Chapter 54
Auren Katin Kasa Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read
Bangaren rita kuwa tana aje wayan ta cigaba da wanke wankenta, Allah Allah take ta gama ta tafi wajen khady domin kai mata sakon molly data bata ta sayo mata, wato itama yar hannu ce shiyasa take kokarin siyeta da abubuwan mayen, ita kuwa khady sauqi ne yazo mata har gida don yanxu rita ce aminiyarta don itake kawo mata komai kuma ita ke mata introducing abubuwa sabbi wanda hakan ba karamin dadi takeji ba.
Saida ta gama gyare gyare sannan ta aje wayan nata a daki tayi wanka sannan ta shirya cikin casual dressing dinta na kafirai, riga da mini skirt sannan ta fito ta wuce sama wajen dakin khady, saida kwankwasa mata kafin ta shige ciki, akwance ta tarar da ita, ganin rita yasa khady mikewa tana fadi ‘’my girllll, hope todays molly is powerful’’ murmushi rita tayi sannan ta zauna gefenta tace ‘’ma, todays molly is so powerful but the money high o,’’ jin haka yasa khady miqewa ta wuce wajen da take aje hand bag dinta, anatse ta zaro yan dubu dubu guda biyar sannan ta dawo gaban rita, hannu rita ta miqa ta karba, saida ta kirga kafin ta zaqulo yar takardar daga kwankwasonta ta bata, hannu na rawa khady ta fuzge sannan ta fara kokarin budewa, tana ganin molly tayi maza ta bude ta shaqa, wani irin bari jikinta ya fara sannan ta afka abakinta, ko minti biyar batayi ba ta lula, ruf ta fadi don wannan mai shegen karfi ce, ganin khady ta jeme yasa rita dariyar mugunta tace ‘’shegun yara kunfi kowa iya kananun iskanci, iyayenku na daki kuma kuna daki kuna naku iskanci,’’ ahankali rita ta fara bude jakar khady, saida ta yasheta tass sbd tasan cewa idan har ta farka bazata tuna duk wani abu data aje ba, saida ta kwashe yan zobinan gold dinta sannan ta wuce drower dinta ta kwashi English wears dinta wanda suka mata sannan ta tattara komai waje daya ta dawo gaban khady ta kuma kecewa da dariya sannan tace ‘’tunda har kin lula nima saina kwashi rabona,’’
Saida rita ta kwakuleta tass kafin ta fice daga dakin, khady wadda azaba ta fara dawo da ita daga cikin hayyacinta yasa ta fara aman wahala.
Bayan fitar rita kuwa salima tana ankare da ita hakan yasa tayi saurin wucewa cikin dakinta ta dauki wayanta sannan ta dawo dakin su, ahankali ta soma laluben number amra wadda ta rubuta acikin paper kafin akwace masu wayan data bar masu, hakan yasa tayi saurin lalubar number tayi dialing, kusan sau biyar wayan ba’a dagawa hakan yasa salima ta fashe da kuka, tana cikin kukan taji karar kofar rita, hankali atashe ta mike tana labewa jikin kofar har saida rita ta rufe kofar dakinta, hankali atashe ta jawo wayan ta kashe wayan sannan ta wullata cikin drower, rita kuwa agajiye ta dawo daki bata bi takan wayanta bama ta kwanta abinta.
Washe gari duban duniya rita tayi ma wayan ta, amma bata samu ba hakan yasa hankalinta tashi sosai, ta koma dakin khady koda ta shiga bata sameta ba, haka yasa ta juya zata fuce jin kakarin amai yasa ta tsaya sannan ta wuce toilet din khady, zaune ta tarar da ita tana kwara aman wahala, saida rita ta taimaka mata tayi wanka sannan ta futo, ta kwanta.
Rita kuwa tsabar dariyar mugunta dake ciyo ta yasa tama manta da batun waya.
Kwana hudu Kenan rita na neman waya harta gaji ta shirgama khady karyay cewa saida wayar ne zata samu ta dunga karba mata molly, haka yasa khady ta shiga dakin mummyn su haj kareema, ta kwaso kudi masu yawa acikin drower ta lokacin haj kareem ta shiga toilet, saida ta diba mai isarta sannan ta futo ta wuce daki, nan ta tarar da rita tana jiranta. Duka kudin kuwa khady ta bata, batama tsaya kirgasu ba.
Rita kuwa dadi kamar zai kashe ta, tana komawa daki ta kwashi dubu biyar sannan ta boye sauran daman ranar zataje sayan groceries don haka tayi shirin tafiya da dubu biyar dinta don ta sayo sabuwar waya.
Salima kuwa saida ta jera kwana biyar tana kiran amra bata samunta don duk sai dare take samun yin wayan don tsoro takeji sosai kar akama ta tana wayan. Bangaren amra kuwa duk cikin dare sai an kirata da wannan number da matar tace wrong number, ganin hakan yasa tayi tunanin qila mistake suke suna kiranta, wanda yawancin kiran sai dare ake mata kuma lokacin tayi bacci.
Bayan kwana biyar salima kullum saitayi kiran number amra, yanxu tashin hankalinta charging wayan da yake neman mutuwa gashi tana tsoron zuwa dakin rita dauko charger don karta gane cewa itace da dauka wayan ta gashi jikin salim yayi wani mugun tsanani don yanxu abin nashi harda seizure idan ya fara saiya dauki wajen minti ashirin kafin ya dawo daidai. ✍️✨***Auren Katin Kasa ***✨✍️
(Unexpectedly falling❤️🇦🇪)
Paid book 📚