← Book details Ba Mahaifiyata Bace Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 5

Sashe 3

Ba Mahaifiyata Bace Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Washe gari da sassafe Anilat tayiwa sulaisa sallama ta wuce gida, tana shiga cikin gidan afalo ta tararda dukka mutanan gidan ko kallo basu ishetaba ta miki hanyar dakinta zata shiga, Anilat ina kikaje jiya da daddare, bansaniba, waike didi nafuskanci kin fiye sa ido inaruwanki da inda naje , yau kwanan saif 3 Baya zama a gidannan kintaba tambayar sa ina yake zuwa saini ,saukar wani gigitaccen mari taji a kuncinta hagu da dama harsai da taga taurari ,ihu takwada tai kukan kura taikan,benazer ,yayinda benazer ta makata da bangon falon saida kanta ya fashe ,didi dataga benazer tana kokarin kashe anilat ai da sairi tazo ta fincike benazer tai hurgi da ita gefe ,sannan ta kama hannun Anilat takaita daki tadawo falon', tana zuwa ta damki wuyan benazer ta shaketa tana cewa , ubanme taimiki wayasa ki dukanta, sokike ki kashemin " ya yaukam zaki ga yadda ake tsantsar azaba a gidannan, haba momy bakijin rashin kunyarda da take yimiki ,tayidin daidai lokacinda takara makata ajikin bango, hannu ta kara sawa ta riko wuyan rigar benazer takara wurgi da ita jikake temmm daidai shigowar irfan ,dagudu yazo ya rike hannun didi yafara bata hakuri akan tasaki benazer karta kashemasa yar uwa amma kashi shima damkarsa tai tai hulli dashi ,jikake temmm tunda ya tumu da ginin gurin komotsi bai sake yiba , aiko benazer dataga haka batasan lokacin da ta hankade didi ta sunkuci irfan ta nufi hanyar fita ,tana tafe tana kuka, ahaka hartakarasa asbitin dake kusada gidansu ,Allah sarki baiwar Allah ko dan kwali babu akan duk gashinnan yabazo ya rufemata fuska da Baya ,kafartako ko takalmi bata tsaya sawaba ,aguje ta fada cikin asbitin ,mutanen suka fara guduwa sunzata mahaukaciyace ,wata likita ta hango tafito daga wani daki dagudu benazer ta karasa gurin ta tafara mata magiya, likita kitaimakeni dan uwana zai mutu ,kitausayamin, karbar irfan akai daga hannunta aka shiga dashi, yayida aka rufa akansa, dawowa likitan ta karayi ,tasamarmata kudin daza abiya domin samun lafiyar irfan , sai lokacin benazer tatuna batada ko sisi kuma batada inda zata samo kudi, likitar takara kalla yayinda tace, doctor dan girman Allah kitaimakeni kada dan uwana yarasa ransa,wlh banida kudi ,amma kome kika ce nayi miki zanyi kodan dan uwana tasamu lafiya, tom shikkenan kudin aikin dan,uwanki zakibiya naira dubu 1,50 , haba doctor inana zan iya samo naira dubu dari da hamsin kitausayamin, okay bakince zaki iya aikiba ,to shikkenan zaki dinga min wanki da shara da wanke wanke ,da girki harlokacin da dan uwanki zai samu lafiya ,wannan shine kadai taimakon da zan iya yimiki, durkusawa tai taimata godiya sannan tacigaba da zama agurin ,gaba daya duk tarude sabida tunanin halimda irfan yake ciki, gaskiyane momy bata kyautaba ,anya kuwa itadin ce ta haifemu, to idan (BA MAHAIFIYATA BACE) tokenan wacece ta haifemu ,kuma meyasa muke zaune agurinta ,ina dangin mahaifinmu, wanene babanmu, meyasa bata kaunarmu, meyasa tafi fifita Anilat da saif akanmu, memukai mata, laifinme irfan yayi ma momy harda ya cancanci wannan wukuncin, meyasa batadamuba alokacin data bugashida gini, anya kuwa ? Tambayoyi kalakala ta dingayi azuciyarta tana sakesake da warwara,

To masu sauraro daman ance laifin dadi karewa free pages ,BA MAHAIFIYATA BACE book 1 game bukatar cigaban littafin saiya tuntube ni tawannan number 09166764540 littafin BA MAHAIFIYATA BACE nakudine ,zaka samu complete dinsa akan nera 300 kacal ngd

BA MAHAIFIYATA BACE by Hafsat Umar dangoro yarmutan BAKIN RAFEE
Complete book. Cigaban free pages.

To benazer tana tsaka da wannan tunanin ,saiga doctor yakaraso gurin , aslmualaikum, aminwa alaikumussalam ,yarinya juyo ki saurareni benazer ce ta juyo tana sauraransa zuciyarta cike da fargabar kardai irfan ya mutu, doctor ne yafara maga ,yarinya inaso kidauki dangana me kyau ko mara kyau kiyi hakuri da dukkan abinda zanfadamiki ,nan danan benazer ta gigice doctor meyasa mu dan uwana kodai ya mutune, aa yarinya dan,uwanki yana nan araye saidai yasamu matsala a kwakwalwasa sakamakon buguwar dayayi ayanzu bazai kara tuna komai a rayuwarsa ba ,nashiga uku tadora hannu aka tana rusa kuka yanzu shikkenan doctor nima ya mantani kenan,yanzu bazai dawo yadda yakeba har abada, sorry ba haka nake nufiba ,da ikon ubangiji idan yaga wani abun da i tsoratar dashi ko kuma yaga abinda yake matukar so arayuwarsa to zai iya tuna wani abun koya tuna gaba daya, ,to doctor ina irfan din yake ,ki tsaya nagama miki bayani tukunna doctor yafadamin bakida kudin aikin daza amawa dan uwanki , kuma tace tadauki nauyin kudin aikin daza amasa dubu dari , kuma kinsan aikin dubu dari da hamsinne, amma da sharadin zakimata aiki, kuma kudin dazaki mata aiki tabiyaki bazai taba isaba ,dan haka zamu hadamiki da sharar nan asbitina inzaki iya saini na biya ragowar dubu hamsin din, muryarta tana rawa tace likitta komene zan iya indai bai sabawa addinin muslinciba, daga kafada dayayayi alamar be damuba ya koma ciki ,Inda tatashi tashiga dakinda irfan yake, karasawa tayi gaban gadonsa ta zauna ,zubamishi idotai kuma shima ita yake kallo ,tana binshi da kallon tausayawa ,shikuma yana binta da kallon tuhuma ,hannunsa ta ruko tana kuka irfan dina kaganeni, cikamin hannuna ni bansankiba ya ture hannun ta ,janyo shi tai jikinta tana kuka yanzu irfan kamata da benazer,kamanta da addarka ,why?meyasa ,kaifa din dan,uwanane ,likita yacemin kamanta komi dan Allah karka ce bazaka zauna tare daniba ,idan kaki yarda dani babu wanda zai taimaka maka ,ayanzu nice uwarka nice ubanka irfan karka gujeni takara fashewa da wani sabon kukan, ta durkushe akasa tana kuka kamar ranta zaifita tana cewa ,momy me mukai miki meyasa bazaki nunamana soyayyar iyayeba ,ina abbanmu yake ,wayyo Allah rayuwarmu, sannan ta daga kanta sama da hannunta, tafara addu ,a Allahumma ajirni fi musibati ,Allah idan wanna jarabawarce sular shigata aljanna Allah kasa na iya cinyeta ,ya ubangiji nidin me raunice inason shi ,bazan iya jure ganinsa a hakaba , ya allah ka bawa dan uwana lafiya ,shiko irfan ganin yadda ta damudashi ,hartake kuka akan bashida lafiya yasa ya fahimci kodai ita din mahaifiyar shice ,sakkowa yayi daga kan gadon ,ya rungumeta tsam ajikinsa yana cewa ,marmar kidaina kuka kinji ,cak benazer tatsaya da kukan datakeyi marmar kuma ,bayadda zatai haka tabar shi a ita dince mahaifiyarshi,naam irfan dina nadaina kukan ,nan ta kakaro murmushin karfin hali tana yimasa , marmar yaushe zamu koma gida ,Kayi hakuri irfan bayanzu ba sai kasamu lafiya, marmar meyasa naganki babu abinda waccan tasa anan dinta ,yana nuna mata kanta, sai lokacin tafahimci hijabi yake nufi ,turkashi ita tama manta shaf ahaka tafito daga gida babu hijabi babu dan kwali,babu takalmi , to kenan taya za ai takoma gida ,ta dakko ,daga idotai ta kalli irfan ,irfan bari naje na dawo ka koma ka kwanta, tom kana ya koma ya kwanta

Futatai daga asbitin cikin sanda tana bin mutanan gurin da kallo ,tana tsaka da wanan tunanin ta hango wani mutumi yasha jallabiya ,kansa ta kalla tai murmushi ,tafiya taciga ba ,da yi harta karasa gurin matashin saurayin da tagani ,tana isa ta fincike mayafin da ya lulluba ta lulluba a jikinta shiko dagowa yayi ya na kallonta dan ya ga yarinyar bataimasa kama da me hankali ba ,yana tsaka da wanan tunanin saijiyay ta cizge nadin da yayiwa gashinsa ta daure kanta ,tamiki hanya taigaba ko kallonshi bataiba,
Gabadaya gashin kansa da ya nannadene ya zubo a gadon bayansa ,kawai yabi bayan yarinyar da kallo , exqued dinsane suka tafi zasu bita ,dasauri ya dakatar dasu cikin harshen larabci, suko mutanan gurin daga mecewa wow saimasu gulmar wanan macece ko namiji ,

Zaune take agaban wasu bakaken mutane masu sanye da jajayen kaya suffarsu abun tsoro ,wani me suffar samudawane daga cikin su da alama shidin ogansune ,karasowayayi gurin tsohuwar da take zaune agaban wani koko cikin kokon yana dauke da wani abu jajur da alamadai jinine ,daukar kokon yayi ya kurba ,ya tuntsure dawata mahaukaciyar dariya ha ha ha ha ha, akinki yacika ya kammala ,amma dasharadi muddum kika bari yadawo cikin hankalinsa ya gane ita din yar,uwarsa ce ,to tabbas yarki bazata taba yin aureba ,domin muddum yakasance yana cemata marmar to babu wanda zaiganta ya ji yana sonta kowa tunani zaiyi matar aurece, ha ha ha ha ha ,kinga sai ki cigaba da wulakantata amatsayin yar aikinki, kada kibari asamu matsala ,idan aka samu matsala tasakafa ta bar zama agidannan to taku takare ,ha ha ha ha ha, tsohuwar ce ta bude baki tace ,sarkin matsuffa, nifa bahaka nakeso abartaba ,inaso ka rabata da wanan kwwunnata ,ha ha ha ha ha ,bazai taba yuwuwaba dole zata kasance ame kyau dinta kuma ba wanda zai aureta ha ha ha ha ha, Amma sarkin matsuffa menene dalilin dayasa kace kada nabari tasa kafa tabar gidan , ha ha ha ha ha ,munduba mungani muddum sukai arba da BAUTBOUN , dagaranar mungama yawo komai zai lalace ,ayanzuma ,sun hadu sa armu d'aya Basu hada idoba ,amma shiya kalleta ta kuma bata kalleshiba ,dazarar kin bari BAUTBOUN da BENAZER sun kasance guri daya sunyi mu amalar aure tare ,to fa ranar tamu ta kare komai namu zai lalace asirinmu zai tonu ,No no ,bazai yuwuba wlh indai ina raye bazan taba bari BAUTBOUN da BENAZER su haduba, ha ha ha ha ha , zaki iya tafiya .

Tashin hankali , shin wanene BAUTBOUN, wacece wannan tsohuwar , me BENAZER taimata , shin BAUTBOUN zai auri BENAZER ko a,a mucigaba da tafiya domin sanin yadda zata kaya
Chapter 3 · 0% Book details