← Book details Tsatsuba Book 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
CHAPTER 2 OF 3

Part C.

Tsatsuba Book 3 Complete Hausa Novel · about 11 min read

Na Abdul'aziz Sani Madakin Gini
Posting By Abubakar Saleh AlQuyraemey
08138873799 For More Littattafan Yaƙi
.
Lokacin da Hulkas yazo nan a zancensa sai shima sarki shardas jikinsa yayi sanyi ruwan hawaye ya subuto daga cikin idanunsa ya janye jikinsa daga jikin na hulkas suka fuskanci juna yana mai rike kafadunsa yace yakai dana kayi sani cewa ko kadan nima bana son abinda zai sosa maka zuciya kuma babu abin da nake so sama da ganin farin cikinka amma in ba don haka ba da tsawon sa a daya zan kasance a cikin zumudi da dokin dawowarku lafiya kaida mahaifiyarka domin kune ginshikin rayuwata, haka dai sarki shardas da yarima hulkas sukayi ta hira ta bankwana har asubahi ta riskesu basu sani ba a sannan ne hulkas ya fara gyangyadi kafin a jima barci ya daukeshi faruwar hakan keda wuya saiga shadila ta shigo sanye da rigar barci wacce ke baiyana kyakkyawar surar jikinta babban abinda ya daurewa sarki shardas kai shine bai taba ganin murmushin shadila ba a duk sa adda zata shigo turakarsa da daddare sai yau tun a farkon ranar da ya satota daga sansaninsu ya kawota wannan gidan sarauta saboda ya tabbatar da cewar ta tsaneshi kamar yadda ta tsani mutuwarta kai tsaye shadila ta fado kan sarki shardas ta fara jan hankalinsa domin ya kwadaitu da ita maimakon ya karbeta hannu biyu sai kawai taga ya bangajeta ta fadi can gefe daya akan gadon ya dubeta a fusace yace menene dalilin da yasa yau kika shigo cikin turakata kina mai murmushi alhalin baki taba yi mun murmushi ba a dukkan dararen da suka shude na barcinmu??
.
Koda jin wannan tambaya sai shadila ta bushe damahaukaciyar dariya kamar ba zata daina ba karfin dariyar nata baisa yarima hulkas ya faka daga barcin da yake yi ba mai nauyi saboda kasancewar barcin mai nauyi ne daga can sai shadila ta tsuke bakinta ta daina yin dariyar tana mai murtke fuska ta dubeshi tace yakai mijina na dole ka sani cewa ban taba jin kaunarka ba a cikin zuciyata dai dai da darajar kwayar zarra kaine ka rabani da farin cikina kuma kaine ka shayar dani gubar bakin cikin da har abada ba zan iya amayar da ita ba sai dai ajalina ya zame mini saukin ciwon data sa mini Abinda yasa kaga na shigo cikin turakarka ina murmushi a yau ba komai bane face farin ciki bisa sanin cewa gobe zan rabu da ganin wannan fuska taka kuma ba zan sake ganinta ba har sai bayan a kalla sati byu ka sani cewa duk sa adda na kalli fuskarka sai naji kamar bakin kumurci nake kallo haka kuma duk sa adda ka kwanta dani nakanji mugun bakin ciki tamkar na kashe kaina saboda ba masoyina hailu bane yake amfani da wannan kyakkyawan jiki nawa, yanzu na kawo maka kaina ne gareka domin ka more iya son ranka saboda kwanaki goma sha hudu masu zuwa a mafarki jikin nawa zai zama na masoyina wanda ka datse rayuwarsa ka mayar da dansa maraya koda shadila tazo nan a zancenta sai zuciyar sarki shardas ta kama tafarfasa kamar zata kone jikinsa ya kama tsuma ya daga hannu da nufin shararawa shadila mari amma sai ya kasa saboda tsoron kada ya maretan hulkas ya farka daga barci ya gane abinda ya faru tsakaninsu koda shadila taga sarki shardas ya kasa marinta saita sake bushewa da dariya a karo na biyu ba tare da tace dashi uffan ba sai tasa hannayanta biyu ta dauki danta hulkas ta rungumeshi a kirjinta ta juya ta fice daga cikin turakar shi kuwa sarki shardas sai ya bita da kallo kawai cikin tsananin takaici da bakin ciki fuskarsa nayin gatsine yana jin kamar ya zare takobi yaje ya sareta gari na wayewa sosai sai sarki Shardas ya kirawo mataimakin sarkin yakin kasar wanda ake kira sadauki marzanu ya dubeshi yace ina son ka zabo zakwakuran dakaru mutum dubu biyu daga cikin manyan dakarunmu kayi musu jagora a cikin rakiyar matata da dana yarima hulkas izuwa birnin ishtanbul kayi sani cewa zan baku guzuri ishashshe kuma zan baku kudade masu yawan gaske domin ku kawai da dukkan bukatunku amma ku sani cewa idan kuka dawo daga birnin istanbul naga kwarzane guda daya a jikin matata ko dana ko kuma kuka dawo mini dasu babu lafiya ko babu rai a bakacin rayukan iyalanku daku kanku.
.
Koda jin wannan batu sai sadauki marzanu yarisina yace an gama ya shugaban nan take marzanu ya juya da sauri ya nufi wani bangare daban na gidan sarautar domin ya hado kan dakarun daya dace suyi masa rakiya a cikin wannan gagarumar lafiyamai hadari kafin rana ta take tuni kowa ya gama kimtsawa daga cikin jama ar da zasu yi wannan tafiya shadila da yarima hulkas kuwa sai suka caba ado mai daukar hankali suka shiga cikin keken dokin sarauta, sadauki marzanu da sauran dakaru kuwa suka hau dawakai cikin gagarumar shigar yaki suka sa keken dokin a tsakiya sai kuma kuyangi guda uku kacal da aka tanada domin su yiwa shadila da hulkas hidima a cikin wannan tafiya.
.
Ba tare da bata lokaci ba wannan zuga ta kama hanyar fita daga cikin gidan sarautar, abinda ya daurewa yarima Hulkas kai shine rashin ganin sarki shardas a wannan safiya bare suyi sallama har ya budi baki zai tambayi shadila dalilin da yasa sarki baizo sunyi bankwana ba sai.
.
Kawai ya hango sarki shardas a can saman bene yana dago masa hannu kuma idanunsa sun ciko da kwalla nan take zuciyar yarima hulkas ta karaya shima ya ji hawaye ya zubo masa take yaji kamar ya fasa yin wannan tafiya kawai sai hulkas ya daka tsalle ya duro kasa daga kan keken dokin ya ruga da baya izuwa inda sarki yake can saman bene, babu shiri mai jan keken dokin yaja linzami ya tsaidashi itama shadila sai ta duro daga cikin keken dokin a dimauce don a zatonta wani mugun abune ya faru amma sai taga ashe yarima ne ya ruga izuwa inda sarki yake.
.
Lokacin da sarki shardas yaga yarima hulkas ya rugo izuwa gareshi sai shima ya gangaro da gudu daga saman benen da yake tsaye ya tari yarima a tsakiyar filin gidan sarautar suka rungume juna kuma suka kama kuka a lokaci guda saboda bakin cikin rabuwa yarima hulkas ya dada kankame sarki, yace yakai abbana mene ne dalilin da yasa kaki zuwa muyi bankwana tun dazu alhalin kasan cewa ina ciikin kewarka da tunanin rashinka a kusa dani.
.
Sa'adda sarki shardas yaji wannan batu sai ya janye jikinsa daga cikin nasa suka fuskanci juna a lokacin da kowannansu ke zubar da hawaye sarki shardas ya numfasa yace yakai dana kayi sani cewa ni jarumi ne kuma gwarzon mayaki wanda bai taba zubar da hawaye ba komai wuya da azaba kuma komai farin ciki da bakin ciki tun daga kuruciyata kawo izuwa girmana amma yau gashi kai ka sani na zubar da hawaye ina mai tabbatar maka da cewa in banda mahaifiyarka babu wani mutum wanda na taba jin ina sonsa dari bisa dari a cikin zuciyata sai kai kuma a halin yanzu soyayyata a gareka ta linka dari bisa dari fiye da komai kuma kai kadai ne mutumin da nake jin cewar ba zan iya cutar da shi ba bisa duk irin laifin da zakayi mini koda kuwa bakin cikin abin dakayi min zai zamo sanadin ajalina.
.
Koda jin wannan batu sai yarima hulkas ya sake rungume sarki ya fashe da matsanancin kuka yace yakai abbana tabbas nasan kana kaunata fiye da kima amma ni ina jin kusancinka a raina fiye da kusancin jini da hanta inaji a raina cewar idan babu kai a wannan duniyar ba zan rayu ba kuma ina jin cewar rashinka a kusa dani dai dai yake da jefani cikin kurkukun da babu ci ba sha kuma babu hasken da mutum zai iya ganin ko da tafin hannunsa face matsanancin duhun daba zai misaltu ba koda jin haka sai sarki shardas ya janye jikinsa daga cikin na yarima hulkas kansa na sunkuye yana zubar da hawaye kawai sai ya daga hannu ya yiwa sarkin yaki marzanu inkiya nan take marzanu ya rugo ya dauke yarima hulkas ya ruga da shi izuwa bakin keken dokin ya sashi a ciki itama shadila sai ta koma cikin keken dokin ta zauna nan take aka sakarwa dawakan linzami keken dokin yayi gaba su sadauki marzanu sukabi keken dokin a baya suna maiyi masa kawanya gaba daya gefe da gefe don tabbatar da tsaro.
.
Nan dai sarki shardas ya bisu da kallo har sai da suka kule ya daina ganinsu sannan ya juya ya koma cikin gidan sarautar cikin tsananin bakin cikin rabuwa da yarima hulkasa bai ankara ba saiji yayi hawaye ya kara zubo masa a wannan lokaci kuma inda yake wucewa akwai dakaru a tsaitsaye kuma ga bayi barori da kuyangi suna ta kai kawo da hidimomi
duk wanda yaga hawaye a idanun sarki sai kaga ya firgice domin kowa ya san cewa a tarihin rayuwar sarki shardas babu wanda ya taba ganin hawayansa sai yau da yake an san irin shakuwar dake tsakanin sarki shardas da dan sa yarima hulkas kuma an san cewa yau sun rabu sai kowa ya gane dalilin zubar da hawayan nasa.
.
Abin da mutane basu sani ba shine wannan hawaye bana soyayyar hulkas bane ba kadai har da takaicin tunanin ainihin alakarsa da hulkas gami da sanin cewa hulkas ba jininsa bane da kuma bakin cikin rashin samun soyayyar shadila a gareshi ta gaskiya kai tsaye su sadauki marzanu suka durfafi cikin daji suka sukayi ta tafiya babu sassauci babu tsoro ko shakkar wani abu saboda sun yarda da kansu.
.
Tabbas masu iya magana sunyi gaskiya da sukace dole a ce da mijin iya baba hakika komai yawan yan fashi da shirinsu idan suka hango wannan runduna ta su sadauki marzanu saikaga sun fasa taresu sun bace daga kan hanyarsu, ba komai bane ya haddasa hakan ba face kwarjininsu kuma ido ba mudu bane ammma yasan kima ma ana kai da ganin dakarun marzanu kasan sun cika zaratan jarumai masu tarwatsa maza domin dukkansu sun kasance manya manya masu kirar mutanen farko, gashi jikinsu a murde yake kuma sun tara kwanji da jijiyoyi kai kace da dutse aka yi gabobin jikin nasu irin shigar yakin da sukayi kuwa mai ban tsoro ce domin kowannansu yana daukeda miyagun makami yaki irin wanda idanu basu saba gani ba kai ba wai yan fashi ba hatta mugayan dabbobin daji da bakaken aljanu wadanda suka kasance azzalumai suna ganin wannan runduna sai kaga sun bace daga wajan saboda boka barwas ya shirya wadannan dakaru tuntuni da karfin sihirin tsafi mai tunkararsu sai cikakken shiryayye abin kwatance a duniya.
.
Kwana uku kacal wadannan dakaru suka shafe suna
tafiya suka iso birnin askandariya suna shigowa suka iske birnin a cike makil da jama a duk inda mutum ya duba babu abinda zai gani face kawunan jama a fiye da rabin jama ar da suke gani baki ne wadanda sukazo halattar gasar jarumtaka mafi akasarin bakin kuwa sarakai ne da attajirai da yayansu da kuma fatake da shahararrun bokaye tabbas gaba da gabanta aljani ya taka wuta lokacin da keken dokin gimbiya shadila ya kunna kai cikin birnin sadauki marzanu da dakarunsa na biye dashi sai gaba dayan jama ar dake wajan suka dare suka basu hanya kuma kowa ya zuba ido ana kallonsu aka zama kauyawa ba komaine ya haddasa hakan ba face ganin irin dukiyar da aka kashe wajan kera keken dokin da gimbia shadila ke ciki da kuma kayan yakin da dakarunta ke sanye da su domin an sanya jarin wani sarkin ne gaba daya nan fa sarakuna masu ji da kansu ma suka ringa raina kansu basu san sa dda suka rinka leken cikin keken dokin ba domin suga wanda yake ciki amma da yake an saki labulan keken dokin damar hakan bata samu ba a gunsu nan fa aka bi keken dokin a baya duuu har izuwa kofar gidan sarautar birnin ana isa sai akayi cirko cirko.
.
Kawai sai sadauki marzanu ya zaro wata wasi ka ya baiwa masu gadin gidan sarautar yace su kaiwa sarkinsu, wasikar na isaga sarki hulbasu yana budeta yayi arba da hatimin sarki shardas cikin zumudi ya mike tsaye zumbur ya taho da sauri izuwa kofar gidan sarautar yazo gaban keken dokin yana mai cewa lale marhaban da gimbiya shadila matar sarki shardas na Birnin Romaniya.
.
Koda jin wannan batu sai jama a suka zuba idanu domin suga gimbiya shadila saboda labarinta ya gama bazuwa a nahiyar gaba daya ana ta surutun tsananin kyawunta santaleliyar kafarta ta fara zurowa kasa daga cikin keken dokin tun kafin ma jama a suga ragowar jikin nata suka fara gigita da dimauta ai kuwa tana fitowa gaba dayanta aka yi arba da kyakkyawan surar da Allah yayi mata sai mutane suka kama sambatu wasu kuwa basu san sa adda suka kama dalalar da yawu ba tamkar masu hauka sabon shiga.
.
A wannan lokaci shadila na sanye da wata shudiyar doguwar riga damammiya wacce ta baiyana dukkan siffofin jikinta a fili.
.
Wohoho! kyawu kyauta ce daga Allah. Mutum ba zai iya baiwa kansa ba, kai ko namijin da bai cika namiji ba idan yayi arba da wannan gimbiya a wannan lokaci sai ya zama namiji domin mace ce doguwa wacce bata kasance siririya ba kuma ba kakkaura ba tana da dara daran idanuwa masu dan karen haske da fari hancinta dogone siriri tamkar fikakken alkalami a kasansa an dasa mata dan kankanin baki kamar yankan wuka, cikinta a shamule yake tamkar bata taba cin komai ba kugunta mai fadi ne sosai ga mazaune masu tudu kirjinta a cike yake fal kamar bata taba shayarwa ba gashin ta baki ne sidik kuma dogo ya zuba har kasan marar ta sai haske da kyalli yake kamar madubi ganin wannan kyan yasa na kasa ci gaba nake cewa sai Allah ya kaimu gobe.
.
TSATSUBA
Littafi Na Uku (3)
Chapter 2 · 0% Book details