Sashe 1
Abilkisu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
To kamar yadda kuka sanni ni benaxir yar
yawo ce ina kwaso labari da darussan yau
da gobe na rayuwanmu.
Na kawo na afrah.
Dana indo dakuma na aliya.
Harda ina
tunanin gunwa zani sai aliya taban satan
amsa inxo gun Bilkisu mai gadon zinare.
Hakan kuwa akayi domin takanas daga
bauchi nazo har garin gombe domin na
tuntube bilkisu labarinta tun daga farko.
Amma fa ba karamin wahala nasha ba kafin
ta amince tabani.
Don dai nace mata nida
yan makaranta na zamu dau darasin
rayuwana saboda kowa rayuwarsa akwai
darasi.
Gani ga balkisu .zata fara bamu
labari yanuwa kubiyoni muzuba na zomaye
Hmnnn sunana Bilkisu saad.
Baba na
maigarin kauyenmu ne.
Natashi cikin wahala
da talauci.
Mu 36 ne a gun mahaifina
matarsa guda hudu.
Akwai rahama
.siddiqa.suwaiba sai kuma mahaifiyata
aisha..
Mu takwas ne agun mahaifiyata.
Sai
uwargidansu rahama tana da yara 10cif
dukkansu mata.
Siddiqa tanada 9 sai.
Suwaiba tana da 8 .
Gidanmu babban
gidane.
Haka zalika matsaloli da matsifar
cikinta.
Idan kana da baki ka kwace kanka.
Sharri da makirci kuwa sai
tubarkallah.mahaifiyata macece mai hakuri
da shariya hakan yasa duk matan gidan ita
take cutuwa.
Mu biyu ne mata sauran
shidan duk mazane.
Mahaifina manomi ne
sosai.
Don haka kowani yaro inyataso gona
yanufa.
Bai yadda da karatun boko ba.
Matan kuwa kinagama islamiyya kikai
shekara 15 zai aurar dake .
Auren dangi
akeyi tunda natashi banga anyi auren bare a
gydanmu ba.
Da dadi daba dadi kowa aka
samu acikin yayan bappanmu zaa hadaki.
Shima yayansa sunkai 46.
Ahaka nataso
yanxu shekarana sha hudu.
Iba islamiyya.
Aladace kullum dare dare a gydanmu sai
munfito yara munyi hira dayake yayan
kishiyan umma na akwai saannina.
Da
khadija da aisha dakuma maryam.
Duk
dakinsu daban amma kanmu daya .
Duk
cikinsu nafisu nutsuwa fasali kyau dakuma
ilmi.
Khadija da maryam akwai rawan kan
tsiya da surutu gasu da buri.
Basuson zuwa
islamiya sai suyita cin kudin samari.
Ganin
duk garinmu ana daraja gidanmu.nikuwa da
wannan abun dasuke zan dauki littafina naje
gun ummata tamin karin littatafai.
Ta ban
labarin dazasu amfaneni.
Ummata irin
mutannenan masu lura da kuma hangen
yaransu hakan yasa bata wasa da
lamrukanmu.
Kanwata fatyma wacce muke
kira hajja teema.
Don tanada sunan kakarmu
mamar mai gari.nikuma saboda kirar hutun
da Allah yayimin kuma ya kasance kakana
tafi sona duk jikokinta.
Take cemin yar gata
hakan kuwa akayi baa kira na da bilkisu
saidai yargata.
Kamar kullum nadauko littafin fiqhu na
bayan sallar isha antaru a tsakar gida sai
hira ake.
Khadija ce ta ke tadin saurayin
dasuka hadu a dandali wai yabata kyautan
dari.
Daya bata sai tamaka masa a fuska
wai yamata kadan hakan yasa yabata dari
biyu.
Shine suka sayo doya da kwai sukeci.
Ina kallonsu sai dariya suke ban ina karatu.
Nagama hajja wato kakarmu tace yargata
zomana.
Naje kusa da ita tace anata labarin
ke kinja gefe.
Nayi murmushi nace inna
kema kinsan ban kware a surutu kaman
khadija ba.
Tayi murmushi tace hakane.
Yau
mekike karantawa nace rukunnan sallah.
Anan nazauna na biya mata.
Aka zubo mana
tuwon daren mu tuwon dawa miyan kuka.
Namike naje mukaci sunaci suna tadinsu
dama sunsanni sarai ba magana nake ba.
Bayan mun idda namike nacewa hajja teema
kixo muje mu kwanta tace toh.
Muka shiga
muka samu inna akan sallaya wanda
aladarta ne sai tafi awa biyu akan sallaya
bayan sallar isha.
Muka kwanta muna
hiranmu na ya da kanwa.
Umma tace ina su
abdul tana nufin yayanmu na fari nace mata
yau baishigo gida ba.
Dama ina nemansa
yaban 35 zan siya littafin fiqh.
Tace kekam
kullum bakida abunyi sai tara littafi? nace
uhm bazaki ganebane umma su suke sawa
mu saya.
Batace komaiba har mukayi bacci.
Dasafe da asuva bayan idar da sallah sauga
yaya abdul yashigo bayan sungana magana
da umma zaifita nace yaya kasayamin littafi
yajuyo yace nawane nace 35 yamikomin
hamsin yace kibawa hajja teema sauran
canjin nakarba ina godiya .
Dayamma
nashirya tsaf zantafi islamiya nida hajja
teema.
Munshirya cikin manyan hijabai
nikam harda liqab.
Muka wuce.akwai wani
kofar shago inda samarin anguwan suje
taruwa sunsan fuskokin yan gydanmu kaf.
Ni
ce natare musu hanya.
Basu taba ganin
fuskat ba.
Akwai wani ahmed ya yanke
shawaran sai yabude wataran kowa yagani.
Danasan da wannan rana daban fitoba.
Ina
tafiya naji sallama ban amsaba hajja teema
ce ta amsa .
Yace da yarki zanyi magana
batace komaiba haka zalika nima bance
komaiba mukaxo daidai ahagon yanata
binmu.
Muna xuwa gun samarin yasha
gabana kawai yatube min liqab da karfi
hakan yasa hijabi nama tafadi.
Gashina dake
kwance har gadon baya suka zubomin a
fuska cikin azama da bacin rai nadauki
hannu na kwashe shi da mari.
Zamu karasa gobe.
Gud nyt
Rike fuskarsa yayi bashi kadaiba dukka
samarin gun kowa na mamaki biyu.
Kyaun
fuska na dakuma marinsa danayi.
Shikuwa
marin baidameshi ba salati naji yayi yana
hamdala.
Hakan yasa namayar da hijabi na
nace hajja teema mutafi da Allah.
Muka isa
islamiyya .
Muna dawowa ne naganshi da
abokanshi suna zaune kokesuke fada sai
Allah.
Dayake mu biyar muke tafiyan dasu
khadija maryam da aisha sai hajja teema.
Cikin nutsuwa muka wuce.
Har lokacin jikina
bari yake don bantaba taba jikin namijiba
bacin yayuna sai akanshi.
Hakan yasa umma
na ta tambaya nakuwa gayamata komai .
Tamin fada sosai akan illan marinshi da nayi
a cewarta wai namiji baa masa haka .zai
iyacewa sai yarama kuma ba yadda na iya.
Zai rama ta mumnunan hanya Allah kare.
Nayi shiru amma jikina yayi sanyi.
Da magriba muna zaune mukaji inna rahama
na ihu tsakar gyda tana matsifa .
Ummata
bata leka ba sanin mexai biyo baya.
Ni da
hajja teema muka leka.
Aikuwa saida mukayi
dana sani.
Inna rahama ta jawomu wai mu
muka dauke mata daddawan data shanya a
rana.
Nida hajja muka zaro ido nace inna
wlh munji kina matsifane muka leko.
Karya
kuke munafukai uwarku takoya muku sata
ko? hajja teema cikin bacin rai tace kinga
inna.
Ki kare akanmu wlh karki karasamin
uwa cikin zancenki.
Aikuwa data jawo hajja
tarinka kirba.
Umma naji bata leko ba.
Inna
sadiqa ta fito tace kara mata.
Nima yar
nakeson daka.
Dasu maryam take cemin wai
tsabar wulakanci ance yargata ta mare mata
saurayi.
Na zaro ido nace inna banganeba.
Tace zaki gane don uwarki.
Yara saikace
kune masu gida komai ku? suka kamamu
suka jimda su yaya abduo basunan balle su
kwace mu.
Ummanmu kuwa badama tashiga
yanxu sai su mata taron dangi mukaci
kukanmu.
Umma ranta yabaci sosai ta
yanke shawaran gayawa maigari.
Bayan
yadawo tasanar dashi ya aika akiramu
dukka harda su maryam.
Yace tunda ni
bazaku barni na hutaba kullum acikin dukkan
yara kuke yau ku daki na wannan gobe na
wancan to ya isa haka.
Kowa taje tashirya
nanda sati biyu zan aurar da
maryam.khadija.aisha.dakuma bilkisu.
Tundanake a rayuwata bantaba shiga tashin
hankali irin wannan ba.
Wannan ai matsiface
baba zai dauken yabadani ina gani akan
yayuna.
Kuka nafarayi yace ku bacemin
anan.
Su maryam kuwa basuce komaiba.
Asali murna suke don suna da tsayayyu a
dangi nice dai daban da kowa.
A daki umma
tayi tagumi tace kiyi hkr danasan haka
maganar zata dawo dabanjeba.
Nayi shiru.
Hajja ma ta tsorata sosai ita gani take zaa
hada da ita.
Gydanmu aka fara shirye shiryen biki mu
hudu.
Haka gydan bappanmu ma zasu fitar
da maza hudu.
Baba yakiramu ko muna da
tsayayyu a dangi kowa tafada nata .
Nikuwa
nace banidashi.
Haka kuwa akayi kamar
yadda akeyiwa duk wacce bata fitarba zaa
hadata da kowaye.
Aka daura aurenmu.
Dangin umma na sun hallata sosai naga
gata kasancewa ni ce mace tafari da zaa kai
a dakinmu duk yayuna mazane.
Aka daura aure .
Baba yace kowa tawuce
dakinta da yamma.
Ba ko ina bane sai gidan
baffanmu.
An yanka mana gefe guda.
Kowa
ciki da falo da bandaki.
Kicin kuwa haduwa
zaayi kowa ta girka abunta.
Bansan mijina
ba amma gyra kam nasha .umma tarinka
min waaxi karki biyewa mutane kizauna da
zuciya daya dakowa baruwanki da sa ido wa
rayuwan wani.
Tamin waazi sosai sanin
datayiwa gidan.
Dare dare aka kai kowacce
dakinta.
Aka barmu daga mu sai halinmu..
Ina zaune a yafe gashi ni ba kawayeba.
Yayi
sallama yashigo akasan makoshi na amsa
masa.
Yaxo gefena yazauna tare dacewa
tashi muyi sallah.
Natashi nadauro alwala
mukayi sallah.
Yamin addua sannan yace
hau ki kwanta.
Jikina nabari don tunda nake
bantaba kebewa danamiji ba.
Yahau gadon
rumfan shima amma tagefe guda mukayi
bacci.
Tun ina dar dar har na sake jiki.
Duk
abinnan banga fuskansa ba.
Balle nagane
waya mijin..
Da asuba yatashen shima yayi
masallaci.
Bayan na idar nadan jinginu da
bangon ina tunani shikenanfa nadawo matar
auren dole.
Hmnn.
Sallama yayi na tsugunna
na gaysheshi ya amsa.
Batare da yakara
cewa komai ba ya dale kan gado.
Nikuwa
namike da xummar namana abun karyawa.
Kirana yayi KE kixo ki kwanta kawai zaa
kawo anjima.
Nace to jikina a sanyaye a
zuciyana nace tabbas baisan wa aka aura
masa ba shima.
Nakoma kan sallayata har
gari yawaye agun bacci ya kwashen.
Bayan
nafarka naga bai nan amma ga abincinnnan
an ajiye.
Benaxir intakaita miki watana hudu cif
bansan mijin danake aureba.
Inyafita da
asuba sai dare yadawo kuma fitila bayi
barina naga fuskarshi.
Shima bai taba
ganinaba.
Muryarshi kuwa kamar na mawaki
zaki ga dadin sauraro amma bai fiye
maganaba.wataran ni nake kwana nikadai
dare dare yakan sanar dani zaiyi tafiya .
Wataran yayi sati wataran kuma sati biyu.
Su maryam da khadija kuwa harda ciki.
Kasancewar mu tubali daya yasa bamu cika
hayaniya dasuba.
Asalima kanmu a hadene
saidai bani shiga cikinsu kamar yadda nake
a gyda.
Ganin zaman banzan yayi yawa yasa
na yanke shawarar sayarda awara anan
nasanar masa wata rana dare dare ya
amince harda bani jari.
Nafara sanaata ba
kama. hannun yaro.watarana naje ganin
gyda muna hira da ummata sai take
tambayana game da rayuwan aurena ina
bata amsa.
Anan ta fahimci bansan komai
akan aureba balle namata bayani in akwai
matsala.
Anan tafahimtar dani komai nace
mata umma fa ko fuskanshi ban saniba.
Tayi
mamaki kwarai namata bayanin komai.
Tace
to ke zaki gyra rayuwar aurenki.
yawo ce ina kwaso labari da darussan yau
da gobe na rayuwanmu.
Na kawo na afrah.
Dana indo dakuma na aliya.
Harda ina
tunanin gunwa zani sai aliya taban satan
amsa inxo gun Bilkisu mai gadon zinare.
Hakan kuwa akayi domin takanas daga
bauchi nazo har garin gombe domin na
tuntube bilkisu labarinta tun daga farko.
Amma fa ba karamin wahala nasha ba kafin
ta amince tabani.
Don dai nace mata nida
yan makaranta na zamu dau darasin
rayuwana saboda kowa rayuwarsa akwai
darasi.
Gani ga balkisu .zata fara bamu
labari yanuwa kubiyoni muzuba na zomaye
Hmnnn sunana Bilkisu saad.
Baba na
maigarin kauyenmu ne.
Natashi cikin wahala
da talauci.
Mu 36 ne a gun mahaifina
matarsa guda hudu.
Akwai rahama
.siddiqa.suwaiba sai kuma mahaifiyata
aisha..
Mu takwas ne agun mahaifiyata.
Sai
uwargidansu rahama tana da yara 10cif
dukkansu mata.
Siddiqa tanada 9 sai.
Suwaiba tana da 8 .
Gidanmu babban
gidane.
Haka zalika matsaloli da matsifar
cikinta.
Idan kana da baki ka kwace kanka.
Sharri da makirci kuwa sai
tubarkallah.mahaifiyata macece mai hakuri
da shariya hakan yasa duk matan gidan ita
take cutuwa.
Mu biyu ne mata sauran
shidan duk mazane.
Mahaifina manomi ne
sosai.
Don haka kowani yaro inyataso gona
yanufa.
Bai yadda da karatun boko ba.
Matan kuwa kinagama islamiyya kikai
shekara 15 zai aurar dake .
Auren dangi
akeyi tunda natashi banga anyi auren bare a
gydanmu ba.
Da dadi daba dadi kowa aka
samu acikin yayan bappanmu zaa hadaki.
Shima yayansa sunkai 46.
Ahaka nataso
yanxu shekarana sha hudu.
Iba islamiyya.
Aladace kullum dare dare a gydanmu sai
munfito yara munyi hira dayake yayan
kishiyan umma na akwai saannina.
Da
khadija da aisha dakuma maryam.
Duk
dakinsu daban amma kanmu daya .
Duk
cikinsu nafisu nutsuwa fasali kyau dakuma
ilmi.
Khadija da maryam akwai rawan kan
tsiya da surutu gasu da buri.
Basuson zuwa
islamiya sai suyita cin kudin samari.
Ganin
duk garinmu ana daraja gidanmu.nikuwa da
wannan abun dasuke zan dauki littafina naje
gun ummata tamin karin littatafai.
Ta ban
labarin dazasu amfaneni.
Ummata irin
mutannenan masu lura da kuma hangen
yaransu hakan yasa bata wasa da
lamrukanmu.
Kanwata fatyma wacce muke
kira hajja teema.
Don tanada sunan kakarmu
mamar mai gari.nikuma saboda kirar hutun
da Allah yayimin kuma ya kasance kakana
tafi sona duk jikokinta.
Take cemin yar gata
hakan kuwa akayi baa kira na da bilkisu
saidai yargata.
Kamar kullum nadauko littafin fiqhu na
bayan sallar isha antaru a tsakar gida sai
hira ake.
Khadija ce ta ke tadin saurayin
dasuka hadu a dandali wai yabata kyautan
dari.
Daya bata sai tamaka masa a fuska
wai yamata kadan hakan yasa yabata dari
biyu.
Shine suka sayo doya da kwai sukeci.
Ina kallonsu sai dariya suke ban ina karatu.
Nagama hajja wato kakarmu tace yargata
zomana.
Naje kusa da ita tace anata labarin
ke kinja gefe.
Nayi murmushi nace inna
kema kinsan ban kware a surutu kaman
khadija ba.
Tayi murmushi tace hakane.
Yau
mekike karantawa nace rukunnan sallah.
Anan nazauna na biya mata.
Aka zubo mana
tuwon daren mu tuwon dawa miyan kuka.
Namike naje mukaci sunaci suna tadinsu
dama sunsanni sarai ba magana nake ba.
Bayan mun idda namike nacewa hajja teema
kixo muje mu kwanta tace toh.
Muka shiga
muka samu inna akan sallaya wanda
aladarta ne sai tafi awa biyu akan sallaya
bayan sallar isha.
Muka kwanta muna
hiranmu na ya da kanwa.
Umma tace ina su
abdul tana nufin yayanmu na fari nace mata
yau baishigo gida ba.
Dama ina nemansa
yaban 35 zan siya littafin fiqh.
Tace kekam
kullum bakida abunyi sai tara littafi? nace
uhm bazaki ganebane umma su suke sawa
mu saya.
Batace komaiba har mukayi bacci.
Dasafe da asuva bayan idar da sallah sauga
yaya abdul yashigo bayan sungana magana
da umma zaifita nace yaya kasayamin littafi
yajuyo yace nawane nace 35 yamikomin
hamsin yace kibawa hajja teema sauran
canjin nakarba ina godiya .
Dayamma
nashirya tsaf zantafi islamiya nida hajja
teema.
Munshirya cikin manyan hijabai
nikam harda liqab.
Muka wuce.akwai wani
kofar shago inda samarin anguwan suje
taruwa sunsan fuskokin yan gydanmu kaf.
Ni
ce natare musu hanya.
Basu taba ganin
fuskat ba.
Akwai wani ahmed ya yanke
shawaran sai yabude wataran kowa yagani.
Danasan da wannan rana daban fitoba.
Ina
tafiya naji sallama ban amsaba hajja teema
ce ta amsa .
Yace da yarki zanyi magana
batace komaiba haka zalika nima bance
komaiba mukaxo daidai ahagon yanata
binmu.
Muna xuwa gun samarin yasha
gabana kawai yatube min liqab da karfi
hakan yasa hijabi nama tafadi.
Gashina dake
kwance har gadon baya suka zubomin a
fuska cikin azama da bacin rai nadauki
hannu na kwashe shi da mari.
Zamu karasa gobe.
Gud nyt
Rike fuskarsa yayi bashi kadaiba dukka
samarin gun kowa na mamaki biyu.
Kyaun
fuska na dakuma marinsa danayi.
Shikuwa
marin baidameshi ba salati naji yayi yana
hamdala.
Hakan yasa namayar da hijabi na
nace hajja teema mutafi da Allah.
Muka isa
islamiyya .
Muna dawowa ne naganshi da
abokanshi suna zaune kokesuke fada sai
Allah.
Dayake mu biyar muke tafiyan dasu
khadija maryam da aisha sai hajja teema.
Cikin nutsuwa muka wuce.
Har lokacin jikina
bari yake don bantaba taba jikin namijiba
bacin yayuna sai akanshi.
Hakan yasa umma
na ta tambaya nakuwa gayamata komai .
Tamin fada sosai akan illan marinshi da nayi
a cewarta wai namiji baa masa haka .zai
iyacewa sai yarama kuma ba yadda na iya.
Zai rama ta mumnunan hanya Allah kare.
Nayi shiru amma jikina yayi sanyi.
Da magriba muna zaune mukaji inna rahama
na ihu tsakar gyda tana matsifa .
Ummata
bata leka ba sanin mexai biyo baya.
Ni da
hajja teema muka leka.
Aikuwa saida mukayi
dana sani.
Inna rahama ta jawomu wai mu
muka dauke mata daddawan data shanya a
rana.
Nida hajja muka zaro ido nace inna
wlh munji kina matsifane muka leko.
Karya
kuke munafukai uwarku takoya muku sata
ko? hajja teema cikin bacin rai tace kinga
inna.
Ki kare akanmu wlh karki karasamin
uwa cikin zancenki.
Aikuwa data jawo hajja
tarinka kirba.
Umma naji bata leko ba.
Inna
sadiqa ta fito tace kara mata.
Nima yar
nakeson daka.
Dasu maryam take cemin wai
tsabar wulakanci ance yargata ta mare mata
saurayi.
Na zaro ido nace inna banganeba.
Tace zaki gane don uwarki.
Yara saikace
kune masu gida komai ku? suka kamamu
suka jimda su yaya abduo basunan balle su
kwace mu.
Ummanmu kuwa badama tashiga
yanxu sai su mata taron dangi mukaci
kukanmu.
Umma ranta yabaci sosai ta
yanke shawaran gayawa maigari.
Bayan
yadawo tasanar dashi ya aika akiramu
dukka harda su maryam.
Yace tunda ni
bazaku barni na hutaba kullum acikin dukkan
yara kuke yau ku daki na wannan gobe na
wancan to ya isa haka.
Kowa taje tashirya
nanda sati biyu zan aurar da
maryam.khadija.aisha.dakuma bilkisu.
Tundanake a rayuwata bantaba shiga tashin
hankali irin wannan ba.
Wannan ai matsiface
baba zai dauken yabadani ina gani akan
yayuna.
Kuka nafarayi yace ku bacemin
anan.
Su maryam kuwa basuce komaiba.
Asali murna suke don suna da tsayayyu a
dangi nice dai daban da kowa.
A daki umma
tayi tagumi tace kiyi hkr danasan haka
maganar zata dawo dabanjeba.
Nayi shiru.
Hajja ma ta tsorata sosai ita gani take zaa
hada da ita.
Gydanmu aka fara shirye shiryen biki mu
hudu.
Haka gydan bappanmu ma zasu fitar
da maza hudu.
Baba yakiramu ko muna da
tsayayyu a dangi kowa tafada nata .
Nikuwa
nace banidashi.
Haka kuwa akayi kamar
yadda akeyiwa duk wacce bata fitarba zaa
hadata da kowaye.
Aka daura aurenmu.
Dangin umma na sun hallata sosai naga
gata kasancewa ni ce mace tafari da zaa kai
a dakinmu duk yayuna mazane.
Aka daura aure .
Baba yace kowa tawuce
dakinta da yamma.
Ba ko ina bane sai gidan
baffanmu.
An yanka mana gefe guda.
Kowa
ciki da falo da bandaki.
Kicin kuwa haduwa
zaayi kowa ta girka abunta.
Bansan mijina
ba amma gyra kam nasha .umma tarinka
min waaxi karki biyewa mutane kizauna da
zuciya daya dakowa baruwanki da sa ido wa
rayuwan wani.
Tamin waazi sosai sanin
datayiwa gidan.
Dare dare aka kai kowacce
dakinta.
Aka barmu daga mu sai halinmu..
Ina zaune a yafe gashi ni ba kawayeba.
Yayi
sallama yashigo akasan makoshi na amsa
masa.
Yaxo gefena yazauna tare dacewa
tashi muyi sallah.
Natashi nadauro alwala
mukayi sallah.
Yamin addua sannan yace
hau ki kwanta.
Jikina nabari don tunda nake
bantaba kebewa danamiji ba.
Yahau gadon
rumfan shima amma tagefe guda mukayi
bacci.
Tun ina dar dar har na sake jiki.
Duk
abinnan banga fuskansa ba.
Balle nagane
waya mijin..
Da asuba yatashen shima yayi
masallaci.
Bayan na idar nadan jinginu da
bangon ina tunani shikenanfa nadawo matar
auren dole.
Hmnn.
Sallama yayi na tsugunna
na gaysheshi ya amsa.
Batare da yakara
cewa komai ba ya dale kan gado.
Nikuwa
namike da xummar namana abun karyawa.
Kirana yayi KE kixo ki kwanta kawai zaa
kawo anjima.
Nace to jikina a sanyaye a
zuciyana nace tabbas baisan wa aka aura
masa ba shima.
Nakoma kan sallayata har
gari yawaye agun bacci ya kwashen.
Bayan
nafarka naga bai nan amma ga abincinnnan
an ajiye.
Benaxir intakaita miki watana hudu cif
bansan mijin danake aureba.
Inyafita da
asuba sai dare yadawo kuma fitila bayi
barina naga fuskarshi.
Shima bai taba
ganinaba.
Muryarshi kuwa kamar na mawaki
zaki ga dadin sauraro amma bai fiye
maganaba.wataran ni nake kwana nikadai
dare dare yakan sanar dani zaiyi tafiya .
Wataran yayi sati wataran kuma sati biyu.
Su maryam da khadija kuwa harda ciki.
Kasancewar mu tubali daya yasa bamu cika
hayaniya dasuba.
Asalima kanmu a hadene
saidai bani shiga cikinsu kamar yadda nake
a gyda.
Ganin zaman banzan yayi yawa yasa
na yanke shawarar sayarda awara anan
nasanar masa wata rana dare dare ya
amince harda bani jari.
Nafara sanaata ba
kama. hannun yaro.watarana naje ganin
gyda muna hira da ummata sai take
tambayana game da rayuwan aurena ina
bata amsa.
Anan ta fahimci bansan komai
akan aureba balle namata bayani in akwai
matsala.
Anan tafahimtar dani komai nace
mata umma fa ko fuskanshi ban saniba.
Tayi
mamaki kwarai namata bayanin komai.
Tace
to ke zaki gyra rayuwar aurenki.