← Book details Auren Katin Kasa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
CHAPTER 8 OF 12

Chapter 60

Auren Katin Kasa Part 1 Complete Hausa Novel · about 9 min read

KANO NIGERIA
Salima tun sanda wayan rita ya mutu hankalinta ya tashi , ga samu ga rashi, kullum idonta akan motsin rita yake sbd tanason duk yanda za ayi ta lalubo charger kafin ta kamata, ganin yau kwata kwata bataji motsinta ba yasa tayi saurin fitowa, tun kafin takai bakin kofar dakin saiga rita ta yo corner din dakin su, hannunta riqe da kayan da ta sato daga dakin khady, ganin salima wanda dukta jeme a tsaye gaban dakinta yasa ta saurin cewa ‘’keeee what are you doing here, wayace ki fito daga dakin ku?’’ juyowa salima tayi afurgice tace ‘’dan Allah kiyi hkuri daman yunwa mukeji shine nazo na fada maki’’..tunawa da abubuwan da ta kwaso a hannunta kuma batason salima ta gane yasa tace ‘’jeki zan kawo maku’’..da sauri kuwa salima ta koma daki don kada ta rafko ta.

Haka suka dunga kame kame ita da rita dukda har yanxu bata kamata rudu rudu ba, tun salima na saka rai akan charger harta hakura kawai ta aje wayan cikin kayansu na sawa ta boye.
 
Daddy kuwa duniya sabuwa ya bude, don wannan gidan nasu salima da amra na gadon su, shi ya bada haya wanda tashin farko ya samu kusan 100 million for rent duk shekara, wannan abu yayi mashi dadi sosai, daga gefe kuwa yana sane da su salima da halin da suke ciki, ya kyalesu ne don dasu zaiyi threatening amra domin ta biyashi kudin da yake tura mata, ya bari ne sai sun gama wahala yanda idan ta gansu hankalinta zai tashi kuma daya tambayi abu wajenta bazata qi bashi bashi ba, sannan yana jiran time ne kafin ya fara aiwatar da qudurun shi akansu.
Wannan Kenan…………..
 
 
Abuja Nigeria
 
The taura estate
Babban gidan dake ciki taura estate motar da ta dauko ALIF-SUDAIS daga airport ta kutsa kai ciki, gidane mai dauke da part biyu daya babba daya karemi, tundaga bakin gate zaka gane gidane bana qananun mutane ba, ahankali driver ya soma bude bayan haddaddiyar lexus, farar kafar wanda ke cikin motor ne ya bayyana, ahankali ya karasa fitowa, kyakyawan babban mutumi ne sanye da kundura irin ta masarautr kasashe waje na larabawa kana ganinshi zaka san badan Nigeria ba ne, malam labaran wanda ke zaune gefen bencin mai gadi ne ya dago yayi ma mutumin kallo daya, ahankali ya soma dafe kanshi don idon har ya fara tuna wani abu saiya dafe kanshi dake sarawa, da sauri mai gadin ya karasa ya fara kwasar gaisuwa wajen babban aminin mai gidan, Alhaji kabiru wanda ke saukowa daga benen gaban gidan ne ya karaso gaban abokin nashi, fuskarsa dauke da murmushi sukayi musabaha ta manya,anatse suka fara gaisawa, ahankali alh kabiru yayi mashi iso har cikin tamkeken parlor wanda ke dauke da hoton AMAR DA AMAN DA KUMA AMMA, zama alif yayi akan kujera 3 seater sai kabiru ya zauna gefen tashi wadda itama 3 seater dince suna fuskantar juna, kara gaggaisawa sukayi sannan ya umarci da afara kawo ma baqonshi abin sha.

Amma wadda ke tsaye gaban gas cooker tana juye chicken peper soup ta kalli mai aikinta tace ‘’da alamu baqin Alh sun iso, ki aje sharan da kike ki wanke hannunki ki fara kai masu drinks da ruwa kafin na fito’’, amsa mata tayi da to sannan ta wuce tayi abinda aka umurceta, anatse aka shirya komai shaqe gaban su, kafin ammin ta fara fitowa daga kitchen din, sanye ta ke da doguwar riga ta tsadadden lace, wadda ta amshi jikinta sosai kuma tayi mata kyau ba kadan ba, tayi daurin ture kaga arziki wanda ya fito da fuskarta sak irin ta amar , karasowa tayi suka gaisa da alif baqon alh kabiru wanda itadai tunda take da kabiru bata taba sanin ina suka hadu ba, shidai alif din duk farkon shekara sai ya zo kasar kuma zuwan nashi lokaci guda babu sanayya, tun tana mamaki hartazo kuma ta cire kanta daga cikin mamakin hakan don ba huruminta bane.
Suna gama gaisawa ta wuce sama wanda kusan bene uku ne,sallah kawai tayi sannan ta fara laluben aman, don yanxu kwana biyu ya dan natsu yana dan zaman gida,baya fita kwata kwata,kiranshi tayi kusan sau biyar bai dauka ba ganin haka yasa ta kyaleshi kawai tayi kwanciyar ta don tunda alh kabiru ya sanar da ita zaiyi Baki bata zauna ba.

Bata wani dade da kwanciya ba saiga alh kabiru ya shugo, tana ganinshi tayi mamaki don bai fiye shigowa dakin nata ba don ita kanta bata son haka, hannunshi riqe ta milk mai sanyi, karasowa yayi da fara’arshi sannan yace, ‘’wifey kinsha gajiya nasan baki saka komi ah cikinki ba, ga wannan na kawo maki’’..abinda yake burgeta ta wani bangare da kabiru, akwai shi da soyayya da nuna kulawa, dukda wani sa’in tana jin nauyin karbar ko wace irin soyayya daga gareshi don hakan yana tuna mata da baban amar.

Godiya tayi mashi sannan ta karba, saida ta shanye sannan ya umurceta data kwanta sannan ya lulluba mata bargo don ta samu ta huta, cikin yan mintuna kadan bacci ya dauketa kuwa mai nauyi sosai.

Kabiru na fita ya sauka qasa sannan ya umurci yar aikinsu lantana data je dayan part din domin gyarama baqonshi, tana gamawa kuwa yayima abokin shi iso zuwa dayan bangaren wanda nanne bangaren sa lokacin da matarshi ta farko wato amina maman aman ta zauna kafin ta rasu.
Ba laifi part din akwai dan girma don yana dauke da dakuna biyar da katon parlor, kofofi biyar ne duk kusan iri daya saidai kofa dayace akayi mata wani smart opener handle, suna shiga ciki basu wani tsaya ko ina ba suka wuce dakin, saida alif ya saka thump print dinshi sannan shima kabiru ya saka nashi suka kutsa kai ciki.

Karfe hudu da rabi daidai na yamma yayi ma amra da haifa a rosalle private lounge, dan karamin waje ne kamar sauna, da kuma spa sai wajen shaqatawa, zama sukayi ta wuraren kujerun wajen, kowannensu zullumi ne tap a zuciyoyinsu hade ta kuma dan fargaba, sun dauka wajen minti talatin wajen karfe biyar da rabi saura, ‘’are you amra?’’ jin an kira sunan amra yasa suka dago da kansu atare, wata matace wadda akalla zata kai shekaru 35 harda yan kai, miqewa sukayi atare gaba dayansu suna kallonta, sanye take da kayan ma’aikatan wajen, kamarma itace ke handling wajen spa din, murmushi tayi masu sannan tace ‘’lets go’’..atsorace suka fara binta har cikin sauna, inda ta basu kayan spa suka saka bathrob mai laushi, kofar dakin sauna shige suka bita har ciki, wuri suka zauna itakuma ta fara hada incense saida ta gama tukunna ta zaune gefensu tace ‘’na barku a zaune tun daxu ko, daman inason na tabbatar da gaske kuke kafin na bayyana agabanku,’’..murmushi sukayi atare sai a lokacin suka danji dama dama, kallonta haifa tayi sannan tace,’’mune muka kiraki jiya ni sunana haifa wannan kuma amra’’..ta nuna amra, saida suka gabatar da kansu kafin ta tambaye su dalilin nemanta da suke, nan suka fada mata komai game da buqatarsu basu boye mata. Shuru tayi nayan mintuna kafin ta dago tace ‘’na tausayama halin da amra take ciki, amma ni ayanxu na daina harkar taimakon samun katin qasa, don kamar yanda kuka gani ni worker ce anan, wannan ne abinda nake yi don na taimaki kaina’’..shuru amra tayi hawaye na zubo mata ta tsugunna har qasa gaban matar tace ‘’aunty ki taimake ni, wallahi qanne na suna cikin mawuyacin hali, inason taimakon su’’.. tana kaiwa ta fashe da matsanancin kuka sosai, kallonta matar tayi, zuciyarta ta gama karaya tace ‘’get up please kinji, zan taimaka maki, amman duk abinda ya buyo baya babu sunana aciki,kuma baku sanni ba baku taba ganina ba sbd I can’t risk my own life and my children,’’..miqewa amra tayi tana share hawayenta sannan suka fuskanceta dakyau suna sauraron abinda zatace ‘’first of all, shi katin kasa na nan dubai yana da wahalan samu sosai, na farko akwai hanyar aiki wanda akeyima government for 30 years kafin asamu, na biyu kuma auren dan kasar wanda shi kuma shekara biyar akeyi kafin asamu shikuma dole ki biya wanda zai aureki kuma kudi ne mai yawa sosai, na uku shine idan kinada wanda kike soyayya dashi kuma sai marriage consent group management sunyi bincike akan soyayyar taku don ke ba yar qasar bane, hadarin wannan shine yawanci kasarnan basa yarda da auren wanda ba cikin al’adarsu yake ba,so if acikin danginshi an samu wanda basu amince da auren ba koda kuwa yaro ne dan shekara hudu to fa auren bazai yuwu ba,ahaka ma acikin uae marriage consent group idan aka samu wanda bai gamsu da soyayyarku ba to shima hakan zaisa aqi approving din katin kasar.

Jin wannan tashin hankali yasa suka kasa cewa komai, haifa ce tayi kokarin tsaida natsuwanta tace ‘’yanxu sister babu wata hanyar?” kallonta matar tayi sannan tace “gaskia babu ayanxu saidai ku zabi daya aciki, zanyi kokari ni kuma daga nan na taimaka maku yanda zaku tafiyar da komai cikin sauqi dan komai yana da wahala dole sai tayi preparing kanta’’, …kallon amra matar tayi sannan tace ‘’why are you silent, I thought da bakinki kince kinason taimakon yan uwanki, har kin karaya ne tun daga yanxu, in kinsan zaki karaya dakin fada min tun wuri da bazan tsaya ba ina bata lokaci na ba’’ mikewa tayi zata tafi da sauri amra ta riqo hannunta tace ‘’dan allah aunty ki tsaya, na amince ki zabamin duk wanda yafi sauqi don na taimaki yan uwa na’’…..jin haka yasa matar ta dawo ta zauna kusa dasu tace ‘’okay, yanxu dai aikin government bazai yuwu ba, so kinada wanda kikeso anan kuma dan qasar??’’..girgiza mata kai amra tayi alamun ah ah,..nunfasa matar tayi sannan tace ‘’okay yanxu kinga guda biyu cikin abinda nayi listing bazai yuwu ba, yanxu last option, kinada 50,000 dollars da zaki iya badawa, shima zanyi kokari ne na roka maki…’’ jin wannan uban kudin yasa amra da haifa zaro ido atare sukace ‘’50,000 dollars’’!!!!!...kallon kallo sukayi fuskar amra kamar tayi kuka tace ‘’ni arayuwata ban taba riqe less than 10,000 dollars ba’’..haifa ma hankali atashe tace ‘’ni yanxu konaje na nema wajen abu bazan taba samu ba’’…kallonsu matar tayi sannan tace then I can’t help you guys saidai idan tsoho zaki aura, ana samunsu beggers dinnan, idan muka samu wani mai sauqi zai karba 30,000 dollars,’’…jin haka yasa haifa saurin cewa no bazai yuwu ba, banda homeless mutane, girgiza kai matar tayi sannan tace ‘’well babu abinda zan iya maku yanxu’’ ta tashi ta nufi hanya zata wuce, shesheqar kukan amra ne ya tsaidata ahankali ta tako har gabansu sannan tace,’’there’s only one solution and it’s the very risky of all, amma shi a cikin shekara daya zaki samu katin qasa and naji ance bashida wani tsauri da long process’’..jin haka yasa suka miqe suna kallonta itama kallonsu tayi sannan ta cigaba’’the only last option is getting an army officer, be it senior or junior, that’s the only solution’’ tana kaiwa nan ta fice abinta tana cewa ‘’duk yanda kukayi deciding you can contact me’’…..hankali atashe suka fito daga sauna suka chanza kayansu wanda suka aje ah spa lockers din wajen,…gida suka wuce kowannen su zullumi cike aciki zuciyansu.
 
Aranar amra bata samu issanshen bacci ba, tabbas solution daya gareta wanda shine neman army officer, amma yanxu wata sani da zata nema taimakon wajen shi, har wajen karfe uku na dare bata runtsa ba, salla ta mike tayi sannan ta roka allah ya kawo mata mafita cikin gaggawa. ✍️✨***Auren Katin Kasa ***✨✍️
(Unexpectedly falling❤️🇦🇪)

Story and written by:
QueenMarh👸🏼


Paid book 📚
Chapter 8 · 0% Book details