Part C
Tsatsuba Part 1 Complete Hausa Novel · about 9 min read
Marubuci Abdul'aziz Sani Madakin Gini
Posting By Abubakar Saleh AlQuyraemey
Domin Samun litattafan Yaƙi Contact 08138873799.
Yanzu saika mayar dani cikin wannan jaka da ke hannunka domin idan na haura rabin sa a a waje iskar duniya zata zamo sanadin ajalina saboda tsananin tsufana.
.
Koda gama fadin hakan sai nayi sauri na dauke aljani subauratu da yan yatsan hannuna biyu ina karkarwar jini na mayar dashi cikin wannan jaka sannan na rataya jakar akan kafadata ka tsaya na shigo cikin wannan gidan sarauta, lokacin da Huzallatul Marwasu yazo nan
a labarinsa sai sarauniya Larbisa ta cika da tsananin mamaki da farin ciki a karon farko a rayuwarta sai ta kama Huzallatul Marwasu da hannayanta biyu ta rungumeshi tana mai cewa tabbas kaine wanda zaka share mini hawayena saida Larbisa da huzallatul marwasu suka shafe sa a bakwai suna hira a wannan rana tare sukaci abincin dare sannan tasa aka kaishi masauki kuyangi sukayi masa wanka aka caba masa ado abinda ya baiwa larbisa mamaki shine lokacin da sukaci abincin loma daya jal Huzallatul Marwasu yayi yace ba zai iya cin komai ba.
.
Sa adda Huzallatul Marwasu ya tsinci kansa a cikin kasaitaccen daki bisa kan luntsumemen gida na alfarma ga kyawawan kuyangi sunayi masa tausa sai ya kama kyalkyala dariyar farin ciki ba sassauci tamkar sabon mahaukaci.
.
A wannan rana dai bai rintsa ba saboda farin ciki kashe gari da sassafe sarauniya larbisa ta fito fada ta zauna kuma ta tura aka kirawo dukkanin fadawanta asannan ne kuma ta tura aka kirawo Huzallatul Marwasu koda aka je sai aka iske huzallatul marwasu yana ta faman shara bacci bai tashi ba da aka koma aka shaidawa sarauniya larbisa saitace a kyaleshi yaci gaba da barcinsa har saiya farka da kansa. Al amarin da ya baiwa kowa mamaki kenan domin ba a taba ganin sarauniya larbisa ta girmama makaskanci ba haka dai Sarauniya Larbisa da fadawanta sukaci gaba da jiran Huzallatul Marwasu har saida ya farka da kansa daga barci yayi wanka ya kimtsa sannan akayi masa jagora izuwa fadar koda shigowar huzallatul marwasu sai gaba dayan fadawan larbisa suka kura masa idanu suka cika da tsananin mamaki domin basu shaida shiba cewar shine wannan almajirin da yazo yai bara yana neman abin da zaici cikin farin ciki Larbisa ta mike tsaye ta taryo Huzallatul Marwasu ta jawoshi har zuwa kan karagarta ta zaunar dashi sannan ta dubi yan majalisarta cikin natsuwa tace yaku yan majalisar birnin DAULATUL LABARUS kuyi sani cewa wannan Almajiri da ya Lume gaba daya. A dai dai wannan lokacine hawaye ya zubo mini saboda na san cewa shi kenan na rabu da mahaifina kasarmu da yan uwana har abada yanzu ne zan fuskanci sabuwar rayuwa irin wacce ban taba tsintar kaina ba a ciki kamar yadda mahaifina yayi mini bayanin tafiyar da zanyi da sharuddan daya gindaya mini a cikinta banyi wasa da guda daya ba
haka naci gaba da tafiya babu waige kuma babu magana hakika naga abubuwan Al'ajabi da yawa a cikin tafiyar tawa kuma na sami ilimi mai yawa da wayewa akan sanin mutane da al adu iri iri gaba dayan rayuwa ta ta shekara arba in da biyar din a cikin tafiya ce ta kare na shiga dazuzzuka iri iri masu mugun hadari amma duk bala in da na shiga da duk masifar da ta tunkaroni sai naga na tsira daga sharrinta, babban abinda ya bani kariya kuwa ba komai bane face wannan jakar sihiri ta Abbana sau tari sai naji wani abu mai rai yana ta motsi a cikin jakar harma nakanji kamar yana magana amma idan na bude jakar sai naga babu komai a ciki face tarin wannan zinare haka kuma idan na kasa kunnena akan jakar sai naji tsit babu wani surutu a ciki a ranar da na iso wannan birni ne guzurina ya kare na kamu da tsananin yunwa na tunkari wannan gidan sarautar sai naji wani abu na tsalle a cikin jakar sihirin kawai saina bude jakar duk da cewa ina da yakinin ba zanga komai ba bisa mamaki sai nayi arba da wani dan mitsitsin Aljani mai rafkeken kai wanda girman jikinsa bai wuce na fara ba cikin tsananin firgici na yarda jakar a kasa na ruga da guda ina waige, sai da na iso daf da kofar gidan sarautar nan sai kawai naga wannan jaka ta baiyyana a gabana tsaye cikin iska cikin firgici na yunkura da nufin na juya da baya kawai sai naji an rikeni gam na kasa koda motsa dan yatsanan hannuna take naga wannan dan guntum Aljani ya baiyana akan hannuna yana mai kyalkyala dariya wani abin mamaki. Shine mutane nata kai kawo a gabana amma bamai iya ganin Aljanin kuma ba a jin dariyarsa daga can sai aljanin ya murtuke fuskarsa yace yakai
HUZALLATUL MARWASU kayi sani cewa yanzu kai ne ubangijina tunda mahaifinka ya bar duniya lallai babu abinda zai rabani dakai face mutuwa sunana SUBAURATU IBN KIMASASA, nine jikan sarkin boyaen Aljanu na farko na dari tara da casa'in da tara nine kadai a cikin fadin duniyar nan nasan inda wannan littafin TSATSUBA yake wanda mahaifina ya rubuta kuma ni kadai ne na rage daga cikin zuri ar gidanmu gaba daya daga yau ka saki jiki dani domin ni ne kadai zan saka a tafarkin da zaka zamo gwarzon jarumi ka daina mugun cin
abincin kuma ka sami daukakar dako mahaifinka bai samuba.
.
Yanzu saika mayar dani cikin wannan jaka da hannunka domin idan na haura rabin sa a a waje iskar duniya zata zamo sanadin ajalina saboda tsananin tsufana koda gama fadin hakan sai nayi sauri na dauke aljani
subauratu da yan yatsan hannuna biyu ina karkarwar jini na mayar dashi cikin wannan jaka sannan na rataya jakar akan kafadata ka tsaya na shigo cikin wannan gidan sarauta, lokacin da huzallatul marwasu yazo nan a labarinsa sai sarauniya larbisa ta cika da tsananin mamaki da farin ciki a karon farko a rayuwarta sai ta kama huzallatul marwasu da hannayanta biyu ta rungumeshi tana mai cewa tabbas kaine wanda zaka share mini hawayena saida larbisa da huzallatul marwasu suka shafe sa abakwai suna hira a wannan rana tare sukaci abincin dare sannan tasa aka kaishi masauki kuyangi sukayi masa wanka aka caba masa ado abinda ya baiwa larbisa mamaki shine lokacin da sukaci abincin loma daya jal huzallatul marwasu yayi yace ba zai iya cin komai ba sa adda huzallatul marwasu ya tsinci kansa a cikin kasaitaccen daki bisa kan luntsumemen gida na alfarma ga kyawawan kuyangi sunayi masa tausa sai ya kama kyalkyala dariyar farin ciki ba sassauci tamkar sabon mahaukaci.
.
A wannan rana dai bai rintsa ba saboda farin ciki kashe gari da sassafe sarauniya larbisa ta fito fada ta zauna kuma ta tura aka kirawo dukkanin fadawanta asannan ne kuma ta tura aka kirawo huzallatul marwasu koda aka je sai aka iske huzallatul marwasu yana ta faman shara bacci bai tashi ba da aka koma aka shaidawa sarauniya larbisa saitace a kyaleshi yaci gaba da barcinsa har saiya farka da kansa Al amarin da ya baiwa kowa mamaki kenan domin ba a taba ganin sarauniya larbisa ta girmama makaskanci ba haka dai sarauniya larbisa da fadawanta sukaci gaba da jiran huzallatul marwasu har saida ya farka da kansa daga barci yayi wanka ya kimtsa sannan akayi masa jagora izuwa fadar koda shigowar huzallatul marwasu sai gaba dayan fadawan larbisa suka kura masa idanu suka cika da tsananin mamaki domin basu shaida shiba cewar shine wannan almajirin da yazo yai bara yana neman abin da zaici cikin farin ciki larbisa ta mike tsaye ta taryo huzallatul marwasu ta jawoshi har zuwa kan karagarta ta zaunar dashi sannan ta dubi yan majalisarta cikin natsuwa tace yaku yan majalisar birnin DAULATUL LABARUS kuyi sani cewa wannan Almajiri da yaZo ya nemi abincin da zaici a wajena shine wanda zai cika mini babban burina na duniya koda jin wannan batu sai fadawan suka sake cika da mamaki larbisa taci gaba da bayani tana mai cewa yaku yan majalisata ina so ku sani cewa na taraku ne a nan domin na sanar daku cewanan da kwana uku zanyi shiri nida wannan bako nawa mai daraja domin mu yi tafiya izuwa neman abinda zai biya mini bukatata saboda haka zan bar amanar kasata a hannunku kuci gaba da tafiyar da mulki kamar yadda nake gudanar dashi ku sani cewa ina daga can inda nake zan rinka ganin duk abinda kuke yi duk wanda yayi mini wani abu ba dai dai ba sai dai a wayi gari aga gawarsa idan akwai wani mai korafi a cikinku bisa wannan hukunci da na yanke sai yayi yanzu naji?
.
Lokacin da fadawan Sarauniya Larbisa sukaji wannan batu sai sukayi shiru suka kama kallon junansu aka rasa wanda zaice kala koda ganin haka sai larbisa ta sallami dukkanin fadawan nata suka fita suka barsu su biyu kacal ita da almajiiri Huzallatul marwasu tsawon yan dakiku da fitar fadawan sai larbisa ta dubi huzallatul marwasu tace yakai dan boka mai daraja ina son ka fito da in aljani sabauratu ibn kimasasa daga cikin jakarka ta sihiri domin ina da wadansu tambayoyi masu matukar muhimmanci da nake son zanyi masa dangane da wannan gagarumar tafiya da zamuyi koda jin wannan batu sai huzallatul marwasu ya fiddo jakar sihirinsa daga cikin babbar rigar jikinsa ya ajiyeta a gabansa sannan ya bude ya zura hannunsa a ciki ya dauko aljani subauratu bn kimasasa ya ajiyeshi a kan dan karamin tebur na zinare dake gaban sarauniya larbisa.
.
Nan take subauratu yayi sujjada ga sarauniya larbisa yana mai bude fukafukansa ya kwashi gaisuwa sannan yace da ita yake sarauniyar duniya fadi duk irin tambayoyin da kike son ki gabatar dasu a gareni ko kuwa adadin su yakai na yawan gashin dake jikin rago ko tinkiya domin babu wata iska anan wacce zata dami tsufana. Lallai zan baki amsoshin tambayoyinki ko da kuwa zan kwana dubu a zaune ina yi miki jawabinsu koda jin wannan batu sai sarauniya larbisa ta bushe da da dariya sannan tace aini tambayoyina guda uku ne kacal tambaya ta farko itace naji Huzallatul marwasu yace abokan tafiyarmu izuwa inda zamu samo littafin Tsatsuba su hudu ne kuma ukun cikinsu matane na hudun kuma namijine to wai shin menene amfanin kowanne daya daga cikinsu a cikin wannan tafiya kuma a wane garuruwa zamu riskesu,
.
Tambaya ta ta biyu itace akan wane dalili wadannan abokan tafiya tamu su hudu zasu yarda suyi mana rakiya zuwa wannan tafiya mai tsananin hadari?
.
Tambaya ta ta uku itace ta karshe shin kasan dalasiman tsafin da za a karanta a lalata gaba dayan tsafin dake cikin littafin tsatsuba?
.
Sa adda Aljani saubaratu yaji wadannan tambayoyi guda uku daga bakin sarauniya larbisa sai yayi shiru yana mai kura mata idanu cikin Al ajabi ba wani abu bane ya sa yayi shiru ba kuma ya kura mata idanu ba face tsananin kyawunta da ya dimautashi.
.
Koda larbisa ta fahimci halin da Aljani saubaratu ya shiga saita daka masa tsawa ta ce shin zaka bani amsar tambayoyina ne ko kuwa zakaci gaba da kallona ne har saika gaji nan take Aljani saubaratu ya shiga taitayinsa ya dubi larbisa cikin nutsuwa ya ce ki gafarceni ya shugabata kiyi sani kinyi mini tambayoyi ne masu matukar mahimmanci a cikin wannan tafiyartamu kuma wadanda zasu dauki dogon lokaci ina yi miki bayaninsu to nima jin wannan tambayoyi yasa zan dakata sai kuma gobe idan mai duka ya kaimu, a huta lafiya.
Ku Taba Nan Domin Karanta Littafin Tsatsuba Na Biyu Wannan Abdulaziz Sani M/Gini Ya Rubuta.
TSATSUBA
Book 1