← Book details Al'ajabin Masarauta Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 6

Sashe 3

Al'ajabin Masarauta Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Book ɗin al'ajabi wani sabon kabcene me matuƙar al'ajabi da ban mamaki, kabcene wanda ya banbanta da sauran books na masu ban al'ajabi kamar irinsu ( MEJO NAJEEB,,, SOLDIERS FAMILY,,,,IZZAR MULKI,,, JEJI GIRL,) inaga sune Books masu ɗauke da abin al'ajabi to wannan kabcen dabanne sam ba irinsu bane, idan kuna so kukashe ƙwarƙwatar karatu to kigarzayo domin samun damar karanta book ɗin AL'AJABI.

ROMANTIC LOVE STORY 💋 KAMAR YADDA AKA SABA HUMMM MY LOVELY SISTERS ABUNFA BA'A MAGANA KAWAI MUTSUNDUMA ACIKIN WANNAN LABARI ME TAKEN AL'AJABI 💃

Book 1

Page 15 & 16

"Yace "ranka yadaɗe inada magana please idan ba damuwa. "Okay munajinka Cewar ameer. "Yallaɓai Wlh dama wata makarantace acikin garin Adamawa wadda Alhaji yasiya yo yace duk lokacinda yaranshi sukazo akaisu suga wurin sabida kusan yaza'ayi aikin, shine nace kozakuzo mujecan kuga wurin? Yaƙarasa zancen cikin ladabi agaresu.

Kallon princes sameer sukayi atare dominjin amsar daze bada sabida shine kawai ze iya kawo matsala tafiyar, amma se sukaga bece komaiba, dudda hakan basuyi mamaki sabida sunrigada sunsan wayeshi, juyawa Anwar yayi gun wannan matashin kamin yace "shikenan badamuwa amma bazamu samu damar zuwa yanzu ba sedai idan mun ƙara dawowa sabida yanzu daganan gida muka nufa. Dasauri wannan matashin yace "please yallaɓai Dade anduba lamarin domin Wlh mutanen wannan yankin suna matuƙar buƙatar tallafin ilimi acikin rayuwarsu gabaki ɗaya akan duhun jahilci suke rayuwa wannan dalilinnema yasa Alhaji siyan wurin domin kawo musu hasken addini, yaƙarasa zancen cikin alamun riƙo. Ido yarima sameer yaruntse daƙarfi yanajin wani irin zafi aranshi domin aduniya yatsani yaji Cewar wata halitta narayuwar rashin ilimin addini domin koba nazamani dai bazaka rasa abin kusantar uban gijinkaba. Shi kuwa Anwar ajiyar zuciya yasauke tareda buɗe baki zeyi magana kenan yaji ɗaukar cool voice ɗinshi yana faɗar "it's okay we will going to Adamawa state now. Yana gama faɗar Hakan yajuya zuwa motarsu cikin takonshi na ƙasaita wadda kallo ɗaya zakamishi kasan cewar shiɗin jinin sarautane.... murmushi dukkansu sukayi kana suka mara Mishi baya, seda suka shiga motarsu duka kana Ameer yaleƙo tareda baya ɗaya daga cikin hadiman su umurnin anunawa wannan saurayin me suna imam, motar daze shiga sutafi tare tunda shine yasan wurin. Aiko cikin sauri yacika umurnin shi kana sukaja motocinsu sukabar wurin, tareda nufar garin Adamawa state.

MAYE BALWA

"Danejo danejo wai kina inane? Kikabarni inata famar kiranki sekace wata sa'arki. Innawuro ce keta famar dokawa danejo kira kamar zata tsaga gidan....Ita kuwa danejo tana bayi ne shiyasa bata amsaba har seda tafito domin pappi ɗinta yahanata amsa kira abayi yagaya mata ba kyau Hakan shiyasa koda innawuro zata dafata bazata taɓa amsawaba se lokacinda tafito, to yanzumu hakance takasance, fitowa tayi dabuta ahannunta tana faɗar"na'am ganin Anan innah ina bayine...wani banzan kallo tawatsa mata kafin taja tsaki cikin takaicin yarinyar tace ungo maza jeji hayin barmo ki kaiwa hansai kuma kitsaya tagama ki karɓomin saƙona tukkunna kidawo, tafaɗa tana dungurawa danejo nera ɗari ahannu. Tokawai tace mata kana ta ɗauki ƴar sandarta tafice daga gidan, tafiya takeyi ahankali ita kaɗai tana wasada sandarta kuma aranta tana tunanin pappi ɗinta domin yau kwana biyu kenan bezoba kuma idan yayi wannan kwana biyun jitakeyi kamar shekara biyu ne yayi, amma tasan tunda har yacika kwana biyu yau to tabbas yau zezo ko gobe, Hakan dai take tafoyarta hankali kwance ita kaɗai kuma gashi wurin nada nisa sosai amma ahakan take tafiya batareda tasakawa ranta ganin nisan wurinba domin tabbas datasa Hakan aranta toda anyanke mata tafiyar sedai ahakan ma anayi ana ɗan kusantota da unguwar sabida se anfita rugarsu gabaki ɗaya anwuce ruga har biyu kana akai inda innawuro ta aiketa, kuma tasanda Hakan ammata turata sabida mugunta.

Matafiya

Tsaye suke acikin babban filin makarantar MAYE BALWA wadda tajima dawatsewa bakowa aciki kuma ba komai na anfani takoma tamkar kango, sunjima suna zagayen makarantar kafin su samu wani wuri daga gefen makarantar suka zauna suna tattaunawa da hakimin garin, bayan suyi magana da wani company gine,gine dake cikin garin Yola, suna jiran ƙarasowarsu domin suɗamƙa kwangilar gyaran makarantar hannunsu..basu jima awurinba manager company yazo, Hakan yake nuna musu tsare tsaren ginin makarantu dasuke dashi a laptop ɗinshi suna dubawa..shikuwa yarima sameer ya lumshe kyawawan idanuwanshi masu launin ruwan madara, yana sauraren bugun zuciyarshi dayakeji tamkar zata tsinke wani irin fargaba da faɗuwar gaba yakeji wanda besan daliliba kuma abin seƙara kusantoshi yakeyi...sukuwa sunacan suna aikinsu hankali kwance domin nema sukeyi suyi sugama subar unguwar domin babu alamun ko sunsan miye hotel balle suyi tunanin samunshi Anan kusa, sesun koma cikin gari tukkunna.

Danejo

Taje inda innawuro ta aiketa tadawo tana tafe tana tana tsilla sandarta sama gaya duk tazubo sumar kanta tarufe mata rabin fuska da ƙirjinta ɗaya har zuwa cibiyarta sabida tsawon sumar dakuma tsantsinta, tafiya takeyi ita kaɗai awurin domin kamar jeji hakan wurin yake sabida anfita daga cikin gari kuma ba'a ƙarasa cikin rugar Fulanin dake maƙwabtaka fawirinba,tayi tafiya menisa kafin tazo Dede inda motocinsu suke, da mamaki take kallon motocin bawai ɗan bata taɓa Ganin mota ba a'a kawai de tayi mamakin ganinsu awurinne, ahankali taƙarasa wurin cikin sanɗa tana leƙensu....Sukuwa basuma sanda akwai mutum awurinba. Tajima tana kallonsu basusaniba harta juya zata tafi sekawai idonta yasauka akan yarima sameer dake lumshe da Ido yasaka hannu ɗaya yaɗage setin zuciyarshi dayakeji kamar zata ɓalle tafoto waje...ido tawaro cikin tsananin fatin ciki dajin daɗi taƙarasa gunshi sam bata damu da mutanen dake wurinba cikin ɗauki tariƙo hannunshi tana faɗar "pappi cikin sweet voice ɗinta me daɗin sauraro...wani irin zabura princes yayi sabida wani mugun shuck dayaji lokacinda hannunta yasauka anashi, tareda buɗe lulu eyes ɗinshi akan kyakkyawar fuskarta, wanda yayi sanadiyyar tsanantawar bugun zuciyarshi.

Sukuwa duka ido suka waro musamman brothers ɗinshi dasukasan waye yarima sameer dakuma yadda yake ƙyamatar mata, amma imam, Hakimi, da manager company duka kallon mamaki ne suke mata gatadai kallo ɗaya zaka mata kasan cewar ƴar fulanice ta asali wanda akasani da kunya da kawaici amma gaya tariƙe hannun namiji kuma babban mutum me daraja irin yarima sameer agansu batareda taji kunyarsuba.

Shi kuwa wani mugun kallo kawai yakebinta dashi amma kasa cewa komai kowani dogon motsi yakasayi...cikin mamaki danejo kebinshi da kallo tunda tabuɗe ido aduniya take Ganin pappi ɗinta bata taɓa yimai maganaba yashareta se yau, atake gabanta yafaɗi tsoro da fargaba duk suka rufeta dara daran idanuwanta masu masifar haske suka canja kala atake suka cikoda ƙwallah, dasauri ta russuna wurin ƙasan ƙafafunshi taƙara kamo hannunshi ɗaya muryarta na rawa take faɗar "pappina bakada lafiya ne? Miyasa kayi shiru? Ko wani abun wannan mutanen sukayima? Miyasameka pappi? Kayi magana dan Allah. Taƙarasa zancen tana saka Mishi kukan dake fita har zuciyarta..

"Ikon Allah ke baiwar Allah sakeshi mana aina kika sanshi dazakiga mutum kawai kizo kiriƙeshi kinamai kuka? Cewar imam cikin mamaki...banza tayi dashi domin burinta kawai pappinta yayi magana amma shiru se ido kawai dayake binta dashi...shikuwa imam agarzuƙe yayo kanta yana masifa "waifa wannan wani lokacin Fulanin nan naruga ba hankaline dasuba tashi kibarnan kona tattakaki yanzu Wlh. "No karka daketa Cewar Ameer yana tasowa daga inda yake zaune yaduƙo kusan inda take gurfane riƙeda hannun yarima sameer yace "ƙanwata sakeshi muyi magana kinji, Yafaɗa cikin alamun rarrashi...dagowa tayi da jajayen idanuwanta masu masifar girma tawatsamaisu tareda girgiza kanta duka sumar data rufe rabin fuskarta tayi baya atake asalin fuskarta ta bayyana. Azabure ameer yayi baya sedai yayi ƙarfin halin hana kanshi faɗuwa, hakama duk wanda ke wurin seda yarazana Ganin tsananin kyawun wannan yarinyar gakuma gashi har gadon baya kana ƙwatar idonta kaɗai ta isa tashedama tabbas aljanace sabida kasan cewar ƙwayar idonta lite blue sedai acikin ido farine ƙal amma yanzu yakoma ja sabida kukanda tayi. Duk wanda ka kallah awurin natsuwa ta ɗauke Mishi amma Banda zaratan samarin dasukayi ta maza suna kallonta... ɗan seta kanshi yayi kana yaƙara cewa a'ina kikasanshi ƙanwata? Domin yaga dai taƙi ta sakeshi kamar yadda yabuƙata...ƙwallar dasuka cika idonta ne suka ƙara zubowa kana tace "pappina ne...!

Book ɗin AL'AJABI Paid book ne akan 1k kacal complete ga duk me buƙata domin a complete yafito duk wanda keson posting kullun 700 ne zaki iya tura kuɗinki ta wannan account ɗin 👉2276776261 sha'awanatu ƙasim UBA bank, kana kitura Shedar biyanki a wannan nomber 👉 07037092176 on whatsapp.

Autar alheri ✍️

🪐🐦‍🔥🪐 *AL' AJABIN*🪐🐦‍🔥🪐

🪐🐦‍🔥 *MASARAUTA*🐦‍🔥🪐

🪸🪸🪸🪸🪸🪸 Daga💪Alƙalamin👇🪸🪸🪸🪸🪸🪸

Dr Yasmeen Ahmad😚

Autar alheri ✍️

Al'ajabi, hummm

Book ɗin al'ajabi wani sabon kabcene me matuƙar al'ajabi da ban mamaki, kabcene wanda ya banbanta da sauran books na masu ban al'ajabi kamar irinsu ( MEJO NAJEEB,,, SOLDIERS FAMILY,,,,IZZAR MULKI,,, JEJI GIRL,) inaga sune Books masu ɗauke da abin al'ajabi to wannan kabcen dabanne sam ba irinsu bane, idan kuna so kukashe ƙwarƙwatar karatu to kigarzayo domin samun damar karanta book ɗin AL'AJABI.

ROMANTIC LOVE STORY 💋 KAMAR YADDA AKA SABA HUMMM MY LOVELY SISTERS ABUNFA BA'A MAGANA KAWAI MUTSUNDUMA ACIKIN WANNAN LABARI ME TAKEN AL'AJABI 💃

Book 1

Page 17 & 18

"Kana tace "pappina ne kuma inasanshi banaso wani abun yasameshi, kace yayi magana dan Allah kowani abun kuka masa ne? Tafaɗa cikin yanayin tausayi domin duk zuciyarta ta karaya Ganin pappinta yaƙi cewa komai...ajiyar zuciya Ameer yasauke kana yadubi yarima sameer daya lumshe kyawawan idanuwanshi tun lokacinda kalamanta suka fara dukan dodon kunnenshi, kana yace "princes kasan wannan yarinyar ne? Yatambaya badan abashi amsaba domin yasan ba abinda yarima sameer zece Mishi idan kuwa zasu kwana awurinne, sedai ga mamakinshi yaji cool voice ɗinshi yana faɗar "I no her, yafaɗa kamar meciyon baki, kafin yaƙara motsa laɓɓansa cikin gajiyawa yake faɗar
"please just sey her get from my saint, YafaÉ—a, zuciyarshi ada gule.
Chapter 3 · 0% Book details