jin zan iya faɗa muku yanzu.. amma zan faɗa muku ranar da zuciyata ta shirya, sannan ranar da zata bukaci gaskiyar, kawai ku sani, akwai abubuwan da baku sani ba game da Ni.. da kuma dangina, ina me baku hakuri ku daina damun kanku akan haka, Nima tunanin hakan yana saka Ni cikin kunci, kuma shine babban dalilin daya sa sometimes zaku kamani ina kuka a ɓoye" Umma ta karasa maganar cikin rauni wanda har kana iya ji daga muryanta
Duk kallon Umman suke cike da tausayinta, kamar zasu yi kuka haka suke ji, dan dagaske Umma na cikin rashin nutsuwa, Azrah ta ce
"Toh Umma kiyi hakuri yanzu kar ki kuma shiga damuwa, everything will be alright In Shaa Allah then'' Umma ta gyaɗa musu kai ta ce
"Ku yafe min ba zan iya faɗa muku yanzu bane, amma ranar da lokaci yayi zan buɗe muku komai, zaku san komai a ranar" Zahra ta ce
"Toh Allah ya kaimu lokacin Umma" Umma ta amsa da Amin tana kallon 'ya'yan nata cike da tausayinsu
Azrah ta miƙe ta fita dan zuwa tayi wanka, bata dade sosai ba ta shirya cikin atamfa da kuma hijab ɗinta, ɗakin Umma ta nufa tana kallon Umma tace
"Umma idan baki bukatar komai yanzu zamu iya tafiya kasuwar?" Umma tace
"A'a ban jin akwai abin da zan bukata, inma akwai ai zan yi" Azrah ta ce
"Toh ai bana son kina yawan fita ne saboda yadda Mama ke behaving, amma idan baki fita ba bata kalle ki ba balle ta gaya miki magaan" Umma tayi murmushi kawai, Azrah kuma tana kallon Zahra ta ce
"Ahm, Zahra tashi mu tafi" Zahra ta miƙe suka ma Umma sallama daga haka suka nufi kofa
Haka suka ɗauki hours a kasuwa, suka nufi ainahin shop da Azrah ke siyayyar ta, suka masa list ɗin abin da suke so, ya juya ya fara ɗauko musu, Azrah kuma na faɗawa Zahra yadda zata yi da kayan, Mai shagon yayi dariya ya ce
"Yarinyar nan ke da azama kamar ba mace ba"
Azrah tayi dariya ta ce
"Neman halak da wuya ne dan haka nake yi da kwazo'' ya ce
"Gaskiyar ki ne, toh Allah ya saka ma neman mu albarka" suka amsa da Amin
Bayan sun gama siyayyar su, suka tare adaidaita saho suka yi ciniki sannan suka shiga, har kofar gida ya kai su
Bayan su shiga suka samu tashin Umma kenan daga bacci zata fita dan yin alwalar Zuhur, Umma na kallonsu ta ce
"Sannunku da zuwa" suka amsa mata, zama suka yi suka fara nuna mata kayan da suka tsiro, Umma ta ce
"Ma Shaa Allah, Allah sanya albarka a ciki" suka amsa da Amin daga haka Umma ta fita
Can yamma bayan sun kulla kayan da zasu kulla idan na yi ne kuma duk sunyi, suna zaune suna hira kawai suka jiyo murya ana sallama
"Assalamu Alaikum! Wai Akwai mutane kuwa a gidan nan?"
Zahra ta ɗaga kai tana kallon Azrah tace
"Ya Fatima ce fah" sai kuma ta miƙe da sauri ta fita tana amsa sallamarta ta ce
"Ki karaso mana" Azrah ta bi bayan Zahra tana murmushi
"Ohh Fatima.. I missed you, ki karaso mana" ta faɗa cike da zumuɗin ganinta
Fatima ta harareta ta ce
"Sai kace da gaske kike toh Ni dai wajan Umma na zo" daga haka ta shiga cikin dakin
Gaishe da Umma tayi, Umma ta amsa cike da fara'a tana tambayar ta ya gida, bayan sun gaisa, Azrah ta ce
"Haba mana yanzu fushi kike da Ni?" Fatima ta ce "ai mutuncin ki yayi yawa ne Azrah"
Azrah tayi dariya ta ce
"Yauzu dai na baki hakuri toh" Fatima na Murmushi ta ce
"Nayi hakuri ba dan halinki ba sai dan kinci albarkacin Umma" duk suka yi dariya...
Bayan sun ɗanyi hira Azrah da Zahra suka raka ta har kusa da gidan su sannan suka juyo
Bayan Magrib... bayan sun idar da sallan Magrib, suna zaune suna karatun Alkur'ani harda Umma, wani yaro ne yayi sallama hakan yasa suka ɗan yi shiru Zahra ta ce
"Wa'alaikumus Salaam, me kake so?" Ya ce
"Wani ne yake sallama da Azrah a kofar gida" Zahra ta kalli Azrah da sauri, Azrah ta ɗauke kai ta ce
"Kace bata nan" Umma tayi saurin cewa
"Kace tana zuwa" ya ce "toh" daga haka ya juya
Azrah tace "Umma Ni fah ban san shi ba" Umma ta ce "Eh ai idan kika fita zaki san sa, amma kawai daga magana sai kice baki nan" Zahra ta kama ta ce
"Ah tho, kika san waye ne? Kika san me ya kawo sa? Kila ma sako ne" Azrah tana turo baki haka ta miƙe ta ɗauki hijab dinta ta saka sannan ta fita
Bayan ta buɗe kofar gidan ta ɗan leka sai kuma ta ga Mutumin yana tsaya, ɗan calming kanta tayi tun kafin tayi magana yace
"Assalamu alaikum" ya ɗan kalle sa sannan ta ɗauke kanta zuwa wani wajan ta ce
"Wa'alaikumus Salaam" ya ce
"I'm sorry nasa kin fito ba tare da shiri ba ko?" Azrah ta ce masa "Uhmm" a takaice
Ya ce "Sunana Muhammad, tun kwanaki wajan shekara guda kenan yanzu na ganki amma ban samu damar miki magana ba sai yanzu da nake jin cewa nan ne gidan ku" Azrah without interest ta ce
"Ok, akwai wani abu ne?" Ya ɗan ƙalleta sai kuma ya ce
"Dama ina so ki bani dama ne if possible" Azrah ta ce
"I'm sorry to say already akwai sadaki a kaina, thank you" ya ce
"Kash.. but please can I get your number ko da gaisuwa ce sai muna ɗanyi" tana murmushi ta ce
"Ai banda waya yanzu ne, thank you" yana kallonta ya ce
"Toh shikenan, Thank you too, sai na sake zuwa please" daga haka ya juya ya tafi ita kuma ta juya zata karasa cikin gidan, dama bata wani fita ba a bakin kofar ta tsaya, tana shiga cikin zauren kawai taji an rungumota ta baya, da sauri ta juyo kanta tana kallon Abdul da mugun mamaki, nan take ya toshe mata baki, kokuwa ta fara da shi zata kwace kanta amma ya jata zuwa backyard ɗinsu, har sannan Azrah na kokuwa da shi, tana samu ta ɗan sauke hannunsa daga bakinta ta zunduma wani ihuuu wanda kusan kowa yaji ihun nata a gidan ta ce
"Waaaalllllll!!!"
Umma ta miƙe wanda da sauri wanda kusan tare suka mike da Zahra
Bappah daya shigo gidan kenan ba shiri yayi inda yaji muryan azrah
Kamar a mafarki Bappah ya Gwale ido yana kallonta a hannun Abdul baiyi wata wata ba yayi kansa a mugun guje ya fincikota sannan ya sauke wa Abdul wata a zaɓaɓɓen mari, bai bari ya dawo daga processing ba ya sake wanke sa da mari, Azrah data ja gefe tana kuka, sai ga Umma da Zahra suma sun yi wajan, tsayawa suka yi suna kallon ikon Allah, Mama da karasowarta kenan tayi sauri ta tare Bappah, Bappah bai san sanda ya jefar da ita gefe guda ba
Umma na kallon Azrah ta ce
"Meya faru?" Zahra sai huci take kamar zata caƙumosa dan yadda zuciyarta ke tafarfasa ita kaɗai tasan me take ji, a rayuwarta ta tsana taga an taɓo Azrah, a hankali Azrah ta ce
"Nima bansan me ke faruwa ba kawai ya toshemin baki yana laluba na ne" Bappah sai huci yake yana ma Abdul wani kallo
Mama ta fara salati ta ce "ji wata sharri? Yanzu ke ko kunyar mu baki ji zaki buɗe baki kiyi irin wannan sharrin?"
Bappah yana pointing ɗinta yace "kina wajen ne abun ya faru? Kin lalata tarbiyyar yaro sai sanda yaga dama yake zuwa gida ana magana kice yana legas yana tara kuɗi ko? Ki jira Kiga hukuncin da zan ɗauka akan sa wannan lokacin" daga haka Bappah ya juya zai bar wajan, da sauri Mama tasha gabansa ta ce
"Yanzu har ka yarda da abinda tace kenan?, bayan kasan yarinyar nan ba kunya gareta ba, ta tafi waje ta buɗe ido tazo ta kamasa shine har zata masa sharri kai kuma sai ka hau kai ka zauna"
Umma tayi wani murmushi ta kama hannun Azrah, Zahra ta ce
"Ihun ta aka ji ko nasa? Sannan tayaya za'a ce ita ta kama sa idan banda sharrin" sauke mata mari Mama tayi, Umma da har tayi gaba riƙe da hannun Azrah ta jiyo tana ma Mama wani kallo ta ce
"Karki kuskura ki sake ɗaura hannunki a jikin 'yarta, dan ko Ni bana daura musu hannu balle wacca bata san wahalan su ba tace zata mare min su" zata yi magana strictly Bappah ya nuna Mama cikin ido ya ce
"Karda ki kuskura ki sake ɗaura mata hannu" with shock Mama ke kallon Bappah, ya juya ya bar wajan, Umma ta kama hannun Azrah tayi gaba, Zahra ta fara tafiya ta ce "kuma Allah saiya saka min" tana kaiwa nan ta falfala a guje tayi gaba
Mama ta juya ta kalli Abdul da ko a jikinsa kuma babu alamun shi aka mara ta ce
"Uban mayasa ba zaka buɗe baki kama Bappahn naku magana ka ce ba kai bane itace ta fara kama ka? Sai kuma ka tsaya kamar saɓalota" ya ɗan taɓe baki ya ce
"Toh ai ba karya bane, tsaya ma tukun nan taya za'a ce zan buɗe baki nace wai itace ta kamani tayaya ma abin zai bada hankali" Mama ta sake baki tana kallon sa, ya mike ya karkaɗe rigar jikinsa ya ce
"Da kin wuce da tsayuwar da kika tsaya kika yi" daga haka ya ratsa ta ya wuce ta bisa da kallo har sannan kuma mamaki bai barta ba
Bayan Umma ta shiga ɗaki da Yaranta har sannan kuma Azrah na sheshekan kuka, Umma ta ce
"Kuyi hakuri daɗin abun Bappahn ku bai goyi bayan su ba, ai Shikenan" Azrah ta share hawayenta ta ce
"Umma Kinga yadda yake taɓani ne? Yanzu ace babu kowa kuma fa?" Umma ta ce
"Ɓai isa ba kuwa, dan Allah ba zai basa sa'a ba" Zahra dake huci tace "Allah ya taimake sa da ace Bappah da wancar Matar basu kusa zai sha mamaki na wallahi" Umma dai bata ce komai ba
Can Zahra ta sake cewa ai
"Ni dake yasan bana masa wasa kuma ina da baki ai koda wasa baya min magana dan yanzu zan gwada banma gane sa ba, tunda bawai a gidan yake da zama ba
Wayan Azrah ne ya fara ringing, duk zaton ta Khalil ne sai kuma zarah ta miƙa mata ta ce
"Karɓa Dada ne ke kiran ki" karɓan wayan tayi ta kai kunne....
Episode 41: The Storm within
Mama ta koma ɗakinta cike da fushi. Har yanzu tana jin zafin abinda aka ce akan ɗanta Abdul. Ta zauna gefen katifarta, ta faɗa duniyar tunani sai kuma ta fara masifa da murya da har makwabtaka zasu iya jinta dan ba kaɗan ba take ɗaga muryan sama ta ce
"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un! Ashe haka duniya take?! Ashe haka mutun zasu shigo gida ya samu yara da ubansu da uwarsu dan kawai ya samu waje a zuciyar wani sai ya maka sharri ya dinga ƙirƙiro karyar da za ta watsa mana mutunci?! Abdul ɗina fa! Ɗa na! Ai ko Allah kaɗai zai saka min... wallahi tallahi sai Allah ya saka min..."
Habibah da Siyama dake zaune a dakin suna sauraron masifarta, Siyama ta juyo da tsiwa ta matsa kusa da Mama yadda a waje ba za'a iya ji ba ta ce
"Amma Mama... ki ɗan nutsu, ki daina wannan ɗaga muryan,
kema kin san halin Ya Abdul... ba wai ina cewa haka bane amma ai kema kin san irin dabi'unsa, Saf zai iya aikata irin haka ba tantama"
Mama tayi saurin ja da baya, kamar waccan taji mugun abu haka ta ware ido tana kallon Siyama
"Ke asu wa?! Ke ce wa?! To sannu uwata wacca zaki gwada min kin fini sanin halin Abdul ɗin, wato kina bin bayan cewa zai iya aikata hakan kenan ko? Toh Abdul ba ɗan iska bane sai dai idan ke ce, mara kunya"
Siyama ta juya ta koma gefe ta zauna ta fara hawaye, ta tsana duk sanda Abdul yake gida
Habiba ta ce
"Mama... dama hakura kika yi da wannan maganar mana, tunda abu ya faru, shikenan amma haka zai sa mutanen waje su ji, Abu tun jiya ake abu guda fa knn''
Mama ta miƙe cikin fushi, ta daga hannu sama kamar mai rantsuwa ta ce
''Ai shikenan sai kawai ku fito fili kuce haka ne ma! Ke Habibah, idan ba zaku tsaya da ni ba, ku fice! Kowa ya fice min daga gani na"
Habibah ta zuba mata ido kawai, ta girgiza kai ta koma ta zauna
Mama ta zauna zuciyarta cike da raɗaɗi ta kuma ce wa
''Yarinyar can... wallahi sai Allah ya tona mata asiri, ita da take rayuwar waje ba? Haka zata zo ta haifa mana ɗa a gidan nan mara uba...''
Zahra ta fito daga ɗakinsu tana daura ɗan kwali, tana shirin fita domin yin alwalar sallar Isha'i. Mamaki yasa ta buɗe baki dan bata ɗauka mama ta ɗauka abun nan so personal ba, Umma kuma jin muryan Zahra yasa tai ta fito, fuska cike da gamsasshen natsuwa da tsantsar kulawa ta tsoma magsna
"Zahra... Azrah... ku karaso Nan zan mu ɗanyi wata magana ne"
Suka ƙaraso suna kallon juna, kowannensu ya zauna a gabanta cikin ladabi
Umma cikin nutsuwa
''Ku saurare ni da kyau... bana so daga yau duk wata maganar da za ta fito daga bakin Mama, ko wane irin zagi ne, ko wane irin ƙaryane... kada ku kula ta da 'ya'yanta, balle har ku tanka mata, Na fi kowa sanin yadda take. Kuma ke Zahra...'
Ta juya da hankali tana kallonta kai tsaye
Umma ta ce
"Ke dai, ke da bakin nan mai zafi... bana so naji kin ce zaki mayar mata da magana, Komai tace kiyi shiru''
Zahra ta ce "ta tabe baki cikin dan haushi ta ce
''Toh Umma... ai ni ma ba wata magana ce nake so nayi ba, dama alwala zani yi'' Umma ta ce
"Da ba alwala kike so ki fita kiyi ba, da na hana ki fita nace kiyi a cikin nan, amma yanzu yazo da haka sai a hankali
Zahra ta mike ta ɗan ja tsaki a ƙasa sosaita ce
''Toh... naji'' Fita tayi dan yin alwalar
Azrah ta juyo da sauƙin murya
''Dama ni ma Umma ba kula su nake yi ba" Umma ta gyada mata kai kawai ta ce
''lna fata ki ci gaba da hakuri... duk tsanani, Allah na tare da masu gaskiya'' azrah ta mike dan zuwa ta samu Zahra a compound din
Suna cikin magana ne sai suka ji shigowar Bappah, Bappah daya shigo koda wasa bai yarda ya kalli wani a compound ɗin ba
Zahra da Azrah suka kalli juna, ba tare da sun ce komai ba suka cigaba da alwala.
Washe gari kamar yadda ake tsammani, Mama ta tashi da wuta a zuciyarta. Duk yadda kake tunanin kafin gari ya waye zata sauko amma inaa, sai gashi da safe kamar ƙara ƙonuwa tayi, tana aikin kunna wutar da zata daura abinci amma bakinta na nan… ba ruwansa da shiru
Ita kadai take magana ta ce "Allah ya isa, wlh ba zan yarda ba, Sharri a rana tsaka, 'yarta dake rayuwa ita kaɗai acan ba'a ce komai ba sai wa nawa ɗanne za'a ma sharri"
Ganin haka yasa Umma da kanta ta fita tayi musu breakfast gudun kar ta saka su Zahra a samu issues
Har Umma ta gama girkin ta koda wasa bata kalli side ɗin Mama ba,
Ganin maganganun yayi yawa yasa Umma ba tare da ta ɗago ba, ta ce
''Ina yin shiru ne saboda zaman lafiya. Ai itama Azrah ɗin 'ya ce, shaketa da yayi kuma fah?
Mama ta harare ta ba tace komai ba. Bayan sun gama breakfast, kowanne ya shige ɗakinsa, Mama na kwasar gwangwaninna alalen tana kaiwa store, jin an buɗe kofar gidan an shigo yasa ta ɗan leka
Abdul ya shigo cikin gidan daga ball, jiki yayi fam-fam da zufa, yana shan ruwan goran hannunsa, jin murmuring din Mamansa ita kaɗai, ya san lamarin bai lafa ba har sannan
Abdul ya ce "Mama wai wannan maganar ba zai wuce miki ba ne? To ko a titi mutane na jin muryanki, kawai dai so kike ki ɓata min suna''
Mama ta dafe kirjinta tana kallonsa da takaici
''Haba Abdul, sharrin da za a maka a gaban ido na kuma nayi shiru? Ai wannan so kawai suke su ɓata maka suna a gari"
Abdul ya juyo ya kalleta kai tsaye ya ce
''Ni dai Mama kiyi shiru. Kin san kowa dai a wannan layi yasan irin tarbiyyar da Umma ta ba Azrah da Zahra, kinga kuwa babu wanda zai yarda cewa sharri aka musu, sai ma zagina da mutane zasu yi"
Mama ta riƙe bakin kofar kitchen tana kallon da mugun mamaki
"Abdul... Yanzu kenan nayi shiru har mahaifinku ya yarda knn? Ai Shikenan"
Abdul yace "toh ai yadda kike ta yaɗa maganar ma wani abu ne, at least kiyi shiru har Bappah ya manta''
Yana gama maganar ya juya ya fara tafiya zuwa ɗakinsa, ba tare da ya ƙara ce mata komai ba Mama ta tsaya baki buɗe ta bisa da kallo
Kamar za ta fashe da kuka, ta ajiye kwanukan hannunta tayi shiru tana kallon wani waje ta ɗauki lokaci mai tsayo bata gama processing ba
Can sai ga Bappah ya dawo, ya shigo cikin gidan ko magana bai yi ba, ba kamar yadda ya saba, ɗakin Umma direct ya wuce
Umma da 'ya'yanta suna zaune suna hira cikin raha da nishaɗi Kallo ɗaya zaka musu ka fahimci sun samu cikin kwanciyar hankali
Bappah ya shiga da sallama ya ce "Assalamu alaikum"
Duk suka amsa masa da "Wa'alaikumus salam Bappah"
Bappah ya kalli Azrah da nutsuwa ya ce
"Azrah zaki je gidan Dada gobe ko jibi in Allah ya kai mu. Kwana biyu zaki yi. In kin dawo sai ki fara shirin komawarki India"
Azrah ta sunkuyar da kai ta ce
"Toh Bappah, nagode" haka kawai taji yanzu kuma bata son karatun ma, Bappah ya juya ya fita
Umma ta ɗago tana kallon Azrah ta ce
''That's good, dama Nima wannan tunanin sai dana yi, yana da kyau dama ace kinje ɗin duba da yadda idan kika koma makarantar sai kinyi shekara kafin ki dawo''
Azrah ta gyada kai a hankali tana jin zuciyarta na bugawa, ta ce
"Ina missing Dada ma wlh, Zan je''
Zahra dake gefe tana goge hannayenta da tissue ta ce tana dariya
''Ki tafi ki huta da masifar gidan nan, kije ki sha soyayyar grandma''
Daga nan suka cigaba da hira cikin natsuwa da annashuwa, har maganar ta canza zuwa na siyayya da kayan makaranta
Washegari da safe, Azrah bayan ta idar da sallah, bata koma bacci ba kamar yadda ta saba, ta zauna a bakin katifarta tana duba list ɗin abubuwan da zata tsiyawa Dada, kananan jakka biyu ne gefenta daya kayan tafiyarta ne, daya kuma kayan da zata kai wa Dada
Zahra ta shigo da cup ɗin kamu a hannunta ta ce
''Waiii, tun yanzu kika fara haɗa kayan ki? Ke dai tafiya na burge ki'' Azrah ta yi murmushi tana sake nadewa wani gown cikin jakkan ta ce
''Ni fa bana son nayi komai cikin gaggawa ne, In har zan tafi gobe, toh na gama haɗa kaya na tun yau, Sannan bana son zuwa gidan Dada ba tare da tsaraba ba''
Zahra ta zauna kusa da ita
"Wane tsarabar zaki kai mata kenan?" Azrah ta ce
"Nayi list ne, kayan miya, goro, Omo da sabulu, kuka da daddawa, da turaren wuta, Duk na san abubuwan da Dada ke so, Ina so na je kasuwa yau da yamma in sayo komai''
Zahra tayi dariya ta ce
''Toh sai mu tafi tare, ai nima akwai wasu abubuwan da nake son siya a kasuwa, sannan In kuma na raka ki zaki saya min shawarma?"
Azrah tayi dariya ta ce
"Ke da kika ce dama kina son zuwa kasuwar amma kuma kike cewa zan siya miki shawarma"
Zahra ta wani turo baki tana dariya, suka cigaba da shirya kayan tare
Koda suka kammala shirya kayan, Azrah ta ɗauki wata hijabi sannan ta fice zuwa ɗakin Umma, domin sanar da ita zata je kasuwa
Bayan ta shiga ta ce "Umma ina son zan leƙa kasuwa yanzu in sayi kayan da zan kai wa Dada''
Umma ta ce "Toh madallah, Ki kula da kanki, kuma ki tafi tare da Zahra"
Azrah ta ce "Toh Umma"
Daga nan suka fita tare da Zahra suka nufi kasuwa
Lokacin da suka kammala, suka dawo gida Azrah na farinciki saboda ba komai ke birge ta ba kamar ta faranta wa Dada rai
Zahra ta ce
"Lallai Dada zata ji daɗin siyayyar nan Ya Azrah"
Azrah ta dan kalli ledar hannunta ta ce
Dada ta cancanta koomai da na sayo yau zuciyata na cike da farin ciki sbd hakan"
Dakin Umma suka wuce direct, suka samu Umma a zaune tana karatun Qur’ani, Azrah ta zauna kusa da Umma, Zahra kuma ta ajiye ledojin gaban Umma
Azrah ta ce "Umma ga siyayyar ki gani, gobe sai gidan Dada in shaa Allah"
Umma ta rufe Qur'an ɗin ta ajiye , sannan ta fara kallon kayan ta cw
"Allah ya tabbatar da alkhairi, Allah ya kaiki lafiya, ya dawo da ke lafiya, Ki tabbatar kin kula da kanki sosai idan kika tafi" ta karasa maganar tana buɗe ɗayan laidan ta ce
Gaskiya kinyi kokari Azrah, Allah biya ki, itama zata ji daɗi nasani"
Azrah ta ce "Amin ya Rabbi, Nagode Umma"
Washegari da safe...
Umma da kanta tayi musu breakfast, bayan sun karya Azrah ta tafi tayi wanka bata daɗe ba ta gama shiryawan ta, duk suna zaune suna jiran zuwan Bappah
Zahra ta ce
"Wannan blue hijabin ya miki kyau, Dada zata yi murna da ganinki"
Azrah tayi murmushi ta ce
"Toh Allah kaimu lafiya dai"
Bappah ne ya buɗe labulen ɗakin yana kallon su ya ce
'idan kin gama shiryawan ki fito ga mai taxi ya iso"
Azrah ta miƙe tana kallon Bappah ta ce "Tog Bappah, dama na gama shirya wa"
Daga nan suka fito zuwa kofar gidan, Umma ta mika mata laidan data saka mata ruwa da kuma cincin data ajiye mata, Bappah ya bude motar sannan suka shiga suka nufi tasha
A hanya, Bappah ya dinga janta da hira irin ta uba da 'ya yana mata nasiha akan rayuwa, tafiya, da yadda zata rike kanta a ko'ina ba tare da taji tsoron wani ba sai Allah
Bappah ya ce "Kada ki manta inda kika fito, ki tsaya a kan mutuncinki, Kada ki ɗauki abunda ba naki ba, ki kauda ido akan duk wata kelekelen duniya"
Azrah ta amsa cikin ladabi ta ce
"Insha Allah Bappah, Na gode sosai"
Suna isa tasha, Bappah ya saya mata tikiti sannan ya raka ta har gaban mota, ta shiga motar
Bappah nata tsaye har motar ta tashi
Bappah ya mata whispering da "Allah ya kai ku lfy Azrah, ki kira Umma da zarar kin isa"
Motar ta ja ta tafi... Azrah na gyaɗawa Bappah kai tana waving dinsa
A cikin mota Azrah taji wani nutuwa,Kullum idan tana hanyar gidan Dada akwai wani sanyi da nutsuwa da zuciyarta ke ji. Bayan tafiya na kusan awa guda da rabi, suka isa garin. Bayan fitowa daga mota, ta tare mai adaidaita saho ta faɗa masa inda zai kaita
Tana shiga gidan, Dada tana zaune a baranda tana faman jan tasbihi tana zaune akan sallaya
Dada ta ɗaga kai tana kallon Azrah da mamaki karara a fuskanta ta ce
"Eyyy! Wannan kamar Azrah nake gani!"
Azrah ta karaso da gudu ta rungume Dada tana dariya ta ce
"Dadaaaa! Gani na iso!"
Dada ta riƙe haɓa ta ce
"Allahu Akbar! Jikata ta zo! Kai Allah na gode, ya kika baro gidan?"
Azrah ta ce"duk lafiyan su Klau suna gaishe ki"
Dada ta miƙe ta ce "mu shiga ciki kawai dama iska nake sha anan ɗin" azrah ta mike tana ɗaga kayanta suka shiga ciki
Siyayyar data ma Dada ta miƙa mata, Dada ta ce
"Ke har da tsaraba? Allah miki albarka yarinyar nan"
Episode 42: A Storm of Silence
Da daddare...
Azrah na zaune a tsakar gida tare da Dada bayan sauran yaran da ke yawan zuwa wajen ta sun koma gidajen iyayensu. Daga gefe Dada ta kalleta cikin muryan kaka da jika ta ce
"Azrah gashi na sallami yaran nan sun koma gidajensu na manta basu siyo min maganin sauro ba, Ki taimaka ki je ki tsiyo mana maganin sauron, wannan garin sai da maganin sauro inba haka ba sauron nan sai suyi ajalin mutum"
Azrah ta amsa da ladabi ta ce
Toh Dada" ta mike cikin nutsuwa, ta ɗauki hijab dinta dake gefenta ta fice waje dan tsiyowa
A waje kuwa, wasu samari uku suna zaune a gefen wani gida few houses da gidan Dada, ɗaya daga cikinsu ya hango ta tana zuwa sai ya langwabar da kai ya ce
"Yarinyar nan fa... Amma baƙuwa ce ko? Amma tana da kyakkyawa ce"
Dayan daga cikinsu ya amsa
"Ai jikar Dada ce, takan zo lokaci zuwa lokaci ai, a cikin garin Katsina take ai, Azrah sunanta kamar"
Suna cikin Maganar Azrah ta karaso shagon dake wajen da suke zaune ko da wasa bata yarda ta kalli inda suke zaune ba, har ta tsiya abinda zata siya ta juya zata gida
"Assalamu Alaikum" daya daga cikinsu ya fada cikin fara'a
Azrah ko kallon su bata yi ba, balle ta amsa, ta wuce kai tsaye kanta a ƙasa
Saurayin da ya fara magana ya kalli abokansa ya ce
"Kai! Wannan yarinyar ba kalan 'yan matan mu na Nan bane, ji yadda ta wuce ko kallon mu bata yi ba"
Ɗayan saurayin yayi dariya ta ce
"Ai idan na tsaya mata a gaba, duk yadda take ji da kanta sai ta kulani"
Bayan Azrah ta dawo daga tsiya magani ta shiga gidan cikin gidan da sallama a bakinta, Dada tana zaune a kan tabarma tana karanta wani littafin addu'o'i
Dada ta ce "Sannu da zuwa, kin samu maganin kuwa?"
Azrah ta ce "Eh Dada na samu"
Suna cikin magana ne aka fara kiran sallar Isha'i daga masallacin dake jikin gidan
Dada ta ce "An fara kiran sallah, mu yi sallar sai mu kwanta ko?"
Azrah ta kyalkyale da dariya ta ce "Haba Dada, haka kike kwanciya da wuri? Daga sallar Isha'i sai bacci?"
Dada ta girgiza kai da murmushi a fuskarta ta ce "Eh mana, toh me za a yi da dare idan ba baccin ba? Sai dai bacci, ai ba kamar ku matasa da kuke da wayoyinku a hannun ba dake hana ku bacci da wuri ya ɗauke muku hankali"
Azrah ta ce "Ni kam ban saba da kwanciya da wuri ba Allah ma ya gani"
Daga haka suka tashi suka gabatar da sallar Isha'i cikin natsuwa, Bayan sun idar suka zauna, Dada ta fara ba Azrah labari ganin tace mata bata saba kwnaciya da wurin ba
Dada ta ce "Kin ga wannan Bappah ɗin naku? Allah sarki yaro me min biyayya, baki ga da ba yadda yake da mugun arziki, kafa unguwar nan babu wanda ya kaisa arziki da manyan gidaje, yana daga cikin manyan masu kuɗi na yankin nan, irin kula da Bappahn ku ya bani a rayuwa? Babu kalar rayuwar jin daɗi da banyi ba, amma Allah sarki, Allah ya jarabce shi da karayan arziki"
Azrah kamar zata tambaye ta aina aka dauko Umman su amma sanin Umma bata kaunar su sani sai kawai tayi shiru
Suna cikin hirar su kenan sai ga wani yana doka sallama a ƙofar gida, can kuma sai wani ƙaramin yaro ya shigo ya gaishe da Dada
Yaron ya ce "Dada ana magana da bakuwarki a waje wai inji wani mutum"
Dada ta washe baki cike da sha'awa "Toh, gata nan zuwa"
Ta kalli Azrah da murmushi ta ce "Tashi ki fita ki ji kiga wanda ke tambayarki"
Azrah ta ɓata rai ta taɓe baki ta ce "Ni fa ba inda zanje" Ta ja hijabinta ta kwanta akai
Sai kuma ta sayar da yaron da sauri ta ce "Kaiii, je ka ce masa tayi bacci"
Dada ta yi shiru tana kallon Azrah wanda kana ganinta bata so abinda Azrahn tayi ba, kawai ta miƙe ta wuce kan gadonta ta kwanta ta juya mata baya ta ce
"Toh, idan kin gama zama ki kashe mana wuta, ni dai sai da safe"
Azrah ta san Dada ba ta ji daɗin rashin fitarta ba, amma kuma bata ji zata iya fitan bane, ta murmusa kawai, ta ɗauki wayarta, duk da tana sanmanin Khalil na bacci, amma haka ta fara dialling numbern sa
Wayan sa na fara ringing ga mamakinta kawai sai ya ɗaga kiran, da damuwa sosai a muryan sa ya ce
"Azrah? Are you okay? I've been calling you all day"
Azrah ta ce "I'm fine, Khalil! Sorry... I travelled to my grandma's place, The network here is poor and I kept the phone inside most of the time"
Ya sauke wani ajiyar zuciya ya ce "I was worried, you didn't reply to my WhatsApp or Imo call, I thought something happened"
Azrah tayi murmushi har yana iya jin sautin ta ce "No, not at all. I'm safe, Just didn't want to be too glued to my phone here"
Khalil ya ce "Okay then, I'm relieved, How's the place? Calm?"
Azrah ta ce "Very calm, Simple life, Just the usual village routine"
Khalil ya ce "Hmm. By the way, I only have one more paper left next week, Once I'm done, I'll be flying back to Egypt"
Azrah tayi shiru na wani lokaci. Zuciyarta taji ya fara bugawa da sauri da sauri ta ce
"So you'll be gone before I return?"
Khalil ya ce "Maybe... but I'm not staying long, I'll come back, just because you'll be here"
Azrah ta ce "Why would you come back? You'll be done with school right?
Khalil ya ce "I'll start my PhD, in Shaa Allah, I told you, you're the reason I want to build here, With you in my future Azrah, I see purpose"
Azrah tayi shiru tana son gano maganarsa sai kuma tayi blushing, haka kawai take jin wani tranquility na sauko mata
By 10pm ta fara jin bacci ta ce
"Khalil... I'm really sleepy now" ya ce
"Alright. Sleep well, beautiful, Sweet dreams"
Azrah ta ce "You too"
Bayan ta kashe wayan ta mike ta fita zuwa waje, tayi alwalan bacci sannan ta koma ɗakin, kan gadon ta hau a hankali sannan tayi addu'r bacci ta kwanta tana jin zuciyarta fess
Washe gari bayan sallar asuba, bayan Dada da Azrah sun ɗan tsaya sunyi karatun Alƙur'ani tare, kowannensu ya koma gado. Nan ko suka koma bacci, basu suka tashi a bacci ba sai wajen ƙarfe tara na safe da rabi, Dada ta tashi tana kallon agogon ɗakin, ta juyo da murmushi tana kallon Azrah da ke kwance ta ce
"Azrah... Azrah, kin ki tashi har tara ya wuce ashe"
Azrah ta bude idanu cikin kasala ta ce "Na tashi Dada"
Dada ta ce "Toh tashi mu ɗan ci wani abu dan yunwa nake ji"
Bayan Azrah ta miƙe sai kuma ta ce
"Je ki tsiyo mana koko da kosai kawai idan yaso sai da rana muyi girki"
Azrah ta gyada kai ta ce "Toh Dada"
Dada ta ce "Ko baki ci? Kar Kije ki sayo abin da baki ci kinga an shiga hakkin ki"
Azrah ta yi dariya ta ce "Haba Dada, shekara guda nayi a India amma kamar wadda na taso can da zance bana ci, Ni dai ba zan ƙi koko da kosai ba kema kin sani"
Dada ta kyalkyale da dariya ta ce "Toh shikenan, jeki ki tsiyo mana a makwabta"
Azrah ta shirya cikin doguwar riga mai sauƙi da gyallen sa, ta fito tana tafiya a hankali, jiki ya bata idanu na bin ta, hakan ya sa ta ɗan daga kai, kawai taga yawancin mazan garin da suke zaune a gefen titi ko a ƙarƙashin bishiya duk ita suke kallo
Wasu na zuba mata ido kamar za su ci ta da kallo. Wasu na faɗa wa juna daɓi’un 'yan birni irin “
"Waccan fa jikar Dada ce, ko da wasa ba zata kula ku ba, gwara ku daina wahalar da kai"
Azrah kuwa, ganin irin kallon da t
ake mata, sai kawai ta sauke kanta ƙasa, ji take kamar zata fadi, ji tayi ranta ya ɓaci, zuciyarta cike da takaicin su, tayi alkawarin ba zata sake fitowa aika ba,
Ta sauri ta karasa wajen mai koko, ta tsiyo musu da kosai, sannan ta juya zuwa gida da sauri zuciyarta na addu'ar Allah ya kare ta ya kaita lafiya dan ji take kamar har kafafunta na harharɗewa.
Azrah na zaune a gefen tabarma tana ɗan matsa kafafunta da hannunta, tana kallon Dada da ke kokarin kwashe sauran abin da suka dafa da rana. Bayan sun gama cin abincin ranan tare, suna hirarsu sai ga yaran dake zuwa wajan Dada sun cika gidan yara da manya wanda yawanci su san zo ne saboda Azrah, dan yawan wanda suka zo sai da Dada tayi mamaki dan wasun basu saba shigowa ba
Azrah kuma ba karamin sake wa tayi da yaran ba, wanda suka dinga shan hirarsu tare, har basu kaunar tafiya yadda Azrahn ta sake musu fuska
Samarin garin kuwa haka suka dinga aikawa a musu magana da Azrah wanda ko da wasa bata fita ta kalli mutum ɗaya a cikin su ba, Gaba ɗaya sai abun ya fara damun Dada, musamman ganin yadda take ƙin mu'amala da mutanen garin.
Bayan sun idar da sallar Isha'i ne Dada ta juya tana kallon ta, ta ce
"Zo Azrah, akwai maganar da zamu yi"
Azrah ta zauna tana kallon Dada da hankali
Dada ta ce" Akan meyasa za'a ta zuwa wajenki ke kuma kiki fita? Ko a tunanin ki za'a zuba miki ido ne? Aure fa dole ne Azrah, ko dan Kinga Bappah'n ku bai takura miki bane shiyasa kike koran wanda suke son ki"
Azrah ta juyar da kanta gefe, tana avoiding eye contact da Dada, ta ce
"Yanzu fisabilillah Dada, idan zan ma kula mutane sai na kula mutanen nan?"
Dada ta zaro idanu, cikin mamaki tana kallonta ta ce
"Ban gane ba? Su ɗin ba mutane bane? Ko menene?"
Azrah ta lumshe ido ta ce
"Gaskiya nikam ba suyi min ba, kuma gaskiya ko da zan auri mutum nafi son mai ilimi ne harga Allah"
Dada ta ɗan yi shiru tana kallonta can ta ce "Su ɗin basu da ilimi kenan suka ce miki?"
Azrah ta ce "Toh Nima ban sani ba, amma gaskiya ba wanda yayi min a cikin su.
Dada ta sauke ajiyar zuciya, tana ɗan girgiza kai ta ce
"Toh, gaskiya zan yi magana da Bappah'n ku, Dole ya saka ku fara fitar da miji, Ni wallahi banga hankali tattare dake ba, Haka kike son zama? kina ƙin mutane da suke son ki?"
Azrah ta turo baki ta miƙe tana jan gyale kanta ta ɗaura ta wuce kan gado ta ce
"Dada Ni dai gaskiya ba zan iya auren 'yan nan ba, shiyasa ma ba zan fara fita ba, Ni dai yanzu zan kwanta sai da safe"
Dada ta bita da kallo tana jin takaicin abin da tayi ta cigaba da mitar ta
"Ku 'yanmata yanzu kun raina auren da mutunci, Ke yanzu da kike da kyau, kina da ilimi, amma bakya da sauƙin kai ƙautaƙauta, taya mazan zasu iya tare ki?"
Azrah ta shige cikin bargo tana murmushin ta, bata damu da mitar Dada ba, ta ina zata fara da waɗannan mazan da basu da kamun kai...
Da sassafe bayan sallar Asuba, Azrah ta zauna tana gyara kayanta na cikin jakkanta, tana kallon ledojin da Dada ta ajiye mata gefen kayanta, sai ga Dada ta shigo fuskanta da alamar rashin jin daɗin rabuwa ta ce
"Toh Azrah, yau zaki barni kenan?"
Azrah ta ɗan yi murmushi ta ce
"Eh Dada, dama Bappah yace yau zan koma, gobe ko jibi zan fara shirye-shiryen tafiyana makaranta"
Dada.ta ce "Allah ya kai min ke lafiya ya kuma karemin ke"
Azrah ta ce "Zan dawo Dada, idan muka sake Hutu" ta rungume Dada tana jin ƙamshin tsantsar ƙauna da kulawa
Bayan sun karya kumallo tare, Azrah ta duba duk ledojin da zata ɗauka, ciki har da kayan da ta siya wa Mai sunanta Zahra
Dada ta ce "kar dai ki manta da kayan Mai sunana tahm, dan akan wannan haka zaki dawo ki sake ɗauka mata"
Azra ta yi dariya ta ce "Toh Dada, ba zan manta ba"
Tasha....
Dada na tsaye a jikin Motarsu har motar ta cika
Dada ta ce "Ki cigaba da zama da tarbiyyar da muka baki ko a gida ko a can Indian din, ki nisanci faɗa da mutane, ku cigaba da kuka da ibadunki kuma"
Azrah ta ce "Insha Allah Dada"
Haka motar ta tashi, suka kama hanyar cikin garin Katsina....
*Scene: Gida*
Suna isa cikin Katsina, Azrah ta tsara mai adaidaita ya kaita har kofar gida...
Zahra ce ta fara tarbar Azrah da murna, jin karan Napep ta fito da sauri ai kuwa ita ce
Zahra ta rungume tana daukan mata Jakkanta ta ce
"Eh Lallai Dada ta ɓata ki, ji yadda kika koma"
Azrah ta ce "Ko kadan, wannan sharrin ki ne kawai" daga haka suka shiga cikin gidan
Episode 43: Between Paths and Promises
Bayan wasu kwanaki...
Kamar yadda suka saba kowa na harkar sa ne a gidan tun faruwan wannan incident ɗin Azrah da Abdul, yau Laraba saura kwanaki Azrah ta koma India saboda week din da zasu shiga za'a yi resuming. buɗe idonta tayi ta jawo wayanta ta kunna, kallon lokacin da tayi pass 9am yasa ta miƙe zaune, bayan ta gama tattaro nutsuwarta sannan ta miƙe ta nufi ɗakin Umma
Zahra ta ɗaga kai tana kallonta ta ce "Ya Azrah ke da zaki yi resuming next week ai kamata yayi da safe zaki tafi dan ayi clearing dinki da wuri kar a samu wasu issues"
Azrah na murmushi ta zauna gefenta tana kallon ta, ta ce
"Gaskiya dai, yau nake son zuwa Scholarship Board don karɓar final clearance dina, da zarar sun sa hannu, shikenan na gama komai sai tafiya idan Allah ya yarda"
Umma ta shigo daga waje da veil dinta a kafaɗarta tana kallon Azrah da har sannan idanuwanta bai game washewa daga bacci ba ta ce
"Ki tabbatar komai na cikin file ɗin ki Azrah, Passport ɗinki, admission letter, medicals, da sauran takardu, ban son sai kin tafi kuma kice baki dau kaza ba"
Azrah ta ce "Toh Umma, na haɗa komai tun jiya, sai dai na shirya yanzu kawai na tafi"
Umma ta ce "Kiyi sauri ki je saboda ki samu ki dawo da wuri dan ganin yaushe ne tafiyar naki kar kuma ace available flight jibi ne"..
A cikin dogon wata Maroon Abaya da ta amshe fatar jikinta tayi mugun kyau Azrah ta shiga harabar Scholarship Board Office, Bayan ta cike wasu forms, ta miƙa takardunta ga jami'in da ke duba su.
Officer ɗin ya ce "You've been cleared already for departure. Your documents are intact. Just make sure to report to the embassy before Friday for your visa stamping"
Azrah da murmushi ɗauke a fuskarta ta ce "Thank you so much sir. I appreciate it"
Officer ɗin ya ce "Safe trip ahead. You've made the country proud, keep it up Miss Azrah"
Azrah na murmushi ta ce "In Shaa Allah, sir"
Tana fita daga ofishin, ta sauke ajiyar zuciya tana jin wani sabo yana yi, buɗe handbag ɗinta tayi ta Ciro wayarta ta kira Bappah don shaida masa cewa ta gama komai
Bappah na ɗagawa Azrah ta ce "Bappah na gama clearance, Zasu aika da report din zuwa Embassy, yanzu sai dai na shirya dan kai musu sumin signing"
Bappah ya ce "Alhamdulillah, Amma dole sai an kai can Embassy ɗin kenan?"
Azrah ta ce "Eh haka dai suka ce"
Bappah "Toh shikenan, bari muga yadda abin zai kasance" daga haka ya katse kiran
Azrah ta fito daga cikin harabar scholarship board hannunta rike da takardun clearance da suka tabbatar da tafiyar nata nan kusa ne, Duk da rana bawai yayi bane amma hasken rana ya ɗan dusashe kamar za a yi ruwan sama, iska mai ɗauke da ƙamshin kasa yana kaɗawa, alamar dai ruwan zai sauko anytime
Haka kawai ta tsinci kanta tana farin ciki atleast zata koma India as Level 2 students, wani murmushin ne ya sake kubucewa a fuskantar tana gyara veil ɗin kanta saboda iskan da ake yi, wani abu ne yayi flashing a kwakwalwarta nan take taji zuciyarta ya buga, tafiyar nata ma taji bata wani dauki, yanzu haka zata koma can baya nan? Taya zata fara copping, hawaye taji amma bata bari ya zubo ba
A haka take tafiya a hankali harta isa bakin titi. Ta nufi inda za ta tare adaidaita, tana tsaye tana ganin duk Napep ɗinda zai wuce da mutane a ciki, wata mota ta yi parking a gabanta. Bata buƙatar
kallon wanda yake ciki domin ta riga da ta san motar, Motar Honorable ce
Duk da yadda zuciyar ta ke bugawa da sauri da sauri amma haka ta dake taki kallon direction ɗin motar, Ji tayi kamar ta juya ta bar gurin amma wata murya cikin zuciyarta tace mata kar tayi hakan dan duk walwala da suke ciki tsilansa ne ko ba komai bayi deserving haka daga gareta ba
Kawai samun kanta tayi ta karasa jikin motar a hankali kamar wacce aka ma dole, Ya sauke glass ɗin gefe yana murmushi
"Assalamu Alaikum Azrah," ya ce da wata very calm voice dinsa
"Wa'alaikum salam, Ina wuni, Sir?" Ta amsa cikin ladabi, kanta a kasa as usual
"Alhamdulillah, Ya karatu? Yaushe zaki koma kuma?" Ya tambaya yana kallon ta da kyau
"Alhamdulillah, Insha Allah jibi zan tafi, abinda ya kawo ni nan dinma yanzu dan clearance din ne" Ta amsa, tana ƙoƙarin kin kallonsa dan tana jin idanuwansa akanta
Ya kai hannunsa cikin dashboard ɗin motar ya ciro wani bundle na kudi, yana miƙa mata ya ce
"Karɓi wannan ba yawa dai, ko ruwa kya siya da shi"
Azrah ta ja baya da sauri ta ce "Nagode sosai, Sir, amma…"
Ya yamutsa fuska, yayi saurin katse ta yana fadin
"Ke yanzu har kin fara jin girma ko? Naga ba roka kika yi ba kawai naji na baki kyauta ne"
tayi shiru tama rasa tunanin da zata yi, har sannan kuma bai sauke hannunsa daga mika matan ba, ta miƙa hannu a hankali ta karɓa, ta ce
"Thank you sir, Allah ya saka da alkhairi" ta faɗa ƙasa ƙasa
"May Allah be with you, Azrah" ya faɗa yana kallon ta kamar yana da wata tambaya a zuciyarsa amma ya rasa ta ina zai fara, sai kallonta daya zuba mata ido yake yi, ita kuma ganin kallon ya fara yawa yasa ta ce
"Amin" a takaice dan yanzu babu abinda take so kamar ya bar wajan, kawai ya ja glass ɗin motar sama a hankali, sannan ya ja motarsa ya tafi
Azrah ta tsaya na ƴan dakiku kafin ta nufi gefen titi, ta tare adaidaita saho, zuciyarta cike da abubuwa masu nauyi da babu wanda take da damar faɗa musu su kuma fahimce ta.
Azrah na shiga gida bayan dawowarta daga scholarship board, ta samu Umma a ɗaki tana kulla kanwar sayarwa, ta zauna kusa da ita cikin natsuwa, tana fuskantar ta da murmushin data kirkira ta ce
"Umma na dawo…"
"Umma ta ce "Sannu da zuwa 'yata, ya abin naku ya kasance?"
Azrah ta ce "An gama komai, sai dai sun ce dole ne na tafi embassy a Abuja nayi signing kafin a bani visa"
Umma ta kalli Azrah da mamaki ta ce
"Me ya sa ba za su aika irin wancan tafiyar naku ba? Naga ai wancan haka suka yi babu wani signing da kika je yi ko?
Azrah ta ce "Wallahi ni ma ban sani ba, haka kawai aka ce za a je wannan karan ban san kuma menene yasa su fadan hakan ba Nima Umma"
Umma ta sauke ajiyar zuciya, nan da nan har fuskarta ya cika da damuwa ta ce "Toh yanzu kenan zaki tafi Abuja?"
Azrah ta ce "Haka suka ce Umma"
Umma ta ce "Amma fah ace kawai kije kiyi signing ki dawo naga za'a kashe kudi ga kuma tafiya a gabanki kina bukatar wasu abubuwa naga ai"
Azrah tayi shiru tana nazarin maganar Umma, tasan Umma tayi gaskiya dan yanzu ace taje ta dawo ma, babu wani lokaci kuma dole zasu kashe kuɗi, kawai ta jawo wayanta ta shiga text na Honorable without second thought ta fara typing...
Faɗa masa cewa ance sai ta tafi tayi, sannan ta danna send message ɗin ya tafi
Bayan mintoci kaɗan sai ga message dinsa shima ya reply dinga back
"Ki haɗa Everything yanzu za'a zo a karɓa za'a tafi dashi yanzu idan ya so a dawo miki da shi gobe tunda flights zasu bi"
Azrah ta ji dadi sosai da wannan sakon nasa, ta juya tana kallon Umma sannan ta shiga narrating mata...
Da Daddare bayan sallar Magrib
Honorable ya aiko mata da saƙo
"Ina waje zaki iya bada wa a kawo min"
Azrah ta ɗan tsaya tana kallon message ɗin sai kuma ta wuce daki da sauri ta fito da komai na takardar signing ɗinta ta fita zuwa waje..
A hanya zuciyarta cike da nauyi, da kunya, ta fita bata ga motarsa a kofar gidan nasu ba sai ta hango motarsa daga nesa, ya tsaya houses away from their home, Ashe yayi hakan ne saboda mugun kunyar Bappah daya ke ji yasa ba zai iya karasowa ba
Ta karasa har inda yake, bayan sun gaisa ta miƙa masa takardar, buɗe motar yayi ya karɓa, yana kallonta cike da regret da kuma tausayinta ya ce
"Na karɓa, In Shaa Allah idan suka isa bayan Isha'i gobe za'a miki signing"
Ta gyada kai kawai, sannan ta juya ba tare da ta kalli fuskansa ba ta fara tafiya tana jin wata irin sanyi a zuciyarta, cike da godiya da kuma tambaya Me yasa ta kirasa har ta basa? Me yasa yake damuwa da damuwarta har kulawa da ita haka?
Habibah da Siyama da suka shigo layin nasu a gajiye ashe tun daga nesa suke kallonsu, bakin ciki ƙarara ya bayyana a fuskokinsu su, suna shiga ko Bappah dake compound basu lura ba suka wuce dakin Mama dan kai mata gulma, da rahoto
Azrah ta karasa cikin gidan nasu tana shiga taga Bappah tsaye a tsakar gida, hannunsa goye a bayansa yana kallon ya dakatar da ita ya ce
"Ke Azrah... da wa nagani kina magana a jikin mota?"
Azrah ta tsaye cak, ta sauke idanunta kasa ta ce
"Eh... Honorable ne Bappah"
Bappah da wani expression ya ce "Honorable? Me kike yi da shi a wannan lokaci toh?"
Azrah ta ce "Bappah… ai Umma ce naga maganar kai takaddun Embassy ya dame ta shine na tura masa text akan dole sai na tafi Abuja signing shine yazo ya karba yace akwai masu zuwa Abuja a daren nan, gobe sai kawai a min signing a turo mana"
Bappah ya ce "Toh kenan shine ba zaki sanar dani ba?"
Azrah ta sauke idanu ƙasa, muryarta na rawa ta ce
"Ai baka gida ne Bappah, kuma naga kar ayi wasting time ne tunda tafiyar yazo ne akan idan ka dawo zan maka baya Ni"
Bappah yayi shiru, yana kallon ta, sai can ya ɗan gyara tsayuwarsa ya ce
"Next time duk wani abu da ya shafi tafiyarki ko wani abu ki sanar dani farko, uwarki mace ce, ni nake da alhakin ki, kinji ko?"
Azrah ta gyada kai da ladabi ta ce
"Na fahimta Bappah, in sha Allah bazan sake ba"
Bappah ya ce "Ki je kiyi sallah lokaci yayi"....
Azrah na kwance a kan katifarta, tayi nisa cikin tunanin da take yi, yanzu ga maganar Umma da Bappah wanda bata san yadda zata yi ba, ga maganar idan ta tafi Khalil baya nan,rabon data shiga damuwa kila tun lokacin da take neman kudin Waec, wayanta dake gefenta ta jawo tayi dialing numbern khalil
Khalil bugun farko ya ɗaga ya ce
"Hello my Azrah…Muryarsa cike da natsuwa
Azrah ta ɗanyi shiru jin My daya ce, sai kuma ta dake ta ce
"Hey... Khalil, how was your trip?
Khalil ya ce "Alhamdulillah. I just landed safely in Egypt this morning. I've been trying to reach you"
Azrah ta ce "I know…"
Khalil ya ce "Hmm, it's okay. I missed your voice"
Azrah tayi shiru, tana kallon ceiling kamar tana kokarin danne wani abu a zuciyarta, ita dai yau bata fahimce sa ba, sai jin muryan sa tayi ya katse mata tunaninta ya ce
"Are you okay?"
Azrah ya ce "I don't know... I was really looking forward to this India trip, but now that you're gone back to Egypt, it doesn't feel the same"
Khalil Softly "Azrah your journey is still valid, Our dreams don't pause just because we're far apart"
Azrah at this point ya sake daure ta ne da maganganun sa, kawai samun kanta tayi da ce masa
"I guess... I just wish you were still around" sai kuma ta rufe Fuskarta da sauri kamar yana ganin ta
Khalil ya ce "Don't worry, I'll be back before you even realize it And besides, I want you to talk to someone... my mom"
Azrah da mamaki ta ce "Your... mom?"
Khalil ya ce "Yes. She's here with me, She keeps asking about you. Let me put her on"
Azrah ta ji gabanta ya fadi, murya wata Mata ne, with very calm voice tayi mata sallama
"Salam Alaikum dear Azrah"
Azrah tana murmushi ta ce "Wa'alaikum salam Ma..."
Mama Khalil ta ce Khalil talks about you all the time. You must be special. May Allah bless your journey and protect you always deat"
Azrah na Murmushi haka kawai taji wani farin ciki ya mamayeta ta ce "Amin... Thank you so much Ma"
Mama Khalil ta ce "In shaa Allah we'll meet someday, Stay strong and stay focused. Good night, sweetheart"
Ta mayar da wayar ga Khalil. Sallama suka yi sannan ya katse kiran. Azrah ta sa wayar a gefenta, ta lumshe ido bata san ma tana murmushin dake kubuce mata ba.
Washegari... Azrah na zaune a dakinsu tana gyaran kayanta, wani ya leko yace ana sallama da ita a wajen, hakan yasa Umma ta shiga ciki dan sanar mata
Umma ta ce "Azrah ki je ki, ana neman ki wai a waje nace ko honorable ne"
Azrah ta mike da mamaki, ta fita zuwa kofar gida sai taga
Honorable tsaye da takardu a hannunsa, ta karasa inda yake tsaye a jikin motar sa, tun kafin tace komai ya ce
"Good evening, Azrah"
Azrah ta dan sunkuyar da kai ta ce "Afternoon sir"
Honorable yana mik'a mata takardun ya ce "Gashi har an samu an gama, sai tafiya ta rage yanzu Jin Shaa Allah"
Azrah ta karba da ladabi tana murmushi ta ce
"Thank you so much sir. Allah ya saka da alheri"
Honorable ya ce "Ameen. Make sure you go through them idan da matsala sai kiyi magana"
Azrah ta ce "In shaa Allah. Nagode sosai"
Ya juya ya shiga motar sa, Azrah kuma ta tsaya kallon takardun a hannunta Sai kuma ta juya a hankali ta nufi hanyar shiga gida
Episode 44: The Crossing Point
Cike da tashin hankalin Siyama ta ce "Mama! Mama ina kike ne wai?"
Ganin kamar Mama bata nan yasa Siyama ta zauna kamar wadda aka hankaɗata ta ce
"Habibah kin ga wannan motar kuwa? Wannan ba irin motocin unguwar nan bane fah, ace Mama na raye wani ya zo ya tsaya wa Azrah fa!?"
Habibah ta ce "Naga sanda yake miƙa mata abu fah, Tabbas akwai wani abu a kasa dan ba kowa ke zuwa wa yarinya gida a irin wannan unguwar da irin wannan mota ba kai tsaye ba, wani mai kuɗin ne zai kula 'yar talakawa idan ba wani abun yake kawo sa ba"
Mama ta shigo rike da kaya a hannunta, tana kallon su ta ce, "Lafiya Nagan ku haka ?"
Habibah tayi saurin cewa "Mama wallahi akwai abin da muka gani zauna ki ji, Wani mutum ne ya zo a babban mota wajen Azrah"
Mama ta kafe su da ido, taji jinta da ganinta ya ɗan dauke, can ta ce a hankali "Kun tabbatar?"
Siyama ta ce "Eh Mama, a layin nan fah ya parka motar, can kofar gidan Maman shafa'afu ya tsaya, harda mika mata wani abu, ta karɓa tana murmushi"
Mama ta ajiye kayan hannunta kamar an zuba mata ruwan sanyi, tayi tagumi sai kuma ta fara girgiza kai ta ce
"Ni Uwani ina da rai har wani zai sake zuwa wajen Azrah? Inaaa wannan sai dai a mafarki"....
Azrah ta gama saka kayanta cikin trolley, tana dubawa don tabbatar da babu abinda ta manta. Sai ga Umma ta shigo tana rike da leda a hannu, ta ajiye ta a gefe ta ce
"Gashi nan Azrah. Na san abubuwan nan zasu miki amfani a India kafin ki samu acan, Citta ce, yaji, kanwa, da kuka, sannan ga kaninfari da tafarnuwa ma a ciki"
Azrah ta rungume Umma da godiya a fuskarta "Nagode Umma, Allah ya saka da alkhairi."
Umma ta zauna a gefenta, ta dauki wasu kaya cikin trolley din, ta ce
"Amma har yanzu baki iya jera kaya ba Azrah. Duba yadda kike barin space kamar wanda zata dawo gobe. Ki bari na nuna miki yadda ake jera kaya irin na tafiyar nesa"
Suna cikin haka sai ga Zahra ta shigo tana kallon su da murmushi, ta rike ƙugu tana cewa
"Iyyyeee! Kayan tafiya ma sai Umma ce ke jera miki? To sannu yar gatan Umma"
Azrah tayi dariya "Ke ai kin sani, ko ban fada ba Ni 'yar gatan Umma ce"
Umma ta ce "Ina ruwanki da mu?
Dole na taimakawa ɗiyata"
Suka yi dariya gaba ɗaya, cike da annuri
Daga haka suka fita zuwa dafa abinci tare a kitchen, suna cikin girkin Azrah ta ce da Zahra cikin taushin murya
"Zahra wlhi duk da farin cikin tafiyar nan, gaba ɗaya inajin wani irin a zuciyata, taya zan bar Umma cikin wannan sabon yanayin da Bappah ya tsiro da shi, Gaskiya ina jin tausayinta matuka"
Zahra ta tsaya tana kallonta, ta ce
"Kada ki damu Ya Azrah. Ki je ki yi karatunki. Kila Allah yasa in kika gama kika fara aiki Umma ta samu sassauci, Kuma kin san ni, baki na baya shiru. In shaa Allah ba wani abu zai kuma faruwa. Nayi niyyar tackling komai da kaina"
Azrah ta juyo tana kallon Zahra da murya kamar mai shirin kuka, "Nagode sosai Zahra. Allah ya miki Albarka, ya kuma cika mana burukanmu"
Bayan sun gama girki, suka shigar ɗaki suka zauna suna ci dukkansu a plate ɗaya suna ɗan hirar su gwanin sha'awa, Zahra ta dauko wayar Azrah wadda ke ta ƙara "Samira ce" ta faɗa mata tana miƙa wayar da murmushi a fuskarta
Azrah ta karɓa, tayi picking ta kai kunnen ta "Wallahi dazu nayi ta kiran ki baya shiga" ta faɗa
"Eh, dazu sun kashe WiFi ne" cewar Samira daga dayan bangaren na wayar, ana jin muryarta cikin nishadi "Yaushe ne zuwanki yanzu?"
"Gobe da safe zan tafi Abuja, da yamma kuma zamu tashi In Shaa Allah''
"Allah ya kawo ki lafiya kawata" Samira ta faɗa
"Amin, nagode"
Samira ta ce "Kin san an canza mana hostel?"
Azrah ta ce "Haba dai!"
"Wallahi, Na gama mana komai fa ɗazu, sai kin zo dai zaki gani yafi namu na farko komai"
Azrah ta yi godiya sosai, sannan suka yi sallama, ta daura kanta a cinyar Umma tana jin sanyi a zuciyarta, duk da shirye-shiryen tafiya da excitement ɗin shiga 200 Level ta ji wata damuwa ce ke danne zuciyarta
Duk suka yi shiru kowa da kalar tasa tunanin, Bappah ya turo ƙofar ɗakin, ya tsaya yana kallon Azrah ya ce
"Ke Azrah, tashi kije ki faɗa wa Mama tafiyar ki gobe ne, kar sai gobe kice zaki mata sallama"
Zahra ta ɓata fuska ta ce ƙasa ƙasa "Hmm tabdijam…"
Bappah ya fice daga ɗakin, Umma tama Zahra wani kallo ta ce "Sannu mara kunya, itama ki zugata ki huta kawai"
Zahra ta kama bakinta "Nayi shiru" ta faɗa
Azrah ta miƙe jiki a sanyeye Zuciyarta cike da rashin kwarin gwiwa ta fita zuwa dakin Mama, da sallama ta shige, Mama na zaune da 'ya'yanta, Siyama da Habibah suna gefe suna hira da dariya
Azrah ta zauna da ladabi, ta gaishe ta Mama ta amsa da kyar tana kallon wani waje "Dama gobe zan tafi makaranta ne" Azrah ta faɗa a hankali
Mama ta yi kamar bata jita ba. Can kuwa ta miƙe ta shige ɗakinta kamar bata da buƙatar ci gaba da zama a wajen, Siyama da Habibah suka cigaba da dariyarsu da hirarsu kamar Azrah ba ta wajen
Azrah tayi ta zama har kusan minti biyar kawai ta miƙe tana kallo Siyama ta ce "Sai da safe"
Siyama ta kalle ta da wani wulakantaccen kallo ta ce "Sai kace mayya, ki tafi mana"
Azrah bata ce komai ba duk da kalaman sun taɓa ta, ta juya ta fita, cikin zuciyarta tana ta addu'ar Allah ya karesu da kiyayyar mutane da hassadansu
Tana shiga ɗaki, Umma ta kalleta ta ce "Kin mata ɗin?"
Azrah ta zauna a ƙasa cikin sanyin murya tace "Hmm, ai ko kallona Mama bata yi ba"
Zahra ta kyalkyale da dariya ta ce "Madallah! Me ya kai ki tun farko?" Sai ta kalli Umma ta gumtse dariyarta
Umma ta mata wani kallon hakan yasa ta mike ta ce "sai da safen ku" Azrah ma ta miƙe tabi bayan Zahra tana ma Umman sai da safen ita ma
Washegari da safe, Umma da kanta ta daura girki. Kamshin abincin duk ya cika ko ina, Azrah na gama shiryawa, ta zaune tana gyara travelling document dinta a cikin jaka, Bappah ya shigo cikin ɗakin yana kallon agogo ya ce
"Kiyi sauri ku gama breakfast kafin nan zan je na taho da mai taxi" daga haka ya juya ya fita ba tare da jiran amsar su ba
Umma ta kalli Azrah ta ce "Kiyi sauri ki samu ki yi breakfast kafin Bappah'n naku ya dawo"
Azrah ta zauna tana ci, duk taste ɗin abincin taji babu wani taste a bakin ta, gaba ɗaya jikinta ya yi sanyi, sai ga Bappah ya dawo, ya turo ƙofar ɗakin yana kallo ta kai tsaye ya ce
"Fito mu tafi" sannan ya ƙara da cewa "kije kima Mama sallama"
Umma ta taɓe baki, tana kokarin danne damuwar da ke cike da zuciyarta. Azrah tayi shiru, sai ta mike jiki ba ƙwari ta nufi sashin Mama. Ko da ta shiga, ta tsuguna da sallama, Mama bata ko kalleta ba, tace a hankali "zan tafi Mama" a fusace Mama ta juyo tana mata wani kallon tsana ta ce
"Wai ni kam ba jiya kinmin sallama ba? Ko sau nawa ake yi ne?"
Azrah bata ce uffan ba ta juya ta fita, ta iske Bappah ya riga ya saka kayanta a cikin booth ɗin taxin, ta tsaya ta kalli Umma da Zahra, tana jin kamar tayi kuka
Rungume Umma tayi da sauri, hawaye na gangarowa fuskarta. Zahra ta rungumeta itama, idonta cike da kwalla.
"Yanzu sai kawai na tafi na barku? Anya banso kai na daya wa ba?" ta faɗa da muryar kuka
Umma ta shafa bayanta tana faɗin "Haba Azrah, sai kace wannan ne tafiyar ki ta farko? Be strong, ko so kike ki hakura da karatun?"
Cikin tsawa Bappah yace "Ke! kizo mu tafi"
Azrah ta janye jikin ta daga jikin Umma da Zahra, tana share hawayen ta, ta shiga taxin babu shiri
A haka suka nufi hanyar airport, zuciyar Azrah na dukan uku uku, kuma har sannan tana share hawayen daya ki tsaya mata
Sun isa airport bayan tafiyar 40 mins, Bappah yana kallon agogo, sannan suka shiga cikin, sashin departure suka nufa, Azrah ta fito daga cikin motar tana jan trolley ɗinta. Fuskar Bappah ta kalla wanda babu walwala ko kaɗan
"Ki bi layi nan ki fara clearing" ya faɗa mata yana nuna mata sashen, ta gyaɗa kai sannan ta nufi wajen
Clearing ɗinta ya ɗauki ɗan lokaci kaɗan. An duba passport, visa, da takardun scholarship ɗinta. Komai ya tafi daidai. Bayan ta gama, ta dawo wurin da Bappah ke tsaye yana waya. Sai da ya gama sannan ya kalleta ya ce, 'Zan wuce yanzu. Allah ya kiyaye hanya, kina isa kuma ki kira mu"
Kafin ta amsa, ya juya ya fara tafiya, tabi bayansa da kallo tana jin zuciyarta yana wani iri at least ai ko amsarta sai ya ji, taji hawaye na shirin zuba ta goge da sauri kafin mutane su fara ganin ta
Azrah ta zauna a waiting area tana jiran jirginsu ya tashi. Tana bin mutane da idanu
Kiran tafiyar su ya fito da ƙarfe tara da rabi, ta mike, ta tura trolley ɗinta a hankali, zuciyarta cike da rudani da fargaba. Bayan kammala bincike na tsaro, ta hau jirgin. Ta zauna a gefen window tana kallon window, Lokacin da jirgin ya tashi, kawai samun kanta tayi ta fashe da kuka
Sun sauka a Nnamdi Azikiwe International Airport, Abuja bayan kusan awa guda. Lokacin da suka sauka, ta fito da jakar hannunta tana dube-duben inda zata jira next flight ɗinsu zuwa India, tana kallon agogo dake nuni da karfe shaɗaya saura
"Flight ɗin zuwa India karfe biyar ne" ta faɗa a ranta
Ta samu guri mai sanyi ta zauna, ta cire hijabinta kadan ta sake mayar da shi daidai. Wani sanyi na airport ɗin yana sanya mata natsuwa, sai dai duk da haka, cikin zuciyarta tana tausayin Umma da Zahra, ga tunanin India, da Khalil ba zai kasance tare da ita ba
ita dai tana zaune tana ta tunani tunani, harda tunanin Future dinta da bata san ya zai kasance ba, kawai sai ga message ɗin Samira ya shigo akan ta turo mata lokacin da zasu tashi saboda zata zo ɗaukanta idan ta isa, murmushi tayi bayan ta gama karantawa
Yayinda agogo ya nuna ƙarfe 4:30pm, wata jami'ar jirgin sama ta fito tana sanar da fasinjojin da za su tafi India su fito domin a fara clearing. Azrah ta miƙe tana gyara hijabinta, ta janyo trolley ɗinta a hankali, zuciyarta cike da kaɗaici
Tana cikin tafiya zuwa layin clearing ne kawai idanunta suka sauka akan wata mata da ta taimaka mata tun ƙuruciya har zuwa girmanta
Mummy ce! Tana tare da Suhaila da Saif. Without second thought, Azrah ta saki trolley ɗinta ta ruga da gudu taje ta rungumi Mummy tana dariya kamar karamar yarinya, Mummy ta kalle ta da mamaki kafin ta buɗe hannu ta rungumeta da kyau
"Azrah! Is that you?"
Azrah ta cire kanta daga jikinta tana gyaɗa mata kai da fara'a ta ce
"Eh Mummy, nice to see you!"
Suhaila ta nufi gareta da murmushi tana cewa
" My Azrah? Gaskiya kin canza sosai"
Azrah ta saki Mummy ta rungume Suhaila tana gaishe ta, sannan ta juya ta ga Saif da ke tsaye gefe yana danna waya kamar baya cikin duniyar nan. ta ɗaure fuska ta ce masa
"Barka da warhaka, ina wuni"
Sai dai bai ko kalleta ba, sai dai ya ɗan gyara tsayuwarsa yana murmushin gefen baki kamar wanda aka takura masa ya mata kallon sama da kasa sanna ya ɗauke kansa
Mummy ta ce "Me kike yi a nan Azrah?"
Azrah ta ce "Mummy, ai na samu schoolarship a India yanzu haka zan shiga Level 2 ne ma"
Mummy da fara'a cike da murna ta ce
"Ma Shaa Allah! Congratulations dear, da fa har ina tunanin zuwa in nemi ki, ashe kin koma makaranta? I'm so proud of you!"
Suhaila ma tayi murna sosai, ta karɓa lambarta. Azrah ta ce
"Zan kira ku in shaa Allah idan na sauka"
Daga haka suka yi sallama, ita kuma ta wuce zuwa inda ake boarding
Clearing ya gudana cikin sauƙi. Tana shiga jirgin, ta samu kujerarta kusa da window ta zauna tana tura trolley ɗinta sama, tana gyara zamanta da takarda da passport a hannunta, ita bata san meyasa ba tafi enjoying jikin window
Ta kalli gefenta, wani matashi ne kallon farko zaka gane wayayye ne kuma ilimi ya zauna a jikinsa, yana sanye da farin t-shirt da jacket mai ɗan tsawo, Kallon da yake mata kamar yana son mata magana ne, sai dai Azrah tayi kamar bata lura ba, ta gyara zamanta ta kalli window.
Bayan 'yan mintuna, wani flight attendant ya fara magana da microphone
"Ladies and gentlemen, welcome onboard flight 6E-211 to New Delhi. Our flying time will be approximately 9 hours. Please fasten your seat belts..."
Azrah ta ja numfashi, ta gyara belt ɗinta kamar yadda aka umarta. Tana jin yadda idanun wannan ke yawo a kanta amma taki juyawa
Lokacin da jirgin ya daga sama, ta lumshe idanuwanta tana ɗora kanta jikin kujerar. A cikin zuciyarta, ta roƙi Allah ya sa tana gama wannan karatun ta samu aikin yi dan Zahra ma ta samu ta yi
Bayan tafiya mai tsawo suka sauka a airport ɗin New Delhi
"India…" ta faɗa a hankali.
Episode 45: A New Beginning but Old Shadows
Azrah tana tsaye a cikin harabar jirgin saman New Delhi, iskan wajen yana kaɗa hijabin jikinta, tana raba idanu cikin nutsuwa da kulawa, tana neman inda zata kalli Samira. Hankalinta duk yana kan nemanta da idanu cikin cunkoson mutane, jin Idanu tayi yana yawo a kanta, hakan yasa ta ɗan juya wannan saurayin dai ta gani wanda ya zauna kusa da ita a jirgi
Yana tsaye yayi folding hannayen sa ya zuba mata Idanu da murmushi a fuskarsa, daga bisani ya karasa inda take har sannan da murmushin a fuskarsa ya ce
"Hi... I'm Ayman"
Azrah ta ɗaga ido ta kalleshi, without any interest ta ce
"Azrah"
Ayman ya gyara tsayuwarsa, yana ƙoƙarin samun cikakken kulawarta ya ce
"You seem new here... Are you here for studies?"
Ta ce a takaice "Yes"
Tana maida hankalinta wajen neman Samira, Ayman ya sake cewa
"Well, if you don't mind, I can drop you off. My ride is here already"
Ya nuna wata mota da ta tsaya a gefe tana jiran sa.
Azrah ta kauda kai ta ce da girmamawa
"No need. Thank you"
Kafin ma ya ƙara wani yunkuri, sai ga Samira ta bayyana daga nesa da alama itama Azrahn take nema. Kamar ance ta kalli gefen da Samiran take kawai suka haɗa ido, Azrah bata sake bi ta kan Ayman ba, ba tare da wata ɓata lokaci ba, ta nufi Samira da fara'a, suka rungumi juna azrah da fara'a ta ce
"Samira!"
Samira ta ce da dariya
"Ma Shaa Allah kun dawo lafiya! You look so tired!"
Azrah ta ce "Wallahi ba kadan ba"
Samira ta kama trolley ɗinta tana cewa
"Let's go. Friend ɗina ne ya kawo ni, a can yayi parking motar sa"
Azrah bata yarda ta sake juyawa ba balle ta kalli Ayman, suka nufi inda motar ke parke
Suna karasawa bakin motar, saurayin Samira ya fito cikin girmamawa ya karɓi trolley ɗin Azrah ya saka cikin booth, yana cewa
"Welcome to India"
Azrah ta ce da ladabi "Thank you, sir"
Ya ɗan murmusa ya rufe booth ɗin sannan ya zagaya ya shiga motar, Samira ta kama hannun Azrah dan taga idan ba haka ta mata ba kamar bata da niyyar tafiya ne, ta buɗe mata back seat bayan ta shiga ta rufe sannan ta shiga gaban motar, tada motar yayi suka bar wajen
Samira ta juyo da ɗan dariya a fuskarta ta ce
"Ke kin san an canza mana hostel kuwa?"
Azrah bata san sanda tayi murmushi ba dan aikin Samira kenan maimaita labari, ta ce
"Haka kika ce jiya, ba har kin gama mana komai ba? Sannu da kokari"
Samira ta ce
"Toh yau zaki sha mamaki da kyansa! Amma fa akwai rules sosai… ai sai dai mun haɗa da hakuri amma idan ba haka ba wata kila zan iya breaking rule ɗin wata rana Nikam"
Bayan sun yi tafiya me nisa wani eatery mai mugun kyau saurayin Samira ya parka, yana kallon Samira yace
"Baby mu shiga" Samira na murmushi ta ce "Alright Babe" sai kuma ta juya ta kalli Azrah dake bayan motar ta ce "Sauko mu shiga" tana faɗa haka ta sauka saboda tuni shi harya fita
Azrah taji kamar ba zata iya shiga ba amma Samira ta jata suka shiga ciki, abinci sosai ya musu order bayan sunci sun koshi wanda Azrah gaba ɗaya tana jinta not comfortable, bayan sun gama ya musu takeaway sannan suka fita, kama hanyar school dinsu yayi
Bayan sun shiga cikin makarantar a daidai hostel ɗinsu yayi parking, sannan ya sauka ya sauke musu trolley, bayan Azrah ta sauka tana kallonsa ta ce
"Nagode sosai. Allah saka da alkhairi" murmushi kawai ya mata sai kuma ya maida kallon sa ga Samira ya ce
"Zan dawo da yamma, ki saka min time da zan dawo"
Samira ta gyada kai da murmushi sannan suka yi sallama
Suna shiga hostel ɗin, Azrah ta kasa ɓoye mamakinta ta ce
"Lallai wannan hostel din yayi mugun kyau, kalli tsarin ɗakunan, ai wannan kamar gida ne"
Samira ta ce "kyau kam yayi harya gaji, amma fa rules ɗin kamar gidan sojoji" ta karasa maganar tana dariya
Bayan sun shiga ɗaki, ta cire kayan jikinta, ta shiga wanka, bayan ta fito ta saka doguwar riga mara nawi, ta yi sallah, tana idarwa ta jawo takeaway ɗaga ta fara ci a hankali duk da ba sosai take jin yunwa ba amma bata wani ci a eatery ɗinba
Wayarta ta ɗauka ta kira Bappah, yana ɗaga wa ta ce
"Assalamu alaikum Bappah"
"Wa'alaikumus salam, Azrah Kin isa lafiya?
"Eh Bappah, yanzu muka iso hostel"
"Ma Shaa Allah, sannu da hanya, ki kula da kanki" ta ce "In Shaa Allah"
Tana katsewa ta kira Umma, tana ji kamar hawaye zai zubo bayan Umma ta ɗaga ta ce
"Umma na iso..."
"Alhamdulillah, Allah ya miki albarka" ta ce "Amin Umma…"
Daga nan ta kasa ci gaba, sai kawai ta ajiye wayar tana danne hawayen da ke shirin zuba mata,
Umma ta fahimta ta ce
"Azrah kar kiyi kuka, Allah zai miki jagora, Ki dage da karatu, wata rana sai labari" ta ce "In shaa Allah Umma..."
Da haka ta katse kiran, Azrah ta zauna tayi shiru, bata ma san ta faɗa duniyar tunani ba....
Mummy, Suhaila da Saif suna fitowa daga filin jirgi suka nufa zuwa parking lot
Mummy ta ce "Wlhi yarinyar nan ta burge ni sosai, kawai dan aikin data mana ji yadda ta zo ta rungume ni da farin ciki kamar mahaifiyarta ce ni... Allah ya albarkace ta"
Suhaila ta ce "Ni ma burgeni take yi Mummy, Ko kadan ba ta da girman kai, Ga gaisuwa, ga natsuwa, ga ilimi da hankali"
Saif da ke tsaye a gefe yana danna waya kawai ya shiga motar yana cewa
"Toh dama ma uban wa zata wa girman kai? 'yar gidan talakawa, classless sannan you expect her tayi girman kai?" Yayi wani irin dariya ya ce "wonder shall never end"
Mummy ta juyo da mamaki tana kallon Saif ta ce
"Ni da nake tunanin baka ma kula da ita ba, sai yanzu ne zaka yi magana? Ashe kaji gaisuwar data ke maka ma kawai dai baka ga daman amsawa bane"
Saif ya ɗan tabe baki,
"Na lura da ita mana, toh me zan mata Mummy?"
Suhaila ta ƙyalƙyale da dariya,
"Toh ai hakan ma ya fi! Tunda mutun yana iya gane ta a ko ina da sauki"
Mummy ta gyara zamanta a cikin motar ta ce
"Dan Allah Suhaila ki cigaba da taɓa ta, idan ta gama makaranta Maybe wani yana neman mata sai na haɗa su"
Suhaila ta ce
"In shaa Allah Mummy"
Mummy ta kuma cewa
"Yarinyar mai hankali ce. Allah ya kare ta daga sharrin makiya ya kuma rufa musu asiri"....
Bayan Azrah ta gama cin sauran abincin da saurayin Samira ya siya musu, mugun bacci ne ke shirin ɗaukarta. Ta ɗaga idanunta masu nauyi tana kallon Samira wacce ke zaune a gefen gado tana latsa wayarta, sai tace da kasala
"Samira, wannan ne Deen ɗinki?"
Samira ta kalleta da murmushi da yayi saurin bayyana, ta tallaɓi kumatunta sannan ta ce
"Wai wanda ya kawo mu? A'a, bashi bane fah"
Azrah ta zuba mata ido na wasu dakiku tana mamakin halin irin na Samira, ta ce da tausasasshen murya
"Amma shine kike bin sa? At least ki hakura tunda kince an riga an yi introduction da wanda zaki aura"
Samira ta yi dariyar raina hankali tana taɓe baki, ta ce,
"To sai me idan I'm taken? Ni ba zan kula wani ba kenan? Toh ai shima Deen ɗin ya riga da ya sani cewa haka lifestyle dina yake. Ina ma abin daya fara haɗa mu kenan saboda irin macen da yake so kenan"
Azrah ta kasa cewa komai. Mamaki ne ya hana ta motsi ko furta wani abu, dama haka ake? Tana da wanda zata aura, amma har yanzu tana mu'amala da wasu samari ba tare da wata damuwa ba? Kuma a ganinta, hakan normal ne.
Ba tare da wani ƙarin magana ba, Azrah ta miƙe tana hamma, ta ce,
"Good night Samira"
Ta jawo lafiyayyen duvet ɗinta ta faɗa kan lallausan gadon, sannan ta rufe jikinta gaba ɗaya. Bacci mai nauyi ya kwashe ta cikin mintuna kaɗan.
Washegari da safe, karfe takwas saura Azrah ta farka daga barcin da ya dauketa bayan tayi sallahn asuba, Samira ta farka tun kafin bakwai, tana video call da wani ne, Sanda Azrah ta bude idonta, Samira ta juyo da murmushi ta ce
"Hey... Good morning sleepy head. Ki tashi ki shiga wanka mana, kar mu bata lokaci"
Azrah ta janye duvet ɗin jikinta tana hamma, sannan ta mike da kasala. Ta ɗauki towel da kayan wankan ta, ta wuce toilet. Bayan kusan minti 30 ta fito tana goge kanta da tawul.
Shiryawa ta fara, ta saka doguwar riga marar nauyi ash gray color, wacce ta tsaya mata ƙasa da guiwa, tare da white straight pants da karamin hijab white, sannan ta saka farin flat shoe ɗinta, ta ɗauki jakarta ta tsaya gaban madubi tana kallon kanta
Samira bata wani ɓata lokaci ba ta fito, ta fara shiri itama cikin sauri, ta yafa blue veil mai laushi a kanta, bayan ta gama saka kayanta fitted top light blue da palazzo white trousers. Ta ciro lip gloss tana shafawa a leɓenta, tana kallon Azrah ta ce
"Idan nace ban gane ki ba just believe me, wanna kyau haka" Azrah bata kulata ba
Suka fito daga hostel ɗin, bayan sun isa centern makarantar, suka tsaya a wani eatery suka sha tea da cookies sannan suka nufi department ɗin Azrah dan mata course registration na level 200.
Sanda suka isa, suna cikin department ɗin Business Administration, Samira na rike da hannun Azrah, a haka suke tafiya
Azrah dai binta take yi ɗan gaba ɗaya kunya take ji ganin duk yawancin Malaman sai sun mata magana, ga students mate ɗinta, wanda bata magana da su ma duk magana suke mata
Wani lecturer ne ya fito daga office yana kallon su, da fara'a ya ce
"Hey! Azrah, right? Welcome back!"
Azrah ta ce da murmushi
"Good morning sir, yes, thank you"
"We were impressed with your last session's result. You did really well!, keep it up" ya ce yana duba wani takarda, ta ce
"Thank you sir, I'm here for my 200 Level course registration"
Ya juya yana kallon wani matashi lecturer wanda ke gefensa,
"Please take her to the course adviser to complete the level two registration."
Matashin lecturer din, wanda suke kiransa "Black," ya yi murmushi yana kallonta da fara'a ya ce
"You're very much welcome, Azrah. Don't worry, we'll sort you out"
Ya karɓi takardunta ya ce,
"Follow me."
Azrah da Samira suka bi bayansa. Yana mata bayanai game da tsarin karatun ta, da courses da za a fara musu. Azrah taji daɗi sosai ganin courses ɗin an rage musu ba kamar na hundred level ba, har Office ɗin suka shiga
Suka zauna a office ɗin, aka cika mata komai, aka bata har da timetable. Har wani dalibin India da ke gefe ya ce
"Nice to meet you, Azrah."
Ta amsa da murmushi kawai
Bayan sun gama, Black ya ce,
"You can go now, lectures start next week"
Azrah ta gode masa da ladabi. Suka fito daga building din da Samira, a hanya suna dariya irin yanzu sun zama 200 L students
Zaune suke a cikin falon gidan cikin natsuwa da walwala irin ta family, Mummy na zaune akan 3-seater, gefenta Suhaila tana jingina da kujera, A resting chair kuma Daddy ne zaune yana duba wani file sai Saif dake zaune gefensa, yana danna wayarsa tamkar ba ya cikin hirar nasu
Suna tattaunawa akan muhimmancin ilimi da tasirin sa ga rayuwar mutum. Ana cikin haka ne Suhaila ta ɗago kai cike da kawo musu reference
"Mummy dan Allah baki lura ba yadda Azrah ta kara kyau ba? Gata ta kara girma, looks very mature"
Mummy ta jinjina kai tana murmushi ta ce
"Yarinyar tana birgeni wallahi. Yadda take da nutsuwa da kwazo. Gata da ilimin addini da na zamani, kuma ga tarbiyya"
Sai kuma ta ce "Allah ya cika mata burinta"
Suhaila ta ce
"Amin Mummy. Wlh ina mugun jin tausayin yarinyar, duk da basu da shi amma bata da kwaɗayi ko kaɗan sai tarin hankali"
Daddy ya ɗago kai yana kallon Mummy ya ce
"Wanene wannan yarinyar kuma?"
Mummy ta amsa tana dan dariya
"Kai! Dear, Azrah ce wacce tayi mana aiki shekaru biyu baya a can gidan da muka zauna. Karamar yarinya ce amma tana da hankali sosai"
Daddy ya jinjina kai ya ce
"Yeah right! Yanzu na tuna. Yarinyar akwai ladabi ba laifi"
Saif ya gyara zamansa kadan, amma bai ce komai ba
Sai kuma Mummy ta rabka tagumi sai can kuma ta ce
"Da ace Saif yana jin maganata da shawarata ai da yanzu Azrah matar sa ce, ba wannan yarinyar daya kawo ba wai zai aureta ba, Kawai saboda class sai mutum ya mance da sauran qualities"
Saif ya dago kai da sauri, yana kallon Mummy da mamaki ya ce
"Mummy?!"
Suhaila tayi dariya ta ce
"Wallahi Nima tun ba yau ba nake masa sha'awar Azrah. Amma Ya Saif ko kaɗan baya kaunar yarinyar
Saif ya mugun ɓata rai yana kallon Suhaila ya ce
"Enough Suhaila! Kowa da taste dinsa, okay? Ni bana ra'ayinta kuma ba zan taba yinta ba, period!!"
Daddy ya fara dariya ya ce
"It's okay. Kar ku matsa masa. Ya riga ya kawo wacce yake so, kuma kowa da ra'ayinsa ai"
Mummy ta taɓe baki cikin rashin gamsuwa ta ce
"Ni dai na faɗi tawa. Azrah ce wacca nake so ba waccan da ban gamsu da halinta ba, amma duk da haka ba zan ki wanda ya zaɓa ba, idan hakan zai faranta masa"
Saif ya saka Bluetooth dinsa a kunne sannan ya cigaba da danna wayansa
Episode 46: Not Looking for Attention
Samira ta bawa Azrah gift ɗin system wai Daddynta ne ya bata, wanda ba kaɗan ba Azrah tayi murya sosai. Bayan sati guda da tafiyan Azrah....
Tun kafin asuba Azrah ta farka, wani irin nutsuwa take jin, ta miƙe ta wuce toilet tayi alwala, nafila ta dinga yi, bayan ta idar da sallar asuba, bata sauka akan sallayar ba, hannunta a sama tana roƙon Ubangiji tana hawaye
"Ya Allah, Ka dafa min. Ka saka min albarka a wannan semester, Ka daidaita sakanin Umma na da Bappah, ka bamu hanyar da Zahra ma zata yi karatu. Ka bani nasara, kamar yadda Ka bani a baya… Ameen"
Ganin Samira ta tashi yasa ta miƙe akan sallayan ta koma kan gado tana Azkar ɗinta.
A yau zata fara lectures a matsayin 200 Level student a Department of Business Administration.
Bayan ta fito a wanka, ta saka sky-blue fitted shirt mai kyau, da high-waist black jeans da hijab nata neatly styled, soft makeup tayi wanda ya ƙara bayyanar kyawunta. Tana cike da annuri, confidence ɗinta na bayyane gradually, Samira da ta fito daga toilet tana gyara towel dinta ta tsaya tana kallonta ta ce
"Ahhh Azrah lallai yau harda wani kwalliya, dan Allah ko ke fah, kalli yadda kika kara wani kyau, In da akwai best dressed award, you'd win it without stress"
Azrah tayi murmushi ta ce, "Samira karki fara pls, dan yau ne zan fara lecture shiyasa"
Bayan ta shirya, suka fita tare suna ɗan hirarsu. Suna isa department ɗin Azrah suka yi sallama, Samira ta juya zuwa nata department, Azrah kuwa ta nufi Public Admin building da sauri
Tana isa cikin department ɗinsu, kafin ta karasa ma, wasu daga cikin classmates ɗinta suka taho da fara'a, suna ta hugging dinta da fara'a
Wata colleague ɗinta Sarah ta ce "Azrah! OMG you're back!"
"Welcome back Azrah"
"Look at you, fresh and glowing!"
Azrah ta yi murmushi tana gaisawa da kowa da kowa cikin fara'a da mutunci. Ta lura da yadda attention ɗin mutane ya koma kanta kamar kowa yana son yi mata magana ko zama kusa da ita ne, Amma kamar kullum, ta kasance mai sanyin hali da nutsuwa, tana amsa gaisuwa cikin fara'a da ladabi
Zuciyarta cike da godiya ga Allah, wani irin farin cikin take ji musamman ganin yadda mutane ke nuna mata kauna, duk hanyar lecture hall suka nufa
Azrah na zaune a cikin ajin, bayan gaisawa da 'yan class dinta ta bude laptop dinta, tana duba syllabus ɗin su online duk contents na semester din tana kokarin fahimta da tsara time table ɗin karatunta, matan gefenta ne suke magana akan an kawo musu wasu students
"An ce an kawo mana sabbin students"
Azrah ta dago kai daga laptop ɗinta, ta kalli daya daga cikin su, matashiyar 'yar India mai suna Sarah, Cikin curiosity da dan mamaki Azrah ta tambaya
"Dama haka ake yi? Ana shigo da sabbin students a Level 2 ne?"
Sarah ta gyara zama tana kallon Azrah da fara'a, ta ce
"A'a, su actually sun fara karatu a wani college daban ne, yanzu ne suka yi transfer zuwa nan. So they're not entirely new, just new to this campus, but I'm not sure fa"
Azrah ta gyada kai tana sauraronta, Sarah ta dan kalli gefe, sai ta ce
''Actually, su uku ne. Baki gansu ba ne? Suna nan a can baya… oh!"
Ta duba inda suka zauna ɗazu amma bata gansu ba, ta ce "Ah, yanzu ma sun tashi... strange"
Azrah ta juya baya inda Sarah take kallo, amma babu kowa, ta juya ta cigaba da kallon syllables ɗinta sai ga wani lecturer ya shigo lecture hall ɗin, Nan kowa ya fara samun waje yana zama
Azrah ta rufe system ɗin ta koma ga notes dinta, nan suka fara lectures ɗinsu na farko wannan year 2 ɗinsu
Bayan lectures ɗin 4 hours lecturer ɗin ya fita, nan aka fara fita, miƙewa Azrah tayi, tun jiya ta ke jin ciwon kai, daɗewan lectures ɗin kuma kamar yana son saka mata zazzaɓi ne, da kyar ta fito tare da Sarah, tana jin kamar ƙafafunta ba nata bane saboda wani jiri data Fara ji
''Oh my God, I need food and sleep, ASAP...'' ta ce a hankali
Suna tafiya a corridor ɗin da ke hanyar fita daga department ɗin, sai kawai Azrah tayi missing step, gaba ɗaya ta kasa tsayawa, kafin Sarah ta iya kai mata hannu, kawai ta faɗa... kai tsaye kan wani matashi
Bamm!
Guy ɗin ya ja da baya da sauri, abokinsa ya matsa gefe, ganin yadda komai ya zo sudden. Shi kuma ya ɗaga kai da sharp expression kamar bai yarda da abinda ke faruwa ba
Kafin Azrah ta ce komai ko tayi recovering, ya sa hannu ya ture ta daga jikinsa. Sarah ta rike ta da sauri,
"I.. I'm sorry... I didn't mean to" ta faɗa da ƙaramin muryarta
Sarah ta kwaɓe fuska ta ce
"Akan me zaki ce sorry? Bai san tsautsayi bane? Da har zai turaki back"
Azrah ta juya a hankali domin ganin wanda ta buge and her eyes locked with his
"Sadeeq...!?"
Even he was stunned. He blinked. Twice.
Kamar ba shi ke tsaye a gabanta ba. His jaw tightened. A hankali ya janye idanunsa daga nata, sai ya kalli Sarah da wani cold, sharp look
"This dirty village girl almost landed on me, kuma kina defending dinta?" Ya ce da ƙasƙantacciyar murya
Sarah ta buɗe baki da mamaki tana masa wani bad look
Azrah ta tsaya kallonsa da mamaki dan shi ta lura bashi da manner ne at all ta ce
"Hey ka ɗauka da ganganne zan faɗo maka jiki? I said I'm sorry"
Sadeeq ya matso kusa da Azrah, yana kallonta ta up and down with pure disgust
"Wani sorry? Do you think that changes anything? Why are you even here? Attention kike nema ne ko me?" Sai ya numfasa ya cigaba
"You girls with nothing to offer always try to get noticed. You don't belong here, face it"
Azrah ta daure fuska, muryanta na ɗan rawa ta ce
"Kayi hakuri ya fiye maka komai, I didn't ask for this, Stop acting like I planned it"
Sadeeq ya saki dariyar rainin hankali
"Of course. Kamar yadda ba ke kike yawon a social media da fake cuteness ɗin nan ba, kin fi kowa innocent ko? Hakan ba attention kike nema ba?"
Sai kuma ya ɗaga gira ya ce
"Let me guess, kina tunanin yanzu ke wata ce mai class ko? To kuma kina deceiving 'yan gidan ku akan kina karatu ne while ke kina sheke ayarki a kasar mutane"
"Enough!" Sarah ta faɗa da karfi, tana daga masa hannunta sama
Shi kuma a fusace ya koma kan Sarah, wani kallo yake mata
Ganin haka yasa Sagir ya karasa wajen, ya kama kafadarsa ya juyar da shi yana kallonsa ya ce
"Let's go, me amfanin wannan abun yanzu?"
Sadeeq ya janye hannunsa, ya juya garesu ya watsa musu cold glare, sannan ya juya ya fara tafiya
Azrah ta tsaya zuciyarta na bugawa da ƙarfi. A duk duniyar ta babu wanda ta tsana kamar Sadeeq da Saif, duk da bata san wanene shi ba amma kullum tsautsayi ke haɗa su
Kawai Hawayen da ta ke rike wa ya fara sauka a hankali. Tayi ƙoƙarin mayar da shi amma ina zuciyarta ta ƙi jurewa
"This isn't the first time..." ta faɗa a ranta, yayin da zuciyarta ta cika da painful flashbacks.
Ta tuna lokacin da ta watsa musu ruwa ba da gangan ba, yadda suka mata embarrassing comment a gaban mutane, Now again, publicly insulted wani irin mutum ne shi da bazai yi tunanin hakan zaiyi hurting ɗinta ba
Ta ɗago kai, ta kalli yadda mutane da yawa suka tsaya suna kallonsu, hawayen taji kamar an kara musu karfin gudu ne, tabi Sadeeq da yayi nisa da banza kallo
"Why me? What did I ever do to him?"
Sarah ta kama hannunta tana faɗa a hankali
"Azrah don't cry, please. Akan me zaki zubar da hawaye akan shi? Akan guy ɗin da bai san mutunci mace ba?"
Ta kama gefen veil ɗinta ta share mata hawayen da suka jike kuncinta
"Dalla ki share hawayenki. Shi da har ya tafi shine zaki damu kan ki, Let's go"
Azrah ta ɗan gyara veil dinta,
a haka suka nufi cafeteria, inda suka zauna a wata corner da ba hayaniya sosai
Aka kawo musu abinci, basmati rice da chicken, amma Azrah har sannan tana jin ɗacin abun daya faru, hakan yasa Plate ɗinta kamar ba a taɓa shi ba, dan sakura ma take yi
Sarah ta lalle ta, cike da kwantar da murya ta ce
"Toh yanzu sai ki saka damuwar wani mugun mutumin nan a rai? Sai ki ci gaba da tunanin sa har kin manta da kanki? Ko kin manta yunwa kike ji ne, Waye shi da zai ɓata miki rai haka?"
Azrah ta yi ƙoƙarin murmushi kawai sai ga hawaye ya sake zuba tayi saurin sharewa ta ce
"I just... wish Khalil was here. He wouldn't let anyone speak to me like that..." Ita kanta bata san ta faɗa hakan bama, zuciyarta ta cika da kewarsa. Tasan da yana nan, da suna tare lokacin kuma ba zai bari wani ya mata wannan rashin kirkin ba, sai yanzu ne gaske-gaske ta fara jin the emptiness da barinsa ya bari a rayuwarta
Daga haka, ta ɗauki spoon a hankali, ta fara cin abincin kaɗan-kaɗan
Sarah ta jinjina kai, ta ce
"That's more like it, Don't let any lowlife ruin your day"
Bayan sun gama, suka tashi suka nufi lecture hall domin last lecture ɗinsu na ranar, Azrah tayi ma kanta alkawarin zata daure ta fara koyon yadda za ta tsare kanta koda da bakar magana ne ta mayar da martani
Bayan sun yi nisa daga wajen, har yanzu fuskar Sadeeq cike take da rashin jin daɗi, Kamar yana jin wani ƙazami abu ne ya shige jikinsa
Ya dafe goshinsa da ɗan ƙarfi ya furta a takaice da ƙiyayya
"Wai dama wannan yarinyar nan a nan take karatu ne? Who the f** does she think she is?"
Ya saki dariyar takaici.
"So just because she has a pretty face now she thinks she can go around bumping into people like she owns the school? Har ta iya buge Ni?"
Sagir dai shiru yayi, yana tafiya a hankali ba tare da ya kula shi ba Kamar ma bai ji me Sadeeq ke cewa ba
Sadeeq ya tsaya cak, ya juyo da sauri yana hararar abokinsa
"Sagir you won't even say anything? Kamar baka ga abinda ya faru ba? Or you're not even shocked to see her here?"
Sagir ya dan ja dogon numfashi, ya janye idanunsa daga fuskarsa ya ce da wata muryan dake nuni da baiji daɗin reaction ɗin Sadeeq ba
"Shock? Akan me? Wannan yarinyar video dinta da kai ka fara turo min lokacin da ya tafi viral kana cewa I should stalk blog profile zanga tana yawo"
Ya ɗan kalle sa
"To what's the surprise in seeing her here now?"
Sadeeq ya cika da haushi jin abinda Sagir ya ce, a fusace ya ce
"You didn't see what happened? The way she bumped into me like she was craving for attention!"
Sagir ya ɗago kai ya kalle shi da wani kallo mai wuyar fassarawa ya ce
"Itace tace maka tana neman attention? Or it's just what you assumed?"
A take fuskar Sadeeq ta canza fuskar da take nuna jin tozarta a mugun fusace yace
"Wait... Sagir are you supporting her right now?"
Ya ɗan yi dariyar ɓacin rai.
"Don't tell me you're taking her side after what she did!"
Sagir bai ce komai ba ya nufi wata kujera can gefe, ya zauna a hankali yana kokarin calming down, bai so ya shiga wani pointless argument da Sadeeq ba, musamman akan magana da ba ta da tushe sosai
Zuciyar Sadeeq kuwa har yanzu cike take da ɗaci kawai ya bar wajen dan baya bukatar sake haduwa da Sagir a yanzu
Azrah ta buɗe ƙofar ɗakinsu da sallama a bakinta, da ƙyar take ɗaga ƙafafunta, alamar gajiya da da ɓacin rai, Samira da ke kwance tana daddanna phone ɗinta ta ɗago kai tana kallonta. Cikin murmushin mamakinta ta ce
"First day lectures ɗinma har sai kin zauna till the end Azrah? Dan Allah ki rage wannan serious mood ɗin naki, I mean, you already sabi sosai, just be reading at night kawai mana"
Azrah ta murmusa, murmushin da bai kai zuciyarta ba, sannan ta karasa cikin ɗakin tana cire kayan jikin cikin nutsuwa, ta ɗaura towel akan zata shiga wanka sai kawai ta kwanta akan gadon dan bata ji zata iya yanzu
Samira ta ɗan tashi da sauri, ganin yanayin Azrah ya canza ba yadda ta santa ba ta ce
"Azrah... lafiya kuwa? What happened?
Azrah kamar dai jira take da tambayar ta miƙe zaune a hankali, hawaye suka fara zuba mata
Samira ta miƙe a hankali, ta karasa inda Azrah take ta zauna kusa da ita tana zuba mata ido cike da damuwa ta ce
"Tell me Azrah, meya faru pls?"
Da ƙyar Azrah ta buɗe baki, muryarta na rawa, ta fara cewa
"Samira... yau na shiga one chance. I didn't mean to... it was just a mistake, wlhi amma bai kula da hakan ba yaci mutuncina cikin mutane"
Samira ta ƙara matsowa kusa da ita ta ce
Tell me everything... me ya faru?"
Azrah ta sauke ajiyar zuciya, hawaye na zubo a idonta, ta fara ba da labarin yadda ta faɗi jikinsa a dalilin jiri da take ji, da yadda ya hanƙaɗata kamar ƙazanta, irin harshen da ya yi amfani da shi, da kalmomin attention seeker, 'yar gidan ba kowa, da kuma ba karatu bane ya kaita, duk dai abun daya faru sai data sanar mata
Samira ta dafe ƙirji da takaici ta ce
"What?! Shine kika tsaya kika ce masa sorry kuma kika tsaya kuka? You didn't give it back to him?
Episode 47: Echoes of Resentment
Azrah ta share hawayenta, ta ce
I was shocked... and honestly, the worst part is... I've heard that before, Sai na tuna Saif ma ya taɓa ce min haka wai I'm attention seeker Kuma... it hurts more when it starts to feel true"
Samira ta girgiza kai cike da ɓacin rai ta ce
"Wait... shine kika tsaya kika yi shiru? Ko kuka? Like... after all the insults?"
Azrah ta ɗan share fuskarta tana cewa a hankali
"I think... maganar da yayi... gaskiya ce somehow"
Samira ta sake baki da mamaki ta ce
"Wait... what?? Wani irin magana ne haka?"
Azrah ta numfasa da ƙyar ta ce
"He said I'm just looking for attention"
Idonta ya cika da hawaye, zuciyarta na ƙuna, ta ce
"And it's not even the first time I'm hearing that fah nace miki, Even Saif once said same thing... Shiyasa nace haka"
Samira ta dafe goshi da takaici, ta ce
"No way. wlh Azrah, there's no Nigerian guy that has the guts to say you're seeking his attention. Sai dai he is the one chasing yours. And if he's not it's his loss, not yours!"
Azrah ba ta ce komai ba, tana kallon wani waje
Samira ta ja tsaki ta ce
"Ke kuma, sai kika tsaya ya gama fadin duk abin daya zo bakinsa just like that? You should've opened your mouth and taken your respect back!"
Azrah ta ce da sanyi
"Wallahi nama rasa how to react. You know yadda ake kallon mu ai... Kowa attention ɗinsa fa ya koma kanmu ne"
Da ƙyar ta miƙe, ta nufi toilet ba tare da ta sake cewa komai ba zuciyarta na ci gaba da kuna, da kalmomin da har yanzu ba su dena damunta ba.
Da daddare, har lokacin Sadeeq ya kasa samun nutsuwa. Komai na ranar ya tsaya masa a rai kamar a jikin sa har sannan Azrah na nan, yadda ta faɗo kansa, yadda kallon ta ya tsaya masa da abinda ta faɗa. Komai yana dawowa masa tamkar a lokacin abin ya faru
Zaune yake akan kujerar parlon su, ya kunna TV yana kallon wrestling amma hankalinsa ba ya kan kallon, hannunsa riƙe da cup ɗin coffee amma shima bai kai bakinsa ba. Ya rasa me yake damunsa, tunanin incident ɗinma ya daina ya kasa, sai faman jan tsaki yake
Sagir ya buɗe kofar ya shigo cikin parlor da sallama. ya jefa ma Sadeeq kallo ɗaya ya ɗauke kai. Sai kuma ya karasa ya zauna a gefensa ya ce
"How's the night, Sadeeq?"
Sadeeq ya yi banza da shi, Sai can kuma ya ɗan kalli Sagir daya ke danna wayansa ya ce
"Duk Abbah ne ya jawo min. Da ya barni a Nigeria... yaushe hakan zai faru pls? Yaushe zan haɗu da wannan yarinyar ma dan Allah?"
Sagir ya juyo da mamaki yana kallonsa ya ce
"Wait... har yanzu kana thinking about that girl ne? You're not serious wallahi"
Sadeeq bai ce komai ba sai ya miƙe, ya nufi bedroom ɗinsa ba tare da ya ce uffan ba. Sagir ya bi shi da kallon gefen ido, ya girgiza kai a hankali, ya kwanta akan kujerar parlon yana kallon ceiling"
A bangaren Azrah kuwa, itama hakan ne, ta kasa mance komai gani take kamar kowa yasan da zagin daya mata, ji take ta tsane sa, tsaki tayi ta miƙe ta nufi toilet don yin wankan bacci, da ta yi wanka, ta sanya sleepwear dinta sannan ta kwanta, amma zuciyarta bata daina mata zafi ba balle ta manta, Sai gashi wayarta tayi ringing Khalil
Cikin sauri ta ɗaga kiran kamar dama jiran kiran nasa take.
"Hello..." ta ce da wata kasalalliyar murya
Bayan sun gaisa, Khalil yayi shiru kamar mai nazari
"Azrah, what happened?"
ya yi tambayar da damuwa
Azrah ta ɗan yi shiru, sai ta ce
"Me ka gani da zaka ce haka?"
"Seriously? You think I won't know when something is wrong with you? That means I don't really care, huh?"
Yace da murmushi dan karfafa mata gwiwa tayi trusting ɗinsa
Azrah ta sauke ajiyar zuciya "Okay…" ta ce a hankali.
Ta fara ba shi labarin duk yadda abun ya faru, tana faɗa tana jin ciwon abun na sake tashi, kamar yanzu abin ke faruwa
Khalil yayi wani irin shiru, shi kaɗai yasan yadda yake boiling inside, dakyar ya buɗe baki cikin tsananin fushi ya ce
"Who the f** is this guy? Waye shi har zai ce kina neman attention dinsa? Yaushe kika zama mace mara daraja har wani zai zo ya wulaƙanta ki haka?, shi har ya isa ya Kalle ki balle yace kina neman attention ɗinsa?"
Yadda yake maganar da karfin gaske kuma cikin tsananin fushi, Azrah dai tayi shiru, tana mamakin yadda zafin maganar ke fita daga bakinsa, tone ɗinsa kaɗai ya isa ya nuna mata cewa ya fita jin zafin abu, amma lokaci guda zaka fahimci cewa tsansan kishine
"I'm not in the mood now" ya ce daga ƙarshe
"Let's talk tomorrow. Sleep tight, dear"
Ya katse kiran ba tare da ya jira me zata ce bama
Samira dake gefe tana game, ta ɗago tana dariya
"An taɓo miki sarkin kishi, baby girl"
Azrah ta juya da kai tana kallonta ta ce
"Waye yace miki kishi yake yi?"
Samira ta kyalkyale da dariya ta ce
"Ke baki ji yadda yake magana ba? The tone alone was jealous enough. Wallahi yana kishi"
Azrah ta mayar da kanta ta rufe idonta, bata ce komai ba
Sai dai wani sanyi ya ratsa zuciyarta dan yanzu ji take kamar duk damuwarta ma an yaye mata shi ne tass daga zuciyar
Washegari kamar yadda ta saba, Azrah ta farka da wuri. Bayan sun isar da sallar asuba, tayi azkar ɗinta cikin nutsuwa. Daga nan ta kwashe kayan wanke-wanke da basu yi jinya da daddare ba ta fita dasu zuwa kitchen ta soma wankewa, bayan ta gama wanke wa ta dawo ɗakin da su sai taga Samira already ta daura musu breakfast tana mopping ɗakin
Hakan yasa Azrah ta wuce toilet bayan ta ajiye plates ɗin, ta yi wanka. Bayan ta fito, Samira har ta gama komai, ta zuba musu breakfast a plate, tana cikin zuba tea a cup
"Zauna mu yi breakfast kafin na wuce nayi wanka" Samira ta ce tana matsowa kusa da gadon
Dukkansu suka zauna suna breakfast dinsu, bayan sun gama, Samira ta wuce toilet, Azrah kuwa ta gyara wajen sannan ta zauna gaban mirror
A hankali ta shafa lotion ɗinta, ta kama gashin kanta da kyau ta taje shi, ta kama da ribon fari wanda ya haɗu da fresh complexion dinta, Daga nan ta fito da kayan da zata sa, straight jeans mai light blue, tare da white short-sleeve shirt da tiny embroidery a chest ɗinta, tayi tucking neatly, sannan ta ɗaura open Abaya akai, ta saka flat black shoes da matching handbag. Kallon kanta tayi a mirror ta ɗan murmusa, tana jin kamar zata iya fuskantar komai yau.
Ta zauna bakin gado kenan tana duba time, sai Samira ta fito daga toilet tana goge fuskanta, Bats ɓata lokaci ba ta gama shiryawa
fita daga hostel ɗin suka yi, suna hira irin na safe cikin raha da dariya. A hanya suka rabu bayan sun iso faculty, Azrah ta shige department ɗinta Samira kuma ta karasa
Yayin da take tafiya cikin corridor na department ɗinsu, ta ci karo da wasu daga cikin classmates ɗinta, ta tsaya suna gaisawa da ita cike da annashuwa. Bata bar wajen ba sai Sarah ta iso, tana dariya da sauri ta rungume Azrah
"Good morning bestie!"
Azrah ta amsa da murmushi, "Morning, hope you had a restful night"
Sarah ta gyada kai da fara'a "Let's go to the lecture hall yanzu, mu samu front seat please"
Azrah ta ce "Yes, let's"
Kamar an ce ta kalli gefe, sai idonta ya faɗa cikin na Sadeeq, wanda ke tsaye a gefe da hannayensa cikin aljihun wandonsa, sanye da fitted black T-shirt da dark jeans. Yayi mugun kyau irin wanda idan ka kalle sa sai ka sake kallonsa, sai wani cold expression a fuskarsa.
Itama Azrah tana kallonsa kenan, shima ya ɗago kai... ido ya faɗa cikin na juna, wani tsinkewar zuciya suka ji a lokaci guda
Ba tare da ta ɓata lokaci ba Azrah ta ɗauke kai da sauri, fuska a ɓace kamar wanda taga abu mara kyau. Shima Sadeeq ya ɗauke kansa cikin sauri yana jin wani haushin sake ganin ta da yayi, me take yi a department ɗinsu? Abin da ya ayyana a zuciyarsa kenan
Azrah da Sarah suka zauna a front seat cikin hall ɗin, amma zuciyar Azrah ta nemi nutsuwarta ta rasa
Yayin da lokacin lecture ya yi, lecturer ɗinsu ya tunkaro hall ɗin. Wannan yasa students ɗin dake waje suka fara shigowa cikin hanzari, kowanne yana neman kujerar da zai zauna
A ƙarshe, su biyu suka shigo cikin tafiyar kasaita da kuma jiji da kai,
dake duk yawancin ma sun girmi students ɗin tunda su karin karatu suka zo not as fresh student, hakan yasa babu wata alaƙa ko gaisawa da su. Ko fuska basu sake wa kamar ba su da sha'awar zama da kowa ballai har a saba
Sadeeq yana kallon gabansa ne, har sai da ya karasa seat ɗinsa, Sagir dake binsa a baya kawai idonsa ya sauka kan Azrah, Kallo ɗaya ya mata sannan ya ɗaga kansa akanta, kana kallon fuskarsa zaka gane akwai tsananin mamaki da ɗan wani abu dabam a idonsa
Ya zauna a seat ɗin da Sadeeq ya zauna, daidai lokacin da lecturer ɗin ya shigo, sake kallon direction dinta yayi sannan ya ɗauke kansa.
Sai kuma ya ɗan kalli Sadeeq ta gefen ido ganin ko Sadeeq ya lura da ita, sai dai kamar baisan da zaman Azrah a ajin ba, ya cigaba da duba laptop dinsa yana gyara glasses ɗin idon sa
Sagir ya ja numfashi bai san sanda ɗan murmushi ya kuɓuce masa ba, A ransa kuwa ya ce "Let’s see what happens when Sadeeq finds out…"
Lecturer ɗin yana tsaye gaban class ɗin yana scanning ɗin students ɗin da suka zauna da nutsuwa. Ya ɗan ɗaga murya cikin seriousness ya ce
"Before we start today's topic, let me ask a question from the last reading"
Zuciyar kowa ta fara bugawa wasu suna sunkuyar da kai, wasu na duba note kamar suna son sake kallon abinda aka musu a previous class din, Aji ya dauki shiru, tamkar babu kowa
"Anyone?" ya ƙara tambaya, idonsa na yawo cikin ajin.
Sai ya ɗan tsaya, yana kallon list na attendance. Ya ɗaga kai cikin authority
"You… Miss Azrah"
Zuciyar Azrah ta ɗan tsinke, Bata yi expecting ba. Ta kalli Sarah, wacce ta ɗaga mata gira kamar irin you got this. A hankali, Azrah ta miƙe tsaye, tana gyara hijab dinta, ta ɗan natsu kafin ta fara magana
"Sir, The reading focused on the structure of Indian public administration and how it evolved post-independence. It highlighted how the British legacy influenced centralized control, and how the democratic system later reshaped the bureaucracy. The chapter also discussed the roles of civil services, particularly the IAS, and how federal and state governments share administrative responsibilities"
Muryarta ta kasance cikin nutsuwa da ladabi, tana faɗin bayanan kamar mai karatu, duk da slight tension a zuciyarta. Amma yadda take articulate ideas ɗinta ya janyo hankali duk wanda ma baya sauraronta ma, sosai kowa yayi shiru yana sauraron ta
Sai a sannan Sadeeq, wanda tun farko bai ɗago kansa ba balle yasan wake magana sannan ya ɗaga kai da mamaki wannan yarinyar
Eyes met
He froze Idanunsa suka tsaya a kanta The girl? Aji ɗaya da shi? Kuma har tana iya magana haka? A take zuciyarsa ta fara bugawa da sauri, kamar ba shi da control.
Ya kasa ɓoye shock ɗin da ke bayyane a fuskarsa. Zuciyarsa na bugawa da irin "Why ita kuma again?"
Sagir dake gefe ya kalle shi sideways, ya lura da reaction ɗinsa, ya ɗan murmusa a ransa yana ayyana yadda Sadeeq yake feeling ynz
Azrah kuwa ta gama bayani, ta tsaya daidai inda ya kamata, bata ja maganar ba. Lecturer ɗin ya ɗan gyada kai da gamsuwa ya ce
"Well done, Miss Azrah. You're absolutely right"
Ta murmusa kaɗan ta zauna. Sarah ta bubbuga kafadarta da jin daɗi.
Sadeeq yaji kamar ya yi yaya ne, bai taɓa jin abu ya dame sa ba sai wannan karan, wani irin zuciyar sa ke tafarfasa, imagine taya zai zauna aji ɗaya da wancan 'yar gidan ba kowa ba
Ana gama lectures, kafin lecturer ya kai ga rufe laptop ɗinsa gaba ɗaya, Sadeeq ya miƙe tsaye tamkar wanda aka yiwa allura. Ba tare da kallon kowa ba, ya nufi kofa kai tsaye, shi kaɗai yasan meyake ji, Sagir ya juyo ya bishi da kallo, ya girgiza kai kawai.
"What the hell is she doing here?" Sadeeq ya furta da haushi a ransa
"Of all places, why this school, why this department… why my class?" Yana jin kamar duniya na kokarin yi masa dariya ne, Yarinyar data gama raina sa huh?
Azrah da kanta ke ƙasa tana shirin tashi, sai idonta ya sauka a jikin mutumin da ya fice kamar wanda ke shirin tashi sama. Tsayawa tayi cak, zuciyarta na bugawa. Tana kallon bayan Sadeeq da sauri da mamaki wani abu na ratsa ta, tsinkewar zuciya da tsoro da rudani a lokaci guda.
"Anya kuwa? Shine ne?" Ta tambayi zuciyarta.
"Amma ai India muke... Ba yanda za'a yi naga Nigerian na ɗauka ɗan India ne"
Tana kokarin ɗauke kai, suka haɗa ido da Sagir wanda ya juyo ya kalleta. A nan ne ta tabbatar cewa shine, Sai ta sauke ajiyar zuciya a hankali, ta ɗan taɓe baki da mamaki da ɗan fargaba.
"So, it's really him"
Sarah ta miƙe tana fuskantar Azrah, ta ce da murmushi, "Let's go, sweetheart"
Azrah ta gyaɗa kai ba tare da ta ce komai ba. Tana ƙoƙarin boye rudanin da zuciyarta ke ciki. Duk da hakan, zuciyarta na ta faman tambayoyi da bata da amsarsu.
Daga haka suka nufi kofa, suka fice daga lecture hall ɗin cikin natsuwa
#Jiddatulkhayr
08110615256
Episode 48: Turbulence
Sadeeq na fita daga lecture hall bai tsaya ko ina ba sai parking lot. Zuciyarsa banda ta farfarsa babu abinda yake yi. Ya buɗe motarsa da karfi, ya shiga, ya rufe kofar, ikon Allah ne kawai yasa bai fasa glass ɗin ba.
Zuciyarsa na bugawa, numfashinsa yana seizing. Ya dafe steering yana fidda hucin ɓacin rai
"Wannan yirinyar… wannan jakar yarinyar! What the hell is she doing here?" Ya furta da ƙarfi, yana jin bakinsa na ɗaci
"Bayan wannan many incident, I still hate her. Still!" Ya danna horn da karfi kamar yana sauke haushinsa ne akan akan motar.
Bai san how long yake wannan wajen ba, sai kawai jin Sagir ya buɗe motar ya shiga yayi. Sagir bai ce komai ba har sai da ya zauna for some minutes sannan ya juya yana kallon Sadeeq ɗin ya ce
"You good?"
Sadeeq ya juya ya zuba masa idanunsa da baka gane menene a cikinsu ya ce "Do I look good to you? You saw her right there, right in our class!"
Sagir ya gyara zamansa yana kokarin natsar da Sadeeq ya ce
" saw her, yes. But why are you reacting like this? That was days ago, bro"
"Days ago? Days ago she made me look like a fool! She made me feel like I was chasing after trash!"
Yayi ƙasa da murya da haushi mai tarin yawa ya ce
"And now she's here… in my space"
Sagir ya ja numfashi ya ce "Wannan makarantar ba taka ba ce kai kaɗai Sadeeq. She didnlt beg to be here, infact naga ita tama riga mu farawa"
Sadeeq wani kallon yake masa ya ce "I swear, idan har zata zo ta raina min hankali kamar da… I won't take it this time, Dan ba karamin bata mamaki zan yi ba"
Sagir ya juyar da kansa gefe yana kallon waje ya ce da sassauƙar murya
"Let it go Man. You're better than this"
Sadeeq ya dafe kansa, yana jin kamar zuciyarsa na masa nauyi sbd har sannan duk abin daya faru na masa flashing, Ganinta, jin muryarta, yadda class ɗin ya yi shiru tana magana ya hana shi sukuni
Sai ya furta a hankali
"She still gets to me… and I hate it"
__________
Azrah da Sarah suka karasa cafeteria suna tafiya a hankali, amma Azrah hankalinta baya tare da ita, tunaninta yana can a kan Sadeeq, Tana jin kamar zuciyarta tana saukowa da wani nauyi daban "Toh amma anya wannan shi ne? Da wannan jiji da kai, da wannan girman kai, har yanzu bai gama degree ba? Taɓe baki tayi tunawa yanzu suna same level
Duk da kasancewar abinci a gabanta, bata iya ci sosai ba. Sarah na kokarin sata dariya amma Azrah tana nan cikin tunanin da ta gagara gane kansa, a haka dai suka wuce lecture hall suka yi last lecture ɗinsu kafin duk suka wuce hostel.
______
Azrah tana isa hostel ta bude kofar ɗakin su da key, ta tura kofar a hankali ta shiga, kamshin turaren Samira ya buge ta, fitowarta kenan daga toilet, tana goge gashinta da tawul.
Samira ta ɗan ɗaga kanta tana kallonta ta ce, 'Welcome back Azrah. Hope lectures sunyi kyau?"
Azrah ta zare takalmin ta, ta ajiye jakar ta sannan ta zauna a bakin gado tana kallon Samira har sai da ta ƙarasa goge jikinta sannan ta ce a hankali
'Samira... kin san wanene yazo class ɗinmu yau? Ko kuma nace wa nagani a class ɗin mu?"
Samira ta ɗan tsayar da shafa man data Fara ta ce
"Wayee? Malami kuka yi ɗan Nigeria?"
Azrah ta girgiza kai ta sauke ajiyar zuciya a hankali ta "Sadeeq ne"
"Wait... Sadeeq? Which Sadeeq?! Samira ta tambaya da sauri tana dafe kirjinta
Azrah ta gyaɗa kai a hankali, "Wannan arrogant guy ɗin da na faɗa masa jiki, Ashe ajin mu daya ne. Yana cikin sabbin DE students ɗinmu... ashe degree ma bai gama ba, a haka yake wulakanta mutane kamar wani Acting President"
Samira ta zaro idanu ta ce "You're kidding me!"
Azrah ta yi tagumi ta ce "I wish I was, Gashi kwatakwata bayi da wani good mu'amalat da mutane, Kuma yanzu... guess what? Na fara jin kamar tsoronsa nake yi wllh"
Samira ta fara tafe hannu cike da al'ajabi ta ce "Matsala ta dake kenan, shiyasa ko wani banza yake taka ki mana, tsoron sa akan uban kine shi?"
Azrah ta gyara pillow ta kwanta da murmushi ta ce
"Wlh bansa meke damu na ba Nima Samira, ina son canza kai na sbd wannan eran da muke ciki, amma na komai"
Samira ta tsare ta da ido can ta ce "I know what's wrong. You're beginning to catch feelings shiyasa kike jin tsoron nasa"
Azrah bata san sanda ta miƙe zaune ba tana kallon Samira ta ce "haba Samira me kike faɗa ne haka? Imagine fah"
Azrah ta dafe kanta ta cigaba "Duk duniya babu wanda nake jin tsana irin wannan mutumin. And now I have to sit in the same lecture hall with him, mu fuskanci juna kullum, Samira I don't know how I'm going to cop"
Samira ta ce "You will cope. Saboda ba shi bane future ɗinki, Education ɗinki ne future, Idan ya sake miki wani abu, we report. Amma kar ki zubar da self-worth ɗinki saboda irin halin sa"
Azrah ta zuba mata ido, cikin shiru mai zurfi Zata iya? Gashi ba wanda ta tsana kamar shi yanzu kuma tsoron sa ne take yi
_______
Sadeeq na zaune a kan gado, file ɗinsa a cinyarsa, yana cire wasu takardu daga cikin file ɗin yana wurgi gefe da su kamar wanda amfanin su ya kare, wasu kuma yana zubawa idanu kamar dai yana son su karanta kansu ne, Sagir na tsaye a bakin kofar ɗakin yana kallonsa, yana dai binsa da idanune yana kallon ikon Allah, shi dai yasa son ya gama waɗannan abubuwan ya tmby sa dalilin da yasa ya bar lecture hall kuma ya ki yin attending last lecture ɗin
Yana gama ɗaukan wanda zai yi amfani da su ya saka wasu papers ɗin cikin envelope, ya rufe shi da sauri sai kuma ya miƙe tsaye, ba tare da ya kalli Sagir ya kama hanyar fita
Sagir ya daure fuska ya ce a hankali "Where are you going?"
Sadeeq ya juyo da wani kallo mai kaifi, idonsa sunyi ja dan ɓacin rai ya ce da tsawa "Department"
Sagir ya matsa gefe yana kallonsa, har ya fita Sagir bai ce uffan ba. sannan ya dawo ya zauna a gefen gadon, yana kallon envelope ɗin da Sadeeq ya bata
"Me zai je department yi yanzu? Bayan pass 4 ne, lecturers duk yanzu sun fara tafiya" Sagir ya furta a hankali, yana jefa kansa cikin tunani
A bangaren Sadeeq kuwa, wani irin driving yake na marasa hankali a haka harya isa cikin school yayi parking sannan ya sauka ya shiga cikin department ɗin wanda har ya fara shiru saboda rashin students dayawa a wajen, kallo ɗaya zaka masa ka san cewa ba lafiya bane.
Yana isa department, sai ya tarar da yawancin lecturers ɗin sun tashi. A haka dai a hankali ya karasa har gaba office ɗin HODn su, yana gwaɗa buɗewa yaji a kulle
Cikin takaici, ya juyo yana barin wajen ba tare da ya ce da kowa komai ba duk da yadda wasu suka bisa da kallo
_______
Daddare Samira ta fito daga bathroom daure da towel a jikinta tana goge sumar kanta da tawul, tana humming wata sabuwar wakar India. Azrah dake kwance a gadonta tana karanta wani PDF, ta ɗaga kai da murmushi tana kallon ta.
Bata jima ba bayan ta gama shafe shafenta ta buɗe wardrobe tana bi da ido sai kuma ta zaro wata riga da wando crop top fitted da high waist trouser, tana jan zip ɗin sa a hankali, a haka ta saka, Sai kuma ta yi light makeup, ta sa turare me ƙamshi mai kama da vanilla flavor sannan ta gyara gashin kanta ta buɗe shi ya zubo akan kafadunta
Azrah ta tsaya kallon ta, fuska cike da mamaki da rashin yarda dan yanzu tasan dai dare ne
"Ina zaki haka Samira?" Ta tambaya a hankali.
Samira ta dan juyo da murmushi ta ce "Wani birthday party ne zamu je, it's just for tonight. Zasu yi celebration a Westrend Club ne"
Azrah ta zaro ido "Wai Club? Samira, da kin hakura kawai. Babu kyau ki fita da irin wannan shigar... kalli yadda kika yi fa, wannan ba dressing ba ne da ya dace da ke! Infact har a addininki"
Samira ta kalli kanta a mirror, sai ta ɗan murmusa, ta matsa gaban Azrah ta zauna gefen gadon.
"Haba mana Azrah, it's only for today. You know I don't do this always… and besides, I need a little fun, wallahi semester ɗin nan ya fara damuna da pressure ne"
Azrah ta numfasa, tana kallon samira ta na girgiza mata kai ita dai bata son ta tafi
Samira ta miƙe, ta ɗauki small clutch bag ɗinta, ta ɗauki wayarta sannan ta saka a cikin Jakkan, ta wuce wajen takalma ta ɗauki wedge heels. Tana gab da fita ta tsaya ta kalli Azrah tace, "Ki rufe kofar idan na fita ta ciki... and don't worry, I'll be fine''
Azrah ba tace komai ba, tana kallon ta har ta fice. Azrah ta koma ta jingina da bango tana sauke numfashi. Sai kuma ta tashi a hankali ta nufi bathroom. Ta yi wanka sannan ta fito daure da tawul, ta zauna bakin gado ta shafa lotion duk wannan abun daga ke yi jikinta babu ƙwari
Bayan ta gama, ta saka modest pyjamas nata long-sleeved top da dogon wando. Sai ta kwanta kan gado, amma bacci yaƙi zuwa. Zuciyarta na ɗauke da nauyin tunani da damuwar Samira. Wani murya a zuciyarta na cewa
"It's her life, Amma ba zata iya barinta ba, Allah ka tsare mana zuciyarmu da abokananmu"
Washegari da asuba wajajan karfe 4 Sadeeq ya farka da wani irin nauyin zuciya da bai saba ji ba. Tunanin azabar yadda ganin Azrah kullum cikin class ɗaya yana masa nauyi, zuciyarsa cike da ƙiyayya da takaici, yana jin kamar yana shirin kamuwa da ciwon zuciya. A haka ya dinga sallah har asuba tayi. Ko breakfast bai yi ba, ya zare wata envelope daga drawer, yana rike da shi a haka har ya kai bakin kofa ya fita
Ba tare da sun gaisa da Sagir ɗin ba
Ya isa department ɗinsu, ya tarar lokacin ne ma cleaners ke aikinsu, ya tsaya a bakin kofar yana kallon agogon hannunsa lokaci zuwa lokaci, zuciyarsa cike da fushi da tsoro, tsoron abin da zai fuskanta idan har aka ce babu mafita.
Bayan kusan minti talatin, aka buɗe Office ɗin, wajan da students zasu shiga su jira, kai tsaye ya nufi office ɗin HODn ganin an ajiye tag ɗin yana nan hakan ya fahimci ya shiga ta baya kenan, Ya tsaya gaban ƙofar ya kwankwasa a hankali, daga ciki aka ce "Come in."
Ya shiga cikin office ɗin, yana dan lumshe idanu saboda AC ɗin da ke kaɗawa da sanyi. HOD ɗin yana zaune yana duba wasu files ya ce
"Yes, Mr. Sadeeq, what can I do for you this early?"
Sadeeq ya ƙara matso kusa, ya ajiye envelope ɗin a gaban sa. “
"Sir, I want to request for a departmental transfer"
HOD ɗin ya ɗago kai da mamaki, "Transfer? At this time of the semester? Are you sure of what you're saying?"
Sadeeq ya dan gyaɗa kai, fuskarsa daure ya ce "Yes sir. I don't think I can cope in this department anymore"
HOD ya ɗan janye files ɗinsa, ya juyo da kyau yana kallon Sadeeq ya ce
"Mr. Sadeeq, you are already registered, your Previous results, your class attendance, your course forms, all are already in the system. The only way you can change department now is to start afresh from 100 level. And that will be next academic year, not this one"
Cikin sauri Sadeeq yace "Sir, there must be a way, even if I lose some credit hours"
"No way" HOD ya katse shi. "System ɗin nan rigid ne. Any attempt now is like starting over again completely. My advice? Stay, finish this semester. Next session you can apply early and get approval in time"
Sadeeq ya tsaya yana kallon HOD kamar wanda aka watsa ma ruwan sanyi. Bakinsa a rufe, zuciyarsa na bugawa. Bai sake cewa komai ba, ya ɗauki envelope ɗin shi a hankali ya juya ya fita daga office ɗin kamar wanda ya rasa last hope ɗina.
Yana fita daga department ɗin, lokacin an fara morning lectures ko nufar class ɗin bai yi ba. Sai hanya ya bi da sauri ya koma gida, zuciyarsa cike da takaici. Yana shiga parlour ya jefa envelope ɗin gefe ya zauna ya jingina da kujera, yana jin numfashinsa na tafiya da sauri. Kamar mai shirin fashewa da kuka amma haushinsa ya hana shi yin komai.
Jiddatulkhayr
08110615256
Episode 49: When Paths Cross Again
Kamar yadda aka saba, bayan ƙarfe 8 na safe ɗalibai suka fara cika lecture hall ɗin department ɗin. A yau kam Azrah tazo da wuri, tare da Sarah suka zauna a seat ɗin gaba, kaman yadda zuciyarta tun jiya ya kasa samun sukuni, har lokacin bata daina jin yanda zuciyarta ke rikicewa duk sanda ta tuna da Sadeeq ba, amma ta ƙudiri niyyar yin ignore dinsa gaba ɗaya idan ma ya tabbata ajinsu ɗaya ne
Ana shiga first lecture ɗin, ta fara kallon gefe da gefe kamar tana neman wani, ta lura Sagir na zaune a bayansu, amma har zuwa ƙarshen lecture ɗin bata ga Sadeeq ba. Kuma data zo ko a hallway bata Kalle sa ba, hakan yasa ta ɗauka ko latti zai yi ne tunda ta kalli Sagir
_______
Sagir ya ci gaba da kallon ƙofar lecture hall, yana sa ran zai shigo, amma har aka gama lectures ɗin ranar bai bayyana ba. Sosai Sagir ya shiga damuwa, zuciyar sa cike take da tambayoyi babu me basa amsar su kuma sai Sadeeq, a sanin sa ai Sadeeq ya riga sa fitowa toh me yasa yaki shigowa lectures ɗin?
Azrah kuwa a lokacin na ɗaya daga cikin rare moments da take jin nutsuwa a zuciyarta a cikin lecture hall. Tana ɗan rubuce-rubucenta sai idonta ya sake yawo a aji. Ganin babu alamar shi yasa ta ɗan saki murmushi, wanda Sarah ta lura da shi.
"Why are you smiling?" Sarah ta tambaya da dariya.
Azrah ta ɗan ɗage gira tana cewa, "Nothing fah" ta mayar da idonta kan notebook dinta. Amma a zuciyarta ta ce
"Maybe he saw me yesterday and couldn't handle it... Good for him" sake wani dariyan tayi
Sai dai a zuciyarta, ba wai farin ciki bane sosai, damuwarta Allah yasa ya hakura kawai da karatun saboda ita, domin yanzu babu wanda take ji tsoronsa da tsanarsa irin Sadeeq
________
Bayan wani lokaci.... Sosai Azrah ta fara sabawa da sabuwar rayuwarta musamman yadda Sarah ta manne mata kamar Sisters. Wannan sabuwar alaka ta sa ta fara samun kwanciyar hankali a department ɗin, musamman yanzu da Khalil baya kusa da ita. Da ba don kasancewar Sarah ba, da lallai Azrah da wuya ta iya coping da wannan sabon yanayi.
Sarah ba wai kawa ce kawai ba, tana da kwazon karatu, ga nutsuwa, sannan kullum tana ƙoƙarin ganin Azrah na murmushi. Hakan ya sa Azrah ta sake sosai tare da jin dadin kasancewarta a makarantar.
Tare suke tafiya daga department, suna hirar su cike da fara'a da dariya. Har gaban hostel Sarah ta rakata, tana kallonta tana murmushi ta ce
"Bestie wai banda number ɗinki fa har yanzu. Wannan ai laifi ne"
Azrah ta karɓi wayarta tana murmushi, ta saka mata number ɗin sannan ta ce
"Dial it yanzu, dan na yi saving Nima kafin ki kira ina who is it?" Dariya suka yi
Sarah ta danna kiranta, wayar Azrah ta fara ringing sai ta katse.
Sai kuma ta rungumeta sosai tac ce "Zan dawo anjima fa, don't miss me too much!"
Azrah tayi dariya tana gyaɗa kai ta ce "Toh, sai kin zo ina nan ina jiranki Sarah"
Daga haka suka rabu, Azrah ta juya ta nufi hostel ɗinsu zuciyarta cike da kwanciyar hankali, tana jin kamar a karshe rayuwarta ta fara samun canji ne, a cikin wannan sabon yanayin rashin Khalil....
Tana shiga ɗakin, Azrah ta samu Samira kwance, bacci sosai take yi, hatta numfashinta ma a hankali yake fita alamar gajiya. Bata ko kuskura ta tashe ta ba, kawai ta cire kayanta a hankali ta shiga toilet.
Bayan ta fito daga wanka, ta saka simple gown mai laushi, sannan ta fesa turare kaɗan a jikinta. Khalil ne kawai ya sake faɗo mata a rai dan wannan turaren ma shine ya tsiya mata. Ta nufi inda suke aje abinci, tana sa ran za ta samu, amma babu komai
Ta ɗan kalli kitchen, amma taga komai a wanke a ajiye wajensa hakan yasa ta fahimci Samira bata yi abinci ba. Ta san Samira tana ƙoƙarin dafa musu abinci kullum, hakan yasa bata ji zafin rasa abincin da bata samu ba, ta san wata rana za ta iya gajiya kamar yau.
Cikin nutsuwa ta kunna gas, ta ɗaura tukunya tana cewa a ranta "Let me take care of this today"
Ta fara girki, komai take ɗauka a hankali gudun karta tashe ta a baccin
________
Sagir na komawa gida, ya tura ƙofar parlon cikin nutsuwa. Yana shiga ya hangi Sadeeq na zaune a parlourn, yana kallon TV amma duk alamu sun nuna ba kallon yake ba. Fuskar nan tasa ba walwala, idanunsa ko keftasu baya yi alamun yayi nisa da tunani, dan ko alamu sun nuna bema ji karan shigowan Sagir ba. Sai da Sagir ya yi magana sannan ya daga kai ya kalle shi kamar wanda aka farka daga mafarki.
Sagir ya zauna gefensa yana facing dinsa, ya ce "Baka je lectures yau ba kuma naga kai da safe ka rigani fita ma, lafiya kuwa?"
Sadeeq ya ja numfashi sannan yace a takaice, "Naje canza department ne"
Sagir ya zaro ido da mamaki, ya sake baki yana kallonsa. Daga baya yayi dariya mai cike da mamaki ya ce
"Kamar ya kaje canza department kuma?"
Sadeeq ya ce a fusace
"Do you think zan iya zama a wannan department ɗin ina kallon wancan kucakar yarinyar? How? Taya zan cigaba da rayuwa ina fuskantar ta kullum? Dole inyi nisa da ita, I can't stand her!"
Sagir ya kwashe da dariya yace, "Man calm down! Kamar kana tsoronta fa? Saboda ita zaka canza department? Ashe ma kenan she's really something tunda kai da kanka zaka bar course dinka saboda ita. To ka ga kenan yau da gaske saboda ita ne baka zo lectures ba…"
Sadeeq yayi shiru ya ɗauke kai kamar bai ji maganar ba
Sai ga wayarsa ta fara ringing. Ganin sunan mahaifinsa yasa ya ɗaga wayar da sauri ya ce
"Assalamu Alaikum Sir..."
"Wa'alaikumus salam, Sadeeq. How are you?"
"Alhamdulillah Sir, ya gida? Ya su Mami"
"Alhamdulillah. Lafiya lau"
Sai can Sadeeq ya ƙwantar da murya ya ce
"Sir, dama… if possible, I was thinking maybe I should just come back home and continue taking online classes, then help more with the company..."
Shiru ne ya biyo baya daga can. Sai murya Baba ta dawo a tsanake kamar ya gamsu da maganar nasa ya ce
"Yanzu kuma meya faru? Bayan duk kuɗin da aka kashe, duk kokarin da akayi, yanzu ne zaka dawo da magana baya?"
Sadeeq ya dafe kansa ya ce "Sir, I think I can't cope here...
A fusace mahaifinsa ya ce "Saboda me? Dama ai ba son ranka bane shiyasa ba zaka yi karatun ba ko? Tunda farko ance ka yi degree kai ka nace kana so ka fara da diploma, haka kuma aka ce ka kawo matar aure ka ce kai baka da budurwa, ance za'a zaɓa maka Mata kace baka so, komai naka kullum a juye yake! Toh yanzu kuma sai ka ce ba zaka iya karatun ba?"
Ganinsa ya fara fusata sosai yasa Sadeeq ya sauke muryarsa ya ce
"I'm sorry sir, I'll stay... I'll continue..."
Mahaifinsa da ƙarfi cike da masifa ya ce "If you like ka zauna, if you like ka dawo. Kayi yadda kake so. Amma ka daina bani excuses marasa tushe" yana kaiwa nan ya kashe kiran ba tare da wata sallama ba
Sadeeq ya sauke wayar a hankali, ya lumshe idanunsa, zuciyarsa kamar zata fashe, yama rasa wani tunanin zaiyi takamaimai
Sagir wanda tun ɗazu ke kallonsa cike da mamaki ya ce "Wow... Har haka ne? Ban san lamarin ya kai haka ba. Amma think of it taya zaka ce wa Baba irin wannan magana?"
Sadeeq bai tanka sa ba, sai kawai ya miƙe da zafin rai ya wuce cikin bedroom ɗinsa, ya rufe ƙofan da ƙarfi
Sagir ya bishi da kallo, yana girgiza kai ya ce
"Tabbas, this girl really broke his balance..."
Da yamma kafin Magrib, Azrah na zaune a spot ɗin karatunta a cikin ɗakin, Samira kuma tana zaune tana cin abinci a hankali. Bata daɗe da farka daga bacci ba, hakan yasa sai yanzu take cin abincin
Azrah na cikin karatunta sai ga wayarta ta fara ringing. Tana duba me kiranta kawai murmushi ya bayyana a fuskarta ganin sunan Sarah. Tana ɗauka ta ce
" Hey! Bestie"
Sarah tace "Gani a bakin hostel ɗin ku fa"
Azrah ta ce da fara'a "Ina Room 12, Plot B. Kawai ki shigo mana"
Ta kashe wayar tana dariya.
Samira wadda take cin abincinta a gefe, ta ɗago kai tana kallonta ta ce
"Bako zaki yi ne?"
Azrah ta yi dariya tana girgiza kai tace
"A'a fah... baƙuwa dai. Classmate ɗina ce, very close"
Samira ta ce "okay"
kamar ba ruwanta, ta cigaba da cin abincin
Ba a jima ba aka fara knocking. Azrah ta miƙe da sauri, ta buɗe ƙofar. Sarah ce tsaye tana murmushi kawai ta rungume Azrah sosai, tana cewa
"Bestie!"
Suka shiga cikin dakin.
Idanun Samira na binsu, tana kallon Sarah kai tsaye da wani expression, Sarah na kallon Samira da sauri ta ce
"Ohh hey you!"
A taƙaice Samira ta amsa da, "Hey."
Sarah ta ce "How are you?"
"Fine" ta sake bata amsa without interest
Azrah ta ja hannun Sarah suka zauna a bakin gado tana cewa
"She's my sister" Azrah ta faɗa tana murmushi
Sarah ta zaro ido tana kallon su, ta ce
"Really? But you don't even resemble"
Azrah tace
"Yeah, I know. Happens sometimes"
Daga nan Azrah ta zubo mata abinci, ta kawo mata da ruwa, suka fara hira suna dariya sai suka dawo kan karatunsu. Ana haka lokaci ya ja. Sai kusan 9 na dare wani saurayin Sarah yazo ya ɗauketa. Ta yi sallama da Azrah sannan ta bar ɗakin.
Sarah na tafiya Samira ta juyo tana fuskantar Azrah
"Bana son yarinyar nan" ta faɗa kai tsaye
Azrah ta kalleta da dariya
"Come on Samira, she has no problem wallahi. She's a nice person"
Samira ta gyaɗa kai ta katse ta, "And so? Sai me idan nice ce? Zata wani zo tana kiran ki 'bestie' a gabana?"
Azrah ta lumshe ido tana jin wani iri, sai yanzu ta gane ainihin abin da Samira ke nufi, shiyasa taga ko kaɗan bata sake ma Sarahn ba, ta ce a hankali,l
"Haba Samira, me a ciki ne? Just classmate ce fa, ke fa kuma sister ce wadda kullum tare muke"
Kafin ta gama, Samira ta ce a fusace
"Me a ciki kika ce? Tunanin ki ba ya ganin ni da kike tare kullum? Wacce kike kwana da ita, kuka da dariya tare..., ita kika cewa bestie?"
Azrah tayi shiru sai kuma taji babu daɗi duk da ta gano cewa Samira kishi take yi amma sai taji babu daɗi
_____
Azrah na kwance a gadonta, dakin shiru ne sai karan AC, Daga gefe Samira tana kwance tana shirin yin baccin ita ma, amma Azrah ba ta iya rufe idonta ba. Tunani ya mamaye zuciyarta.
Dole ta mike zaune tana kallon Samira. A hankali ta ce,
"Samira..."
Samira ta ɗan juyo da kai ta ce "Hmm?"
Azrah ta ce "Kinsan yau Sadeeq bai zo department ba?"
Samira ta ɗan bude ido kadan tana kallonta, sannan ta miƙe ta zauna tana murmushi
"Toh Allah yasa dan kene ne yaki zuwa" ta ce tana dariya
Azrah ta ce "Ai dana zo naga kina bacci, ina ta Allah² ki tashi na baki lbrn sai ga Sarah shiyasa na manta, kuma fah ɗan uwansa ɗin nan ya zo" Samira ta ce
"Nikam tsoro na ma kar fa kuzo kuyi irin na indiawa tunda kunga a kasar su kuke, daga baya ku fara soyayya"
Azrah ta jefa mata pillow tana murmushi ta ce "ki daina irin haka, bana son maganar sa ma daga yau"...
Washegari da safe kamar yadda suka saba, kowanne daga cikinsu ya tashi tare da shirin zuwa class.
Azrah da Samira kamar yadda suka saba sun gama shirin su, suka fita tare suka rabu a hanya.
Sarah da Azrah suka haɗu a wajen department. Kamar kullum, sai dariya da hirar karatu, suka kama Hallway suna lbrn wani course, suna cikin tafiya ne, can nesa ta hango Sagir yana zuwa shi kaɗai babu Sadeeq.
Azrah ta ɗan lumshe ido, cikin zuciyarta tana tunani "Toh har yanzu ba zai zo ba? Ko ya daina lectures ɗin ne gaba ɗaya?" Daga haka har suka isa lecture hall Sagir ɗin ma bata sake Kallonsa ba
Bayan wasu mintuna, sai ga Sadeeq da Sagir suka iso tare, kamar kullum Sagir yana tafiya cike da izza, Azrah ta ɗauke kanta cikin sauri kamar ba ta gan su ba. Sadeeq ma ko kallonta bai yi ba. A haka kowa ya karasa wajen zaman sa.
Lecturer ya shigo, students suka gaishe shi. Bayan ya gama introductory ɗinsa, sai ya ce
"Today I want to give you all a class assessment, and I'm thinking of making it a group work so you can collaborate and learn together"
Students da dama suka amince da shawarar. Sai ya fara raba su group-by-group. Kowane group zai kunshi students hudu.
Sagir na gefe ya kalli Sadeeq da murmushi yana cewa
"Man gwara da ka zo, gashi da yanzu zaka rasa group"
Sadeeq ya kalle shi da harara ba tare da ya ce komai ba.
A ƙarshe, sai gashi lecturer ya hada Group E da Azrah, Sarah, wasu maza guda biyu, da kuma Sadeeq.
Da Sagir yaji sunayen, ya fashe da dariya a ransa ya ce
"Allah kenan" dariya sosai yake yi ya ce "Wannan zai zama fim!"
Sadeeq ya tamke fuska sosai kamar zai fashe. Ba tare da ya matsa ko ya kalli kowa ba, ya tsaya a gefe yana hura hanci
Lecturer ya ce
"Kowane group ya samu wani leader da zai jagoranci aikin, This work will carry 40 marks, so I expect seriousness"
Ɗaya namijin da Sarah suka ce a tare, "Azrah should be the group leader!"
'yan group din suka fara murna
"Yes, she's smart. Muna da hope yanzu" wani yace.
Sadeeq ya kalli su da mamaki da bacin rai. Da ƙarfi ya ce
"No way! How can you appoint this arrogant little brat as our leader? She won't rule over me!"
Kowa yayi shiru a group ɗin suna Kallonsa, Azrah na kallonsa da wani irin kallo, sai kuma ta yi murmushi ta juyar da kanta, ba ta ce komai ba. Sarah ta juya da sauri tana kallon Sadeeq da ɓacin rai
Wani yana kallon Sadeeq yace "Sbd semestern nan ka fara zuwa, tana da mugun ilimi, I'm telling you this mune zamu ci idan itace tayi ruling dinmu" a fusace Sadeeq ya ce "And so what!?"
#Jiddatulkhayr
08110615256
Episode 50: When Pride Meets Consequences
Lecturer ya ba su list, ya ce su rubuta sunan group ɗinsu da members da kuma leader. Wani daga cikin su ya miƙa paper ga Azrah, "Please write our names"
Azrah ta ɗauki biro, ta rubuta nata, Sarah da da sauran mazan. Sai ta ɗago tana jiran Sadeeq ya faɗi sunansa
Amma Sadeeq ya yi kamar bai ganta ba, wani mugun kallo ya zuba mata. Ya ɗauke kai gaba ɗaya
Wani daga cikin su, mai saukin kai, ya karbi paper daga hannunta ya ce
Brother, please mana. Just your name"
Sadeeq ya ce da tsawa "Ka rubuta mana, Sadeeq Mahmud"
Ya wuce kamar wanda zai tashi sama, ya ja dogon tsaki ya koma kujerarsa.
Usman ya kalli Azrah yace,
"Sorry dear, kar ki kula sa"
Azrah ta girgiza kai kawai, ta yi murmushi mai ɗaci tana mai cewa
"Maybe he has his reasons..."
Sarah ta zo kusa da ita tana dariya ta ce
"Bestie congratulation dai. Yanzu zamu ga yadda zai yi ai"
Azrah ta ce "Shi ya sani fah, dan Ni kam ba ruwa na"
Lecturer ya tattara papern su, ya sake jaddada cewa
"This group work is important. I'm giving you all two weeks, and I expect the leader to organize and submit on time. Remember 40 marks!
Kowa ya koma kujerarsa. Sarah da Sagir suka yi eye contact da murmushi
Bayan lectures ɗin ranan ya ƙare, kowa ya fita. Sadeeq na gaba yana tafiya cikin hanzari, Sagir yana biye da shi yana murmushi.
"Wannan test ɗin zai zama film!"
Sadeeq bai ce uffan ba. Zuciyarsa cike da cinkushe, yana jin zafi, takaici da tsanar kansa da yaki yin karatu tun da farko balle har ya dawo ya haɗu da wannan brat ɗin
A gefe kuma, Azrah da Sarah suna tafiya tana cewa,
"Na tabbata wannan zai ƙara min wahala a wannan aikin ba lallai ya bada haɗin kai ba"
Sarah ta ce "Don't mind him. We'll make sure he works whether he likes it or not"
Azrah ta ce a hankali, "Innkuuma ya zabi ya ɗauke kansa... Ni kuwa ba abinda zan ragu da shi"
Suka yi dariya dukkan...
________
Bayan kwana biyu da aka raba group ɗin, duk sun shiga cikakken yanayin aikin project din, dan kowa baya jin zai yi wasa da 40 marks. Babu wanda bai fahimci cewa Azrah ce ke ɗaukar nauyi gaba ɗaya na group dinta ba, dan a kowanne lokaci, ko a cikin lectures, ko bayan ta koma hostel, aikin group ɗin na gabanta. ita kaɗai ke duba references, tana compiling ideas, tana saka duk ideas a cikin laptop ɗinta. Duk da cewa group ɗinsu ya ƙunshi maza huɗu amma sai dai aiki bai taɓa zuwa hannunsu ba. Sadeeq kuwa, sai kallo, babu participation, ko tsaki, ko kuma kallon banza da yake Binta da shima.
Sarah ce kaɗai ke kawo ɗan sauƙi, tana yawan zuwa hostel ɗin su Azrah domin taimaka mata, musamman wajen gyaran English da kuma layouts. Lokacin da Samira ke fita yawon ta, Sarah da Azrah kan haɗu su shafe awa biyu ko fiye suna reviewing rubutun da kuma yadda za su gabatar da shi. Duk cikin ayyukan nan, Azrah bata ce uffan ba akan rashin hadin kai daga Sadeeq, ita tasan me take shiryawa a kansa dan ya raina aikin da take yi tun farko balle ma ya ƙi bata sunansa
Ranar da aka tsara za a yi presentation ta iso. Tun safe aka fara shigowa babban hall ɗin. Students sun sha kyau, sun yi shirin showdown, saboda lecturers ɗin sun ce wannan ne CA ɗin 40 marks, kuma zai yi tasiri sosai a ƙarshen semester.
An daidaita hall ɗin da kujeru, lecturers hudu suna gaban hall ɗin, suna da record list da suna rubuta sakamakon kowane group. Aka fara da Group A, sai B, har C. Duk group leader na fitowa yana gabatar da aikin su da sunayen membobinsu da results. A wasu groups, mutum biyu ko uku ke presenting. A wasu kuma, leader kaɗai ke gabatarwa. Ana yi ana dariya, ana tafa wa, ana jin yadda wasu ke presenting din abun dariya
Sagir da Sadeeq suna zaune a bayan hall, Sadeeq yana danna wayarsa, idonsa ko kaɗan baya kallon speaker, shi da badan attendance da za'a dauka ba da babu abinda zai kawo sa wajen ma, Sagir na kallon sa cikin takaici, amma ya ƙi cewa komai.
A ƙarshe, aka kira group ɗin su Azrah. Wanda shine group na karshe kenan
Group E, leader Miss Azrah, please come forward!
Gaba ɗaya hall ɗin ya ɗan yi shiru kamar suna jira su ga yadda zata kaya. Azrah ta miƙe cikin nutsuwa, ba tare da wata rawar jiki ba. A hannunta akwai laptop ɗinta da hardcopy na aikin. Ta kalle su Sarah ta saki murmushi, su kuma suka daga mata hannu cike da goyon baya da fatan nasara
Azrah ta tsaya a gaban projector, ta danna slide, sannan ta fara da tsiririyar voice ɗinta da kwanciyar hankali
Good day esteemed lecturers and fellow coursemates. On behalf of my group, I'll be presenting our work on 'The Impact of Technology on Education in India.…'
Kamar yanda take da ƙwarewa wajen karatu, haka ma gabatarwarta take. Tana tafiya da audience ɗinta cikin nutsuwa, tana amfani da charts, statistics, da references. Ta ci gaba da bayani ba tare da bata lokaci ba, har sai da malamai suka fara gyaɗa kai da murmushi.
A lokacin da ta karasa ta ce
…in conclusion, we believe technology has redefined access to education, but challenges like poor electricity and internet coverage remain a big obstacle…
Gaba ɗaya hall ɗin ya kaure da tafi, musamman daga inda sauran 'yan group ɗinta suke. Hatta lecturers suka ce
"That was a brilliant presentation. Very concise and well structured. What's your group list and the results?
Azrah ta ɗan yi murmushi tana kallon lectures ɗin ta ce
Our group members include: Sarah khan, Ibrahim Adamu, Mustapha Ahmed… and myself, Azrah
Shiru ya biyo bayan hakan. Sagir da Sadeeq suka ɗaga kansu da sauri suna kallonta. Sarah kuwa da ke kusa da Mustapha, ta girgiza kai tana kallon Azrah da jin mamaki irin wannan confident ɗin
Sadeeq ya runtse idonsa da ƙarfi zuciyarsa na bugawa kamar zai bar kirjinsa, A ransa ya ce Tana nufin ko sunana ba za ta faɗa ba? Despite being part of the group?
Sagir ya ce a hankali
"Bro… an cire ka"
Sadeeq bai ce komai ba, sai dai ya lumshe idonsa yana jin wani irin daci a zuciyarsa da bai taɓa ji ba. Yana jin ana tafa mata daga ko'ina, kamar ana ƙara masa zafi a jiki. Wannan wulakancin ya masa ciwo fiye da duk abinda ake zato
Lecturer ɗin ya ɗan ɗaga murya ya ce
"We take this seriously. Anyone not listed in the group work will automatically score zero. There's no excuse"
Sagir ya juya yana kallon Sadeeq, yace
"Wannan ba raini bane? Ka duba yadda tayi kokari, me a ciki idan itace ce group leader din pls? Ai sun yarda cewa tana da kokarin ne har suka bata shiyasa. Waye ya sa ka cikin group? Ai tunda ba ita bane just obey your lecture ba Shikenan ba?"
Sadeeq bai amsa ba, sai ma miƙe wa da yayi ya fita daga hall ɗin a hankali. Babu wanda ya lura da fitarsa sai Sagir da Sarah.
Lecturers suka cigaba da random wrap-up. A ƙarshe, aka ce
"That brings our group presentations to an end. Those who didn't participate or weren't listed, better luck next year"
Mutane suka fara tashi, ana dariya, wasu suna murna, wasu kuwa sun shiga damuwa.
Azrah ta koma inda Sarah take, Sarah ta rungume ta da murmushi ta ce
"Bestie you killed it. Wallahi you killed it!"
Azrah ta yi murmushi kawai tana jin wani irin sauƙi a ranta. Amma a zuciyarta tana jin abu biyu nasara… da kuma rashin kyautawan data ma Sadeeq
sai ga sauran mambobin group ɗinta, Ibrahim da Mustapha suka nufota da murmushi a fuskokinsu. Ibrahim ya ce
"Azrah wallahi kin burge ni sosai. Mu godiya da kokarinki. Kin ceto mu"
Mustapha ya ce yana dariya
"In next semester aka ce group assessment, wallahi ni na riga na saka a raina ina cikin group dinki ne, kawai ki rubuta a list dinki"
Duk suka yi dariya, Sarah ma na dariya ta ce
"Ai in za ku shiga sai kun biya! Aikin Azrah ba kyauta bane"
Sauran students daga wasu groups ma suka fara zuwa wasu 'yan mata, da wasu maza suna mata murmushi da kuma tattara murnan yadda tayi handling aikin. Wata daga cikinsu tace
"Next group project, please let me be in your group. I no wan wahala"
Azarh sai dai kawai tana binsu da murmushi ne amma ta gagara cewa komai
A yayin da suke kama hanyar fita daga hall ɗin, suna tafiya a hankali suna hira, sai suka ci karo da Sagir a bakin corridor. Ya tsaya a gabanta cikin wani yanayi da ba a iya fassarawa ba
Ya kalleta ya ce da sautin muryar da ba mai ɗaci ba, amma ba ma da annuri ba
"Sannu da presentation ɗin… it was impressive"
Azrah ta tsaya ta kalle shi da kamewa, ta ce a takaice
"Thanks"
Sagir ya gyara tsayuwarsa ya ce
"Amma… me ya sa kika cire sunan Sadeeq?"
Azrah ta ɗan sauke ajiyar zuciya ta ce a hankali
"Saboda ya ce baya cikin group ɗin, ya gaya min tun farko ba zan masa ruling ba, sannan ya ce ai ban kai ba, so what's the point of listing him? A gaban kowa fah yaki yarda na saka sunansa"
Sagir ya yi shiru. Kamar yana nazarin abin da zai ce mata ne, gaskiyar maganarta ta doki zuciyarsa sbd yasan tafi Sadeeq gaskiya, ya dai ɗan gyaɗa kai kawai ya ce
"Hmm… okay then. Aiki ya yi kyau"
Daga nan ya wuce ya barta tsaye da Sarah, wacce suke tafiya tun da farko. Sarah ta ɗan tabe baki tana kallon bayansa, sannan ta kalli Azrah ta ce
"Kin min daidai wallahi. Dama tun da farko ban gane me ya sa kike saka sunansa ba"
Azrah ta murmusa kawai ta ce
"Ba komai. Yanzu dai mun gama ya kuma wuce"
Sarah ta kama hannunt suka cigaba da tafiya, a cikin zuciyarta Azrah na jin nauyin da rashin yarda da kanta da farko. Amma yanzu... ta san darajarta, reaction ɗin Sadie kaɗai ya nuna mata cewa tayi daidai
Azrah na komawa hostel ɗin su, tana jin gajiya amma zuciyarta cike da farin ciki da kwanciyar hankali. Tana tura kofar ɗakin ta shiga da sallama, bata ga Samira ba amma tana jin kara a toilet ta leka sai taga Samira na tsugunne gaban mashin tana wanke kayanta, kanta daure da towel, hannunta cikin ruwa
Azrah ta saki ajiyar zuciya cikin murmushi tace
"Samiraaa... kin san me ya faru kuwa?"
Samira ta dago tana kallonta, tana goge gumi da bayan hannunta tace
"Lafiya dai ko?"
Azrah ta karasa ta zauna a bakin toilet ɗin akan wani kujera tana kallon Samira da take jiran jin Meta faru, ta ce
"Kin tuna da CA ɗin nan da aka ce group work? To yau presentation ɗinsa muka yi ai, baki nan da safe shiyasa ban faɗa miki ba. Guess what? Na cire sunan Sadeeq daga cikin group members, a haka nayi submitting"
Samira ta sake baki cike da mamaki, sannan tace da dariyar mugunta
"Gaskiya kin min daidai... kin biyani! Ai irin wancan mutumin yana bukatar a nuna masa nan duniya ne kowa yana da daraja kuma duk ɗaya muke"
Azrah tayi dariya tana gyara zamanta, ta ce
"Ni dai na huta. Kowa ya taya ni aiki sai shi ne babu sannu balle madallah sai zagi da banzan kallo ɗaya ke bi na da shi, amma ina tunanin za a bawa kowa credit banda shi kuma?
Samira ta ja dogon tsaki ta ce "Halan kin manta mutumin daya zage ki in public ne" Azrah tayi shiru kawai
_______
A bangaren Sadeeq kuwa, yana shiga gida, zuciyarsa cike da wata irin daci da ba zai iya bayyana wa ba. Yana wucewa kai tsaye ya shiga ɗakin sa, ya zauna gefen gado yana kallon bango kamar mahaukaci. Ya dafe kansa da hannayensa biyu, yana jin yadda zuciyarsa ke tafasa
Yafi minti nawa yana zaune a haka, bayan wani lokaci sai ga Sagir ya shigo cikin ɗakin da sallama. Ya tsaya yana kallon sa, wanda bai ma juya ba balle ya Kalle sa, sai dai kawai ya ce cikin wata irin murya mai ɗauke da haushi da raɗaɗi
"Man... kaga abinda yarinyar nan ta min kuwa?"
Sagir ya ƙarasa cikin ɗakin yana kallonsa, kafin ya ce komai, Sadeeq ya cigaba da faɗin
"Har ni zata cire sunana daga group list? Me nayi mata da zata har haka? And the worst part tayi presenting perfectly! Kai, nasan sun ci 49 marks ɗin nan! Kuma ni ba wai ace bana ciki!"
Sagir ya buɗe baki da mamaki yana kallon sa. A hankali, yaga wani Sadeeq daban, ba wai Sadeeq daya sani ba, amma yana iya jin tsananin damuwa a cikin furucinsa
Sagir ya zauna a gefensa, ya ce
"Toh... kana so na kira ta ne?"
Sadeeq ya ɗaga kai da sauri ya ce a fusace
"No! Ka barta. Idan ka kira ta yanzu zata raina ni. She already did!"
Sagir ya langaɓe kai yana kallonsa, sannan ya ɗan yi dariya ya ce
"Toh since baka cikin group ɗin kuma baka yi presenting ba... ai next year zaka dawo kayi resetting course ɗin. Simple"
Wani kallo mai kaifi Sadeeq ya watsa masa, sai kuma yayi shiru. Zuciyarsa na wani irin harbawa
A hankali yayi ƙasa da murya ya ce
"I really hate her with passion. How dare she? Ni fa zata cire?"
Sagir ya miƙe tsaye yana girgiza kai, ya ce
"To ai da baka bukatar zama a group ɗinta ne. Ita ma taga hakan yasa ta cire sunanka, dan kar ka wulaƙanta, kuma kai karka takura mata. Ta sauwake ma dukkan ku biyun ne"
Yana kai wa nan, ya miƙe ya fita ba tare daya jira me Sadeeq ɗin zai ce ba, Sadeeq ya bisa da wani irin kallo, kallo mai cike da jin haushi da rashin yarda.
Sadeeq ya lumshe idonsa yana jin kamar zuciyarsa na konewa. Ba zai iya cewa komai ba. Kawai ya zube da baya a gadonsa, yana jin zuciyar sa ta fara ɗaukar wata hanya da bai shirya ba...
#Jiddatulkhayr
08110615256
Episode 51: The Becoming of Azrah
Yau kamar kullum, Azrah ta dawo daga lecture gajiya fal tattare da ita, sai ta tarar da Samira ta fito a wanka tana shiryawa, Azrah na cire hijab ɗinta ta ce
"Samira lafiya kuwa? Wannan shirin fa kamar tafiya zaki yi" ta karasa maganar ne ganin yadda ta ciro duk kayan wardrobe ɗin Azrahn
Samira ta ɗan kalli agogo tace,
"Kiyi sauri ki shiga ki watsa ruwa, ba zan ce komai ba yanzu sai mun fita tukun nan"
Azrah ta ja dogon tsaki "Ke kuma ai duk lokacin da kike boye min abu haka ake..."
"Ki shiga wanka, Azrah!" Samira ta katseta da dariya, tana tura ta cikin ban ɗaki wanda ko kaya Azrahn bata cire ba
Azrah ta kwace kanta ta cire kayan jikinta sannan ta shiga toilet ɗin
Bayan mintuna ta fito, ta saka kayan da Samira ta ciro mata, shigar modest gown, tana kokarin gyara veil ɗinta. Har yanzu ba ta fahimci inda za su ba. Daga haka ta bi Samira kawai
Samira kuwa kai tsaye suka tafi wata eatery wuri mai nutsuwa da kyau, wanda Samira ba ta taɓa zuwa da ita ba a baya.
Suna shiga, Azrah ta ɗan tsaya cak. Idonta na kallon wani mutum da ke zaune ya bada baya, haka kawai taji zuciyarta na bugawa da sauri, ta kalli Samira wanda take murmushi ta ce "mu shiga mana", step ɗaya tayi, sai da zuciyarta ta buga ganin wanda ya jiyo....
"Khalil"
"Ya Salaam!" ta furta a hankali, zuciyarta na bugawa,
Khalil ya miƙe tsaye da murmushin kwance a fuskan sa ya ce "Azrah..."
Cikin gasgata shine ko A'a dan ganin komai take a mafarki ta ce "Khalil? Kai ne?"
Samira tana dariya ta ce
"Ni zan je can, enjoy yourselves!"
Khalil ya nuna mata kujera, ta zauna still idonta akansa yake dagaske gani take kamar a mafarki.
"Kai ne a India? Yaushe kazo? Me yasa ba ka gaya min zaka zo ba?"
Khalil ya yi murmushin, reaction ɗinta ba kaɗan ba ya basa dariya kuma duk abin da zai gani a idanunta kaunar sa ne, ya ce
"Because I needed this moment to be real. Jiya na dawo India a karo na biyu ba da niyyar karatu ba sai dan ke Azrah. Na fada wa Samira ne kawai Sbd nayi surprising ɗinki, I wanted to see your face, not through a screen this time, Shiyasa kika ganni anan"
Shiru ya dan ratsa tsakaninsu. Kowa da kalar tunanin daya ke yi, sannan duk zuciyoyinsu yana bugawa ne da shauki da kaunar junansu
Sai Khalil ya ci gaba "Azrah, nayi ƙoƙari in mantaki tun farkon haɗuwar mu da kika nuna baki da ra'ayi na, Nayi ƙoƙari in daina son ki. Amma ko a cikin duhun yanayi, duk rintsi duk wuya duk wata sassa na jikina yana kiran sunanki a zuciyata. Na dawo... not just for business... but for you, Please karki ce baki So na"
Azrah ta rasa inda zata saka ranta da jin wannan kalaman nasa, ta ɗauke kallonta daga gare sa, tana jin yadda zuciyar ke kara tsananta bugu. Hawaye suka gangaro a hankali. ta ce
"Why now, Khalil? Why after all this time?"
Khalil ya matso kusa, ya kama hannunta, ta zare hannunta daga nasa, yana kallonta ya ce
"Because now, I'm ready. I'm done running. I want to fight for you. I want to be the man that deserves you"
Ta rufe Fuskarta da tafukan hannunta ta fashe da kuka, ba kuka na bakin ciki ba, sai dai na cike da nauyin so da tsoro a lokaci guda. Khalil ya miƙe, ya durkusa a gabanta, yana share mata hawayenta da da handkerchief ɗinsa mai kamshin turare ya girgiza mata kai, dakyar ya ce
"Don't cry, please. Not for me. Not today"
Suna cikin wannan halin ne Samira ta dawo da take-away a hannu, tana kallonsu da murmushin jin daɗi ta ce
"Yanzu na tabbatar… wannan so ba zaku iya boyewa ba" ta kare maganar tana dariya.....
RAYUWAR AZRAH A INDIA GURGUJE.......
Rayuwa a India ta cigaba da juyawa cikin sauyin lokaci da sauyin hali. Duk da kasancewar Azrah ta saba da sabuwar rayuwa, har yanzu akwai abubuwan da har kullum suke koya mata sabon darasi. Ta shiga Second Semester 200 Level cikin nutsuwa da kwarin gwiwa, sai dai har yanzu tsakanin ta da Sadeeq babu wata jituwa. Duk lokacin da suka haɗu a lecture hall, kallo ɗaya suke yiwa juna su ɗauke kai, wanda har yau ta rasa abin data masa wanda ya tsane ta har haka
Sai dai a gefe guda, dangantakarta da Sarah ta ƙara ƙarfafa. Sun zama kamar 'yan uwa, ba kawai saboda suna classmates ba, A'a saboda sun haɗa zuciya wajen karatu da rayuwa gaba ɗaya. Kowace rana bayan lectures, suna fita karatu, library ko wani quiet spot da za su nutsu su maida hankali. Karatu ya ɗauke musu hankali, sun kaucewa abubuwan da ke ɗaukar lokaci marar amfani. Ba ruwan su da wani social activities na schl, ba yawan yawo. Wannan haɗin kai ne ya ƙara basu ƙarfi a makarantar da ke cike da kalubale sannan yasa kawance su yayi mugun karfi ..
Wata rana, ana tsakiyar semester, iyayen Sarah suka zo daga Pakistan domin duba 'yarsu. Cikin farin ciki Sarah ta gabatar da Azrah a matsayin ƙawarta mafi kusa ma makarantar. Hakan ya sa iyayen nata jin daɗi, musamman mahaifiyarta da lokaci guda taji Azrahn ta kwanta mata a rai... Sun ɗauki hotuna tare da Azrah, sunyi hira sosai har da dariya wanda hakan yasa Azrah sake wa da su. Mahaifin Sarah mai barkwanci ya kalli Azrah yana dariya ya ce "Ke da kyau da hankali ba kamar kawarki ba, lallai Sara ta yi sa'a dai" duk suka yi dariya...
Duk da yadda karatun su yayi zafi, Azrah bata katse waya da gida ba. Ita da su Umma kullum sai sunyi waya. Har sau da dama Umma na cewa, "Azrah, karki manta kina nesa amma zuciyata na tare da ke, hakan ke saka min kamar muna kusa wlh, Ki kula da kanki Allah sa ki gama a sa'a" Wadannan kalmomi ne da ke ba Azrah ƙarfin gwiwan karatu
Khalil kuwa duk da cewa bai fara PhD ɗin ba, yana yawan ziyartar Azrah, musamman every end of 2 months. Amma duk da zuwan nasa, ba lallai su zauna sosai ba, saboda Azrah kullum cikin karatu take. Khalil yakan ce "Azrah, I'm proud of how focused you are" Kuma hakan yana ƙara mata kwarin gwiwa
Lokacin semester ya ja har ta gama 200 Level. Bayan exams, ta tafi gida Nigeria domin hutu. Wannan hutun ne ya zama na ƙarshe da zata koma gida kafin ta kammala degree. Tayi amfani da lokacin sosai, kasancewa da Umma da Zahra, Sake dage wa wajen kara karfin Sana'o'inta, wanda a wannan hutun ma sai data je gidan Dada sbd ba zata sake dawowa ba sai bayan ta kammala
Dawowarta daga hutu ba karamin canzawa tayi ba. tana cikin sabuwar natsuwa, sabuwar kwarin gwiwa. Shigarta 300 Level kamar sabon babi ne a rayuwarta. Wannan lokacin ba kamar da ba ne, dan sake dawowa da kwarin gwiwa sbd ganin har sannan tana first class kuma tayi alkawarin ba zata sauka a wannan class ɗin...
Cikin wannan semester ne kuma Deen, Saurayin Samira ya zo India. Da yake ɗakinsu Samira zai sauka, hakan ya sa Azrah ta tattara kayanta ta koma gidan Sarah tun kafin ya iso, Azrah sam bata ji daɗin wannan lamarin ba, dan ko data ma Samira magana akan rashin dacewar haka tunda ba wai an ɗaura musu auren bane da kawai ya kama hotel amma Samira ta nuna A'a babu komai, wanda hakan yasa har ya koma Azrah taki yarda su haɗu ballai su gaisa wanda ba kaɗan ba Samira taji haushin hakan. A bangaren Sarah kuma hakan ya ɗaure musu ƙawance sosai. Sun cigaba da karatun su tare.
Lokacin IT..... Wannan siwes ɗin ne ya daure Azrah sosai. Ko kadan bata samu sauƙi.. kullum cikin aiki saboda ƙwazonta, ga aiki da reports da ake bukata kullum. Takan dawo gida a gajiye, wani lokacin har taji kamar ba zata iya copping ba. Amma haka ta dage da juriya. Wani lokaci Sarah kan ce "Azrah kina bani mamaki wallahi. I wish I had your strength" Azrah kuma sai ta ce "Nima nasan Allah ne ke taimako na amma nima bansa ya ake nake wannan aikin ba"
Cikin wannan semester ɗin ne aka saka ranar auren Samira. Ana hutu da sati biyu za a yi. Samira ba kaɗan ba tayi murna, wanda tun a lokacin ta fara shirye-shiryenta
A cikin wannan tafiya, rayuwar Azrah ta canza sosai. Ba wai ta canza a fuska bane, amma zuciyarta ta sami sabuwar haske. Ta daina tsoron magana. Ta daina tsoron mutane especially Sadeeq daya sata a gaba, ko kaɗan ta daina shakkarsa. Yana yin yadda ta koma akwai wata rana da Sagir ya ce mata "Miss Azrah, you're a silent power"
A ƙarshe semester ya zo ƙarshe. Ta fara shiri don final year. Idan ka ganta yanzu, zaka rantse ba ita ce yarinyar da ta zo India da boyayyen murya da rashin confident ba, Azrah ta girma sosai ta kara hankali, da nutsuwa, da hangen nesa.
Wata rana tana hostel, Samira ta kalleta tana murmushi ta ce
"Azrah do you remember the first day you entered this hostel? You were so quiet and scared. Look at you now you're glowing with confidence"
Azrah ta yi dariya da bata shirya yi ba, ta lumshe ido ta ce
"Wallahi Samira I went through a lot. But I survived. And I've changed... a lot"
Final Semester ya zo kamar ambaliya ya mamaye komai.
Deadlines din sun zama kamar ƙaya,
Pressure kuwa? sai ka ce mutum rasa ransa zai yi dan wahala da su project
Amma Azrah ba ta ja da baya ba.
Tuni ta saba da wannan yanayin, ta san yadda ake tsallaka wahala da juriya
Yanzu ba ta jin tsoro idan assignments suka taru.
Ba ta kuka idan ta kasa gane wani abu.
Zata tsaya, ta numfasa, tayi addu'a… sai ta soma aikatawa
Sarah kuwa, ta zama ginshiki gare ta.
Su biyu kullum library, dare da rana.
Wani lokaci har kwana suke yi a faculty.
Ma'aikatan tsabta ma sun saba da fuskar su.
Khalil kuwa yana kiran ta akai-akai.
Kamar yana jin lokacin da zuciyarta ke buƙatar karin ƙarfi.
Basa daɗe wa a wayan dan baya son hanata karatu, amma muryarsa na kawo salama sosai a rayuwarta, yakan ce
"Azrah kin kusa. Kar ki bari haskenki ya mutu, First class din nan dai karki sauka please"
Wannan ya zama kamar zikirinta a zuciya.
Sadeeq?
Har yanzu yana nan, yadda yake a farko, sai dai kuma tsanarta a zuciyarsa ya karu ne sakamakon bata tsoron sa ynx, yana ja mata tsaki itama zata yi, idan ko kallon banza ya mata haka zata rama dan tasan bai isa yace zai mata komai ba, da tuni tayi reporting ɗinsa
Amma duk da rashin jituwa tsakaninta da Sadeeq, ƙwazon Azrah da hazakarta na ci gaba da ja hankalin sa a sirrance.
Yakan ganta tana daurewa da karatu ba kakkautawa,
kuma sau da dama sai ya kasa dauke idanuwansa daga kanta ko da kuwa ba zai taɓa yarda da hakan ba.
Sai gashi ranar paper na ƙarshe ta zo.
Azrah bata runtsa ba duka dare tana maimaita notes dinta.
Da asuba, jikinta rauni, amma zuciyarta cike da ƙarfi da shiri.
Ta saka hijabinta akan sleepwear ɗinta da ko cirewa bata yi ba, ta dauki pen and exams card dinta
ta furta "Bismillah" kafin ta fice.
A cikin hall, zukata na bugawa da tashin hankali.
An raba question paper da booklet, Lokaci ya fara.
Hannun Azrah bai tsaya ba da rubutu ba, yadda kasan rubutun flowing yake yi haka take rubutu
Bayan awa uku da fara exams ɗin… sai aka ce pens down.
Farinciki ya barke.
"Finally!"
Azrah ta kalli kewayenta, fuskoki cike da murmushi, runguma, murna...
Ta juya ta kalli Sarah,
suka yi dariya mai sa hawaye.
Duk suka fita a hall ɗin, suka dauki hotuna da abokan su, wasu suka rungumi malamai,
har ma daga karshe duk suka tsaya waje ɗaya suka dauki group selfies a ƙarƙashin butterfly
Gaba ɗaya abin kamar mafarki.
Bayan exams ance karsu tafi saboda zasu tsaya har result ya fito sannan ayi convocation kafin su tafi, hakan ya zama kamar suna da ɗan gajeren Hutu kenan,
Amma Azrah bata samu hutu sosai ba.
A mafi yawan lokacin, tana cikin tunani ne.
"Shikenan kenan? Ina shekarun nan suka tafi?"
Ta tuna da kanta lokacin farko da ta zo yarinyar nan mai kuka.
Ta tuna da Umma, Zahra, da Khalil, da rayuwa gaba ɗaya.
Ta gane cewa ta canza... sosai.
A yanzu dai suna jira sakamako,
sakamakon da zai tabbatar da ta kammala digiri.
Gaba kuma shine convocation, ranar da tun shekarunta na farko take mafarkin sa.
Ranar wata Laraba da yamma ne
Bayan sun karɓi rigunan graduation ɗinsu,
Wanda ke ɗauke da sunan su da tambarin department,
Azrah da Sarah suka saka tare da wata Pant, suka fita da fara'a a fuskokin su.
Suka tafi zuwa department,
Inda suka fara ɗaukar hotuna da lecturers ɗinsu,
Kowa cike da murna, dariya da farin ciki.
Fuskar su ta bayyana cewa an cimma babban burin rayuwa.
Azrah ta ji zuciyarta na tafasa amma na farin ciki,
Wannan ne ƙarshen wata babbar tafiya.
#Jiddatulkhayr
08110615256
Episode 52: The Day Before Convocation
Wani sanyi ne mai daɗin gaske ya yake sauka. Azrah ta gyara kwanciyarta amma jin surutun wasu a hostel ɗin yasa ta buɗe Idanunta wanda yake cike da bacci, Ta miƙe a hankali tana jan bargonta, karasa jikin window tayi, sannan ta ɗan yaye labulen taga. Rana ce ke shirin fito da sauri ta juya ta kalli agogo, tabbas yau sun makkara
"SubhanAllah," ta furta tana murza idanunta
"Ke Samira ta shi, mun makkara fah, almost 6am fah" ta faɗa tana hanyar ban ɗakin, bayan ta fito ta hau kan sallayan. Bayan sun idar da sallan suka yi azkar ɗinsu na safe
Kamar karfe 7:10am... Samira ta ce "Azrah can't believe gobe ne fah..."
Azrah cikin murmushi "Gobe shine final show, Ni ba wannan bama muyi mu karya kar Sarah ta fara damun mu da kira ne"
Suka nufi kitchen ɗin su, inda suka dafa tea da toasted bread. Duk da excitement ɗin da ke zuciyarsu, amma sun san tabbas zasu yi missing juna"
8:30am..
Samira ta ce "Gaskiya ya kamata mu tafi yanzu, Sarah tace ta riga ta isa tun karfe shida..."
Azrah ta ce "Bari na ɗauko card ɗin SPA ɗin daga drawer ɗina" daga haka ta nufi wajen drawern
Bayan sun gama shiryewa suka fita daga hostel ɗin. Suka kulle ƙofar ɗakin su. Tsayawa suka yi suka gaisa da wasu neighbors a corridor, sannan suka wuce.
Harabar hostel ɗin a cike yake da yan mata masu shiri especially grad students, Kowa a cikin wani yanayi ne na shauƙi da farinciki. Suna tafiya suna gaisawa da friends har suka fito bakin gate, inda suka kira bold, driver ɗin da zai kai su.
Bayan sun shiga motar suka kama hanyar Spa ɗin. Samira ta ce
"I can't believe four years just flew like that" Azrah ta amsa da
"It's not just four years. It's four years of pain, growth, and strength" Samira cikin dariya ta ce
"Hmm... And friendship. Don't forget that" Azrah tayi dariya bata sake ce mata komai ba
Suna isa SPA ɗin, suka fito daga mota suna murmushi. Cikin SPA ɗin suka shiga, A can gefe suka hango Sarah ana mata foot massage.
Sarah ta daga kai tana dariya ta ce
"Sannu bestie! Kun jima wallahi, ku kara so nan" Azrah na Murmushi ta ja hannun Samira suka yi wajen tana cewa
"Mun makkarae ne fa. Kuma kar ki manta ni da Samira muna da salon delayed beauty"
Samira ta ce "kar ki min sharri Nikam" duk dariya suka yi
Staff ɗin SPA ɗin suka zo suka tarbe su da fara'a
"Sannu da zuwa Darlings. Ku biyo mu nan please"
Suka bi su ciki, inda aka nuna musu kujerun su, babu bata lokaci suma aka shiga musu gyaran fata
A cikin SPA, ana tsaka da scrubbing da body massage, bakinsu ya gagara shiru, kamar duk damuwar da suka sha na makaranta kamar basu yi ba
Tun kafin ayi nisa kowa sai kallon Azrah yake, su Sarah da Samira sun saka Azrah gaba da tsokana.
Sarah cikin dariya ta ce
"Toh wallahi Azrah ki fa shirya. Gobe kawai ki saka hulan grad sai kuma ki saka wedding gown a ɗaura aure"
Samira ta ce "Khalil zai zo ya tafi dake kai tsaye gidansa kawai!"
Azrah ta tabe baki tana dariya
"Ku kuka sani, ko kuma Samira da ya rage 2 weeks bikinta ita ce za'a daura auren gobe ba"
Ana nan wasy ma'aikatan SPA ɗin suka iso da wata body oil suka ce za su yi final moisturizing.
Dayar tana kallon Azrah ta ce "Wow! Your skin is so beautiful and clear!"
Wata kuma ta ce "Very soft! What do you use?"
Azrah ta kalli Sarah tana dariya ta ce "wlh babu komai daga Allah ne kawai"
Sarah ta kwafa ta ce "Mune fa da muke baki da kulawa" duk aka yi dariya
A haka har suka gama cikin annashuwa da dariya, suka wuce wani saloon dake kusa. Aka musu gyaran gashi, aka dora musu setting cap, gyara ba na wasa ba suka sha, Kowa na kallonsu kamar bride squad suka fito.
Bayan gyara, suka hau bold suka koma makaranta. Suka wuce students unit direct suka karɓi graduation gown ɗinsu wanda ke dauke da sunansu da logo na department.
On the way back to hostel
Suna tafiya suna hira sai wayar Sarah ta fara ringing. Tana dubawa taga "Mum Mie" ke kira. Ta ɗaga cikin sauri.
Sarah cikin muryar farin ciki ta ce "Hello Mum…" bayan Mamanta ta faɗa mata wani magana sai Sarahn ta ce "What?? Already??”
Ta kalli Azrah cikin farin ciki tana dariya sosai ta ce
"They said they've landed! Their flight just landed now at the airport!"
Azrah ta ce "Oh wow! That's amazing! Ma Shaa Allah"
Sarah tayi hugging Azrah tana dariya ta ce
"I'm off! I have to go and pick them up right now!"
Azrah ta rike hannunta ta ce "Please send my greetings to them. I can't wait to meet them again!"
Sarah na dariyar farin ciki ta ce "I will. Later today inshaAllah zan zo, ynx ki huta fa!"
Azrah tayi mata sallama, sannan ta juya ta ce
"Samira nagode sosai. Zan wuce sai anjima na shigo"
Samira ta ce "Allah ya kaiki lafiya. See you later"
Daga haka ta juya su kuma suka cigaba da tafiyar su
Suna isa hostel din cikin gajiya da annashuwa, fuskokinsun nan ya kasa boye yanayin farin ciki da suke ciki, da jin dadin ganin sun kammala shirye-shiryen gobe.
Azrah da Samira suka shiga cikin dakinsu, suna dariya suna tunanin yadda gobe zata kasance.
Bayan sun cire kayan jikinsu suka saka kayan mai sauki, sannan suka tsaya gaban mirror.
Suka zuba ido suna kallon kansu, sabbin fuskoki, sabbin fata, sabbin kyawu.
Samira ta shafa fuskanta ta ce
"Azrah wlhi yau dai ace ki kai attending wedding sai dai a ɗauka kece matsayin amarya"
Azrah ta tabe baki cikin dariya ta ce
"Haba Samira, ai gobe ma bikin ne amma bikin karatu, ba bikin aure ba"
Duk suka fashe da dariya
Azrah ta juyo ta kalli kanta a mirror sosai. Sai ta ji wani abu ya tokare mata zuciya a hankali ta zauna a bakin gado tayi tagumi sai kuma dan tayi distracting kanta ta janyo wayarta, ta danna video call wa Umma
Umma ce ta ɗauka da murmushin da kullum ke kawo mata natsuwa.
Azrah ta ce "Assalamu Alaikum Umma...
Umma cikin fara'a ta ce
"Wa'alaikum salam diyata, yau kuma wannan farin cikin duk na gobe ne?
Azrah tace "Umma baki ga yadda na kara kyau bane ina shining?"
Umma ta ce "kin kara kyau fiye da kullum ma!"
Azrah ta murmusa
"Umma, wallahi yau mun gaji... Sai ki ga gyaran jiki da gyaran gashi da aka mana"
Umma ta ce "Allah sarki. Ina Samira?"
Azrah ta ce Gata nan…" ta matsa wayar a zuwa ga Samira, karɓa tayi suka gaisa da Umma sai kuma ta bawa Azrah wayan bayan sun gaisa
Sai ga Zahra ta leko daga gefe tana dariya ta ce
"Ahhhh! YaAzrah! What are you turning into like this? Wallahi you look like one Indian princess!"
Azrah ta fashe da dariya ta ce
"Zahra dan Allah ki barni haka, har kin ga gyaran jikin kenan?"
Ta ajiye wayan tana nuna musu hannunta da fuskanta
Umma dai murmushi kawai take, zuciyarta na cike da alfahari
Ta ce "Wlhi da ace da hali ko muna da kuɗi, sai dai ki ganni a India yau. I swear I for wear sari mu haɗu mu ɗauki hoto!"
Azrah na dariya ta ce "Ina kaunar ku sosai. InshaAllah gobe everything will go well"
Umma cikin taushin murya ta ce
"Allah ya sanya albarka Azrah a karatun ki, Allah ya cigaba da haskaka miki lamuranki kamar yadda yake haska miki ko da yaushe" Zahra ta turo baki ta ce
"Ni fah?" Umma na murmushi ta e "Duk kan ku nake nufi"
Azrah ta ajiye wayar a gefe, idonta ya kaɗa sosai. Gobe zata karɓi certificate na digiri… ta tsaya har zuwa wannan mataki.
Kwanciya tayi tana tunani, sai wayarta ta fara ringing. Tana dubawa taga Khalil ke kira.
Ta dan tsaya kafin ta dauka, zuciyarta na bugawa da sauri.
Tana daga wayar, muryarsa ta fito da saukin da ya saba dashi ya ce
"Princess fito waje…"
Azrah ta zaro ido
"Wani waje? Don't tell me ka zo India wai?"
Khalil da dariya ya ce
"Toh sai ki fito ki gani"
Kafin ta ce wani abu ya kashe kiran. Ta kasa motsawa na dan lokaci.
Samira wacce ke kwance a kan gadonta ta kalleta cikin mamaki ta ce
"Lafiya? Hope all is well?"
Azrah ta mike tsaye tana tabe baki ta ce
"Khalil yace yana waje…"
Samira ta fashe da dariya
"Wai, gsky yana da romantic touch Khalil din kin nan. Dama nima Deen dina ya zo mana! Amma yana can yana hidimar shirin bikinmu. Hmmm…" ta karasa da dariyar zolaya
Sai kuma ta ce "Toh bestie, tafiyarki lafiya!"
Azrah ta nufi wardrobe ta zaro wani vintage green veil, ta daura shi luff a kanta, cikin sanyi jiki ta fara tafiya, zuciyarta na bugawa da sauri, tanason ganin sa amma bata tsammanin yau yau ba
Tana karasa kofar hostel, sai tagan shi tsaye a can gefe, hannunsa a aljihunsa, yana kallon wasu students dake wucewa
Khalil ya juyo kamar ya ji fitowarta. Idon su ya hadu.
Ta karasa wajensa a hankali, murmushinta cike da jin dadi da hawayen da bata san na menene ba ta cs
"Assalamu Alaikum…"
Khalil ya murmusa yana kallonta cike da So ya ce
"Wa'alaikum Salam. Kinsan ɗauka kamar karya nayi miki ko?"
Azrah ta girgiza kai tana dariya da hawaye ta ce
"Wallahi ban taba tunanin zaka zo yanzu bane…"
Khalil ya numfasa, yana kallo kamar yana jin tausayinta ya cw
"Bazan zo ba? Sai dai not your graduation. Na zo ne… tare da su Ammah da little sis dina. Da harda Grandma me kama dake amma bata jin daɗi ne yasa bata biyo mu ba"
Azrah ta zaro ido sosai tana kallonsa cike da dunbun mamaki ta ce
"You mean… your biological mother da sister?"
Khalil ya gyada kai
"Eh mana, Sun sauka a hotel yanzu. Na bar su can, nace let me come see your face first"
Azrah ta rasa me zata ce. Idonta ya cika da hawaye, ta lumshe su.
Khalil ya matso kusa kadan, ya ce
"Haba mana, common. Ki daina kuka, ba na so ki bata wannan glowing face dinki kafin graduation... "ya dan yi dariya
Ta daga kai ta kallesa, da murmushi mai cike da jin dadin kulawarsa.
Wannan mutumin... kullum yana shigowa rayuwarta a lokacin da take bukatar shi fiye da komai.
Bayan sun ɗanyi hira na dan lokaci can ya kalleta da murmushi ya ce
"Yau da daddare, zan dawo… mu fita tare, just to refresh your mind before tomorrow. What do you think?"
Azrah ta tsaya, zuciyarta na bugawa. Ta rasa ko ta amince ko ta ki.
Sai dai kafin ta gama tunani, sai kawai ta samu kanta da gyada kai a hankali ta cd
"Toh... okay"
Khalil ya yi murmushi mai sauki ya ce "Good. Ki huta yanzu kafin Anjima na shigo"
Ya juya, ya bar wajen a hankali. Ta tsaya tana kallonsa har ya ɓace daga ganinta.
Zuciyarta cike da wani sabo daɗin da ba ta saba ji ba. Sai ta juya, ta koma hostel.
Tana shiga dakin, ta tsaya a bakin ƙofa tana kallon Samira wacce ke danna system
Azrah ta ce cikin mamaki da dariya
"Samira… can you imagine? Ammah da Intisar sun zo India! Purposely dan Ni?"
Samira ta juyo da sauri kamar wanda aka ce wani abu ta sake baki tana kallon ta sai kuma ta ce
"Kar dai ki cemin Maman khalil kike magana?"
Azrah ta jinjina kai, murmushinta na yawo a fuska ta ce
"Ita fa… ta zo. Intisar ma tana tare da ita, har yanzu na daina amsa mamaki"
Samira ta zare ido, tana kallonta ta ce
"Lallai… wannan matar tana sonki da gaske. Kuma ba ƙaramin so Khalil ke miki ba…" ta dan harare ta da wasa
"Gobe convocation, amma yanzu kam ya nuna miki ke ce First Class Heart Holder"
Azrah tana murmushi ta ce
"Hmm… ni dai kawai ina fatan Allah ya sa mu gama lafiya mu koma gida lafiya"
Samira ta ce ta janyo ta gefe ta ce
"Wlh ki rike sa hannu bibbiyu, dama ace nice uwar miji zata so Ni? Kalli yadda uwar Deen kwatakwata bata So na amma tana pretending sai kace Ni ban sani ba" Azraj ta ce "ki cigaba da addu'a komai zai wuce"
Bayan sallar Maghrib, Azrah ta jima tana addu'a da godiya ga Allah. Zuciyarta cike da nauyin farin ciki da sabuwar fargaba. Duk da gobe rana ce ta farin ciki, tana jin wani irin nauyi a ranta irin wanda ba komai ke kawo shi ba, sai deep emotions
Ta shige bathroom, tayi wanka cikin nutsuwa. Ruwa na sauka a jikinta kamar yana wanke damuwa da gajiya. Bayan ta fito, ta shafa lotion mai kamshi,
Sai ta ɗauko wani classy fitted gown mai hasken pastel pink, ta saka wanda ya lulluɓe jikinta cikin kyau. Sai ta ɗaura karamin veil mai ɗan shimmering simple but elegant.
Wayarta ta yi vibration. Khalil ne.
"I'm outside" kawai ya rubuto.
Ta ɗauki jakkan ta, ta juya tana kallon Samira tace
"Bye bye Samira, see you later
Samira ta ɗaga hannu kawai tana kallonta da dariyar irin yau ga itama zata bi saurayi.
Azrah ta fita, heel ɗinta na kara a corridor. Tana fita ta hangosa, tsaye a gefen mota, sanye da simple t-shirt da jacket, amma charming as always.
Idanunsu suka haɗu. Bayan ta karasa
Khalil yana buɗe mata mota ya ce
"Shiga My Queen"
Ta yi dariya, ta shige.
Shima shiga yayi ya tada motar suka bar makarantar. Babu wata hira mai yawa, amma every silence had meaning.
Azrah ta juya tana kallon sa ta ce "Toh dama ina za mu je ne?"
Khalil ya murmusa
"Wait and see"
Bayan dan tafiya, suka isa wani shahararren mall a cikin garin. Suna shiga ciki, ya nufa da ita wani luxurious gown store, Azrah ta juya kallonshi da mamaki. a ranta tana whispering ma kanta "Don't cry, please don't cry…"
Ya matso kusa da ita, muryarsa a hankali ya ce
"Pick any… I want you to look exactly like the Queen that you are tomorrow. You deserve nothing less"
Idanunta suka cika da hawaye. Ta mayar da kai gefe tana ƙoƙarin danne su. Ta zabi wani dark green long gown mai uban kyau, wanda ya bayyana simplicity na masu class.
Khalil ya ɗauka mata gold heels da bag da suka dace da stones din kayan. Daga nan suka wuce Jewelry section, inda ya zabi mata wani slim gold necklace, light gold earrings da tiny gold wristwatch
Daga haka suka nufa wajan biyan kuɗi, bayan anyi clearing ɗinsu aka saka musu kayansu a wani designer bag, suka kai musu booth ɗin mota.
#Jiddatulkhayr
08110615256
Episode 53: A Day to Remember
Daga nan suka nufi eatery mai kyau. Suna shiga suka zauna a corner mai dan soft lighting. Azrah ta zaɓi pasta da grilled chicken, shi kuma ya ɗauki burger da fries. Bayan an kawo musu suka fara ci a hankali without saying uffan
Can Khalil yana murmushi ya ce "Do you remember your first semester?"
Azrah ta dan sosa kai tana dariya ta ce
"Don't remind me… I was too lost wallahi"
Khalil ya ce "And now… you shine. You didn't just survive, you bloomed"
Azrah ta zuba masa ido, zuciyarta cike da soyayyar sa. Tana ji kamar zuciyarta tana karanta ƙaunarsa har cikin numfashinta.
Ta ɗauki ice cream da aka aje mata, banana flavor, ta fara sha kamar bata son sha shi kuma ya zuba mata ido. Bayan sun gama yayi clearing Bill sannan suka fito, inda yayi parking suka karasa, suna shiga ya tada motar straight schl dinsu ya wuce. A kofar hostel ɗin yayi parking. Ta buɗe kofar motar, ta juyo tana kallon sa da murmushi a fuskarta ta ce
"Thank you... I don't even know what to...."
Yayi saurin matsowa kusa da ita, ya daura yatsansa a bakinta ya ce
"Shhhh... no thanks. Just shine tomorrow. That's all I want"
Ta ɗan lumshe ido, jikinta yayi sanyi. Sai kuma ta karasa sauka a motar, ta dauki laidan sayayyan, ta shige cikin hostel
Tana shiga dakinsu babu kowa As expected, Samira bata nan. Ta ajiye designer bag a gefen gadon ta wuce toilet ta watsa ruwa. Bayan ta fito, ta saka soft pajamas, ta kwanta akan gadonta.
Ta jawo wayarta. Ta rubuta masa sako
"Thank you for everything. For believing in me. For seeing the light I didn't even know I had. I'll shine tomorrow, for us..." tana turawa ta kashe wayanta nan da nan bacci ya kwashe ta
Yau ta kasance itace ranan da duk wani mai karatu a makarantar yake burinta, Da asuba Azrah ta farka, kamar yadda ta saba, miƙewa tayi a hankali bayan tayi addu'ar tashi daga bacci, ta wuce toilet tayi alwala ta fito, cikin nutsuwa ta gabatar da nafilfilo sannan sai sallar Asuba. Bayan ta gama, ta zauna tayi Azkar, zuciyarta cike da godiya da farin ciki. A hankali ta ɗauki wayarta ta shiga video call wa su Umma.
Duk da dare ne a Nigeria, suna cikin annashuwa da fara'a suka amsa kiran.
"Kin tashi lafiya 'yar albarka?" Umma ta faɗa da murmushi.
Azrah ta amsa da dariya, "Lafiya lau Umma, Umma yau ne fah"
Zahra ta ɗora kanta a kafaɗar Umma ta fito ta cikin waya, tana kallon Azrah kamar zata yi kuka ta ce
"Yaya da ace da hali da na zo, sai dai kawai ki ganni" dariya ta yi
Suka yi hira cikin nishaɗi, suna tayata murna. Bayan ta kashe kiran, Samira ta juyo daga gado tana kallonta.
"Jiya na dawo kina bacci kuma Naga... waɗannan kayan masu tsada fa... kar dai saurayin ki Khalil ne ya siyo miki?"
Azrah ta ƙyalƙyale da dariya, sannan ta gyada kai cikin kunya.
Samira ta ware ido tace "Lallai wannan Khalil ɗin yana so ki fito as Queen fa!"
Suka yi dariya daga haka Samira ta sauko a gadon itama. Can suka fara shirye-shiryensu. Sai ga kiran Sarah ya shigo wayan Azrah
"Yaushe zaki taho?"Sarah ta tambaya
"Da ɗan anjima ne" Azrah ta amsa tana saka tooth paste a brush din hannunta
"Toh yanzu zan tafi makeup studio, daga nan sai mu shigo da su Mamana" cewar Sarah
Daga haka suka yi sallama. Bayan sun gama breakfast, sai ga kiran Khalil ya shigo
Bayan Azrah ta ɗaga "Ki fito Azrah, ina bakin hostel" muryarsa mai taushi ta karade kunnenta
Azrah ta ɗan lumshe ido ta ce "Yanzu kuma?" Ya ce
"Eh mana My shay, ke da Samira"
Ta kashe kiran tana kallon Samira ta ce
"Khalil na waje ne, yace mu fito yanzu"
Samira ta tashi da sauri tana cewa
"Ke muje, tashi muje mana, yanzu haka wani abun alkhairin ne naga guy ɗin yana son slaying"
Da suka fita, Khalil ya tsaya yana kallon Azrah kamar zai haɗiye ta. Yana murmushi, shi ko ɗan keftawa baya son yi
"Assalamu alaikum" ta ce a kunyace.
"Good Morning princess" yace da taushin murya. Samira ma gaishe sa tayi, bayan ya amsa gaisuwar Samira
Sai ya kalli Azrah "Ko akwai wani abu da za ku bukata a ciki? Idan babu kuma ku ɗauko kayanku da za ku sa da dai duk wani abu da zaiyi completing dress ɗinku, zan kai ku wajen makeup ne, daga can zan karasa da ku venue ɗin kawai"
Azrah ta daure fuska kamar mai son kuka ta ce "Nifa ba zanyi ba wallahi"
Khalil ya kwaɓe fuska kamar zai yi kuka shi ma, exactly yadda tayi yayi copying ya ce "Ni kuma nace sai Queen tayi"
Wannan ne yasa Azrah ta yi dariya tana ja da baya
Samira na hararan Azrah ta ce "Nikam bari naje na dauko kaya na" sannan ta juya ta shiga cikin hostel. Azrah ma ta bita a baya, daya kai Samira gwara duk rashin son ta tayi kawai
Bayan sun fito daga hostel ɗin, Azrah da Samira kowaccensu na ɗauke da small trolley bag ɗin kayan ta. Khalil ya budewa Azrah ƙofa ta shiga bayan ya karɓi trolley ɗin, yasa a booth tare dana Samira, ya zagayo ya zauna a driver seat ya ja motar cikin nutsuwa da kulawa suka bar makarantar
A hanya babu mai magana sosai, hakan yasa cikin motar shiru... kowa da kalan tunanin da yake yi. Kallon gefensa Khalil ke yi ta gefen ido, yana kallon ta a hankali yanda tayi shiru, yanda idanunta ke kallon titi
Bayan wasu mintuna suka isa shagon makeup. Wurin ya kasance babban waje ne, mai tsabta, cike da kyalli da kwararrun ma'aikata. Da suka shiga ciki aka tarbe su da murmushi cike da girmama customers
"Welcome ma'am, happy convocation day!"
Ɗaya daga cikin makeup artists ta faɗa da fara'a tana kallon Azrah, wacce ta yi simple shigar safe, amma kyau da haske ya gama bayyana tun kafin a taɓa fuskar ta. Daga haka suka shiga ciki
Azrah ta zauna a gaban first mirror , Samira kuma a gefen ta. Wata babban makeup artist ce ta zo da kayan aikin ta tana kallon Azrah da murmushi ta ce
"Wow... you are naturally beautiful. Today you'll shine like a queen dear "
A hankali aka fara mata makeup, suka fara da moisturiser, suka shafe mata a fuska da luf-luf, sannan suka fara da foundation, concealer, powder da eyeshadow mai launin rose gold wanda ya shiga da bag and shoe dinta, Lips dinta aka yi soft nude pink, sannan aka gyara mata gira cikin nutsuwa.
Ana tsaka da yi, wata daga cikin staff din wajen tace
"Lallai mu dai zamu baki card ɗinmu dan munsan zamu samu customers ta wajen ki? Wlh irin wannan kyau dole ya jawo mana mutane ne"
Sauran suka amsa da "yesss" wata tana ɗaukar hotonta da izini tana cewa tana son zata saka a page ɗin Makeup artist ɗin su a Instagram.
Samira na gefe tana kallon Azrah tana dariya, tace
"Toh! Dama ai nace miki ki shirya zama amarya amma kika ki"
Azrah ta harare ta cikin madubi tana murmushi.
Bayan makeup aka ce su shiga VIP changing room. A can kowaccensu ta cire kayan jikinta ta saka kayan da zata je wajen da shi, Azrah ta zaro kwalin gown ɗinta da Khalil ya siya mata, tana buɗewa zuciyarta kamar zata fashe. Wannan green velvet gown ne mai ɗan ɗaukar ido, fitted ne, shoulder ɗinta a buɗe kadan, sannan ya kama jikinta har kasa ta bayan kamar follow me, kana ganinta kamar queen ɗin da za ta hau sarauta.
Ta saka gown ɗin, ta saka takalmi da bag ɗin da suka haɗa da kayan. Wani ɗan gold necklace mai kyau da agogo ta saka, sannan ta ɗan juya a gaban mirror. Bayan sun fito
"SubhanAllah…"
Wani staff ɗin shagon ya faɗa yana kallonta, wanda da alama kamar musulmi ne
"Wallahi this is beyond beauty"
Har Azrah ta rasa inda zata sa kanta, ba don girman kai ba, sai don yadda ta ga kanta daban. Wannan ba Azrah ɗin da ta fara shekarar karatu ba bace. Wannan wata sabuwa ce, mai kwarjini da nutsuwa, mace mai daraja. Ji tayi kamar ba zata iya shiga cikin mutane da wannan shigar ba.
Samira ta fito itama cikin nata shigar mai kyau. Suka kalli juna suka fashe da dariya.
"We're ready for the world" Azrah tace a hankali tana kallon kanta.
Khalil yana tsaye a waje yana danna wayarsa, amma zuciyarsa tun tuni ta gama tafiya cikin shagon. Bayan ya ɗauki lokaci yana jiran su, sai yaji kamar ba zai iya jurewa ba, "Let me see for myself" ya faɗa cikin zuciyarsa.
Sauka yayi a motar. Ya bude ƙofar salon ɗin a hankali, yana shiga ne kamar wanda aka kira sa. Sai idonsa ya sauka a kanta.
Azrah na tsaye a gaban mirror tana ɗan gyara bracelet ɗinta, ita da Samira suna dariya. Da Khalil ya hangota sai ya tsaya cak. Fuskar sa ta cika da wani irin mamaki ne lokaci guda.
"Innalillahi... Azrah?"ya furta a hankali kamar mai mamaki.
Salon ɗin ya dauki dariya. Wata staff tace
"Calm down, sir? Kar ka cinye mana customer"
Khalil ya karasa a hankali, yana kallonta tun daga ƙafarta har zuwa saman gown ɗinta, yanda tayi shigar, makeup ɗinta da kwarjini da nutsuwa da kyau da yake gani a fuskarta. Ya tsaya gabanta, ya lumshe ido yana jin wani sanyi a zuciyarsa
"Honestly... I've never seen anything more beautiful'' yace da sanyi kamar zai shige jikinta
Azrah ta ɗan ja baya tana murmushi, tayi ƙasa da kai.
"Khalil stop… People are watching"
Ya ɗan matsa kusa, kamar zai rungume ta, sai ya ja burki da kyar ya tsaya ya ce
"At this point, sai dai in ɗauke ki in gudu"
Wata staff ta ce
"Ku tsaya mu ɗauki hoto fa kafin ku gudu!"
Azrah da Samira suka tsaya kusa da juna, Khalil kuma ya tsaya a gefen Azrah yana kallonta yadda kasan zai cinyeta ko kuma irin rayuwar sa depends on that. Hakanan suka ɗauki hotuna da dama, group pictures, close-up da har da candid ɗin Khalil yana kallon Azrah da murmushi.
Bayan sun fito, Khalil ya bude musu ƙofa suka shiga motar. Yana zagayawa ya zauna a driver's seat ya kunna motar. Har suka bar salon ɗin suna dariyan staffs ɗin
Yana driving, bai ce komai ba sai da suka kusa shiga makaranta, sannan yace a hankali
"Azrah, yau kin sa ni na sake gaskata cewa mace zata iya haskaka duniya… sai dai na zata.."
Azrah ta lumshe ido, ta dafe ƙirjinta tana jin zuciyarta yadda yake bugawa. Ta san yau ba kawai graduation day bace, yau rana ce da aka tabbatar da darajarta, taya zata so Khalil less a rayuwarta?
________
Hall ɗin da aka tanada domin Convocation ya sha ado tamkar ana shirin liyafar sarauta. Fitilu masu sheƙi suna haska ko'ina, red carpet ya shimfiɗe tun daga ƙofar shiga har zuwa bakin stage. Kujeru masu furanni sun zagaye hall ɗin, kuma banners masu dauke da sunayen makarantar da "GRADUATION 2025" sun manne ko'ina cikin hall din.
Manyan baki sun fara shigowa tun karfe 8 na safen, minista, shugabannin kamfanoni, sarakuna, iyaye da dangi daga ko'ina, kowa cikin shigar alfarma. Kamshi kuwa ba zaka gane wani kalan kamshin turaren bane kake ji dan kowa kamshi na musamman yake bugawa, babu abin da kake ji sai sautin dariya da gaisuwa daga ko'ina.
A wajen makaranta kuwa, cunkoson mutane da motoci ya hade titin. Jami'an tsaro na kai da komowa, da 'yan media suna daukar hoto da bidiyo, wasu kuma na tambayar graduates don jin yadda suke ji a wannan ranan
Duk makarantar ta ɗau zafi, har sai da aka saka loudspeakers a wajen hall domin waɗanda ba su samu shiga ba su ji abin da ke faruwa ciki.
Jerin sunayen students suka fara karantawa cikin tsari. Kowanne department da list ɗin students ɗin su
Sun iso hall ɗin convocation Khalil yayi parking inda yasan idan zasu bi su shiga rana ba zai taba su ba. Ya kalle Azrah bai san sanda murmushi ya ƙuɓuce masa ba. Sai kuma ya sauka ya zaga ya buɗe mata kofar motar yana murmushi har sannan kuma ya gagara ɗauke idonsa a kanta ya ce
"Ready, Graduation Queen?"
Azrah ta gyada kai, zuciyarta na bugawa da sauri da sauri. Tana ji numfashinta kamar na seizing a hankali. Samira data sauka ta karasa gaban motar itama ta rike hannunta, sako kafarta tayi kasa sannan ta fita daga motar a hankali, kayan su kadai abin a juyawa a sake kalla ne
Da suka shiga hall ɗin, kallo da murmushi suka fara bibiyar su daga ko'ina da Sautin dariya, wasu ma suna ta hugging dinsu suna gaisuwa, wasu kuwa a hostel suka san fuskan juna, shiyasa sai suyi ta gaisawa at least wannan ranan nasu ne Azrah taji kamar ta koma hostel ta canza kayan barin yadda taga kamar attention ɗin mutane ya koma kanta ne
A gefe kuma 'yan department ɗinta ne suke zaune kamar shine spot ɗin nasu, abokai, classmates suna murmushi, ihu, suka karɓe su da farin ciki. Wani yace da da karfi
"Haba! Graduation queen din mu ce! The best of all" duk suka fara dariya. Sarah ta zo da sauri, ta rungumi Azrah, ihu ta fara, mutane na bin su da kallo.
"Wow, look at youyyy?" Sarah ta faɗi tana bin Azrah da kallo tun daga sama har zuwa kafarta, Azrah ta yi dariya, ta ce "Ke Sarah bana wani son tsokana irin taki".
Ceremony begins
Mai jawabi 'Master of Ceremonies' ya fito, ya yi sallama, ya gabatar da manyan baki, Vice Chancellor, Deans, Malamai, parents, dangi. Dukkan hall ɗin ya yi shiru, fitilu sai aikin haska ko ina da colors masu kyau
MC ya ce "Barkan mu da wannan rana ta tarihi, ranar da muke taya daktocinmu, sarakunan karatu da graduates masu murna. Yau rana ce da ilimi ya tsaya mana gaba data ke jiran mu!"
Ya fara da kiran sunayen graduates su je stage su karɓi takardun su. Da department na Business Administration ya fara. Kowa na fita zuwa karɓa, amma zuciyar Azrah na bugawa da karfi ta rasa me ke damunta yau ne na bugawan zuciya
Sai MC ya ce......
#Jiddatulkhayr
08110615256
Episode 54: The Crown on the Stage
MC ya ce "Now presenting… Best Student of the Year…"
Hall ɗin ya yi shiru, sautin muryar MC ya cika hall ɗin. Aka fara murmuring kowa da wanda yake ambata ganin kamar shi za'a ba wa, wasu kuma suna sake nanata sunan Azrah ne
MC ya ce "Azrah Muhammad Ibrahim!"
Mutane suka dinga tashi daga kujerar su dan ganinta, wasu mamaki ne fal ransu ganin yarinya ce, wasu cikin farin ciki especially coursemates ɗinta, Khalil dake gefensu Ammah ya gyara camera a wayarsa da sauri, Samira ta yi ihu tana tayata murna.
Azrah ta miƙe ta nufa zuwa kan stage, a hankali take tafiya, fuskarta na cike da farin ciki da mamaki, banda idanunta daya cika da ƙwalla. Ta isa stage. MC, VC ya mikawa da award da medal. Hakan yasa Azrah karasa wajensa, VC ya miƙa mata cike da faran ciki, kameru na ɗaukar su a hoto banda basu yin video ga kuma 'yan jaridu
Bayan ta koma ta zauna riƙe da award ɗin, Sarah kamar zata cinye ta, ga Samira data bar cikin nata Colleagues ta dawo wajen Azrah duk suna taya ta murna itakam ta zama so emotional ne.
MC ya ci gaba "Next award: Best in CGPA, First Class"
Sauti da ihu ya ƙaru. Bayan hall ɗin yayi shiru na sanadiyyar da MC yayi magana, a hankali ya sake furta sunan Azrah. Wannan karon, zuciyarta ya tsananta da bugawa, A hankali ta miƙe, nan ma colleagues ɗinta suka fara ihu, nan ma ta sake karɓa awards ɗin, an haɗa mata da bouquet na flower
Bayan haka, MC ya cigaba
"Special Award: Most Talented in Business Skill"
Kowa ya yi shiru, daga staff zuwa dalibai, MC yayi murmushi ganin sunan wanda zai sake kira hakan da yayi kuma ya sake jan hankalin mutane kowa na son sanin wanene, MC ya sake kiran sunan Azrah, ji tayi komai ya tsaya mata na wasu dakiku, Sarah ta taɓa ta ce
"Azrah Ki tashi mana" hakan yasa ta miƙe trying hard not to cry, Project supervisor ɗinta kuma shine lokacin IT yayi supervising dinta ya ɗaga mata hannu yana murmushi ya ce
"You represent excellence. May this achievement be just the beginning"
Ta karɓi award ɗin cikin ladabi. Hall ɗin ya cika da tafi, dariya da ihu. Azrah ta juya, zata sauka nan ta ga Khalil ya tsaya tare da masu hotuna yana Mata hoton, Idanunsa na kallonta cike da ƙauna da alfahari. Murmushin ta mayar masa, ta sauka sai ga Samira ma ta biyo ta
Aka kuma kiranta wanda wannan karan ta kasa hakura ta fashe da kuka, A ƙarshe, VC ya karɓi wani graduation gown irin wanda sai anyi honoring dinka za'a saka maka, daga mataimakinsa, ya daura mata 'tag' a wuyanta irin na VIP, sannan ya saka mata gown ɗin ya kwanta hannu a kan kafadarta. VC yayi hoto da ita, Deen and other staffs, kowa ya tashi yana ihu, classmates, abokai, duka suna taya ta murna
Azrah ta kasa rufe baki zuciyarta cike da jin kai, farinciki, godiya. Murmushi ya zama hawaye na farin ciki, idanuwa ya gagara controlling kansa sai hawaye ne ke zuba
Speech Time
MC ya miƙa mata mic. Stage ya yi shuru. Hasken fitila ya ƙara haske akan ta. Duk mutanen hall ɗin na kallonta.
Azrah ta ɗago kai, ta fara da muryar ta mai sanyi
"Assalamu alaikum wa rahmatullahi wa barakatuhu. First of all, Alhamdulillah ga dukkan godiya ga Mahalicci na Ubangiji Mai rahama, wanda Ya ba ni damar sanin ilimi, Ya shiryar da ni, Ya kare ni daga sharrin duniya da zuciyata, da badan da yardan sa ba bazan taɓa zuwa matakin da nake yanzu ba
Ga malamaina, da suka tsaya wajen bamu shawara akan karatu, da ilimi da kuka bamu.. wannan nasara ba tawa kadai ba ce, nasarar mu ce gaba ɗaya. Ga iyayena musamman Ummana ina godiya da yarda da Ni da suka yi, dakuma tsayin daka akan addu'ar nasara a rayuwata
Kuma ga abokiyar karatuna, classmates ɗina, Godiya nake muku. Duk sanda naji na gaji da karatu ku kan tuna min cewa kada na bari wahalar dana sha a farko ya tafi haka nan, na dake ta cigaba da tafiya da first class dina, wannan result da nake rike da shi yanzu, da badan ku ba, da wata kila ba result dake jikin bane, dan friends suna taka rawa sosai wajen rugujewar mutum
A ƙarshe, ga ke, matashi da matashiya da ke sauraro na, kada ku yi watsi da mafarkin ku. Kada ku bari matsaloli ko yanayi ya tsorata ku. Ku ci gaba da dagewa, ku riƙe manufa, ku ɗauki ilimi a matsayin haske, saboda haske baya tsufa, baya ƙarewa.
Wannan darajar da na samu, zata iya kai Ni inda ban zata ba, ba don na girma ba, A'a certificate ɗin ne take da girma, dan wajen aiki babu ruwansu da girman mutum sai dai girman karatunsa. Zan kuma so ace yau zan tafi viral a media, ba don a Sanni ba, A'a amma don in yi amfani da ita don sauƙaƙa wa wasu, su da ba su da damar zama a nan. Ku tuna "With great privilege comes great responsibility"
Nagode da saurarata da kuka yi. Allah Ya taimaka mana, ya sanya mu zama haske a kowanne fage da muka shiga. Wassalam"
Dukan hall ɗin ya ɗau tafi. Malamanta with pride suke kallonta, iyayen yara kowa kallon sha'awa yake mata, musamman wanda suka je kasar karatu daga Nigeria, ji suke ina ma ace 'yar su ce
Khalil ya juya, zai koma inda yake, hotunan daya mata ba adadi, daurewa ne, murmushi, hawaye, murna, duk sune a fuskanta
Azrah ta sauka a stage ɗin, tana jin wani sanyi a jikinta, ita kam babu abin da zata cewa Mahaliccin ta sai 'Alhandulillah! SubhanAllah!' dan Allah ya gama mata komai a rayuwarta, a hankali ta juya zata bawa MC mic ɗin data yi amfani da shi
Sarah ta cusa kanta ta wuce gaba tana hawaye mai murmushi. Azrah na sauka daga stage, ta rungume ta kamar zasu faɗi, ta ce
"You killed it! Wallahi kin gama karatu da girma! This is just the beginning Bestie"
Azrah ta fashe da kuka tana riketa, sai da suka kusa zuɓe wa, bayan ta miƙe ta daidaita kanta bata son saka hannu a fuskar dan karta bata makeup dinta, zasu fara tafiya kenan sai ga MC ya sake ɗaga murya, ya ce
"Please, we need Miss Azrah back on stage. A very special guest, His Excellency, the Governor of New Delhi, would like a photo with her!"
Hall ɗin ya sake kaurewa da tafi. Azrah ta zaro ido, tana kallon Sarah kamar "Seriously?", amma duk da haka ta ɗaga rigarta kaɗan ta koma stage tana murmushi wanda hawaye kuma har sun fara zuba
Gwamnan ya miƙa mata hannu cikin girmamawa, yana cewa
"Congratulations, young lady. You're a bright star" ita kuma sai ta wayence kamar irin tana girmamasa ne yasa taki yarda ta basa hannunta
Ya damƙa mata wani giant check na ₦50 million equivalent, kyautar girmamawa daga Mai girma gomna. Hoto aka musu tare da gwamna da VC, fitilu na ta haska su kamar tauraruwa.
Kafin ta sauka, sai ga wasu sun haura kan stage ɗin. Khalil. Ammah. Intisar. Nufan ta suka yi, amma kallon daya Azrah ta musu ta fahimci Mom dinsa ce da Intisar tun da dama tasan da zuwan nasu, murmushi ta sakar wa Ammah da Intisar
Ammah ta ƙaraso da fara'a, ta rungume Azrah kamar 'yar ta, ta ce
"Congratulations sweetheart. We're very so proud of you"
Azrah ba ta iya cewa komai ba sai murmushi da hawaye. Tana jin kamar mafarki ne. Intisar, kyakkyawa, mai fara'a, ta rungumata itama ta ce
"So you're the Azrah. Now I see why Khalil talks about you every second, Congratulations Sister in-law"
Azrah ta ɗan zumburo baki cikin kunyarta, Samira ta fito daga baya da sauri tana dariya, ta ce
"La! An bar ni a baya fa! Ana hoto da dangin ‘yar uwa ta bana ciki?"
Suka fashe da dariya. Aka sake komawa stage, aka musu kamar family photo, Azrah a tsakiya, Khalil yana kallonta kamar zai shige jikinta, tana ta ja baya amma ba ta tsira daga Kallonsa ba, ita mamaki yadda ko kunyar Ammah da Intisar baya yi, balle kuma idon mutanen hall ɗin.
Ganin haka ne yasa mutane suka fara shiga especially neighbors ɗinsu a hostel da kuma colleagues dinta
Daga nan suka sauka suka koma kujerunsu. Duk data gaji, Azrah ta tsaya kallon sauran shirye-shiryen da suka rage, zuciyarta cike da godiya, da natsuwa. Wannan rana ba zata taɓa mantawa da ita ba.
Lokacin da ake ta gabatar da program, a can gefe guda, Sagir da Sadeeq suna zaune suna kallon program din, Sadeeq daya ke jin kansa baka gane abin da yake zuciyarsa, Sagir kuwa sai murmushi yake ganin yarinyar da at least ya Santa ne tayi wannan breaking record a wata kasa ai ba karamin abun murna bane, ya ɗan kalli Sadeeq sai kuma ya ɗan matso kusa da shi yana murmushi ya ce
"Bro, gaskiya this Azrah girl is a gem. Ta burgeni wallahi. Karatu, nutsuwa, kuma yanzu look at her, kamar princess a cikin movie, please bata burgeka ba?"
Sadeeq ya juyo ya kalleshi da irin kallon rashin hankali, ya ɗan ja tsaki cikin rainin hankali ya cr
"Tchh… Ai duk 'yan mata idan convocation ya zo sai su yi kama da wata Queen. Bari kaga gobe sai kowa ya manta da ita"
Sagir ya murmusa kawai, amma zuciyarsa cike da sabuwar sha'awa da girmamawa ga Azrah. Ba ya jin kamar za a iya mantawa da ita haka nan. Bari ma da abu ne na fannin ilimi, kawai dai ya san halin Sadeeq ne ba lallai ya fadi wani good side of her ba, amma karya ne yace bata burgesa ba
A gefe kuma, wayoyin mutane na ta aikin mata ɗaukan hoto. Daya daga cikin professional photographers ɗin da ke wurin tun farko ya ɗauki hotonta lokacin da take karɓar award, ta ke murmushi cikin kyau, da gown ɗinta da tag a wuyanta. Wannan hoton ne ya fara yawo da sauri a kafafen sada zumunta.
Wasu daga cikin su sun saka caption ɗin
"From India with excellence Nigerian Asset Shines Bright!"
"Meet Azrah, The First Class Beauty with Brain, Business Admin Star!"
"Class, Grace & Intelligence. Nigeria is proud of her"
Blogs irin su NaijaGist, PulseNG, da CampusDigest suka fara wallafawa. Hoton ya fara yawo har da short clip ɗinta tana karɓar award da kuma lokacin da ta ke bada speech, da lokacin da take karɓan check a hannun gomna, da VC, dukka dai.
WhatsApp, Twitter, Threads, Instagram duk cike da suna da hotonta. Wasu har sun fara saka mata
#AzrahTheQueen
#NaijaAssetInIndia
#BrainsAndBeauty
Azrah dai ba ta san an fara haka ba tukun nan, amma duniya tunj har ta fara jin labarinta
Wannan rana ta zame mata rana ta tarihi, ba kawai saboda takardar digiri ba, sai dai saboda ta fara bayyana a duniyar da ba ta sa ran shiga haka ba.
Bayan an kammala program, an bar kowa cikin nishadi da mamaki bisa yadda Azrah ta tashi da lambobin yabo fiye da kowa, MC ya rufe taron cikin girmamawa da yabo ga dukkan graduates.
Azrah na sauka daga students stage, tana shirin fita daga cikin hall ɗin ne sai ta hango Maman Sarah tana tsaye tare da wasu sauran iyaye. Ta karasa wurinsu da girmamawa tana murmushi ta ce
"Barka da warhaka, Ma"
Maman Sarah ta rungumeta tana murmushi ta ce
"Yar albarka. Na ji daɗin ganin ki a haka. Allah ya baki sa'a a sauran lamarinki"
Suna cikin gaisawa ne ta juyo ta ga Maman Khalil da Intisar har sun fitar da wani katon buhu daga cikin motarsu. Buɗe buhun ya bayyana abubuwa daban-daban
Wani babban memo wanda aka saka hoton Azrah a kai da rubutun
'Congratulations Azrah, You made us proud!"
'Mug Cups' masu hotonta da kalmomin yabo.
'Towel da customised jotters, da wasu gift packs masu kyau sosai.
Azrah ta zaro ido da mamaki tana kallon kyautar. Ba ta iya magana ba kawai ta fashe musu da kuka ta juyo tana kallon Khalil ta ce
"Khalil… meye duk wannan?"
Khalil ya sosa ƙeya yana murmushi
"Just to remind you of how far you've come. And how proud we are" Yana gama magana kawai taga zai rungumata da niyyar share mata hawaye, ta ja baya da sauri tana masa wani kallo, murmushi kawai yayi
Ammah ta kama hannunta ta ce
"Na san ba za ki manta da wannan rana ba. Kuma ba za mu manta dake ba Sweetheart, ki daina kuka"
Azrah ta rungume ta, hawaye na sauka a gefen fuskarta
"Nagode sosai Ammah… Ban san me zan ce ba"
Samira ta karɓi wasu daga cikin gift cups ɗin, tana dariya
"Yau kinga Azrah ta koma celebrity. Come on, let's share this with your fans"
Suka fara rabawa wasu daga cikin classmates ɗinsu da friends. Kowa sai dariya da murna yake yi, isn't easy ka gama degree successful.
Bayan su Ammah sun tafi,suka zauna a waje suna shan iska, Khalil ya ɗauko wayarsa ya kunna video call dasu Umma, yana fara ringing Zahra ta ɗaga tana dariya, Umma ta ce
"Ma Shaa Allah My dear, Allah ya kareki min ke"
Zahra ta ce "Ya Azrah Queen of the Day!"
A haka suka dinga hirarsu, Khalil dama shi bai san wani sirkantaka ba haka ya zage suna hirarsu yana kara bawa su Umma labarin event ɗin, Umma ma da bata taso cikin wannan In-law things din ba tana biye masa, har suka yi sallama
Ganin yamma nayi Khalil ya miƙe yana kallon su ya ce
"Let me take you all back to the hostel. It's been a long, beautiful day"
Suka miƙe suka fara tafiya zuwa mota. Kowa na nan cikin annashuwa, da farin ciki
Washe gari bayan grand celebration na graduation ɗinsu, Azrah ta farka da karar wayarta cike da notification. Kusan minti-minti tana jin vibration, messages, calls, tags da reposts. Dama ita ba ta saba da irin wannan attention ba, sai take jin kamar duniya na kallonta ne
Tana kwance, tana daddanna wayar ne Sarah ta buɗe ƙofar ɗakin da murmushi a fuska ta ce
"Laaahh! Madam celebrity har kina da dama kwanciya?"
Azrah ta kalleta da murmushi.
"Wallahi notifications ɗin nan sun hanani bacci ma"
Sarah ta ƙaraso tana kallon screen ɗin wayarta.
"Yesss! Look! Wannan fa influencer ne mai 2.5 M followers! Yana cewa he wants to interview you!"
Azrah ta kafe wayar da ido.
"Wait... what?! Interview kuma? For what?"
"Bayan hotonki ya karaɗe blogs? Cikin rigar gown ɗinki da awards tags da VC ke ke saka miki gown? Gonma yayi hoto da ke kina tunanin wannan kaɗai ba zai saka duniya ta sanki ba ne?"
Ta dafe kanta. "This is too much for me wallah"
Sarah ta ce, "Relax. This is your moment, own it"
______
Yayinda suke hira, wayar ta fara ringing Khalil Calling. Tana ɗagawa, muryarsa mai sanyi ta sauka a kunnen ta wanda har sai data ji tsikan jikinta ya tashi
"Hey, graduation queen. Hope you slept well?"
Ta ce "Ka ga irin messages da hotona ke yawo kuwa?"
Ya yi dariya. "Na gani. Na kuma ce ai sai yanzu duniya za ta fara ganinki sosai, dan wannan ba komai bane a rayuwarki illa introduction"
Ya ja numfashi sai kuma ya cigaba "Azrah, please don't panic. Ni zan taimaka miki da interviews da duk wani abu. Just enjoy the moment"
Muryarta ta yi rauni ta ce "Na gode, Khalil. I really mean it"....
Episode 55: Returning In Glory
Bayan sallar Azahar, Khalil ya dawo tare da Ammah da Intisar.
Khalil ne ke driving a bakin hostel ɗin yayi parking motar, sun zo da niyyar ɗaukan Azrah zuwa small dinner da suka shirya mata. Azrah ta fito cikin shigar modest da kyau, har ta karasa jikin motar Khalil kallonta yake yi, kallonta kamar yana tunanin "yaushe za ta daina birgeni?"
Wani babban expensive restaurant suka isa, direct VIP suka shiga dan already an gama komai jiran su kawai ake su iso, at this point Azrah ji take kamar duk duniyar Allah ya fi sonta. Ammah ta riƙe hannun Azrah bayan sun zauna tana kallonta da murmushi ta ce
"Sweetheart, ke na daban ce, and it's a blessing to us to have you. I can't wait na hadu da Ummah ki properly. In kin koma gida, in shaa Allah"
Azrah ta kasa amsa. Sai da hawaye suka cika idonta ta ce, "In shaa Allah Ammah. Zan gaya mata" Khalil da Intisar kuma sai kallonta suke suna murmushi. A haka suka gama small party dinsu suka mayar da ita hostel wanda duk sunyi enjoying moment din
A bakin kofar hostel suka yi dropping ɗinta, ta sauka tana murmushi, tare da ɗaga musu hannu, sai kuma ta juya ta shiga hostel ɗin, bayan ta karasa kofar ɗakin taji a kulle, hakan yasa tayi knocking, muryan Samira ta ji ta ce
"Who is it?" Azrah ta ce "Ke, nice fah" Samira ta kalli Sarah da sauri sai kuma duk suka miƙe suka nufi kofar, a hankali Samira ta buɗe kofar kuma still tana rike da shi iya kanta kawai ta sa a wajen tana kallon Azrah ta ce
"Hey you! Ki rufe idon ki" Azrah ta girgiza kai ta ce
"Please bana son wani abu wai shi surprise" muryan Sarah ta ji
"Then, ki koma inda kika fito" duk suka yi dariya
Da sauri Samira ta rufe mata ido lokaci guda wanda yazo ma Azrahn ba zata, sannan Sarah ta buɗe musu kofar da kyau, Samira kuma ta jata ciki, sannan ta daga hannunta daga fuskar Azrahn
A kan gado Azrah ta ga wani beautiful photo album, cikinsa cike da hoton ta na graduation, hotunan su da lecturers da su Sarah da Khalil duk dai, sai dai nasu Ammah ne babu. Sai kuma wani babban flower bouquet
Samira da Sarah suka hada baki wajen cewa 'Suprised"
Sai kuma Samira ta ce, "We just wanted you to always remember how far you've come"
Azrah ta rungume su tana hawaye ta ce
"Ban san me zan ce ba... But I love you so much"
Cire kayan jikinta tayi ta wuce toilet ta wasa ruwa sannan ta fito ta saka simple lounge wear, wide black palazzo da white cotton shirt, ta ɗaura vintage akanta, ba karamin kyau tayi ba, kamar tasan Khalil zai zo kawai sai ga kiran sa yace ta fito yana bakin hostel, mamaki tayi wato yana kai su Ammah ya sake jiyo wa kenan?
Tana fitowa a hostel ta ganshi zaune a cool down ɗin, dariya tayi ta ce "hostel dinmu ma ya gama sanin fuskanka" kwaɓe fuska kawai yayi, zama tayi a gefensa tana Kallonsa kamar yadda shima yake kallonta tana son jin meya kawo sa kuma? Sai wayanta yayi karan alamun shigowan message,
Unlocking passcode ɗin tayi, tana kallon 'mobile photographer mai suna @NaijaCampusStars ya tura mata DM yana cewa
'Hi brilliant, we saw your story at convocation. Nigeria is proud! Would you grant a short interview for our blog? We'd like to feature you as 'Nigerian Asset in India' Will you be available today?"
Da mamaki take karanta sakon, ganin mamakin fuskanta yasa Khalil ya ce "Lafiya My shay?" Miƙa masa wayan tayi ya kalla, karɓa yayi bayan ya karanta kawai ya rungume ta, da sauri ta miƙe tana masa wani kallo, tsosa kansa yayi yana murmushi ya ce
"Go on, I know you will inspire many" ta zauna gefen sa making sure ta bar distance sosai, ta amsa."Let's do it"
Miƙewa tsaye yayi, ta ɗaga kai tana Kallonsa ya ɗaga mata gira ɗaya ya ce "Yes, tashi mu tafi, baki da wani time idan ba yau ba, suma yau suke so" kauda kanta gefe tayi, ita har ga Allah yau ta gaji amma bata son masa musu, kuma kamar a nan schl ɗin za'a mata, hakan yasa ta miƙe a hankali
A Interview Location, sun haɗu da manema labarai a wani conference room Mai kyau a cikin Facultyn su, haske camera sun haskaka fuskarta, suna ɗauke da hotuna da videos. Reporter ya fara tambayoyi cikin English amma Azrah ta amsa da mix na Hindi da Ingilishi
Reporter ya ce "Azrah, you've graduated top of your class. How does it feel to make Nigeria proud from far away?"
Azrah ta ce "Alhamdulillah. It's not just my pride, it's our pride, students from home and abroad. Ina fatan wannan zai ƙara matsayin mata da suke neman ilimi"
A tsanaki ta bada labari, daga lokacin shiga first year, ƙalubale, har zuwa idan aka sake timetable bata rintsawa ko da kuwa wata ɗaya gaba za'a fara exams ɗin. A karshe, ta ce
"My message to everyone out there: When you hold purpose, no distance, no struggle can stop you"
Ba karamin daɗi suka ji ba, bayan sun gama mata suka yi musu godiya, Khalil yace musu ko da kuwa zasu yi posting ne kada suyi tagging acc ɗinta. Nan take kuwa aka fara comments akan glimpse post da suka daura akan su jira full episode tonight .
A hostel, Samira da Sarah suna zaune suna kallon feed ɗin phone ɗinsu suna ta 'wow!'.
Washegari da safe Azrah bata yarda ta koma bacci ba duk da gajjiyar dake tattare da ita, wanka tayi ta fito ta shirya cikin palazzo dinta, sannan ta fita ta je scholarship board unit, tana shiga ta gaishe su, suka taya ta murna da fata samun babban rabo, Suka duba Clearance Form, suka yi lissafin ajin ta, ta sa hannu sannan kuma aka ba ta Graduation Clearance, ta karɓa tana musu godiya
Daga nan ta nufi department office, don farewell da HOD, project supervisor, lectures, staff, kowa cike da sakin fuska yake amsa mata gaisuwan sannan suna taya ta murna
"Congratulations, Azrah! Allah ya sa mu sake haduwa a manyan matakai!" Project supervisor ɗinta ya faɗa dan lokacin sun saba sosai, dariya ta masa, ya ce
"Okay, ba zaki ce Amin ba ko? Then, ki dawo masters kawai bamu gaji da kallon ki ba" gyaɗa masa kai kawai tayi.
Ta shiga hostel da yamma, bayan ta dawo daga wajen Khalil, ta samu travel documents ɗinta a hannu Samira, ga bag ɗin kayanta, duk a shirye. Murmushi tayi dan tasan ta wanna ɓangaren Samira ce ke gyara musu
Haka daren ranan suka cigaba da gyaran kayansu, duk gifts da awards ɗinta ta saka a wani babban schl bag Sannan ta rufe sa
Washegari da Asuba, wani irin sanyin asuba ya lullube su. Tun da suka farka karfe huɗu, wanka kowacce su tayi sannan suka sa kaya kafin lokaci an fara kiran asuba, suka gabatar. Duk zuciyarsu cike take da farin ciki da alhini, yau ne ranar komawansu gida. Samira ce ta shigo ɗakin bayan ta mayar da komai Hostel unit harda key ɗinsu sannan ta dawo, samun Azrah tayi tana saka takalmin ta, Azrah ta miƙe tana tura trolley bag dinta, banda wanda kuma ta goya a baya, Samira na bayanta da nata kaya, fuskar kowaccensu dauke da murmushi mai ban kwana cike da kuma jin kewar wajen tun kafin su tafi
A waje, Khalil yana tsaye kusa da motarsa yana jiransu. Yana sanye cikin simple white shirt da dark blue jeans, idonsa yana bin kofar hostel kamar zai hango su kafin su fito. Da suka fito, murmushi ya sakarwa Azrah har suka karasa wajen sannan ya karɓe akwatin, cike da zolaya ya ce
"Toh 'yan gida, sai wani mura kuke irin zaku koma gida ko?"
Azrah ta watsa masa hararan wasa, Samira ce ta gaishe sa, daga haka duk suka shiga motar. A hanyan su ta tafiya airport Khalil sai tsokanarsu yake yi, yana musu dariya, amma duk da haka fuskar sa na nuna rashin daɗi na rabuwa da Azrah da zai yi, har shi kansa a yau zai bar India zai koma gida dan already su Ammah sun tafi, amma nasa jirgin sai yamma ne. Karar shigowar message Azrah taji a wayanta, buɗe wa tayi taga daga Sarah ne ta turo mata 'safe flight mssg' wanda kuma itama ta ce in the next 30 mins zasu tashi
At the Airport , Final Handover
Da suka isa airport, aka fara yin final clearing. Khalil ya riƙe passport ɗinsu yana musu checking ɗin komai, boarding pass, luggage tag, ID, har ya tabbatar da komai lafiya sannan ya danka musu
Azrah ta kalli agogo, zuciyarta tana raurawa. Sai ta kalli Khalil ta ce
"Thank you for everything. I mean… for all"
Khalil ya ce "Karki ce min thank you Azrah. You've earned all of it. And more's coming"
Gift bag Khalil ya miƙa mata, ta girgiza masa kai, ya haɗe ransa sannan ya damka mata, Azrah ta bude bag ɗin
- Wani letter envelope mai shining For your future plans, ya rubuta a ciki.
- Notebook like diary but designer
- Wata wristwatch mai kyau
Cire envelope ɗin tayi taga 'Dear Queen, this is not good-bye. It's see you soon. I'm proud of you, and I'm ready to build tomorrow with you"
Idanunta sun cika da hawaye. Ta rungume shi ba tare data san tayi hakan ba ma, zuciyarta ta cika da godiya.
Samira ta ƙarasa wajen su, tana kallon su da dariya ta ce
''It's okay lovebirds. Khalil please, don't make us miss our flight fa!'' a daburce Azrah ta zare jikinta daga nasa tana tsinna kai, kawai tayi gaba
Khalil na kallon su har suka wuce security check, ya dan daga musu hannu da murmushin da ya cika da ƙauna da alfaharinta, ji yake kawai a daura auren a Nigeria shi kuma kawai ya wuce da ita Egypt a yau din .
Suna zaune a cikin jirgin international flight, Azrah ta kunna wayarta na dan lokaci kafin take-off. Duk da cewa wayan nata na flight mode ne, so take taga ko Kuma tayi replying ɗina back, ganin bata ga wani sako daga Umma ba har zata sauka sai kuma ta ɗanyi scrolling nan taga wani sabon DM daga wani renowned Nigerian author/journalist mai suna Mr. Abdul-Majeed Bello, wanda ya tura mata message kamar haka
"Saw your story from India. Interested in a national youth-focused feature. Could we arrange an interview when you're settled?"
Shiru tayi tana tunani dama tafiyar ba ta kare ba kenan?Sai kawai ta rubuta masa reply
"Will be honored. I'm landing Nigeria today. Let's stay in touch"
Daga haka ta kashe wayar gaba ki ɗaya.
Bayan jirgin ya sauka Abuja International Airport da yamma. Fuskarsu cike da annuri, iskan Nigeria ta bugi fuskokinsu Samira ta ce:
"Azrah kina jin wannan ƙamshin ƙasan daban ko? Gida ne... finally" dariya Azrah tayi ta ce
"Finally fah"
Bayan sun sauka, aka sake Immigration clearing, aka amshi kayan su, aka karɓi jakunkunan su, komai lafiya.
Bayan hutawa kaɗan a airport lounge, suka shiga local flight zuwa Katsina. Duk da gajiyar tafiya, Azrah na ta kallon window tana ta kallon garuruwan ji take kamar ta ganta kawai yanzu a jikin Umma
Fitowar su daga jirgi a Katsina Airport duk a gajiye suke, gajiyar tafiya tun daga India zuwa Abuja ga kuma daga Abuja zuwa nan, amma Azrah na jin wani irin dadi a zuciyarta kaman mafarki ne. Samira na gabanta, suna tafiya tare da trolley bags ɗinsu yayin da
Basu dade ba, sai suka hangi wani farin Toyota Matrix a bakin parking lot. Driver ɗin su Samira ya fito cikin fara'a yana amsar kayan su da gaisuwa, sannan suka zuba a booth. Azrah ta gaishe sa, duk shiga motar suka yi
Daga haka suka kama hanyar gida. Tafiyar kamar na 40 minutes ne, amma zuciyar Azrah na bugawa da anticipation. Ta rasa wane fuska zata fara gani, Umma ne, Zahra ko Bappah, ji take kamar zata yi hawaye sai yanzu ta tabbatar ashe ba karamin missing dinsu tayi ba
Ganin motar ta shigo unguwar, yaran unguwa kamar sun san ita ce zata sauka, suka fara gudu suna dariya da ihu
"Anty Azrah ta dawo! Anty Azrah ta dawo daga india!"
Wasu har suna kokarin bude mata kofa kafin driver ya tsaya. Bayan drivern yayi parking yaran suka fara kwasar jaka, trolley da leda suna yi mata kallon admiring , sai uban gaisuwa da suke mata wanda baya karewa, har lokacin bata gama sauka ba, sai taga Zahra ta fito da gudu daga cikin gida
"Yaaayyy Sisterrrrrr!!"
Bata tsaya ba, ta rufo Azrah da wani irin gudu ta rungumeta kamar zasu faɗi kasa. Duk da hand bag ɗin a hannunta da wayan ta, Azrah ta sake su ta rungume ta da karfi
Azrah tana murmushi cikin hawaye ta ce "Zahraaa... kin girma har haka?"
Zahra ta ce "Toh ke kin Kalle ki ne? Ni kam kamar bake bace kawai dai kaman kine bai tafi ba... Ke jiya Umma ko bacci bata iya ba "
Samira ta sauko ta ce
"Eh Lallai Zahra, Azrah kawai kika sani ko?" Zahra ta sake Azarha ta juya tana kallon Samira ta ce "Laaa yi hakuri Ya Samira, idan ba, ban ganki bane" dariya tayi daga haka ta rungume ta suka Gaisa, Samira ta ɗaga musu hannu ta koma motar
Suna dariya suka shiga cikin gidan yaran kuwa sun zuba mata Idanu haka suka bita a baya
Kafin ta kalli kowa, straight to Umma's room Azrah ta nufa, tana ɗaga labulen ƙofar, sai taji ƙamshi na turaren Umman ya buga hanci ta
Umma dake tasbihi Azrah ta tafi kanta da gudu ta faɗa tana dariya ta ce
"Ummaaa... na dawo Umma..."
Umma ta mike tana kamo ta da hannu biyu, suka rungume juna cikin kukan farin ciki. Babu wanda ya iya magana na wasu seconds, sai hawaye da murmushi da suke yi
Umma ta ce "Kin dawo lafiya?, 'yar Albarkan Ummanta kin cika mana burukanmu, Allah baki aikin yi yarinyar nan"
Azrah dake murmushi ta ce "Da addu'arki Umma na cinma burin. Kuma ba zan fasa neman yardarki ba har abada"
Zahra ta tsaya gefe tana kallonsu da murmushin ita ma. Sannan Umma ta share hawayenta ta ce
"Yanzu dai ki huta, nasan kina bukatar hutun"
Yaran unguwar kuwa sai shiga suke dakin suna
"Anty Azrah sannu da zuwa! Anty Azrah sannu da zuwa!"
Gidan ya cika da annashuwa. Har maƙwabta suka fara ‘shigowa gaishe da ita.
#Jiddatulkhayr
08110615256
Episode 56: Homecoming
Umma da Zahra suna zaune suna ta hirarsu, Azrah ta fito daga ɗaki ta wuce zuwa compound ɗin gidan dan yin alwala, Umma ta bita da kallo sai kuma ta kalli Zahra ta ce
"Nikam baki ga yadda Azrah ta canza ba?" Zahra tayi dariya ta ce
"Wlh Umma Nima naga ta kara girma sosai kamar ba ita ba".
Azrah ta shiga ɗakinta tayi sallar la'asar cikin nutsuwa. Tana idarwa ta kwanta cinyar Umma. A lokacin ne ta fara jin gajiya sosai bayan dogon tafiya, nan da nan kuwa bacci mai daɗi ya ɗauke ta
An fara kiraye kirayen Magrib ta farka. Ta miƙe zaune tana murza idanunta wanda yake cike da bacci, mamakin yadda tayi bacci a cinyar Umman tayi, ta juya ta kalli Zahra na kwance kan darduma tana kallon hotunanta na a wayanta data buɗe mata kafin tayi bacci, yayin da Umma tana ƙara bin ta da kallo cike da farin ciki ganin yarda 'yar nata ta girma
Azrah ta ɗan yamutsa fuska da wasa, ta ce
"Toh! Gaskiya yanzu zaki fara gani da idon k, bari na baku album gift da aka bani nan zaki fi gani…"
Ta mike, ta nufi wajen akwatin ta wanda ke cikin ɗakin su. Babban jakkan da Samira ta tara mata gifts a cikin ta ɗauka, komawa ɗakin Umman tayi, ta zauna zata buɗe jakkar, Umma ta miƙe ta ce
"Mu je muyi sallah kafin nan" daga haka suka wuce zuwa ɗauro alwala wanda gidan shiru dan babu Mama balle Yaranta
Bayan sun idar Azrah ta buɗe jakkan tana kallon Umma ta ce
"Ga certificate ɗina nan first class, da awards ɗin nan... Best in CGPA, Best Student of the Year…" ta miƙawa Umma Zahra ta sake baki tana ware idanu
Ta mika musu Result ɗinta. Umma ta karɓa tana murmushi, tana kallon certificate ɗin tana hawaye. Zahra kuwa ta miƙa hannu tana kwasar envelopes ɗin tana karanta sunan Yayarta da ke ji kin.
Umma ta ce "Allah Sarki… Azrah kin cika mana burinmu, Allah ya yasa ki samu aiki, ya baki miji na gari" Azrah sai murmushi take ta gagara cewa komai
Zahra ta ce "Antyyyy… ke ce fa Most Talented kuma! Harda Best Student? A wata kasa? Kai Allah mun gode maka"
Suka yi dariya gaba ɗayansu, sai Azrah ta ce
"Zaki iya fiye da hakan ma Zahra"
Ta juya ta fito da wani ƙaramar bag wanda Intisar ta bata. A ciki akwai gift packs da gold jewelry da ta bata a wajen small party da suka yi, sai kayan da Ammah ta mata wanda ta raba wa colleagues ɗinta mugs da hotonta a jiki, memo pads, cards, sannan wasu envelopes na kuɗi daga wasu VIPs da suka ji labarinta. Daga Umma har Zahra buɗe baki suka yi dan suma sun gagara magana
Ta jawo wayarta, ta bude banking app ɗinta, ta nuna musu alert na credit transfer
Ta ce "Wannan kuwa… kuɗin governor of New Delhi ne. Check ya bani shine tun acan aka mayar min acc din, Nace sai na dawo gida zan muku bayani"
Zahra ta rufe baki ta ce "Kiiiiiiiii... Allah ya ga wahalar mu, Shikenan yanzu munbar talauci knn! Gobe gobe kuma sai ki sayi mota ki bani ki ce nice driver"
Azrah ta harareta ta ce "Shikenan sai kawai na tsiya mota? Sannu Zahra" dariya Zahra tayi
Umma na murmushi mai hawaye ta ce "Wannan kenan Azrah. Wannan ba kawai ilimi bane, soyayyar Allah ce. Allah ya dube wahalar ki shiyasa ya mayar miki cikin ruwan sanyi"
Azrah ta ce "Na san babu inda zani sai da yardarku. Wallahi duk inda na kai, addu'ar ku ce"
A haka suka ci gaba da hira, suna duban gifts ɗinta, certificates da hotuna. Zahra ta ɗauki gift mug daya ta ce
"Wannan mug ɗin kuwa tuni zan fara amfani da shi. Yau dai ga cup ɗin 'yan gayu da hoton Yayata, ni zanna shan koko dashi kullum"
Banda farin ciki babu abin da suke ciki, har ba zasu iya misaltawa ba, Umma da Zahra na jin kamar suna mafarki da yadda Azrah ta dawo ba kawai da certificate ba, amma da wani irin nasara da ba'a iya auna ta. Kuma har a zahiri, sun gane Azrah ta canza ta girma, ta natsu, ta ƙara haske da wayewa.
Jin karan shigowar su Mama da Yaranta yasa Umma ta kalleta cikin murmushi ta ce
"Azrah tashi kije ki nuna wa Mama dan kar Bappah'n ku ya dawo tace ai bata san da zuwan ki ba irin na wancan lokacin''
Azrah ta gyada kai, duk da bata ji wani murnan zuwa ba, tayi murmushin dole, ta miƙe, ta ɗauki graduation gift packs guda biyu, mug cup guda biyu ɗin da aka buga hotonta da sunanta, da kuma memo hardcopy ɗin da aka rubuta Congratulations, Azrah Muhammad Class of Excellence Ta daure vintage a kanta sannan ta miƙe tana kallon Umma ta ce
"Ai wannan ɗin sun yi ko?" Umma ta ce "Eh, amma ki dauki harda result dinki mana" Zahra ta kyalkyale da dariya tana tafe hannu ta ce
"Toh me amfanin nuna mata bayan ko sanin muhimmancin sa bata yi ba balle tasan me abin yake nufi" Azrah bata san sanda tayi murmushi ba kawai ta fita..
A sashin Mama, sun cika dakinta da ihu, Mama na zaune gefenta kuma Siyama, Habibah kuma tana gefen Abdul. Hirarsu suke yi amma babu nutsuwa, ana dariya da shewa
Amma da Azrah ta shiga, duk cikin ɗan lokaci suka yi shiru,
duk Idanu suka zuba mata dan yadda canjin da ya bayyana gareta ya tsorata su ba kaɗan ba
Fuskarta ciƙe da fara'a, dressing dinta simple amma classy. Idon Mama ya sauka a kanta tun daga kai har ƙafa, a zuciyarta tace 'Ita ce wannan matsiyaciyar? Sai kace wata ‘yar minister hmm zama bai kamani ba
Azrah ta zauna a kasa tana kallon Mama, sannan ta ce
"Ina wuni Mama"
Mama ta ɗan gyara zama tana ɗauke kai, ta amsa da,
"Uhm. Yauwa"
Siyama ta taɓe baki tana kallon gefen, Habibah kuma kamar ta fi kowa ɓacin rai. dan miƙewa tayi ga bar dakin. Azrah bata kulasu ba. Ta miƙa gift ɗin da murmushi ta ce
"Ga wannan Mama, daga makarantar ce, saboda graduation ɗina, ɗazu na dawo"
Mama ta karɓa ba tare da godiya ba ta ce
"Toh"
Shiru ya biyo bayan hakan. Azrah ta miƙe cike da nutsuwa, ta kalli Mama ta ce
"Zan tafi Mama, sai anjima"
"Toh" inji Mama ba tare da ta kalleta ba.
Ta juya ta fice cikin natsuwa ta saka a ranta like wannan normal ne a wajenta dan da sabo ta saba da rashin kirkin Mama
Da ta shiga ɗakin Umma, ta zauna, tana kallon su Zahra da murmushi. Umma ta ce
"Ya kuka yi da ita?"
Azrah ta gyara zama ta ce "Na je Umma, na gaishe ta, na kuma bata gift ɗinta"
Kafin Umma ta ce wani abu, sai suka ji muryar Bappah daga compound ɗin yana magana da wani. Azrah ta miƙe da sauri, zuciyarta cike da farin ciki ta karasa bakin kofar ta daga labule, idanunta suka sauka a kansa, da sauri ta sauka har kasa tana dariya, ta tafi da gudu ta rungume shi ta ce
"Bappah na!"
Bappah ya saki murmushi yana shafa kanta ya ce
"Iyyee… yarinyar Bappah ta girma! Toh yaushe kika iso?"
"Ɗazu ne fah Bappah. Bappah ka zo na nuna maka certificate dina da awards!"
"Toh muje mana. Yar bappah ta gama degree" inji Bappah yana dariya
Suka shiga ciki, Umma da Zahra suna zaune, Zahra ta tamke fuskarta kamar bata san me dariya ba
"Toh yarinyata, nuna min certificate ɗin" cewar Bappah bayan ya zauna
Azrah ta ɗauki jakar certificate dinta, ta fiddo manyan awards, da plaque trophy. Ta miƙa masa certificate ɗin, album da dai komai. Bappah yana karantawa yana girgiza kai cike da alfahari
"First Class? Sai wannan 'yar Baba. Most Decent Student? Best in Business Skill? Haba sai Azrah ɗina!" Ya rungume ta ya manna mata kisa a forehead dinta ya ce
"Allah miki albarka, Allah yasa wannan shine mafarin nasara"
Azrah ta kuma fito masa da wasu kyaututtuka da aka bata, ta jawo wayanta zata nuna masa alert ɗin, Zahra ta mata wani kallo ta fake idon Bappah ta kwashe wayan ta ce
"Bappah kuma an bata kyautar 10 Million" Azrah ta dinga kallon Zahra ganin ta rage wajen 30 mil a kuɗin
Bappah ya kasa boye mamaki
"Azrah nikam ma bansan me zance ba, harda 10 mil kuma?
Umma ta zuba mata ido tana murmushi ta ce
"Allah Ya saka musu da alheri. Allah Ya kare ki daga idon hassada, mu de mun gode"
Azrah de tagumi tayi ta rasa me zata ce jin Zahra ta rage amount din....
Bappah na fita Azrah ta kalli Zahra tun kafin tayi magana Zahra ta riga ta "Toh so kike a faɗa masa dukkan kuɗi yaje ya faɗawa Matarsa tazo ta samu a gaba ko kuma ya karɓi some amounts yace zata ja jari"
Washegari da safe, bayan sun kammala breakfast, Azrah na zaune gefen Umma tana duba wayarta. Ta juya tana fuskantar Umma da murmushi ta ce
"Umma ai jiya da daddare wani kamfani ya sake turo min sako suna so suyi hira dani. Na ce musu zan je yau"
Umma ta kalleta da ƙwarin gwiwa ta ce
"Toh mana tashi ki shirya. Ai irin wannan dama ba'a watsar da ita ba"
Azrah ta gyada kai, ta miƙe cikin nutsuwa, ta fita compound ta shiga bayi, tayi wanka, ta fito ta wuce ɗakin su, bayan ta gama shafe shafenta tasa wata light brown abaya mai kyau. Tayi kwalliya light, sannan ta ɗauki jakarta da mayafinta. Ta wuce zuwa ɗakin Umma tana kallon ta ta ce
"Umma sai na dawo"
"Allah Ya kiyaye hanya" inji Umma tana kallonta da kulawa.
Tun data fita daga gida 'yan layinsu, duk wanda ta hadu da shi sai ya gaishe ta Manya da yara har hakan yaso ya fara bata kunya, kowa da abin da yake faɗi
"Yarinyar Bappah kin dawo lfy?"
"Masha Allah, muna taya ki murna"
"Wannan ce 'yar India din nan ko?" Irin maganar da ake ta yi kenan
A haka har ta isa event center ɗin da ake shirin yin interview ɗin. Kamfanin "SheLeads Africa" ne suka gayyace ta. Bayan an kammala shiri, aka fara gabatar da ita ga jama,'a.
Tambayoyin da suka mata sun haɗa da
1. "Za mu so ki faɗa mana, me ya ja hankalin ki zuwa business administration?"
Azrah ta ce "Tun tasowa ta na taso ne cikin sana'o'i wanda a lokacin Umma na kanyi min faɗa dana bari amma kuma ban hakura ba, sannan duk abin dana saka a gaba idan har na sana'ace ina samun cigaba, shiyasa naji kawai na karanci course ɗin dan aiki a Manyan companies"
2. "Wane challenges kika fuskanta a wajen karatu da kuma yanda kika shawo kansu?"
"Rashin sanin yare da sabon yanayi ya sha banban, amma da addu'a da support daga gida da friends na, na tsallake komai"
3. "Me zaki iya cewa matasa musamman mata masu burin yin karatu a waje?"
"Su daure, su kasance da kyakkyawan niyya da tsari. Kuma su kasance masu kima da mutunci, domin shine darajar su, ba wai suje da niyyar sharholiya ba"
4. "Me kike shirin yi yanzu da kika dawo gida?"
"A halin yanzu, ina shirin fara NYSC da kuma kafa small business da ya shafi skin care products ne"
Anan aka rufe interview ɗin da kyaututtuka, aka bata branded gift box, certificate of appearance, da wata brown envelope. Tayi godiya sosai sannan ta fito da murmushi a fuska.
Yana zaune a Babban Office ɗinsa, yana kallon TVCnews da suke hasko ta a masayi live video, ganin kamar yasan fuskar sai kuma ya dauki wayar sa ya shiga IG nan ya dinga kallon post din da aka dinga yi akanta, ba shiri yabi ya duba history dinta kamar yadda aka bayar, abin daya fi connecting da heart ɗinsa shine ganin yadda aka bata awards na best a bangaren business skills lumshe idonsa yayi yana nazari sai kuma ya miƙe zaune yayi dialing wani number....
Azrah ta fito a wajen tana kokarin tsayar da keke-Napep kenan, sai ga wayar Samira ya shigo
"Hello Samira!" ta faɗa bayan tayi receiving call ɗin
Samira ta ce "Baby Girl! Kin ji labari kuwa? NYSC portal an buɗe fah yanzu yanzu!"
Azrah ta ce da mamaki
"Serious? Toh ai tunda har na fita, zan tsaya a café yanzu kawai in cika komai, kafin na koma gida"
Suna dariya suka yi sallama.
Azrah ta karasa wani café, ta shiga, shiga tayi da sallama bayan sun amsa tace zato registration ne na service, ai kuwa cikin sauri suka taimaka mata aka yi mata registration, aka duba requirements, aka shirya, sannan aka tura. Tayi godiya ta fito da murmushi a fuskarta
Ta ɗauki hanya zuwa gida, zuciyarta cike da natsuwa da kwanciyar hankali, tana tunanin yanda komai ke sauka a bisa hanya. ..
Bayan kwana biyu da dawowar Azrah gida, gidan ya sake samun ɗan sauyi. Wata rana da safe, aka ji karar horn a kofar gida. Sai ga Dada. Duk suka fita da murna don tarbar ta.
Zahra da Azrah suka fi nuna excitement, akan su Habibah da Siyama, suka shiga mata da jakunkunanta, suna mamakin bazatan zuwa da tayi.
Bayan kwana biyu da zuwan Dada, wata rana tana zaune da Bappah a dakin sa, ta kallesa cike da damuwa tace
"Ɗan nan, gaskiya wannan lokacin ne daya dace, ya kamata kowa daga cikin yaran nan su fito da wanda suke so idan suna da shi, a samu a aurar da su"
Bappah ya gyara zamansa yana nazari, sai ya ce
"Ai wlhi Dada wannan abin kullum na cikin raina. Wani lokacin idan na kalle su, ina ganin yanzu ne lokacin da ya dace ace sun fara barin gida" a haka dai Dadda da Bappah suka yake hukunci.
Washegari da rana, Bappah ya tara duka 'ya'yansa harda Dada dake gefe ga Mama ma data zauna wai tana jiran saƙo ne, a filin gidan. Yana kallon su cikin natsuwa ya ce
"Na kira ku ne dan muyi magana mai muhimmanci. Lokaci ya yi da kowannen ku ya kamata ta fito da wanda take so na aurar da ku nima na huta"
#Jiddatulkhayr
08110615256
Episode 57: Between Pride and Destiny
Caraf Mama ta saka baki yanda kansa da ita ake magana, dama da gayya zamanta a sakar gidan, tana murmushim Mugunta ta ce da Bappah
"Ai gaskiya kuwa kayi tunani akan yaran nan dan Nima kullum zuciyata tsinkewa yake idan na gansu har su huɗu" Bappah ya gyaɗa kai irin gamsuwa da magananta Dada dai ko da wasa bata kalli direction ɗinta ba Mama ta cigaba
"Yanzu, musamman yarinyar nan Azrah idan baka sa ta fito da miji ba cikin gaggawa ba toh akwai mugun matsala, dan yanzu haka samarukan ma sun fara tsoronta dan gani ake yadda jikinta ya buɗe kamar wata matar aure ga kuma zaman kanta da tayi a uwa duniya na wajen shekaru huɗu zuwa biyar kawai ka lallaɓa koma da waye ka turata kawai"
"Ya ishe ki Uwani! A gaban idona kike wa jikata irin wannan mummunar lazafin da siffanta mata waɗannan maganganun? Uban waya ce ke ki gantalar da rayuwar yaran naki? Ita Habibah da Siyama basu girmeta bane?" Dada tayi maganar cikin tsawa kuma kana ji kasan ranta a mugun ɓace yake
Mama tayi saurin cewa 'Kiyi hakuri Dada, wai dan naga yanzu tafi kowa girman jiki ne a gidan da tsayi shiyasa na faɗi hakan"
Dada ta ce "Uban girman jikin, yaran naki da suke zuwa titi kamar 'yan tasha su zasu fara fito da miji yanzu, Azrah kuma naga uban da zai sake ce ta fito da miji idan ba yin kanta ta kawo mijin ba, Service ma zata tafi dan haka kar na kara jin wani ya mata maganar miji" Dada ta kare maganar tana huci
Duk sun yi mamakin yadda Dada ta ɗan tsawata mata, Mama kam ta kura mata ido tana hararanta kasa kasa amma ta kasa cewa uffan kuma. Fuskar ta cike da haushi, amma bata da daman tankawa
Azrah kuwa murmushi take yi, tana mamakin yadda Mama ta mugun tsanarta, ita dai ko yau ta ce wa Khalil ana neman sa tasan tabbas zai zo da gudu ma, dan yanzun ma ba karamin damunta yake ba
Zahra kuwa sai humming take yi da ƙarfi tana haɗe gira tana hararan Siyama da Habibah wanda da farko har sun fara murna sai dai yanzu kuma sunyi tsit
Bappah ya kalli duka 'ya'yan sa da Mama sannan ya ce
"Ni dai na ce kowacce idan tana da wanda yake zuwa wajenta ko ta ke so, sai ta ce. Idan kuma babu, sai mu soma bin hanyar da ta dace. Amma ba auren dole a gida na"
Yana kai wa nan, ya miƙe daga kujera ya shige cikin ɗakin sa yana barin su da mamakin yanda Dada ta mayar da lamarin daidai musamman ga Azrah
Azrah suna haɗa ido da Mama ta Banka mata wani irin kallon tsana, A zuciyarta kuwa, sai ta ji wata nasara domin tasan kalaman Mama ba wai damunta zai yi ba, bane illa kishi da mugun nufi. Amma shiru ya fi akan tayi wani reacting
Mama ta miƙe daga inda take zaune kamar wadda aka cin zarafi, fuska cike da fushi da ƙyashi. Ba tare da ta yarda ta kalli Dada, ko su Azrah ba, ta nufi ɗakinta kamar wanda zata tashi sama. 'Ya'yanta kuwa kamar jira suke, suka bi bayanta, kowacce cikin ranta tana nazarin abinda Bappah ya faɗa ne
Azrah da Zahrah suka tsaya na ɗan lokaci, suna kallon juna da wani irin kunci da takaici da ke cike da zuciyarsu. A ƙarshe, suka miƙe jiki a sanyaye, suka shiga ciki, Dada na bin su a baya da tausayinsu da yake ratsawa cikin zuciyarta
Sun so su zauna su taɗa wa Umma labarin komai, amma ganin Dada na kusa yasa suka hakura, suka shige ɗakinsu, bayan su zauna, Zahrah ta furta tana girgiza kai
“Ji wannan matar fa… Ana maganar aure, zata wani ce ke ki fito da miji, kamar bata san cewar yaran nata sun girmeki ba, idan banda mugunta me ma na kiran sunanki, kila tana tunanin ke baki da shi ne, saboda ace za'a miki auren dole" tana kare maganar taja tsaki
Azrah tayi wani irin murmushi, da wayewar tunani ta ce cikin nutsuwa
"Ko a jiki na. Na faɗa miki ita ya dama. A tunaninta ta sha wahala ne dole mu ma mu sha. Amma zata yi mamaki da mijin da zamu aura In Shaa Allah, idan kuwa fatan tsiya ne ya kare kan nata yaran"
Zahrah ta zaro ido tana kallon Azrah da wani irin mamaki baki buɗe ta ce
"Wai ke ce da confidence haka? Wannan ba Azrah da muka sani ba ce ne gaskiya...."
Azrah ta ƙara murmushi ta ce
"Nima ban san yaushe na canza ba… Amma I guess India ta gyara ni tun tuni"
Zahra ta ce da dariya
"Alhamdulillah. Ni haka nake son ganinki dama, mai juriya, mai kwatan 'yancinta mai kwarin gwiwa, ba Azrah mai jin kunya da shakkar komai ba"
Dariya suka yi gaba ɗaya kafin kowacce ta kwanta cikin tunani....
Washe gari da safe, Azrah na zaune gefen katifarta tana shiryawa, sai taji wayarta ta yi kara, Message Received ta duba. Call-up number! NYSC! Hannunta na rawa ciƙe da murna da fargaba ta buɗe saƙon
"Dear Corps Member, you have been posted to: Nasarawa State Orientation Camp..."
Cikin hanzari ta fito tana kwalawa Umma kira,
"Umma! Dada! An yi posting ɗina!''
Umma ta miƙe da sauri ta ce
"Subhanallah! Ina suka turo ki?"
"Nasarawa State!" Azrah ta amsa tana dariya. Umma tayi dariya har da hawayen farin ciki
"Allah Sarki... Allah ya kaimu lafiya Azrah. Wannan shi ne mafarkin ki!"
Dada ta kalli Azrah, ta dafa kafaɗarta "Allah dai ya baki aikin yi Azrah"
Da yamma, suna cikin hirar su Azrah tana bawa Dada labari yadda India ta canza rayuwarta daga rayuwar karatu, al'adu, zuwa yadda ta rika sawa kanta damuwa ganin kamar ba zata iya gamawa ba da farko, wannan tsorata da tayi ne yasa ta dage ashe ya taimaka mata
Dada ta ce "Tabbas ai kin bamu Mamaki, nace ashe dai jikar yawa ba daga nan ba. Ko da yake ai ilimin Muhammadu kuka ɗauko dan shima haka yake tun yana karami" Zahra ta wani kalle Dada ta ce
"A'a dai ilimin Umman mu dai, ba wani Bappah, idan Bappah ne mayasa su Siyama kan su ƙwanƙone" Dada ta sake baki tana kallon ta, Azrah ta fara dariya dan ba kaɗan ba reaction ɗin Zahra ya bata dariya, Dada ta yi ƙwafa ta ce
"Nace miki haka ilimin Bappah'n ku kuka ɗauko, yanzu anan wake maganar wasu Siyama ko wa? Naga ai wannan basu da saiti dan kan Mamarsu suka ɗauko amma ba na Bappah ba" Zahra ta fashe da dariya ta ce
"Ashe kema kin gane, ai wannan yaran babu abin da suka baro na Uwarsu"
"Assalamu Alaikum!" Sallamar da aka yi ne yasa suka yi shiru
Zahrah ta miƙe ta leka dan ganin wanene, sake baki tayi ta "Laaa Ya Samira ce!"
Azrah ta miƙe da sauri cikin farin ciki. Samira ta shigo cikin annashuwa ta gaishe da su Dada, da Umma, kafin Azrah ta ja ta zuwa ɗakinsu.
"Look what I brought for you! Tunda kin ki maganar" Ta ɗauko ashoben bikinta tana miƙa mata
Azrah tayi dariya ta ce "Kinsan ko Jiya sai dana yi tunanin hakan, sai kuma nace Maybe toh kowa zai sa Abaya ai"
"Ni kuwa babban kawa nake so ki kasance Azrah! Means zaki dawo gidan mu ana saura 3 to 4 days Dan muyi komai tare" Ta ce tana murmushi.
Azrah ta ɗauki kayan, tana kallon su da murmushi. "Wow! Samira... wannan sosai ya yi kyau daɗi na dake akwai iya zaɓan abu"
"Saura two weeks fa! Ki gaggauta kai dinki. Zamu yi events kala uku ne, Bridal shower, Pajamas night at the hotel, sai Dinner. Komai classic nake so ya kasance sannan ya tafi viral"
Azrah ta ɗan yi murmushi, amma dai tayi shiru, ita hotel da Samira ta ambata ne ya tsaya mata a rai, tana kallon Samira ta ce
"Na sanki ba zaki yi abin raini ba, but Pajamas night a hotel?"
Samira na Murmushi ta ce "Yep ana ne friends ɗina maza ma zasu samu suyi attending, tunda Kinga bridal shower Deen zai iya cewa zai zo Maybe dan hoto"
Azrah ta ce "Kuma Pajamas wear zamu yi ko? A hakan zamu haɗu da Male friends ɗin naki kenan ko?"
Samira ta ɓata rai ta ce "Ni fah matsala ta da ke kenan Azrah, gaki a zahiri kamar wayayya amma inaaa ko kaɗan baki waye ba, abu kaɗan kice Maza" Azrahn tayi murmushi ta ce
"A'a ba haka bane, amma ina jiye miki ne, like mijin ki ba zai ce komai ba? Wani kallo Samira ta mata ta ce
"Dan bashi da hankali sai yace wani abu? Eh lallai ma" Azrah tayi shiru bata ce komai ba, Samira ta ce
"Ni fah da gaske farkon gani na dake dana ga kina sa su palazzo da veil idan ba na ɗauka a mugun waye kike ba ashe ba haka bane, kawai yadda kike dressing ne"
Azrah tayi murmushi ta ce "Haka mutane ke cewa fah, toh mu de yadda muka taso muka samu Umman mu ke dressing kenan" Samira ta ce
"Ba wannan ba, Zaki zo ɗin ina?"
Azrah ta ɗan haɗiye yawu ta ce "Hmm... Zamu gani. In na samu dama, sai na shigo ranan pajamas ɗin" Wani harara Samira ta mata ta ce
"Ke sai fa kin zo, Nama gaya miki"
Suka ɗan yi hira, sai Samira ta miƙe, Azrah ta raka ta har bakin ƙofar gidan, Mama dake zaune da wata makwabciyar su, ta bita da kallon banza, su kuwa dariya suke basu ma lura da ita ba har ta fice sannan ta juyo, Mama ta miƙe tsaye ta ce
"Dan Uwarki saboda bamu kai ki Gaishe mu ke da 'yar iskar kawar naki bane shine zaku wani wuce kamu bamu da daraja a idonku sbd yadda uwarki ta kama ta kimtsa miki wani abu ko?" Azrah na tsaye hatta gama magana sannan ta ce
"Uwata dake ɗaki shine zaki ce ta zuga ni? Toh ai naga bamu ganki bane da mun gaishe ki" Wani ashar Mama ta dukunkuno mata sai ga Dada ta fito tana
"Kai.. kai.. wai meke faruwa ne" kafin Mama tayi magana Azrahn ta ce
"Dan bamu gaishe ta bane kuma wlh Dada bamu ganta bane Shiyasa" Dada ta ce "zo ki shige" bayan Azrahn ta shige Dada ta ce
"Uwani ki rinka rike girman ki, kinga yarinyar nan hakuri gareta amma Kinga yanzu har tafara mayar miki da magana, kar ki bari lokacin da zai zo kina faɗa tana faɗa" daga haka ta wuce ciki ita ma
Azrah ta shiga ɗaki Umma tana murmushi ta iske Umma na gyara zanin gado, sai ta ɗan tsaya gefenta ta karɓe zanin gadon ta ce
"Umma, ga ashoben bikin Samira ashe abin daya kawo ta kenan, tace babban kawa zan mata wai"
Umma ta ɗan ɗaga kai tana kallon Azrah da murmushi ta ce
"Allah ya kaimu bikin lafiya, ya sanya albarka a rayuwar aurensu, ya basu zaman lafiya da zuri'a nagari"
Azrah ta amsa da "Amin" cike da jin daɗin addu'ar mahaifiyarta, ta karasa gyara mata ɗakin sannan ta nufi ɗakin su. Zahrah na zaune tana ta duba wani littafi, Azrah ta zauna kusa da ita.
"Kin san me? Samira tace events uku zata yi bridal shower, pajamas night a hotel, da dinner night, Amma nikam maganan pajamas night ɗinne ya dame Ni kuma wai nice zan mata babban kawa, shine matsalar"
Zahrah ta ɗaga kai da ɗan mamaki ta ce
"Toh meye a ciki? Naga ba ke kadai zaki je ba. Kuma tare da friends ne, mata fa. Ni ban ga wani matsala ba tunda ba wai wani kika bi ba, wedding event kika je"
Azrah tayi dariya tana kallon Zahra ta ce "Hmmm... Nima fa ba zuwan nake tsoro ba. Baki san Samira bane, tana son shagali da social life sosai. Kuma da Maza za'a yi fah"
Zahrah ta ce "Allah ya kyauta dai. Amma wannan pajamas night ɗin banga aibin sa ba, just wear after dress akan wear ɗin ba Shikenan ba?
Azrah ta gyada kai ta ce "Zan je bridal shower kawai, in yayu sai dinner. Sauran sai na bari"
____
Da daddare, bayan kowa ya gama cin abinci, Azrah ta je dakin Bappah da wayanta a hannu ta shiga message da NYSC posting ya shigo mata. Tana ɗan tsoro, amma ta tattara ƙarfin gwiwa, ta mika masa wayar
Bayan sun gaisa ta ce "Bappah, ga inda aka tura Ni"
Bappah ya karɓa, ya karanta, ya ɗan gyara zama. "Nasarawa... Masha Allah. Allah ya tabbatar da alheri, ya sa ki gama lafiya"
Azrah ta saki numfashi dama tsoronta kar Bappah yace zata yi nisa ne, ta ce "Amin Bappah. Na gode sosai
________-
Washe gari da safe, Azrah ta tashi da wuri, ta shirya cikin wani simple blue material, ta saka jilbab ɗinta dogo har kasa, ta fesa turaren, sannan ta kira Zahra
"Zahrah mu tafi kasuwan yanzu bana son shiga da rana ne, gwara na fara shirin tafiya Camp fa tun yanzu ba sai Anjima ba"
Bayan sun ma Umma sallama suka fita, direct kasuwa ta wuce, A can Azrah ta fara siyan kayan da zata buƙata na tafiya camp
Riga da wando farare (white top and joggers), Towel da toiletries, Mosquito net ,Waist pouch, Water bottle, Canvas da socks, Padlock da file folder, Undergarments da white veil
Zahrah tana ɗauka tana ajiyewa cikin bakko, suna dariya suna ta lissafin abubuwan da ya rage.
"Kin san kuwa sai na je da medical report?" Azrah ta ce tana kallon list ɗin
Zahrah ta ce "Medical report kuma? Baki da lafiya ne?" Azrahn tayi dariya ta ce
"Chap, zan tafi da shine ɗan su sake Ni, Yaushe zan zauna inyi missing bikin Samira" Zahra ta ce
"Ohh, Nagane"....
#Jiddatulkhayr
08110615256
Episode 58: A New Beginning in Olive Khaki
Bayan sun dawo gida, ɗakin Umma suka shige, Azrah ta ajiye kayan tana kallon Umma ta ce
"Zan wuce asibiti yanzu, in karɓo medical report da zan tafi da shi, Umma"
Umma ta ce "Medical report kuma Azrah? Name kenan?" Azrah ta ce
"Ai dama ba zan zauna a camp ba Umma, ina shiga zan dawo gida abu na" Umma ta ce
"Toh Allah baki sa'a, sai kin dawo"
Ta ɗauki jakarta, ta sha ruwa sannan ta fita...
A hanya tana tafiya mutanen unguwar nasu ke kallonta da murmushi da girmamawa
"Laa ga 'yar India..." wani dattijo ya faɗa da dariya.
Azrah na murmushi ta gaishe da mutumin, yayi ta saka mata albarka tana gaba kaɗan ma taji wata mata tana cewa
"Kunga ga 'yar gatan ƙasar nan"
Azrah ta murmusa kawai, tana jin sanyi a zuciyarta. 'Yau ni ake kira da 'yar gata... daga Azrah mai wahala ta biya kuɗin karatun ta zuwa Azrah da ake yi wa kallon alfahari'
Tana shiga asibitin unguwarsu, ta tarar da wani ɗan saurayi receptionist, ta shiga ta gaishe sa, ya amsa mata yana washe baki, ta ce
"Ina son medical report sir, zan shiga camp ne kuma gaskiya ina da issues na ɗauke wan numfashi"
"Wow! Congratulations!" Ya ce yana dariya cike da son wasa da ita, ita kuma ganin haka yasa ta ɗan dena murmushi, ya ce
"Zo nan, za mu duba BP da weight ɗin ki, sai ki jira Dr. Farida ta baki final clearance"
Bayan Dr. Farida ta zo, tace tunda na camp ne ta zauna za'a cika mata ba sai an wani gwaje gwaje ba, Azrah ta koma gefe ta zauna tana daddanna wayenta, sai kawai ta ci karo da wata tsohuwar ƙawarta. Suka gaisa cikin jin daɗi kafin suka rabu, can aka kira sunanta
A ƙarshe, ta karɓi medical report ɗinta, an sa mata stamp da signature ta ce
"Na gode sosai. Allah ya kara girma"
Dr Farida na murmushi ta ce "enjoy your camp, baby girl" ta sake godiya
Azrah ta fita daga asibiti cike da farin ciki, zuciyarta na cike da fatan alheri, tana ma kanta addua a zuciyarta
"Ya Allah, ka bani ikon daukan nayin kaina da wanda basu da karfi da kuma iyayena" a haka dai hatta isa gida...
Washe gari da safe bayan sun gama breakfast Azrah ta dauki ashoben da Samira ta kawo mata, fita tayi ta nufi shagon ɗinki dake unguwarsu, bayan ta isa ta shiga da sallama, ganinta yasa ya ce
"Ahh mutanen India kin dawo ashe?" Azrah na murmushi ta ce
"Eh fah, dama ɗinki na kawo maka Ya Adam, amma dan Allah a satin nan nake so, bikin ne zamu yi" ya ce
"Baki da Matsala ai, dole na ajiye ɗinkin kowa na kama na ki" tana murmushi ta miƙa masa kayan ta ce
"Nagode kwarai"
Ta zaɓi ɗinke gown mai kyau wanda ya dace da bikin dinner, sai kuma irin ɗinki daya dace da gown ɗin bridal shower ta ce
"Please ka gama cikin sati ɗaya, akwai tarin events kafin bikinta ne, kar ka min daɗin baki kai ma kasan na sanka" yana dariya ya ce
"Haba ai da ba yanzu bane, ki kwantar da hankalin ki, baki da matsala da Ni Ko kaɗan yanzu" daga haka ta masa godiya ta koma gida...
Da yamma bayan Azrah ta dawo gida a gajiya daga gidan Maman Azizah, tana so ta shiga ɗaki ta huta, amma tana jin cewa akwai wasu abubuwa da har yanzu ba ta gama shiryawa ba
Su Umma, Zahra da Dada suna zaune a tsakar gida suna cin tuwo da miyar kuka. Azrah ta zauna cikinsu sakamakon kira da Umma ta mata akan ta zauna su ci, bayan ta zauna tana ɗan jujjuya cokali ba tare da ta kai baki ba
Zahra ta kalle ta da mamaki.
"Ya Azrah lafiya kika yi shiru haka?"
Azrah ta ɗago kai a hankali tana kallonta ta ce
"Zahra... Wallahi bana jin daɗin yadda kike zaman gida haka. Kina wasting potential ɗinki. Gaskiya ki gwada JAMB, idan baki samu ba ko Nursing school sai ki gwada, sai Allah yasa ki samu admission kamar kowa. Ai naga Ummaru Musa Yar'adua University na kusa, za ki iya zuwa kullum ba sai kin zauna a hostel ba"
Umma ta daɗe tana kallonta, sai ta ce
"Gaskiya ne. Ki sake gwadawa Zahra, ko da ni ban da hali, amma zan yi iya bakin ƙoƙari na, Nima dama bana jin dadin zaman naki"
Azrah ta ce "A'a babu ruwanki anan Umma, wannan a kaina yake, dama ai burin karatu na dan na gama na fara aiki ne dan na cikawa Zahra burinta na zama likita"
Zahra ta ɗan sunkuyar da kai ta ce
"Toh zan yi tunani a kai..." Wani kallo Azrah ta mata
Da Daddare Azraj ta shiga ma Mama sallama, bayan ta shiga dakin da sallama, ta ce
"Mama na shigo ne dan miki sallama zan tafi camp gobe"
Mama tayi banza da ita, ta yi kamar bata ji ba
Azrah ta ɗan yi murmushi mai ciwo sannan ta miƙe ta juya.
Washegari da safe, bayan Azrah ta gama shiryawan, ta fito riƙe da ɗan Jakkanta
Ta je ta rungume Umma ta ce
"Allah ya bar min ke Umma, ki kula da kanki sosai kuma karki manta da min addu'a as usual"
Umma na murmushi tayi kissing forehead dinta
Dada ta ce
"Allah ya kiyaye hanya, ya kare mana ke a can ɗin, kar fah ki kuskura ki sake jiki da mutanen da rabuwa zaku yi, dan baki san cikin su ba" Azrah na murmushi ta gyaɗa mata kai, daga haka ta musu sallama
Zahra ta raka ta har wajen motar. Suka yi sallama cike da ƙauna. daga nan ta wuce tasha, bayan ta siya ticket ta shiga motar tana jiran ya cika
After some hours, motarsu ta isa Lafia, Nasarawa State. Tana sauka, ta goya jakkanta ta fita bakin tashar ta ɗauki keke Napep zuwa wata garage inda ta shiga wata karamar mota mai tafiya wata kauye inda shi zai kai su garin da camp din Lafiya ta ke, tana zuwa ta samu mota kuwa hakan yasa ta shiga dake ƙaramar mota ce harta cika, hakan yasa suka dauki hanyar garin. Ita dai tana cikin motar ne amma gaba ɗaya tunaninta baya nan tayi shiru tana tunanin yadda rayuwar camp ke burgeta, Camp uniform, discipline, early morning drills, Amma Sam taji duk wani excitement ɗin babu, duk taji basu burgeta, Samira ce ke yawo a ranta, taya zata yarda tayi missing bikin Samira guda
A orientation camp, an tarbe dubbun coppers ɗin da tsari. Bayan sun gama duk wani wahala aka nuna musu hostel, tana zaune a hostel ɗin mata tana tuna wahalan da suka sha, registration, ta cika dukkan takardu. Har da kai medical report ɗinta, da abin da aka ce mata wai
"Zaki jira, zamu duba report ɗin" ta rabka uban tagumi gani take ba zasu duba ba, yanzu kenan zata yi missing bikin Samira? Kuma gaskiya bata jin zata iya da duk wani wahalan camp, gaskiya bata jin zata iya bcos at this point jikinta ya saba da Hutu sosai
Washegari ganin har sannan ba'a kirata ba hankalin ta ya sake tashi, musamman data ga first day ɗinta, yadda aka dinga wahala ta sake tsorata
Kawai aka zo aka kira sunanta
"Corper Azrah Muhammad Ibrahim?"
"Yes, Sir!" ta ce zuciyarta na bugawa
"Your medical report states you have an issue that requires attention. You're hereby released temporarily to go sort out your health concerns"
Azrah ta sauke numfashi a zuciyarta ta furta
"Alhamdulillah, how will I start copping here, chap wannan ba Azrahn da bace wanda bata sanin wahala da Hutu"
Da sauri taje ta ɗauki jakkanta ta saka exit letter da clearance, daga nan, tayi sallama da roommates dinta wanda ko kaɗan bata ji su saba ba, fita tayi ta hau mashin ya kaita inda zata samu motar da zai kaita cikin garin Lafiya, ta shiga mota tana murmushi, duk da haka, wani bangare na zuciyarta ya na ce nata
'Hope ba wata matsala da za ta biyo baya ba?'.....
Azrah na sauka daga mota a unguwar su, tun kafin ta shiga gida har mutane suka fara kallon ta da mamaki da gulma, irin ba kowa ke dawowa daga camp cikin kwana ɗaya zuwa biyu ba, amma ita kam tazo. Bata damu da fassarar da mutane zasu yi ba, tunda burinta ɗaya ne ta halarci bikin Samira
Tana shiga gida, Zahra dake shirin ɗaura abincin dare ta nufo ta da mamaki.
"Kar dai har sun barki? Ashe dai medical report ɗin zai yi amfani, but how pls?"
Azrah tana murmushi ta ce "Long story ne Zahra, na gaji Anjima zan fada miki" daga haka ta shige ciki
Da Daddare duk suna zaune a sakar gidan, har da su Umma da Dada. Kowa da tambayoyinsa. Ita kuwa sai dariya take, tana basu amsa cike da sha'awa
"Chap, camp ɗin nan wahala ne, kunga yadda suke wahala? Ni ina zan iya, ai na godewa Allah daya sa yayi daidai da bikin Samira da ba zanyi tunanin kai wata medical report ba, Allah ya so Ni su ma sai suka sake ni da wuri"
Dada ta kalleta da murmushi mai cike da fahimta ta ce
"Toh ai dama tun kina yarinya baki son wahala daga baya har mamaki nake ganin yadda kika iya fadi tashi na wahala nace chap yaushe kika koyi hakan kuma" a haka dai suka dinga hira har goma na dare yayi wanda yasa suka wuce ɗaki
Washegari da safe, bayan sun ɗanyi baccin safe Azrah da Zahra suka shiga kicin, suna girkin breakfast, Azrah ta juyo tana kallon Zahra ta ce
"Ni kam Bappah har yanzu yana nuna halin nan nashi wa Umma ko?"
Zahra ta ja dogon numfashi, ta ce
"Wlhi har yanzu. Umma dai tana da haƙuri ne kawai, amma halinsa yana damunta. Ni kam na kudiri aniyar magana da Dada Kafin ta koma, idan ba zai yu ba kawai ya rabu da ita Yaya, muje can ki tsiya mana karamin gida mucigaba da rayuwarmu mu kaɗai"
Azrah ta dafa kafaɗarta
"Good idea Zahra. Lokaci yayi da za a daina yin shiru kan abu mai zafi irin wannan" a haka suka gama girkin su...
Washe gari, Zahra ta tafi karɓo wa Azrah dinkin ashoben Samira. Da ta dawo gida, ta ajiye leda gaban Azrah ta ce
"Ki duba, ki gwaɗa kar kuma ya matse ki sai ranan biki ki gani, amma tailor ɗin yayi kokari Ya Aazrah"
Azrah ta buɗe kayan. Wani ubansu ɗinki ne mai ɗaukar ido, an yi shi da chiffon inner, ga bayan anyi wani following"
"Subhanallah! Dada ta ce.
"Ki gwada mana!" Zahra ta hura hanci tana dariya ta faɗa
Azrah ta shige ɗaki, ta fito da kayan a jikinta, kayan sun zauna kamar an yi musu ne a jikin nata. duk kallonta suke da sha'awa
Dada ta ce "Azrah, ai wannan kanma sai a ɗauka ke ce amarya, amma kalli wannan jelan dake binki fa?"
Azrah ta yi dariya kawai "Allah yasa dai ido karya min yawa"
Zahra kam banda dariyar Dada ba abin da take yi, ta ce "ce miki aka yi jela ce?"
Dada ta ce "Oho ai gashi nan naga yana binta".....
Ranar da za a fara Bridal Shower, tun safe Azrah ta tafi gidan su Samira daga can suka tafi guest house ɗin'da zasu zauna har a gama bikin,
Azrah na cikin jere kayan event, Samira ta karaso da sauri, ta ce
"Ina Jewelries ɗina Azrah? babu wannan dishes ɗin da wrapping tape? Gaskiya na manta su nake ji" ta kare maganar tana dafe kanta
Azrah ta ɗaga hannu alamar bata sani ba ta ce "idan babu kawai ki kira Deen ya kawo miki yanzu"
Samira ta zaune cikin riƙicewa tayi dialing numbern sa, yana shiga ya ɗaga kiran ta ce
"Dee mun bar kaya a motar ka fah, ka kawo min yanzu mana"
Ya ce "Baby Ina wani very important abune, kar na bar wajen kuma suki yi me kyau, bari zan bawa wani aboki na ya kawo miki yanzu" ta ce
"Alright Dee" daga haka ta katse ta miƙe tana kallon Azrah ta ce
"Abokin sa zai kawo min yanzu, idan ya zo sai ki fita ki karɓo min Please" Azrah ta ce
"Alright" daga haka Samira ta wuce kan gado ta kwanta, sauran friends ɗinta da cousins din suna zaune a cushions din dakin suna labarin su suma
Dakin babbane, irin manya dakuna na guest house wanda yake ɗauke da bed and cushion sets,
Samira dake kwance tana jira a kawo musu breakfast sai ga kiran Deen ya shigo, ta ɗaga ya ce
"An kai already Baby, Ki tura kowani ya je ya karɓa"
Samira ta ce "Toh shikenan" tana kallon Azrah ta miƙe zaune ta ce
"Azrah Please kije gashi ya iso" Azrah ta miƙe ta ɗauki veil ɗinta ta yafa shi sannan ta fita.....
Thank you Safiyya and Fatima💕😻🫂
Episode 59: Bridal shower
Tunda Azrah ta fito daga ɗakin, a hankali take tafiya kamar wacce bata ɗa laƙƙa a jiki. Kafafunta na yin nauyi a ƙasan, zuciyarta na bugawa, lokacin data bar corridor ɗin ta taka harabar guest house ɗin, gabanta ya fadi ganin wata mota a gefe maza biyu suna tsaye suna kallon wani direction, sun bata baya.
A hankali ta karasa har wajen, zuciyarta na kara tsananta bugawa kamar zata fashe. Tayi sallama cikin kasala, a tare suka juyo… idanunta suka sauka a kansu...
Zuciyarta ta yi freezing. Duniya ta tsaya mata cak na wasu dakiku, ta ɗauke kanta da sauri, ta ja baya kamar wacca aka watsa mata ruwan zafi, zata bar waje a ranta tana ayyana 'Maybe not them... maybe I'm wrong'
Amma kafin ta juya gaba ɗaya, Sagir yayi saurin cewa da fara'a, "Hey Azrah, ke ce zaki karɓi aikan?"
Ba tare da ta kallesu ba, tana kallon wani gefen daban, ta ce da kyar
"Eh, nice... ka ɗanyi sauri, because I don't have time to waste"
Sadeeq ya juyo a fusace yana hararanta, ya ce
"Baki da lokacin batawa? Mu ne marasa aikin yi kenan?"
Sagir ya ci gaba da murmushi kawai yana kallon yadda ta bata rai
Azrah ta buɗe hannaye alamun bata sani ba ta ce
"Ta ina zan sani toh? Tunda ba tare muke rayuwa ba"
Sadeeq daya ji ransa ya fara tafarfasa ya ce
"Ke kina da rashin kunya sosai! Kinsan de mun girme ki a ƙalla zamu baki shekaru sama da 10 ko 12 ko fiye da haka ko? Amma baki da respect ko kadan, get this straight, we are not your mate"
Azrah ta juyo da kallon kansa ta haɗe rai tana dariya mai ciwo, ta ce
"Oh wow! So dama nace maka ina neman sani ne da zaka faɗa min? Are you okay?"
Sadeeq ya ɗaga hannu da niyyar zai mareta, Sagir ya rike hannunsa da sauri cike da mamakin reaction ɗinsa ya ce
"Bro, calm down. Ba haka ake yi ba"
Azrah tayi wani dariya ko ɗigon tsoro babu tattare da ita ta ce
"Da ka barshi ya mare ni ai. Idan yana gadaran ni ba 'yar kowa bace, ya mare ni kawai sbd ganin ba wanda zai ɗau min fansa, wlhi he will be shocked da next move ɗin, idan karya ne ya gwaɗa"
Sadeeq ya ce a fusace
"Kaga dakikiyar yarinyar nan ko? If I keep watching you one day, I might hurt you definitely!"
Azrah ta ce
"Kai ma kasan ba dakikiya bace ni. Duniya ma ta san da hakan, And thank God tare muka gama degree, ka san irin kokarina balle kace kokari sai yaran masu kuɗi dan gasu mun gansu degree din ma dakyar suka kare"
Sagir, ganin drama din ba zai kare ba, ya koma mota, ya ɗauko abin da za'a ba ta ya miƙa mata. Azrah ta karɓa a fusace, bata kalli ko ɗaya daga cikin su ba, ta wuce ciki kai tsaye zuciyarta na tafasa
Sagir ya riƙe hannunsa a hankali yana fadin, "Calm down please, take it easy"
Amma Sadeeq ya fisge hannunsa cikin fushi, ya wuce mota kai tsaye, ya buɗe ƙofa ya zauna, ya bugi steering da karfi yana hucu, idanunsa yayi mugun jaa sbd ɓacin rai, yana kallon Sagir kamar zai shake shi ya ce
"Akan me zaka bata message din?!"
Sagir ya tsaisaita nutsuwarsa, yana kokarin kwantar masa da hankali ya ce
"Toh ai abin da ya kawo mu kenan. Kuma amarya ce ke bukatar sakon ba ita ba"
"Kai ina ruwanka? Ma kai aka bawa sakon da har zaka bata?!" Sadeeq yayi magana a fusace, sai kuma ya kara cewa
"Wallahi ni niyya ta tun farko in juya da message din, in tafi. Bata kai matsayin da zan bata sako ba!"
Sagir ganin abin na Sadeeq ba karewa zai yi ba ya fara danna wayansa, sai kuma ya ɗaga kai ya Kallesa ya ce
"It's okay bro. Amma gaskiya, this time ba laifin ta bane. Kai ne ma ka fara daukar magana da zafi, tunda bata kula ka ba da kaima ka kyaleta"
"Toh wai yanzu baya na kake bi, ko bayanta ne?!" Sadeeq ya ce, yana kallon Sagir daya ki yarda ya ɗago,
Sagir ya daure fuska, yace a nutse
"Eh, bayan gaskiya nake bi. Kuma this time, itace da gaskiya. Ka wuce gona da iri gaskiya, tunda da Ni tayi sai Karka tanka mata"
Wani irin tsawa Sadeeq yayi masa, cikin fushi ya saka key, ya kunna mota yana huci, sai kawai ya fige su da wani irin mugun gudu suka bar harabar wajen
Azrah hatta karasa cikin wajen tana jin yadda zuciyarta ke tafarfasa, da karfi ta buɗe dakin ta shiga, inda Samira ke zaune tana breakfast ta karasa, Samira tana kallonta ganin yadda ranta a ɓace, bata kai ga magana ba Azrah na kallonta ta ce cikin raɗaɗi da rashin jin daɗi ta ce
"Akan me yasa sai Sadeeq ne zai kawo aiken? Kawai zai tsaya ya raina min hankali, har da zagi na?, an gaya mai zan ɗauki wannan shiit ɗin ne"
Samira ta kalle ta da tausayi, ta ce
"Sadeeq kuma? Toh kiyi hakuri Azrah, amma Ni kam ban san shine zai kawo ba, haba taya ma nasan shi zai kawo sai kawai nace ke ki fita bayan nasan ke da shi kamar fetur da ruwa ne"
Azrah ta mike da cike da haushi ta ce
"Dama akwai wani bayan shine da na tsana? Shi kaɗai wanda zai zo ya gaggayamin magana? In har zan ci gaba da haduwa da shi a bikin ki, to na hakura"
Samira ta ce "Ban gane ba Azrah? Saboda shi sai ki fasa attending biki na kike nufi? Azrah ta ce
"Akan meyasa zan zauna inda nasan zan haɗu da shi? Bayan kema kinsan sab zai zageni harda iyaye na, ana kallona ana girmamani karyasa a fara min kallon kaskanci" Samira ta ce
"Please Azrah ki daina kallon background ɗinki, wlh dukkan mu nan Ni da cousins dina bamu da abin da kike da shi duk da kuɗin iyayenmu, kuma me kuka rasa? Ci ko sha? Ki godewa Allah ki zubar da maganar Sadeeq a gefe"
Samira ta ƙara bata hakuri cikin
sanyi murya, tana kokarin sassauta mata zuciya dan ta huce.
Daga nan suka gama shirye-shiryen su, suka yi makeup tare da sauran friends ɗin Amarya da cousins nata. Ba karamin kyau Amarya tayi ba, kayan data saka ma super expensive ne, kana ganin ta kasan ruwan naira ne yayi magana, Azrah tuni ta manta da wani ɓacin rai ta fara ma Samira pictures tana dariya.
Wata cousin ɗin Samira tana kallon Azrah ta ce "Finally zamu ga angon da aka fi 5 years ake ɓoye mana" Samir tayi dariya, Azrah ta ware ido ta ce
"Har ku baku san sa ba? Chap toh ko Ni ban taɓa ganin hotonsa ba sai dai a rufe fuskansa da sticker sannan a ɗora a status" duk dariya suka yi, Azrah ta ce
"Ashe dai ki ce Ni an min gata da nake waya dashi sometimes"
Ya SubhanAllah, bayan Azrah ta saka kayanta duk ɗakin suka fara wow, Samira ta mata whisper a kunne 'this is d reason I like you, Sbd nasan zaki fitar dani kunya as bride BestFriend" Azrah taki kulata
Daga haka suka nufi wajen event ɗin.
Bayan sun shiga cikin venue, wayar Azrah ya fara ringing, tana ganin Khalil ne ta ɗauka tana jin son sa na karuwa mata a rai, suka gaisa
Khalil ya tambaya, "Har kun isa wajen event ne?"
Azrah ta amsa, "Eh, mun iso fah"
Khalil ya ce, "Mu yi switching to video call lemme see ur beauty"
Bayan sunyi switching Khalil ya dinga kallonta sai kuma ya ce
"Haba Azrah, so kike wasu mazan su kalla mini kyan ki?"
Azrah ta yi dariya, "Babu maza, zalla mata ne, ka kwantar da hankalin ka"
Daga haka, wata kawar Samira ta karaso, tana kallon Azrah, ta ce
"Amarya, na son magana dake sister"
Azrah ta yi sallama da Khalil cikin kulawa, sannan ta nufi wajen Samira.
A haka aka fara event ɗin, cike da wasanni na 'girls play' inda suka yi words game, raye-raye, da hira mai dadi tsakanin kawayen Samira da cousins dinta, Wasu suna tsokana da dariya, wasu na yin 'group selfies', wasu kuma suna bada kyawawan kalamai ga amarya. Amma sun ci sun sha, magana ake ta expensive dishes
Lokacin da aka kammala, suka tashi suka fita daga hall ɗin. Mota ta iso ta mayar da su
Bayan sun isa guest house ɗin da za su kwana, Azrah ta zame jikinta daga hannun Samira ba tare da ta lura ba, ta fita daga ɗakin kamar me waya, sannan ta fita daga cikin wajen ta nufi bakin titi, tana samun abin hawa ta shiga da sauri kafin ma wani ya fito ya ganta, taga haka ta isa zuwa gida.....
Mutumin da ya ga hirar da aka yi da Azrah a TVCnews, yana zaune cikin natsuwa yana kallon PA ɗinsa, ya ce
"Please, ina son zan yi magana da yarinyar nan, make sure a san inda take. Ina ganin zata mana amfani anan sosai."
PA ɗin ya amsa da "Toh shikenan sir, zamu ga yadda za mu aika mata da sakon gayyata. Allah ma yasa ta yarda"
Mutumin ya mike ya fice, kana ganin, shi mutum ne mai matuƙar kulawa da alhakin aikinsa...
Yau ne kuma ranar pajamas night na Samira da za a yi. Azrah tun da tayi sallan Asuba take jin bata wani jin daɗi amma sai ta dauko ko dan tunawa da Sadeeq da tayi ne, bayan ta idar da sallar asuba tana kan Azkar matsanancin zazzaɓi ya rufera, tana daurewa har da fara rawar sanyi. Kawai ta kwanta a wajen ba tare data bari Dada da Zahra suyi noticing ba...
Bayan ta gama wanke wanke, Zahra ta daura abinci, ta shiga dakin su dan tambayar Azrah me za'a yi, ta ga tana rawar sanyi, cikin damuwa ta ce
"SubhanAllah, me ke damunki? Baki da lafiya ne?"
Azrah ta amsa, "Ban ɗauka zai yi haka bane, ban paracetamol na sha pls zai sauka"
Zahra ta mike da sauri, ta nufi dakin Umma, ta ce
"Umma, Ya Azrah ba lafiya fah" da sauri Umma tayi ɗakin ko karasa sauraran Zahra bata yi ba
Dada ta dawo daga dakin Bappah Kenan ta shiga dakin tana mamakin ganin Umma da tayi dan Umma bata shiga haka kawai, sai ta ga yadda Azrah ke rawar sanyi ta ce
"Oh Ni bata da lafiya ne?" Umma ta ce "Eh, bari mu karya mu tafi asibiti"
Daga haka Umma ta nufi waje ta karba girkin da kanta tayi musu breakfast din. Lokacin Samira ta kira ba adadi
Ta kuma kira sai Zahra ta ɗaga kiran, bayan sun gaisa, Zahra ta fada mata cewa Azrah ba lafiya
Samira ta ce, "Bayan guduwan da tayi jiya, shine zata iya cewa bata da lafiya yau? Ki ce mata sai ta zo pajamas night ɗin nan, duk plan ne, dama ta gwada min bata so, idan kuma Sadeeq ne ba zasu haɗu ba tayi trusting dina"
Zahra ta yi shiru, daga baya tace, "Wallahi bata da lafiya Ya Samira"
Samira ta ce, "Zan kashe waya, ki ce mata sai ta karaso Ni dai kam"
Daga nan ta katse kiran.
Bayan sun gama karyawa cikin hanzari, Umma da Dada suka shirya Azrah da sauri, suka fice zuwa asibitin unguwar, Azrah na ta juyi, zazzaɓin ya hana ta ma sukuni. Zahra na gefe idanunta cike da tausayi.
A asibiti, aka karɓe ta da gaggawa, aka yi mata gwaje-gwaje, aka haɗa da drip. Likita ya tabbatar cewa zazzaɓin ya haura sosai, kuma tana bukatar kulawa. A nan take aka yi admitting ɗinta
Bayan an mata allura da ruwan da aka saka mata yasa ta samu bacci
wayar Umma ce ta sake ringing na ba adadi, ta daga taga Samira ce
Da ta ɗaga kiran, suka gaisa, Samira tace da damuwa
"Umma, Zahra tace Azrah ba lafiya. Gaskiya na damu dan ina ta kira kuma bata ɗauka"
Umma ta amsa cikin sanyin murya
"Eh, Zazzaɓi ne ya kamata sosai, har sai da muka zo asibiti, an bata gado amma tana gama shan ruwan zamu koma gida"
Samira tayi shiru kadan, sannan ta ce, "Allah ya ba ta lafiya, Umma. Ki ce mata ina gaishe ta,Allah bata lafiya
Umma ta ce, "Ameen. Na gode da kulawa"
Bayan wasu sa'o'i data kammala shan drip, lokacin kuma zazzaɓin ya ragu, likitoci suka sallame su. Azrah ta fito da rauni amma jikinta na samun sauƙi, suka koma gida.
Umma ta fita da niyyar dafa mata potato da tace tana son ci, ya zamana daga Azrah sai Zahra a ɗakin
Zahra ta dan huta kadan, sannan ta nufi ɗakin Umma inda Dada take nan
Bayan ta shiga ta zauna ta ce
"Dada akwai wani abu da nake so na gaya miki tun ba yau ba"
Dada ta kalle ta da kulawa, "Ina jinki Zahra"
Zahra ta sauke ajiyar zuciya, ta ce
"Wlhi Dada, Bappah baya kulawa da Umma. Ko kallonta baya yi, ko wani abu ya faru, sai Mama yake saurara. Umma kamar wata baiwa ce a cikin gida, bata ishe Bappah kallo ba, abinci kuwa kuɗin da ake bawa Yaya a scholarship shi take turo mana muke tsaya mu ci, idan Kinga Bappah ya kashe kuɗi toh akan Mama da Yaranta ne, mu kuma gaskiya mun gaji da wannan halin nasa"
Dada kallonta take with shock harta gama magana, ranta yayi mugun ɓaci, sai yanzu ta lura tun zuwanta Bappah koda wasa bata gansa a dakin ba, tana kallon Zahra ta ce
"Ke kin tabbatar da Wannan maganar?"
Zahra ta gyada kai ta ce "Haba mana wannan fa fin shekara kenan?"
Dada ta ce da murya mai cike da tausayin Umma
"Idan har ni ce na haifi Bappah, idan ba wai ya canza halinsa bane, to tabbas sai ya saki Mama. Umma amanace a gare mu, kuma ba zan bar wulakanci ya cigaba ba, har shi ya manta halarcin da Ummanku ta masa? Wato gashi butulu ko? Gani yake kowa ya gujeta ba? Toh tabbas zai sha mamaki na wannan karon"
Zahra ta lumshe ido, cike da jin sauƙin zafin da zuciyar ta yake yi
Dada ta dafa kafadarta, "Kiyi hakuri, zan ɗauki mataki akai"
Wannan page ɗin naki ne Ibtisam😻
Episode 60: Wedding whispers/ hidden hearts
Umma ta gama dafa potato ta zuye a wani bowl sannan ta wuce cikin ɗakin, ta shiga da sallama Dada ta amsa mata tana binta da kallo har ta zauna gefen Azrah ta ce
"Azrah ta shi ki ci ko?" Azrah ta buɗe idonta dake lumshe ta ce
"Umma kamar bana jin yunwa yanzu fah, anjima zan ci" Umma ta ce
"Anjima ai zai yi sanyi, ba zai miki daɗin ci ba, balle ma ke da baki son abinci yayi sanyi" Azrah ta ɗan miƙe zaune ta kai hannu ta karɓi bowl ɗin ta kai spoon ɗaya bakinta sai kuma ta girgiza kai ta ce
"Umma yanzun ina jin tashin zuciya ne kar nayi amai" Umma ta ce "toh Shikenan ki bari toh sai anjima ɗin" daga haka ta karɓe abincin ta ajiye a gefe sannan ta rufe
Ta miƙe zata fita, duk wani move ɗin Umma, Dada na binta da ido ne, ji take kamar zata zubda mata hawaye, bata san abin Bappah ya cigaba ba, dole ma ya rabu da Mama dan me take tsinanawa? tarbiyar ma ta kasa bawa yaranta sai faman tara samarikan banza da daddare, sai da Umma ta fita sannan Dada ta sauke ajiyar zuciya
Zahra ce ta shigo ɗakin tana kallon Dada ta ce
"Bata ci abinci bane naganta kwance?" Dada ta ce
"Dama ba lallai ta iya ci ba, sai a hankali ai" Zahra ta gyaɗa kai tana kwanciya cinyar Dada, jin wayan Azrah na ringing ne yasa Zahra saurin miƙe wa taje ta ɗauki wayan, ganin Khalil ne yasa sai ta kalli Azrah amma ganin bata buɗe ido ba kawai ta ɗaga kiran dama sai kira ya ke tayi, bayan tayi masa sallama
A hankali ta ce "Ai in-law Ya Azrahn ba lafiya ne, har sai da aka kwantar da ita a asibiti bamu daɗe da dawowa gida ba" jin me Zahra ta faɗi yasa Azrah buɗe idonta ta Kalleta sai kuma ta kara rufe wa, Zahra kuma jin yadda gaba ɗaya Khalil ya daburce yasa ta yi saurin cewa
"A'a da sauki sosai fah, yanzu ma dan tana bacci ne, amma tana farkawa zata kira ka In Shaa Allah" daga haka suka yi sallama
Dada ta ce "waye ne mutumin?" Zahra na murmushi ta ce
"Toh wanda ke son ta ne daga Egypt" Dada ta zaro ido ta ce
"Kai! Ko dai su Umman naku ne suka haɗa su?" Zahra ta ce
"Su Umman mu kuma? Su waye kenan? A can India fah suka haɗu shima yaje karatu ne" Dada ta sauke ajiyar zuciya da sauri jin me tace ta ce
"Ohh, Nagane! Ashe acan ta haɗu da shi kenan?" Zahra ta ce
"Su waye su Umman na mu?" Dada ta ce
"Babu kowa fah" Zahra tayi dariya ta ce "Naga da alama dai tsufa ya fara miki yawa" Dada ta ɗauki mafificin gefenta zata buga mata Zahra ta bar wajen tana dariya. Jin muryan Bappah yasa Dada yin wuff ta miƙe
Fita tayi ta sauka daga bakin baranda cikin ɗakin Umma, ganin yadda Bappahn ya nufa yasa taji zuciyarta tafarfasa ta ce
"Kai Muhammadu zo nan" Bappah sai daya ji wani mummunar tsinkewar zuciya ya juya yana kallon Dada sanda ya juya ya fara takowa inda take, ganin haka yasa ta fara tafiya zuwa wajen dakin Bappah dan yafi ciki a gidan ba lallai a ji daga waje ba, binta a bayan yayi, tana karasa wajen ta tsaya tana Kallonsa har ya karasa, ita tasan yadda zuciyarta ke mata kuna, ya duka zai gaishe ta ɗaga masa hannu ta ce
"Bana bukatar gaisuwarka Malam! Ka riƙe gaisuwar naka nace" Bappah ya sauke idonsa daga kanta dan yaji ba zai kuma iya ci gaba da kallon nata ba, ya ce
"A gafarci idan nayi wani kuskuren ne Dada" Dada ta ce
"Wannan ai ba kuskure bane, wannan wulakanci ne da kuma tsantsan butulci" Bappah da rashin fahimta yake kallonta ya ce
"Kamar ya Dada?" Ta ce
"Ina duniya zaka wulakanta bitti, Muhammadu? Tun kasa bai rufe min ido ba? Kuma ina rayuwa cikin gidan tare da ku? Yanzu ace nayi nisa da ku ashe duka da zagi zaka mata, idan na mutu kuma korarta zaka yi?" Bappah ya riƙe kansa dake sara masa ya ce
"Kiyi hakuri zan gyara, sharrin shaidan ne, hakan ba zata sake faruwa ba" Dada tayi shiru dan bata son tana tunowa jin zuciyarta na kara ɓaci ne, ta ce
"Ka tabbatar ka canza halinka Malam, idan ko ba haka ba, ina me tabbatar maka sai na maka baki akan Uwani sannan kuma ka sake ta har abada" da sauri Bappah ya ɗaga kai yana kallonta ya ce
"Zan ma canza, amma Dada ki janye wannan kalama" ta ce
"Kai ne zaka janye ta ta hanyar nuna min cewa ka canza ba wai sai ina nan ba, har bayan bana tare da ku, yanzu kai ba abun kunyar ka bane agaban 'ya'yanta kake wulakantata ko kunyar ido na ace baka ji ba ka cigaba da bayyana wannan mummunar halin naka" dogon tsaki taja sannan ta bar wajen
Da Daddare... Ga ba ɗaya Samira ta shiga damuwa na rashin Azrah, a haka duk suka nufi hotel ɗin da zasu yi event ɗin, bayan sun isa ko minti biyar basu yi da zuwa ba sai ga mai Makeup ta karaso, nan cousins ɗin amarya da few friends ɗinta suka fara shiri cikin pajamas wear ɗinsu, bayan an gama ma amarya makeup itama ta saka nata, wajen da zasu yi ba karamin haɗu wa yayi ba, dan ya sha balloons deco, kamar yadda Azrah tayi sensing kuwa harda Male friends ɗin Samira haka suka cika wajen, an fara gudanar da event ɗin cikin nishaɗin wani friend ɗin Samira American dude ne ya shigo ta dalilin map da yake amfani da shi, yana shiga tsabar farin cikin ganin Samira ya karasa wajen ya rungume ta jikinsa yana mata congratulations, masu videos kuwa basu fasa yi ba, tana dariya ta zame jikinta suna gaisawa, a haka suka cigaba da shagalinsu har aka gama, bayan sun koma destination ɗinsu duk a gajiye suke saboda rawan da suka sha wanda ko a bridal shower basu yi wannan rawan ba, suka shiga hirar event ɗin cike da nishaɗi, Samira ta jawo wayarta tana murmushi ta shiga page ɗinta da Azrah ta mata ya jiki sannan ta tura mata pictures da suka yi a wayanta ta tura mata daga haka ta kashe wayan.
Azrah na ɗan ci sauran faten dankalin da Umma ta dafa mata da yamma, Zahra na gefenta tayi dariya ta ce
"Body system ɗinki yasan baki son zuwa wannan pajamas ɗin shine daga dawowa daga bridal shower zaki wani kwanta jinya, wato yanzu an kare ga kuma jikin naki ya fara warwarewa, Azrah ta ɗanyi murmushi kawai itama tunanin da tayi kenan amma hakan ya mata daɗi dan da ba haka ba bata isa tayi escaping ma Samira ba, wayanta ne ya fara ringing, Zahra ganin Khalil ne yasa ta kyalkyale da dariya ta ce
"Shi baya gajiya ne da kira? Daga jin baki jin dadi fah shikenan kuma ya kara zuzucewa" Azrah ta harareta tana ɗaga kiran gami da kai wayan kunnenta yadda Khalil yake mata sai data fara dariya ta ce
"Calm down, na samu sauki fah" ya ce
"Da ace Abbu na nan da tuni yau zaki ganni, amma dake Ni nake handle komai I've to wait for him first kafin nace zan yi wani abu ma" Azrah ta lumshe ido ta gagara cewa komai cos she's so emotional da yadda Khalil yake nuna mata So ko dan shine first love ɗinta bata sani ba, a hankali har suka kammala wayan, Whatsapp ta buɗe tana son ganin storyn Samira, 20+ messages ɗin Samiran taga ya shigo, buɗewa tayi taga Sakon fatan samun sauki data mata sai kuma hotuna a kasan message ɗin, har ta fara reply ɗinta sai kuma ta daka ta har sai da pictures din suka gama downloading, shiga tayi ta fara kallo, hamdalah tayi a ranta ganin yadda friends dinta da cousins ɗinta suka yi dressing ɗin, gashi duk babu me hula ko ɗankwali aka, sai attached cap wanda zaka ɗauka gashi ne shi duk suka saka, har Samira babu komai kanta banda wani flower da aka kama mata gefen gashin nata da shi, fasa tura message ɗin tayi dan kar ma Samira ta dauka cewa ta gani, ba karamin daɗi taji ba tunawa da cewa ashe wayanta baya nuna ko taga message, daga haka ta sauka ta kashe wayan baki daya ma.
Washe gari Saturday ya kasance shine ranan daura auren Samira, kuma a yau din za'a yi dinner, wanda tun safe take gwada numbern Azrah taji ko jikin nata ya sauka ta ce tazo, hakan harya fara ba wasu friends ɗin nata da cousins haushi, cos gani suke they're nothing kenan tunda ita damuwarta Azrah ce, ita kuma yi tayi kamar bata ma fahimci me suke ciki bama.
Duk suna zaune ɗakin Umma wanda yanzu kam jikin Azrahn da sauki sai dai bata gama warwarewa ba, breakfast suke, Azrah ta ɗaga kai tana kallon Umma ta ce
"Umma ina so na tafi bikin Samira" Umma da Dada har haɗa baki su ke wajen cewa
"A baki da lafiyan?" Azrah ta sauke idonta ta ce
"Yanzu kam naji sauki fah" Umma ta girgiza kai ta ce
"A'a gaskiya kam, ko magani baki gama sha ba kice zaki wani fita? Ina dakyar kika iya fitowa nan saboda jiri shine sai na barki ki tafi biki cikin bainan nasi, A'a kiyi hakuri kawai" Dada ta ce
"Ah toh, fita ba naki bane, sai kuma da lafiya ake komai, ki hakura idan kika kara warwarewa sai ki tafi har gidan nata ko?" Azrah ta gyaɗa musu kai kawai, tana kallon Zahra ta ce
"Toh Zahra karki kunna wayata nasan zuwa yanzu Samira zata fara nema na, gwara kawai ta nema taji a kashe ya fi".
Ya SubhanAllah! Sai yau kawayen Samira suka ga dalilin daya sa take ɓoye Deen, duk da daɗewan da suka yi tare, sannan kuma ta cire shi a masu ganin status ɗinta dan karma tayi mistake ɗin daura wata har ya gani, basu taɓa ɗauka gayan ya haɗu iya haɗuwa ba, namiji ne wanda kallo ɗaya ba zaka iya ɗauke idonka akansa ba. kowa sai bin Amarya da ɓoyeyyen Angota ake yi da kallo, ba karamin perfect match suka bayar ba, dukkansu shigan white and golden suka yi, Amarya tasha gwala-gwalai, har extra kyau ta kara yau, they both can't believe wai yau sun mallake juna, dama ana daura aure yana gama pictures da iyaye sa, shi da friends ɗinsa suka karkato zuwa gidan Aunt ɗin Samira, inda anan ta kwana, inda yana hoto da Amarya kuma zai ɗauke ta ya mayar da ita gidansu dan mata nasiha sannan akai ta gidansu, sanda ya ɗagota zuwa jikinsa ihuu ake ana kara daukan su a hotuna, kana kallon fuskokinsu kasan suna cikin farin ciki, kana kallon yanayin match ɗinsu kuwa zaka san dalilin daya sa suka zaɓi each other, Dan dukkansu iyayensu ba daga nan ba wajen Naira, bayan an gama hotuna aka mayar da amarya gidan su, inda ta fara pictures da Aunts and other relatives nata, gaba ɗayan su suna cikin farin ciki, Samira tayi hoto tare da iyayenta sannan aka tafi da ita zuwa Babban Parlorn mahaifinta inda Yayan Mahaifin nata ya mata nasiha sosai, daga nan kuma aka ɗauki Amarya za'a tafi da ita gidan su Deen, wanda ta fara kuka ba kukan rashin so ba, sai dai kukan sabo, bayan an kaita gidan su Deen, duk da yadda mahaifiyarsa bata Son ta amma ba zaka taɓa cewa ba, karɓa na alfarma aka ma amarya da 'yan rakiya, wanda duk sai da nata 'yan uwan suka yi murna da yarda aka tarbe su.
Magrib nayi aka zo aka fara shirya amarya wanda karfe bakwai nayi aka ɗauki amarya sai venuen dinner, wanda duk ya kalle su sai ya yaba da yadda amarya da angonta suka haɗu.
Da Daddare suna zaune Zahra na basu labari wai ita a dole sai sunji tatsuniyan da take basu, wanda tuni hankalin Dada baya jikinta, mamakin yadda tama Bappah magana kuma yayi burus da maganar ta take yi, ashe har zata iya ma bappah magana akan abu yayi banza? Wato duk maganganun Zahra haka yake ba shakka data ce fiye da shekaru yake wannan ɗabi'un, murmushi tayi tana cin alwashin idan ita ta haifesa toh sai ta sa komai yazo karshe, tun safe take lura dashi bata ga ko kafar sa ba, jiya ta ɗauka zai shigo amma same thing, sake wani murmushin tayi ganin yadda Mama da Yaranta suka ma dai na zaman sakar gidan kuma tasan saboda ita ne, sana'ar ma Mama ta de na, idan ta gama wanda su Siyama zasu kai mata garage da asuba idan ta kule ɗaki bata fitowa sai zata unguwa ko makwabta, gaishe da Dadan ma ta de na shi yanzu .
Zahra na kallon Azrah da ta jinkina jikin Umma ta ce
"Yaya na kunna wayanki?" Azrah ta girgiza mata kai kawai, Zahra ta ce
"Kai Yaya tun safe fah wayanki a kashe" Azrah ta ce
"Ai nasan dalilin yin hakan, idan har ba haka nayi ba da yanzu Inaga Samira ta kusa tsine min, gobe zan kunna sannan zan kirata naji ina aka kaita, In Shaa Allah sai ki raka Ni dan yanzu kam naji dama dama"
Zahra ta ce "Toh Shikenan Allah kai mu" Azrah ta amsa da "Amin"
Kamar yadda Dada tayi nisa cikin tunani haka Umma ma, dan basu ma san me Zahra da Azrahn ke tattaunawa ba.
#Jiddatulkhayr
08110615256
Episode 61: Words That Cut Deep
Daga wajen Dinner aka ɗauki Amarya sai gidanta, gida ne na gani na faɗa, kowa sai san barka yake mata, wanda tuni 'yan rakiya suka kama gabansu aka bar daga amarya sai Angonta.
Washe gari da safe, bayan sun idar da sallar asuba, tun kafin gari ya waye saboda zafin da ake yi a garin ga azrah kuma da bata gama warwarewa yasa suka shimfida tabarma a kofar ɗakin Umma duk suka zauna, bayan Umma ta gama lazuminta ta miƙe ta nufi kitchen ta fara duba abin da zasu ɗaura, a bangaren Mama ma da Yaranta suna waje saboda abinci da zasu fita da shi tallah, suma tun idar da Sallah suka hura wuta kasancewar dama haka suke, ba shiri duk suka gaida Dada wanda ba yabo ba fallasa ta amsa musu, Mama ma wacca kamar an sata dole ne itama ta gaida ta, yadda Dada ta amsa ma su Siyama haka ta amsa mata ita ma. Umma ce ta fito daga kitchen ɗin tana kallon Azrah ta ce
"Azrah me kike so a dafa?" Azrah ta ce
"Ko ma menene Ni zan ci, kawai ki dafa abinda kike da ra'ayi Umma" Umma ta juya ta koma cikin kitchen ɗin, Azrah ta jinginar da kwanta, Zahra ta miƙe taje ta fara ciro kayan wanke wanke, bayan ta haɗa kayan ta ɗauki roba ta wuce wajen da ruwa yake zata ɗiba, ajiye bokatin tayi a kasa zata saka moɗa cikin randar da nufin ɗebawa kawai tajiwo muryan Mama
"Toh mara kunya, agwagwa sarkin wasan ruwa sai ki ɗiba kaɗan ko?" Zahra data tsaya har sai da Mama ta kare maganarta ba tare data juya ba ta taɓe baki da gayya ta soma harda ɗayan hannunta cikin ruwan ta ɗibo
"Kam bala'iiii, saboda ke mara tarbiyya ina miki magana kiyi da hankali shine zaki wani fara wasa da ruwan?" Mama tayi maganar a kufule, Zahra kuma cike da tsiwa da rashin tsoro ganin Dada na tsakar gidan ta ce
"Toh baki ganin yanzu ne na ɗiba moɗa ɗaya? Tun fa ban fara ɗiba ruwan ba kika yi magana, toh ko kofi ɗayan ne zai ishe ne?" a fusace Mama ta ce
"Uban ki shegiya mara tarbiyyar, ai gado ba karanbani bane" Dada da abin duniya de ya ishe ta, mamakin yadda ko ta idonta Mama bata gani ba take irin waɗannan maganganun yasa ta ce
"A gaba na kike zakin ubanta? Kuma ki kirata shegiya, Uwani? Yanzu fisabilillah tun kan ta ɗiba ruwan nan kika fara magana, kofi guda data diba shima ya zama magana" Mama ba tare da komai a ranta ba ta ce
"Ah ai naga ba Uban nata bane ya tsiya ruwan jiya, Ni na cire kudin shiyasa nasan zafin hakan" Dada ta gyaɗa kai ta ce
"Eh ba shakka, toh ai kin kyauta" Zahra cike da kullata dan ba kaɗan ba ta tsane Mama akan abubuwan da Bappah ke ma Umma, ta ce
"Ai naga gidan uba nane, naga kuma da makudan kuɗaɗen da kika karɓa wajensa kike tsanaar ai" Umma ta leƙo ta mata kallon warning
Mama ta ɗauke kanta, yaranta kuma suna cigaba da aikin gaban su, da gayya Zahra ta ɗibi ruwan dayawa, wanda ko a farko bata yi niyyar diba ba, daga haka ta wuce wajen wanke wanketa ta fara yi tana wake waken habaici, Azrah tayi murmushi kawai dan bakin Zahra ba zai taɓa shiru ba
Da sallama Bappah ya shigo gidan, dawowarsa daga masallaci kenan, yazo zai wuce inda Umma ke girki zai nufi wajen ɗakin Mama yasa Umma cewa
"Barka da Safiya" ba tare daya amsa ba ya cigaba da tafiyarsa, Dada da tun shigowarsa take Kallonsa da muryanta wanda yake ɗauke da tsantsan bacin rai ta ce
"Muhammadu" Bappah ya tsaya cak, sai kuma a hankali ya juya ya nufa inda suke, Zahra ta taɓe bakinta tana jin yadda zuciyarta ke ƙuna, yana karasa wajen ya cire takalmansa ya hau kan tabarman, Azrah ta ce
"Barka da safiya, Bappah" kai kawai ya gyaɗa mata sannan ya juya ga Dada ya ce
"Barka da safiya" Dada ta ce
"Riƙe gaisuwar ka Malam" cak Mama ta tsaya da aikin gabanta ta ɗago tana son jin dalilin da yasa Dada ta kirasa har take masa magana cikin fushi, Bappah ya tsaya kallon Dada, lokacin guda jikinsa yayi sanyi ya sauke kansa ƙasa, ta ce
"Ba zaka tambaye jikin Azrahn bane?" Ya juya yana kallon Azrahn ya ce
"Baki da lafiya ne?" Dada tayi wani irin murmushin mai haɗe da takaicin, cikin kunar rai da masifa ta ce
"Ta ina zaka sani? Na ce ta ina zaka sani tunda ba sanin lamarinsu kake yi ba?" Bappah ya ce
"Amma Dada..." Cike da zafin rai Dada ta ce
"Dalla kamin shiru, ina Ni zan gaya maka magana ka tsallake ko? Ni zance kayi abu ka gani ba zaka iya ba ko? To yau zan kawo karshen wannan masifan data shigo gidan nan" a hasale ta miƙe ta ce
"Duk ku bar aikin da kuke ku zo nan" Siyama da Habibah suka kalle juna sai kuma suka kwashe da dariya, Dada ta sake baki tana kallonsu da kunar rai ta ce
"Ƴan iska mara sa tarbiyya har Ni zan yi magana ku kwashe da dariya? Har kun isa? Ko da yake banga tarbiyya ba a jikinku ba, zan muku uzurin wannan" Mama ta taɓe baki ta cigaba da jera gwangwaninna alalenta a kan faranti, Dada ta ce
"Ina cewa nayi ina son magana da ku ko?" Umma ta karasa kai abincin data kwashe ɗaki ta fito ta zo ta zauna kan tabarman kusa da Azrah tana kallon wani direction taki yarda ta kalli Bappah, Zahra ta miƙe ta karasa itama ta zauna amma ta bawa Bappah baya, Bappah na son mata magana amma ya kasa, bayan duk sun karaso Dada ta ce
"Toh Alhamdulillah, tun zuwa ta gidan nan na lura da wani abu dake faruwa ba dan wani ya buɗe baki yace hakan ba sai dan na lura kuma abun na cigaba" tana kallon Bappah ta ce
"Kai kuma shekaran jiya ba na maka magana ba ne?" Kai Bappah ya gyaɗa mata, ta ce
"Shine kuma kaga ba zaka iya ba ko? Toh yanzu ina so ka juya ka saki Uwani tunda gwara ita tana da 'yan uwan da zata koma gare su" Duk sai da suka ɗago suna kallon Dada da mamaki banda Zahra data fara gyaɗa kai tana murmushi irin Dada ta biyatan nan, Umma zata yi magana Dada ta ce
"Ban saka bakin ki ba Bitti, kuma bana bukatar jin komai daga kowa, abun dana faɗa kawai nake so ya aiwatar" Mama tayi wani murmushi, a hankali Bappah ya ce
"Dada kiyi hakuri ba zan iya ba" zaro ido Dada tayi waje tana kallonsa, ta ce
"Ba tambayar ka iyawa ko rashin iyawan nake son sani ba, damuwata nace ka sake ta, ko baka ji nane?" Nan da nan Bappah ya birkicewa Dada shi gaskiya ba zai iya ba, Dada kam abin ma tsoro ya fara bata, ta ce
"Toh zaka iya sakar Bitti?" Without second thought Bappah ya gyaɗa mata kai ya ce
"Eh, zan iya" Dada ta fara salati tana tafe hannu, ita komai take gani kamar alamara ta ce
"So nake nasan laifi guda da baiwar Allahn nan ta maka" ya girgiza mata kai, a fusace ta ce
"Babu shine kake wulakanta ta da yaranta? Wannan wata irin masiface, kuma har zaka iya furta mun ita zaka iya saka? Duk da halaccin data maka a baya? Lallai kai babban butulu ne, ko ka bata hakuri da alkawarin ba zaka sake kwatankwacin hakan ba ko kuma ka rabu da wadda kake so, sannan duk ranan da kayi gigiyin sakanta na sallamawa duniya kai" a razane Bappah ke kallon Dada, ta sake magana cikin tsawa ta ce
"Nace ka nema yafiyarta kuma ka mata alkawarin komai yazo karshe ba zaka kuma ba" to her surprised Bappah ya juya yana kallon Mama yana jiran go ahead ɗinta kafin ya ma Umma magana, ba Dada ba hatta yaran sai da suka tsaya kallon Bappah da wata irin matsanancin mamaki, Dada ta fara tafe hannu ta fashe da kuka ta ce
"Sai yanzu na fahimci abin dake faruwa, sai yanzu na gano bakin zaren, haba Ni dama nasan wannan ba halinsa bane" ko da wasa Umma bata juyo ba, Mama ta miƙe tana tsaki ta ce
"Toh sai me? Aikin banza" Tana kallon yaran nata ta ce "Dalla ku tashi muje mu karasa abin da zai kawo mana kuɗi" har zasu fara tafiya sai kuma ta tsaya tana kallon Bappah ta ce
"Kai Malam, tashi ka wuce ciki kaje kayi baccin safen ka, dan wannan rikicacciyar Uwarta ka sai a hankali" Dada ta gwale ido, tsumtsum Bappah ya miƙe ya wuce ɗakinsa, Dada tana kallon Zahra ta miƙe ta ce
"Gobe dole na koma gida, dole na shiga cikin daji neman magani, ina raya ba za'a kassara min ɗa ba" Mama da har ta karasa gaban murhu jiyo abinda Dada ta ce sai da gabanta ya faɗi amma ta dake, samun kanta tayi ta gagara karasa aikin, tana kallon su Siyama ta ce
"Ku, ku zoku karasa dukka aikin nan" daga haka ta shige cikin ɗakinta. Umma dake kan tabarma ta miƙe ta wuce ɗakinta, tuni Dada tabi bayanta haka duk suka wase banda su Siyama da suka cigaba da aikin su
Azrah data kwanta kan katifarta tana kallon ceiling Zahra ta shigo daga dakin Umma, tana kallon Azrah ta ce
"Yaya, tabbasa akwai abin dake bayan labule da ake ɓoye mana, kuma koma menene yana da la'akari da Bappah da Umma kuma" Azrah ta sauke ajiyar zuciya tana kallon Zahra ta ce
"Zahra koma menene muyi hakuri har sai sanda Umma taji comfortable za ta faɗa mana, amma na roke ki mu daina ganin hakan" Zahra ta gyaɗa kai ta zauna, sai ga Dada ta shigo tana share hawayenta.
Umma ta saka kanta jikin bango ta lumshe ido tana jin wani hawaye me zafi, ita bata so maganar sakar Mama ba, amma ai itama mutunce kuma tabbas tana bukatar farin ciki itama ai.
Mama ta kira wata Yayarta a waya, tana ɗaga wa ta ce
"Baki san me ke faruwa ba, kina jin wannan shegiyar kakar yaran nan wai dan Malam baya kula shegiyar Matar can shine harda cewa sai ya sake Ni" a ɗayan ɓangaren a razane ta ce
"Se kuma ya sake ki ɗin?" Mama ta ce
"Toh yama isa ne? A gabanta ya nuna shi ba zai iya ba, shine na kira ki yanzun ai sabo kuma zama bai kama Ni ba dan cewa take gobe zata koma gidanta zata wuce daji dan neman magani wai, kiji min lukutar masifa da rikicacciyar tsohuwar nan" tsaki ta ja ta ce
"Ai tunda har ta iya buɗe baki ta faɗi abin da zata yi ai Shikenan, tana tafiya muma zamu je a ɗora inda aka tsaya, idan ta tafi ba zata ma ta kara tako garin nan har ta mutu, ba Shikenan ba" cike da murna Mama ta ce
"Yauwa! Ai kuwa hakan shine, idan tasan wata bata san wata ba" a haka suka yi sallama.
Washe gari duk dangi da abokan arziki suka dinga zuwa ganin gidan amarya, musamman wanda suke nesa duk sunzo sun sake mata fatan Alkhairi sannan duk suka tafi, gida ya watse daga Deen sai Samiransa, tana kwance jikinsa tana trying numbern Azrah ta sake ji a kashe, Deen dake shafa fuskarta ya ce
"Baby har yanzu baki same ta bane?" Ta gyaɗa masa kai ta ce
"Duk na damu, tun jiya fah nake kiran nata a kashe ban san ko jikin nata bane, ga wayar Umman ma a kashe" ya ce
"In shaa Allah ba jikin nata bane, ki kwantar da hankalinki tana kunna wayan nasa definitely zata kira" kai kawai ta gyaɗa masa.
Da yamma suna zaune duk a sakar gidan, suna ɗan hirarsu, wanda Dada tayi hakan ne saboda a ɗauke wa Umma tunanin data wuni tana yi, Zahra ta ce
"Ni kam ba zaki kunna wayan ki bane? Tun fah jiya a kashe, kuma kin san cewa Samira zata iya neman ki fah?" Azrah ta ce
"Haka ne, ina ji wayar Umma ma akashe yake da yanzu ta kira" Zahra ta wuce ciki ta ɗauko wayan, tana kunnawa kuwa yadda kika san kamar jira yake sai ga message ɗin Khalil, Zahra ta ce
"Gashi message ya shigo inaga ita ce" Azrah ta karɓi wayan tana dubawa, ai kuwa taga Khalil ne, messages ɗin sa sai shigowa suke yana tambaya lafiya tun jiya wayanta a kashe? Last message ɗinsa ne ta kurawa ido
'Idan Mutum ya sauka a Abuja, ina kuma zai nufa? I mean your destination" Zahra ta ce
"Ya Azrah lafiya?" Azrah ta mika mata wayan ta ce
"Ɗan karanta min" Zahra ta karɓi wayan ta karanta mata yadda itama ta karanta, Umma ce ta kalle su ta ce
"Waye ne?" Azrah ta ce
"Khalil ne" Zahra ta riƙe haɓa ta ce
"Laa kar dai ya zo kasar nan ne? Ahab tun jiya kin kama kin kashe waya kila hankalinsa ne ya tashi shiyasa ya zo" Azrah na tunani a ranta ai yace Abbu baya nan shine kuma zai bar aiki ya zo
Umma tayi shiru tana kallon Azrah, Dada ta ce
"Wannan wanda yake son ta kika ce ba'indiyan nan?" Zahra ta ce
"Na ce miki ɗan Egypt fah, karatu ne ya kaisa India" Dada ta gyada kai cike da tunowa ta ce
"Ba shakka haka kika ce" sai kuma ta washe baki tana murmushin ta ce
"Allah Sarki, Ni har naji hankali na ya kwanta da shi"
Azrah na kallon Umma ta ce "Umma me zan ce masa?" Umma ta ce
"Sai ki faɗa masa mana, tunda abin daya bukata kenan"
A take ta shiga masa typing, tana gamawa ta danna send, a take sai ga kiransa ya shigo kamar dama jira ya ke yi, tana ɗaga wa sai data ji yadda ya sauke ajiyar zuciya ya ce
"Habibty Ina next zan shiga?" Ta ce
"Wai kana Nigeria ne yanzu?" Ya ce
"Ba dole ba, na damu tun jiya, Ammah ma ta damu, shiyasa ta ce na zo na neme ki" Azrah ta kalli Umma sai kuma a hankali ta ce
"Toh sai ka karaso" daga haka ta sauke wayan daga kunnenta, Umma na kallonta ta ce
"Ki ciro kuɗi sai a masa abinci Azrah" Zahra ta fara murna zata ga Khalil, dama tasu yazo ɗaya musamman wajen surutu, Dada ta mike ta ce
"Ai har cikin gidan ma ya kamata a nemo masu gyarawa ko da almajirai ne a biya, su share mana shi tass"
#Jiddatulkhayr
08110615256
Episode 62: Beyond the Food
Ko da su Azrah suka dawo daga kasuwa Dada taasa yara sun gama gyara gidan, su datti da abinda be kamata ba duk an cire, hatta wanke wanken da Mama ta tara fam na aikin safenta tasa yaran suka wanke suka ajiye mata a kan barandanta, zuba kayan siyayyar suka yi a gaban Umma, ta ɗauki ledan tana dubawa ko daidai suka siyo, ganin dai dai yasa ta ce
"Bari Ni na ɗaura abincin, ku kuma kuje ku gyara kazar" Zahra ta tsare Umma da Idanu ta ce
"Toh su waɗannan ɗin me zakiyi da su Umma?" Umma ta ce
"Zan haɗa masa Mahshi ne da koshari, nasan zai so sosai, amma idan ba haka ba ina shi ina iya cin abincin nan" Zahra ta ɗan ɓata fuska ta ce
"Toh su ɗin me" Umma ta ce
"Eh lallai har kin manta, ai da kuke kanana sanda muke GRA kan mu dawo nan sometimes nakan muku ai, ko da yake ba lallai ko Azrah ta tuna ba, kina 2 to 3 years lokacin" Zahra tayi shiru sai kuma ta kalli Azrah dan akwai tambayoyi a bakinta, Azrah ta harareta, Zahra ta ce
"Toh ke Umma aina kika koya? Naga dai ke ba me son yawo bane?" Umma ta kalle ta sai kuma ta rasa abin cewa, Azrah ta ce
"Ke dalla tashi mu je mu ɗaura, kin san dai Abuja to Katsina a jirgin yanzu zaki ji yace sunyi landing" Azrah ta kare maganar tana ɗagota, Zahra ta ce
"Tsaya mana Umma ta bani amsar tambaya ta" Azrah ta ce
"Abinci kam ai duk wanda kake son koya zaka koya yadda ake watsa su a YouTube, wani recipe ɗinma sai ki ɗauka a china aka kirkira" daga haka Zahra ta miƙe, Umma ta sauke ajiyar zuciya
Mama dake zaune duk a dagule take har idonta ya tsoma jaa Yayar nata ta ce
"Yanzu kuma damuwar ta menene ne? Ke ma kin san wannan wanda ya miki aiki karshe ba irin na Maman Asabe bane wanda kwana biyu zai lalace, Ni banga ma amfanin zuwan naki bama tun da har munyi magana" Mama na kallonta ta ce
"Ke ma kin san wancan tsohuwar ta saba ɓata min aiki ne, damuwata mu rigata tafiya, kar taje ta ɓata komai ne" wani dariya ta yi, ta ce
"Har kina tunanin zata rigamu tafiya? Ko ce miki daga nan zuwa neman mafita zata yi? Ai dole gida zata fara nufa kafin ma koma menene" Mama ta sauke ajiyar zuciya ta ce
"Yadda kika san na shake ta, a gaba na Ni da Yaranta take cewa sai ya sake Ni? Ai kuwa tunda taso raba mu nima sai na rabata da shi kuma har abada" ta ce
"Yauwa, ko kefa? Amma kin wani lakabawa kan ki damuwa? Ki ware kije ki cigaba da harkokinki, kima daina zaman ɗaki kamar wata matsoraciya dan bamu gada hakan ba" murmushin Mugunta ta fara yi....
Message ne ya shigo wayan Azrah, Dada ta ɗauki wayan ta bita kitchen da shi wanda sun ma kusa kammala komai, ta ce
"Ungo Azrah, naji wayan ne yayi ƙara nace ko shine" Azrah ta karɓi wayan, buɗe message ɗin tayi taga shine, kallon Zahra tayi wanda ta tsare ta da idanu ta ce
"Meye ne?" Azrah ta ce
"Cewa yayi yana kirana bata shiga gashi kuma sun sauka, na zura masa map location" Zahra tayi dariya ta karɓe wayan daga hannun Azrah tana sliding ta ce
"Tun ɗazu nake lura da ke, gaba ɗaya kamar wacca ke tsoro" shiga Whatsapp tayi ta tura masa sannan ta ajiye wayan ta ce
"Yanzu zai karaso, je kiyi wanka zan karasa tattare wajen" jiki a sanyeye Azrah ta miƙe sannan ta wuce ɗaki ta ɗauki set ɗin wankanta ta wuce ban ɗaki, tana fitowa ta sanya wani palazzo dinta da blouse daya taɓa cewa ta masa kyau a ciki, harda shafa lipstick, Umma ma already ta gama abinci kala biyun data dafa, wani warmern Azrah me shegen kyau Zahra ta ɗauko a cikin kayan taro, yaga kwallin tayi tana miƙawa Umma ta ce
"Umma saka a nan" Umma tayi shiru tana kallon Zahra sai kuma ta karɓa ta saka, kafin kace me sun gama komai harda tattara wajen
Tun da bolt ɗin daya ɗauka suka bi layin unguwar yake ta bin gidajen da yaran unguwar suke wasa a waje, ga yara barkace wasu babu takalma wasu duk jikinsu fututu dai, shi dai abin ya koma masa kamar Tv yana mamakin kuma suma waɗannan da iyayensu, ga yaran yawancin su baka ke ne, tunani ya fara toh anya ba ɓatar hanya suka yi ba, shi dai sanin fatar Azrah da mutanen unguwar be masa iri ɗaya ba, a daidai kofar gidan suka tsaya
Zahra na kallon Dada ta ce
"Idan ba naji karar tsayuwar mota ba"
Azrah ta lumshe ido jin yadda zuciyarta yake bugawa kamar zai fashe, wayanta ne ya fara ringing ta gagagra motsi, Dada ta ce
"Ikon Allah, ko baki ji ana kiran ki ne" Zahra tayi dariya ta ce
"Ina ga tsoro take ji" Dada ta ce "kamar ba'a waye kike ba? Nikam wannan kauyancin naki ko zamanin mu ba'a yi shi ba, munafuka sai kace a India ɗin haka kike yi" Tuni Zahra tayi picking call ɗin, jin yace mata ya iso ne yasa ta miƙe ta ce
"Toh yana kofar gida wai" daga haka ta nufi waje
Ganin bolt yasa ta karasa wajen tana dariya, ganinta ya kai hannu zai buɗe ta rigasa buɗewa, dan yana ganinta yaga Azrah kawai Zahra bata da hasken Azrah ne, matsa baya tayi ya samu ya sauka, tana murmushi ta ce
"Welcome to Nigeria, my brother-in-law to be! Be ready oh, we don't only serve food, we serve drama too, with love of course!" Dariya yayi ya ce
"Zahra, ba zaki taɓa canzawa ba wallahi. Har yanzu kina da wannan sharp mouth ɗin, amma I like it!" Ware ido tayi ta ce
"To ai ba haka kawai ake so na ba, wannan sharp mouth da ka ce shiyasa kowa small thing zai ce Zahra" ta kare maganar tana dariya tana gaba yana binta a baya, ya ce
"Haka ne, amma duk wanda ya so ki sai ya shirya da spicy attitude!" Juyowa tayi ta kalle sa, sai kuma tayi dariya, bayan sun shiga cikin gidan, Inda suka gyara masa a compound ɗin nan ta ajiye sa, sannan ta wuce cikin ɗakin Umma
Tana kallon Dada ta ce
"Na barsa inda aka gyara masa, zai shigo ai ya gaishe ku ba?" Dada ta ce
"Eh, zai iya shigowa" Azrah ta miƙe ta wuce ɗakin su da wuri, Dada ta bita da kallo tace
"Ji wani munafurci" Zahra ta kwashe da dariya sai kuma ta fita, tana kallon Khalil ta ce
"Bari ka gaisa da su Umman mu" ya ce
"Ya jikin Azrah?" Zahra ta ce
"Ta samu sauki fah, tana ciki ai" ya miƙe ya bita zuwa ciki, da sallama ta shiga, yana biye da ita a baya, sallama yayi wanda hakan yasa zuciyar Umma bugawa jin muryansa a zahiri, da sauri ta ɗaga kanta tana kallonsa har ya zuwa, gaida Dada yayi wanda duk gaisuwar nasu ma kame kame ne dan Dada dai ba wani turanci take ji ba, shi kuma ba Hausa yake ji ba, Zahra ce ke faɗa mata abinda yake cewa sai ta amsa da murmushi, bakinta dai ya kasa rufuwa ganin Khalil, ya juyo da kallonsa ga Umma wanda ita kuma da sauri ta sauke idonta daga Kallonsa, sai daya ɗan tsaya yana kallonta sannan ya gaisheta, Umma ta amsa masa da fara'a, shi kuma kawai ya samu hira, sai ba Umma labari yake ita kuma tana kakkauce masa, ya ce
"Umma Nikam ainahin ki 'yar nan ne?" ba tare da Umma ta kalle sa ba ta ce
"Eh" ya ce
"But Umma duk generation ɗinki babu wanda ya haɗa dangi da 'yan Egypt" Umma ta ɗan kalle sa, dan bata san dalilin daya sa ya tsare ta da waɗannan tambayoyin ba, Dada jin ya ambaci Egypt yasa ya washe baki tana kallon Zahra ta ce
"Me yake cewa wai?" Zahra ta ce "labarin hanya da ya biyo yake bata" Dada ta ce
"Ai ho, na ɗauka ai wani abun ne" Umma kuma ganin Khalil zai sa mata magana a baki ba shiri ya sa ta ce
"Son, kaje kaci abinci, nasan ka gaji" yana kallon Zahra kansa tsaye ya ce
"Ina take?" Zahra ta ce
"Muje kaci abinci yanzu zata fito" daga haka ya miƙe ya fita Zahra na binsa a baya, wani ajiyar zuciya Umma ta sauke
Bayan ya zauna, Zarah tace masa tana zuwa, ɗakin su ta shiga tana kallon Azrah dake zaune tayi tagumi ta ce
"Tunda ba zaki fito ba yace zai koma yanzu" tun kafin ta gama rufe bakinta sai ga Azrah ta miƙe tsaye tana hararan Zahra, hanyar fita tayi ba tare data ko kalleta ba, tazo ta wuce su Dada
Tun da Azrah ta sauke kafarta daga kan baranda ya zuba mata idanunsa, har ta karasaso wajen ba ɗauke ba, zama tayi cikin sanyin muryanta ta ce
"Sannu da zuwa, ya hanya? Ya ce
"Saura kiris Nima ambulance ta kwashe Ni zuwa asibiti, Haba Habibty" dariya tayi ta ce
"Yanzu mawa ka bar masa kula da Companyn Abbu?" A takaice ya ce
"Cousin" ta ce
"But why?" Ya ce
"Kina tunanin a yadda nayi ta kiranki wayan ki a kashe hankalina zai iya kwanciya? Ai ganin damuwar ne Ammah ta ce Nazo na duba ko lafiya" ta ce
"Da ban kunna waya ta ba fah? Ya zaka yi da ka iso Abuja?" Yayi shiru na some seconds sai kuma ya ce
"Wani alternative zan nema, ai tunda akwai history ɗinki a media nan zan shiga nace a faɗa mini wani state kike, daga nan kuma nasan komai zai zo da sauki" ta sauke idonta daga kallonsa ta ce
"Thank you so much, Amma nasa ka bar aikin ka" ya ce "Shiiitttt bana son jin komai" daga haka tayi shiru
Zahra ce ta ajiye masa kyawawan warmers a gabansa, zata miƙe Azrah ta riƙe ta, hakan yasa ta ɗan zauna, Khalil na kallon ta ya ce
"Ai a koshe nake Zahra" Zahra ta ɓata rai ta ce
"Yanzu zanje nace wa Umma duk wahalan data yi a banza kace ba zaka ci ba" da sauri ya tare ta yace
"No please, I didn't mean so, zan ci" Zahra na murmushi kawai
Azrah ta muɗe masa warmers ɗin tana Kallonsa ta ce
"Wanne zan fara zuba maka a ciki ko dukka?"
Khalil was super shocked daya ga abinci dake cikin warmers ɗin, Mahshi da koshari and it's his fav, ko a can Egypt abinda Ammah take dafa masa kenan bai san sanda ya ce mata both, Zahra ta miƙe zuwa ciki ta ce tana zuwa, while ita tayi hakan ne dan bata son ta sa Khalil ya zama not comfortable
Bayan Azrah tayi serving dinsa, kazan da ita tayi ne kawai bai ci ba amma Mahshi da koshari kam yaci ba kaɗan ba, bayan yasha bottle watern dake gefe ya juya yana kallon Azrah with full attention ya ce
"Wait.. aina kuka tsaya? Dama ana kawo Egyptian Foods ne nan?" Yayi tambayar ne dan jin yadda aka dafa haka yake so, ko Inteesar ce ta dafa baya ci idan ba Ammah ba, amma sai wannan ya basa mamaki, Azrah tayi dariya ta ce
"Nope, Umma ce ta dafa da kanta" Kallon Azrah ya dinga yi ba kyaftawa sai kuma ya ce
"Please Azrah aina Umma ta iya? Or ko kuna da dangantaka ne da mu?" Azrah ta dinga kallon sa sai kuma ta ce
"Gaskiya ban san inda ta koya ba, amma kamar ya muna da alaka da ku?" Ya ce
"Kema kin sani, tun farkon haɗuwar mu na sha ce miki idanunki yana min kama da Granny na, yadda kike wasu abubuwan naki like her, but sai nace maybe resemblance ne, amma yanzu dana ga Umma like na fara wasu tunani" Azrah ta ce
"Toh gaskiya mukam bamu da wani alaka da ku, duk da yadda mutanen unguwar nan suke mana lakani da cewa mu biracial ne, while maybe sunga hasken namu ne dan both Umman mu da Bappah Fulanin nan Katsina ne, kuma kasan Fulani kyawawa toh Maybe dan mu mun haɗa both parents din ne nake ji" Khalil ya girgiza mata kai ya ce
"Akwai abun da zaki ɓoye min ne Azrah?" Azrah da rashin fahimta ta ce "kamar Yaya kenan? Gaskiyar abin da nasani ne kuma haka umma ta faɗa mana" yayi shiru yana ture wannan banzan tunanin daya fara amma ina other hand zai so hakan ta kasance, ganin yana yin sa yasa Azrah ta ce
"Ya su Ammah da Intisar?" Ya ce
"Suna gaishe ki, zan haɗa ku ai, itama ta damu, kusan kullum sai ta min maganarki" ya ciro wayarsa a aljihun zaiyi dialing..
Mama ta shigo gidan da sallama a bakinta tana jin katso 90 na damuwarta yanzu babu, sallamar ne ta tsaya a bakinta sakamakon tozali da Azrah da Khalil, kifta idanunta tayi still kuma bata ɗauke idanunnata ba, Azrah ta ɓata fuska ganin kallon ƙurallan da take musu, Mama da tsantsan mamaki take kallon su, wanda har ta shigo tsakiyar gidan bata sani ba, kuma ta gagara ɗauke kanta a kansu, wannan idanun nata mai kyaifi ta zuba musu, shi kansa Khalil sai daya ji kallon nata har ɓargon jikinsa
Sauke nasa idon yayi kasa sannan ya gaishe ta, ɗauke kallonta tayi a kansa tana kallon Azrah da wani matsiyacin kallo, hakan yasa Azrah ta gagara cewa komai, ɗakinta ta wuce direct
Tana shiga ta zube kan kafafunta ta daura hannu aka ta ce
"Na shiga Uku, kar de saurayin Yarinyar nan ne" kawai ta fashe da kuka ta fara share hawayen ta ce
"Ni shikenan, ace sai irin wadannan ne zasu ke zuwa wajen yarinyar nan, kai Inaaa wannan ba me yiwa bane" kamar wanda aka tsikara kuma ta miƙe ta zauna ta sake fashewa da wani kukan..
Azrah ta sauke idonta kasa ta ce
"Kayi hakuri" yana murmushi ya ce
"For?" Ta ce "reaction ɗinta mana" ya ce
"Ohh, nikam banga komai ba, is she ur Aunt?" Kai ta girgiza masa ta ce
"My stepmom" daga haka bai sake cewa komai ba, dialing numbern Ammah yayi yana fara ringing ta ɗaga kiran, ya miƙawa Azrah wayan

Episode 63: Beyond the Threshold
Azrah ta miƙe tsaye ganin shima ya tashi kamar zata yi kuka ta ce
"Ba zaka bari sai gobe ba?" Dariya yayi ya ce
"Zan bi ta Lagos ma akwai wani abokin Abbu acan zan tsaya akwai wani deal da zamuyi ne" ta ce
"Pleaseeee, ka ga sai gobe mu tafi gidan Samira ka mata congratulations ko?" Dariya yayi ya ce
"Haba mana, Ni da zan dawo soon, ai Abbu na zuwa dole zaku gansa anan saboda maganar mu" kauda kai tayi, tayi dialing numbern Samira, Samira dake kwance tana chatting taga wayan Azrah, ɗagawa tayi ta ce
"Ai Azrah kin kyauta, ina Ni zaki wulakanta, kuma dan wulakanci ki ki kunna wayanki" Azrah ta ce
"Easy Madam, kema kinsan dan banda lafiya ne, bari za'a miki murnan aure" Samira ta taɓe baki ta ce
"Who?" Azrah ta ce
"Zaki ji da kunnan ki" daga haka ta miƙa ma Khalil, yana karɓa ya ce
"Hey, Samira" Samira dake kwance ta miƙe zaune da sauri ta ce
"Oh my God, don't tell me Kai ne Ya Khalil?" Dariya yayi ya ce
"Yes" daga haka ya mata fatan zaman lafiya, Samira ta masa godiya ta ce
"Chap, wato bata da lafiya shine ka zo ko?" Ya ce
"Ai it's must, Samira" daga haka suka yi sallama, Azrah ta karasa da shi ɗakin su Umma nan yayi musu sallama tare da Dada, Zahra ta fito tana dariya, ta ce
"Au, ai Ni na ɗauka sati guda zaka mata, ashe ma ba sonta kake yi ba" dariya yayi ya ce
"Ina addu'ar ranan da Allah zai cire miki wannan tsokanar naki" ta ce
"Nahhh! Kar kamin wannan addu'ar, barni da kayana" daga haka suka raka sa har jikin bolt ɗin, Azrah ta fara kuka, me Zarah zata yi banda dariya shi kuma duk ya birkice ya fara bata hakuri, Zarah na kallon Khalil ta ce
"Kasan me?" Ya girgiza mata kai, ta ce
"Ka shiga ciki kawai, kaga jikin wancan ginin ko?" Ya gyaɗa mata kai, ta ce
"Toh masallaci ne, yanzun nan zan je na kira maka Bappahn mu sai aje a ɗaura muku aure kawai ka tafi da ita Egypt ɗin yanzu tunda ta gaji da kallon mu kuma kuka take zata bika" har ta gama maganar Azrah bata ɗauke idonta akan Zahra ba, Khalil yana kallonta ya ce
"Yes, please! Bari na kira Ammah, zaki fara wa su Umma magana ne?" Zahra ta fashe da dariya ganin fah shi da gaske ya ɗauka take nufi, Azrah tayi saurin kwace wayarsa ganin har zaiyi dialing numbern Ammah ta ce
"Kai baka san halin Zahra bane? Sai kuma ka biye mata Please" ya langwaɓar da kai ya ce
"But at least ai ta kawo way out ne, please ayi hakan" ya kare maganar kamar zai mata kuka, ta ce
"Chap, I'm not ready for this now.." Zahra ta katse ta ta ce
"Amma ai kinsan ki masa kuka dan zai tafi ai" Azrah ta harareta, ta mayar da kallonta ga Khalil ta ce
"Safe flight" ya ce
"Wait.. amma ai bamu gama magana ba" ta ce
"Ka tafi dan wannan shawarar Zahra ba zai yi working ba"
Siyama da Habibah ne suka nufu su, tun daga nesa suke kallon motar har suka matso kusa
Azrah dake masa murmushi ta juya zata shiga gida, kallo ɗaya tama su Siyama ta ɗauke kanta ta shige, Zahra zata shige ya dakatar da ita, wai gift box ya mika mata ya ce
"Wannan na sistern ki" ya mika mata ɗayan ya ce "wannan naki ne" and this ya mika mata wani envelope ya ce "Na Umma and Jiddah" Azrah ta tsaya kallonsa da rashin fahimta sai kuma ya ce
"Ohh I mean Granny, kin san haka mu muke kiran GrandMa ɗin mu" ta ce
"Ohh, haka fah, ashe fassaran sa da Arabic kenan" murmushi ya mata, ta dinga masa godiya sannan ta shige cikin gidan tana murna
"Mama wallahi baki gansa bane, ɗan kasa waje ne fah, na shiga uku kullum samarin arziki sai dai wajenta zasu dinga zuwa Ni Siyama" Mama ta mata tsawa ta ce
"Shegiya ki rabu da Ni, naji da wanda yake damu na, ce miki nayi zan hakura harta aure sa?" Habibah ta ce
"Kamar mu kam bamu da Sa'a ne su fah kyawawa masu kuɗi kuma suke zuwa musu" Mama ta buge bakinta ta ce
"Shegiya dakikiya kawai, nace muku ku zuba ido ku gani, daga yau ya bar zuwa kenan, ce muku aka yi haka kawai honorable ya daina zuwa? Lallai ne ma"
Siyama ta ce "Mama Ni ai na yarda da maganar ki, dan wancan ma haka kika ce, toh yanzu kuma sai ki janye bakinki kar kuma ki sake cewa Bappah ta fito da miji tunda ba rasawa suke yi ba" Mama ta ce
"Ai yanzu kam ba zan kuma faɗan hakan ba" hijabin jikinta data zo dashi ko cirewa bata yi ba ta kuma sake miƙe wa ta nufi kofa gida da shi...
Umma na kallon Zahra ta ce
"Ke kuma saboda baki da hankali yana mika miki sai ki karɓa?" Zahra ta ce
"Toh Umma sai nace masa A'a ? Ai dan mu ya tsiyo, toh me ma zaiyi da shi Fisabilillah?" Dada ta ce
"Kyaleta, haka dama take, idan ita bata so ai Shikenan amma me anfanin maida hannun kyauta baya? Ai wannan ba koyarwar Annabi bane" Zahra ta ce
"Ah toh" Dada ta ce
"Nikam raba mana kuɗin me sunana, dama tafiya a gaba na da neman magana kamar yasan ina neman kudi kuwa, kai Allah masa Albarka" Umma na kallon Zahra ta ce
"Bata kudin dukkan kawai Zahra" Zahra ta ce
"Kai Umma saboda me toh?" Umma ta ce
"Magani zata je nema, kuma nasan babu kuɗi sosai a wajenta" Dada ta washe baki ta ce
"Amma dai ba'ayi haka ba, raba shi gida uku sai ki bani biyu" duk yadda Umma taki karba sai da Dada tasa aka bata, Zahra kuwa nata gifts ɗin expensive Egyptian Abaya ne, haka Azrah sai dai nata a haɗe da cosmetics..
Yana kallon Ogan nasa ya ce
"Sir, an samo min duk wani bayane akan yarinyar, amma yau wajen 2days kenan nake nemanta amma bana samunta" yana kallonsa ya ce
"Kuma ka tabbatar babu wani abu da ba daidai bane a info ɗin? Ya ce
"Sir, na tabbata komai daidai ne, harta unguwar data ke da zama na sani yanzu" yana kallonsa ya ce
"If so, why not ka tafi har gidan su mana, ka kai mata request ɗin mu, ina ga hakan zai fi" yana kallon sa cike da girmamawa ya ce
"Toh Shikenan, hakan kuwa za'a yi ranka shi daɗe"...
Mama tana zaune dirshen a gabanta ta ce
"Ina komawa naga yaron, baki ga soyayyarta dana gani a Idanunsa ba, nashiga uku Ni Uwani! Yanzu da raina zan lamunci wani harya raɓe Azrah?" duk maganganun da take yi cikin kuka ne
Ta ce "Ni matsalata dake gajan hakuri, banga amfanin juyowa da kika yi ba, balle har ki tsaya kuka, tunda kin san cewa zan mu tafi ai dole zamu haɗu duk sai ki faɗa masa damuwar naki"
Mama ta ce "gaskiya daga yanzu ma bana bukatar naga wasu na zuwa wajenta, bakin jini zan sa a saka mata sannan karta auru ta dauwama a haka" Yayarta Hajiya kaltume tayi dariya me isarta ta ce
"Ni bansan me yasa ba kinfi kishi da 'yar fiye da Uwarta" Mama ta ce
"Hmm.. ba zaki gane bane, na tsane ta ne, kuma Kinga yadda tauraronta ke haskawa yanzu sai tayi kudi ko ta auri me kuɗi ta taimake Uwar nata kuma" dariya Hajiya kaltume tayi,
Mama ta ce "Hmm.. Ni bana fatan ma wani yazo wajanta, yawo nake so ta fara ta zama annoba a gari, idan har zata san namiji toh ɗan-iska knn" duk dariya suka kwashe da shi...
Da Daddare suna dinner duk waje ɗaya, Umma tana kallon Azrah ta ce
"Ɗazu fah a radiyo naji ana sanarwa next week za'a fara registration ɗin Jamb, kuma naga kin yi maganar kanwarki ranan" Azrah ta ce
"Yauwa, toh Allah kaimu lokacin" tana kallon Zahra ta ce
"Sai ki zama alert kafin nan, ana buɗewa kuwa In Shaa Allah zamu tafi, amma yanzu naji ba sai kinyi Umar Musa Yar'adua, kawai ki tafi Al-qalaam" Umma ta ce
"Meyasa kuma?" Azrah ta ce
"Saboda ta samu ta gama da wuri Umma" Umma tayi shiru, Zahra ta washe baki ta ce
"Yesss.. kenan za'a tsaya mini sabuwar waya da sim ko?" Umma ta ce
"Ba'a sani ba" dariya Azrah ta mata, Umma ta maida dubanta kan Azrah ta ce
"Ke kuma fah?" Azrah da rashin fahimta ta ce
"Bangane ba kuma Umma?" Umma ta ce
"Maganar inda zaki yi service mana, naga baki maganar ne yanzu" Azrah ta sauke ajiyar zuciya ta ce
"Bari gobe idan muka tafi gidan Samira, idan zamu dawo muka tsaya katsuwa muka ma Dada sayayyan komawa, jibi kuma idan muka rakata tasha daga can zan duba organization da zan yi" Umma ta ce
"Toh ko zaki yi a Organization din Baban su Suhaila ne" Azrah tayi shiru tunawa da Saif yasa jikinta yin sanyi, ji take ta tsane sa da sauri ta cewa Umma
"A'a Umma, zan nema wani wajen"...
Bayan sun gama shirin bacci, Azrah ta ɗauki wayanta ta shiga chat ɗinta da Khalil, long appreation message ta tura masa, ji take idan zuciyar ta ya daina son Khalil bai mata adalci ba, da tunanin sa bacci ya kwashe ta..
Washe gari... Bayan su Azrah sun gama karyawa sun yi duk wani aiki sannan Azrah ta shiga wanka, tana fitowa Zahra ta shiga, kafin Zahra ta fito tuni har Azrah ta gama shiri, ɗakin Umma ta wuce suka fara hira, Dada ta ce
"Nikam ya Khalil ne? Kin masa maganar ya turo ɗin" Azrah ta ɓata rai ta turo baki ta ce
"Ni ki daina min maganar nan" Dada ta sake baki tana kallonta ta ce
"Ai kuwa baki isa ba, bari na gama da abin gaba na haka zan sa duk sai kun fito dashi ku bar gidan nan, da haka za'a zuba muku ido wai?" Azrah ta ce
"Toh Nikam baki ganin Ni yarinya ce, kawai dan na gama degree da wuri shikenan?" Dada ta fara salati tana tafe hannu, Umma murmushi tayi kawai,Dada ta ce
"Ubanki toh, ki tambayi ita Ummar naki duk da a waye take da karatunta kuma amma Bappahn ku ya aurota tana shekara sha bakwai 17 yrs, amma ke yanzu da kika kai 20 kina da bakin magana" Zahra data gama shiryawa ne itama ta shigo tana kallon Dada ta ce
"Tama fi 20yrs Dada" Azrah ta ce "ina ruwanki " Zahra ta ce
"Wai a taimaka miki ne fah, naga kamar baki son Khalil yayi nisa da ke e" Azrah ta san next move ɗin Zahra so take ta tona mata asiri ta mike ta ce
"Mu tafi Zahra" tana kallon su Umma ta ce
"Sai mun dawo" Dada ta ce
"Zaki je ki dawo ai, nasan maganin ki" bata kulata ba suka fita
Azrah suka tsaya a house numbern da Samira ta faɗa musu, knocking gate ɗin suka yi, gatekeeper ya leƙo ya ce
"Wa kuke nema?" Azrah ta ce "wajen Amarya muka zo, kawarta ce" buɗe musu gate ɗin yayi suka shiga, Innalillahi kyaun gidan ba komai bane ta waje, compound ɗin kaɗai abin ka tsaya kayi ta kallo ne, suka karasa entrance ɗin, dake First door ɗin glass door ne yasa Azrah kiranta a waya, sai ga Samira ta fito da murmushi a fuskan, tana buɗewa ta rungume Azrah a jikinta tana dariya ta ce
"Allah sarki kawata, har kin rame" kama hannun Zahra da Azrah tayi suka shiga cikin parlorn, gani suke anya a Katsina suke? Sai ka rantse wannan parlon a wata kasar take, bayan sun gaisa Azrah ta ce
"Kai Samira gidan ki kam har ya gaji da kyau, Allah dauwamar dake, mutu karaba In Shaa Allah'' Samira tayi murmushi ta ce
"In shaa Allah naki sai yafi wannan Azrah, ina miki fatan hakan tun ba yau ba" Azrah tayi murmushi, Samira ta harareta ta ce
"Amin zaki ce, ko kawai koma wa kika samu aura zaki yi" Azrah tayi dariya ta ce
"Kema ai kinsan cewa ina da burin idan nayi aure na huta, ko ban aure mai kuɗi ba at least zanyi aiki bana son yarana suyi wahalan dana yi Samira" Samira ta ce
"Good, balle ma mai kuɗin ne" daga haka ta mike taje ta kawo musu su snacks da ruwa ta zauna tana kallon Azrah ta ce
"Da ace kin faɗa min tun jiya zaki zo ko kuma kafin Deen ya fita yau da na ce masa ya tsaya ku gaisa, yana son sannin wacece wannan Azrahn" Azrah tayi dariya ta ce
"Gidan ki kuma ai gidan zuwa nane wata rana zamu haɗu" Samira ta ce
"Ai kuwa"
Sun daɗe a gidan Samira, wanda har sannan Deen kuma bai zo ba, can suka tafi
Kasuwa suka bi, sai da suka ma Dada tsayayya sosai sannan suka koma gida
Ba Dada ba hatta Umma sai data yi murna ganin irin tsiyayyar da suka mata, Dada kam harda hawayenta tana ta musu addu'a
Da yamma suna zaune suna planing yadda karatun Zahra zai kasance, wani yaro ne yayi sallama a kofar ɗakinsu, Umma ta amsa masa, ya gaishe da Umma sannan ya ce
"Umma ana sallama ne da Anty Azrah a waje" Caraf Azrah ta ce
"Wani kuma? Waye shi ɗin?" Yaron ya ce
"Nima ban san sa ba, tambayar gidan nan yayi da aka nuna masa shine ya ce na shigo na miki magana" Azrah tayi shiru yaron ya ɗaura
"Naga yana kama da masu aikin banki" Azrah ta ce
"Toh fah" Zahra ta ce
"Je kace gata nan zuwa" zata yi magana Umma ta ce
"Ai dole ki fita kiji koma wanene"......
Episode 64: The Unexpected Offer
Jiki a sanyeye ta miƙe, hijabinta ta ɗauka ta saka, sannan ta fita, a compound ko da wasa bata kalli inda Habibah take ba harta fita, tana fita ta dinga kallon motar dake parke, folding hannayenta tayi tana tsaye, a ranta tana ayyana ta basa 30 secs idan bai sauko ba zata koma gida a binta ne, bata gama wannan tunanin ba sai gashi ya sauko, wani direction take kallo ta ɗan juya, ganin ba yaro bane yasa yana karasa wajenta ta gaishe sa, ya amsa da fara'a ya ce
"Miss Azrah, right?" Ta ce
"Yes, sir." Mika mata envelope ɗin hannunsa yayi ya ce
"Muna ta neman ki kwana biyu bamu samunki shiyasa we just decided mu kawo miki har gida" kallonsa take cike da mamaki kuma har sannan taki karɓa ta ce
"I'm sorry to ask.. for?" Ya ce
"Ki karɓa mana, it's request, Ma" Ma daya kirata da shine yasa taji wani, sai kuma ta saka hannu ta karɓa ta ce
"Daga ina kenan?" Ya ce
"Daga Majestic Vaults Ltd" ɗan zaro ido tayi sai kuma tayi saurin composing kanta ta ce
"Okay, Thank you! Zan iya tafiya?" Ya ce
"Yes, duk wani abu da kike bukata na cikin envelope ɗin" daga haka ya juya zuwa wajen motarsa, itama ta shiga gida
Azrah ɗakin Umma ta shiga, duk kallonta suke cike da son jin ba'asi, ta zaune gefen Umma tana cewa:
"Wani Mutum ne Umma, Nima ban san sa na, ya bani wannan envelope ɗin wai it's a request ne ko mema? Ni na manta, amma dai wai zan samu duk wasu bayane a ciki" Umma tayi shiru sannan ta ce
"Ina fatan ba wani abun bane ko? Ni bana son irin abu haka sai a ɗaga maka hankali kana zaman zamanka" Zahra data kagu taga menene a ciki ta ce
"Toh Ya Azrah ki buɗe mana, kila ma wani Alkhairin ne, ko kuma ana nemanki za'a yi hira da ke" Azrah bata ce komai ba a hankali ta fara buɗewa, papern cikin ta ciro, da sauri Zahra ta karasa wajenta ta zauna tana son ganin menene
Wani ƙara Azrah ta saka tana miƙawa Umma papern ba tare data karasa karanta ba ta fashe da kuka, Duk hankalinsu ya tashi, Dada ta fara salati, Zahra tayi saurin karɓe papern tun kafin Umma ta karɓa, Azrah dai ta kafa kanta kan gwiwowinta tana kuka, Zahra tana fara karanta heading ɗin ta fara jin zuciyarta na bugawa, kallon appointment request ne yasa ta ce
"Mtswww, Umma aiki fah suke tambayarta idan zata yi da su, sai ta tuntuɓe su" tana kare maganar ta mika ma Umma papern
Dada ta ja wani dogon tsaki itama ta ce "Haba ai wannan ɗaukar alhaki ne, Ni har yanzu mamakin ki ma nake yi, yadda kike wasu abun sai kace bake ce kika tafi India ɗin ba Zahra ce" Zahra ta fara dariya ta rungume Azrah
Umma ta ce "Alhamdulillah! Allah mun gode maka" sai kuma tana kallon Azrah ta ce "Sai gobe ki tafi har can Companyn, kinga kawai sai kiyi service ɗinki a wajen kawai" Azrah ta ɗago tana share idanunta
Zahra ta ce "Chap! Amma dai Yaya kinyi sa'a, wai Majestic Vaults Ltd ne suke nemanki? Companyn da mutane ke haukan applying amma basu samu, gaskiya Alhamdulillah kawai zamu ce" Azrah ta sake daukan papern tana kara karantawa, Dada kamma haɗe rai tayi dan ba kaɗan ba ta tsorata su.
Da Daddaren.. suka gama haɗawa Dada kayanta waje guda, washe gari da safe kuwa, daga Bappah har Mama ba wanda Dada tayi wa sallama a cikinsu, duk da Umma taso mata maganar amma ganin yadda Dadan ta tamke fuskarta sai yasa ta tsuke bakinta tayi shiru, Zahra da Azrah suka rakata har tasha sai da motar su ta tashi sannan suka dawo gida.
Umma na kallon Azrah cikin kulawa ta ce,
"Tashi kiyi wanka, ki shirya ki tafi Majestic Vaults Ltd. Kar su ɗauka baki da seriousness, su ce maybe baki so"
Azrah ba tare da musu ba ta nufi ɗaki, zuciyarta na wani irin bugawa, ta fito ta nufa bayi ta watsa ruwan, tana jin dumi yana sakar mata gajiya, bayan ta fito, ta shafa shea butter cream ɗinta mai ƙamshi, sannan ta fesa vanilla mist da yake sakata kamshi kullum kamar orchid.
Ta saka riga cream white silk blouse, da high-waist navy blue pants masu kyau, sannan ta ɗora light gold wristwatch da ƙaramin handbag ɗinga mai launin lilac. Ta saka ƙaramin gold earring, ta kama gashinta da ribon, sannan tayi rolling veil navy blue akanta
Ɗakin Umma ta nufa, dama Zahra tana jiran fitowanta ne, da sauri Zahra ta ce
"Eh lallai, ai ko basu yi niyyar baki aiki ba dole zasu baki Yaya, tabb yau kamfanin nasu sai yasan da zuwanki!"
Azrah ta ɗan harare ta, sai ta ce da Umma
"Toh Umma bari na tafi"
Umma ta matso kusa da ita, ta kama hannunta da cike da kauna ta ce
"Allah ya ɗauraki akansu su baki wannan aikin kamar yadda suka buƙata, ki fita lafiya, ki dawo lafiya"
"Ameen, Umma na" Ta amsa da murmushi
Tana fita bakin titi ta nufa, ta tsaya taran abun hawa, Bolt ta gani, ta tsare sa, bayan ya tsaya ta buɗe ta shiga ta ce da driver ɗin
"GRA, Majestic Vaults Ltd" daga haka ya ja motar suka fara tafiya, murmushi tayi a ranta tana mamakin yadda wai yau ita ce take tsaran bolt? A da can baya ko Anty Suhaila da Mummy sun bata kuɗi mota ta gwammaci ta taka da kafa, amma yanzu mashin ɗin ma bata hawansa, hamdalah tayi
Tun da suka shiga GRA taji bugun zuciyarta ya tsananta, ta rasa dalili, kawai ta fara ambaton Allah, a daidai gate ɗin motar ta tsaya, ta sauka tana bin ginin dake ɗaukar ido da tsari, kamar wani financial HQ a kasashen waje, tinted glass walls, lambu mai kyau a wajen gate, da gate mai kyau wanda security personnel biyu ke tsaye.
Ɗayan daga cikinsu ya ce
"Good morning young lady. Who are you here to see?"
Azrah ta ɗan firgita, ta ce
"Uh… actually… I don't know the name. I received a request"
"A request?" ɗayan ya ce da rashin fahimta "From who, exactly?"
Buɗe jakkarta tayi ta zaro envelope ɗin daga ciki, ta mika musu
Da suka karɓa, suka duba stamp da signature da ke jikin, nan take fuskokinsu suka canza, ɗayan ya ce
"Oh, you're the one. Sorry for the questioning, ma'am. Please come in"
Suka buɗe mata gate ɗin cike da girmamawa, suka ɗan taya ta shiga cikin premises ɗin. Ta shige ciki tana bin walkway mai tsabta da kyau da kallo, tafiya take amma kowa kallonta yake yi, ma'aikata, receptionists, har da su cleaners, sai kawai tayi she's not comfortable
Ta tsaya gefe, ta buɗe jakkar ta fito da papern ta ɗauki numbern jikin, ta zaro wayarta, ta yi coping sannan ta shiga dialing...
Ba'a ɗaga ba sai ga wani Muutumin ya karaso wajenta, gaishe sa tayi ya amsa, ya karbi envelope ɗin daga hannunta, kamar wanda aka aiko, sannan ya duba sunanta da rubutun ciki, ya danyi murmushi, ya ce
"Ohh, Miss Azrah ke ce kenan. Office ɗin yana 3rd floor, Room 3B Executive Wing. Come, I'll show you"
Yayi gaba tana binsa a baya, suka isa har wajen lif, ya buɗe mata, bayan lif ɗin ya buɗu, suka shiga tare, har suka hau 3rd floor, yana yi mata kwatancen inda Offices yake"
"Just by the right, bayan small lounge ɗin nan, zaki ga Office ɗin da nake nufi akwai silver label a jikin kofa, 'Executive Manager Investments' "
Azrah ta fito daga lif ɗin tana masa godiya, ta karasa gaban Office ɗin da aka faɗa mafa, tana knocking, daga ciki aka ce
"Come in"
Tana shiga, ta tarar da secretary mace mai fara'a tana kallonta
"Good morning" Azrah ta ce da nutsuwa.
"I'm Azrah… I was invited here, An ce in kawo appointment request"
Secretary ɗin ta duba takardarta sannan ta ce
"Yes, you can come in. You're expected"
Ta buɗe mata ƙofar wani Office mai kamar parlor cikin girmamawa. Azrah ta shiga da ɗan nutsuwa, amma zuciyarta cike da anticipation, a gaban tebur, ta tarar da wani mutum zaune yana duba wasu takardu.
Yana kallonta da murmushi
"Azrah, right?"
Ta ce "Yes, sir"
"Good. Na tabbatar kin gane ni, ko?"
"Yes, I remember" ta amsa da murmushi.
"Mai Company ɗin Mr. Abubakar Alhassan, yana hanya, dama shi ke son ganinki personally"
"Ba damuwa, sir"
Ta zauna a kan kujerar da aka nuna mata, tana gyara veil ɗinta. Bayan ƴan mintuna, ƙofar Office ɗin ta sake buɗewa, wani mutum ya shigo cikin nutsuwa da kwarjini.
Azrah ta miƙe da sauri, ta gaishe shi cikin ladabi ta ce
"Good morning, sir"
Ya amsa da fara'a
"Morning. She's the girl?" ya tambayi PA dinsa.
Ya ce "Yes, sir"
"Great! Come with me" Ya ce da ita, yana shiga cikin babban Office ɗinsa still anan office ɗin
Azrah ta biyo shi, zuciyarta na bugawa da sauri har sannan, bayan ta zauna, ya ce
"Can I see your CV?"
Ta zaro CV daga jakarta, ta mika masa cikin ladabi. Yana dubawa, ya gyara zamansa ya Kalleta ya ce
"So... kina so ki yi aiki da mu?"
"Eh sir. Amma... I just finished camp, I haven't done my NYSC service yet"
Ya ɗago kai yana kallonta da natsuwa
"Ba matsala, you can still work here zaki samu ribar koyo da ƙwarewa a lokaci guda"
Azrah ta ce
"Thank you very much, sir"
Ya ɗanyi murmushi, ya ɗora hannunsa kan takardunta
"Na kalli wasu interview videos dinki da kuma transcript na hirarki da aka yi da ke, gaskiya, I was impressed. Ina jin kamar this company needs someone like you"
Zuciyar Azrah ta sake kara gaba da bugawa, Kamar hawaye zai zubo mata, amma ta daure
Ya ci gaba
"Though yanzu babu vacant office, amma MD yana waje, sai kin zauna a Office ɗinsa na wucin gadi, ke zaki rika masa arrangement. Zaki koyi yadda Company ke tafiya, idan MD ya dawo, you'll officially become his PA"
Ya ɗan ja numfashi sannan ya ce
"Daga nan, zaki rika attending meetings da manyan investors daga ƙasashen waje. I see you as someone who can represent us perfectly"
Azrah ta dafe kirjinta da sauri,ta ce
"Thank you so much, sir. I'm very honored… Really, thank you"
Duk da ta daure ji tayi kamar ta rushe da kuka. Wannan dama ta zo da wuri fiye da yadda ta zata. Amma zuciyarta na jin cewa wannan mataki ne na farko zuwa tafarkin da Allah ya shirya mata...
Yana kallonta da fara'a ya ce
"You're welcome, Miss Azrah. Zaki iya tafiya yanzu, amma ki ce da secretary ta nuna miki Office ɗin MD"
"Okay, sir. Thank you" ta ce cikin ladabi, sannan ta mike.
Tana fita daga parlour ɗin Office ɗin, ta juyo ta kalli PA ɗin ta ce
"Nagode sosai, sir"
Ya daga kai ya ce
"Ba komai. Good luck"
Ta juya zuwa wajen secretary ɗin, tana murmushi ta ce
"Please, zaki iya nuna min Office ɗin MD?"
Secretary ɗin ta ɗan ƙame, sai kuma tayi murmushi ta ce
"Toh... MD baya nan ai"
Azrah ta ce
"Eh, na sani, aka ce can zan zauna kafin ya dawo"
Zato idanu secretary tayi tana kallonta ta ce
"An ɗauke ki ne?" Azrah tayi murmushi
Cikin dan karairaya da jinkiri, secretary ɗin ta miƙe, ta ce
"Toh, come"
Azrah ta lura da yadda fuskar secretary ɗin ta canza, amma bata ce komai ba. Suna tafiya a hankali har suka isa gaban wata ƙofa mai faɗi, secretary ɗin ta nuna kofar ta ce
"This is it"
Ta juya ta bar Azrah, ba tare da wata sallama ba. Azrah ta ɗan kalli bayan ta, sannan ta shiga ciki a hankali. A lokacin, wasu masu gyara da sanitation ne a cikin Office ɗin suna kan share-share da gyaran wajen, amma already sun gama da cikin
Suna ganin Azrah suka ce
"Good afternoon, ma"
"Afternoon, sannu da aiki" ta amsa da girmamawa
Tana shiga ciki, ta zauna a kan kujeran office ɗin cikin natsuwa, ta sauke ajiyar zuciya, sai ta ɗauki wayarta, ta kira Umma.
"Umma... sun karɓe ni fa! Wallahi, kamar mafarki. Mai kamfanin da kansa ne ya bani appointment letter yanzu yanzu"
Zahra ta karɓi wayar da karfi daga Umma, ta ce
"Yessss! Na fada miki! Soon zaki tsaya mota ai" Azrah taja tsaki tana dariya
Umma ma tana murna, tana ta yi mata addu'a, bayan sun gama wayar, Azrah ta ɗan ja numfashi, tana jin kamar tana farkon wani sabon babi na rayuwarta, dialing numbern Khalil tayi, suna gama waya, ta shiga kiran Sarah..
A haka tana zaune har wurin 1:00pm, ta fita neman masallaci. Ta ga wata Christian girl tana tsaye da file, ta tambaye ta
"Excuse me, please… Masallaci fa?"
Yarinyar ta nuna mata hanyar masallacin cikin fara'a. Azrah ta gode mata ta wuce.
Kanta a kasa ta nufi Masallacin, ta lura da yadda wasu ma'aikata ke kallonta da mamaki. Ita ta rasa dalilin daya sa ake kallonta
Bayan an idar da sallah, wasu maza biyu suka zo wucewa kusa da ita, daya daga cikin su ya ce
"New vacant?"
Ta ɗan yi murmushi, ta ce
"Yes"
Ya ce "Welcome"
Ta ce "Thanks"
Dayan ma ya ce
"Sannu da zuwa beautiful" Yana murmushi.
"Na gode" ta amsa
Tana ciki Office ɗin, wata mace ta zo tayi knocking. Azrah ta ɗaga kai, matar ta ce, mai Company yana nemanki
Nan take Azrah ta miƙe, ta gyara veil ɗinta, ta fito tare da bin matar. Suka karasa wani babban Office, wanda aka kawata shi da zane mai kyau da tambarin Majestic Vaults Ltd, nan ta fahimci ashe office ɗin ɗazu bai kai nasa na yanzun ba
Mr. Alhassan ɗin na zaune yana duba wasu takardu, yana ganinta ya miƙa mata wata takarda.
"Ga appointment letter ɗinki, Azrah. Welcome officially"
Ta karɓa da hannu biyu, ta ce
"Thank you very much, sir. I really appreciate this opportunity"
Ya yi mata murmushi ta ce
"I believe you'll do well"
Tana fita daga Office ɗinsa, ta dawo cikin nata,tana shiga Office ɗin MD, ta zauna ta buɗe envelope ɗin. Ganin salary details da position description da allowances ya sa ta zaro ido, tayi ‘yar kara tare da toshe baki
"Subhanallah!"
Sai ta ɗan dafe ƙirji, zuciyarta cike da godiya da kuma mamakin irin wannan gagarumar damar da bata taɓa zato ba… sai kuma tayi saurin yin sujjada..
Episode 65: Friends or More
Tana fito daga office ɗin, har zata tafi ganin Mr. Alhassan yasa ta ɗan tsaya, daya karaso wajenta ya ce
"Toh Miss Azrah sai gobe ko? Akwai rules and regulations zamu baki gobe In Shaa Allah, amma ba'a zuwa mana 8am" ta gyaɗa kai ta ce
"Okay, sir. Thank you"
Juyawa tayi ta nufa wajen stairs, takawa take a hankali harta sauka, bata yarda ta kalli secretary dake gefen stairs tana waya ba, Miss Safiyya ta ja tsaki ganin ta wuce, haka kawai taji ta tsana wannan sabuwar ma'aikaciya ɗin nan, daga haka ta wuce sama
Azrah tana fita, tayi sallama wa security personnel dake zaune bakin gate, a hankali ta fara tafi, wani mota ya tsaya gefenta, ta ɗan kara sauri, taga motar ma ya tsake gaba, ɗan tsayawa tayi ta juya taga waye ne, sauke glass ɗin yayi yana mata murmushi ya ce
"Sister" ganin bata gane sa ba ta ɗan yi jimm, murmushi ya sakar mata ya ce
"Naga kamar ke sabuwar ma'aikaciya ce a wajen mu" kai ta gyaɗa masa, ya ce
"Toh shigo na rage miki hanya, dan nan arean ba lallai ki samu abun hawa da wuri ba" ta girgiza masa kai ta ce
"No need sir, thank you" ganin ba zata shige yace "Alright, good night" daga haka ya kara gaba, Allah ya taimake ta taga wani Napep yazo wuce wa tayi saurin tsayar dashi.
Tana sauka a Napep ɗin ta shige cikin gidan da ɗan saurinta, Umma ta samu ta idar da Sallah ta zauna tana mikawa Umma appointment letter ɗinta, Zahra ta shigo da gudu ta faɗa kanta ta ce
"Yeeeee, my sister" dariya tayi, Umma bayan ta gama karantawa tana kallon Azrah tana kokarin mayar da hawayenta ta ce
"Allah mun gode maka, Allah ka mana komai" Zahra tana kallon Umma ta ce
"Umma menene?" Umma ta girgiza mata kai ta ce "Babu" Azrah ta karbi papern ta mikama Zahra
Zahra ta buɗe baki da sauri tana kallon Yayar nata ta ce "Ni fah dan Allah Yaya ki tsiya mana mota, ai ko kuɗin account ɗinki ya kare naga na aikin ki zai taru" Umma ta ce
"Ke baki da damuwa sai asiya mota Zahra?" Zahra ta ce
"Eh mana Umma, wlh so nake ina shiga idan zan tafi wani wajen" Azrah ta ce
"Zamu tsiya kuma ki shiga Zahra, amma ba yanzu ba, yanzu maganar makarantar ki ne a gaba"...
Bayan ta idar da Sallah Zahra ta kawo mata abinci, tana ci tana basu labarin yadda wajen yake, wayanta ne yake ringing, ɗauka tayi ganin Suhaila yasa tayi receiving takai kunne tare da cewa
"Hello.. Anty Suhaila". Bayan sun gama wayan tana kallon Umma ta ce
"Umma Anty Suhaila ce 'yar Mummy, wai idan bana wani abu dan Allah na tafi gobe gidansu" Umma ta ce
"Allah sarki, Toh ya zaki yi da aikin naki kuma?" Ta ce
"Idan na taso daga aikin sai na tafi Umma, ko?" Umma ta ce "Toh Allah kai mu"...
Ita kaɗai take zaune cikin Maza uku dake zaune a cikin parlorn nata, hira suke cike da nishaɗi, banda dariya ba abinda suke, kana ganinsu kasan suna enjoying moment ɗinsu, ga abinci da su drinks da suke ci suke sha,Farouk ya ce
"Kai Samira, kice kina kashe mijinki da girki masu daɗi haka?" dariya tayi ta ce
"Wai kai baka taɓa cin girki na bane sai yau? Kai Farouk fear Allah" duk dariya suka yi, Ahmad ya ce
"Kila dai bai taɓa bane, ko kuma tsanti yake yi, amma girki kam sai dai mijinki yayi hakuri haka wata rana zamu kwashe jiki muzo muci" suka sake dariya ta ce
"Ai sai ka biya Ni, amma haka kawai ba zaku sakani wahala ba, shima mijin nawa wata rana fita muke mu ci" Ahmad ya ce
"Kai Samira, amma ance baƙon ka annabinka fah" ta ce
"Sai ka kawo matarka na koya mata idan har da gaske kake" karan buɗe gate suka ji, Aliyu da tun ɗazu bai ce komai ba ya ɗago yana kallonta ya ce
"Kee Samira kar dai mijinki ne yazo?" Ta gyaɗa masa kai ta ce
"Shine" ya ce "ina ba zai yi maganar ya ganmu anan ba?" Ta ce
"Toh me a ciki idan ya shigo ya ganmu hakan? What is it? Ai friends dina ne kuma bashi da say" Umar ya ce
"Ahtoh, kuma tare ya ganmu, sannan mu ba other room muke shiga ba balle yaji kishi ko ya raba tsakanin" sallamar Deen yasa duk suka yi shiru
Ya karasa cikin parlorn yana binsu da kallo, Samira ta miƙe ta karasa ta yi hugging ɗinsa ta ce
"Welcome back, Deen" murmushi yayi mata ya ce "thank you" duk da yadda yaga dressing ɗinta kuma ba mayafi amma ya daure, karasa cikin parlorn yayi suka fara gaggaisawa da shi, ya miƙe yayi hanyar ɗakinsa, Samira dake binsa a baya tana kallonsu ta ce
"Besties bari ina zuwa" sai da Deen ya tsaya babu shiri ita kuma ta kusan buge shi dama dab da shi take bin sa a baya, kallonta yayi sannan ya kalli mutanen dake parlon sai kuma ya wuce corridor tana binsa, yana shiga ɗakinsa tana masa maga kawai ya buge kofar nasa ta karfi, ɗan tsayawa tayi tana mamakin reaction ɗinsa sai kuma taja tsaki ta fasa shiga cikin ɗakin ta koma parlorn, samun su tayi already sunma fara fita tana murmushi ta ce
"Okayy, tafiya ba sallama?" Farouk yace
"Nope, ai mijinki ya zo kuma Kinsan zai bukaci kulawar ki" ta ce
"Alright! Sai munyi magana" ta koma parlorn ta kwanta kan kujera ta ɗauki wayarta ta fara Game, sai ga Deen ya fito kamar zai tashi sama ko da wasa bata kalli direction ɗinsa ba
"Uban me waɗannan kattin suke min a gida?" Ta tsinkayi muryan sa, ba tare da ko ta Kallesa ko ta bar abinda take yi ba ta ce
"Kamar ya kenan? Abokai na ne kuma sun zo tayani murna ne, sai me kake son ka sani?" Da wani irin expression Deen yake kallon Samira ya ce
"What?! Your friends kike faɗa min?" Kara volume ɗin game ɗinta tayi sannan ta ce masa
"Nace friends ai kaji Ni? Wait... Dan na bika a baya zan haɗa maka ruwan wanka shine zaka wani bugomin kofa?" Sai kuma ta tashi ta zauna ta ajiye wayan nata a gefe tana Kallonsa, kamar yadda yake kallonta
Ya ce "Friends fah kika ce min Samira? All my thoughts cousins dinki ne harda tsayawa mu gaisa ba tare da komai a raina ba but Besties da kika ce ya tsaya min and now... Kina faɗa min cewa Friends ɗinki ne?" Ta ce
"And so what Dan nace maka friends ɗina ne? Karya kake so na maka? Ko wani abu ne dan friends ɗina sun zo gidana dan taya Ni murna" wani tsawa Deen ya mata wanda sai data ɗan rikice tana kallonsa a tsorace ta ce
"Deen? Yau Ni zaka ma ihuu?" Ya ce
"Nayin Samira, don't tell me duk mazajen da suke zuwa gidan nan Are all your male friends?" Sai ya kama kansa ya fara nanata innalillahi wa'inna ilahi raji'un
Tsaki taja ta ce "Ji yadda kake magana? Yanzu idan wasu suka ji a waje ɗauka zasu yi na kawo kwarto ne" ya ce
"Idan suka ɗauka hakan karya ne? Ai kwarata ma kike kawo, kalli dressing ɗin jikinki kuma kina zaune comfortable a cikin su"
Samira ta ce "Enough Malam! Ba zaka zageni na ɗauka ba, karka sake cewa na kawo kwarto, da wannan rayuwar ka ganni kuma ka yarda zaka aure Ni a haka, kai baka taɓa bina India bane har kawata ta bar mana ɗakin, kwanaki nawa kayi? Abu ta taɓa shiga tsakanin mu ne? Kai ma kasan wacece Samira, bana iskanci, amma ina da Male friends shine yanzu zaka fara min ihuu akan wani abu da bakomai bane" tana kaiwa nan ta barsa tsaye ta wuce ciki abinta kamar zata tashi sama, tana shiga daki ta faɗa kan gadonta ta fashe da kuka sosai....
Dada tana zaune da yaran kwabta da suke shigo mata ta miƙawa ɗayan yarinyar da take da wayo ta ce
"Ke, danna min lambar Azrah, jikata na india in nan ne" yarinyar ta karɓa tana murmushi ta nemo numbern Azrah ta ce
"Laaa, Dada ashe ma dazu ta kira" Dada ta ce
"Allah sarki, Ni nasan zata kira ai" daga haka ta kai wayan kunnenta ganin ya fara ringing
Azrah da har sannan tana basu Umma labari wayanta ya fara ringing, ganin Dada yasa tana murmushi ta ce
"Umma surukarkice" daga haka ta ɗaga tana sallama
Dariya Azrah tayi jin abin da Dada tace, ta ce
"Fatan kin isa lafiya?" Dada ta amsa da "Lafiya Klau, gobe zani wancan kauyen idan Allah ya kaimu neman maganin nan, Bappahn naku bayan tahowata ya shigo ko ya muku magana?" Zahra takarɓe wayan dan duk suna ji, ta ce
"Chap, Dada wai yanzu ke dauka kika yi zai shigo ko ya mana magana? Sai dai idan wancan matar nasa bata nan" Dada ta ce
"Shikenan, ai idan tasan wata bata san wata ba, Ni dai Karku ƙullace mahaifinku dan Allah" Zahra ta ce
"Toh shikenan" daga haka suka yi sallama..
Washe gari tun asuban fari Mama ta gama duk wani abu da zata yi, tana kallon Habibah ta ce
"Dan Allah kiyi da jiki mana kije ki cewa zulai ta baki kuɗin Adashe na, jiya an wuni zuwa nemanta amma bata nan" Habibah ta miƙe tana guguni ta ce
"Haba Mama! Dan Allah bai yi safe ba?" Mama ta ce
"Dan ubanki tafiya zanyi kice min yayi safe" hakan yasa ta miƙe ta nufi kofar kamar mara laƙƙa, fitan Habibah nada wuya sai ga Sallaman Hajiya kaltume, Mama dake zaune kofar ɗakinta ta amsa, ta ɗaga kai tana kallonta ta gaisheta, bayan ta amsa ta ce
"Ta shi mu tafi, zama ai bai kama mu ba" ta ce
"Wai na kara kuɗin wajena yayi yawa dan kar ace ya gaza shine na aika Habibah ta karbo min ɗaukan adashe na" Hajiya kaltume ta ce
"Matsala ta dake baki da planing ne, tun jiya me ya hana ki karɓa" ta ce
"Anje bata nan ne ai" Zahra data fito haɗa wuta, dan daura wa Azrah ruwan wanka kafin ta daura musu breakfast ko da wasa taki kallon direction ɗin su, Hajiya kaltume ta ce
"Wancan ba ita bace shegiyar?" Mama ajiyar zuciya ta sauke ta ce
"Wannan kanwarta ce, ai duk sunyu tsayi, sai ma Kinga 'yar iskan zaki ga abinda nake magana, Uhmm ai ita da aure sai kuma lahira idan ana yi" Hajiya kaltume ta ce
"Ikon Allah, kice duk de da Uwar suke kama?" Ta ce "kwarai kuwa, barin 'yar iskan ba" daga haka sai ga Habibah ta shigo da sallama Mama ta mike ta ce
"Bani" mika mata kudin tayi ta ce
"Mama baki ga yadda ta dinga matsifa ba wai kamar tashin duniya na bita karban Kudi da sassafe" Mama ta ce
"Ita ta sani kuma, tunda ta bayar ai hikenan" daga haka su Mama suka fita.
Zahra na shiga daki ta ce
"Umma, Mama fah tafiya tayi ita da wancan Yayar nata" Umma ta ce
"Toh ina ruwanki" Zahra ta ce
"Ni a jikina nake ji ba Alkhairi bane tafiyar nan nasu, amma dai Shikenan" daga haka ta koma wajen girkin nata
Bayan Azrah tayi wanka tayi shirin ta cikin rigar Abaya tayi rolling, ta fito ta wuce ɗakin Umma ta ce
"Umma zan tafi" Umma ta ce "Allah bada sa'a, ki kula da kanki, ki rike tarbiyyar da muka baki" Azrah ta ce "In Shaa Allah Umma" tana kallon Zahra ta ce
"Zahra ki ɗauki ATM dina a pink handbag dina ki mana cefenan rana kar ki sake mana abinci ba nama" Zahra tayi salle ta ce
"Ai kuwa toh kaza zamu ci" Azrah ta mike ta ce
"Ke kika sani" Zahra na dariya ta ce
"Toh Ni dai zan saya harda shawarma" Azrah dai ta fita ba tare data kula ta ba.
Kamar jiya Azrah na shiga cikin kamfanin haka idanu suka bita har Office ɗinta, tana haura sama ta ga Sakatariyar PA, hakan yasa ta ce "Good morning" ta yamutsa fuska ta ce "Fine" Azrah sai taga wani iri a fine a ɗin data ce, kawai sai ta kama hanyar office dinta, haduwa tayi da Merry zata fito daga parlorn Office ɗin hakan yasa ta gaida Azrah da ladabi,Azrah ta amsa mata da fara'a sannan ta shige ciki, cleanern daya gama aiki ya gaishe ta ta amsa masa shima da sakin fuska..
Merry ta shiga office ɗin PA, Miss Safiyya ta ce
"Kin haɗu da wancan yarinyar?" Merry ta ce
"Yes Ma, she's so nice" tsaki Miss Safiyya tayi ta ce
"Fuck the Nice din, banza daga zuwanta baki ga an bata Office ɗin MD ba, shekarunmu nawa anan? Sai ita za'a bawa, kalli yadda take wani jijji da kai irin gata Slay queen, sai wani dressing take kamar ba 'yar nan ba, ko yadda Mazan nan suke kallon mu a Mata yanzu zasu daina tunda suna kallon wannan fuskan nata data sha uwar bleaching"
Sauke ajiyar zuciya Miss Merry tayi, ta ce "Nikam gaskiya Banga wani abu game da ita ba, kuma ai dama daga ganinta kema kin san ba mate dinmu bane, Maybe she's from rich family ai ko daga kallonta ma, wata kila ma ɗan uwan Mr. Alhassan ne dan naga jiya sau biyu tana office dinsa amma Banga wani abu bad ba, wanda ya fika ai dama ya fika " wani tsaki taja ta ce
"Dalla bar nan, Banga za'a yi wani abun arziki da ke ba" a ranta kuma ta kudurci niyyar shafawa Azrah bakin fenti a wajen, wanda har sai an korata, ko da sharri ne sai ta mata. Miss Merry tuni tayi gaba tana mamakin halin Miss Safiyya
Azrah kuwa a office ɗinta, bayan ta gama waya da PA daya faɗa mata wasu aiki da zata yi, hakan yasa taje ta karba, a zuwanta ta sake haduwa da Miss Safiyya, Miss Safiyya ta tamke fuskarta, abin ba kaɗan ba ya bawa Azrah mamaki, ta lura tunda tace mata zata zauna office ɗin MD na wucin gadi shikenan ta canza mata while da farko da fara'a ta karɓe ta...
Bayan ta gama aikinta, da aka tashi, ta tsari wani taxi ta faɗa masa address ɗin gidan Mummy wanda Anty Suhaila ta turo mata not long ago
Episode 66: A Bumpy Star
A daidai kofar gidan ta sauka, motar dake parke a kofar gidan tabi da kallo a ranta tana addu'a Allah sa Saif baya gidan, ta karasa jikin gate ɗin tayi knocking, mai gadi ya buɗe mata ta gaishe sa ta karasa shiga, a kofar parlorn tayi sallama, wata mai aiki ta buɗe mata kofa, tana kallon yarinyar ta ce
"Mummy tana nan?" Yarinyar ta gaisheta sannan ta ce
"Eh, tana ciki" ta ce
"Anty Suhaila fah?" Ta ce
"Eh duk suna ciki" masa mata yarinyar tayi daga bakin kofar ta karasa shiga parlorn tana kallon mai aikin ta ce
"Ɗan yi musu magana mana dan Allah" kai ta gyaɗa sai kuma ta wuce ɗakin Anty Suhaila, bata daɗe ba ta fito ta ce
"Gata tana fitowa" godiya Azrah tama yarinyar, wayanta ta ciro ta fara chatting da Sarah, tun ɗazu taga message ɗinta tana mata korafi, Anty Suhaila ta fito ta ce
"Sannu da zuwa Azrah" Azrah tana murmushi ta ajiye wayan hannunta tana murmushi ta ce
"Ina wuni, Anty Suhaila" Suhaila ta zauna tana kallon Azrah tana murmushi, ba kaɗan ba tayi murna ganin yadda Azrah ta canza, ta ce
"Sorry, na ɗago ki ko?" Azrah na murmushi ta ce
"A'a bakomai, dama ina son zuwa gaishe da Mummy ai" Suhaila ta miƙe ta ce
"Bari nama Mummy magana ɗin" daga haka ta wuce zuwa ɗakin Mummy, tare suka fito tana ma Azrah murmushi harta karaso, Azrah ta gaisheta Mummy na murmushi ta amsa mata
Bayan mai aiki ta kawo mata ruwa, ta ɗauka tana sha dama ishi take ji, kamar yadda Suhaila take kallonta da sha'awa haka Mummyn ma, Mummy ta ce
"Yanzu kam karatu ya kare ko? Ko ma kin fara service ne?" Azrah ta gyaɗa kai ta ce
"Eh Mummy, har na fara" Mummy ta ce
"Toh Ma Shaa Allah, Allah ya kawo miji nagari" Azrah tayi murmushi kawai, Mummy ta ce
"Sai kuma kika ga na neme ki ko?" Azrah dai kallonta take ta kagu taji abin da yasa tayi mata kiran,
Mummy ta ce "Dama ba komai bane Azrah, CV ɗinki nake so ki kawo, dama tun tuni nayi alkawarin kina gamawa zan bawa Baban Saif ki fara aiki a companyn su"
Azrah tayi murmushi ta ce "Nagode sosaii Mummy! Amma Mummy yanzu already har na fara" Mummy ta sake baki tana kallonta ta ce
"Toh Ma Shaa Allah, namiki murna sosai, amma kin daɗe ne? A kuma ina ne?"
Azrah ta ce "A nan Majestic Vaults Ltd ne, jiya ne ma na fara" Mummy ta ce
"Kash! Allah sarki, bansan meyasa ba nafi son ace kina tare da Babansu ne amma hakan ma yayi kyau Allah ya taimaka" Azrah na Murmushi ta ce
"Nagode sosaii, Mummy"
Tunda ya fito idonsa na kanta, har sai data ji Idanu na binta ta ɗaga kai ai kuwa suka haɗa ido, ta ɗauke kai da sauri, ya shigo parlorn zai wuce yana kallon Mummy ya ce
"Zan tafi Mummy" Mummy ta ce
"Ga Azrah baka ganeta bane?" Da sauri ya juyo yana kallonta, ita kuma taki koda wasa ta Kalle sa ta ce
"Barka da warhaka" bai amsa ba, Mummy tana masa wani kallo ya ɗauke kansa daga kanta yayi hanyar fita, Anty Suhaila ta kirkiro murmushi dan bata ji daɗin abin daya mata ba, ta ce
"Azrah yanzu kam kamar 'yar can, kin maje tare da su" murmushi tayi tace
"Kai Anty Suhaila" sai kuma tana kallon Mummy ta miƙe ta ce
"Mummy bari na tafi, dama daga wajen aikin nayi nan" Mummy ta ce
"A'a shine ba'a saka miki abinci ba" daga haka ta shiga kwala ma mai aikinta kira, Azrah tayi saurin cewa
"No, Mummy kiyi hakuri bari kawai zan tafi kar dare yayi" Mummy ta ce
"Toh Shikenan, ki Gaishe min da su Ummanki" tana murmushi ta miƙe tayi musu sallama, fita tayi tana tafiya a hankali, tsayawa tayi cak tana kallon Saif daya tunkarota yana danna wayansa ba tare daya san tana wajen ba, ganin da gaske kanta zai yi zata ja baya tuni ya faɗo mata ta sake baki tana ganin abin kamar almara bata san sanda ta fashe da dariya ba abun ba kaɗan ba ya bata dariya, tsaisaita kansa yayi ya juyo ya wani tamke fuska yana kallonta, gyara Jakkanta tayi itama ta ɗaure fuska, ya ce
"Me yasa kike wani abu kamar mara hankali? kinyi laifi kina wani yage baki kina dariya" ta ce
"Ohh really? Kai fa ka faɗo min kai, amma ji yadda kake magana, ai sai dai nace maka next time idan ba'a ɗakin ka kake ba ka dinga kallon gabanka ba danna waya ba! Cos wata rana zaka iya faɗi kan matar wani ya zama maka matsifa kuma" daga haka taja kanta ta wuce sa, baki buɗe ya bita da kallo harta fita, sai kuma ya fasa shiga cikin gidan dama mantuwa yayi, yayi saurin fita, lokacin daya fita yayi daidai da lokacin da take shiga taxi, ya tsaya yayi folding hannayensa yabi abin data hau da kallo, rashin a mugun ɓace ya shiga motarsa kawai yaja motar ya bar wajen.
Mama dai na zaune tayi wulli wulli da Idanu tana Kallonsa, tun safe da suka fita basu suka isa wannan kauyen ba sai yanzu, ga kuma bayanai mara daɗi da mutum ke faɗa musu. Hajiya kaltume ta ce
"Mu yanzu Babbar damuwar mu wannan rikicacciyar Uwarta sa karta sake tako kafarta a gidan, garinma baki daya idan da hali.
Mutumin kamar wani dodo ya ce "an gama wannan, har an aika komai" Mama ta ce
"Toh yarinyar fah? So nake ta zama annoba a gari, ta zama bata da aiki sai bin Maza, ta ɗauko ciki wa Uwar sannan uban yasan da cikin yadda zai sake tsanarsu" ya ce
"Za'a yi mai yuwa, amma aikin na da hatsari saboda akwai kariya tattare da ita" Mama ta dafe kai ta ce
"Ko nawa ne zamu bada, ayi me yuwar shine damuwa ta" wani murmushin yayi ya ce
"Akwai sirri game da saurayin nata daya ke Egypt, zamu raba tsakaninsu sannan zamu saka mata bakin jini kamar yadda kika bukata"
Mama na murmushi ta ce
"Sannan kuma ka kara tsanar Mahaifiyar nasu a zuciyar mai gida namu, na fi son taga kayan bakin ciki kafin ya saketa ta koma garin nasu" ya ce
"Duk an gama" zaku ajiye kuɗi sannan zaku dawo wata watan dan ganin ko anci karfin aikin" dariya suke yi, jiki na ɓari ta ajiye kuɗin hannunta cikin wani kwarya dake gefe..
Dada ta shigo gidan nata a mugun gajiye amma tana hamdala da samun nasara da tayi, makwabciyarta ta samu tana share mata tsakar gidan harta hura mata wuta ta ɗaura mata girki, Maman Amira ganin Dada ta hada kan sharan tana ma Dada sannu da zuwa
Dada tayi ɗaki ta ce
"Maman Amira zo Kiga wani ikon Allah, ashe dai mutumin yau ba Allah a ransa, haba Nima dai nasan Muhammadu na ba halinsa bane" ta kare maganar tana zama tare da ajiye hijabin jikinta tana matsal ƙwalla, Maman Amira ta shigo tana kallon Dada ta ce
"Alhamdulillah, anyi nasara kenan ko Dada?" Dada ta zauna ta fito da magungunan tana kallo ta ce
"Babu tsoran Allah a zuciyar Uwani, an tabbatar min ta cire duk wani So na Bitti da 'ya'yanta a ran Muhammadu, hatta wani kula da tausayi duk ta cire masa, yara kuma basu sani ba suna ta kullatan mahaifinsu" ta kare maganar tana tagumi kamar zata yi kuka, Maman Amira ta ce
"Kiyi hakuri Dada, yanzu kam ai Shikenan tunda kin karbo maganin karya sihir ɗin, gobe gobe idan yaso duk yadda za'a yi su samu maganin su fara amfani da shi ko?" Dada ta mike ta ce
"Ai dole fah, dan abin ya isa hakan kuma, har shi Malam zan masa maganin da kai ba, yana samun sauki kuma zance ya sallame ta dan ba zai zauna da muguwa mara addini ba" Maman Amira ta mike tana kara jajanta al'amarin, fita tayi dan kara karasa aikinta..
Mummy dake zaune suna dinner, bayan ta gama cin abincin tana kallon Suhaila ta ce
"Suhaila Kiga yarinyar nan yanda ta canza? Ni na mata murna wlh, kamar da bata sha wahalar rayuwa ba"
Suhaila ta ce "Ai tun ɗazu nake son miki maganar nan ne sai ga Daddy, nace rayuwa juyi juyi ne, daɗin karatun opportunity na zuwa Shikenan sai kaga rayuwarka ta canza ta hanyar samun aiki"
Mummy ta ce "tausayin take bani, zan tambayi ɗan wajen Antyn ku idan baida wanda yake so kawai sai na haɗa su"
Suhaila ta ce "Ina ga zai yarda ma, daya samu Mata mai hankali, gashi duk tsilla tsillan Ya Saif da choice dinsa inda ya kare kenan, me zata nunawa Azrah Fisabilillah ai sai dai buɗewar ido"
Mummy ta miƙe ta ce "Allah kyauta kawai" daga haka ta wuce ɗakin ta...
Azrah na zaune tana bawa Umma yadda suka yi da Mummy, Umma ta ce
"Allah Sarki, Matar nan tana son ki ne, ai kuwa mun gode mata kwarai" Azrah ta ce
"Ni kam ma Umma tunani na fah wani maganar ne sai kawai naji abin da ta faɗa ashe taimako zata min, ai kuwa nace yanzu nama fara already" Umma ta ce
"Ai a hakan ma mun gode mata da kulawa"
Suka yi sallama da Umma suka wuce ɗaki, Azrah ta kwanta bayan tayi azkar ɗin baccinta, ta ɗauki wayanta zata kira Khalil kawai ta tuna da incident ɗinta da Saif kawai ta fashe da dariya, Zahra ta tsaya kallonta ta ce
"Lafiya? Shafamin Meya faru ne?" Azrah ta mike zaune tana dariya ta ce
"Baki san Meya faru ba? Ɗazu dana tafi gidan Mummy, ina wannan arrogant ɗanta dana ke baki labarin" da sauri Zahra ta gyara zama ta ce
"Eh.. ina jinki" Azrah ta ce "Toh muka haɗu da shi a Parlorn su, da ba dan Mummy na wajen ba ko? da bazan gaishe sa ba amma kunyar idonta yasa na gaishe sa ya share Ni" Zahra taja tsaki ta ce
"What's funny here toh?" Azrah ta ce
"Ai matsala ta dake baki cin riban zance baki tsaya kinji meya faru ba har kin fara magana" Zahra ta ce
"Toh ina ji" Azrah tayi dariya ta ce
"Shikenan a compound ya buge Ni, Ni harga Allah abin dariya ya bani sosai, kawai zai ɗauko min wannan dirty attitude ɗin nasa, kawai bansan sanda na fara dariya ba na faɗa masa maganar dana ga dama nayi gaba abu na" Zahra ta ce
"All thanks to Allah daya tura mana ke India, inba haka ba da yanzu kin fara wannan kukan naki kina cewa ya gaya miki magana" karan wayanta ne yasa ta ɗauka tana mamakin mai kiran nata a wannan dai dai lokacin, ɗaga kiran tayi ta kai kunne
A ɗan ruɗe ta ce "Meya faru Samira?" Samira dake jikin dressing mirror ɗinta ta kasa magana tana share hawayenta
Nan da nan hankalin Azrah ya mugun tashi, ta ce "Kina jina? Ki faɗa min meya faru ne kina ɗaga min hankali kuma" Samira ta share hawayenta ta ce
"Azrah dama soyayya karya ce?" Azrah taji gabanta yayi mummunan faduwa ta ce
"Sorry dear, Ki faɗa min menene kar kisa na fara wani banzan tunani" dakyar Samira ta ce
"Nayi regretting auren Deen, Azrah" Azrah ta fara girgiza mata kai ta ce
"Noooo Samira, stop saying this plss, Meya faru ne? Kimin bayani" Samira ta ce
"Can you imagine Deen ya canza min, har Ni Deen zai mara? Aure just 1 week?" tana kai wa nan ta fashe da kuka, Azrah taji wani zufa na karyo mata, nan da shiga bawa Samira hakuri da kalmomin da zai kwantar mata da hankali amma ina Samira ba fahimtar ta take yi ba, karshe Azrah ta ce
"Gobe zan zo Samira In Shaa Allah, yanzu kiyi hakuri ki kwanta kinji"
Zahra ta ce "Meya faru Yaya?" Azrah ta ce
"Ban gama fahimtar ta ba Zahra, sai gobe idan Allah ya kaimu, dan yanzu kam kuka ma take yi" Zahra ta ce
"Toh Allah ya kyauta yasa ba abin da zuciyata take rayamin bane" Azrah dai ta kasa cewa komai, daga haka kawai ta kashe wayanta ta kwanta, dan ko kaɗan bata son wani abu da zai ɗaga mata hankali, tuni tama manta da wai dama Khalil zata kira..
Washe gari da safe, bayan sun idar da Sallah tayi Azkar ɗinta ta fita zuwa wajen Zahra dake hura wuta ta ce
"Bari na fara wanke wanke kafin ki karasa hura wutan" Zahra ta ce
"Nahhh, ki bari ke da kinsan dokar aikin naki shine zaki fara wasa tun yanzu" Umma ce ta leƙo ta ce
"Azrah ana ta kiran ki" Azrah ta mike tana jin zuciyarta na bugawa, kafin ta karasa wayan ya yanke, kawai ta bi Umma cikin ɗakin tana shirin dialing sai ga message ya shigo, kallon message ɗin ta dinga yi, Umma ta ce
"Lafiya?" Ta ce
"Eh, Umma! Wai idan da hali na shigo kafin karfe bakwai za'a gwada min wani training ne muna da baki sannan kuma yau MD zai dawo"
Umma ta ce "Toh sai kiyi ki karya ki tafi ko?" Ta ce
"Toh Umma"..
Episode 67: Azrah's Dawn, veil to victory
Azrah ta wuce waje, kallon Zahra data ɗaura ruwan tayi ta ce
"Kinga juye min ruwan wankan a haka, bari na shiga nayi, sauri nake yi"
Zahra ta ce "Toh amma ba zaki je ko ciro kayanki ki fara ba, kafin ki fito ya kara zafi tunda yanzu na daura"
Azrah ta ce "Okay" daga haka ta wuce dakin, ta ciro kayan da zata saka, ta kuma fitowa Zahra ta juye mata ruwan, daga haka ta wuce toilet bata wani daɗe ba ta fito ta wuce daki, bayan ta gama shafa mai ta saka wani uban open Abaya mai shegen kyau pink color, da wani gown a ciki, tayi ɗauri sannan ta daura veil ɗin, ta shafa lipstick a pink lips ɗinta, ta dauki, phone pouch ɗinta pink color sannan ta cire wanda yake jikin wayan dama Black color ne ta saka pink one, ta ɗauki handbag ɗinta da takalminta, dakin Umma ta nufa ta ce
"Umma zan tafi" Umma ta ce
"Toh naga ai baki karya ba?" Azrah ta ce
"Za tsiya abu a hanya naci Umma" Umma ta kalli agogo dake nuni da 6:45am ta ce
"Toh kiyi sauri, Allah bada sa'a" Azrah ta ce
"Amin Umma, Nagode" daga haka ta wuce compound ɗin, Zahra tayi wani salle tana kallon Azrah baki buɗe, tun kafin tayi magana Azrah ta ce
"Ina ba zaki daina wannan shirmen naki ba ko? A haka zaki fara higher institution ɗin?" Zahra ta ɓata rai ta ce
"Toh sai aka ce haka zanyi a can ɗin? Ai kema kin san dan kyau da kika yi ne yasa nayi wannan abu" sai kuma ta washe baki ta ce
"Dama yau ne kika haɗu da wannan ɗan rainin hankalin Wlh, kaiii gaskiya yau zaki girgiza Majestic" tuni Azrah tayi gaba dan ba zata iya biye wa Zahra ba.
Daga gate ta gashe da security personnel da murmushi cike da girmama sannan ta shiga ciki, PA ɗin Mr. Alhassan ta gani tsaye yana waya, bayan ta karasa ya ce
"Yauwa, Miss Azrah... welcome on board
"Thank you, sir" Azrah ta ce da ladabi
PA ɗin ya murmusa. "We're expecting some important guests today for a business collaboration. You'll be attending the meeting with the MD Idan Allah ya kawo sa, it's a great opportunity for you to gain experience. This unit may eventually be under your leadership, so it's good to observe early. For now, please have your breakfast. Your office has just been set u'
Azrah ta ce "Thank you very much, sir" sannan ta juya ta nufi office dinta.
A hanya, ta hangi Miss Safiyya tana shirin gaisheta kenan sai taga ta juya da sauri tana kai waya kunnenta. Azrah ta ɗan tabe baki, ba tare da cewa komai ba ta wuce.
Tana shiga office ɗinta, ta kalli breakfast da aka ajiye mata, Irish potato ne da flask ɗin hot water. Ta haɗa tea, ta zuba chips ɗin a plate sannan ta fara ci. Tana tsakiyar cin abincin ne wasu cleaners biyu suka shigo da ladabi, suka gaishe ta
"Good morning ma" ɗayan ya ce
Azrah ta amsa da murmushi, “
"Good morning"
Ɗaya daga cikin su ya ce, "Dama zamu gyara waɗancan papers ɗin ne, kuma PA yace idan ba matsala zaki iya wucewa wajen meeting ɗin yanzu"
Azrah ta mike, ta ɗauki jakarta. "Toh nagode. Amma please, idan kun gama, don't turn on the AC''
Suka ce, "Yes ma!" cikin haɗin murya, suna kallonta da girmamawa
Tana fita, cleaner Adamu ya kalli abokinsa Ishaq ya ce
"Chap! Allah ya sa dai wannan ne MD kar wancan ya dawo, an taɓa mace mai sauƙin kai irin wannan ne ma? Babu takama, babu ji da kai, babu kyama"
Ishaq ya ɗora "Gaskiya kaff tarihin Majestic kam babu, gata da kyau ba kaɗan ba. Ga iya wanka kamar baturiya, ga kuma mu'amamat. Chap! In ka tuna Safiyya fa... Kafin ta maka magana daya ta maka ihuu ɗari"
A can bangaren kuma, Azrah na ta duban hanyar da za ta bi, amma bata ma san wajan ba. Tana juyawa ta kalli mutumin jiya wanda zai rage mata hanya, ya ce
"Hey Miss"
"Good morning" Azrah ta amsa da fara'a
"Morning. Meeting venue ɗin kike nema?"
Ta gyada kai
"Toh mu tafi" ya ce. Suka tafi tare har suka isa conference room.
Suna shiga kowa ya bita da ido mata da maza. Saboda kallon ya yi yawa, kawai ta bi bayan wanda ya raka ta ta zauna a gefensa. Daga bisani, wasu daga cikin ma'aikata suka fara zuwa gaisawa da Abubakar da ke gefenta. Duk gaisuwar kuma saboda tana wajen ne suke zuwa yi, hakan yasa ta gaji ta tashi daga wurin ta koma wani kujera a gefe.
PA ya shigo tare da Mr. Alhassan. Bayan sun zauna, suka fara gabatar da manufar taron
"Mun haɗu a nanne domin business collaboration tsakanin kamfaninmu da na wasu, wanda zai shafi joint-distribution network na kayayyakin gida da na waje. Za a raba kayayyaki daga supply centers zuwa branches, kuma kowane bangare zai amfana da shared logistics, a haka Mr. Alhassan ya gama musu bayanin in short
PA ya miƙe ya ce "This is Miss Azrah, our new staff. She'll be joining this department fully soon"
Mr. Alhassan ya kalli Abubakar da Mahmoud ya ce "Idan MD bai shigo yau ba, then you two will work closely with her to attend to our guests"
Suka amsa da ladabi, "Yes sir"
Miss Merry da ke gefe, na satan kallon Azrah, zuciyarta cike da sha'awa da gamsuwa da kyan ta da kamun kai ba kaɗan ba ta mata kyau yau. Amma Miss Safiyya kam, kamar ta daura hannu a kai ta kurma ihuu dan kusan kowa na satan kallonta ...
Can wajajen karfe goma sai ga manyan baƙin nan sun shigo cikin girma da ƙima, manya ne, cikakkun 'yan kasuwa masu kima daga wata herbal company dake Abuja. aka tarɓe su da fara'a da girma har zuwa ɗakin taron
Mr. Alhassan ya miƙe da murmushi, yana cewa
"Welcome sirs, please have your seats"
Suka zauna, sannan ya ce
"MD bashi da lafiya a safiyar nan, amma mun shirya komai. And here's our capable staff, Miss Azrah, she'll be handling the session along with Abubakar and Mahmoud"
Abubakar da Mahmoud sun kalli junansu da mamaki, Mahmoud ya kai masa raɗa, "Wannan sabuwar yarinyar za ta jagoranci taro irin wannan?"
Azrah kuwa ta natsu, ta maida hankali, duk da yadda bakin suka zuba mata idanu amma bata bari ya tada mata hankali ba.
Daga haka Mr. Alhassan ya fita
Tattaunawar ta fara.
Mahmoud ya gabatar da slides ɗin business proposal din
"...Wannan hadin guiwa tsakanin kamfaninmu da naku zai bada damar a hada herbal da nutritious products cikin sabbin tsare-tsare da packaging. Zamu samar da supply chain daga nan Katsina zuwa Abuja, sannan mu bude subsidiary..."
Sai ɗaya daga cikin manyan bakin ya kalli Azrah, ya ce
"I'm impressed by how organized your documents are. Did you supervise this?" ba ita ba hatta su Oga Mahmoud sai da suka yi mamaki, ga wanda yayi magana amma ma wanda sukr tambaya daban
Azrah ta ce da ladabi, "Yes sir. I was responsible for putting the proposal together"
Wani daga cikinsu ya ce, "Excellent. You speak well too. It's rare to see young people this composed"
Sauran suka gyada kai. Tun kafin Mahmoud ko Abubakar su ƙara bayani, ɗaya daga cikin manyan ya ce
"Honestly, I don't see a need for delay. If this young lady is leading this, we are ready to sign MoU"
Azrah ta ɗan zaro ido amma ta maida kanta kasa da sauri, Abubakar kuwa yayi murmushin mamaki, Mahmoud ya ce cikin ƙasa da murya
"Nasan za'a rina haka, baka ga kallonta da suke yi ba"
Bayan tattaunawa mai armashi aka gama komai lafiya. Suka fito gaba ɗaya suka raka manyan bakin har zuwa wajen motarsu.
Ɗaya daga cikin su ya juya yana kallon Azrah ya ce da fara'a
"Keep it up, young lady. I see greatness in you"
Abubakar da Mahmoud na gefe, suna kallon ta da murmushi
Sallama suka musu cike da girmama juna, motar su ta ja suka fita.
Mahmoud da Abubakar suka kalli juna, suka saki dariya kaɗan. Mahmoud ya ce
"Toh yanzu me kake tunani?, ka gani da idonka ai"
Abubakar ya ce
"Wallahi wannan yarinyar ta tara hankali da nutsuwa, sai ka ce ta shekara goma tana wannan aikin, jikin few seconds harta san me zata ce"
Daga nan suka juya suka nufi office ɗin Mr. Alhassan, tare da PA ɗinsa
Suna shiga, PA ya ce,
"Kun gama taron kenan?"
Mahmoud ya ce,
"Eh, kuma abun ya yi kyau sosai. Wallahi abokan hulɗar nan sun yarda da komai cikin sauƙi saboda Azrah"
PA yana murmushi ya ce
"Shikenan fa, dama irin su Azrah ya kamata a saka a irin wannan position ɗin. Sbd kyau, natsuwa da basira, hakan zai jawo mana manya"
Mr. Alhassan kuwa yayi shiru yana kallonsu, sai ya girgiza kai a hankali yana ce
"Wasu mazan idan suka ji mace ce za ta jagoranci abu shikenan fah. Idan da namiji ne da har yanzu muna nan muna musu, sai ana ɗagawa head office kafin su amince"
Suka yi dariya gaba ɗayansu, Mr. Alhassan ya ce
"Ku faɗa mata ta tafi gida ta huta. Gobe zata cigaba da reports"
PA ya ce,
"Zan gaya mata. Ta cancanci ta hutu"
PA ya kalli Mahmoud ya ce,
",Mu dai mu rike ta da kyau. Akwai future a tare da ita"
Oga Mahmoud ya ce
"Dan ma baka wajen ne sir, da zaka sha mamaki yadda komai ya tafi babu wani inda inda fah"
Bayan sun fito daga office ɗin, Abubakar ya kalli Oga Mahmoud ya ce
" Inaga kawai a bar mata wannan wajen, tafi dace wa da shi" ya ce
"Dama nan aka bar mata ai, yanzu sai ka wuce kaje ka sanar da ita zata iya tafiya saboda ta huta" ya amsa da
"Okay, Sir" daga haka suka rabu
Azrah tayi nisa cikin tunaninta, tana tunanin yadda zata je gidan Samira, sosai hankalinta ya tashi dan Samira ba kasafai take kuka ba, kuma babban damuwarta yanzu haka wayan nata a kashe yake
Buɗe Office ɗinne yasa ta ɗago da sauri, duk zaton ta ko MD ne tunda aka ce ya dawo gari Maybe yau ma ya shigo Companyn, ganin Oga Abubakar ne yasa tayi murmushi ta ce
"Weldon sir" ya ce
"Thank you, Miss.. zaki iya tafiya yanzu tunda babu wani abu but make sure gobe ma da wuri zaki shigo" bata san sanda ta sauke wani ajiyar zuciya ba ta ce
"Ohh, thank you sir" ya bar bakin kofar, ita kuma da sauri ta mike ta ɗauki jakkanta sannan ta sauko, ko da suka haɗa ido da Miss Safiyya da take sauka, tayi saurin ɗauke idonta da farko, dan bata ga wani amfanin magana da ita ba, tayi hanyar fita, Miss Safiyya ta bita da kallo, tass ta kare mata kallo sai kuma taji wani abu ya tokare ta a throat ɗinta, ta juya ta wuce office ɗinta da saurinta.
Azrah na isa bakin titi ta tsayar da abin hawa, a daidai kofar gidan Samira ya sauke ta, ta sauka ta buɗe handbag ɗinta zata bata kuɗinsa taga wata motar ta shigo layin, ko da wasa bata kalli motar ba ta wuce jikin gate ta fara knocking, gateman na buɗe mata taji motar ta tsaya, amma hakan bai sa ta juya ba kawai ta shige abinta, tana isa entrance ta kira Samira a waya, fortunately ya shiga ba kamar ɗazu ba, Azrah ta ce
"Gani a kofar entrance" tana gama faɗa ta katse kiran, ko minti ɗaya bata yi ba sai ga Samira ta buɗe mata, rungumeta Azrah tayi cike da damuwa suka wuce ciki
Bayan ta zauna a kan kujera tana kallon Samira ta ce
"Ko dai bacci kike?" Samira ta girgiza mata kai ta ce
"A'a fah! Kar dai kun tashi daga office ɗin? Dama da wuri kuke ta shi?" Azrah ta girgiza kai ta ce
"Not at all, kawai dai sun ce naje na huta ne sai kuma gobe" Samira ta gyaɗa kai cike da gamsuwa
Azrah na kallonta da damuwa ta ce
"Samira me yake faruwa ne pls? Hankali na ya gagara kwanciya tun jiya" nan da nan Samira ta fara kuka, Azrah ta dinga bubbuga bayanta a hankali kamar yadda ake ma yara har tayi shiru, tana kallon Azrah ta ce
"Azrah, har Ni Deen zai ɗaga hannu ya mara? Ina son da yake min? Bayan ihu da masifan da yake min yanzu har ya kai ya taɓa Ni" Azrah da ta zama speechless ta ce
"Toh me kika masa Samira har da zai ɗaga hannun ya mare ki?" Samira ta fara share ƙwalla ta ce
"Azrah kawai dan yaga friends ɗina Maza sun zo min taya murna shikenan muka fara samun misunderstanding, wai kuma dan ina faɗa masa cewa ai tare ya ganmu ba zai raba mu ba shine ya mare Ni, tun daga lokacin har yanzu ban sake saka shi idona ba" ta karasa maganar tana share hawayen, tun data fara magana kuwa Azrah sake baki tayi tana kallonta, gaba ki ɗaya ma ta rasa ta ina zata fara, Samira jin tayi shiru yasa ta ce
"Bana son faɗawa Daddy ne, ace tun yanzu mun fara samun matsala, amma Ni kam gaskiya ba zan zauna yace zai taɓa Ni nayi shiru ba"
Azrah ta riƙe hannayenta guda biyu ta ce
"To be honest Samira Deen na mutuwar son ki, Deen yana son ki Shiyasa har yake kishi akan ki, maganar auren ku kuma ki cire 3rd party, I'm sorry to say na kira Daddy da 3rd party, Amma duk sanda kuka shirya kan ku su Daddy zasu na jin ba daɗi ya mara musu 'ya, but Samira a wannan labarin Deen laifin shi shine guda ɗaya na marin ki da yayi" Samira ta ɗaure fuska ta ce
"Yanzu sai ki ce duk laifi na ne ba?" Azrah ta gyaɗa kai ta ce
"Exactly kin fahimta, gaskiya Samira kinyi Babban kuskuren kawo wasu mazan da ba muharramanki ba har gidan aurenki kuma ki iya buɗan baki kice wa mijinki cewa Friends ne? Ya kike so yayi idan bai zama Mad at you ba?" Ta ja numfashi ta ce
"Samira ko Ni da nake budurwa bani da friend na miji ko guda ɗaya talkless of ace wai har suna zuwa min gida muna gaisawa, ba wajen mijinki kaɗai ba hatta wajan Allah ma kina da laifi, ki nemi yafiyar mijinki sannan ki tuba"
Ya kasa daurewa, so kawai yake yaga wannan kawar nata, musamman da muryan nata ya zama so familiar a kunnensa, keyn hannunsa ne ya faɗi, jin karan yasa Samira da Azrah duk juyawa, yana ɗagowa suka haɗa ido da Azrah bai san sanda ya sake sake keyn ba ita kuma ta miƙe tsaye..
My apologies for the inconveniences, jiya da yau duk bana gida ne, in shaa Allah gobe zamu cike na ran Friday, thank you.
Episode 68 & 69 : The Return of the prodigal son
Samira ta ɗaga kai tana kallon Azrah, sai kuma ta juya ta kalli Saif dake kallonta shima, da sauri ta zauna tana kallon Samira sai kuma ta ɗauki Jakkanta tace
"Bari na tafi" At this point Azrah ta shiga ruɗani kar dai shine Deen, amma idan ba haka ba meya kawo sa gidan?, Samira ta ɗaure fuska ta ce
"Daga ganinsa shine zaki wani ce zaki tafi? Dama baku taɓa haduwa ba ai" sai kuma ta juya ta kalli hanyar ɗakin Deen, dan tuni ya shige, ta miƙe ta ce
"Barin masa magana" daga haka ta wuce zuwa ɗakin nasa, Azrah tayi tagumi, tunani iri da kala na zuwa mata rai tana kore sa, bata son believing abinda zuciyarta ke raya mata
Samira ta buɗe ɗakin nasa ta shiga ciki sannan ta kulle, ta jingina da kofar tana kallon Saif daya yi tagumi, ta ce
"Ka kyauta, ko kaɗan bana tunanin waɗannan halayen daga gare ka" bai ɗago ba kuma bata ga alamar zai ɗago ba, ta ce
"Toh ga kawata Azrah da nake yawan maka taɗinta" sai sannan ya ɗago yana kallonta babu kiftawa, maganar da tayi ya sake tabbatar masa da abinda yake tunani haka ne, lokaci guda jikinsa yayi sanyi, Samira ta katse masa tunaninsa ta ce
"Itama zaka nuna mata wannan sabon halayyar naka ne? Duk da bata sanka da haka ba, ko ba zaku gaisa ba tayi tafiyarta?" Saif ya ɗago yana kallonta yama rasa abin da zaiyi ko ya ce, baya jin zai iya zuwa, a hankali ya ce
"I'm sorry Samira, ba zan iya fita ba cos ina fama da headache ne" Samira ba tare data ce masa komai ba ta juya ta fita abinta
Bayan ta karasa cikin parlorn taga Azrah tayi tagumi ta ce
"Lafiya?" Azrah ta sauke hannunta tana murmushi ta ce
"Hmm gajiya ne in faɗa miki" Samira ta ce
"Da nashiga kuma wai akan zaku gaisa na same sa ya shiga wanka ne" Azrah ta kirkiri murmushi ta ce
"Kar ki damu, yanda kuka samu misunderstanding ɗin nan kamata yayi ace kina tare da shi" Samira ta ɓata rai ta ce
"Yanzu kuma sai ki ce zaki tafi?" Azrah tayi murmushi ta ce
"Toh sai na zauna?" sai kuma tayi saurin cewa "Yauwa.... I'm sorry to ask... Me ma sunan mijinki?" Samira ta ɗanyi shiru sai kuma tace
"Deen?" Azrah ta ce "Ai wannan ba suna bane, naga kamar love name ne ko?" Samira ta girgiza kai ta ce
"Nope, sunan sa ne, ai ainihin sunansa Saifuddeen" tuni Azrah ta fara jin zufa, Samira ta ce
"Amma me na tambaya ta?" Azrah ta ce "Nothing" daga haka ta miƙe bata kaunar wani tambaya da Samira zata mata, Samira ma ta miƙe ta ce
"Kin dai nace sai kin tafi, Ni da zaki dawo nan ne da zama ma da yafi miki tunda yafi kusa da Office dinku, Kinga sai weekend kina tafiya wajen su Umma" Azrah bata san sanda tayi wani murmushi ba tace
"Baki da hankali amma, yanzu ba sai kin raka Ni ba, ki tafi wajensa Ni zan wuce" daga haka ta fita
Samira ta juya ta wuce ɗakin Deen, buɗewa tayi ta shiga ya ɗago kai yana kallonta harta karasa shiga ta samu waje ta zaune tana kallonsa, ya ce
"Ina take?" Ta ce "ta tafi ai" ya ce
"Aina kika santa? Kika ce ita ce Azrah ɗin dama?" Ta ce
"Eh ita ce, tare da ita ai na tafi India tun farkon samun admission dina, sai ya zama har muka gama tare muke zama" Deen yayi shiru sai kuma ya ce
"Kuma ita ce wannan wanda ta karɓi lots of awards?" Ta ce
"Yes" ya ce
"Amma bata yi kama da ita ba ai naga" Samira ta ce
"Saboda lokacin tayi makeup ne ranan grad ɗin namu Shiyasa ka ganta da yanzu da banbanci" ya gyada kai ya ce
"But da ita ce kike haɗa mu waya wani lokacin?" Ta sake gyaɗa kai ta ce
"Sure ita ce! Duk wani abu dana ce maka Azrah toh ka sani ita ce dai wannan" Saif ya sauke ajiyar zuciya, Samira kamar wacca ta tuna abu ta ce
"Wait...ka santa ne?" Ta sauri ya girgiza kai ya ce
"A'a no" ta ce
"Amma mayasa kake min tambayoyi a kanta, itama ta tambaye Ni sunanka" ɗan ware ido yayi ya ce
"Kawai dai kar wata rana ta zo miki ne nace ban santa ba taji ba daɗi" duk da tambayarta daya so yi amma sai ya hakura ganin kar ta gano sa, Samira ta zuba masa idanu kamar me son gano wani abun
Azrah tana sauka ta shige cikin gidan da sauri, ko kallon Mama dake zaune tana 'yar wake waken ta bata yi ba, tun data shiga keken nan har suka iso bata sani ba dan gaba ki ɗaya ta faɗa duniyar tunani, dakin Umma ta shiga ganin babu kowa a ciki yasa ta shige ɗakinsu tana faɗawa tayi kan katifarta tana sauke numfashi, Zahra ta ce
"Da kafa kika zo ne?" Azrah ta ɗan kalleta sai kuma ta miƙe zaune ta ce
"Ina Umma?" Ta ce
"Tana wanka" Azrah ta ce
"Hmm baki san me yau ya faru ba?" Zahra ta karaso wajenta tana kallonta ta ce
"Meya faru toh?" Azrah ta fara bata labarin abin daya faru, ita kuma Zahra sake baki tayi tana kallonta har ta kai aya sannan ta ce
"Toh yanzu duk wannan zumuɗin bada labarin na mene ne? Ko dai son sa kike yi ne ban sani ba?" Azrah ta ɓata rai ta ce
"Wannan wani banzan magana ne kuma? Kamar ya nake son sa?" Zahra ta buɗe hannayenta alamun bata sani ba ta ce
"Toh ai zai iya yuwa kema ɗin baki sani ba, ko baki san akwai irin waɗannan mutanen bane?" Azrah ta koma ta kwanta a katifarta ta juya mata baya, Zahra ta ce
"Yi hakuri kawai dai yadda naga kike wani maganar ne kamar irin kin so hakan" Azrah ta ce
"Idan banda iskanci a dalilin meyasa har zan so sa bayan na san cewa mijin Samira ne, ai kawai mamaki nayi"
Zahra tana murmushi ta ce "Okayyy, Nagane" Azrah tayi banza da ita, duk yadda Zahra ta so ta kula ta haka taki kulata, Umma ta leƙo ta ce
"Kin dawo ne Azrah" jin muryan Umma yasa Azrah ta miƙe zaune ta ce
"Eh Umma, ai na shigo ban ganki ba" Umma ta ce
"Eh ina wanka ne" daga haka ta juya ta koma ɗakinta, Azrah ma miƙewa tayi ta bi bayan Umma, tana shiga ta same ta tana zaune ta ce
"Barka da gida Umma" Umma ta ce
"Kun yi abin da aka ce zaku yi ɗin ne?" Azrah ta gyaɗa kai ta ce
"Eh, mun gama komai amma MD din bai shigo ba kila sai gobe ne" Umma ta gyaɗa kai ta ce
"Toh Allah ya kaimu" ta amsa da "Amin"
Har daren ranan Azrah taki kula Zahra, duk wani abu da zai haɗa su sai ta san yanda zata yi tayi avoiding dinsa, Zahra har ta hakura da mata magana dan ko tayi sai ta share ta...
Yafi minti biyar da parka motar a kofar gidan amma ya gagara sauka balle ya shiga cikin gidan, gaba ɗaya ya faɗa duniyar tunani ne wanda yama rasa yadda zai yi da tunanin daya addabesa, ringing wayan nasa ya fara wanda ya farkar da shi daga doguwar tunanin daya shiga, kallon wayan yake yi kamar me tunani, ya kai hannu zai ɗauka sai kuma kiran ya katse hakan yasa ya sauka a motar ya shiga cikin gidan nasu, a hankali yake tafiya as usual da wannan kasaitar nasa, yana buɗe kofar parlorn ya shiga da sallama, idonsa ya sauka kan Mummy da wata cousin sister dinsa, tana Kallonsa ta kwaɓe fuska kamar zata yi kuka sai kuma ta ɗauke kanta daka kallon sa, shikam kallo ɗaya ya mata sannan ya ɗauke kan sa, ya zauna ya ce
"Barka da warhaka, Mummy" ta ce
"Yauwa Saif, ya gida? Ya Samira kuma?" Ya ce
"Lafiya klau" shiru yayi, Mummy na kallon cousin sistern sa ta ce
"Daughter baki ga Yayanki bane?" Turo baki tayi kamar zata yi kuka ta ɗan Kalle sa ta ce
"Ina wuni, Yaya" ba tare daya Kalle ta ba ya amsa, daga haka ta miƙe ta wuce dakin Mummy, ya ce
"Mummy me yarinyar nan take yi a gidan nan?" Ta ce
"Ban sani ba, bata da ikon zuwa ne sai da akwai abin da zata yi? Tun da kace baka son ta ai magana ya kare balle ma kayi auren ka ai" shiru yayi, Mummy ta ce
"Toh yanzu kuma meya kawo ka a wannan lokacin? Ba ɗazu ka zo ba? Wai meyasa Deen baka jin magana ne sai kayi ta barin yarinyar nan ita kaɗai duk kwana biyun nan ina lura da kai" ɗan sosa kai yayi ya ce
"Abu Nazo dauka fa Mummy" daga haka ta mike zuwa ɗakinta, Saif ya miƙe ya nufa dakin Suhaila kai tsaye, knocking yayi, Suhaila ta ce
"Who?" Ya ce
"Ke buɗe mana" jin muryansa yasa ta taso tazo ta buɗe masa, ta tsaya tana Kallonsa da mamaki ta ce
"Daga ina kuma?" Ya ce
"Gida mana, mu zauna a second parlor magana nake so muyi idan babu matsala? Ta ce
"Hope all is well dai?" Ɗan bata rai yayi ya juya ya shiga Second parlorn ya zauna, sanin ba zai ce mata komai bane yasa ta bisa a baya, tana shiga ta zaune kujerar dake kallon nasa ta ce
"Ina jin ka?" Yayi shiru yana tunanin ta inda zai fara ya rasa, can ya ce
"Please ina wannan wanda kwanaki tayi aiki a gidan nan?" Suhaila da rashin fahimta ta ce
"Wacce kenan? Kasan ba mutum daya bane ai" ya ce
"Wanda dai last ta mana kafin mu bar kasar nan?" Ta ce
"Ohh wai Azrah, kai ya Saif dai, sai kace baka san sunanta ba, bayan ko jiya ma kun haɗu a nan" ya gyada kai ya ce
"Ai ban sani bane" wani kallo take masa ya ce
"Me kika sani game da ita?" Ta ce
"Kamar ya kenan?" Ya ce
"Inda tayi karatu, da dai wai yadda tayi rayuwa" ita dai Suhaila at this point ta gagara gane kan Yayan nata dan ko kaɗan shi ba me son maganar mutum bane ballai ma na Azrah, ta ce
"Toh Ni dai abin da zan iya cewa shine sanda take aiki anan gidan dai nasan tana karatu data gama secondary kuma gwamnati ta ɗauki nawin ta zuwa India, kuma she did well wlh Ma Shaa Allah abin sai wanda ya gani lokacin tayi ta trending ai a media ko baka gani bane?" Yayi shiru shi kwatakwata wanda ya gani da wannan sunan bata masa kama da ita ba, abin da ya daure masa kai, haka dai Samira ta faɗa masa itama, throughout yau abin daya wuni kenan a media yana searching dinta kenan, ya ce
"But bata yi kama da ita ba ai wacca na gani ba" yayi maganan dan son jin wani karin bayanin, Suhaila ta ce
"Tayi make up ne, shiyasa" Saif ya ce
"Ohh, Amma bayan dawowanta ta cigaba da aikin ne?" Wani kallo ta masa ta ce
"Wani aikin kuma? Lallai ne ma, tayi degree shine zata zo ta cigaba da aikin aikatau? Amma kai mugu ne, ai sai ka mata fatan aiki a babban waje" ya ce
"Okay" ta ce
"Amma na tambaye ka mana, duk waɗannan tambayoyin kuma fah?" Ya ce
"Nothing, kawai naji na tambaya ne" ta ce
"Yanzu kuma? Kai da ka tsana a maka maganar ta?" Ya ce
"Toh yanzu kuma naji ina so naji Shiyasa kuma na tambaya" Ta yi 'yar dariya ta ce
"Ya Saif kenan! Da ban sanka bane toh" daga haka ta miƙe tayi hanyar dakinta ta ce
"Good night" ya jingina da resting chair din ya lumshe ido bai san minti nawa ya dauka ba kawai ji yayi Mummy ta ce
"Kai kuma fah Malam? Dama baka tafi ba?" Ya buɗe idonsa yana kallonta sai kuma ya miƙe, Mummy ta ce
"Ni kam ko akwai matsala ne?" Ɗan ware ido yayi ya ce
"Matsala kuma Mummy, A'a, sai da safe" daga haka ya nufi kofar fita"...
Samira ga baki ɗaya yau dai ta kasa gane kan Saif, fushin ma tun daya zo babu shi, tana zaune jikinsa suna kallon photos ɗinta kamar yadda ya bukaci hakan, hamma ta fara ta ce
"Ni fah Deen bacci nake ji" ya ce
"Alright, ai it's already late" daga haka ta miƙe ta wuce kan gado.
Washe gari kamar ko da yaushe Zahra ta fita ta hura wuta, Azrah ta fito dan taimaka mata, Zahra dake fifita wutan murhun ta ce
"Yaya miko min tukunyar wutan ya kama" Azrah dake tattare cikin kitchen ɗin saboda yadda ya ɓaci ta miƙe ta ɗauki tukunyar ta ce
"Bari na ɗibo miki ruwan" daga haka ta wuce wajen randa, ta buɗe kenan zata ɗeba ta jiyo muryan Mama
"Kar ki kuskura kice zaki ɗiba ruwan nan idan ba haka ba zaki sha mamaki na ainun" Azrah ta ɗan tsaya sai kuma ta juya ta kalli Mama dake bakin kofar barandanta ta ce
"Mama ruwan wanka zan ɗiba fah" Mama ta kundundumo mata wani ashar ɗin ta ce
"Toh ki ɗiba ruwan tunda uwarki ki ce ta ɗibo" Zahra ta ajiye mafificin hannunta tana kallon ikon Allah, Azrah ta juyo a zuciye ta dawo wajen kitchen, Zahra ta ce
"Mama ruwan wanka fah zata ɗiba ba wanki zata yi ba" Mama ta sake baki ta ce
"Toh sannu mara kunya fisararriya ai nasan dole sai ke ɗince zaki yi magana, toh kizo ki diba tunda ke ce me gashi a ka" Zahra ta ce
"Toh ai naga randan ma namu ne, kuma ruwan cikin ma Bappah ne ya tsiyo mana jiya" Mama ta ce
"Dan Allah Zahra idan kin isa ki zo ki diba tunda haka ne" Zahra ta miƙe ta karɓe tukunyar hannun Azrah ta ce
"Naga ai randan namu ne kuma Bappah ne ya biya kudin ruwan da masu moya suka kawo, kuma ai wajen aiki zaki" Mama ta tsaya tana kallon ikon Allah tana wani irin murmushi tare da kaɗa kafa
Azrah tayi saurin rikota ta ce
"Zahra ki bari, zanje na ɗibo a gidan Maman Nana ai suna da rijiya" Zahra ta ce
"Wlh ba zaki je ba, haka kawai ki wani fita ɗibo ruwa? Da girman ki? Ai wanda yake gidan nan da shi zaki yi" Umma ce ta leƙo tana kallon Zahra ta ce
"Zahra idan na isa da ke kada ki taɓa ruwan nan" Zahra ta tsaya kallon Umma, Umma ta juya ta shige ɗakinta, Zahra ta fashe da kukan takaici tana cewa
"Ni dai Umma kin cuceni, haka kawai ki wani ce in kin isa da Ni?" Bil hakki take Kukanta, Mama taja tsaki ta ce
"Ai da kin gwada daga ke har Uwar naku zaku sha mamaki na" Zahra ta dinga hararanta tana murguɗa baki, Azrah ta ɗauki bucket ɗin, Zahra ta karɓe ta wuce tafita zuwa neighbors ɗinsu, bata wani daɗe ba ta shigo da ruwan a kanta har sannan tana goge hawayen daya ki tsaya mata, ta zuba sauran a tukunya sannan ga ajiye bucket ɗin ta shiga ɗakin tana turo baki, Umma taki kulata Azrah kuma tayi tagumi, kwana biyu har sun huta da bala'in Mama ashe ba canzawa tayi ba
Zahra ta zauna gefen Azrah tana cuno baki, Azrah ta kalli Umma ta ce
"Idan na dawo anjima Ni da Zahra zamu tafi siyayya Umma, duk wani abu da muke Sharing zamu bar musu mu fara amfani da sabo, hatta gas Umma zamu tsiya, ba Shikenan ba?" Umma ta ce
"Nima tunanin hakan na fara dan kar ta cigaba da iko da kayan gidan" Azrah ta miƙe ganin lokaci yana wuce wa ta fita daga dakin ta wuce toilet.... Bayan ta gama shiryawan tama Umma sallama sannan ta tafi..
Tun data shiga taga sai gyara ake a cikin Companyn, hakan yasa ta wuce office ɗinta bayan ta gaisa da PA nan ta fahimci gyaran da ake yi..
Tana zaune a office chair ɗinta tana duba aikin da akwai a ranan, wasu cleaners data kira suna ciro mata wasu tsofaffi file...
Da gudu motar sa ta shigo layin, hakan ya sa securities dake zaune bakin gate ɗin wangale masa gate da sauri, kusa kan motar nasa yayi cikin haraban wajen sannan yayi parking a parking space nasa, dama ba wanda yake parking a wajen. Security ɗayan ya kalli abokan aikin nasa ya ce
"Yanzu kuma ai shikenan bamu da wani freedom tunda har Allah yasa mutumin nan ya dawo" ɗayan ya ce
"Hmmm ai yanzu komai zamuyi sai dai muyi taka tsantsan"
Buɗe motar yayi ya sauka kamar ba zai sauka ba, wanda yake zaune a kujeran me zaman banza ya sauka shima
Duk wasu securities da cleaners na compound ɗin haka suka dinga zuwa suna miƙa gaisuwa, a dakile yake amsa musu banda abokinsa dake amsa musu da fara'a, a haka ya wuce sama cike da izzah, duk wasu kananun ma'aikata suka fito da niyyar tarban sa, office ɗinsa ya wuce kai tsaye, Azrah dake zaune a office chair tana kallon system ɗin gabanta, wanda cleaners da ta kira suna aikin fiffito da office file ɗin, yana isa bakin kofar office ɗin nasa ya tsaya kallon office ɗin a buɗe juyawa yayi ya kalli wanda ya biyo sa da briefcase dinsa a hannu cike da masifa ya ce
"Waya bar min office a buɗe? Ko idan aka gama gyaran ba'a san a kulle min bane?" Cike da ladabi Ishaq ya ce
"Sorry sir, PA dinka ce a ciki wanda ta zauna a matsayin MD na wucin gadi" da husky voice ɗinsa ya ce
"And then waya bata wannan guts ɗin?" Azrah dake cikin Office ɗin tayi wani murmushi a ranta tana ayyana lallai ita da wannan MD ɗin zasu kwashe 'yan kallo dan daga jin yadda yake magana bashi da kirki, hakan yasa ta maida idanunta kan system ɗin gabanta tana ɗan zuya kanta akan office chair din, dan ba zata bari ya fara raina ta ba, yanzu tasan kanta not like before, Ishaq ya ce
"I'm sorry sir, Nima ba wai na san komai bane" Cleaners da suke ciki suka miƙe dan duk a tsorace suke suna so su fita karya kama su, Azrah ta juya tana kallonsu ta tamke fuskarta with serious tone ta ce
"Nace ku bar aikin ne da zaku wani mimmiƙe? Toh ku karasa aikin dana saka ku" Ba tare data Kalle su ba ta cigaba da dannan system ɗin, da izzah ya shiga office ɗin tare da wanda suke bayansa, takaici ne ya kamasa ganin yadda take juyi da kujerar kamar kuma batasan ya shigo ba, a fusace ya ce
"Ko baki san mutane sun shigo bane?" Ba tare data ɗago ba ta ce
"Su Mutanen basu iya sallama bane? Ko haka aka koya musu?" Ba shi ba hatta cleaners da suke cikin Office da wanda suke bayansa da abokin nasa duk da tsananin mamaki suke kallonta, Adam na kallon ɗayan cleaner ya ce ƙasa ƙasa
"Amma ina ga wannan bata san wanene MD ba ne, ina ga saboda baƙuwa ce a wajen" karaf a kunnen Azrah, sai sannan ta janye idanunta daga kan system ta kalli Adam ta ce
"Toh shi wanene da ban san sa ɗin ba? Haka ake treating mutane dama? Ko kuma dan yana gadaran shine MD sai yayi ta faɗa wa mutane maganar daya ga dama" da sauri Adam ya sauke kansa dan tsoro ya shige sa ganin ya sake jawo wata maganar, sai kuma ta ɗauke kanta daga kansa ta mayar bakin kofar dan ganin wanene wannan mutumin, bata san sanda ta mike da sauri ba, shima ja da baya yayi yana kallon with shocked written all over his face.....
Jiddatulkhayr writes
Episode 70: Azrah vs MD Sadeeq, The outburst scene
With shocked clearly written all over his face yake kallonta, nuna ta yayi da yatsa ya ce
"Me kike min a cikin Office? Waya baki guts ɗin shiga min har da zama a kan office chair dina bayan Ina da kyankyami ba'ko wace kazama take shigar min Office ba? Sannan ke dole inda nake sai kin je ne?"
Miss Safiyya da karasowanta kenan, murmushi ta fara duk da bata ga meke faruwa ba amma yadda taji MD na ɗaga murya tasan definitely da Miss Azrah ce
Azrah tayi dariya cike da ɓacin rai ta ce
"Really? Ashe kai wani ne ko? Toh a idon wanda basu san ko kai wanene bane, amma Ni bai wuce na maka kallon coursemates ba, idan har Ni ban kiraka da kazami ba kai kana da bakin kira na da ƙazama ce? And mind you baka kai ko kusan kai wa har na taka inda kake ba, ka sani nan ma sai da aka bini har gida aka bani appointment ba tare da consent ɗina ba balle request, kai ne ɗan wahala da kake fama da wannan kujerar MD ba Ni Azrah ma" tana gama faɗan haka ta juya zata ɗauki Jakkanta
Ba MD ko Manager ba, harta securities, clearens, sauran ma'aikatan wajen kallon Azrah suke da baki buɗe dan tun da aka kafa wannan ma'aikatan wajen shekara da shekaru babu wanda ya taɓa faɗawa MD magana, tun kuwa kafin ya fara aiki a company, wasu kuwa sunji daɗin hakan amma tabbas suna tausayinta, MD yama rasa wani magana kuma zai ce dan binta da kallo yake haka as-manager
PA ne ya ɗan tsaya yana daga bakin kofar ya ce
"Meke faruwa ne haka?' cike da takaici MD ya fara magana da ihu, anzo an bawa wannan kucakar yarinyar seat ɗina har zata faɗa min magana Ni da Office Dina? Toh tabbas yau zata san wanene Ni a wannan Company inaga baku faɗa mata wanene Ni ba?" Tun kafin PA yayi magana Azrah ta rigasa ta ce
"And so what? Ga ka ga Company ka cinyeta, yanzu ma zan bar muku kayanku gayyar tsiya, kai ne ya dame ka amma Ni kallon nothing nake mata, PA ya yi kasa da murya yana kallon MD ya ce
''Haba Sir Sadeeq Alhassan, bacin rai ba naka bane, bata san wanene kai ba sannan ai itama ba ita ta bawa kanta office ɗinba, Mr. Alhassan ne da kansa ya bata wannan wajen yace na wucin gadi kafin ka zo, Sadeeq banda huci babu abin da yake yi tabbas azrah ta masa abinda ba zai taba mantawa ba a bainan nasi zata masa wannan cin mutuncin
PA ya Kalle ta ya ce "Miss Azrah please ki basa hakuri Kinga ɗan Mr.Alhassan ne" wani murmushin takaici azrah tayi ta ce
"I'm sorry Sir amma gaskiya ba zan basa hakuri ba, shi yazo ya zageni kuma kace na basa hakuri dan yana gadaran ubansa wani ne? Kuma dama haka Companyn naku yake sai abin da yaga dama zai wa mutane kuma ace a basa hakuri? Da nasan haka ne tun farko ba zan karbi wani offer daga gare ku ba, sannan shima dana san anan yake ko da wasa ba zan fara zuwa ba dama" tana kai wa Nan ta ratsa ta gefen Sagir ta fita, duk aka bita da kallo, Sadeeq ya tamke fuska ya ce 'Out' duk cleansers da suke mata aiki a ciki suka fara fita, Miss Safiyya ta karaso wajensa tana karairai zata masa magana ya sake tamke fuska yana kallon mutanen bayansa yace 'leave, i don't want to see anyone here" duk suka juya suka fara barin wajen
Azrah da sauri sauri take sauka kan stairs samuwarta ta ganta a gida shine kawai, duk da ta tsaya da izza a gaban MD ta mayar masa da magana, amma zuciyarta cike take da nauyi da haushi, bata taɓa jin rauni irin wannan ba wulakanci a fili, kuma gaban mutane zai mata, wato shi duk inda ya ganta sai ya nuna cewa she's nothing bata damu ba amma kazama daya kirata for that matter
Tana fita daga building ɗin, hawayen da ta riƙewa suka fara gangarowa, bata bari kowa ya gani ba sai ta sa hannu tana sharewa da sauri kuma with style, ta nufi gate da niyyar barin harabar kamfanin gaba ɗaya
A daidai lokacin ne motar Mr. Alhassan ta iso gatekeeper ya buɗe masa, ya shigo da nufin parking amma idonsa ya sauka kan Azrah da ke tafiya cikin sauri, tana share hawaye.
Sosai yaji hankalinsa ya tashi ainun, zuciyarsa na buga da sauri kawai ya tsaya da motar dab da ita, ya sauke glass cikin damuwa ya ce
"Azrah... Ina zaki haka?"
Tayi shiru na sakanni, sai ta ce a hankali, muryarta na rawa
"Gida, Sir"
Yayi shiru yana kallonta, idonsa na yawo akanta yana Studying dinta, ganin yadda take share hawayen ne kuma ya ce ba shakka wani abu ne ya faru
"Hope all is well?" ya tambaya, cikin karamin murya, kamar yana tsoron amsar da zata basa
Azrah ta girgiza kai, "Yes Sir"
Amma yadda tayi magana kai ka san cewa akwai, tayi maganar ne in pain Mr. Alhassan ya tsaya yana kallonta kawai yayi gaba da niyyar parking ya sauko yaji maganar da kyau, wata irin damuwa na ratsa shi dan shi akwai tausayi, Me ya faru? Wanene ya taɓa ta haka?" ya faɗa a zuciyarsa.
Azrah kuwa ganin yayi gaba da motarsa yasa tayi saurin fita, har tana harɗe ƙafafuwa dan bata san me zata ce masa ba idan ya tambaye ta, hakan yasa ta fita, fortunately tana fita kuwa ta samu wani adaidaita kawai ta shiga ba tare da sunyi ciniki ba
Mr. Alhassan ya sauko a motar sa sai kuma bai ganta ba, bin building ɗin yayi da kallo ganin bata nan yasan kuma ba wai shiga ciki tayi ba dan bai ci ace har ta isa ba, kallon wani yayi a bakin gate ɗin ya ce
"Ina wannan yarinyar?" Mutumin cike da girmamawa ya ce
"Ai ta fita, Sir" ..
A cikin mintuna kaɗan da Azrah ta bar kamfanin, labarin abin da ya faru tsakanin ta da MD Sadeeq Alhassan ya bazu kamar kamar wani abu. Daga masu gadi zuwa cleaners, daga ma'aikatan admin zuwa technical team, kowa na magana, kowa na mamaki kuma
"Wallahi yau yarinyar nan Azrah ta gama biya na" inji Ishaq yana dariyar mugunta
Adam kuwa ya ce "Kai baka ga bakinsa yayi shiru ba?, habaa gaba da gabanta ne ai ya ɗauka yadda ya saba mana haka zai nama kowa bai san ba kowa ake wa hakan ba, gashi ta gwada masa cewa su ne aikin ta dama, yau ai munga karyan ta kare ai, amma ban so data tafi ba"
A second floor, wasu ma'aikata suna ta faɗin yadda suke ganin MD bai kyauta ba, kuma yadda Azrah ta tsaya da ƙima duk da zafin zuciyarta amma da bata biye masa ba
Amma a Reception, Miss Safiyya ba zaka iya cewa ka kalan expression dinta ba, ta ce
"Ni dai wallahi na tausaya mata" ta faɗa tana daure fuska, jin kowa yayi banza da ita ta kuma cewa
"Amma gaskiya yarinyar nan tana da matsala, babu manners ko kadan a tattare da ita, wa ya ce ta tsaya faɗa da MD a gaban mutane? Wannan ba wayo bane rashin tarbiyya ne"
Miss Merry kuwa ta tsaya gefe tana kallonta da mamaki sai dai bata ce komai ba, amma cikin ranta tana jin cewa Safiyya babu wanda ya kaita murna, Mahmud ya ce
"Ke dama Miss Safiyya kin taɓa bin bayan gaskiya ne? Duk da bana wajen amma yadda ake maida zance gaskiya MD bai kyauta ba kuma ko a gabansa zan fadi hakan, taya zai fara faɗa mata magana anyhow" Abubakar ya ce
"I'm telling you, kawai ka fara faɗawa mutum magana dan ka gansa a office dinka? Aikin da yarinyar nan tayi a ɗan kwana biyu data yi a Companyn nan MD sai dai yayi a sati biyu, wani tsiyar yake aikatawa" Mahmud ya miƙe haka ma Abubakar suka fita daga wajen gaba ɗaya...
Yadda Mr. Alhassan yake jin mutane na magana suna kallonsa sai su yi shiru yasa ya fahimci a nan kila aka ɓata mata rai, ya shiga office ɗin yana kallon PA ya ce
"Wai me na ji ana faɗa akan Azrah da MD ne ban gane ba?"
PA ya jinjina kai ta ce "Wallahi Sir, komai ya faru ne a gaban ido na. MD ya shigo ya same ta a office dinsa, ya fara faɗa ba tare da ya tambaye ta yadda ta shiga ba, ya kirata da sunaye marasa daɗi..." Daga haka ya shiga basa abin daya faru har inda yace ta basa hakuri
Mr. Alhassan ya ɗaga masa hannu da sauri,
"Stop right there! Kai ba ka san halin Sadeeq bane? Kana tare da shi amma kai ba ka karanta shi ba? Idan har ka ga mutum kamar Azrah ya kai matakin cewa zai bar ma'aikata duk da yadda kace min ita ba 'yar kowa ba, kai baka kamata ka tsaya gefe ba ka zuba ido ba, ba zaka iya dakatar da ita bane? Wannan ba laifi ba ne kawai cin mutunci ne, kuma kai da kanka kasan wanda ya bata office ɗin a wucin gadi toh akan meyasa Sadeeq zai mata haka kuma ka bi side dinsa?"
PA ya sunkuyar da kai ya ce"I'm sorry Sir"
Mr. Alhassan ya jinjina kai cikin ɓacin rai ya ce
"Bana son hakan. Wannan company ba gaban wani bane, da wanda bai iya sarrafa harshen sa ba, ba zai mulka mutane ba. And if Azrah leaves, wallahi we lose more than just one staff we lose the trust of the future"
Ya juya ya fita, zuciyarsa cike da zafi, wannan abin ba zai tsaya nan ba...
Azrah har ta isa gida hawaye bai dena gangaro mata ba, amma sai hamdala take tunda har ta faɗa masa maganganun da ransa ya so, tana shiga gida ta wuce ɗakin Umma, Umma na kallonta ta ce
"Lafiya kuma?" Azrah ta gyaɗa kai ta ce
"Kai na ke ciwo Umma, ga kuma rana yau har ido na yana so ya tashi wanda yayi kwana biyu bai ta shi ba" Umma tayi ta kallon Azrah sai kuma ta ce
"Toh Allah ya yaye miki?" Ta masa da
"Amin" daga haka ta miƙe ta wuce dakin su, ganin Zahra tayi tana zaune bakin katifa tayi uban tagumi, ta ce
"Ke Zahra lafiya dai?" Zahra ta ce
"Ina Kiga ga lafiya? Yau Bappah a sakar gida ya zage Umma tass kamar zai dake ta wai dan ta shiga ban daki Habibah bata samu ta shiga ba saboda zata fita tallah" Azrah ta ce
"Amma Ni kam Bappah lafiyar sa?" Zahra ta ce
"Wlh yau ko Mama tayi hankali da Ni dan zan iya zaginta tass babu ruwa na, baki ga yadda rai na ke tafarfasa ba" Azrah ta zauna tayi tagumin itama, Zahra ta ce
"Bari na daura girki, wanda mukayi ɗazu Azizah da Baby sun zo gaishe da Umma ne shine aka zuba musu" Azrah ta ce
"Kar ki damu, dama ba yunwa nake ji ba, ai naga sha biyu ne yanzu" Zahra ta miƙe, Azrah ta ce
"Har sun tafi ne?" Zahra ta ce
"Eh, dama aika zasu wuce ne" daga haka ta fita compound.....
Mr. Alhassan yana tsaye kan Sadeeq da Sagir inda ya ke shiga ba tanan yake fita ba, ya maida kallon sa kan Sagir ya ce
"Kai meyasa baka faɗa masa gaskiya ne? Haka ake yi? Ko da yaushe duk abin da yayi shine daidai?" Sauke kansa ƙasa yayi ya ce
"I'm sorry sir, za'a gyara" Mr. Alhassan ya ce
"And ka je ka nemi inda yarinyar take ka bata hakuri" da sauri Sadeeq ya ɗago kai yana kallon mahaifin nasa, Mr. Alhassan ya ce
"Idan kuma ba zaka iya ba, just tell me ban isa da kai ba" yana kai wa nan ya fice daga office ɗin, Sagir ya kalle Sadeeq ya ce
"Kuma zaka je ɗin?" Sadeeq ya masa wani kallo
Sagir ya ce "Ahtoh na ɗauka ai zaka yi ne, know your worth, yanzu Mr. Yana cikin ɓacin rai ne amma nasan ba zai saka ka ba, yin hakan zai sa yarinyar ta raina ka ainun" Sadeeq ya jinginar da kansa ya kumshe ido, Allah kaɗai yasan kalan yadda zuciyar sa take yau....
Tunda Zahra ta ga Mama ta fito ta ɗaga muryanta tana wake waken habaicin ta,Siyama ta kalli Mama jin abinda Zahran ke cewa
"Duniya makaranta, kayi me kyau kaga sakamako mai kyau, kayi tsiya tun kafin ka mutu ka gani cikin kwaryan ka, jahilici dai bata yi ba, kai jahili ai babban masifa ce" Mama dai sai kallonta take yi, ita kuma Zahra tana girki ta tana kuma ɗaga murya amma ko da wasa taki yarda ta kalli inda Mama take
Can ta miƙe ta wuce zata ɗauki turmi da tabarya, Mama ta ce
"Idan bana Uwarki bane toh kada ki kuskura ki taɓa" Zahra ta juyo a fusace tana kallon Siyama claiming cewa ta ɗauka ita ce tayi maganar ta ce
"Ki daina zagin Uwarmu dan baki ga abin zagi a jikinta ba tunda 'ya'yanta nitsassune" Siyama ta sake baki, Mama ta ce
"Kambala'i da Ni kike Zahra ?" Zahra ta juya tana kallon Mama ta ce
"Kinji nayi dake ne? Ai da siyama nayi da har zata zagi Uwarmu, kuma naga turmin Bappahn mu ne ya tsiyo da har za'a hana mu amfani da shi"
Mama a zuciye ta karasa wajen zata mareta, da sauri Zahra taja baya ta ce
"Mena miki?" Ta ce
"Uwarki kika yi shegiya" Zahra ta ce
"Ni ba shegiya bace, sannan ba Uwata ba" Mama tayi kukan kura ta yi kan Zahra tana cewa
"Ni zaki faɗawa magana?" Ta shaketa kamar zata kasheta, Siyama tana tafi da dariya, kamar wadda aka wurgo Azrah daga daki haka ta faɗo compound ɗin ta ce da wani irin muryan da basu santa ba
"Ki sake min 'yar uwaaaaaa" tana huci ta karasa kan Mama ta finciko Zahra wanda idan ka kalli Azrah a wannan lokacin sai ka tsorata hatta idonta sai daya yi mugun jaa, tana kallon Mama ta ce
"Baki isa ki dake ta ba tunda Umma mu bata taɓa dukan yaranki ba" Sallamar Bappah ne yasa Mama ta fashe da kuka ta fara faɗin
"Yanzu har ya kai da zaku iya ɗaga hannu ku dake Ni?" a gigice Bappah ya karaso ya ce
'"Menene?" Mama tace "daga musu magana shikenan Uwarsu ta saka su suka kama duka na" Siyama ma ta fashe da kuka
Sai ga Umma ta fito tana kallon Mama ta ce
"Kiji tsoron Allah, ki sani yana ganinki" Bappah rai ɓace ya juya yana kallon Umma ya ce
''ki je na sake ki" a fusace Zahra ta ce
"Dama ba ɗaukan nawinmu kake yi ba balle ya dame ta, Umma banda wahala babu abin da take sha anan" Umma kam tsabar shock ta gagara magana, Azrah da Zahra suka fashe da kuka
Mama ta yi wani buɗaaa tana juyii
Sallama aka yi duk suka juya.....
#Jiddatulkhayr
08110615256
Episode 71: A Throne in the Fire
Ta karaso cikin gidan tana kallon Bappah, a zuciye Azrah ta kama hannun Zahra da nufin su shige ciki, Umma ta dake tana kallon makwabciyarsu sirkan Maman Nana kafin ta gaishe ta Dattijiwan Matan ta ce
"Haba mana ashe kana gida ake wannan hayaniyar Malam Muhammadu?, na ɗauka baka nan ne ai har na shigo" Bappah ya gagara cewa komai,
Zahra ta ƙwace hannunta ana Azrah ta tsaya kallo, Mama tayi kasa da murya ta ce
"Yaran nan ne basu da kunya Mama, kalli wai har Ni yaran nan zasu ce zasu yi faɗa da Ni?" Kallo ɗaya Dattijiwan ta mata ta ɗauke kanta, Zahra ta ce
"Kakan Nana karya take, duk ihu da masifan da kike ji ba muryanta bane? Yanzu fa daga zan ɗauki turmi shikenan fah ta fara masifa, harda sa Bappah'n mu ya sake Umman mu, dama kuma ko kallonta ya daɗe baya yi" Sirkan Maman Nana ta fara salati ta ce
"Haba Bappah? Ina kallon ka kamar mutumin kirki? Ashe dai abin dake yawo a unguwa haka ne? Yanzu fah jin hayaniyar su yayi yawa ne shine na fito a gigice dan nayi musu magana ashe kana nan? Ikon Allah" mayar da kallonta ga Mama tayi ta ce
"Ke kuma ga ke ga duniya, idan me kyau kika yi zaki gani idan akatsin haka ne ma shima zaki gani" Umma da har ta isa kofar ɗakinta zata shiga ta ce mata
"Maman Azrah kiyi hakuri, zaki ga ribar hakurin ki wata rana, wanda bai ga ribar hakurin sa ba toh hakurinsa ya gaza ne" Umma murmushi tayi kawai ta ce
"Nagode Mama" daga haka ta karasa shiga dakinta, ita kuma ta juya ta fita, Mama ta bita da harara ta yi wani tsaki ta ce
"Ji jaraba" daga haka ta wuce nata ɗakin aka bar Bappah tsaye a wajen shikaɗai wanda ya kasa ɗaga kafar sa ma
Zahra tana tsaye kan Azrah a ɗakinsu ta ce
"Kuma kina ganin za'a samu ne?" Azrah ta ce
"Kina tunanin wai ko ba za'a samu ba zamu kwana gidan nan ne yau? Ai dole zamu samu inda zamu kwana, dan duk gadaranta Umma bata da kowa ne anan, kuma zata ce zata ga yadda zamuyi" Zahra ta ce
"Toh kiyi wa Umma magana ko?" Azrah ta girgiza kai ta ce
"Yanzu kuma sai Umma tace A'a, ko baki san halin Umma bane?" Zahra ta ce
"Lallai baki san ko Umma ranta yayi mugun ɓaci ba, hakuri fah take for how many years now? Haba mana" daga haka Azrah ta ɗauki hijabinta ta saka ta buɗe wani jakkanta ta ciro ATM card dinta sannan ta fita..
Bata wani ɗau lokaci ba sai gata ta shigo ko da wasa bata kalli inda Mama da Yaranta suke zaune ba, kana ganinsu kasan cike suke da farin cikin, Sallama tayi a bakin kofar ɗakin Zahra ta leƙo, mika mata takeaway guda biyu tayi ta ce
"Ga shi kije kuci da Umma kafin na dawo" tana kallonta ta ce
"Ina zaki je kuma?" Ta ce
"Ina zuwa idan na gama zaki sani" daga haka ta juya ba tare data jira abin da zata kara faɗa mata ba....
Can yamma Azrah na duke a kan tabarman Maman Nana, tana jin nasihan da Kakan su Nanan ke mata ta ce
"In shaa Allah Kaka, dukkan mu burinmu kenan mu zama na gari mu farantawa Umman mu" ta ce
"Ma Shaa Allah, Allah yayi muku Albarka, kuma hakan karya sa ku ce zaku juyawa mahaifinku baya don koma menene shi uba ne a gare ku" gyaɗa mata kai tayi, wani matashin mutuni ne ya shigo ya zauna yana kallon Mahaifiyarsa ya ce
"Mama an gama komai" ta ce
"Sai ka bata komai a hannunta, fatan kuma duk shaidun sun saka hannu?" Ya ce
"Tun ɗazu aka gama wannan, gobe dai ya rage mu tafi kotu" ta gyaɗa kai cike da gamsuwa, kallon Azrah yayi haka yasa Azrah ta ce
"Sannu da kokari, mun gode Allah saka" ya ce "Amin"
Miƙa mata key yayi da envelope ɗin, ta karɓa tana sake masa godiya, daga haka ya juya ya fita, Kakansu Nana ta ce
"Gaskiya Ni dai da kunji ta nawa Allah ba zan bari ki tsiya ba, dan daɗin abin ma naga nan makwabtane amma ai da cikin gidan ne ya dace ku zauna" Azrah tayi murmushi ba tare data ce komai ba, dan tasan babu wanda zai fahimci halin da suke ciki, miƙewa tayi tana kallonta ta ce
"Bari na tafi gida, kar Umma ta fara nema na" ta ce
"Toh Shikenan, Allah kara rufa asiri" ta amsa daga haka ta fita, lokacin data shiga gida ta samu already har an fara kiraye kirayen Magrib, gidan nasu kamar wanda ake cin kasuwa haka ya zama, Mama da tawagarta su Maman Asabe, su Hajiya kaltume ne zaune a compound din, taɓe baki tayi ko kallon daya daga cikinsu bata yi ba ta wuce daki direct, Umma da Azrah har haɗa baki suke wajen cewa
"Ina kika je?" Azrah ta zauna tana kallon su, sai kuma ta miƙawa Umma envelope ɗin hannunta tare da key, Umma taki karɓa ta ce
"Me wannan Azrah?" Zahra ta ce
"Toh Umma ki karɓa mana sai ki gani" Azrah ta ajiye mata, Umma ta buɗe tana fara karanta contents ɗin ta sake baki tana kallon Azrah, sai kuma ta fara share hawayen daya fara gangaro mata, Zahra ta rungumata Itama tana share nata hawayen, Azrah kam kallo window take bata so ta sake wani kukan bayan wanda tasha ɗazu, Umma dakyar ta ce
"Why Azrah?" Azrah ta kalle Umma tana kokarin maida nata hawayenta ta ce
"Umma hakan ne mafita, idan ba hakan ba bamu tsira ba, kiyi hakuri nayi ba tare da shawarar ki ba" Umma ta ce
"Allah ya miki Albarka, Allah kare min ku ya daukakamin ku" ta amsa da 'Amin' daga haka suka miƙe dan yin alwala, saboda har an fara tada ikama, Zahra ta ɗauki pure-water ta miƙawa Azrah ta ce
"Kar mu taɓa ruwan ballai ta samu bakin gaya mata magana" Umma ta ce
"Kuma bana son duk me zasu ce ku tanka musu, ko da wasa kada ku mayar da martani"
Daga Zahra har Azrah babu wanda ya tankawa Umma, Zahra ta fita ko kallon matan dake sakar gidan bata yi ba ta wuce toilet, Azrah kuma ta zauna tana alwala, bayan Zahra ta fito sai ga Umma ma ta fito tana tsaye bakin kofar ɗakin tana nata alwalan, su Mama kam banda shewa da hira babu abin suke yi ko haraman yin Sallahn basu da shi, Kamar daga sama suka ji muryan Mama tana faɗin
"Wai Ni kam yau naga jaraba, kamar dole ku bar gida amma kun gagara?" Umma ta shige ɗaki haka ma Azrah, Zahra ta ce
"Wannan gayyar tsiya? Dama idan banda ƙaddara zaki ganmu anan ne? Ai dan wlh tun farko kar mu bar nan aga kamar muna gudun mahaifinmu ne yasa muke nan amma kema kinga kalar mu kinsan bamu yi kama da wanda zamu zauna a wannan kejin ba" Mama ta sake baki tana, Maman Asabe ta fara salati tana tafe hannu, Siyama ta miƙe a zuciye tayi kanta, Zahra ta ce
"Wlh ki taɓa Ni zaki sha mamaki na yau" kamar remote haka ta tsaya Azrah ta fito ta kama hannun Zahra suka shiga ciki, nan kuwa matan gidan suka fara magana suna jajanta rashin ɗa'an Zahra
Umma na kallon Zahra ta ce
"Ina ban isa dake ba ko?" Zahra ta tura baki daga haka ta wuce kan sallayanta...
Can da daddare Azrah na zaune tana faɗa wa Umma ai gidan dake kallon nasu ne, Zahra ta ce
"Yaya nikam dama ba'a unguwar nan bane" Azrah ta girgiza kai ta ce
"Muna neman urgent ne Zahra, wannan kuma ɗan kanin mijin Maman Nana ne ya taimaka wajen nemo mana, shiya wuce gaba har aka gama komai, ashe tun sanda wanda suke gidan suka tashi aka sa a kasuwa saboda yayi tsada ne ba'a tsiya ba"
Umma ta ce
"Wannan ɗin ma is Okay ai, Allah saka masa Albarka" Zahra ta ce
"A'a Nima ba wai kushe wa nake yi ba,kawai nafi so muyi nisa da nan ne, amma ai naga kaf unguwar nan babu gidan daya kai wannan kyau, kawai girma ne bashi da shi"....
Washe gari da safe tun da suka yi sallahn asuba Azrah ta fita, wanda kafin ta fita ta hana Zahra hura wuta, akan zata kawo musu kayan karyawa dan karma su taɓa wani abu balle su sake samun musanyan yawu da Mama..
Tun da safe ake ta hada hada a Company, ba karamin murna ba suke ciki na ganin nan take daga shiga wannan join hand da su suka samu wannan riban, hakan yasa ake sabon shirin tarban su dan su sake haɗa hannu,
Manyan baki ne da suka zo ranan suka sake zuwa, attajirai masu saka hannun jari wannan karan ma sun zo ne domin ƙarin haɗin gwiwa da Majestic Vault Ltd, An karɓe su hannu bibbiyu, cikin girmamawa da alfarma.
Kamar yadda suka bayyana, zasu ƙara saka hannun jari saboda abin da suka fara ya riga ya haifar da about 20 million na riba, kuma yanzu suna shirin haɗa jari da wani babban kamfani a kasar waje wanda zai kawo musu close to 100 million, a sati biyu zuwa wata guda, Wannan ne ma ya sa suka fara murna, Mr Alhassan yasa Mahmoud da PA su raka su MD idan sun gaisa sai su bar musu su karasa
Suna shiga suka sake gaisawa na biyu cikin alfarma
Ɗaya daga cikin baƙin rashin ganin Azrah ya kalli abokinsa sai kuma suka ce
"We want to meet the person we started working with…"
Sai PA ya nuna musu MD, bakin suka sake kallon juna... ɗaya daga cikinsu ya ce
"Wait... is this the same person?"
Ɗayan mutumin ya ce
"No, it's not. Where's the lady?"
Mahmoud yana tsaye yana sauraren su amma be ce komai ba, yasan za'a rina tun daga yadda ranan suke kallonta musamman Babban Alhajin cikinsu, kamar ya sani kuwa sai Alhajin ya juyo garesa ya ce
"You know her, right?"
At this point Sadeeq ji yake kamar ya ɗaura hannu a ka sabar bakin ciki, ya tamke fuska, Sagir ya ɗan kalle sa shima
Mahmoud ya ce "Oh yeah... sorry, she left the company" Kafin ya basa masa sai ga wayan Oga Mahmoud yana ringing, ya ce 'excuse me" daga haka ya miƙe ya fita
Bakin suka kalli juna dan jin me yace, Alhaji kan ya mike tsaye ya ce
"This MD is not even competent"
Sauran ma ganin Babban su ya miƙe suma suka mike, suka ce
"We can't proceed with this"
PA duk ya daburce ya miƙe da sauri shima yana kokarin sayar da su, ya ce
"Please, at least let's talk..." A fusace Alhaji ya ce
"We know what we want. She was the reason we returned" PA ya sake baki yana kallon su, Sadeeq ya buga kujeran gabansa ya miƙe
Duk yadda PA ya so tsayarda su, suka fita, Sadeeq ya tabe baki, Sagir ya mike yana kallonsa ya ce
"Let's go jare, waste of time" Sadeeq ya ce
"Yan isaka kawai, banda iskanci ya kawo su wai ba za suyi aiki da wani ba? Toh sai me?" Daga haka ya wuce kamar zai tashi sama ya tafi office dinsa,Sagir na binsa a baya
Cikin bacin rai PA ya shige office ɗin Mr. Alhassan yana huci ya ce
"Sir, sun tafi! Sun ce ba zasu cigaba da business ɗin ba..."
Mr. Alhassan ya dafe kai, kafin ya ce komai, sai ga Mahmoud ya shigo yana cewa
"Sir, I heard they left?"
Mr. Alhassan ya ce, "Yes... sun tafi sai" Mahmoud ya furta da takaici
"Honestly Sir, tun farko bai kamata a tura Sadeeq ba. But I'm sorry for saying this…" Mr Alhassan yayi shiru yana rasa me zai ce, yana ji tana ganin zai rasa waɗanda kuɗaɗen
Mahmoud ya ja numfashi, sannan ya ce
"Sir. Aikin da yarinyar nan Azrah tayi cikin two to three days, Sadeeq baya iya yin rabin hakan a cikin two weeks. She's smart, eloquent, and she knows how to attract investors. That man in the delegation, I think he likes her. That's why they returned in the first place" ya numfasa sai ya ci gaba
"Kalli kuɗin da muka samu ta sanadiyyarta 20 million in less than 3 days. Wannan irin kuɗin sai mun dauki 15 months muna work kafin mu tara shi"
Mr. Alhassan ya zuba masa ido, amma ya gagara cewa komai, sai dai zuciyarsa cike take da abinda ya kasa faɗi... Wanda tun farko yasa ya nema yayi aiki da ita wato.. Azrah, ita ce ginshikin nasarar da suke bukata, yasan zata ja masa manyan investors Shiyasa ya bata wannan seat ɗin"
Yana kallonsa ya ce "Mahmoud, i think zamu nemi yarinyar nan shine mafita" ya gyaɗa masa kai cike da gamsuwa...
Ba ita ta dawo gidan ba sai wajajen karfe hudu na rana, a mugun gajiye ta shigo, babu Mama balle yaranta a gida, tana shiga ɗaki Zahra ta ɓata fuska ta ce
"Sannu Yaya, kin kyauta, haka kawai ki wani ce mu jira ki zaki kawo mana abun karyawa sai karfe huɗu zaki wani shigo mana gida?"
Azrah ta dafe goshinta ta ce "kash! Kin san na manta kwata kwata, amma ya kuka yi?" Zahra ta ce
"Kuɗin da Khalil ya basu Umma dama wanda Dada ta bata ba ta taɓa ba, shine naje na tsiya mana abinci" Azrah ta ce
"Ahh, toh Alhamdulillah tunda kun ci" tana kallon Umma ta ce
"Umma naje nayi wani gyare gyare ne, sannan na tsiyo abubuwan da zamu bukata, yanzu zamu iya komawa can idan babu damuwa, nama fi so mu koma tun kafin matan nan ta dawo da Yaranta" Umma ta ce
"Toh Allah yayi albarka" daga haka duk suka mike..
Episode 72 & 73 The Return of Azrah
Gida ne mai ciki da parlor sai kitchen wanda ke ɗauke da cabinet, sai toilet na zamani, dake kitchen ɗin ne a fakon ya sa suka fara tsaya dubawa, sabbin warmers guda hudu, ɗan karamin gas, sai robibin aiki, da wasu kayan aikin da zasu bukata a kitchen ɗin, Umma ta ce
"Ayyah Azrah kudin ba zasu kare ba?" Azrah tayi dariya ta ce
"Duk yawansu kuma sai su kare yanzu?" Suna shiga parlor dai ga center carpet da ɗan deep freezer sai curtains, Zahra dai banda murmushi babu abinda take yi, musamman ganin gidan tiles ne, ɗayan dakin suka shiga nan
Azrah ta ce "wannan naki ne Umma, ɗayan kuma na Ni da Zahra ne, a weekend za'a kawo gado da wasu abubuwan" Zahra tayi hugging ɗinta ta ce
"Alhamdulillah, Allah mun gode maka" kafin nan duk kayansu da yara suka taya su shigowa da su wanda ke compound suka fara shigowa da su ciki, kafin dare duk sun gama aiki.
Mama tayi tagumi ta ce
"Ohh toh ina suka shiga kenan?" Siyama ta ce
"Ke Mama ya akayi kika san cewa basu nan?" Ta ce
"Ki kalli kofar nasu mana, rabi a buɗe yake kuma babu labule, na leka kuwa naga wayam, dama babu wani abun arzikin a dakin nasu ai" Habibah ta ce
"Toh ina suka tafi?" Mama tace
"Ki tambaye Ni na tambaye wa?, naga kusan tare muka dawo gidan"
Bappah dake ɗakinsa sai juyi yake akan gadonsa, tun safe ya rasa meke masa daɗi, haka kawai yake share hawayen dake zuba masa wanda shi kansa bai san dalili ba, ya miƙe ya zauna yana dafe da kansa, buɗe idanunsa da suka yi ja yayi, ya kurawa kofar ɗakin ido yana jin maganganun su Mama dake sakar gidan, a hankali ya miƙe ya isa zuwa kofar ya saka mata sakata yadda ko mutum ya tura ta waje ba zai buɗu ba, ya koma ya zauna sai kuma ya kwanta yana kara jin abin da yake ji na jikinsa na tsananta....
Kafin Isha'i kaff layin unguwar nasu ya gama karaɗewa da cewa su Azrah ne ke wannan gidan, dama karamar unguwa ce hakan yasa duk maganar ya bazu, mutanen da suke shiri har sun fara shigowa suna musu murna, ɗayan ɓangaren kuma banda zagin Mama da Allah wadaranta ba abinda suke faɗi, dan duk gidan da suke shiri da su Umma haka suka dinga Maganar ta da kuma mugayen halayyarta...
Mama dake zaune suna fantayawa da Yaranta sai ga Maman Asabe kamar an jefo ta haka ta faɗo musu gida, Mama na kallon ta ta ce
"Lafiya Maman Asabe da Daddaren nan?"
Maman Asabe ta samu waje ta zauna ta ce
"Mu fah dama mun saba da fitar dare kawai bana zuwa miki ne, wannan halin tun na kauye ne ya bi mu har nan" Mama ta ce
"E, ko" Mama Asabe ta ɗan kalli kofar ɗakin Bappah sai kuma tayi kasa da muryanta ta ce
"Ke Nikam me naji yake yawo a unguwar nanene?" Mama ta ce
"Kar de kinji labarin sun gudu ne?" Maman Asabe ta wani kalle ta ta ce
"Kamar ya kuma? Bayan ga gidan da suka koma kuma, shine ai nazo naji ta bakin ki" Mama ta zaro ido ta ce
"Ni fah ban san maganar ba, kawai dawowa muka yi naga bata nan, dama kin san inda ta koma ne?"
Maman Asabe dai ta hangame baki tana kallonta Mama ta ce
"Haba Maman Abdul, gaki ga kishiyarki gida na kallon juna shine ai nazo jin ba'a si" Mama ta wangale idanu tana kallon Maman Asabe kamar idon zasu fado kasa ta ce
"A'a.. ban.. ban gane gida na kallon gida ba?" Maman Asabe ta ce
"Gidan da 'yan Borno suka ta shi nan suka koma fah!" Mama tayi saurin dafe bishiyar wajen jin kamar jiri ne ke son ɗibarta ta ce
"Wai wannan gidan mai tayils kike magana? Da pilawa ta waje dai?" Mama Asabe ta ce
"Kwarai kuwa, shine dai gidan da suka koma, magana kuma har ya gama karaɗa unguwar nan, shine Nima na zo jin ya aka yi kuma?" Mama dai har sannan bata gama fita a mugun shock da ta shiga ba, da sauri tayi wajen kofar, ta tura kofar gidan nasu don sake tabbatar gidan 'yan Borno ne ke kallon nasu, ai kuwa ta kalli gate ɗin gidan na kallon kofar nasu, ta juyo tana haɗa zufa, ta zauna kan tabarma, Siyama ta miƙe ta fita sai kuma ta dawo ta ce
"Tabbas Umma gidan ne suka koma, kinsan ya akayi na gane?" Maman Asabe ta ce
"Yaya?" Ta ce
"Ai gidan ba'a kunna wutan sakar gidan saboda ba kowa amma yau wutan a kunne yake, sannan kuma jikin gidan ga kwalaye da alama ma ina ga har Tv suke da shi" Mama ta ce
"Dan ubanki rufe min wannan mugun bakin naki, wani irin Tv kuma? Ai sai dai su kalla a lahira ba nan ba" sai kuma ta kalli Maman Asabe ta ce
"Ina ga kuwa Mazan da Azrah ke bi su suka kama musu hayar gidan, ai kuwa idan haka ne ba zan damu ba, su suka sani" a ranta ta fara gyaɗa kai cike da bawa kanta cewa aikinta ya fara ci, kila har Azrah ta fara yawo kamar yadda ta bukaci ayi mata asirin, wani dariya ta yi tunawa da Dada har sannan bata ga kafarta ba hakan ya tabbatar mata duk cikin aikin ne, sauke ajiyar zuciya ta yi, Mama Asabe ta mike ta ce
"Toh Nikam sai da safe" daga haka ta fita, Siyama ta fashe da kuka ta ce
"Shikenan Mama duk sanda aka musu Mugunta sai ya koma Alkhairi, ki kalla gidan da suka koma wannan ai mugun ci gaba ne" Habibah kam na bakin baranda tama gagara cewa komai, Mama ta ce
"Dama fah mutumin ya ce zata fara yawo ne, kuma ina ga Mazan da ta fara bine suka biyo ta kuma suka kama musu haya" Siyama ta sake fashewa da kuka ta ce
"Toh ko muma ai namu Mazan bama su kuɗi bane, amma ace dole ko Mazan banzan ne ma sai masu kuɗi?" Habibah ta ce
"Toh sannu ko?" Siyama ta kalle ta sai kuma tayi saurin share hawayenta, Mama dake kallonta ta ce
"Toh ai naku na arziki ne ba Mazan banza bane" ta gyaɗa mata kai kawai amma tana jin kishin Azrah, sai kuma ta ce
"Kila ma wancan saurayin nata ɗan kasan waje ne ko?" Mama ta zaro ido tunawa da Khalil da tayi sai kuma ta ce
"A'a ba shi bane, dan an raba su da wannan, an shafe ta a kwakwalwarsa ma" daga haka Siyama ta miƙe zuwa ciki ba tare data ko sake bi ta kan Mama ba.
Suna zaune suna cin abincin da Azrah ta taho musu da shi, Umma na kallon yaran nata ta ce
"Bana so ko da wasa ace wani abun zai haɗa ku da Mama ko yaranta wani ya ce zai tanka, ko a hanya ne ta zage ku bana kaunar ku tanka, sannan Zahra ke baki jin magana kwatakwata ba'a isa da ke ba, toh this should be the last time da zan miki warning akan su" Zahra ta ce
"Yanzu kamma aina zasu ganmu Umma? Ai sai dai hange daga nesa" Umma ta girgiza kai dan lamarin Zahra na bata tsoro.
Miƙewa Azrah tayi tana kallon su ta ce
"Ni kam sai da safe" Umma ma ta mike ta ce
"Yama ka mata ace mun kwanta yanzu, tunda gobe ina zaku je wajen cika Jamb ɗin Zahran ko?" Azrah ta ce
"In shaa Allah" daga haka suka yi sallama. Azrah na zaune bakin katifarta tana replying message ɗin Khalil wanda ya wuni kira bata ɗauka ba saboda struggling, Zahra ta zauna gefenta ta ce
"Sannu Yaya kinyi kokari, amma gobe zaki tsiyamin wayan? Naga kin ce zanyi registration ɗin Jamb" Azrah na kallonta ta ce
"Mantawa yau ɗin ma nayi, da na zo miki da shi amma Kinga ai ba wannan nutsuwar" Zahra na murna ta ce
"Amma kuma ai zan iya tafiya Ni kaɗai ko kuma na bi ta gidansu Layla saboda kar kiyi missing wajen aiki" Azrah taji gabanta ya fadi tana kallon Zahra sai kuma a hankali ta ce
"Ai na bar wannan aikin Zahra" Zahra ta fara salati, Azrah ta ce
"Dan Allah kada ki faɗawa Umma for now idan ba haka ba zata hana mu gyaran gidan nan yanda ya kamata, in shaa Allah zan nema wani wajen, ko service dina na gama a can ne Kinga kafin na gama kuma sai na fara neman aiki idan ban samu ba ko Honorable zanma magana" Zahra ta yi shiru ta ce amma meya faru?", Azrah tayi mata narrating komai ta ce
"Toh Allah yasa hakan shine mafi alkhairi" daga haka suka kwanta.
A bangaren Mr. Alhassan kuma, yadda kasan yayi disowning ɗin Sadeeq ne da Sagir, ko a masallaci da suka haɗu a Magrib haka ya share su kamar bai san su ba, haka da suka yi Isha'i ma wanda yanzu hakan kuma ya fara damun Sadeeq, shiga parlon su yayi da sallama, ya karasa ciki kansa a kasa bayan ya gaisa da mahaifiyarsa yana kallon Mahaifin nasa ya ce
"Barka da warhaka, sir" ba tare da ya Kallesa ba ya amsa, Sadeeq ya yi ta zaune yana jiran jin mai Babansa zai ce masa amma yaji shiru, shi wannan silent ɗin Mahaifinsa ne baya so, ganin sun kusan shafa 30mins bai ce masa komai ba sai ma news daya maida hankali yana kallo kawai ya miƙe ya ce
"Sai da safe, sir" still ba tare da ya kalle sa ba ya ce
"Allah tashe mu lafiya" daga haka ya nufi kofa ya fita jiki ba kwari..
Yau tunda suka tashi suka bar gida ita da Zahra basu dawo ba, wajen sha ɗaya saura yayi parking a kofar gidan nasu, wanda ke driving ɗin ya sauka yana kallon wani yaro ya kira sa, yaron na zuwa ya ce
"Gani" ya ce
"Ka shiga gidan nan ka ce ana sallama da Azrah a waje" yaron ya gyaɗa kai ya tafi da gudu ya shiga gidansu Azrah, Mama dake aiki a sakar gidan ta ɗago jin sallamar yaron ta ce
"Ya ne?" Ya ce
"Wani ne ke sallama da azrah a waje" Mama ta ajiye abin hannunta ta ce
"Wani kuma kamar Yaya?" Ya ce
"Eh Nima ban san su ba, a mota suka zo" Mama ta zaro ido ta ce
"A mota kuma?" Ya ce
"Eh, a mota suka zo" Mama ta ce
"Na shiga uku Ni Uwani" yaron na kallon ta sai kuma ya ce
"Amma mutanen fah Babba sosai ne" kamar ma polis ne saboda sun sa bakin wando da rigar sama shima baki" sai kuma ta sauke ajiyar zuciya bayan wani tunani ya fado mata a rai ta ce
"Je ka ce musu sun bar unguwar nan" yaron ya juya ya fita ya koma gun mutanen ya ce
"Ance wai na ce maka sun bar unguwar nan" da sauri suka kalli juna sai kuma suka kalli yaron, dayan dake zaune ya ce
"Inji wa kenan?" Ya ce
"Kishiyar Mamanta" ya ce
"Ko zaka ce musu zan iya shigowa?" Yaron ya rufe bakinsa da hannu bibbiyu ya ce
"Kaiii, matar fah tana da masifa, yadda tace min basu nan idan na koma zata zageni ne koma ta dake Ni" mutumin ya miƙa masa dubu daya ya ce
"Mun gode ko?" Ya karɓa yana murna da gudu ya kama hanyar gidan su
Mr. Alhassan yana kallon PA ɗinsa ya ce
"Kaji kuma abin daya ce, amma haka kawai sai ace sun tashi? Ina suka koma kuma kenan?" PA ya numfasa ya ce
"Dole tambaya zamu yi, Sir"
Wani keke Napep ne yazo yayi parking a gabansu, Sai ga Azrah ta sauka, Zahra ta biyo bayanta, mai keken ya sauka ya fara sauke musu kayansu dake booth ɗin Napep ɗin, kana kallonsu kasan ba karamin gajiya suka yi ba, Azrah ta buɗe handbag ɗinta ta Ciro kuɗi ta mika wa mai Keken
Mr Alhassan zai yi magana sai PA ya rigasa ya ce
"Sir, ai sune a gabanmu" Mr Alhassan ya ce
"Ko zaka musu magana kafin nan?" Daga haka ya sauka, Azrah ta kira yaran dake wasa a wajan wanda basu zuwa makaranta ta ce
"Kalli, ku kama ku shigar mana" Zahra ta miƙa mata file ɗin hannunta tana kallon ta , ta ce
"Ke Yaya ki shiga min da file ɗina Ni kuma zan karasa shiga da sauran kayan" Azrah ta ce
"Toh, sannun Babbah" Zahra na dariya ta ce
"Wai taimako ne" duk juyawa suka yi jin ana musu Sallama, Azrah taji gabanta ya faɗi ganin PA ne, sai kuma ta kalli Zahra ta ce
"Zahra ki shigar da kayan ina zuwa, ki sa yaran ma su taimaka miki" Zahra ta gaishe sa sannan ta fara kwasan kayan zuwa cikin gidan nasu, a hankali Azrah ta gaishe sa tana wasa da fingers ɗinta, shi kansa ma kunyarta ya ke ji kawai daurewa ne, ya ce
"Miss Azrah ka Mr. Alhassan yana son magana da ke, ko zaki iya karasa wa?" Azrah ta juya da sauri jin wanda ya ambata sai kuma ta kalle sa cike da mamaki, dan gani take kamar mafarki ne, kai kawai ta gƴaɗa masa sannan ta fara tafiya a hankali zuwa wajen motar, tana karasa wajen, ya buɗe kofar motar, Azrah taki kallonsa tana kallon kasa ta ce
"Daddy ina wuni" ya ce
"Miss Azrah kina lafiya?" Ta gyaɗa masa kai, ya ce
"Me yasa yau da jiya baki je aiki ba? Kuma shekaran jiya ma baki jira aka tashi ba kika taho abin ki?" Azrah ta sauke kanta ƙasa ta gagara cewa komai, ya ce
"Kin bar aiki da mu ko?" Ta ɗan kalle sa amma ta kasa basa amsa, ya ce
"Amma ina son na tambaye ki, Ni na dauke ki aiki ko Sadeeq?" A hankali ta ce
"Kai ne" ya ce
"Toh mayasa duk abin da yayi miki baki yi reporting dinsa ba kawai kika yanke hukunci kuma ba tare da wani consent dina ba?" A hankali ta ce
"I'm sorry, Sir" shiru yayi bai ce mata komai ba, ita kuma jin shirun yayi yawa yasa ta kalle sa taga ita yake kallon, a hankali ya ce
"Ki dawo aiki gobe idan na isa da ke a matsayin Mahaifi" ta gyada masa kai ta ce
"In shaa Allah " ya ce
"Good! Ina kuma son duk wani abu da zai faru tsakanin ki da MD just let me know ni zan yi tackling issue ɗin In Shaa Allah" ta ce
"Nagode" ya ce
"Toh Allah miki Albarka, ki gaida iyayenki" ta gyada masa kai, daga haka suka yi sallama ta wuce ciki
Tana shiga Zahra tayi saurin cewa "har ki tsiya katin?" Azrah ta fahimci Umma ta tambaye tana ina ne shine Zahra tace hakan, murmushi ta yi ta ce
"Eh na tsiya" Umma ta ce
"Azrah wannan kashe kuɗin bai yi yawa ba? Kar fa kice komai sai kin siya, nikam daga haka ya isa" Azrah ta zauna tace
"Umma kin ga Allah ya taimake mu muna zuwa aka fara mata, ta nuna miki Jamb slip ɗin?" Umma ta ce
"Eh Nagani, medicine ɗin ta cika, Toh Allah bata sa'a" Azrah ta ce
"Amin Amin" Umma ta ce
"Amma nayi faɗa gaskiya, ina laifin Umaru Musa Yar'adua amma kawai sai ki kama ki saka mata Alkalam?"
Azrah tayi murmushi ta ce
"Umma kawai addu'a zaki yi Allah ya kawo wasu hanyoyin, kuma ai kuɗin dake account dina In Shaa Allah zata gama karatu cikin kwanciyar hankali ba zata yi lacking wani abu ba" Zahra ta rungumeta tana jin hawaye na taruwa mata, wai yau ita ce zata yi Uni kuma ace private, tunawa da hakan ya fashe da kuka...
Umma ta miƙe ita da Yaranta suka sake gyara gidan tass, wunin ranan haka dai 'yan unguwa suka dinga tururuwar shigowa taya su murna wasu ma gulma ce ke kawo su, amma kowa sai Barka yake musu da suka fita ƙangin Mama...
Can Azrah da Zahra suna ciki while Umma na tare da bakinta a nan parlor, Zahra bayan ta gama jin abin da Azrah ta faɗa mata ta ce
"Ai tunda mahaifinsa da kansa ya zo har gida yayi honoring ɗinki, kawai ki koma aikin Wannan ma ai wani dama ce wanda zaki bakanta masa, hakan zai basa haushi kuma idan kin goma ko da wasa karya ga murmushinki" Azrah ta ce
"Yadda kika san na tsane Saif haka shima, dan ina jin tsana ɗaya na musu"....
The following day..
MD Sadeeq ya dinga kallon cikin Office ɗin nasa wanda an sake creating wani Office a can gefe, ga Office chair da dai duk wani abu da ma'ailaci zai bukata haka aka yi a edge ɗin office ɗin, infact yadda nasa yake haka na wannan dinma yake, mamaki ya fara toh wani MD za'a ɗauka ko me? Idan ba haka ba baiga amfanin a cikin Office dinsa ayi creating wannan wajen ba, sauke ajiyar zuciya yayi, Sagir ne ya shigo office ɗin yana kallonsa ya ce
"Yana ganka haka kuma? Sadeeq ya nuna matsa wajen da hannun sa, Sagir ya kalli wajen sai kuma ya ce
"Ku biyu ne a office ɗin yanzu kenan?" Sadeeq ya buɗe masa hannu alamar bai sani ba shima daga haka ya karasa ya je ya zauna, Sagir ya dauki abin da zai ɗauka ya fita shima yana mamaki..
Tun da ta iso bakin gate, masu gate suke gaishe da ladabi suna murmushi, alamar dai sunyi murna da zuwanta ne, a haka ta shiga duk wani cleaners da kananun ma'aikata haka suka dinga gaishe ta ita kam kunyar yadda suke gaishe ta take yi, tana hawan 2nd floor ta haɗu da Oga Mahmoud, da ladabi ta ce
"Ina kwana, Sir" ɓata rai yayi ya ce
"Kawai sai ki wani tafi, haka ake yi?" Ta ce
"I'm sorry sir" murmushi ya mata ya ce
"It's Okay toh" daga haka yayi gaba, ta wuce office ɗin PA tana buɗe wa ga kuma Miss Safiyya tana kokarin fitowa, kishi da kyashi clearly written all over her face, Azrah ma ta tamke fuska ganin ba zata bata hanya ba kuma dama tun a gida tayi alkawarin babu wanda zata ragar masa idan zai kawo mata wargi, ta ce
"Idan ban manta ba kamar nan hanya ce ko?" Sake baki Miss Safiyya tayi tana kallon Azrah, Azrah ta raɓa ta gefenta ta shige cikin Office ɗin ba tare da wani izini ba, ganin PA ya fito a main Office ɗin Mr Alhassan ya sa ta gaishe sa ya amsa ta ce
"Sir, amma Daddy na ciki?" Ya ce "Yes, barin masa magana" daga haka ya shige ciki"
Miss Safiyya tayi wani irin humming ta sauka da sauri a ranta tana shirya abin da zata yi wanda zai sa a Kore Azrah, fitowa yayi yace
"Zaki iya shiga" shiga tayi kanta a kasa, ya ɗago yana kallonta da murmushi a fuskan sa ya ce
"Welcome on board Miss" ta ce
"Thank you, Sir " ya miƙe ya ce
"You can follow me, zan nuna miki office ɗin ki" ta ce
"Okay" daga haka ta juya ta bisa a baya, Office ɗin MD ya shiga, Sadeeq ya ɗaga kai ganin mahaifin nasa ya ce
"Sir, kana son wani abu ne?" Kai ya girgiza masa yana jiran Azrah ta shigo, sai gata ta shigo da sallama, da sauri Sadeeq ya Kallesa sai kuma ya sake kallon ta, kamar ya kurma ihuu haka yake ji, Mr Alhassan ya ce
"So, Miss wancan ne spot ɗinki, a matsayin PA ɗin sa, sannan idan akwai abin da bai gane ba zaki iya taimaka masa" murmushi ne yayi escape a fuskanta ta ce
"Okay sir, zan taimaka masa ai ko sanda muke degree tare da shi naka yi duk waɗannan abubuwan su joint hand din nan, group din mu ɗaya da shi kuma nakanyi guiding ɗinsu, at the end group ɗinmu ne ke winning" Idan akwai abun da ya taɓa ɓata wa Sadeeq rai kuma abun kuka toh shine wannan, Mr Alhassan na dariya ya ce
"Wait.. Tare kuka yi degree" ta ce
"Of course, yes sir! Tare muka yi" ya ce
"Very good, Shiyasa dama ai nace nasan zaki taimaka masa, though kina aiki ne a karkashin sa amma definitely zaki saka sa a hanya, yadda ake yi da abokan saka hannun jari ma duk sai ki koya masa" itama tana dariya ta ce
"Toh shikenan, In Shaa Allah zan koya masa" ya ce
"Very good" daga haka ya juya ya fita, ta ɗan kalli direction ɗinsa wani kallo ɗaya zuba mata har sai data tsorata amma ta dake ta zauna a office chair ɗinta, sai kuma ta miƙe ta ɗauki remove ta rage Acn office ɗin, shi dai Sadeeq ya gama koma wa kamar wani mutum mutumi ne, zuciyar sa kuwa banda tafarfasa babu abin da yake yi...
Miss Safiyya tana share hawayenta ta ce
"Shine kuma har zata sake zuwa? Mu dai mun zama useless a Company, ace har ta fi mu matsayi duk da ihun da tayi wa MD kuma shine za'a barta a Company, kalli any small thing yadda MD ke ihu wa mutane yana sallamar su a aiki duk taka tsantsan muke dashi amma tayi musayar baki da shi shine zasu dawo da ita?" Ita dai Miss Merry ko da wasa bata ma kalle inda take ba, dan yanzu tama fara tsoron Miss Safiyya ɗin
#Jiddatulkayr writes
08110615256
Episode 74: The Glory that sparkled Envy
Bayan wasu kwanaki, kamfanin ya shiga jerin manyan kamfanonin da suka yi fice. Duk da cewa Azrah da Sadeeq na cikin office ɗaya, amma tamkar ba'a waje ɗaya suke ba, kullum fuskan nan nasa a tanke yake, ko kaɗan baya shiga wani sabgarta, yana avoiding Azrah ta ko'ina. Idan akwai wani aiki zai haɗa su, sai dai ya saka wani yayi mata magana, ko kuma ya aika mata ta hanyar Miss Merry. Ya kama girmansa fiye da yadda ita take tunani
Azrah kuwa, duk sai take jin rashin jin daɗin canjin da yayi, gani take bata kyauta masa ba, amma ta share tana nuna class. Tana aiki da ƙwarewa dan karya yi disgracing ɗinta kuma hakan ya ƙara ɗaga darajarta a idon kowa. Har wasu ma'aikata sun fara tunanin, kamar akwai bitter past tsakaninsu, ko kuwa?
Ga baki ɗaya dai Companyn kowa mamaki yake yi yadda kuɗi ne ke shigowa non stop, ba PA ba hatta Mr Alhassan mamakin hakan yake yi, investors da clients sai karuwa suke saboda Azrah, duk wanda ya zo sai ya ce 'Ina waccan smart lady ɗin?' Wasu kuwa su zo da niyyar business ne amma fact ɗin sonta suke yi, kuma ba da wasa suke yi ba, Kamar yadda ta ƙi yarda da su, sai su koma suna tambayar toh ta basu sister ɗinta Zahra wanda wata rana ta take biyota, har kofar gida kuwa suke bin su, Zahra ta fara ƙonewa da DM requests da gifts amma yanzu gaba ki ɗaya damuwarta ta samu ta fara karatu ne, dan medicine ba zata hada 1st 3yrs ɗinta da soyayya ba
Mama kuwa an kusa kai ta Emergency. Duk lokacin da ta leƙa ƙofar gidan su Azrah, sai taga sabuwar mota ko wani mai fitinannen daukar ido, da sunan sun zo neman Azrah ne, Su Siyama da Habibah kuwa ba su da peace of mind. Kuka suke ba dare ba rana 'akan meyasa sai wajensu kawai zasu na zuwa banda mu?, ko dan sun fi mu kyau ne?' hakan na ƙara tunzura Mama da azabar blood pressure.
Sadeeq kuwa, ya zama kamar volcano dake a tsage, abu kaɗan masifan da ihuu wa mutane, iyakacin rashin fitar da file akan lokaci sai ya ce 'You're fired' ma'aikatan companyn suna rawar jiki idan suka ji motsinsa Sbd tsoro kowa mugun shakkarsa yake harda Azrah wanda kuma a hakan ita ce mai iya faɗa masa magana
Yanzu Mr. Alhassan ma ya fara ja da baya. Yana ganin kamfanin na tafiya smoothly, amma a boye yake monitoring komai, ba kaɗan ba kuma yake appreciating Azrah
Kamar kullum.... Azrah na zaune a gaban system ɗinta, idonta na bin rubuce-rubucen da ke cikin screen ɗin, gaba ɗaya hankalinta ya tattara a cikin files ɗin da take compiling, office ɗin a nutse yake babu hayaniya as usual, sai kawai suka ji sallama
"Assalamu Alaikum" duk suka ɗaga kai suka kalli kofar,Sagir ya shigo da murmushin da ko shima bai san na menene ba, dan duk sanda zai shigo office ɗin wannan yanayin zaka gansa ciki, dan yanzu dai ya mayar da Office ɗin wajen zuwansa kenan ko ba dalili. Kuma duk sanda ya zo, sai ya nemi wani abu da zai haɗa sa da Azrah amma ita kuwa, tamkar tana kallon iska idan ya shigo ko da wasa bata tanka masa, iya kaci idan yayi mata magana da amsa masa a takaice
Ya karaso cikin Office ɗin, ya zauna a kujera, yana kallon Sadeeq ya ce
"Man, yau fah tun dazu ban jika ba"
Sadeeq, ba tare da ya kalle shi ba, ya ce a takaice "Okay"
Sagir ya dan yi dariyar unbothered ya ce
"Okay kuma zaka ce?"
Sadeeq ya ɗago idanunsa daga system ɗin gabansa yayi masa wani kallo mai nauyi ya ce
"So?"
Kamar zai cigaba da magana, sai ya fasa, dan wannan halin Sagir ɗin takaici yake basa, ya mayar da kansa kan system ya cigaba da typing ɗin sa
Sagir ya juya yana kallon Azrah ya ce
"Miss Azrah, ba gaisuwa ne?"
Azrah bata ko kalle shi ba kawai ta ce
"Oh, good morning"
Sagir yana murmushi ya ce
"Morning! Ya gida? Ya kowa da kowa? Kuma fa ina son miki sannu yadda kike fama client da investors"
Azrah ta dan ɗaga kai ta masa kallo ɗaya, ita yanzu haushi ma yake bata, abokinsa ne kuma take shakka, a takaice ta ce
"Fine"
Zai cigaba da wani small talk ne kenan, sai kawai ta miƙe alamar conversation over
Sagir ya bita da kallo, ita kuma ta nufi kofa zata fita kenan sai ga Oga Mahmoud ya shigo, Azrah ta saki fuskarta lokaci guda da murmushi ta ce
"Yaya na! Wallahi yanzu nake tadinka a raina!"
Mahmoud ya yi dariya yana karasa shiga cikin Office ɗin ya ce
"Really? Toh ai gashi nan nazo gaishe da kanwata"
Azrah ta ce cikin zolaya
"Ai kuwa naji daɗi!"
Sagir na gefe yana kallonsu kamar ya haɗiye zuciya haka yake ji. Wani irin kallo ya wurga musu, wanda bai faɗa komai ba amma ya ce abubuwa da dama. Sai kawai ya miƙe ya fice daga Office ɗin kamar zai tashi sama
Sadeeq ya bisa da kallon gefen ido sai kuma ya ja tsaki
Mahmoud ya mika mata wani file ya ce
"Zaki iya turawa investors ɗin jiya Team no. ne"
Azrah ta ce "Alright, yaya" ta karɓi file ɗin cikin ladabi
Yana fita, ta koma ta zauna tana buɗe files ɗin, ta furta a hankali cikin zuciyarta
'Wani lokaci shiru ya fi magana...'
Kamar karfe goma ta fita zata siya abinci saboda bata karya ba a gida ta fito, ta kalli yadda ake hidima a wajen da deco abin ya bata mamaki a ranta tana ayyana maybe baki za'a yi, bayan ta koma ta cigaba da aikinta, duk wani aiki da take yi tana yi ne da natsuwa, kamar kullum.
Mr. Alhassan ya fito a office dinsa yana kallon PA dinsa ya ce
"Ka tabbatar kowa yana wajen taron a harabar Company cikin mintuna goma, dan mu samu mu gama da wuri kar mu shiga lokacin mutane"
Kafin kace mene duk ma'aikatan suka hallara wajen kamar yadda ya bukata, kowa sai kallon abun gabansu suke yi wanda ya ɗauke hankalin kowa
Wata dalleliyar mota ce baka, banda sheki babu abin da Motar take yi, ga wani ballons da flowers da aka yi deco da shi aka zagaye motar, kowa yana tsaye ne dan jin dalilin kiran nasu
Mr. Alhassan yana zuwa wajen taron ya kalli kowa, yayi sallama sannan ya ce
"Mu fara da addu'a, domin duk abin da muke yi, sai da taimakon Allah"
Wani daga cikin staff ya jagoranci buɗe taron da addu'a cikin natsuwa
Nuna musu motar yayi da hannu, aka juya ana kallon motar, kowa yana kallon motar ne da mamaki da tambaya a rai kuma
Mr. Alhassan yana kallon PA ɗinsa ya ce
"PA you can take over"
PA ya fito da wata paper ya fara karantawa a nutse
"Wannan mota, mallaka ce da management na Majestic Vault Ltd. suka yanke shawara akan a bawa wa Miss Azrah Muhammad a matsayin yabo da godiya saboda irin ci gaban da ta kawo wa wannan kamfani. Contribution ɗinta ya zama wani abu da ya zarta tsammanin mu, har ya janyo mana sabbin hannun jari da kwastomomi da dama kuma har daga wasu manyan kasashen"
Da karfi zuciyar Azrah ta buga, ta tsaya da aiki na wasu dakiku, she still can't believe, hawaye suka fara zuba kamar an kunna famfo, tana son gaskata abin da kunnuwanta suka ji, tayi saurin rufe fuska da tafin hannunta, amma kuka taci karfinta
Oga Abubakar ya matsa kusa da ita, ya ce a hankali yana murmushi
"Iyyeee... to idan kuka zakiyi, sai ki bani motar nan tunda baki so kawai"
Wani dariya mai taushi ya biyo bayan maganar tasa yana kallon ta haka kawai yake son nutsuwarta
Sadeeq da ke tsaye a nesa yayi folding hannunsa, ya ɗan ɗago ya kalli Azrah, sannan ya ɗauke kai
Miss Merry ta kalli Safiyya sai kuma dariya ya ƙuɓuce mata, ta dinga danne dariyarta
Safiyya kuwa ba zata iya riƙe wannan baƙin cikin ba kawai kuka ta fashe da shi, wanda ya ja hankalin mutane. Sai ta goge hawayenta da sauri ta ce tana murmushi
"Congratulations dear, na tayaki murna"
Azrah ta kalli Mr. Alhassan cikin hawaye, ta ce da murya mai rauni
"Sir, wallahi ban san me zan ce ba, I'm just speechless, Nagode… Nagode sosai, wannan babban kyauta da ban taɓa tsammani ba. Inaga nafi ku jin daɗin kasancewa a wannan Company"
Mr. Alhassan ya kalleta cikin natsuwa ya c
"Mu ne ya kamata mu gode miki, Azrah. Domin duk abinda kika kawo, ba abu bane da kowace mace za ta iya. Kin cancanci fiye da haka"
Aka fara tayata murna amma she's so emotional, kowanne ya koma bakin aikinsa.
Bayan an tashi daga aiki, Mr. Alhassan ya kira Oga Mahmoud ya ce
"Ka tabbatar an kai mata motar gida yau. Mu nuna mata it's not just a gift it's a mark of trust and recognition"
Mahmoud ya gyaɗa kai yana murmushi ya ce
"Za ayi Sir. Ba matsala"
Oga Mahmoud ya karasa office ɗin su Azrah, yana murmushi, ya ce
"To Madam, ga motarki can... yanzu sai mu tafi na kai ki gida ko? Ko dai sai a kawo miki daga baya?"
Azrah, tana kallon sa cikin mamaki da girmamawa, ta girgiza kai tare da ce
"A'a, yaya na... let's go, wallahi har yanzu kamar mafarki nake ji"
Daga haka suka karasa har parking space, ya buɗe mata ƙofar motar da kansa, ta shiga, shi ma ya zagayo ya shiga driver's side. Suna tafiya cikin nutsuwa, ba wanda ke cewa kala, sai murmushi a fuskar Mahmoud.
Suna isa kofar gidan su, Azrah ta sauka tana cewa
"Thank you so much yaya... Allah ya saka da alheri"
Mahmoud ya kalleta da murmushi, ya ce
"Ameen dear, you deserve this, za'a buɗe gate ɗin sai na shigar miki ko?" Kai ta gyaɗa masa daga haka ta nufa cikin gidan
Ta shiga cikin gida cikin sauri da excitement, tana shiga parlour ta tarar da Umma da Zahra suna hira
Cikin daƙilewar kuka, ta faɗa kan Umma ta rungumeta ta ce
"Ummaaa..."
Umma da Zahra suka tsorata da yanayinta suka hada bakin fadin "Lafiya?"
Umma ta ce "Lafiya Azrah? Me ya faru?"
Zahra ma dai duk ta kagu taji menene ta ce "Ya Azrah me ne ne?! Kin firgita mu fa! Kiyi mana bayani please"
Azrah ta kalli su cikin hawaye, sannan ta ce
"Wallahi Umma... sun bani mota... A Company! Kyauta daga management.... Mota Umma! Mota! Mota fah.."
Suka zaro ido gaba ɗaya har haɗa baki suke a tare
"MOTA?!"
Ta gyada musu kai, tana sheshsheƙar kuka. Zahra ta ruga da sauri ta shiga ɗaki ta ɗauko mayafi tana cewa
"Allah na gode maka!! Ina motar take? Yana waje ne?" Duk a rikice take, kai ta gyaɗa musu
Umma ma ta saka mayafi suka fita waje, a lokacin Oga Mahmoud yana tsaye kusa da motar, yana jiran ta buɗe masa gate ya shigar da shi ciki
Suna fitowa, ya gaishe da Umma da ladabi ya ce
"Assalamu alaikum Umma, barka da yamma"
Umma ta amsa masa
"Wa alaikumus salam ɗan nan, Allah ya saka da alheri. Muna godiya sosai"
Suna gama gaisawa Umma ta koma ciki. Zahra kuwa tana rawa tana cewa
"Motaaa... motar Azrah ce! Wallahi yau akwai asarar hawayen masu sharri da mahassada"
Ta karɓi keyn gate tana dariya da waka, ta buɗe gate ɗin, Oga Mahmoud ya shiga da motar cikin compound, ya park a parking space.
Azrah ta kalli motar, sannan ta kalli Oga Mahmoud
"Nagode sosai yaya. Allah ya saka"
Yana dariya ya ce "Ameen. Keep being you. Allah ya ƙara daukaka"
Ya juya ya bar gidan. Azrah ta tsaya tana kallon motar kamar har yanzu bata tabbatar da gaskiyar abun ba
Jin fitar sa yasa Umma da Zahra suka sake fitowa, murnan kuwa ba kaɗan ba suke yi
Umma tana tsaye ta dafe hannu biyu bisa kirjinta tana kallon motar, tana ɗaurawa bata son tayi hawaye ta ce
"Innalillahi wa inna ilaihir raji'un! SubhanAllah, Alhamdulillah! Wannan ba karamin nasara bane, Allah na gode maka! Ya Allah bani da abin cewa ka cigaba da kare min yara da ɗaukaka musu, abu kamar a mafarki?"
Zahra na gefe tana dariya, tana yawo da key kamar wata sabuwar amarya ta ce
"Ai ko ba komai, an sha gaban gidan nan yau. Mota a kofar gidan mu? ba drama ba!? Kuma wai namu?" Ta fada tana wakar harda rawanta, Azrah ta fara dariya ganin Zahra kam kamar bata da hankali...
'Yan unguwa kuwa sun fara spreading news
Wata mata ta fito shago ta kalli wata makwabciyarsu bayan sun gaisa ta ce
"Ahhh... Kina da labari? An ce Azrah ta samu mota daga wajen aikinta, wai saboda yadda take kokari!"
Matar ta ce "Ai da gaske ne, har company sun zo da kansu suka kawo motar, kin san gidan nasu na kallon na da ai, saboda Bappah'n su ya sake Ummansu"
A gefe guda kuwa, Miss Safiyya na zaune a ɗaki da ido jajir, gumi na keto mata duk da sanyin AC. Kuka takeyi a hankali, zuciyarta cike da haushi da kishi, tun data dawo Mama ta gagara gane kanta, tun tana lallaɓata harta hakura
Maman ta ta shigo da plate na jallof ɗin shikafa da yasha kayan haɗi, tana cewa
"Safiyya, tashi ki ci abinci mana, me ke damunki haka ne? Kin ki faɗa min kuma kin ki cin abinci, ya kike so nayi?
Ta girgiza kai cikin kuka ta ce
"Bazanci ba Mama"
"Lafiyarki kuwa?" Ta tambaya cike da damuwa
"Eh Mama" Sai kawai ta boye kanta a filo, Mama ta zauna tayi tagumi tana kallonta sai kuma ta ajiye abincin ta fita
Bayan mamanta ta fita, Safiyya ta share hawaye, a cikin zuciyarta ta ce
"Wannan abin ba zai tsaya haka ba. Wallahi sai na raba Azrah da wannan Companyn. Sai na ga yadda zata ci gaba da haskawa ba tare da aikin ba"
Tayi murmushi mai cike da makirci, alamar kudirin da zata fara aiwatarwa...
Episode 75: The Company's Betrayal
Abdul na zaune ga ƙwanon tuwa a gabansa yana ci, Siyama da Habibah suka shigo gidan a guje suna kwala wa Mama kira, kallonsu yayi ya daka musu tsawa, cike da magana irin ta 'ya'ya marasa tarbiyya ya ce
"Ubanku aka muku a wajen da zaku wani shigo mana gida haka?" Ko kallonsa basu yi ba, Mama ta fito daga dakin hankali tashe tana kallon su ta ce
"Uban me ya faru kuma? Tunda na lura banda son ku saka min ciwon zuciya baku da wani buri"
Siyama ta fashe da kuka ta ce
"Mama kina ji fah ɗazu aka kawo wa Azrah motar har kofar gidan su" ɗabas Mama ta zauna a kasa tana kallonsu, Habiba ta ɗaura
"Mama ko mu marasa sa'a ne? Komai ace can gidan" tana kai wa nan ta fashe da kuka, Mama ta ce
"Bakin ku kullum banda tsiya babu abin da kuke fata wa kan ku, yanzu inji ubanwa ya ce muku an tsiya mata mota?" Sallamar wata makwabciyarsu suka ji, takara so cikin gidan, Siyama da Habibah suka wuce ciki, tana murmushi ta ce
"Akwai alale ne?" Mama na mata wani kallo ta ce
"Dama na taɓa yin alale warhaka ne?" Ta ce
"Ayyah ashe ya kare, kwaɗayi nake ji Shiyasa na ce bari na shigo ko zan samu saura ne" Mama ta tamke fuska, har zata fita sai kuma ta dawo tana murmushi ta ce
"Ashe abun alkhairin ya faru? Mantawa nayi ban miki murna ba" Mama ta ce
"Aina abun alherin ya same Ni?" Ta ce
"Kawai sai muka ji 'yarki Azrah tayi mota ba?" Zuciyar Mama da ɗazu bai samu ya tsinke ya faɗi ba shine yanzu yayi skipping na wasu dakiku tana kallon Matan wanda har ta soma jin dishi dishi, ta dake ta ce
"Toh yanzu ke uban me ya kawo ki? Gulma ko jin kwakwaf?" Abdul ya miƙe yana kallon matar ya ce
"Kee dalla wuce ki tafi" sakeke take kallon Abdul sai kuma tayi murmushin takaici ta juya ta ce
"Allah baku hakuri" daga haka ta fita, Mama tayi tsuka ta ce
"Wallahi duk gulma ce ke kawo su" tana kai wa nan ta fara share hawayen fuskanta, a tare Habiba da Siyama suka fito, Siyama ta ce
"Ai gashi kinji da kunnenki, da gaske yanzu mota gare su" Mama duk da damuwar da take ciki ganin damuwar yaranta yasa ta dake ta ce
"Ku dallah ku share hawayenku, ai na faɗa muku mutumin ya ce maza zasu fara sintiri kofar gidan, yanzu kar ku sha mamaki wani daga cikin 'yan iskan nata ne ya tsiya mata, toh me abun damuwa" Siyama ta sake fashewa da kuka ta ce
"Ai haka zaki ce dama, kullum ma banda hakan babu wani abun cigaba, dan ba ke bace kike fita ake gaya wa magana shiyasa, ina yanzu a hanyar mu ta dawowa wannan tsohuwar bakin hanyar ta ce mana mu banda tallah da yawo babu abin da muka yi, ko kunya bamu ji ne ace 'yan-uwan mu suke nan a nutse kuma kullum ci gaba suke yi, kiji fah abin da ta faɗa mana" Mama ta sauke ajiyar zuciya
Abdul ya ce "tun ba yau ba haka Mama take lafta mana magana kuma yaki yiwa, kuma maganinku ai da kuka yarda" Mama ta masa wani kallo ta ce
"Ubanka shegen yaro Ni zaka karyata kenan?" Ɗaga hannun sa bibbiyu yayi ya ce
"Mijinki kenan! Ai yana ɗaki" Mama ta sake baki tana kallon sa, ta lura tun daya dawo ya sake ɓantarewa, Siyama ta ce
"Mama Ni kam na yarda ko 'yan iskan ne suna zuwa waje na Nima" Mama ta ce
"Amma baki da hankali yarinyar nan" Habiba ta daura
"Gaskiya Nima Mama ina so, ina ga idan zaki koma ma Malamin kice ya haɗa harda mu" daga haka ta miƙe tayi ciki, Mama ta rabka uban tagumi tana tunanin wata mafitan kuma, Siyama ta miƙe ta bi bayan 'yar uwanta...
Dariya tayi ta ce
"Kai Samira! Toh yanzu yaushe zaki zo gani?" Samira a ɗayan ɓangaren ta ce
"Ai dole nazo gani, dan ma yanzu Deen na lallaɓa Ni idan nace ya kawo Ni nasan zai kawo Ni" Azrah tayi dariya ta ce
"Toh yanzu bai fi muku ba akan wanan faɗan naku?" Samira ta ce
"Dama can shi ya ɗaura Ni akan wannan yanayin fah, shi a dole rayuwar turawa, wayayyar mace, amma yanzu ai idonsa yayi clear, ya gane Allah ɗaya ne, Nima nagane kuskuren hakan musamman yadda kike nutsar da Ni" Azrah ta ce
"Ma sha Allah, Allah kara haɗa kawunan ku, yanzu yaushe kenan zaki zo" ta ce
"In shaa Allah gobe zan sa ya kawo Ni" Azrah ta ce
"Toh Allah kaimu" daga haka suka yi sallama ta kashe wayar...
Da sauri ta fito a office ɗin, duk da cewa babu ko wani maaikaci saboda tun tuni aka tashi, kalle kalle take dan sake tabbatar da cewa babu wani cctv a wajen sannan ta sauko a hankali, bayan ta karasa bakin gate, tana murmushi masu gadi suka tambaye ta
"Kin ga wayar naki? Ta gyaɗa kai ta ce
"Ai dama nasan anan na bari, ina haurawa kuwa na gani" suka ce
"Toh Alhamdulillah" fita tafi, ta shiga motarta ta kunna motar sannan ta bar layin
Daya daga cikin gateman ya ce
"Kalli dama matar nan na saka hijabi ne?" Yayi dariya ya ce
"Baka ganta duk a birkice ba? Har wani jaa idonta yayi ina ga duk ta ruɗe ne akan neman wayar nata" dariya yayi ya ce
"Ashe dai duk burgane idan har akan ɓatan wayanta zata yi haka, ita ai kullum ji take da kanta ita wata siyar ce kamar tafi kowa da munin fuskanta a wajen" dariya sosai ɗayan yayi ya ce
"Ga uban girman kai, gashi a Gaishe ta taki amsawa, amma yau harda fara'a dake abun ta take nema" duk dariya suka yi...
Maman Amira ta shiga ɗakin Dada da sallama ta ajiye mata plate ɗin abincin ta ce
"Dan Allah Dada ki samu ki ɗan ci abinci ko da kadan ne, zama da yunwar ma zai kara miki wani ciwon ne" Dada ta ce
"Zan ci Maman Amira, amma yanzu kam ki tashi ki tafi gidanki Kinga har Magrib yayi" ta gyada mata kai ta ce
"Amma Dada wannan ciwon naki Allah na tuba bada saka hannu ba kuwa? Dan na lura tunda kika dawo fah kullum kike kwance" Dada tayi murmushi ta ce
"Ke ma ai kinsan wannan ciwon bana Allah bane, ace jiki baya tashi sai na shiga Mota zani cikin Katsina? Yau sati nawa ana fama da abu ɗaya" Maman Amira ta ce
"Toh nikam Ina ga ko zanma Maman Amira magana idan abokinsa dake jan keke Napep a cikin garin Katsina sai a basa maganin ya tafi da shi ko?" Dada ta gyada kai tana hawaye ta ce
"Ai da hakan ma zai fi, amma matar nan ta cuce Ni da ɗana da kuma jikoki na, gashi suma yanzu basu kira na wanda ba halin su bane kila har su bata barsu ba, Uwarsu da bata da kowa ne abin tausayi" Dada ta miƙe dakyar tana hawayen bakin ciki, ita da garin ɗanta amma bata isa zuwa ba, Maman Amira data yi tagumi ta ce
"Toh nikam anya ba kai ki gun masu magani zamu yi ba? Ai su zasu gano bakin matsalar" kai kawai Dada ta gyada mata...
Washe gari Azrah ta tashi da cramps, sosai yake galabaitar da ita, hakan yasa tayi ta shan bacci da safe, wanda Umma ta hana Zahra tashin ta, tuni Zahra ta gama nata shirin ta saka wani Abaya daga cikin uban kayan da Azrah ta musu shopping last week, ba kaɗan ba tayi wani sihirtatcen kyau, ta maka face mask dan ta tsane takuri gashi harta Lecturers ɗinsu ba barinta suke ba, sallama tama Umma sannan ta fita. Can wajajan karfe goma Azrah ta farka, Umma ne ta shigo ɗakin tana kallonta ta ce
"Ya jikin naki kuma?" Azrah dake riƙe da cikinta tana juye juye ta ce
"Ya ɗan sauka, amai nake ji kuma yanzu" Umma ta miƙe ta ce
"Ina zuwa" daga haka ta nufi kitchen bata wani daɗe ba ta dawo ɗakin, ta ajiye kayan hannunta sannan ta ɗaga Azrah zaune, cup ɗin ruwan zafi data tafasa mata da Habbatus sauda ta miƙa mata, Azrah ta karɓi kaɗan tasha, Umma ta saka towel a ruwan zafin tana matse ruwan tana ɗaura mata a mararta a haka wani baccin ya sake ɗaukarta, hakan yasa Umma kwantar da ita, ta ɗauki roban ta fita da shi
Yau tun da safe da suka shigo Companyn kananun maganganu ne ke tashi, Mr Alhassan ya kasa zaune sabar asarar kuɗin da yake fuskanta wanda zai yi, PA ma ya girgiza ba kaɗan ba da jin wannan lamarin
2nd floor ɗin companyn ya cike da hayaniya, a reception har zuwa gaban HR, ana jita-jitar wani 'matsanancin bincike da ake yi da wasu masu knowledge a harkar cyber security, kowa na jiran su san me ke faruwa.
Sadeeq ya shigo cikin hanzari yana yamutsa fuska kowa basa hanya yake yi a haka har ya nufi office dinsa kai tsaye yana mamakin abin daya ji, baya kuma kaunar yayi zargin kowa, har lokacin ba a ga Azrah ba kuma a office, wanda hakan ya sa tambayoyi suka ƙaru.
Miss Merry data shiga cikin Office ɗin PA wanda su suna can sun haɗa zufa, tana kallon Miss Safiyya ta ce
"Yau banga Miss Azrah ba, ko lafiya amma? Dan wannan ba halinta bane na rashin zuwa"
Safiyya ta harareta ta ce
"Haba mana Miss Merry, ke baki ji kamar wani abu ya faru bane kuma ana zargi a cikin staff ne sai kuma yau bata zo ba, toh Allah da dai lafiya"
Miss Merry ta ce
"Ban gane ba? Wai wani maganar kuma kike yi haka? Dama an san abin daya faru ne? Tou Ni a bakin ki na fara ji ma" jin me ta ce yasa miss Safiyya ta yi saurin cewa
"Noo! Nima hakan naji fah amma kasa kasa ne, I'm not sure"...
Mr Alhassan ransa a mugun ɓace yana kallon PA ɗinsa ya ce
"Ka yi calling meeting cikin gaggawa" hakan kuwa akayi
Kowa ya taru daga Mr Mahmoud, Oga Abubakar, Safiyya, Sagir, Merry har ma da kananun staff
Tension ya cika conference room din
Mr. Alhassan ya kalli su gaba ɗaya sannan ya ce
"Mun samu matsala da confidential document da aka tura jiya ga wani babban investor. Bayanai sun nuna akwai sauyi da aka yi a cikin file ɗin. And this could cost us a major deal, waya ke son ganin bayan mu har haka?"
Dakin ya ɗauki shiru kowa da tunanin da yake yi
Ya kalli IT manager ya ce
"Malam Haruna, ka faɗi mana abin da ka gano"
Haruna ya buɗe system, ya haɗa projector a hankali ya soma magana
"An yi login daga account din Miss Azrah Muhammad, IP ɗin kuma ya fito ne daga system ɗinta, timestamp ɗin da kuma files sun nuna changes da password dinta aka yi, duk wadannan abubuwa sun faru ne misalin ƙarfe biyar na yamman jiya"
Gaba ɗaya cike da tsananin mamaki suka ce
"Subhanallah!"
Wani staff ya ce
"No wonder bata zo aiki yau ba!" Wannan ai cin amanar kamfani ne!" Duk hall din suka fara reasoning da maganar sa na yau bata zo aiki ba
Sagir ya ce
"Dama ai kun san ita ce ta fi shige da fice da investors. Maybe ta fara amfani da damar data samu ne"
Oga Abubakar ya harare shi,
"Ka rufe mana baki Sagir! Bincike ake, ba ka yanke hukunci ba, We're not sure yet, unless an ji daga gareta"
Sadeeq wanda tun farko yake gefe amma bai tanka ba, ya ɗan gyara zama, ya ce cikin taushin muryansa
"Maybe system ɗinta ne aka yi hacking, ba lallai ba ne ita da kanta, hakan zai kuma iya faruwa, for now kada a yi saurin yanke hukunci"
Sai kawai Miss Merry ta ce tan dariya
"To ai ko hakan ne, ita ce ke da alhakin password dinta. Komai ya faru daga bangarenta ne, Sir"
Miss Safiyya na kaɗa jiki ta miƙe cike da jan hankali ta ce
"Amma idan ba ita bane mayasa yau taki zuwa?"....
Tension ya kara tashi sosai a Companyn lokacin da zancen ya kareɗe ko ina, wasu ma daga junior staff na waje sun fara cece-kuce
"Ni na farka da mugun mafarki yau, ashe dama wata fitina zata tashi anan ne" inji Ishaq
"Tunda ta fi kowa shahara, ta fi kowa da kusanci da manya, maybe ta samu chance ne da Company" Adam ya ce
Wani ya ce "Hmmm! Ai wallahi dama bana jin daɗin irin shigar data ke yi. Wata kila ai da kuɗin Company tun da can take kamfalawa, amma ai wannan rashin godiya ne, ina anan aka bata kyautar mota shine kuma zata aikata haka wa Mr Alhassan?".
Yadda hayaniyar yayi yawa yasa Mr. Alhassan ya sake komawa cikin su ya dakatar da hayaniya,
"Ba wanda zai yanke hukunci kafin mu ji daga gareta, sai ta dawo gobe, za mu ji bayani cikakke daga bakinta, amma yanzu investigation zai ci gaba"
Sadeeq ya miƙe a fusace ya bar conference room ɗin, har zai shiga office ɗinsa kuma sai kawai ya fasa ya fita gaba ɗaya daga Companyn.....
#Jiddatulkhayr
08110615256
Episode 76: Truth in the shadows
Bayan Sadeeq ya bar conference room ɗin cikin ɓacin rai, ya wuce kai tsaye zuwa office ɗinsa ya ɗauki car key da sauri, kamar wanda zai tashi sama haka ya fito cikin sauri, parking space ya wuce tun kafin ya karasa ya buɗe motar, bayan ya shiga motar, ya zauna yana kallon steering, zuciyarsa cike da ruɗani,
"Even her number I don't have… not to talk of knowing where she lives" ya furta a hankali, yana jin wani iri bakin ciki a zuciyarsa
Ya dafe kansa da hannayensa, yana sauke numfashi a hankali. Sai kuma ya tada motar, amma tunanin ta ina ma zai fara kawai sai ya kashe ya sauka. Cikin sanyin jiki ya koma office dinsa
Yana shiga ya kalli Sagir na zaune, ɗaga kai yayi ya ce
"Man me kake tunani akan wannan case ɗin? Is like naga kamar baka so da aka kira sunanta ba?" Sadeeq bai amsa ba ya karasa wajen zamansa ya zauna, Sagir ya ce
"Magana fah nake maka?" Wani dirty look ya basa ya ce
"Toh me zance tunda kun gama yarda?" Sagir ya sake baki ya ce
"Wait... Don't tell me you have feelings for her now? Shiyasa kake son kare ta?" Wani dariyan da bai shirya bane Sadeeq ya fara sai kuma lokaci guda ya koma ainahin Sadeeq dinsa ya ce
"I have feelings for her ka ce???"" Sagir ya ce
"Of course yes, naga sai kare ta kake yi?" Wani dogon tsaki Sadeeq yaja ya ce
"You are not serious, Kai ma kasan bana bin bayan karya, duk tsanar dana ma mutum ba zan taɓa ganin an zalunce sa ba, that's all, Amma idan kana ganin hakan ne, It's Okay duk yadda kace daidai ne" daga haka Sadeeq ya cigaba da abin da yake yi ya bar Sagir baki buɗe...
Azrah na zaune tana kallon Umma da ta sata gaba tace sai ya cinye abinci, Azrah ta marairaice ta ce
"Umma kema kin san bana iya cin abinci fah, ai kuma na sha tea" Umma ta ce
"Tea dama abinci ne? Kuma Ni ban san baki ci ba sai dai acan India kika koyo" Zahra ta ce
"Umma toh ki kyaleta anjima sai ta ci" Azrah ta gyada kai ta ce
"Please Umma" Umma ta ce
"Kin kira kin faɗa musu kuwa? Kar suga baki zo ba?" Azrah ta ce
"Bari na kira" ta ɗauki wayanta, tunanin babu wanda take da numbern sa a wajen yasa tayi shiru, numbern Sadeeq da Sarah ta turo mata not long ago bata ji zata kira ba, sai kuma kawai ta dake ta kira, yana fara ringing taji zuciyar na bugawa, ji tayi kamar ta kashe amma ya hakura, har ya katse bai ɗauka ba, haka ta kara kira shima har ya yanke bai ɗauka ba
Tana ajiye kiran zata faɗa wa Umma bai dauki wayan ba sai ga wayanta ya fara ringing, tana ɗauka taga Smaira ne, dama tana expecting ɗinta, Umma ta ce
"Su ne?" Ta girgiza kai ta ce "A'a, Samira ce" Umma ta miƙe ta fita daga ɗakin
Azrah ta kai wayan kunnenta bayan taɗaga ta ce
"Ke gani a gidan ku wannan masifaffiyar stepmom ɗin naku ta fara balbaleni da masifa, wai kun bar unguwar?" Azrah tayi murmushi ta ce
"Ki tsaya wajen, ga Zahra zata zo ɗaukan ki" daga haka ta katse kiran, tun kafin tayi magana Zahra ta ce
"Kila can ta tafi ko?" Azrah ta gyaɗa mata kai ta ce
"Yanzu dai ki dauko ta"
Zahra na fita taga motar dake parke ashe ma a kofar gidan nasu yake, ta karasa jikin motar, Samira na mata murmushi, Zahra ta leka ta gaishe da Saif sannan ta mayar da kallonta ga Samira ta ce
"Toh gashi ai naga kina kofar gidan" sauka tayi ta ce
"Wannan shine rashin sanin kuwa, in ba haka ba me ma zai kai Ni can gidan balle stepmom dinku ta min rashin kirki" suna shiga compound Samira ta ce
"Wow, Ma Shaa Allah! Wlh ya fi muku da kuka dawo nan akan can, kai gaskiya na muku murna" Zahra na murmushi ta ce
"Mun gode" tun kafin su karasa idon ta ya faɗa kan motar dake parking space ta ce
"SubhanAllah! Don't tell me wannan ne motar Azrah ɗin?" Zahra na murmushi ta ce
"Shi ne fah" tuni Samira ta karasa jikin motar tana bi da ido tana kara yaba kyaun motar, a haka suka shiga parlorn
Bayan ta gaishe da Umma ta musu Allah sanya Albarka ta mike suka shiga ciki, Azrah tana murmushi ta ce
"Matar Deen" Samira na dariya ta ce
"Haba Azrah shine baki faɗa min abun arziki ba? Da badan nazo kallon motar ba Shikenan Ni ba zan san kun bar gidan can ba" Azrah ta ce
"Toh ai gashi yanzu kin sani" Samira ta ce
"In faɗa miki gida kam Ma Shaa Allah, na muku murna wlh kawata" Azrah murmushi kawai tayi, Samira ta ce
"Wait.. ko dai kina cycle ɗinki ne naga kina wani abu kamar wata mai laulayi?" tayi maganar tana zare veil ɗin jikinta tana haurawa kan gadon
Azrah ta ce "toh ai kema kin san yadda yake galabaitar da Ni" Samira ta ce
"Sannu, shine kike wani yi kamar mai ciki? Toh ai ko Ni ina jin bana yin haka" Azrah bata san sanda ta fashe da dariya ba ta ce
"Samira just tell me kina da ciki ba sai kin kawo wani reference ba" Samira na murmurshi ta ce
"Oho, duk yadda kika ɗauka dai dai ne" Azrah ta kura mata ido ta ce
"Ki ce sirrin daya sa kike ta glowing kenan? Ah Ma Shaa Allah, Allah raba lafiya, na kusa zama mother ashe" ta amsa da Amin sai kuma ta ce
"Ke ban baki labari, last week dai mutumin ki sai gashi a gidan mu" Azrah ta taɓe baki sanin halin Sadeeq ɗin da Saif duk ɗaya ne, a ranta ta ce ai dole suyi abota...
Sai can yamma sannan Saif yazo ɗaukanta, Azrah ta raka ta bakin gate ta ce
"Toh sai Anjima" Samira ta mata wani kallon ta ce
"Anan zaki tsaya? Kuma ba zaku gaisa da shi bane?" Azrah ta kirkiri murmushin ta ce
"Muje, na ɗauka ba zaki so bane" har Azrah suka isa jikin motar Saif bata sake fuska ba, koda zasu gaisa wani wajen take kallo a haka ta koma gida.....
Da yamma bayan duk ma'aikatan sun tafi, Sadeeq ya fito daga office ɗinsa kai tsaye ya nufi wajen masu gadi, suna ganin sa duk suka miƙe suna gaishe sa ya amsa sannan ya ce
"Tambaya nake son muku please" suka amsa da okay sir, ya ce
"Ku tuna, jiya bayan kowa ya tafi, akwai wanda ya dawo cikin building ɗin nan ne?"
Daya daga cikin masu gadin ya ce
"Eh ranka ya daɗe, Miss Safiyya ce ta dawo, wai ta manta waya" kallonsa Sadeeq yake yi ba kiftawa, sai kuma ya ce
"Kamar da misalin karfe nawa ne?"
"Wajen biyar da da wasu mintinan haka sir" suka amsa
Wani tunani ne ya fado masa a rai, idan bai manta ba jiya da yake cikin Office kafin ya tafi gida kamar yaga Safiyya ta ɗaura story, da sauri ya ciro wayansa ya shiga Whatsapp ya buɗe status ɗin Safiyya yaga da gaske hakan ne, tun around 3:00pm ta yi updating da 'Bad/stressful day' wani murmushi ne ya ƙuɓuce masa ya ce
'Hmm…' sai kuma yana kallon su ya ce "Thank you" daga haka ya wuce
Kallon juna suka yi, sai yanzu suma suka tuna da zuwanta jiya, nan suka fahimci dalilin tambayar nasu da yayi
Yana haurawa sama ya nufi system room, ya kunna CCTV, a hankali ya fara kallo, dai dai time ɗin da suka faɗa masa ya yi forwarding, har sai daya tabbatar da ganin Safiyya ta shigo building din, ta fita, sannan daga footage na second floor ya kuma ganinta a wajen da leak ɗin ya faru.
Murmushi ya sake "Game over..." ya furta, sai ya miƙe ya fita daga room ɗin.
Da daddare... Sadeeq na zaune gaban mahaifinsa Mr Alhassan fuskan nan nasa baka gane ina ya nufa ya ce
"But Dad, why would you expose her name like that in public? You know Azrah better, Amma hakan zai ɓata mata suna" Mr. Alhassan ya ce
"Dokar Majestic Vaults Ltd kenan muka bi, ba'a ɓoye laifi. Ni kuma na fara yarda ne saboda bata zo aiki ba yau, kuma ai ba a shaidar mutum..." Sadeeq yayi murmushin takaici ya ce
"I've left cash, files, and other valuables on my table countless times" sai yayi shiru yana girgiza kai ya ɗaura
"But... She never touched anything that wasn't hers"
Mr. Alhassan ya dan yi shiru yana kallon ɗan nasa a hankali ya ce
"Kayi gaskiya... Kawai dai nima rai nane ya ɓaci saboda asarar da zanyi"
"Good night, Sir" Sadeeq ya furta yana murmushi takaici daga haka ta miƙe ta bar parlon
Mahaifiyarsa ta ce
"Alhaji, kar kaji haushin sa akan hakan, kasan shi baya son ganin an zalunci wani ko an ɓata ma wani suna ne" ya gyada mata kai ya ce
"Na fahimta"....
Azrah ta farka da safe har sannan akwai ciwon maran, amma hakan bai hana ta shiryawa da wuri ba, ga wani kyau na musamman data yi.
Ta saka doguwar riga Maroon color, an mata ɗinki fited gown ya zauna luf a jikinta, ta ɗaura Black open Abaya a kai, ta saka simple gold accessories da low heel shoe, ta ɗauki Maroon handbag , ba karamin kyau tayi ba, ta fito daga ɗakin ta samu Zahra na breakfast already...
Da ta isa Majestic tun daga bakin gate ta kalli yadda gatekeepers suke kallonta sai tayi alaƙanta hakan da maybe ta fuskanta ya kumbura ne tunda idan cycle ɗinta ya zo haka yake mata, tun daga first floor har zuwa can sama, mutane sai magana kasa-kasa suke idan sun ganta, amma sai ta ɗauke kai daga kowa ganin kamar wata baƙuwa haka suke kallona, tazo wucewa a row ɗin office ɗinta kenan, sai ta haɗu da Miss Safiyya wadda ta sha gabanta tana murmushi mai cike da kallom mugunta, ta ce
"In ba a cika kwano ba, ruwa ba zai ɓullo daga gefe ba… Yau ne kwanon naki zai cika kuma dole zai zube Azrah"
Azrah ta tsai da tafiyarta, zuciyarta na bugawa ta juya tana kallon Safiyya da har ta cigaba da tafiya, ta bi bayanta da kallo, haka kawai taji bata fahimci maganarta ba kuma sai ta samu kanta ta da zargin something isn't normal dan yau kallon na daban ake mata ga kuma Safiyya yanzu
Kawai ta juya ta karasa office, tana shiga Sadeeq ya ɗago kansa for the first time in his life ya kalle ta in a very calm and soft voice, ya ce
"Meyasa jiya baki zo ba?"
Azrah ta tsaya cak, tayi shiru, ta juya bayanta tana kallon ko zata ga wani, ganin babu kowa a bayanta hakan yasa ta fahimci da ita yake yi, hakan yasa a hankali ta ce
"Banda lafiya ne"
Sadeeq ya ce
"To me yasa baki sanar ba?"
Azrah ta dan juya kanta, ta ce
"Na kira ka, baka ɗauka ba ai, Ni kuma banda numbern kowa" kallonta yake ba kiftawa, so yake yaji ina ta samu numbern sa sai kuma ya tuna suna group ɗaya na schl sai ya taɓe baki, ya dan lumshe ido, tunawa jiya da gaske yaga missed call from unknown, yayi shiru, bayan wasu some seconds, sai kuma ya ce
"It's okay"
Ta karasa ta zauna, duk da haka tana jin wani iri a jikinta, kamar ta tambaye sa lafiya? Sai kuma ta karasa ta zauna ta fara aikinta
Kamar karfe 9:30am, ta sauka kasa domin siyan light food, tana hanya wani staff ya kira ta gefe, yana kallon gefe da gefe kamar mara gaskiya ganin babu kowa yayi kasa da murya ya ce
"Please Miss Azrah, ba domin cutarwa ba, amma akwai abu da ya dame ni, wannan zancen da ake yi yanzu... cewa ke kika fitar da bayanan company... ba gaskiya bane ko?"
Azrah lokaci guda taji wani irin jiri yana neman kwasarta har sai data kusan missing balance ɗinta ta dafe abu tana kallon sa still trying to process me yake nufi ta ce
"Wani bayanan na fitar? Kamin bayani yadda zan gane please? Aihoo shine dalilin daya sa kowa yake min wani kallon yau?"
Staff ɗin ya dan yi shiru bai san bata sani ba, ya ce
"Please Miss ki rufamin asiri kar kice daga baki na kika fara ji, za'a yi calling meeting, dole zaki ji, amma yanzu dai ki taimaka min ki kwantar da hankalin ki, duk yadda mutane suke yaɗa maganar sosai jiya, sai dai ni dai na yarda da ke, ba zan taba ganin ke zaki cutar da kamfani ba"
Ta gyada kai cikin sanyin murya ta ce
"Na gode sosai"
Abincin data fasa tsiya kenan ta koma sama, taji zuciyarta na ƙuna kamar tayi kuka, kamar ma ta koma gida gaba ɗaya. Sai dai tunawa da halin da ake ciki, da yadda mutane zasu ɗauki hakan a matsayin hujja, yasa ta cigaba da aiki a system ɗinta wanda bata ma fahimci me take yi bama, kawai ta bari ta dafe kanta. A take kuma ta tuna maganar Miss Safiyya
"Yau ne kwanon naki zai zube" kawai tayi murmushin takaici
karfe goma na safe. Aka ga notices na Emergency Meeting at Conference Room by 10:00AM. Attendance is Mandatory
Kowa ya hallara. Staff duka sun cika dakin taron, wasu suna tunani da fargaba, wasu na tsoron abin da zai fito fili. Azrah ma tana daga cikin masu zama a gefe, da idanun jaa da ke bayyanar da baƙin ciki, sai kuma Sadeeq ya shigo cikin fara'a mai cike da natsuwa, ya zauna a gaba. Kallon farko yayi wa duka staff din, sannan ya fara magana da nutsuwa
"Kafin wani yanke hukunci a kan wani, yana da kyau mu samu cikakken bayani. Jiya na karɓi wani file wanda ya kunshi bayanai masu mahimmanci game da companyn nan, da kuma inda aka tura bayanan sirrin, wanda ya turo min, ya yi hakan da niyyar kare martabar kamfanin, sannan kuma a yanke wa mai laifi hukunci. Ina so ya tashi ya faɗi hujjojin sa
Wani staff mai suna Umar ya tashi tsaye ya ce
"Sir, ni ne na turo maka file ɗin jiya, na same shi ne daga system na Azrah. Duk evidence ɗin na nuno yadda aka fitar da bayanan clients da kuma wasu confidential projects, harda bayanan sirrin"
Sadeeq ya gyara zama, ya ɗan kalli gefe inda Manyan Staff suke zaune harda su Mr Alhassan da PA ɗinsa, sannan ya ce
"Thank you! Now, Mr. Tanimu, please... you're the Head of Cyber Security! Let's hear from you"
Mr. Tanimu wanda tun farko Sadeeq ya sa shi bincike a ɓoye, ya tashi, ya bude laptop dinsa, ya haɗa projector. Duk dakin ya yi shiru, ya fara bayani cikin harshen da kowa zai fahimta ya ce.....
#Jiddatulkhayr
08110615256
Episode 77: The Final showdown
"Binciken da muka gudanar bayan rahoton da aka samu, ya nuna cewa an yi amfani da official login details na Azrah, amma daga external device. IP address da aka yi amfani da shi yana nesa da inda Azrah take based a lokacin wanda location ɗinta ya nuna mana tana 'Kofar Marusa' wanda kuma lokacin ɗin wanda ya aikata anan GRA ne
Yana nuna map akan projector
"An yi amfani da VPN don a ɓoye asalinsu, amma mun samu tracking na na'urar da aka shigo da ita cikin network ɗin. A cewar firewall logs, an yi accessing bayanan daga wani system na second floor da yamma misalin karfe 5:17PM na jiya"
Miss Safiyya ta fara zufa, Sadeeq sai murmushin gefen baki yake yi, Mr Alhassan ya zuba ido yana ganin abin da bai sani ba
Mr. Tanimu ya danna wasu screenshots
"Wannan shine footage na CCTV. Ga wanda ya shiga office din a jiya kenan"
Cikin video, aka ga Miss Safiyya na shiga office da dan emergency badge wanda yawanci ana bari staff su rika amfani da shi idan suna buƙatar komai da gaggawa. Mutanen Conference room din suka soma fadin 'Subhanallah… Innalillahi…'
Azrah ta runtse ido, hawaye na zuba, a hankali ta shiga gode ma Allah, ashe abin dake faruwa kenan bata sani ba?
Wani daga cikin staff yace
"Allah Ya isa! Tun zuwanta ake cutar da ita kawai saboda tana da kamala ba ruwanta da kowa"
Miss Safiyya ta mike tana ihu tace
"Wallahi karya ake min! Wannan kawai shiri ne! Na shigo domin wayata dana manta ne, ban taba taba wani system ba!"
Amma Mr Tanimu yace cike da nutsuwa
"A'a Safiyya, muna da full access log, an yi transferring bayanai ne daga system ɗin Azrah zuwa flash, kuma flash ɗin an saka a system ɗinki"
Mr Alhassan wanda tun farko yake cikin tsananin mamaki kuma yake ganin kokarin ɗan nasa, ya girgiza kai kawai, ba ya buƙatar karin bayani kuma
Sadeeq ya gyara zama, ya ce
"Now my turn. Na duba CCTV footage tun daga lokacin da aka fitar da bayanan har zuwa lokacin da aka turo min. Na kuma gano cewa lokacin da aka ce an aika da info, Azrah bata ma cikin building. Kuma lokacin da aka ce system ɗinta ne aka yi amfani da shi, an riga an rufe shi daga server central monitoring system. Wato... ko ma wanene ya yi haka, ya ɗauki access ta amfani da shirin cutar da ita, amma yanzu gaskiya ta fito, idan kuma har sannan akwai mai Ja za'a iya tambayar masu gadi su fada muku jiya cewa Samira ta dawo wannan maaikatar"
Azrah ta lumshe ido, hawaye ya fara tsintiri a fuskar ta. Staff da yawa suka juya suna kallonta da tausayawa da mamakin kuma yadda Safiyya taso mata makirci sai gashi ba'a je ko ina ba asiri ya tonu
Sadeeq ya kalli mutanen room ɗin ya ce
"Kowa ya sani, Majestic Company tana girmama gaskiya da amana. Dukkan matakin da ya dace da wanda ya aikata hakan, za a ɗauka"
Dakin ya kaure da murmurmushi da 'Alhamdulillah' amma duk da haka, Sadeeq bai daina kallon Azrah ba cike da wani irin tausayinta
Bayan bayanan da aka bankado gaskiya, har sannan wasu daga cikin manyan kamfanin musamman Mr. Alhassan, suka kasa sauya matsayinsu, duk da an tabbatar da rashin laifin Azrah, da laifin Miss Safiyya ce, Mr. Alhassan ya kalli sauran board members yace da kakkausar murya
"Koda gaskiya ta bayyana, dama tuni zucin mutane ta cika da koƙonto tun jiya. Ba zai yiwu mu cigaba da aiki da wanda aka kama da irin wannan laifi ba, musamman idan har zata iya lakawa wani irin wannan cin amanar, that shows weakness in judgment"
Ya juya ya kalli Miss Safiyya da Azrah, ya sauke ajiyar zuciya, ya ce
"Miss Safiyya, daga yau ba zaki cigaba da aiki da Majestic ba. And for you Azrah… we appreciate your dedication. Kuma muna mai baki hakuri akan rashin fahimta daga farko"
Miss Safiyya ta fashe da kuka tana roko
Azrah ta kalle su da idanunta wanda suka cika da hawaye, ta bude baki zata yi magana, sai bakinta ya rufe da kuka,dakyar ta ce
"Sir… please… ka yafe mata, ban taba fatan wani abu zai faru da Majestic ba. And… ita ma Safiyya ta gane kuskurenta. Please, give her another chance. I'm okay, I've forgiven her"
Tashin hankali ya sake shiga zuciyar Safiyya ganin anshigo da white envelope, da sauri ta durƙusa gaban Azrah tana kuka, tana cewa
"Azrah please… ki yafe min. Wlhi sharrin zuciya ne da shaidan da yayi galaba akai na, ki tausaya min ki musu magana kar su koreni, ki gafarceni"
Mutane suka fara watse wa daga taron musamman da aka ga Mr Alhassan ya fita, kowa da abin da yake cewa
"Allah ya kyauta… Amma wannan halin, wlh da wuya a sake yarda da mutum"
"Tafiyar da kamfanin na bukatar mutanen da suke tsayayyu da rikon amana amma irin su Safiyya ai sai su saka a Kore ka lokaci guda ba gyara ba dalili"
Azrah ta kama hannun Miss Safiyya ta ce
"Ki tashi mu je Office din Mr. Alhassan. Ba za a bar ki a haka ba, zamu basa hakuri"
Suka tafi tare. Azrah na kukan tausayi, ta tsaya gaban Mr. Alhassan, tana rokonsa
"Sir… Na yafe mata da zuciyata ɗaya,, Kuma wannan kamfani da shine suke cin abinci, please a bar ta cigaba da aiki, idan yaso ta ɗauki alkawarin ba zata sake ba, I'll be more professional idan tana nan"
Mr. Alhassan ya gyara zama, ya yi shiru, ya kalli Azrah da kyau sannan yace
"This shows strength… not weakness, kin kara samun girma a idona, Azrah. You're rare"
Ya juyo ga Miss Safiyya ya ce
"Wannan ita ta ce ta ce a yafe miki, don haka... welcome back. Amma ki sani, this is your final warning" da sauri ta gyaɗa kai tana musu godiya fuskanta duk ya ɓaci da hawaye da majina....
Oga Mahmud ya shiga office ɗin Sadeeq fuskansa karara takaici, ya ce
"Kai gaskiya dole in baka labari daga ganin yadda kake zaune comfortable baka san Meya faru ba"
Sadeeq ya bar abin da yake yi ya ce
"Me ya faru kuma?" Oga Mahmoud ya ce
"Hmm.. ai Azrah ta je ta roƙi a bar Miss Safiyya, haka take kuka, tana roƙon Mr. Alhassan har ya amince"
Sadeeq ya tsaya cak, yaji ransa ya ɓaci, idanunsa suka kaɗa da takaici, cikin masifa ya ce
"Are you serious right now?! Wani irin hauka ne wannan? Wace irin zuciya gareta?! How can she beg for someone who tried to ruin her life and career?! This is madness!" Yana gama maganar ya daga desk din gabansa, sai kuma ya miƙe, ya fice da sauri daga office din, kai tsaye ya tafi inda Azrah ke zaune a room din
Ya buɗe ƙofa ba tare da knocking ba, ya tsaya gaban ta yana huci ya ce
"Azrah! Are you out of your mind? Ki gaya min dalili guda ɗaya da yasa zaki ce a bar wacce ta kusa lalata miki rayuwa! Wanne irin tausayin banza ne wannan?!"
Azrah ta ɗago idanunta masu hawaye ta ce a hankali
"Because I know what it feels like to be wrongly judged… and I wouldn't want anyone else to go through it, not even her"
Sadeeq ya tsaya yana kallonta da takaicin jin abinda ta faɗa, kamar ya sharara mata mari haka yake ji, dakyar ya ce
"Amma ai you saw evidence with your eyes, right?" Azrah ta girgiza masa kai ta ce
"Last chance za'a bata ai" ya tsaya yana kallon ta kamar zai yi magana… amma ya kasa sai kuma ya juya yana girgiza kai ya fice daga room ɗin.
Bayan shekara biyu.......
Fix your posture, the real show is about to begin.........
Ehhh yanzu wasan zai fara....
Rayuwa ta sauyawa Mama da Yaranta, wanda banda Allah wadaran babu abin da ake faɗi a kansu a cikin wannan unguwar, gashi yanzu samun kuɗinta ta ba kamar da ba, su samu wanda zasu ci abinci ma yana zama matsifa a gare su
Bappah kuwa tun wancan lokacin har zuwa wannan tsawon lokacin a kwance yake, jikin har sannan babu daɗi, gashi nan gashi nan ne dai...
Mama ta ci nasara akan Azrah da 'yar uwanta Zahra, wanda yanzu babu wanda yake tunkaran su da maganar aure, harta Khalil ya daina kiranta ko ta kira sai ya gwada bai santa ba, karshe dai ta hakura ta ɗau dangana
Tsakanin Sadeeq da Azrah a Majestic sai abun daya tabarɓare, tsana ce sosai a tsakaninsu, ko kaɗan baya ragar mata itama haka ko kaɗan bata basa girmansa musamman yadda ko agaban kowama zai iya zaginta. tsakanin sa da Staffs ɗinsa kuwa kamar yadda yake haka nan ma yanzu, abu kaɗan zai kore ka, barin da yanzu Mr. Alhassan baya zama
Safiyya kam kamar Azrah ta kara wutan tsanarta ne, duk wata hanya da za'a ga bakinta haka nan take bi, kuma har sannan bata daina bin duk wasu plan na ganin ta kawo Azrah kasa ba
Sadeeq ko kaɗan bai tsira daga tarkon Mata ba, haka nan Mata zasu ta kawo masa kansu suna masa tallah, amma ko kaɗan baya kallonsu, musamman Miss Safiyya har kuka ta sha masa amma yayi kamar mai San tana yi ba
Samira da Saif sun samu babu girl, wanda yanzu kuma ba wani zaman lafiya suke samu ba, har hakan yasa Mummy saka baki a lamarin, wanda shi yayi alƙawarin sai ya sake aure...
Yana zaune yana kallon abokinsa dake basa shawara ya ce
"Kai kana ganin zata yarda ne?" Saif ya girgiza kai ya ce
"Bana tunani gaskiya, dan ko kallo na bata yi, na faɗa maka ai tun farko yadda nayi treating ɗinta ina ga kamar tana da riko ne" ya ce
"Nahhh, kar ka ga laifin ta, tun farko dama bai kamata ka kyamace ta ba, ko da kuwa daga ina ta fito balle ma she's so beautiful, ga ilimi ga kuma iya daukan wanka"
Saif ya ce "Yanzu ban san yanda zan yi ba, ai Shiyasa ko da wasa dana san tana aiki tare da su Sadeeq ban taɓa zuwa ma'aikatar ba, ko na samu Mummyn ne?" Ya ce
"Yes wannan ma is a good idea, ka same ta kuyi magana idan yaso sai ita ta mata magana ta dawo wajen ku da aiki, daga nan kuma ita Mummy sai ta shige maka gaba wajen nemanta" sauke wani ajiyar zuciya yayi ya ce
"Amma da kamar wuya ta yarda, gaskiya yanzu ina regretting, gata da hankali, ilimi, da kuma sanin ya kamata, wlh tsoro na kar ta ki yarda saboda Samira" ya ce
"Zan yi tunani akan hakan kuma, and for now ka fara maganar ta dawo wajen naku da aiki, zaka ninka mata kuɗin salarynta, ko daga baya Sadeeq ya sani kana da bakin cewa baka san a wajan take ba"....
Azrah ta ɗauki papern da Zahra ta ajiye mata ta warware, karanta contents ɗin tayi baki buɗe, Zahra dai taki yarda ko da wasa ta kalli direction ɗinta, Azrah ta miƙe ta karasa inda Zahra take zaune akan Sofa ta ɗaka mata dundu sai da yayi kara Zahra ta sa ihuuu tana turo baki, Umma dake zaune akan 2 seater ta ce
"Aaaa, toh sannun Azrah da duka mini 'ya" Zahra ta turo baki ta miƙe ta karasa wajen Umma, Azrah ta zauna tana kallon Umma cike da masifa ta fara magana
"Yanzu Fisabilillah Umma dan Zahra zata tsiya textbook shine ba zata iya faɗa min da baki ba sai ta rubuta min?" Umma ta ce
"Ayyah Azrah, kila tana ganin abubuwan suna yawa ne" Azrah ta ɓata rai tana hararan Zahra, Zahra ta ce
"Allah Yaya kunya nake ji, kalli last week haka kika tsiya min text book biyu kusan dubu ɗari, ga uban school fees, ga transport, haba mana, kullum ke kina cikin bani kenan? Ko ke baki cin kudin ki kamar yarda nake ci ba" Azrah ta bata rai ta ce
"Toh sai ki daina tunda haka kika ce 'yar rainin hankalin, nasha ce muku duk sanda kike bukatar wani abu don't even ask me kawai dauki ATM dina kiyi using amma yanzu kina da bakin cewa wani abu" dariya Zahra tayi ta rungume Azrah, Umma na kallon yaran nata cike da sha'awa tana kuma fatan Allah kawo musu maza nagari...
Siyama ta shiga kai wa Bappah abinci a ɗakinsa, tana shiga taga Bappah numfashin sa na sama kamar wanda zai tsume bata san sanda ta sake kwanan hannunta ba ta kwalawa Mama kira, ganin hakan ba mafita bane yasa ta fice a guje, kusan cin karo tayi da Mama da take zuwa itama dan jin menene ne, tana kallon Siyama ta ce
"Ke lafiya?" Siyama bakinta na rawa tana haki tana nuna mata ɗakin Bappah ta ce
"Bappah ne.. bappah ne.. numfashinsa.. kamar.." inaaa Mama taga ba zata iya tsayuwa jiran bayanan Siyama ba, kawai ta shiga ɗakin a guje, ai kuwa ta same sa kamar ma yana struggling ne da numfashin, ta karasa kansa da sauri tana kiran sunan sa amma abin kamar gaba ma yake yi, ta ce da Siyama
"Ke fita ki kira mana abin hawa mu wuce asibiti, wannan ya fi karfin mu anan" ba shiri Siyama ta wuce waje a guje, bayan kusan minti biyar ta dawo ta ce
"Mama ga mai adaidaita sahun a waje" Mama ta ce
"Ɗan masa magana ya taimaka mana ya fitar mana da shi" haka kuwa suka yi, daga nan suka nufi asibiti da Bappah kamar ma babu rai tattare da shi....
Mama dake zaune a ward tayi tagumi abun duniya sun haɗu sun mata yawa tana tunani sai ga likita ya fito ya ce
"Zaku biya kudin gado, sannan kuɗin ganin likita da kuma magunguna da allurai da za'a masa, ga shi yana fama da Mental trauma dole ku fara ajiye kuɗi a kasa a ƙalla ya kai 100k" Mama ta zaro ido ta ce
"Dubu ɗari kuma likita?" Ba tare daya kalle ta ba ya ce
"Eh idan kuna bukatar samun saukin sa ba" Mama ta fito tana share hawaye, yanzu ina zata fara? Gashi not long ago ta kaiwa boka 200k kuma aikin data saka sa na samari suyi ta zuwa wajen 'ya'yanta amma har yanzu shiru....
Episode 78: The Beginning of the End
Mama na zaune can yamma tayi tagumi, Siyama ta zo ta zauna gefenta ta ce
"Mama kina jin likitan abin da ya ce yana damun Bappah?"
Mama ta ce "wai menene?" Ta ce
"Hmm wai damuwa da ciwon zuciya wanda mutum ke fuskanta bayan wata mummunar abu daya same sa, kamar tashin hankali, ko wani abu daya girgiza sa shine ya shiga wannan abun" Mama tayi shiru tana tunani sai kuma ta kalle ta da sauri ta ce
"Ai ya daɗe bai shiga ba, Ni sai yanzu ma nake kara tunawa, tun lokacin daya rabu da wancan kunamar shikenan yau lafiya gobe babu ai shikenan tunda haka ya zaɓa ma kansa ya je can ya karata yanzu da wanne zan ji? Da rashin abinci da bamu da shi ko da kuɗin jinyarsa?" Wata likita ta karasa tana kallon Mama ta ce
"Haba baiwar Allah, tun yaushe ake jiranki da ki kawo ko da wani abu ne a samu a fara basa kulawa amma har yanzu shiru.. kamar ma baki damu bane naga.. idan baku shirya bane ɗauki mijinki ku tafi" Mama ta bi yarinyar da kallo, sai kuma ta kalli Siyama ta ce
"Gaskiya ba abin da zai sa naci bashi, idan kuma ta gagara sai dai yayi ta zama a haka, ai shi yaga daman shiga wannan halin" Siyama ta ce
"Uban me su Azrah suke da ba zasu bada kudin ba? Dole sai kin wani wahalar da kanki ne Mama? Kawai zan je na sanar da su nace su bada kuɗi mun kashe wanda zamu iya sauran kuma su cigaba" Mama ta ce
"Daya fi, idan kin sanar da su Ni zan koma gida dan banga zan iya zama a asibiti ba gaskiya".....
Karan shigowar message yasa ta dauki wayar tana buɗe sakon, sai kuma ta ɗaga kai tana kallon Dada ta ce
"Dada ya shigo kuɗin, Allah ya saka musu" Dada da yanzu ta fara samun ɗan karfi ta ce
"Har nawa ne ta turo?" Maman Amira ta ce
"Ai dubu ɗari ta turo" Dada ya fashe da kuka tana girgiza kai ta ce
"Allah musu albarka, ya nuna min aurensu, Allah basu maza wanda zasu kula da su harda mahaifiyar su" Maman Amira na Murmushi ta ce
"Amin Amin" Dada ta ce
"Idan kin huta sai ki tsiya min kayan abinci, wata satin kuma sai na sake komawa gun mai maganin nan, amma yanzu kira min Azrahn" Maman Amira na murmurshi ta shiga kiran layin Azrah, yana fara shiga ta miƙa wa Dada
"Hello Dadan mu" Azrah ta faɗa tana dariya, Dada ta amsa da
"Allah sarki 'yar albarka! Ke da kike fama da makarantar 'yar uwarki shine wannan watan zaki kara kuɗin da kike turowa?" Azrah ta ce
"Toh ai zaki yi magani Shiyasa, yanzu ya jikin naki kuma?"
Dada dake share hawayenta ta ce
"Alhamdulillah da sauki" Azrah ta miƙawa Umma, Umma bayan sun gaisa ta ce
"Ayyah Dada ina son na sake zuwa na duba jikin naki amma dake duk suna fita kuma nakanyi abinci kafin su dawo Shiyasa bana son mu bar gidan ba kowa sai Zahra tayi Hutu tukun nan" Dada ta ce
"A'a karki damu Bitti, yanzu ai jikin da sauki sosai ma, kawai kin san samun saukin ne sai a hankali" bayan sun yi sallama ta kashe wayan..
Almajirin su dake sakar gidan yana shara yaji ana knocking, ya ce
"Waye ne ? kofar a buɗe take" yau ne rana ta farko da Siyama ta fara shiga cikin gidan duk tsawon lokacin nan, ta karasa tsakiyar compound ɗin tana taɓe baki, Zahra da tun daga parlorn suka jiyo muryanta, wuff ta miƙe ta fita bakin kofar parlorn tana kallonta ta ce
"Ya aka yi?" Siyama ta ce
"Toh Ubanku ne bashi da lafiya kwance asibiti, mun kashe iya wanda muka ga zamu iya sauran idan kun ga zaku iya tohh, idan kuma ba zaku iya ba sai ku bari ya karasa mutuwan" Zahra tayi wani dariya ta ce
"Wato ubanmu ba naku ba? Well,sannan idan ya mutu kune ai abin kuka bamu ba tunda bamu sara ci, ko sha ko sutura ba" Siyama ta mata wani kallo tana jin yarda tafara boiling inside tace
"Idan kuka ga dama kar ku taimaka masa, ruwan ku" ta juya zata tafi, Zahra tayi saurin cewa
"Tunda har kuka zo neman taimako, ko nace bara ai shikenan za'a taimaka masa ɗin ba dan halin ku ba" Siyama ko juyowa bata kuma yi ba ta fice daga gidan, dan ji take zata iya makure Zahra idan har ta tsaya ɗin
Zahra na shiga parlorn Umma ta mata wani kallo ta ce
"Ke da waye?" Zahra ta turo baki tana kallon Umma sai kuma ta ɗauke kai ta ce
"Wai ubanku ne bashi da lafiya yana asibiti sun kashe wanda zasu iya sai mu cigaba, haka ta faɗa min fa Umma, ai manners ne ta rasa" Umma ta ce
"Shine har hakan zai baki damar cecekuce da ita? Idan ke mai manner ne sai ki tura aniyarta tunda kuma Ubanku ne, ya shafe ku kuma"
Ta zauna tana kallon wani wajen ta ce
"Umma ai Ni komai nayi laifi ne a wajenki, baki ga laifin ta na yarda tayi magana ba sai nawa dana bata amsa daidai da tambayarta" Azrah data kasa ɗauke kanta akan Zahra ta ce
"Bappahn ne bashi da lafiya?" Zahra ta ce
"Eh, kuma yanayin maganar inaga jikin ba wai da sauki bane" Azrah ta ce
"Wani asibitin kuma?" Ta ce
"Oho ai bata faɗa min ba" Azrah ta ce
"Matsalata da ke kenan, bansan yaushe zaki koyi tambayar mutum abu mai muhimmanci ba
Azrah ta kalli Umma ta ce
"Umma yaushe zamu je duba sa?" Umma ta mata wani kallo ta ce
"Ke da Zahra amma ko?" Zahra ta ce
"Ah toh, Amma banga dalilin daya sa zaki ce harda Umma ba, mune dai ya kamata" daga haka Azrah taja bakinta tayi shiru sai kuma ta miƙe ta ɗauki veil ɗinta tayi hanyar fita
Umma ta ce "Ina zaki kuma?" Ta ce
"Zan tambaye su ne, ai tunda suka mana magana kila abin yafi karfin su ne" Umma ta gyaɗa mata kai, daga haka ta yi hanyar waje..
Da sallama ta shiga cikin gidan nasu, Siyama da Habibah duk suna zaune, babu wanda ya amsa mata, ta ce
"Ai ko ba zaku kulani ba ai amsa sallar tawa wajibi ne akan ku ko?" Siyama ta ce
"Bayan maganar da Zahra ta gama gaya min, shine kike tunanin sake kula ku?" Azrah ta ce
"Toh ai naga ba Zahra ba ce anan, tunda na shigo nayi sallama ai sai kuji dame na zo" Siyama ta ce
"Toh muna dai ji ko?" Ta ce
"Ba komai bane sai dama ina so nasan wani asibiti aka kai sa sannan wani ward ne"
Siyama ta taɓe baki ta ce
"General Amadi Rimi specialist, wat kika ce ko me, Ni ban rike ba" Azrah ta juya ta ce
"Nagode" daga haka ta fita daga gidan, gidansu ta koma tana shiga ta samu Zahra ta daura girkin dare, ta shige dakinsu tana kallon Umma ta ce
"Umma bari inaga Ni zan tafi yanzu" Umma ta ce
"Zahra fah?" Zahra ta daga murya daga kitchen ta ce
"Ke kije amma Ni ina girki sai gobe In Shaa Allah" Azrah ta wuce dakin su ta ɗauki jakkanta daga haka ta fita...
Azrah ta shiga cikin asibitin da saurinta kamar wadda ake turata, hannunta rike da jakarta, idonta cike da damuwa, tana isa bakin 1st ward kawai, ta hango Mama zaune akan kujera, suna haɗa ido ta ɗauke kanta kamar bata son ganinta
Ta isa har inda Mama ke zaune, kafin ma ta samu damar gaishe ta
Mama ta tamke fuska ta ce
"Ki wuce can… likitan na jiranmu a office dinsa"
Bata ce komai ba, ta juya da sauri, zuciyarta na bugawa, ta nufi inda aka nuna mata, tana shiga ta zauna kan kujera jin ta gaji, bayan ta gaishe sa ta ce
"Ni ce 'yar malam Muhammadu… nazo ne dan biyan kudin asibitin"
Likitan bai ɗago ba har sannan ya ce
"Waye shi toh?" Ta ce
"Ga dai wanda suka zo tare tana can zaune"
Sai sannan likitan ya ɗago daga rubuce-rubucensa, yana kallonta da launin tambaya a idanunsa ya ce
"Dama kuna da kuɗin biyan ne kuka barshi yana galabaita?"
Azrah ta lumshe ido, wato ba'a ma fara ma bappah wani treatment ba? Ta daure ta ce
"A'a… ba tare muke zaune da shi ba, amma ni 'yarsa ce, don Allah likita… me ke damunsa ne amma?"
Likitan ya sauke ajiyar zuciya, sannan ya daidaita muryarsa ya ce
"Patient ɗin naku na fama ne da mental trauma"
"What!? Mental trauma kuma?" Azrah ta maimaita da fargaba, tamkar kamar bata ji ba
"Eh" ya ce, yana kallonta da tausayawa
"Wannan wata irin cuta ce da ke shafar tunani da yanayin hankali, mutum zai iya shiga wani hali na rashin gane inda yake, ko ya manta da abubuwan da suka gabata, wasu lokuta yakan rikice ne, ko ya zama mai shiru, zuciyarsa tana cikin firgici, kwakwalwarsa kuma ba ta iya daidaita tunani kamar da"
Hawaye Azrah ta fara sharewa, ta ce
"Amma likita meya ke haifar da hakan?" Ya ce
"Damuwa da shock, sai kuma yawan tunani" Azrah ta ce
"Don Allah likita… ku fara masa magani yanzu, ga ATM ɗina nan, ku ciro kuɗi ko nawa ne, kawai burina ya samu sauki"
likitan ya girgiza mata kai, ya ce
"A'a, zaki je unit ɗin biyan kuɗi ne, su cire daga can"
Azrah ta miƙe, ta karbi bill papern a hannun likitan, ta fita da sauri ta nufi unit din, ta biya duk abin da ake buƙata, bayan ta gama, ta tsaya ta siya masa abinci, sannan ta dawo cikin asibitin..
Data isa ward ɗin, wucewa tayi. ba tare da ta ko kalli Mama ba, ta buɗe ɗakin da Bappahn yake ta shiga, lokacin har an ɗaura sa kan medications, ta ajiye abincin a gefe, ta zauna kusa da Bappahn tana kallonsa da tausayi
Ba kaɗan ba Bapphan ya rame yayi baki, sai take jin bata kyauta masa ba, bata sauke hakkinta na 'ya akansa ba data bari har yayi going through, hawaye ta fara sharewa, a ranta tayi alkawarin komai tsadar kulawa, ba zata sake barinsa ya shiga haka ba
Motsin Bappah ya fara, ta kura masa idanu a hankali ya buɗe yana kallon saman ɗakin, sai kuma taga yana motsa bakinsa, ɗakin yake bi da kallo har idonsa ya sauka a kanta, ta karasa jikin gadon tana masa murmushi tare da ce masa Sannu, ya sauke idonsa kasa, yana kokarin tashi, ta taimaka masa harya tashi ya zauna, ta ɗauki takeaway ta buɗe abincin ta ajiye masa akan cinyarsa, ta sake ɗauko yoghurt ɗinma ta ajiye masa ta ce
"Bappah ka ci, nasan kana jin yunwa" kallonta yayi sai kuma ya sake sauke kai, likita ne ya shigo hakan yasa ta mike ta fita
Ba Azrah ta bar asibitin nan ba sai pass 9pm, kafin ta karasa gida har 10pm yayi
Washe gari..
Azrah tana cikin tsaka da aiki a office ɗinta, duk tunaninta na wajen Bappah ne, tana Allah² ta gama aikin gabanta ta tafi asibitin yanzu, sai ga wani staff ya buɗe office ɗin, lokacin babu Sadeeq, yana kallonta ya ce
"Mr Alhassan yana kiranki, Miss Azrah"
Tayi saurin gyara veil ɗinta sannan ta miƙe tabi bayansa, ta nufi officen, tana shiga ta same shi tsaye, yana gyara takardu a saman desk.
"Sir, you called me?" ta tambaya
"Yes Azrah" ya ce, yana murmushi , ta gyaɗa masa kai, ya ce
"Zan tafi wani business trip na kwana biyu. And I want you to take over my position temporarily"
Azrah ta zaro ido sosai, bata ma san tayi hakan ba, sannan tace da sauri
"Okay sir… but I'm sorry to say why me, please? Ga MD Sadeeq, ga su Oga Mahmoud?"
Mr Alhassan ya yi murmushi, yana kallonta kai tsaye ya ce
"Saboda na yarda da ke, and I believe you'll handle things with sense and maturity"
Tayi shiru, zuciyarta cike da mamaki dan ita bata wani son fifitata da yake yi, sai kuma ta tuna zata samu hutu kwana biyu, kawai ta dan sunkuyar da kai ta ce
"Okay sir"
Sai kuma tayi saurin yin shiru dan bata so amsawa ba amma ya zata yi?, Hakan kuma in other hand ya mata, musamman ganin zata samu hutu daga matsin lambar da ke tsakaninta da Sadeeq kwana biyun nan, ta least dukkansu zasu huta
Mr Alhassan ya mike, ya kalleta cike da kwarin gwiwa
"You can take over, Miss" ya fada yana wucewa daga office ɗin
"Okay sir" ta amsa, tana kokarin boye yadda take ji, sai kuma jiki ba ƙwari ta nufi kofa
Daga nan ta koma office dinta, ta tattara wasu takardu and other stuffs dinta, sannan ta koma zuwa office ɗin nasa, tana shiga ta zauna, zuciyarta na dukan uku uku...
Episode 79: Whispers of power, and Hidden Games
Ɗaga kanta tayi jin an buɗe ƙofar office ɗin da sauri
Turus!!! Sadeeq ne tsaye a ƙofar, yana kallonta da mugun mamaki
a kan kujerar Mr. Alhassan? wanda tana zaune comfortable abinta
Idanunsa cike da astonishment, ya shigo cikin office ɗin, sai kuma ta ɗauke kanta cikin rashin shiri fuskarsa kaɗai ya isheta da tsoro
Ta fiye yake yi zai ɗauki abu, da sauri ta miƙe tsaye
"Get out!" ta faɗa da ƙarfi
Ya tsaya yana kallonta, sai kuma yayi murmushi irin murmushin muguntan nan
Direction ɗin da ya nufa ne kawai sai ya fasa ya nufe ta, da sauri ta ce
"Nace get out!" ta kara maimaitawa.
Ta kalli gefenta, ta danna security alert button
Yana kallonta, har yanzu da mamaki a fuskansa sai ya ce cikin husky voice ɗinsa
"Really? Well, who are you? And what gave you the audacity to sit on that seat?"
Cikin some seconds, securities uku suka buɗe ƙofar suka shigo
Azrah ta ce da su
"Ku fitar min da shi daga office ɗin nan!"
Sadeeq ya gyara tsayuwarsa yayi folding hannayensa yana kallon ta da mugun mamaki
Suka tsaya suna kallon juna, ɗaya daga cikinsu ya ce a hankali
"But Miss Azrah, it's MD Sadeeq"
"And so?!" ta ce da ƙarfi
"Nace ku fitar min da shi! Ko baku ji nane?"
Ƙofar aka buɗe
Mr. Alhassan ya shigo
Duk suka juya suna kallonsa, shima su yake kallo ya ce
"What is it?" Azrah ta tsaya ta faɗa masa abin da ya faru
Sai ya kalli securities ɗin, sannan ya kalli MD Sadeeq
Har yanzu Sadeeq bai iya magana ba, yana kallon ikon Allah ne kawai, dan wannan ya wuce tunaninsa
Mr. Alhassan calmly ya ce
"Meyasa zata saka ku aiki kuma ku ƙi yi? Ku aiwatar da abinda ta ce!"
Sadeeq ya tsaya yana kallon Babansa, Securities dinma sun kasa zuwa kusa da shi
Da suka fara zuwa toward him kawai ya ɗaga musu hannu sama, sai kuma ya fice cikin fushi kamar zai tashi sama
Securities ɗin suka bi bayansa suna girgiza kai, suna mamakin audacity da capacity na Azrah.
Azrah ta sauke ajiyar zuciya, ta ce
"I'm sorry sir. Wannan ba zai kuma faruwa ba"
Mr. Alhassan ya murmusa ya ce
"It's okay, Miss. Amma kina kai zuciya nesa pls"
Ya ɗauki briefcase dinsa da ya manta, sannan ya fita...
Sadeeq ya ɗauki makullin motarsa, ba ya jin zai iya ci gaba da zama a wurin nan yau, dan zai iya illata Azrah,
Yana shirin fita sai ga Safiyya ta sha gabansa.
Duk da cewa gabanta na dukan uku-uku, sai ta fara murmushi da wani dirty look da take masa
ta ce da marairaiciyar murya
"Sir... kamar ranka a bace fah? Ina zaka je haka?"
Wani kallo mai cike da ƙiyayya ya jefa mata
Shi a cikin ransa babu wata halitta da ya tsana kamar Safiyya, rashin kamun kanta ya fi komai bata masa rai
Ya ce da murya mai cike da ɓacin rai
"Zaki tashi gaba na, ko sai na hankade ki!"
Sai ta ja da baya sum-sum, ta ba shi hanya
Yayi tafiyarsa kamar zai tashi sama har ya isa wurin motarsa, ya shiga. Kai tsaye gida ya wuce
Yana isa, yayi parking da hanzari, ya fito cikin ɗacin rai
A hanyar entrance ya haɗu da wata cousin ɗinsa ta karasa da sauri tana shirin magana masa magana
Ya kafe ta da ido, ya tamke fuska bai ce komai ba, sai kuma ya wuce ta tamkar bai santa bama
Ɗakinsa kai tsaye ya nufa
Yana shiga ya rufe ƙofa, ya saka mata key
A gefe guda kuma, Mr. Alhassan ya shigo gida
Yayi mamakin ganin motar Sadeeq a harabar gidan yayi parking, ya sauka cikin mamaki..
Mr Alhassan ya tura ƙofar parlour ɗin a hankali, fuskarsa ɗauke da damuwa. Matarsa da ke zaune tana duba waya ta ɗago kai da murmushi
"Barka da zuwa Alhaji, fatan ka wuni lafiya?" Ya ce
"Lafiya kalau Sadeeq yazo gida ne?"
"A'a ban ganshi ba gaskiya"
Mr Alhassan ya ɗan gyaɗa kai cikin mamaki ya ce
"Na ga motarsa a waje ne... Kuma kin tabbata bai shigo ba?"
Cousin ɗin Sadeeq, da ke kan shiga parlour, ta karasa ta ce
"Eh ya shigo sir, amma kai tsaye ya wuce dakinsa"
Fuskar Mr Alhassan ta cika da damuwa 'Hmm… me ke damunsa kuma?' Ya juya ya nufi ɗakin Sadeeq, yana knocking har sau uku kafin daga baya ya buɗe ƙofar da ƙyar.
"Ina wuni sir" Sadeeq ya furta da ƙarfin hali
"Me ya hana ka zama a office? Me ya kawo ka gida a wannan lokaci?"
Sadeeq ya kawar da kai, "Nothing sir"
"No, ka faɗa min gaskiya. Wani abu ya faru ne? Ko dai maganar ɗazu ne?"
Sadeeq ya ja numfashi ya ce
"Haba sir, duk Kai kake sa yarinyar nan ta raina ni? Taya zaka bata kujerarka, kuma duk yadda ta wulakanta ni, sai ka goya mata baya?"
Mr Alhassan ya karasa shiga cikin ɗakin ya zauna a gefen gado ya ce
"Haba Son. Idan na tsaya maka za'a ɗauka dan kai ɗa bane, gaskiya kawai nake bi. Kuma kaima kayi hakuri ka rage wannan rainin hankalin da kake nuna mata, ka duba fa da kai kaɗai take samun issues fah, kuma kai ma kasani tun kafin ma na bata kujerar ta riga ta cancanta, kuma harsh da kake mata ba zai sa ta girmama ka ba"
Sadeeq ya yi shiru, ya lumshe ido
Mr Alhassan ya miƙe ya ce
"Idan na isa da kai, ka koma office yanzu, bana don shiririta"
Sadeeq ya dan jinjina kai, "Okay sir"..
Oga Mahmoud yana kallon Abubakar ya ce
"Bana son wannan aikin ya kwana, ka tabbatar ka gama su yau ɗin nan?" Sai kuma ya maida kallonsa ga Safiyya ya ce
"Kema make sure kin karasa" Oga Abubakar zai yi magana ya ɗaga masa hannun alamar baya son jin komai daga garesu, ya ce
"Ina son idan kun gama da wannan ne na baku sabon aikin kafin Mr Alhassan ya dawo daga trip" da mamaki Abubakar ya ce
"Wai dama baya nan ne? Office dinsa kuma haka zai zauna a kulle kenan? Toh ai no need mu wahalar da kan mu muce sai mun gama aikin yau" wani kallo Oga Mahmoud ya masa ya ce
"Toh office ɗinsa a buɗe yake, Azrah ce ke office ɗin kafin ya dawo, kuma kasan bata wasa da aiki" saura kiris Miss Safiyya ta faɗi sabar razana sai kuma tayi saurin kama kanta tana kallonsa sai kuma ta miƙe ta ce
"I'm coming, sir" daga haka ta fita
Office ɗin Mr Alhassan ta wuce direct, da shige ciki without permission sannan ta buɗe ainihin inda yake zama, turus ta tsaya ganin Azrah akan seat ɗinsa, Azrah ta ɗaga kai tana kallonta, mamaki ne ya kamata ganin idanun Safiyya ya cika da hawaye, kafin tayi magana Safiyya ta juya ta fita da sauri har tana buge Merry da zata zo submitting wani file, office ɗinta ta wuce ta ɗauki jakkanta a ranta tana rantsuwar a satin nan sai ta saka abun da sai an Kore Azrah, a haka har ta bar harabar wajen..
Azrah ta fito a office ɗin hannunta rike da handbag da kuma keyn motar ta, tana shirin sauka ganin Sadeeq yasa tayi saurin komawa baya sai ta wayence cewa waya take yi, ganin ya shiga office ɗinsa kawai ta sauka, parking space ta wuce sai kuma ta shiga..
Horon tayi a kofar gidan su, almajirin su ya buɗe mata gate ta shiga da motar tayi parking, hankalin ta duk na kan Bappah, a haka ta wuce parlorn su da sallama, Umma ta amsa mata, bayan ta shiga ta gaida Umma sannan ta wuce ciki, bayan taci abinci tayi sallah tana kallon Zahra ta ce
"Zahra ki tashi ki shirya mana, ko kin manta zamu asibiti duba Bappah ne?" Zahra ta ce
"Amma dai kin san cewa karatun medicine nake yi ko? Tun ɗazu sai maganar fita kike yi, toh Ni ya kike so nayi da karatun ne wai?" Azrah ta sake baki tana kallonta sai kuma ta ce
"Banyi tunanin zanji wannan maganar daga bakin ki ba, kaff 'ya'yan Bappah akwai wanda yake gudun ɓacin ransa ne idan ba ke ba Zahra?" Zahra ta miƙe ta nufi wajen wardrobe ɗinta tace
"Ni karki wani fassara Ni, ba gashi zan sa kaya ba? Ai shikena" basu wani daɗe sosai ba suka nufi asibiti a hanya suka saya suka tsiya masa abinci, yoghurt sai fruits
Suna isa ward ɗin da Bappah yake suka karasa ɗakin, da Sallama suka shiga, daga Mama har yaran nata babu wanda ya amsa, Zahra ta wuce ciki ba tare data Kalle su ba, Azrah ta gaisheta amma kamar bata san tana yi ba, sai Bappah dake zaune hannunsa riƙe da plate ɗin shinkafa fari da manja, kai ma kana gani kasan ba abincin mara lafiya bane, suka karasa jikin gadon nasa, Mama kuwa ta kura musu ido, tama daina jin taɗin da take yi da yaran nata, Zahra ta karɓe plate na hannun Bappah ta saka masa wanda suka tsiyo a cinyarsa, duk wannan abun tun data gaishe sa taki kara cewa komai balle ta yi magana da shi, hakan da take yi ma dan ta kona wa su Mama rai ne, Azrah ta ce
"Amma yanzu ya jikin dai ? Akwai improvement ina?" Bappah ya gyaɗa kai ya ce
"Anjima ma za'a sallame mu", Azrah ta ce
"Toh sai mu jira mu tafi tare kawai tunda da mota muka zo"
Zahra ta mata wani kallo ta ce
"Amma kin san cewa karatu nake yi ko? Ni da zan koma yanzu shine zaki wani ce sai Anjima" Azrah ta Ciro kuɗi a jakka ta miƙa mata ta ce
"Gashi sai ki hau keke" Zahra ta tsaya kallon Azrah da mugun mamaki, sai kawai ta share hawayen daya gangaro mata ta miƙe ta ɗauki jakkanta, Bappah yayi saurin cewa
"No Azrah, ki tashi ku tafi, Kinga kar dare yayi" Azrah bata so ba amma kawai ta Ciro kuɗaɗen dake cikin jakkanta ta saka ma Bappah a aljihun sa ta ce
"Toh Bappah sai kun dawo, In Shaa Allah anjima zan shigo na duba ka" ya ce
"Allah miki, Albarka" ta amsa da Amin, ya ce
"Inaa...." Sai kuma yayi shiru ya kasa karasawa Azrah ta kura masa ido, sai kuma ya gyaɗa mata kai, hakan yasa tayi hanyar kofar tana wa su Mama sallama duk da tasan ba amsawa zata yi ba, Mama ta ce
"Dan Allah tunda kun gama da abin da ya kawo ku, ku tsaya a matsayin ku" Azrah bata jiyo ba tayi wacewarta
Tana karasa jikin motar ta taga Zahra harta kusa bakin gate, hakan yasa ta shiga motar, ta isa inda take tana mata horn amma Zahra ko da wasa bata jiyo ba, Azrah tayi gaba sannan tayi parking ta sauka ta karasa wajenta da sauri ta ce
"Zahra baki jin ina miji horn ne?" Zahra ta ce
"Ina bukata ne nace miki? Ai da kin tsaya kin taho da su tunda su ne naki, sune dolenki" Azrah ta tsaya kallonta, Zahra zata yi gaba Azrah ta jawota ta ce
"Me haka Zahra? Akan wannan abun ne ranki sai ya ɓaci? Toh I'm sorry" dakyar dai ta shawo kan Zahra har ta yarda ta shiga motar daga haka suka isa gida, tun da suka shigo layin take kallon motar dake parke a kofar gidan Bappah, mutumin yana tsaye a jikin motar kamar yana jiran wani, bayan ta isa kofar gidan su, Zahra ta sauka ta shiga da niyyar buɗe mata gate, Azrah ta juya tana kallon mutumin, sai da gabanta yayi mummunan faduwa ganin fuskansa wani yaro daga cikin gidan nasu ya fito yana masa magana, sai kuma ya juya ya karasa jikin motar sa ya shiga, harya tada motar Azrah bata ɗauke kanta daga kansa ba, tabi motar da kallo a hankali ta furta
"Toh me Saif yake yi a nan? Idan aika Samira ta mata ai ba can gidan zai tafi ba ai, tunda nan din yake kawo ta" haka kawai taji bata yarda da zuwansa ba, taja motar ta ta shiga cikin gidan..
Safiyya ta shigo cikin gidan nasu pass 9pm, da sanɗa sanɗa take tafiya harya ta samu ta shige ɗakinta without letting anyone notice her, tana shiga ta sauke ajiyar zuciya, ta zauna bakin gadonta ta fito da abin jakkan tana kallon, lokaci ɗaya ta fara dariya Mugunta ta ce
"Azrah naki ya kare, ba sai gona ta zaki shiga ba? Hmm, kinyi saurin trusting ɗina, but dole na ɗau mata ki dan ba zaki cigaba da hanani baccin dare ba" buɗe kofar ɗakin aka yi, da sauri ta mayar da abin bayanta, Mama ta karasa shiga cikin ɗakin tana kallonta ta ce
"Ina kika tafi da daddaren nan?" Safiyya ta rike kanta ta ce
"Kai na ke ciwo, da magrib na shigo naga kina sallah shine kawai na ɗan fita tsiyan magana" tana kallonta ta ce
"Kin ci abinci kuwa?" Kai ta girgiza mata, ta ce
"Toh tashi kije ki ɗiba" da sauri ta ce
"Zan ɗiba dama amma sai nayi sallah fah Mama" ta gyada mata kai ta mike ta ce
"Good night, Allah ya kara sauki" kai kawai gyada mata daga haka ta fita...
Umma ta ce
"Azrah tashi ki fita Kiga ko wane ne mana, amma ai hakan babu kyau zai zama kamar wulakanci ne" Azrah na ɓata rai ta miƙe, Zahra sai dariya take yi
Azrah ta fita, ta tsaya jikin gate ɗin su tana jiran wanda yazo wajen nata ya sauko yazo, ai kuwa bata wani daɗe ba sai gashi ya sauko, da mamaki ta juya da sauri tana kallon sa, ya karasa yana kallonta ya ce
"Barkan ki da warhaka, idan babu damuwa zamu iya samun wajen mu zauna? magana nake son muyi me muhimmanci" Azrah tana kallonsa cike da mamaki ta ce
"But... Are you really okay?" Sai kuma ta juya zata shiga gidansu, yayi saurin shan gabanta, rai bace da kuma ɗan sawa ta ce
"Saif ka fice min a hanya, kar na maka abin da zaka kasa yarda cewa Ni ne" yaja da baya yana kallon ta, ta wuce cikin gidan su rai ɓace...
Episode 80: Safiyya's cruelty
Kamar wanda aka jefo ta haka ta faɗa parlorn Umma ta ɗago tana kallonta ta ce
"Ke kuma fah? Sai kace wanda aka jefo ki" Zama tayi akan kujera tana kallon Umma ta ce
"Umma ji rainin hankali fah, Saif ne yazo. Ko Uwar me zan masa ohonsa" Zahra dake karatu ta ajiye littafin, ta maida attention ɗinta kan Azrah, Umma ta ce
"Kenan ma baki saya kinji mai zai ce ba kika shigo ko?" Ta ce
"Toh Ni nasan me zan masa ne, ai ko sauraron sa banyi ba na shigo a buna, balle ya buɗe baki ya fadi abinda zan iya zaginsa akai" Umma ta ce
"Innalillahi, yanzu shi yace miki wani abu zai faɗa miki?, idan kuma wani abune daga gidansa kuma fah, tunda ba sau daya kike nutsar da Samira ba, kawai baki saureresa ba ki wani shigo kina wani irin magana" Azrah ta ce
"Umma naji a jikina ba dangane da gidansa bane, kuma ko a idanunsa naga babu wani abu daya shafi wancan, kuma abin daya fi tsaya min a rai shine ɗazu nagan sa a kofar gidan Bappahn mu, uban me yaje yi? Da bai san nan bane sai nace kila ɓatan hanya ce, na washe sa fiye da komai wlh, ko ganinsa bana ma son yi, duk munafurcinsa kuma ya koma kansa" Umma dai bata ce komai ba, Zahra ta fara dariya ta ce
"Umma baki mamakin Ya Azrah ne yanzu? Wannan Nonchalant habit ɗin nata fa duk babu, ji yadda take magana" Umma dai bata ce komai ba, Azrah ta miƙe tana kallon Zahra ta ce
"It's not time that changes you, it's people" daga haka ta wuce ɗakin su dan bacci take ji, har ma tama manta da zuwa duba Bappah, nan da nan bacci ya kwashe ta
Bayan kwana biyu, yau ne last day ɗinta a seat ɗin Mr Alhassan saboda yau ne zasu dawo daga business trip, ba kaɗan ba ita da Oga Mahmoud suka tsaya a Companyn saboda ko MD baya zuwa, they dedicate their time ma kamfanin, aiki tukuru suke yi, yauma as usual tana office ɗin Oga Mahmoud suna cika wasu file da zasu yi join hand da wasu kamfanin sannan suna son suyi arranging lokutan da zasu saka musu dan ganawa, Sagir ne ya buɗe office ɗin ya shigo, daga Azrah har Oga Mahmoud suka ɗaga kai suka kalle sa kamar wani haɗin baki kuma suka sauke kansu kan aikin gaban su ba tare da ɗayan su yace kala ba, karasa wajensu yayi yaja kujera ya zaune ya ce
"Oga Mahmoud ya kokari kuma?" Miƙa masa hannu Oga Mahmoud yayi suka gaisa daga haka kuma ya mayar da hankalinsa ga Azrah suka cigaba da abin da suke yi, ita kuma ko da wasa bata kalli direction ɗinsa ba balle tama gaishe sa, ta ce
"Allah baki hakuri idan wani abun na miki tunda ko magana babu?" Azrah tayi kamar bata ji sa ba, ganin Oga Mahmoud ya ɗan kalleta yasa ta ce
"Ohh, I ni na ɗauka cewa mun gaisa tun tuni fah" ya ce
"A'a fah! Naga ma kwana biyu aiki na muku yawa ne ke da Yayan naki" kai kawai ta gƴaɗa masa sai kuma ta cigaba da aikinta, daga ita har shi babu wanda ya kara kula Sagir, dan kanshi ya mike ya fita, Oga Mahmoud ya ɗauki files ɗin ya ce
"Ta shi mu tafi ko?" Ta miƙe tana bin bayansa a haka suka isa first floor, kallon Sadeeq suka yi, Oga Mahmoud ya ce
"Ka kyauta da rashin zuwa MD, wato saboda Oga baya nan shine kake abin da kaga dama ko?" Sadeeq ya tsaya har suka karaso ya mika masa hannu suka gaisa sai kuma ya shige cikin office dinsa, suma shiga suka yi amma daga shi har Azrah babu wanda ya kalli juna
Suna cikin aiki kuwa sai ga Safiyya ta shigo, tunda taji labarin ya shigo yau shine ta taho office ɗinsa, wani bankin ciki ne ya turnike ta ga ganin yadda Azrah tayi shigarta, a ranta kuwa tana ayyana yau wasan zai fara, ta wuce gaban kujeran Sadeeq tana masa magana kallo ɗaya ya mata ya ce
"Kee! Fita" ta wani ɓata rai tana masa wani kallo, tunawa da Azrah na office ɗin karya mata wani wulakanci hakan yasa ta fita..
Saif na kallon Suhaila ya ce
"Ke ba zaki iya mata magana bane?" Ta ce
"Ya Saif, Ni fah babu ruwa na, yarinyar nan tana mugun kallon mutunci na, ana zaune kalau ba zan sa ta raina Ni ba, kayi hakuri kayi fighting ma kanka" Saif ya sauke ajiyar zuciya yana kallon wani direction sai kuma yana kallon ta ya ce
"But.. at least zaki ɗan iya mata da wasa kiga reaction ɗinta" wani dariyan da bata shirya bane tayi ta ce
"Babu wasa sakanin da ita saboda kallon Yaya take min, dan haka ba zan zubar da wannan girman da take bani ba" shiru yayi na wani lokaci yama rasa me zai ce ne, ita kuma kallonsa take cike da tausayinsa, is hardly ya faɗa abin dake damunsa unless abin yafi karfin sa ne, apparently abun na damunsa ne tunda har ya iya magana, ita dai kallonsa take
Mummy ta fito daga ɗakinta, ya sauke ajiyar zuciya sannan ya miƙe ya ce
"Mummy bari na tafi" ta ce
"Ka saya ka ci abinci, yau Fave dinka fah aka dafa" daga haka ta wuce kitchen...
Karfe ɗaya duk kusan dukka staffs ɗin suka fito daga office ɗinsu suka wuce masallaci, waɗanda ba musulmai bama sun wuce wajen cikin abinci, Safiyya ta bari sai data ji karan ana ruku'u na biyu ta cikin speaker hakan yasa tayi wani murmushi ta kwashe files ɗin kan table dinta ta fita zuwa office ɗin MD, bayan ta shiga ta wuce wajen fridge ta buɗe, wani Hollandia ta ɗauka, zata buɗe jakkanta kuma tunanin me tayi kuma sai kawai ta fita da shi zuwa nata office ɗin, toilet ta wuce ta ajiye akan wash hand basin, ta ciro wani allura a cikin jakkanta ta coka ta gefe yadda ba za'a gane ba ta juye abin dake ciki alluran sannan tayi shaking sai kuma ta ɗauka ta fito, sake daukan file tayi ta wuce office ɗin da sauri ganin ana shirin sallama ta buɗe fridge ɗin dake side ɗin Azrah ta saka a ciki ta kulle ta fito da sauri har tayi hanyar office dinta kuma sai ta canza hanya ta sauka kasa kawai, tana isa eatery ta shiga tana sauke numfashi dan har hannunta ɓari take, wani murmushi tayi sanin ko wani maaikaci dole zai nema abu ya saka ma cikinsa musamman Azrah da bata fiye cin abinci ba, har ta gama cin abinci bata ga Azrah ta shigo ba hakan ba karamin daɗi ya mata ba, miƙe wa tayi ta nufi sama kamar zata shiga office ɗin kuma sai ta fasa ta wuce nata.
Azrah na zaune Oga Mahmoud ya shigo office ɗin, yana kallonta ya ce
"Miss kin kusa kuwa?" Kai ta girgiza masa ta ce
"A'a no, yanzu fah nayi rabi" ya ce
"Please ki samu ki gama yau, gobe muna da visitors kuma nasan definitely gobe Mr Alhassan zai iya shigowa" ta ce
"Kar ka damu sir, zan gama komai In Shaa Allah, ai Shiyasa na bar Office ɗinsa saboda sanitation da ake yi" kai kawai ya gƴaɗa mata sai kuma ya mayar da kallonsa ga Sadeeq ya ce
"Look! Sadeeq nikam babu abin da zance maka,but don't provoke your father, idan har yasan kalar rashin maida hankali da kake yi lokacin da baya nan ba zaiji daɗi ba, try all your possible best ka saka komai inda yake" ya ce
"It's Okay" daga haka shikam ya jiyo ya fita...
Miss Safiyya ta leko office ɗin tana murmushi ta isa gaban Sadeeq amma tana satan kallon Azrah ta ce
"Sir, akwai wani new company ne a Lagos da suka buɗe naga ana tallah a Instagram nace why not mu musu introducing kan mu" yayi banza da ita kamar ya bawa iska ajiyarta, Azrah tayi wani murmushi ita bata taɓa kallon mutun kalan Safiyya ba, kamar mayya haka sai tazo office ɗin,
Safiyya ta ce
"Ina ga yau dole ma na tsaya a Company na karasa duk wasu abubuwa na tunda gobe Oga Head na dawowa, alternative kawai zan nema ko wani abu na saka a ciki na i think zai fiye min" still bai tanka ta ba, alamar yasan da mutun a wajen ma baiyi ba, sai ma aikin system dinsa da yake yi, Safiyya ta mike ta fita daga office ɗin
Sadeeq ganin hamman da yake yi ne yasa ya miƙe ya buɗe fridge ɗin gefensa zai dauki abu mai sanyi dan ya hana sa bacci amma yaga babu wani drinks, dan neman magana ya wuce wajen na Azrah ya buɗe, itama niyyar ta ta miƙe ta ɗauki Hollandia da ɗazu ta gani dan ya kara sanyi, kawai gani tayi Sadeeq ya ɗauka ya wuce wajen zamansa, a hankali ya buɗe ya zuba a cup, kusan rabin cup ɗin ya shanye, can da yake cikin aiki ya saka zuba wani ya sake shanyewa, Azrah ta sauka kasa ta siya Hollandia ta sake dawowa Sama, ta buɗe kenan tana fara sha sai ga Safiyya ta shigo da wani file ta wuce gabanta ta ajiye ta ce
"Miss Azrah, wannan ba naki bane? A can office ɗin na gani" tana maganar ne duk hankalin ta akan Hollandia gaban Azrah, Azrah ta ɗauka ta sake sha, wani farin ciki ne ya lulluɓe Safiyya ganin yadda take kwankwaɗa, Azrah ta karɓa ta ce
"Na Oga Mahmoud ne" Safiyya ta ce
"Ohh! Bari na kai masa" ko lura da Hollandia'n gaban Sadeeq bata yi ba, ta fita ranta fess
Sadeeq ya jingina da kujeran da yake kai jin wani abu da lokaci guda ya saukar masa a jiki, ɗakin ma kamar ya fara juya masa haka yake gani, mamaki ya fara toh dama bashi da lafiya ne bai sani ba?
Wajajen karfe 4:00pm wajen yayi sitt, saboda an tashi, Azrah ta miƙe akan tana son tayi Sallah, ta wuce ta bayan kujeran Sadeeq wanda idonsa a lumshe ta dauki praying mat, buɗe ido yayi lokaci guda jinta a bayansa haɗa ido suka yi sai da gabanta ya faɗi ganin yadda idonsa ya zama, a haka ta raɓa sa ta wuce, a ranta tana ayyana Shiyasa yake ta juye juye maybe bashi da lafiya ne, sai kuma taji bata kyauta ba da bata tambaye sa ba, a hankali ta furta ina ruwanki Azrah?
Har ta dawo ta ajiye Sallayan yana nan a wajen haka, har wajajen 4:30 tana aiki, ganin zata iya dare ta miƙe ta fara tattara wajen, har ta buɗe kofa zata fita sai kuma ta tuna Alkhairin daya taɓa mata na cire ta a zargi at least ya taɓa taimaka mata, karasa wajen kujera tayi ta ce
"Sir, lafiya kuwa?" Buɗe lumsansun idanunsa yayi, kawai gani tayi ya jawo ta kansa, a rikece zata miƙe tana
"Are you okay?" Sake jawota yayi suka zube a kasa, fige veil ɗin jikinta yayi, ta fara ture sa ta ce "Amma shayeshaye ka fara ko?" Ganin ya zame mata ɗan kwali yasa ta wanke sa da mari tana kokarin ƙwatan kanta amma inaaa ba zata iya haɗa karfinta da Sadeeq ba, kururuwa ta fara masa ganin abin daya fara mata, nan da nan ta sake rikice masa, ihuuu ta fara yi da dukkanin karfinta hawaye na zuba a idanunta, ganin zata ja masa mutane ya sanya yayi saurin rufe mata baki da bakinsa,
"Innalillahi wa'inna ilahi raji'un! Sadeeq Are You Mad!!!!???" Inaa Sadeeq bai san ana yi ba, ita kuma sai kururuwan neman taimako take yi tana bubbuga desk din wajen saboda bakinsa daya rufe mata nata, tana samu ta cire nata bakin ta kwala wani ihuuu tana Azo a taimake ta
Yadda ya zama frozen ne sai kuma ya haɗa duk karfinsa ya karasa wajen ya janyo Sadeeq ya wanke sa da lafiyayyayun maruka zafafa, sai sannan Sadeeq ya fara dawo sense dinsa,
Azrah kuma ta fashe da kukan bakin ciki ta dafe kanta tana sake sabon zunduma kuka
Ya juya zai fita saboda bai ma san me zai ce ko yayi ba, he is so much disappointed, Azrah tayi saurin shan gabansa ta durkusa kanta a kasa tana me sake fashewa da kuka kamar zata shiɗe dakyar ta ce
"Believe me sir, Ni bada ra..." Kasawa tayi ta sake fashewa da kukan, rasa me zai yi kawai ya raɓa ta gefenta ya wuce
#jiddatulkhayr writes
08110615256
Episode 81: A silent Nikah
Azarh harta isa gida bata sani ba, ga idanunta daya yi mugun jaa, tayi parking kofar gidan ta kifa kanta kan steering tana cigaba da kukanta, sai data yi mai isarta sannan ta share hawayenta, buɗe handbag ɗinta tayi ta fito da powder ta shafa a fuskar nata saboda jaa daya yi abun ka da farar fata, ta mayar da jakkan inda ta ɗauka, horn ta danna, sai kuma da sauri ta juya kallonta zuwa kofar gidan su dan tun farkon shigowanta layin ta kalli mota guda biyu a kofar gidan Bappah'n su, tsurawa motar Idanu tayi kamar mai son ganu wani abu, ganin an buɗe mata gate ɗin ne yasa kawai mayar da kanta kan abin gabanta, bayan tayi parking sai data sake ɗaukan wasu lokuta sannan ta sauka, tana shiga parlor taga babu kowa, ɗakinsu zata shiga sai ga Umma ta fito a kitchen, da sauri ta ɗauke kanta tana kallon wani wajen ta ce
"Umma ina wuni" Umma ta ce
"Lafiya, ya aiki" ta ce
"Alhamdulillah" Umma ta kura mata ido ganin taki kallonta, sai kuma ta ce
"Umma bari na ɗan huta kaina ke ciwo" Umma ta ce
"Toh ki sha magani, Allah ya sauwake" ta gyaɗa kai daga haka ta shige ɗakin, Umma tayi shiru na wasu seconds tana kallon kofar ɗakin sai kuma ta juya ta koma kitchen abunta
Ko da Zahra ta dawo daga makaranta Azrah tayi pretending tana bacci, bayan kukan data sha ɗazu kafin zuwan nata, Zahra nata haɗa kayanta da zata koma hostel da su, jin ana kiran Magrib yasa Zahra ta isa bakin gadon tana kiran sunanta a hankali ta ce
"Yaya ki tashi Magrib fah yayi" miƙe wa tayi ta wuce toilet bata bari sun haɗa ido da Zahra ba, Zahra kam ko noticing bata yi ba ganin daga bacci ta tashi a zatonta
Sadeeq tun bayan daya dawo sense ɗinsa yaji duniyarma gaba ɗaya ya fice masa a rai, yayi regretting fara aikinsa ma a wannan wajen, dakyar ya samu ya lallaɓa ya koma gida, nan ma ko shiga side ɗinsu baiyi ba, ɗakinsa ya wuce, nan da nan zazzaɓi ya sauka masa, har ya ɗauki waya zai kira Sagir sai kuma ya hakura, bai taɓa abu yayi regretting ko ya zubar da hawaye ba sai akan wannan abun.
Umma na kallon Zahra ta ce
"Amma Ni kam Azrah yau lafiya kuwa? Naga damuwa tattare da ita ko zaki mata magana kiji?" Zahra ta ce
"Ni fah da farko Umma i thought ko baccin daf Magrib ne ya canza mata mood Amma naga tana avoiding komai ma, magana ma bata son yi min balle kuma ta kalle Ni" Umma ta yi shiru ita dai tasan 'yarta kuma tasan ba karamin abu ke damunta ba, a hankali ta ce
"Toh ki koma wajenta Maybe ta iya faɗa miki tunda taki fitowa nan ko abinci ma taki ci, idan hakan bai yi working out ba zan tiseyeta da kaina sai ta faɗa min" daga haka Zahra ta miƙe ta wuce ɗakin nasu, tana shiga taga Azrah tayi rub da ciki, ta karasa wajenta tana kallon ta, taɓa ta tayi ta ce
"Yaya mene?" Ga mamakinta kawai gani tayi Azrah ta fashe da kuka, nan da nan hankalin Zahra ya tashi, ta miƙe zata je kiran Umma da sauri Azrah ta rikota ta ce
"No please, Zahra kar kimin haka, kar ki ɗagawa Umma hankali" Zahra ta rungumeta ta ce
"Toh menene? Meyake damunki da har ba zaki iya faɗa ma Umma ba" Azrah ta share hawayenta tana kallon Zahra, sai wayanta ya fara ringing ɗaga wa tayi taga Samira ce, kallon agogo tayi sai kuma tayi receiving tana daurewa dan kar ta fahimci wani abu, tayi sallama, amma maimakon ta amsa mata sai kawai ta ji ta ce
"Azrah!" Daga nan kuma ta fashe da kuka, ai Azrah tuni ta manta da nata damuwar ta ce
"Samira lafiya? Meya faru, ki daina kukan nan please" dakyar Samira ta saita kanta amma still a muryan kuka ta ce
"Azrah kiji wai Saif yana neman aure? Ni Saif zai yi wa haka? Yaushe yaushe muka yi aure har zai fara maganar aure, Nadrah fah ko 2yrs bata kai ba, ina laifin after 10 yrs" tana kaiwa nan ta sake fashewa da kuka, Azrah taji gabanta na duka uku uku ta ce
"Au.. aure.. kuma Samira? Shi ya faɗa miki yana neman auren?" Samira ta ce
"Kuma dan wulakanci bai faɗa min ba, Matar abokinsa ne tace min aure yake nema" da sauri Azrah ta katse ta tace
"Kuma wacece wanda yake neman?" Samira ta ce
"Ni ina zan sani? Ɗazu take faɗa mini" Azrah ta ce
"Kin faɗa masa cewa kin sani ne?" Ta ce
"U'uhm" Azrah ta ce
"Good, kar ki gwada masa and I'm assure you auren nan ba zai yiwu ba, haka nake ji a jikina, i just want you to calm down, zan taya ki da addu'a kuma" ta ce
"Har naji daɗin dana yi magana da ke, thank you dear" a haka Azrah ta kwantar mata da hankali kafin su yi sallama
Zahra na kallonta ta ce
"Kinga yadda ake yi idan mutum na damuwa ko? Dole zaka samu za'a yi comforting dinka" Azrah ta yi murmushi ta ce
"Zahra yanzu ba zan iya magana akai ba, but tomorrow In Shaa Allah" Zahra ta dinga kallonta sai kuma ta ce
"Allah ya kaimu, bana son takura miki ne, Umma ma ta shiga damuwa" Azrah ta sauke ido tana sake jin damuwar na dawo mata sabo fil.
Kallon Sagir take ta ce
"Ai Ni rabo na da Sadeeq tun safe, ko daya dawo bai shigo nan ba, motar sa kawai aka ce min an gani, nan na fahimci ya dawo kenan" miƙewa Sagir yayi ya ce
"Toh shikenan, bari na wuce kawai" ta ce
"A'a ban gane ba, ba zaka shiga bane?" Ya ce
"Toh ai Ma'am yaki buɗe kofar ɗakin nasan kuma definitely yana ciki" tayi shiru sai kuma ta ce
"Toh Allah ya tashe mu lafiya" ya amsa da "Amin" sannan yayi gaba
Tana zaune akan kujerar kawai ta miƙe tana kwalawa mai aikinta kira, da sauri ta fito tana
"Gani Hajiya" ta ce
"Sadeeq yaci abinci kuwa?" Ta ce
"A'a ko nan ai bai shigo ba, ina jin yana ɗakinsa ne" kai kawai ta gƴaɗa mata daga haka ta wuce part ɗinsa, knocking tayi ta ji shiru, ta daɗe tana knocking amma shiru a hankali ta ce
"Sadeeq zo ka buɗe min bana son wannan shashancin" nan ma bata ga alamar zai buɗe ba, ta ce
"Sadeeq nace ka zo ka buɗe min kafin ranka ya ɓaci ko? Ko na kira mahaifinka ne" motsin da ta ji, after some seconds taji yana buɗe wa, kallonsa ta tsaya yi, sai taga ya bar jikin kofar ya koma cikin dakin, shiga tayi, shi kuma tuni harya kwanta, da sauri ta kai hannu ta taɓa sa ganin yanayin sa, sai kuma ta ja baya da sauri ta ce
"Dama baka da lafiya ne Sadeeq shine zaka yi wani shiru kamar yaro karami" ganin yadda har fuskansa tayi ja, sai kuma da sauri tayi unlocking wayanta, searching numbern Sagir tayi ta yi dialing yana ɗauka ta ce
"Sagir idan baka yi nisa ba kazo ka kai ɗan uwanka asibiti" daga ɗayan ɓangaren ya ce
"SubhanAllah ba shi da lafiya kenan! Gani zuwa toh" ita dai tana ta zaune akan sa har Sagir ya dawo, Sadeeq dakyar ya ce
"Ni fah I'm fine Mami, babu wani abu dake damu na, ya tafi kawai" wani kallo ta watsa masa ta ce
"Sagir i know you, Dan Allah kuje a duba sa, idan ta shine sai dai yayi ta zama a haka, gashi our family doctor baya nan" Sagir yana masa wani kallo ya ce
"Kalli yadda ka ka koma shine har kana da bakin gardama" shi dai Sadeeq yaki kulasa..
Ana tafiya da Sadeeq asibiti kuwa suka yi admitting ɗinsa, tun tafiyan su Mami ta kasa samun nutsuwa...
Washegari Azrah ta farka da wani zazzaɓi zazzaɓi na rashin baccin da bata samu ba, sai juye juye take ta yi sai kusan asuba kuma ya ɗauke ta, amma she's pretending cewa she's more than okay, Umma dai duk tana kula da yanayinta, bayan Zahra ta kawo kayan karyan wansu suna cikin taking ne Umma ta ce
"Amma yau zaki tafi latti naga har yanzu baki shirya ba ko wanka baki yi ba fah" murmushi ta yi, ta ce
"Ba zan tafi ba Umma" Umma taji hankalin ta bai kwanta ba ta ce
"Kin samu matsala ne kika gagara faɗa mana Azrah?" Ta ce
"Matsala kuma Umma? A'a kawai yau ina Hutu ne, ina so na huta" Umma tayi shiru ba wai dan ta yarda da Azrahn ba sai kuma ta kalli Zahra da har ta miƙe ta ce
"Yau zaki koma ko sai gobe?" Ta ce
"Umma na gama haɗa kayan da zan yi using a week din nan dana gaba, text ɗin nan ina so na ci sa ne bana wasa ba" Umma ta ce
"Toh Allah ya baki sa'a, in shaa Allah ba zaki samu matsala ba" Zahra ta rungume Umma ta ce
"Nagode Ummana" wayan Azrah dake ringing yasa ta ɗaga ganin Dada ya sa ta ce
"Umma Dada ne, Umma ta ce
"Toh ɗaga mana" ɗaga wa tayi ta kai kunne tare da sallama, daga ɗayan bangaren Dada ta ce
"Azrah na sako muku aika a motar Katsina idan kun karbi aikan zan muku bayanin komai" Azrah ta mata sallama da gaisu, bayan sun gaisa Dada ta ce
"Ai yanzu komai zai zo karshe, idan na gama wani abu da nake yi gobe ko jibi In Shaa Allah ina shigowa" Azrah ta ce
"Allah kai mu, yanzu jikin naki da sauki ne?" Dada ta ce
"Sauki kai, sauki sosai ma kuwa nake faɗa miki, ashe duk an ɗaure min kune akan ba zaku auru ba, kai labari dai sai na shigo, ina so ku fara amfani da maganin ne daga yanzu" Umma ta karɓa suka gaisa da Dada sannan suka yi sallama..
Zahra ta ce
"Chap, ai na fasa koma wa school yau, bari naje nayi lectures na dawo gida" Umma ta ce
"Ke kika sani, ba wanda zai sa miki baki balle kice mu muka canza miki ra'ayi"...
Bayan su Azrah sun karbo Maganin har Dada ta musu bayanin yadda zasu yi amfani da shi, Zahra data dawo gida tun ƙarfe biyu duk suna zaune suna mamakin maganganun da Dada ta faɗa a hakan ma tace wasu maganar sai ta shigo
Suna zaune aka dinga knocking gate ɗinsu, Zahra ta miƙe ta fita dubo wanene, bayan ta buɗe taga wani yaro ta ce
"Kai lafiya?" Ya ce
Ya nuna mata wani mota dake bayansa ya ce
"Wancan mutumin ne yake son yayi miki magana" Zahra ta kalle wajen motar sai kuma tace
"Muje" daga haka ta nufi wajen motar, ɗan babban mutum ta gani a ciki wanda a ƙalla zai yi mate ɗin Bappahnsu, ta ɗan ritsina ta ga gaishe sa, da fara'a ya amsa mata ya ce
"Please idan babu damuwa ina so zan shigo, amma kafin nan Umman ku tana nan?" Murmushi tayi ganin mutumin very calm ta ce
"Eh tana ciki, ko na mata magana ne" kai ya gyaɗa ya ce
"Yes if possible please, ina so zamu yi wata magana" ta ce
"Toh bari na mata magana" daga haka ta koma gida tana shiga taga Umma na kallon Sunnah tv Azrah har ta shige ciki, ta ce
"Umma wani ne wai yake son zai yi magana da ke idan babu damuwa yana so a masa iso zuwa ciki" Umma tayi ta kallonta sai kuma ta ce
"Waye shi?" Zahra ta ce
"A'a ban san sa ba, kawai dai abin daya yi requesting kenan" Umma ta miƙe ta ce
"Okay, ki ce ya shigo, bari na dauko hijab ɗina" Zahra ta fita Umma kuma ta wuce ɗakinta dauko mayafi...
Bayan ya shigo suka gaisa da Umma, Azrah dake cikin ɗaki hankalin ta yayi mugun tashi bayan Zahra ta sanar mata ai wani ne yazo wajen Umma zai yi magana da ita, zuciyar sai tsinkewa yake yi, ita da Zahra suka saka kunne suna son jin me ya kawo sa, Azrah na son lekawa taga fuskarsa amma babu dama
Yana kallon Umma calmly ya ce
"Ashe kin dawo nan da 'yaran namu" Umma ta katse sa ta ce
"Amma ban gane wanene bane" yayi murmushi ya ce
"Eh ba lallai gaskiya ki gane Ni ba, amma ina ga tun sanda kuke can GRA na san ki lokacin yaranki suna kanana" Umma dai tayi shiru tana kallon wani wajen
Ya gyara zama ya ce
"Hajiya, I think we're all matured enough, babu wasu kwana kwana saboda mu ba yara bane, amma gaskiya abin dake tafe dani ban san yadda zaki karɓe sa ba" Umma dai bata ce komai ba, ya ce
"Hajiya yadda na yaba da yanayin halayyar ki, tun sanda naji aurenki ya mutu nake son na tunkare ki amma ban san yadda zaki ɗauka ba, sai yanzu kawai nace barin dai daure nazo" shiru yayi yana kallon yanayin Umma da baya gane ko menene ba, ya ɗaura
"Hajiya idan babu damuwa ina so ki bani damar na aureki, na miki alkawarin rike miki 'ya'yanki duk da already sunma girma" Umma bata san sanda ta juya tana kallonsa cikin ido ba, Zahra da Azrah suka juya suna kallon juna
Umma tayi wani murmushi ta ce
"Gaskiya A'a, babu wani tsarin aure a rayuwata kuma, 'ya'yana kuma zan cigaba da rike su, yanzu kawai sai na ce zan iya aure hakan yama yi making sense ne? Just imagine babba da Ni" wani dariya yayi ya ce
"Hajiya kar ki manta ke ba wata shekara ce da ke ba, baki wani tsufa da har zaki ce hakan ba, nawa mate ɗinki wanda a yanzu 'ya'yansu kanana ne, sai dai Maybe idan saboda yaranki ne baki son kara auren" Umma tayi shiru tunawa da sanda tayi aure she's just 18 da kuma kalubalen data fuskanta tun daga sannan da kuma kalar kalubalen data samu tun daga gida, sai kuma a hankali kamar mai shirin kuka ta ce
"Kayi hakuri.. bani da wannan burin a tsarin rayuwata na yanzu" ya ce
"Kiyi hakuri zan baki lokaci kiyi tunani, dan Allah kar kice A'a, ki tuna idan yaranki mata suka yi aure haka zaki cigaba da zama ke kaɗai anan?" Umma taki kulasa ya miƙe ya ce
"Na barki lafiya" daga haka ya nufi kofar ya fita, Umma ta kasa cewa wani abu, Zahra da Azrah suka fito, Zahra ta fashe da dariya ta ce
"Umma kice kinyi kasuwa" wani kallo Umma ta wurga mata ta ce
"Dama label kika yi?" Babu wasa a tone ɗin Umma ko kaɗan, Azrah ta ce
"Allah ya kiyaye Umma tayi aure, idan Bappah ya dawo kuma fah?" Zahra ta ce
"Allah ya kiyaye Umma ta koma gidan Bappah, ga talauci ga kuma shegen wulakanci, gwara ta tafi inda zata huta, ke baki ga shegiyar dalleliyar motar sa bane" Umma ta ɓata rai wanda sai da suka sha jinin jikinsu ta ce
"Bani son kallon ku, ku ɓace min" duk suka mike sum sum suka koma ɗakinsu
"Al fatiha" duk suka shafa fatiha, wani ya ce
"Alhamdulillah Allah basu zaman lafiya da zuriya ɗayyiba" Bappah dai ya kasa cewa komai, tunanin ya Azrah zata ji cewa ya aura mata aure da wani? Idan kuma bata son sa kuma fah? Wannan wani irin ma ɗaura aure ne kamar wani almara....