Sashe 4
Alakakai Complete Hausa Novel · about 8 min read
gashi kuma idan nabude tagar dakin ruwa yajikani. Nasake mikewa tsaye naci gaba da safa da marwa hakika indai har ba dauke ruwan nan akayiba to da kyar zan iya barci. Gashi kuma tuni karfe dayan dare ta gota. Dakin danake ciki matsakaicine kamar dai sauran gidajen gwamnatin dake gurin. kujeru ukune kacal adakin kamar aya gami da tsohon gadon katakon dake dakon katuwar sabuwar katifar dana saya kwanaki biyu da suka wuce. daga bangaren arewa na dakin akwai talabijin mai kala da bidiyo asamanta. sannan kuma asaman bidiyon fulawace ta roba acikin kofin tangaran Amatsayina na TAURARON JARUMAN WASANNIN FINA-FINAN HAUSA dole ne naga nayi kokarin kawata dakin danake kwana koh don taren bakin dake tafaman sintirin kawomin ziyarce-ziyarce dare da rana. Yawan bakin da suke kawomin ziyara ne yasa kawuna ya waremin bangare guda agidan ya sanya katanga tsakanina dashi domin nasamu damar ganawa da bakina, tunda dai haryanzu banyi aure ba . MAFARIN RIKICIN KENAN WANNAN RUWAN SAMAN. [20:28, 1/19/2018] +234 806 858 0203: ALAƘAƘAI-06 . (m) Nazir Adam Salih . Na koma bakin gadon na zauna sannan na cire rigata na kwanta, inajin zazzafar iskar da fankar dakin ke busawa akan fuskata sannan kuma lokaci guda ina mai adu'ar Allah yasa a dauke ruwan saman koh na bude kofar dakin nasha iska. Na rufe idanuna amma barci ya kasa daukata gashi kuma gobe tashin asuba zanyi domin awashegarin ne zamu fara sabon fim din kamfanin SINAD PRODUCTION mai suna MUTUWA DA MAFARINTA TAKE TAFE, amatsayina na jarumin fim din dole ne nasamu isashen bacci domin na sami nutsuwar yin abin da daraktana yace nayi, toh sai gashi kuma zafi na neman hanani barci. toh ashe abun daban saniba shine bayan zafin dake addabata akwai wani al'amari daban dazasu kawo wa shirin fim din nawa matsala. . Ban san sa'ar da barci ya daukeniba acikin barcin ne nayi mafarki wai ana ta bubbuga kofar dakin danake ciki nayi firgigit na farka ina mutsutstsuka idanuna sannan ne to naji ana buga kofar dakin danake kwance nayi shiru cikin mamaki ganin mafarkin nawa ya zama gaskiya sannan kuma nayi mamakin shin wanene ke buga min kofata cikin wannan talatainin dare. Nadubi agogon dake makale ajikin bangon dakin wanda ke dauke da hoton yan wasan da muka shirya wasan fim din DAREN MUTUWA dasu karfe biyu da rabi na dare Tsoro ya kamani domin kuwa banga wanda zai bugamin daki ba cikin wannan daren sai koh BARAWO Aka sake bubbuga kofar dakin Das Das kamar ana bugun kwarya da sillan kara Nayi mamakin jin bugun kofar dakin babu karfi domin kowane ne ke buga kofar dakin hakika yana tausayamata aka sake bugawa raf raf raf har sau uku. Gumi yafara kwararowa kan fuskata hakika acikin mafiya yawan finafinan danake fitowa ni jarumine mai zafi marar tsoro to amma fa azahiri tsoro ne dani kamar farar kura dan karamin yaro ma yana iya tsoratani da bindigar wasan yara saboda tsorona. . ABUN TSORO SAI MA GABA JARUMI HILAL [20:28, 1/19/2018] +234 806 858 0203: ALAKAKAI-07 . TA'AZIYYA GA IYALAN DAN UWA ABOKIN CHART WANDA DUK POSTING DINA SAI YA KARANTA YAKUMA YI COMMENT IBRAHIM ABUBAKAR . ALLAH KAYIWA IBRAHIM ABUBAKAR KADUNA GAFARA KASA ALJANNAH CE MAKOMARSA DAMU GABAKI DAYANMU AMIN . (m) Nazir Adam Salih . Me yuwuwa kawuna ne nace da kaina to amma kuma ban yadda da kalaman da zuciyata keyiba domin nasan tun da kawuna ya ware min bangarena daban bai taba koda lekowa ba idan kuwa shine to nasan tabbas ba lafiya ba to amma kuma idan shine ai kiran sunana zaiyi gami da kwankwasa dakin, jikina ya sake daukar bari na juya a hankali na dubi 'yan kayan dake dakin indai dan wannan ne sai nabasu su tafi. Acikin fina finan danayi nasha arangama da barayi da yan fashi na daddakesu wasu kuma kamasu nake in daure to amma wannan daban wasane, yanzu kuma shine zahiri tunda gasu akofar dakina, Na zargi kaina saboda barin kofar gidan danayi abude,ko da yake daman kuma kullum ahaka take kwana saboda maziyarta da abokan arziki dasuke yawan zuwa gurina da daddare to amma ba karfe biyu da rabin dare irin wannan ba........... Raf Raf Raf aka ci gaba da kwankwasa kofar Na yunkura hantar cikina na rawa na nufi kofar dakin, ina ta salati da salalallami. Wai.....wai wane ne? Nace muryata ashake ban iya shaida muryar amatsayin tawa ba. Maimakon abani amsar sai naji an sake kwankwasawa, Wa......Nene? Na sake kuma tambayar shiru ba abani amsa ba haushi ya kamani sannan sai na tuno da fim din DAREN MUTUWA Muntaba wani sin mai kamar wannan inda barayi suka zo suna kokarin balla kofata nikuma na bari sai da suka gama jingina ajikin kofar sannan na bude suka zubo cikin dakin kamar an hankadosu nikuma nabisu na daddakesu. To yau ma zan kwatanta. Nace cikin zuciyata Saidai kuma wannan karon inhar Allah yabani sa'a suka zubo cikin dakin to tsallakewa zanyi na gudu. . Aka sake kwankwasa kofar awannan karon da karfi. jin haka shiyasani tunanin komai bugun kofar kafadarsa ya jingina ajikin kofar yake kokarin balle kofar dakin. Nan da nan nayi wuf na zare sakatar dakin na janyo kofar da karfi. Sai naji sakayau kamar na janyo gadon kara babu abin da yabiyo baya. . Ashe dai ko agaske jarumi ne wata zazzakar murya tace dani Nayi sororo ina duban abin haushin dake tsaye akofar dakin cikin mamaki daya sani wangame baki fayau ina dubanta Atsaye abakin kofar sanye da bakar riga doguwa da jan lullubi jikinta na digar ruwan saman daya doke ta, wata mace ce ajin farko a jerin kyawawa. Shin ko na iya shigowa, sanyi nakeji gaskiya, gashi kuma duk kayana sun jike Na sake kallon katuwar akwatin mai taya dake hannunta na dama Nace Malama Lafiya? Daga ina kike Meya kawo ki gidana cikin wannan daren? Ta dubeni sannan ta jefeni da wani lallausan murmushin Allah kashemu dan dadi, tace Lafiya kalau HILAL ,daga wata nisan duniya na tawo domin kawai na ganka, na dade ina ganin finafinanka ina kaunarka raina na Begen ganinka. Shine naga bazan iya jurewa ba sai nazo naganka tun daga maiduguri Nake motar mu ce ta lalace ahanya shine mukayi dare yanzun ma direban motar ne yaga nayi dare shine na roke shi yakawoni nan , Tayi shiru tana dubana. Jarumi Hilal, Ina fatan yanzu dai ka gamsu Shin na iya shigowa, sanyi nakeji wallahi Hilal. Na matsa gefe guda ta shigo cikin dakin zuciyata cike da tunane tunane ta ajje akwatin atsakar dakin sannan tajuyo ta dubeni. In bazaka damu ba dan Allah nunamin inda bandaki yake so nake na shanya kayana duk sun jike jagaf. To ke kuma ki zauna dame Ina dubanta baki bude Tayi murmushi Sai na zauna aciki idan sun sha iska saina mai dasu jikina nafito, Sannan fa takura min idanu tana dubana ko kiftawa batayi Oh Hilal yau dai Allah ya nunamin kai wallahi kada kaga irin son danake ma duk cikin yan wasan hausa babu wanda nake kauna kamar ka zakayi mamaki idan nacema acan maiduguri akwai kawayena da suke kirana da suna HILAL tayi shiru tana dubana me yuyuwa koh dan ganin duk surutun da takeyi ban tanka mata ba Hilal yaya kake yimin irin wannan kallo ne, koh haryanzu baka amince dani ba? Bahaka bane malama amma abin dake bani mamaki shine zuwanki cikin wannan tala-tainin daren kuma...... Ta katseni. Nace dakai motar muce ta lalace, Haba Hilal nifa bakuwar kace. To naji na yarda amma kuma yaya akayi kika san gidana. Haba hilal Mutane nawane suke ziyartarka arana daga jihohi daban daban kawayena nawa ne suka zo gurinka ai kwatancen gidanku ba wuya tunda agidajen gwamnati kake ga kuma lamba daman kuma ance kai kadaine abangarenka daban amma kada ka zargeni agurin maziyartanka naji. Mukayi shuru muna duban juna sannan sai tasake cewa Nunamin bandakin Hilal kada mura ta kamani da wannan jikakken kayan jikin nawa. zo muje nace da ita na shiga gaba tana bina abaya Bandakin gidan acan baya babban falon yake saidai kuma zaka iya shiga bandakin tacikin falon akwai kofar dazata kaika ciki Ga kofar nan Nace da ita ina duban yala-yalan gashin kanta Hakika kyakkyawace ajin farko ta dubeni sannan ta sake jifana da murmushi ta shige bandakin ta rufo kofar gararamm a daidai lokacin ne toh aka saki wata aradu Rugugugu......... . INA MAI AMFANI DA WANNAN DAMAR A YAU GURIN MIKA TA'AZIYA TA GA MEMBERS DIN SOYAYYA RAYUWA GROUP FACEBOOK & WHATSAPP DAKUMA IYALAN IBRAHIM ABUBAKAR KD BISA RASUWAR SA INA ROKON ALLAH YA GAFARTA MASA YASA ALJANNAH CE MAKOMARSA YA BAIWA YAN UWA DA IYAYEN SA DA MATAR SA HAKURIN JURE WANNAN GAGARUMIN RASHI DA SUKA YI ALLAH YA YI RIKO DA TAIMAKON YARAN DAYA BARI TABBAS IBRAHIM BAZAMU TABA MANCEWA DA KAI BA ADUK LOKACIN DA MUKA TASHI YIWA KAWUNAN MU ADDU'A . Hadiza Sirajo INA TAYAKI ALHININ RASHIN ABOKI NAGARI [20:28, 1/19/2018] +234 806 858 0203: ALAKAKAI-08 . (m) Nazir Adam Salih . (c) Yarima Gangariya . MASU KARATU KUYI HAKURI DA WASU YAN KURA KURAI DA ZAKU CI KARO DASU TUN DAGA NA DAYA ZUWA NA 10 TAYANDA WASU SHAFUKAN ZAKU GA NA MAIMAITA SU KUMA HAKAN YAFARU NE SABODA WASU DALILAI NA KUSKUREN RUBUTU DANAYI TUN A FARKON LABARIN KUMA ZAIYI WAHALAR WARWAREWA SAI AKASHI NA 10 ZAREN LABARIN ZAI DAWO DAIDAI NAGODE. AMMA INA NEMAN AFUWAR KU . Na sake mikewa tsaye akaro na biyu naci gaba da safa da marwa cikin dakin. In har ba dauke ruwan akayi na bude tagar dakin ba zaiyi wuya in zan iya barci. Banda wannan kuma al'amuran da suka faru ma a yammacin ranar sun isa su hanani barci na daga kaina na dubi agogo karfe daya na dare daidai. . Sa'ar da muka baro kamfaninsu alhajiji (Sinad Production) sai Lauriyya tace saita rako ni har gida. Kiyi hakuri lauriyya kinsan yanzu ba kamar da bane sa'ar danake agidana yanzu kinga agidan yayana nake kare. Duk da yake dai bangarena daban ne to amma fa mutanen unguwa sun gama sa min ido dan sanin kanki ne duk yan fim yan isa aka daukesu ana son mune ana kuma kyamar mu. Lauriyya ta fahimci abinda nake nufi. Toh hilal