← Book details Zanjirata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 7 OF 13

Sashe 7

Zanjirata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sakkowa yike daga step yana waya yana karasowa yakashe yace "ammi ni zanfita" to kagaida ummin kace ina nan zuwa, "to zataji" yauwa, yana fitowa sojojin gurin suka sara mishi ko a jikinshi yawuce yanufi gurin motocin da zasu tafi dasu wanda gabaki daya black ne wadda ke tsakiyace kawai White me tintak yanufeta yana zuwa aka bude mishi seat din baya yashiga aka rufe, nan suka cilla motocinsu kan titi basu zame ko inaba se unguwar wuse, nan naga dankara dankaran gidaje na alfarma naga sun tsaya bakin wani dankareren gida suna horn ba bata lokaci getman ya wangale suka shige suna gama parking yafito sojojinshi suka sara mishi yafara tafiya kenan yaji an rungumoshi ta baya ko ba,afadaba yasan waxemai haka "yau agari ai naso baka tsoro wlh " kadauka ni irin Kane me yawo da allura kawai ,murmushi yace bkm yaudai zakasha magana gurin ummi, a haka suka karasa dankareren falon gdn suna isa "yau wa nike gani a gidannan kamar Mahmud " ummi ina yini ,baxan amsaba tunda baka zuwa gaidani "natuba ummi" lfy yakabro su ammin ,lfy tacema tana gaidake "ina amsawa" a haka suka cigaba da hirarsu da ashraf ,ummi tasa me aikinta uwani tacika musu gabansu da abin motsabaki , kadan yaci suka dora da hirarsu ta abokai ,ummiko tanata karanta daily thrust dinta ,sunan zaune sega sallamar abdurrashid suka amsa " ummi tace yaude manyan baki muke tayi marasa zuwa gaida umminsu"ummi ina yini ,baxan amsaba sorry ummi aikine kemi yawa shiyasa "lfy badan halinkuba" yauwa umminmu ,nan yakarasa yaba manyan abokanan nasa hannu suka gaisa "kai duk inda zaka da securities ne wai baka sirrin kanka ne" eh naji da inta yawo da allura fa kamar wani tela ,har ummi seda ta dara , sunan suna hirarsu Sega sadiya tafito taci kwalliya kamar zata dinner kayanta matsatsu sun dameta dakyar take ninfashi ba laifi kyakyawace fara , bata lura dasuba ta karaso tace ummi zanje gdn su afra "biki lura da yayyanki bane " se lokacin ta dago tagansu aiko tana ganin hadda da Mahmud ta washe baki ta matsa kusa dashi tana me kallonshi fuska dauke da murmushi "ina yininku " lfy suka fada amma banda Mahmud daketa faman danna wayarshi ,dama tunda yahangota ta tawo yadakko wayarshi saboda beson takurarta ,cikin zuciyarshi yace tana mace amma se rashin aji yana wannan tinanin ne"ya Mahmud ashe ankai twins din ammi school " adan dakile yace eh ,dankarma takara yimishi wata maganar ,dataga yayimata haka seta miki tace ummi ni zan wuce "sannan takai dubanta gurinshi tana me kallonshi tace ko baxan dawo in sameku ba ya Mahmud a gaidar min da ammi senaxo ,ya abdurrashid a gaidar min da momma " zataji inji abdurrashid ,shiko dan guntu tsaki yayi a kasan makoshi saboda yarinyar tacika surutu seta sashi ciwon kai ,a dan dakile yace zataji. Itako ko ajikinta haka taja motarta tabar gdn , haka suka cigaba da hirarsu se a na magriba suka wuce masallaci seda sukai isha,I sannan suka shigo dan yiwa ummi sallama "kutsaya kuci abinci sekace baki " munkoshi ummi , da muna jin yunwa da dakanmu zamu iba"to seda safe ko sena kara ganinku ka gaida ammi kaikuma ka gaida momma "zasuji, har bakin mota yarakosu suka hau ,sunxo futa motar sadiya tazo shigowa tadaga mai hannu shiko ko kallonta beyiba a haka har suka wuce gd ,suna isa yafito cikin takunnan nashi wanda inba saninshi kaiba zaka dauka yanayinshine saboda takama ,haka ya isa main falo yatadda ammi da abbu a dining , shima beyi watawataba yawuce dining yaja kujera " nadawo " yakabarosu ?,lfy sunce suna gaidake "ina amsawa" nan tayi serving dinshi seda suka gama suka dawo falo, yace gobe zan wuce anyimun kiran gaggawa "amma dawuri haka " eh munkoma hutufa tun last week ,ok Allah yakaimu "seda safenku " yawuce part dinshi yana xuwa ya tube yayi wanka yasaka jallabiya White ya kwanta jikin filo yana mejin kewar abin begenshi ,yahankada filon da yike kai yadakko hoton wata baby mekyau ,ya gyara wanciyarsa yadora hoton a kirjinsa "I MISS YOU MY HEART BEART" a haka bacci me nauyi yayi gaba dashi ,5:00am yafarka yayi addu,ar tashi daga barci yaje yayi wanka sannan yayi raka,atanil fajr yayi sallah asuba yana idar wa yayi azkhar sannan ya shirya cikin kakinsa na sojoji sosai yayi masa kyau ,yanufi stairs se baxa kamshi yike yana sakkowa yaga ammi ma tasha kwalliyatta cikin wani tsadadden lace pink se baxa kamshi take kasan cewar zatai masa rakiya airport, yakarasa kusa da ita yayi mata side hug morning ammi " morning son dama kai muke jira abbunka ma yanxu ze futo wuce dining bara nayi mishi magana"ok yawuce yaja kujera yazauna , tana waigawa taga yafito shima se baxa kamshi yike "mujeko" suna zuwa tace me za,a zuba maka "black coffee se chips and egg source " tana gama zuba mishi taxuba nata da abbu , suna gamawa suka fito suka hau motocinsu se nmdi azikiwe suna isa ciki naga sun nufi wata kofa karama sega wani fili ya bayyana kowa nata harkokinshi nan naga sun nufa suna zuwa wani guri aka tsaida masu hadahada, nan nahango wani private jet me kalar kayan army mekyan gaske , suka tsaya " allah yabada abinda akaje nema"Ameen yace tare hugging dinsu duka , nan yanufi gurin jet din, yana isa dukka sojojin gurin suka kame shiko ya wuce abinshi yashiga sannan sauran soldiers din suma suka shiga , nan jirginsu yadaga se *U.S.A * wannan kenan.
[7/23, 5:27 PM] Aisha Umar Ibrahim: 🦚🦚🦚🦚
ZAN JIRATA
🦚🦚🦚🦚

WRITTING

BY

AISHA UMAR IBRAHIM ✍️

*DEDICATED

To

MARDIYYA SA'EED

©️ HIKIMA WRITER'S ASSOCIATION📚
{_ home of peace, joint of entertainment to educated and enlighten our readers_}

PAGE 1️⃣3️⃣➡️1️⃣4️⃣

Tana gaba suna baya har suka isa wani block ,nan tashiga suma suka bin bayanta suna "ga new students nan kuzauna a wannan seat din kusa da waccan kunga duk ba'a gama kawowa ba daga yau nan ne seat dinku " ok sukace tawuce tayi gaba abunta, nan suka zauna "am maryam Ahmad what of you" nan sukai mata introducing din Kansu "sis ki koya mana abinda akai bama nan .

" subject daya ne shima kuma topic daya akai saboda yanxu ake kawowa English ne kawai shima kuma noun akai"a'ah kyaleshi anmana a school dinmu "ok" .

Haka sukai ta hirar su banda amatujabbar, sede in anyi wani abun tayi murmshi kasancewar ita bame yawan surutu bace ,sunan zaune teacher din basic science ne ya shigo .

"Good morning sir " morning how are you "fine " ok seat down "our topic today is characteristics of living things " nan suka maida hankalinsu kanshi har yagama yafita, wani yashigo shima har yafita akai break sukaci abinci suka dawo ,nan teachers suka yiyi musu lesson, ana gamawa suka koma hostel suka shiga wanka suka fito suka shirya cikin check blue dark wanda yayi masifar ansan jikinsu sannan aka kada bel suka wuce mosque ,suna dawowa suka wuce dining hole sukaci abinci sannan suka koma hostel suka dauki schools bags dinsu suka wuce mosque ana idar da sallah suka wuce furef .

5:30 suka dawo cikin hostel suka zauna bakin bed din amatujabbar "sis wlh ina missing yaya Mahmud " tabe baki tayi "niko ammi da abbuna kawai nike missing amma banda wannan masifaffan " aiko sena fada mashi " niko zanso inga bross dinnan naku "aiko zaki ganshi ran visiting inbe koma ba " Allah yakaimu "Ameen . shiru tayi dasu har ana kiran sallar magriba " sis dan Allah karki fadamasa"ok dama wasa nake miki "ok to kutashi mu wuce mosque" to nan suka wuce daga nan suka wuce dining hole suka ci abinci sannan suka wuce night praf basu suka dawo ba sai 10:00pm, nan kowa yakwanta kan gadonshi a haka sukaita hirarsu kamar sun dade da sanin juna "nidai nakwanta seda safanku saboda kar nayi late gurin zuwa class " muma bara mu kwanta bye ,nan suka kwanta kowacce tayi bacci asuba ta gari wannan kenan.

Inna ce zaune a gaban kaninta mlm shu'aibu tana koramai jawaban abunda suka faru jiya da ita "ba wani abubane illah sihiri amma bari nabaki wani rubutu dakuma addu'oin da zaki rinka yi insha Allahu koma menene ze karye da yardar Allah " nan tayi mishi godiya tatafi gida abunta .

Tana isa gd hartayi hanyar part dinta sai taji mutum yana kakarin amai, sekuma tajuya tayi hanyar part din cikin sauri don zatonta ma bappa ne , tana zuwa taga falon bakowa se Haj. Safiya daketa kwara amai , cike da kulawa takarasa gurinta "meyasameki safiya " kai kawai ta iya daga mata nan takira binta me aiki tagyara wajen itakuma takamata takaita part dinta nan inna tagyarata se uban sannu take mata dan tana ganin kirkin haj. Safiya bata rainata , shiyasa itama ta dauketa kamar 'yatta ta kwantar da ita kan bed tarufamata blanket sannan tafito cikin sauri.

"Bappa! Bappa !! Bappa!!!" Cikin sauri yakaraso har yaso yayi tuntube "gani inna" mekake yi har karfe 10:00am a gd , kuma ga matarka bata lfy kunshige daki kunbarta banda Allah yakawoni kenan da sede ta mutu ko "ai hkr inna wlh banjiba" kira salmanu yadubadata da'allah yarinyarnan tana jin jiki"to bara nayi mishi waya"to.

Dr. Salman yazo ya yaduba hajiya safiya ,inda yayimata test yatafi dan zuwa yadubo yadawo yafadi sakamako ,be dade ba segashi yadawo dauke da murmushi yakalli alh aliyu(bappa)"matarka nadauke da juna biyu na wata uku da sati 2 " be wani damu akan zanceba ganin irin kallon da baraka ke mishi ,nan baraka takarasa sakkowa "shege a gdn nan bade a nan ba " inna kau bakinta nauyi yayimata harta kasa furta komai ,har baraka tagama iya shegenta "dana ko yata bashege bane " juyowa baraka tai to waye ubanshi? "kinfini sani" kada kai kawai baraka tai zan maganinki , tayi gaba abunta"se anjuma safiya ki kula da kanki kinji" ngd inna.
Chapter 7 · 0% Book details