ABOUT THIS BOOK
Description
“ACTION” Faɗin wani ƙaton baƙin mutum dake zaune kan kujerar roba.
Yana sanye ne da riga t-shirt da wando three-quarter, wiyarsa na ɗauke da sarƙan cross, sai p- cap da ke kansa, a kallo ɗaya za ka fahimci babban arne ne, duba da shigarsa da kuma fuskarsa da babu hasken musulunci ko kaɗan.
Take masu cameras suka fara ɗaukan video na wani saurayi dake tsaye shi da wata budurwa. Saurayin shi dai dogon wando ne jikinsa da riga mai dogon hannu, sai macen dake tsaye gabansa, riga ce iya gwiwa ke jikinta, ta matseta sosai, ya bi jikin ta ko ina, sannan ga kanta wanda ta sanya attachedment kai ka ce kashin tane dan yarda ya zauna.
A karo na ba adadi na yi murmushi, ina tsaye daga gefan Director, duk na ƙosa a ban dama da na shiga filin nima.
A lokacin da ya kalleni alamun zai yi min sign na shiga filin, take wani duka ya shiga fatata, wanda ya sa na tsala ihu ina dawowa duniyar gaskiya, baki na yana faɗin.
“Director see meeeee." A ɗan gigice na tashi daga barcin da ya ɗauke ni a mota.
Tsaki na ja mai tsayi wanda babu wanda zai ce daga ƙaramin bakina ya fito, take na kalla gefan da na ji wannan dukan. Sai idanuna suka haɗu da na ƴaƴanta da ke dallamin harara.
“Shashasha!, fitar min a mota, saboda ke na yi latti, yanzu 8:12am, ni da zamu shiga Lecture 8:00am. Fitar min a mota, in banda hauka daga gida zuwa nan shine za ki yi barci, harda shegen mafarkin nan ne hauka.” ta faɗa cike da ɗaga murya, murmushi na ɗan yi dan wallahi ina so naga ina ɓa ta mata rai.
“Stop insulting my dream ehe, because it means more to me than anything else in life.” Murmushi kallon mahaukaciya ta yi min.
“Hmmmm yaro man kaza, fita kafin na makeki, kuma wallahi idan ba ki bar wannan maganar ba sa na faɗa ma Dad."
“Uhmmmm a huce haka Ashenty." Na faɗa ina buɗe motar.
Makarantar mu na kalla wanda manyan motoci ne ke ta sauke yara, har na fara tafiya na tsaya cak da jin abin da take cewa.
“So you left your lunch bag with me, right?."
Dan nasan sai 6pm zan koma gida shi yasa na koma baya tare da ɗaukan lunch bag ɗina.
Ga ƙaton jakka ga lunch bag, ɗauka na yi sannan na marairaice fuska, kallon yayata nake wacce muke maka da ita, sanye take da dogon hijabi ɗinkin Jalbab, maroon colour, ta yi ƙyau sosai, fara ce mai dogon hanci, ga ƙaramin baki, sannan ga fararen idanuwa masu ɗaukan hankali, ba ƙyarya muna da ƙyau mai sunan ƙyau, dan Dad ɗin mu shuwa ne Mom kuma buzuwa ce.
“Uban me kika tsaya yi, rifomin ƙofata.” ta faɗa tana son ta da motar.
Fiƙi-fiki na yi idanuwa sannan cikin ladabin da nake yafa ma kai na idan ina bukatar abu a wajen ta nace.
“Auntyna.....Aunty Aishataahhh." Murmushi ta yi dan tasan sauran.
“Please give me some money for break.” Na faɗa cikin salon magiya.
“A gabana Mom ta baki ₦500, to kuɗin me zan kuma baki?." Tsaki na ja a cikin raina, amma da yake ina so sai na ce.
“Wallahi bayarwa zanyi, wata yarinya zan ba kyauta.”
“Hmmmm.” ta faɗa tana ciro ₦500 daga jakkarta, bani ta yi, na amsa ina washe baki har dimple ɗina na lotsawa.
“Ko duk duniya za su taru bazan yadda ke ce za ki yi ƙyautar kuɗi ba, hmmm na sanki fa." Da haka ta figa mota da gudu dan dama ita gwanace da iya wasan mota.
Murmushi na yi ina ɗaga kafaɗa, dan ko a jikina, da haka na nufa bakin get, har an fara taran latti, amma da yake ansan ban yin latti sai suka bar ni na wuce.
Babban makaranta ne wanda a ido kasan na masu kuɗi ne. Duk wasu masu ji da kuɗi to yaransu a school ɗin nan suke. School ne wanda akwai Musulmai da kiristoci, uniform ɗin mu, blue and white ne, Rigar blue mai gajeran hannu zuwa gwiwa, sai farin riga ta ci mai dogon hannu da ƙwala.
Musulmai mukan sanya legis a ciki, sannan gaba ɗaya bama sanya hijab, sai hula. To Ni wani lokacin ma nawa na jakka, haka nake yawo na da gashin kaina. A lokacin islamiyya ne kawai muke sanya hijab blue har ƙasa .
Tafiya na fara yi cikin babban makarantar, har na hau stairs, bene na ƙarshe a can S.S section yake, ina hawa na nufa S.S.3, hamdala nayi ganin babu teacher, shiga na yi kai na tsaye, bayan na yi signing da rubuta time ɗin da na shigo, akan wani book dake kan desk na teacher, dan haka tsarin yake shiyasa ko wani class akwai agogo babba daga saman whiteboard, Dan kana shigowa ka duba tare da rubuta lokaci.
Da mazan dake set ɗin gaba muka fara gaisawa ta hanyar tafawa, haka muka dinga kashe tafi muna cewa.
“Hey/Hello.”.
Haka sai da na bi kowa na ajin, mu 24, maza goma mata sha-huɗu.
Sit ɗin ƙarshe na nufa wanda a nan nake zama, kowani desk mutum biyu ne, akwai wajen aje bag da lunch bag, ajewa na yi ina gaisawa da wacce take gefena, wato mutumiyata.
“Jennifer, how are you?.”
“Am fine Dear Rose.” mur
mushi na yi dan sunan na a school kenan *Rose*, saboda ina son sunan.
Comments
Sign in to comment.