Sashe 6
Bakin Artabu Part 1 Complete Hausa Novel · about 2 min read
ce ta zahiri wacce babu sihiri ko tsafi acikinta. Nan take kowa ya sallama ya gamsu cewa lallai sarki uhaisu nezai jagoranci wannan gagarumin yaki da za a tafi izuwa birnin misra. Sai da rana ta fadi sannan sarki uhaisu ya farka daga barci domin huce gajiyar shi. A sannan ne kuyangi suka ™Nasiru Muhammad™ kai shi kewaye suka yi masa wanka a cikin bahon zinare mai cike da ruwan kamshi na turaren miski da furanni iri-iri. Bayan angama yimasa wanka an shafeshi da mai sai aka kawo masa kayan yakinsa ya sake sanya su ya mayar da hular karfensa yasa a kansa sannan ya taho fada yana zuwa cikin fada sai kowa ya mike tsaye don girmamawa, hatta sarki daksur kuwa. Maimakon sarki uhaisu yaje ya zauna sai dubi sarki Daksur yace, "a kawo mini dokina yanzu zamu kama hanya mu durfafi Birnin MISRA. Batare da gardamar komai ba kuwa sarki Daksur yasa aka kawowa sarki Uhaisu dokinsa ya hau kawai sai ya kada linzamin dokinsa ya juya da baya ya fice daga cikin fadar. Cikin hanzari sarki Daksur ya bayar da umarni ga dukkan sauran mayaka da a fita ayi hawa abi bayan sarki Uhaisu. Nan da nan kuwa aka bi wannan umarni. Kaico! Tashin han kali ba a samasa rana. Inda ace mutun yana wannan wuri idan yaga irin tsananin yawan wadannan mayaka da kuma irin maggan makaman da suka debo dole ne ya firgita domin gani zaiyi kamar zasu iya tashin duniya gaba dayanta a cikin rabin sa'a. Gaba dayan mayakan da suka fito wannan yakin babu abinda suke son gani face fuskar sarki Uhaisu da kuma irin kirar jikinsa amma sai gashi har yanzu bai cire hular karfen dake kansaba kuma bai kwabe kayan yakin da suka rufe jikinsa ba su kansu kuyangin nan da suka yi masa wanka dukkansu dimaucewa sukai suka fita haiyacinsu saboda ganin irin tsananin kyawun surar da allah ya baiwa sarki Uhaisu. MENENE ZAI FARU A WANNAN GAGARUMiN YAKI DA ZA A YI A BIRNI MISRA? WACE CE MATAR DA SARKI UHAISU ZAI AURA? Mu hadu a BAKIN ARTABU na biyu domin jin cigaban wannan kasaitaccen labari. ==============