Sashe 3
Bakin Artabu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
suka rabu tun suna jarirai, har izuwa lokacin da kika gudo izuwa nan kofar birninmu tare da mijinki aka kashe shi a gaban idanunki". Batare da bata lokaciba Humaira ta kwashe dukkan labarinta ta zaiyane wasu yazila. Ai kuwa tana gama bayar da labarin, Yazila da Dabira suka fashe da matsanaicin kuka saboda bakin ciki kuma suka harzuka ainun. Cikin tsananin fusata Yazila ta mike tsaye ta dubi Dabira tace , "yake 'yar uwata kizo mu tafi izuwa birnin kisra yanzu domin mu dauki fansa akan sarkin kisra da sarkin yakinsa. " Koda jin wannan batu sai dabira ta kama kafadun yazila tace, "yake 'yar uwata kiyi sani cewa zuwa da shiri yafi zuwa da wuri. Ina tabbatar miki da cewa ahalin yanzu wadannan abokan gabar tamu ba a zaune suke ba, harma sunyi gagarumin shirin yaki sun taho nan garin domin su baje wannan birnin namu. Labari ya riskemu....." Kafin dabira ta gama fadin abinda ke bakinta sai sarki Raihan ya tari numfashinta yace, "yake Dabira ai wannan jawabi bana bane, nawane". Dabira tayi murmushi tace, "ka gafarceni yakai abbana hakika na wuce gona da iri". Shima sarki Raihan sai yayi murmushi sannan ya dubi yazila yace, "yake 'yar uwar Dabira kiyi sani cewa a halin yanzu a ko yaushe abokan gaba zasu iya baiyana a kofar birninmu kuma labari ya riskemu cewa sun zo da mayaka masu tsananin yawa da ya wuce misali domin har gudummawar mayaka suka samu daga sauran kasashen makwabtaka. Tabbas yanzu bamu da wani zabi wanda yafi mufita mutari abokan gabar nan tun gabannin su iso". Koda sarki raihan yazo nan azancensa sai yazila ta dubi Dabira tace, "yake 'yar uwata kisani cewa nice sarkin yakin birninmu kamar yadda kike sarkin yakin nan birnin, saboda haka nasan dukkan sirrin mayakanmu da irin yanayin yakinsa, lallai zan bayar da gagarumar gudummawa a wannan yaki daza ayi kuma na tabbatar da cewa ba karamar barna zan yiwa su sarki Daksur ba. Babban burina shine, na kashe sarkin yaki da sarki Daksur da hannuna". Koda jin haka sai Dabira tayi murmushi tace, "ni kaina burina kenan domin dole ne mu dauki fansa akansu bisa bakin cikin da suka jefa mahaifiyarmu a ciki. Ya ke 'yar uwata tunda dai yanzu allah yasa kin karbi addinin musulunci na san cewa zuciyarki zata sake kekashewa ga barin tsoro kuma zaki sami kwarin gwuiwa fiye da da can, saboda haka ina ganin idan muka hada karfi da karfe ni dake a wannan yaki zamu iya samun nasara akan abokan gaba ". Kafin yazila ta budi baki tace wani abu sai sarki Raihan ya tari numfashin Dabira yace, "ba haka bane yake 'yata,ke dai kawai munemi taimakon allah, amma ai karfinmu ko dabarar mu baza su sa musami nasara ba akan makiya ba domin na tabbatar da cewa suma baza su fito ba kai tsaye sai da kyakykyawan shiri irin wanda basu taba yin kamar saba. Yanzu abin da nake so dake yake Dabira ki tafi tare da 'yan uwarki yazila ki tara dukkan mayakan kasar nan ku fara shirye shiryen dabaru na yaki wanda yakamata kuyi, nima yanzu zan je na tara dukkan 'yan majalisata domin mutattauna akan wannan yaki, amma dai kusani nine wanda zan jagoranci wannan yaki inyaso kubiyu kurufa min baya idan allah yasa narayu abayan wannan yaki ™Nasiru Muhammad™ kuma nasami nasara za a daura aurena da mahaifiyarku domin mun daidaita junanmu". Sa'adda sarki raihan yazo nan a jawabinsa sai yazila da dabira suka kamu da tsananin farin ciki basu san sa'adda suka rungume sarki ba a tare lokaci guda suka sumbaci goshinsa. Batare da bata lokaci ba Yazila da Dabira suka fice daga cikin dakin da sauri suka nufi wani bangare daban na gidan sarauta inda suka iske wani barde a tsaye cikin shigar yaki. Dabira ta dubi Barden tace, "ma za ka busa kahon tara mayaka domin yanzu nake son mu shirya yadda zamu bullowa wannan yaki". Koda jin haka sai barden yacika Umarni. Ai kuwa nan take dakaru suka dinga tuttudowa daga wajen gidan sarauta suna rugawa izuwa filin fada suna taruwa da jeruwa a sahu-sahu. Wannan shine abin yafaru abirnin misra bayan jaruma yazila taga mahaifiyarta da 'yar uwarta Dabira kuma ta karbi addinin musulunci. *** *** A can birnin kisra, bayan sarkin yaki da sarki Daksur sun yi bincike a cikin halwar tsafi sun ga duk abinda ya faru ga jaruma yazila wadda ta bijire musu kuma tazama babbar abokiyar gabarsu sai hankalinsu ya duguntsuma ainun domin sun tabbatar da cewa aikin dake gabansu ba kadan bane. Bisa wannan dalili ne sarki daksur yasa aka shiga sauran kasashen kafirai dake makwabtaka don neman gudummawar Dakarun yaki. Duk sarkin da wasikar ta iskeshi sai yaba da hadin kai ya aiko da dakarun masu yawa da makamai da kuma isasshen guzuri. A yamma da birnin kisra akwai wata babbar kasa mai suna tashwar. Birnin tashwar na karkashin mulkin wani sadaukin saurayi ne, kyakykyawan gaske mai tarin arziki da karfin mulki. Wani iko na allah shi dai wannan sarki baya tsafi kuma ™Nasiru Muhammad™tsafi baya tasiri akansa. Bisa wannan daliline gaba dayan sarakunan dake mulki a nahiyar suke shakkarsa domin ba a taba kai masa hari ba ko wargi. Shi dai wannan sarki ana kiransa da suna Uhaisu bn kairuf. Sarki uhaisu yana da matukar karfin damtse na allah ya isa, domin komai girman giwa idan yayi mata naushi daya sai ta fadi kasa idan zai jarraba karfinsa ya kansa karti dari su rufar masa shi kadai, sai dai kaga ya bazarda su gaba dayansu sun baje a kasa suna yoyon jini a hanci da baki. Idan kuwa ya naushi mutun iya karfinsa tofa ko kashin karfe gareshi sai ya karye. Sarki uhaisu bashi da wani addini don haka bai matsawa kowa ba a kasarsa duk addinin da mutun yaga dama yana da ikon yinsa. Wannan ya samo asali ne tun daga iyayensa da kakanninsa, haka ya taso ya samesu, basa addini kuma basa hanawa ayi. Akwai wata rana sa'adda mahaifin sarki uhaisu ke kan gangarar mutuwa wato yana kwance acikin jinyar cutar ajali awannan yammaci da suka ka daita su biyu kacal a cikin turakar sarki sai uhaisu ya dubi sarki yayin da hawaye ya zubo masa yace, "ya kai abbana ina son nayi maka wadansu tambayoyi guda biyu wadanda suka dade suna yawo acikin zuciyata" Koda jin wannan batu sai mahaifin nasa ya kamo hannunsa ya dorasu akan kirjinsa kuma ya kura masa idanu alokacin da shima idanunsa suka ciko da kwalla sannan ya budi baki da kyar yace, "ya kai dana na san tambayoyinka dake ranka kuma na dade ina jiran ranar dazaka gabatar dasu agareni. Tabbas yanzu ne lokacin daya dace kayi mini wadannan tambayoyi domin tun kana karami na boye amsarsu, kuma gashi harka girma kakai munzalin dazaka gajeni amma baka san amsar tambayoyin ba wadannan suke faman damunka acikin zuciya. TAMBAYARKA TA FARKO AKAN ADDINI CE. Kana so kasan dalilin dayasa bamu da addini? Tambayarka ta biyu kuwa itace kana so ka san dalilin da yasa naki yin aure, kuma kaima ban taba nuna maka ina da ra'ayin kayi aure ba? Kasaurara da kyau kaji amsar wadannan tambayoyi naka kuma kayi amfani da basirarka wajen amfani dasu domin idan baka nutsuba har abada bazaka sami daraja da daukaka ba irin wadanda na samu a rayuwata. Dalilin dayasa bamu da addini shine, mahaifina kafin yarasu nayi masa irin wannan tambaya, domin yadda ka taso babu addini. Kuma babu aure haka nataso amsar da yabani itace. "Ya kai dana kayi tunani yanzu addinai sun yi yawa a cikin wannan duniya, akwai masu bautar rana, wata, ruwa, wuta, gumaka, dabbobi da sauransu. Kai wasu ma aljanu suke bautawa. Mahaifina yaga yamin cewa addini guda daya ne, kuma ubangiji daya ne wanda shine na gaskiya mai ikon komai da kowa. A wannan zamani babu wannan addini kuma kaima zaka riski wannan addininne a karshen rayuwarka, abu ne mawuyaci kasan wannan addini amma wata kila in ka sami haihuwa danka yasan wannan addini. To ka gaya masa cewa duk ranar da wani gagarumin yaki ya taso ya halarceshi domin a wannan tafarki ne zai san wannan addini na gaskiya har ya fahimceshi kuma ya aminta da shi " Sa'adda mahaifina yazo nan azancensa sai na cika da mamaki na dubeshi nace, "ya kai abbana ashe baka gaya min cewa yaki ba zai taba zuwa birnin tashwar ba? Ya kuma yanzu kake mini batun yaki ?"™Nasiru Muhammad™ Koda jin haka sai mahaifina yaja numfashi tamkar ransa zai fita, a sannan yace, "bana nufin yaki zai zo har nan ya riskeka, ina nufin za'a aikomaka da sakon gayyata. Lallai ka amsa gayyatar, amma kafita yakin kai kadai, kada ka kuskura ta tafi da kowa idan har kana son kasan addinin gaskiya. Dangane da tambaya ta biyu dake ranka kuwa ba wani abubane face batun aure. Tun da mahaifiyarka ta rasu ban sake yunkurin aureba. Haka mahaifina ya kasance, shima mahaifina haka rayuwarrsa ta wanzu har izuwa kan kakanmu na arba'in da daya. Abinda nake nufi anan shine duk wanda yai aure acikinmu haihuwa daya yake samu kuma sai matarsa ta mutu, shima sai yamutu yabar abinda ya haifa. Lokacinda aka haifeka sai naji babu abinda nake so a duniya sama da kai, kuma naji ina son kayi nisan kwana a duniya. A cikin gidan sarautar nan akwai wani daki guda daya wanda ba'a shigarshi kuma kai ma baka taba ganin an shigeshi ba, haka ne?" Kodajin wannan tambaya sai na jinjina kaina nace, tabbas na san da wannan daki kuma na dade ina mamaki da tunani akansa." Mahaifina ya sake ajiyar zuciya yace, "Akwai wani aljani bawanmu a cikin wannan daki wanda bama bauta masa shima kuma baya bauta mana, amma zaman amana ne da kauna tsakanin zuri'armu da tasa. Duk abinda zai samemu a rayuwa shi wannan aljani ne ke sanar damu. Zidane kd. Marubucin ya cigaba da cewa: ============================== ============================= A iya tsawon rayuwata ta duniya sau daya na taba. Ganawa da wannan aljani kuma shine ya gaya mini cewa kada na kuskura na kara yin aure a rayuwata. Idan kuwa nayi sai an kawo harin yaki izuwa kasata an kawar dani. Yakai dana kaima kayi amfani da wannan nasiha wacce wannan aljani yayi