← Book details Alakakai Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 15

Sashe 3

Alakakai Complete Hausa Novel · about 8 min read

wani abu danake ganin zai iya kawo min wasu dunkulallun kudi saida na sayar dasu. Acikin makonne na biya jama'a da dama basussukansu ni kuma nakoma gidan yayana inda daman tun farko acan nake kafin na samu abin duniya UNGULU TA KOMA GIDANTA NA TSAMIYA . To saidai kuma abin bakin ciki duk da kadarorina dana sayar basu isa biyan bashin da ake bina ba. Gashi kuma haryanzu babu wani labari daga gurin masu shirya fina finai wadanda ada suke ta bina agindi agindi suna rokona danazo na fito musu a fim yanzu da sun hangoni sai su fara buya domin duk labari ya ishesu acikin kankanin lokaci kamar wutar daji cewa wai kasuwar fim ta daina yi dani......... Wannan duk wani Abune daya shude Abaya. . LABARIN AKWAI DAMBARWA KU DAI KASANCE DANI [20:27, 1/19/2018] ‪+234 806 858 0203‬: ALAKAKAI 03 . (m) Nazir Adam Salih . Wannan duk wani abune daya shude abaya . Hilal aka kira sunana abaya na juya firgigit Lauriyya ce har yanzu tsaye ajikin makunnar lantarkin tana kallona idanunta sunyi rau-rau kamar zata fashe da kuka. Tunanin me kakeyi Hilal? Ta tambayeni bakinta na rawa na juyo ahankali hannayenta harde da juna makale abayanta. Kikace Emaka yazo nemana? Lauriyya ta gyada min kai bata yadda ta bude bakinta ba ina tsammanin da tayi magana alokacin fashewa zatayi da kuka. Sauran cikon kudin kwalin kaset din daya buga mana yazo karba nace da ita batareda na iya hada ido da ita ba. Ban da shima su shafi'i sunzo wai karbar kudin kayan kwastum... Haladu da sabo da ma duk sunzo maganar cikon kudinsu... Tsahon lokaci babu wanda ya sake cewa kala nida ita can bayan wasu yan dakiku sai lauriyya ta matso daf da inda nake tsaye inata faman karatun wasikar jaki ta dafa kafadata tace dani. Juyo ka dubeni hilal... Ina da shawarar da nake tsammanin me yiwuwa ta zama mafita agareka. Adaidai lokacin aka saki wata katuwar aradu data girgiza ofishin sannan wata walkiya mai tsananin haske ta harko cikin ofishin duk kuwa da kwan lantar dake ci. . ***** ******* ****** ****** *** . Na zurawa lauriyya idanu ina kallonta sannan kamar wani sahorami domin bansan me zance da ita ba ganin bance da ita komai ba sai ta dafa kafada na sannan ta sunkuyo da kanta tace dani. Ka gafarce ni hilal ba wani abu ne yasa nake tare dakai ba haryanzu sai don...... Ta kasa karasawa tausayinta yakamani haryanzu iska ake ta ketawa awaje saikuma sautin yan kananan kwayoyin ruwan da iska ke ta alakoro dasu akan rufin gidaje kafin isashshen ruwan ya karaso. Cigaba lauriyya.... Ke nake sauraro nace da ita a sanyaye lauriyya tayi dan jim na yan dakiku kana saitace cikin karyayyyiyar murya. Kau.....narka ce ta rike ni har zuwa wannan lokaci ina tare dakai.... Duk abinda ya same ka kamar ni ya shafa ne domin lokacin danazo garin nan kai ka karbeni ka mutuntani ka maida ni mutum. Banida cewa akan abinda tace dan haka sai nayi shiru ina sauraron abinda zataci gaba da cewa. Hilal.....abinda nake kokarin baka shawara akai shine me zai hana muje kamfanin fina finan su ALHAJIJI me yiwuwa...... Bata karasa ba sakamakon sauyin yanayin data gani karara a fuskarta. Haba lauriyya wace irin magana kikeyi ina ni ina wani Alhajiji kuma? Lauriyya ta dada matsowa gareni kamar zata kankameni. Hilal ka saurari abinda nake son fada ma dan Allah nsan dole bazakaji dadi ba domin zan saka yin abinda baka so ba. Ta dan saurara. Duk acikin yan shirin fim shi kadai ne nasan baya bakin ciki dakai.... Shiyasa tun jiya nake tunanin me zai hana muje mu gani ko zai samo ma wani fim din ajefaka aciki koda a mataimakin jarumi ne saikaga kadan samu wani abu ka rage bashin dake kanka. Tayi shiru tana dubana. Nayi dim na yan dakiku ina jujjuya kalamanta acikin zuciyata. Lauriyya abinda nake so ki lura dashi shine mutumin nan fa babu irin nacin da baiyi min ba sa'ar da nake kan ganiyar tashe na akan nazo nayi masa jarumi a finafinansa amma naki... Ke din nan da kanki sau nawa yana bugo waya ina cewa kice dashi bana nan....? Duk da haka dai hilal..... Haka nan zaka daure muje ai durkusawa wada ba gajiyawa bane ni nasan ba zai wulakanta ka ba tunda dai koda ada din ma ai ba fitowa kayi kiri kiri kace dashi bazakayi masa fim din ba. Na girgiza kai sa'ar danaji tayi shiru. Lauriyya ban ki shawarar ki ba amma abinda kamar wuya wai gurguwa da auren nesa ina ta faman nuna miki Annabi kina runtse idanu abinda nake so ki gane shine tuni labari ya watsu aduk fadin duniyar fina finan hausa cewa kamfaninmu ya fadi bama wani tasiri akasuwar fim shiyasa kikaga fa kowa ya gujeni an daina rububin sa ni a fim domin ana ganin nazama asara. To in dai kuwa hakane wacce irin hauka ce ta hau kan alhajiji da kike tsammanin zai sani cikin fim dinsa in janyo masa asara sa'ar danayi shiru saina lura tuni hawaye ya fara sartu akan kumatun lauriyya. . Daina cewa zaka janyo masa asara Hilal....abin da nake so ka gane shine ba kaine ka daina tashe ba kamfaninmu ne ya karye ya daina tashe amma ni nasan ita duk duniyar nan basu yarda ba ni nayi imani da cewa kana nan akan HILAL dinka jarumin jarumai. Kukanta yafara bayyana a fili. Nayi sauri na rike hannayenta nace da ita a sanyaye. Daina kuka lauriyya shikenan na yarda zamuje to amma kuma wani hanzari ba gudu ba. Lauriyya ta dago kai tana share hawaye cikin rashin fahimta. Yanzu idan mukaje bamu dace ba kinsan fa labari zai watsu aduniyar fina finan hausa cewa tsohon jarumin jarumai yafara tallan kansa..... Wacce illa kike tsammanin hakan zata janyowa durkusashshen kamfaninmu? Lauriyya ta bata fuska tace. Hilal so dai kakeyi saika bata min rai ko? Da dai bana son na fada amma yanzu ka takura ni saina fada? Na dubeta cikin mamaki me zaki fada? Lauriyya ta harareni gamida murmushin yake tace. Alhajiji yana mutuwar kaunata nice dai ban bashi hadin kai ba. Ni nasan ko yana so ko baya so dolene idan nayi masa magana yasaka acikin sabon fim din zaiyi. Tana gama fadin haka ta kama hannuna ta fara jana kamar wani karamin yaro.......... . SOYAYYAR GASKIYA AKWAI DADI BA IRIN SOYAYYAR SU O'O BA [20:27, 1/19/2018] ‪+234 806 858 0203‬: ALAKAKAI-04 . (m) Nazir Adam Salih . Tana gama fadin hakan saita kama hannuna ta fara jana kamar wani karamin yaro. . Zo mu tafi dan Allah kada afara ruwa. Nabita abaya sumi sumi kamar tunkiya muka shiga cikin iskar damina. Jarumin jarumai Na kira kaina da kaina sannan sai na saki daddadan murmushi. Lauriyya ta lura Murmushin me kake? Na girgiza kaina nace babu komai.... Kece kawai kika burgeni, . ****** ********* ************* . Sa'ar da muka isa kamfanin fina finai na alhajiji sainaga toge abaya abjikin wani kantin kayan karau nace da lauriyya Jeki kuyi magana dashi ni bazan karasa ba... Lauriyya ta dubeni zatace wani abu saikuma ta fasa me yiwuwa itama ta lura da taron yan alabaku mu samun fim dake tare birjik akofar kamfanin duk kuwa da uwar iskar da ake ketawa. Lauriyya ta rike hannuna tace. Toh shikenan hilal jirani anan naje na dawo ta lura da fuskata haryanzu a murtuke take cikin damuwa. Kada ka damu hilal komai zai zama daidai in Allah ya yarda. Kaidai ka jirani. Tana gama fadin hakan saita matsa hannuna sannan ta jefeni da wani boyayyen murmushi mai kunshe da dubban manufofi ta juya tana rausaya ta nufi cikin kamfanin. . Na duba agogona bayana na jingine da itacen wayar lantarki dake daf da kantin na cika da mamaki sa'ar danaga tuni har mintuna goma sha uku sun shude da shigar lauriyya cikin kamfanin. Adaidai lokacin da damuwata ta fara tsananta saina hangi lauriyya ta fito alhajiji kuma yana biye da ita cikin fara'a akwai alamun farin ciki karara a fuskarsa me ywuwa na murnar zanyiwa kamfaninsa fim ne. Sa'ar da kuma na tuna da cewa nifa ayanzu ta kare min sai nafara tunanin to me yiwuwa ganin lauriyya ta nemi alfarma agurinsa ne yasashi murna. Ina nan tsaye har suka iso gareni. Yallabai! Yallabai!! Alhajiji yace dani cikin wata murya mai sautin amon alburushi sannan ya cafki hannuna kamar zai tsaga minsu saboda riko. Alhajiji kato ne baki mai katon ciki da dogon gemu babu gashin baki fuskarsa cikakkiya ce a mulmule kamar kwallon kafa duk sa'ar da yayi dariya saikaga ya zama tamkar mutum mutumi wannan ce tasa dayawa daga cikin shakiyan jaruman fina finan hausa suke so suga yayi dariya dan kawai su sha dariya. Wata shekara an taba fitowa dashi cikin wani shirin fim na abin dariya amatsayin dan daudu. . Saika rabe kuma daga nan Hilal ai SINAD PRODUCTION kamar gidan kace. Ya dubi lauriyya cikin murmushi itama kuma ta dubeni da murmushin yaudara ta kifta min idanu. Mu shiga daga ciki Hilal.... Wallahi nayi farin ciki da ganinka domin kaya ya tsinke agindin kaba daman yanzun nan nake kokarin buga ma waya saiga Lauriyya domin akwai wani babban fim dinmu na shekara da za'a fita gobe kai nake so ka fito a jarumi sunansa. MUTUWA DA FARINTA TAKE TAKE! Sa'ar da na dubeshi na dubi Lauriyya sainaji kamar na fashe da dariya domin ko shakka banayi nasan karya yakeyi dayace wai ni yayi niyyar sawa amatsayin jarumin tun farko kamata yayi a sanar dani tun satin daya gaba tabbas Lauriyya ce ta yaudaro shi. . Loading.......... KASHI NA BIYU 2 [20:27, 1/19/2018] ‪+234 806 858 0203‬: ALAKAKAI 05 . (m) Nazir Adam Salih . BIYU . Daga inda nake zaune ina iya jiyo sautin zubar ruwan saman akan kwanukan gidajen jama'a. . Na muskuta ahankali sannan na mike tsaye na nufi tagar dakin na dan janye gilashin tagar feshin ruwan saman gami da sansanyar iskar ruwan suka bugi fuskata. Nayi sauri na rufe tagar sannan nakoma na zauna akan kujerar ina nazarin dakin. shin wai yaushe za'a dauke ruwan nan ne. iskar dake cikin dakin ta fara karanci, hakan shiyasa fankar dake juyawa ta kasa yin maganin zafin dake addabata,
Chapter 3 · 0% Book details