Sashe 14
Alakakai Complete Hausa Novel · about 8 min read
dan samari kada ka bari matan zamani su haukata ka a banza nace da kaina.... . *********** *********** ************* . Karfe tara da rabi agogon mota ta ya nuna nayi kokari tun sa'ar dana baro ofis na fitar da komai daga cikin zuciyata abunda nafi kauna yanzu a duniya shine isashshen barci domin rabona da barci sa'o'i kusan ashirin da hudu kenan. Nayi fakin da motar a kofar gidana na rufe gilasan sannan na fito zan kulle kofar kenan sai Naji kamar motsi abayana na juya cikin sauri sainaga wata sura ta fito daga cikin duhu ta nufo inda nake. Tun dazun nake jiran zuwan ka JARUMIN JARUMAI. . BAKWAI 7 . Da wacce kuma kika zo? Na tambayi fadila lokaci guda kuma na jingina ajikin motar barcin dake idanuna ya zama tarihi a halin yanzu domin tuni nagama fahimtar fadila ta zama kamar tauraruwa mai wutsiya ganin ki ba. Nazo maka ne da wani babban labari domin dazun na fahimci wani gani gani kake yi min ka daukeni kamar wata yar iska fadila tace tana tabe baki. Fadila abin har Yakai da bakaken maganganu. Yama wuce da haka Hilal duk abin da nake yi ni ba mahaukaciya bace nasan abunda Nakeyi tayi shiru tana maida numfashi Babana yayi min bayanin duk abubuwan da kuka tattauna dashi jiya banyi mamaki ba sa'ar da nazo ofishin ka naga kana neman ka wulakanta ni ashe tallata maka ni akayi. Cool down fadila nace da ita rabi da turanci rabi hausa. Anki ayi cool down din da asama nake ta ci gaba da huci agabana. Ka dubi da kyau Hilal tun daga sama har kasa kaga makusa ajikina? Maganganun ta sun fara bani haushi dan haka sainace. Azahiri dai kam ko shakka babu baki da makusa amma a badini kuma fa... Ta yamutse fuska. Abar kaza cikin gashinta Hilal a kare wanne ne ba bare ba ku yanzu yan fim har kuna da bakin da zaku bude kuce wa wani dan iska? Kai yanzun nan Hilal kana tsammanin kai waliyi ne? Yan mata nawa kuka bata a harkar shirin fim [06:34, 1/31/2018] +234 806 858 0203: ALAKAKAI-25 . (m) Nazir Adam Salih . (c) Yarima Gangariya . Yan mata nawa kuka bata a harkar shirin fim? Kada kice haka fadila ba duka aka taru aka zama daya ba. Fadila ta zabura cikin fushi kamar zata hau ni da duka Kasani Hilal na kasance daga cikin dubban yan matan da Allah ya jaraba da son karance karance da kallon Fina finan hausa wannan ne ma tasa duk inda akayi wani gangami na yan shirin fim sainaje gurin ba don komai ba sai kawai don na ganku Abin da baka sani ba shine ba dade da sanin ka abin da yasa ban taba tunkarar ka nayi ma magana ba shine girman kanka musamman ma a lokacin da kake kan ganiyar tashen ka..... Na katse ta. Fadila duk naji kiyi hakuri don Allah kibar zancen nan mu rabu lafiya Wallahi barci ne a idanuna kamar na fadi nakeji. Tsaho lokaci tana nan tsaye tana ta kokarin dannan bakar zuciyar ta dake ingizota akan dokan danasani. Dole ne na fada maka tarihina Hilal dole ne na fada maka. Domin ka daukeni wata tambadaddiyar yar iska bayan kuma dan uwan ku ne dan shirin fim ya batani...... Bazan taba yafe masa ba har abada tafara kuka. Aure Kam ko zan rasa miji a duniya bazan aure ka ba domin nasan har abada bazaka taba yarda dani ba. Natafi Hilal ka huta lafiya.... Ta juya aguje ta nufi bayan gidan. Na bita da gudu gudu adaidai lokacin da take kokarin shigewa mota. Fadila..... Dan Allah tsaya ki saurare ni ta tsaya cak kafarta daya acikin motar daya kuma awaje. Babu wani abu kuma da zakace dani Hilal.... Me kake son fada? Zancen naira miliyan biyar? BAZAKA SAMI KO KWABO BA. tunda ka nuna min cewa kudin kafi so dani tayi tsaki agabana ta tsartar da yawu. Dubi idanun ka kiri kiri babu tsoro babu kunya. Kai yanzu har kana da bakin magana? Aure ne bazan aure ka ba tuni nafadawa mahaifina dazun bayan nabaro ofishin ka..... Jeka ka tsira da mota matsiyaci. Na yi taku biyu da niyyar kifa mata mari sai wata zuciyar tace dani.. Uhm. Uhm dan samari yi hankali da tangaran. Fadila ta lura da niyya ta. Au dukana zakayi? To Bismillah zo doki nayi tsaye kamar gunki duk kwakwalwata a yamutse. . Fadila ta shige motarta ta rufe kofar gararam sannan ta fizgi motar ta fice da gudu. Jikina na rawa na nufi kofar dakina na lalubi dan makullin dakin dake aljihuna sannan nafara kokarin bude kofar sannan ne to wata takarda ta Fado daga jikin kwadon. Na dubi takardar data Fado akan takalmina da farko na dauka shirme ce amma daga karshe sai zuciyata tace dani Kai duba dai... INA shiga dakin saina lalubo makunnar lantarkin na kunna lokaci guda kuma na bude takardar dan Sako ne kamar haka..... . HILAL. Me yiwuwa zaka so kasan wanda yayi min ciki zan fada Ma sunan sa domin abin yazama wa'azi a gareka ka kuma yi hankali kada abin da ya faru tsakanina dashi ya faru tsakanin ka da sakatariyar ka na lura ita tafi dacewa ka aura. Sannan wanda yayi min ciki sunan sa (ALHAJIJI) FADILA. . ************ ********** ************* . Ban isa ofishina ba sai kusan karfe goma sha biyu na rana wannan ya samo asali ne sakamakon nannuyan barcin daya daukeni. Ahanya sa'ar dana nufi ofishina zuciyata cike take da tunane tunanen abubuwan da suka faru a gareni tun daren jiya. A lokacin ne toh......... . ME KUMA YAKE SHIRIN FARUWA DA KAI HILAL ? KA RASA MILIYAN BIYAR KA RASA TSALELIYAR BUDURWA KAMAR FADILA . YANZU KUMA ME KAKE SHIRIN SAKE RASAWA? [06:35, 1/31/2018] +234 806 858 0203: ALAKAKAI-26 . (m) Nazir Adam Salih . (c) Yarima Gangariya . Ahanya sa'ar dana nufi ofishina zuciyata cike take da tunane tunanen abubuwan da suke ta faruwa a gareni tun a daren jiya. Alokacin ne na yanke shawarar zuwa a ranar nasami mahaifin fadila mu gama kashe magana yanzu kam nagama saduda dacewa nayi sallama da zama miloniya tun da dai na tabbata fadila bazata aure ni ba. Haka ma yafi kwanciyar hankali akalla ka tsira da mota dan samari. Toh amma sa'ar da tunanin lauriyya ya Fado min duk sai Naji hankalina ya tashi bansan inane alkiblata ba. Abu daya dai dana dada tabbatarwa da zuciyata tun adaren jiya shine na share su baki daya daga cikin zuciyata domin ita kanta lauriyya na lura akwai wani abu na rashin gaskiya dake tattare da ita. Ina kokarin fahimtar ko wanne abu ne har har na isa ofishin. Nayi mamakin da ban ga lauriyya a kofar tana hange hangen ta inda zan bullo ba. Nasan ga al'ada ko goma na safe nakai banzo ofis ba zan Harare ta tana ta leke leke to ballantana kuma karfe goma sha biyu cikin gaggawa nayi fakin da motar na nufi ofishin cikin sauri gabana ya fadi sa'ar dana shiga gurin karbar bakin banga lauriyya ba nayi tsaye cak a tsakiyar dakin jikina Yabani cewa lallai ba lafiya ba. LAURIYYA. Nakira sunanta murya a sarkake shiru ta gaida kunnuwana to amma naji kamar motsin mutane acikin ofishina. Nayi taku biyu gaba da niyyar nashiga sai Naji motsin tafiya an nufo dakin saukar bakin. Sannu ahankali naji takun sawu taf taf taf har ta bayyana idonta sharkaf da hawaye tana ganina saita taho gareni ta fashe da kuka. Dan Allah Hilal ka yafe ni.... Ka yafe ni Hilal. Ta sake fashewa da kuka. Yi Shiru lauriyya menene kum? Kuma meke faruwa? Banyi mamakin jin muryata ko rawa batayi domin Daman tuni jikina Yabani cewa ba lafiya ba lauriyya taci gaba da kuka. KA yafe ni Hilal yau zamu rabu dakai...... Bazan taba mantawa da abun dakayi min.... Ta sake fashewa da kuka iko sai Allah nace cikin zuciyata. Wai me ke faruwa ne lauriyya kin ki ki fada min komai sai........ Maganar ta makale a fatar bakina sakamakon wani kwakkwauran motsi danaji acan cikin ofishina. Na juyo na dubi lauriyya nace. SU wanene aciki? Ta dubeni a tsorace ta kasa cewa komai adaidai lokacin ne to sauran mutanen dake ofishin suka fito nayi tsaye ina duban su cikin kaduwa. Mutanen su biyu ne daya namiji ne Kato mai doguwar kasumba yana sanye da shakwara da jamfa da wando na shudiyar shadda kai da ka ganshi kasan akwai kudi zai kai kimanin shekaru hamsin da biyu a duniya dayar kuma mace ce dattijuwa zatayi kimanin shekaru kusan hamsin. Kallo daya nayi nata na gane ta na fahimci ko wacece ita da lauriyya kamar an tsaga kara. Sannunka da kokari bawan Allah. Munji duk taimakon dakayi mata. Nayi saroro ina kallon su banida bakin magana matar taci gaba da cewa. Yau shekara uku kenan muna neman yar banzar yarinyar nan.... Kwana uku ka da daura mata aure ta gudo. Naji zuciyata ta harba akaro na farko saina kalli lauriyya nace.... KINA NUFIN KICE KINA DA AURE? Lauriyya ta fashe da kuka sannan ta nuna katon mutumin da dan yatsa tace cikin kuka... Ka ga mijina nan....... Wai wannan katon za'a aura min katon mutumin ya kamo kafadarta ya hankadata waje tsohuwar da nake tsammani mahaifiyata ce tabi su Abaya. . Jikina na rawa na rufa musu baya tun kafin na karasa waje na hango wata mota daga can baya Kirar Toyota Coralla mutumin ya tura lauriyya aciki tana ta kuka tuni har yara sun fara taruwa suna kallon fim din. Cikin sauri na karasa gindin motar nace. Lauriyya..... Allah ya kiyaye kinji Allah taimake ki katon mutumin ya Harare ni alamun tsana karara suka bayyana a fuskar sa ban zarge shi ba ban kuma ga laifinsa ba shekara ta uku tare da matar sa nasan duk duniya babu wanda ya isa ya fitar dani daga zargin sa. Kaga malam ya isa Jeka kawai abin da kayi da ma ya isa.. Lauriyya ta yunkura acikin motar ta leko da kanta tace. Watarana zamu sake haduwa Hilal.... Nayi maka alkawari. Nagode Allah ya saka maka. Mutumin ya tashi motar sannan ya dubi Mahaifiyar lauriyya yace. GATA DAI YANZU AI MUN GANTA KIN YARDA DAI