Sashe 1
Sakon Karshe Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
SAKON KARSHE
Author
Zulaihat Muhammad Bello
Zully MB
*BRAIN IN PEN WRITERS TEAM*✍🏻📚
marubuci zababben mutum ne da ake zaben shi dan sauya rayuwar al’umma ta hanyar amfani da kwakwalwa zuwa alkalami
*B.I.P (🤝hadin kammu shine nasarar mu👊.)*
Bisimillahirrahamnir raheeem
“SAKON ƘARSHE”
A ranar da ake gab daɗaura aurenta, Ummi ta samu saƙo daga number ɗin da ta shekara biyu tana nema,Number ɗin mutumin da ta taɓa so fiye da komai… Fahad.“Ki fasa auren nan idan har kina sona da gaske. Ina waje.”
Hannunta ya fara rawa.
Kallon mirror tayi, idonta cike da hawaye yayin da ake ta mata kwalliya a ɗaki.
“Ummi lafiya?” ƙawarta Ammi ta tambaya.
Ta share hawayen da sauri.
“Babu komai.”
Amma zuciyarta ta rikice da tsananin tsoro.
Domin shekaru biyu da suka wuce, Fahad ne ya ɓace ba tare da explanation ba.
Ya katse calls, yayi blocking ɗinta ko’ina.
Ya barta cikin ciwo har ta kusa rasa kanta gaba daya.
Yau kuma… ranar aurenta ne da wani daban… sai ga shi ya dawo?
An fita ɗakin ana ta shewa da murna.
Amma ita zuciyarta na wani wajen.
Ta ɗauki hijab ɗinta a hankali ta fita ta bayan gida.
Da kyar ta isa gate saboda bugun zuciyarta.
A wajen gate ɗin kuwa…
Fahad ne tsaye.
Ya rame sosai.
Idonsa sun sauya kamar wanda ya sha wahala.
“Ummi…” ya kira sunanta da murya mai rauni.
Hawaye suka cika mata ido.
“Why now Fahad? Me yasa yau?”
Ya matso kusa da ita.
“Saboda ban taɓa dena sonki ba".
”“Toh ina ka shiga shekaru biyu?” ta fashe da kuka.
Shiru yayi na wasu seconds kafin ya fidda wani envelope daga aljihu.
“Ki karanta"
Hannuntah na rawa ta buɗe.
Result ne na hospital.
"Cancer ta tah furta"
Numfashinta ne ya tsaya cak.
“Ranar da aka gano min ciwon… doctors suka ce bani da lokaci mae yawa,naso ki tsaneni maemakon ki wahalar dakanki akaena shi yasa na tafi.”
Ummi ta girgiza kae tana kuka sosai.
“Ka barni cikin radadi da ciwo saboda kae ka yanke shawara kae kaɗae?”
“Na tsorata ne…”
Kafin ya ƙarasa magana, sae akafara kiran sunanta daga cikin gida.
Lokacin ɗaurin aure yayi.
Ta kalli Fahad.
Ta kalli ƙofar gida.
Rayuwarta gaba ɗaya ta tsaya tsakanin mutane biyu…
Wanda take so.
Da wanda bae taɓa cutar da ita ba.
Fahad ya murmusa cikin ciwo.
“Ki koma ciki Ummi… I just wanted to see you for the last time.”
Yah juya baya zae tafi...
Sae ta riƙo hannunsa.
“Idan mutuwa ce… toh mu fuskanceta tare.”
A karo na farko cikin shekaru biyu…
Fahad yayi kuka sosae.
Fahad ya zaro ido yana kallonta.
“Ummi… kin san me kike faɗa kuwa?”
Ta share hawayenta da bayan hannunta.
“Na shekara biyu ina trying na manta da kae,na yarda ka cutar dani,na yarda ka daina sona… amma duk da haka zuciyata bata taɓa barin sonka ba fahad.”
Daga cikin gida anata shagalin biki.
Ana tunanin amarya tana chan wurin kwalliya.
Alhalin rayuwarta gab da chanxawa gaba daya.
“Amma akwae Adam…” Fahad ya faɗa a hankali".
Sunan saurayin da zata aurane yau.
Mutumin kirki da ya tattara broken heart ɗinta a lokacin da Fahad ya barta.
Ummi ta runtse ido cikin guilt.
“Adam bae taba min laefi ba…”
“Toh ki koma wajensa.” Fahad ya katse ta.
“Kar ki lalata rayuwarsa saboda mara lafiya kamar ni.”
Ummi ta girgiza kae da ƙarfi.
“Don’t say that please.”
Sae dae kafin wani ya sake magana, sukaji wata murya daga bayansu
“Ummi?”
Jikinta gaba ɗaya yayi sanyi.
A hankali ta juya…
Adam ne tsaye.
Sanye cikin farar shadda, idonsa cike da damuwa da ciwo.
A bayansa kuma freinds dinta guda biyu da suka kasa magana saboda tsananin shock dasuka shiga.
Shiru ya mamaye wajen.
Adam ya kalli fahad sannan ya kalli envelope ɗin dake hannunta.
“Waye wannan?”
Ummi ta kasa magana.
Muryarta ma taki fita.
Fahad ne ya sauke numfashi ya ce,
“Ni ne tsohon saurayinta.”
Kalmar ta sauka kamar tsawa,
Adam yayi murmushi mai ciwo.
“Oh toh ashe haka ne.”
“Adam listen”
“Tun yaushe yake nan?” ya tambaya cikin sanyin murya wanda yafi tsoro.
Ummi ta soma kuka.
“Wallahi yanzu yanzu ne…”
Adam ya ɗan jinjina kae yana kokarin daedaeta zuciyarsa.
Sai ya kalli Fahad.
“Har yau kana sonta?”
Fahad bai yi ƙarya ba yace.
“Fiye da komae.”
“And ita fa?”
A karo na farko, Ummi ta kasa kallon Adam.
Shiru nata ya isa amsa.
Numfashin Adam ya ɗan tsaya.
Kowa ya kalle sa zae ga ciwon dake idanunsa.
Amma sai yayi abin da babu wanda ya zata.
Ya cire zoben dake hannunsa ya kamo tafin Ummi ya ajiye mata.
“Ina sonki sosae Ummi…”
ya faɗa muryarsa na rawa.
“But bana son rayuwar da za ki riƙa pretending kina tare dani alhali zuciyarki na wajen wani.”
“Adam please…” ta fashe da kuka.
Ya ɗan murmusa mata cikin karfin hali da radadi.
“Ki tafi wajensa.”
Hawayen Ummi suka ƙaru.
“Ka yafe min…”
Adam ya juya baya a hankali kafin hawaye da yake boyewa su zubo masa.
A ranar da ya kamata ya zama ango
shine ranar da ya rasa matar da yafi so arayuwarsa.
Ummi ta tsaya tana kallon bayan Adam har ya ɓace.
Zuciyarta na mata wani irin nauyi da bata taɓa ji ba.
Fahad ya sauke numfashi a hankali.
“Bae kamata ki bini ba bayan abin da kika gani yanzu.”
Ta juya ta kalle shi da jajayen idanunta.
“Ka taɓa barina saboda kai ka yanke shawara kae kaɗae,wannan karon ni zan yanke tawa.”
Ya yi shiru.
A wannan daren, labarin abunda yafarune ya cika gidan biki kenan.
“Amarya ta fasa aure.”
“Kuma saboda tsohon saurayinta!”
Maganganu suka cika unguwarsu gari.
Wasu na zaginta.
Wasu na tausayinta.
Wasu kuma suna cewa soyayya hauka ce.
Amma ummi bata damu ba.
Abin da ta fi tsoro yanzu shi ne yadda Fahad yake ƙara lalacewa gaba daya.
Ahaka rayuwa taci gaba da tafiya,har watanni biyu suka wuce asibiti ya zama kamar gidansu.
Ummi ce ke kula da Fahad dare da rana.
Wata rana tana gyara masa pillow sae ya riƙe hannunta.
“Kin gaji…”
Ta murmusa cikin ƙarfin hali da nuna juriya.
“Idan kana tare dani bana gajiya.”
Ya kalleta na wasu seconds kafin hawaye su taru masa a ido.
“Da ace na tsaya tare dake tun farko…”
“Shhh…” ta katse shi.
“Kar mu bata lokacinmu da regrets.”
Sae dae duk murmushin da suke yi, gaskiya ɗaya ce bataba chanjawa
Fahad nata jinya a hankali sauki nasamuwa, doctor ma ya fara basu hope kaɗan.
A wannan daren ne akayi ruwa sosae gari yayi sanyi,asibitin yayi shiru.
Ummi na kwance kanta a gefen gadonsa tana barci saboda gajiya.
Sai ta ji an shafa gashinta a hankali.
Ta buɗe ido.
Fahad ne yana kallonta da murmushi mae rauni.
“Ummi…”
“Hmm?”
“Ina so ki min alƙawari.”
Ta tashi zaune.
“Anything.”
“Idan na mutu…”
“Fahad!” ta dakatar dashi da kuka.
Amma ya riƙe hannunta.
“Ki saurare ni please.”
Hawayenta suka soma zuba.
“Idan na tafi… kar ki tsaya kina kuka har ki manta rayuwarki,ki cigaba da rayuwar,ki yi aure,ki yi farin ciki.”
Ta girgiza kae tana kuka sosae.
“Bana son jin wannan.”
Ya murmusa.
“Amma ni ina so ki sani cewa even after me...zaki rayu.”
Ummi ta sunkuyar da kanta a ƙirjinsa tana kuka kamar zuciyarta zata fito.
A hankali ya rungumeta.
Karo na farko cikin shekaru… ya ji salama.
Washegari da safe,ummi ta fita siyo masa tea saboda ya ce yana so.
Mintuna goma kacal ta ɗauka.
Da ta dawo…
Ƙofar ɗakin cike take da nurses.
Gabanta ya faɗi.
“Excuse me…” ta faɗa tana ƙoƙarin shiga.
Wata nurse ta juyo da idanun tausayi,a lokacin ne tea ɗin hannunta ya faɗi ƙasa ya fashe.
“Patient ɗin…” nurse ɗin ta fara magana cikin sanyin murya,
“I’m sorry.”
Duniyarta ta tsaya cak,a hankali ta ƙarasa bakin gadon.
Fahad ne kwance… idanunsa a rufe… kamar mai barci.
Amma wannan karon… ba zae kara tashi ba.
Ummi ta tsaya tana kallonsa na wasu seconds kamar ƙwaƙwalwarta taki yarda da abunda take gani.
Sai kuma ta riƙe hannunsa cikin rawar jiki.
“Fahad…?”
Shiru.
“Fahad stop joking please…”
Shiru.
Nan take ta fashe da wani irin kuka da yasa har nurses suka juya saboda tausayinta.
Ta rungume gawarsa tana girgiza kae.
“Ka yi min alƙawarin zaka rayu dani har abada…”
Amma babu amsa.
Mutumin da ta fi so a duniya…
ya tafi.Tayi kuka sosae har tagodema Allah kamar wacce xatayi hauka haka takoma
Shekara ɗaya bayan rasuwar Fahad.
Ummi ta sake komawa rayuwarta a hankali bah kamar shekarun baya ba.
Ba saboda ta manta da shi ba…
Sai saboda ta tuna alƙawarin da tayi masa.
Wata rana tana gyara tsofafin kayansa, sai ta ga wata wasika a cikin littafi,hannunta narawa ta bude.
“Dear Ummi,
Idan kina karanta wannan,tah nasan bana cikin duniyar nan,na san zan cutar dake da tafiyata, amma ki yarda dani… kasancewarki a rayuwata shine abu mafi kyau da Allah ya taba bani,kada ki tuna dani da ciwon abunda namiki na barinki danayi na tsayin shekaru biyu danayi abaya,ki tuna da yadda kika sani farin ciki ko a lokacin da nake gabar mutuwa.
And one more thing…
Akwai mutane da yawa da zasu so ki a rayuwa,amma babu wanda zae taba sonki irin yadda nasoki.
"Fahad.”
Hawayen ummi ne suka zubo akan takardar.
Sae dae a karon nan… tana murmushi.
Saboda duk da ending ɗinsu bai kasance forever ba…
Soyayyarsu ta kasance irin wacce mutuwa ma bata iya gogewa……✍
END
Zully MB
DARASIN dake cikin labarin
Soyayya tah gskya tana tare da sadakarwa da kuma juriya,bakowace soyayya ce take karewa da aure bah,dan karasa wanda kake so hakan bawae yana nufi rayuwarka taxo karshe bah kenam