CHAPTER 29: Between Two Worlds
Beyond The Veil Part 1 Complete Novel · about 11 min read
Yau ta kasance Monday, kuma kamar yadda aka saba, ta taso da wani irin nauyin gajiya da ya mamaye jikinta, A hankali ta buɗe idanunta waɗanda har yanzu suke cike da kasala, ta saka hannu ta jawo alarm ɗin dake bedside wanda yana ta bugawa ta kashe shi, Idonta na lumshe, ta sake mayar da duvet ɗin ta rufe fuskar nata
A gefe kuwa, Samira na kan dadduma, tana karatun Qur'ani da murmushi a fuskarta ta ce
"This is the disadvantage of always stressing yourself Azrah, Gashi yanzu baccin ma bai ishe ki ba, ko tashi kin kasa kuma Kinsan yau Monday ne till down kuke yi"
Azrah ta buɗe idanunta a hankali, ta fara karanta addu'ar tashi daga bacci, ta miƙe zaune tana zare duvet daga jikinta, sannan ta ɗan harare Samira da murmushi a fuskarta wanda ke cike da bacci da kuma gajiya, a calendar ɗinta na yau, akwai presentation da za ta gabatar a class ɗin Introduction to Business Strategy Ko da yake ta shirya, amma damuwa da tsoron yi kuskure na damunta sosai, ɗan tsaki tayi ta ce
"Why do Mondays always come with so much stress? Gosh!"
Sai ta dafe kanta, ta tashi, ta saka dakalmin ɗaki sannan ta nufi toilet
Samira ta fara dariya bayan ta rufe Qur'an ɗin gabanta ta ce
"Ke kaɗai na taɓa jin kin ce Monday comes with stress, toh ba dole ba, kin wahalar da kanki during weekend at least ki huta tunda weekend ne, amma kina ta karatu kamar 'yar Mango Park"
Ta ɗan girgiza kai
"Hmm, ke kika ga zaki iya, Ni kam ko exam ne ba zan iya wannan wahalar ba"
Bayan Azrah ta fito daga toilet wajan da dadduman yake ta nufa sannan ta tada sallah, bayan ta idar ta fara azkar da sauri ganin zata iya makkara yau, bayan ta gama ta miƙe ta ciro kayan da zata saka a ajiye akan gado, ita da Samira suka haɗu suka yi breakfast tare, suna ganawa Azrah ta miƙe saboda Samira ta fara saving ɗin su, wayar Azrah ta fara ringing, ganin me kiranta yasa ta ɗan kalli Samira kafin ta ɗaga ta kai kunne ta ce da murmushi
"Morning, gani nan fitowa, pls"
Samira ta miƙa mata abincin data saka mata a plate, karɓa tayi ta zauna bakin gado ta fara ci a hankali
Ta tashi ta saka high-waist skirt blue mai kyau da rigarta mai kyau royal blue, ta yi rolling veil, ta rataya tote bag ɗinta, sannan ta saka sunglasses, ta saka wani blue snicker, Kafin ta nufi kofa sai kuma ta juya ta kalli Samira da murmushi ta ce
"Hey girl, bye! Sai mun haɗu anjima"
Samira da tuntuni ta zubawa Azrah ido sai kuma tayi murmushi ta ce
"Chai! Wannan kyau kam sai kin saka Khalil ya rasa nutsuwarsa anyway sai kin dawo"
Azrah ta share maganar kamar bata ma fahimci me take nufi ba, ta buɗe kofar ta fita abinta, tun data fito daga hostel ɗin Khalil ya zuba mata ido, bayan ta isa inda yake sannan ya dawo da numfashin sa yana mata murmushi, bayan sun gaisa cikin fara'a, karɓan jakkanta yayi ya rike daga haka suka fara tafiya a hankali suna dan taɓa hira har ya raka ta kofar lecture hall ɗinsu, colleagues ɗinta suna ta shiga ta tsaya tana kallon sa, murmushi ya mata ya ce
"Best of luck on your presentation" Kai ta gyaɗa masa sannan ya miƙa mata Jakkanta ya juya,
Da ta shiga class ɗin, students sun cika a hall ɗin, Malamin su na business Dr. Anand har ya fara kiran sunaye students suna gabatar da na su, da sunan ta ya zo, Azrah ta tashi da natsuwa amma bakinta bai bar addu'a ba, ta tafi gaban class, duk da fargaba, ta gabatar da presentation ɗinta cikin kwazo, tana amfani da PowerPoint sannan da nutsuwa kamar wata gogaggen ce
Bayan ta gama, dukan students suka tafa mata Dr. Anand ya ce, "Excellent, Miss Azrah. Your strategy is not only brilliant but realistic" tayi murmushi a ranta tana cewa ai dole tasan komai game da business dan da hakan ta taso, siyasa kullum entrepreneurship tafi kowa ganewa sannan tafi kowa yawan tambaya..
Wajen la'asar bayan ta wuce masallaci tayi sallah tayi evening azkar ta nufi library lawn, inda take samun natsuwa, ta zauna tana karatu, tayi wajan 1 hour tana karatu sai ga Khalil ya zo kamar yadda ya saba, ya zauna kusa da ita ba tare da yayi mata magana ba dan yaga kamar she's reading ne, ajiye hot coffee da snacks ɗin hannunsa yayi a kan table ɗin gabanta
"Take a break plsAzrah, you'll burn yourself out one day"
Tayi murmushin da bata shirya ba ta ce
"I don't have time to waste, every minute counts"
Wani kallo ya mata ya ce "At least let your body breathe" ya kare maganar yana kai mata coffee bakin ta, wani kallo ta masa sai kuma ta girgiza kai ta karɓi cup ɗin a hannusa
Suna zaune a hankali tana sipping coffee da snacks ɗin gabanta, sai ga wata ƴar department ɗinsu 'yar Ghana ce tazo wucewa turuss ta tsaya tana kallon su da mamaki ta ce
"A'a! Wait Azrah... Na taɓa jin kinyi Hausa, and ina yawan kallon ki da wannan, Are You Egyptian?"
Azrah tayi murmushi ta ce
"No.. ni ƴar Nigeria ce" Yarinyar ta sake baki tana kallon Azrah da mamaki sai kuma Azrah ta katse mata tunaninta ta ce
"We're somehow related ne" yarinyar ta dinga kallon Azrah sai kuma ta ce
"Then, are you halfc.." bata karasa maganar ba wani Library attendence ya katse ta yace kar suyi breaking rules ɗin Library, daga haka ta wuce gaba..
Bayan sallar asuba, har sannan garin bai gama wase wa ba, Mama ta leƙo daga ɗakin ta dan tabbatar da cewa babu wanda ke tsakar gidan ko kuma wanda basu koma baccin asuba ba, Idonta duk a kumbure da kuma rashin bacci da bata samu tayi ba, ganin babu kowa babu wata motsi kuma ta sanya hijabi a kanta cikin hanzari ta fita, zuciyarta na bugawa da sauri-sauri kamar wanda za'a kama ta, bin layin nasu tayi da kallo ganin babu wani mutane yasa ta nufa bakin titi inda suka yi da Maman Asaben zasu haɗu
Bata ko kai minti uku ba sai ga itama ta karaso, kallo ɗaya zaka mata ka gane cewa itama hankalin ta ba a kwance yake ba. Bayan sun gaisuwa, Maman Asabe ta ce
"Nikam muyi mu bar nan saboda har sannan Baban Asabe bai gama yarda da tafiyar nan nawa ba" Mama ta gyaɗa mata kai ta tare musu abun hawa, suka hau adaidaitan suka nufi tasha ba tare da wata hira a tsakaninsu ba
Motar da suka samu ta nufi wani kauye, wanda ba kowa yasan kauyen ba, sannan ba wai ƙauye ne da mutane dayawa ke rayuwa a can ba, tafiya ce me nisa, da zafin rana da ƙurar kan hanya, amma zuciyar Mama cike take da bege da kuma fargaba. Bayan sun sauka, sai suka ci gaba da tafiya da ƙafa, tafiya mai nitsa suka yi, suka nufi wani lungu inda wani ɗan bukka ke zaune a kan dutse mai duhun gani
A nan ne bokan yake, wani tsoho ne wanda idanunsa jajir ga kuma wani manyan mark a fuskar nasa, yana tausa yatsun sa kamar yana jin abubuwan daga mutanen ɓoye kamar dai suna faɗa masa abin da ya kawo su Mama
Maman Asabe ce ta fara yi masa bayani, tana zayyana halin da Mama ke ciki da yadda al'amura suka sauya a gidan bayan a baya wajan shekaru sha 15 ba haka bane,
Tsohon ya saki wata dariya mai cike da ma'ana, sannan dariyar nasa ma abun tsoro ce ga jajayan hakuransa da ya bayyana ya ce
"Abin da za'a yi aiki akan ita Matar (Umma) ba ƙaramin aiki bane, amma akan mijin naku za'a iya dan akwai wata hanya, sai dai da wahala... sai ku shirya dan zaku kashe kuɗi"
Mama ta gyaɗa masa kai irin ta gamsu koma yaya ne, Kamar yadda yawanci irin waɗannan al'amura ke faruwa, ta Ciro kuɗi ta mika masa kuɗin duk da babu tabbacin nasara a maganar nasa
Wasu magani ya miƙa musu sannan ya faɗa musu yadda zasu yi komai da kuma yadda za'a juya tunanin Bappah
A haka suka fito, suka sauko daga kan dutsen, sun sake shan gajiyar tafiya kafin suka isa bakin titin, sun fi minti arba'in babu mota balle alamar shi, kamar ƙaddara na son su zauna su sake tunani akan abinda suka aikata..
Bappah dake tsaye kan Umma yana mata sannu, dan tun jiya haka ta gagara bacci, da alamar dai ciwonta ke son ta shi, A mugun fusace Dada ta ce
"Dama Muhammadu tsoran ita Uwani kake yi ne da har zata fita tun safe ba zata faɗa maka ba?" Bappah da ransa ya ɓaci ya ce
"Ai kina ganin yadda take wasu halayyar nata Dada, sau nawa zanyi magana amma ko da wasa bata ɗaukan maganata da muhimmanci" wani dogon tsaki Dada ta ja ta ce
"Kalli tun safe ace bata gidan, hakan yana nuni da cewa Yaranta rufa mata asiri suka yi ba'a gida ta kwana ba, yanzu Ni da tsufana zanyi girki ko kuma ita wannan dake kwance babu lafiya ce zata yi Fisabilillah" Bappah ya miƙe yana kallon Dada ya ce
"Bari na saka yara su nemo su Siyama sai su ɗaura abincin Ni kuma sai na kaita asibiti kafin ita Zahran ta dawo" Dada tayi saurin tsayar da shi ta ce
"A'a dakata, wa zai ci abincin su? Baka kallon kullum wari suke ne? Daga nayi magana suna wanka Shikenan suka ƙullace Ni, gani suke kamar bana son su bayan Ni kuma numfashina dauke Wa yake suna tunkaro Ni" Umma ta miƙe a hankali dana dafe da kanta ta ce
"Bari zan daura abincin Dada" Dada ta ce
"Rufamin asiri" daga haka kuma ta miƙe ta fita daga ɗakin ta nufa inda kitchen yake.
Kafin Yamma jikin Umma ya sake rikicewa wanda aka tafi asibiti da ita, Zahra sai kuka take yi, kuma har sannan babu labarin Mama dai...
Dakyar Khalil yasa Azrah ta mike zai kaita har kofar hostel ɗin, dan yaga har gyangƴaɗi ma ta fara amma tana ta forcing kanta wai one page zata kara shikenan, bayan ya kawota har kofar hostel kamar koda yaushe ya tsaya har ta shiga sannan ya juya ya bar kofar
Azrah ta shiga ɗakin nasu kamar wata ƴar maye sabar bacci, da kalli Samira na waya da wani saurayi, ko wanka ta gagara kawai ta sanya sleepwear ɗinta ta hau kan gado, bayan Samira ta gama wayar ta ce
"Azrah you and Khalil are becoming too close o, just saying..." Azrah da bacci harya fara fizganta ta ce
"He's just a friend Samira"
Wani dariya Samira ta yi ta ce "Hmm, okay o, time will tell"
Azrah tayi wani murmushi duk da itama bata san sanda suka shaku har haka ba, duk lokacin da ya yi mata magana, ta kanji wata sanyi a zuciyarta, Amma ta kan jaa kanta gefe ta ce "I'm not here for love, I'm here for purpose"...
Washe gari tunda ta tashi taji tana son tayi waya da gida, dan jiya tayi ta kiran Bappah amma baya ɗaga wa, dialing numbern nasa tayi da damuwa a fuskarta wanda itama kanta bata san damuwar menene ba, luckily sai Zahra ta ɗaga bayan sun gaisa Azrah taji damuwa sosai a murya Zahra ta ce
"Zahra tell me menene ke faruwa pls? Zahra tayi shiru sai kuma ta ce
"Ya Azrah jikin Umma ya ɗan tashi ne Jiya, amma yanzu muna asibiti da sauki" Zahrah ta kare maganar tana cikin kwantar da hankali
Azrah bata san sanda ta miƙe ba hawaye har sun fara wanke mata fuska, muryanta har shakewa yake ta ce
"Umma ba lafiya kuma Zahra? Innalillahi wa'inna ilahi raji'un, waye a kanta? Idan aka nema kuɗin magani me yawa kuma fah? wa zai yi jinyarta yanzu, wayyo ni anya banso kai na da yawa ba" tana kai aya ta fashe da kuka, duk yadda Zahra taso bata baki ganin yadda hankalin ta ya tashi amma ko kaɗan Azrah bata saurareta ba
Daga karshe ma ta kashe wayar tana jin kamar tayi flying zuwa gida, kawai ta zube a wajan ta fashe da matsanancin kuka, haka ta wuni a ɗaki ko lectures ɗinma taki zuwa
Da yamma Khalil ya lura da damuwarta ya ce
"You look worried Azrah, Everything okay?" Azrah dake kallon wani waje tun tuni ta sauke idon ta kasa ta ce
"My mom's sick, She's everything to me, Ji nake ba zasu iya jinyarta ba kamar Ni" Khalil dake kallon ta cike da tausayinta ya ce
"Wish her quick shifa, then I'll pray for her too, And if you ever need anything... even silence, I'll be here"
Haka kawai taji maganar sa yayi tasiri a zuciyarta duk da ba wai yace mata Umman ta samu sauki bane amma haka kawai ta samu wani peace
Ta fahimci cewa tana rayuwa tsakanin duniyoyi biyu tsakanin burinta da kuma abubuwan da zuciyarta ke kokarin shigowa da su
Da daddare, tana zaune bayan kammala karatu, zata kwanta tana ta trying numbern Bappah amma baya shiga, Samira ta ce
"Ya jikin Umman?" Azrah ta ce
"Har sannan ban samu nayi magana da su ba, ina ta kira baya shiga" Samira ta ce
"In shaa Allah zata samu sauki kawai ki kwantar da hankalinki Azrah" Azrah ta gƴaɗa mata kai kawai ..
This book costs 500. Make the payment to Hauwa Jibrin, Wema Bank account 0421255553, and send proof of payment to 08110615256.