← Book details Bakandamiyar Gumurzu Fita Ta Daya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
CHAPTER 8 OF 36

Chapter 9.

Bakandamiyar Gumurzu Fita Ta Daya Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read

A gabashin filin kuwa katuwar rumface wadda sarakuna suke zaune a cikin ta a gefen damar wanan rumfa kuwa wata karamar rumfa ce wadda take shake da manya-manyan kujeru zaune akansu wazirai ne da hamshakan attajirai, da manya-manyan hatsabiban bokaye wanda suka shahara, hagundin wanan rumfa kuwa wani dogon membari ne wanda shima cike yake da wasu kananu kujeru a gaban kujerun kuwa wani karamin teburi ne da yake dauke da manya-manyan takardu zaune a kan kujerun kuma alkalan gasa ne sanye suke da wasu fararen kaya masu shige da babbar riga sanye akansu wasu huluna ne na saki wanda akayi su da gashin ragon dawa kallo daya zakayi musu kasan lallai mutanen kirkine domin dukkansu dattijaine masu kamala da kwar jini sanye a idanuwan kowanne daga cikinsu wani sihirtaccen gilashin wanda yake zuko duk wani abu na nesa ya dawo kusa kaganshi yadda kasan ka taba hakan zai basu damar ganin duk wani abin dake faruwa a wanan fili ba iyakar nan amfanin wanan gilashi ya tsayaba yana taimaka musu wajan ganin duk wani algus da jarumin gasa yayi domin su samu samar yin hukunci bisa adalci alkalan gasar sun fito ne daga bangare biyu akwai manya-manyan likitoci wanda aka yadda dasu a wanan kasa ta ruma sanan akwai hatsabiban bokaye wanda suka san duk wani tuggu na sihiri da makircinsa.
Zagaye da filin kuwa wasu hatsabiban kasurguman mazajen fama ne tunjim cikin sulke kallo daya zakayi musu kasan sun cika jarumai kuma hatsabiban matsafa domin bayan sulken dake jikinsu kuma damatsansu cike suke da guru da laya wanda hakan zai nuna maka a shirye suke tsaf dasu tunkari duk wani hatsabibi hakika tsarin wanan katon fili na gasa yayi ga duk wanda ya kalli wanan fili zai haka zai bada wanan sheda.
Tashin sarki nawwar ne tasa hayaniyar dake wanzuwa a wanan fili ta lafa sana daga baya ya daga hannunsa sama lamarin da yasa filin ya ida yin shiru kenan kama mutuwa ta gitta sana ya fara magana cikin nuna isa da izza abin da zai baka mamaki shine ....

BAKANDAMIYAR GUMURZU
Littafin Umar Abdulhadi Mari
Ebook created by Shuraih Usman
Published at www.hausaebooks.com.ng


(IBNI ABDULLAHI ABDULLAHI)
BAKANDAMIYAR GUMURZU.
Chapter11.
Yayin da sarki nawwar yazo nan jawabinsa sai ya tsaya sana ya koma kan kujerarsa ya harde yana mai fuskantar filin gasar lokacinne shugaban alkalan gasa ya tashi hannunsa na rike da wani katon karfen da aka kwakware tsakiyarsa sana karshensa aka fadadashi kamar kaho ya kafa wanan katon kafen a bakinsa ya fara magana nan take muryarsa ta karade daukacin filin ya fara magana kamar haka yanxu batare bata lokaciba zamu fara wanan gasa ta gwarzon gwaraza don haka muna umartar jaruman gasa da su bar wanan fili su tafi wajan da aka tanadar musu nan take jaruman gasa suka rabu kashi ukku kowani kashi ya tunkari wani babban daki da aka tanada na musamman domin jaruman gasa mutane suka shiga nasu aljannuma haka dodannima haka kowani rukuni daga cikin rukunannan ukku sai da sukayi mamaki mutuka yayin da suka shiga wanan dakin gani bangon dakin cike yake da makaman yaki kala-kala da wanda suka sani da wandama basu taba ganiba kafin daga bisani suka zauna suna mai saurare nan take wanan alkalin gasar ya dauko wata takarda da akayi ta da jemammar fata wadda take dauke da sunayen jaruman gasa ya fara magana kamar haka wanda zasu fara fafatawa a yau sune SADAUKI DALƘUS da JARUMI SALJAM wanda dukansu sun fito ne daga jinsin mutane nan take "yan kallo suka zuba ido domin ganin wanan sadaukai ba'ajima ba sai gasu sun bayyana suna mai fitowa daga wanan katon daki na jaruman gasa tabbas kowa na filin saida ya girgiza dagani sadauki dalƙus domin shine ya fara fitowa daga wanan dakin sadauki dalƙus bakar fata ne kuma duk inda ake neman kato to sadauki dalƙus yakai gashi dukkan illahirin jikinsa a murde yake yadda kasan an jera masa duwatsu gashi da tsawo kallo daya zaka masa kasan cewa jarumin gaskene kuma fasa taro yana bayyana filin ya dau shewa da ihu yana zuwa tsakiyar wanan fili ya ja tunga yana mai dagawa masoyansa hannu nan take filin ya kara kaurewa da shewa, bayyanar saljam ce ta kara sawa filin ya kara kaurewa da ihu inda mabiyansa suka fara kiran sunansa saljam, saljam,.. Tabbas shima jarumi saljam ba bayaneba wajan girman jiki da murdewa hakama kwarjinisu da dalƙus zai iya zuwa daya banbancinsu da dalkus kawai tsawo ne domin shi saljam yanda kasan ragowar samudawa haka yake kafin ka samu mai tsawonsa a mutane sai ka jima, da bayyanar jarumi saljam aka buga kugen fara gasa nan take suka fukanci juna sai a lokacinne suka ƙarewa junansu kallo tabbas ko ba'a gwadaba sun san za'a sha fama kafin daya daga cikinsu ya illata dan uwansa..
January mar Abdulhadi Mati ▶ DANDALIN LITTATTAFAN YAKI AND HAUSA NOVEL BY (IBNI ABDULLAHI ABDULLAHI)
BAKANDAMIYAR GUMURXU.
Chapter 8 · 0% Book details