CHAPTER 30: Silent Bonds
Beyond The Veil Part 1 Complete Novel · about 11 min read
Hankalin su Umma yayi mummunan tashi ganin har gari ya fara duhu kuma babu wani abun hawa a ƙauyen sai dai manyan motoci dake zuwa suna wuce wa, Mama Asabe ji take kamar zata fashe da kuka ta ce
"Ohh yau naga ta kai na, Allah ka turo mana mafita" Mama tayi wani dogon humming ta ce
"Hmmmm, ai gwara ke kin tambaya kawai kince yau zaki koma ne, kina da bakin cewa baki samu mota bane amma Ni fah? Babu wanda yasan da na fito" Maman Asabe dai babu bakin magana tayi shiru, har sannan kuma suna takawa ko zasu samu mota, can Mama ta tuna da Dada ai bata san sanda ta ja burki ta tsaya ba ta ce
"Nashiga uku" da mamaki Maman Asabe ta juya tana kallonta ta ce
"Lafiya dai?" Mama ta girgiza kai ta ce
"Ina lafiya kuwa? Ai na manta cewa Kakansu yaran nan tana nan, ai Shikenan yau kuma sai abinda ta mance ne ba zata ce a kai na ba" Maman Asabe tayi wani dariya ta ce
"Eh lallai Kema Maman Siyama akwai ki da kasada, ina ma laifin kiyi karya, chap zaki koma ki same ta kuwa" Mama kan idan hankalin ta yayi dubu toh ya tashi dan saf tama gama manta da Dada.
Dada dake tsaye a tsakar gidan tana kallonsu Siyama da ko wacce Fuskarta babu yabo babu fallasa suna kallon Dada da har sun gaji da jarabarta, ta ce
"Ba magana nake muku ba? Ace har dare yayi babu Uwarku balle labarin ta ko dai ɓata tayi ne bamu da labari?" Siyama ta ce
"Toh muma ina zamu sani ne" a fusace Dada ta ce
"Uwarku 'yan iska kawai, ace kun kwana ɗaki ɗaya da safe baku ganta ba amma kuka tafi tallarku kamar yadda kuka saba shine zaku wani ce min baku san inda take ba? Wa zaku mayar yarinya da zaku wani ce baku san inda take ba" Habibah ta miƙe ta ce
"Nikam ban sani ba Dada, ga Ya Siyama ki tambaye" Dada ta juya ta wuce ɗaki a fusace tana mita ita kaɗai
'idan taga dama karta dawo gidan kawai'..
Bappah dake zaune bakin kofar ɗakin da Umma take ciki shi da Zahra duk hankalin su a tashe suna addu'ar Allah bata sauki sai ga likitan dake dubata ya fito, Bappah ya miƙe yana kallonsa, Dr. Ya ce
"Alhamdulillah jikin da sauki ba yadda ake expecting bane, zuwa safe za'a sallame ku kafin ta gama shan drip da zata sha" Bappah ya sauke ajiyar zuciya ya ce
"Toh Alhamdulillah! Nagode Dr." Zahra ma murmushi ta fara tana hamdalah, likitan yayi gaba Bappah ya koma ya zauna..
*****
Mama de dakyar suka samu wani mashin suka hau kai su biyu ya fitar da su a wannan ƙauyen zuwa wani ƙauye da yafi wanda suka fito mutane, har tasha Mai mashin ɗin ya kai su sannan suka sauka, basa kuɗinsa suka yi suna godiya, ya tada mashin ɗinsa yayi gaba, Mama suka shiga cikin tashan suna rarraba ido, wasu masu lodin Lagos suka ce
"Ina zuwa? Laigas ce?" Mama ta girgiza kai da sauri ta ce
"Cikin Katsina Malam" sake baki yayi yana kallonsu ya ce
"Katsina kuma a daren nan? Ai dole sai da safe dan babu wasu fasinja, garuruwa masu nisa ne ake lodi da dare" Mama suka kalli juna sai Maman Asabe ta ce
"Malam toh ka taimaka a kaimu mana tunda gamu mu biyu kuma muna son komawa Katsinan ne yau wlhi" Mutumin ta ce
"Zaku biya kudin dukka seat ɗin kenan?" Maman ta ce
"Iya kuɗin motarmu gare mu" ya girgiza kai ya ce
"A'a saboda ku biyu ba zamu sha mai mu tafi Katsina a cikin daren nan ba" duk yadda suka so a taimaka musu abu kam yaki, karshe suka koma gefe akan zasu kwana a tashar sai gobe da safe su tafi amma kana ganinsu duk hankalin su baya tare da su barin ma Mama...
****
Yau ta kasance Ranar Juma'a ce, kuma kamar yadda aka saba, Azrah ta tashi da sassafe, ta yi sallah, ta karanta Suratul khaf kafin ta miƙe ta fara shirinta gaba ɗaya yau bata da wani kuzari balle walwala haka ta kwana da Umma a rai, dukda bambanci awanni dake sakanin India da Nigeria hakan bai hanata kwada numbern Bappah ba dan tasan yanzu karfe sha-biyu ne na dare, jin a kashe kawai ta ajiye wayan, bata yi mamakin rashin ganin Samira da bata yi a ɗakin ba
Tana cikin shiri can sai ga Samira ta buɗe kofar ɗakin ta shigo waya kare a kunnanta tana dariya, ta wuce wajan shoe rack ta ajiye jakkanta ba tare da la'akari da Azrah ba, tana juyawa suka haɗa ido da Azrah, ta ce
"Kai Azrah, yau kuma lecture ɗin 6 hours ne fah, shine zaki tafi tun yanzu, I hope you're ready"
Azrah ta gyara veil dinta tana murmushin karfin hali ta ce
"I'm always ready" gyada kai tayi ta ce
"Toh ya jikin Umman kuma?" A takaice ta amsa da "Da sauki"
Har zata fita Samira ta ce
"Azrah Deen ɗina yana gaishe ki wai kuma ya jikin Umma" Azrah ta ce
"Ina amsawa, ki ce masa da sauki, thank you"
***
Khalil ya tsaya a bakin lecture hall ɗinsu tun kafin su gama, yana jingine da jikin bango, hannunsa cikin aljihun wandonsa, kamar wanda yake da wata damuwa haka ya bayyana a fuskarsa, Idanunsa na kan kofar lecture hall ɗin tuntuni
Bayan ɗan wani lokaci students ɗin suka fara fitowa, Sai gashi Azrah ta fito cikin nutsuwa, fuskarta ta kasa boye damuwar da take ciki, tafiya take a hankali kuma cike da gajjiya, kamar ance ta juya kawai ta kalli Khalil dake tsaye ya zuba mata Idanu, ɗan murmushi tayi sannan ta juya tafiyar nata zuwa direction ɗinsa, shima yayi murmushi mai shauƙi wanda ke bayyanar da farin cikin ganin ta
Bayan ta karasa wajen da yake tsaye, tun kafin tayi magana ya riga ta, ya ce
"So, today you didn't even wait for me to walk you to class?"
Azrah ta ɗan yi murmushi tana girgiza kai ta ce
"It wasn't intentional"
Ya ɗan tsaya yana kallonta, ganin yadda damuwar ta bayyana sosai a fuskarta dan duk yadda tayi kokarin ɓoyewa amma bata san ya riga da ya gane ba, kafin ya ce
"How's Umma doing? Any improvement?" Azrah ta ɗan sauke ajiyar zuciya ta ce
"We haven't spoken yet today... But I believe it's morning already in Nigeria, I'll try calling again" har sannan yana kallon cikin idonta
"Do so please, May Allah grant her complete healing" ya faɗa da sincerity a muryarsa
Azrah ta ɗan lumshe ido a hankali "Ameen" ta amsa da sanyin muryarta
Suka tafi wani student spot da ke kusa da hostel ɗin su, Khalil ya siya mata fried rice da shaka, dan kwana biyu ta cika sa da tayi missing fried rice, a karo na farko da take ci ba tare da yin dogon gardama ba.
Yana kallonta ya ce "You're not just smart, you're strong, But sometimes, strength is letting someone else help too"
Duk da bata gama gane mene nufi ba ta ce masa
"Thanks, but I'm just doing what I have to"
A ranta, tana kallon Khalil a matsayin mutum mai kirki ne kamar yayanta ba wani abu fiye da haka. Amma a duk lokacin da ya zauna kusa da ita, tana jin kwanciyar hankali, irin wanda bata saba ba sannan ga wani irin nutsuwa da take tsintan kanta a ciki, Amma wannan ba soyayya ba ce a wajenta trust ne kawai
Daidai lokacin da ya raka ta har bakin hostel ɗinsu, Samira ta gansu tare tun daga nesa, ta zuba musu ido amma babu wanda ya kula da ita har tayi shigewarta cikin hostel ɗin, sallama suka yi yana sake ma Umma fatan samun sauki, daga haka tayi shigewarta shi kuma ya kara gaba
Tana shiga ɗaki taga Samira na canza kaya da alama daga toilet ta fito, Azrah ta mata murmushi, tun kafin tayi magana ta riga ta, ta ce
"Azrah... ni kam zan fara sa ido a kan Khalil gsky, I don't trust him anymore
Azrah ta ɗan murmusa ta ce
"He's just a kind person, nothing more fah"
Samira ta ce
"Just saying o. Before you catch feelings unknowingly Ni dai ba ruwa na"
******
Mama basu suka iso gida ba sai wajajen karfe sha biyu, har an sallame Umma daga asibiti, ga Zahra dake compound tana girki Dada kuma na zaune kan tabarma tana yankan alayyahun, Bappah na gefe suna ɗan hira, Mama dake waje ta ɗan leƙo dan ta duba ko da mutane a compound ɗin kawai idonta ya faɗo cikin idon Dada data ɗaga kai itama zata fara mitan har sannan Mama bata zo ba, da sauri Mama ta ja baya tana jin bugun zuciyarta na kara tsananta, Dada ta ɗauke kai kamar bata ga komai ba, bayan Mama ta gama haɗa duk wani dauriyarta ta shigo da sallama a bakinta, Dada ta ɗauke kanta ta mayar kan yankan alayyahun da take yi tayi kamar bata ma ganta ba
Zahra dake wanke wanke dan tayi calling attention ɗin Bappah da Dada yasa ta ce
"Mama ina wuni" Bappah ya ɗaga kansa yana kallon Mama dake rakuɓe rakuɓe, bai san sanda ya miƙe ba ya ce
"Tattara kayanki ki koma inda kika fito" Mama ta maraice ta ce
"Dan Allah Karka min haka mana, kayi hakuri zan maka bayani" Bappah ya mata wani kallo ya ce
"Idan kika yarda na shiga da kaina ƙwaso miki kayan ba zaki ji daɗi ba" Mama tana kallon Dada amma ita kuwa ko da wasa bata ma ɗaga kai ba balle ta sa ran zama ta saka baki a maganar na su, Bappah da yayi kamar zai yi kanta ai bata san sanda ta nufa ɗakin a saba'in ba, Bappah da ransa yayi mugun ɓaci ya koma ya zauna
Dada data gama yanka alayyahun gabanta ya ce da Zahra
"Zahra zo ki ɗauka, na gama" Zahra ta miƙe ta nufi inda Dada ke zaune wanda ita kuma tuni ta yi cikin ɗaki dan ba zata sa baki a maganar nasu ba, Bappah kam tagumi yayi yana kallon wani wajan daban, sai kuma can ya miƙe kamar wanda aka tsikara yayi ɗakin Mama
Mama da tayi tagumi tana zaune kawai taga Bappah miƙewa ta yi da sauri ta fara bashi hakuri
"Nasan nayi kuskure Malam amma ka tausaya ka yafe min" Bappah ba wasa a muryansa ya ce
"Na gaya miki tun kafin rana ya gana yi ko yamma ki tattara kayanki ki bar min gida" Mama ta fashe da kuka tana basa hakuri a gigice, daga haka ya juya ya bar kofar ɗakin
Ɗakin sa ya nufa bai kai ga zama ba sai ga Dada ta buɗe labulen ɗakin tana kallon sa ta ce
"Ba baki zan saka muku a case ɗinku ba amma maganar ta bar gidan baiyi ba, duk wani hukuncin da zaka ɗauka ka ɗauka amma ta bar maka gida kam bai taso ba" Bappah ya gyaɗa mata kai kawai, ta sake labulen ta bar kofar
*****
Da Daddaren Azrah na zaune bayan tayi wanka ta saka kayan bacci yau ko karatun daren ma bata fita ba dan tana jin babu wani abu da zata fahimta, ta dauki wayarta tayi dialing numbern Bappah
"Yaya Azrah" Zahra da tayi receiving call ɗin ta faɗa
Azrah ta ce "Ya jikin Umman kuma? Karki ɓoye min komai kinji" Umma da Bappah ga kuma Dada dake gefe duk suka zubawa Zahra ido dan basu zata cewa har Zahra ta faɗa mata ba, Zahra kuwa ta sauke kanta cike da jin kunya ta ce
"Da sauki sosai, har an sallame mu ma" Azrah da damuwa ya mata yawa har kana jin a muryan ta, ta ce
"Dan Allah ki faɗamin gaskiya, wlhi yau haka na wuni babu wani walwala tattare da Ni"
Bappah ya karɓi wayar ya ce
"Ya karatu Azrah?" A hankali Azrah ta ce
"Alhamdulillah Bappah, ya jikin Umman mu Bappah?" Bappah ya ce
"Ga Umman naku bari na miƙa mata taji sauki sosai, ban san dalilin da yasa Zahra zata ɗaga miki hankali ba"
Azrah ta ce da ladabi
Toh Bappah miƙa wa Umman wayan" Bappah ya miƙa mata wayan, ta ce
"Azrah ki kwantar da hankalin ki na samu sauki sosaii dama ɗan ciwon kai ne" Azrah ta sauke wani jiyar zuciya da jin muryan Umma har relief ta samu ta ce
"Toh Umma, Allah kara miki lafiya" Umma ta ce
"Amin, nasan halinki ba lallai kinci abinci ba, yanzu tunda kinji na warke sai ki kwantar da hankalin na ki ko?" Azrah ta gyaɗa mata kai kawai tana murmushi, ta gaisa da Dada wanda duk tsokanarta take yi
Bayan sun kashe wayan Umma ta ce
"Zahra ban yarda koda wasa idan banda lafiya ki sake kira ki faɗawa Yayarki ba, Kinsan halinta da ɗaga hankali musamman da tayi nisa ya kike so tayi?" Bappah dake kallon Zahra wanda taki kallon sa ya ce
"Ta ce min na bata waya zata kira Azrah nace mata A'a harda kashe waya ashe an gudu ba'a tsira bane dan tuni ta feshe mata" Zahra ta turo baki kamar zata yi kuka ta ce
"Toh Nima ba rikicewa nayi ba amma ai haka kawai ba zan faɗa ba" Dada ta ce
"Zo abinki ki zaune nan sai naga wani ya sake miki magana"
This book costs 500. Make the payment to Hauwa Jibrin, Wema Bank account 0421255553, and send proof of payment to 08110615256.