← Book details Zanjirata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 10 OF 13

Sashe 10

Zanjirata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

*
Shirye -shiye sosai suke sabo da gobe za'ah yiwa su Mahmud Karin girma .

*
amatujabbar ko ta samu sauki amma dai yanxu bata fiye zaman faloba sosaiba saboda kunya takeji .

*
Yau takama Friday anata shirye -shiye sosai gdn alhaji abdulkhadir minister of petrol, bayan anyi sallar juma'ah za'ah tafi *HILTON* *HOTEL* dan gudanar da taron wannan kenan.

*
4:00pm mutane suka fara tafiya Hilton hotel .

*
Su amaturrahman ko ammi wata me kwalliya ta dakko masu dan ta tsaramata yan biyun nata wato QUEEN TORCH,amaturrahman tafara yiwa sannan akaiwa amatujabbar ita ma ,wata hadadiyar gown white long sleeve da adon stone pink ammi ta dakko ta basu suka sa , bayan sunsane aka daura musu dankwali ,daurin zamani wato daurin tauban ansa musu touch din pink .

*
ammi ce tashigo dakin cikin tata kwaliyar wato Dubai lace " wow tace masha Allah my tweens wallahi kunyi kyau sosai "mungode suka hada baki gurin cewa ,nan tace sufito su tafi .

*
Guri yayi guri domin har an fara gabatar da taro ko ina ka kalla soldiers ne na kasa -kasa kowa'inne da irin kayansu .

*
Wata range rover ce Baka wuluk tashigo harabar hotel din tayi parking ,kafa daya tazuro saida akai 3mins sannan zuro dayar tafito tayi masifar kyau sosai cikin takun 'yammata masu ji da aji suka fara tafiya ,yayinda duk hankalin mutanen yayo Kansu suka shiga suka zauna abunsu .

*
Sai daga idanun yake ko ze hangota can yahangota kusada ammi suna hira abunsu nan aka fara karramasu .

*
Da akazo kanshi aka canza masa hula red sabanin ta da blue ce nan yasa hular gabaki daya soldiers din gurin suka Sara masa.

*
Hotuna aka Shiga yi Inda akai musu su suka gdn sannan akai da dai-dai sannan akai musu su uku ,ana cikin hoton takalminta ya goce tayi baya zata fadi harda rumtse ido se taji tafada kan mutum dagowar da zatai sukai 4 eyes dashi " are you okay "kai kawai ta iya daga masa .

*
Haka akaita gudanar da abubuwa daga karshe sukai gd cikeda gajiya .

*
Shigowa tayi a gajiye ta tarar suna kallon aljazira ta zauna saiga abba da nur sunxo sun rumgumeta " Umma sannunku da gd "yauwa falmata " baba sannu da gd" yauwa falmata ya daliban naki "lfy lau" nan suka ci gaba da kallon news dagowar da zatai taga an nuno shi ,nan tinaninta ya dawo mata "Umma shine! Umma shine!! Umma shine !!!" Shine wa...............🖊️

🏃‍♀️🏃‍♀️🏃‍♀️
Votes
and
Comments
Share plz
💞💞💞💞💞

Written
By:- [ EEHO ]
❤️❤️❤️
[7/23, 5:36 PM] Aisha Umar Ibrahim: 🦚🦚🦚🦚
*ZAN* *JIRATA*
🦚🦚🦚🦚

WRITING

BY

AISHA UMAR IBRAHIM ✍️

*DEDICATED

TO

MARDIYYA SA'EED

©️ HIKIMA WRITER'S ASSOCIATION📚
{_home of peace, joint of entertainment to educated and enlighten our readers_}.

Ina godiya da irin ruwan comments &votes din danake gani Allah ya barmu tare😍😍😍🥰.

PAGE 2️⃣1️⃣➡️2️⃣2️⃣

*
Shine !"shine wa" mijina nane "meke damunkine falmata " niba sunana falmata ba sunana hafsat anacemun hansai ,nan ta rinka basu lbrn rayuwarta harda bacewar da yarta tayi.

*
Su yagana da MLM hamdala sukaiwa Allah da yasa falmatansu ta dawo mind din ta ,nan suka shiga bawa hansai lbr tin daga farkon tsintarta dasukai Sannan yagana tace "tunda daga lokacin muka rike har Allah ya saukeki lfy kullum addu'armu Allah yasa ki dawo hayyacinki musan a ina kike " godiya sosai tai musu harda kukan farinciki nan mallam yace insha allahu gobe zamu tafi *ABUJA* insha allahu godiya, takarayimusu gami da kara kallon kyautar da Allah ya kara bata ta yaran .

*
Suna shigowa suka wuce part dinsu tsabar gajiya head din kanta kawai ta iya cirewa tai kwanciyarta kasancewa yau amaturrahman ce dayin addu'ah" sis baxaki ta shi kicire kayaba sai ammi taxo ko " ko maganinki baki shabama "malama kiyimana addu'ah inbaxakiba inyi tawa inkwanta" suna cikin haka saiga ammi tashigo "my Angels har kunyi shirin kwanciya ne to ayi addu'ah " a'ah ammi ina nan ina fama da sis kuma ma ko maganinta batashaba ammi .

*
"Tashi dan gidanku kicire kayannan kisha magani nasan dai gudun magani kike shiyasa kina dawowa kika kwanta to tashi shiyasa ina cikin su hajiya zainab na tuno natawo nasan basha zakiyiba " tashi tai ta wuce toilet tahada ruwa mai zafi a bathtube tayi wanka tafito sanye da towel da karami kuma ta dauro a kanta saboda jikewa da yalwatacen gashin ta yayi Sannan ta jona hand dryer ta busar da kanta Sannan tayi shafa Sannan tabude makeken wardrobe dinsu ta dakko wata sleeping dress wadda hajiyar Riyadh ta kawomusu me colour din blue-black tasa Sannan ta dakko band blue-black tasa a yalwatacen gashinta ba karamin kyau tayiba kasan cewarta farar fatace ta wuce kan bed ta zauna tana jiran ammi ,bata jimaba saiga ammi tashigo hanunta rikeda magungunanta da faro .

*
Tana zuwa bata tafara kukan shagwaba wai ala dole maganin daci gareshi a canza mata Wanda bashida daci nan ammi tace"amaturrahman kije ki kiramun Mahmud nasan yanxo yana gun abbunku " to tace tare da tafiya tana zuwa tace"YAYA wai kazo inji ammi "binta yayi cikin takunsa mai dauke da natsuwa har suka isa.

*
" salamu alaikum" ammi ce ta amsa itako amatujabbar tasan kwanan zance sai ta kauda kanta gefe tare da cewa"ammi kibani maganin nacefa zansha "nan ammi ta mika mata nan tafara yin kamar zata kuka tafara sha tana gamawa tafara yunkurin amai .

*
Tsawa ya daka mata wadda take gigitata yace" inkikai aman nan sai kinsha wani ai kin iya tashin mutane suna bacci ko ".(kunji fa fans din amatujabbar 🤣🤣🤣).

*
Nan ta waiga ta taga amaturrahman har tayi bacci ,fara tashinta tayi ammi tace" me zatai miki" ammi ita cefa dayin addu'ah "to kwanta sarkin rigima nai muku ".

*
Jinjina kai kawai yayi yai gaba abunshi .

*
Nan ammi tayi masu addu'ah tare da kashe hasken dakin takunna musu bed side lamp ta wuce part dinta gurinsu hajiya suka cigaba da hirarsu.

*
Yau dawani irin faduwar gaba da ciwon kai dan ko fita bai samu yiba inna ce tace " fahad jeka kiramin abbanka " nan ya shiga part din abbansa da gudu , fadawa yayi jikinsa ,ganin bacci yake farkawa yayi tare da cewa "my boy lfy " cikin hausar Sa wadda be kwareba yace inna na kiransa .

*
Tashi yayi tare da kama hanunshi suka nufi part din inna .

*
Suna isa yayi sallama tare da gaidata nan tace" lfy naga baka futa ba kaga Ali kacirewa kanka damuwa yanxu dai ita safiya addu'ah mu take buqata Allah dai yajikanta,jiyama banda na dameka da bazaka je gurin taronnanba"ameen innah "nima yanxu kwanannan wasu mafarkai nake tayi insha allahu gobe zamuje gurin sha'aibu" Allah ya kaimu innah,nan sukaita hirar abunsu .

*
Karfe 7:00am suka futo cikin shirunsu na uniform kalar blue-black da light pink do guwar riga ce iya guiwa blue-black sai ta ciki light pink me dogon hannu da doguwar sucks har guiwa sunyi kyau matuqa ,uniform din sun amshi jikinsu suka shiga sukaiwa su ammi sallama Sannan suka futa suka hau motarsu kirar *YARIS* fara Sol me bakin tintac wadda abbu ya tana zar musu dan zuwa school hamisu driver ne yajasu sai *NIGERIAN**TURKISH* suna zuwa aka amshesu Sannan aka nuna musu class dinsu wato S.S.1 A ,suka nufi class din suna shiga sukai sallama suka zauna wani seat dake gaba, nan saiga wasu yammata Wanda baxasu wuce adadin shekarunsuba suka zo gabansu suka ce "sannunku friend" .

*
Daya dagacikinsu tace "am mardiyya Muhammad suleja " dayarma tace "am Khadija Ibrahim" nan suma amaturrahman ta gabatar musu da Kansu , sukaita hira kamar sun San junansu itako amatujjabar tana dan jefa musu baki in na dariyane tayi .

*
Suna cikin shiri su saiga hafixu yayi sallama nan suka gaisa yagana tashiga bashi lbr abunda ya faru, yayi farinciki sosai Inda yace shima dashi za'aiwa hafsat rakiya ,nan suka shiga mortar mlm suka dau hanyar abuja .

*
3:00pm suka iso cikin garin abuja suka nufi unguwar *WUSE* suna zuwa ta nuna wani danqareren estate tace musu "nan ne " nan sukai horn gate man yafuto dan ganin waye saida ya matso kusa yabude baki tare da cewa "hajiya " aiko da sauri ya bude musu get suka tura hancin motarsu cikin gdn yagana da malam sai kalle-kalle suke ganin aljannar duniyar da yarsu tafito suna tsayawa, hakan yayi daidai da futowar bappa da fahad a hanunsa tana futowa taruga da gudu ta rungumeshi shima sakin fahad yayi tare da da rungumeta suka saki wani marayan kuka dakyar suka saki junansu tare da shiga cikin gdn, suma su yagana suka Shiga, fahad ne ya Ruga da gudu yaje yace inna tazo abbanshi na kuka, aiko tare suka tawo tana zuwa tai 4 eyes da hansai "mezan gani haka kamar hansai Allah da iko yake " .

*
Baraka na kitchen taji abunda inna tace futowa tayi, tayi turus ganin da gaske hansance .

*
Nan inna ta fashe da kuka tare da Neman gafarar hansai, hansai tace ta yafemata nan kowa ya ba kowa lbrn bayan rabuwa ,nan suke cemata hajiya safiya ta rasu wajan haihuwa ,nan tai musu ta'aziyya bappa ma yayita yiwa su yagana godiya .

*
Suna dawowa daga school su kai part dinsu amaturrahman ce tafara yin wanka Sannan amatujabbar tana futowa ta tarar da amaturrahman tasa bakar Arabian gown tayi roling da red bell, itama shirin tayi cikin wata peach din Arabian gown tayi rolling da black bell suka nufi part din ammi suna zuwa tace "kuje Hamisu driver yakaiku a siyo abunda za'ah Buqata " to sukace tare da yi mata sallama suka tafi .

*
6:57pm suka shigo a gajiye suka wuce part din ammi ,nan ammi ta bubuda abun da suka siyo tace" asa cake din a pridge "to suka ce suka wuce suka Sa a pridge Sannan suka wuce part dinsu sukai wanka suka kwanta ,asuba tagari.

*
5:30am suka tashi amaturrahman tace" happy birthday my lovely sis "thanks tace itakuma ta wuce toilet dan dauro alola .
Chapter 10 · 0% Book details