← Book details Bakandamiyar Gumurzu Fita Ta Daya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
CHAPTER 29 OF 36

Chapter 33.

Bakandamiyar Gumurzu Fita Ta Daya Part 1 Complete Hausa Novel · about 2 min read

Ganin babu wanda yayi nasarar koda lakutar jikin abokin karawarsa ne yasa wanan jarumai biyu ƙara fusata haɗe da tunxura, fusatarsu da tunzurarsu ce tasa wanan yaƙi ya ƙara caɓewa haɗe da cukurkuɗewa kowanne daga cikinsu ya ƙara zage dantse haɗe da buɗewa abokin karwar sa salo-salo na ƙofofin masifar yaƙi cikin baƙin zafin nama da juriya ta ban mamaki suke kaiwa junansu sara da suka haɗe da dukan junansu hannu da ƙafa duk wanda aka kaiwa sarako suka yana kaucewa ko ya kare kafin ya maido martani sai kaga an kaimasa duka da hannu ko da ƙafa amma saikaga kamar walƙiya ya kare ko ya kauce cikin ƙwarewa da bajinta saikaga shima ya maida raddi da masifa tayi masifa wanan jarumai sukaga iya yaƙi yana neman zuwa ɗaya sai kowa ya fara tunanin canza salon yaƙi domin ya samu damar lahanta ɗan uwansa ba tare da an kai ruwa rana ba hakance tasa kowanne daga cikinsu himmatuwa haɗe da ƙara zage dantse wajan safkewa dan uwansa salo-salo na masifar yaƙi ana cikin wanan turmutsutsu ne sai Basadaukiya ta shammaci sadauki salka ta daka wani uban tsalle haɗe da juyawa a sama sau ukku sana ta dire nesa kaɗan da inda sadauki salka yaja tunga sana ta gyara tsayuwarta jaɗe da yin murmushin mugunta hade da raini wanda yake nuni da cewa wuyar aiki ai bama 'a faraba domin wanan yaƙi da sukayi kamar sharar fagene, shi kuwa sadauki salka wani irin kallo yayiwa Basadaukiya wanda ke nuni da cewa "wai wanan yarinyar dame take taƙamane" ba'ayi auneba sai ganin Basadaukiya akayi tayi shiga tsalle sama haɗe da ware hannayeta kamar mai fukafiki haka ta sulmiyo ƙasa tayi di dirar mikiya akan sadauki salka, baiyi aune ba sai ganinta yayi a samar kansa kafin yayi wani kyakyawan yunƙuri tuni ta kawo masa wani bahagumen sara cikin baƙin zafinnama ya kare amma kafin ya ankara tuni ta sanya gwiwar ƙafarta ta masa wani wawan duka a fuska duk da yayi ƙoƙarin kaucewa amma sai da tayi nasarar samu gefen fuskarsa wananne yasa sadauki salka yaji wani azababben raɗaɗi ya ratsa masa ƙwaƙwalwarsa duk da haka abin bai tsaya nanba domin kuwa Basadaukiya wulƙila jikinta tayi haɗe da juyowa ta ƙara kawo masa walfta kamar shaho... (IBNI ABDULLAHI ABDULLAHI)
BAKANDAMIYAR GUMURZU.
Chapter 29 · 0% Book details