← Book details Bakin Artabu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 7

Sashe 4

Bakin Artabu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

mini kuma kada ka kuskura ka shiga dakin da wannan aljani yake domin ku gana sai ranar daza ka fita wannan gagarumin yaki da aka gaiyaceka. " Har kullum sarki Uhaisu baya mancewa da wannan jawabi na mahaifinsa don haka sai ya hakura da batun aure gaba daya a rayuwarsa saboda yana son yayi nisan kwana a cikin daular mulki daya tsinci kansa a ciki. A ranar da wasikar gaiyata izuwa yaki ta riski sarki Uhaisu daga birnin kisra sai yacika da tsananin farin ciki domin yasan cewa lokacine yazo da zai cika babban burinsa na duniya domin yasan mahaifinsa ya gaya masa cewa bayan anyi wannan gagarumin yakinne zai iyayin aure har ya sami magaji kuma lallai zai yi tsawon rai a duniya. Lokacin da maga-takarda ya gama karanta wasikar gayyata a fadar sarki Uhaisu fadawansa suka ga ya cika da farin ciki sai mamaki ya kamasu domin su a saninsu babu sarki ya tsana sama da yaki kuma babu abinda yafi so sama da zaman lafiya. ™Nasiru Muhammad™ Sarki Uhaisu ya kasance mutum mai adalci, tausayi da jin kai, gashi da karrama mutane, wato bai iya wulakanci ba bashi da izza da jin kai irin na sarakai, duk da cewa allah ya bashi karfi, kyawu da dukiya mai yawan gaske. Bisa wannan baiwa da allah ya baiwa sarki Uhaisune ya zama cewa 'yan mata, 'ya'yan sarakai, attajirai da manyann matsafa suka kamu da tsananin kaunarsa, wasu da yawansu a dalilin kamuwa da sonsa ne ma suka kamu da cututtuka saboda rashin samun kaunarsa. Wasu ma sanadin ajalinsu kenan. A duk sa'adda sarki uhaisu ya ci ado kuma yayi hawa ya fito daga cikin gidansa sai dai kaga mata suna fitowa da gudu domin kawai su ganshi. Idan dakaru suna hanasu zuwa kusa dashi sai kaga suna kuka kamar wadanda akayiwa mutuwa. Duk wacce ta sami nasarar koda taba dikin sa ma kuwa sai kaga sauran mata na rungumeta don su sami albarkaci. Idan kuwa maca tasami nasarar koda taba hannun sarki Uhaisu ne sai dai kaga ta yanke jiki ta fadi sumammiya saboda tsananin farin ciki. Daga wannan rana kuwa mata sun dinga kai mata ziyara kenan suna bata kyaututtuka ba adadi. Hakika a tarihin nashiyar kasar tashawar ba a taba samun saurayi mai farin jini ba a wajen mata kamar sarki Uhaisu, kuma labarinsa ya bazu ko ina, har zuwa ake yi daga kasashe daban-daban domin kawai aganshi. Tabbas duk mutumin da yake shakka akansa da zarar yazo ya ganshi dole yake gasgatawa. Komai hassadar mutun da kushensa idan yayi arba da sarki Uhaisu take yake sallamawa. Sukansu maroka idan sarki Uhaisu ya fito suka fara yi masa kirari sai masu rasa irin kalmomin dazasu rinka fada wadanda suka dace da shi akwai wani maroki wanda yafi kowa iya kodashi, shine ya kance dashi: Kaico! Ina gwanin wani ganawa? Ga saurayi uban samari tauraron kyawawa mai magance yunwa da kishirwar yan mata. ™Nasiru Muhammad™ Gaka jarumi. Sarki sadauki mai ragargazar maza yau fa ga mai tekun zinare mai shanye kogunan attajirai. Ga ruwan sanyi mai sanyaya zuciya talakawa kufara nan ga bargon kankara mai kashe gobara daga kogi. Marhaban da babbar gona nomanta sai shekara dubu ! Aduk sa adda marokin ya haukace ya kama sambatu saboda sai da dinare ya rufeshi ruf tamkar an nutsar da shi a cikin yashi tun yana kirari. Ya koma yin waka sannan ya fashe da kuka ya dinga mari da cizon kansa har sai da aka tattarashi shi da dukiyar daya samu aka kaisu gidansa lokacin da sarki uhaisu yaga fadawansa sun cikada mamaki bisa ganin yadda ya kamu da farin ciki don jin sakon gaiyata izuwa yaki. Kuma ya fahim cewa hankalinsu ya dugunzuma ainun sai ya dubesu yayi murmushi sannan yace. ” Yaku yan majalista ku kwantar da hankalinku. Ku sani cewa wannan yaki bai shafi kowa ba awannan kasa tawa face nikadai. Don haka nikadai zan shirya na tafi wannan yaki. ” Koda jin wannan batu sai mamaki da fargaba suka dada kama yan majalistar wazirin sarki uhaisu wanda ake mazwan ya dubishi cikin tsananin damuwa yace. ” Haba ya shugaban kasani cewa mu da sauran talakawanka muna. Matukar kaunarka kuma tunda ka hau kan karagar mulki bamu taba rabuwa da kaiba dai-dai da rana daya. Mun tabbatar da cewa idan babu kai babu wanda zai iya yi mana mulki acikin adalci irin naka. Tayaya kake tsammanin zamu iya barinka ka tafi yaki kai kadai ? Katuna fa cewa baka da mai gadonka bare idan muka rasaka musami halifanka?" Lokacin da waziri yazo nan a jawabinsa sai sarki Uhaisu ya mike daga kan karagarsa yayi tafiya izuwa tsakiyar fadar sannan ya tsaya ya dubi jama'a gabas da yamma, kudu da arewa, kawai sai hawaye ya zubomasa ya ce, "ya ku jama'ar birnin tashwar kuyi sani cewa a iya rayuwata ta duniya babu abinda nake kishinsa kuma ™Nasiru Muhammad™ nake matukar kaunarsa sama da birnina da jama'ata. Yau shekara a shirin da takwas a duniya amma ban taba zuwa yakiba. Duk wannan daukaka da ni'ima wacce nake da ita a duniya bata gani ba sai jitake yi kawai. Yau gashi dama tazo wacce za a sanni. Bugu da kari. Ina mai sanar daku cewa wannan yaki da zan fita ne zan cika babban burina na duniya harna sami damar aure na sami wanda zai gajeni yaci gaba da yi muku irin mulkin da nake muku bayan babuni. " Koda sarki UHAISU yazo nan a zancensa sai fadar gaba daya ta rude da shewa, mutane suka cika da farin ciki asannanne sarki Uhaisu ya sallami kowa fadar ta watse nan labari ya bazu ko ina a kasar cewa gobe sarki Uhaisu zai fita yaki shi kadai kuma ga sakamakon da zai biyo baya idan ya fita yakin. Nan fa jama'a suka yi farin ciki da bakin ciki ba face rabuwar daza a yi da sarki izuwa tsawon kwanaki ko watanni ba a san ranar da wowarsa ba. Haka kuma ba a san irin hadarin da sarki zai gamu da shiba akan hanyarsa, babu tabbacin zai iya tsira da rayuwar sa duk da an san irin gagarumar jarumtakarsa amma kuma ai ba a taba ganin kwazonsaba a filin yaki ba. Dayawa daga cikin jama'ar gari kuwa basu yi bacciba a wannan dare, musamman mata. Duk gidan da kaje sai kaga ana koke-koke tamkar mutuwa akayi. Yayin da dare ya raba sai sarki Uhaisu ya shiga cikin wannan daki na musamman wanda tunda aka haifeshi bai taba shiga ba. Kofar dakin a lullube take da yana gaba dayanta alamar cewa an dade ba'a shigaba tsawon shekara da shekaru. Batare da fargabar komai ba sarki Uhaisu yasa kwagirin sarauta ya share wannan yana sannan yasa daya hannun nasa ya murza marikin kofar dakin nan take kofar ta bude ya kunna kai ciki.™Nasiru Muhammad™ Da shigarsa sai ya ga dakin faba daya a haskake yake da wani irin haske na musamman wanda bai taba ganin irin saba kuma yarasa daga ina hasken yafito. Babu komai acikin dakin face wata farar kujerar karfe guda daya jal a ajiye agefe daya. Sai sarki uhairu ya dubi gabas da yamma. Kudu da arewa na dakin. Amma bai gawata halita nai rai acikiba. Kawai saiya ya juya da baya domin ya fiche daga cikin dakin. Har ya iso bakin kofa yasa kafarsa guda a waje sai yaji an kira sunansa da wata murya wacce tabbas ya taba jin muryar amma sai yakasa tuno mai muryar cikin hanzari da mamaki uhairu ya waigo. Kawai sai yayi arba da wani tsohon aljani. Siriri mai dogon fuska gashin kansa da gemunsa fari ne fat kai da gani kasan cewa yadade aduniya. Aljanin na zaune akan wannan farar kujera fuskarsa cike da annuri. Kallo daya mutun zai yiwa aljanin ya tabbata da cewa yana cikin koshin lafiya domin akwai alamun kuzari a tare da shi babu wata nakasa mai nuna alamu tawaya ko gazawa bisa dalilin tsufa. Aljanin ya sake kiran sunansarki uhaisu akaro na biyu yace. ” Haba dan uwana ya zaka juya ka fito ko gaisawa bamu yiba alhalin yau ne ranar farko da zamu fara ganawa ”. Koda jin haka sai sarki uhaisu ya mai dawa aljanin martanin murmushi yataho gareshi cikin sanyin jiki. Da isowar uhaisu daf da aljanin sai ya mike tsaye cikin girmamawa yayi masa nuni da kujerar da yake zaune akai yace dashi ya zauna. Uhaisu ya dubi aljanin cikin mamki yace. ” Saboda meza kace na zauna akan kujerarka wacce kasaba zama a kanta tun kafin a haifi kakan kakana ? ”. Da jin wannan batu sai kwallah ta ciko a idanun aljanin sannan yace. ” Yakai uhaisu ka sani cewa kaine sarki na arba in da biyar daga cikin sarakan da suka yi sarauta a gidannan kuma kowanne sarki yayi zamaninsa tare dani. Amma gaba ™Nasiru Muhammad™dayansu babu wanda ya shigo cikin dakin nan ya mai da mini da martanin murmushi sai kai kadai. Kai ne kadai sarkin daya shi shigo wajena cikin kwanciyar hankali da saukin kai bada jin tsoro ko izza ba. Turbude fuska kamar wanda aka aikawa da sakon mutuwa yace. ” Bani ne zan sanar da kai wanna addini ba kai da kanka zaka ganeshi zuciyarsaka ta gamsu da shi “. Koda gama fadin haka sai aljani aznaihul markas ya bace bat tamkar bai taba wanzuwa ba a cikin dakin muryarsa na cewa sai mun sake saduwa idan har ka dawo gida a raye cikin nasara. ”Nan take sarki uhaisu ya fice daga cikin dakin ya janyo kofar ya rufeta. Aikuwa yana rufe kofar sai yaga yana ta sake lullubeta tamkar ba a taba bude kofar ba. Nan dai sarki uhaisu ya tafi izuwa turakarsa zuciyasra cike da sake sake da zullumi abinda ya fara yawo a ransa shine. Bayanin karshe da aljani aznaihul markas yayi masa cewa sai sun sake saduwa idan ya dawo a raye kuma cikin nasara. " Shin wannan batu yana nufin kenan babu tabbacin zai tsira da rayuwarsa ? Kuma babu tabbacin zai sami nasara acikin burinsa na duniya?" Nan take hankalin Uhaisu ya dugunzuma. Ya rasa abin da ke masa dadi aduniya, amma da yatuna matsoraci bashi zama gwani, kuma ya tuna shima jarumine sadauki mai tarwatsa maza, sai yaji dukkan tsoro
Chapter 4 · 0% Book details