← Book details Auren Yarinta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 5

Sashe 4

Auren Yarinta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Karasa wa tayi kitchen tana kallon shi bude fridge tayi taga kaza da egg da kayan miya
Murmushi tayi ta fara fida kayan da zata bukata
Wanki kaza tayi ta daura ta saman gas ruwa ta saka kadan ta dauko gishiri(salt) Tuna wa tayi inaa tana ye mata fada akan bata son saka gishiri da yawa spoon ta dauko ta saka spoon daya bare dai na kara kada yaki ji spoon biyu ta saka ta dauko magi kalla kalla ta saka ta saka kayan kamshi tuni gida ya fara kamshin wahala 🤣
Egg ta fashi guda 10 ta saka one cube tea spoon na salt ta saka ta kada kwan da kyau juyawa tayi gurin kaza ta zube ta ta zuba oil naman ta kama dauka tana saka wa cikin kwai sa'an ta soya
Bayan ta gama wanan soyar
Ta daura shikafa da miya ta yanka cabeji ta dafa kwai 5 ta hada cosolo sugar ta saka ciki da yawa domin bata ma saka spoon ba tunda zaki ni ae ba zai ye yawa ba
Zobo ta hada mai sanyi ta jira su akan Diner sai murmushi taki ye
"Nasan Yaya Aziz zai ji dadin abinci nan sosai"
Da gudu ta bar gurin ta saki watsa ruwa ta saka kaya light make up tayi ta nufi dakin shi
Knowking ta fara ye sanu sanu ama bai ce ta shigo ba kuma bai bude kofa ba abun ya bata mata rai sosai ta fara buga masa kofa kamar zata bala ta
Ranshi a bace ya bude kofa da nufin ya fara ye mata fada ganin kwalleyar ta yasa yayi shiru kamar ba zai ye magana ba ya ce
"Lafiya kiki buga man kofa.....!!??
Jikinta na rawa tace
"Yaya Aziz nasan baka ce kome ba na kirka maka abinci pls ka sauko kace zanji dadi idan kazo"

Bata jira amsar sa ba ta wuce.
Bata rai yayi ya rasa abunda zai ye yaji ko kar yaji wata zuciya ta bashi idan bai ji ba zata iya gaya ma dad tunda yarinya ce kome zata iya
Haka ya daure ya sauka
Ita kuwa tana bakin teble tana jiran karaso wan shi
Yana zuwa ta ja masa kujera ya zauna
Thanks kwai yace mata...
Fara serving insa tayi
Tana gama wa ta samu guri ta zauna ta buga uban tagumi tana kallon shi
Wani kamshi ni ya duki hancin sa lumshe idon yayi ashe dai ta iya girki let me test dai..
Spoon ya dauka ya kai spoon daya wani irin abu yaji wanda ba zai ma iya misilta shi ba
Kallon ta yayi
"Yaya Aziz kace kaza mana nasan tayi dadi sosai"
Fuskan shi za ban tausai ya debi kadan ya kai ga baki kokarin Amai yaki ye da sauri ta meki ta zuba masa zobo
Ta nika masa da sauri ya Amsa ya fara kora ma bakin shi yana hadewa bai ida hadiye sauran ba ya tuda shi
Kallon shi taki ye "lafiya meki damun ka meyasa ka tuda zobon baka sha ba"
Tashi yayi tsaye ya reki cikin shi sai kokarin ye amai yaki a dadafe ya hau sama yana taure ya reki cikin sa har ya kai dakin shi Amai yayi mai yawa sai da ya gama ya dawo kan gado yana mai da nunfashi
Wanan wani irin hauka ni abinci ko mutuwa......!!!!

Abun ba karamen bata mamaki yayi ba meyasa ya wuce yana kokarin Amai....?
Haura wa tayi sama ta shiga dakin shi,
Shikuwa yana kwance kan gadon shi sai mai da nunfashi yaki ye
Reki kugu tayi ta fara zazaga masa masifa
"Wanan wane irin iskan ce ni zan dafa maka abinci kazo nan ka kwanta duk uban wahalar da na sha oyah ka tashi muje kace ko na kawo maka shi nan"
Tashi yayi yana fuskan ta Ta

"How dare you... Waya baki izinin shiga man kitchen "

Sakin baki tayi tana kallon i kon Allah

"Kaji ka da wata magana ae ba maza aka sani da kitchen ba mata aka sani don haka nayi maka girki ka tashi muji ka karasa"
"No way. Bazan ce wanan kazamin abinci ba"

"Eh lalai Yaya Aziz ka rama mutani ni zaka ce ma haka"

Nuna ta yaki ye da yatsa
"Ki fita man daga daki idan ba haka ba zaki jiya a jikin ki"

Ita kuwa daman akwai ta da saurin fushi fita tayi daga dakin ta rufe masa kofa gam....
Dakin ta tashiga ta saka lock sai fada taki ye ita ka dai
Har dare yayi bata fito ba
Fridge inda ki cikin dakin ta. Bude ta dauki jus ta hada da biskit sallah tayi ta kwanta bacci mai dadi yayi awon gaba da ita

Washe gari..... A hankali taki bude idon ta saukowa tayi kan gadon ta sai meka taki ye gurin labude ta nufa ta bude ganin safiya ta waye yasa ta ji dadi lumshe idon ta tayi taja wani dogon nunfashi beautiful day ta furta
Nan ta shireri ce daman aikin ta kinan idan safiya ta waye tayi tsaye tana shakar iska mai dadi daga bisani ta watsa ruwa dakin Aziz ta shiga
Kallon shi taki ye yanda yaki baccin sa hankali kwance zugum tayi tana kallon shi wani abu ta tuna da shi tayi murmushi ta koma dakin ta da gudu banga abunda ta dauko ba ta koma dakin shi hawa tayi kan gado tana ye masa wani abu.. Dariya ta kamaye ta fita daga dakin
Nasan duk fushin ka idan ka tashi yanzu zaka dai na
Kwanan shi yaki ye cikin kwanciyar hankali.. Wayan shi ni tayi ringing reject yayi domin yana jin dadin baccin da yaki ye saki kira aka ye karamen tsoki ya ja wai wanan wanini ya ki kirana cikin daren nan
Dago fuskan shi yayi ganin haskin da ki cikin dakin shi yasan gari ya jima da waye wa
Dauka yayi yah ni
Banji abunda yace masa ba yace ya bashi 2mnt ga shinan saukowa
Sauka yayi kan gadon shi yana nishi guda guda.
Har zai shiga toilet ya watsa ruwa kuma sai ya fasa don baya son ya karya alkaware yace nan da 2mnt zai sauko kuma yasan idan ya tsaya wanka zai jima sosai haka ya fita dakin shi Tun a sama ya hango su sunkai su 15 waton abokan shi suna zauni kan kujera ko wanin su reki da cup in jus Nafisa kuwa sai murmushi taki ye masu
Kallon ta yayi "I hope bata lalata masu abun sha ba"
Abokinan da ya hango shi sama ya meki tsaye yana bugun na kusa da shi duba ango guda guda suka fara tashi sun ka saki baki suna kallon shi har ya karaso kusa da su kallon su yaki ye
"What happen meyasa kuki ye man wanan kallon kamar kun ga dodo"

Nafisa kuwa ba abunda taki ye sai dariya.
Kallo daya yayi mata ta saida dariyan ta.
Dukan su suka saka dariya. Aminu kuwa har kasa ya kai yana dariya..

Kallon shi yayi
"Meye abun dariya a ciki pls saje up"

Tashi yayi.
"Tell me what wrong with my face....!

Jan shi yayi har gurin dinner area gurin da aka laka mirrow ya kai shi ya nuna masa.
Wani ihu ya buga dukan su sai da suka razana dukan su sukaye shiru
Nafisa kuwa bata san lokacin da ta saki dariya ba
Karasawa yayi kusa da ita
"How dare you???
Murmushi tayi "Yaya Aziz kaga yanda kayi kyau kuwa kaga nayi maka gira na shafa maka eye shadow ji yanda bakin ga yayi kyau da na shafa maka jan baki ga blush so beautiful da mace kaki da kayi kyau sosai.. Shiyasa aki cewa soyaya dadi ae wanan duk cikin soyaya ni"
Bai san lokacin da ya daga hanu ya wanka mata mare ba sai da ta kai kasa
Aminu ya yo kan shi

"Aziz kana da hankali kuwa? Matar ka zaka mara"
"Enought Aminu bana son jin kome let me fresh up"
Haurawa yayi sama Nafisa kuwa ga kunya ga zafin mare da Aziz yayi mata kuka taki ye sosai dukan su sun tausaya mata tashi tayi ta dauko Hijab inta ta fita daga gida.......

*Tofa ko ina Nafisa zata ji muje zuwa*🚶🏻‍♀

*lipton girl*🥤
[12/17, 3:13 PM] 💙lipton girl💙: *AUREN YARINTA*
🍹🍹🍹🍹🍹🍹🍹🍹

*Daga Alkalamen*✍🏻
*Khadija s dogarai (lipton girl)*🥤

*A short story*🍹

________________________

https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/

*~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~*

*~We are bearer's of so golden pen🖊~*

*~we write assidiously perceive no pain~.*

*~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~*

*~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~*

*Addu'a Idan Ya Sauka A wani masauki a Halin Tafiya ko waninta.*

أَعُوذُ بِكَلِمَاتِ اللَّهِ التَّامَّاتِ مِنْ شَرِّ مَا خَلَقَ.
A'oothu bikalimatil-lahit-tammati min sharri ma khalaq.

Ina neman tsari da kalmomin Allah cikakku daga sharrin abin da Ya halitta.

*Dedication*
👇🏻

*HK nayi missing in ki over*😘😘😘

🌤Page 12&13.... 🍹

°°°°Ya kusan awa daya yana bathroom, da kyar ya samu ya goge kwalliyan da tayi masa, ranshi ba karamin bace yayi ba, shi yasa auren yarinta ko hauka baiyi ba, yarinya zata mai dani mahaukaci wanda bai san abunda yake nufi ba, bazan dauki wannan iskan ci nata ba zan gyara mata zama.

Kaya ya saka ya sauka inda ya tarar da abokan shi suna zaune suna jiran sa sai firan su suki ye.

Guri ya samu ya zauna, Muktar ya kamayi masa dariya.
"Mijin Yarinya har an fito".
Watsa masa harara yayi.
"Sorry".
Cigaba da hira sukayi.
Daga bisani suka koma gidajen su.

Muktar ne ya tsaya suna magana da shi.
Chapter 4 · 0% Book details