← Book details Tsatsuba Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 1 OF 3

Gabatarwa

Tsatsuba Part 1 Complete Hausa Novel · about 19 min read

TSATSUBA

Book 1

Part A

Marubuci Abdul'aziz Sani Madakin Gini


Marubucin ya fara da cewa....

Sarauniya Larbisa ta kasance gagarumar attajira, kuma gagarumar mayakiya mai mulkin wata kasa babba wacce tafi dukkan sauran kasashen duniya girma da yawan jama ah a zamaninta sarauniya larbisa ta tara zakakuran mayaka wadanda suka kasance GUGUWAR ANNOBA domin duk kasar da suka durfafa da yaki sai sun murkusheta komai karfin mayakanta babbar matsalar sarauniya larbisa itace bata tsafi kuma tsafi baya cinta bokaye sun tabbatar mata da cewa ba zata taba haihuwa ba sai ta lalata dukkan tsafin dake duniya gaba daya idan kuwa tana son ta lalata dukkan tsafin duniyar dolene ta tura a nemo mata wani littafi mai suna TSATSUBA wanda aka rubutash sama da shekaru dubu arbaIn da suka gabata.

.

Asalin wannan littafin mallakin sarkin bokayan Aljanu ne na farko wanda shine ya kirkiro dalasiman tsafi guda miliyan dubu Arba'in daya rubucesu tsaf a cikin wannan littafi kuma yayiwa littafin lakabi da suna TSATSUBA. Duk wani tsafi na duniya mafarinsa kenan kuma makarinsa na cikin wannan dalasimai tsawan shekaru dubu Arba in din da suka gabata bokayen duniya da yawansu suka bazama neman wannan littafi har suka hallaka bisa wannan tafarkkuma duk wanda ya tsananta nemansa hallaka sukeyi saboda tsananin tsaron da aka yiwa littafin. Lokacin da sarauniya sarauniya Larbisa taji wannan batu na littafin TSATSUBA sai hankalinta ya dugunzuma ainun ta rasa abinda ke mata dadi a duniya bayan tayi dogon tunani da nazari saita watsa shela a ko ina a cikin duniya cewa duk wanda ya samo mata wannan littafin na TSATSUBA shi zata aura kuma zata raba kasarta da dukiyarta ta bashi kaso daya shidai wannan littafi na TSATSUBA duk wanda ya mallakeshi sai ya mulki komai da kowa na duniya hatta dabbobi da tsuntsaye kuwa domin zasu rinka bin duk umarnin da ya basu bisa wannan dalili ne matsafa da sarakai da manyan jarumai suka bazama neman littafin TSATSUBA suka rinka mutuwa a kokarin neman nasa.

.

Abin tambaya a nan shine waye zai iya baiwa sarauniya Larbisa littafin TSATSUBA alhalin yasan cewa idan yana tare da littafin ita kanta zai iya mallakarta kuma zai sami kowace irin dukiya da yake so ko matsayi?

.

Masana da matsafa sun tabbatar da cewa babu wata mai kyan fuska da kyan jiki tamkar gimbiya Larbisa a zamaninta kuma a wannan lokaci data bayar da shelar a nemo mata littafin TSATSUBA shekaranta ashirin daidai a duniya kuma tun tana da shekara goma sha biyu ta hau kan karagar mulki.

.

Sarauniya Larbisa bata da wani buri wanda yafi ta sami magajinta kafin tsufa ya risketa don kada mulkinta ya tafi hannun wanda ba jininta ba kasancewar itace kadai ta rage a irin zuri ar gidansu. Wata rana sarauniya Larbisa na zaune a fadarta ana tafiyar da harkokin mulki kamar yadda aka saba saiga wani almajiri ya shigo yana bara har dakaru sun tareshi zasu koreshi waje sai sarauniya Larbisa tayi musu tsawa suka kyaleshi nan take Larbisa ta mike tsaye daga kan karagar ta taka taje har wajen almajirin ta kama sandarsa ta rike ta dubeshi tace zan baka abinci kaci ka koshi yanzu ya kai wannan tsoho amma ba zaka iya biyana ba da komai domin ni bana bukatar abinci ko dukiya koda gama fadin haka sai sarauniya larbisa ta juya ta ja tsohon har zuwa cikin gidan sarauta. Al amarin da ya baiwa kowa mamaki kenan hatta mutanan gari da sauran masu fada aji saboda ita dai sarauniya larbisa bata kasance mai tausayi da jin kan talakawa ba kuma tana da tsananin rowa bata bayar da abin hannunta face akan bukatarta kawai.

.

Lokacin da sarauniya Larbisa takai wannan almajiri cikin babban falo na turakarta wanda girmansa yakai na wani gida guda sai tsohon ya zama cikakken dan kauye ya kama kalle kalle domin bai taba tsintar kansa a cikin waje mai ni ima da daula ba irin wannan gaba daya falon a shimfide yake da wata irin dadduma mai tsananin laushi da zarar ka taka daddumar sai kaji kamar zaka nutse a cikinta saboda taushi kujerun dake zagaye a falon gaba daya anyi sune da zinare kuma sun kai kamar guda dari biyu. A tsakiyar falon an ajiye wani katon gunkin tsuntsun dawisu akayi shi da karfen jauhar mai launin kore da rawaya kuma anyi masa wata hikima ruwa na ta zuba a cikin dawisun yana taruwa akan wani katon faranti na lu'u lu'u abin dai akwai ban sha awa da ban al ajabi.

.

A saman rufin falon kuwa wadansu irin fitilu ne sama da guda dubu daya wadanda suma da lu u lu u akayisu sai sheki da walwali suke tayi. Baya ga wannan wani irin kamshi na tashi a cikin falon wanda mutum bai san ko daga ina yake fitowa ba duk inda almajirin ya duba a cikin falon sai yaga kuyangi ne tsala tsala sunata hidimar goge goge da gyare gyare tabbas wannan wuri Ya cika aljannar duniya. Almajirin ya dubi kujerar sai tayi masa kwarjini ainun ya ga cewa shidai bai kasance basarake ba ina shi ina zama akan irin wannan kujera kawai sai ya zauna a kasa dirshan bisa wannan darduma mai taushi koda ganin haka sai sarauniya Larbisa da kuyanginta suka bushe da dariya domin basu taba ganin wanda yayi wannan kauyancin ba. Sarauniya Larbisa ta dubi shugabar kuyangin wacce ake kira da suna HULAIRA tace da ita aje a kawowa bakona duk irin kalar abincin dake gidan nan hulaira tace an gama ya shugabata nan take hulaira ta juya ta fice daga cikin falon ita kuma sarauniya larbisa saita dubi almajirin tace bayan ka huta zan dawo gareka da yamma domin muyi yar hira kafin na sallameka ka tafi saboda kazo mini da bayani wanda yaje fani a cikin wasi wasi da kace idan na ciyar da kai zaka ciyar dani har abada alhalin ni babu abinda na nema na rasa na gada abinci ko dukiya lallai ba zaka tafi ka barni a cikin duhu ba saika wayar mini da kai.

.

Koda gama fadin haka sai sarauniya ta wuce izuwa can cikin turakarta sai data jima tana tafiya sannan ta kule almajirin ya daina hangota nan fa almajirin ya shiga sakar zuci yana mai cewa a ransa wai shin yaya cikin turakar sarauniya zai kasance a kyau da kawatuwa?

.

Lallai dole ne ya ninka nan falon a komai jim kadan da tafiyar sarauniya Larbisa saiga wadansu kuyangi daban su goma sha biyu sun shigo cikin turakar kuma kowacce na

dauke da katon faranti abinci akan kowanne faranti akwai abinci kala shida nan take kuyangin suka ajiyewa almajirin farantin abincin a gabansa suka juya suka fice.

.

Al amarin daya firgita gaba dayan kuyangin dake cikin falon kenan suka fara tunanin anya kuwa wannan almajirin mutunne a iya zamansu a gidan sarautar basu taba ganin

mutumin da ya taba cinye koda kwano daya na abincin kasancewar kwanukan manya ne kuma cike suke taf da abinci sau tari sai mutane biyar sun taru suke iya cinye kwano daya lokacin da almajirin ya gama da abincin farantin dake gabansa sai ya janyo wani farantin ya gwamutsa abincin kwanon shidan akan farantin duka ya kama ci nan da nan ya karar da abincin ya janyo faranti na uku koda ganin haka sai gaba dayan kuyangin suka firgice suka ruga wajen falon a dimauce suna ihu kuma suka tsaya a can bakin kofar falon suna leken almajirin.

.

Abu dai kamar wasa sai da almajirin ya cinye gaba dayan abincin dake kan farantin yayi gyatsa dama an kawo masa ruwan inibi cikin tambulan guda koda ya kafa tambulan din a bakinsa sai yayi masa kurba uku ya zukeshi duka shi kuma wannan tambulan din sau tari idan aka cikoshi da ruwan inibi komai yawan bakin da sukazo gidan basa shanye shi gaba daya sai kaga sun rage wani abu sa adda kuyangi sukaga almajirin ya cinye gaba dayan abinci kuma ya shanye ruwan inibin sai suka kara dimaucewa suka ruga izuwa cikin gidan sarautar suna ihu da fadin cewa tabbas Aljani ne a cikin falon sarauniya ba mutum bane koda jin wannan bushara sai dakarun tsaro na gidan sarautar suka zare makamansu suka ruga zuwa cikin falon sarauniya larbisa suka yiwa almajirin kawanya.

.

Al amarin da ya matukar baiwa almajirin mamaki kenan kuma ya tsorata shi domin bai san laifin da ya aikataba har akazo aka yanyameshi haka.

.

Ana cikin wannan haline sarauniya Larbisa taji wannan abin Al ajabi sai itama ta cika da tsananin mamaki cikin hanzari ta mike tsaye daga kan kujerar da take zaune ta taho cikin falon nata da shigowarta cikin falon ta iske dakarunta sun yiwa almajirin kawanya suna tsuma ba tare da sun afka masa ba ga dukkan alamu suma sun tsorata ne bisa ganin gagarumin aikin da yayi nan take sarauniya larbisa ta dakawa dakarun tsawa suka ja da baya har ta hango almajirin zaune a tsakiyar su yana kyarma cikin alamun tsananin tsoro har ya jike sharkaf da gumi.

.

Al amarin da ya baiwa sarauniya larbisa mamaki kenan nan take ta gamsu a cikin zuciyarta cewa lallai wannan almajiri ba aljani bane mutum ne domin inda aljani ne babu abinda zai sa ya tsorata bisa ganin dakarunta izuwa kansa Larbisa ta dubi dakarun nata da dukkan kuyangin dake cikin falon tace kowa ya fita ya barsu cikin gaggawa suka bi wannan umarnin falon yayi tsit tamkar mutuwace ta gifta.

.

A wannan lokacine sarauniya larbisa ta tashi taje har daf da almajirin ta zauna tana mai yi masa wani irin kallo na rashin yarda tace yakai wannan tsoho bani labarinka ka sanar dani komai bisa gaskiya idan kuwa kayi mini karya ba zaka fita daga nan a raye ba. Lokacin da almajirin yaji wannan tambaya sai yayi ajiyar numfashi nan da nan idanunsa suka ciko da kwalla har hawaye ya zubo masa sannan ya dubi sarauniya yace ni dai sunana HUZAILATUL MARWASU kuma na fito ne daga can kudancin duniya a wata kasa da ake kira MADINATUL SAUWABA mahaifina ya kasance kasurgumin matsafi wanda yayi nisan kwana a duniya domin sai da ya shekara dari hudu da arba in da uku a duniya sannan ya mutu lokacin ina da shekara shida kacal a duniya. Duniya kuma nine dan auta kuma tun ina jariri uwata ta mutu ta barni a wannan lokaci ragowar yan uwana su hudu duk sun haura shekara ashirin sai mai ashirin da yaya wadannan yayye nawa sun taso da hikima gami da saurin daukar ilimin tsafi a wajen ubanmu nan da nan kowannansu ya zamo shahararren boka ni kuwa saina taso da dakikanci duk abinda aka koya mini bana iya yi ko karanta mini dalasiman tsafi mahaifina yayi bana iya biyawa kamar yadda ya biya haka kuma na kasance malalacin gaske bana iya yin aikin komai ko da kuwa sharar gida ne bisa wannan daliline sauran yan uwana suka tsaneni bugu da kari saina taso da tsanancin cin abinci mai yawan gaske amma kuma idan naci na koshi ina iya yin kwana ashirin da daya ban kara cin komai ba sai dai nayi ta shan ruwa wani abin mamaki kuwa shine a tsawon kwana ashirin da dayan bana kawai da bukatar bawali ko bayan gida sai dai ta kai cewa an cinye gaba dayan abincin dake gidanmu wanda mahaifimu ya tanada a rumbu wanda a takaice zamu iya.shekara goma muna amfani dashi duk wani halaiya tawa bata taba sa mahaifina ya tsaneni ba face ma yana dada nuna mini soyayya da janyoni a jikinsa su kuwa yan uwan nawa sai haka yasa suka dada tsanata ya zamana cewa idan mahaifinmu ya aikemu cikin gari ko kasuwa sai suyi mini dukan tsiya akan hanya wani lokacin ma dukan kawo wuka sukeyi mini har sai jama ar gari sun kwaceni sai dai a dawo dani gida jina jina kafin a kawoni gida sai yan uwan nawa su rigani komawa suce da mahaifinmu sun hadune da abokan gabarmu yayan wani bokan garinmu an fafata yaki sau uku hakan na faruwa don haka sai mahaifin nawa ya hanani fita ko ina ya zamana cewa kullum muna tare dare da rana ko barci mahaifina zaiyi sai ya tabbatar da cewar ina kwance akan kirjinsa...


Zan dakata anan sai kuma gobe idan Allah mai kowa da komai ya kaimu a huta lafiya.

Ku Taba Nan Domin Karanta Littafin Tsatsuba Na Biyu Wannan Abdulaziz Sani M/Gini Ya Rubuta.

TSATSUBA

Book 1

Part B

Marubuci Abdul'aziz Sani Madakin Gini

Posting By Abubakar Saleh AlQuyraemey

Domin Samun litattafan Yaƙi Contact 08138873799.


A kullum idan na tuna irin yanayin halittar da na taso ciki na dakikanci lalaci da cin tsiya saina kamu da tsananin bakin ciki nayi ta kuka shi kuwa mahaifin mau sai yayi ta rarrashina yana mai cewa ya kai dana kayi sani cewa akwai ranar da zaka rabu da duk wadannan matsaloli amma sai a bayan mutuwata bayan kayi wata doguwar tafiya lallai kafin mutuwata zan sanar dakai bangaren da zakaje a cikin duniya domin ka rabu da wannan matsaloli A sannan ne zaka sami wata gagarumar daukaka irin wacce ni kaina ban samu ba kayi hakuri da duk irin musgunawar da yan uwanka zasuyi maka daga nan har izuwa ranar mutuwata domin hakuri naka shine zai kaika izuwa kan tafarkin daukakarka nasan cewa yan uwanka basu da wani buri wanda yafi su hallakaka saboda ya zamana cewa ba zaka mallaki komai ba daga cikin dukiyar dana tara babu yadda basuyi ba don su hallakaka amma sun kasa domin ina baka kariya ta musamman duk abin dake faruwa ayayin da kuka fita kasuwa ina gani daga nan a cikin madubin tsafina duk sa adda kaga jama ar gari sunzo sun ceci rayuwarka daga hannun yan uwanka toba mutane bane sukazo nine na rikide zuwa siffar mutane nazo na muku, wannan bakar wahalar da kake sha a hannunsu itace alamun samun daukakarka tanan gaba.

.

A duk sa adda mahaifin namu yazo nan a zancensa sai na fashe da kuka nace ya kai abbana yanzu idan ka mutu waye zai iya ci gaba da ciyar dani alhalin yanzu kana ciyar da nine da karfin Sihirin tsafinka ?

Idan baka nan ya za ayi na tsira daga sharrin yan uwana?

.

Dajin wannan tambaya sai mahaifina yayi murmushi yace nayi maka alkawari ko a bayan raina ba zaka fuskanci matsalar komai ba kuma ba zaka sha wahalar komaiba sannan wahalar ba zata yi dogon lokaci ba.

.

Haka dai mahaifina yaci gaba da rarrashina yana bani mamaki a duk sa adda nake cikin damuwa ko tashin hankali wata rana da farkon dare sai mahaifina ya kamu da matsananncin rashin lafiya har ya kama kumallon jini nan fa muka hadu mu biyar din a kansa a lokacin da hankalina ya yi matukar dugunzuma na fara kuka su kuwa sauran yan uwan nawa ko kadan babu alamar wata damuwa a fuskarsu kawai sai suka kama yake mahaifin namu ya dubi sauran yan uwan nawa yace dasu ku tafi izuwa cikin daji ku nemo mini ganyen bishiyar Suljara Shine kadai abinda za a jika mini nasha na sami sauki koda jin wannan batu sai hankalin yan uwan nawa ya tashi babban cikinsu ya dubi mahaifin namu cikin Alamun matukar damuwa yace yakai abbanmu ka sani cewa bishiyar suljara yana da matukar wuyar samu a duk cikin dazuzzukan garinmu zamu iya kwana a cikin daji muna nemansa dajin haka sai mahaifinmu ya fusata yace shin yanzu wahalar da zaku sha a cikin daji tafi lafiya ta muhinmanci kenan a wajanku idan har ba zaku tafi neman wannan ganye ba yanzu take zan lalata dukkan sirrin tsafin da kuka mallaka kuma ta kone dukkan dukiyata dake cikin gidan nan koda jin wannan batu sai yan uwan nawa suka juya suka fice daga cikin dakin suna gunaguni cikin fishi sai bayan yan uwana sun dade da tafiya daji sannan mahaifina ya mike zaune da kyar sannan ya janyoni izuwa jikinsa ya rungumeni akan kirjinsa kawai sai naji hawayen idanunsa na zuba akan fuskata cikin karfin hali ya budi baki yace yakai dana ka saurara Da kyau ka nutsu kaji jawabin da zan maka idan har ka ka rike abin da zan gaya maka yanzu lallai zaka sami daukakar da tafi tawama kayi sani cewa na aiki yan uwanka ne izuwa daji domin na sami damar da zan sanar dakai babban sirrin dana adana maka a cikin zuciyata tsawon shekara da shekara ka sani cewa tsananin kaunarka da tausayinka da nake ji bisa.yanayin halittar da ka kasance ne yasa na adana maka wannan babban sirri. A yau kuma nan bada dadewa ba wa adina zai cika na bar wannan duniya da zarar kaga na mutu kayi sauri ka shiga cikin turakata ka dafa bakin akwatina na karfe da hannunka na hagu take akwatin zai bude zakaga wata jakar gata a ciki saika dauki jakar ka ratayata a kafadarka ka fice daga gidan nan, kana fita zakaga gidan nan ya nutse izuwa cikin karkashin kasa ya bace bat tamkar bai taba wanzuwa ba awajen, daga nan sai ka juya ka nausa yamma kayi ta tafiya har saika fita daga cikin garin nan ka nausa daji, duk iya tsawon tafiyar da zakayi ka da kayi wage ko da zakaji sukuwar giwaye a bayanka, duk inda ka gamu da mutum ko aljan kada kayi masa magana kuma idan yayi maka magana kada ka amsa ba zaka riski wani gari ba sai bayan kwana ashirin da daya , kana shiga garin ka bude wannan jaka zaka iske babu komai a cikinta face dinare mai yawan gaske saika nemi abinci mai yawa wanda zai isheka ka koshi ka siya amma ka tabbata cewa a boye zaka cinye wannan abinci ba a gaban jama ba, kada ka kuskura ka kwana a wannan gari da zarar ka koshi saikayi harama ka sayi doki kahau kaci gaba da tafiya ina mai tabbatar maka da cewa saika shekara Arba'n da biyar kana wannan tafiya kana ta keta dazuzzuka da birane a sannane zaka cika shekara hamsin da daya a duniya kuma a wannan lokacine guzurin dake cikin jakarka zai kare, ka iso wani babban birni inda wata mashahuriyar sarauniya ke mulki. A sannan ne yunwa zata gallabeka don haka ka nemi hanyar gidan sarauta kana zuwa fada ka wuce kai tsaye zuwa gaban karagar mulkin kana mai yin bara kana cewa waye zai ciyar dakai yanzu ni kuwa na ciyar dashi iya rayuwarsa?

.

Tabbas wannan sarauniya zata sa a baka abinci da zaka koshi bayan nan ka tambayeta babban burinta na duniya lallai zata zo maka da batun wani littafi waishi TSATSUBA lallai kaine zakayi jagora bisa tafiyar da za ayi ta neman wannan littafi tabbas za a samu wannan littafi har bukatar wannan sarauniya ta biya a sannan ne zaka sami lada mai tsoka daga wajan sarauniyar kamar yadda tayi alkawarin zata bayar ga wanda duk ya samo mata littafin TSATSUBA,

.

A cikin tafiyar da zakuyine zaka sami daukaka irin wacce babu wani boka da ya taba samunta har duniya ta shube ba za a manta da kaiba

a cikin tarihi, amma ka sani cewa zaka sha tsananin ukuba a cikin wannan tafiya kuma zakuga abubuwan Al'ajabi da yawa.

.

Sa adda mahaifina yazo nan a zancensa sai na cika da Tsananin mamaki na dubeshi cikin alamun rashin fahimta nace ya kai abbana yanzu nida nake malalaci matsoraci kuma dakiki ya za ayi na iya jagora a cikin wannan gagarumar tafiya alhalin ma ban san inda za a je ba asamo wani littafi wai shi TSATSUBA?

.

Yayin da mahaifina yaji wannan tambaya saiya ya yunkura domin ya bani amsa amma sai tari ya sarkeshi yaci gaba da aman jini, Al amarin daya dugunzuma hankalina kenan na dimauce naci gaba da matsanancin kuna ina mai kankame mahaifina, daga can saiya daina wannan kumallon sannan ya janyeni daga cikin jikinsa muka fuskanci juna sosai a lokacin da idanunsa ke lumshewa yana budewa da kyar ya budi baki yace yakai dana abin kaunata kayi sani cewa muddin kana tare da wannan jaka ta guzurinka babu abinda zai gagareka kuma babu wani tsautsayi da zai saka rasa rayuwarka.

.

Sai kun shekara daya da rabi sannan zaku isa inda littafin TSATSUBA yake kuma wannan jaka taka itace zata rinka yi muku jagora , ba zaku sami nasarar zuwa inda wannan littafi yake ba sai kun hadu da wadansu jarumai guda hudu, uku mata ne daya namijine ma abota wani addini da ake kira musulunci, wannan jaka taka itace zata kaiku wajen wadannan jarumai guda hudu, sa adda naji wannan batu saina kara cika da mamaki bisa yadda za ace jaka zatayi magana a cikin wannan doguwar tafiya alhalin bata kasance abu mai raiba kuma ba magana takeyi ba har na budi baki zan tambayi mahaifina ta yadda wannan jaka zatayi mana jagora a cikiin tafiyar sai naji gaba dayan jikinsa ya sandare kamar gunki idanunsa kuwa sun kafe, cikin dimauta na girgizashi amma ko motsi baiyiba, kawai saina rungumeshi na fashe da kuka cikin sauri na maida shi shimfidarsa na kwantar dashi sannan na ruga zuwa cikin turakarsa.

.

Da shigata sai naje na dafa bakar akwatin mahaifin namu da hannu na na hagu faruwar hakan keda wuya sai akwatin ya bude nayi arba da wata jaka wadda akayi ta da fatar damisa koda na dauki jakar sai naji tana da dan nauyi kawai saina rataya jakar a kafadata na fita da sauri daga cikin gidan, ai kuwa ina fita sai naga gidan namu ya kama nutsewa cikin karkashin kasa har saida ya Lume gaba daya. A dai dai wannan lokacine hawaye ya zubo mini saboda na san cewa shi kenan na rabu da mahaifina kasarmu da yan uwana har abada yanzu ne zan fuskanci sabuwar rayuwa irin wacce ban taba tsintar kaina ba a ciki kamar yadda mahaifina yayi mini bayanin tafiyar da zanyi da sharuddan daya gindaya mini a cikinta banyi wasa da guda daya ba haka naci gaba da tafiya babu waige kuma babu magana hakika naga abubuwan Al'ajabi da yawa a cikin tafiyar tawa kuma na sami ilimi mai yawa da wayewa akan sanin mutane da al adu iri iri gaba dayan rayuwa ta ta shekara arba in da biyar din a cikin tafiya ce ta kare na shiga dazuzzuka iri iri masu mugun hadari amma duk bala in da na shiga da duk masifar da ta tunkaroni sai naga na tsira daga sharrinta, babban abinda ya bani kariya kuwa ba komai bane face wannan jakar sihiri ta Abbana sau tari sai naji wani abu mai rai yana ta motsi a cikin jakar harma nakanji kamar yana magana amma idan na bude jakar sai naga babu komai a ciki face tarin wannan zinare haka kuma idan na kasa kunnena akan jakar sai naji tsit babu wani surutu a ciki a ranar da na iso wannan birni ne guzurina ya kare na kamu da tsananin yunwa

na tunkari wannan gidan sarautar sai naji wani abu na tsalle a cikin jakar sihirin kawai saina bude jakar duk da cewa ina da yakinin ba zanga komai ba bisa mamaki sai nayi arba da wani dan mitsitsin Aljani mai rafkeken kai wanda girman jikinsa bai wuce na fara ba cikin tsananin firgici na yarda jakar a kasa na ruga da guda ina waige, sai da na iso daf da kofar gidan sarautar nan sai kawai naga wannan jaka ta baiyyana a gabana tsaye cikin iska cikin firgici na yunkura da nufin na juya da baya kawai sai naji an rikeni gam na kasa koda motsa dan yatsanan hannuna take naga wannan dan guntum Aljani ya baiyana akan hannuna yana mai kyalkyala dariya wani abin mamaki Shi ne mutane nata kai kawo a gabana amma bamai iya ganin Aljanin kuma ba a jin dariyarsa daga can sai aljanin ya murtuke fuskarsa yace yakai HUZALLATUL MARWASU kayi sani cewa yanzu kai ne ubangijina tunda mahaifinka ya bar duniya lallai babu abinda zai rabani dakai face mutuwa sunana SUBAURATU IBN KIMASASA, nine jikan sarkin boyaen Aljanu na farko na dari tara da casa'in da tara nine kadai a cikin fadin duniyar nan nasan inda wannan littafin TSATSUBA yake wanda mahaifina ya rubuta kuma ni kadai ne na rage daga cikin zuri ar gidanmu gaba daya daga yau ka saki jiki dani domin ni ne kadai zan saka a tafarkin da zaka zamo gwarzon jarumi ka daina mugun cin abincin kuma ka sami daukakar dako mahaifinka bai samuba.

Ku Taba Nan Domin Karanta Littafin Tsatsuba Na Biyu Wannan Abdulaziz Sani M/Gini Ya Rubuta.

TSATSUBA

Book 1
Chapter 1 · 0% Book details