← Book details Beyond The Veil Part 1 Complete Novel Local reading mode
READING PART 1 OF 4

Gabatarwa

Beyond The Veil Part 1 Complete Novel · about 302 min read

BEYOND THE VEIL

Hauwa Jibrin Sulaiman
Jiddatul-khayr writes

Young talented writers association (YOTA)

All praise is due to Almighty Allah who has granted me the strength, time, nd inspiration to write again. It's by His mercy that I return to u my beloved readers with another story frm the depths of my heart.
To everyone who supported my previous works, thnkyou for walking this journey with me. Your love, your feedback, and your encouragement continue to fuel my passion.
Now, I come back with something new a different style, a fresh voice, and a story I hope will touch your soul in ways words alone cannot explain.
I pray you receive it with open hearts, just as you’ve welcomed me before.

Before diving into the story, I want to express my deepest appreciation to *Na'ima Sulaiman Sarauta (Nimcyluv)*. 
Her thoughtful suggestions and careful edits have greatly improved this work. 
I am truly grateful for her time, encouragement, and belief in my vision. 

Thank you Shugaba Nimcyluv, and I Love you so much.

Wannan littafin kuɗi ne, 500 ne as ongoing book, idan ya kammalu kuma 1k ne document ɗin, thank you.

Free page

Episode 1: Unspoken possessiveness

Tana dukunkune cikin duvet ɗin ta, saboda ruwan da akayi jiya da daddare wanda yasa garin ya ɗauki sanyi, buɗe idanun ta me cike da bacci tayi, ta ɗan yaye duvet ɗin da ya rufe mata har kan ta, agogon ɗakin ta kalla, da sauri ta miƙe zaune cikin muryan ta mai daɗi tace "SubhanAllah, it's already 6:30am? Oops.., I woke up late today" sai kuma ta fara karanta addu'an tashi daga bacci, sauke kafafun ta masu laushi da haske tayi ta saka Indoor slippers daga haka ta mike tsaye, ta yaye Night cap ɗin kanta saboda takurawa gashin ta da yayi tana yamutsa fuska, hakan ya ba ma gashin na ta damar sauka har gadon bayan ta, gƴara tsadaddan gadon ɗakin nata ta shiga yi, bata ɗau lokaci ba kuma ta gama, wardrobe ta wuce ta buɗe wani kimono ta ɗauka ta sa akan sleepwear ɗin jikin ta ta sauka kasa da sauri, kitchen ta shiga don haɗa breakfast, cikin sauri take haɗa Sandwich ɗin wanda bai ɗauke ta wasu lokuta ba ta gama, ta tafasa tea ta juye a tea flask, daga haka ta kai su kan dining, ta haura sama da sauri dan yin wanka.

Bata tsaya shafa mai ba, kawai ta wuce ta ɗauki simple Abayan ta ta sanya, ta ɗauki Office bag ɗin ta ta rata ya, ta juya tana kallon fuskar ta a madubi, ganin pink lips ɗinta sun fara bushewa yasa ta shafa lips balm

Cikin sauri yake shiri, mamakin kansa yake yi dan is hardly ya makkara, bayan ya fito parlorn yana gyaran neck tie ɗinsa daga haka ya wuce kitchen yana bin gurin da kallo ko zai samu abin sawa a cikin sa ganin kitchen ɗin alamar anyi girki yasa ya wuce dinning Luckily ya ga Sandwich dake cikin plate rufe da mesh food cover, ya ja ɗaya daga kujerun dining ɗin ya zauna ya yaye laidar ya taɓa flask jin akwai tea ya juye a cup sannan ya fara breakfast hankalin sa kwance yet in a hurry way, bayan ya gama ya koma parlorn dan haɗa kayan da zai tafi da shi office

Tun daga sakkowan ta daga stairs take kallon sa sai kuma ta ɗauke kai, ya ɗan kalle ta shima sannan ya ɗauke kai, dinning ta wuce, da sauri ta kalle sa ganin ya gama breakfast da kayan da ta gama making ta sake kallon waste plate ɗin, ta ɗaga kai ta kalle sa sai kuma ta ce

"Wait, is it the breakfast I just prepared that you ate?" Ba tare da ya Kalle ta ba ya ce

"What are your eyes telling you? I ate it because I saw it was already prepared."

Ɗan tsaki ta ja, saboda ran ta yayi mugun ɓaci ta ɗan saci kallon sa ganin zai fita ta ce

"Amma ai wannan bai dace ba, dama kana cin abincin gidan ne ko kuma neman magana ne?"

Ba tare da ya Kalle ta ba ya ce "This is my house, and I will do as I please, so stop asking me whether I ate or not, I will do whatever I see fit."

Ta ɓata fuska tana kallon sa har ya fita sannan ta bi sa da harara, ta ɗauki Officebag dinta ta bi bayan sa ta samu already har ya shiga Mota itama wajan nata motar tayi kawai ta tsinci muryar sa

"Kar ki kuskura ki fita da wannan kayan jikin naki, you're behaving like someone who isn't married."

Ta ɓata fuska ta kalli agogon hannun ta, sai kuma ta Kalle sa taga mugun kallon da yake mata, kawai ta samu kanta da juyawa ta wuce cikin gidan, ba'a ɗau lokaci ba sai gata ta sake fitowa da Hijab a jikin ta, ganin shigar ta yasa ya fara tada motar sa, ita kuma ta wuce wajan motar ta, ganin tayan a sace yasa tayi wajan sa da sauri dan har ya fara reverse

Ta ce "Wait.. mota na da matsala barin bika kawai"

Wani kallo ya mata sannan ya wuce ta ya fita, ta tsaya baki a bude, kawai tayi ordern bold

Tana zaune a office ɗinta tana aiki a system ɗin gaban ta wani ogan ta ne ya shigo da sallama a bakin sa, ta ɗaga kai tana kallon sa sai kuma tayi murmushi ta ce

"Good morning, sir."

ya ce "Morning, hope kin gama da aikin jiya?."

Ta ɗan buɗe baki tana kallon sa sai kuma ta miƙe ta ce

"I'm so sorry, wallahi Jiya saboda hadari na manta but I’m going to do the work now."

Ya juya ba tare da ya ce mata komai ba ya fita daga office ɗin nata, ta bisa da kallo sai kuma ta miƙe ta buɗe wani File cabinet  ta Ciro wani paper tana duba wa sannan ta ɗauki wayanta ta shiga e-mail tana kallon ko yayi daidai daga haka ta miƙe zuwa wani Office ɗin.

Ba tare da tayi knocking ba ta buɗe kanta tsaye ta shiga, Ajiye cup ɗin hannun sa da yake sipping yayi yana kallon ta da mugun mamaki, ta taɓe baki kamar ba shine ya gama cinye mata breakfast a gida ba amma gashi yana sake wani breakfast ɗin a Office

Ya ce "Don't you know how to knock or say hello before coming in?"

Dama da haushin yaki mata left take, ta Kalle sa kamar ba zata ce komai ba sai kuma ta ce

"Aikin da Jiya kaki ka min ne yanzu Oga Mahmud yace nayi na kai masa"

Wani kallo ya mata sai kuma ya cigaba da aikin gabansa ba tare da ya sake bin ta kan ta ba

Ta tsaya for almost 5 min ba tare da ya sake ko kallon ta ba hakan yasa ta jawo system ɗin gaban sa ta gyara zamar ta ta soma aikin operating system ɗin nasa

With lots of shock yake kallonta ta ya buɗe baki zai yi magana a fusace aka buɗe kofar office ɗin, duk suka juya lokaci guda ta miƙe tana washe baki ta ce

"Baba!, Welcome"

Ta kasan ido ya Kalle ta sai kuma ya maida kansa kan mutumin da ya shigo ya ce

"Good morning, sir."

Mutumin ya karasa har cikin office ɗin ya zauna har sannan da murmushi shinfiɗe a fuskar sa cike da dattako ya ce

"Daughter, I hope you’re doing well"

Ta ce "Alhamdulillah Baba"

kallo ɗaya ya masa ya ce "Baka ga message ɗina bane? Ko kuma kiran nawa ne zaka ce baka gani ba?"

Ɗan sotsa kansa yayi ya saci kallon inda take sai kuma ya maida kallon sa ga dattijon ya ce

"I'm very sorry, Sir. Actually, I had some work I needed to finish first, then I planned to come over har gida na same ka, shiyasa sir"

Ya miƙe ba tare da ya ce masa komai ba yana kallon ta ya ce

"Daughter idan aiki ba zai miki yawa ba akwai special assignment da zan baki tunda mijin naki baya maida hankali ga aikin sa"

Da murmushi a fuskarta ta ce

"Alright Baba, nayi alkawarin maida hankalina na gama cikin kankanin lokaci"

Murmushi ya mata daga haka ya fita, dama supervising company ya zo yi, duk inda ya shiga gaishe sa ake cike da girmamawa

Sauke ajiyan zuciya yayi ba tare da ya ce komai ba, idon sa na kanta har ta kammala aikin da zata yi ta miƙe

Ya ce "Bana bukatar sake ganin ki anan please"

Ta juya tana masa wani kallo ta ce  "Haba? Toh ka rantse naji?"

Wani kallo ya mata, ta taɓe baki ba tare da ta sake kula sa ba ta fita, first floor ta wuce rike da papern da ta gama printing ɗin su out, a bakin Office ɗin Oga Mahmud ta danna door bell, bayan an bata izini yasa ta shiga ta same sa ga kuma Baba dake gefen sa yana duba wani files ta ce

"Here's it sir, Na gama"

Karɓa yayi yana dubawa ya ce

"Well, thank you"

Daga haka ta fita daga office ɗin zuwa nata office ɗin.

Da Yamma bayan karfe 4pm duk yawanci ma'aikatan duk sun fito da niyyar tafiya gida

Hango sa da tayi yasa ta fara tafiya da sauri dan ta rantse a motar sa zata koma gida

Ta tsaya tana magana da wata ma'aikaciya ganin ya nufa motar sa yasa tayi wani murmushi dan ta kasan ido take kallon sa ganin ya shiga yasa tayi wajan da sauri ta buɗe kofar gaban motar

Shi da yake shirin tada motar ya ɗaga kai yana kallon ta da mamaki ya ce

"Are you out of your mind opening my car without permission?"

Ta ce "Why would I need permission when it’s my husband’s car?"

He gave her a sharp look ya ce "Alright then, get in let's see."

Ta ce "Yanzu ma kuwa" ta zauna har da gyara zamanta ta saci kallon sa taga wani irin kallon da yake mata ta ɗaga kafaɗa ta ce

"Baba ne ya ce kar na hau bold tunda ga ka, siyasa ban masa kardama ba, amma ka ce na sauka wallahi sai na je na faɗa masa"

Hango Baba da yake saukowa tare da guards ɗin sa hakan yasa ya tada motar ba tare da ya sake kallon ta ba, ta taɓe baki ta toshe kunne ta da Bluetooth dan bata bukatar jarabar sa

A hanya taga ya parka dai dai wani babban eatry ya sauka ya shiga ciki, bai wani dade sosai ba sai gashi ya fito rike da laidar takeaway ta dinga kallon sa har ya karaso motar tana mamakin takeaway ɗaya da ta gani, tayi kwafa har sai daya ɗan Kalle ta.

Bayan sun shiga cikin parlorn na su, yana gaba tana baya, ya wuce dining ita kuma ta wuce sama, yana ajiye takeaway ya wuce dakin sa dan canza kaya, tana laɓe a stair wall ganin har ya rufe dakinsa ta fito da sauri tayi dining ta ɗauke takeaway ta haura sama da gudu tana dariya, tana shiga dakin ta ta danna masa key, kan tsadaddan bedside dinta ta ajiye sannan ta cire kayan ta ta wuce toilet dan yin wanka.

Bayan ya sanya jallabiyar sa ya fito, bai lura da babu komai a dining ba sai daya karasa, sake baki yayi yana kallon kan table din sai kuma ya shafa kansa bai san sanda murmushi yayi escape a fuskar sa ba ya shafa fuskarsa ya wuce kitchen dan duba wani Alternative ɗin.

Yau tun da ta tashi haka kawai take jin bata son wannan family meeting ɗin nasu, haka kawai take jin fargaban haɗuwa da sauran family member ɗin sa.

Kamar kullum ta ɗaura 'yar karamar kimono akan sleepwear ɗin jikinta ta sauka ta girka breakfast har da shi bayan ta gama ta jera su a dining sannan ta wuce sama dan wanka.

Bayan ta fito a wanka ta shafa tsadaddun lotion ta feshe jikin ta da expensive Perfumes sannan ta saka tsaddadan lace tayi daurin daya amshe ta ta daura laffaya ta dauki flat shoe da wani dan karamin hand bag, ta saka Black space sannan ta sauka.

Tun daga stairs yake kallon ta, He couldn't take his eyes off her har ta karasa dining ɗin, sannan ya sauke ajiyar zuciya

Ba tare da ta Kalle sa ba ta jawo flask din tea ta zuba, ɗan daga idon ta tayi suka haɗa ido yayi gyaran murya ya ce

"Baki iya gaisuwa ba ne?"

Ta Kalle sa ta ce
"Idan na gaishe ka ɗin amsa wa zaka yi?"

Yayi kasa da murya yace "Don't please" ta Kalle sa sai kuma taji ba daɗi

Har suka gama breakfast ba wanda ya ce da ɗan-uwansa kala, bayan sun fita ta ɗauka a motar sa zata bi sa, sai kuma taga ya nuna mata nata motar, ta ɗan kalli wajan sai kuma taga har an gyara mata hakan yasa ta koma cikin gidan dan dauko nata keyn.

A Babban compound ɗin da ya gaji da kyau aka yi decorating, a tsare wajan zaman suke, ga su VIP chairs ga kuma reserved seats, wanda wannan taron once in a while ake yin shi sbd Extended family gare su, wanda already mutane sun fara taruwa kowa yana zama a spot din sa

Amira ta kalli Zainab ta ce "Kin san wa nake son kallo?"

Zainab ta ce "Nope, sai kin faɗa"

Amira ta ce "Matar Crush ɗina mana, ina so naga da me ta fini, naji ance ƴar ghetto area ce kuma She came from a poor background"

Zainab ta yamutsa fuska ta ce "ƙaryan tsiya anan ya kare ai, I doubt she can speaks or understanding English, yanzu idan ya tashi tafiya business trip ɗin sa sai muga yadda zai yi da mata 'yar ghetto"

Duk kwashewa suka yi da dariya

Wata cousin ɗin su ce tazo wucewa tana cewa "Yanzu Yaya zai shigo da matar sa"

Juyawa suka yi suka Kalle ta, Amira tayi saurin cewa

"Hajara wait.. wai Yaya ne zai shigo yanzu?"

Kai ta gyaɗa mata ta ce "Sure! Harda Matar sa, kinsan ba'a san ta ba"

Tana kai wa nan tayi gaba ta bar su, Amira ta miƙe ta ce "Zee, ta shi mu je can gate na ganta da kyau kar sai ta zo nan mutane su hanani kare mata kallo"

Zainab ta miƙe tana cewa "haka ne fah"

Hajara dake waya da Yayan ta ta ce "Okay Yaya, yanzu haka ina car park Ina jiran shigowar ku"

Bayan sun isa can farkon compound ɗin suka tsaya, basu wani daɗe ba sai ga motar sa ya kuso kai Zainab ta kalli Amira ta ce

"Wallahi dama a cikin mu ya ɗauka, gamu duk final year student a uni, bari dai yau mu kare ma matar nasa kallo tass" Amira ta mata wani kallo ta ce

"Dama Ni ya ɗauka ko mu?" Ta karasa maganar da harara

Yana gama parking Hajara ta karasa tana masa Sannu da zuwa, hakan yasa su Zainab karasa wajan suma Amira ta kashe murya ta fara magana cike da shagwaɓa, Hajara ta ce

"Yaya Anty Azrah fah?"

Bata kai ga rufe baki ba sai ka motar ta ta shigo compound ɗin, Amira duk suka mayar da hankali su kanta dan ganin ta wato har mota ta iya yanzu

Bayan tayi parking ta buɗe motar wanda tuni Hajara ta karasa wajan dama kiran da ya mata kenan akan ta shiga da ita saboda rashin sanin ta da aka yi, sauke kafafun ta tayi kasa wanda take sanye da flat shoe red henna kafarta ya karama kafar nata kyau da haske, Amira suka kalli juna da Zainab

Ta karasa fita a motar wanda fuskar ta yana ɗauke da murmushi ganin Hajara, sai da numfashin Amira ya kusa ɗauke wa sanda idon ta ya faɗa kanta, Zainab kam tuni ta manta wani class ta sake baki tana kallon ta

Zainab ta juya tana kallon Yayan su da ya fara gaba ta ce

"Yaya ina Matar ka? Ko ba zata zo bane"?"

Pointing mata inda Hajara ke rufe mata motar yayi, da sauri ta juya tana kallon Amira data gama mutuwar tsaye

Hajara na rike da ita suka karasa har in da suke ta ce "Hey Cousins, ga Matar Yaya"

Duk sun kasa cewa komai hakan yasa Hajara taji wani iri daga haka suka wuce wajan taron

Amira ta kalli Zainab wanda har sannan idon ta ya gama cika da hawaye ta ce

"I doubt ba ita bace" Zainab tayi dariya dan ta fahimci kishi ne ta ce

"Sai kuma ya manta matar ta sa? Ita ɗin ce sai dai ba yadda muke expecting bane kila karya Anty ta mana"

Amira ta bar wajan dan bata jin zata iya sake tsayuwa a gidan nan.

#Jiddatulkhayr
08110615256
*BEYOND THE VEIL


Hauwa Jibrin Sulaiman
(Jiddatulkhayr)

Young talented writers association (YOTA)


Free page

Episode 2: A Glimpse into Azrah's Life


Tsane ruwan dake zuba daga kanta tayi, ta ɗaura ɗan karamin towel ɗinta sannan ta sanya hijab a jikinta, ta dauki shower gel ɗinta da shampoo dake kan tagar ban-ɗakin wanda ko plasta babu balle window, tura kofar ban-ɗakin tayi ta fito cikin ɗan matsakaicin compound ɗin nasu, Mama dake kwashe abincin talla tana zuba wa a cikin robar tallan ta ɗaga kai tana mata wani banzan kallo ta ce

"Ace yarinya ƴar gidan talakawa amma ki dage ke lallai sai da wannan sabulun turawan zakiyi wanka ke ga ƴar gold ko? Mu da muke wanka da Omo ai mutuwa muka yi"

A hankali ta buɗe baki ta ce

"Mama bani fah aka yi, bawai nace nafi karfin wanka da Omo bane" Mama ta bita da wani kallo ta ce

"Ai karya zan miki, ba abinda kika iya banda yawon iskanci, yo yawan iskanci mana wai ke gaki ƴar boko ko?"

Azrah ba tare da ta sake kallon direction ɗin Mama ba ta wuce zuwa ɗakin dake kusa dana Mama ta shige ciki

Umma ta ɗaga kai tana kallonta ta ce

"Sai dana ce miki ki daina fita da wannan sabulun ruwan amma baki ji" kallon Umma tayi cike da mamaki sai dai bata ce komai ba ta wuce daki direct dan sanya kaya

Bayan ta gama shafa lotion dinta ta dauki well ironed uniform dinta wanda daga gani kasan ya gama koɗewa ta sanya sannan ta fito rike da jakka a hannun ta, tana kallon Umma ta ce

"Ina Zahra Umma?"

"Na aike ta ta tsiyo sigari" Umma ta mayar mata da amsa

Ta ce "Toh Ni zan wuce makarantar kar na makkara" Umma ta ce

"Toh Allah ya bada sa'a Azrah, ki kula da kanki" ta gyaɗa mata kai daga haka ta nufi compound ta samu Mama da wata makwabciyar su da alama magana suke yi

Mama tayi wani murmushin takaici ta ce

"Wato ke Azrah baki da aiki sai zuwa makaranta saboda baki son aikin gida ko?"

Makwabciyar ta su wanda ake kira da Maman asabe ta ce

"Toh ai sai ku hana ta ai tunda bata isa ce muku A'a ba, dan Ni banga amfanin wani makarantar boko ba" Mama ta ce

"Yo dama me suke koya a makarantar idan banda iskanci? Nawa zaki ga yarinya wai ita boko daga karshe shikenan ta koma karuwar gari"

Tuni Azrah ta fita ba tare da ta sake waiwayosu ba ko tanka musu

Gidan su kawarta Fatima ta tsaya, tana sallama sai gata ta fito itama cikin shirin makaranta daga haka suka wuce zuwa makaranta

Bayan ta dawo daga School babu kowa compound ɗin su ta wuce dakin Ummanta ta shiga da sallama, Zahra dake jikin Umma tana cin abincin ta ɗaga kai tana kallon Azrah ta ce

"Sannu da zuwa Anty Azrah"

Azrah ta gyaɗa mata kai tana kallon Umma ta ce

"Barka da rana Umma" 

Umma ta ce "Yauwa Azrah, ya karatun?" Ta ce

"Alhamdulillah Umma" daga haka ta miƙe ta wuce ta shige dakin da yake nasu bata daɗe ba sai gata ta fito tana sanye da doguwar riga da hijabi Umma na kallon ta ta ce

"Ba zaki ci abinci bane zaki tafi?"

Azrah na Murmushi ta ce "A'a Umma nasan abincin ba yawa idan naje gidan Mummy ba zan rasa abin da zan ci ba, amma wannan na bar muku ke da Zahra"

Umma tayi shiru tana kallon 'yar nata cike da tausayi

Azrah ta yanke mata tunaninta ta ce

"Toh Umma na tafi" Umma ta gyaɗa mata kai ta ce

"Allah ya tsare" Zahra ta miƙe ta raka ta har bakin kofa sannan ta koma

Wani babban gidane wanda ya gaji da kyau a Barhim estate, dake jihar Katsina, a bakin gate ɗin tayi knocking mai gadi ya leƙo ganin ta ya wangale mata gate ɗin ta shiga tana mai gaishe sa ya amsa mata, daga haka ta nufi cikin entrance ɗin gidan, a balcony taga Ya saif na zaune

Ta ce "Ina wuni Ya saif"

Ko kallon ta bai yi ba balle tasa ran zai amsa mata kuma bata yi mamaki ba dan idan da sabo ta saba dama ba gaisuwar ta yake amsawa ba, tana shiga parlorn taga Mummy na zaune ga kuma Suhaila a gefen ta tana shan fruits, duk ɗaga kai suka yi suna kallon ta har ta karasa cikin parlorn ta duka jikin wani kujera ta ce

"Ina wuni Mummy"

Mummy da murmushi shinfiɗe a fuskar ta tace "Lafiya kalau Azrah, ya su Umman ki?" Ta ce

"Alhamdulillah" ta maida kallon ta ga Suhaila ta ce

"Ina wuni Anty Suhaila" itama da murmushi shinfiɗe a fuskarta ta ce

"Lafiya Azrah, kar dai yauma takowa kika yi da ƙafa?" Azrah murmushi kawai tayi, Suhail ta ce

"Ke baki ganin nisan unguwar taku ne? Ace tun daga Kofar Marusa har nan Barhim estate ki tako a ƙafa?" Azrah murmushi kawai tayi dan yanzu har ta daina ganin nisan

Mummy ta ce "Ai yabi jikinta ba zata iya dai nawa ba" Azrah ta miƙe ta fara tattara parlorn da ba wani datti sosai yayi ba tana gamawa ta wuce kitchen

Nan ma ta fara gyara kitchen ɗin bata dau lokaci ba ta gama sannan ta tara kayan wanke wanken a sink ta fara yi cikin kankanin lokaci ta gama ta daura abinci, Mummy ta shigo kitchen ɗin tana bi da kallon, ɗaya daga cikin abin da take son aikin Azrah kenan tana da tsafta yarinyar sannan bata da gandan aiki shiyasa kawai take managing duk da Azrah idan ana School ba da safe take zuwa ba, ta juyo tana kallon Mummy ta ce

"Mummy kina bukatar wani abun ne na kawo miki?" Mummy ta ce

"A'a yi aikin ki kawai, zan dauki abu ne" Azrah ta gyaɗa mata kai kawai ta cigaba da aikin gaban ta

Sai karfe biyar ta gama aikin gidan tass da abincin, ta duka a parlorn tana kallon Mummy ta ce

"Mummy zan tafi gida" Mummy ta ce

"Toh shikenan Azrah, sai gobe ko?" Ta gyaɗa mata kai, Suhaila ta ce

"Gashi nan dubu uku ne, kiyi using ma week din nan kina hawa keke ki daina wannan takowan da ƙafa dan Allah", Azrah ta sa hannu ta karɓa ta ce

"Nagode sosai Anty Suhaila, Allah ya biya ki da Aljanna" ta ce

"Is Okay Azrah, Amin thank you" daga haka Azrah ta bar parlorn

Suhaila ta kalli Mummy ta ce "Wallahi Mummy ina son ganin rayuwar yarinyar nan yayi kyau, Allah bata miji mai kuɗi da zai iya riƙe ta sakani da Allah" Mummy ta ce

"Wallahi Nima ina mata sha'awar gidan Hutu, gata da hankali ga kuma ilimi kamar wacca ba makarantar gomnati take ba" Suhaila ta ce

"Wallahi Nima ilimin ta dai mamaki yake bani, ga kyau kamar wacca ita tayi kanta, kwatakwata bata yi kama da 'yar gidan talakawa ba" Mummy ta ce

"Dan kawai naga Yayanki basu shiri ne amma da wallahi na masa maganar ya aure ta dan banga wani abu na qualities ɗin mace ace bata da shi ba" Suhaila ta ɗan yi frowning face ɗinta ta ce

"Shi ya sani, ai na taɓa masa maganar kamar wadda na kara masa tsanarta a zuciyar sa, wallahi duk macen da zai kawo dakyar ta wuce Azrah da wani quality ɗin wallahi"

Mummy ta miƙe tana hanyar bedroom ɗinta ta ce

"Zan gwada masa magana gaskiya idan har zai yarda" Suhaila ta ce

"Hmm" ta cigaba da danna wayan ta.

A gajiye Azrah ta isa gida, ta shiga dakin Umman su da sallama a bakin ta, Umma dake koyawa Zahra Tauhidi ta ɗaga kai tana kallon ta harta karasa cikin ta zauna tana sauke ajiyar zuciya dan ba karamin gajiya tayi ba, Zahra ta miƙe ta fita daga ɗakin, Azrah ta ce

"Barka da yamma Umma" Umma na kallon ƴar nata cike da tausayin wahalar da take sha ta ce

"Sannu Azrah, Allah miki Albarka ya baki future mai kyau wanda ba zaki sha wahala ba" Azrah ta ce

"Amin Umma"  Zahra ta shigo da ruwa a hannunta ta karasa inda Azrah ke zaune ta miƙa mata ta ce

"Gashi Anty Azrah" karɓa tayi tana faɗin

"Nagode Zahra"

Kafa kofin ruwan tayi a baki bayan ta sha ta sauke tana kallon Umman nasu ta miƙa mata kuɗin da Anty Suhaila ta bata

Umma ta ce "Kuɗin me kuma Azrah?"

Azrah ta ce "Anty Suhaila ce ta bani wai na daina tafiya da ƙafa shine da zan dawo naki hawan a daidaita nace sai a biya ma Zahra kudin Islamiyyanta sai ta koma ko?"

Umma na kallon ta hawaye yana cikowa daga idon ta dakyar ta maida sa dan bata son yaran nata su fahimci haka amma zuciyar ta cike take da tausayin irin wahalar da Azrah zake ciki ta ce

"A'a Azrah, gaskiya ne ki daina wannan takun kinga wajan da nisa sosai kawai ki ajiye tare da ke sai kina amfani da shi wajan tafiya ko?" Azrah ta girgiza mata kai ta ce

"A'a Umma, har dubu uku ne fah" ta zare dubu ɗaya ta miƙa ma Zahra ta ce

"Gashi gobe ki kai kudin makarantar ki saiki fara zuwa ko?" Zahra ta karɓa ta ce

"Nagode Anty Azrah, Allah ya mayar miki" Azrah ta harareta sai kuma ta mayar da kallon ta ga Umma ta ce

"Ina ga ba zan saka a asusu ba kawai zan nema abin da zan kara na sana'a ko Umma, sai wannan ya zama kamar naki ne" Umma tayi shiru tana kallon ta

Azrah ta mata murmushi ta kalli agogo ganin Magrib ya kusa yasa ta miƙe ta ce

"Bari nayi shara sai na ɗaura abincin dare" daga haka ta wuce cikin compound ɗin na su.

Da daddare bayan sallahn Isha'i sai ga Bappah ya shigo gidan Mama na zaune a tabarma tana lissafin Kuɗi, ga kuma Habiba da bata daɗe da dawowa daga talla ba, ganin Bappah yasa ta tura kuɗin kasanta tana "Sannu da zuwa Malam" Habiba ta ce

"Ina wuni Bappah" Bappah ya karasa ya zauna yana faɗin

"Fatsuma ba zaki daina tura yaran nan talla ba ne?" Tayi kicin kicin da Idanu ta ce

"Haba Malam, ina yanzu tallan ne ke rufa mana asiri, ina daga kai har matar ka duk da shi kuka dogara amma sai kana wani maganar kuma" wani kallo yake mata sai aka doka sallama daga bakin kofar, ya miƙe yana amsawa daga wajen mutumin ya ce

"An kawo gawayi ne, muna sauri zamu yi gaba" Bappah ya kalli Mama data taɓe fuska, sai ga Azrah ta fito Zahra na biye da ita a baya suka yi gate ɗin da sauri tana faɗin

"Ku shigo min da shi, gani zuwa"

Bayan ta karasa fita ta samu suna kokarin shiga da shi, matsa musu tayi har suka shigo mata da shi cikin compound ɗin ta irga kuɗin su ta miƙa masa, karɓa yayi ya irga ganin ya cika ya juya ya ce

"Toh sai da safe" sai sannan ta lura da Bappah dake tsakar gidan da murmushi a fuskarta ta ce

"Sannu da zuwa Bappah" Zahra ma ta juya tana gaishe sa.

Juye gawayin dukka tayi akan wani buhu ta shiga aikin kullawa a laida ita da Zahra, can Mama ta gagara hakuri ta fara masifa

"Gaskiya za'a daina kulla mana gawayi a gida, dubi yadda ake ɓata mana gida da gawayi"

Daga Azrah har Zahra ba wanda ya tanka ta

Suna aikin su cike da nishaɗi, can sai ga Siyama ta shigo tana waka da kayan tallah a hannunta, kamar wata ƴar tasha ta zuɓe akan tabarman tana faɗin

"Gaskiya yau nagaji Mama, dole gobe da safe ki barni nayi bacci gaskiya"

Mama ta ce "Dan uwarki tallan ma kice ba zaki ba daya fi miki" taɓe baki tayi tana kallon Habiba ta ce

"Ke tashi kije ki sako min abinci mana" Habiba ta ce

"Toh shine zaki wani cemin ke sai kace baki san sunana ba" ta karasa maganar cike ta tsiwa, Siyama ta sake baki tana kallon ta zata kai mata duka sai ga Bappah ya fito daga ban ɗakin hakan yasa ta miƙe zuwa ɗebowa da kanta tana faɗi

"Zan kama ki kuwa dan Uwarki"

Azrah har suka gama kulla gawayinsu ba tare da sun kalli direction dinsu ko kulasu ba

Tana shiga ta same Umma na zaune tana jan carɓi har sannan, Umma ta ɗaga kai tana kallon su ta ce

"Sannu da kokari, kuyi hakuri da rayuwar da kuke ciki yanzu, wata rana sai labari In Shaa Allah" Azrah taji hawaye na taruwa mata girgiza mata kai tayi ta ce

"Ki daina cewa haka dan Allah Umma, Ni buri na kawai ki samu lafiya ne" miƙewa tayi tana kallon Zarah ta ce

"Muje mu kwanta ko?" Zahra ta miƙe tana bin bayan ta suka wuce ɗakin su.

Kamar kullum Azrah ta gama duk wani aiki da tasan tana yi, ta kawo duk wani abu da Umma zata bukata ciki, kallon Zahra tayi wanda itama ta fito cikin shirin makaranta ta ce

"Dan Allah Zahra kuna tashi ki dawo gida kar ki tsaya a hanya saboda Umma ko?" Zahra ta gƴaɗa mata kai ta ce

"Toh Anty Azrah, ba zan tsaya ba" Ta na kallon Umma ta ce

"Umma Ni zan tafi, idan ana bukatar gawayi yana waje" Umma ta ce

"Toh Allah bada sa'a, Allah yayi muku Albarka" duk suka amsa da Amin sannan suka fita

Mama dake zaune tana abincin tallan ta ce

"Wallahi yau bari Bappahn naku ya dawo anjima, gaskiya ba waccan zata sake fita a gidan nan da sunan wai zata makaranta, dan Banga dalili ba ace sai nine zanna ciyar da ku" Gaishe ta suka yi, ta bi su da harara basu kuma bi ta kanta ba suka fita, Azrah ta kama hanyar makarantar su haka ma Zahra.

Mummy na kallon sa ta ce

"Magana fah nake maka Saif" Saif ya tamke fuskarsa jin maganar da Mummy ta gama dan ko kaɗan be kawo abinda zata ce masa ba, Suhaila dake danna wayanta ta ɗan saci kallon sa sai data kusan dariya dan ganin reaction ɗinsa, saidai ta ɗauke kanta ta cigaba da danna wayanta, Mummy ta ce

"It's Okay tunda ba zaka iya bani amsa ba, ka mayar dani banza ai" ya tsosa kansa ya ce

"Haba Mummy, how on earth zaki haɗani da wannan low class din, for that matter ma wannan teen ɗin" Sahulai bata san sanda ta fara dariya ba wani kallo ya wurga mata Mummy ta ce

"Ka dai bi duniya a sannu da hankali, dan naga kamar ka ɗauke ta da zafi nikuma dama shawara na kawo maka ganin yarinyar tana da hankali ga tsafta kuma kyakkyawa ce" taɓe bakin sa yayi ya miƙe ya bar parlorn, Suhaila ta ce

"Dan Allah Mummy karki sake ce masa komai, zamu ga kashen classic babe ɗin nasa ai"

"Hmmm" kawai Mummy ta iya cewa.

Yau ma kamar kullum, bayan ta dawo a makaranta ta gama shirin tafiya gidan Mummy ta fito tana sanye da Hijab ɗin ta, Zahra ta ce

"Anty yaushe zaki sake illoka? Kinga yadda ake tambaya a ajin mu kuwa?" Murmushi tayi ta ce

"Maybe idan na dawo yau, dan bana son kashe kuɗin" gƴaɗa mata kai tayi, mayar da kallonta ga Umma tayi ta ce

"Umma bari na tafi ko?" Ta ce

"Sai kin dawo, ki kula da hanya sannan ki kula da kanki dan Allah" kai ta gƴaɗa mata ta ce

"In Shaa Allah Umma" Umma tana miƙa mata ɗari biyu ta ce

"Gashi wannan ki hau abin hawa tunda Kinga jiya sunyi magana" Jim kaɗan tayi tana kallon Umma sai kuma ta miƙe tana faɗin

"A'a rike kuɗin ki Umma, akwai ɗari biyu a waje na" daga haka ta musu sallama ta fito ɗan karamar tsakar gidan na su, sai da gabanta ya faɗi kallon step bro ɗinta Abdul dake tsaye a kofar Mama yana binta da wani mayen kallo, tunda ta Kalle sa sau ɗaya ta ɗauke kai dan bata kuma bukatar ta sake haɗa ido da shi, sai data zo fita ba tare da ta Kalle direction ɗinsa ba ta ce

"Ina wuni" bata jira amsar sa ba tayi fice warta, wani a daidaita data gani yazo zai wuce tayi saurin taran sa da faɗa masa inda zai kaita dan ta gama tsorata da Abdul dukda bata yi niyyar tafiya da keke ba

#Jiddatulkhayr
08110615256
BEYOND THE VEIL
Hauwa Jibrin Sulaiman
(Jiddatulkhayr)

Young talented writers association (YOTA)


Free page

Episode 3: Ghetto, But not broken


Knocking babban gate ɗin tayi, gatekeeper ya leƙo ganin ta yasa ya buɗe mata, ta shiga tana

"Ina wuni Baba" ya ce

"Lafiya lau Azrah" daga haka ta shige

A daidai kofar shiga parlorn taci karo da Saif da shima yake ƙoƙarin fita daga parlorn littattafan hannunsa yayi watsi a ƙasa, da sauri taja baya tana zara ido dan bata san yana fitowa ba, ganin papers ɗinsa a kasa yasa da sauri ta duka ƙasa tana faɗi

"Dan girman Allah kayi hakuri Ya saif, wallahi ban sani bane"

Shi kam Saif with shock har sannan yake kallonta har ta gama tattara masa sannan ta miƙe cike da ladabi ta miƙa masa ganin bai karɓa ba yasa ta ɗaga kanta for the first time bayan incident ɗinsu ta Kalle sa, ganin wani irin kallo da yake mata yasa ta sake furta

"Dan Allah kayi hakuri, wallahi bansan kana fitowa bane" cike da izza sannan da tsansan kyama ya ce

"Are you doing this just to seek attention? So, ki cire ranki idan har wannan ne ke knocking a kwakwalwar ki, saboda ba zan taɓa cewa ina sonki ba, Stupid" ya ciro Handkerchief a aljihun sa sannan yayi wrapping hannunsa kafin ya karɓi papers da take miƙa masa ya bar wajan

Azrah tafi minti 2 kamar tana processing maganar sa, sai kuma ta juya ta bi inda ya bi da kallo sannan ta harare wajan sai yanzu maganarsa yake jiƙa mata dan ita ko kaɗan yadda ya nuna kyamarsa gareta bata damu ba ɗan karamin tsaki ta'ja sannan ta karasa cikin parlorn da sallama Suhaila ta gani zaune tana danna system ɗinta da murmushi a fuskarta ta karasa ciki ta duka ta ce

"Barka da warhaka Anty" sai sannan Suhaila ta ɗaga kanta tana kallon ta amma har sannan wannan murmushin beyi fading daga fuskarta ba ta ce

"Sannu Azrah, ya hanya da su Umma kuma?" A hankali ta ce

"Lafiya klau, duk Alhamdu Lillah" Suhaila ta ce

"Ma Shaa Allah" Azrah zata miƙe Suhaila tayi saurin cewa

"Wait.. ke da waye ne? naji kina bada hakuri?" Azrah ta Kalle ta sai kuma ta ce

"Ya Saif ne, ban sani bane na buge sa" Suhaila ta jinjina kai daga haka Azrah ta wuce kitchen dan ganin aikin da zata fara Suhaila ta bita da kallo tana cigaba da murmushi dan tasan dole Saif zai ɗauka da wata manufa tunda ɗazu Mummy ta gama masa maganar Azrahn.

Har Azrah ta gama aikinta tana jinta moody kuma tasan definitely abinda ya faru tsakanin ta da Ya Saifuddeen ne ya canza mata yanayi haka ta karasa aikinta sannan ba tare da walwala ba, bayan ta fito daga kitchen yayi daidai da shigowar Mummy, Azrah ta karasa tana karɓan kayan hannun Mummy meanwhile tana gaishe ta, Mummy ta amsa da fara'arta tana tambayar ta ya aiki.

Bayan ta gama ajesu a position ɗinsu ta koma parlorn tana kallon Mummy ta ce

"Mummy zan wuce gida" Mummy ta ce

"Miƙomin wayata akan Centre table na kira Suhaila ta kaiki naga garin da hadari sosai ne" Azrah ta wuce inda wayar Mummy yake ta ɗauka ta kai mata, Mummy na karɓa tayi dialing numbern Suhaila tana ɗauka ta faɗa mata tana neman ta a parlorn, ba'a ɗau lokaci ba sai ga Suhaila ta fito daga ɗakinta tana kallon Mummy ta ce

"Gani Mummy" Mummy ta ce

"Dama wai ko zaki kai Azrah gida ne naga garin da hadari" Suhaila tayi shiru ta ce

"Why not Yaya Deen Mummy? Kar na fita kuma ruwa ya sauko kuma Kinsan jikina baya son sanyi" Mummy ta ce

"Eh kuma fah haka ne" tun kafin ta karasa rufe baki Azrah ta katse ta da

"Mummy ina fita zan samu abin hawa Karki damu" Mummy ta ce

"Toh shikenan, Allah ya tsare" da Amin ta amsa sannan ta musu sallama ta fita.

Kura ake yi ga garin ya fara duhu sakamakon hadarin, a haka ta dinga tafiya tsoron kar ayi ruwa yasa kawai ta tsare keke ta shiga, tana isa unguwarsu ta samu already su har an idar da ruwan da aka musu, ta shiga cikin gidan nasu babu kowa a sakar gidan haka yasa ta wuce ɗakin Ummanta kawai, da sallama ta shiga ta samu Ummar na kwance Zahra na zaune gefen ta tana karatu da sauri ta karasa ciki tana faɗin

"Umma baki da lafiya ne?" Murmushi kawai ta mata ta ce

"A'a Azrah, kawai dai mura ne yake damuna Maybe saboda ruwan da akayi ne" Ayrah na kallon Zahra ta ce

"Zahra ko zaki tsiro mata magani ne?"

Zahra ta ajiye littafinta a gefe ta miƙe zata zo karɓa kuɗin sai kuma Ayrah ta ce

"Barshi ma kawai bari naje da kaina dama ranan da na tsiyama Umma magani ina binsa canci" Umma ta ɗaga kai tana kallon Azrah da har ta miƙe ta ce

"A'a Azrah ke da ko hutawa baki yi ba kuma ace zaki sake fita? Ki bari nace miki sanyin garin ne ya sake tado min da muran' Ayrah bata ji zata iya ba gaskiya kallon Umma kawai take yi.

Tunda hanya ta biyo da su wani ghetto area dake Kofar Marusa yake ta masifa yadda kasan wanda ke driving ɗin ne ya lalata hanyar can wanda ke driving ya ɗan juya ya Kalle sa ya ce

"Dan Allah Karka isheni da jarabarka, sai kace Ni na ɓata hanyar"

Sadeeq a ƙufule ya ce "Amma kuma ai kaika biyu da mu hanyar ko? Babu wani hanyar da zamu bi ne sai wannan for that matter?"

Sagir ya ce "Enough please, Ina kace kana sauri shi yasa na biyu da kai ta shortcut amma ji yadda kake ɗaga jijiyan wuya sai kace wanda na maka laifi" tsaki Sadeeq yaja ganin yadda motar nasu ke wani hawa da sauka suna wani rawa a motar sabar yadda suke bin ɓacaccen hanyar, can motar su ta kafe taƙi tafiya, Sagir ya juya yana kallon Sadeeq ya ce

"What is it?" Wani banzan kallon Sadeeq yama Sagir jin banzan tambayar da yake masa

Sagir yayi murmushi ya ce

"Ina ji motar gaskiya ba zata iya tafiya ba sai mun sauka a ga menene ne"

Sadeeq yayi humming kawai ba tare da ya Kalle Sagir ba sai ma danna wayan sa da yake yi, ganin haka yasa Sagir shima ƙwafa ya gƴara zaman sa a motar ya ciro wayansa yana ayyana a ransa yau zai gwada ma Sadeeq bashi kaɗai keda miskilanci da izza ba, they were like that for almost 10 mins

Can Sadeeq ya ɗaga kansa yana kallon Sagir ya ce

"Let me have the key tunda baka ga damar kaimu ba" Sagir ya masa wani kallo yana danne dariyarsa ya ce

"So, dama ka iya magana ne? Lokacin da nake tambayen ka ya zamu yi ai shareni kayi" ɗan kallon sa Sadeeq yayi ya ɗauke kai, jin ana shirin tada sallahr Magrib yasa ya Kalle Sagir ya ce

"Idan zaka iya sauka muje muyi sallah sai mu san matsalar motar toh" daga haka ya buɗe kofar ya fita ba tare da ya san ko Sagir ɗin zai sauko ba, Chemist dake gabansu ya nufa dan tsiya musu pure water da zasu yi alwala dan they're not sure ko masallacin da ruwa.

Azrah tafiyanta take a hankali tana bitan haddan da zata bada ran Saturday, hanyan Chemist ɗin ta nufa dan tsiyama Umma magani, gaba ɗaya she's out of thoughts dan can kasan zuciyarta tana tuna mata next year zata shiga SS3 ya zata yi idan kudin WAEC da NECO ɗinta bai cika ba, wani mota ne da yayi kanta horn ɗin da ya danna ne yasa ta yin tsalle dan kaucewa motar saidai ta faɗa cikin wani ruwa da-ya taru a kasa sakamakon ruwan saman da aka musu, ruwan yayi salle ya fesu a jikin Sagir, da sauri ya ja baya yana me buɗe baki yana kallon ta da mamaki ganin yadda ta ɓata masa kaya, Sadeeq ya taɓe baki ya ce

"This is just a glimpse of what the ghetto girls do, that’s why I hate interacting with them" (wannan kaɗan daga cikin abinda ƴan matan ghetto zasu maka kenan, shiyasa na tsani abinda zai haɗani da su kenan)

Azrah ta ɗaga kai tana kallonsa cike da ɓacin rai, dan ba kaɗan ba maganganun sa sun daketa ta ce

"Wait... Don't insult anyone, because not everyone would do such a thing, Poverty is not madness pls, Even me, it was a mistake and I only did it to save life not intentionally, Be guided, please"(Dakata... Kada ka zagi mutumin da baka sani ba, domin ba kowa ne zai aikata irin hakan ba, Dan talauci ba hauka bane, don Allah, Ni ma kuskure ne kawai nayi, kuma nayi shi ne don ceton raina ba da gangan ba, kasan me zaka faɗa gaba) sai kuma ta kalli Sagir dake tsaye shock clearly written all over his face ta ce

"Dan Allah kayi hakuri, bansani bane nayi hakan ne danna kaucewa motar ne" kai kawai ya gƴaɗa mata dan ya rasa ma me zai ce sai kuma ya kalli Sadeeq wanda yake tsaye har sannan shock dinta bai barsa ba ya kyalkyale da dariya ya ce

"Be guided please" sai kuma ya sake kwashewa da dariya, Sadeeq ya tamke fuskarsa ko alamar wasa bai bari ba, yana kallon mai shagon ya ce

"Ka bamu ruwan mana kar sallah ya barmu" Mai shagon da shima dramar su ya masa daɗi dukda cewa shi ma kame-kamen turancin yake amma saf ya fahimci duk abinda ke faruwa kuma yaji daɗin amsar da ta mayar masa ya ce

"Ai ranka shi daɗe kaff unguwar nan babu wanda ya kai yarinyar nan ilimi da iya turanci dukda a makarantar gwamnati take amma wallahi daban take, kar kayi mamaki dan kaga ta mayar maka amsan da Turanci" Sadeeq ya juya zai bar wajan mai Chemist ɗin yayi saurin cewa

"Yi hakuri Alhaji, ga ruwan abin duk bai kai ga haka ba" Har sannan Sagir bai daina dariya ba dan shima bai ɗauka tana jin turanci har haka ba, dukda ma shi akama laifi amma shi yanzu incident ɗin dariya yake basa ya sake kallon Azrah sannan yayi wajan mai Chemist ɗin ya karɓi ruwan yabi bayan Sadeeq da sauri dan ganin har an kusan ruku'u.

Azrah ta karasa wajan mai Chemist ta ce

"Maganin mura zaka ɓani da canci na da nake binka kwanaki" yana kallonta ya ce

"Nawa ne ma? Sannan wani irin maganin mura?".

A hanyar su ta komawa gida duk kalan masifan da Sadeeq yake ma Sagir akan yadda ya dinga ɓare baki yana dariya kamar wawa shine yafi bashi takaice, yana masa fighting right dinsa amma jibi yadda at long last ya basa kunya

Sagir ya ce "Like seriously yarinyar bata burgeka ba?" Wani kallo Sadeeq ya wurga ma Sagir wanda shi hakan dariya ma yake kara basa, dakyar ya sauya kansa meanwhile yana tuki ya ce

"And she's so beautiful ya Allah" Sai sannan Sadeeq ya Kalle sa ya ce

"Toh ai ba muyi nisa ba zamu iya komawa wajan mai Chemist ɗin sai ya kaimu gidan su yarinyar ko?" Sagir ya ce

"Wallahi zan so fah, da gaske na juya kan motar zuwa wajan?" Wani kallo da Sadeeq ya sake jefa masa yasa ya fara dariya ya cigaba da driving ɗinsa kawai.

Tun daga bakin kofar gida Bappahn ya fara doka sallama har ya shiga cikin ƴar sakar gidan nasu wanda duk sanda ya shigo yana doka sallama sunsan wani abu ne ya faru

"Fatsuma!" Ya daka ma Mama kira wanda hakan yasa ta fito da sauri tana kallonsa ta ce

"Lafiya Malam?" Wani kallo yake mata ya ce

"Ina Abdul yake?" Ta buɗe masa hannu alamar bata sani ba ta ce

"Kaga Malam rabona da shi fah tun da safe"

Bappah ya ce "Toh ki sani ki jama ɗanki kunne idan ba zai natsu ba zai barmin gida gaskiya, ace kullum idan aka tashi kwatancen yaran unguwar nan marasa jin magana toh Abdul na ciki, yanzu ace wai Jiya da daddare ashe sunyi kokarin shiga gidan wani fah? Hakan ya dace ne Ni shikenan bani da ƙima balle daraja a idon duniya?" Mama dake masa wani kallon sha tara ta ce

"Haba Malam sai ka gama tiririn ɗan naka ne a duniya kafin ka rufa masa asiri?" Ya ce

"Toh shikenan, ki cigaba da zancen rufa masa asiri wallahi Karki sa baki a mummunan matakin da zan ɗauka a kansa" daga haka ya wuce fuuu sai ɗakin sa.

Siyama ce ta shigo da sallama kamar mara gaskiya tana bin gurin da kallo ganin baya nan ta ce

"Mama ina Bappahn?" Mama ta taɓe baki ta ce

"Ke kuma me na wani abu kamar mara gaskiya" ta ce

"A'a nikam ki kyale Ni, bana son jaraban Bappah" daga haka ta wuce ciki ta bar Mama da bakin cikin abinda Bappah ya gama mata kuma tasan definitely Umma ta ji su, wani dogon tsaki taja sannan ta wuce cikin dakin ta.

Har kofar gida Sagir ya sauke Sadeeq wanda har suka je inda zasu suka dawo bai sake kula Sagir ba, bayan ya sauka zai kulle car door din Sagir ya ce

"Good night Aboki, please be guided" Sadeeq ya tsaya yana kallonsa sai kuma ya ce

"Look! Idan har ba zaka daina shirmen nan naka ba wallahi ba zan sake haɗa hanya da kai ba balle wani aiki ya sake haɗa mu" Tun kafin Sagir yayi magana ya wuce zuwa babban gate ɗinsu wanda gidan sai ka ɗauka a wata kasar take.

Umma sai kallon Azrah take wanda tun ɗazu tayi tagumi, kana ganin ta kasan yau tana moody, Umma ta ce

"Damuwar me kike saka ma kanku Azrah? Kina bukatar wani abu ne?" Azrah ta sauke hannunta da tayi tagumi tana kallon Umma ta ce

"Nothing fah Umma, kawai dai na gaji ne" Umma ta ce

"Toh tashi kije ki kwanta, Kinga ƴar uwarki kam ai ta kwanta kuma ke kike bukatar hutu" ta girgiza mata kai ta ce

"Idan na kwanta kuma aka zo siyan abu kuma fah Umma?" Umma ta ce

"Sai na fita na bayar" Azrah tayi murmushi dan ita a kalan tausayin Umma da take ji ba zata bari tana aikin wahala ba saboda kar kanta ya fara ciwo balle har taje ta fama ma kanta matsala, ga kuɗin aiki wajan 30Mil ta'ina zasu fara, kamar Umma tasan tunanin da take yi ta ce

"Ai ba zan yi hayaniya ba balle har kan ya fara ciwo Azrah, balle ma kwanan nan ma ai kan yana ɗan ciwo amma ai yana tafiya kuma ba tare da ciwon ya ta shi ba" Azrah ta ce

"Toh Allah kara miki lafiya Umma, burina nayi karatu na samu kuɗi da za'a rabaki da wannan ciwon ne" Umma ta ce

"Amin, Allah cika miki buri".

Har Azrah ta kwanta amma kuma sai ta kasa manta da maganar wannan strangern ga kuma Ya Saif, haka kawai taji ta tsane su with passion, wato talaka bashi da wani ƙima ko daraja kenan? Wato talaka bashi da aiki sai zama mutumin banza? Wannan ne babban burinta na son cinma buri a karatu saboda ko dan kujewa irin wannan wulakanci, tasa hannu ta share hawayen fuskanta sannan ta miƙe zaune tayi addu'an bacci ta gama shafe jikinta ta kwanta.

Washe gari tun safe Mama ta ɗaurawa Habiba tallah, wanda Siyama na gefenta suna dafa abinci da itama zata fitar tallah.

Azrah dake kallon Umma ta ce

"Umma toh barin tafi kasuwan ko da wani abun da kuma zaki bukata?" Umma ta ce

"A'a babu Azrah! Allah tsare min ke" ta amsa da

"Amin" a compound taga Mama da Siyama suna ta girki suna magana, a hankali ta ɗaga kai tana kallon Mama ta ce

"Ina kwana" Mama ta ɗago tana mata wani kallon banza ta ce

"Karki fita ko ina, ki dawo dan yau dake za'a je tallah gareji sai dai ki mutu amma sai kinje"

Azrah taji hawaye yana shirin taruwa mata, amma ta hana kanta haka, tayi wucewar ta kofa ba tare da ta sake kallon Mama ba dan tana jin wallahi ko dukan mutuwa za'a mata ba zata tallah gareji ba, sai kace ƴar iska mara kunya.

#Jiddatulkhayr
08110615256


Free page

Episode 4: Beneath the surface

Mama tabi Azrah da kallo baki buɗe har ta fita, ta fara tafe hannu tana salati ta ce

"Yau Ni Azrah zata ma rashin kunya? Har ina mata magana zata iya tafiya ta barni tsaye? Saboda ganin bani na haifeta bane ko kuma so take ta nuna min cewa ban isa da ita bane" Siyama ta ce

"Ai dama za'a rina, yanzu gani take ai tafi ƙarfin tallah balle tayi, mune dai ya zama mana dole" Mama ta ce

"Wallahi bari Bappahn ku ya dawo, zanyi maganin ta sai dai idan har ta daina cin abincin gidan nan ne" Siyama ta ce

"Toh Kema Mama ai Kinsan ba zata ba kika tsaya ɓata bakin ki a banza, baki ga kalar fatarta bane, ai gani take ita ƴar hutu ce mune dai ƴan wahala" Mama ta tamke fuska ta ce

"Toh me a fatar nata?" Siyama ta ce

"Yanda yake sheki mana, Kema Kinsan Manyan maza ne ke siya mata waɗannan sabulun turawan mai uban tsada, kuma Kinsan maza basu kashewa mata kudi haka kawai wlhi" Mama ta fara dariya ta ce

"Ai kuwa Nima har sannan mamaki baya barina sai na ratsa aina take samun su, Ahap ba sunce ita ƴar boko ba? Muna nan mu zuba da su saita kawo musu abin kunya, waye kuma bai san Matan boko ba?" Siyama ta miƙe tana faɗin

"Ai muna kallon su kuwa".

Ba Azrah ta dawo gida ba sai wajajen karfe 11am a mugun gajiye ta karasa cikin gidan nasu wani almajiri yana biye da ita rike da wani bakko a kofar ɗakinsu ta ajiye na hannunta sannan ta karɓi na hannunsa ta fara kaiwa ciki, ta kuma fitowa ta basa laɗan aikinsa sannan ta karasa ciki ta zauna kan laidar dakinsu tana kallon Umma dake zaune tana karanta wani lissafin musulunci, Umma ta rufe littafin tana kallonta ta ce

"Sannu Azrah, kinsha wahala kam" ɗan murmushi tayi ta ce

"Sannu da hutawa Umma" fara cire kayan bakkon tayi tana nunawa Ummanta kayan da tayi tsari tana faɗa mata kuɗaɗen su Umma ta ce

"Ɗazu naji kamar kun sami matsala da Mama?" Nan da nan annurin fuskarta ya washe tana kallon Umma ta ce

"Kiji fah Umma, wai tallah gareji zata bani na kai mata, nikuma nasan ba zanyi ba shiyasa kawai nayi tafiya ta" Umma ta ce

"Kinyi min daidai dan Banga dalili ba, idan Nima ina son na saki tallan ai da tuni na fara turaki amma dake bana son yarana suna tallan shiyasa ban fara barinku kuna yi ba tun farko, sai dai kawai yadda naga tana masifa na san dole zata haɗa ki da Bappahn kune sai kisan me zaki ce masa" Azrah ta ce

"Toh shikenan" Umma ta ce

"Miƙamin laidan sai na fara kulla busheshshin kayan miyan, kawai ke kije ki shirya ki tafi gidan da kike aiki Karki yi rana tunda yau baki je boko ba, danma suna hakuri ne kawai wlhi" Azrah ta miƙe ta bawa Umma laidar daga haka ta wuce cikin ɗaki ta fara shiryawa, har zata sa wani ƙuncen Abayan Anty Suhaila data bata sai kuma ta fasa tunda aiki zata no need kawai ta sanya wani riga da skirt ta ɗaura hijabinta daya ɗan koke ta fito tama Umma sallama sannan ta fita.

Tunda ta shiga parlorn taga Saif yana zaune babu kowa hakan yasa ko kallon direction ɗinsa bata yi ba ta kama hanyar kitchen ya ce

"Ke kuma haka aka baki tarbiyya baki iya gaisuwa ba?"

Tayi kamar bata ji sa ba, cos kawai dan tana aiki a gidansu ne kuma yaron Mummy ne amma da sai ta faɗa masa bakar magana akan bakar maganar daya gaya mata jiya dan sai yanzu abin ke kara jiƙa mata kuma ta ɗau alwashin koda wasa ba zata kara Gaishe sa ba balle ya sake cewa tana son jan hankalin sa ne gareta, attention ɗinsa take nema, harta shige kitchen bata Jiyo ba ya bita da kallo baki buɗe, sai kuma yaji takaicin magana da yayi dan wannan raini ne ma gashi baya so wani abun ya sake haɗasa da ita, yayi dana sanin maganar da ya mata yafi cikin ƙwando

Harta gama girki ta fitar kan dinning bata ga Mummy da Suhaila ba, hakan yasa kawai ta girka abinda tayi kwana biyu bata dafa musu ba, tana gama duk wani activities dinta na gidan ta fito parlorn da niyyar tafiya, idonta akan na Saif dake dining ɗin yana cin abinci ya faɗa, da sauri ta ɗauke kanta daga haka ta fita a Parlorn tana mamakin ai kyankyaminsa na banza ne, idan har yana kyamarta akan meyasa zaina cin girkinta ita wannan abin ne yafi bata dariya da tasa kalar saftan.

Tafiya kawai take abinta ba tare da komai ba, sai dai kawai tunanin yaushe zasu gama wannan wahalar a duniya? Few houses da gidan Mummy ta kalli wani mota na parke shima gidan ba karya ya haɗu fiye da tunanin me tunani maza uku na jikin motar da alama dai hira suke, ita dai kullum ta shigo unguwar nan sai tayi fatan suma Allah ya basu koda ƙwatan waɗannan ɗinne.

Kamar ance ɗaga ido kawai idonta ya sauka a cikin nasa, ta gane sa clearly, dan babu ko wani doubt tasan shine tamke fuskanta tayi zata ɗauke kai sai kuma ya sauka a cikin idon Sagir, wanda shima clearly ya gane ta, da sauri ya taɓa Sadeeq ya ce

"Be guided please, gata can" sai kuma ya kwashe da dariya dan shi abin na mugun basa dariya dan duk duniya babu me iya faɗawa Sadeeq magana sai Mami, amma sai gashi ƴar yarinya ta faɗa masa, kuma babu shakku balle nadama saima lots of confidence da take dashi

A fusace Sadeeq ya zuya yana ma Sagir wani kallo ya ce

"Enough please, wait... Do I have any business with her? Ko dai kana neman hanyar da za'a haɗa ka da ita ne?" Sagir kallonsa kawai yake ganin How serious he is

Al'amin ya ce

"She's beautiful, girlfriend dinka ne Sadeeq?" ya kare maganar in very calm tongue, Dan shi bai san abinda ke wakana ba, a mugun fusace Sadeeq ya shige motarsa ya kunna motar wanda kawai figarta yayi da gudu har sai da Al'amin ya matsa masa ganin zai iya buge su, ya bisa da kallo sannan ya maida kallon sa kan Sagir ya ce

"Me amfanin hakan da yayi?" Sagir ya ce

"Alakanta sa da ita da kayi ne ya basa haushi, baka ji yana tambaya yana da business ne da ita ba?" Al'amin ya taɓe baki ya ce

"So? And isn't she beautiful ko dan nayi admiring ne yaji haushi? Sagir ya ce

"Nace maka dan ka haɗasa da ita ne fah yaji haushi" taɓe baki Al'amin yayi ya ce

"Then, shi yaji wajan, amma ai wannan tafi ƙarfin sa".

Azrah dake tafiya taga wucewar motarsa kamar wanda zai tashi sama dan bata san sanda ta koma gefe da gudu ba, sai kuma ta bisa da harara tana taɓe baki.

Da yamma tana karatun babu kowa a ɗakinsu dan Ummar da Zahra sun fita, a cewar su tana ɗan zaga unguwar kar zaman gida kullum kuma ya jawo mata wani ciwon gwara tana excerses

Muryan Mama taji ita da Bappah ga Habiba ma dake sa baki, amma ta gagara sanin akan me suke magana, haka kawai yaji hankalin ta bai kwanta da wannan maganar nasu ba saboda yadda tasan yau kuma ita da Mama sai Allah, rufe littafin tayi ta maida hankalinta tana sauraron su, Bappah ya ce

"Toh ke Fatsuma ai shikenan tunda taki tallan kawai ki kyaleta" Mama tayi wani ashar ta ce

"Kana nufin duk iskancin data min da nuna min ban isa da ita a ya tafi a banza kenan? Harda buga ɗan karamin kofar mu da muƙe managing ɗinsa fah, ace ai ko bata sanni ba bai kamata ina mata magana tayi wucewarta ta barni tsaye ba, Ni kayan takaicin ma yadda ta gaggayamin magane yafi komai ɓata min rai" Bappah ya ce

"Bansan sau nawa kuma zance kiyi hakuri ba, maganar tallah kuma tunda tun farko Uwar bata so shikenan, amma dole zan ɗau mataki akan yadda tayi miki ai" Mama ta masa wani kallo ta ce

"Toh gaskiya Malam sai dai Matar ka da yaranka su fara girkin su amma Ni gaskiya nagaji, Ni nawa yaran ba sonsu nake ba da nake tura su tallah ai, wato nata yaran ne ƴaƴan gata ko? Wallahi na daina saka musu abinci daga yau ɗin nan" Bappah ya ce

"Haba ke kuwa Fatsuma, ai abin duk bai kai haka ba, tallah kuma tunda kince sai sun fara zuwa ai wannan dole ne, dole ne sai sunje amma sai dai kar ana shiga hakkin lokacin karatun su tunda suna zuwa makaranta" sai kuma ya shiga ƙwalawa Azrah kira

"Ke Azrah! Kina ina ne ina magana ba zaki fito ba" Azrah dake sauraron su ta ajiye littafin hannunta ta share hawayen daya gangaro mata she wish Umma na nan, ta miƙe jiki babu ƙwari, jin ya sake doka mata kira yasa ta ce

"Na'am Bappah gani fitowa" Muryan Mama ne ya biyo bayan nata tun kan ta rufe bakin nata ta ce

"Dan uban ki ana magana ba zaki fito bane ko sai na shigo na fito dake" buɗe labulen kofar tayi ta fito koda wasa bata kalli direction ɗin Mama ba tana kallon Bappah ta ce

"Bappah gani" Bappah ya ce

"Kema yanzu kin canza hali ko? Akan wani dalili zata na faɗa miki magana kice mata A'a sannan tana miki magana kawai sai ki tafi ki barta a tsaye? Haka ake yi ko kuma Uwarku ce ta koya miki" Azrah ta share hawayen daya gangaro mata tana kallon Bappah ta ce

"Bappah nifa ban mayar mata da magana bafa, kawai nace Ni ba zani tallah bane kuma wai tallan a gareji ba zan iya zuwa bane Bappah shiyasa nace A'a , amma kuyi hakuri dan Allah" Bappah na mata wani kallo ya ce

"Kin kyauta ma kanki, yanzu daga yau zaki fara tallan kema kinji? sai kar kuyi nisa"

"Babu tallan da zata yi dan Banga wanda zai ɗaurawa Azrah tallah ina da rai ba" Murya Umma ya dake kunnuwan su wanda basu lura da shigowa nata ba ga kuma Zahra a gefenta, karasa cikin sakar gidan tayi tana kallon Bappah da mamaki dan tasan shima baya son tallan nan amma ji lokacin guda ya yarda, Mama ta katse mata tunanin ta

"Ai ita take ɓata yaran Malam, ba'a isa a ɗau mataki akan su ba sai tace ita kaza, ga ita mai ƴara ba" Mama ta kalli Zahra dake gefen Azrah ganin yayarta na kuka yasa itama farawa ta ce

"Azrah kama hannun kanwarki ku wuce ciki" Azrah ta juya Zahra na biye da ita a baya

Umma tana kallon Habiba dake zaune sai washe baki take tana dariya ta ce

"Kema Habiba tashi ki wuce ciki" Habiba ganin Bappah yasa ta ɗan ɓata rai ta wuce ciki tana gunaguni

Mama na kallon Bappah ta ce

"Malam kayi hakuri amma gaskiya I'm very disappointed in you, ace har zaka yarda a tura yaranka tallah? Idan har ina son suyi tallah da tuni na fara ɗaura musu, ko Azrah dake sana'a iri da kala naga a gida take yi sai dai wasu lokutan a fitar kofar gida amma rana tsaka kace zata fara fita tallah" Mama ta riƙe kugu tana kallon Umma ta ce

"Toh sannu Uwar Agwagwa, ai ta gwada bata so ina Kema zaki so" Umma ta ce

"Tabbas kuwa ba zan so ba" Bappah yana kallon dukkan su ya daka musu tsawa, Mama ta ce

"Shikenan Malam tunda har abin haka ne, Ni kuma daga yau na daina abinci dasu, su koma girka abincinsu su daina dogara da Ni" Bappah zai yi magana Umma ta rika sa

"Baki san abinda nake addu'a akai ba kenan? Dama taya idan banda zalunci ace kece zaki na girki sai kinga dama ki tsokara mana sannan kuma ki haɗa da gori, wallahi tafi Nono fari a waje na" Bappah ya ce

"Yanzu ke da kike murnan an raba girkin ya zakiyi, kin samu ana rufa miki asiri shine kike da bakin magana ko?" Ta ce

"A'a ta rufa maka asiri dai, sannan ai dama cinmu da shanmu a kanka yake Malam, dan haka sai ka fara providing mana muma" Mama da shock take kallonta dan bata ɗauka hakan daga gare ta ba, taso ta bata hakuri ne

Ita kuwa daga haka ta juya ta wuce ciki, tana shiga Azrah tayi kanta da sauri tana faɗin

"Umma kiyi alwala ki zauna da shirin ki ana magrib sai ki kwanta ki huta Kinga kinyi magana dayawa Ni tsoro na ma kar ciwonki ya tashi ne" Umma na Murmushin karfin hali ta ce

"Karki damu Azrah, ba zai tashi ba In Shaa Allah" daga haka ta wuce ta kwanta akan dadduman dake shimfiɗe a Parlorn.

Har dare yayi Mama bata kawo musu abinci ba, Azrah dake zaune ta kalli Zahra ta ce

"Zahra zo ki raka Ni" Zahra ta mike tare suka wuce kitchen ɗin, tuba tsohuwar mukubur ɗinsu sukayi suka fito dashi fili, Azrah ta ɗauki gawayi a wanda take sayarwa ta hura wutan, ta wuce ɗaki bata daɗe sosai ba ta fito tana mika ma Zahra kuɗi ta ce

"Zahra je ki tsoho mana taliya laida ɗaya sai a sa miki mangyaɗa gwangwani ɗaya kinji? Kiyi sauri dan Allah" Zahra ta amsa da "toh" ita kuma ta zauna nata cigaba da fifita wutan.

Bayan sun gama girkinsu suka shiga ciki da shi, mikawa Umma suka yi, Umma ta ce

"Amma mayasa kika tsaya Azrah? Azrah ta ce

"Toh haka zamu kwana da yunwa Umma? Ai abinci dole ne" Umma ta ce

"Toh ai naga a cikin kudin kine Azrah, kuma bana son kina taɓawa saboda gaba" Azrah ta ce

"By then, Allah zai kawo mana wani In Shaa Allah" Umma tayi shiru tana kallonta, suna kan cin abincin sai ga Bappah ya shigo, Umma ta ce

"Sannu da zuwa" ya amsa da "yauwa" yana kallon su Azrah ya ce

"Ku shiga ciki ko?" Ta shi sukayi suka wuce ciki, ya maida hankalinsa ga Umma ya ce

"Amma mayasa zaki ce kina son zakuna girkin ku?" Wani murmushin takaici Umma tayi ta ce "Toh dama ai ba zamanta nake ba, kuma ai ba ita ya kamata ta ciyar da mu ba" Bappah ya ce

"Toh ai zamana kike kuma Ni na tsara hakan" Umma ta ce

"Yanzun saboda gudun karka na tsiyo mana kayan abinci ne yasa kake son naje na bawa matarka hakuri Malam? Lokacin da ka dauki kuɗin da ka siyar da machine dinka ka bata da niyyar tana juyawa ana samun wanda za'a ci Ni ka tambayi shawara balle kuma ka bani Nima ina juyawa? Amma ai gashi kullum gori da kuma gadara da akan ita take ciyar damu ya ishe Ni, kaima sai kayi hakuri akwai ka cigaba da siya mana namu muna yin sa daban" Bappah yayi shiru yana kallonta.

Duk kallon Daddy dake bayani suke, a hankali Saif ya ce

"Amma ai Daddy Suhaila ya kamata ama magana saboda Normally mata na riga maza aure amma tana her late 20s sai ni kaɗai" wani kallo Daddy ya masa, Mummy ta ce

"Deen yaushe zaka daina haɗa kanka da kanwar ka ne wai?"

Daddy ya ce "Saboda ita macace idan miji bai zo ba ba ita zata je ta nema ba, kai kuma na miji ne, a haka ne kake son na ɗaura ka akan business Dina ba tare da kana da aure ba? Ai hankali na ba zai kwanta ba ina turawaka different countries" ya ɗan kalli Daddy shi ya tsane anything pertaining wannan so called company, ya fiso independent life ne amma ba zasu gane ba.

#Jiddatulkhayr
08110615256
*BEYOND THE VEIL (LABULEN SIRRIN)*


YOTA ID/026

Wattpad © Jiddatulkhayr
Instagram © Jiddatulkhayr writes

Free page

Episode 5: When hope seems lost

Azrah data fito sanye da uniform ɗin makarantarta tama Umma sallama harta tafi bakin kofa kuma ta tsaya ta juyo tana kallon Umma ta ce

"Dan Allah Umma kar kice zakiyi girki ko wani aiki, Kinga ba'a son wani abu da zai sa ciwonki ya tashi ko ya jawo miki ciwon kai" Umma tayi murmushi ta ce

"Naji Azrah, Allah muku Albarka, ki tafi kar kiyi latti ko?" Azrah ta gyaɗa ma Umma kai ta nufi kofa.

Azrah tunda ta isa makaranta, ta lura da yanayin da ya ɗan sauya, An taru a harabar makaranta yayin da Principal ke magana da ɗalibai

"Ku sani tun kafin ku shiga SS3, dole ne a biya kudin candy, Wannan tsarin ne tun daga sama, kuma ba za mu ɗauki ɗaliban da ba su biya ba idan har an rufe"

Maganar tayi nauyi sosai a zuciyar Azrah. Candy din dai wani nau'in horo ne na makarantarsu kafin jarrabawar WAEC, kuma kudinsa yana da ɗan yawa sai dai bai kai kuɗin WAEC ba, amma idan mutum yaci za'a tura sunan sa ga gomnati ya biya masa WAEC da NECO

Sai dai kamar yadda aka santa, Azrah bata bari damuwarta ta bayyana a fuska ba. Ta cigaba da sauraro cikin natsuwa, amma zuciyarta cike take da nauyi tana kokarin hana kanta hawaye,

Gaba ɗaya wannan ranan haka ta wuni a school babu wani laƙƙa a jikinta dan ita sanmaninta sai anyi 3rd term ne zasu biya.

A hanyanta na komawa gida, bata ma lura da abinda ke faruwa a gabanta tafiya take absent-minded ko hirar da kawarta Fatima take mata da 'Em.. eh.. A'a" take amsa mata ba tare da tasan tana hakan bama. Kamar wacce aka kunna ma zuciyarta wuta ko aka zare fahimtarta"

Tana isowa gida, taji aroman girkin Umma, ta karasa ɗakinta, ta aje jaka da schl stuff, sannan ta fito da sauri zuwa kitchen dan bata ga Umma a main spot ɗinta ba, A nan ta tarar da Umma tana tuka tuwo

"Umma! Na gaya miki fa ba'a so ki na aiki! Kina so ki fama ciwon kai naki ne? Dan Allah ki daina! Ki ƙoma ciki ki zauna ki huta mana!"

Umma ta juyo da murmushin mai laushi ta ce

"Na gama yanzu. Bari na koma daki Azrah" Azrah ta ɓata fuska tana kallon Umma dake mata murmushi

Da ta juya ta fita, Azrah ta bi bayanta cikin sauri, tana shiga ɗakin, ta zauna kusa da Umma tana kallon ta idon ta cike da damuwa ta ce

"Umma yau a makarantar mu wai mu tanadi kuɗin candy saboda a wannan term ɗin zamu yi kafin mu shiga SS3 duk wanda yaci shi gomnati zai biyawa kudin jarabawar waec da neco" Umma tayi murmushi ta ce

"In shaa Allah kina cikin wanda zasu ci Azrah, na yarda da addu'a sannan na yarda da ke" Azrah na kallon Umma kamar bata fahimci me take nufi ba, a hankali ta ce

"Umma kamar baki gane ba, zamu biya kudin candyn ne yanzu fah, toh ni da nake tara kuɗi akan sai na shiga ajin karshe ne, amma yanzu zamu biya" Umma ta sauke ajiyar zuciya ta ce

"Azrah, ki kwantar da hankalinki kinji? Ai tunda Bappah ya ce ya bawa Mama kudin WAEC ɗinki, danta juya jari dashi ai akwai sauki, Zamu samu mafita in shaa Allah" Azrah ta ɗan saki ajiyar zuciya

"Toh Umma, ni dai na yanke shawara zan fasa asusun nan nawa, Ko da bai ishe ni ba, amma zan yi ƙoƙari, Ni bana so wannan damar ta wuce ni saboda kuɗi"

A dai-dai lokacin Zahra ta turo ƙofar da sallama a bakinta, bayan ta gaishe su ta tsaya binsu da kallo sai kuma tayi dariya ta ce

"Kamar dai magana mai muhimmanci kuke ko?... Me ke faruwa?"

Azrah ta ɗan ƙalleta, bata da niyyar faɗa, sai dai Zahra ta matsa har taji labarin

Zahra ta haɗa gira ta ce, "Ai ni dai bazan lamunci a hana Azrah karatu ba saboda kuɗi, dole Mama ta amo da kuɗin da Bappah ya bata tunda ya hana miki Umma, ko kuma wallahi shi Bappahn zai sake bada wani" ta kare maganar ranta a ɓace

Azrah ta dubi 'yar uwarta, zuciyarta na sauƙa kaɗan Kodayake har yanzu bata da tabbacin yaya zata magance matsalar candy idan Mama ta ce 'Aa' kuma tasan zata iya dan bata damu da karatun nata yaran bama, idan Bappah ya ce bashi da kuɗi kuma fah? amma kalaman su Umma da Zahra sun rage mata nauyi a zuciya.


Da Rana bayan ta dawo daga makaranta, tana cikin shirin fita gidan Mummy sai Umma ta kirata ita da Zahra, suna zauna ita da Zahra a dakin suna kallon Umma, Umma ta kalli ‘yayanta da nutsuwa ta fara da

"Ku sani rayuwa ba zata taɓa zama daidai da yadda muke fata ba, ku kalli mahaifinku a baya da yadda yanzu kuma rayuwa ta canza masa, Amma duk da haka, kada ku taɓa rasa bege, Idan kun wayi gari da lafiya, ku gode wa Allah, sai dai yana da kyau kuma addu'a da positive thoughts, Rayuwa karshen ta ba komai bane, komai sai dai a barshi..."

Muryarta ta yi rauni yayin da kalmomin ke fita kamar ana taune su, Zahra ta lumshe ido, Azrah kuwa bata ce komai ba, amma zuciyarta cike take da ɗumbin damuwa, Kalaman Umma sun shiga zuciyarta fiye da yadda take sammani, amma gaba ɗaya sai suka sinci kamar wani abu na shirin faruwa dasu ne,

A haka ta tafi gidan Mummy kamar kullum, tana shiga compound ɗin, sai ga Saif, yana shirin fita, matsawa gefe tayi ta wucesa ba tare da ta gaishe sa ba, with shock ya dubeta daga sama zuwa ƙasa da kallon rainin da yake ma mutane, tasa kai ta wuce cikin gidan amma sai haka kawai take jin bata kyauta ba.

Kamar yadda ta saba, ta nufi kitchen tayi wanke-wanke, shara, sannan ta daura girki, Amma yau akwai wani abu dabam, Tana jin wani nauyi a zuciyarta, yadda taga gidan kamar an tattara wasu kaya, sai kuma take tunanin ko kalaman Umma ne suka dame ta? Ko wani abu ne ba ta iya fassarawa ba?

Bayan ta gama, ta fito parlour, inda ta tarar da Mummy da Suhaila suna zaune, ta musu sallama da murmushi, suka amsa, amma yau murmushinsu kamar dole ne, Yanayinsu ya nuna babu annuri, Hakan ya sake tsinka zuciyar Azrah bata tsaya tambaya ba, ta tafi gida.

A gida, ta tarar da Mama tana zaune a tsakar gida tare da ‘yan matanta Habiba da Siyama suna lissafin kuɗin tallar su, Azrah ta gaishe da Mama da ladabi, amma sai ta amsa a wani duƙule

"Duk wanda ya ɗaukawa kansa rayuwar boko, daga ƙarshe sai ya zama ɗan iska gashi dai muna ganinsu a gari, duk jariran da ake yarwa a titi nasu ne" Habiba da Siyama suka kwashe da dariya

Azrah ta share, ta riga da ta saba da irin maganganun Mama, ta wuce zuwa dakin Umma, sai dai a bakin ƙofa taji kukan Zahra dake durƙushe a baƙin kofar

"Zahra, meya faru?!" Ta tambaya cikin firgici

"Umma... tunda kika tafi gidan Mummy bata da lafiya, yanzu ma tana kwance…"

Bata jira cikakken bayani ba, ta fita da gudu, ta nufi cikin ghetto area ɗin unguwarsu, can inda ta san Bappah ke zama kusa da masallaci wato majalisarsu ta nufa, tun daga nisa tana hango shi, ganinta yasa ya miƙe nan ta sanar masa ba tare da bata lokaci ba, Bappah yaje ya sayar da mai adaidaita suka ɗauki Umma suka fito da ita wanda idonta a kulle bata son haske ko kaɗan

A nan sakar gidan sai ga Mama dake sanya ta juyo ta Kalle su sai kuma ta taɓe baki ta ce

"Ni wallahi banda cin kuɗin mu a hanyar asibiti! Ban ga komai ba da zaku rika wahalar da jama'a Ciwon kai ne ko mutuwa ce? Ciwon talakawa ma ai masifa ce, da ci za'a ji ko da kuɗin asibiti! Ki dai mutu ki huta da wannan ciwon naki!"

Zahra dake kuka ta tsaya cak ta ce

"Zafin ciwo ai ba mutuwa bane, wanda yake da lafiya ma sai ya mutu ya bar wanda yake jinya sa duk ikone na Ubangiji"

Da shock suke kallon Zahra, Azrah ta kama hannun Zahra zuciyarta na ƙuna dan bata da lokacin saɓani, yanzu burinta tana son Umma ta samu lafiya ne.


Kekensu na tsayawa a cikin asibitin Nurses suka fito da gadon emergency, suka tarbe su cikin gaggawa Umma na kwance a kan gadon hannu, zuciyarta na bugawa a hankali. Azrah da Zahra na binsu a baya, Bappah na kokarin danne damuwarsa shima

Bayan an shigar da Umma ciki, wani nurse ya fito yana tambayar wanda zai karɓi bayani

"An gano high blood pressure da strong migraine ne, kuma yanzu tana buƙatar magunguna masu ƙarfi da jinya ta musamman Za'a buƙaci a sayi magunguna, sannan za'a duba kansu da CT scan domin tabbatar da cewa ba ciwon brain tumour natan bane ya kara girma..."

Maganar ba ta gama fita daga bakin nurse ba, ya mika wa Bappah takarda, Azrah ganin Bappah yana tsaya kawai karɓa ta karɓi takardar da hannunta mai rawa, ₦89,500 Tana kallon amount ɗin kamar bata fahimta ba Idanunta suka kada da hawaye

"Zahra…" ta kira da muryar da ta karaya, Zahra kudin nan… babu shi."

Zahra ta matso kusa, itama hawaye na bin kuncinta ta furta

" Bappah fa? Ko Mama?" Ta kare maganar tana starring Bappah da manyan idonta

Azrah ta girgiza kai, ta kalli nurse din da har yanzu yana jiran su

"Please… just start with something, we will get the money" ta ce da muryar da ta cika da fargaba da kuma rauni

Nurse din ya girgiza kai. "We'll wait for the deposit Ma, We can’t administer some of the medication without it"

Azrah ba ta san lokacin da hawaye suka zubo mata ba, tayi saurin juyawa ta fita daga asibitn ko sake waiwayo Bappah batayi ba, zuciyarta na tsinke

A bakin asibitin, ta zauna a jikin bango, tana kokarin shan iska da tunanin ina zata fara zuwa? Amma numfashinta ma kamar yana barinta ne

"Toh ya zan yi? Ina zan samu kudi yanzu?" Ta furta da karfi, kamar tana magana da mutanen arean ne

Tana nan zaune, sai wata tsohuwar mata ta shigo da wani yaro mai ciwon sikila, tana neman taimakon kuɗin da za'a ma yaronta karin jini, Azrah ta kalleta zuciyarta tayi wani irin sanyi kamar itama ta fara hakan, Bata jin zata iya bari Umma ta shiga cikin hadari saboda kudi.
Nan take ta tashi da sauri

Zata fita neman kudi, Ko da ta je gidan su suhaila ne ta roƙi Mummy? Ko ta nemi wani daga cikin makusanta da bata taɓa tunani ba? Ko ta kai wayar Umman ta saida?

Zuciyarta ta yanke shawara ɗaya Zata yi duk abin da zai tabbatar da Umma ta samu lafiya.

Ta juya cikin hanzari, Fuskarta cike da hawaye amma kwarin gwiwa ya fara ɗagata tana feeling hope yana kusa, wannan ba lokaci bane na kuka kadai lokaci ne na neman mafita


Tana dawowa gida, Azrah ta shige ɗakinta da sauri, ta duƙufa ta zaro ƙaramin akwatin da ta sakawa ƙey a cikin leda 'asusunta A hankali ta zauna ƙasa, zuciyarta na bugawa kamar zata fito waje, Tayi addu'a kafin ta ɗauko ƙaramar guduma daga ƙarƙashin gado, sannan ta ɗan tsaya tana kallon akwatin kamar tana tambayarsa, "me zan samu a ciki?"

Taaah! Guduma ta sauka
Taaah! Na biyu
Har sai da akwatin ya fashe, ga kuɗaɗen da ta tara

Ta fara tattarawa da rawar hannu ₦37,500 Kawai.
Ba ma ya kai rabin kuɗin ba... Ta dafe goshin ta ta furta

"Ya Allah" hawaye na gangaro mata, kamar waccan aka aikata ta miƙe da sauri

Bata tsaya tunani ba, ta ɗauki kudin cikin leda ta zura a jaka, ta fita da sauri, harta isa asibitin tana addu'a, office ɗinsu ta wuce ta miƙa kudin ga nurse din

Ya karɓa, ya gyara rigarsa, yana duban takardar This is not complete, but we'll start her on injections while we await the balance"

Azrah ta ɗaga kai, "Please just don't let her get worse"

Aka shigar da Umma dakin jinya, suka soma aikin duba lafiyarta Amma duk da haka, komai sai cikakken kuɗin CT scan da wasu tests, har yanzu ba'a fara ba.

Azrah ta dawo gefen Bappah da ke tsaye a waje, yana kallon ƙasa kamar wani da aka zarga da laifi

"Bappah… akwai saura kaman ₦50,000…" muryarta na rawa.

Bappah ya yi shiru. Daga nan ya ɗan karkatar da kansa "Azrah… gaskiya… banga inda zan samu ba yanzu, ba hanya Azrah"

Kamar an buɗe tankin hawaye a idonta Azrah ta fashe da kuka, ta durƙusa a gaban Bappah, zuciyarta na tafarfasa "Bappah don Allah, Umma zata mutu ne kafin a samu kudin?"

Zahra dake gefe ta sa hannu ta ja Azrah daga gaban Bappah, "Zo mu tafi Aunty Azrah, Kukan nan ba zai canza komai ba Bappah kuma ba asaransa bane"

Suka koma bakin bench suka zauna, Shiru ne ya ratsa tsakanin su Kawai sautin sanyi da famar numfashi na ban tausayi ya cika sararin zuciyoyin su

Azrah ta kalli Zahra ta daure da murmushi na karya, sannan ta ce

"Ina zuwa Zahra"

Zahra ta ce, "Ina zaki je kuma?"

Azrah ta girgiza kai "Zan samo kudin ne Ko da sai na kai wayan Umma ne, ko na yi aiki da karfi, sai na samo…"

Ta fice da sauri wasiyyar Umma na dawo mata wa da yake mara sanya mata jiki, Wannan shine lokacin jarabawa,

Har yamma tayi, Azrah tana yawo kamar mara tushe a cikin gari. Ta shiga layi-layi, ta tambayi duk wani mutum da ta ke da kwarin gwiwar cewa zai iya taimakawa abokai, tsofaffin ma’aikata, har ma da 'yan adashe da ta taba yi da su Amma kowa da dalilinsa: wasu sun ce sun riga sun ci adashen, wasu kuma suka ce babu cash yanzu Wani ma yace mata “kiyi hakuri, rayuwa tayi tsada sosai.”

Azrah ta zauna a gefen titi wani lokaci, tana kallon mutane suna wucewa. Ranta ya yi nauyi Ji take kamar duniya ta ninka mata A zuciyarta bata ma sake tunawa da cewa tana da aikin a gidan Mummy ba balle ta tuna da zuwa gidan nata neman kudin duk ta manta, Abinda kawai ke gabanta shine Umma

Daga Magrib Azrah ta miƙe da sauri Kamar wacce ta hango mafita, ta yi tafiya cikin sauri-sauri, har ta dawo asibitin tana cikin tsoro, ko lafiya? Ko ciwon ya tsananta? Ko akwai wani abu da ta rasa?

Tana isa, ta zarce kai tsaye dakin da aka kwantar da Umma, Ta saki ajiyar zuciya lokacin da ta ganta a can, kwance da idonta rufe, amma tana numfashi a hankali, ta kalli Zahra da itama tana saye a jikin glass ɗin tana kallon Umman ta ce

"Zahra ya jikin Umman?"

Zahra ta ɗago kai, ta ce da sauki, "Baki samu kudin ba ko?"

Azrah ta girgiza kai a hankali, hawaye na cika idonta "Wallahi babu wanda ya iya taimaka min Na gwada ko'ina Zahra... ko'ina"

Zahra ta kama hannunta "Ki zauna kawai ki huta Allah zai kawo sauki, Mu dake da addu’a"

Azrah ta zauna, zuciyarta a karye, jiki ba ƙarfi Gaba ɗaya ji take kamar duniya ta juya mata baya

A yanzu bata da wani mafita sai dai tsayawa da addu'an kawai.


*BEYOND THE VEIL* (LABULEN SIRRIN)


YOTA ID/026

Wattpad © Jiddatulkhayr
Instagram © Jiddatulkhayr writes


Free page

Episode 6: A Ray of Hope

Da daddare misalin 2:30am Azrah na zaune akan dadduma a gefen gadon da Umma ke kwance, ta shafa fuskarta da tafin hannunta, idanuwanta sun kumbura da kuka hatta gaji, tunaninta duka yana kan Umma da ke kwance cikin rashin lafiya, tana ta mika kuka zuwa ga Allah masu mafita ya kuma bawa Umma lafiya

"Ya Allah... Ka bawa Umma lafiya. Ka ba mu mafita, ko daga inda bamu zata ba..." ta furta a hankali, kamar kada kalmomin su farka da Umma da ke kwance kusa da ita.

Tun da yamma Zahra da Bappah suka koma gida, Azrah ta rage ita kaɗai a asibitin ta rasa ina zata fara neman kudin da zata cika deposit ɗin maganin da likitoci suka bukata kafin su cigaba da duba Umma, a haka take tun lokacin da su Bappah suka koma har sanda take kan sallayan

Tayi shiru ta faɗa duniyar tunani, wani tunani ne ya faɗo mata a zuciyarta, Sai kawai ta tuna da Mummy, ta tuna da aikin da bata je ba a ranar, aikin da ke kawo mata ƙananan kuɗaɗen da take adanawa, A hankali ta fara jin wani hope, hope ɗin da yasan bata da tantama akai, dan she's very sure Mummy ba zata ɓata kunya ba, whispering ta yi

"Idan na roƙi Mummy ta bani kuɗin aikina na wata uku nan gaba, zata iya bani... zan iya amfani da su na cika balance ɗin kuɗin maganin Umma" ta faɗa a ranta, Wannan tunanin ya dan taɓa zuciyarta da fatan cewa watakila mafita na kusa.

Bayan gari ya waye tana zaune amma gaɓa ɗaya she's spaced out, Zahra ce ta shigo ɗauke da ƙaramar kulan abinci, Azrah ta ɗaga kai tana kallonta harta karasa ciki sai kuma ta kalli bayan Zahra kaman tana hoping ganin wani, Zahra ta zauna a kan wani kujera. Bayan sun gaisa, Azrah ta ɗan murmusa kamar tana son tambayar Zahra sai kuma tayi shiru, can ta ce

"Ya Bappah? Ko yana waje ne?"

Zahra tayi ƙwafa tana girgiza ƙafa ta ce

"Dalla ki bar ni da Bappah! Ni wallahi na gaji da halin ko in kulan sa, just imagine bai zo duba Umma ba, balle ya fara maganar clearing bill, shi baya ma tunanin aina kike samun kuɗi balle yaji tsoron tarbiyyar ki" ta karasa maganar cike da takaicin Bappah

Azrah da tunda farko ta tsaya kallon Zahra da shock har sannan bata janye idonta akanta ba cos Zahra na mugun bata mamaki idan sometimes tace wani abu ko kuma ta aikata wani abu, tayi kasa da murya ta ce

"Zahra ki rage zafi, Koda me ya faru Bappah mahaifinmu ne, bai dace mu raina shi ba... mu dai cigaba da roƙon Allah harya gane abinda yake ba daidai bane" Zahra ta taɓe baki ta ɗauke kanta daga Azrah dan bata ji zata iya cigaba da wannan maganar da ita ba

Can kuma sai ga Nurses suka shigo suka duba Umma, bayan ta karya suka mata allura, wani daga Nurse ya kira Azrah ya sake jaddada mata cewa dole sai an cika kudin ko kuma su sallame su zuwa karfe biyu

Azrah ta dafe kanta data ji ya tsara mata , Nurse ɗin ya juya ya fita, ta juya tana kallon Zahra da rinannun idonta, ta roƙeta ta zauna ta kula da Umma, ita kuma ta fice cikin sauri, ta kama hanya a kafa zuwa gidan Mummy, a zuciyarta addu'a da fatan zata Mummy zata yarda ta bata kuɗin aikin nata kamar yadda ta yanke hukuncin tambayarta.

Azrah na tafiya absent-minded jikinta yayi sanyi kamar wadda aka cirewa laƙƙa, tafiya take kamar bata san inda take dosa ba tunaninta na zagaye ne da damuwa, da tunanin yadda zata ceci rayuwar mahaifiyarta idan har Mummy bata yarda ba, Har ta isa gidan Mummy bata ma lura da yanayin hanya ko mutane ba knocking tayi gatekeeper ya buɗe mata

Tana shiga ta tarar da Mummy zaune tare da Suhaila da Saif, suka ɗaga kai suna kallonta harta karasa ciki parlorn ta gaida su, Mummy ta kalle ta ce

"Azrah meyasa baki zo jiya ba?"

Azrah ta durƙusa kusa da kujerar da Mummy take, ta sauke ajiyar zuciya tana cewa

"Umma ce Mummy... bata da lafiya sosai har anyi ta dinta a asibiti hakan ne yasa ban samu zuwa ba."

Mummy da Suhaila suka ce

"SubhanAllah," sannan suka fara mata addu’a da fatan sauƙi, amma banda Saif wanda ko kallonta bai yi ba, balle yayi magana, Har lokacin Azrah na duke a gefen kujerar Mummy, kamar wata mara galihu, ganin har sannan tana duke Suhaila tama Mummy magana da ido wanda yasa Mummy ta ce

"Menene Azrah?"

Azrah ta kalli Mummy da idonta cike da hawaye ta ce
 
"Dan Allah Mummy, ina roƙon ki ki bani kuɗin aikina na wata uku gaba… zan yi amfani da su ne wajen cika kudin asibiti na Umma, ba mu da wani mafita sai hakan ne, ki tausayamin"

Wani shiru ya biyo bayan kalamanta Mummy ta zuba mata ido, tana nazarin yanayinta, Azrah harta fara cire hope kawai ta tsinkayi murya Mummy

"To Azrah, Nima yanzu da nake zaune akan kaya ne wlhi, Jibi idan Allah ya kai mu zamu bar ƙasar nan gaba ɗaya" da sauri Azrah ta ɗaga kai ta Kalle ta sai yanzu ma yanayin parlorn da babu wasu kaya ya dawo mata da kuma yadda shekaran Jiya ta kalli wasu curtain changes a gidan

Tana kallon Mummy kamar wadda ke kokarin processing maganarta, sai hawayen da ke makale a cikin idonta suka fara gangara saman kumatunta Kafin ta ce komai, Mummy ta miƙe tana cewa

"Mu shirya mu je mu duba Umman tunda ba wai wani abun muke yanzu ba and it's good ai"

Suhaila ta bi ta a baya, amma Saif ya cigaba da zama kamar bai ji komai ba balle su saka ran zashi

A asibiti ganin yadda Umma ke kwance cikin rauni, ya sa Mummy ta cika duka kuɗin da ya rage suyi balancing na asibiti ba tare da wata tambaya ba, Nurse ɗin suka karɓa suka tabbatar da an biya cikakken kuɗi Azrah da Zahra ba su iya boye farin cikinsu ba Sai godiya suke ta yi kamar rayuwarsu ta ta'allaka a kan hakan ne

Bayan sun gama komai suna dakin da Umma take Azrah ta sanar da Umma, hawaye ya fara sauka idonta ta daga hannunta tana yi musu addu'a

"Allah ya saka da Alkhairi ya biya muku dukkanin bukatunku, Allah muku fiye da yanda kuka faranta mana,

Da zasu tafi Azrah ta raka su har bakin mota, Suhaila ta riƙe hannunta ta ce

"Zaki zo kafin mu tafi ko?"

Azrah ta gyaɗa kai tana murmushi, tana jin tun yanzu ta fara missing ɗinsu"

Washegari da safe, aka sallami Umma daga asibiti bayan an bata magunguna masu ƙarfi. Bayan sun dawo gida, suka zagaye Umma suna kallonta cike da tausayi Umma na kallon Azarh ta ce

"Azrah ki tashi ki je ki yi sallama da Mummy, sai kuma ki sake musu godiya pls, live ina musu fatan Allah kaisu Lafiya" Azrah tayi shiru tana kallon Umma sai kuma ta wuce ciki ta sanya hijab ɗinta ta fito

Sallama tama su Umma, dama tana son zuwa ta sake musu godiya kuma tana son suyi sallama, amma haka kawai take jin kamar wani nauyi ne a zuciyarta da ta kasa sauke tun ranar da Mummy ta sanar mata zasu bar kasar, har ta isa gidan Mummy tunanin da take kenan

A parlour ta same su Mummy, Suhaila da wani mutum da ba ta taɓa ganinsa ba a gidan amma da alama shine Babban su Suhaila dan ga kama ya tabbatar mata da hakan, Fuskar sa cike take da natsuwa da annuri, Yana zaune yana tattaunawa da Mummy a hankali, duk suka ɗaga kai suna kallonta

Suhaila ta miƙe da murmushi ta rungume ta kamar ƴar uwarta,

Bayan ta Gaishe da dukkansu Mummy ta ce

"Azrah ya gida? Ya jikin Umma?"

Azrah ta gyaɗa kai, tana ƙoƙarin hana kanta kukan da ke shirin zuba Amma kafin ta iya cewa komai Mummy ta nuna mata kujera

"Zauna mana, me ke damunki Azrah? Kin yi wani iri..."

Azrah ta zauna tana jinta wani iri, ta buɗe baki zata mata godiya sai  kawai kukan da ta ke riƙewa ya kubuce, tana sharar hawaye tana cewa

"Mummy… nagode… ban san yanda zan saka muku ba…amma zan cigaba da muku addu'a har karshen rayuwa ta, Allah ya saka da Alkhairi…"

Mummy ta rungume ta, tana shafa kanta amma itama she's speechless dan ba kaɗan Azrah ke bata tausayi ba, Har Baban Suhaila wato Daddy ya ce

"Young lady keep on praying kinji? Kuma no matter how no matter what karki bar makaranta,  amma ki daina godiya sbd dan Allah suka taimaka miki"

Suhaila ta tashi ta shige ɗakinta tana cewa

"I'm coming Azrah" daga haka ta shige bata ɗau lokaci ba sai gata ta fito tana rike da wani ɗan ƙaramin Ghana Must-Go cike da kaya ta ce

"Ga wasu kayan sawa da ban so Azrah, sabbi ne sai kuma turaruka da shower gel... Nasa zaki bukace su"

Azrah ta rufe bakinta da hannunta, tana kallon ghanan dake gabanta, ta ɗaga kai tana kallonta da thank you face ɗinta amma ta gagara cewa komai, tana tunanin me ta musu data cancanci irin wannan kulawa daga waɗanda ba su da alaƙa ta jinin, ta duka ta fara mata godiya Suhaila ta tamke fuska ta ce

"Mention not, please"

Da zata koma gida Daddy ma ya zaro kuɗi daga aljihunsa wanda ko irgasu baiyi ba ya miƙa mata

"Ga wannan ki ƙara da duk abin da kike buƙata Allah ya ba Umma lafiya" wanda hakan yasa take tunanin Mummy ta masa maganar ta kenan

Wannan karimcin ya gama karya Azrah, hawaye ta fara yi, tana sharewa ta miƙe ta ɗauki ghanan tana kallon su

"Mummy… Daddy… Suhaila… na gode Allah rufa muku asiri duniya da Lahira"

Suhaila ta ƙara rungume ta ta ce

"Zanyi missing dinki Azrah gashi baki da way"

Azrah ta gyaɗa kai cikin hawaye, tana jin wani abu mai zafi da daɗi a zuciyarta abu da bata taɓa ji ba tun lokacin da rayuwa ta haɗa ta da su

A haka ta bar gidan, Ghana Must-Go ɗinta a hannu, zuciyarta cike da sabbin tunani da sabuwar rayuwar da zata fara babu aiki

Da Ghana Must-Go ɗinta a hannu, Azrah ta shiga cikin gidan su cikin nutsuwa as Azrah dinta, ta tarar da Mama zaune a tsakar gida tare da ‘yaƴanta uku Habibah, Siyama da Abdul da alama akwai abinda suke yi

duk suka ɗaga kai suka kalle ta
Azrah ta ce da ladabi tayi sallama

"Assalamu alaikum."

Mama ta amsa da da wani irin murya tana dariya

"Wa'alaikumus salam ƴar boko" sai kuma tayi shiru tana kallon ganan hannunta ɗin

Habibah ta kwaɓe fuska, tana faɗin

"Wato kaya ta samu ko me? Ta wani shigo mana da ghana must-go kamar wacce ta dawo daga hutu ko jihar Ni Habibah?

Siyama ta ɗora da dariyar rainin hankali ta ce 

"Dalla malama, saurayinta ne ya bata kaya mana, Kin san haka suke, wannan kayan da take sawa a banza ne aka ce miki, kwadayin duniya kawai yake kaita"

Azrah ta lumshe ido, bata ce uffan ba tayi kamar bata ji ba, ta ɗauki hanyar ɗakin Umma

A ɗakin Umma na kwance amma idonta a buɗe tana kallon sama kana ganinta kasan tana nazari ne Azrah ta shiga da sallama tana kallon Umma

"Umma ya jikin?" ta tambaya cikin damuwa

"Alhamdulillah Kin dawo? Lafiya?" Umma ta ce tana ƙoƙarin tashi daga kwanciyarta

Azrah ta zauna kusa da ita, ta bude ghana must-go ɗin a hankali, ta nuna mata kayan Suhaila ta bata da turaruka da sabbin kayan wanka Umma ta kasa boye mamakinta

"Subhanallah… daga ina duk wannan?" ta tambaya cike da fargaba

"Su Mummy ne suka bani Umma" ta ciro kuɗin tana mika mata ta ce

"Babansu kuma ya bani wannan kuɗin Umma"

Umma ta jinjina kai tana mamakin hali irin nasu Mummy ko kaɗan basu kyamar Azrah kamar yadda wasu masu aiki kema housegirl dinsu

Azrah ta bar ɗakin ta koma nasu har sannan tana jin muryar su Siyama a tsakar gida tana suna cewa

"Yanzu haka ba kowa zata dinga kulawa ba, ita gata sai wani ji take da kanta saboda fatar jikinta take ji da shi, duk dai mun sani wallahi bilicinne"

Azrah ta share hawayenta ta sani ba kowa zai fahimci gaskiyar al'amuranta ba amma ta san cewa zata ci gaba da aikinta domin rayuwa, ba zata tsaya jira jin ra'ayin kowa ba


Bayan Azrah ta gama shirya kayan a daki, tana kokarin jera su a cikin ɗan karamin wardrobe ɗinsu dake mane a bango sai ga Zahra ta shigo dakin da sauri

"Yaa salam! Azrah! Wannan kayan kuma fah?" ta tambaya tana duban jakar da mamaki

Azrah ta yi murmushi kaɗan "Su Mummy ne suka bani, Kayan Suhaila ne da wasu sabbi ne ma… har da turaruka da sabulun wanka"

Zahra ta kalleta ta buɗabaki

"Kayan nan duka daga can?" Ta zauna kusa da jakar, tana buɗewa a hankali.

Tana ɗaukar kaya ɗaya bayan ɗaya tana dubawa, sai ta girgiza kai "Subhanallah…Anty Azrah wannan kayan fa masu kyau ne sosai wlhi ga su masu tsada kayan da ba kowa ke iya samu ba"

Azrah ta ce da ƙasa-ƙasa

"Wallahi nima ban yi tsammani haka ba, hmm kawai daga na roƙi Mummy ta bani kuɗin aikina na wata uku nan gaba zan yi amfani da shi wajan maganin Umma, sai kawai suka bani komai… har da clearing bill ɗin asibitin Allah Sarki, Alhamdulillah my perfect Rabb"

Zahra ta daina kallon kayan tayi tagumi tana kallon Azrah cike da tausayawa

"Allah ya saka mu da Alkhairi, Anty Allah na kallon wahalar da kike sha, shiyasa yake dafa miki a komai" Azrah tayi murmushi ta ce

"Amin… da fatan Umma zata samu sauƙi in Shaa Allah " Zahra ta koma kan kayan ta cigaba da kallo ta ce

"Wannan kayan zan ara wani lokaci fa gaskiya" suka yi dariya tare Azrah ta miƙe ta koma wajan wanda ɗazu ta ware su

"Zahra! ta kira ta a hankali

Zahra ta ɗago kai "Naam?"

Azrah ta ɗauko wasu kaya daga ciki riguna, hijabai da sabulun wanka ta miƙa mata

"Ga waɗannan tun ɗazu dama na ware miki baki ne"

Zahra ta zaro idanu "Ni kuma fa? Wallahi ba zan karɓa ba! Ai naki ne"

Azrah ta girgiza kai tana dariya "ashe zan miki duka kuwa idan kika ce A'a, munsha wuya tare Zahra, wait what are sisters for? Kuma nayi niyyar rabawa tun kafin na shigo gida, Ki karɓa don Allah ko kuma naci kaniyan ki"

Zahra ta tsaya kallonta na ɗan lokaci, idonta cike da hawaye a karshe ta karɓa a hankali

"Nagode Anty Azrah, Allah ya saka miki da Alkhairi"

"Ke... Zanci jam'iyar ki" Azrah ta faɗa da tana murmushi

Sai suka ci gaba da rarrabe kayan, suna dariya da tsokana a tsakaninsu.


Dama a weekdays ne kawai zamu ke update banda weekend amma saboda week daya wuce an samu issues shiyasa zamu yi update yau, thank you darlns

*BEYOND THE VEIL* (LABULEN SIRRIN)


YOTA ID/026

Wattpad © Jiddatulkhayr
Instagram © Jiddatulkhayr writes


Free page

Episode 7: Pathways to Hope


Da yamma saboda hadarin daya haɗu yasa garin ɗaukar zafi hakan yasa Umma na zaune a bakin ƙofar dakin, tana shan iska tana jingine da bango Azrah da Zahra suma sun fito suka zauna kusa da ita, amma ba wanda ke magana a cikin su kowa da tunaninsa a zuciya, sai dai lokaci-lokaci su kanyi magana a gefe

Can sai ga Bappah ya buɗe kofar gidan yana tunkaro harabar gidan Zahra ce ta fara hangonsa, idonta ya ciko da hawaye dan tunda aka sallame Umma bata sake saka idonta a nasa ba, ta miƙe tsaye da sauri kamar wacce aka sikara tana kallon Bappah daya kusa zuwa inda suke dama ganinsu yasa zai karaso, tana taɓe baki tana ɓata fuska Umma da Azrah sai kallonta suke dan basu ma lura da Bappahn ba sai data miƙe

Bappah ya ƙaraso, idonsa na kan Zahra da yake yawan ce mata 'Mamana' Amma yanzu Zahra ta riga da taji bata wani son Bappah duba da yadda ya maida Mama a gidan, taji ta washe sa Kamar dai yadda tayi alkawarin duk wanda zai zubar da darajar Umma ba zata lamunta ba

Ganin da gaske inda suke zaune Bappah zai karaso yasa Zahra guduwa cikin ɗakinsu, Bappah with shock written all over him yake kallonta ganin zata shige yayi saurin cewa

"Mai namiki uwata?" Ya tambaye ta da ɗan faɗa a muryarsa, yana kallonta cikin rashin fahimta

Zahra ta tsaya cak, ta juyo da hawaye a fuskarta ta ce

"Ni bana sonka Bappah, Tunda kai ka nuna baka son Umma, to nima haka"

Zuciyarta cike da takaici da ciwon da ta sha ganin Umma na kwance a asibiti yayin da Bappah bai taɓa bada ko sisi ba balle ya nuna damuwarsa akan Umma ba wato ma idan ta mutu asarar su, Ta juya da sauri ta shige cikin ɗakin Umma tana sharan hawayenta

Bappah ya tsaya cak, kamar wanda aka zuba masa ruwan sanyi, Bai taɓa tsammanin Zahra zata iya furta hakan a garesa ba Daga cikin duka yaransa Zahra ce wanda yafi nuna mata tsantsan So a fili kuma itace wanda baya ganin laifinta sannan itace wanda idan ya ajiya kaya ko bece ta wanke ba zata kwashe ta wanke masa shiyasa ya fi sonta, amma yau maganarta ya basa mamaki dan bai taɓa sammani ba

Azrah ta sauke ajiyar zuciya, tana kallon yadda Bappah ya kasa cewa uffan, kamar wanda ya sara dukkan thought ɗinsa, ta kalli Umma wanda itama daga gani she's speechless ne, a ranta tana mamakin hali irin na Zahra kamar bata mata magana a asibiti ba, but koma me Bappah zai yi su barsa da halinsa kawai

Mama ce ta fito tana share hannunta da ɗan guntun zanin dake ɗaure a jikinta tana wani murmushi makirci tana kallon Bappah dake tsaye kamar gunki ta tamke fuska ta ce

"Lafiya Malam?"

Bappah ya juyo gareta ya mata one look ya wuce ba tare da ya ce uffan ba,

Azrah ta juyo ta kalli Umma, wacce ke kallon samata ce

"Umma Allah ya sa hakan ya ishe shi darasi Thank God Zahra ce ba wata bace ta faɗa masa maganar"

Umma ta yi shiru na wani lokaci, sannan ta ce ƙasa-ƙasa

"Ƙwata kwata banji daɗin abinda Zahra ta aikata ba, amma bansan ya zanyi da ita ba"

Mama dake tsaye jikin ɗakin ta tayi wani dariya ta ce

"Ni dai dama tun farko nace yaran nan basu da tarbiyya! Ashe dai ba kawai yarinya ce mai tsegumi ba, har da rashin kunya! Wannan shi ne ilimin boko kenan? Allah ya kiyaye da ace yaran Alhaji Lado ne, wallahi ba haka zasu tashi ba! Amma Malama ya zuba muku ido yana kashe kuɗin mu akanku amma sai rashin kunya da rashin ɗa'a da kuka koyo, yanzu kuma har shi kansa Malam baku bari ba"

Ta kalli Azrah da ke gefe kamar ba ta ma jin mitan, idonta na kan Umma kamar tana jiran ta mayar mata da martani amma sai Umma bata ce uffan ba, Zahra kuwa ta fito daga ɗakin da taga mitar Mama bata da iyaka Bappahn ma baice komai ba amma tana cika musu kunne da magana

Tana rike da kugunta ta karasa cikin gidan tana takawa kamar ba zata taka kasan ba, ta tsaya a kusa da inda sun Umma ke zaune ta zuba mata kallo ɗaya mai cike da raini da rashin jin tsoro, Sannan ta juya kamar ba ta bukatar ɓata lokaci akanta kuma, zauna kan tabarman da Umma da Azrah ke zaune

Mama ta ɗan zaro ido da mamaki, amma tunda ba wanda ya tanka mata sai ta taɓe baki ta juya da jin haushi ta shige ciki tana banbami musamman yadda Bappah ko magana ya kasa

Bayan an ɗan yi shiru, Umma ta sauke ajiyar zuciya sannan ta ce da kakkausar murya

"Zahra, Azrah… ni ba wai ina son halin da Bappah ke nuna mana bane, amma fa ku sani, kowane hali da yayi, Bappah mahaifinku ne Kuma rashin girmama uba ko da ya yi kuskure.. kuskure ne iri ɗaya, gaskiya ba zan lamunci haka daga gare ku ba musamman ke Zahra dan ke ce baki jin magana" Azrah ta lumshe ido ta ce

"Umma kin faɗi gaskiya"

Zahra ta kalli Azrah sai kuma ta kalli Umma sai kuma ta kwanta a cinyarsa ta ce

"To Umma idan shi mahaifine, Mayasa baya adalci ko nuna muku soyayya? Ai tunda ya daina ganin mu a matsayinsa, to mu ma zamu daina ganin sa as Bappahn mu na baya"

Umma ta girgiza kai, zuciyarta na ƙuna amma ta san halin Zahr idan ta kuɗirci abu a zuciyarta, sai Allah kuma

Washegari...

Azrah na zaune a aji amma gaba ɗaya hankalinta baya jikinta Malamar da ke karatu a ajin tana musu bayanin salla dalla yadda zasu gane amma Azrah bata jin komai cos tayi nisa sosai a duniyar tunaninta, abin daya dame ta  yanzu shine maganar candy kuma

Tunda ta shiga makaranta da safe, taji wasu 'yan ajinsu suna tattauna cewa an sake fitar da sabuwar candy sannan an saka dateline shikenan kuma hankalin ta ya kara tashi zuciyar ta kuwa ta buga da ƙarfi

"Mummy..."Ta faɗa a ranta, "Allah sarki! Maybe sun manta da maganar candy name amma da nasan kila zasu taimaka"

Kuma yanzu da ba a san lokacin dawowarsu ba, sai taji komai ya sake birkice mata. Damuwa ta shige zuciyarta har tana jin kamar ana sara mata kanta sabar lokaci guda da kanta ya fara ciwo,  Tayi kokarin kame kanta ganin bata yi kuka ba amma idanunta suka cika da hawaye

Fatima kawarta ta lura da yanayin Azrah tun bayan shigansu ajin, ta matsa kusa da ita a hankali ta ce

"Azrah lafiya? Me ke damunki ne? Kin yi shiru tun safe fah"

Azrah ta girgiza kai kamar bata da bakin magana ganin kallon da Fatima take mata yasa ta ce

"Fatima... I'm lost, Mummy ta bar kasar nan, Kinsan da kuɗin da take bani karshen wata nake tarawa kuma nake jari, yanzu kuma ina zan samu aiki? Ga kuma maganar candy data tsakanin a rai"

Fatima ta kamo hannunta cike da rarrashi  ta ce

"Karki damu Azrah, Allah yana tare da ke zai finding miji wani way out, just trust him In Shaa Allah komai zai wuce"

Azrah ta gyaɗa kai, hawaye na gangarowa a gefen fuskarta ta kwanta tana jin hope

Ko da Azrah ta dawo daga makaranta, ta shiga gidar da sallama amma babu kowa hakan yasa ta wuce ɗakin su, ganin Zahra bata nan yasa kawai ta ɗaura girki kamar yadda ta saba ta dafa tuwo da miyan kuka sbd fav ɗin Imma ne tana gama wa ta kama shara, share dukka gidan harda ɗan compound ɗinsu haka kawai take jin wani iri sbd yanzu da ace Mummy na nan da tana can gidanta, babu aikin data manta batayi ba amma kallo ɗaya zaka mata ka fahimci cewa ba ta cikin hayyacinta

Umma tana kallonta tun daga lokacin da ta shigo, tana lura da yadda Azrah ke tafiya kamar wadda aka zarewa laƙƙa, tana aikin ne amma babu walwala tattare da ita, balle annuri

Bayan sunci abinci, Umma ta juyo da kallonta kanta

"Azrah lafiya dai ko?" Ta tambaya cikin taushi da kulawar Uwa

Azrah ta ɗaga kai tana ƙoƙarin yin murmushi amma hakan ya gagara ta dake ta ce "Lafiya kau Umma, babu komai"

Amma me? Yadda tayi maganar ya sake bayyana yadda take cikin damuwa cos kasan daurewa take, Umma ta kura mata ido tana cigaba da kallon ta da tausayi

"Zo nan ki zauna kusa dani" Umma ta faɗa a hankali.

Azrah ta masa ta zauna a kusa da ita, Sai dai ba ta iya jurewa ba kamar dama jira take hawaye suka fara gangarowa daga idonta tayi ƙoƙarin ɓoye su amma ta kasa

"Azrah!" Umma ta ce cikin tsoro tana dafe kafadarta

"Me ya faru? Kin min bayani, Karki tsorata Ni dan Allah, wani abunne ya same ki ko aka miji?"

Azrah ta share hawayen da sauri

"Umma Mummy ta tafi sun bar ƙasar... bana jin kuma nan kusa zasu dawo, bansan wani aiki zanyi na samu aikin da zanna samun kuɗi irin aiki wa Mummy ba, ga maganar candy na matsowa Umma, wannan sana'ar dana ke yi kuma babu wani riba Kema kin sani"

Umma ta dafa kanta, tana shafa gashinta kamar yadda zata lallashi yaro

"Azrah idan kina magana haka sai naga kamar baki godewa Allah, yadda kike da riƙon addini da karatun Alkur'anin ki ba zai tafi a banza ba, In Shaa Allah, Allah zai baki wata mafitan sa saboda masu zuciya irin taki Allah ba zai bari haka nan ba, balle ma kuɗin a jinyar mahaifiyarki kika kashe kuma ai kuɗin Candyn ki na wajan Mama dole Bappah ya baki dan ba zan bari ki fara biya ba har sai shi Bappahn yaki, dan wannan ai responsibilities dinsa ne"

Azrah ta kwanta kan cinyar Umma tana jin nawin zuciyarta na sauya wa zuwa wani sanyi haka kawai taji wani hope yana zuwa mata dan ba kaɗan ba kalaman Umma sunyi tasiri a kanta, ido ta kurawa ceiling kamar tana karanta wani abu daga cikin ceiling ɗin

"Umma…" ta faɗa a hankali
"Kina ganin... idan na fara yin wasu handmade stuffs zan iya samun kuɗi da kaina? Kamar zasu fi kawo kuɗi akan su gawayin nan da kayan mita ko?" Umma ta kalleta da mamaki

"Wane irin stuffs kike nufi?" Azrah ta ɗan murmusa da

"Kamar accessories, scented oils, ko natural soaps, Na koya wasu tun lokacin da aka taɓa kawo tallafin koyar da handmade stuffs, sannan ga tutorials akan YouTube da na rubuta a littafina, kuma ai Mummy har ta fara koya min tun kafin su tafi..."

Umma ta gyara zama cikin kulawa da damuwa ta ce

"To ki fara kinji ƴar Albarka, Kin daɗe kina ƙoƙari Azrah Allah ya saka miki albarka"

Azrah ta ɗan sake numfashin hope

"I guess this is the time, I want to do something that will remind me of Mummy, kuma idan na samu kuɗi zan riƙa taimaka miki da kaina ba sai sai jiran albashi ko Alkhairi daga mutane ba"

Umma ta dafa hannunta "Ina alfahari da ke Azrah, Allah Ya taimaka miki, Ya saka albarka a abin da kika sa a gaba"

From that moment, hope started to plant itself again in Azrah’s chest, Duk da cewar zuciyarta tana cike da kewar Mummy, amma hakan bai hana ta ganin cewa watakila, this is the beginning of her own story her own path


Da dare, Azrah ta zauna a ɗakin su, hannunta rike da karamin diary dinta littafin da take rubuta tunani, mafarkai da ideas nata, Ta buda littafin tana kallon rubutunta

"Brand name: Azrah Scents & Naturals. Handmade soaps. Lip balms. Oils. Goal: Start small. Grow slow. Stay pure."

Tayi murmushi a hankali, zuciyarta cike da fatan Alkhairi Sai dai tana cire kudi a jaka domin ta fara tantancewa sai ta tsaya cak, Kudin da Daddyn su Suhaila ya bata ya kusa raguwa, Bata ma tsaya lissafa ba, ta san ba zai isa ta fara business da shi ba ganin amount ɗin da zata fara

Ta sauke ajiyar zuciya tana kallon ceiling, zuciyarta cike da tambayoyi

"Ya zan yi yanzu? I was ready… but maybe ba yanzu ba, Maybe this dream has to wait."

Kafin ta rufe diary ɗin sai zuciyarta ta kuma faɗi, Tana tuna halin da suke ciki, kayan abinci sun kusa karewa, babu wake, babu su manda balle albasa, ta leƙa Amma dake nata ɗakin sai ta dafe zuciya da hawaye a idanunta, tana mugun tausayawa Umma

"Toh idan kuwa ba zaki iya business yanzu ba, ki yi abu mafi alkhairi" kamar me whispering haka tayi maganar

Washegari, Azrah ta tashi da sassafe ta shirya, bata tafi makaranta ba, kasuwa ta wuce, duk kudin da ya rage a hannunta ta siyo kayan miya: albasa, attarugu, tumatur, su wake, kuka da daddawa, wanda zata na kullawa a gida, sauran kuɗin kuma ta wuce ta siya musu kayan abinci kawai, a gajiye ta dawo gidan ta zauna tana nunawa Umma siyayyar da tayi Umma ta ce

"Da nasan zaki kashe kuɗin nan dukka da ban barki kin shiga da shi kasuwa ba Azrah, da ko deposit kika kai na candyn ki" Azrah ta ɗan bata fuska ta ce

"Toh Umma haka zamu ta zama babu abinci? Kuma ai naga ke kika kwantar min da hankali" Umma ta ce

"Shikenan, Allah miki Albarka, sai duk cinikin da kika yi ki dage da sawa a asusu" ta gƴaɗa mata kai

Umma ta ce "Allah Ya sanya albarka Azrah"

Azrah ta share zufa daga goshinta tana murmushi. 
"
Na fara daga nan Umma, Even if I couldn’t start the big dream today… I can feed my family, And that’s enough for now" .

Baya sallama Isha'i, iska mai sanyi na kadawa kadan-kadan, a harabar gidan, Azrah na tsugunne ita da Zahra suna kulla gawayi, suna ajiyewa a gefe

Gaba ɗaya gida shiru ne dan da alama ma babu s siyama, sai muryoyin su dan suna sana'ar nema da shaawa

Can sai ƙofar ɗakin Mama ta bude da karfi! Mama ta fito ta tsaya tana musu wani kallo cike da kiyaye ta ce

"Yanzu har dare ba zaku ƙyale gidan nan ya huta ba?! Wannan gawayin nan naku ya hanani numfashi saboda ƙura, gidan nan ya zama kamar kasuwa sbd jama'ar ku da kuke tara mana"

Azrah ta yi shiru bata ce uffan ba tana ƙoƙarin kammala na hannunta su shiga ciki

Zahra ce ta dago kai, tana magana kasa-kasq

"Mama ai kullum naga ana sayar da tuwo a gidan nan, ba wanda ya taba cewa kuna bata gida da tara Matan unguwa ma, su taru suyi ta dariya da gulma a nan gidan amma ba'a taɓa magana ba sai wanda zai siya gawayi a bakin kofar gida shine za'a ce muna tara mutane" Azrah ta sake baki tana kallonta with shock, ita kuwa ta fusge kamar ba itace ta gama magana kasa kasa ba

Mama ta daga hannu da sauri tana yi musu ashar

"Ni kike wa magana da rashin kunya ke?! Uwarki zanci shegiya fitsararri ƴar tasha mara tarbiyya kawai"

Zahra ta gyara zama, amma bata ƙara cewa komai ba saima karatu data Fara, Azrah ma tayi kamar ba ta jiyo ba dan bata son fitinan Mama ga Zahra kuma bata iya shiru ba

A nan ne Bappah ya shigo daga waje yana bubbuga takalmi

"Me ke faruwa ne kuma da daddare haka?"

Mama ta nufo shi tana cewa da ƙara

"Ka rabani da waɗan nan yaranka, wallahi ba su da tarbiyya! Azrah da Zahra sun gaji halin Uwarsu, harni zasu faɗawa magana dan nace suna ɓata mana gida dagawayi shine zasu zageni"

Bappah ya tsaya yana kallonsu Kallo guda ya yi wa Azrah, sannan ya kai ga Zahra, ya sauke ajiyar zuciya bai ce komai ba

Ya juya ya wuce ɗakinsa bayan gaishe sa da suka yi wanda ko amsa bai basu ba, Azrah ta gyara buhun gawayin ta shiga ciki a hankali, ba tare da ta kalli Mama ba, amma tana jin zafin kalamanta

We're just trying to survive, Mama.

*BEYOND THE VEIL* (LABULEN SIRRIN)


YOTA ID/026

Wattpad © Jiddatulkhayr
Instagram © Jiddatulkhayr writes


Free page

Episode 8: A Setback

Bayan wasu kwanaki.... Rayuwa ta cigaba da tafiya musu jita iya yau, amma Azrah koda wasa bata taɓa cire hope ba, tana kuma gwagwarmayarta kamar yadda ta saba, da safe makaranta da yamma sana'a da daddare kuma karatu, Bata da hutu amma zuciyarta na ɗauke da burin zama wani a gaba da hoping bright future, Duk sanda take jin kamar ta gaji, sai ta tuna da cewar babu wani wanda zai gina mata gobenta sai ita. Kuma kullum da safe tana saka ₦500-800 a cikin asusunta da take kiyayewa kamar rainta tana fatan zata kai target kafin lokacin candy

Zahra na taimaka mata sosai, ita ke kai kayan sana'ar da Azrah ke sayarwa makarantar su, Zahra ke kai mata snacks data Fara kanti da kuma makarantar ta, Zahra na ɗaukar nauyin kai kaya ko da rana rana ce bata jin ko wahala as per as zasu samu kuɗin da suke tarawa cos basu dogara da kowa ba takan yawan cewa "Ni da Yayata wallahi mun rantse sai mun fita a cikin wahalar rayuwa, wata rana Umma zata yi rayuwar farin ciki"

Wata rana.. bayan sun gama morning assembly a makaranta, Principal ta hau stage da muryarta mai hope da kwanciyar hankali

"Important notice to all students: Registration for the Candy program is closing in three days. Students intending to sit for the WAEC exam this year should complete their registration by 12 PM tomorrow to avoid missing the deadline. After this time, the final list of participants will be submitted to the relevant authorities"

Azrah ta tsaya cak, Saura kwanaki uku? Zuciyarta ta buga, Hannunta ya fara sanyi, idona ya fara tara ruwa, a zuciyarta ta ɗauki ƙudurin Yau saita gayawa Bappah duk abinda zai yi kawai ya karɓa mata kuɗin a wajan Mama dama ai responsibilities dinsa ne

Da ta dawo gida bayan ta huta kaɗan, sannan ta fita zuwa ɗakin Bappah, wanda ke zaune yana karanta wani jarida, da sallama ta shiga ta gaishe sa

"Bappah…" ta furta a hankali, Ya ɗago kai da murmushi ya ce

"Na’am?"

"Bappah dama ina so na roƙeka ne, Ka taimaka min da kuɗin registration na candy, Sauran kuɗin da nake da shi kaɗan ne sannan kuma jibi zasu rufe" Bappah ya ce

"Shine baki yi magana ba sai yau Azrah" tayi kasa da murya ta ce

"Bappah kaine kace ai kana sane lokacin dana taɓa maka magana sannan ai kace ka bawa Mama kuɗi ta juya, siyasa banyi magana ba" Bappah ya ɗan gyara zama

"Toh ni bani da kuɗin, amma zan karɓo daga wajen Mama idan har zata iya bayarwa" Azrah ta ji wani farin ciki ya lulluɓe ta ta ce

"Nagode sosai Bappah" ya miƙe itama miƙewan tayi ya fita tana biye dashi a baya ɗakin Mama ya nufa sai kawai ta tsaya a compound ɗin tana jiransa, can ta fara jiyo muryan Mama tana faɗin

"Ni babu wani kuɗi a wajena yanzu Malam, Kuɗin magani da sayen abinci sun cinye komai, Ka duba wani wuri kawai dan Allah, amma taya kuɗi zasu zauna ne"

Bappah yayi shiru na ɗan lokaci kafin ya fice daga ɗakin da hannunsa a aljihun wandon sa, Bai ce uffan ba har ya wuce Azrah dake tsaye da idonta cike da hawaye

"Bappah…?" ta kira shi da ta kira sa muryan ta kasa kasa, Amma bai tsaya ba balle ya kalle ta

Zuciyarta ta tsinke, tayi ta kallon dakin Mama, sai kawai ta nufi dakin Umma da hawaye suna gangarawa daga idonta

"Umma… shikenan kenan?" ta faɗa cikin kuka

Umma ta nufe ta, ta rungume ta sosai "Ki daina kuka Azrah, Wallahi Allah zai kawo miki mafita, Kuɗi ba shine komai ba, Ni na san irin ƙoƙarin da kike yi, Allah kuma ba zai bar ki ba" Azrah ta girgiza kai

"No Umma, saura 3days fah! Ya zanyi toh?" Umma ta ce

"Ya ku kayi da Bappahn naku kuma?" Ta ce

"Wai bashi da kuɗi, sannan kuma Mama wai ta gama kashe kuɗin akan kayan abinci da magani, just imagine waɗannan makudan kuɗin ne ta kashe su Umma" tana gama magana ta sake fashewa da kuka, Umma taji ranta ya fara tafarfasa ta ce

"Wuce ciki Azrah" daga haka ita kuma tayi ɗakin Bappah ranta a mugun ɓace tana shiga da sallama ya ɗago kai yana kallonta ya ce

"Lafiya kika tsaya min a kai?" Ta ce

"A'a, i doubt much!" With shock Bappah ke kallonta ya ce

"Ina jinki toh tunda ba lafiyar kike son a zauna ba" ta ce

"Gaba ɗaya nawin da Allah ya ɗaura maka ka yarda su, ka bar yaranka mata suna ɗaukar ɗawainiyar kansu, yanzu idan har Azrah ta biya kuɗin nan ai dai ka tambaya aina ta samu amma kai ko a jikin ka, yanzu yarinyar nan so kake ta fara wani tunanin na daban ko me? Ya za'a yi tace maka za'a kulle abu kace baka da kuɗi"  yayin saurin katse ta ya ce

"Toh karya nayi ina da kuɗin ne?" Ta ce

"Idan baka da kuɗin ai da lokacin da ka sayar da mashin ɗinka sai ka bani kuɗin na ajiye musu ko ka bani na ja jari amma ka ɗauka ka bawa Matarka yanzu kuma tana cewa ba zata bayar ba saboda ita ai bata san darajar karatun ba"

Muryan Mama suka jiyo wanda tana kan yaye labulen ɗakin Bappahn "Eh bansani ba kam, saboda ke da kike da karatun da shi kansa Malam ɗin duk rayuwa ɗaya muke a gidan nan dan ina jin gwara Ni ma dan duk nafi walwala daku" tana dasa aya ta tuntsere da dariya

Umma ta juyo dan ita bata da lokacin exchanging words da ita ba, dan lokuta da dama tana bata uzuri dan jahilci ke damun ta tayi ficewar ta ba tare da ta sake bi ta kan Bappahn ba.

Haka Azrah ta zauna banda kuka babu abin da take yi ko abinci ta kasa ci, tun Amma na rarrashinta harta hakura ta kyale ta.

Bayan Magrib tana zaune a bakin katifarsu ta ce "Saura kwana uku kawai…" ta faɗa a hankali "Me zan ce wa kaina idan na rasa damar nan? Sai dai kawai in ci gaba da sayar da kayan miya kenan? Bani da wata mafita kenan?"

Zahra ta zauna gefenta ta riƙe hannunta "Yaya ki daina kuka please, Allah yana tare da mai haƙuri Ki duba irin wahalar da kika sha,kina da buri, Allah ba zai barki haka ba, keep on positive mindset"

Azrah bata iya magana ba Kukanta ta cigaba, A haka har ta gaji da kukan har bacci ya ɗauketa.

Around 2:45 na dare Umma na zaune akan darduma, tana jan carbi, tun ɗazu ta tashi tayi ta salloli tana ma Azrah addu'a sannan Allah ya cire su a wannan wahalar da su ciki

"Ya Allah ka gani, Ba mu da kowa sai Kai, ka yaye wa ‘yata damuwarta, Ya Rabbi ka bata wata mafitan wanda zata ɓullowa wannan lamarin ka tabbatar mata da abinda yake Alkhairi"

Meanwhile a ɗakin su Azrah, Zahra ma sallan take yi tana taya 'yar uwarta addu'a Allah ya kawo musu wata mafitan

"Allah Ka amsa addu'ar Azrah, Ka sa tana da rabo a wannan candyn, Ka duba irin ƙoƙarinta ka bamu wata hanyar da za'a biya mata kuɗin" a haka suka yi ta mata addu'a har asuba tayi wanda Azrah bata ma san sun mata addu'ar ba

Da safe bayan sun idar da Sallah sun gama azkar ɗinsu Azrah ta fita ta fara aikin tattare gidan tana gamawa ta kama wanke wanke sannan ta ɗaura breakfast

Umma dake kallon Zahra ta ce

"Zahra je ki kira min Azrah" bayan Zahra ta fita ko kallon Mama da Yaranta dake bakin murhu suna abincin tallan batayi ba dan yanzu taji ta tsane Mama with passion dan da tana gida abin nan ya faru da tana ji zata iya gaya mata magana, ta wuce su ta wuce inda Azrah take jefa ɗan wake

Siyama ta sake baki tana kallon Zahra da mamaki ganin ta wuce su ba magana ta ce

"Toh yarinyar nan rashin kunya ta karo kenan?" Mama tayi dariya ta ce

"Kyale shegiya suna cikin tashin hankali ne ai yanzu"

Zahra na kallon Azrah ta ce

"Anty Azrah inji Umma idan kin gama ki zo tana neman ki" Azrah ta gyaɗa mata kai kawai.

Umma na kwallon Azrah bayan sun gama breakfast ta ce

"Azrah jeki ɗauko asusun nan ki fasa muga nawa ne kuɗin sai mu san nawa zamu cika" Azrah ta miƙe jiki ba ƙwari duk da yanzu ta hakura ta dai na kukan

Bayan sun fasa asusun suka irga kuɗin suka ga ₦21,000 ne sauran wajan ₦16,000 Umma ta numfasa ta ce

"Zanje gidan su Aziza anjima, koda rance ne zan karɓo, sai ku shirya ku tafi makarantar Azrah dan ba zan barki a gida ba balle ki cigaba da kukan nan"

Murmushi kawai Azrah tayi, ta tattara kuɗin tasa a fos ɗin Umma sannan ta kai cikin ɗakin Umma ta ajiye akan mirror.

Wajajen 12:20pm Abdul ya dawo gidan tun daga bakin kofar yake ta doka sallama amma yaji gidan shiru, ya shiga ya kalli direction ɗin Mama yasan cewa su Siyama suna can wajan tallansu Mama kuma yasan ta shiga wajan Naman asabe ɗakin Umma ya kalla kamar zai fita sai kuma ya karasa ya shiga

Kalle kallen cikin ɗakin su Azrah ya fara sai kuma ya shiga ɗakin Umma idon sa akan fos ɗin ya sauka da murmushi ya karasa ya buɗe fos ɗin ai kuwa yayi tozali da kuɗin dake ciki da sauri har hannunsa yana rawa ya ciro kuɗin ya saka a aljihun sa da sauri ya fito, Azrah da ta taso a makaranta ta shigo gidan da mamaki take kallon Abdul daya fito daga ɗakinsu ta sake baki tana kallonsa ko kallonta bai yarda yayi ba ya fice daga gidan gaba ɗaya


This book costs 500. Make the payment to Hauwa Jibrin, Wema Bank account 0421255553, and send proof of payment to 08110615256.

#Jiddatulkhayr
08110615256

*BEYOND THE VEIL* (LABULEN SIRRIN)


YOTA ID/026

Wattpad © Jiddatulkhayr
Instagram © Jiddatulkhayr writes


Free page

Episode 9: The Missing Funds

Kamar wadda aka dasa ta a wajan haka ya tsaya tana bin inda ya fita da kallon mamaki kamar wadda take shirin sensing ɗin abinda ya kaisa ɗakinsu jiki ba ƙwari ta karasa cikin ɗakin tana bi da kallo, wanda ganin babu wani abu daya canza yasa ta cire hijabinta ta kwanta dan kanta ke mata ciwo, bata daɗe ba sai ga Umma da Zahra wanda a hanya suka haɗu bayan sun shiga da sallama Azrah ta miƙe zaune tana kallon Umma ta ce

"Umma an dace kuwa?" Umma ta zare Hijabin jikinta tana sauke ajiyar zuciya, Zahra ta Kalle Umma ganin kamar mata ji Azrah bane yasa ta ce

"Umma Yaya fah magana take miki wai an samu?" Umma ta girgiza kai ciƙe da lallashi kuma da kwanciyar da hankali ga ƴaƴanta ta ce

"Ba'a samu ba amma ta ce zuwa anjima idan ta samu kuɗin da take bin wata zata aiko min" Azrah taji hawaye ya fara taruwa mata ta ce

"Ina ga zan cire rai kawai Umma, kila bani da rabone a karatu" Zahra ta ce

"Balle ma za'a samu in shaa Allah" Umma na kallon Azrah amma ta kasa cewa komai dan gaskiyar maganar kenan bata samu ba, miƙewa Umma tayi ta wuce ɗakinta da niyyar kwanciya sai dai tun daga bakin kofar take kallon fos ɗinta dake buɗe a yashe a bakin kofar ta ɗinga kallo babu ko kiftawa zuciyarta na bugawa da ƙarfi sai kuma tabi ɗakin da kallo, Zahra dake kallon reaction ɗin Umma ta ce

"Umma menene? Wani abu ne?" Umma ta girgiza kai ta ce

"Ina ganin kamar wani ya shigo fa kalli fos ɗin nan a yashe a ƙasa" ai a saba'in Azrah ta miƙe Zahra ta karasa bakin kofar da wuri ta shige Umma ta karasa ta ɗauki fos dake ɓuɗe babu komai a ciki ta ce

"Kambala'iiii wani tsinannan ne ya shigo mana cikin gida harda sace mana kuɗi" ta karasa maganar tana riƙe ƙugu kamar tana gaban wanda ya sace kuɗin, Azrah tayi murmushin karfin hali ta koma ta zauna tayi tagumi dan bata masan me zata ce ba, she's just speechless

Zahra banda masifa da tsinewa wanda ya ɗauki kuɗin babu abinda take yi, Umma ma ta koma ta zauna tana kallon Azrah, Azrah ta ɗago kai tana kallon Umma, Umma ta ce

"Dan Allah waye zai mana wannan abu har haka ko tausaya mana ba zaiji ba" Azrah ta girgiza kanta tayi kasa da muryanta yadda Zahra ba zata iya ji ba ta ce

"Umma shigowa na naga Ya Abdul na fitowa daga ɗakin nan sannan kuma bai yarda ya haɗa ido dani ba kuma ko kara second baiyi ba a gidan ya bar gidan" Umma tayi shiru tana kallonta da mamaki

"Dan uwarshi shi ya ajiye kuɗin da zai ɗauka, sannan kuma kika kyalesa har ya fita baki yi wani abu ba?" Zahra ta karasa maganar da zafin rai, Azrah tayi shiru dan bata so taji ba

Fitowa tayi daga ɗakin tana kallon Azrah ta ce

"Just imagine shine kika tsaya kallonsa har ya fita halan?" Tana maganar ta mayar da kallonta ga Umma ta ce

"Wallahi sai ya biya kuɗin nan ko kuma wallahi zai sha mamakin abin da zan masa" Umma ta sake baki tana kallon Zahra da mamaki dan tana ga kamar Zahra ta manta wanene Abdul, wanda har Siyama ya girma amma take maganar zai sha mamaki, ta zauna tana huci ta ce

"Yanzu idan Mamansu Aziza ta kawo na wajan ta kuma ya za'ayi? Sannan yau fah saura kwana biyu kenan?" Ai Azrah bata san sanda ta mike ba tana kallon Umma wanda har sannan hawaye ya fara zuba a idon ta tana kallon Umma ta ce

"Umma ina zuwa bari naje makarantar mu na tambaya zan iya biyan zallan neco da kaina tunda ba yanzu za'ayi ba amma yanzu kam babu wani hope to Dan ba zamu samu wannan kuɗin daga yau zuwa gobe ba" kafin Umma tayi magana harta fice

Zahra ta fito compound ɗin tana bi da kallo ko zata ga wani abu mai amfaninsu sai dai bata gani ba ga kuma kofarsu a garkame dama sune basu kulle kofa sai dai su tura su kulle babu key

Azrah tana shiga cikin makarantar su ta wuce office ɗin principal ɗinsu wanda da alama yana da bako kuma suna magana ne, ta tsaya a bakin kofar tana jiran ya fito, tafi minti biyar sai can aka buɗe kofar wani mutum ya fito daga office ɗin ta ɗan matsa masa baya tana kallonsa ta gaishe sa ya amsa mata yana washe mata baki ya ce

"Ya aka yi ƴanmata?" Ta girgiza masa kai ta ce

"A'a wajan principal ɗinmu nazo" ya matsa mata da sauri yana

"Toh toh toh shiga mana, ashe Kema ƴar makarantar ne, ai shikenan" daga haka ya sauka akan dakali ita kuma ta tura kofar officen ɗin ta shiga da sallama principal ɗin ya ɗago kansa yana kallon Azrah yana murmushi ya ce

"Azrah ke ce?" Kai ta gƴaɗa masa ta ce

"Yes sir, good afternoon" ya ce

"Afternoon, have a seat mana" ta zauna tayi shiru tana kallon sa sai kuma ya ce

"What is it? Akwai matsala ne Azrah ?" Ta gƴaɗa masa kai ta ce

"Sir, regarding maganar candy ne, wallahi kuɗin da muka tara an sace kuma bamu san inda zamu samu kuɗi daga yau zuwa gobe ba" yayi shiru sai kuma ya ce

"SubhanAllah! A garin yaya kenan? Allah ya tsare" ta ce

"Amin, shine yanzu nake so naji koda an rufe zuwa nan da a fara maganar registration ɗin NECO zan iya ma kaina?" Ya girgiza kai ya ce

"A'a daga can ministry of education za'a muku amma gaskiya sai wanda suka zana candy suka ci sune za'a ɗauka sunan su a biya musu both SSCE Exams ɗin, Kinga ba zaiyu ba sai dai idan zaki je wata makarantar ne kawai kiyi amma sai private school" tayi shiru kamar mai nazari can ta ce

"But sir, ina neman favor please a ka taimaka min yadda Allah ya taimaka maka ka rufamin asiri ka biya min wallahi kafin mu gama candyn Zan mayar maka da kuɗin ka" kallonta yake babu ko kiftawa sai kuma yayi murmushi ya gyara zamansa yana shafa fuskarsa ya ce

"Ai Azrah baki san me ba, duk sunan da muka kai musu muka ce sune wanda suka ci candy toh za'a biya musu kuɗin WAEC da NECO sannan kuma the best student za'a biya musu Jamb harda sponsoring karatun su" Azrah ta fara jin wani hope da maganarsa ta gyara zaman ta fuskarta ya fara bayyana alamun murmushi ta ce

"Okay, kuma duk daga government house ɗin kenan, Allah sarki governor, toh dan Allah Sir ka taimaka min sai kasa harda sunana mana" yayi murmushi ya ce

"Yadda kike kyakkyawar gaske har sai kin bada hakuri wai? Toh uban waye bai san kokarin ki a makarantar nan ba, ko baki yi candy ba zan saka sunan ki" Azrah ta share hawayen fuskanta ta ce

"Nagode sosai sir, Allah maka fiye da yadda ka faranta min"  wani kallo yake mata wanda yasa godiyan da take masa maƙalewa tana kallonsa da mamaki ganin inda yake kallo Shima yayi shiru yana kallonta, sai can ya ce

"Zan iya taimaka miki Azrah, Amma you know, not everything comes for free..." Gabanta ya faɗi ta ce

"Excuse me? Ban gane ba sir" yana murmushi ya ce

"You're a smart girl Azrah, A pretty one too, Think about it" ya kare maganar yana kashe mata ido ɗaya meanwhile yana kokarin kai hannun sa jikinta

Azrah ta miƙe da sauri, hawaye na taruwa a idonta ta ce

"Thank you Sir, But I didn't come here to sell myself" wani murmushi yayi yana nuna mata hanyar fita ya ce

"Then, out"

Ta juya ta fice, jikinta ba ƙarfi.
Amma zuciyarta cike da karfin hali da hope ta fita daga building ɗin kamar wanda ruwan sama ya mata duka

Tayi ta tsaye a waje, tana kallon gate, tana ma kanta magana

"Ko da nayi kuka… ko da na rasa wannan damar… ban rasa mutuncina ba" ta harari gate ɗin tana jin zafi a zuciyarta ta kama hanyar gida

Harta isa gida bata daina mamakin principal ɗinsu ba wato yanzu babu wanda zai yi taimako saboda Allah, bayan ta shiga gida ta wuce ɗakin su taga Umma na zaune ga Zahra gefenta suna jin wani program a radiyo Umma ta ce

"Ya akayi Azrah?" Azrah ta girgiza kai tace

"Babu wata mafita kawai Umma" daga haka ta wuce ɗakin su Zahra ta bita da sauri ganin mood dinta ta ce

"Ya ake ciki Anty? Ba zai taimaka miki ba?" Azrah tayi murmushin dole ta ce

"Babu wanda zaiyi taimako saboda Allah sai ya nema ya lalata ka" Zahra ta sake matsowa kusa da ita ta ce

"What do you mean? Wai ba iskanci zai yi da ke dan Ubansa?" kai kawai Azrah ta gyaɗa mata kai, Zahra tayi wani murmushi ta ce

"I wish Ina wajan wallahi sai ya raina kansa banza jaki kawai, ce masa akayi talauci hauka ne da har saboda shegiyar wata waec zaki tsaɓawa Allah" ta miƙe tana jan wani dogon tsaki ta bar ɗakin dan ita taji harta tsane mutumin.


Yamma ta gama lullube garin ga wani hadari mai ɗauke da iska garin yayi daɗi, daga nesa da kuma neighbors ɗin kana jin hayaniyar yaran unguwar da ihun su alamun wasa dai suke, mutane na gaisawa, wasu kuma na dawowa daga kasuwa da gajiya rubuce a fuskokinsu

Bappah ya dawo gida yana shigowa kamar yadda ya saba bai yarda yayi making any sounds ba ya danna ƙofar ɗakinsa ya shige ba tare da kowa ya lura da zuwansa ba, A can cikin dakin, ya cire hularsa ya aje ya kwanta dan baya son kowa yasan yana nan

Haka Umma ta wuni a gidan bata da wani sukuni ganin yadda Azrah ma ke cikin tashin hankali, tana jin shigowar Bappah ta miƙe da sauri ta nufe ɗakinsa gudun kar anjima Mama tazo ta makale dan yanzu ita da bappah take son magana ba wani third party

Ta tura kofar ta shiga da sallama fuskarta cike da damuwa bayan sun gaisa ta ce

"Malam... dan Allah ka sauraren Ni kuma ka duba lamarin nan" ta ce da sanyi muryarta kamar wacce ke buƙatar taimakon sa

Bappah ya ɗago kai daga inda yake zaune, yana gyara zamansa ya ce

"Lafiya Bitti?"

Umma ta tura ƙofar ta rufe, sannan ta matso kusa "Yau an ɗauke kuɗin candyn Azrah daga inda ta ajiye Malam, Kuma an ce Abdul an ganshi yana fitowa daga ɗakinta yau, Na san ba wani shaida, amma akwai ayar tambaya ai Malam, kuma kai ka fi kowa sanin halinsa"

Bappah ya lumshe idanu yana sauke numfashi da ƙarfi, ya furzar da Islam bakinsa Bai ce komai ba, sai ya miƙe tsaye da sauri, Ya fice zuwa filin sakar gida cike da fushi kamar wanda zai tashi sama Kuma yasan Abdul zai ai kata

"Ke Fatsuma?! Ina ɗanki yake ya za'ayi ya shiga ɗakinsu Zahra ya sami makuɗan kuɗi masu mugun yawa na candyn ta? Gidan nan ba na sata bane! Ki kiransa tun da wuri ya dawo da kuɗin nan kafin ya kashe! Kuma bana son jin wani abu makamancin haka, wallahi sai na ɗauki mataki!”

Zahra dake zaune a bakin ƙofar ɗakinsu ta miƙe da sauri, zuciyarta cike da takaici, sai ta fara zazzaga tsinuwa ga wanda ya ɗauke kuɗin "Wallahi duk wanda ya saci kuɗin nan Allah zai nuna masa, tun daga yau ba sai gobe ba, Sannan rayuwar sa ba zata taɓa kyau ba, zai kare a roko kuwa, Kudin da aka tara da hawaye da yunwa ya zo kawai ya ɗauka kamar ba komai ba ko kuma nace kamar shi ya ajiye?"

Kafin kowa ya yi wata magana, sai ga Mama ta fito daga ɗakinta cikin hanzari kamar wacce aka kork

"Sharrin banza da wofi! Duk faɗin gidan nan, sai ɗana kuke zargi? Abdul ba barawo bane! Wani irin rashin adalci ne haka Malam? Kaje ka biye wa banzar matarka" ta kare maganar da mugun karfi tana son tayi eye contact da Bappah ai kuwa suna haɗa ido Bappah ya zama mute, gashi ta cika gidan da surutun da kowa ya sani idan Mama ta fara sai ta gama take hakura

Bappah ya juya kamar zai ce wani abu amma sai ya ƙasa, Ya juya ya koma cikin ɗakinsa zuciyarsa na tafarfasa Haka ma Umma tayi shiru, ta dawo ɗakinta da zuciya mai rauni da shakku

Zahra kuwa ta cigaba da zama a bakin ƙofa, tana huci kamar tanderu ta ce a kaikaice

"Ni dai ban ce da kowa ba, amma duk wanda ya sace kuɗin nan shi da yin kuɗi sai a lahira idan ana yi amma shi da uwarsa da kannansa sai dai suga a maƙwafta, kuma Allah ya isa, dan  barawo barawo ne!"

Mama ta juyo cikin hargowa "Dan Uwarki da ni kike yi Zahra? wani kike faɗar waɗannan maganganun?"

Zahra ta kalle ta da idonta da babu tsoro, ta ce

"Na ce wanda ya saci kudin, amma Kinga na kira suna? Ai Ni da wanda ya sace nake magana"

Mama tayi shiru tana Binta da wani banzan kallon, Zahra ta ɗauke kanta ta cigaba da addu'o'in ta daga karshe Mama ta koma ciki.

Da daddare har Azrah ta kwanta kawai ta sake tuno yadda suka yi da principal ɗan saki tayi ta gyara kwanciyar ta kawai wani magana daga maganar principal ya faɗi mata da sauri ta miƙe zaune tana tunanin ambatan gomnati da yayi, ai gwamma na kowa ne why not gobe kawai ta tafi government house idan har zaiyu, murmushi tayi ganin ga wani Alternative kuma jikin ta bai bata zata yi loosing wannan karan ba da wannan tunanin ta kwanta a ranta.


This book costs 500. Make the payment to Hauwa Jibrin, Wema Bank account 0421255553, and send proof of payment to 08110615256.
*BEYOND THE VEIL*(LABULEN SIRRIN)


YOTA ID/026


Wattpad © Jiddatulkhayr
Instagram © Jiddatulkhayr writes


Free page

Episode 10: When fate opens the right door

Washe gari tun asuba'in fari Azrah ta farka, damuwa ce fal a zuciyar Azrah, Ba ta yi baccin kirki ba, she's just pretending saboda Zahra, sosai idanuwanta sun kumbura saboda rashin baccin kirki, salloli ta dinga yi har akayi sallah sannan itama ta daura, tana cikin sallah Zahra ta tashi ta fita itama dan ɗauro alwala, tana starring waje ɗaya tana ƙoƙarin gamsar da kanta cewa yau tana da mafita dan da tunanin Jiya ta kwana kuma da shi ta tashi kuma ta gama making mind ɗinta up

Dan bata da wani sauran lokacin and kuma ba zata hakura ba sai ta gwada trying luck ɗinta, zata rubuta candy, Kuma yau ita ce ranar da ta yanke shawarar tunkarar wajan no matter what zata je

Da ƙarfe takwas da rabi na safe, ta fito cikin tsaffin doguwar riga da mayafinta mai launin Maroon wanda ya sake bayyana tsantsan beautyn ta, amma fuskarta cike take da fargaba dan babu annurin amma hakan bai ɓoye kyaunta ba, ta ɗaura jakarta a kafaɗa, cike da takardun candy, da kuma result ɗinta tun daga JSS1 to SS2 da kuma many awards certificate data samu wasu na spellings wasu kuma na best student wasu kuma na debate ne, Zahra ta fito daga ɗaki tana kallonta da mamaki ta ce

"Ina kuma zuwa da sassafen nan Yaya?" Azrah ta mata murmushi ta ce

"Zan je wani waje ne Zahra... Idan na dawo zan baki labari" ta kare maganar da assurance da kuma murmushi karfin hali, Zahra ta ce

"Allah Ya tsare ki Yaya, ya kuma baki sa'a koma menene na san it's going to be best" Zahra ta karasa maganar amma zuciyarta cike take tambayoyi.

Azrah ta leƙa ɗakin Umma ganin tana bacci kawai ta fita ba tare da ta tashe ta ba

Haka ta dinga tafiya da ƙafa, wasu motar su tsareta amma taki tsayawa wasu kuma su biyo ta amma duk babu wanda ta tanka musu, idan sun gaji dan kansu suke kyaleta a haka harta isa....

A gaban Government House taga wani motar na tsaye amma bata ma kalli inda motar yake ba dan wannan bashi ne a gabanta ba

Securities na wajan suna zaune, sai ga wani a bakin gate yana dube-duben masu shigowa da fita Azrah tana tunkaran sa, tana takawa cikin nutsuwa, sai dai a zuciyarta damuwa da tsoro sun fi yawa

"Ke! Ina zaki?" daya daga cikin securities ɗin ya tsayar da ita da tsawa kamar ba dan adam ba

Azrah ta ɗan ja baya da tsoro amma bata bari yayi affecting ɗinta ba cos yanzu ba tsoro bane a gabanta, ta ce

"Don Allah ina son naga gwamna ko wani Babba a ciki" wani kallo ya mata alamar bai gane ba? Irin is she even Okay? Ta ce

"Dama na zo ne akan maganar taimako, ina son na gan..." Tuntsurewa suka yi da dariya dan ba kaɗan ba ta basu dariya ɗayan yana kallon abokin aikin sa ya ce

"Is she even Alright?" ɗayan ya Kalle sa dan shima abin da mamaki ya ce

"I doubt much" Azrah tayi saurin cewa "I'm much Alright sir, taimako zaku min fah, dama government house ba wajan taimako bane?" Ya ce

"Ke! Koma baya! Bamu da lokacin wannan rubbish ɗin naki"

Azrah ta kafe su da ido, idonta cike da ƙwalla Sai wani ɗayan security mai taushi ya kalle ta sai kuma yayi kasa da murya

"Ke! Wayarki akwai kati?"

Ta ɗaga kai da mamaki take kallon sa ta ce "Eh... me zaka yi da ita?"

"Ki kira wanda kika zo nema, idan har da izini kika zo, zai fito ya shiga dake ko kuma ya kira waya ya ce a barki ki shiga"

Azrah ta yi shiru, toh waya ai bata da ita, ace tana da waya ai ba zata ma tsaya a wajan ba da tuni ta sayar, kuma ko da akwai wayan wa zata kira a ciki? Wa ta sani? Sai kawai ta ce "Ban da waya, banzo da ita ba"

"Eh toh, idan baki da waya, kuma baki da wanda zai fito ya shigar dake ko ayi waya, ya kike so mu miki?, wannan ma ai raini ne"

Azrah ta saki ajiyar zuciya

"Wallahi ba raini bane, dama... na zo ne akan maganar candy jarabawar sakandire, Ina nema ne a taimaka min da kuɗin rijista, Ban da wanda zai taimaka min ne sai nayi tunanin nan zan samu mafita tunda ai nan kowa zai iya kawo kukansa kuma a share masa"

"Ke! Ki juya! Bamu da lokacin sauraran karatun novel ɗinnan naki"

Amma kafin ta juya, wannan motar da ta gani tun ɗazu a wajan mai plate no ɗin gwamnati ta kuso kai zata shiga ciki, Azrah ta matsa gefe da sauri tana gyara mayafinta. Da sauri security ya buɗe musu gate, Matar cikin motar ta hango Azrah tana kade hannunta kuma duk tayi abin tausayi, kuma taji Convo ɗinsu, sai ta leƙa ta ce

"Wannan yarinyar fa?"

"Wani matsiyaciya ce da take cewa wai tana son a taimaka mata da kuɗin jarabawa" Matar ta ce da sanyin muryarta

"Ku bari ta shigo, muna buƙatar jin irin waɗannan yaran and she looks serious and responsible"

Security ya harareta amma ya ce

"Ke! Shigo"

Azrah ta kafe shi da idanu na godiya amma bata ce komai ba Tayi shigarta ciki, zuciyarta cike da fargaba da fatan Alkhairi

A cikin ginin Government House...

An kaita wani ofis na musamman a sashin kula da harkokin jama'a wato Public affairs Unit, banda addu'a babu abinda take yi, fatan Allah bata Sa'a kawai take duk da yanzu taji hankalin ta ya kwanta

Bayan ta zauna na mintuna wani mutum mai kamala kuma alamar girma ya shigo Shine Honorable Ibrahim Yusuf ɗaya daga cikin ‘yan siyasan da suka fi riƙewa a jihar da taimako ga al'umma, kallo ɗaya yama Azrah ya ɗauke kansa, Yana magana in very calm way kamar ba wani Babba bane a jihar yana kallon matar dake kofa ya ce

"Who is this girl?" Ta ɗan risina ta ce

"She came for help concerning education, sir" ya ce

"Let me speak to her, bring her in" daga haka ya shige ofis ɗin dake cikin wannan, Matar ta shiga da ita ciki sai kuma ta fito

"Assalamu alaikum" ta faɗa kanta a kasa ya ce

"Wa’alaikumus Salam" ya amsa mata ya ce

"Have a seat" ta ce

"thank you sir" sai sannan ta zauna

"An ce kina da matsala ne akan candy right?"

"Eh ranka shi dade, Sun ce za'a rufe rijista saura kwanaki biyu yau, kuma kuɗin jarabawar wanda na tara da kuɗin sana'ata an sace kuma babu enough time it's already late balle na sake tarawa, kuma a gida ma bamu da su... Na zo ne don neman taimako"

Ya zauna yana kallonta da mamaki

"Kin zo Government House ke kaɗai? Ba tare da rubutaccen wasiƙa ba? Ko wakili ba?"

Azrah ta girgiza kai "Eh... I follow my heart ne na taho Ina ganin idan akwai inda zasu saurare ni to nan ne"

Honorable Ibrahim ya gyara zaman sa dan banda mamaki ta babu abinda yake yi, kuma iyakar gaskiyar ta yake gani a kwayar idonta, maganar kuma itake tara kuɗin sana'ar ya tsaya masa a rai ya ce

"You mena you hustle and still go to school? Sannan ke kika tara kuɗin registern da farko?"

Ta gƴaɗa masa kai ta ce

Yes sir, Ina sayar da kayan miya, ina ƙulla gawayi da daddare, Zahra kanwata tana taimaka min da kai kaya makarantar su, and other stuffs Mun kai rabin kuɗin da ake nema sai aka sace su"

Kawai ya tsaya kallon ta ita kuma ta ɗauka bai yarda bane yasa ta ciro file daga jakkanta ta miƙa masa ya karɓa yana mamakin ganin results dinta, ba kaɗanba ta basa tausayi yasan tasa karatunne a rai shiyasa ya ce

"Me yasa kika cigaba da ƙoƙari duk da wannan wahala?"

Sai Azrah ta kalle shi da idanuwa masu ɗauke da tarihi ta ce

"Saboda bana son zama kamar wasu mata da suka saida mutuncinsu saboda jarabawa Ina da burin zama likita Ina son taimakon mutane... kamar yadda bani da wanda ya taimake ni"

Ya lumshe idanu yana sauraren kalamanta kamar yana karanta littafi mai sutsar da zuciya ya buɗe idon yana kallon ta ya ce

"Ki ba ni tarihin rayuwarki... daga farko, Ina son jin wane irin yara ne ke fuskantar irin wannan rayuwar "

Azrah ta sauke ajiyar zuciya sannan ta fara... ta faɗa masa yadda rayuwa ta canza bayan lokacin da karayar arziki ta samu Bappah, Yadda take aikatau a gidan mutane da irin sana'ar data yi wanda ba zata iya irgasu ba, da yadda Umman ta take fama da lalura har yasa ta bata kuɗin data tara, yadda suke fama dan ita ke ɗaukan nawin kanta da mahaifiyarta sai kanwarta, Bata ɓoye komai ba

Ya ɗaga kansa cike da tausayi ya ce

"Alright... I will help you In Shaa Allah Amma before that give me your number"

Azrah ta kalli ƙasa ta ce

"I don't have a phone sir" ya ce

"No phone? Hmm… Okay, give me your mother's number then"

Ta fara furta masa numbern Umman yana typing a wayan sa ya ce

"Where do you live?"

Ta faɗa masa sunan unguwarsu da kwatancin gidan su

Ya ɗan yi shiru sai can kuma ya ce

"You're brave Azrah, You could've ended up in something else, but you're still focused" ta ce

"Na zaɓi mutunci sir, Ko da wahala ta min yawa, nasan one day definitely zanji daɗin hakan" Ya murmusa

"I respect that! From today, I'll personally support your education in shaa Allah, But I also want you to report back after your exams kunji?" Idanunta cike da hawaye ta ce

"Nagode sosai sir, Allah ya saka da Alkhairi, ya kare ka"

Ya miƙa mata kuɗi
"This is for your Tp"

Ta karɓa da duka hannayenta biyu tana jin babu irin kalmomin da zata iya masa godiya da shi, tana share hawayenta

Ya miƙe tsaye yana kallonta "Ill call your mom, Take care"

Tunda Azrah ta fito daga ciki gani tayi kamar a mafarki ne dan she never expect this, bata taɓa kawo hakan ba balle harta shiga ciki, ta sake share hawayen ta for the countless times ta fito, tana fita ta kalli wani taxi ganin kuɗin da ya bata dayawa ne kawai ta tsare sa ta faɗa masa inda zai kaita sannan ta shiga, har suka isa unguwarsu bata san sun iso ba sbd yadda ta faɗa tunani.
Ko da kuwa bata samu kuɗin candy kai tsaye ba, amma yadda Honorable Ibrahim ya saurareta da mutunci da kuma yadda ya karɓi lambar Umma ya tabbatar mata da cewa akwai hope

Tana shiga cikin layin su Zahra ce ta fara ganinta daga bakin titi wacca ta fita mikawa wani yaro gawayin daya tsaya, da gudu ta nufe ta

"Yaya Azrah! Sannu da zuwa! Ya akayi? Ina kika je? Naga is like your happy" duk ta jero mata waɗannan tambayoyin lokaci guda

Azrah ta janye mayafinta ya ɗan koma kafaɗarta, tana sauke ajiyar zuciya ta ce

"Bari mu shiga cikin gida mana na huta kadan, sai na faɗa miki" Azrah na gaba Zahra na Binta a baya suka shiga

Zuciyar Umma cike da tuhuma da mamaki tana kallon Azrah daga jikin kofa data fito daga ban ɗaki, zuciyarta na bugawa ta wuce ɗaki alamar bata so suyi maganar a tsakar gidan hakan yasa su Azrah binta a baya tana shiga ta juyo tana kallon Azrah ta ce

"Ina kika je Azrah?" Azrah ta zauna tana sauke numfashi tana kallon Umma cike da nutsuwa ta gaishe da Umma ta amsa

"Azrah daga ina kike haka?" Umma ta kuma jefa mata tambayar, Azrah ta ce

"Umma daga Government house nake" ta karasa maganar tana ciro bunch of money da yana bata, a take Zahra da Umma suka haɗa bakin cewa

"Daga Government house kuma?" Abin yaso bata dariya ta ce "Eh daga can nake"

Azrah ta zauna, ta ajiye jakkanta sannan ta fara bayani, Cikakken bayani, tun daga shigarta Government House, drama da securities, zuwa taronta da Honorable Ibrahim, Sai da ta kai karshe sannan ta ce

"Shine ya tambaye ni tarihin rayuwata, ya karɓi lambar ki... ya ce zai kira, idan Allah Ya yarda, zai taimaka"

Umma ta zuba mata ido, tana mamakin yadda ‘yar cikin cikinta ke da wannan ƙarfin hali da hikima, Kafin tace komai Zahra ta ce

"Yaya Azrah... Gaskiya I salute ur courage, yanzu kenan zakiyi waec da necon cikin kwanciyar hankali, Allah saka masa"

Azrah ta ce "Ba mu tabbata ba har yanzu... amma ko bai bani ba ace ma bai kira ba ai kuɗin daya bani na mota dashi zan yi amfani dan wallahi nasan nan ya kusa 80k"

Umma ta zuba mata idanu, ba don tayi shakkar Honorable ɗin ba, sai dai fargabar yadda duniya take a lalalce ta ce

"Allah Ya kawo mafita, idan har da manufa ɗaya yake son taimaka miki Allah basa iko, Amma ina fatan babu wani abu da kikayi wanda zai kawo mana matsala...?

Azrah ta girgiza kai "Wallahi babu Umma"

Umma ta sauke ajiyar zuciya "To Allah Ya saka masa, ke kuma Allah miki Albarka"

A bangaren Honorable Faruq...

Bayan tafiyar Azrah da yamma Honorable ya kira lambar da aka bashi, Umma ce ta ɗauki wayan ta kai kunne

"Assalamu Alaikum, ni Honorable Ibrahim ne daga Government House. Ina magana ne akan ‘yar ku Azrah"

Umma ta ce cikin girmamawa "Wa'alaikumus Salam, eh ranka shi dade, Allah ya saka da Alkhairi, ta dawo gida ai tun ɗazu"

"Na kira ne in tabbatar muku da cewa za mu taimaka mata da kuɗin candy. Ba za mu bari irin azamar da take da ita ta tafi a banza ba, sannan zanyi kokarin ganin sunanta ya shiga cikin wanda zasu samu scholarship da yarda Ubangiji"

Umma ta ji kamar ta saki ihu dan murna, idonta ya fara tara kwalla, tana fara masa godiya ya katse ta da wuri

Ya ce "Ku ci gaba da tarbiyyarta yadda kuke yi, sannan ku barta akan dream ɗinta, Karku hanata tunda har ta iya neman na kanta kuma ta iya ɗaukan karatun ta"

Bayan sun gama magana yace su turo da acc details wanda ba ɓata lokaci suka tura amma sai da suka sha mamaki ganin ya turo 500k instead 50k da suke nema.

Da daddare... acikin ɗaki Zahra da Azrah suna zaune a saman katifar su, Azrah ta jingina da bango Zahra na kallonta kamar zata yi tambaya can ta kasa daurewa ta ce

"Yaya... kina tunanin yanzu rayuwarmu zata fara sauyawa ne?'

Azrah ta ce da sanyin muryarta

"Zahra wallahi ni ma haka nake tunani kuma nake fata, Amma ba zan sa rai sosai"

Zahra ta langwabar da kanta, tana murmushin da ke nuna kwanciyar hankali


Washegari da safe...

Duk suna zaune bayan sun gama breakfast suna lissafin yadda zasu yi, Azrah kuma tana so su gama ta shirya zuwa makaranta kawai wayan Umma yayi ringing, Zahra ta daga da sauri tana mikawa Umma ta ce "Umma honorable ne"

Umma ta ɗauka ta gashe sa ya amsa cike da girmamawa yace

"Mun tura details ɗinta zuwa Government Education Board. Zata iya zuwa ta cike form ɗinta da gaggawa idan waec ko neco ya fito zata kai musu anan ne scholarship dinta zasu bata, amma zata jana Jamb da farko"

Umma ta fashe da kukan, su Azrah suna jira ta gama ta basu bayani saboda su basu jin komai amma yanayin umma kuma sun san wani abunne

Wani mako bayan nan...

Azrah ta kammala rijistar candy da taimakon honorable Kamar mafarki, amma gaskiya ce Haka rayuwarta ta fara ɗan buɗewa as not expected.


#Jiddatulkhayr
08110615256
https://whatsapp.com/channel/0029Vaq17Di3WHTWv5ju0w3Z

*BEYOND THE VEIL*(LABULEN SIRRIN)


YOTA ID/026


Wattpad © Jiddatulkhayr
Instagram © Jiddatulkhayr writes


Free page

Episode 11: A visit that stirred Hearts


Tun bayan kiran da Honorable Ibrahim ya yi wa Umma da cike da mutunci, zuciyarsa ta kasa samun nutsuwa, ya zauna a ofishinsa yana tunanin Azrah yadda take magana da nutsuwa, kyakkyawan tarbiyyarta, tausayin da ke cikin idonta duk da irin mawuyacin halin da take ciki. Ba kawai ya ji tausayinta ba ya fara jin wani abu fiye da haka.

Yana komawa gida daren nan, maimakon ya wuce kai tsaye ya shiga gida as usual, ya zauna a cikin motarsa yana kallon hoton daya ɗauka da camera ɗin CCTV lokacin da take zaune a office ɗin

"Wannan yarinya... me ke damunta har haka? Kuma me yasa na kasa mantawa da ita tun jiya?" Yayi maganarsa shi kaɗai kamar yana jiran jin amsan daga garesa kuma.

Zuciyarsa na masa tambayoyi da yawa, A daren ranar bai samu bacci ba cos duk lokacin da ya rufe ido, sai hoton Azrah ya bayyana a zuciyarsa. Yanzu kam ya sani ba iya tausayi ba, zuciyarsa ta fara jan shi zuwa wani sabon yanayi, Ya fara tunanin "Me zai hana in taimaka mata gaba ɗaya? Ko... ko kuwa aure... ?".

Washegari....

Azrah na zaune a kitchen tana girkin abincin rana da misalin karfe 10 na safe, tana so ta kammala ta taje gidansu Fatima dan karɓan wasu takaddun da zasu fara na jarabawar candy wanda yanzu tana hundred percent assurance zata zana both waec da neco saboda ko bata ci candy ba tana da kuɗin da zata biyawa kanta balle ma bata fatan hakan, muryan Maman asabe da Mama taji a compound ɗin suna magana Mama ta ce

"Ke Ni yanzu abin nasu ma ya fara tsorata ni, Ni fah kullum idan aka ga yarana sai ace yaran wancan matar ne masu tarbiyya amma banda nawa dan suna zuwa tallah, amma wallahi Naman Asabe ina faɗa miki lafiyayyan abinci suke ci kuma ba Malam bane ya tsaya musu" Naman asabe ta riƙe haɓa ta ce

"Iko sai Allah, toh daga ina kenan suke samun kuɗin da suke siyan kayan abinci ni Uwani?" Mama na kwashe abincin sana'arta ta ce

"Yanzu ke har sai nace muku gashi? Yarinyar da ake ganin tafi kowa kyau a unguwar mana ita yasan inda take zuwa suke bata kuɗi" Maman asabe ta riƙe haɓa ta ce

"Kice yanzu dai ker take kallon mu?" Mama ta ce

"Tun yaushe kuma, ranan fah haka wani ya kawo mata kaya cikin Ghana, gashi bata wanka sai da sabulun turawan nan, ke baki ganin yadda jikinta yake wani sheki Ni" Maman asabe ta ce

"Bariki, wato shi yasa take jin tafi karfin yaranmu siyasa ko magana bata musu" Mama tayi wani humming,

Zahra ta fito a zuciye ta karasa inda Azrah take zaune ta ce

"Anty Zahra tashi ki shiga ciki zan karasa" Azrah ta Kalleta ta ce

"Ki bari zan karasa kawai, though nagama ai" ta sauke stew ɗin kan wutan tana mikawa Zahra kulan abincin, ta karbi kulan ko kallon su Mama batayi ba balle su sa ran gaishe su, tana hanyar ɗakin Umma ta ce

"Kai jahilci ma bai yi ba, Yaya kiyi sauri kizo ki tafi kinsan baki da lokacin ɓatawa" daga Mama har Maman asabe suka ɗaga kai suna kallon Zahra da har ta shige ɗakin Umma, Mama ta miƙe ta wulwulo wani ashar ta jefa mata ba, ta fara banbamin masifa da ashar

Azrah ta wuce su ko kallon inda suke bata yi ba, dan ita tana mamakin hali irin na Zahra, harta shiga ɗakin Umma bata Kalle su ba, Umma ta ce

"Zahra nace ki fita ki basu hakuri, basu haife ki bane da zaki jefa musu magana?" Zahra ta ɓata fuska ta ce

"Umma kinji na zage su dan Allah? Ko kinji na kira sunan wani? Kawai fa ina magana da Yaya ne nace ta shigo ciki saboda jahilci beyi ba"

Azrah ta zauna ta ce "it's okay Umma, yanzu idan ta fita maganar kuma zai dawo sabo saboda kinsan ba zasu kyaleta ba"

Zahra ta miƙe ta wuce ciki, ba tare data kalli Umma ba dan wallahi Umma ne ke taka mata burki

Kamar yadda kwana biyu honorable ya kasa manta Azrah haka yau ma har ya isa ofis, amma ba zai iya aiki yadda ya saba ba, yana jinsa very weak, kawai ya ɗauki waya ya kira wani amininsa a Education Board, yana ɗaga wa bayan sun gaisa ya ce

"Please idan yarinyar nan ta sake zuwa akan cika scholarship ɗin da nace a bata pls a sanar dani, Kuma ku tabbatar bata shiga wata matsala ko cin mutunci a kowanne mataki, sannan bana bukatar wani daga cikin staff ya nema mata magana idan ba abinda ya shafi cika maganar scholarship ɗin bane"

Mutumin ya yi mamaki, sai dai baice komai ba a haka suka yi sallama.

Kwana biyu bayan haka...

Rayuwa na tafiya musu yadda suke so, Alhamdulillah yanzu ba zasu ce ga wani abu da suke bukata ba, sun bunƙasa sana'ar su ba tare da sun dogara da Bappah ba.

Azrah  tana can jikin katifa tana gyara jaridun da suka tsufa na Bappah tare da wasu old books ɗinsa da sometimes take karantawa, Zahra ta shigo tana kallon Azrah ta ce

"Aunt Azrah! Umma na kiran ki"
Tayi saurin mike wa, zuciyarta na tafi ya fara bugu da karfi dan haka kawai taji wannan kiran bata yarda da shi ba

A cikin ɗakin Umma, ta tarar da Umma tana riƙe da wayarta a kunne, Azrah yanayin data ga Umma na waya ta fahimci da Honorable take waya, ta sake baki tana kallon Umma da zuciyata take jin yana kara sannanta bugawa, Umma ta miƙa mata hannu alamar ta zauna sai kuma tayi sallama da honorable, Umma na kallon Azrah ta ce

"Azrah mutumin nan ne Honorable, ya ce zai zo gidan nan gobe"

Azrah ta buɗe baki amma ta kasa cewa komai sai kallon Umma da take ba ko kiftawa, Umma ta cigaba

"Ya ce yana so ya zo ya gana da mahaifinki"

Kamar saukan a rasu haka Azrah taji a kunnuwanta, jikinta yayi sanyi, Me zai ce? Me zai nema? Ta rasa abin cewa sai kallon Umma kawai take yi.

Da yamma bayan Bappah ya dawo daga Majalisar sa, Umma ganin Mama bata nan yasa kawai ta miƙe ta nufa hanyar ɗakinsa da sallama ta shiga ya ɗaga kai yana kallon ta ya ce

"Allah sa lafiya dai, dan bana son tashin hankali Bitti" Umma ta dinga kallon sa sai kuma ta daure ta zauna tunda ba abinda ya kawota ba kenan ta ce

"Malam dama honorable Ibrahim ne yace zai zo gidan nan gobe, toh yace yana son magana da kai ne" Bappah ya dinga kallon ta kamar bai fahimci me take nufi ba ya ce

"Ban gane ba? Me kuma haɗi na dashi? Sannan ina kika sansa?" Umma ta ce

"Shine wanda ya biyawa ƴarka kuɗin candy, yanzu kuma yana bukatar haɗuwa da mahaifinta ya ce, shiyasa na maka magana" sai sannan Bappah ya sake fuskansa ya washe baki ya ce

'Toh..toh.. ai sai kiyi bayani tun farko, shikenan Allah kawo sa goben, Allah yasa kuma Alkhairi ne zai kawo sa" Umma ta taɓe baki ta miƙe ta fita daga ɗakin Bappah

Bayan ta koma ɗakinta a'a usual kamar yadda ko wani garin Allah ya waye rana ɗaɗɗaya ne bata ɓuya tayi kuka haka yanzu ma tana shiga ɗaki ta wuce ta zauna a bakin katifar ta ta zauna ta rufe fuskanta da ɗankwalin ta tana share hawayen daya fara gangaro mata, tana jin zuciyarta na kuna bata san yaushe zata daina wannan kukan nata ba, bata san yaushe zata jita at ease ba, sometimes takan yi dana sani amma it's already late balle ta gƴara, jin motsin Zahra yasa ta goge fuskarta ta kwanta kamar mai bacci....

Da daddare bayan Isha'i Zahra ta dawo daga aika, idonta akan roban sauran awara da ya rage a cikin roban da ake fita da shi talla, bin compound ɗin tayi da kallo ganin babu kowa yasa ta tafi da ɗan sauri amma tana yi dan karta making any sounds, buɗe robar tayi ta juye sauran awara da akalla zaiyi na 2k a kasar hannunta dan kamar zai zuɓe ma saboda laidar ya masa kaɗa, jin motsi daga bayi yasa tayi sauri ta shige ɗakinsu tana ɗan leka ta jikin labulen taga Siyama ce ta fito, karasa cikin ɗakin tayi tana dariyar mugunta ta zauna tana miƙawa Umma katin data tsiyo mata

Azrah dake kallon ta da mamaki ta ce

"Aina kika samu wannan uban awaran Zahra?" Zahra ta jawo plate da Azrah ta gama cin abinci ta juye a ciki tana cewa

"Gidan su kawata na biya na karba, kinsan dama jita muka haɗa kuɗi shine yau ta mana" Zariya ɗiba ta koma gefe ta fara ci, Umma ta ɗauki guda biyu ta kai baki, Zahra ta ce

"Umma kara mana" Umma ta girgiza kai ta ce

"A'a Zahra wannan ma ya min" wani ashar suka biyo daga can compound, Zahra ta fara jin awaran da sauri kamar wacca take da ciwon yunwa, jin kalmar da Siyama ta faɗa ga kuma Mama ta fito itama tana masifa yasa Umma da Azrah kallon Zahra data ki haɗa ido da su, Siyama ta ce

"Wallahi Mama na shigo da awarar nan, kawai daga shiga bayi shine fa aka ɗauke"

Umma na kallon Zahra ta ce

"Zahra mayasa zaki yi haka? Baki san sata bane hakan?" Zahra ta taɓe baki ta ce

"A cikin kuɗin Yaya da suka ɗauka ne na cira" Umma ta ce

"A'a bana son haka Zahra, wannan ba hali mai kyau bane, wanda ya maka mara kyau ka saka masa da Alkhairi haka rayuwa take sai Kiga rayuwar ka yana kyau" Zahra ta taɓe baki ta juya taki kallon su Umma, Azrah ta ce

"Umma ɓata bakin ki kike da Zahra, amma Zahra bata jin magana wallahi" Umma ta ce

"ɗauki awarar ki mayar musu, sannan sai ki biya su kuɗin wanda kika ci" Zahra ta miƙe a zuciye ta fita compound ɗin ko kallon su Siyasa da suke zabe zage da tsinuwa bata yi ba, direct waje ta nufa tayi ɗan gaba da gidan su ta tara almajirai tana musu sadaqa.

Washegari...

Tunda suka tashi suka gyara gidan, Umma take gidan Maman Aziza ta karɓi aron dadduma mai kyau wanda idan at least honorable yazo zai iya zama akai, suka gƴara gidan suka share tas.

Kusan ƙarfe huɗu na yamma, wata mota ce ɗalleliya ta shigo cikin unguwar ta su,  Kowa sai kuskus ɗin magana ake yi, wata babbar mota ce me tinted glass ta tsaya a gaban gidan su Azrah wanda har yaran unguwar sun fara taruwa suna kallon motar

Zahra ce ta fara leƙa kofar gidan dan ganin menene bayan ta samu labari daga yaran unguwar da suka shiga suka shafa musu, tana leƙa wa ganin motar ta koma ciki da sauri ta ce

"Aunt Azrah Motar Honorable ce wallahi!"

Azrah ta kalli kanta a madubi Zuciyarta na cike da ruɗani, ta shafa ƙirjinta a hankali, tana jin kamar numfashinta yana tsayawa ta ce

"Ya aka yi kika san shine?" Zahra ta ce

"A kofar gidan nan fah naga ya tsaya, kuma waye yace zai zo idan  bashi ba, hala ma sonki ya ke wallahi" Azrah ta wurga mata wani kallo daya sa ta zanye bakinta tayi shiru

Can sai ga wayan Umma ya fara ringing, bayan sunyi magana ta wuce ɗakin Bappah ta sanar da shi akan ya iso

Bappah ya fito cikin shadda mai kyau, ya karasa har kofar gidan ya shigo da shi, suka zauna anan compound akan dadduman da aka shimfiɗa, ko kaɗan bai nuna ma kyama ko wani abu ba

"Barka da yamma Honourable" Bappah ya ce cikin ladabi

"Lafiya lau Baba, Na gode da damar da ka bani"

Honorable ya sake gaishe da Sallah cike da girmamawa, ya kawo maganar yadda za'a duba lamarin su Azrah game da scholarship akan dan Allah Bappah ya barta idan ta samu, ya ce

"Na sha mamakin yarinyar nan, Tana da ilimi, nutsuwa, da burin rayuwa"

Bappah ya ɗago kai ya kalle shi.ya ce "Haka ne sun gado hakan ne daga mahaifiyar su" sai kuma Bappah yayi shiru jin wani bakon yanayi da lokaci guda ya ziyarci jikinsa


Honourable yayi shiru kamar mai nazari sai kuma ya dake ya ce

"Dama na zo neman Alfarma ne ina kuma fatan zaku taimaka min" Bappah ya dinga kallonsa toh me suke da shi da har zasu iya ba sa, can Bappah ya ce

"Allah yasa muna dashi ma tukun" Honorable ya numfasa ya ce

"Idan har ba'a ma Azrah miji ma ina neman Alfarman a bani aurenta dan Allah" Bappah yaji tambayar a ba zata dan this is the least da zai kawo ran sa, ganin shirun Bappah yasa ya ce

"Nayi maka alkawarin ba zan hanata karatu ba, sannan zan gina mata future mai kyau da yardan Allah, dan Allah ka taimaka min"

Bappah ya sake yin shiru, sai daga bisani ya ce

"Zan tambayi iyalina, Amma ba zan hana ƴata cika burinta ba... in har hakan ba zai rusa rayuwarta ba"

Honorable ya ce

"Nagode kwarai, Allah ya saka maka ya tabbatar mana da Alkhairin sa" daga haka Bappah ya raka honorable har waje wanda ƴaran unguwar sun taru jikin motar suna kallo

Bayan tafiyan honorable Bappah ya shiga ɗakin Umma direct inda ya tarar da su zaune duk suma sun kosa suji make faruwa

Bappah yayi gyaran murya ya ce

"Toh abinda ya kawo sa wai yana so a basa auren Azrah ne idan ba'a mata miji ba"

Daga Umma har Azrah da wani expression suke kallon Bappah wanda ba zaka iya tantance what exactly fuskar su ke nunawa ba, Azrah ta fara girgiza kai, Umma ta ce

"Amma Malam ai Azrah tayi karama, ko gama secondary school bata yi bafa"

Bappah ya ce "Toh ai ba yanzu bane Bitti, dole zamu ce amsa sai ta gama secondary school, kuma yace ba zai hana ta karatu ba, zai barta ta cika burinta"

Zahra ta ce "Ahtoh, dama nasan mutum irin honorable ba zai hanata karatu ba" Umma ta ɗauki pillon gefenta ta wurga mata ta ce "ta shi ki bani waje mara kunya" Zahra na dariya ta miƙe ta koma ɗaki

Azrah da har idonta ya cika da hawaye, umma ta riko hannunta cike da lallashi, Bappah yana kallon Azrah ya ce

"Na san wannan ba burinki bane Azrah, Amma idan har zai bar ki ki cigaba da karatu, ya dace mu karɓa, amma think first"

Zahra ta sake lekowa
"Ina ganin ki yarda wlh Yaya, Kema ai kin san irin wahalar da muke ciki, Kuma ya ce ba zai hana ki komai ba"

Azrah bata iya cewa komai ba sai hawaye, can ta ce

"Na yarda... amma fa... ban san me rayuwa zata bani gaba ba, I'm just scared" tunanin ciwon Umma data yi kawai yasa taji ta amince masa.

Daren ranar...

Azrah na kwance, idonta biyu tana kallon sama, tana jin zuciyarta ya mata nawi, tayi addu'a da fatan hakan ba zai zama kuskure ba a rayuwar ta, dukda tana jin tsoro, but duk sanda ta tuna Umma kuma sai tayi calming kanta down"

A bangaren honorable kuwa..

Honorable yana kwance a kan gadonsa, Hoton Azrah da ya ɗauka a government house yana kwance a fuskar wayar, kuma tun ɗazu yake kallo, Yayi murmushi

"She's different Ya Allah" ya faɗa a hankali.


This book costs 500. Make the payment to Hauwa Jibrin, Wema Bank account 0421255553, and send proof of payment to 08110615256.
*BEYOND THE VEIL* (LABULEN SIRRI)


YOTA ID/026


Wattpad © Jiddatulkhayr
Instagram © Jiddatulkhayr writes


Free page

Episode 12: Whispers and Watchful Eyes

Tun bayan tafiyan honorable har bayan kwana biyu bata sake jin motsin sa ba, dama koda yake kira da wayan Umma ne, har taji hankalin ta ya kwanta dan ta mayar da hankalinta sosai akan karatunta da kuma jarabawar da suke yi...

Tana fitowa a exams hall ɗin, ta zauna a jikin wani wall tana maida numfashi saboda zafin da hall din yake da shi, fifita kanta take yi, kamar ance ta ɗaga kanta kawai idonta ya faɗa cikin na Sagir, tana processing ɗin inda ta taɓa kallon face ɗinsa amma ganin ta kasa tunawa kuma har sannan ita shi ma ita yake kallo yasa ta ɗauke kanta zuwa wani direction amma me? Idon ta ya sauka cikin na Sadeeq, nan take taji wani bugawar zuciya, ɗan yamutsa fuska tayi ta ɗauke kallonta daga gare sa, sai yanzu ta tuna inda ta taɓa kallon sa, wani tsaki ta ja ta miƙe daga zauna da take, sake haɗa ido tayi da Sagir wanda yana mata murmushi amma koda wasa bata mayar masa ba, gaba ta kara sai kuma ta jiyo murya Fatima

"Azrah!" Cak ta tsaya ba tare data juyo dan bata bukatar sake haɗa ido da su, Fatima ta karaso ta na cewa

"Okay.. da ban fito ba da tafiya zakiyi ki barni?" Azrah tayi murmushi ta ce

"Ke, I'm moody ne, kuma naji na bar wajan" daga haka suka kama hanyar gida..

Azrah tana isa kofar gidan su ta fara jin hayaniyar Zahra da Habiba, da sauri ta karasa shiga gidan tana kallon Zahra data sha ɗanmara tana zazzaga ma Habiba magana kamar yadda itama Habiban tayi da alama dambe suke shirin yi yasa taje da sauri ta riko Zahra tana cewa

"Zahra kina da hankali? Ki wuce mu shiga ciki" Zahra ta kwace kanta ta ce

"Kinsan me tamin ne Yaya? Daga ajiye kuɗin gawayin da wani ya tsiya a waje na fah ta ɗauke, ina kan zuba masa kayan miya a laidar fa, kuma ina ganin kuɗin a hannunta shine wai ba zata bayar ba, Mamanta kuma wai taci Uwa ta, ce mata aka yi Habiban ta isa min wani abun ne?" Azrah ta ce

"It's Okay, ki barta kawai tunda tace bata ɗauka ba, kina amfani da ilimi not all the times zaki tsaya faɗa" Habibah ta wawulo wani ashar ta jefa ma Azrah ta fara zazzaga mata magana, Zahra ta kwashe da dariya ta ce

"Wallahi sai kin biya wannan kuɗin ko kuma bashi kika ci" daga haka tabi bayan Azrah da sauri, bayan ta shiga ta samu already Azrah harta zauna tayi wani iri ta Zahra tw ce

"Yaya mene ne kuma?" Azrah ta ce

"Wallahi ban faɗi maganar dan nayi hurting dinta ba, sai dana faɗa kuma ya dame Ni" Zahra ta ja tsaki.

Washe gari.... Tunda Ayrah ta tashi yau haka kawai take jinta so tense, idan ta tuna wai Honorable zai zo gidan kuma wajenta zaizo sai taji kamar tayi kuka, tana tunanin wai da kansa zai zo?, ba wai magana a waya ba, ba kuma ‘yan aike ba, at this point bata san ko haduwar ta dashi Alkhairi ne ko akasin hakan ba, Tunanin nan ya ishi Azrah tun tashin ta daga bacci..

Zaune take a bakin katifarsu ta jingina da bangon ɗakin, tana starring one place, Zahra na gefenta, tana kokarin goge mata hijabin da zata saka, domin Umma ta ce kada ta fita da gyalle tayi using hijab sbd idan mutum kamar Honorable zai zo cikin gidan at least tayi shigan mutunci

"Kina jin tsoro ne ko kunya?" Zahra ta tambaya tana kallon fuskarta

Azrah bata amsa ba, Kamar zata fashe da kuka, amma ta ɗan daure, ta kalli gugan da Zahra ke mata ta ce
"Zahra... bana son wannan attention ɗin"

"To me kike so?" Zahra ta ce da dariyar mugunta
"Karatu ne kike so ko? Toh Mango park uwar karatu sai kin shanye komai a bokon kenan? To ai Kuma ya ce ba zai hana ki karatu ba ai ma yafi Sadeeq ko Saif ne ma?"

Zancen Saif ya tsinka zuciyarta, tana mata wani banzan kallon ta ce

"Waye kuma Sadeeq?" Zahra ta buɗe hannayenta alamun bata sani ba sai ta fara dariya ta ce

"Toh Nima na san sa ne? Kawai naji sunan ne yafito min daga baki" Azrah taja tsaki ta ɗauki littafinta tana forcing kanta da karatu

Can yamma sai ga wasu yara biyu sun shigo gidan da gudu suka yi wajan dakin Umma suna wai wani a waje yace a kira masa Azrah, Zahra tayi saurin cewa

"Okay, je kuce gata nan fitowa" Sai kuma ta mayar da kallon ta kan Azrah tana Murmushin Mugunta, ko da wasa Azrah taki kallon direction dinta kuma bata tashi ba, dan ita tasan yadda zuciyarta yake bugawa da karfi

Ganin bata da niyyar tashi yasa Umma ta ce "Azrah ke baki ji ance ana miki magana bane a waje? Kuma ai kinsan dole honorable ne amma kikayi kamar baki ji ba, ko dan kina ganin yanzu Shikenan zaki iya masa abinda ranki ke so saboda yana son ki" jiki ba ƙwari ta tashi ta wuce ciki bata jima ba sai gata ta fito sanye da Hijabn da Azrah ta goge mata

Tunda ta fita kofar gidan bata gansa ba sai motarsa dake parke hakan ya tabbatar mata yana cikin motar ne amma sai kawai ta tsaya tana kallon wani waje

A wajan honorable kuwa tun fitowanta yake kallonta bai san sanda murmushi tayi escape daga fuskarsa ba, bayan ya kare mata kallo sanin ba zata karasa ba yasa ya buɗe motar ya sauka ya taka har inda take tsaye yayi ƙasa da muryansa ya ce

"Muje cikin motar ranki shi daɗe, cos nan duk wanda yazo wucewa sai ya Kalle mu" ta gagara ce masa A'a haka tabi sa har motar, ta shiga da sallama

"Assalamu alaikum" ta furta muryanta ya soma rawa

"Wa'alaikum salam" Honorable ya amsa da murmushi mai ɗaukan hankali

Yana kallon yadda ta takuren waje guda kana ganinta kasan she's not comfortable da spot ɗin, a hankali ya ce

"Hope kunyi magana da Bappah and kinsan me ya kawo ni wajan ki right?" Kai kawai ta gƴaɗa masa, tana Allah² ya gama maganarsa ta fita dan ji take numfashinta kamar yana seizing ya ce

"Well! Duk da nasan ke ya kamata na farawa magana amma magana da Balpahn ku shine ya fi, and I want you to relax please Karki sa komai a ranki nayi miki alkawarin ba zaki taɓa dana sani ba Azrah" ya kare magana yana kallon ta amma ko making any move da zai nuna zata iya basa amsa bata yi ba, ya kuma cewa

"Karatu Shine burinki?" Ta ɗan Kalle sa sai kuma ta ce a hankali

"Yes, sir" ya ce

"Zan taimaka miki ki cika wannan burin naki, amma bana so ki ji tsoro, wannan ba abu ne da zai hana miki karatu ba, Rather, I want to support you even if you want to become a professor ne Azrah"

Ta ɗan Kalle sa, sai kuma ta fara jin nutsuwa ta ce

"Amma aiki fah? Zaka barni nayi? Cos ina son taimakawa Umma na da kanwata" ya ce

"Bazan hana ki ba, In Shaa Allah" ta gƴaɗa masa kai ya ce

"Kince baki da waya ko?" Nan ma kai ta gƴaɗa masa ya ce

"Okay" wani ɗan karamin paper ya miƙa mata ya ce

"My private line, sai kiyi saving da shi zaki na kira na" ta karɓa daga haka ya sauka ya buɗe bayan motar ya Ciro wani laida sai kuma ya koma motar har sannan laidar na hannunsa

Siyama da Habibah da suka taso daga tallan su duk a gajiye suke kamar wanda aka musu duka lis, tafiyan ma dakyar suke yin ta, ko hirar da suka saba ma babu dan duk shiru suka yi suna tafiyar su, Sai kwatsam suka hangi wata mota mai haske da sheki 'black Lexus SUV', na tsaye a bakin ƙofar gidansu

Habibah ta tsaya cak tana karewa mota kallo, sannan ta runtse ido tana ƙoƙarin processing ɗin fuskar data hango duk da ta ganta amma bata son believing cewa ita ce
"Kai Habibah... kamar Azrah nake gani daga motar can fah!" Siyama ta faɗa a daƙile

"Wallahi nima dai kamar ita nake gani... ko da yake sai dai mu je ciki mu tambayi Mama ko kuma idan muka je kusa ai zamu gani wacece"

Da sauri suka nufo gida cike da ƙudurci, da kuma tabbatarwa idonsu cewa ba ita ɗin ba ce.

Honorable ya ɓata rai ganin yana miƙa mata laidan tana ce masa ta gode ya ce

"Ba zaki karɓa ba ko? Roƙa kika yi da zaki ce A'a ina kyauta na baki? So, babu kyau maida hannun kyauta baya" da kyar Azrah tasa hannu ta karɓa tana masa godiya

Lokacin da suka iso kofar gidan yayi daidai da sanda Azarh ta juyo tana kallon Honorable cike da kunya tana karban laidan tana masa godiya, suka kalli juna ai basu san sanda suka yi hanyar cikin gidan da gudu ba

Suna shiga gida, kai tsaye suka nufi dakin Mama da zuciyarsu ke ƙuna da tafarfasa cike da hassada

"Mama! Wallahi mun ga wata a mota a kofar gida, kuma kamar Azrah muka gani a ciki!"  Mama ta tafe kirjinta ta miƙe tsaye a secs sannan ta zaro idanu ta ce

"Azrah? Wace mota? Me kuka gani?" 

Siyama ta zayyano duk yadda suka gani, Habibah kuma na gyara mata inda ta kauce
Mama ta nufi kofar gida a hanzarce tana leƙa, amma tuni motar ta fice

Azrah tana ganin reactions ɗinsu taga sun shiga da gudu tasan definitely Gulma zasu kaiwa Mama shi yasa ta fara Allah² ya tafi bata son draman su Mama su fara nunawa a gaban bako, yana cewa

"Toh sai an jima, sai munyi waya ko?" Ai bata san sanda ta gƴaɗa kai ta sauka da sauri ba tana gyara laidar hannunta ta nufa cikin gidan da sauri

Ya bita da kallo harta shige cikin gidan sannan ya shafa fuskan sa ya tada motar ya bar unguwar nasu.

Mama ganin babu mota wajan wayam yasa ta koma ciki da sauri wanda a lokacin har siyama da Habibah suma sun fito ɗan su sake kallo ganin Mama na musu wani kallo yasa suka leka waje da sauri suka ga babu wata mota a wajan.

Azrah na shiga ɗakinsu Umma da Zahra suna zaune har lokacin suna jiran shigowanta duk kallon ta suke harta ajiye laidan hannunta a gaban Umma

"Wannan fa, daga ina?"  Umma tayi tambayar

Azrah ta sunkuyar da kai "Honorable ne ya ce in karɓa, har da wannan..." ta miƙa wani envelope,  sannan ta ɗaura
"Kuma wallahi Umma naki karɓa shine ya matsa min"

Zahra ta matso kusa tana buɗe laidar ta ce

"Toh a dalilin me ba zaki karba ba? Naga ai ba roka kika yi ba sannan kuma...." maganar ne ya maƙale a bakinta sakamakon ido huɗu da tayi da wani babban waya a cikin kwalinta ta saka wani ihuuu ta tashi tana tsalle sai kuma ta rungume Azrah tana

"Wallahi dalleliyar waya ya tsiyo miki Yaya duba ki gani, ai wallahi kin more, chap kuma shine zaki tsaya kina nuku nuku da irin wannan mutumin" Azrah ta turata daga jikinta tana hararan ta

Umma ta ce "Sannu Zahra, wato idan kene karɓa ma zakiyi har kike ce mata a dalilin me zai sa taki karɓa ko?" Tana dariya ta cigaba da buɗe laidar wasu haɗaɗɗun Abaya ta ciro tana zara ido

"Kalli Yaya! Egyptian Abaya ce wallahi" Azrah ta mike tayi hanyar ɗakin su, Zahra ta taɓe baki ta cigaba da buɗe laidan ganin ɗayan laidan, laidan chocolates ne yasa ta miƙe ta ce

"Nayi nan, dama anan nafi karfi" Umma ta ce

"A'a karki taɓa komai Zahra ki tsaya har Bappahn ku ya dawo ya gani tukun nan" Zahra taki kallon, Umma itama tayi ɗakin.

Zahra na shiga ciki ta ce

"Wayyo chocolate, lallai dan siyasan nan ya sha kwana, ya iya soyayya wallahi, yasa yadda zai sace zuciyar mutum" Azrah ta ɗauke kai kamar bata san tana wajan ba.
 
Siyama da Habibah dake tsaye a tsakar gida duk suna jin abin da ke faruwa and yadda Zahra ke magana da karfi da kuma ihun ta suka juya suka koma cikin ɗakin Mama suna faɗa mata

Mama data yi tagumi ta wurga musu wata ashar ɗin ta ce

"Yanzu sai ku ɗaga min hankali ai, ina zan samu nayi bacci yau kince min kunga Azrah a mota? Wato ma har saurayi tayi? Na shiga uku Ni Uwani" ta karasa maganar tana kuma sake wani tagumi

Siyama ta ce "kila wanda take yawo da sune fah Mama, amma Ni nasan ba zai so ta ba"

Mama ta ce "Ai ina fatan hakan kuwa, yadda ƴan unguwa zasu sako ta gaba, ace ma ciki tayi Shegiya sai naga idon Uwar tata ai"

Washegari  wata babbar motar kaya ce ta sauke kaya a kofar gidansu Azrah, Mai motar ya ce kayan abinci ne daga Honorable  buhunan su shinkafa, cartons ɗin spaghetti da macaroni, kaza frozen, indomie, sugar, da sauransu.

Gaba ɗaya layi ya cika da surutu.
Mama ta fito da sauri tana kallo zuciyarta na tafarfasa, ga kawarta Maman asabe ma data shigo tana taya ta aiki

Ta koma cikin gida ta kwalla wa Bappah kira, bayan Bappah ya dawo daga nuna musu ɗakin Umma suka fara shiga dashi dan shima ya rasa bakin magana, Mama na kallonsa ta ce

"Wannan wane irin abu ne? Me ke faruwa? Don Allah ka faɗa min gaskiya!" 

Bappah ya cije lebensa, ya ɗan ɗago ido yana kallon ta, a hankali ya furta

"Honorable ne dai ya ce yana son tallafa musu... kuma yana da wani niyyar Alkhairi ne" 

Mama ta goge zufa "bangane tallafa musu ba? Toh kai ba zaka ce musu ba'a bukata ba, tsayama Malam wani Alkhairin kake magana kuma akai?"

Yayi kasa da murya "Ina ji kamar dai Azrah yake so"

Mama tayi wani ashar da sai da Bappah yaja baya

"Wato ƴar kishiya ce za'a ce ana so? Kai ba zaka nuna musu Siyama ko Habibah ba? Amma sai kayi shiru?"

Magana da suke wa Bappah yasa yayi waje danjin me zasu ce, Mama ta wuce ɗakin ta hankali tashe, Maman Asabe na binta a baya danjin meke faruwa.


This book costs 500. Make the payment to Hauwa Jibrin, Wema Bank account 0421255553, and send proof of payment to 08110615256.
*BEYOND THE VEIL*( SIRRIN SIRRI)


YOTA ID/026


Wattpad © Jiddatulkhayr
Instagram © Jiddatulkhayr writes

Free page

Episode 13: The List They Tried to Erase


Yau tunda garin Allah ya waye duniyar tama Mama zafi ta rasa me ke mata daɗi, abincin da take a gida yau kam hakura tayi dan bata jin zata iya, tunda taga irin Alkhairin da honorable yake da kuma ɗawainiyar shikenan ta rasa sukuni yau kuma da Bappah ke waya da honorable a gabanta cewa magabatan sa zasu zo tambaya da saka rana shikenan ta sake ruɗewa kuma duk yadda ta dinga ma Bappah da ido amma ya kasa bin maganarta balle yayi stopping Honourable, ita kaɗai ke zaune a ɗaki tana ta faman sakawa da warware wa da tunani, hannunta rike da hijab amma har yanzu bata sa ba, wata makwabciyarsu ne ta leƙo siyan Alale ganin ko murhu ba'a kunna ba yasa ta shiga ɗakin Mama da sallama, Mama na kallon ta cike da abin duniya ya mata yawa ta miƙe ta fara magana a zafafe

"Maman ladi wallahi tallahi, idan har aka ce ba za'a fasa zuwa tambaya ba wallahi ko nawa sai na kashe, sai na kashe ko nawa ne nace, dan ba zan iya zama in kwashi bakin ciki ba ina ji ina gani ƴar kishiya ta shiga gidan Hutu" Maman ladi ta sake baki tana kallon ta sai kuma ta ce

"Haba Maman Abdul, dama rabon da Allah ya bawa wani akwai wani mahalukin da zai hana ne? Ni dai shawara ta ki hakura idan ba mijin ta bane ba za'a taba yin aure ba amma muddun mijin ta ne wallahi duk kinki sai an ɗaura" Mama ta katse ta

"Kimin shiru! Kada ki sake min maganar kaddara anan! Me yasa rabon zai fara da Azrah toh? Me yasa Azrah ce kaɗai bayan ina da nawa yaran" Maman ladi kam abin ma mamaki yanzu ya fara bata tana kallon tsantsan kiyayer Umma a idon Mama

Mama ta miƙe tsaye ta fara zaga ɗakin tana huci kafin ta tsaya, har sannan Maman ladi bata daina kallon Mama cike da mamaki ba, Mama ta ce

"Ki barmin kofar ɗaki dama na daɗe da sanin cewa bakin ku ɗaya da ita ai shiyasa zaki zo kina kare ta naga kema ƴaƴa matan gare ki amma ai har yanzu suna zuɓe a gaban ki! Idan ma Ni kaɗai ce toh sai nasan yadda za'a yi a fasa wannan zuwa gaisuwar wlhi, Malamai kuma nawa ne a cikin garin nan"

Maman ladi ta sake labulen ɗakin Mama ta ce "Ni Kinga tafiya ta, Allah ya yaye miki" daga haka ta nufa kofa sai kuma ta tsaya ta juyo tana kallon kofar ɗakin Umma sai akwai ta fita abinta.

Bayan wasu kwanaki

Bayan sun gama candy har saura kwana biyar su fara WAEC, Azrah ta faɗa duniyar karatu sosai dan koda yaushe tana riƙe da littafin ta, tana kuma kokarin kula da kasuwancinta kamar yadda ta saba, sosai honorable ya bata space ganin ta ɗauki karatun first priority ɗinta sannan zuwan ma ya daina sai dai har sannan basu bukatar komai dan yakan kawo musu everything enough. Wata rana yazo kamar kullum ta same sa a motar sa ta gaishe sa dan har sannan bata iya kallonsa balle ta iya magana mai tsayi a gabansa sai dai a waya, nan ma bawai takan yi sosai bane, tana ta sauraronsa wanda rabin Maganan ma shi kaɗan sa yake yi, ya ɗan ja hankalinta da tambaya

"Azrah, please give me Zahra's full name and age da kuma wani aji take yanzu, I want to do something for her" Azrah ta kallesa cike da mamaki sai dai bata ce komai ba

"Sir... Her name is Zahra Muhammad Sulaiman, She's sixteen, she's in Jss3" honorable ya gƴaɗa kai ya ce

"Perfect! I like her courage... remind me to send someone" Azrah bata fahimce shi ba amma saboda bata iya masa magana yasa tayi shiru kawai

Mama tayi sallama a gidan Maman asabe, Maman asabe ta fito daga ɗakinta tana gyara zanin jikinta ta ce

"A'a Maman Siyama kece a gidan namu, toh karaso mana" Mama ta karasa ta zauna tayi tagumi tana kallon Maman asabe ta ce

"Kinga ba zama ya kawo ni ba, yanzu so nake ki taimaka min ki bani shawara mai zan aikata wanda zai sa a fasa auren yarinyar nan" Maman asabe tayi shiru dan ita bata san me zata ce ba can ta ce

"A'a ga shawara nan, ina kince mutumin ɗan siyasa ne ko? Kawai a ɗauki fuskarta a ɗaura akan video ƴan iskan mata sai a kai masa Kinga ba zai so ace zai haɗa iri da ita ba ko dan kar a ɓata masa kujerar mulkinsa" Umma tayi wani shewa harda miƙewa tsaye ba tare data san tayi hakan ba tana kallon Maman Asabe ta ce

"Toh ai har kin fini tunani, yanzu wa zamu samu su mana wannan aikin ne? Nifa a shirye nake dana kashe ko nawa ne?" Maman Asabe ta ce

"Zan kira Garba naji ya za'a yi dan nasan ba zai rasa sanin masu yi ba" Mama ta fara dariya ta ce

"Kinga kuwa yadda ƴa unguwar nan suke kallonsu kamar gold zasu fara kyamar su suma".....

Umma da yaranta suna zaune suna hirar su cike da sha'awa da ban sha'awa, sai ga wayan Azrah ya fara ringing, Azrah ta ce

"Dan Allah Zahra ɗauka kice ina bacci"  Umma ta kalleta Zahra ta ɗauki wayan bayan sun gaisa ta isar masa da sakon da Azrah ta bata ya ce

"It's Okay, dama ke nake son gani Zahra, ki fito ina kofar gida" daga haka ya katse kiran Zahra na kallonsu ta ce

"Yace wai dama da Ni yake son magana" Umma ta ce

"Toh ki tafi" daga haka Zahra ta ɗauki hijab ɗinta ta fita

Tana isa jikin motarsa ya sauke glass ɗin yana kallonta, murmushi tayi ta ce

"Sannu da zuwa Sir" honorable Ibrahim ya ce

"Sannu Zahra, kin kammala homework ɗinki kenan?" Zahra tayi murmushi ta ce

"Na gama tun ɗazu Sir" Ya ce

"Ma Shaa Allah" wani envelope ya ɗauka a dashboard ɗinsa ya mika mata ya ce

"Take this, naki ne idan kin shiga ciki sai ki duba ko?" Ta karba tana masa godiya, daga haka ya tafi

Da sauri ta shiga dan tana son kallon menene a ciki, Umma da Azrah sai kallonta suke bayan ta Ciro da papers ɗin envelope ɗin Azrah ta karba da sauri dan ganin kamar admission letter ne, sake baki tayi tana kallon papers ɗin, One of the best school ya mayar da Zahra sannan ga receipt na biya mata school fees tun daga SS1 to 3, ga kuma sauran receipts na other stuff, sanin wane shi shiyasa ko maganar interview ba'a nema a mata ba aka gama mata komai, Azrah taji hawaye ta mikawa Umma takaddun ganin yan kashe wajan 1.5M, lokacin da Zahra tayi tozali da sunan makarantar bata san sanda ta miƙe tsaye tana ihu da salle salle...

Azrah na karbar notice daga wani student, dake itace headgirl sai ga wani student ya zo yana kallon ta ya ce

"Senior Azrah principal na kiran ki a office, wai kije" Azrah ta kafe sa da kallo kamar bata gane ba sai kuma ta ce

"Where is he kace?" Ya ce

"Yana office ɗinsa ne" kai ta gƴaɗa masa ta sallame ɗalibin gabanta, Kalle Kalle ta fara ko zata ga Fatima dan ita tun wancan maganar daya gwada mata taji ta tsane sa kuma bata son zuwa office ɗinsa ita kaɗai ganin bata ga Fatima ba kawai ta nufa jiki ba ƙwari

Da sallama ta shiga ta same tare da wani Malami ta ce

"Sir, gani" ko kallonta bai yi ba ya cigaba da magana da ɗayan Malamin har ya gama masa bayanan sannan ya fita, Azrah dake kallon wani waje taji muryan sa

"Azrah look I want to help you, But I can't fight government for a stubborn girl like you" Azrah cikin nutsuwa

"Thank you Sir, amma I'll be fine" Principal ya tsaya kallon ta da mamaki dan bai taɓa expecting haka daga gareta ba, ya ce

"Okay! Out of my office! Since you feel big!" Ta juya ta fita ba tare da taji ɗar ko wani tashin hankali ba dan hundred percent sure honorable ya gama saka sunanta and he has nothing to do sai ya karata da iskancinsa

Da kallo baki buɗe ya bita with lots astonishment, yafi some secs yana processing sai kuma yayi dariyar mugunta ya jawo wani long book da aka saka result ɗinsu na candy a ciki,  cire sunanta daga cikin jerin sunayen da gwamnati zata biya musu WAEC yayi, yana dariyan mugunta ya ce "Zanga me tsaya miki kuwa, zanga karshen rashin kunya ai"

Azrah na fita ta duba bata ga Fatima ba kawai tayi tafiyarta tana mamakin hali irin nasa, tsaki tayi tana sake godewa Allah daya haɗata da honorable sai yanzu ma take sake ganin honorable Ibrahim a matsayin wani wall a gareta...

Zahra na wanke wanke while Azrah na kitchen tana tuka abincin dare, ta gama kwashe abincin a kula ta kai ɗakin Umma sannan ta kwashe waste dishes takai ma Zahra daga haka ta wuce ɗakin Umma ta zauna,  Zahra dake wanke wanke kamar daga sama taji shigowan Abdul wanda da fito ma ya shigo gidan ɗan kallonsa tayi ta ɗauke kai ta cigaba da abinda take yi, ɗan tsayawa yayi ya Kalleta ya ce

"Ke dan Uwarki baki ganni bane da ba zaki gaishe Ni ba?" Tayi kamar bata jisa ba, ya gƴaɗa kansa ya ɗauki buta ya nufa hanyar banɗaki, ajiye kayansa yayi a wajan sannan ya shiga

Zahra ta kai sauran kayan data wanke ta fito tana kallon hanyar toilet inda ya ajiye kayan a kasa, taka wa tayi a hankali harta isa wajan kallon wayansa da tayi a ajiye tare da wasu stuff ɗinsa ne yasa bata san sanda murmushi ya ƙuɓuce mata ba ta ɗauka da gudu tayi ɗakin Umma ta shiga tana haki, Umma na kallonta ta ce

"Wani rashin gaskiyan kika aikata Zahra?" Azrah ta kalleta sai kuma ta cigaba da abinda take yi, Zahra ta zauna tana murmushi

Umma ta kalli wayan hannun Zarah ɗin ta ce

"Zahra wannan wayan waye kuma? Sannan Meyasa zaki shigo a guje?" Ta kare maganar tana tamke fuskan ta, Zahra ta ce

"Dama nayi rantsuwa ai Umma, wayan Abdul ne kuma nace sai ya biya kuɗin daya ɗauka, so yanzu ne right time, ya biya ba tare daya sani ba kamar yadda ya ɗauka ba tare daya tambaye mu ba" Umma ta ɓata rai ta ce

"Zahra bana son wannan halin naki, bana son kina ɗauke abun mutane da sunan kina rama abin da suka miki, how sure shi ya ɗauka" Zahra ta ɓata rai ta ce

"Bayan Yaya ta kama sa" Umma ta ce

"Ki mayar masa nace, obey before complain Zahra" Zahra ta turo baki tana kallon Azrah irin tasa bakin nan amma Azrah yi tayi kamar bata ma san meke faruwa a wajan ba, Zahra ta ce

"Ai naga shi ya fara sace kuɗin candy ɗin Yaya Azrah ranan, Da ba dan Allah ya turo Honorable ba, da ai har yanzu muna kuka"....

Abdul yana fitowa a banɗaki yazo kwashe kayansa sai baiga wayansa ba da sauri ya zazzaga kayan nan ma baiga komai ba, wani ashar ya yi, sake duba kayan yayi da bai gani ba ya fara ihu

"Mutum daga dawowansa sai sata! Wallahi idan ban ga waya ta ba yau za'a ga abinda zanyi a gidan nan ashe baku Sanni bama kenan" Umma tana kallon Zahra da suke jin ihun Abdul da zage zagensa ta ce

"Zahra bani wayan idan ba zaki maida masa ba" Zahra ta ja baya da sauri ta ce

"Umma nayi rantsuwa fah" wani kallo ta mata wanda yasa ta miƙe ba shiri.

Bayan kwana biyu..
An manna sunayen waɗanda gwamnati zata ɗauki nauyin WAEC dinsu, Principal ya ƙaraso da takarda a hannun sa zai manna a notice board saboda kowa ya gani, ya ɗaga hannunsa zai manna sai gani yayi...

"Azrah Muhammad... number one?" With shock written all over him yake kallo

Yayi shiru, ya tsaya, ya kasa motsi, while ga students duk shi suke jira ya manna ɗin su gani hankalin su ya kwanta amma principal ya kasa koda ce uffan ne, kamar me whispering ma kansa ya ce

"Amma.... I removed it myself"...


Bayan kwana biyu..
Zahra ta fara sabuwar rayuwa a private school da honorable ya maida ta, Azrah na cigaba da karatu da kasuwanci sannan har sannan bata barin ibada.

Wata rana ta shiga school saboda research Principal ya kirata bayan ta tafi office ɗinsa ya sassauta nuryansa ya ce

"Azrah..Kin cancanta everything and more, Sorry for before"

Ta kalle sa sai kuma ta rasa me zata ce masa ta ɗan kalle sa taga ita yake kallo sai kuma ta mike ta fita a office ɗin ba tare data ce masa kala ba, principal ya bita da kallo yana mamakin yaushe tazo tana masa kuka akan ya taimaka mata amma yanzu wai yaze a cire sunan ta akan mistake ne sai kawai aka masa warning cewa idan beyi hankali ba zai iya rasa aikinsa.

Da yamma Azrah na tsakar gida tana kulla gawayinta sai ga Siyama da Habibah sun shigo ko da wasa bata ɗaga kai ta lalle su ba, sai kawai taji dariyarsu Siyama ta ce

"Kin ji ‘yar masu baiwa ko?A yanzu ma ita ce first name a list ko?" Habibah ta ce

"Ƴar gayu mana, ai yanzu jin kanta take ita wata shegiyar ce"

Azrah ba ta ce musu komai ba, sai ga Zahra ta fito

"Eh mana, ai dole taji da kanta ko kunga tayi kama da kalarku ce? Ai duk wanda ya ganta yasan ba ƴar gidan wahala bane, balle ta tsaya biyewa jahilai" Azrah ta juya tana kallon Zahra

Siyama da Habibah suka yi kanta da gudu suna zaginta amma ina tuni ta wuce ɗakin su ta window ta sa bakinta tana zagin su

Siyama ta ce "idan ba tsoro ba ki fito mana" Zahra ta ce

"Idan ba girma ya faɗi ba ina ke ina faɗa da Kanwar bayan ki? Ai shine maraban jahili da mai ilimin kenan, yanzu kun taɓa ganin Anty Azrah na cacan baki da ku"

Saukan mari taji da sauri ta juya tana kallon Umma sai kuma ta fara kuka, Umma ta ce

"Zahra ki shiga hankalin ki, bana son Wannan neman maganar naki"

Har sannan su Siyama basu fasa zage zage da suke ba daga karshe Azrah ta koma ɗaki.

Da daddare Mama na zaune a ɗakinta ga yaranta kewaye da ita can ita kadai ta furta

"Auren nan dole sai an fasa dan ba zan yarda ina ganin ƴaƴan Bitti suji daɗin rayuwa ba"...

Few Free pages ya rage, better ku biya kafin labari ya fara ɗaukan zafi

This book costs 500. Make the payment to Hauwa Jibrin, Wema Bank account 0421255553, and send proof of payment to 08110615256.
*BEYOND THE VEIL*(LABULEN SIRRI)


YOTA ID/026

Wattpad © Jiddatulkhayr
Instagram © Jiddatulkhayr writes

Free page

Episode 14: The Price of a Daughter


"Ke Maman Asabe, yau ba sai kin zauna ba, mu tafi yanzun nan kafin ya fita tunda kince baya zama" cewar Mama tana takawa da sauri cikin riga da zani da mayafi daya rufe mata har kunnenta.

Maman Asabe tayi wani murmushin mugunta "Toh ai ni dama a shirye nake na ɗauka sai kin huta zamu" ta miƙe ta fara bin bayan Mama Wanda har tayi gaba ta ce

"Wannan mutumin da ake kira Garba dai ba wasa bane, ya taɓa jefa wata ‘yar unguwarmu na can zango cikin matsala har iyayenta suka koreta"

Dukkansu suka nufi bakin titi cikin shigarsu na gaggawa dan babu waccan take cikin nutsuwarta, Mama na ta furzar da iskan baki ta ce

"Ni wallahi ba zan bar yarinyar kishiyata ta fi nawa ba, Ai na haifi ‘ya’ya mata har biyu, ko ɗaya cikinsu ba ta taɓa ganin arziki ba sai wannan Azrah ɗin, In banda isa da ɗabi'a irin tata koda wasa bata yarda tayi wanka da Omo Bansan aina take samun waɗannan kuɗin ba gata sai uban saka kaya sai ka rasa aina take samun waɗan nan"

Maman Asabe ta ce

"Ki kwantar da hankalinki, Idan wannan mutumin Garba ya haɗa video ɗin nan da muke so, wallahi Honourable sai ya gudu da ƙafarsa ko sake waiwayo ta ba zai yi ba, wannan fa har tsoronsa nake kamar ba mutum bane sai kace machine ne".....

Bayan sunje sun faɗa masa yadda suke so ya zama, lokacin da suke hanyar komawa gida, Mama sai murna take dan yanzu hankalinta ya gama kwanciya ta ce

"Wallahi na san wannan abun zai yi tasiri, Yanzu sauran kawai mu nemo hoton ta ko wani short video nata kamar yadda ya faɗa"....

Da daddare a ɗakin Bappah, Umma na zaune tare da shi, duk sunyi shiru ba mai magana a cikin su, sai can Bappah ya daga kai yana kallon Umma ya ce

"Bitti, Honourable ya kira, jibi ne zasu zo a saka ranar auren wai,
ya ce komai ya shirya yanzu"

Umma ta dinga kallonsa kamar wanda ya dawo hayyacinsa dan ita bata yarda da changes ɗin nan nasa gareta ba sai sannan ta sauke ajiyar zuciya ta ce

"Allah ya nuna mana, sannan muma Allah ya bamu abinda zamu fita kunya da shi"

ya amsa da Amin, daga haka ta miƙe ta fice daga ɗakin nasa tana jin damuwarta yana dawowa sabo full bata san yaushe zata goge wannan zanen kaddarar ba? Ita yaushe ne zata samu nutsuwa ga ciwon daya sata a gaba tana tsoron ta mutu yanzu ba tare da ta sake waiwaye wannan......

Bappah ma ya miƙe ya nufa kofa yana haska compound ɗin yana dube dube sai ga Abdul ya shigo gidan yana fito kamar wanda bai san sallama ba

Bappah ya daka masa tsawa sannan yana masa wani banzan kallo ya ce

"Ni dai na gaji da halin ka Abdul, kullum baka taɓa abu kamar nagari, ina ka je bana ganin ka kwana biyu a gidan nan?"

Abdul ya ɗan taɓe baki, "Toh ai ba wani abu nake ba sannan ba wani wajan nake zuwa ba..." Bappah ya daka matsa tsawa

"Toh idan ba wani abu kake ba, sai kayi ta yawo? In baka daina ba wallahi zaka bar min gida na rantse dan bana son iskancin banza da shashanci"

Abdul ya wuce ɗakin Mama yana huci, Mama na zaune tana tsince wake ta ɗaga kai ta kalle shi

"Me ya faru kuma?" ta tambaye shi

"Wannan tsohon faɗa faɗa kamar shi kadai ya fi kowa ganin laifi? Ni dai gaskiya na gaji kija masa kunne, tahm" ya fadi yana zama akan wani ruɓeɓɓen kujera

Mama na kallon yaran nata ta ce

"Yauwa ga wani aiki ya samu, hoton Azrah nake so ko kuma video nata, duk wanda ya kawo min yana da dubu goma"

Siyama da Habibah suka haɗa baki wajan cewa "Ni zanyi" wani kallo Abdul ya musu wanda yasa Siyama ɗauke kai tana hararansa yana kallon Umma ya ce

"Umma ba wanda zai yi a cikin su, naga ba waya garesu ba taya zasu fara, kema kin san wannan aikin nawa ne kawai" Umma na Murmushi ta ce

"Toh ka samu ka kawo min zuwa gobe da safe" yan kallon Umma ya ce

"Zan kawo miki kamar yadda kika ce amma ina fatan kuɗi na ba zasu yi ciwon kai ba ko? Kinsan bana wasa da harkan kuɗi" Umma ta ce

"Kana kawo min zan dasa maka kuɗin ka" ya gƴaɗa kai daga haka ya miƙe zuwa ɗakinsa dan kwnaciya

Washe gari da safe, Zahra ta fito cikin sabuwar uniform ɗinta tsaf-tsaf! Farar rigar da Black skirt sun yi mata kyau fiye da zaton mai zato

Azrah dake wanke wanke a sakar gida ta ɗaga kai tana kallonta ta ce

"Zahra ina zaki haka da wuri?" Ta kare maganar cike da zaulaya

Zahra ta yi murmushi,ta ɗaga jaka "Sabuwar makaranta mana, Private school ma kike ji, Allah ya saka ma Honourable, Allah ya ƙara masa fiye da haka"

Azrah ta yi murmushi bata da buri fiye da ganin Zahra na Murmushi ita da Umma, amma Maganar honorable Ibrahim babu wanda ya san me ke cikin zuciyarta, Hope and pain suna fafatawa

Tana gama aikinta ta fara kulla gawayinta ba tare data kalli Mama da Maman Asabe da suke tsakar gidan suna haɗa kayan tallah, tana ji suna jefa mata magana amma sai tayi kamar bata ma fahimce su ba ma dan ta basu uzuri yau ta sake gaskata rashin ilini na haifar da komai but how iyn earth zaka na ma ƴar cikinka habaice

"Wasu suna jin cewa idan sun iya abinci da sana'a sannan sunyi candy, to sun gama rayuwar kunci fah, daɗi ne zai biyo baya, ai muma mun yi fiye da haka" inji Maman Asabe tana kallon Azrah kai tsaye

Azrah ta shige kitchen ba tare da ta ce komai ba, Ta ɗauki gawayi zata hura dan ɗaura wa Umma ruwan wanka

Abdul ne ya shigo kamar zai wuce, tuno deal dinsa da Mama yasa ya tsaya ya ciro wayarsa, ya ɗan juyar da camera

Azrah da bata san komai ba ta zauna tana kan ketta ashana ya ɗauketa ba tare data sani ba, su Mama ganin haka suka wuce ɗaki da sauri suna jiransa fuskokin su cike da murmushi

Yana shiga ɗaki ya ce da Mama
"Na gama nawa, miko min kuɗin"

Mama ta amshi wayar ta ciro dubu goma ta mika masa

"Gashi Allah ya saka"

Daga nan ita da Maman Asabe suka fita zuwa wata shago, suka kira Garba

"Garba! An samu, gashi nan a waya, amma ba ta nawa wayan bane zamu turo maka kafin yamma"

"Tura min kafin karfe biyu dai" Garba ya fada da murya mai sanyi amma mai cike da mugunta

Mama ta yanke kira tana kallon Maman Asabe ta ce

"Yanzu ya zamu yi gashi dai kuma kema wayar naki karama ce kuma yace kafin karfe biyu"

Maman Asabe ta ce

"Sai muyi amfani da wayar asabe na kawai"

Da daddare bayan Mama ta tura masa 50k yace zata kara masa ita bata san kuma ya zata yi ba amma damuwar ta ba anan yake ba tunda aiki za'a mata

Sake kiranta yayi ta ɗaga ya ce

"Na tura ma babban namu videon, yanzu zaki cika da sauran kuɗin ko?" Mama ta ce

"Naji wannan ba matsala bane, shi ogan naku me yace?" Ya ce

"Yace a basa 24 hours, zai gama aiwatar da komai"

Mama tamiƙe tana hamada ta ce

"Toh Ni yanzu damuwata gobe zasu kawo gaisuwar nan ne fah ina so tun kafin su zo ya kalli videon nan" Garba ya ce

"Kina da gaggawa ne matsala ta dake wannan harkan ba yanzu muka fara ba amma sai ki bi kiyi ta harzuka mu idan kuma ba'a yi daidai bafa" Mama zata yi magana ya katse kiran abin sa

Washe gari da yamma misalin 4:30pm

Unguwar Kofar Marusa  ta cika da  SUVs gwanin ban mamaki Black Prado, Range Rover, har da wasu manyan Hilux. Yara suka cika titi suna tsalle da dariya ganin motoci a arean su, mutane suna ta leƙowa ta window ganin meke faruwa

Bayan Abokin Bappah ya shigo dasu cikin compound ɗin da aka gyara ba zaka taba cewa gidan bane, duk suka zazzauna aka fara gaisawa cike da mutunta juna..

Mama daga cikin dakin ta ji hankalinta ya kasa samun sukuni ta tafi jikin labulen ta yaye labulen tana leƙansu... "Na shiga uku Ni Uwani!" Ta furta a hankali ganin manyan mutane da ke cikin gidan

Zahra ma leƙawan tayi ta ce

"Laaah! Wallahi manyan mutane ne Yaya... ga su can suna zazzaune" ko kallonta Azrah bata yi ba tana fama da zazzabin da take ji kamar zai rufeta ne

A tsakar gidan duk suka gama introducing kansu da kuma abun da yake tafe da su

"Munzo tambaye da kuma saka rana gaba ki ɗaya"

Bayan duk sun saka baki Bappah yace a bari sai bayan ta gama exams ɗin ta sannan da sati sai ayi bikin wanda duk sun tafi a akan hakan

Anan ake faɗawa Bappah Honorable Matan sa biyu

Bappah yayi shiru sannan ya ce Allah ya haɗa kansu shi kuma ya basa ikon yin adalci a tsakanin su

Sannan wani dattijo ya mika envelope yana cewa

"Ga Sadakin mu 1 million naira"

Gaba ɗaya wajen ya ɗauki silent gasp

Wani abokin Bappah ne yayi breaking silence ɗin da cewa

"Amma bai yi yawa ba? Kaɗan mai albarka ake so ai" wani dattijo ya ce

"Hakan ma ba laifi bane Babban fatan shine Allah ya basu zaman lafiya"

Da zasu tafi Bappah da abokansa suka raka su har bakin mota suna godiya
Bayan tafiyan su Bappah suka ɗanyi magana da abokansa sannan suma ya raka su kafin ya dawo cikin gida dakin Umma direct ya shiga

Bayan ya zauna ya gama musu bayanin abinda ya faru sannan ya miƙa ma Umma kuɗin ya ce

"Ga Sadakin ta nan sun bada" ya fada yana kallon Umma da Zahra

"Na wa ne?" Zahra ta tambaya da karamin muryan ta

"Million daya"

Umma da Zahra suka zaro ido, "Miliyan ɗaya!?" Bappah ya gƴaɗa masu kai

Bappah ya kuma cewa: 
"Amma fa... akwai wata magana da suka faɗa min"

Umma ta dago da sauri ta ce
"Wace magana?"

"Wai Honorable yana da Mata, Mata biyu ma"

Zahra ta zaro ido ta ce "Ya Salam!" Umma kam ma ta gagara magana dan bata san me zata ce ba at this point, Mata bama Mata ɗaya ba har biyu? Hakan na nufin Azrah zata je ta uku Inaaa bata san sanda ta girgiza kai ba ta kalli kofar ɗakinsu Azrah, nan da nan fuskar ta ya cika da damuwa ta, rayuwarta ne yayi flashing a brain ɗinta nan da nan jikinta yayi sanyi tana kallon Bappah ta ce

"Allah ya zabar mata mafi alkhairi, amma wallahi jikina yayi sanyi da wannan maganar"

Bappah ya ce "Ni kaina sai da jikina yayi sanyi ba kaɗan ba" Zahra ta ce

"Gaskiya duk son hutuna ba zan so Yaya Azrah ta shiga kan kishiyoyi har biyu ba, dan Yaya ba magana take ba dama nice nasan yadda zan kwace ƴanci na" Umma ma tunanin da take kenan sai gashi Zahra na faɗa

Meanwhile... Mama

Mama tun lokacin data lekasu ɗin nan tana daki tana share zufa Tana jin tafiyarsu Bappah ya dawo, ta fito da sauri.

"Me ke faruwa a gida? Su waye su din ne?"

"Sun zo tambayar auren Azrah ne har sun bada sadaki" Bappah ya amsa mata a takaice, Umma ta zaro ido waje abinda bata son ji ke nan

"Sadaki?!" ta faɗa da karfi Bappah ya ce

"Eh" Mama a na kallonsa ta ce

"Na wa?"

Bappah ya ce cikin sanyi murya
"Million daya"

Mama ta durƙusa, ta dafe ƙirjinta, nan da nan idonta har ya cika da hawaye "Na shiga uku! Azrah zata shiga gidan hutu? Har an sayar da rana ga sadaki million daya?" Bappah ya ce

"Ki tashi ki gode wa Allah, ki kuma tsanya mata Albarka sai Kiga Allah ya kawo wa su Siyama ma" wani bad look ta masa ta ce

"To kuɗin fa?"

"Na bawa Ummanta itace uwarta ai"

Mama tayi shiru, sannan ta wuce daki tana gyara zaninta daya kusa faduwa, ba tare da bata lokaci ba ta sanya hijab ta fita waje, bata ko damu da cewa Maghrib ya kusa ba, gidan Maman Asabe ta nufa dan bata jin zata iya hakura dan yanzu ma ita kaɗai tasan me take ji

Da daddare.. Umma na zaune a ɗakin su tana yanka fruits, Azrah na kusa da ita tana gyara notes ɗinta wanda tun ɗazu take avoiding magana da Zahra dan bata son jin komai game da saka rananta Umma ta sauke ajiyar zuciya ta ce

"Azrah ina son ki bani hankalin wani abu zan fada miki... "

Azrah ta dago kanta, ta ajiye pen ɗin hannunta tana kallon Umman

"Sun zo tambayar aurenki ɗin sannan an basu... sun bada sadaki... million daya..."

Azrah ta janye hannunta daga Umma, ta rufe book ɗin gabanta Idonta ya yi jajir lokaci guda, Umma ta sake gyaran murya ta ce

"Amma... akwai wata magana, sun ce yana da mata har biyu fah Azrah" Azrah tayi shiru tana ta kallon Umma cike da mamaki kamar bata fahimci me take cewa ba

Sai kuma ta kalli kasa tana jin zuciyarta na bugawa kamar wanda ake controlling bugawan

Umma ta kalli yarinyar nata cike da tausayawa ta ce

"Allah ya zabar miki mafi alkhairi Azrah, Amma wallahi jikina yayi sanyi, sai dai ba hakan yake nufin bashi ne mafi Alkhairi ba, zan cigaba da miki addu'a" sai sannan Azrah taji hawayen idonta ya soma zuwa ta ɗan kalli Umma sai kuma ta sauke idon ta kasa dama tun farko taga ya mata kama da mai mata, kuma tun farko ya mata girma yanzu kuma ga wata maganar mata har biyu ta share hawayen daya gangaro mata ta miƙe ta fita ba tare data kalli Umma ba...


This book costs 500. Make the payment to Hauwa Jibrin, Wema Bank account 0421255553, and send proof of payment to 08110615256.
*BEYOND THE VEIL*(LABULEN SIRRI)


YOTA ID/026


Wattpad © Jiddatulkhayr
Instagram © Jiddatulkhayr writes


Free page

Episode 15: A Cry Beneath the Veil

Tafiya take cikin sauri kamar bata ganin gabanta ko kula yaran dake gaishe ta bata yi damuwarta ta ganta gidan Maman Asabe, zuciyarta banda bugawa babu abinda take kamar waccan ba zata isa gidan ba. Tana isa gidan Maman Asabe, ko kwakkwaran sallama bata yi ba ta shiga

Ta tarar da ita tana shirin yin Sallah, Maman Asabe ta ɗago tana kallonta da mamaki, Mama ta ce

"Maman Asabe wallahi abin da nake tsoro shi ya faru yau!" Ta karasa maganar tsantsan bakin ciki yana bayyana a fuskarta

A mugun razane Maman Asabe ta gwalo ido tana kallonta ta ce

"Ban gane ba? Sun zo kenan kike nufi ko kuma an saka rana ne?" Mama ta sake share zufanta na countless times ta ce

"Su dai sun iso, Motoci sun cika titin mu fah yadda kika san ƴar gidan gomna za'a zo tambaya, ashe sadaki suka kawo, Ni duk ba wannan ba Sadakin ne yafi tsaya min a rai Maman Asabe" ta kare maganar tana share hawayen bakin ciki da suka fara sauka kan kuncinta, Maman asabe ta dafe kirjinta ta ce

"Innalillahi wa Inna ilaihi raji'un!" Mama ta ce

"Mu shiga ciki tsayuwa anan bai kama mu ba, ki kira mana Garba muji me ake ciki yanzu"

Bayan Mama sun kira shi harya katse bai ɗauka ba sai can kuma gashi ya kira back, muryarsa da sauti mai ƙarfi cike da Mugunta ya ce

"Yanzu na karɓi confirmation, video ya tafi hannun sa, Kuma na sa anyi forward zuwa numbern sa kai tsaye"

"Ya ce me?" Mama ta tambaya

"Baice komai ba tukuna... ya karɓa ne kawai, Amma ya ƙara cewa za'a ji daga gare sa da daddare ko gobe da safe"

Mama ta kashe wayar, ta miƙe tana kallon Maman asabe tace zata koma gida. ta nufi gida a hankali kamar wacca kwai ya fashe mata a ciki. Bata karasa ɗaki ba kawai ta tsaya nan sakar gidan ta fara Alwala tana idarwa ta wuce ɗakinta ta kama sallah, tana idarwa ko addu'a bata fara ba sai ga su Siyama sun shigo kamar wanda aka wurgo su haka suka faɗa ɗakin, fuskokinsu kamar wanda basu taɓa sanin wani abu wai shi murmushi ba

"Mama... gaskiya ne wai motoci sun cika kofar gidan nan? Sunce har Governor ya zo? Kuma akan maganar Azrah ce ko?" Habibah tayi maganar cike da damuwar da ya bayyana ƙarara a fuskanta

Mama ta kalle su, idonta ya cika da hawaye, tayi ajiyar zuciya sannan tace

"Toh ku zauna mana zan gaya muku amma kun tsaya min a ka"

Duk zama sukayi Siyama so kawai take taji ance mata A'a, duk Idanu suka zuba mata, Mama ta ce

"Wannan abinda kuka ji gaskiya ne, sun zo, kuma sun bada sadaki Naira na dukan Naira har miliyoyin ɗaya fah, biki kuma tana gama jarabawa za'a yi"

Kafin ta ƙarasa Habibah ta fashe da kuka, Siyama ta rike kanta tana fadin

"Ya Allah! Amma meyasa haka? Me yasa Bappah zai yarda bayan yasan na girme ta, har Habibah ta girme ta amma sai ya fara aurar da ita kuma?"

Mama ta share hawayenta, ta dafe kirjinta

"Ku kyaleni mana... wallahi yau ɗin nan zuciyata ta yi nauyi, kar ku kara min wata damuwan kuma... Allah ya zabar mana mafita".

Daren ranar, Azrah bata iya rintsawa ba, ta juya daga hagu zuwa dama, daga dama zuwa hagu aikin kenan, zuciyarta cike da rikice-rikicen da basu da suna, ta rike pillow ɗinta kamar zai ba ta amsa, tana starring waje guda

"Yaya zan zauna a matsayin mata ta uku? Ni da ko fiye da 18 ban yi ba? Yaya makomata zata kasance a gidan cikin manyan Mata? Umma, Zahra, Bappah... duk suna mafarkin jin dadina, Amma me zai faru da ni?"

Zuciyarta tayi mata nawi sosai gashi bata son ko da wasa ta daga ma Umma ciwonta, A hankali ta miƙe, tsakar gidan nasu ta fita ta ɗauro alwala sannan ta koma daki ta shimfiɗa sallaya ta fara sallah tana faɗa wa Ubangijinta damuwarta.

Bayan ya dawo gida very late ɗakinsa ya wuce direct, ajiye expensive phones ɗinsa yayi a bed side sannan ya cire kayan jikinsa ya wuce toilet dan fresh up, yana fitowa ya ɗaura sleep wear ɗinsa, ya haɗa tea yana sha wayansa yayi kara alamar shigowan message kallon wayan yayi sai kuma ya ɗauke kansa baya son wani damuwa shiyasa kawai ya tsaya a bangarensa saboda yana bukatan rest and probably bazai wuce first wife ɗinsa bace ta turo da sakon, miƙewa yayi ya ajiye cup ɗin sannan ya koma kan gado yayi sliding wayan new number ya gani amma sai ya share ya shiga searching numbern Azrah magana ya mata a Whatsapp ganin bata online kawai sai ya sauka har zai fita a Whatsapp kuma sai ya danna ya shiga wannan numbern, videos ya gani haka kawai yaji gabansa ya faɗi saboda yadda message ɗin ya shigo ba sallama balle wani content kuma private line ɗinsa ne ya daure ya danna download na video ɗin, nan take ya buɗe, playing video din yayi bai san sanda ya tashi daga kan gadon ba ba shiri yana zaro ido meanwhile yana girgiza kai trying all positive kar ya yarda da wannan videon.

Fita yayi a Whatsapp ɗin ya zauna speechless ganin hakan ba mafita bane kawai ya ɗauki ɗayan wayansa wani number yayi dialing ana ɗaga wa ya ce

"Ka duba DM ɗinka na tura maka abu, Find out who sent the video, Get me everything, names, locations, the sender's intent, I want to know who is trying to ruin this.." Bai karasa ba kawai ya katse kiran jin wani tsarawan da kansa ke masa

Honorable ya sake kallon fuskar Azrah da ke cikin video ɗin, yana jin wani abu mai wuyar fassara, tsakanin so, ƙiyayya da rudani, amma abu guda ya bayyana a zuciyarsa "She will be mine. No matter what" but yanzu yana son ya san dalilin hakan da gaske ne ko kuma sharri ne.

Washe gari da safe Mama ta tashi da mugun zazzaɓi wanda har hakan yasa ta gagara ɗaura abincin tallah, Zahra tunda sassafe ta gama shirin school ɗinta ta tafi, Azrah da itama ta tashi da zazzaɓin ta ɗaura breakfast ta kama aikin gidan saboda in few days zasu fara waec yasa bata zuwa makaranta tana cikin wanke wanke sai ga Siyama ta shigo gidan ko kallon ta Azrah bata yi ba, Siyama ta ce

"Sannu Malama, ai yanzu kina ji da kanki shiyasa ko magana baki ma mutane saboda kina jin Yanzu kinfi karfin mu ko? Toh ki sani gwara ki daina murna dan wannan ba inda zai kai ki kina nan cikin gidan nan"

ko da wasa Azrah bata kalli direction dinta ba ta kwashe kayan data wanke ta kai kitchen ta fito zata share compound ɗin ta kalle ta har sannan tana tsaye rike da kugunta ta taɓe baki, wani ashar ta jefa mata, sai sannan Azrah ta kalleta ta ce

"Look! Ki kama kanki please, kiyi maintaining wannan respect bond ɗinda ke tsakanin mu, Kinga nace wani abun ne? Balle kiyi tunanin saboda gaisuwar da aka kawo har zai sa na canza?"

Wani shewa Siyama tayi duk da bata fahimci wasu daga cikin maganganun Azrahn ba, tayi kamar zata kamata da faɗa dama jira take ta tanka mata sai ga Bappah ya fito daga ɗakinsa ya ce

"Siyama Karki kuskura, ke yanzu ba abin kunya bane a gareki kina neman tsokanan Kanwar ki? Just imagine fah? Ke waya hana ki fito da mijin da har kike wasu maganganun" Siyama ta kalle Bappah sai kuma ta fashe da kuka ta wuce ɗakin su tana jin haushin abin da Bappah ya mata

Azrah na shiga ɗakin Umma ta ce

"Azrah no matter what kar ki ce zaki na biye musu, harda rashin ilimi ke damun su, amma mutum me ilimi ai ba zai yi haka ba" Azrah ta ce

"Umma I'm always avoiding their dirty words, always pretending banji ba, yi nake kamar bansan suna yi ba ɗazun ma banyi niyyar kulata ba amma yadda naga take juya maganar wani iri shiyasa nace tayi respecting kanta" Umma ta sauke ajiyar zuciya ba tare data sake magana ba.

Yau tunda honorable ya tashi Matansa basu gane kansa ba babu wannan murmushin da ya saba musu balle wasa da dariya, kuma sun tambaye sa bashi da lafiya ne yace Lafiyan sa kalau, haka kawai yake avoiding mutane dan jiya ya kasa ma baccin kirki shiyasa gaba ɗaya ya tashi moody ganin ba zasu kyalesa ba duk da baiyi niyyar fita office ba kawai ya shirya ya gwammace ya tafi can inda babu wanda zai takura sa.

Yana zaune a office yayi nisa cikin tunani yaji wayansa ya fara ringing ɗauka yayi tare da kaiwa kunne ba tare da yayi magana ba, wanda ya kira sa ya ce

"Sir, mun samu information game da sender ɗin yanzu haka na tura maka everything a DM ɗinka" sai sannan ya sauke ajiyan zuciya ya ce

"Mind you, bana son jin wannan magana ya fito daga gare ka and ina son ganinsa, make sure kun kawo min shi but Everything should be done secretly please" Mutumin ya amsa da toh cike da ladabi, bayan ya katse kiran sai yanzu yaji wani kwanciyar hankali, a hankali ya miƙe ya fita.

Umma data shiga cikin gidan zuwanta kenan daga gidan Maman Azizah ta kalle Mama na zaune ta ce

"Barka da Rana Maman Abdul" wani kallo Mama ta mata cike da tsana ta ce

"Wani munafurcin ne kuma harda wani gaishe Ni? Dama magana kike min ? Ko kuma so kike ki gwaɗamin ƴarki zata shiga gidan daula ne? Toh ta shiga mu gani mana" Umma tayi murmushi ta girgiza kanta ta ce

"Allah ya baki hakuri, miji kuma wallahi duk ina musu addu'a Allah basu nagari wanda zai riƙe su da mutunci ban cire su siyama ba dan duk kallon 'ya'ya na nake musu" Mama ta ja wani dogon tsaki ta ce

"Aikin banza, Uban waya ce toh ki musu idan duniya da gaskiya ai sai kice tunda Siyama ta girme su a basa ita amma ai baki yi hakan ba, sannan kuma naga har wani tsiya kuka tsiro daga ke har 'ya'yan naki" Umma bata kara ko Uffan ba ta wuce ciki abinta

Zahra dake cin abinci ta ɗaga kai tana kallon Umma cike da takaici ta ce

"Allah Umma da baki kula wancan matar ba, bata da hankali bata iya magana ba, ji fah wata mugun fatan da take wai ayi auren a gani? Lallai ma wallahi" har ta karasa maganar Umma bata daina kallon ta cike da mamaki ba ta ce

"Sannu Zahra, ita ba Uwar ki bace da zaki ce wai wancar matan? Toh kar naji kar na gani kin sake faɗin haka, kinji?" Zahra ta ɗauke kai ta cigaba da cin abinci ta.

Honorable ya shiga ɗakin da aka ajiye Garba a ciki, fuskansa ba yabo ba fallasa ya shiga ciki ya zauna akan kujerar dake opposite da wanda Garba ke zaune amma kansa a kasa, Honorable yafi minti biyar yana kallon sa sannan yayi gyaran murya, Garba ya ɗan ɗaga kansa kaɗan ya ɗan kallesa dan yana avoiding eye contact da honorable

Honorable ya ce "Waye kai?" Garba ganin Honorable ba mutumin da zai ce zai kawo masa wasa bane yasa ya ce "Sunana Sadiq" wani murmushi honorable yayi ya ce

"Ina son sanin komai game da wanan videon da ka turomin" Garba ya ɗan kalle sa sai kuma ya sauke kansa ya ce

"Duk abinda yake ciki ba faking bane, ita ce" Honorable ya gyaɗa kai ya ce

"Are you sure?" Garba ya gyaɗa masa kai ya ce

"Eh babu tantama" Honorable ya ce

"Ina son pure gaskiyar abin nace maka? Zan iya baka kuɗin da baka yi expecting ba" Garba ya ce

"Gaskiyar kenan, yarinyar ce kowa ya santa da wannan halin" honorable ya ce

"Then Meyasa katuramin? Did I request?" Ya girgiza masa kai ya ce

"But I'm trying to protect you ne bana son ka faɗa tarkonta" wani murmushi mai wuyar fassarawa yayi sannan ya miƙe ya ce

"Good for you, Weldon" daga haka honorable ya fita a wajan a bakin kofar ga sojoji suna tsaye tare da wasu police, ganin Honorable suka ja baya cike da girmamawa, yana kallonsu ya ce

"Zaku iya aikin ku, make sure har sai ya faɗi komai, dan naga yana son playing ɗina" daga haka ya wuce motarsa yana kara jinjina alamarin a ransa, fuskan kam nata ne amma yadda yaga body ɗin ko kaɗan baiyi kama da nata ba dan wancan jikin fat ne hakan ya tabbatar masa ba ita bane dan yasan Azrah bata da wani kiɓa.

Duk yadda sojojin nan suko so ya faɗa musu gaskiya ki yayi daga karshe suka hau dukansa babu ji babu gani, ganin akan ɗan 50k ɗin da yayi aiki wanda karshe ma bashi kaɗai ya ci kuɗin ba har wanda ya haɗa masa videon suka raba amma gashi akan sa ana neman a halakasa yasa ya fara ihu yana zai faɗa, suka tsaya da dukansa suna kallon sa suka ce

"Waya sa ka? Kuma videon waye wannan" yana haki ya fara magana ga hawayen daya ke sintiri ya ce "Ba videon ta bane haɗawa aka yi" wani soja ya haɗe rai ya ce

"Who?" Garba ya fara girgiza kai alamar suyi hakuri, ganin zasu cigaba da jibgansa yasa ya fara ihuun zai yi magana, nan take ya faɗa musu plan ɗin wanda suka saka sa aiki, wani police ya fita waje nan ya sanar da Honorable, honorable ya ce ayi arresting ɗinsu suma

Police station suka wuce nan suka ɗebo rundunar polisawa wanda sai ka ɗauka yaki za'a tafi ganin su ma kaɗai sai ya tsinkar maka da zuciya, harda polisawa Mata suka ɗauka, duk suka shiga motar suka kama hanyar gidan su Mama..

Maman Asabe dake tsakar gidanta tana daka ga kuma Yaranta suna gefe suna wanki suka ji an baka kofar gidan da sauri ta ɗago kai tana kallon polisawan da bata san adadin su ba suka cuso kai kai tsaye, ta fara ja da baya Yaranta ma duk cike da tsoro suke kallonsu wani police yayi magana da tsawa ana tambayar waye Maman Asabe, nan duk matan gidan suka dinga fitowa daga dakin su abinka da gidan yawa, ana kallon abinda yake faruwa, wani police ya shigo da Garba wanda duk jikinsa a fashe bakinsa jini ganin haka zuciyarta ya tsinke, nuna musu ita yayi wanda take aka saka mata ankwa tana kuka tana rokon su ba ita bace wallahi Mama ne wata police ta ɗauke ta da mari wanda sai data ga stars ba shiri tayi shiru Yaranta suka fara kuka, cikin unguwarsu duk aka fito ana son ganin meke faruwa suka fito da ita suka wurga ta bayan motar cike da kaskanci kuma da rashin tausayi, Asabe ta fita da gudu tayi hanyar wajan sana'an Baban su, su kuma suka ja motarsu suka bar unguwar wanda tuni an fara magana kasa kasa, Maman Asabe banda kuka mai tsuma rai babu abinda take yi, ta tsinewa Mama yafi a kirga...

This book costs 500. Make the payment to Hauwa Jibrin, Wema Bank account 0421255553, and send proof of payment to 08110615256.
*BEYOND THE VEIL* (LABULEN SIRRI)


YOTA ID/026


Wattpad © Jiddatulkhayr
Instagram © Jiddatulkhayr writes


Free page


Episode 16: The Weight of Shame

Motocin ƴan sanda ne suka faka a daidai kofar gidan Bappah, yaran unguwar duk suka fito harda manya dan ganin meke faruwa, haka ƴan sandan nan maza da mata suka sauka zuwa cikin gidan, banka kofar su da bata da karfi suka yi, Umma dake compound tana alwala ta ɗaga kai tana kallonsu gyara mayafinta tayi tana kallonsu ganin sun nufe ta...

Yara da har sun fesawa Mama cewa ƴan sanda sun cika layinsu kuma jin sun nufi sashin Umma yasa ta fito tana murmushin mugunta tana son taga komai da za'a yi ayi a gabanta

Babu rahama ko alamun wasa a fuskokinsu, ɗaya daga cikin su ya ce

"Wacece Uwani?" Umma da kalli Mama da fitowan ta kenan bata bata ma ji su ba, a hankali tana kallon polisawan ta ce

"Gaskiya ban santa ba" wani tsawa suka daka mata dan they're very sure gidan ne la'akari da cewa Maman Asabe ce ta kawo su, Zahra ce ta fito tana kallonsu sai kuma ta kalli Mama dake murmushin mugunta irin polisawa suna ma Umma tsawa, a hankali ta ce musu

"Sir, gata can wanda kuke neman, itace Uwani" juyawa suka yi, ita dai Umma ta zama speechless, Mama kuma ba jin Zahra ta yi ba kawai gani tayi ƴan sandan sun nufeta kamar ta gudu amma ta dake tsoron kar ace bata da gaskiya ko kuma a harɓe ta, wani kallo suke mata wani ya ce

"Ke ce Uwani?" Mama ta gyaɗa kai zuciyarta na bugawa ta ce

"Eh nice... Ohh A'a bani bace ashe.." wani kallo wata ɗaya daga cikin polisawan kawai ta kama hannun Mama ta dasa mata anƙo, Mama ta fara magana tana cewa

"Wannan wani irin wulakanci ne... Mutum ba tare da yasan laifin da yayi ba sai ku kama sa? To ku jira mana mijina ya dawo" wani kallo Wani police ya mata wanda yasa ta haɗiye maganganunsa janta matar take yi har ta fita da ita waje, ai nan da nan Mama taji wani zufar ya sake gangaro mata sakamakon ido huɗu da tayi da Maman Asabe, cike da kaskanci suka wurga ta cikin motar ga ƴan unguwar duk an taru ana kallonsu.....

Wurin da aka kai su Mama ba wurin da ake kai masu laifi bane kawai, amma wurin da ake ƙoƙarin murkushe mutumtaka ne, Su Mama suna zaune a cikin Naman Asabe harta gaji da tsinewa Mama tayi shiru, wajan banda zarni babu abinda yake yi, Wani ɗan sanda yana tsaye a gabansu da duk da akwai noise mask a fuskar sa amma ya daura hannunsa akan hancinsa kamar wanda yake jin warin, yana kallon su Mama da idanu masu cike da raini ya ce

"Ku ne kuke daukar hoton wata Hajiya ku saka mata fuskar karya, kuna tunanin zaku tsallake hakan ne? Lallai ba ku san waye Honorable ba ne yasa kuka fara wannan jahilcin naku, wannan ba a film bane ko littafi, it's reality ne"

Mama ta sunkuyar da kanta ba don tana jin kunya ba, sai don takaici, tana jin kamar ta tashi ta zazzaga masa zagi jin wai Hajiya ma yake kiran Azrah, amma ta san hakan ba zai kawo mata mafita ba sai ma ta karama kanta wani laifi

Daga nan aka fitar da su zuwa wani ɗakin na daban, can suka wuni. Ba abinci, ba ruwa. Maman Asabe tana tsaye akan Mama ta dinga tsinewa mata tana faɗin

"Ina zaman zamana gashi kun jefa ni cikin ukubar bala'i, yanzu na koma gida nace wa Naman Asabe mene? Yanda yasha zamini kunne da ke idan ya sake Ni ina zan shige Ni asu?"

Mama ba tace komai mata komai ba, tana jin yunwa amma yunwar ba ta tada mata hankali kamar kalmomin tsinuwa da wulakanci da Maman Asabe ke zuba mata ba

Meanwhile..... Umma tana tsaye da rashin natsuwa, Idanunta har jaa yayi saboda tashin hankali tana jin kamar zata yi kuka tana kallon Zahra ta ce

"Zahra je ki kira Bappahn ku" Zahra ta taɓe baki sannan ta ɗauki mayafinta ta nufi hanyar inda Bappah ke zama, tun kafin Zahra ta isa, ta ci karo da shi a hanya, yana dawowa gida, fuskarsa cike da damuwa.

"Bappah!" Zahra ta ce da sauri "An kama Mama da Maman Asabe an kaisu station!"

"Me?" Bappah ya tsaya cak yana kallon Zahra da idanu masu cike da tambaya

"Wace irin magana ce haka? Station? Ina ne? Dama da akace polisawa sun taru kofar gida kamasu kenan akayi ko ya? Sai kuma ya kama tafiya da sauri har haɗe kafa yake yi ya isa gida ga Zahra dake binsa a baya

Anan compound yaga Umma na tsaye har sannan ga kuma Azrah dake zaune itama tayi tagumi, anan Muna ta fara sanar da Bappah abinda idanunta suka sani

Suna cikin wannan ruɗanin ne sai ga sallamar wani mutum, Mijin Maman Asabe ne, sau kuma.da Asaben daga bayansa, ya karasa ya mikawa Bappah sannan ya fara masa magana

"Ai wallahi ni banga laifin matarka ba, amma nasan halin Maman Asabe, zata iya shiga rigima fiye da haka, ita dan haka kullum a garin tara mutane suke jefa ta cikin masifa" inji mijin nata

Asabe dai na gefe tana ji tana kallon su, ba ta ce uffan ba sai ga su Siyama da Habibah sun shigo gida da sauri, fuskokinsu cike da damuwa, Asabe ta watsa musu wani banzan kallo cike da tsana sannan ta juya zata koma gidan su

Bappah da Mijin Maman Asabe suka tashi suka kama hanyar station ɗin unguwar su domin su san inda aka kaisu, Amma ba'a kai su station na unguwar tasu ba, Sun zagaya kusan rabin stations ɗin garin amma basu same su a can ba

Daukar washegari da kyar suka samu inda suke da taimakon wani police ɗin, Su Mama suna cikin yanayi mai raɗaɗi ba duka aka musu ba, amma sun sha wahala ba kaɗan ba wulakanci, yunwa, rashin barci, da tsoro Lokacin da Bappah ya tambayi bail, aka ce masa

"Bailing ɗinsu? Haba ku kuwa duk girman laifin nan, toh honorable bai yarda a bada bailing dinsu ga kowa ba" with shock Bappah yake kallon sa ya ce

"Honorable kuma?" Police ɗin ya gyada masa kai yace "Eh shi, yarinyar da zai aura ne suka ɗaura hotonta akan na wata matan banza wanda sun tura masa hakan kuma zai iya ɓata masa kujerar takaransa...

Bayan fitowar Bappah da mijin Maman Asabe daga ofishin 'yan sanda, jikin su babu ƙwari, ya gama sanyi wanda duk basu yi sammanin haka bane abun ya faru, haka suka fito kowannensu na dauke da fuskarsu mai nauyin laifin da suka aikata, Suna ƙoƙarin danne kunya da takaici dan ba kaɗan ba sun dasu kunya...

Bayan su Mama sunyi laushi iya laushi ga abincin kuma kamar yadda kasa ma karamin yaro zaka bada haka suke sako musu, can kusa da Magrib sai ga Honorable da kansa ya iso ofishin 'yan sandan fuskar sa ɗauke da ƙiyayya da mamaki....

"Ina mamakin ku akan me zaku ɗauki hoton mutum ku ɗora masa karyar da bata da tushe? Wannan fa cin mutunci ne! Wannan kuma ɓata wa mutum sunane" Honorable ya faɗa da murya mai ƙarfi

Mama da sauri ta furta "Wallahi sharrin shaiɗan ne ya yi mana tasiri"

Maman Asabe kuwa cikin rawar murya tace

"Ni Mama Abdul ce ta saka ni, ita ce ta ja ni cikin wannan magana da masifar, amma a gafarta mana yallabai"

Garba kam ya zauna ne tamkar ba a kansa ake magana ba ko kallo bai yi ba balle awa ran zai ce wani abun

Honorable ya ce "Me dalilinku na hakan kawai nake so baki? Duk shiru suka yi sun gagara basa amsa

Honorable ya mike fuska a daure ya ce "Na tabbata koma da ƴaƴa kuma yanzu ace ma naku aka yi wa haka zaku ji daɗi?"

Suka fara basa hakuri da neman afuwa amma ko kallo bai sake yi musu ba, ya juya ya bar wurin cike da taimacinsu

Da yamma Bappah ya fito daga ɗakinsa yana bin compound ɗin da kallo wanda yana son tabbatar da babu kowa, bakin kofa ya nuna yayi dialing ana honorable yana sake kaka cikin gida to be sure babu wanda zaiji wyan, Honorable na ɗaukawa cikin sigar natsuwa da tawali’u, ya fara da bashi hakuri

"Alhaji ina neman Alfarman mana" Honorable ya ce

"Ina jin ka Baba, menene? Bqppah ya ce

"Wannan matan da kasa aka kama da ɗayan Mata ta ce ka tausaya mata ka sake su, in shaa Allah hakan ba zai kara faruwa ba"

Honorable ya yi shiru na ɗan wani lokaci sannan ya ce

"Shikenan Bqppah zan sa a sake su amma saboda kai, kuma ban yaɓa dauka ai ɗayan matar ka bace" bayan gama.wayansu har sannan honorable bai daina jinjina wannan labarin ba...

Bayan wayar Honorable ya kira ofishin ‘yan sanda, ya bada umarni da a sako su Mama da Maman Asabe, amma kafin hakan, sai da suka sha masifa da gargaɗi mai tsanani daga hannun jami'an tsaro, an sake su ne kawai saboda girmamawar da Honorable ke wa Bappah, ba don suna da wani cancanta ba.

Rayuwar da suka yi a ɗan wannan wajan banda faɗa babu abinda suke yi kamar basu san junansu ba haka suka koma

Da suka dawo gida, Bqppah ya ɗaga kai yana ma Mama wani kallon tsana ya fara mata masifa kamar zai dake ta, ga taikaicinsa su Habibah da Siyama da yanzu sun ma daina zaman gidan, yana kallon Mama wani one look ta masa wanda ba shiri yayi sitt

Bayan magariba, jama'a suka fara shiga yin ja je, wannan yana fita wani zai shigo kamar wanda suke zuwa karɓan sadaqa tsabar gulma

Habibah da Siyama ne suka kulle ƙofar gidan suna masiyan gadon
"Gulma za ta kashe m
su, kai Allah wadaran naka ya lalace"

A bangaren Maman Asabe kuwa tunda tasa kafarta a cikin gidan mijinta ya fusata ƙwarai, har sai da ya kusa duka ta saboda fadan da yake mata

"Sau nawa nake ce muku bana son kallon matar nan kuma mu'amala amma bakya ji ko? Ga irinta ai nan, Kin jawo mini kunya!" Cewar mijinta


A gidan honorable komai na tafiya lafiya a ido, amma a zuciyar uwargidan nasa kamar wacca ake hura wuta. Uwargidan Honorable Hajiya Maryam,
ta saba ganin Mijinta a cikin natsuwa da kamun kai, A.amma kwanan nan tana jin canji wani abu da bata iya fassara ba

A daren ranan, matarsa ta biyu, Hajiya Rabi, ta shigo dakin uwargida da fuskar da ke ɗauke da wani nauyin magana. Ta zauna a gefen katifa, tana kallon uwargida da murmushin karya

"Anty... wallahi ban san ko zan faɗa miki ba, amma zuciyata ba ta barni lafiya, sau na huta brain ɗina zai dawo

Hajiya Maryam ta ɗago kai

"Me ke damunki haka Rabi?"

Rabi ta saki ajiyar zuciya. "Wallahi naji wata magana ce da ban jin ya kamata ki zauna baki sani ba, Sun ce mijinmu yana shirin sake aure shi yasa kwana biyu yake diverting zama gida ga kuma changes da suke ganinsa da shi,

Maryam ta ɗan yi dariya mai taushi
"Wannan magana ba sabuwa bace Miji namiji ne, ai..."

Sai Rabi ta katseta da gaggawa. "A'a Anty ba kamar sauran zance ba Wannan karon gaskiya ne,.kuma yarinyar kamar ita tayi kanta

Fuskar Maryam ta sauya. Wannan karon zancen ya ɗan dame ta "Yanzu ke faɗin haka? Wato magana ce da har take da tushe?"

"Eh kuma yarinyar kamar ita tayi kanta, Ni wallahi duk na tsorata"

Daga nan Hajiya Maryam tasa masa ido sosai nan taga yadda maganar Rabi gaskiya ne

Ba tare da ɓata lokaci ba, sai ta kira wata amintacciyar kawarta da ke da alaƙa da wani jami’in bincike, ta roƙe ta da a taimaka a gano wacece wannan yarinyar da ake danganta da mijinta, tace a tantance komai: asali, danginta, makarantar ta, da inda take zuwa.

"Ni ba zan zauna a raina ni ba dole kuma kowa ya bani respect Dina kuma ya gama aure a duniya" cewar Hajiya Maryam,

"Ko aure zai yi, dole na san wa zai aura"

A haka aka fara bincike cikin sirri, aka sa ido, ana bibiyar yarinyar da aka ji ana ambata. Zancen ya fara ɗaukar zafi, yayinda masu bincike suna yara duk wata information suna adana musu


This book costs 500. Make the payment to Hauwa Jibrin, Wema Bank account 0421255553, and send proof of payment to 08110615256.*BEYOND THE VEIL* (LABULEN SIRRI)


YOTA ID/025


Wattpad © Jiddatulkhayr writes
Instagram © Jiddatulkhayr writes


Free page


Episode 17: The Silent Thunder


Wani babban parlon ne wanda ke ɗauke da duk wata kayan more rayuwa ta duniya, wata mata ce ke zaune a kan wata sofa tana ƙaɗa kafa har sannan zuciyar ta bata daina tafarfasa ba, tana danna wayar hannunta ne ba tare data san me take yi ba, wata mata ce daga cikin wanda ta saka su mata aiki ne ta shigo cikin nutsuwa amma idonta na ɗauke da wani sirri mai nauyi tana murmushi dan tasan Hajiya zata ji daɗin wannan samo dukkanin bayanan akan wannan yarinyar amma kuma ba lallai ta iya jura jin menene ba

"Barka da zuwa" Hajiya ta faɗa cikin kulawa

"Nagode Uwargida a gidan honorable, na samo miki dukkannin bayanan amma... kuma sai kin daure zuciyarki" ta kare maganar tana avoiding eye contact da Hajiya
Hajiya ta ɗaga gira tana kallonta alamun sauraro

Sai matan ta miƙa mata wani envelope dake dauke da wasu pictures na wata yarinya da kuma rubuce da bayanai ta ce

"Sunanta Azrah Matar da aka cewa Honorable yana da niyyar aura kenan Hajiya, amma karyan su tasha karya, na tura ƴan leƙe-leƙe sun binciko min cikakken bayani akanta"

Hajiya ta karɓi takardun tana duba hoton Azrah, lokacin da tayi ido huɗu da hoton nan take jikinta ya ɗaura rawa, numfashinta ya fara seizing, zuciyarta na bugawa da ƙarfi,
Fuskarta ta cika da mamaki da kuma tsoro da lokaci guda ya kamata

"Wannan... irin wannan kyau... balarabiya ce ko?!"  Hajiya Maryam tayi tambayar ba tare data san ta furta hakan ba

"A'a duk da dai ance kamar ita mahaifiyar yarinyar ba'a san assalinta ba amma tabbas mahaifinta ɗan nan Katsina ne, mazauniyar kofar Marusa a Ghetto area suke ma Hajiya"

Kusan saura kaɗan Hajiya ta sake fisari a jikinta, da kyar ta miƙe ta nufi ɗakinta ta kasa tsayuwa ta kasa kwanciya, ta kasa zaune zuciyarta na cike da ɓacin rai da mamaki da kuma kishi daya cika shi fam

Kamar wanda aka tsikara sai ta miƙe da sauri ta fara shiri, cikin fushi ta saka kaya ko ɗaura ɗankwali bata yi ba ta fita zuwa compound da sauri wajan motarta ta nufa ta shiga ciki har wani jiri take ji amma ta tada motar ta figa a mugun guje kai tsaye gidan co-wife ɗinta ta nufa

Tana parking ta nufa entrance ɗin ba tare data tsaya ta rufe motar ba ko ta dawo da nutsuwarta ba, tin daga balcony ta fara kwaila mata kira, da sauri Hajiya Rabi ta fito tana kallon kishiyarta da mamaki, tun kafin tayi magana ta katse ta ta ce

"Kin ga wacce Honorable ke shirin aura? Kin san daga ina take? Wallahi wannan ai tozarci ne!"  Hajiya Rabi ta tsaya cak yana kallon ta da mamaki sai kuma ta ce

"Babban Macece kenan zai aura?" Hajiya Rabi ma ta mata wani kallo ta ce

"Take this and see" ta kare mata maganar tana miƙa mata hotunan Azrah,wani zaro ido tayi tana kallonta bayan ta karɓi hoton itama tana kallo, murmushin takaici tayi ta ce

"Ai bamu ga ta zama ba, ina mu ina bari ya auro mana wannan? Ai mun shiga uku idan har ya aureta mulakanci kuma sai wanda muka gani" Hajiya Maryam ta ce

"Ke duk ba wannan ba, tashi zakiyi mu je mu tabbatar da gaskiyar lamarin... sannan mu bawa yarinyar concrete warning tunda daga ghetto area take ba abinda zasu iya yi, shi kuma tunda har bazai tsayar da hankalinsa ba munsan wata idan bai sani ba, ita kuma zata gane tsakanin mata akwai ruwan zafi".

A haka Hajiya ta sake sa aka kawo mata wani info wanda yayi daidai dana farkon, tana gama karantawa ta mikawa co-wife dinta ta ce

"To yanzu kin ga da idonki ko? Nace miki komai haka ne ba wata tantama, ta shi mu je, yau zasu gane akwai banbanci tsakanin mai power da wanda bai san ma me powern ba"

Hajiya da co-wife ɗinta ba su yi wata-wata ba suka nufi unguwar Kofar Marusa, Motarsu mai tsadan gaske na karaya ƙasa a cikin layin ghetto, wanda ba kasafai ake ganin irinta ba a wannan unguwar, wanda tun shigowar su layin yara suka fara bin motar da gudu suna kallon motar

A bakin ƙofar gidansu Azrah suka parka motar, Hajiya ta fara sauka  sannan Hajiya Rabi karewa layin suke da kallo, kallon ma kallon kƴama

Kamar wanda ba zasu taka kasa ba suka nufi kofar gidan da kakkausar murya Hajiya ta fara sallama

"Assalamu Alaikum!"

Zahra ce ta fito tana daure da darduma a kafaɗa, alamar ta idar da sallah kenan, ta zare ido ganin manyan mata biyu cikin shigar masu hali da izza, tana kallon su ta ce

"Wa'alaikumus Salam Ina wuni?" Duk kallon Zahra suke wanda itama ba maraba da Azrah sai dai Azrah ta fita haske sannan ta fi tsayi

"Yauwa, Ina ɗakin Maman Azrah?" Cewar Hajiya ba tare da murmushi ba saima wani kallo data ke bin compound ɗin da shi

Zahra ta nuna musu ɗakin da hannu, ba tare da wani jinkiri ba suka shiga

Umma ce ta tarbe su da murmushi duk da bata san su ba
"Sannu da zuwa, ga waje ku zauna" ta yi maganar tana shimfiɗa musu dadduma, Umma ta ɗago ganin ta basu wajan zama amma basu zauna ba, cike da wulakanci Hajiya ta ce

"Barkanmu dai, amma ba zaman lafiya ya kawo mu ba, mun zo ne kashedi ma ƴarki Azrah" Hajiya Rabi ta karɓe ta

"Mun samu labari cewa diyarki Azrah na da alaƙa da mijinmu  Honorable, har Office ɗinsa take binsa, toh muna baki kashedi da gargaɗi ta rabu da shi tun kafin lamari ya lalace muku, Kuma ku gaya mata cewa mu ba sa'anninta ba ne, ba zata iya shiga cikin rayuwar mu ba balle har ta fara tunanin kishi da mu" har suka kai aya Umma na kallonsu

Jikinta yayi sanyi Zahra wacce ta tsaya a bakin ƙofa da ruwa a kofi, bata san sanda ta tsaya cak ba idanu ta zuba musu itama

Azrah kuwa daga cikin ɗaki ta ji komai jikinta yayi mugun sanyi Zuciyarta ta cika da fargaba da nauyin abin da ke faruwa ga kuma wani tsoro da lokaci guda ya dira zuciyarta

Ba tare da jiran ko tsammani ba matan suka juya suka fita, da suka kai bakin ƙofa suka ci karo da Mama da tun shigowar su ta fito jin abin da ya kawo su ta nufi bakin kofa da sauri shine zasu fita suka ci karo

Mama ta ja su gefe cikin rawar murya, amma tana kokarin yin magana da ladabi, wani kallo suke mata wanda a cike yake da wulakanci, ta ce

"Kuyi hakuri ku saurare ni... Ni ma lokacin da aka kawo ita mahaifiyar Azrahn sai da nayi kusan barin gida, saboda kwatakwata ko kallo ban ishe Malam ba, gani yake ya dauko mace mai karatu sannan kyakkyawa kuma yadda zai iya nunata a kamfafoninsa, amma haka na tashi na fara neman mafita har daga karshe na samu mafita har zuwa yanzu... yanzu idan har kuna da ƙarfin hali, ba wai na kuɗi ba dan nasan kunfi karfin wannan toh kuyi iya kokarinku ku hana auren, kafin komai ya wuce gona da iri ko kuma a ɗaura auren ku shiga uku dan asiri baya cin su"

Amma Hajiya da co-wife ɗinta suna kallonta da wani irin kallo na kyama da wulakanci Kamar dai "wacece ke da zaki bamu shawara?" 

Mama dai bata damu ba ta juya ta shiga cikin gidan, tana girgiza kai kamar wacce ta bata san komai ba

Bayan tafiyar su Hajiya da Hajiya Rabi Umma ta zauna dirshen a ɗakinta, zuciyarta cike da raɗaɗi ta dade a wajan ba tare da ta ce uffan ba, kafin ta kalli Zahra da ke tsaye gefe tana kallonta tuntubi ta ce

"Har ga Allah wannan abin kunya ne, toh me su kuma na zuwa da kansu? Ashe haka auren mai mata yake jawo wa? Wataƙila ba mu yi tunanin daidai ba tun farko..." Ta faɗa cikin tausayin ƴar uwarta

Azrah ta fito a daga ɗakin duk tayi kalar tausayi idonta har yayi mugun ja, Bata kalli kowa ba ta zauna kusa da Umma, sannan a hankali ta ce

"Umma ni bazan ci gaba da wannan ba, Zuciyata ba za ta iya jure irin wannan wulakanci ba Idan har auren Honorable ke nufin raini da tozarci daga matansa to ni na hakura ko da kuwa me zai bani ne"

Umma ta kalleta da idanu masu cike da ƙauna da tausayi amma gaskiyar magana kenan itama hakan ne a zuciyarta tun farko, amma bata so ta hana ‘yarta farin ciki dan bata san ko tana son Honourable ɗin ba, kawai ta ɗan dafa kafaɗar Azrah da murmushin amma dan bata san me zata ce mata bane cos she's speechless....

Bayan Magrib kamar yadda honorable ya saba zuwa haka yau ɗin ma yazo kamar koda yaushe, yayi parking motar sa ya sauka sannan ya karasa zauren gidansu ya kirata a waya

Azrahn dake gefen Umma har sannan babu wanda yace wani abu cikinsu taji wayanta yana ringing kallon Umma da Zahra ta yi, Umma ta mata alama data yi picking, bayan su ɗanyi magana sai kuma ta wuce ɗaki ta saka Hijab ɗinta sannan ta fita

Bayan sun gaisa ta kasa haɗa ido da shi har sai daya ce yau lafiya? Tana kallonsa sai kuma ta sauke ido ta ce

"Alhaji don Allah ka gafarce ni Na yanke shawara… bazan iya cigaba ba, ka hakura da Ni dan Allah" ya dinga kallonta da mamaki duk yadda yaso ta faɗa masa dalilin haka ki tayi daga baya ganin ba zai hakura ba yasa ta faɗa masa cikin tsoro.... Ta karasa ta ce "kuma gaskiya tsoro nake ji, Ni ba zan iya zama cikin matanka ba harga Allah"

Honorable ya tsaya yana kallonta da mamaki da kuma tausayi ya ce

"Azrah… listen to me, duk abinda suka aikata sunyi shi ne without my knowledge... I've been trying to protect you shiyasa banma taɓa faɗa musu wani abu game da ke ba"

Amma kafin ya gama magana ta fara girgiza kai hawaye na gangarowa daga idonta ta ce

"Bazan iya ba wlhi ni yarinya ce ba zan iya zama da manyan mata ba... Zuciyata ta gaji kuma Please… just let me go"

Wani irin shiru ne Honorable yayi ya tsaya yana kallon ta kamar yana neman kalmomin da zasu sauya zuciyarta… amma babu wata da zata shige zuciyarta a lokacin

Azrah ta share hawaye a hankali, sannan ta kalli Honorable da ido masu ɗauke da tsoro

"A'a" ta ce cikin murya mai sanyi "Ni ba zan iya zama da matanka ba Sun fi ƙarfi na, Rayuwarsu da tawa ba iri ɗaya bane, Wayon su da salon su sun sha banban da ni, Bazan iya rayuwa a cikinsu ba, kayi hakuri kawai ka kyaleni ko dan saboda Umma ta"

Honorable ya langwabar da kai yana kallonta ya ce

"Azrah please, give me a chance to explain bazan bar ki haka ba saboda ina ƙaunarki, and I promise you, zan kare ki"

"Ka riga ka kasa kare ni!" Ta katsesa cikin sanyin muryanta da kuma wani confidence ɗin magana "Ka gani fa! Sun zo har gida, Ina laifina anan da nayi har hakan ya shafeni pls? Why not su fara maka magana tunda ai kai kace kana so na"

Sai ta fashe da kuka ta juya tana kokarin shiga ciki Honorable ya tsaya cak, zuciyarsa na kuna, amma ya kasa cewa komai. Ya sauka daga matakin kofar, ya rigata shiga cikin gidan zuciyarsa a matuƙar ɓace

Yana shiga ciki, ya hangi Zahra na alwala, ya dakatar da ita a hankali

"Zahra jagoranceni zuwa dakin Umma mana"

Zahra ta kalle shi da damuwa bayan ta gaishe sa sannan ta tafi cikin zuwa ta faɗa wa Umma. Bayan ƴan mintuna ta fito ta ce

"Zaka iya shigowa"

Honorable ya shiga ya gaishe da Umma cikin ladabi sannan ya zauna

"Wallahi Umma, ban san abinda ya faru ba sai da naji, Ina neman afuwa a madadin matana, nasan bai dace hakan ba it's sign of disrespect nayi alkawarin kuma hukunta su"

Umma ta gyara zama tana dubansa cikin natsuwa ta ce "Ba komai Honourable, wlhi komai ya wuce sannan dan Allah Karka musu magana balle wai hukunci" yayi shiru yana kallon wani waje haka kawai yaji ya kasa maganar da yayi niyyar mata kawai ya miƙe ya fita daga ɗakin

Yana wucewa bakin kofa, yaga Azrah tsaye  har yanzu tana bakin kofa, idonta jajir. Bai tsaya ba, ya wuce kai tsaye zuwa motarsa, ya shiga ya tada motar zuciyarsa cike da haushi da damuwa

Azrah ta juya jiki a sanyaye, ta shige ɗakin Umma. Umma ta bita da kallo na tausayi, sannan ta sauke ajiyar zuciya Zahra tana gefe ta ce

"Allah sarki shi. Wallahi yana da hali na mutanen kirki, amma matansa... Allah dai ya kyauta"

Umma ta ɗan murmusa "Zahra, har yanzu ke yarinya ce ba zaki fahimci komai yanzu ba"

Yana isa gida, Honorable bai zauna ba ya nufi ɗakin uwargidansa rai ɓace

"Big shame on you, idan banda jahilci da rashin sanin menene hankali ina ku ina zuwa gidansu yarinyar? Ni na kai kaina shine laifi ya zama nata? I'm warning you idan bakuyi hankali ba wallahi You will definitely regret"

Uwargidansa ta zabura tana kallon sa da mamaki "sbd ita har zaka iya gaya mana magana Alhaji? Yanzu sbd wata banza"

"Sure! And mind you, wallahi hakan bai isa yasa na fasa ba, sannan rashin hankalin ku zai iyasa ku tunzura su" murmushin takaici yayi kawai yabar ɗakin zuciyarsa cike da takaicin su.

This book costs 500. Make the payment to Hauwa Jibrin, Wema Bank account 0421255553, and send proof of payment to 08110615256.
Episode 18:The Breaking Spell

Kamar yadda yanda rana ke fitowa ba tare da izinin kowa ba, haka ne ma rayuwa ta ci gaba da juyawa tsakanin su Azrah da Honourable ba tare da wani communication ba, dan tun daga wancan ranar bai sake zuwa ba sai dai yakan kirata lokacin zuwa lokacin wanda kwata kwata ya kasa gane kan Azrahn, kana ganinsa kuwa kasan yana cikin damuwa wanda hakan bai fasa bayyana a fuskarsa ba

Kamar koda yaushe Hajiya Maryam ta fito cikin ƙasaita da izza irin nata, makullin motar ta a hannunta sannan ɗayan hannun nata tana riƙe da fashion designer bag, tana sanye da sun glasses, ta wuce inda Mijinta ke yawan zama a backyard dan wajan shan iskansa kenan, ɗan taɓe baki tayi tana kallonsa tana ayyana damuwar daya sama kansa saboda wata banza can, ta karasa inda yake ta ce

"Darling" a ɗan firgice ya juyo alamun ta yanke masa tunaninsa ya ce

"Azrah!" Ɗan dakata wa tayi tana kallonsa da mugun mamaki, wani murmushin takaici da kuma bama kanta tabbacin hanyar da zasu bi yanzu shine best way out, dan tana da tabbacin cewa idan har ya auri Azrah, zata ɗauke musu matsayin su gaba ɗaya a zuciyar Honourable, Zuciyarta taji ya buga cike da tsoro, kishi da fargaba, Honorable kuwa shi bai san ya ce Azrah ba kallon yadda ta faɗa duniyar tunani yake ya ce "Maryam zaki fita ne?" Sai sannan ta ɗan kalle sa sai kuma ta ɗauke kai ta juya ta bar shi zaune baki buɗe haka ya bita da kallo sai kuma ya ɗauke kansa daga kallonta ya jingina kansa a resting chair dake zaune akaj

Tana parking a kofar gidan ko kashe motar bata yi ba ta ɗauki handbag ɗinta, wayanta ta ciro a Jakkan sannan tayi dialing numbernta tana ɗaga wa ta ce

"Ina bakin gate ɗinki" daga haka ta katse kiran tayi cilli da wayar a wajan mai zaman banza ta kifa kanta da steering motar tana jin wani zafi a ranta, Allah ya gani dan co-wife ɗinta ma ba yanda zata yi ne amma da zata zauna da kishiya ne? Balle mace irin Azrah, ɗan tsaki ta jaa, can sai ga Hajiya Rabi'a ta fito tana karasowa ta buɗe front seat ta zauna tana kallon Hajiya Maryam ta ce

"Shine ba zaki shigo ba?" wani kallo ta mata sai kuma ta ɗauke kai ta ce

"Bamu da lokacin ɓata wa, kuma Kinsan kauyen nisa gare sa amma kike wasting mana time da nasan wajen da tuni nayi gama abuna ai" Hajiya Rabia ta gyara zamanta ita kuma Hajiya Maryam ta tada motar suka bar unguwar..

suka tafi wani kauye a can cikin wani gari dake cikin jihar Katsina can wani tsohon daji suka nufa, wanda ba kowa ke iya shiga ba sai wanda suke shawara da shaidan ko suke bin huɗubar shaidan, bayan sun yi parking suka sauka suka fara nufa wani hanyar da zai sada su da fadan Mutumin wanda ba zaiyu su shiga da mota ba dole sai da ƙafa, Suna isa wajen wani dattijo mai murya katti wanda kallo ɗaya da zai yi ma mutum zai karanta zuciyarsa, kallonsu yayi ya kwashe da wata kalan muguwar dariya irin ta bosawa sannan ya nuna musu inda zasu zauna, Hajiya Rabia ta fara magana

"Mun zo ne domin wata yarinya me suna Azrah, tana bamu sleepless night.. yarinyar kyakkyawar ce, kuma harga Allah muna son a nisanta ta da Mijinmu, dan ya kwallafa rai a kanta yana son aurenta mu kuma gaskiya ba zamu iya juren wannan bakin cikin ba"

Dattijon ya yi dariyar da ke tsoratarwa ya ce

"Wannan yarinyar ba mai sauƙi bace, ta gina kanta da addu'o'i da azkar, sannan kuma tun daga can garinsu an dafa naman su da magungunan kariya, toh kunga ba wani tsafi da zai yi tasiri a kanta idan kuma kuna so za'a iya mata wani aiki amma aikin zai yi wahala sosai sbd Akwai hatsari ana samun matsala kaɗan zai juyawa kanku" yana kare maganar ya sake shekewa da dariya mai tsoratarwa, kallon juna suka yi sannan suka sake maida kallon su ga Mutumin,yana wani irin abu tare da bubbuga kasa ya ce

"Idan kuma kuna so tunda ita akwai hatsari akan ta, Amma mijinku fah? Nan da nan aikin zai kamasa"

Nan take suka yarda, suka bada kuɗi masu yawan gaske sannan sun bi dukkan umarnin da aka dinga ya musu, ya ce

"Za'a fara da cire Azrah daga tunanin Mijinku ? Za'a rufe zuciyarsa da rashin sha'awar ta balle tunaninta kuma, za'a mayar da tunaninsa bisa ga abubuwan daban-daban sannan za'a saka masa ƙiyayyarta mara adadi a zuciyarsa......"

Tun bayan da suka dawo daga wannan ƙauyen nan, kamar ranan aka fara musu aiki dan tun daga wannan ranan honorable ya daina kiran Azrah, da farko ta ɗauka ko yawan aiki ne na office sai kuma taga shirun yayi yawa, duk da bata son sa amma sai kuma haka kawai ta fara jin wani iri kuma da shirun nasa..
Azrah ta fara jin zafi a ranta.

Tun abin na damu ta har ta mayar da hankalinta ga karatunta da kasuwancinta, ta fara rubuta WAEC ɗinta cikin natsuwa, tana kuma aikace-aikacen gida sbd yadda Zahra ma ta mayar da hankalinta ga karatunta,  Mama da yaranta kuma basu fasa ci gaba da wurga masu Umma da Azrah habaici habaicen da suke musu ba...

Wata rana da yamma Bappah ya dawo daga inda yake zama ya shiga compound ɗin da sallama Azrah ce kaɗai ke tuka abinci ta gaishe shi ya amsa har yayi gaba sai kuma ya tsaya ya ce

"Azrah idan kin gama inason ganin ki ko?" Ta ce "Toh Bappah" bayan ta gama komai ta ɗauki abinci ta kai cikin ɗaki tana kallon Umma ta ce

"Umma barin je Bappah na kirana" Umma ta amsa mata da 'Toh'

Tana shiga ɗakin Bappah tayi sallama ya amsa mata ta shiga ciki ta zauna ta ce

"Bappah gani" ya ce

"Azrah me ke faruwa tsakaninki da Honourable ne? Ban sake jin labarinsa ba daga gare ku, kuma yanzu na daina kallon sa yana zuwa wajan ki lafiya?"

Azrah ta dan yi murmushi mara sauti ta tsunkuyar da kanta kasa sai kuma tana wasa da fingers ɗinta ta ce

"Bappah Inaga ba Alkhairi ne shiyasa, dan yanzu ya daina kirana kuma Nima na mayar da hankalina ga karatuna siyasa banma bi ta kansa ba, kuma yama daina kiran at all"

Bappah ya girgiza kai "To cire shi a zuciyarki, Allah zai kawo wanda yafi shi, sannan zan kirasa muyi magana idan har ya fasa ne sai ya janya a maida masa sadakinsa dan ba'a nema akan nema, Kada ki damu zamu taya ki addu'a Ni da Umman ku"
Azrah ta amsa da "Amin" kanta a kasa har Sannan...

Rayuwa ta ci gaba da tafiya, Azrah ta ƙuduri niyya ta tabbatar da cewa ba aure ne rayuwa kaɗai ba, Duk wata mafarkin da take da shi game da Honourable dama akan Umma ne sbd lafiyarta

Ta mayar da hankali sosai wajen ganin karatunta ya tafi successful tana komawa gida kullum cikin gajiya amma hakan baya karya mata gwiwa ba, Azrah ta daina jiran sakon Honourable, ta mayar da gaba ɗaya hankalinta wajen nasara ne wanda dama tun tasowanta takan dage kan karatu da kuma sana'a

A bangaren Honourable kuwa, tun daga wannan lokacin duk sanda ya fara tunanin Azrah haka kawai tsoro ke kama sa, duk sai yaji kamar a birkice yake, duk da cikin duhun da yake, amma can ƙasan zuciyarsa bata daina tunanin ta ba kuma baya iya kiran ta duk da wata tsanarta da yake ji a ransa, amma bai san dalili ba, haka kawai ya fice daga hayyacinsa..

Kamar kullum yau ma ta taso daga makaranta tana hanyar gida kamar yadda ta saba tun tana karama kanta a kasa yake idan har tana tafiya, tazo zata tsallake babban titin wajan kamar ance ta kalli gefenta kawai ta kalli Ya Saif ya fito a motar sa yana tsayan abu, nan da nan murnan ta ya dawo ta ma manta cewa ta gaji ashe da gudu ta karasa jikin motar ganin kamar komawa motar zai yi tana isa ta sake masa murmushi ta ce

"Barka da Rana Ya Deen" Saif ya juya yana mata wani irin kallon sannan ya bita da kallo ya ce

"Ke lafiya zaki wani zo min jikin motar?" Ta ɗan kallesa sai kuma ta dake ta ce

"I'm Azrah sir, baka gane Ni bane halan, please numbern Mummy da Anty suhaila zaka taimaka ka bani lokacin bani da waya amma yanzu an tsiya min

Dakata wa yayi daga shiga motar yana mata wani irin banzan kallo ya ce

"Malam lafiya? Ko dai kina Bara ne ban sani ba?" Azrah ta tsaya kallonsa with shock sai kuma a hankali ta ce

"Bara kuma akan me? Ko kaga na maka kama da mai raba ce ban sani ba?" Wani kallo yake binta da shi ya ce

"Zaki matsa min ne da kazantar ki ko sai na hanɓare ki kin faɗi tukun nan?" Ja da baya tayi tana kallonsa sai kuma tayi murmushin takaici a ranta tana ayyana cewa da badan Mummy bace Mahaifiyarsa ba, ba abin da zai sa ba tafa faɗan masa bakar magana ba, ko sake kallon direction ɗinsa bata yi ba tayi gaba abinta

Da daddare ta fito daga ɗakin Umma tana haɗa kayan wanke wanken da zata yi and gobe tana da exams da safe, bayan ta ɗibo ruwa ta fara kenan sai ga Mama ta fito daga ɗakinta, Azrah ta ɗan Kalle ta sai kuma ta mayar da hankalinta ga abinda take yi ta ce

"Barka da dare Mama" Mama dake murmushi ta karasa har wajan da take ta ce

"Yauwa Azrah, wanke wanke kike yi kenan? Ba zaki bari da safe ba"

Azrah ta ɗan tsaya tana kallonta saboda sai taji wani iri da yadda Mama ta mata response sbd gaisuwar su ma is hardly ta amsa balle harta nuna wani concern akan su, a hankali ta sauke idon ta kasa ta ce

"Eh da safe ina da jarabawa ne Zahra ma itama tana da makaranta shiyasa" ta gyaɗa mata kai ta ce

"Ayyah, ai naga dare yayi ne shiyasa nace da kin hakura, amma tunda zaku fita da safe gwara kiyi abinki yanzun" Azrah tayi murmushi dan Allah² take Mama ta bar wajan dan kawai ta samu kanta not comfortable, Mama ta gyara tsayuwarta ta ce

"Nikam yaushe ne ma bikin naki? Ko da shike ance kina gama Wannan jarabawar da sati ko? Saura mako nawa yanzu kenan?' Azrah ta sauke idon ta kasa ta ce

"A'a ina ga yanzu ba zai yiwu ba" Mama ta zaro ido irin with much concern ta ce

"Ban gane ba? Wani abu ya faru ne? Ko kuma canza ra'ayinki kika yi?" Azrah tayi shiru dan bata san me zata ce mata ba dan basu saba magana da Mama cikin lumana ba balle har su ɗauki more than a minute suna magana, Mama ta ce

"Kinyi shiru Azrah"

"A'a Inaga ya fasa ne, kuma Nima na fasa shiyasa" Azrah ta bata amsan a takaice, Mama tayi wani murmushi tana ta bin Bappah ya gaya mata yaki gashi yanzu cikin ruwan sanyi ta samu amsar tambayarta, wani murmushin ta sake yi tunawa da shawarar data bawa Matan honorable wanda yanzu ta fara tunanin sune suka bi, daga haka ba tare data sake ce mata komai ba ta wuce ɗakin ta murna fal ranta sai yanzu taji watse

A kwana a tashi a sarar mai rai.. har ta gama rubuta exams ɗinta successful, sanan an saka graduation date wanda yanzu gobe za'a yi....

Ana gobe graduation ɗinsu gida ya dauki salo na dabam, duk yadda Umma da Zahra suka so ta ɗanyi wani abu ki tayi amma daga karshe haka Zahra ta haɗa mata wasu abu ba tare data bari Azrahn ta sani ba, Umma ma gani take atleast ta ɗanyi wani abu tunda abu ne na once in a lifetime, Sannan kuma tana so taga kullum tana cikin walwala ne

Da daddare suna zaune kana ganin Azrah kasan tana cikin farin ciki, Zahra ta ce

"Umma dan Allah ki je tare da mu gobe!" Umma ta mata wani kallo ta ce "Yau naga ikon Allah" ɗaukan wani kayan Umma tayi daga cikin kayanta mai kyau tana warwarewa ta ce

"Umma sai fah kinje Kinga yanzu ma zan saka miki kayan ki a kabbasa tare dana Yaya" Umma ta ce

"Toh Uwata Zahra'u" Azrah dai murmushi tayi tana kallon draman Umma da Zahra

Zahra ta gyaɗa kai ta ce "Yauwa koke fah Umma, ai hakan yafi"

Azrah ta fito da dukkan kayan da Anty Suhaila ta bata ta ce

"Zahra wannan yayi ko?" Zahra ta mata wani kallo ta ce

"Ke kike sa a raina ki, me na ɗaukan wannan, sai kinje an kira ki cikin taro aji kunya" ta fizge wannan kayan ta ajiye a gefe wani haɗeɗɗen lace daga kayan da Aunty Suhaila ta ɗauka tana warwarewa ta ce
"Wannan ya fi" Azrah ta dinga kallonta ganin ɗan gyallen sa karami ne ta ce

"Ke Zahra veil ɗin kayan ɗan karami ne sosai" Zahra ta ce

"And so?" Umma tayi murmushi tana kallon yaran nata
Episode 19: Tears of Joy and pride


Yau tunda asuba Azrah ta farka daga bacci and it didn't feel like an ordinary day, today was more than just a day it felt like a milestone, sbd wannan shine take gani a matsayin nasararta na farko, Ranan gama sakandari, lumshe idonta tayi, a moment she had been anticipating for what felt like forever.

Cike da godiya ga Allah she whispered the morning Du'a 'Alhamdu lillahi-ladhi ahyana ba'da ma amatana wa ilaihi-nnushur' buɗe ido ta tayi bata san sanda murmushi yayi escape daga fuskanta ba as she felt a sense of peace wash over her, sake murmushi ma kanta tayi feeling a mix of excitement and nervousness about the day ahead.

Bayan gari ya gama waye wa har Maman Azizah ta iso tare da 'ƴarta Baby, duk suna zaune ɗakin Umma, Zahra ce ta fito cikin wani sihirtaccen kyau sai zuba kanshi take ba zaka taɓa cewa a wannan arean take ba dan bata yi kama da su ba saboda yadda suke behaving da tsantsan ilimi

Azrah kuma an mata wani irin make-up na nutsuwa, wanda ya fito da kyawunta kamar tauraruwa a sararin dare yadda take haskawa, tana sanye da riga da skirt na lace mai ɗinkin zamani da touch na India embroidery, gashinta a nade cikin kwalliya, fuskarta a cike da annuri da kunya, Zahra ta tsaya tana kallonta ta ce

"Ya SubhanAllah.... My very own Azrah idan nace kina kama da ƴan Bollywood! don't say No, pls"
Kowa dariya yayi Mama Aziza ta ce

"Wannan kenan, ai dole Honourable ya ƙellara ido yace shikan ya kyasa dan wa zaiga Azrah ya hakura da ita idan ba sai dai babu kuɗi garesa"

Duk suka fito zasu filin taro, hatta Umma ta kasa ɗaga ido akan Azrah sai taga yau Azrahn ta mata kama sak da mahaifiyarta nan da nan taji hawaye ya taro mata da sauri tayi saurin riƙewa to be sure kar ya gangaro balle ta ɓata wa Azrah rananta...

Mama suka kalla tana kan ɗaura abinci, Umma bata yi mamakin rashin ganin Maman Asabe da bata yi ba, Umma ta ce

"Maman Abdul barkan mu da safiya" Mama ta ɗaga kai ta mata wani matsiyacin kallo, Maman Azizah ce ta yanke ma Mama tunanin da ta fara a rai ta ce

"Mun tashi lafiya?" Mama ta taɓe baki ta ce

"Klau, wato ke da kike can nesa har an sanar da ke amma mu da ake gani zamu ma yarinya baƙin ciki ko kuma musa a fasa taron ai gashi muna gida ɗaya ko sani bamu yi ba" Umma ta ce

"Dan Allah kiyi hakuri, wallahi Nima ban ɗauka zani ba sai Jiya da daddare yara suka sakoni gaba akan lalle sai naje shiyasa" Mama tayi wani humming irin cike da takaici Umma ta ce

"Kuma munyi magana da Bappahn su ai yace ya sanar da ke, maganar gaskiya kuma harga Allah kamata yayi na faɗa miki da kai na amma na mance" Zahra ta tamke fuska tana kallon Umma ganin banda ɓata musu lokaci babu abin da Mama ke yi yasa ta ce

"Umma bari mu fara gaba kar Yaya ta makkara" wani kallon tsana Mama ta bi Zahra da Azrah da shi, Mama Azizah ma data ga ba amfanin mata baya Ni ta ce

"Toh mu mun tafi" sai kuma ta maida kallon ta ga Umma ta ce

"Mu je kar yarinya ta makkara" daga haka suka nufi kofa Mama ta bi su da dogon tsaki....

A babban hall da za'a yi taron, hall ɗin ta cika da jama'a Iyaye, malamai, manyan baki da kuma 'yan jarida, Azrah tana zaune a kujerar gaba tare da wasu colleagues ɗinta, zuciyarta a nutse amma bakinta bai bar ambaton Allah ba dan haka kawai take jin wani faɗuwar gaba

Aka cigaba da gudanar da taron cikin aminci da kwanciyar hankali tare da girmama duk wani baki da yake wajan, bayan 'ƴan ɗanyi wasu daga cikin programs ɗin aka fara bada gifts sannan commissioner da kansa ya fito yayi bayanin akan akwai wasu students guda biyu da gomnati ta basu scholarship zuwa India wanda yana rokon iyaye idan har 'ya'yan su ne karsu hana su fita dan duk kaf garin Katsina mutane biyu ne aka ɗauka, yana gama jawabi aka fara kiran suna....

Kawai aka kira sunanta a matsayin Best Graduating Student 2025, kuma Honourable da kansa ne ya tsaya akan hakan har sunanta ya shiga scholarship list, Scholarship ɗin kuma zuwa wata shahararriyar jami'a ce a kasar India wanda dai sai kana da ƙafa ƙake samu

Zahra ta miƙe tsimɓil tana zara ido sai kuma tayi wani ihu wanda tayi calling attention ɗin mutane, ta rungume Umma tana ihun cewa "Umma Yaya aka kira... Wallahi ita aka kira fah Umma" har sai da Umma ta nutsar da Zahra kafin ta nutsu

Azrah ta miƙe daga kan kujerar da take zaune hawaye ya cika idon ta dan she can't believe, she's still processing ita ɗince ce or not?" A hankali ta soma takawa har ta isa wajan

Yayin da take karɓar certificate da kyautar scholarship masu hotuna suka yi caaa akanta kowa yana faman ɗaukanta ga manyan bloggers ma duk suna fama tanada bayanan su

wani dan jarida ya karasa wajan da Azrah take ya ce

"Miss Azrah, how does it feel to be awarded the best student and chosen for international scholarship?"

Azrah ta gyara tsayuwarta cikin natsuwa ta ce

"It feels like hard work finally paid off, I'm grateful to Allah, my mother, and everyone who believed in me even when it wasn't easy"

Tafawa ta kaure a hall ɗin kowa yana kallon ta cike da sha'awa Sai kuma ya ce

"A special appreciation goes to her mother a woman of strength and humility"

Aka nema mahaifiyarta data fito, haka Umma ta fito ta haye kan stage, an bata kyauta da girmamawa a madadin iyaye mata na makarantar, Kamar ba ita ba, ta tsaya tana murmushi da hawaye a idonta try hard not to cry abu guda daya faɗo mata rai yasa ta tsunkuyar da kai kasa abubuwa suna dawo mata kai fresh nan da nan taji zuciyarta ya karye atimes ji take kamar ta gudu, dakyar ta ɗaga kai tana faking murmushi ta soma magana cike da ilimin sannan da nutsuwa

"Assalamu alaikum everyone, I'm Bitti, Azrah's proud mother, Alhamdulillah, today I'm overwhelmed with joy. As a parent, I want to advise everyone to be a guiding light to their children. Be their first teacher, and prioritize their education. With Allah's blessings, I'm confident they'll excel. I'm thrilled to see Azrah's hard work pay off, and I'm grateful for the scholarship to India. Thank you, and may Allah bless all our children"

Duk wajan kallon Umma ake da mugun mamaki, barin ma wanda suka santa dan basu san haka take da ilimi ba, wajan aka hau tafa mata cike da sha'awa, miƙa mic ɗin tayi sannan ta sauka, kiran Azrah da Zahra aka yi suka tsaya aka musu hoto sannan suka koma wajan zaman su, Maman Azizah ta ce

"Ma Shaa Allah Maman Azrah wlhi ki gode Allah, dan ya miki komai, and also kin sake ɗaga darajarki da yaranki wajan mutanen da suke muku kallon talauci yau kinyi proving ɗinsu wrong cewa babu ruwan talauci da jajircewa wajan neman ilimi"

Umma tayi murmushi ta ce "Alhamdulillah!"

Baby ta tashi ta nufi wajan da Azrah take da murmushi ɗauke a fuskarta

Honourable na daga cikin manyan baki da aka gayyata dan taron, yana zaune daga gefe yana kallon duk abin da ke faruwa, duk da yadda yake jin tsantsan tsanarta a zuciyarsa amma hakan bai sa ya fasa taimaka mata a bayanta ba

Principal kam bai tashi zama spaced out irin na wannan moment ɗinba, bai tashi sanin Azarh nada wanda suka tsaya mata irin na yau ba duk da yasan she deserves it Amma sai masu kafa ake bawa, ranan bai yi mamaki ganin an biya mata wancan kuɗin ba kamar yadda yaga sunanta ne ya fito.

Yayin da ceremony ta kare, kowa yana ta jin Azrah da mahaifiyarta cos ba kaɗan ba suka bama mutane sha'awa fiye da kima bs, lokacin kuwa har hotonta ya fara yawo a kafafen sada zumunta, tare da taken
"The girl from the ghetto now heading to India!"

Azrah sake baki tayi tana kallon Zahra da Baby da suka fara raba takeaway wa colleagues ɗin Azrah duk da ba wani friends gareta ba,Azrah ta ce

"Ina kuka samu wannan?" Zahra ta ce "You think zamu kyale ki haka ne kawai? Just imagine fah, your grad? You must be joking" Azrah ta rungume ƴar uwarta tana jin sonta har ranta

Azrah ta wuce office ɗin principal taje karɓan envelope ɗin da aka tanada dukkanin bayanan dake magana game da scholarship ɗinta and some awards certificate, tana cikin tafiya taji murya yarinya

"Hey girl" Azrah ta juya tana kallon yarinyar da akalla zata bata shekara 5, da murmushi ta ce

"Hey! Good afternoon" mayar mata da murmushin tayi ba tare data amsa ba ta ce

"Congratulations Azrah!" ta amsa da "Thank you" har zata tafi ta ce

"Please Amma are you Nigerian?" Azrah ta gƴaɗa mata kai, ta ce

"Ayyah thought ba ƴar nan kasan bane, ganin how beauty you are, ga kuma sunan ki da is rare" murmushi kawai tayi daga haka ta wuce zuwa office ɗin...

Bayan ta fito ta samu already su Umma har sunyi gaba, tana tafiya a hankali kanta a kasa bata son yadda ake ta kallonta yasa taki yarda ta kalli mutane, ji tayi an rungumeta ta baya ɗan juyawa tayu taga Fatima ce, ta sakar mata murmushi Fatima dake faman ihu tana taya ta murna ta ce

"God! Azrah ina nasan abinda ke faruwa? Ai ina gida ina kwance ina jin labari nace banga ta zama ba, Kai congratulations" murmushi tayi ta ce

"Thank you, 2days ban ganki ba da safe ma ina ta raba ido still ban ganki ba" Fatima ta harareta ta ce

"Dama ke kina damuwa da mutane ne Azrah? Ai saboda rashin kirkin ki yasa na gaji da zuwa gidan ku, tun last papern mu nake ce miki bana jin dadi baki ko leƙo Ni ba, toh ranan ina komawa gida akayi admitting ɗina" Azrah ta ɗan buɗe ido sai kuma ta ce

"I'm sorry please, Allah baki lafiya my friend" daga haka suka fara jerawa, Fatima sai faman maganar wannan scholarship ɗin take yi har Azrah ta gaji da jin maganar, duk kuma inda zasu wuce da wanda ta sani da wanda bata sani ba da manya da kananan hatta malamansu sai congratulations suke mata, a haka har ta tafi gida..

Direct ɗakin Umma ta shiga ta same Umma da wasu few neighbors ɗin su sun shigo taya su murna, Azrah ta zauna tana gaishe su, duk suka amsa mata, ɗaya daga cikin matan ne Matar ta ɗan manyanta ta ce

"Azrah wannan kaɗan ne daga lamarin Ubangiji, sannan Allah ya dube zuciyar ki ke da mahaifiyar ki yadda kika kama kanki kuka tsare mutuncinku sannan kuma yadda kika dage da neman na kanki shiyasa Allah ba zai barki ba, ina so nace miki ki cigaba da wannan kyawawan ɗabi'un naki zaki sha mamakin inda zai kai ki" Azrah ta gƴaɗa ma Matar kai ta ce

"In shaa Allah, Nagode" daga haka ta miƙe zuwa ɗakin su tana shiga Zahra ta rungume ta tana sake wani ihun ta ce

"Ohh Yaya walhi kin biya, God! Just imagine, ai jikina ya bani ne shiyasa na dage Umma sai taje and Umma too did well" Azrah ta ture ta daga jikinta ta ce

"Zahra kadani kasa zakiyi?" Zahra ta ce

"Ba zaki gane bane duk cikin murna ne aswrr, chap waya ga Aunt Azrah a India shikenan Kema sai a ɗauka daga can kike fa" Azrah bata san sanda tayi wani dariya ba ta ce

"Sai kuma su ɗauka Ni ƴar can ne saboda ai ina kama da su?" Zahra bata kulata ba ta zauna ta fara buɗe envelope ɗin tana kallo cike da farin ciki wa ƴar uwarta cos she deserves happiness and more.

Da yamma Umma na zaune da 'ya'yanta baya duk bakin sun tafi, suka share gidan suna cin abincin da Maman Asabe ta kawo musu, jin muryar Bappah suka yi

Tun daga bakin ƙofar gidan, ana jin muryar Bappah yana kiranta

"Azrah! Azrah!"

Azrah dake zaune tare da su Umma da sauri ta miƙe tana amsawa "Na'am Bappah!"

Fuskarta cike da annuri, ta fito ta tsaya bakin kofar ɗakin nasu tana kallon Bappah daya shigo shima fuskarsa cike da annuri

Bappah yana kallonta da murmushi yana jin zuciyarsa cike da alfahari da sonta ya ce

"Alhamdulillah daughter! Duk da i always failed you as a father amma baki taɓa jin ki karaya ba, Allah ya cika miki burinki ya ɗaukaka ki duniya da lahira, Azrah kin kawo wa wannan gidan daraja, Kin kawo min kwanciyar hankali Azrah" ya kare maganar yana ɗora hannunsa a kanta

Azrah ta sunkuyar da kai tana murmushi, zuciyarta cike da farin ciki ta ce

"Bappah you never failed us, bari na kawo maka abubuwan da aka bani"

Ta juya da sauri ta shige cikin ɗakin, Bappah ya bita da kallon tausayi, bayan ƴan mintuna ta fito da wasu envelope da kyaututtuka, award certificate da wasu gifts ne, sai takardu na scholarship da kuma wani dan envelope na kuɗi, ta durƙusa ta mikawa Bappah

"Ga waɗanda aka bani Bappah, ka duba su"

Bappah ya karɓa yana dubawa fuskarsa ta gagara ɓoye farin cikin da yake ciki, ya jinjina kai, sannan ya ce

"Wannan shine abinda ake kira tarbiyya, halacci, da kuma jajircewa Allah ya ƙara miki basira Azrah, Kin fi kowacce mace daraja a idona, Allah baki miji na gari ke da ƴar uwar ki"

Zuciyar Azrah ta cika da taushin ƙauna da farin cikin, rana ce da ba zata manta da ita ba ganin yadda Bappahnta ke mata magana.

Last Free page

This book costs 500. Make the payment to Hauwa Jibrin, Wema Bank account 0421255553, and send proof of payment to 08110615256.
Episode 20: Bitter Hearts, Brighter Futures

A wani babban gida wanda ya gaji da kyau na zamani, babban parlour ne da aka kawata da kayan alatu ga kamshi na Turkish perfume, wani saurayi yana zaune bisa sofa mai laushin gaske mai launin ash, lokaci zuwa lokaci yana shan fruit salad na gabansa ga kuma wayan a hannunsa yana dan dannawa, yana cikin Instagram ne yana kallo, ya mayar da hankali gaba ɗaya akan abinda yake yi, gajiya da kallon hotunan celebrities da yadda ake fake lifestyle yasa zai kashe datan ya sauka

Cikin bazata sai wani hoto ya bayyana a feed dinsa hoton Azrah kenan a wurin graduation ceremony, tana rike da certificate, tare da murmushinta mai kyau da nutsuwa da komai nata ya bayyana
Saurayin ya dan saki fork din hannunsa, yana fadin, 
"Wait... who is this?" Yayi ɗan shiru yana kallon waje guda kamar yana kokarin tuno inda ya santa

Yayi scrolling kadan, ya ga wani shahararren blogger ya wallafa hotonta, caption din kuwa
"From local to global best student of the year, Azrah, bags scholarship to India!" Nan da nan kuma  komai yayi masa flashing a kwakwalwarsa, ɗan taɓe baki yayi

Sake scrolling down yayi sai kuma wani blogger ma ya saka nata hoton da taken
"Meet Azrah, the brilliant beauty who's turning heads!"

Nan take zuciyarsa ta buga, idonsa ya rufe, yana jin wani abu ya dirar masa a zuciyarsa
"No way! Wannan yarinyar gaskiya ce?!"

Yayi screenshot da hanzari har hannunsa na ɓari, ya tura wa abokinsa a DM da Captain

"Dude… kaga abinda nake gani kuwa?! Kuma ka gane ta? Hotonta yana ko'ina! Check bloggers post" Kamar mai nazari sai kuma kawai ya tura, nan take abokinsa ya shiga typing dan already yana Whatsapp ɗin ne

"I told you someone like her can’t be hidden, your heart was right, destiny will find its path" ya tura tare da emojin dariya

Ba tare da yayi replying ɗinsa ba bayan ya karanta kawai ya kashe datan, cos this is unbelievable

A can gida kuwa, Zahra na wanke wanke amma gaba ɗaya hankalinta akan wayan Azrah dake hannunta ne banda scrolling babu abinda take can ta saka wani ihuuu wanda yasa Umma da Azrah fitowa babu shiri dan su tunanin su wani abin ne ya faru, miƙewa tayi ta fara dariya ta ce
 
"Sister Azrah! Blog din @ArewaGist sun fitar da video dinki yanzu nan! Zo ki gani?" Wani kallo Azrah ta mata daga haka ta koma ciki, Umma ta ce

"Bani wayan" ta maraice wa Umma ta ce

"Kai Umma, kiyi hakuri toh ba zan sake ihu ba" Umma ta harareta ta ce

"Idan banda iskanci sai ki wani tsala ihuu kamar waccan wani abunne ya faru da ke? Toh wallahi ki shiga hankalin ki Zahra, kuma make sure ki gama wannan wanke wanke yanzu" daga haka Umma ta wuce ciki tana mita, Umma na komawa ciki Zahra ta kara ihuu

"Kai Yaya Azrah, haba my Aunt Dan Allah ki zo ki gani" Azrah ta miƙe Umma ta ce

"Dalla kyale Zahra da shirmenta" Azrah ta yi murmushi ta ce

"A'a Amma bari naje kawai, dan Ni take wannan abun" daga haka Azrah ta fita zuwa wajan Zahra, Zahra ganin Azrah yasa ta fara dariya tana gaya wa Azrah yadda blog ɗin ArewaGist ya fitar da video nata da hotuna masu kyau harda Captions ɗin da ya saka, sai ga Mama da yaranta sun fito daga ɗakinsu kamar dai sun fita shan iska, sai suka tsaya akan baranda suna habaice habaice duk da sunan sun fito shan iska ne, Zahra kuma ganin haka yasa ta ɗaga murya ta ce

"Kai Aunty Azrah na, chap ai yau kin bada mutane, ace a zakulo ki cikin ɗaliban da suka fi kowa? Kai Allah mun gode maka"

Mama ta zare ido tana kallon Zahra tace

"Ai dole ta ci! Mai uwa a bakin murhu baya kwana da yunwa, dama ai soyayya da Honourable taya zata faɗi?, ko da ake girmama ta a banza ne?, yanzu kuma wai za a ce ta fi kowa ta cancanta da ɗaliban data fi kowa a jihar? Chap!"

Siyama ta miƙe tsaye, tana cije leɓenta da kallon tsana ta ce

"Ni kam duk muna kallon irin su a gari, dama dai Samarika irin su ke ɗaukar nawinsu zuwa waje da sunan scholarship, ashe su kuma suna fitar da sune dan wata manufa na su"

Habibah ta kwashe da dariya har tana faɗi ƙasa Mama ta ce "Ke wallahi ki bar Siyama duk ta san tsiyan irin waɗannan mutane nan"

Umma ta buɗe labulen ɗakin yadda Mama ba zasu ganta ba ta ɗaura ɗan yatsarta a baki da alama kada tayi magana, idanunta suka cika da hawaye amma tayi shiru tana kallon wani direction na daban

Zahra kuwa ta tsaya cak da wanke wanke, sinbil ta miƙe tana kallon Siyama da Habibah tace da karfi cikin haushi

"Eh tabbas Honourable ne ya bata ilimin dake ai tun tana karama take tare da shi, shi kuma ya bata wannan damar, wata dama da ta kai ta inda baku taba zato ba balle tsammani, sannan kuma ya ɗauki nawinta, kuma yanzu ma zai fitar da ita, idan abun haka kawai ake samu kuma ku samu mana? Idan fisari banza ce kaza ma tayi mu gani, wanda kullum ake ganin sune na gari naga har yanzu sun kasa auren balle mashinshini, waccan ake zagi kuma naga har an kawo goro" Zahra ta kwace hannunta ana Azrah dake ta faman cewa tayi shiru

Mama da Yaranta kuwa kamar wadda aka zubawa ruwan sanyi haka suka gagara magana suna kallon Zahra da mamaki

Mama ta sake wata tsimfida ta ce

"Uban waye ke magana? Yarinya ƴar karama sai shegen tsauri da raina na gaba da ita? Allah ya isa tsakanina da wannan yarinya shegiya kawai, wallahi bata da tarbiya!"

Zahra tabi Azrah da kallo ganin harta karasa ɗakin Umma itama bata juyo ba kai tsaye ta kama hanyar dakin Umma, tana shiga, ta samu Azrah harta fara hawaye a idonta, Umma ta dafa su duka tana fadin

"Wannan shine gwagwarmaya kafin daukaka, kuma ba zaka taɓa satisfying mutane ba shiyasa yake da kyau kayi abinda Allah ya hallarta mana ka bar wanda ya haramta, ka kuma dinga hakuri, dan muddun kace pleasing mutane zaka yi you're done wlh, kuyi hakuri komai mai wucewa ne"

Azrah ta share hawayenta tana fadin

"Wallahi Umma bana jin zafin maganarsu, na fi jin dadi da Allah ya bani wannan daman sbd In Shaa Allah karatu zanyi har wata rana Allah yasa na zama successful dan Mama ta gane tunaninta ba haka bane akai na, na san wannan shine farkon sabuwar rayuwata" Zahra ta fara kaɗa kafa Umma ta mata wani kallo ta ce

"Ke kuma Zahra bakin ki baya shiru ko? Dole sai kin tanka ne? Kullum ayi ta miki magana amma ina kwatakwata baki ma san me ake faɗi miki ba"

Suna cikin haka, sai wayar Azrah tayi kara Zahra ta mika ma Azrah wayanta, karɓa tayi taga Sakon daga makaranta ne 'invitation letter' din tafiyarta zuwa India ya iso… da kuma flight itinerary, Zahra ta miƙa ma Umma, Umma ta karɓa tana kallo Zahra ta fara rawa harta ma manta da maganganun Mama

Azrah ta ce "amma Umma har sannan fah bamu yi magana akan zani ko A'a ba?" Umma ta ce

"A'a kuma kamar yaya kenan? Tafiya kam ai zaki mana amma bari na jira har sanda Bappahn ku zai dawo dole yau muyi magana ma" Azrah ta gƴaɗa mata kai

Umma ta ce "sannan kuma karki sake kula Mama da Yaranta please, just be you as usual, Dan yanzu kar ayi wani abu da za'a tunzura su taje ta zuga Bappahn ku, dan kunfi kowa sanin halinta ai"

Zahra tayi kasa kasa da dariyar Mugunta ta ce

"Gaskiya sai Mama tasa wannan abun ya koma Tarihi kuma dan murus zamu ji Bappah yace babu inda zaki" sai kuma ta sake wani dariyan ta ce

"Wallahi da Bappah yasan cewa na cika Fadimatuz-Zahra dan saf zan kai karansa gidan Dada"

Umma ta ɓata rai tana kallon Zahra tace

"Zahra Allah nuna min ranan da zaki shiryu" dariya tayi ta ce

"Har sanda kishiyar ki ta daina Wannan halin nata" dan har sannan suna iya jiyo masifar Mama akan Zahra ta mata rashin kunya su Siyama kuma suna sake zugata, Azrah bata san sanda tayi dariya ba...

Bayan Isha'i Azrah ta kaima Bappahnta abinci yana zaune kofar ɗakinsa yana shan iska ta zauna kusa da shi tana masa maganar scholarship ɗin da kuma message da makarantar su suka turo mata, ya jinjina kai can ya ce

"Ina dai kina so tafiyan ko?" Azrah ta gƴaɗa masa kai ta ce

"Cos Bappah kasan idan ban tafi ba, anan ya zanyi da karatu na? Kuma Bappah gaskiya ina da buri sosai akan karatu dan Allah ku barni na tafi" Bappah ya ce

"In shaa Allah zaki je Azrah, Allah ya wuce mana gaba" ta amsa da Amin, ya ce

"Allah ya yi miki Albarka, ki cigaba da waɗannan halin naki zaki sha mamakin yadda rayuwar ki zata yi kyau fiye da tunani"

Kafin Azrah ta samu damar amsawa sai ga Mama ta fito daga ɗakin ta da sauri, ranta a ɓace, tana rike da ɗan kwalli a hannu kamar wacce taji wani abu mugun abu ta fito ba shiri

"Ikon Allah! Eh ba shakka, ai dama an gama da kai tun ba yau ba, Nawa ƴaran kuma Allah ya tsine musu duk inda suke kenan ko? To ka sani ko ba a saka musu albarka ba, ni na saka musu! Na yafe musu gaba ɗaya!”

Muryarta cike da ƙiyayya da hassada sannan ga haushin rayuwar da bata da tasiri akanta

Sai dai babu wanda ya tanka mata, Azrah ta tsaya cak tana kallonta sai kuma ta ɗauke kai Bappah kuma ya juyo gare ta yana cewa

"Azrah koma ciki, Allah ya bawa Zahra ma nasara, tunda kun yarda da cewa zakuyi karatu, Allah zai saka muku da mafificin alkhairi sannan kuma a sannu zaku sha madarar karatun da kuka yi"

Daga haka ya kwashe abincin gabansa juya ba tare da ya kalli Mama ba yayi ɗakinsa

Mama ta saki dogon tsaki irin wanda ke nuna takaici da rashin gamsuwa, tana harararsu ta ce

"Tashi dai, tashi!" kamar tana korar wata dabba, sannan ta juya ta wuce cikin ɗakinta ba tare da sake kallon direction ɗin Azrah ba, itama Azrahn ɗakin Umma ta nufa amma cikin zuciyarta babu mamakin hali irin na Mama, amma akwai ciwon da yafi dukan da zagi, Rashin son nasarar ƴar mijinki, ga kuma tayi ta abu cike da Yaranta da kuma kankanta..

Hajiya Maryam tana girgiza ƙafa ta gagara cewa komai, Hajiya Rabi ce ta katse mata tunaninta ta ce

"Toh amma ban gane ba? Idan har baya zuwa wajenta kuma kamar yadda yake cewa he has nothing to do with her me yasa zai dage akan sai ta fita waje? This shows that yana sense ɗinsa ko kuma asirin ne ya karya?"

Hajiya Maryam tayi wani humming ta ce

"Ba haka bane, i believe the Malam, saboda ina duba wayansa kusan kullum amma naga babu wani communication tsakaninsa da yarinyar, amma ina so nasan ya hakan ya faru harda kashe kuɗin wajan ganin an bata bayan banda power da yayi using," Hajiya Rabi ta ɗaura

"Ina ga fah ko dai itace ta cigaba da binsa or asirin ya karye" Hajiya Maryam tayi wani murmushi ta ce

"Toh dole zamu koma wa mutumin nan ya dakatar da tafiyar yarinyar, ba inda zata shegiya ƴar gidan talakawa" Hajiya Rabi ta ce

"Ni Kuma a nawa tunanin ina better tayi nisa da shi yadda zai daɗe bai ganta ba har ya manta da ita Kinga muma hankalin mu kwance than a dakile tafiyar nata wanda zasu iya ganin juna kenan at anytime" shiru tayi tana nazarin maganar nata sai kuma ta ce

"A nan ma kina da gaskiya amma Ni dai ko kaɗan ban so ace zata fita ba, shegiya naga sai wani trending ma take yanzu jin kanta take ita wata abu ce" sai kuma ta ja dogon tsaki daga haka ta miƙe zuwa restroom ba tare data kula Hajiya Rabi dake zaune ba, dan ko Hajiya Rabi da take kulawa don ya zama mata dole ne amma she will definitely find a way out a dai cigaba da tafiya, Hajiya Rabi ta bita da kallo this is what she hate from her, sai ana magana ta wani bar wajan without any words, itama tsaki ta ja daga haka ta mike zuwa waje ...
Episode 21: A Girl Torn Between Dreams and Obedience

Washe gari da safe bayan Bappah ya dawo daga masallaci wajajen karfe 8am lokacin Azrah ta tafi makarantarsu kamar yadda aka kirata Zahra kuma ta tafi nata makarantar, Umma najin shigowan sa ta mike dama shi take jira tuntuni, tana shirin fita sai ga shi da kansa ya shigo, komawa baya tayi ta zauna bayan sun gaisa ta ce

"Malam har sannan bamuyi magana game da maganar scholarship ɗin Azrah ba fah"

Bappah ya juyo yana kallon Umma with full attention ya ce

"Wallahi Bitti... ban jin zan iya barin ta tayi wannan tafiyar, Wata ƙasa ba ina laifin anan kasar ne sai ace ko da wani state ɗin ne daban, dan ba kowa ke zuwa India ya dawo lafiya ba, Ina tsoron rayuwarta, ina kuma tsoron abinda zai same mu idan muka bari ta fita…"

Umma ta gagara magana dan bata kawo haka daga Bappah ba ko kaɗan, bai nuna baya so ko wani abu ba, infact da ta tambayi Azrah ya suka yi cewa tayi Bappah alfahari yake da ita yanzu Kuma sai ya mata wani maganar daban, har sannan ta gagara magana Bappah sai kallonta yake yi, ta ɗauke kanta daga side ɗin Bappah

Bappah ya cigaba "Ba wai ina son hanata karatu bane, kin san ni mai son karatun ‘ya’ya ne. Amma ba zan iya kwana lafiya ba idan na san ɗiyata a wata ƙasa ita kaɗai wai da sunan karatu, think about this pls, how do you expect me hankali zai kwanta pls"

Umma ta ɗago kai a hankali duk da nutsuwar dake tattare da ita amma kana iya hango tsantsan ɓacin ranta, nan take fuskanta ya canza, cike da nutsuwarta

"Malam" ta ce da muryarta da ke cike da nutsuwa

"Ni ba zan ce ta tafi ba, kuma ba zan ce ta zauna ba, Amma Allah da ya saka Azrah a wannan matsayi, ba zai saka mata sharri ba saboda kullum cikin addu'a nake ma 'ya'yana, amma a yanzu addu'ata ɗaya ce Allah Ya zaɓar mata mafi alkhairi, Idan tafiya ce alkhairi ne Allah Ya tabbatar mata sannan ya kaita lafiya ya kuma tsare mana ita a can ɗin, Idan kuma babu alkhairi, Allah Ya canza mata da wani abu mafi tsada wanda ba zata ma damu da rashin tafiyar nata ba"

Bappah yayi wani shiru wanda Umma amsar sa kawai take jira, amma shiru kake ji sai karar agogon bango kawai ke kara cikin ɗaki

A cikin zuciyar Bappah kuwa Umma ta mugun ɗaure sa, ko kaɗan bai kawo haka daga gareta ba, wannan yasa ya zama speechless dan ko kaɗan bayan jin zai barta ta tafi kuma, amma yasan idan har ya hanata ya zata ji duba da yadda Allah ya ɗaukakata, har ya kai ga duniya ta san da ita, bai iya yanke hukunci ba kawai yayi shiru, can ya ce

"Zamu jira ta dawo daga makarantar Sai muyi magana da ita kanta muji ta bakinta"

Umma ta gyada kai "Allah ya tabbatar mana mafi alkhairi kawai".

Bayan fitan Bappah duk da yadda taji kanta ya fara ciwo hakan bai sa ta hakura ba kawai ta fita ta ɗaura lunch ko kallon inda su Mama ke zaune bata yi ba, dan banda gulman 'yan unguwa babu abinda suke yi ita da Siyama, su ɗauko taɗin wancan su gama su ɗauko taɗin wannan, a haka dai harta samu ta gama girkin, tana shiga ɗaki kuma ta kwanta dan lokacin ciwon kan nata ya fara tsananta.

Azrah ta dawo gida da yamma duk agajiye, takardunta a hannunta, cikin wani envelope mai dauke da sunan makarantar da zata tafi a India, Fusarta cike da gajiya da kuma rudanin tunani, amma da zarar ta hango future sai zuciyarta ta ɗan sake, tana jin No matter what karatunta zai amfane su nan gaba

Zahra ce ta buɗe mata ƙofa tana murmushi tun kafin Azrahn ta buɗe, ta shiga ɗakin Umman ta zauna

"Makarantar mu sai labarin ki ake yi Yaya ance ma an buga sunanki a wata mujalla wllhi"  ta kare maganar ciƙe da taya 'yar uwarta murna da kuma farin ciki

Azrah ta yi murmushi cike da sisters love ta ce "Toh Zahra" ta ajiye envelope ɗin ta miƙe zuwa ɗakin su, ɗaukan hijabi tayi ta ɗaura towel sannan ta fita zuwa toilet, ruwa ta wasa sannan ta fito, ko data fito taga Habibah da wata kawarta sai kawai ta ɗauke kai ba tare data sake kallon wajan na su ba, kawar Habibah ta ce

"Hey beautiful! Na zo nan dan nace miki congratulations ne" Azrah ta ɗan tsaya tana kallon ta sai kuma ta ce

"Thank you so much" daga haka ta nufi ɗakin su, Habibah ta haɗa rai ta ce

"Dama uwar abin da ta kawo ki Kenan? Toh tunda kin mata murna ai sai ki tashi ki tafi" kawar nata ta miƙe ta ce

"Alright, sai anjima" Habibah ta bita da kallo tana jin ranta na ɓaci

Tana shiga ɗakin Umma ta kalli Bappah da Umma zaune, daga kallon Bappah kawai ta gane akwai muhimmiyar magana, nan tayi sensing jin ta dawo yasa Bappahn shigowa tare da Umma, dukawa tayi ta gaishe su, Umma ta ce

"Shiga ki saka kaya sai ki fito" ta miƙe zuwa ɗakin su bata wani daɗe ba sai gata ta fito

"Zauna mana Azrah" Bappah ya fada da wata muryar da take tsakanin tausayawa da kuma hope

Ta zauna a hankali, ta ajiye envelope ɗin hannunta a gefe wanda ta fito da shi

"Kin san muna alfahari da ke, Azrah, wanda hakan ne yasa Allah yasa duniya ma ta san dake, Amma tafiya waje da sunan karatu ya zakiyi ki tafi wata duniyar da bamu wajan Azarh think about it, Kuma ke mace ce, ƙaramar yarinya" Bappah ya fara mata maganar da yasan zai iya winning heart ɗinta yana kokarin ɗaukar hanyar lura fiye da hankaka

Azrah ta lumshe ido taji hope ɗinta ya fara karyewa, sai dai bata tanka ba tayi shiru har sannan

"Bani da tabbacin cewa wannan tafiya zai zama alkhairi, Amma ni uba ne dole na hango abin da ba zaki iya hangowa ba, Ina son ki fiye da kowa Kuma ina tsoron rasa ki"

Umma ta kalli Azrah, ba tare da ta katse maganar ba amma zuwa yanzu ta fara jin ranta ya fara mugun ɓaci, just imagine kamar yasan wani nawin Azrah balle har yana ce hakan

Bayan shiru mai tsayi a ɗakin Azrah ta ce

"Bappah na fahimta, Kuma zan yi biyayya idan kun ce kar na tafi. Amma ina jin kamar wannan dama ce da Allah Ya bani, Zan so ku yarda da cewa… ba da kaina zan tafi ba, da addu'arku da yardarku kuma" ta kare maganar ciƙe da tausayi dan daga muryanta zaka fahimci tana son tafiya amma maganar Bappah ne yasa ta fara rasa duk wata hope ɗinta

Umma ta ɗan share hawayen da ya cika idonta, bata son tunawa da komai yanzu balle ya karya mata zuciya, bata kuma son tuno da rayuwar baya balle yasa wannan damuwar ya ɗago mata ciwo

"Azrah me yasa kike son tafiya?" Umma ta tambayeta cike da tausayinta

Azrah ta lumshe ido, muryarta na rawa ta ce

"Domin in cika burina na karatu, domin in yi karatu wata kila Allah ya bani aikin yi ko dan mu fita daga wannan wahalar, Domin in nuna wa duniya cewa mace daga ghetto tana da daraja ba lallai sai masu kuɗi ke karatu kuma su zama successful ba sannan waɗanda suke kyamata su sani Allah kan canza lamari wanda yaso a kuma lokacin da yaso, Domin kuma kuyi alfahari da ni, Kuma… domin na zama Misali wa duk wata mace dake da burin karatu amma kuma ta dinga ganin babu wata mafita dan rashin kuɗi"

Bappah ya sauke ajiyar zuciya a hankali sannan ya ɗaga kai daga kallonta da yake yi, bai ce komai ba amma zuciyarsa na whispering masa maganganunta haka ne

A ƙarshe ya ɗago kai, yace
"Bari mu yi sallar istikhara Azrah, Idan alkhairi ne, Allah Ya tabbatar mana ya kuma sanya ma lamarin mu cikin sauki, Idan babu Alkhairi kuma Allah Ya canza miki da wata mafi Alkhairi"

Azrah ta gyada kai cikin hawaye

"Toh Bappah, Hakan ma yayi"

A hankali Bappah ya miƙe ya nufa kofa jin har an fara kiraye kirayen Magrib, Umma ta ɗaga kai tana kallon Azrah sai kuma tace

"Ta shi ki wuce ciki ko?" Azrah ta miƙe ta ɗauki envelope ɗin data ajiye a gefe, Umma na kallonta ta ce

"Wannan kuma fah Azrah?" Azrah ta miƙa mata ta ce

"Umma shine wanda naje na karɓa, sun ɗauki information ɗina ne sannan kuma wai suna son ganin ku gobe" Umma ta ce

"Toh Allah ya kaimu" Azrah tayi shiru tana kallon Umma, Umma ta ce

"Lafiya ?" Azrah tayi murmushi ta ce

"Toh Umma ai gobe suke buƙatar ku idan kuma zan tafi Kinga dole za'a so ace kunje goben" Umma ta ce

"Calm down, dole zamu je goben idan ya so mukayi addu'a idan babu Alkhairi Shikenan" Azrah ta gƴaɗa ma Umma kai, Umma ta ce

"Muje muyi sallah toh" sai ga Zahra ta fito ranta a mugun ɓace, Azrah ta ce

"Zahra lafiya kuwa?" Zahra ta tsaya tana kallon Umma ta ce

"Yanzu Fisabilillah Umma sai kawai yanzu a wani tsira maganar ba lallai Yaya zata tafi ba? Rai na yayi mugun ɓaci wllhi shiyasa ko fitowa ban yi ba, amma dai i knw one thing for sure ko Bappah ya yarda ko kuma na tafi can gidan Dada naje na gaya mata" Umma ta ce

"Karan Bappahn ki zaki kai kenan?" Zahra ta ce

"Ni bance kara ba Umma amma ya za'a yi da farko bai ce A'a ba sai yanzu kawai ya wani ce A'a idan ma zugasa aka yi toh duk Dada zata yi maganin su" Umma ta girgiza kai ta wuce tsakar gidan danyi alwala kullum addu'a take ma Zahra Allah ya shirya mata ita dan tana ganin kamar yarinta ne, Azrah ma ta bi bayan Umma dan yi alwalan.

Bayan ta idar da sallar Magrib taga wani new contact ya turo mata da message, ta jima zaune tana karanta contents ɗin amma bata gane me ake nufi ba kuma numbern ma bata san nawa bane cos taga it's new digit ne daga karshe kawai ta ajiye wayan ta mike zuwa dakin Umma.

Bappah da ya dawo daga Sallar Isha'i, Habibah dake tsakar gida tana waya kallon Bappah yasa ta wuce dakin Mama da gudu ta na

"Mama ga can Bappahn ya dawo" Mama ta ce

"Ke dalla ya zaki wani shigo da gudu har kin razana Ni" ta turo baki tana kallon Mama ta ce

"Mama toh bake kika ce idan ya dawo mu miki magana ba, da nasani ma banzo faɗa miki ba" Mama ta ce

"Ji Shegiya, daga magana shikenan sai ki wani ce da baki zo ba?" Ta kare maganar tana hararanta, miƙewa tayi daga kan sallayan ta cire hijabin jikinta ta wuce zuwa ɗakin Bappah

Sallama tayi, Bappah dake ciki ya amsa ta shiga ta zauna Fuskarta cike da annuri ta gaishe sa, Bappah ya amsa yana mamakin wannan sabon yanayin na Mama

Ta zauna gefen sa ta ce

"Malam Nikam wani magana naji yana yawo a unguwar nan nace Banga zan iya munafurtan kaba dole na faɗa maka" Bappah ya tsaya kallon ta kamar yana karantar abin da ke zuciyarta can ya ce

"Kuma yana alaka dani kenan? Ta gyara zamanta ta ce

"Sosai mana" Bappah ya zuba mata ido ta ce

"Magana kam sai yawo yake wai ka bada ƴarka ana amfani da ita ana biyan ka, yanzu kuma gashi sun nema ka turata India dan sun koma can da aiki shine suka nema ka turata can gashi zaka tura, wai harda cewa kayan abincin da kwanaki honorable ya kawo toh sunce duk saboda ka basu ƴarka ce" Bappah ya kafeta da kallo baka gane expression ɗinsa shi dai ya zuba mata ido yana kallonta ta ci gaba

"Ni dai duk inda naji haka sai na kare ka, ba wannan Bama gashi sunce tana saka kaya masu tsada, gashi bata kallon kowa da kima, idan har da gaske ba turata zaka yi dan su cigaba da amfani da ita ba toh wani kuɗi gareka da idan Amfanin kuɗin ya tashi? Wai toh idan ta tafi can da wa zata zauna?" Tayi shiru sai kuma ta ɗaura

"Kuma maganar su fah da ayar tambaya sosai a ciki Nima da badan nasan halinka ba da na yarda" Bappah ya miƙe ba tare daya ce uffan ba ya fita ya barta zaune, tayi wani murmushi tana kaɗa kafa

Bappah daya fito yaga Umma na idar da alwala ta ajiye butan hannunta ba tare data Kalle sa ba ta wuce ɗakinta, ya bita rai ɓace zuwa ɗakin, ta ɗauki hijab zata saka ya warfe hijabi, rai ɓace ta juyo tana masa wani kallo, ya ce

"Kinga a dalilin banzan ku ga abinda aka fara zuwa ana faɗa a waje akai na ko?" Umma rai ɓace ta ce

"And so?" With shock written all over him yake kallonta
Episode 22: The Night of Istikhara

Ta gyaɗa masa kai dan tabbatar masa da abinda ta ce sannan ta kwace hijabinta dake hannunsa, yana kallonta ya ce

"Okay! Har kina da guts ɗin mayar min da magana? Toh shikenan na riga da na zantar da magana babu inda yarinya zata je, idan kuma bani da iko da ita sai ki faɗa min, and this shows that da sanin ki ma maganar yake yawo a gari kenan ko?" Daga haka ransa a mugun ɓaci ya juya zai fita Umma tayi saurin shan gabansa ta ce

"Kace a dalilin banza na ko? Shin har kana da bakin magana Malam? Dan kawai Matar ka ta zauna ta tsara maka magana shikenan har ka hau kai ka zauna, toh akan 'yata bata da wani hurumin magana dan Banga dalili ba, Matar da ba sona da 'ya'ya na take yi ba shine zata yi murnan wai fitan Azrah? Wai har kamanta wacce Uwani?" Wani murmushin takaici tayi hawaye yana shirin taruwa a idonta ta ce

"Ina kuɗin Waec ɗin Azarh haka ta hana ka ka bani wai zata juya kuɗin, and at long last haka tace bata san da maganar ba da badan Allah ya haɗa Azrah da nagari ba da kila yanzu Allah kaɗai yasan damuwar da take ciki, Malam a bar maganar gori tun Azrah na karama ita ke ɗaukan nawinta, ta kuma ɗauki nawi na dana 'yar uwarta, rashin lafiya na sai inda karfinta ya kare, yanzu kuma da kake maganar hanata wannan fitar da sunan karatu zaka biya mata ne tayi karatun a nan?" Ta kare maganar tana kallon Bappah daya kasa magana ta ce

"Rayuwar dana yi a baya ba zan so ɗaya daga cikin 'ya'ya na suyi ba, ina da yakinin Ubangiji ba zai bar Azrah idan tayi karatu ya tafi a banza ba, wani nake da shi anan? Ina ɗan karatun da nake da shi nake koyar da 'ya'yana a gida kuma shike ɗauke min tarin damuwar da nake ciki, yanzu Ni ina...." Kasa cigaba tayi kawai ta fashe da kuka mai tsuma zuciya dan tayi kwana biyu bata yi kuka ba akan abinda ke cinta a zuciya, juyawa tayi tana share fuskarta da hijab ɗin hannunta, Bappah kam jikinsa ne yayi wani sanyi wanda ya kasa ɗauke idonsa akanta can har zai juya sai kuma ya dawo inda Umma ke durkushe ya ce

"I'm sorry Bitti, I'm sorry Dan Allah ki daina wannan kukan" shima shiru yayi zuciyarsa tayi mugun rauni, he wish shima zai iya canza wannan ƙaddarar amma ba yanda zai yi, yasan Umma deserves happiness and more, a haka ya samu ya lallaɓata harta samu tayi shiru, yana kallonta cike da tausayi ya ce

"In shaa Allah, anjima sai mu tashi muyi mata sallan dare Allah ya tabbatar mana da Alkhairin sa kamar yadda muka ce sannan gobe zan tashi da azumi na mata addu'a" Umma bata ce masa komai ba harya miƙe ya nufa kofa

"Kayi hakuri idan har kalamai na sun ɓata maka rai" Bappah ya tsinkayi muryan ta, ɗan juyowa yayi ya mata murmushi sannan ya fita

Mama dake jikin kofar tun ɗazu ta ja da baya da sauri fuskanta a tamke yake kamar bata san wani abu murmushi ba, ba tare da Bappah ya kalli direction ɗinta ba ya wuce zuwa ɗakinsa, ta bisa da kallo sannan ta kalli kofar ɗakin Umma sai kuma ta wuce ɗakin ta rai babu daɗi dan ba haka taso ba

Zahra ta fito daga ɗakinsu tana kallon Umma, lokacin guda Umma ta tuna da cewa ashe suna ɗakinsu jikinta ne yayi sanyi ta miƙe ba tare data Kalle Zahra ba ta hau kan darduma ta tada sallah, Zahra ta zauna tana jiran Umma ta idar ta bata ba'asin abin da ya faru

Kamar yadda Bappah yace haka kuwa ya faru karfe 2:15am na dare ya farka ya kuma tada Umma

Azrah tana cikin bacci itama ta farka duk da bata san karfe nawa bane hakan bai hana ta miƙewa ba, gƴara ɗankwalinta tayi sannan ta miƙe zuwa waje tana fita taga alamun anyi alwala nan ta fahimci cewa Umma ce, bayan ta idar ta wuce ɗaki ta fara sallah zuciyarta cike da kwanciyar hankali da ɗan tsoro, amma data tuno da kalaman Bappah da na Umma sai taji kwanciyar hankalin yafi yawa than tsoro a haka ta dinga sallah tana rokon Allah, tayi salati sannan ta fara karatun Qurani wanda ita kanta ba zata iya faɗin raka'a nawa tayi ba, Zahra ta buɗe ido cikin bacci ganin Azrah zaune kan darduma yasa itama ta miƙe tana kallonta ta ce

"Sannu da salla Yaya Azrah… Allah amsa mana"

Azrah ta gyada kai, ta ce
"Amin Zahra"

Daga haka Zahra ta miƙe itama, tsakar gidan ta fita dan ɗauro alwala

A bangaren Umma da Bappah kuwa, Suma suna zaune a ɗaki, duk wa 'ya'yan nasu suke wa addu'a sannan kuma da maganar tafiyar Azrah,Umma ta sauke ajiyar zuciya

"Yarinyar nan dai daga gani tana son tafiya, Allah idan har alkhairi ne make it easy to her"
Bappah ya sauke ajiyar zuciyar shima ya ce "Allah dai ya tabbatar mana da Alkhairin sa"

Can kusa da Asuba Azrah ta kwanta, Mafarki tayi, a mafarkinta sai taga tana tsaye a gaban wata babbar makaranta wanda Kyan makarantar da tsarinsa bana faɗa bane sabar haɗuwa, wata murya mai sanyi ta ce

"Ki shiga, ki karanta abubuwa da dama na burukanki, Ilimi kariya ne"

Ta ɗaga kai ta kalli sama, taga duk saman ya cika da taurari, juyawan da zata yi taji ance mata 'Bismillah'

Da Asuba bayan Umma ta ɗaga su daga bacci, Azrah ta tashi tana jin nutsuwa da kwanciyar hankali kamar ruwan sanyi ya wanke zuciyarta, har sannan murmushi take wanda ya gagara barin fuskanta addu'an tashi daga bacci tayi sannan ta miƙe

Tana fitowa daga ɗaki, ta sami Umma na zaune akan dadduman tana lazimi,ta karasa ta rungume ta

"Umma… Allah Ya nuna min alkhairi a mafarki na, Ni dai wallahi nayi mafarkin naga kai na a wani makarantar" ta kare maganar tana murmushi

Umma tayi murmushi tana kallon ta dan ita har sannan bata ji ko kaɗan bata son zuwan nata ba ta ce
 
"Toh shikenan Azrah, Idan alkhairi ne ma zaki tafi da addu'armu, Allah Ya kare ki, Ya ƙara miki daraja da fahimta sannan ya kara muku Imaan"

Tana kallon Umma ta ce

"Allah yasa" daga haka ta miƙe zuwa ɗauro alwala

Bayan sallahn asuba Bappah ya dawo daga masallaci direct ɗakin Umma ya nufa, bayan su Azrah sun fito gaishe sa ya amsa musu da nutsuwa ya ce

"Jiya Umman ku ta ce ana neman mu?" Azrah ta gƴaɗa masa kai ta ce

"Eh sunce suna bukatar ganin iyaye na" Bappah ya ce

"Okay sai ku gama mana abun karyawa da wuri saboda mu samu mu tafi ko?" Umma ta dinga kallonsa, Azrah ta ɗaga kai ta Kalle sa sai kuma ta ce

"Toh Bappah, Nagode sosai" murmushi kawai ya mata daga haka ta miƙe zuwa ɗaura breakfast gudun kar su makkara tunda har yayi magana.

Tun wajajan karfe 9:00am su Bappah suka tafi inda ake neman su, Umma har mamaki take ganin yadda Bappah ya dinga bin kafa ya shiga nan ace ba nan bane sai taga har ya tafi can, hakan ne yasa ta sake kwantar da hankalinta dan tasan addu'ar su ba zata tafi haka kawai ba

Meanwhile

Honorable na cikin office dinsa, yana duba hoton Azrah da ya fito a wata jarida tare da caption din "The girl who fought odds and won"

Zuciyarsa na bugawa da wata sabon soyayya ne, amma sai yake jin mood ɗinsa yana canzawa, haka kawai yake jin ransa na ɓaci ko sanda ya tuno ta sai yaji kamar bashi da lafiya, kifa wayan yayi har na tsawon dakike sannan can ya ɗan samu strength ɗin daukan wayan, dialing numbernta yayi ya tsura na sunanta ido can ganin zai danna call kawai ya fasa ya shiga message yana gama typing kuma kamar mai nazari kuma sai ya tura

Azrah dake zaune ita kaɗai bayan ta kai abincin data gama ɗaki ta ɗaki waya da niyyar game sai kuma ta kalli message daga Honorable ta dinga numbern nasa kamar mai son gani wani abu sai dai bata yi replying ba kawai ta ajiye wayan tana jiran zuwansu Umma ta faɗa mata


Can sai gasu Bappah sun dawo a mugun gajiye, duk wani abu da ake son su cika ko suyi signing sai da suka gama sa, dan daga baya ma sai da Azrah taje ta same su, aka kaita inda za'a mata International passport, kusan everything sun gama kuma duk ya zo musu da dauki barin ma da akaji candidate ɗin honorable ne har wani girma ake kara musu, suna shiga gida sai ga Zahra na alwala da gudu ta je ta rungume su tana murnan kallon sai yanzu suka dawo

Duk ɗakin Umma suka nufa Bappah ya zauna yana kallon Zahra ya ce

"Zahra kawo mana ruwa mana duk a agajiye muke" Zahra ta miƙe tana kallon Azrah daga haka ta fi, bata wani ɗau lokaci ba sai gashi ta dawo ɗakin ta ajiye tana kallon Bappah ta ce

"Bappah an gama komai? Bappah kace min Yes Please" ta kare maganar tana turo masa baki, murmushi yayi ya ce

"Okay, Yes My mom, ba kince nace miki Yes ba ko da amsar No ne" ɗan ɓata rai tayi ta ce

"Toh ai No ɗinne bana son ji Bappah" duk suka yi dariya jin yanda tayi sounding, Bappah ya mika ma Umma envelope ɗin ya ce

"Toh sai ki ajiye dake, ki sa wajan da ba abin da zai same sa please" ta karɓa , Zahra ta fara tsalla ta ce

"Yes Yaya zaki tafi kenan tunda naga wannan" Murmushi kawai Azrah tayi daga haka ta wuce zuwa zuba musu abinci dan tasan duk yunwa suke ji, Zahra ma tabi bayanta tana son ta mata bayanin yadda ake ciki

Umma ta ɗaga kai ganin babu kowa daga ita sai Bappah tayi gyaran murya ta ce

"Yanzu ka yarda Azrah ta tafi ko?" Ya gyada mata kai ya ce

"Yanzu naji nutsuwa sosai ba kamar da farko ba, sannan kuma da babu Alkhairi Allah ba zai bari har muji zamu cike cikin ba, ko kin manta Munyi addu'a ne" murmushi tayi kawai bata ce masa komai ba

Dadadden ranan, bayan sun gama dinner, daga Umma sai Zahra da Azrah, Azrah ta ɗauki wayanta ta shiga message ɗin honorable ta mika ma Umma, Umma ta karɓa tana karantawa sai kuma ta ɗago kai tana kallon Azrah ta ce

"Honorable ne?" Azrah ta gƴaɗa mata kai ta ce

"Eh shine Umma, ɗazu ya turo min" Umma ta gyaɗa kai ta ce

"Yana da gaskiya, dama yaci ace kin buɗe account, yanzu sai gobe kije ko Bappahn ki sai ya raka ki" Azrah ta gƴaɗa mata kai, Umma tace

"Amma me kika ce masa?" Ta ce

"A'a bance masa komai ba tukun, da dana ga yace na basa account number na har da zance masa babu sai kuma naga wani message ɗin nasa yace idan babu naje na buɗe, So, babu wanda na kula daga message ɗin nasa" Umma ta gyada kai ba tare data ce mata komai ba.

Siyama da Habibah suka shigo gidan, ganin Zahra suka fara habaice habaice, Zahra dake wanke wanke bata kulasu ba, Siyama da Habibah suka zauna nan compound ɗin suka cigaba da jefa mata magana

Zahra ta ɗago kai tana kallon cup ɗin hannunta da take wanke wa ta ce

"Kaga kai cup, ka taya Ni jin wannan jahilcin da wasu suka ɗaura wa kansu, taya wanda suke zuwa makaranta za'a na zagi ace ba zasu samu tarbiyya ba" Siyama da Habibah suka kalli zuma sai kuma suka maida kallonsu ga Zahra suna mamakin rashin kunyar da take musu

Zahra ta taɓe baki ta cigaba da maganarta ta ce

"Su fah tallah suke, a cikin maza garage fah, ai ba'a haramta tallah ba amma sai suna zuwa cikin kattin maza da an tashi magana sai suce yaran Umma ba tarbiyya, Toh su banji ko karatun Sallah sun iya" Siyama ta miƙe a zuciye tayi kan Zahra, Zahra ganin Haƙa yasa ta ɗiba ruwan kunfanta a tsoson wanke wanke, Siyama na isowa da niyyar zata fincikota kawai ta watsa mata ruwan kunfan hakan yasa tayi wani kara, ta wanke Zahra da mari, Bappah daya ji ihuu ya fito kenan ya tarar da wannan marin da Siyama tama Zahra ga kuma Habibah ma data tunkaro su, cikin tsawa Bappah ya ce

"Baku da hankali ne?' Habibah zata yi maganar Bappah ya ce

"Ki min shiru mara kunya kawai, taya tana wanke wanke zaku hau kanta da faɗa" Zahra kuwa tun sanda taji Bappah ya fito ta duka ta fara ihuu tana kuka, Bappah ya karasa wajan ya ɗago Zahra zuwa jikinsa yana lallashin ta

Siyama ta ce

"Bappah amma ita ce ai naga ta fara kuma sai ka bi bayanta" wani kallo daya mata ne yasa ta wuce ciki babu shiri tana kunkuni, Bappah ya bawa Zahra hakuri yana tsaye kanta harta gama wanke wanke ya rakata ta kai ciki sannan ya tsata tayi alwalan bacci.

Episode 23: The Hardest Goodbye Begins

Yau gaba ki ɗaya a gajiye Bappah da Azrah suka dawo gida, nan ma yamma lis sai da yayi, sai da Bappah ya tabbatar an buɗe ma Azarh account, sannan suka bi duk wajajen da ake neman su dan karasa abinda ba za'a rasa ba, shiyasa ana idar da Isha'i Azrah ta kama bacci

Bayan dawowan Bappah daga sallahn Isha'i harya shiga ɗakinsa sai kuma ya dawo ɗakin Umma ya ce

"Ki sanar da Azarh ta shirya gobe zamu gidan Dada dan ba lallai daga baya ta samu daman mata sallama ma" Umma ta gyaɗa kai ta ce

"Kamar ka shiga zuciya ta nima abinda nake tunani kenan" Bappah ya ce

"Gobe da safe sai ta shirya" daga haka yama Umma sai da safe.

Washe gari kamar yadda Umma suka yi magana da Bappah, bayan sun idar da Sallah Umma tana kallon Azrah ta ce

"Azrah kije ki shirya kayan ki, Bappahn ku ya ce zaku gidan Dada tunda Kinga maganar naku kamar yanzu zaku tafi" Azrah ta gƴaɗa ma Umma kai a hankali tayi shiru tana kallon waje guda, Umma ta ce

"Lafiya dai ina?" Azrah ta kirkiri murmushi ta ce

"Babu komai Umma" Zahra ta ce

"Nima dai naga tun jiya kin wani canza" Azrah ta harareta ta miƙe zuwa ɗakinsu yin yadda Umma ta ce mata.

Kafin karfe takwas na safe Azrah ta gama shiryawa tana zaune suna hira da Umma tana jiran zuwan Bappah dan lokacin Zahra na makaranta, Bappah ya buɗe labulen ɗakin yana kallon ciki ya ce

"Fito mu tafi idan kin gama shiri" Azrah ta miƙe ta ɗauki ɗan jakkanta, tana kallon Umma ta ce

"Umma zanyi missing ɗinki" Umma tayi murmushi ta ce

"Ya kamata ki fara sabawa tun daga yanzu kafin ki tafi India, yanzu dai ki gaida min Dada" Azrah ta gƴaɗa mata kai, Umma ta musu Allah kiyaye hanya sannan ta koma ta zauna a ɗakinta

Bappah da Azarh suka nufa compound ɗin Mama dake zaune har ta fara tara nata jama'an tana kallon Bappah Zuciyarta na bugawa ta ce

"Malam ina zuwa kuma?" Ba tare da Bappah ya Kalleta ba ya ce

"Gidan Dada zamu" Mama ta taɓe baki ta ce

"Toh ai Shikenan, amma dole sai ka tafi da itane ba zata iya zuwa da kanta bane" sai kuma ta sake taɓe baki dan bata kaunar ko kaɗan Bappah ya tafi garin da Dada take gudun karta ce zata biyo sa dan ta tsana matar nan kamar mutuwa

Ba tare da Bappah ya kara kallon direction dinta ba ya fita, Azrah ta gaisheta wani kallon banza ta aika mata kafin ta cigaba da aikin gabanta tana kallon customers ɗinta.

Bappah na fita ya tsare musu adaidaita ya kaisu har tashan da zasu shiga mutane garin, suna zuwa kuwa wajan mutane biyu ya rage hakan yasa suna shiga Mota ta tashi, basu suka isa ba sai wajajan 11:30am

A kofar gidan suka samu yara na wasa ganinsu yasa yaran suka zo da gudu suna ma Bappah oyoyo, Azrah sai murmushi take wa yaran a haka suka nufa cikin gidan wanda babu laifi gidan da ɗan kayunsa dan duk layin gidan yafi su kyau

Dada tada fito daga ɗakinta zata sauke abincin kan wuta ta sake baki tana kallon Bappah da Azarh cike da mamaki ta ce

"Dama kuna tafe ne?" Bappah ya ce

"Eh Dada" Azrah ta karasa ta rungume Dada cike da farin cikin ganinta ta ce

"Kakana nayi missing ɗinki fah" Dada ta ture ta tana hararanta ta ce

"Eh amma ai baki san hanyar zuwa ki ganni ba" Azrah ta fara dariya, Dada ta bawa wata 'yar makwabciyarsu kulan hannunta ta ce

"Ke Zainabu, kwashe min abincin nan" sai kuma ta maida kallon ta ga Bappah da Azarh ta ce mu shiga ciki, daga haka suka nufi ɗakinta

Dada na kallonsu ta ce

"Ina fatan lafiya dai?" Bappah ya ce

"Lafiya kalau Dada, dama akan maganar da muka fara ne" ta ce

"Oh' okay".

Kwana ɗaya suka yi a gidan Dada sannan suka mata sallama suka dawo cikin garin Katsina, a gajiye suka shiga gida da yamma, Mama suka samu a tsakar gidan tare da wasu mata amma ko kallon direction ɗin Bappah bata yi ba Matan ne ma suka gaishe sa ya amsa musu a takaice ya wuce ciki, Azrah ta gaishe su in jam'i ta wuce abinta ganin irin kallon tsana da Mama ke wasa mata.

Washe gari tun da sassafe Azrah ta kalli message ɗin honorable ta zura wa wayan ido, Zahra ta ce

"Menene?" Azrah ta ce

"Honorable ne wai na tura masa account details ɗina, yau kwana biyu kenan yake damuna" Zahra ta wani Kalleta ta ce

"Okay... You mean ba zaki basa bane kenan or what? Ai wanda ya fika ya fika ne, sannan ai ba roka kika yi ba shine yaga dama" Azrah ta ce

"Toh sai na tura masa kenan kike nufi?" Zahra ta ce

"A'a karni tura masa, amma muga yadda ya ce miki a message ɗin" ta kare maganar tana miƙa mata hannu, Zahra ta karɓi wayan da Azrahn ke miƙa mata, contact ta shiga tayi typing 'my acc no' nan sabon account details ɗin da Azrah tayi ya bayyana, copying acc details ɗin tayi, ta fita a contact ta shiga message ɗin honorable sannan tayi pasting ta danna sent, message ɗin na tafiya nan take ta goge, tayi minimizing ta goge komai sannan ta mika wa Azrah wayanta duk within short secs ta yi hakan wanda yasa ko kaɗan Azrah bata kawo komai a ranta ba ta ce

"Kin gani ba? Ni kuma gaskiya bana jin zan tura masa, baya min magana amma kuma sai ya wani ce zai tura kuɗi? Is like ni kaɗai nake neman taimako" Zahra ta taɓe baki ta miƙe ta fita daga ɗaki ta barta.

Azrah bayan sun gama lunch taji karan message a wayanta, Zahra ta kalli wayan Azrahn da sauri, ko kaɗan Azrahn bata ma ɗauka wani abu ba dan ita gaba ɗaya ta ɗauka mssg ɗin MTN ne, Zahra ta ce

"Yaya Azrah baki ji wayanki yayi karan message bane ?" Azrah ta ce

"Ya wuce message ɗin mtn ne" Zahra ta girgiza kai ta ce

"A haka sai Alkhairi ya wuce ki yanzu idan kuma daga banki ne ko kuma daga inda kika je suka tura miki wani important abu fa?" Umma na kallon Azrah ta ce

"Eh Azrah Kanwar ki tayi magana yanzu ba lokacin da zaki na ignoring messages bane, maybe zai iya zama something important ne ko kuma urgent" Azrah ta jawo wayarta tayi unlocking passcode ɗin, with shock take kallon message ɗin sai kuma ta miƙawa Umma without saying anything

Umma ta karɓa itama with shock take kallo alert ɗin sai kuma ta kalli Azrahn, tama rasa me zata ce, Zahra ta karɓi wayan a hannun Umma tana kallo sai kuma ta gwalo ido ta ce

"Allah sarki honorable, wallahi Allah ne ya turo mana shi dan ya taimaka mana" daga Umma har Azrah kallonta suke sai yanzu Umma ta tuna Azrah ta nuna mata message ɗin daya mata wanda bata masa replying ba, Azrah ma mamaki take toh ya akayi yasan account details ɗin da ko ita bata haddace ba sai Umma data saka ta tayi saying a wayarta

Umma na kallon Zahra ta ce
"Kuma shine ko? Zahra ta gƴaɗa kai ta ce

"Sure! Umma shi'ne, kuma ko hour banyi da tura masa acc details ɗin ba fah" sai kuma ta rufe bakinta da sauri jin me ta gama faɗa

Daga Umma har Azrah kallon Zahra suke da mamaki....

Matan honorable ne ke zaune a katafaran parlorn Uwargidansa, tana shan fruits salad ɗin gabata wanda kwatakwata bata jin taste ɗin saboda rashin appetite, Allah kaɗai yasan yadda zuciyarta ke tafarfasa da wani abu data ji ya tokare ta a throat ɗinta

"Shikenan kenan, yanzu ba iya mukaminsa bane kaɗai yake amfani da shi wajan taimaka mata? Bayan saka sunanta sai kuma yayi amfani da dukiyarsa ne don faranta ran matsiyaciyar yarinyar?" ta furta a hankali, tana cije lebenta

Hajiya Rabi tayi shiru tana kallon Hajiya Maryam da mamaki ta ce

"Amma ya akayi kika san ya tura mata waɗannan huge amount ɗin bayan kince babu wani communication tsakanin su?"

Hajiya Maryam ta ce "kina wasa da Ni kenan, na kuma sake duba transactions ɗinsa na yau sannan naga sunanta, ko ba ita bace Azrah?" Ta karasa tambayar tana mata wani banzan kallon

Hajiya Rabi ta ce

"Ikon Allah, amma malam ya ce ba a cire asirin bafa, Ni har yanzu abun na ɗaure min kai, kai gaskiya na yarda Wannan Yarinyar idan har bamu yi da gaske ba ta shigo gidan nan sunan mu sorry, yarinya kamar mayya asirin ma ba'a jikinta yake ba amma dake ta raɓe sa ji yadda take ɓata mana aiki"

Hajiya Maryam ta juya da sauri tana kallonta ta ce

"Me kike nufi?"

"Cewa yayi  idan muka sake ƙara kuɗi, zamu iya hana tafiyarta gaba ɗaya, sannan za a mantar da ita a zuciyar Honorable, kuma zata shiga kuncin rayuwa"

Hajiya Maryam ta lumshe ido

"Bana so ta samu nasara, bana so ta cigaba da bayyana kamar yadda naga yanzu duniya ta fara saninta balle har wani yaji zai taimaka mata, tabbas zamu ci gaba da plan B, Na shirya kashe ko nawa ne, zan je kauyen nan da kaina gobe da safe" daga haka ta miƙe ba tare data sake ko kallon inda take ba ta wuce ciki abin ta...

A bangaren Azrah kuwa komanta ya fito na tafiya, wanda jibi ne tafiyar na su, jikin Azrah yayi sanyi fiye da yadda take tunani, da yamma suna zaune sai ga Dada ta duro gidan

Mama dake tsakar gida tare da jama'arta ta ɗaga kai jin muryan Dada nan da nan fuskarta ya canza dan ko kaɗan bata so ganinta ba, infact bata kaunar ko ziyara ce ta kawo gidan

Dada ta fara tafe hannu ganin yadda gidan ya cika da makwabta da yaransu duk suna zaune sai hira ake, Mama ta miƙe tsaye da sauri tana canza fuskanta zuwa murmushi, Dada ta ce

"Biki ake a gidan ne ban sani ba? Ko kuma Uwani haihuwa kika yi ne bani da labari irin wannan jama'ar da kika tara mana?" Mama ta fara murmushin dole, duk matan suka miƙe suna gaida Dada cike da ladabi, a dakile ta dinga amsa musu tana bin gidan da kallo, Mama ta karasa wajan zata karɓi jakkanta, Dada ta ɗaga mata hannu alamar ta barshi ganin yadda kayan jikin Maman yayi duku duku ta ce

"Wai har yanzu Uwani baki canza ba? Haka kike tara mutane a gidan ne ko kuma haihuwa akayi bani da labari" Mama ta mata wani kallo ganin bata kallonta da zata juyo tayi saurin ɗauke kai tana bata hakuri, makwabta sanin halin Dada suka fara zame jiki suna fita ɗaya bayan ɗaya

Zahra ta fito a ɗaki da mugun gudu taje ta rungume Dada cike da farin ciki

Nan da nan Dada ta washe baki ta ce

"Me suna kece kika kara girma har haka? Eh lallai dole na dage da taru" daga haka tama manta da sabgar su Mama ta wuce ciki da murnan ganin jikarta..

Washegari da safe, gidan su Azrah ya kara cika da mutane, wasu dan tafiyar Azrah wasu kuma dan Dada ta zo, Kusan kowa ya san gobe ne tafiyarta

Tun safe Zahra da Umma na lura da yanayinta dan gaba ki ɗaya tayi wani Irin shiru wanda gana mata kallo ɗaya zaka gane damuwa ce fal a ranta, Zahra ta ce

"Anty Azrah, menene?" Kamar jira take kawai ta fashe da kuka, jikin Zahra ne yayi sanyi ta karasa wajan da take zaune ta soma lallashinta, Umma ce ta buɗe ɗakin ta shigo sai kuma ta tsaya tana kallonsu da mamaki ta ce

"Lafiya?" Zahra ta ce

"Kuka take Umma" Umma ma kawai daurewa take ta karasa shiga ɗakin ta zauna kusa da Azarh sannan ta jawo ta jikinta

Umma ta soma rarrashinta without saying anything, Azrah ta ce

"Umma yanzu zan tafi in barku? Toh waye zai kula da ke duk da ba fata nake ba idan ciwon ki ya tashi fah? Maybe banyi tunani bane da farko, kuma Maybe naso kaina da yawa shiyasa naso tafiya" Umma ta girgiza mata kai ta ce

"Not at all, Nima ina son ki tafi ko zaki huta Azrah, idan baki tafin bama ba lallai ki cigaba da karatu anan ba, karshe zaki cigaba ne kawai da sana'arki kuma Kinga ina so kiyi karatu wata kila kina da rabon aiki sai kuma kiyi sponsoring kanwarki ko?" Azrah dai sheshekan kuka take wanda gaba ki ɗaya sai yanzu take ganin wannan

Muryan Bappah da Dada suka ji a ɗakin Umma, Umma ta miƙe zata fita kuma sai ga Bappah ya buɗe kofar ɗakin yana kallon su sai kuma ya ce

"Menene kuma?" Umma ta masa bayani ya ce

"Dama ina so Ni da ke da azrah muyi magana kafin gobe" Umma ta bi bayan Bappah, Azrah ma ta miƙe ta bi bayan su, Zahra ta bita da kallo

Azrah ta samu already Bappah na zaune ga Umma sai kuma Dada, ta zauna bakin kofa tana jiran jin me zasu ce mata, nan kowa ya mata nasiha mai ratsa jiki akan karta je can ta canza hali ko ta bar ibadanta, wanda tun kafin a gama Azarh ta gama shan Kukanta...


This book costs 500. Make the payment to Hauwa Jibrin, Wema Bank account 0421255553, and send proof of payment to 08110615256.
Episode 24: Boarding a New Life

An kawowa Azrah traveling documents dinta daga makarantar da ke shirya scholarship ɗin, international passport, visa, da kuma flight ticket.

Zahra ta karɓi envelope ɗin tana karanta "Departure: Abuja International Airport, Time: 9:45am" Sai ta furta da mamaki

"Subhanallah! Wlhi gaskiya ne fa Yaya Azrah, Ohhh soulmate sai yanzu nake gaskata maganar tafiyarki"

Azrah ta karɓi takardun, zuciyarta na dukan da ba'a iya misaltawa ita kaɗai ta san me take ciki, kallon envelope ɗin da Bappah ya shigo mata da shi take yi, A gaban envelope ɗin aka rubuta "Miss Azrah Muhammad" Delegate from Katsina State" Sannan a ƙasa kuma, wani suna: "Miss Samira Kabir  Second Delegate, Katsina State"

Zahra da har sannan murmushi shinfiɗe a fuskarta ta ce

"Ashe ba ke kaɗai ba ce... mutum biyu daga jihar nan kenan? Toh Allah kai ku lafiya"

Azrah ta girgiza kai da murmushin karfin halin ta ce

"Eh, amma dai na san kila ita tana da confidence, amma Ina jin tsoro ne Zahra"

Dada dake gefe tana kallon Azrah da mamaki ta ce

"Yau naga ikon Allah, wai tsoro kike ji? Toh kije kasar mutane kina raɓe raɓe yadda kika saba anan, kar ki cire wannan salalo ɗin naki har mutane su gane su fara raina ki, Ni ina da tabbacin idan Mai sunana ne ina da ya kinin duk inda zata shiga a faɗin duniyar nan ba mai raina min ita"

Umma da tuni ke gefe wanda bata daɗe da idar da salatul-duha ba, shafe addu'ar da ta gama yi, tana kallon Azrah da tausayi ta ce

"Karki ji tsoro Azrah, wannan ba tafiyar ki ba bace kadai harda addu'armu sannan kema ki dage da addu'a da kuma nafil-fili sai Kiga komai ya zo miki cikin sauki" Azrah sauke idon ta da take jin ya fara taruwa da hawaye ta ce

"Umma In Shaa Allah zan dage, masan dole zan yi missing dinku sosai"

Umma ta dan kyalkyale da dariya da hawaye a lokaci daya wanda itama kokarin maida sa take dan karta karya mata zuciya ta ce

"Mu ma haka, amma ai zamu na video call ko ta wayan Bappahn ku ne idan ya gyara wayansa"

Dada ta ce "kar ki ji komai, duk nan zamu dage tukuru wajan miki addu'a da neman nasarar ki"

Bappah ya ce "kin gama haɗa kayan ki" kai ta gƴaɗa masa, ya miƙe ya ce

"Muje na gani" itama miƙewa tayi suka nufa ɗakin su dan duk a ɗakin Umma suke, bayan shigansu ta nuna wa Bappah ghana must-go dake gefe wanda ta saka kayanta a ciki

Bappah ya sauke idonsa kasa saboda wani hawaye da yaji yana shirin zubo masa, daga haka ya juya ya fita bai ko tsaya a ɗakin Umma ba fita yayi daga gidan gaba ki ɗaya

Zahra da Azarh suka fito ɗan hura wuta dan Dada ta fara mita ita akan lokaci take cin abinci, shine zasu hura wuta

Mama da Yaranta suka kalla a sakar gidan, Azrah ta gaisheta amma ko kulata bata yi ba, Zahra tayi kasa da murya ta ce

"Maganin ki, bake 'yar iya ba? Ki cigaba please"

Mama dake tsaye a kofar ɗakinta tana kallon su Zahra dake magana ƙasa ƙasa amma bata san me suke tattaunawa ba but tasan cewa maganarta su ke, Siyama ta ɗauki alayyahun gabanta ta fara yankawa ta cigaba da bawa Habibah labari just to keep their self engaged, Mama ta ce

"Wannan yarinyar tasu suna tunanin tafiyarta zuwa India shine mafita? Toh taje mu gani ɗin" tana kallon yaran nata ta ce

"Ku jira ku gani, ko zata samu damar tafiya filin jirgi balle ta ce da wasu ta san eyapot ɗin? Sai dai ta karanta a labari ko kuma kallo a waya..."

Habibah da Siyama suka dinga dariya, Siyama ta kara da cewa

"Ai babu wani scholarship kawai neman suna take gata a dole ita ba 'yar talakawa ba, bayan gaba da bayanta kam talakawan ne, kuma fah son ta sanu a duniya take yi, Allah ya kiyaye dai"

Habibah ta fara dariya harda riƙe ciki ta ce

"Kai Mama yanzu kina nufin ba zata ba? Ko ɗan eyapot ɗin ba zata ba?" Mama ta ce

"Ke dai ki zuba ido, ba gobe bane ? Ki sauraran kawai Allah kaimu goben"

Azrah ko kaɗan bata ɗauki maganar ta su ba, tasan idan da rabonta ba mai hanata, Zahra ta ce

"Ohh jahilci na damun waɗannan Mutanen, imagine ji yadda Uwarsu ke biye musu, common airport basu iya cewa ba, Allah raba mu da rashin ilimi" Mama tayi wani ashar dan yadda Zahra tayi maganar zasu iya ji, ta miƙe tayi kansa

"Kul karki tsoma dan ina mai tabbatar miki zaki yi nadama idan kika ce zaki taɓa min cibuna" Dada data fito daga ɗaki da sauri ta faɗa dan duk tana jinsu mamakin halin Mama take yi har sannan

Mama ta juya tana kunkuni, Dada ta ce

"Yanzu idan banda raini ace tun jiya na sauka gidan nan amma ko da wasa ban kalla keyar shegun yaranki ba, kin riga da kin nuna musu bani da muhimmanci shiyasa ko sannu da zuwa basu shigo ba, kin kyauta ai, ki cigaba da kissa musu duk abin da kike kissa musu" Mama ta maraice ta ce

"Dada ai basu zama ne a gidan, Jiya da kika iso suna wajan tallah, yanzu kuma zasu fita" Dada tayi wani ashar ta ce

"Wai ke Uwani ba zaki bar wannan halin naki na tura min jikoki tallah ba? Ba zaku iya sana'a a gida ba sai kin tura su uwa duniya suna Mata da sunan tallah? Toh ki cigaba idan tarbiyyar yaran nan ya ɓaci kuyi kuka da kanku"

Sai kuma ta mayar da kallon ta ga su Siyama ta ce

"Dan Uwarku ina magana kuna zaune a wajan ? Nace baku san ina gidan bane?" Duk miƙewan suka yi suka karasa inda take tsaye suna gaishe ta ko amsa bata basu ba ta juya ta wuce ɗakin Umma, Mama ta taɓe bakinta tayi wa Yaranta alamu da su wuce ɗaki

Da yamma Mama na zaune suna labarin ita da wata makwabciyarsu data shigo itama gulman ne ya shigo da ita, sai ga wasu yara suka shigo da sabuwar akwati irin na zamani da kuma wani na riƙe da wani manyan laida daga gani kamar siyayyace a ciki, Mama ta sake baki tana bin yaran da kallo sai kuma tayi saurin cewa

"Ku ina zaku? Waya aiko ku" ganin ɗakin Umma suka nufa yasa tayi wannan tambayar, ɗaya yaron ya juya zai bata amsa sai ga Bappah ya shigo yana

"Yauwa can zaku kai kayan" ai sunɓil Mama ta miƙe tana wani kallon Bappah ciƙe da haushin sa, bata taɓa jin irin wannan tsanar da taji ta fara masa ba, ɗakinta ta wuce ba tare data sake bi ta kan wannan makwabciyarta su ba

A bakin ɗakin Umma suka dire, Zahra ta fito da murnar ganin sabon akwati dan itama taji wani iri data ga 'yar uwarta da zata wani ƙasa kuma Flight zata bi amma ace wai da ghana, ɗauka tayi ta shiga da shi ciki meanwhile tana ma Bappah sannu da zuwa

Bappah ya sallame yaran sannan ya shiga, Umma ta dinga kallon akwatin sai kuma taji kashi saba'in na damuwarta ya tafi, dan tunda gari ya waye tana tunanin yadda yarinyar zata tafi a haka ba tare da shopping ko wasu abubuwan da ba za'a rasa ba

Dada ma ta fito tana kallo ta ce

"Ahtoh yanzu ko kai fah? Dama ina ƴar zamani da irin tafiya irin tamu na tsofaffi ai dole a fitar da ita kunya" Zahra kuwa tuni ta wuce ciki ta jawo hannun Azrah suka fito tare sauke idonta tayi kasa tana ma Bappah godiya, Bappah ya ce

"Azrah ɗauka kije sai ki maida kayan ki ciki ko?" Gƴaɗa masa kai tayi ta miƙe jiki babu lakƙa ta wuce ciki Zahra sai damunta take da surutu

Bappah na fita Umma ta bi bayansa, Mama dake tsaye jikin tagar ɗakinta ta bi su da kallo, ji tayi kamar ta ɗaura hannu a ka tayi ta zunduma ihuu, dogon tsaki  ta ja sannan ta sake labulen

Umma tana shiga ɗakin Bappah shi kuma ganin tana binsa yasan akwai magana, ya juya yana kallon kofa, bayan ta shigo ya matsa mata ya ce

"Ya ake ciki Bitti?" Ta sauke ajiyar zuciya ta ce

" kasan dama ina ta tunanin yadda zata tafi da wannan Ghana sannan kasan tana bukatar wani ɗan siyayya, Allah kara rufa mana asiri, sannu da kokari" ya ce

"Amin, Azrah tana bukatar a mata, ina sane da duk wani wahalhalun da take sha" Umma ta zauna dan ba zata iya juran tsayuwar ba ta ce

"Dama Honorable ne ya turowa Azrah kuɗi wajan 2M wai tayi duk wani abu da zata buka na tafiyar nata" Bappah yayi shiru yana kallon Umma da mamaki, Umma ta ce

"Kayi shiru kuma?" Ya ce

"Toh Ni me zan ce? Ni gaskiya tsoro nake ji idan daga bayan ya ce a biya sa fah?" Umma ta ce

"Bana tunanin zai ce haka, sannan tun daga day 1 ya fara taimaka mata saboda Allah, kuma kaga ai har yanzu ba wai ya ce ya fasa auren nata bane ko?" Bappah ya ce

"Toh yanzu ya za'a yi dan Ni bansan me zance ba" Umma ta ce

"Allah ba zai tozarta mu ba, kawai ayi using wajan tsiya mata wasu abubuwan da ansan dole zata buka ko? And sutura Alhamdulillah tana da su Kuma masu tsada ne dan duk idan ta yi aiki ma ita suka bawa ƙunce,sai dai tana bukatar takalma da wasu abubuwan" Bappah da har sannan a tsorace yake ya ce

"Toh duk yadda za'a yi sai kuyi kawai, idan da wasu abubuwan kamar yadda kika ce sai ta samu ta gama daga yanzu zuwa dare dan Kinga babu wani lokaci ko?" Umma ta gƴaɗa masa kai ta ce

"In shaa Allah, Allah rufa mana asiri sannan yayi mana jagora baki ɗaya" ya amsa da Amin daga haka ta wuce zuwa ɗakin ta

Ɗakin su Azrah ta shiga wanda har Zahra ta fara rearranging mata kayan nata, ga kuma Dada dake gefen katifa suna taɗi da ita, Umma na kallon ta ta ce

"Sannu Dada" Dada ta ce

"Yauwa 'yar nan" Umma ta maida kallonta ga Azrah ta ce

"Azrah ki zo, amma ki fito tare da pen and paper" Azrah ta miƙe ta ɗauki wani jotta da biro a Jakkanta sannan ta bi bayan Umma

A ɗakinta ta same ta bayan ta zauna Umma ta ce

"Kinma Honorable godiya?" Ta girgiza mata kai ta ce

"A'a banyi ba, dan Ni ina tsoron masa magana Umma" Umma ta ce

"Just text him, koda bashin ki ya biya at least ya kamata ki masa godiya balle ba tare da kin tambaye sa ba ne, Okay?" Azrah ta gƴaɗa mata kai, Umma ta ce

"Good, yanzu zaki rubuta duk wasu abubuwan da zaki bukata a can, bance zaki tafi da tarkace bane, just minor things, sannan ki kara takalma tunda naga ɗaya gare ki" Azrah ta gƴaɗa ma Umma kai, Umma ta ce

"Kiyi sauri dan babu wani lokaci fah, at least ku fita yanzu kafin a Magrib kun dawo saboda ki samu ki gama shirya kayan da wuri saboda fitan sassafe zaku yi" Azrah ta sauke kanta kasa tana jin hawaye na taruwa mata, Sallamar Maman Azizah suka jiyo tare da Yaranta mata biyu, Azizah da Baby, Umma ta miƙe tana musu iso.

Bayan sallar Isha'i Maman Azizah da Azrah sai Zahra suka shigo gidan a mugun gajiye da uban tulin siyayyar da suka yi, Umma ta sake baki ta ce


"Ko dai kun manta ba'a tafiya a jirgi da uban kaya ne?" Maman Azizah tayi dariya ta ce

"Zamu san yadda za'a shirya mata kayan yadda ba zaiyi yawa ba".

Kafin sha ɗayan dare sun gama haɗa mata kaya, wanda sai da suka jira Bappah yazo yaga shopping ɗin kafin suka jera mata, bayan tafiyan Maman Azizah da yaranta haka suka kasa bacci, duk suna zaune, Dada kam sai gyangƴaɗin ta take sha daga karshe taga ba zata iya ba kawai ta kwanta abinda

Washe gari, duk da rashin kwanciya da wuri da basu yi ba amma hakan bai hana su tashi da wuri ba, wajen ƙarfe huɗu na asuba suka tashi, Wanka tayi tana fitowa ta ɗaura alwala, duk nafil-fili suka yi suka jira har lokacin asuba tayi, bayan tayi azkar sannan ta miƙe ta saka kaya wanda gaba ɗaya gata nan gata nan ne dai, su Umma ma duk suka shirya suka fito harda Dada, suna jira Bappah da driver su iso

Umma ta zauna tana kallon Azrah kamar bata gama yarda da tafiyar ba, amma tana murmushin karfin halin kawai take dan taga gaba ɗaya Azrahn ta zama so disturb, Azrah ta durƙusa ta rungume Umma tana magana da kukan da ta kasa ɓoye

“Umma in ba dan ke ba, ba zan kawo yanzu ba, ki sa ni cikin addu’arki kullum sannan Allah ya bani ikon yi"

Umma ta ɗago fuskarta, hawaye na gangarowa a fuskarta itama dan yanzu ta kasa ɓoyewa ta ce

"Allah ya yi miki jagora, ya kareki daga dukkan masu sharri, ya baku nasara akan komai, sannan ki tuna ko da duniya tayi duhu, addu'arki tana da haske, means ki cigaba addu'a a ko wani situation mai kyau da mara kyau"

Suna haka sai Bappah ya shigo gidan da ɗan takunkumi a fuskarsa yana duba agogo ya ce

"Mu tafi ko? Lokaci yana tafiya"

Duk suka miƙe Umma ta ce

"Je kima Mama sallama ko?" Daga haka ta fita su kuma duk suka fito suma

This book costs 500. Make the payment to Hauwa Jibrin, Wema Bank account 0421255553, and send proof of payment to 08110615256.
Episode 25: First Flight, New World

Suna isa filin jirgin saman Umaru Musa Yar'adua International Airport, dake cikin garin Katsina, Azrah ta kalli tsarin ginin kamar wata duniya sabuwa, Mutane kala-kala, riƙe da jakunkuna da kuma traveling document ɗinsu riƙe a hannunsu, ta lumshe idonta jin ya fara kawo mata ruwa, idon ta yayi mugun jajir, sai yanzu take jin dama bata yarda da tafiyar ba, gani take kamar a mafarki ne wai yau gata a airport

A cikin masu tafiya, wata kyakkyawar yarinya ce ke tsaye gefe tana duba takardunta, su Azrah na tsaye inda aka kai su dan ansan candidate ɗin government ne, sai ga wani jami'i ya kira sunayen su

"Miss Azrah Muhammad… Miss Samira Kabir…"

Sai suka kalli juna, dan already sun san sunan tunda an rubuta a envelope ɗin, sannan suka matso kusa da mutumin, Samira ta kalli Azrah ta fara murmushi ta ce

"So you're the second delegate from Katsina?"

Azrah ta mayar Mata da murmushin ta ce

"Yeah, Nice to meet you"

'Same here, Let's fly together then" Samira ta ce tana dariya, daga gani irin masu faramfaram ɗin nan ne

Bayan sun kammala komai, kafin su shiga ciki, Azrah ta karasa wajan su Umma dan sallama da su

Zahra ta rungume Azrah tana kuka ta ce

"Karki manta da ni" Azrah ta ce

"Ina zan manta da ke, ke ce rabin raina ai Zahra" ta kare maganar tana fashewa da kuka

Umma ta ce

"Ku bar kuka, kar ku tsorata juna mn Allah zai dawo da ita lafiya kuma cikin aminci da nasara Ina Shaa Allah" Azrah ta gagara kallon direction ɗin su Umma, Bappah ya ce

"Don't cry daughter, zaki saba a hankali kawai kiyi abinda ya kai ki, sannan kuma kar kiyi wasa da addu'a, safe flight"

Dada ma ta dinga bata baki duk da taki yarda ta juyo

Azrah ta karɓi passport ɗinta da boarding pass, ta kalli Umma da Bappah na ƙarshe sannan ta wuce ciki da Samira dake jiranta a gefe, dan bata jin zata iya sake magana da su dan zasu karya mata zuciya

Zahra ta rungume Umma bayan shigan su Azrah, sai yanzu take jin yadda zata yi cuping rayuwarta without her very own sister a gefenta

Har Azrah suka shiga jirgin bata wani cikin hankalinta dan gata nan gata nan ne, A yayin da jirgin ya tashi, a zuciyarta a hankali ta furta

"This is not goodbye, This is me walking into the life I was always meant to live"

Siyama ta kalli agogo ganin ƙarfe tara harya wuce kuma bata ji muryar su Azrah sun dawo ba balle ace sun fasa tafiyan ya sa ta ɗan kalli hanyar shigowa gidan tana jin zuciyarta na mugun tafarfasa


Mama ta fito a ɗaki ta sake baki tana kallon Siyama ta ce

"Ke Siyama uban me kika tsaya yi a gida? Ko tallan ne ba zaki ba?" Siyama ta ɓata rai ta ce

"Toh ai ina jiran ganin dawowan su Azrahn ne, ba kin ce tafiyar ba zai yu ba? Shine nake son ganin dramar a ido na" Mama ta ce

"Dan Allah tashi ki tafi Ni kam, kar kisa nayi asaran ciniki Nikam saboda shegiyar yarinyar nan" Zumburo baki tayi ta ce

"Ni kam ki kyale Ni, nace miki sai naga zuwan su, tallah kuma ke ina ruwan ki tunda ba kuɗin ki za'a kawo miki ba? Ko kin taɓa bamu tallah ba'a kawo miki kuɗin ki bane?" Mama ta sauke ajiyar zuciya ta wuce wajan alalan dake kan wuta ba tare data sake kallonta ba...

Mai keke yayi parking a kofar gidan duk suka sauka, Bappah ya biyasa kuɗin sa shima ya bi bayan su, Siyama dake tsakar gidan tayi saurin miƙewa ta nufa hanyar shiga tana jiran ganin Azrah ta shigo, ta dinga binsu da kallo suna shigowa sai kuma bata ga Azrah ba rai ɓace ta juya zata wajan Mama dan jin ya haka kuma, Dada tayi saurin ce wa

"Ni wai wani irin ruɓeɓɓen tarbiyya aka bawa yaran nan ne? Yanzu Fisabilillah Siyama da a auren kauye ne da tana da yara rututu kila ma da akwai wanda ta kai Zahra, amma ace yarinya kwata kwata ba hankali balle tarbiyya" Zahra ta ɓata rai jin an anbace sunanta

Bappab ya wurgawa Siyama wani kallo ya ce

"Ina baki iya gaisuwa ba ko? Kuma bakinki ba zai iya cewa mutane sannu da zuwa ba ko? Ya miƙi kyau" ta ɗan kalli Umma da Zahra da tuni sun shige ciƙe sai kuma ta kalli Dada ta ce

"Toh sannu da zuwa" Dada ko kallon ta bata yi ba ta wuce abinta, da gudu ta yi dakin Mama tana mai fashewa da kuka ta ce

"Mama kika ce min ba zata ba, toh ba gashi yanzu sun dawo babu ita ba?" Mama ta gwalo ido tana kallon Siyama ta ce

"Kina nufin su dawo babu Azrahn kenan?" Ta ce

"Toh da karya zan miki?" Mama taji wani zufar ya fara karyo mata sai kuma ta ce

"Ke ina ji basu tsaya jiranta bane amma an tabbatar min da ba zata je ba, kila sai jirgin yazo tashi za'a samu wannan matsalar har a korata" Siyama ta fita ba tare data sake kallon inda Mama take ba ma

Jirgin da Azrah da Samira ke ciki ya sauka a Indira Gandhi International Airport, New Delhi da ƙarfe 6:45 na safe, agogon India, Lokacin da suka sauka, gajimare ya rufe sama, iska mai sanyi na busa, tamkar sabuwar duniya ta buɗe musu ƙofa,

Azrah ta kalli ko'ina da idanunta masu cike da mamaki, Mutane suna yawo cikin sauri, wasu kuma suna ta fita a hankali, kowa da kayansa, wasu na magana da Turanci, wasu da yaren da bata taɓa ji ba, sai bin su take da kallo kawai, ta matse hannunta a jakar bayanta domin karfa ta rasa duk wani abu da ke da muhimmanci

"Overwhelming, right?" Samira ta ce, tana dariya sai kuma ta sake cewa

"First time abroad is like stepping into a movie"

Azrah ta yi murmushi dan tun daga kallon farko data ma Samira ta fahimci suna da hali, ta ce

"It feels like I'm dreaming"

Masu karɓar students sun riga sun iso, Suka ɗauke su zuwa wani lodge da jami'ar ta tanada, inda students daga wasu ƙasashe su ma ke sauka. A nan Azrah ta fara fahimtar cewa, duniya fa ba girman Katsina ba ce.

Bayan sun isa masaukinsu kafin a kai su makarantar su, Azrah ta miƙe tayi sallah ko abinci bata ci ba ta kira Bappab video call, lucky ya ɗaga ya ce

"Azrah" kawai Azrah ta fashe da kuka, dakyar Bappah ya lallashe ta, daga haka ya miƙe ya wuce ɗakin Umma dan miƙa musu wayan, tun kafin a gama wayar Azrah ta gama shan Kukanta kamar babu gobe

Meanwhile..... Habibah da Siyama da suke dawowa daga tallah jira kawai suke so suji yara sun fara shafa musu cewa an ai yau Azrah ta dawo amma suka ji shiru, a haka dai suka dawo gidan gaba ɗaya a mugun gajiye, suna shiga ɗaki ko gaisuwa bata ma Mama ba ta ce

"Mama ta dawon yau kuwa?" Mama data yi tagumi tun ɗazu abun duniya ya ishe ta ta ɗan kalli Siyama sai kuma ta ɗauke kanta dan bata bukatar wani magana, Habibah ta kalli yadda Siyama ta kurawa Mama ido ta ce

"Yaya Siyama yadda kika ga Mama haka kam ki sani cewa babu wani fasawan da aka yi" Siyama ta zauna dirshen tana kallon Mama ta ce

"Mama ban gane ba? Kimin bayani mana" Mama ta sauke ajiyar zuciya ta ce

"Siyama kiyiwa girman Allah ki kyale Ni naji da abinda ke damu na" sai kuma ta share idonta ta cigaba

"Ina ga damfarata aka yi, ɗubu ɗari na cire akan a fasa maganar tafiya nan amma sai gashi tun jiya da daddare naji suna waya wai harta isa, gaba ɗaya wannan mahaifiyar tasu bata barni ba balle kuma ta barmin ku, gashi yanzu naga Bappahn ku ya fara sakewa sosai da ita ga kuma yadda ya fara ɗaukan abubuwan Azrah a matsayin uba, ina raya? Inaa dole na sake neman hanya"

Siyama ta miƙe tana taɓe baki dama tun da safe take jiran ganin Azrah ta dawo bata ganta ba ta ce

"Toh yanzu kika gama ce wa damfara ki dubu ɗari shine kuma zaki koma?" Mama ta gyaɗa kai ta ce

"Ai ya zama dole ma kuwa, dan ba zan cigaba da kallon Bappahn ku da wata shegiyar ba kuma"....


Kwana biyu bayan isarsu, orientation ya fara, an gabatar da su da lectures akan life in India, security, culture, da education system. Azrah ta zauna a first row, tana rubuce-rubuce cike da nutsuwa duk wani abu da aka faɗa idan yasan mai amfani ne sai ta rubuta down, ji take har sannan komai a mafarki ne

Wani malami daga jami'ar ya tsaya a gaban students ɗin ya ce

"Some of you are here on full merit, Some on government recommendation, But only one stood out Miss Azrah Muhammad from Nigeria

Daga nan aka danna slide hotonta ya bayyana akan screen, tare da quote ɗinta daga wata hira da tayi a Nigeria immediately kafin ta taho

"Educate a girl, and you awaken a generation"

Gaba ɗaya ɗalibai da malamai, aka bawa Azrah standing ovation

Nan kowa ya juya dan ganin waccece wanna

Bayan taron, wata mace daga UN Women ta same ta, ta ce

"We've been watching your story, We'd love to work with you on our next girl-child campaign"

Azrah ta kafe ta da ido, cikin nutsuwa ta ce

"I'm just a girl with a voice, but I'll speak loud enough for those who can't, thank you"

Samira ta karasa wajan tana murmushi ta ce

"I'm so exhausted wollah mu tafi accomodation ɗinmu" ta karasa maganar tana kamo hannun Azrah sai kuma ta ɗan tsaya tana kallonta ta ce

"Sorry ashe ban miki murna ba, Congratulations, keep soaring, murmushi kawai Azrah tayi tana jin yadda zuciyar ta ke bugawa, sai yanzu ta yarda honorable har sannan yana bibiyanta, dan yanzu ta gama yarda if not waya basu labarinta

Da daddare, Azrah ta tura voice note ma Umma ta wayan Bappah kafin ta kwanta

"Umma thank you, Because of you, I found myself in the world" tun kafin ta fita daga chat ɗinta da Umma taga wani number ya mata magana, ɗan tsayawa tayi tana kallon contents ɗin sai kuma ta sauke ajiyar zuciya a hankali dan yanzu bata kaunan wani abu da zai sake haɗa ta da shi dan tsoro ma take ji amma ya zata yi da wanna huge amount ɗaya turo mata harta taɓa kuma

Da daddare... Samira ce ta buɗe kofar ɗakin ta shigo a gajiye, Azrah ta ajiye wayan ta tana kallonta ta ce

"Tun ɗazu sai yanzu kuma ?" Samira tayi murmushi ta ce

"Ina ga ai yau babu inda ban shiga a makarantar nan ba" Azrah ta ce

"Chap yadda na gajin nan, sannan bacci ma nake ji infact ko waje bana jin zan iya fita" Samira tayi murmushi, ta cire kayan jikin ta ta ɗaura towel sannan ta wuce toilet ɗin


This book costs 500. Make the payment to Hauwa Jibrin, Wema Bank account 0421255553, and send proof of payment to 08110615256.
Episode 26: While She Rose, They Watched

This Morning…

Yau tun da Azrah ta farka, taji wani irin kewar gida ya lulluɓe ta, gaba ɗaya zuciyarta cike take da soyayyar gida, ji tayi dama a mayar da ita gidan, kamar zata yi kuka take ji, bayan ta gama wanka, da zauna yin breakfast ɗinta cikin shiru, yau zata fara lectures amma sai kuma taji wannan excitement yana vanishing, bayan ta gama karyawa ta miƙe tana kokarin shirya tafiya class, sai wayarta ya fara ringing

Da ta duba taga Bappah ne, kafin ta ɗauka kuma sai call ɗin ya yanke, ta san instantly cewa Zahra ce ke son magana da ita

Ta zauna gefen gado riƙe da kayan da zata saka, ta aje wayar tana kallon wani wuri, sai hawaye suka soma tsintiri a hankali, ta share su kamar kar bata son a gani, dan with style ta share fuskar nata, kawai taji muryar Samira daga can edge ɗin ɗakin

"Guess you're already missing home, right? Don’t worry, you'll get used to it, Studying away from home always feels like this at first"

Azrah bata ce komai ba ta cigaba da shirinta cikin natsuwa, ta saka babban palazzo da wata loose riga, sai veil ta lulluɓe kanta da shi, babu wani makeup sai lipstick data yi using amma tayi wata irin tsihirtaccen kyau

Ta rataya totebag dinta, ta ce wa Samira

"Hey, zan shiga school, sai an jima" Samira ta tallaɓi chick ɗjnta tana kallon ta ko kiftawa bata yi ta ce

"Toh! With this outfit someone might think you're actually from this country, kai ki gode Allah Azrah"

Azrah bata kulata ba dan ta fahimci kamar Samira na da wasa atimes, sai kawai ta ce
 
"You're not starting lectures today, right?"

Samira ta gyaɗa kai kawai, ta cigaba da admiring kyau ɗinta, sake sallama suka yi, Azrah kuma ta fice, ta nufi cikin makaranta da zuciya mai rauni amma kafafuwa masu ƙarfi da kuma ƙudurin cikawa Ummanta da Bappah burinsu

Yana zaune kamar yadda ya saba zama a spot ɗinsa, yana ta danna system ɗinsa, yayinda abokinsa ke ta ba shi labari babu kakkautawa, amma duk da yawan surutun, bai ce komai ba yana dai sauraro ne ba tare da ya ɗaga kai ba

Can sai abokin ganin kamar taɗin sa yake shi kaɗai yake surutunsa without giving him attention ya ce

"Ohh, Na manta ban faɗa maka ba ashe you see how your girl is trending? Like, seriously, I'm impressed, she's changing the way people think, ashe sunan ta Azrah wai"

Cak ya tsaya da danna system ɗin, ya ɗago kai ya wani kalle sa, sannan yayi murmushin takaici ya ce

"Wai dan Allah ba zaka daina damuwa da maganar yarinyar ba, will you? If she impresses you that much, why not marry her and end it there? Naga kamar zai fi ko?"

Sagir sake baki yayi yana kallon sa ciƙe da mugun mamaki ya ce

"Ohh really? Me yasa kake raina ma mutane hankali ne wai, ba kai ne rannan kan kira ni about her like a mad person harda turomin pics ta Whatsapp and now I say one thing, you're acting like I crossed the line? See ehn, ko kaine ba zaka ce bata yi impressing ɗinka ba balle ni, so, idan ma sonta ɗinne nasan at least she'll lift our standard!" Ya kare maganar yana masa wani kallo

Shima wani kallon ya raina masa hankali yayi masa ya ce,

"Let me correct you pls, Maybe she'll lift your standard… not mine ka ji?" Sagir ya miƙe yana kallonsa da mamaki sai kuma ya fita ba tare daya sake ce masa komai ba

Dada dake zaune a tsakar gida tana shan iska ta cika kowa da surutu, Zahra na gefenta dan yanzu bata da abokin hira sai Dada, Mama na can bakin ɗakinta itama tana wanki amma ko da wasa taki ta sake kallon direction ɗin Dada tun bayan da ta gaisheta

Wani yaro ne ya shigo gidan da sallama Zahra ta amsa masa ya ce

"Kuka da kanwa nake so na ɗari da hamsin, sai kuma gawayin Naira ɗari" Zahra ta miƙe ta wuce ɗakin su ta ɗauko masa, miƙa masa tayi ya bata kuɗin sannan ya juya ya fita, Dada ta ce

"Wai.. wai.. wai..." Ta kare maganar tana riƙe haɓa, Zahra ta ce

"Me kuma ya faru Dada?" Dada ta ce

"Nikam Abdul na raye kuwa ko ya mutu ne banda labari?" Zahra da rashin fahimta ta ce

"Wani Abdul ɗin kuma wai Dada?" Dada ta ce

"Ungo naki, wani Abdul ɗin kuke da shi bayan Yayan ki" Zahra ta ɗan ɓata fuska dan bata kaunar koda wasa ana cewa Abdul Yayan ta ne amma tunawa da maganar Dada wai ko ya mutu ne yasa ta fashe da dariya ba kakkautawa, Mama dake shanya ta ɗan kalli direction dinsu sai kuma ta ɗauke kai, Dada ta ɗauki mafificin gefenta ta bugi Zahra dashi ta ce

"Ji wani shashanci kuma, ina tambayan ki kina wani babbaka min dariya kamar tabaɓɓiya" Zahra ta tsakaita dariyarta ta ce

"Toh Dada yadda baki ganinsa tunda kika zo muma haka ne, sai ya gama yawonsa zai leƙo gida daga yayi kwana biyu kuma za'a ne mesa a rasa shi" Mama ta ɗaga kai da sauri tana wa Zahra wani kallon tsana, Dada ta riƙe haɓa ta ce

"Ban gane ba? Aure yayi ko meye da kuma baku ganin sa ɗin?" Zahra ta buɗe hannunta ta ce

"Muma ina muka sani, sai ya gama zamansa yake zuwa" Dada ta riƙe haɓa zata yi magana sai Mama ta riga ta ta ce

"Ke Zahra kina yarinya karama sai shegen munafurci da haɗa waje, yanzu Abdul ɗinne zaki ce baki san inda yake ba? Akwai wanda zai ce bai san Abdul ya tafi wajan aiki bane" Zahra ta ɗan buɗe ido tana kallon Mama da mugun mamaki ta ce

"Wallahi Nikam ban sani ba, toh ma magana yake mana da zamu sani?" Mama with shock take kallon Zahra, Dada ta ce

"Ahtoh Nima ai ina da hakkin sanin idan ma aikin ya tafi amma ko da wasa Muhammadu bai faɗi min ba" Mama ta fake idon Dada ta bankawa Zahra wani banzan kallo, Zahra ta sauke idon ta kasa dan ita bata san me ta mata ba

Azrah a mugun gajiye take tafiya, tun safe suna wajen lectures duk da cewa first lectures ɗinsu amma bai zo da sauki ba, dan ma majority of the lectures ɗinma duk introductions ne suka musu, bayan ta isa ɗakin su ta kama door knob ɗin ta murɗa taji a rufe da mamaki take kallon kofar sai kuma tayi knocking tafi minti biyu tsaye amma shiru, kawai ta zauna gashi bata da numbern Samira, wata tazo wuce wa tama Azrah magana fuskarta ɗauke da murmushi

Azrah ta bita da kallo sai dai itama ta mayar mata da murmushin duk da ba wai ta fahimci me take cewa bane dan bata ma taɓa jin wannan Yaren da take mata ba

Kawai yarinyar tayi waving ɗinta har sannan da murmushi a fuskarta, itama Azrahn tayi waving ɗinta back itama da murmushi a fuskarta har sannan, tabi yarinyar da kallo tana mamakin yaren data mata, tana cikin game da wayanta sai ga Samira ta karasa ta ce

"Hey! Sorry na barki kina jira ko?" Azrah tayi murmushi kawai, Samira ta buɗe ɗakin ta ce

"Ban ɗauka zan kai warhaka ba, bari zan baki spare key" Azrah tabi bayanta zuwa cikin ɗakin ta ce

"Baki je lectures bane?" Samira ta juyo ta ce

"Yes yawo na tafi in faɗa miki" Azrah ta dinga kallon ta da mamaki dan Samira mamakin da take bata ya fara yawa, yaushe ma tsana mutanen wajen da har zata ce ta tafi yawo" cire kayanta tayi ta shiga wanka bata wani ɗau lokaci ba ta fito ta sanya simple gown

Bayan ta gama lunch ta ɗauki wayan ta, shiga chat ɗinta da Bappah ta yi, ta tura duk wani vids ɗin orientation ɗinsu sannan ta dropping voice note wa Zahra ganin Bappab baya online yasa ta kashe datan ta kwanta kawai

A bangaren Umma da Bappah kuwa, tun da Azrah ta aiko musu da videon orientation ɗinta da hotuna shikenan gidan ya cika da farin ciki, Dada sai kallon videon take tana maimaitawa da murmushi a fuskanta Bappah ya ce

"Azrah asset ce a garemu, Allah kara mata fahimta da kuma ɗaukaka, ya kare mana ita acan sannan ya tsare mana mutuncinta"

Umma kuwa sai ta dinga ambato
"Alhamdulillah, Allah ka ƙara mata basira, ka kare mana ita a duk inda take"

Dada da tuntuni ta gagara rufe baki ta ce

"Shikenan itama ta maje da mutanen cen, ko da yake dama makwabtaka Uwarta take da su ko?"

Zahra ta shigo, ta zauna kusa da Umma ciƙe da farin cikin daya kasa ɓoyuwa a fuskanta ta ce

"Umma… ni ma zan iya ko?"
Umma ta rungumeta, ta ce

"Zaki iya fin ma Azrah in kika dage, dama duk abinda kace zaka iya toh tabbas ba zai baka wahala ba unless ka saka a rai ba zaka iya bane shine sai kayi ta fama"

Dada ta ɗauke kanta daga kallon su ta ce

"Ohh ni, wai har sannan Bitti baki bin al'adun mu na nan ne?" Sai kuma ta riƙe haɓa tana kallon Umma, dariya kawai Umma tayi

Kan kace me sunan Azrah ya fara yawo a social media musamman bidiyon ta a wajen orientation da kalamanta masu ƙayatarwa hakan yasa unguwarsu ya ɗauki zafi, duk inda kayi scrolling a Facebook da Instagram, hotonta ke yawo da rubuce-rubuce masu taken:
"The Girl Who Spoke for a Generation" hakan yasa wasu daga cikin Mutanen unguwar suka fara tura yaransu makaranta dan ba kaɗan Azrah ta burgesu ba

Zahra dake tabarman da Dada take ga kuma Habibah dake zaune itama kusa da Dada, Zahra dai banda aukin danna wayan Bappab dake hannunta babu wani abun da take yi, wani lokaci ta buɗe baki da karfi irin cike da mamaki tana nunawa Dada Azrah a waya duk kuma tana yi ne saboda Habibah dake wajen ga kuma can Siyama tana hura wuta, wani videon Azrah ta Ciro tana nunawa Dada tana mata maganar kurame data nunawa Mama da ta fito daga daki, ganin Dada ba ganewa zata yi ba ga kuma Habibah a kusa ba daman magana yasa ta ce

"Siyama Habibah ga Azrah an saketa a TV in faɗa muku, Kalli... har UN na nemanta, bayan bloggers dake aukin posting ɗinta"

Mama ta tsaya cak, a kofar ɗakinta Idanunta suka fara kaɗawa, zuciyarta ta tsinke ba kaɗan ba

Wani dogon tsaki Siyama ta ja, dan idon Dada ne amma data gayawa Siyama bakar maganar da har zata mutu bata manta da ita ba sannan kuma ta mata duka

Mama kasa daurewa ta yi ta ce

"Toh ikon Allah... wannan yarinyar haka ta fita har ta kai yanzu an fara saninta a duniya? 'ya Macece fah, Ni tsoro na ma karta ɓaci ne dan wannan ba tarbiyya bace" Dada ta sake baki tana kallon Mama da mugun mamaki tama rasa me zata ce

Habibah kuwa  ta karɓi wayar ta ce da dariya habaici

"Ai duk muna kallon irinsu… su nawa suka fita suka lalace, yanzu ba wai India take ba? Ai kowa yasan kasar da lalacewar yara, sannan ba kuma inda zata je sai da India Zararra" ta gama maganar da habaici, Dada ta ɗauki mafificin hannunta ta kwala mata ta ce

"Ja'ira gaki mara kunya harkin iya habaici, Uban wa ya hanaki ke karatun, ina ji anya kun ma iya karatun Sallah kuwa?" Ta kalli Mama dake ƙoƙarin komawa ɗakinta dan takaici, tayi saurin tsayar da ita ta ce

"Ke kuma yanzu Uwani abin da kike koyawa yaranki kenan? Ji kalman da kike faɗa ai naga itama 'ya take a gurin ki, sannan yadda kika raini yaranki ba Arabic ba boko shine kike tunanin tarbiyya har kike zagin wata? Tallah da suke yawo cikin gari shine kike tunanin zasu zama masu nasara" sai kuma ta riƙe kai ta ce

"Ohhh Ni bansan me ke damun Muhammadu ba da har ya yarda wannan abun ya girma haka a gidan sa"

Mama ta kaɗa kai da takaici, tana ko karin shiga ciki ta ce

"A'a Ni ba fata nake bake ba Dada amma kiyi tinani yarinya ce karama daga ita sai ita a wata uwa duniya fah… muma ga yaranmu a gabanmu In Shaa Allah suma zasu samu nasara" Dada ta ɗauke kai kawai daga ganin ta

Azrah na kwance a kan gadonta tana duba introductions ɗin courses ɗinsu da aka fara yau, Tun dazu Samira ke ta chatting, can sai ta sauke wayarta tana kallon Azrah da mamaki ta ce

"Wait, I thought today was just for introductions?"

Azrah ta amsawa "eh" sai Samira ta ƙara ce mata

"And you're already stressing yourself with reading?"

Azrah tayi murmushi ba tare da ta ce komai ba, Can Samira ta ce

"Wallahi I'm serious o, Ni da I'm in medical line ban shiga panicking ba, sai ke da kike Business Admin?"

Azrah ta yi dariya kadan sannan ta ce

"Kowa da irin system ɗin brain ɗinsa ne Samira Maybe nawa needs early preparation ba sai last minute ba, Plus, I like knowing what each course is all about so that next class won't be hard for me

Samira ta gyaɗa kai tana murmushi, daga ƙarshe sai kawai ta juya ta kwanta, ta bar Azrah da books ɗinta....


This book costs 500. Make the payment to Hauwa Jibrin, Wema Bank account 0421255553, and send proof of payment to 08110615256.

Episode 27: New Soil, Same Roots

Duk da canjin yanayi, yare da al'adu, Azrah ba ta rasa kanta ba. A new land, a new life amma da wata irin natsuwa da kamun kai mai tsafta, ta mugun mai da hankalinta ga karatunta sosai, ga kuma addininta da ko kaɗan bata wasa da shi, kullum kafin ta kwanta sai tayi karatun Alkur'ani sannan tayi addu'o'inta ta kwanta

A cikin group ɗin scholarship students, Azrah na daga cikin manyan masu ladabi da kokari. Malamai sun fara lura da ita ba kawai dan yawan questions da take yi a lecture hall ba, har da nutsuwarta

Wata rana, a middle of a campus tour da aka shirya musu, wani lecturer ya tambayeta

"You're Azrah from Nigeria, right? You scored highest among the African scholars, how did you do it?"

Ware ido tayi tana kallonsa da mamaki  sai kuma tayi saurin realizing ashe tambayarta yayi ta ce

"By holding onto faith sir, family, and a future I want to see"

A nan take wasu dalibai suka fara yi mata kallo na girmamawa, ɗaya daga cikinsu, wata yarinya ‘yar Bangladesh, ta ce mata

"You're so composed, like your strength is from home"

Azrah ta dan tsaya kamar mai nazari sai kuma tayi saurin ce wa

"That's exactly where it's from"

Da daddare bayan ta gama assignments, har sannan kuma Samira bata zo ba, ta kalli agogon ɗakin da yake nuni da karfe sha ɗaya saura, taɓe baki tayi ta ɗauki wayanta ta kunna video recorder, wannan karon ba don jaridu ba amma don for her very own sister Zahra, ta ce

"Assalamu Alaikum Zahra, I miss you irin sosai ɗin nan, i wish you saw what I see here… but I carry you in every book I open, Ki cigaba da kokari, you'll be here one day, too. Tell Umma I'm grateful pls, Tell Bappah I make du'a for him always, Tell Dada I love her and I miss her drama wato ma sai da bana nan ne zata wani zo ta daɗe, And tell Mama…" tayi shiru na dan wani lokaci kamar mai nazari kafin ta ce

"…kawai ki ce mata ina gaishe su and my stepsisters too, Allah ya saka da Alkhairi"

Sai ta kashe camera kawai taji ta fashe da kuka, dama no matter how in har zata yi koda voice note ne ma gida sai tayi kuka amma wannan lokacin  kuka ne na godiya, ba na rashin sabo bane ba...

Ta sha yin godiya da Allah sannan tama Umma addu'a don ta dage akan karatunta ba kaɗan ba, da yanzu zata fara facing many challenges especially in terms of speaking, sannan kuma ya zata yi a lecture hall? Duk sanda ta tuna sai ta ce 'Alhandulillah' sannan tama Umma addu'a.....

Dada na zaune a ɗaki tana jin taɗin da Zahra ke mata ita harta gaji amma da zaran ta gwada mata ta gaji sai ta fara mata kuka hakan yasa dan dole take sauraronta wani ta gane wanin kuma kawai ta bita da Eh, Umma ganin labarin ba karewa zai yi ba ta fito ta ce

"Ke Zahra ke baki gajiya ne wai? Tun tuni kin sata gaba da unnecessary talks ɗinki, kowa ne kamar ke da baya gajiya?" Zahra ta ɓata fuska ta ce

"Kai Umma yanzu kin ji ta ce ta gajine?" Dada ta ce

"Toh Ni inji ne da ba zan gaji ba?" Zahra ta ɓata rai ta koma gefe, Umma ta koma ɗakinta sai ga Mama na sallama, Dada ta amsa ta shiga ta zauna tana bin neat room ɗin da kallo wanda banda kamshin Incense mai daɗi babu abin da yake yi, sai kuma ta taɓe baki tana gaida Dada, Dada ta amsa mata as usual ba yabo ba fallasa, kulan hannunta wanda ya gama cin zamaninsa gashi ya gama koɗewa da alama ma ko wanke shi da kyau ba'a yi ba ta ajiye ma Dada ta ce

"Dada ga abincin" Dada ta ɗan kalli kulan sai kuma ta yamutsa fuska kamar wacca ake wa dole ta ce

"Toh" Mama ta miƙe tana mata kallon kasan ido sai kuma ta fita

Dada tayi tagumi tana bin kulan da kallo, Zahra ta dake tana kallon Dada dake kallon kulan ta ce

"Dada bari na zuba miki abincin ki" ta kare maganar tana miƙewa Dada tayi saurin cewa

"A gidan Uban ki nace miki ina jin yunwa? Zahra ta kunshe dariyar dake cinta ta ce

"Toh bari a ajiye miki sai anjima idan kika fara jin yunwa sai ki ci ko kuma da Daddare ba za'a yi abinci da ke ba kawai sai kici naki tunda kina da shi" a fusace Dada ta fara magana kamar zata daketa ta ce

"Uban gulman dake cinki sai dai ya kare a kanki, toh ke kici mana amma ina ruwanki da ciki na? idan banda gulma ma kinsanni da 'kyankyami kuma Kinsan bana iya cin abincita amma dan munafurci kike wani magana" Zahra ta fashe da dariyar dake cinta ta ce

"Haba Dada, yanzu duk uban wahalar data sha ta girka miki? Kar ya zama asara kuma" Dada ta ce

"Toh ina ruwanki? Nace ina ruwanki? Ina abincin ɗana ake asara ko? Ko da yake ma ai ba asara bane tunda almajirai na ci" Zahra dai ta dinga kallon Dada tana dariyarta, Dada ta miƙe ta fita bata ɗau lokaci ba sai gata da bucket ta ɗauki kulan ta saka a cikin bucket ɗin ta nufa kofar gida da shi, tana kallon almajiri ta kirasa yana zuwa ta miƙa masa kulan ta ce

"Ungo karɓa ka juye ɗan Malam" yana godiya ya karɓa ya juye, sake maida kulan tayi cikin bokatin sannan ta koma cikin gidan

Da Yamma bayan Bappah ya dawo ya zauna akan tabarman da Dada ke zama kullum bayan sun gaisa ya ce

"Yau kuma ina mai sunan naki naganki ke kaɗai Dada?" Dada ta ce

"Na aike ta ne siyanmin goro ne" Dada bata rufe baki ba sai ga Zahra ta shigo da sallama, karasa kan tabarman itama tayi ta zauna tana gaishe da Bappah

Mama dake can gefe tayi ma Bappah sannu da zuwa ciki ciki dan ganin idon Dada ne ma yasa ta yi masa magana amma bata ma yi niyya ba

Bappah ya Ciro wayan sa a aljihun ya shiga Whatsapp ya miƙawa Zahra wayan ya ce

"Ki duba 'yar uwarki ta ajiye miki sako" Zahra ta karɓa ta ce

"Dama yau throughout banyi magana da ita ba, Allah ina missing ɗinta sosai" shiga chat ɗin tayi ta fara downloading vid ɗin bayan ya gama buɗewa tayi playing......

Bayan Dada tayi alwalan Magrib harta shige ciki abinta ita da Zahra, Umma ta fito zata yi sai ga Bappah ma ya fito, murmushi ya sakar mata ya ce

"Bitti'am da wani abu ne?" Umma ta kallesa da mamaki dan kwana biyu Bappah na shayar da ita ruwan mamaki fiye da yadda take zato, ta ce

"A'a me ka gani kuma" ta karasa maganar sanda yayi daidai da lokacin da Bappah ya ɗibo ruwa a buta, ɗan ja baya tayi tana jira ya idar sai ya bata, ajiye mata kujera yayi ya ce

"Zauna sai muyi tare mana" ba musu Umma ta zauna, Bappah idan ya ɗiba sai ya zuba mata

Mama data shigo daga makwabta cak ta tsaya kallonsu dan bata ma san tayi hakan ba, zuciyarta ta fara kuna dama kwana biyu bata samun wani rest of mind balle harta iya bacci mai daɗi, sai da Bappah ya ɗaga kai ya Kalleta suka haɗa ido ya ɗauke kansa sannan tayi realizing cewa ashe a tsaye take a wajan, tayi karfin halin jan kafarta zuwa ɗakinta, Umma kuwa koda wasa bata yarda ta kalli direction ɗinta ba, bayan su idar Bappah ya miƙe ya ce

"Toh bari na tafi masallaci" Umma ta ce

"A dawo lafiya" daga haka ta shiga ciki, tun bata ma tada sallah ba sai ga Zahra ta shigo tayi ƙasa da murya ta ce

"Umma yau kuma soyayya da Bappah ne ya taso haka" Umma ta tamke fuskarta ta ce

"Zaki bar min ɗakin ne ko sai na bangaje ki" Zahra ta ce

"Kai Umma daga tambaya?" Ganin dagaske Umma zata bangajeta yasa ta fita da gudu tana dariya dan she's so happy ganin yadda yanzu Bappah ke ɗaukan su da muhimmanci not like before....

Azrah ta dawo daga lectures cikin gajiya sosai, The only thing on her mind was to freshen up, eat something light, and get some rest, She'd been mentally exhausted from continuous classes, and ga wani azaɓaɓɓen baccin da take ji, dakyar ta karasa cikin hostel ɗin su

Tana buɗe ƙofar ɗakin nasu, kawai ta tsaya turuss, namiji zaune comfortably a saman gadonta, system a gabansa, yana kallon wani abu seriously, Jin an buɗe ƙofa ya sa ya ɗago kansa ya kalli kofar ganin waye ya shigo without knocking, and as soon as he saw her, ya ɗauke kai ya cigaba da abin da yake yi

Azrah ta tsaya shocked na seconds, sannan da sauri ta juya tana cewa "Sorry" ta rufe ƙofar a hankali, Sannan ta tsaya daga waje tana kallon corridor, trying to confirm if she actually entered the wrong room, amma kuma still ɗaki ne dan room number su ne kuma plot ɗin ne, hango wata neighbor ɗinsu da suke haɗuwa kullum da safe tayi ta fito daga ɗakin, hakan ya tabbatar mata cewar tabbas nan ne ɗakinsu.

Confused and uncomfortable, ta ɗauki wayarta ta kira Samira, tana dagawa Azrah ta ce

"Samira kina ina ne?" Samira ta ce "Ina ɗaki, what is it?" Azrah ta ce

"Na shiga ne sai naga wani mutum kuma a ɗakin, so I'm confused ne" Samira tayi dariya ta ce

"Sure! Ki shigo nan ne, ba ɓata kika yi ba" tana kai wa aya ta katse kiran, Azrah tayi shiru har sannan tana processing maganar Samira

Bayan ɗan lokaci Samira ta buɗe kofa da murmushi ta ce

“Come on in jare, I was just in the toilet ne kika shigo, nace kuma ki shigo kin wani tsaya, Aren't you tired?"

Azrah ta shiga cikin ɗakin ba tare da ta kalle direction ɗin mutumin ba. Ta wuce toilet kai tsaye, tayi wanka, ta canza kaya a cikin toilet ɗin sannan ta fito, ko data fito fuskarta a daure, ta zauna a can edge ɗin ɗakin bata ce uffan ba ko kallon direction ɗin Samira bata yi ba

Kawai ji tayi the tiredness was gone, ta buɗe notebook ɗinta ta fara revising notes ɗinta duk da Samira na ta trying to gist with her sai dai hmm da okay kawai take bata a matsayin amsa

After the guy left, Azrah ta juyo ta kalli Samira da ta dawo daga raka sa, ta ce

"Waye shi?

Samira ta yi murmushi ta ce "Friend ɗina ne mana"

Azrah ta kalle ta da wani expression, sannan ba tare da cewa komai ba ta tashi ta fita daga ɗakin

A compound ɗin hostel ɗin ta zauna, staring blankly at one spot not because she was looking at anything in particular, but because she needed air and space from what just disturbed her day...

Kamar yadda kwanaki ke tafiya, sunan Azrah ya ƙara ɗaukaka a cikin Uni, Duk da tana India kamar bata tafi ba, Ana yawan ambatonta a cikin duk wani empowerment event, makarantu suna amfani da labarinta don ƙarfafa gwiwa ma sauran students ɗin

Wasu malamai daga makarantar da ta gama sun wallafa labarin ta a cikin wata mujalla with the caption

"A model student who rose from dust to destiny"

Yaran unguwar su kuwa musamman mata sun fara jin kwadayin zama ita, dan duk yawanci yaran yanzu sun koma makaranta

A ranar wata Girl Empowerment Seminar da aka shirya a school ɗin da Azrah ta gama, principal ɗinsu Azrah da kansa ya gayyaci Umma a matsayin Guest Parent" saboda suna son zata yi speech dan sake ƙarfafawa wasu iyayen gwiwa

Ga manyan da suka yi organizing taron duk suma sun hallara, yayin da aka bawa Umma mic, ta fara magana cike da nutsuwa da kuma tsantsan ilimin anan zaka san cewa Azrah ashe gado tayi

"Ni na kasance nice makaranta na farko ga yarana, ni mahaifiya ce da ta zabi goyon bayan burin ‘yarta fiye da zaɓin jin daɗin kanta, Kuma wannan ba ƙarfi bane harda addu'a ma, da yarda da kaddara kuma sannan da saka a rai zasu iya"

Gaba ɗaya hall ɗin ya cika da shiru ana sauraron bayanan da take yi, cikin extremely grammatically English ɗinta, wata uwa daga can baya ta fashe da kuka tunawa da yadda tayi watsi da karatun nata 'ya'yan gashi sun zama abun 'kyama a gari

"Ya kamata muyi koyi da irin waɗannan mata, kuma da gaske iyaye musamman mata sai kun zama kune makaranta ta farko ma yaranku sannnan suke cinma burin su" cewar principal din makarantar...

Mama dai yanzu duk ta zama kamar zararriya babu abin da ya tsaya mata a rai kamar yadda taga Bappah ya zuba ma Umma ruwa tana alwala, gashi yanzu ya wani rage kulata kuma taga bond ɗinsa da Zahra ya karu ga kuma maganar Azrah da kullum sai yayi yana bada reference a kanta, wannan abun na mugun damunta, and Maman Asabe idan ba wai sun haɗu a hanya bane sai dai su gaisa amma ta daina zuwa dama ita ke raka ta wajan Malaminta...

This book costs 500. Make the payment to Hauwa Jibrin, Wema Bank account 0421255553, and send proof of payment to 08110615256.

Episode 28: First Steps in a New World

Mama bata ankara tana zubar da hawaye ba sai data ji ya ɗiga a hannunta, damuwar duniya sun yi mata yawa fiye da zato, Da hijab ɗin da ta saka bai baya ta fita kamar wadda bata existing a duniyar haka take jinta, zuciyarta cike da ƙunci da ɓacin rai

Gidan Maman Asabe ta nufa kai tsaye, data isa kofar gidan sai kuma ta tsaya tana leƙan cikin gida ko zata ga machine ɗin Baban Asabe, idan babu kuma haka ya tabbatar mata cewa baya nan kenan, A tsakar gidan taga Maman Asabe na tuka tuwa, Asabe kuma na wanke-wanke, ganin haka yasa ta shiga kamar mai tsanɗa tayi sallama cikin ƙasa da murya, Maman Asabe da 'yarta dukansu suka ɗago kai suna kallonta da mamaki

Tafiyar da Mama ke yi ta nuna damuwa ƙarara a fuskantar, Maman Asabe ta tsaya cak da tuka tuwon tana kallonta da alamar tambaya, Mama ta ƙarasa har inda suke ta ce

"Haba Maman Asabe... har akwai abinda zai raba mu haka?"

Maman Asabe ta dan jinjina kai, ta kalle ta sannan ta ce

"Wallahi ban ɗauka da zafi ba, sai dai naga kin guje ni ne, Kuma kinsan Babansu ya hana ni zuwa gidanki shiyasa na tsayar da zuwa ta amma ai koda wasa Banga kafarki ba Kema"

Mama ta girgiza kai, idonta cike da ƙwalla
"Ba wannan ba... yanzu taimako na ke nema, Wallahi rayuwa ta min nauyi, ta juya min baya, na rasa yadda zan yi, yanzu ko bacci dakyar yaƙe ɗauka na da daddare"

Maman Asabe ta kalli Asabe dake wanke wanke ta ce

"Asabe, zo ki karasa tuwon nan" 
Sai ta kama hannun Mama suka shiga ɗaki tana cewa "Kinsan gidan haya yanzu haka sunyi liƙimo ne saf zasu ji me muke faɗa" Mama ta gƴaɗa mata kai, bayan sun zauna Maman Asabe na kallonta ta ce

"Toh me ke faruwa ne? Ina jinki"

Mama ta dafe ƙirjinta dake mata zafi, ta ce da rawar murya
"Wallahi bana jin akwai sauran komai tsakanina da Malam, ya fara share ni kamar ba ni bace Uwargidan sa ba, yanzu soyayya kawai yake ta sheƙawa da wannan shegiyar matarsa, har a tsakar gida zai tsaya yana kissing goshinta ko hannunta... ki Jimin fah?"

Ta share hawayenta tana ci gaba
"Ga uwarsa ma ta tare mana a gida, ko ƙofar ɗakina bata taɓa leƙawa ba, ta mayar da ni kamar ba kowa ba, gashi kuɗin da yake kashewa waccan yarinyar Zahra sai kinsha mamaki kamar bai san su Siyama ba, ke ko nima sai kallon banza ke raba mu"

Kukan data ke tarewa ya ƙwace mata
Maman Asabe da tuntuni take kallonta ta ce

"Ki yi hakuri Maman Siyama, kuka ba zai magance miki matsala ba, Yanzu tashi zaki yi ki fara neman mafita, In har zaki tashi, ni ma zan tsaya miki dan Nima mugun haushinsu nake ji, yanzu sun maida mana unguwar abu kaɗan sai Kiga ana kawo su a misalai, sun sa samarikan unguwa ko kallon 'ya'yanmu basayi saboda ganin waɗancan sai suka raina ma namun"

Mama ta share hawayenta ta ce
"Wallahi wannan shegiyar matar tasa ba zan bar mata gidan haka ba yanzun ma ina tunanin itama wani abun tayi ta jawo hankalin sa, Ni damuwa ta ma ga uban kuɗin makarantar Zahra da yake biya aina yake samun kuɗin oho? Ai dole ma na nema mafita yanzu zaki taimaka min ne"

Maman Asabe ta ce
"To shikenan, mu shirya jibi zamu tafi wancan ƙauyen, wajen Malamin da na faɗa miki kwanaki, zan yi ƙaryar da zan shawo kan Baban Asabe, amma ke, ki nemo kuɗin mota kawai dan Ni Ko sisi bana maganin sa"

Mama ta sauke ajiyar zuciya, kamar an ɗan ɗaga mata wani kaya daga zuciyarta ta ce

"Kuɗi ba matsala bane, ga na Adashe na ma duk suna nan ga kuma wanda nake samu na cinikin abinci ma duk akwai"

Maman Asabe ta ce

"Toh yayi hakan ma, amma yanzu ki rufamin asiri ki tafi kafin Baban Asabe ya shigo dan nasan yanzu haka yana hanya" Mama ta gƴaɗa kai ta ce

"Ai Nagode kwarai, bari nayi maza na tafi" daga haka ta miƙe ta nufi kofa tana ɗan rufe Fuskarta da hijabin jikinta wai ko zata haɗu da Baban Asabe tana fita layinsu ta sauke hannunta kasa tana jin wani mugun relief ba kamar ɗazu da Jiya ba

Lectures sun fara ba wasa ba kama kafar yaro, Kullum tana gama lectures ko ɗaki bata zuwa tana sallah a masallaci zata wuce Library sai dare kuma take koma ɗaki, stress ɗin yanzu is extra ordinary ne, nan ba kamar Nigeria ba ne ko secondary data bari, kullum test, assignment, da reading materials masu yawa, amma Azrah ta zabi tazo ne domin ta canza rayuwarta, ta farantawa mahaifiyarta da Bappah rai, sannan dan kuma ta taimake 'yar uwarta, Sannan kuma ta sa sunan ta a tarihin da babu talauci, wannan shine burinta, da ta tuna haka sai ta kuma kara damke dantse wajen karatu...

Kullum idan ta dawo daga lecture, tana zaune a cool spot dake bayan library tana sake bin duk wani lectures da akayi ranan, bata biye wa friends ko Samira, ba don wani abu ba amma ba ta da lokaci dan takance gwara su ita bata da wani gata daya wuce tayi karatu, mutane da dama basu zafafawa kansu wannan wahalar ba, ita kuma tana fama da charts, calculations, da theory.

Samira kuwa kamar bawai karatun bane ya kawota kasar ko kuma wani abun na daban, Duk da karatun health science take, tana iya amfani da kowane dama wajen jin daɗi, Yau an tafi picnic, gobe group hangout, Kuma ba a rasa ta da friends maza kullum manne da ita, Azrah bata taɓa tsangwamanta ba ko da kuwa idan har zasu zo ɗakinsu ne sai dai ta bar wajan ta koma Library, amma tana mamaki sosai yadda Samira take iya tafiya da mutane ba tare da wani kunya ko shakku ba, ko da yake gani take ai ba kasar da za'a ji kunya bace

A wani yamma da iska ke kadawa a hankali, Azrah na zaune ƙarƙashin wata bishiyar mango a cikin campus wajen da ɗalibai ke zuwa su huta da yin karatu a lokacin free period, cool down ne a wajan masu Kyan gaske, bishiyoyin wajan kuma suke bada iska, gaban ta textbooks ne da notes ɗinta, tana ta karatu cike da natsuwa, ta maida hankalinta dukkan ga abinda take yi

Sai ga wani matashi ya ƙaraso cikin gentle steps, fuskar sa a ɗaure yake kamar wanda yake cikin damuwa, amma idanuwansa na cike da gentle warmth, ya tsaya kusa da ita  cikin very calm voice ɗinsa ya ce

"Mind if I join?"

Sai sannan Azrah ta ɗan ɗaga kai ta kallesa, sai ta yi shiru na wasu seconds kamar me tunanin amsar da zata basa sai kuma ta ce

"Go ahead"

Ya zauna da nutsuwa, yana kallonta can kuma sai ya ce

"You remind me of someone, My grandMa's photo when she was young, The exact same eyes and the smile"

Azrah ta ɗan ware ido tana kallonsa, cike da mamaki, dan kana ganinsa kasan from Arab countries yake, ta ce

"Your grandmother? But I'm Nigerian, and I doubt we're related to Egyptians"

Khalil ya yi murmushi kaɗan

"I know... but I'm serious, there's something about your eyes, your calmness... she had the same aura"

Azrah ba ta ce komai ba, ta juya ta cigaba da karatun ta, tana so ta kauce wa duk wani tattaunawa da ba dole ba ne balle ma taga kamar yana son janta da magane

Shikam ya zuba mata Idanu yana kallonta ne, can ya ce

"I'm Khalil, Master's student, Biochemistry department"
Ya miƙa mata hannunsa yana murmushi

Azrah ta ɗan kalli hannunsa tana mamakin bai ga alamar ta sanya hijab bane, sai ta amsa masa a taƙaice

"Azrah, Business Administration"

Sai ta sake kawar da kanta, tana cigaba da karatun gabanta.

Khalil ya yi ɗan murmushi, ya ja numfashi ya ce

"Sorry for the disturbance, I just... hoped we could be friends"

Azrah ta ɗago kai tana kallonsa sai kuma a hankali ta ce
"Friends? Have you ever seen a real friendship between a man and a woman?"

Khalil ya kalli sama kamar mai tunani, sannan ya ce
"Uhmm...It's possible, I've seen it happen"

Azrah ta girgiza kai ta ce
"I haven't"

Khalil ya ce yana murmushi

"Then let today be your first, Even if you've never seen it before  let's be the start of it"

Azrah ta dan ɗauke kai ba tare da amsa ba, amma wani sanyi ya ratsa zuciyarta lokaci guda ba wai tana jin wani abu gare shi bane kawai kalamansa sun ɗan tsaya mata ne a zuciya, can ya ce

"You study too much, don't you ever rest?"

Azrah tayi dariyar da bata shirya ba, shi kuma ya shagala da kallonta, ta ce
"Resting is a luxury I can't afford now"

Shikenan kuma tun daga wannan ranar kuma khalil kullum say ya samu yadda zaiyi su haɗu da Azrah, Khalil bai taɓa matsa mata ba, ya kasance mai natsuwa da iya zance, yana iya zama da ita awa ɗaya suyi hira kawai ba tare da wani abu mara daɗi ba, sannan yakan koya mata calculation idan har ya shige mata duhu, wannan halayyar tasa ne ya fara janyo Azrah ta fara sakewa a hankali...

Samira, duk da halin ta na zama da maza da yawa, bata taɓa daina nuna kauna ga Azrah ba, dan mostly ita ke girki da kuma wanke plates da wanke toilet sbd yadda Azrahn bata zama sai dai Azrah na kallon ta da mamaki kuma koda wasa bata taɓa yarda ta biye mata ko ta bita wani waje ba

"Wai Samira, don Allah, are all these guys really just friends?" Azrah da zata fita karatun dare ta tambaye ta

Samira dayi wani murmushi ta ce "Wai ke Azrah ba zaki gane ba, I just vibe with people, No strings attached"

Azrah bata yarda da irin wannan rayuwar ba, Ita rayuwa nata na da hankali da shakku dan har sannan kullum sai nasihar Bappah da Umma sunyi knocking kanta....

Sai can wajajen karfe goma na dare Khalil ya raka Azrah har kofar hostel ɗinsu, tana kallon sa da murmushi ta ce

"Alright, good night" shima murmushin ya sakar mata ya ce

"Have a nice dream Azrah" daga haka ta shiga hostel ɗin shi kuma yana tsaye yana kallonta harta shiga sannan ya juya

Tana shiga ɗaki taga Samira na waya murmushi kawai ta mata ta wuce toilet, ko sanda ta fito Samira ta gama wayan, Samira ta ce

"Hey, wannan Dude ɗin fah?" Ba tare da Azrah ta kalleta ba ta ce

"Kawai na guiding ɗina ne da kuma some highlights da yake kara min a karatu" Samira ta tunsire da dariya ta ce

"Ohh really?" Azrah ta tsaya kallonta dan bata fahimci dariyar na menene ba, Samira ta ce

"Stop pretending Azrah, ni ba ruwa na balle kice takura ki zanyi" Azrah bata kuma sake cewa komai ba kawai ta hau kan gado tana addu'an bacci, duk da tana so ta kira Bappah amma kuma ji take baccin yaci karfin ta...

Shikenan tun da semester yayi nisa Azrah ta nemi wata nutsuwa ta rasa, zaman ɗaki kam idan banda bacci bata wani zama, abinci ma daga safe sai dare tuni ta fara manta da wani abinci rana shi yasa sometimes take yawo da biscuits, yauma kamar kullum ne tunda suka fito a lectures ta wuce Library tana karatu kawai taji kamshin turaren Khalil amma ta maze taki juyawa kawai jin muryansa tayi ta ɗaga kai ta lalle sa riƙe da takeaway ya ce

"Today you don't get to say no, You'll eat with me"

Murmushi tayi wanda yake ciƙe da gajiya ta ce

"Okay, you win today" dama yunwar take ji

A haka Khalil ya jata da surutu bayan da suka gama cin abinci dan yana son brain ɗinta yayi resting ne, ya gama faɗa mata burikansa yayi shiru yana kallonta alamun yana jiran jin nata ta ce

"I want to be a powerful businesswoman one day" ta karasa maganar tana kallon wani waje

Khalil ya ce "I believe you will, You have fire in your eyes" dariya kawai tayi ba tare data ce masa komai ba...

As usual sai da dare yayi ta koma hostel, Bayan ta koma ɗaki, ta kwanta tana kallon ceiling, tana tunani, akwai wani abu da ke faruwa cikin zuciyarta kamar sabuwar duniya na buɗewa kan'shi babi zuwa babi a Zuciyarta, wani abu take ji wanda ita kanta bata san dalilin zuwan sa ba, amma ta san bai kamata tana mantawa da dalilin da yasa ta zo ba

"Kaunar kowa ba zata hana ni cimma burina ba" ta fada a ranta, sai kuma tayi realizing me tace, miƙewa tayi ta yi addu'a,

Sai kuma ta buɗe Qur'an ɗin wayanta ta karanta Al-Kur'ani, sannan ta kwanta tana kokarin kawar da komai daga ranta
Chapter 1 · 0% Book details