← Book details Tsatsuba Book 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 1 OF 3

Gabatarwa

Tsatsuba Book 3 Complete Hausa Novel · about 22 min read

TSATSUBA
Littafi Na Uku (3)
Part A.
Na Abdul'aziz Sani Madakin Gini
Posting By Abubakar Saleh AlQuyraemey
08138873799 For More Littattafan Yaƙi
.
Koda gama fadin hakan sai sarki shardas ya mike tsaye ya fice daga cikin turakar ita kuma ta bishi da kallo kawai cikin alamun tsananin damuwa da tashin hankali kamar yadda sarki shardas ya bukata haka al amarin ya kasance, wato daga wannan rana suka ci gaba da renon juna biyun nata tare, ya zamana cewa fiye da rabin rana sarki shardas na bata lokacinsa tare da shadila, yana bata kulawa ko yaya yaga wani abu na damunta take zai tura a kirawo likitoci su dubata sannu sannu bata hana zuwa sai dai a dade ba aje ba kwana a tashi sai cikin shadila ya tsufa ya zamana cewa bata iya yin komai da kanta sai dai ayi mata.
.
A ranar da cikin ya cika wata tara da kwana tara ne nakuda ta zo mata, tana fara nakudar sai kawai akaga yanayi ya sauya ba tare da wanzuwar hadari ba ko tasowar iska sai akaji an fara tsawa da walkiya; al amarin da ya razana jama'a kenan aka kama guje guje.
.
A wannan lokaci da rana ne tsaka ana ta gabatar da hidimomin yau da kullum, nan fa kasuwa ta watse jama'a suka rinka rugawa izuwa cikin gidajensu suna
rufe kofa wasu kuma suka ruga izuwa fada domin a sanar da sarki abindake faruwa don ana zaton ko allolin da ake bautawa ne a kasar suka yi fishi zasu
hallakar da mutanen kasar.
.
Koda jama a suka iso fada sai suka iske boka marwas a tsaye a tsakiyar fadar shi kadai fuskarsa a murtuke yana muzurai koda ganin haka sai jama a suka zube kasa a gabansa aka yi tsit kamar mutuwa ta gifta, wani tsoho mai shekaru da yawa ya dago kai ya dubi boka marwas yace ya kai dirkar birnin Romaniya wannan kuma wace irin masiface tazo mana?
.
Ta yaya tsawa mai ban tsoro gami da walkiya suke faruwa a sararin samaniya alhalin babu ko alamar hadari?
.
Koda jin wannan tambaya sai boka barwas ya bushe
da dariya. Al amarin da ya baiwa kowa mamaki kenan boka barwas ya turbune fsuka yace matar sarkice zata haihu yu zata haifi wani yaro dan baiwa wanda sunansa zai shahara a ko ina cikin wannan duniya daga yau za a sami yalwar arziki a wannan birni namu mai albarka za a sami zaman lafiya da kwanciyar hankali irin wanda ba a taba samu ba har izuwa ranar da wannan yaro zaiyi wata tafiya manufa ya fita daga cikin wannan gari namu.
.
Koda jin wannan batu sai mutane suka rasa abinda zasuyi tsakanin murna da bakinciki domin ta leko ne ta koma, babban abinda ya dugunzuma hankalin mutane a cikin bayanin boka barwas sunji cewar da zarar wannan yaro da za a haifa ya bar birnin duk farin ciki zai yaye don haka sai wasu suka fara tunanin to ai gwara rashin aihuwar yaron da dai a shiga farinciki da farko a karshe kuma a shiga tasku.
.
Nan fa mutane suka kama kace nace kowa na fadin albarkacin bakinsa. Ana cikin wannan haline aka yi wata irin tsawa mafi karfin gaske wacce ta firgita komai da kowa har gidajen birnin gaba daya saida yayi rawa, kasa tayi girgiza bishiyoyi suka kama cin wuta dabbobi suka kama guje guje suna shigewa maboya, mutane kuwa suka rude suka dimauce kamar zasu haukace, A dai dai wannan lokaci ne kukan jaririn Shadila ya cika birnin gaba daya har da amsa kuwwa izuwa cikin dazuzzuka.
.
Faruwar hakan keda wuya sai aka kece da ruwan sama kamar da bakin kwarya wata irin iska mai dadin sanyi ta rinka kadawa kamar ana cikin tsakiyar
damina alhalin ana ranine kuma a lokacin zafi ya addabi mutane faruwar wannan sabon yanayi keda wuya sai murna ta kama kowa gami da mamaki nan fa jama a suka ci gaba da cincirindo a kofar gidan sarautar birnin kowa burinsa shine yayi arba da wannan sabon jariri da aka haifa ko ya sami tabarrakinsa domin tuni kowa ya gama yarda cewa wannan jariri dan baiwa ne tunda gashi ni'ima ta sauka a birnin a irin lokacin da ba ataba samunta ba
shi dai wannan ruwan sama da ya sauka ba ruwa bane daga Allah, ruwane daga shaidanu domin kawai su juyar da hankalin mutanen dake wannan nahiya su dada dulmiyar dasu a cikin hanyar bata mabaiyaniya tunda sunyi imani da shaidanun a matsayin ababan bautarsu, bayan kofar fada ta cika makin da mutane.ana ta turereniya, gashi ruwan sama na dukan mutane sanyin iskar dake kadawa har ya fara addabar jama'a amma saboda naci sunki su tarwatse sai tsulum akaga sarki shardas ya fito daga cikin gidan.sarautar dauke da jaririn da shadila akan tafin hannayensa, jaririn tsirara yake ko al aurarsa ba arufe ba, ga sabon yankan cibi a jikinsa ruwan saman nata dukan jaririn amma ko a jikinsa sai dariya yake kyakyatawa yana ta wutsil wuts irin ta jarirai masu koshin lafiya.
.
Koda sarki shardas ya iso gaban dandazon jama'a sai ya daga jaririn sama yayi kuwwar murna take jama a suka amsa masa kuwar muryoyinsu suka cika birnin gaba daya sai da aka yi haka har sau uku
sannan sarki shardas ya mikawa boka barwas jaririn ya karba, ya fuskanci jama a yace yaku jama ar wannan birni na Romaniya kuyi sani cewa yau allolinmu sun dubi kukana sun bani da alhalin na shafe shekara da shekaru ina neman haihuwar ban samu ba ina mai tabbatar muku da cewar wannan da dana samu rahama nega kasarmu gaba daya don
haka ina son kowa ya kaunaceshi kamar yadda zai kaunaci dan cikinsa,Koda sarki shardas yazo nan a zancensa sai jama'a suka amsa masa da cewar sunyi Alkawari zasu so wannan da tamkar dan cikinsu.
.
Cikin matukar murna sarki shardas ya juya ya dubi boka barwas ya mika masa hannu domin ya karbi jaririn kawai sai yaga fuskar boka barwas a murtuke babu annuri nan dai ya karbi jaririn ya sallami jama'a kowa ya watse aka tafi ana ta murna ana ta kade kade da bushe bushe bayan jama a sun watse sai sarki shardas da boka barwas suka juya suka nufi cikin gidan sarautar suna masu jera kafada tsawon dan lokaci suna tafiya dayansu baice uffan ba sai sarki shardas ya dubi boka barwas yace yakai abin dogaro na yakai shamakin dake tsakanina da allolinmu ina son ka gaya mini dukkan dalilin da yasa ka murtuke fuskarka a lokacin da na umarci jama a dasu so wannan jariri na shadila.
.
Koda jin haka sai boka barwas yayi doguwar ajiyar zuciya sannan ya dubi sarki shardas cikin alamun takaici da damuwa yace ya shugabana ai wannan abu da kayi shine babban kuskurenka na farko a kan wannan yaro da aka haifa, shin ka manta ne cewa a duniya kaf baka da wani makiyi wanda yafi wannan yaro?
Shin ka manta ne cewa a halin yanzu yana matayin danka ne na cikinka, tabbas yadda suke son ka kuma zasu so ya gaji karagarka anan gaba, a lokacin
da ni dakai zamu yi shiri mu tafi neman hular lamsara shine zai hau karagarka ta mulki kuma idan muka je muka samo hular lamsara muka dawo saukeshi daga kan karagarka ba abu bane mai sauki duk da cewar zamu iya hallakashi farat daya a wannan lokaci saboda zamu fuskanci fishin jama a domin a sannan suna kaunarsa fiye da kai kuma suna matukar jin dadin mulkinsa, dolene sai daimu hallakashi a sirrance ta yadda babu wanda zai gane cewar dasa hannunmu, ni abinda nake so dakai kawai shine duk yadda za ayi kada ka kuskura wannan yaro ya san cewa ba kai bane uban sa ba har izuwa tsawon shekaru bakwai da zaka rabu dashi akwai ragowar kurakurai guda biyu wadanda bana son kayi kuskuren aikatasu, a nan gaba domin idan ka aikatasu tofa koda ka mallaki hular lamsara saimun sha bakar wahala kafin mu sami nasarar hallaka wannan yaro kuskuren kuwa shine kada ka kuskura ka bari son wannan yaro ya shiga ranka domin hakan zata iya faruwa don yaron zai taso da tsananin farin jini da shiga rai.
.
Akwai wani magani da zan baka ka rinka sha bayan kowane kwana talatin, indai kana shan wannan akan lokaci babu yadda za ayi son wannan yaro ya shiga ranka shi kuwa kuskuren da zaka yi na uku ba yanzu
zan sanar dakai ba sai idan lokacin da ya dace ka sani yayi.
.
Koda jin wannan batu sai jikin sarki shardas yayi sanyi yana mamaki da tunani har suka kule a cikin gidan sarautar bai kara cewa uffan ba.
.
Da ranar suna ta zagayo sai aka yi gagarumin taro aka gaiyaci sarakaim attajirai, bokaye, jarumai da sauran manyan mutane na nahiyar gaba daya boka barwas ne ya radawa jaririn suna Yarima HULKAS, nan fa aka shiga shagalin suna sai da aka kwana ashirin da daya kullum ana gabatar da walima a gidan sarki abinci da abinsha kuwa saida akayi ta almubazzaranci tamkar a bola ake tsunto su hatta talakawan gari ma sai da suka rinka shirya walima tsawon wadannan kwanaki sarki shardas a cikin tsananin farin ciki yake kai kace yarima Hulkas dansa ne na cikinsa wato jininsa ne hm daga wannan rana wani abin mamaki ya fara wanzuwa a cikin birnin romani ya zamana cewa fatake suna ta tururuwa a cikin birnin suna tahowa daga manyan kasashe na duniya suna kafa tushen kasuwancinsu
a birnin.
.
Nan fa kasuwanci ya sami gagarumar bukasar da bai taba yi ba a nahiyar gaba daya nan da nan talauci da fatara suka yaye, arziki ya yawaita a hannun talakawa, kayayyaki iri iri akayi ta shigowa da su birnin da hajoji kala kala, kai irin kasuwancin da baya juyuwa ma a nahiyar fiye da shekaru daruruwa da suka wuce sai da akazo dashi ana yinsu tamkar dama can an saba dasu.
.
Al amarin shadila kuwa itama ta tsinci kanta a cikin sabuwar rayuwa ta farinciki tamkar bata taba tsintar
kanta a cikin wata damuwa a baya amma da zarar ta tuno da mahaifin hulkas na gaskiya wato Hailur saita kefe kanta a cikin daki tay ta kukanta ta more bata yarda sarki yasan halin da take ciki duk da cewar sarki shardas ya fara shan wannan magani wanda boka barwas ya bashi don kada soyayyar Hulkas ta shiga ransa saida yaji yana kaunar Hulkas din tamkar Dansane bana wani ba a ranar da ya sha maganin ne kadai yake jin ya tsaneshi domin a ranar ne yake tunawa da cewa nan gaba fa wannan yaro ne zai kasheshi muddin bai rigashi mallakar Hular Lamsara ba a wannan rana daga safiya zuwa dare sarki shardas baya kusantar shadila don kada ma yayi arba da Jarumi Hulkas hmm Domin zai iya hallakashi nan take saboda zuciyarsa tana tafarfasa ne kamar zata kone bisa jin tsananin kiyayyar hulkas a cikin zuciyarsa kuma jikinsa na tsuma da kyarma yana jin kamar idan bai kashe jariri Hulkas ba shi zai mutu ne a ranar.
.
A kwana a tashi sarki Shardas yana kiyayewa gami da jure duk irin abinda zuciyarsa ke raya masa akan wannan yaro Hulkas har dai aka sami tsawon shekara Uku. A sannan ne ya tsinci kansa a cikin tsananin so da kaunar yarima Hulkas harma yana ji kamar ba zai iya yin rayuwa ba idan babu shi wani iko na Allah Kuma sai shima yaro Hulkas ya shaku da sarki Shardas ya zamana cewa yama shaku dashi fiye da yadda ya shaku da uwarsa Shadila har takai cewa ko abinci baya yarda yaci sai tare da sarki shardas in ba haka ba kuwa sai dai ya kwana da yunwa shima sarki shardas din baya iya cin abincin shi kadai idan ba tare da hulkas ba kai hatta telan da yake yiwa sarki shardas dinki iri daya dana Hulkas yake dinka musu kullum sai dai kaga sunyi anko sunzo fada tare sun zauna akan karagar mulki duk da rana babu abinda yake rabasu kullum ..
.
Sai bayan hulkas yayi barci akan kirjin sarki shardas sannan shadila ke daukeshi tayi masa shimfida a kusa da gadon sarki domin ko cikin dare idan ya farka baiga Sarki ba sai dai ya fashe da kuka kuma babu mai iya rarrashinsa yayi shiru face sarki din ita kanta shadila lokacin da taga shakuwar sarki da yarima hulkas ta wuce saninta ta wuce duk tunanin mai tunani sai hankalinta ya dugunzuma ainun taji zuciyarta ta fara yi mata gargadi kada ta kuskura ta sanar da yarima hulkas asalin abin dake tsakaninsu a nan gaba idan hulkas ya girma
.
A duk sa adda ta tuno da alkawarin da ta dauka na rufe wannan sirri dakuma gargadin da sarki shardas yayi mata da matakin da yace zai dauka idan ta tona sirrin sai hankalinta ya dugunzuma tayi ta kukan bakin ciki........

TSATSUBA
Littafi Na Uku (3)
Part B.
Na Abdul'aziz Sani Madakin Gini
Posting By Abubakar Saleh AlQuyraemey
08138873799 For More Littattafan Yaƙi
.
Idan ta tuna gargadin da sarki Hsardas yayi mata da matakin da yace zai dauka idan ta tona sirrinsa sai hankalinta ya dugunzuma tayi ta kukan bakin ciki haka dai aka ci gaba da wannan rayuwa har yarima hulkas ya cika shekara shida ya zamana cewa gaba daya mutanen kasar Romaniya suna matukar kaunarsa kai ba ma yan kasar ba hatta baki sonsa suke saboda kyawunsa da farin jininsa da kuma kyawawan halayansa da irin hankalin da Allah ya bashi tamkar bai kasance yaro karami ba sannan ga shi Allah ya bashi jin kai da tausayin talakawa sabanin sarki shardas wanda ya kasance Kasurgumin Azzalumin bawa.
.
Gaba daya zaluncin da sarki shardas ke yiwa talakawa sai da yarima hulkas ya hanashi kamar matsa musu wajan karbar haraji mai yawa kai sumame na mamayar bazato a kamo bayi a kwashe dukiyar talakawa sai dai takai cewa duk inda yarima Hulkas ya gifta a cikin nahiyar kasar sai dai kaga jama a suna yi masa kirari da sarkin Gobe Yadda ake yi masa ladabi, biyayya, da girmamawa kuwa ko sarki shardas ba a yi masa haka duk da cewa kuwa ana tsananin tsoronsa hatta a cikin gidan sarautar kwau Bayi, barori, kuyangi da dakari ma suna bin umarnin yarima hulkas tamkar sarki shardas ne yake basu umarnin, kai sai da takai cewa yarima hulkas yana zartar da abubuwa da yawa ba tare da yayi shawara da sarki ba ko da kuwa shi sarki shardas baya son wannan abu ba zaice uffan ba bare ya hanashi.
.
Ashe duk wannan abu dake faruwa tsakanin sarki shardas da yarima hulkas boka barwas na lura da shi amma sai yayi shiru baice kala ba wata rana da yammaci sarki shardas na tsaye a can saman ginin wata baranda yake cikin harabar gidan sarautar sai ya hango yarima hulkas tare da mahaifiyarsa shadila sun fito rangadi suna kewaye a cikin gidan sarautar sunta rabawa bay dakaru barori da kuyangi kyaututtukanna suturori kala kala. koda ganin wannan al amari sai ran sarki ya baci zuciyarsa tayi bakikirin ya tuna cewa tunda fa aka haifi wannan yaro hulkas rayuwar kasar gaba daya ta sauya duk wani iko nasa kwarjininsa da tsarin mulkinsa ya dakushe ya zama kamar mutum mutumi sai abinda hulkas ya zartar a fada shi ake bi su kansu fadawan sarki shardas basa karbar umarnin sa sai abinda yarima Hulkas ya zartar domin a gaba daya sarakai, attajirai da talakawa sun dauki hulkas fiye da kima wasu ma gani sukeyi kamar ya cancanci a bauta masa kamar yadda ake bautawa sauran alloli na kasar saboda ganin irin abubuwan al ajabin da suka faru daga sa adda aka haifeshi kawo iyanzu duk da cewar yarima hulkas ya sami wannan dama da daukaka bai dauki wani girman kai ba ya dorawa kansa kuma hakan ba ta sa ya raina mahaifinsa ba sarki shardas face ma tsananin sonsa da yake karuwa a cikin ransa, duk abubuwan da yarima hulkas yayi a fada ko yasa aka zartar a kasar sai yaje ya sanar da sarki a yayin da suka kebe kuma ya tambayeshi idan akwai gyara a cikin abubuwan da ya aikata domin yaje ya gyara ko sau daya sarki shardas bai taba nuna cewar akwai abinda hulkas yayi ba dai dai ba bare ma ya nuna masa fishinsa a zahiri ko a badini, haka kuma duk abubuwan da yarima hulkas keyi basu sa shakuwarsa da sarki ta sami rauni ba face ma karuwa da takeyi a kullum su kansu fadawan sarki shardas da duk masu fada aji a kasar suna matukar mamakin yadda wannan al amari ya kasance domin ko a mafarki babu wanda ya taba zaton cewa akwai wani mahaluki wanda zai zo ya iya sauya halayan sarki shardas haka sarki shardas na tsaye a can saman barandar gidan sarautar yana hango yarima hulkas da mahaifiyarsa
shadila suna ta raba kyautar suturori ga hadiman gidan sarautar sai tsulum yaga boka barwas ya baiyana a gabansa take boka barwas ya risina ya kwashi gaisuwa sannan ya juyo ya leka kasan barandar ya dubi yarima hulkas da mahaifiyarsa, barwas ya dago kai ya dubi sarki shardas yana mai ajiyar zuciya cikin alamun takaici yace ya shugabana hakika in ba don ina kusa da kai da tuni ka tafka babban kuskuren da zamu hallaka gaba daya duk da cewa kana shan wannan magani dana baka a karshen kowane wata, kaunar wannan yaro a cikin ranka ta gama yin katutu idan baka yi da gaske ba makiyinka zai samu nasara a kanka.
.
Koda jin wannan batu sai idanun sarki shardas suka zazzaro zuciyarsa ta kufulo har fuskarsa ta kama yatsine saboda fishi ya dubi boka barwas yace yakai dirkar birnin romaniya kayi sani cewa har gobe ban manta da asalin yarima hulkas ba na sani cewa bani da wani makiyi a doron kasa wanda ya fishi don haka duk wannan soyayya da nake yi masa ta banza ce tunda lokaci kawai nake jira wanda zamu tafi neman hular lamsara da ita ne kadai zan sami nasarar hallaka wannan yaro kamar yadda ka fada lokacin da sarki shardas yazo nan a zancensa sai boka barwas ya tuntsire da dariyar farinciki sautin dariyar tasa ne ya janyo hankalin yarima Hulkas da shadila suka Hangosu, cikin tsananin farin ciki yarima hulkas ya baro shadila a inda take tsaye ya ruga da gudu izuwa kan matattakalar bene da zata kai shi inda su sarki shardas suke.
.
Koda sarki shardas ya hango yarima ya taho gareshi sai shima ya tareshi suka rungume juna hulkas na hada idanu da boka barwas sai yaji zuciyarsa ta buga da karfi wani irin tsoro ya darsu a cikin zuciyarsa dama duk sa adda yarima yayi arba da boka barwas sai yaji haka Hulkas ya janye jikinsa daga cikin na sarki shardas yace yakai abbana kayi sani cewa yanzu nake shirin na tafi zuwa turakarka bayan mun gama raba kyaututtuka ga hadiman gidan nan na nemi wata alfarma guda daya a wajanka.
.
Koda jin wannan batu sai sarki shardas yayi murmushi yace haba ya kai dana shin ka taba neman wata alfarma ne a wajena na hanaka? Ai duk abinda kaji zuciyarka tana da muradi kayi nayi maka izini muddin wannan abu ba zai zubar mana da kimarmu da mutuncinmu ba, yanzu sanar dani alfarmar da kake so nayi maka Hulkas yayi ajiyar zuciya yana mai sunkui da kansa kas cikin alamun kunya da damuwa kamar ba zai iya magana ba sannan yace yakai abbana ka sani cewa tun da aka haifeni a birnin nan ban taba zuwa ko da wani garin ba daga cikin sauran manyan biranen dake kasar tamu ba, labari ya zo mini cewar hakimin birnin Istanbul ya shirya gagarumar gasa ta jarumtaka kuma an gaiyato manyan jarumai daga bangarori da yawa na duniya lallai ina son na halacci wannan gasa domin a rayuwata babu abinda nake so sama da ganin mutum mai jarumtaka da iya yaki na dade
ina rokonka akan ka koya mini yaki a matsayina na jarumin da zai shahara a wannan nahiya tamu amma kaki kuma baka taba gaya mun dalili ba tunda baka son ka sanar dani dalilin nima bana bukatar na sani
ni dai yanzu ka amince mini nayi wannan tafiya zuwa birnin istanbul.
.
Koda yarima hulkas yzo nan a zancensa sai sarki shardas yaji hankalinsa ya dugunzuma ainun don haka sai ya yunkura da nufin ya juya ya dubi boka barwas domin ya nemi shawararsa amma sai yarima hulkas ya kama hannayansa yace yakai abbana kayi sani cewa bai kamata a sami shamaki ba a tsakanin da da mahaifi muddin wannan da ya kasance jinin mahaifinsa, babu bukatar kayi shawara da wani akan alfarmar da zan nema a wajanka tunda dai nafi karfinta a wajanka.
.
Koda jin wannan batu sai jikin sarki ya yi sanyi kafin ya bude baki yace wani abu sai boka barwas ya tari numfashinsa ya dubi hulkas yace haba ya kai yarima ai bai kamata kace zaka fita daga cikin birnin nan ba kaje wani wuri ba tunda kasan cewa bincike ya nuna cewa duk ranar da kayi dogon zango kasar nan zata shiga cikin fari da annobar talauci, kafin boka barwas ya gama rufe bakinsa tuni shima hulkas ya tari numfashinsa yana mai cewa amma ai cewa kayi sai idan na fita daga cikin yankin kasar nan gaba daya sannan hakan zata faru ya kai barwas kayi sani cewa kana da iyaka a tsakanin da da mahaifi don haka bai kamata ka wuce gona da iri ba yarima hulkas yayi wannan furuci ne fuskarsa a murtuke yana mai hararar boka barwas amma da ya dubi sarki shardas sai fuskarsa ta juye zuwa annuri.
.
Kawai sai sarki shardas ya maida masa da martanin murmushin yace jeka abinka yakai dana lallai nayi maka izinin ka tafi zuwa birnin istanbul domin idanunka su more da kallon abinda zuciyarka ke so koda jin wannan batu sai farinciki ya lullube yarima hulkas ya rungume sarki shardas yana mai yi masa godiya nan take yarima hulkas ya janye jikinsa daga cikin na sarki shardas ya koma wajen mahaifiyarsa
shadila yana riskarta ya rungumeta yana mai yi mata bushatar cewar sarki ya amince masa yayi wannan tafia nan take itama shadila ta cika da farin ciki amma koda ta dago kai tayi arba da fuskokin sarki dana boka barwas tagansu a murtuke babu annuri sai hankalinta ya tashi nan da nan cikin sauri ta kama hannun yarima hulkas taja shi suka juya da baya suka koma cikin gidan sarautar cikin alamun tsananin fishi boka barwas ya dubi sarki shardas yace wannan shine kuskure na uku wanda na gaya maka cewar kada ka aikatashi amma gashi idanunka sun rufe saboda soyayyarsa ka aikatashi ko dajin wannan batu sai sarki shardas ya juyo da sauri ya fuskanci boka barwas cikin tashin hankali yace ban gane abinda kake nufi ba yanzu saboda kawai na bar yarima hulkas yaje yayi kallon gasar jarumtaka a birnin istanbul shine na aikata babban kuskure?
.
Barwas yace kwarai kuwa rashin aiki da shawarata yasa ka aikata babban kuskure na uku wanda nake ta kokarin hanaka ai tunda dai ka fahimci cewar ban son ka bar yaron nan yayi wannan tafiya bai kamata ka barshi yayi ba bincike ya nuna mini cewar yarima hulkas zai sami wata babbar dama ta yakarmu a cikin wannan tafiya da zaiyi amma kuma a dalilin tafiyar ne shima zai sadu da abinda zai zamo sanadin ajalinsa anan gaba.
.
Lokacin da sarki shardas yaji wannan batu sai hankalinsa ya dugunzuma ainun fiye da ko yaushe yaji kamar ya kirawo yarima hulkas yace dashi ya janye izinin da ya bashi nayi wannan tafiya amma kuma sai yaji ba zai iya ba.
.
Kafin ya budi baki yace wani abu sai kawai yaga boka barwas ya bace bat tamkar bai taba wanzuwa ba a wajan, cikin alamun tsananin damuwa sarki shardas ya juya ya sauka daga kan matattakalar barandar ya nufi cikin gidan sarautar zuciyarsa cike da sake sake da tunani abinda ya fara fado masa a rai shine wai shin yaya akayi nema har ya bari son yarima ya shiga zuciyarsa alhalin ya san cewa ba jininsa bane asalima ba shi da wani makiyi wanda ya fishi a doron kasa tunda komai dare dadewa sai ya nemi daukar fansar ran mahaifinsa hailur a kansa wata zuciyar kuma sai tace dashi hakika babu abinda yafi soyayya hadari a wannan duniya domin inda tun farko bai kamu da son shadila ba da tun sa adda ya kashe mijinta itama zai kasheta dashi kenan ya huta da fargabar komai don da yanzun bata haife masa alakakai ba kuma kadangaren bakin tulu wato yarima Hulkas maimakon sarki shardas ya wuce zuwa turakarsa sai ya wuce zuwa turakar shadila kai tsaye duk inda ya ratsa sai dai kaga hadimai suna zubewa kasa suna kwasar gaisuwa da isarsa dakin sai ya iske shadila tare da hulkas a zaune cikin nishadi da farin ciki suna cin tuffa a karon farko sai hulkas yaga babu cikakken annuri a fuskar sarki shardas kafin hulkas yace wani abu sai shardas ya dubeshi yace yakai dana ina son ka bamu dan lokaci zan tattauna da mahaifiyarka.
.
Koda jin haka sai hulkas ya mike tsaye yana mai yin
murmushi ya nufi kofar fita daga cikin dakin yace babu matsala fitarsa keda wuya sai sarki ya tura kofar ya rufe ta sannan yazo daf da shadila ya zauna ya sumbaci wuyanta suka rungume juna suna soyayya daga can sai yayi wuf ya janye jikinsa daga cikin nata ya hankadata ta fado kasa daga kan kujerar da take zaune ya cafi makoshinta ya shaketa.
.
Nan take idanunta suka zazzaro suka kada sukayi jawur ta fara kakarin mutuwa a sannan ne ya saketa ta zube kasa tana numfarfashi kamar ranta zai fita tana mai kurawa shardas idanu.
.
A fusace shardas ya dubeta yace wannan jan kunne ne nayimiki gami da tuni bisa alkawarin dake tsakaninmu akan wannan yaro zakuyi tafiya tare kedashi zuwa birnin istanbul domin halattar taron gasar jarumtaka na duniya da aka sabayi idan kikayi amfani da wannan dama kika gayawa danki sirrin dake tsakani na dashi a bakacin ranki ki sani cewa duk abinda zai faru tsakaninki dashi boka barwas zai gani a cikin madubin tsafinsa yanzu zan fita na barki kada ki kuskura ki bari danki ya gane cewar nayi miki wani abu yanzu.
.
Koda gama fadin haka sai sarki ya juya ya fice daga cikin turakar yana fita sai shadila ta mike zumbur a lokacin da hawayen bakin ciki da takaici ya zumo mata kawai sai tayi sauri ta dauko wani farin kwalli ta sanya a cikin idanunta nan take idanun nata suka washe sukayi fari kal tamkar bata taba yin kuka ba tana ajiye kwallin saiga yarima ya shigo idanunsa sun ga sa adda ta ajiye kwallin don haka sai ya zargi
cewar akwai wani abu da ya faru tsakaninta da sarki
shardas domin baiga dalilin da zaisa tayi amfani da kwalli ba alhalin dama can ta gama yin kwalliya cikin alamun zargi hulkas ya dubi shadila yace yake ummina menene ya faru tsakaninki da abbana??
.
Shin ya gaya miki wata magana ne wacce ta sosa miki rai?
Koda jin wannan tambayoyi guda biyu sai shadila tayi murmushi tace babu wata magana wacce ta sosa mini zuciya farinciki ne kawai yasa kaga alamun sauyin yanayi akan fuskata domin ya shaida mini cewar zamuyi tafiya nida kai zuwa birnin istanbul koda jin haka sai murna ta kama yarima ya rungumeta yana mai cewa burina ya cika yake ummina lallai idanuna zasu ga abinda suka dade suna mafarkin gani.
.
A wannan rana gaba daya yarima hulkas bai sami damar hutawa ba ko tsayuwa a waje daya saboda murna sai kai kawo yake yana ta shirye shiryen tafiyar da zasuyi gobe.
.
Lokacin da dare yayi sai bacci ya kauracewa hulkas da yake akan gado daya suke kwance tare da sarki shardas sai yarima hulkas ya cika da matukar mamaki bisa ganin yadda shima sarki shardas din ya
kasa yin barci sai juye juye yake yi kawai akan gado
Yarima Hulkas ya dubi sarki cikin alamun mamaki yace yakai abbana wai shin.
.
Mene ne ya hanaka barci ne a yau?
Koda jin wannan tambaya sai sarki shardas yayi murmushi yace yakai dana kai yarone don haka baka son dacin rabuwa da masoyi ba tunda aka haifeka a cikin wannan gidan sarauta ban taba rabuwa dakai ba tsawon sa a daya jal kullum muna tare dare da rana hatta kwanciyar barci bata rabamu yau gashi an wayi gari zakayi tafiya zamuyi rabuwa ta a kalla tsawon sati biyu a cikin wace irin damuwa da kadaici kake tunanin zan kasance?
.
Koda sarki shardas yazo nan a zancensa sai Jikin yarima Hulkas yayi sanyi nan take idanunsa suka ciko da kwalla har hawaye ya zubo masa bai san sa adda ya rungume sarki ba yana mai cewa.......

TSATSUBA
Littafi Na Uku (3)
Chapter 1 · 0% Book details