PART I 💪✋
Miftahuzzarbil Part 1 Complete Hausa Novel · about 41 min read
NA ABDUL'AZIZ SANI MADAKIN GINI 😎
TYPING AHMAD MUNNIR 🤝
POSTING NAJIBULLAH MUHAMMAD 💪
MARUBUCIN YACI GABA DA CEWA...
Kawai sai aka ga wata wawakekiyar ƙofa ta buɗe saiga jemagu na ta tuttuɗowa daga cikin ta har saida guda miliyan dubu ɗaya suka shigo kuma dukkanninsu suka sauko ƙasa suka tsaitsaya cak a waje guda.
Nan da nan mayaƙan nan guda miliyan dubu ɗaya kowa ya hau kan nasa jemagen ya zauna.
Babu abinda zai baiwa mutum mamaki face kowa ya san nasa jemagen, domin idan mutum yayi kuskure ya hau wanda ba nasa ba,sai kaga jemagen yayi wani irin ruri.
Cikin sauri mutum zai sauka yaje ya nemi nasa.
Bayan kowa ya gama hawa nasa jemagen sai kuma aka ga waɗansu jemagun guda biyar sun shigo.
Su dai waɗannan jemagu sun fita dabam da sauran, domin sun kasance masu irin siffa dabam,kuma duk farare ne.
Da shigowar jemagun sai suka sauka a gaban su markahul sabus suka yi layi.
Sarudul Makam ya dubi su markahul sabus yace,
"To ga naku ababen hawan ai saiku hau."
Ba tare da wata gardama ba suka hau.
Daga nan sai Sarudul Makam ya kawo takubban haske da garkuwoyi ya rabawa su markahul sabus.
Sannan yace,
"Ina yi muku fatan nasara, domin yanzu nasarar ku itace nasarar ku bisa abinda kuka zo nema."
Sarudul Makam ya matsa kusa da boka jinshan yace,
"Idan ka dawo saika koya mini hankali kayi mini shegen duka koh?"
Koda jin haka sai mamaki da kunya suka kama jinshan ya sunkui da kansa ƙas.
Sarudul Makam yayi murmushi sannan ya zunguri ɗaya daga cikin jemagun dake ɗauke dasu markahus sabus.
Nan take jemagun biyar suka tashi sama suka wuce kan gaba.
Sannan sauran jemagun guda miliyan dubu ɗaya suka bisu a baya.
Sarudul Makam ya tsaya yana kallon su sa'adda suke ficewa ta cikin wawakekiyar ƙofar nan har saida suka ɓace masa da gani.
Sannan ya tuntsure da mahaukaciyar dariya cikin tsananin farin ciki yana mai cewa,
"Shikenan burina ya gama cika wannan karon."
Haka dai markahul sabus suka cigaba da tafiya a cikin ƙarƙashin ƙasa,sai da suka yi tafiyar kwana uku.
Sannan suka iso birnin Sarudul Hasal wanda ake kira Madinatul Hiluz.
Birnin Madinatul Hiluz ya sha bambam da birnin Madinatul Aslik inda sarki Sarudul Makam ke mulki, domin su gidajensu an gina sune da zallan fararen duwatsu,saidai suma babu ƙasa ko tsirrai sai wannan farin Dutse wanda ya malale ko'ina.
Lokacin da su markahul sabus suka shigo cikin wannan birni na Madinatul Hiluz tsakiyar dare ne,don haka garin yayi tsit,kamar ba mutane kuma garin gaba ɗaya a haskake yake babu duhu.
Mutum bazai taɓa ganewa cewa dare ne ba face ya ɗaga kai sama yaga ƙananan taurari a cikin sararin sama.
Sannan ya hango su markahul sabus kamar tsuntsaye suna shawagi a sama.
Su dai su markahul sabus sun zama tamkar makafi domin jemagun da suke kansu ne ke musu jagora sai inda suka nufa dasu.
Lokacin da jemagun suka iso wani gabjejen fili mai tsananin faɗi da tsawo sai jemagun suka sauko ƙasa gaba ɗayansu suka jeru a layi suka kafa sansani.
Koda su markahul sabus suka duba can gaba nesa da su cikin babban filin sai suka hango cincirindon mayaƙan sarki Sarudul Hasal tamkar yuyar ƙudajen duniya.
Al'amarin daya firgita su markahul sabus kenan,zuciyoyin su suka fara duka.
Markahul sabus ya dubi boka jinshan, sulbaini, salusa da kuma aljani Durmazalu yace,
"Ku dubi mayaƙan can fa yanzu dasu zamu yi yaƙi ai yawansu ya ninka namu sau ɗari.
To wai shin sun san da zuwan mu ne har suka yi shiri haka?"
Kafin wani daga cikin su Jinshan yace wani abu sai suka ga wani doki mai fukafukai ɗauke da sarki Sarudul Hasal ya ratso ta tsakiyar yuyar waɗannan mayaƙa a sama ya taho gare su sai daya rage saura kamu bakwai a tsakaninsu.
Sannan dokin mai fukafukai ya sauko.
Nan fa aka fara kallon kallo tsakanin sarki Sarudul Hasal dasu markahus sabus.
Gaba ɗaya surar jikin Sarudul Hasal iri ɗaya ce sak data Sarudul Makam tamkar Hassan da Hussaini.
Inda suka bambanta kawai shine,shi Sarudul Hasal kunnen sa na hagu a yanke yake, kuma an huda kunnen an maƙala masa wani ƙaton yari mai ƙawanya.
Bayan Sarudul Hasal ya ƙarewa su markahul sabus kallo sai ya tuntsure da dariya.
Sannan ya daka musu tsawa duk suka firgice,hantar cikin su duk ta kaɗawa suka ji kamar su ruga.
Jinshan, Sulbaini, Durmazalu da kuma Salusa suka fara ɓoye fuskokinsu.
Markahul sabus ne ya tsaya ƙyam bai firgice ba.
Sarudul Hasal yace,
"Ya ku waɗannan 'yan tatsitsan halittu yanzu kune jaruman da ɗan uwana Sarudul Makam ya turo don ku yaƙe mu,ku shiga baitul malin mu ku ɗauko ƙahon zinare?
Ƙaryar ku tasha ƙarya, domin ko shi da kansa yazo nan mun fi gaban nan bare ku da waɗannan 'yan mayaƙan nasa da basu taka kara sun karya ba."
Cikin ƙwarin zuciya da tarar aradu da ka markahul sabus ya dubi Sarudul Hasal yace,
"Ya kai wannan sarki kayi sani cewa ba'a sanin maci tuwo sai miya ta ƙare.
Haka kuma ai ba yawa bane alamun nasarar yaƙi, domin mazajen ƙwarai masu zuciyar dutse ƙalilan na iya samun rinjaye akan mazaje masu zuciyar ƙarmami komai yawansu."
(Gaskiya markahul sabus ya faɗi magana 😅😅😅)
Koda jin wannan batu sai zuciyar Sarudul Hasal ta kama tafarfasa tamkar ƙirjin sa zai tsage ta faɗo.
Daga inda yake tsaye markahul sabus na iya hango yadda ƙirjinsa nasa mai cike da gashi irin na zaki ke hurowa kamar zai kumbura ya fashe.
(Ran maza ya ɓaci, markahul sabus ka taɓo tsuliyar dodon dake tsaka da barci😥)
Duk da dakakkiyar zuciya irin ta markahul sabus sai da gabansa ya faɗi shima yaji kamar yayi tsalle ya durga daga kan jemagen sa ya ruga da gudu,amma sai ya dake ya ƙaddara a ransa cewa tabbas yau mutuwarsa tazo.
Sarki Sarudul Hasal ya ɗagawa jama'arsa hannu alamar a afkawa su markahul sabus.
Sannan ya zaburi dokin sa.
Nan take dokin ya zabura a sukwane ya durfafo inda su markahul sabus ke tsaye cikin matsiyacin gudu har yana tashi sama yana sauka suma kuwa dakarun nasa sai suka rufa masa baya sai ga dawakai masu fukafukai a sama tamkar gaba tsuntsayen duniya ne ke taron biki.
Koda ganin haka sai markahul sabus ya waiga ya dubi su Durmazalu yace,
"Ya ku 'yan uwana kuyi sani cewa yau fa mun gamu da gamon mu.
Batun gudu ko ɓuya babu shi kuzo kawai muma mu tare su ayi karon batta ai ita kanta mutuwar ma mutuwa take."
Jinshan yace,
"Wace ce kuma mutuwar ka santa ne?"
Markahul sabus yace,
"Ai ba komai bane mutuwar ba face bala'i da masifa kasan kuwa idan tsanani yayi tsanani suma cinye kansu suke yi."
Yana gama faɗin haka ya ɗaga takobin sa ta haske yayi kururuwa ya zunguri cikin jemagen da yake kai kawai sai jemagen ya ruga da gudu ya tunkari su sarki Sarudul Hasal.
Nan da nan sauran jemagun suka rufa masa baya.
Tun gabanin a haɗu wuri ya cika da ruri da kururuwar mayaƙa na ta cin burin a gwamutsu don a fara tamore.
Koda ya rage saura kamu ɗaya a haɗe sai sarki Sarudul Hasal yayi tsalle sama ya bar kan dokin sa ya bangaji markahul sabus da ƙirjinsa na zaki.
Markahul sabus yayi tsalle ya faɗo ƙasa sumamme.
(😳😳😳😳😳😳 Gaskiya markahul ya gamu da gamon shi kuwa, gaskiya halittun duniyar ƙasa akwai masifa)
****************
Al'amarin daya firgita su Durmazalu kenan suka yinƙura da nufin su juya da baya sai aka afka musu da sara bisa dole suka tsaya suna kare kansu da maida martani.
Nan fa wuri ya hargitse.
Cikin daƙiƙu kaɗan aka sumar dasu Durmazalu ya rage saura dakarun sarki Sarudul Makam da kuma su Sarudul Hasal ana ta artabu.
Idan takobi ta haɗu da takobi sai kaga walƙiya da tartsatin wuta na tashi.
Duk wanda ya sake kuwa aka sari jikinsa take yake narkewa walau a cikin mutanen sarki Sarudul Makam ko a cikin mutanen Sarudul Hasal.
A wannan yaƙi dai Sarudul Hasal ne ya zama GAGARABADAU domin duk inda yasa a gabansa saidai kaga yana karkaɗe maza suna zubewa ƙasa matattu, domin yafi kowa ƙarfi,ƙwarewa, juriya da kuma jarumta.
Sai da aka samu sa'a biyar ana wannan yaƙi su markahul sabus basu farfaɗo ba daga dogon suman da suka yi,kuma duk wannan dudufniya akan su ake yi in ba don ma gawarwakin waɗansu sun danne su ba da tuni an karairaya su.
Koda ya rage baifi saura mutum dubu ɗari huɗu ba daga cikin mayaƙan Sarudul Makam,sai sarki Sarudul Hasal ya juya da baya ya cigaba da ragargazar maza yana ihu da kururuwa mai firgitarwa,yana neman inda su markahul sabus suke.
Kamar haɗin baki sai su markahul sabus suka farfaɗo a lokaci guda.
Cikin sauri suka tutture gawarwakin da suka yanyame su suka miƙe tsaye.
Koda suka yi arba da sarki Sarudul Hasal bisa dokin sa mai fukafukai ya durfafo su yana ihu riƙe da takobi a sama sai suka ruga da gudu cikin tsananin tsoro suna ihu suna waige, domin mutuwa suka gani muraran.
Markahul sabus ne a ƙarshen baya yana waigowa yaga Sarudul Hasal a saman kansa ya ɗaga takobin sa zai fille masa kai.
Saboda tsananin razana markahul sabus bai san sa'adda yace,
"Ya ubangijin musulunci ka cece ni daga wannan bala'i."
Gama faɗin hakan ke da wuya takobin Sarudul Hasal ta dira a wuyan markahul sabus.
Wata ƙara ta faru tamkar dutse aka sara.
Take takobin Sarudul Hasal ta narke.
Shi kuwa markahul sabus sai yaji wani irin ƙarfi ya shige shi wanda bai taɓa jin kamar sa ba.
Kawai sai ya shaƙo wuyan sarki Sarudul Hasal suka kama kokawa da naushin juna.
Nan fa Sarudul Hasal ya raina kansa don cikin ƙanƙanin lokaci markahul sabus ya haɗa masa jini da majina.
Dakarun Sarudul Hasal kuwa suka yi caa akan markahul sabus suna saransa,amma kamar susa suke masa,baima kula dasu ba, kawai sai yaci gaba da tumurmusa Sarudul Hasal.
Da yaga yana neman ɓata masa lokaci sai ya ɗaga shi sama ya fyaɗa da ƙasa ya take wuyansa da ƙafa guda.
Koda ya kama hannunsa guda yaja da ƙarfi sai hannun ya tumɓuke daga gangar jikin.
Sarudul Hasal ya kwarara ihu saboda tsananin zafi da zugi.
Markahul sabus ya cigaba da tsintsinka shi saida yayi filla filla dashi.
Koda ganin yadda akayi da Sarudul Hasal sai gaba ɗaya mayaƙan nasa suka fashe da kuka suka yi caa kan markahul sabus.
Yayin da markahul sabus yaga sunyi nasa rubdugu sai ya ƙwaci takubba biyu a hannunsu ya ci gaba da ragargazar su shi kaɗai ya zama shaiɗani a tsakiyar su ya rinƙa cinikin mutuwa.
Su boka jinshan kuwa da sauran tsirarun dakarun Sarudul Makam suka koma gefe ɗaya suna kallon ikon Allah, domin al'amarin ya wuce sanin su.
Markahul sabus bai gushe ba yana saran mayaƙan nan ba har sai bayan sa'a biyar.
Sannan ya ƙarar dasu gaba ɗaya.
Yana gamawa da sune ya faɗi ƙasa, saboda tsananin gajiya ya kama haki da numfarfashi.
A lokacin ne su boka jinshan suka rugo gareshi don su rungume shi,amma sai Durmazalu ya cafkosu da hannu ɗaya su ukun yace,
"Akul kuka raɓe shi.
Kuyi sani cewa a halin yanzu markahul sabus ya zama ma'abocin addinin musulunci, domin sunan ubangijin musulunci ya kira ya sami wannan gagarumin ƙarfi mai ban al'ajabi.
Duk wanda yaje kusa dashi daga cikinmu ƙonewa zaiyi tunda mun kasance ma'abota tsafi.
Abin da zamu yi kawai mu lallaɓa shi har mu gama ɗebo ƙahonhunan nan guda shida."
Koda jin haka sai boka sulbaini yace,
"To mai ze hana ne muma mu bada gaskiya ga wannan addini na musulunci tunda gashi yanzu a zahiri mun ga ƙarfin ubangijin sa.
Kuma in ba don markahul sabus ya kirawo sunan sa ba,da tuni yanzu gaba ɗayan mu mun hallaka."
Koda jin wannan batu sai aljani Durmazalu yace,
"Duk wanda yayi yunƙurin karɓar wannan addini a cikin ku saina hallaka shi.
Dole ne kubi a sannu mu kammala wannan aiki wanda mai girma shamharu ya turo mu."
Sa'adda markahul sabus yaga su Durmazalu sun noƙe a baya sunƙi zuwa wajen sa sai ya miƙe tsaye ya taho inda suke.
Kafin ya iso daf dasu sai aljani Durmazalu yace,
"Dakata anan karka ƙaraso nan wajen mu."
Cikin mamaki markahul sabus yace,
"Don me zaka ce kada na ƙaraso wajen ku ashe ku ba 'yan uwana bane abokan tafiyata?"
Durmazalu ya bushe da dariya.
Sannan yace,
"Ai daga yau ka zamo dodo a garemu domin kana kusantar mu zamu ƙone, domin ka zama ma'abocin addinin musulunci.
Abin da nake so da kai shine muje yanzu kayi mana jagora mu ɗauko ƙahon zinare a cikin baitul malin wannan gari in yaso mu wuce izuwa sauran duniyoyin guda huɗu mu ɗauko ragowar ƙahonnin.
In dai muka sami nasarar hakan da wannan ƙarfi naka muma zamu bada gaskiya da wannan addini na musulunci."
Yayin da markahul sabus yaji wannan batu sai mamaki ya kama shi daya ji cewar shi yanxu ya zama musulmi alhalin kuma bai san yadda ake shiga addinin musulunci ba,amma kuma ya san cewa tabbas yanzu yayi imani da ubangijin musulunci.
Markahul sabus ya dubi aljani Durmazalu yace,
"Idan har kun amince zaku bada gaskiya ga addinin musulunci bayan nayi muku jagora mun ɗebo ƙahonnin na amince nima."
Ba tare da wani ɓata lokaci ba markahul sabus ya wuce gaba su Durmazalu suka bishi a baya har izuwa cikin baitul malin sarki Sarudul Hasal,suka ɗauko ƙahon zinare.
Sannan suka fito.
Daga nan kuma suka sake nutsewa cikin ƙarƙashin ƙasa suka isa duniya ta uku anan ma aka tafka gagarumin yaƙi,kuma markahul sabus ne sanadin nasarar yaƙin aka ɗauko ƙahon zinare aka wuce izuwa duniya ta huɗu.
A haka dai saida suka je har duniya ta bakwai suka sami nasarar ɗauko ƙahonnin shida suka dawo da baya suka kawowa sarki Sarudul Makam.
Cikin tsananin murna ya karɓa.
Sannan yasa aka ɗebo duwatsun wuta aka basu suka yi sallama dashi suka tafi suna murna shima yana yi.
Koda suka fito daga cikin ƙarƙashin ƙasa kafin wani daga cikinsu yayi wani yunƙuri tuni aljani Durmazalu ya fesawa markahul sabus wani shuɗin hayaƙi.
Take markahul sabus ya faɗi ƙasa sumamme.
Durmazalu yayi sama dasu boka jinshan tare da duwatsun wuta suka ƙule a cikin gajimare suka bar markahul sabus anan cikin daji a kwance bai san halin da yake ciki ba.
Wannan shi ne abinda ya faru gasu markahul sabus bayan sun sami nasarar samo abubuwa guda biyu,waɗanda shamharu ya tura su samowa,don a ƙera kubar MIFTAHUL ZARBIL wacce da itane za'a buɗe fadar sarki Azmul gallar a ɗauko kundin tsatsuban sa.
MU HADU A PART J DON JIN CIGABAN WANNAN KASAITACCEN LITTAFIN.**MIFTAHUZZARBIL**
LITTAFI NA BIYU🤝❤️
PART J ❤️💯🩷
NA ABDUL'AZIZ SANI MADAKIN GINI 👑
TYPING AHMAD MUNNIR 🤝
POSTING NAJIBULLAH MUHAMMAD ❤️💯

********************
Al'amarin su Jafar kuwa lokacin da iskar kundin tsatsuba ta watso su waje cikin tasu duniyar sai suka faɗo gaban kundin tsatsuba,kuma shafi na ɗari uku da ashirin da huɗu ne a buɗe.
Nan fa suka kama haki da numfarfashi kamar ran su zai fita.
Koda Jafar ya dubi Yalisa da Gulzum sai tsoro ya kama shi.
Ba komai bane ya haddasa hakan ba face ganin Yalisa ta ƙara girma sosai,ta zama cikakkiyar budurwa,shi kuma Gulzum furfurar kansa ta ƙaro.
Kamar yadda Jafar ya tsaya yana kallon su cikin mamaki suma haka suke kallon sa cikin matuƙar mamaki domin shima ya girma,ya zama saurayi harda gashin baki a fuskarsa da wani ɗan ƙaramin saje.
Gaba ɗaya kamannin Yalisa dana Jafar sun sauya sun ƙara kyau.
Kamannin Gulzum ne kaɗai basu sauya ba face wannan ƙarin furfura da ya samu.
Jafar ya dubi Yalisa yana mai nuna ta da hannu yace,
"Yalisa kece kuwa?"
Itama sai ta nuna shi tace,
"Jafar kaine kuwa?"
Nan take suka rungume juna suka kama kukan farin ciki shi kuwa Gulzum sai ya bushe da dariyar murna.
Sannan ya dube su yace,
"Ai nasan dole ne kuyi mamakin yadda kuka yi saurin girma haka,amma bai kamata kuyi mamaki ba idan kuka yi la'akari da yawan shafukan da muka shiga a cikin kundi.
Ku duba da ku gani a cikin shafi na ɗari uku da ashirin da huɗu muke yanzu.
Wannan na nuni da cewa yanzu mun sami shekara shida da 'yan watanni a cikin kundi duk da cewar yanzu a cikin gaggawa muke karatunsa,amma bamu isa mu ragewa kanmu lokaci ba ko mu ƙara,dole ne sai mun yi shekara ashirin cif a cikin sa.
Sannan zamu kammala karanta shi."
Koda jin wannan batu sai jikin Jafar dana Yalisa yayi sanyi gaba ɗayan su suka koma gefe ɗaya suka zauna cikin matuƙar damuwa,duk suka yi zugum suna tunani mai zurfi.
Koda ganin haka sai tausayin su ya kama Gulzum ya ƙaraso garesu ya dafa Yalisa yace,
"Ya shugaba ta wai shin tunanin me kuke yi ne haka ke da Jafar?"
Yalisa tayi ajiyar numfashi tace,
"Ni kam ba komai nake tunani ba face mahaifina wanda yau rabona dashi shekara shida kenan.
Haƙiƙa inda nasan wannan al'amari zai kasance mini da ban nemi na karanta wannan littafi ba."
Sa'adda Yalisa tazo nan a zancen ta sai hawaye ya zubowa Jafar yace,
"Yake masoyiya ta kiyi sani cewa nima tunanin nawa mahaifin nake, kuma nayi nadama bisa halina na rashin jin magana da karambani, domin karambani na bai haifar mini da komai ba face tsananin wahala, ƙunshi da tashin hankali.
In da nasan cewa zan shiga cikin wannan hali da ban nemo ki ba,mun ɗauko wannan tsinannan littafi ba."
Sa'adda Jafaru ya faɗi haka sai hawaye ya zubowa Gulzum ya rungume Jafar yana mai cewa,
"Ya kai abokina ka sani cewa ita kazar wahala in dai mutum ya yankata dole ne ya ƙarasa fige ta.
Inda muna da rabon barin wahala da tun haɗuwar mu da jarumi Hubairu zamu rabu da ita, domin da tuni mun karɓi addinin musulunci a hannun sa.
In kuwa mun karɓi addinin musulunci da baza mu buɗe kundin tsatsuba ba har mu fara karanta shi."
Koda Jafar yaji wannan batu sai yayi shiru yana mai nazari a cikin ƙwaƙwalwar sa.
Daga can saiya janye jikinsa daga na Gulzum ya dube shi.
Sannan ya dubi Yalisa yace,
"Kun san wani abu kuwa?"
Su biyun suka kaɗa kai alamar basu sani ba.
Jafar yace,
"In da ace zamu sake saduwa da jarumi Hubairu da mun bada gaskiya ga addinin musulunci,kuma mun nemi gafarar sa bisa cin amanar sa da muka yi, domin ni yanzu ina ji a cikin zuciya ta cewar wannan addini na musulunci shine gaskiya.
Tsafi da bautar gumaka kuwa ba komai bane face toshewar basira da ɓata.
Ku tsaya kuyi tunani inda tsafi gaskiya ne ya za'a yi mu kasa ceton kanmu daga cikin wannan bala'i tunda ke Yalisa kin gaji tsafi.
Kuma me yasa duk irin ƙarfin tsafin sarki Lu'umanu jarumi Hubairu ya sami nasara akan sa?"
Sa'adda Jafaru yazo nan a zancen sa sai jikin Yalisa dana Gulzum yayi sake yin sanyi sosai suka yi shiru basu ce komai ba.
Har Yalisa ta buɗi baki zata ce wani abu sai kundin tsatsuba ya buɗe kansa izuwa shafi na ɗari uku da ashirin da biyar.
Saiga hoton wani babban birni mai ƙayatattun gine-gine.
A ƙasansa anyi rubutu kamar haka:-
--------------------------------------------------------------
*"Wannan birni, birni ne na wuya da daɗi,an ƙirƙire shi kimanin shekaru dubu baya.
Mai karatu shigo cikin sa kasha kallo"*

Koda siririyar muryar nan ta gama karanta wannan jawabi sai iskar cikin kundi tayi fitar burgu ta zuƙe su Jafar suka zama 'yan mini-mini suka shige cikin sa.
Kawai sai tsintar kansu suka yi a tsakiyar wannan babban birni.
Birni ne mai ban sha'awa da ban mamaki.
Gaba ɗaya gidajen garin an gina sune da tubalin zinare,kuma duk iri ɗaya ne babu wanda yafi wani faɗi ko tsawo.
Ko'ina ka duba wata irin ciyawa ce ta lulluɓe ƙasa mai tsananin taushi da daɗin takawa.
Wani abin mamaki shine mutanen garin gaba ɗayan su yara ne ƙanana waɗanda ba sufi shekara bakwai bakwai ba,kuma duk kansu ɗaya shekarun su ma ɗaya.
Gaba ɗayan su kyawawan 'yan matane babu namiji ko guda ɗaya.
Abinda zai ƙara baiwa mutum mamaki shine suna ta aikace-aikace irin wanda manyan mutane masu ƙarfi ke yi.
Kai wani aikin ma ko aljani Gulzum aka sada shi dashi sai ya jigata ainun.
Koda ganin su Jafar sai yaran nan suka yanyame su suna shewa da murna kuma suna tattaɓa jikin Jafar da Yalisa suna masu mamakin ganin irin surar jikin su.
Wasu suka yi ta taɓa ƙirjin Yalisa wasu kuma suka rinƙa taɓa gashin bakin Jafar da sajensa.
Al'amarin daya fusata Jafar kenan ya daka musu tsawa.
Bisa mamaki sai Jafar yaga duk sun razana suna ja da baya sun daina taɓa su.
Ba zato,sai ƙofar wani gida ta buɗe sai ga wata doguwar mace kyakkyawa 'yar kimanin shekaru arba'in ta fito.
Kallo ɗaya zaka yi wa matar ka san cewa tana da nasaba da waɗannan yara, domin kamar su ɗaya da ita.
Matar ta tsaya ta ƙarewa su Jafar kallo.
Sannan tayi murmushi tace,
"Marhaban da manyan baƙi ina yi muku barka da zuwa birnin jinsi ɗaya.
Ku biyo ni izuwa cikin gidana domin mu tattauna muhimman al'amura."
Tana gama faɗin haka ta juya ta nufi cikin gidan data fito daga ciki.
Ba tare da wata fargaba ba su Jafar suka bi ta a baya.
Da shigar su cikin gidan sai kansu ya ɗaure, saboda ganin irin kayan da aka shirya a wani tangamemen falo.
Duk wani abu na jin daɗin rayuwar duniya akwai shi a ciki.
Abinci,abin sha kuwa gasu nan iri-iri harda wanda su Jafaru basu taɓa gani ba a rayuwar su duk da irin yawon da suka sha a cikin kundin tsatsuba.
Duk abinda su Jafar ke buƙata ba sai sun ɗauko ba da hannun su.
Suna miƙa hannu abin zai taso da kansa ya dira a hannunsu.
Bayan sun ci,sun sha,sunyi hani'an sai matar nan ta sake dubansu tayi murmushi.
Sannan tace,
"Yaku waɗannan manyan baƙi masu daraja kuyi sani cewa ni sunana Hasiyatul Lauras.
Gaba ɗaya yaran nan da kuka gani a cikin garin nan 'ya'yana ne ni na haife su.
Duk shekara ina haihuwar 'ya'ya dubu arba'in kuma ban taɓa haihuwar ɗa namiji guda ɗaya ba.
Waɗannan 'ya'ya nawa basa girma iyakar girman su kenan yadda kuka gansu.
Wannan al'amari na jefa ni cikin matuƙar baƙin ciki duk da cewar bamu rasa komai na jin daɗin rayuwa ba.
Ina matuƙar son naga na haifi ɗa namiji kuma ina son ya kasance 'ya'ya na suna girma,amma abu ya gagara.
Yaku waɗannan baƙi kuyi sani cewa ba wani abu ne ya haddasa mini wannan masifa ba face wani azzalumin sarkin dodanni wanda yake zuwa mini duk shekara yana saduwa dani.
Yana gamawa dani zai tashi yayi tafiyarsa.
Bayan tafiyar da da tsawon rabin sa'a saina fara haihuwar'ya'ya har saina haifi guda dubu arba'in.
Shi dai wannan sarkin dodanni komai nasa irin na mutane ne face hannayen sa da ƙafafuwan sa waɗanda suke irin na goggon biri.
Ko'ina a jikin sa gashi ne.
A fuska ya kasance kyakkyawa kuma babu gashi a fuskar sa.
Ya kasance murɗaɗɗen ƙato mai tsananin ƙarfin damtse.
Babu wani makami dake tasiri a jikin sa bare yayi masa lahani.
Idan zaizo ya kan zone tare da mutanen sa waɗanda suka kasance irin sa kuma sukan zo bisa dawakai su da yawa,ba zan iya misalta muku adadin su ba.
Kafin kuzo nan nayi mafarki da zuwan ku,kuma a cikin mafarkin an nuna mini cewa kune zaku yaƙi wannan dodo da jama'arsa kuyi mana maganinsu.
Kuyi sani cewa duk abinda nayi mafarkin sa wannan abu yana faruwa a gaske don haka ni yau ina cikin matuƙar farin ciki da ganin ku."
Yayin dasu Jafar suka ji wannan batu sai suka dubi juna cikin matuƙar mamaki.
Sannan Jafar ya dubi Hasiyatul Lauras yace,
"Yake wannan mata mai baiwar haihuwa kiyi sani cewa mu bamu mayaƙa ba,ta yaya zamu iya tarar wannan basamuden dodo alhalin kince makami baya tasiri a jikin sa da kuma na jama'arsa.
Kuma kince baki san yawan adadin su ba?
Ai ko ba komai sarkin yawa yafi sarkin ƙarfi bare ma mu bamu da ƙarfin."
Hasiyatul Lauras tace,
"Ni dai bani da wata shakka akan ku,na tabbatar da cewa zaku iya kawar da dodo Abulungu da jama'arsa indai kuna da niyya saidai idan ba kwa son ku taimake ni.
Ku sani cewa idan ma baku yaƙi dodo Abulungu ba indai ya iske ku anan sai ya kashe ku, domin bai yarda yaga wata halitta kusa dani ba,face waɗannan 'ya'ya nasa."
Koda Hasiyatul Lauras tazo nan a zancen ta sai Jafar, Yalisa da Gulzum suka sake duban junansu cikin tsananin damuwa.
Yalisa ta cizi yatsa tace,
"Kash!
Sai mutum baya nan sannan ake sanin muhimmancin sa.
Yau ga ranar Mazalish inda tana nan yanzu ne zata yi tunanin dabara cikin gaggawa."
Jafar yace,
"Ƙwarai kuwa ai rashin Mazalish a gare mu ba ƙaramar asara bace."
Shi kuwa Gulzum sai ya matso ƙwalla daga cikin idanun sa yace,
"Haƙiƙa kowa ya tuna da bara baiji daɗin bana ba."
************************
Jafar yayi shiru ya sake shiga sabon tunani da nazari.
Daga can sai ya dubi Hasiyatul Lauras yace,
"Yake wannan mata shin a wani lokaci su dodo Abulungu ke zuwa?"
Hasiyatul Lauras tace,
"Su kanzo ne duk ƙarshen shekara da magriba kuma yau saura kwana goma cif su zo."
Yayin da Jafar yaji wannan amsa sai yayi shiru ya sake yin tunani.
Sannan yace,
"Kince ƙarfe baya tasiri a jikin su,to shin suna iya lalata ƙarfe ne da ƙarfin hannun su?"
Hasiyatul Lauras tace,
"A'a basa iyawa,amma dai suna zuwa riƙe da muggan makamai wasu ma ko a labari ban taɓa jin masu kaifin su ba da tsinin su."
Jafar yayi murmushi.
Sannan ya dubi Hasiyatul Lauras yace,
"Abinda nake so dake shine ki tara 'ya'yan nan naki gaba ɗaya ki gaya musu cewa su fara shiri zamu yaƙi su dodo Abulungu nan da kwana goman kuma kisa a ƙera mana ragar ƙarafa mai yawa wacce da itane zamu kama su Abulungu mu rinƙa watsa musu wuta suna ƙonewa.
Ina ganin da wannan dabara ne kaɗai zamu iya samun galaba akan su."
Koda jin wannan batu sai Yalisa, Gulzum da Hasiyatul Lauras suka cika da tsananin mamakin irin basirar Jafar da yadda yayi tunanin wannan hikima a cikin ƙanƙanin lokaci haka.
Daga wannan rana 'ya'yan Hasiyatul Lauras suka fara ƙera ragogin ƙarfe.
Sannan aka tanadi gunguma-gunguman itatuwa aka kunna gagarumar wuta.
Kuma sai akayi waɗansu majajjawa na ƙarafa waɗanda za'a rinƙa watsawa mutanen dodo Abulungu ɗanyen mai da wannan wuta.
Ita dai wannan wuta kullum ƙara zuba mata gunguma-gunguman itatuwa ake tana ci dare da rana.
Jafar ya raba 'ya'yan Hasiyatul Lauras izuwa kaso uku.
Kaso na ɗaya aikin su shine hawa kan bishiyoyi su ɓuya.
Da zarar mutanen Abulungu sun zo wucewa su jeho musu ragogi.
Kaso na biyu aikinsu kuwa shine watso wannan ɗanyen mai.
Su kuma kaso na uku aikin su shine watsa musu wuta.
Jafar ya samu wani ƙaton kulki ya baiwa Gulzum yace,
"Kai kuma ka ruƙe wannan idan kaga mutanen Abulungu a cikin raga waɗanda wuta bata kama ba kayi ta dukan su da wannan kulki ka kashe na kashewa ka sumar dana sumarwa."
Ba tare da gardama ba Gulzum ya karɓi kulkin yana mai murmushi,amma zuciyarsa cewa yake,
"Anya kuwa shegen yaron nan ba mugunta ya shirya mini ba.
Idan kuma garin dukan dodannin sun kamani fa?
Shikenan tawa ta ƙare."
(😂😂😂😂Kai dai Gulzum akwai shegen tsoro yasin😂)
Haka dai aka cigaba da shirye-shirye har kwanaki goma suka cika.
A rana ta goman ne tunda yamma suka samu wurare suka ɓuya wato suka yi lamɓo suna jiran ƙarasowar su dodo Abulungu.
Har magriba tayi shiru ba'a ji motsin komai ba.
Al'amarin daya sa su Jafar suka ƙosa kenan domin sun matsu waɗannan abokan gaba suzo domin ganin mugun tanadin da suka ya isa su gama da su.
Bayan an saka jimawa kawai sai aka jiyo ƙarar sawun kofaton dawakai daga can nesa.
Jim kaɗan kuma sai ƙarar tayi yawa ta matso kusa kuma ihun dodannin da gurnanin su ya cika dodon kunne da kuma hayaniyar dawakansu.
Koda su Jafar suka hango yawan waɗannan dodonni sai suka firgice,ƙiris ya rage basu tsure da gudawa ba, domin sun san cewa wannan shiri da suka yi bai isa ya gama da waɗannan miyagun dodonni ba.
Har Yalisa da Gulzum sun yunƙura zasu ruga da gudu sai Jafar ya daka musu tsawa yace,
"Ina zaku?
To ku sani cewa idan ma kuka gudu kunyi gudun banza tamkar ma kun fallasa kanku ne yadda za'a yi saurin hallaka ku.
Kawai ku tsaya mu jarraba iyakar sa'ar mu.
Ai da mu mutu ragwage gwara mu mutu jarumai."
A daidai wannan lokaci ne wata zuga mai yawa ta dodanni tazo zata gifta sai masu raga suka watso ragogin su akan su.
Nan take ragogin suka lulluɓe su suka rinƙa faɗowa ƙasa daga kan doki.
Kafin su miƙe tsaye kuwa aka rinƙa watso musu ɗanyen mai da wuta.
Nan fa dodannin suka rinƙa kamawa da wuta suna ci kamar ƙarmami suka rinƙa ihu da ruri mai razanarwa.
Da yake dodo Abulungu na daga can baya sai ya ɗaga hannu sauran dakarun sa suka tsaya cak.
Shima ya tsaya yana mamakin wannan baƙon al'amari domin tunda yake zuwa wannan birni fiye da shekaru arba'in baya ba'a taɓa kawo masa hari ba sai yau.
Abulungu ya hanga da kyau yaga ashe 'ya'yan sune da kansu suke yiwa jama'arsa wannan ɓarna.
Nan take ya baiwa mutanen sa masu kwari da baka umarnin su ruga su harbo dukkanin yaran nan dake kan bishiyoyi masu jeho raga.
Nan take 'yan kwari da bakan suka zaburi dawakansu suka durfafi yaran.
Tun daga nesa suka fara harba kibiyoyi saiga yaran na faɗowa ƙasa matattu.
Da yake suma yaran suna da yawa basu fasa jeho ragar ba, suma masu watso ɗanyen mai da masu watso wuta basu fasa ba.
Nan fa wuri ya ƙara hargitsewa da ihun dodannin dana yaran aka rinƙa gasar ɗaukar rayuka.
Har yanzu dodo Abulungu na daga can baya a tsaye kan doki da wasu fadawan sa da kuma dubunnan dakaru suna kallon abinda ke wakana.
Babu yadda mutum zai iya gane ɓangaren da suka fi mutuwa tsakanin mutanen dodo Abulungu da mutanen su Jafar.
A wannan lokaci Gulzum ya taka muhimmiyar rawa, domin ya ragargaji dodannin nan da wannan ƙaton kulki dake hannun sa.
Da yawa sun baƙunci lahira wasu kuma yayi daga-daga da sassan jikin su ba zasu taɓa moruwa ba.
Jafar kuwa yana daga cikin masu watsawa dodannin ɗanyen mai ita kuma Yalisa tana cikin masu watsa wuta.
Koda dodo Abulungu ya fuskanci cewa babu alamar nasara ga mutanen sa saiya fiddo da wani ƙaho ya busa.
Faruwar hakan keda wuya mutanen nasa dake artabu dasu Jafar suka juya da baya a guje suka koma wajen Abulungu 'yan kaɗan dasu alamar cewa an kashe su da yawa.
SAI MU HADU A PART K DON JIN CIGABAN WANNAN KASAITACCEN LABARIN MAI CIKE DA DIMBIN ABIN AL'AJABI, JARUMTA, DA SOYAYYA.
Najibullahi Muhammad**MIFTAHUZZARBIL**
LITTAFI NA BIYU 🤝❤️
PART K 🥰🤝
NA ABDUL'AZIZ SANI MADAKIN GINI 👑
TYPING AHMAD MUNNIR 🤝🥰
POSTING NAJIBULLAH MUHAMMAD ❤️❤️💯
ONE LOVE 💕😘
MARUBUCIN YACI GABA DA CEWA....

Koda Abulungu yaga haka saiya kwarara ihu cikin tsananin baƙin ciki.
Daga can ya ɗago kai ya dubi sauran dakarun nasa dake baibaye dashi yace,
"Yaku mayaƙa na abin dogaro na kuyi sani cewa haƙiƙa yau Hasiyatul Lauras ta shirya mana mugun nufi na ƙarar damu,amma duk yadda aka yi ta samu taimakon wasu baƙin halittun, domin bata da basirar shirya wannan hikima.
Abin dana ke so daku yanzu shine mu tattara waje ɗaya gaba ɗayan mu,mu haɗa ƙarfi waje guda mu shige su lokaci guda,don ayi ta ta ƙare."
Koda jin haka sai dodannin suka fara jeruwa sahu-sahu a waje guda.
A can ɓangaren su Jafar kuwa tuni sun fara murna,don a zatonsu dodannin sunji tsoro sun gudu,don haka sa'adda suka ga dodannin na jeruwa a sahu-sahu sun ɗauka tafiya zasu yi su bar garin.
Ba zato, ba tsammani kuma sai suka ga dodannin sun taso musu a sukwane gaba ɗayansu ba'a rage ko guda ba.
Nan fa su Jafar suka tsure.
Ita dai Hasiyatul Lauras da rarrafe ta ruga cikin gidanta ta maida ƙofa ta rufe.
Jafar da Yalisa kuwa sai suka ruga bayan Gulzum suka ɓuya.
Sauran yaran nan kuwa masu jeho ragogi da masu watso mai da wuta ko gezau basu yi ba sai kawai suka tsaya suna jiran isowar abokan gaba.
Koda ganin yadda waɗannan yara suka dake suka cire tsoro a zuciyarsu sai Gulzum yaji shima ya daina tsoron komai.
Take yaji ƙwarin gwiwa da ƙarfi ya shige shi.
Kawai sai ya kama wata ƙatuwar bishiya ya cisgota daga cikin ƙasa ya ruƙe ta a matsayin makami ya zamana yana da makami biyu kenan,wato ga ƙaton kulki,kuma ga bishiya.
Da isowar dakarun sai wuri ya ƙara hargitsewa da ihu da kururuwa.
Dodanni na mutuwa yara na mutuwa.
Nan fa aljani Gulzum ya zama kamar ifritu a tsakiyar dodannin nan ya dinga ragargazar su da kulki da bishiya.
Duk inda yakai duka saidai kaga suna zubewa ƙasa matattu ko sumammu.
Duk wannan ɗauki ba daɗi da ake yi Jafar da Yalisa na kan kafaɗar Gulzum sun maƙalƙale sunƙi yarda su sauko ƙasa.
Sa'adda Jafar yaga yaran nan suna ta ƙoƙari duk da cewar ana ta kashe su sai kunya ta kama shi ya dubi Yalisa yace,
"Yake masoyiya ta a gaskiya zamu ji kunya idan har aka samu nasara a yaƙin nan bamu taɓuka komai ba.
Zaifi kyau muyi iya yinmu koda kuwa zamu hallaka."
Ba tare da wata gardama ba Yalisa ta karɓi wannan uzuri nan take suka daka tsalle daga kan kafaɗar Gulzum suka kaiwa yaran ɗauki.
Wannan karon sai Jafar ya shiga cikin masu watso wuta ita kuma Yalisa ta shiga cikin masu watso ɗanyen mai.
Ai fa sai wurin ya ƙara hautsinewa fiye da da, domin Jafar da Yalisa sunfi waɗannan yara zafin nama.
Shi kuwa dodo Abulungu yana cikin ragargazar yaran ne ya hango Jafar, Yalisa da Gulzum yaga irin ɓarnar da suke ta wuce misali sai yayi kururuwa ya zaburi dokin sa ya durfafi Gulzum, saboda ganin cewa yafi ɓarna.
Koda ya riske shi sai suka kaure da matsiyacin faɗa.
Abulungu ya dinga kaiwa Gulzum sara da suka da wata irin lafceciyar adda mai girma da kaifi.
Gulzum ya dinga karewa da kulkin ƙarfen dake hannunsa kuma yana maida martanin duka da bishiyar dake hannunsa.
Duk da girma irin na aljani Gulzum dodo Abulungu ya fishi faɗi da tsawo.
Nan fa suka yi ta Artabu harya zamana kowannensu ya fara gane kuskurensa, domin dodo Abulungu ya samu nasarar yankar Gulzum har sau uku da wannan lafceciyar adda.
Shi kuma Gulzum ya mammaka masa bishiyar nan a fuska ya haɗa masa jini da majina.
Fuskar dodo Abulungu duk ta kumbura ba kyan gani.
Cikin tsananin fushi dodo Abulungu ya shammaci Gulzum ya danƙara masa sara a ƙafa.
Take wajen yayi rami jini yayi tsartuwa sama.
Gulzum ya kwarara ihu saboda tsananin zafi da zugi ya durƙushe a ƙasa,amma sai shima ya shammaci Abulungu ya danƙara masa bishiyar nan a ƙoƙon gwiwarsa.
Take ƙafar Abulungu ta karye ɓas shima ya faɗi ƙasa yana mai kwarara uban ihu.
Koda jama'ar Abulungu suka jiyo ihun sarkin sai suka ruga inda yake suka ɗauke shi suka juya da baya gaba ɗayansu suka sake runtuma wa da gudu suka bar birnin gaba ɗaya,ɗayansu bai tsaya ba face matattun dake kwance fululu a ƙasa.
Nan take Gulzum ya faɗi ƙasa sumamme saida su Jafar suka watsa masa ruwa.
Sannan ya farfaɗo.
Daga nan 'ya'yan Hasiyatul Lauras da ita kanta suka fara haƙa kabarurruka suna binne gawarwakin yaran da suka mutu suna kuka.
Abin dai abin tausayi.😢😢
Babu wanda zai ga sa'adda yaran ke binne 'yan uwansu bai zub da hawaye ba.
A wannan lokaci ne Hasiyatul Lauras ta kawo magani aka sanya wa masu raunuka hadda aljani Gulzum, amma duk da haka bai dawo cikin hayyacinsa ba.
Sai bayan sa'a uku a cikin falon Hasiyatul Lauras.
Bayan farfaɗowar Gulzum ne Jafar da Yalisa suka ruga gareshi suka rungume shi suna kuka, saboda ganin halin daya shiga.
Gulzum ya dube su sa'adda shima idanunsa suka ciko da ƙwalla yace,
"Yaku 'yan uwana ku daina kuka saboda wannan hali dana shiga, domin ni namiji ne kuma an san namiji sha gwagwarmaya ne.
Koda na mutu a wannan yaƙi bai kamata ku damu ba tunda nima na salwantar da rayuka da yawa.
Yanzu babu abinda ya kamace mu face tunanin yadda zamu sake tarar waɗannan mugayen dodonni, domin tabbas sai sun dawo mana."
Koda jin haka sai hankalin Jafar, Yalisa da Hasiyatul Lauras ya dugunzuma aka rasa wanda zai ce ƙala.
A sannan ne Jafar ya fara da cewa,
"Tunda aka fara yaƙin nan bai ga Salusa ba."
Nan take ya tambayi Yalisa da Gulzum ko sunga Salusa?
Gulzum ya sunkui da kansa ƙas cikin alamun karayar zuciya yace,
"Ai salusa ta mutu kuma dodo Abulungu ne yayi mata wawan duka aka take kanta ya rugurguje duk da cewa kuwa na dutse ne, domin tarwatsewa yayi, yayi filla filla.
Yanzu haka gawarta na nan a inda muka gwabza yaƙi ni da Abulungu."
Yayin da Gulzum yazo nan a bayanin sa sai jikin Jafar da Yalisa ya ƙara yin sanyi kuma suka sake tsorata ainun da wannan bala'i da suke ciki.
Saida Gulzum ya kwana bakwai yana jinyar jikinsa.
Sannan ya sami ƙwari,harma yake iya takawa da ƙafarsa.
Tsawon waɗannan kwanaki ana ta ƙera sababbin ragogin ƙarfe da kuma majajjawar watsa ɗanyen mai da wuta.
Ice kuwa saida aka tara wanda inda za'a shekara ana ƙonawa bazai cinye ba.
Wannan karon dai sai Jafar ya bada shawarar a rarrabu wuri-wuri ayi kwantan ɓauna.
Ma'ana kada a tsaya a waje guda saboda ya san cewa suma su dodo Abulungu da sabon shiri zasu zo kuma da sabuwar hikima.
Su Jafar dai suka zamo kullum a cikin shiri da jira,don sun san cewa lallai su dodo Abulungu zasu iya zuwa a koyaushe.
Saida aka kwana goma sha huɗu ana jiran aga ɓullowar su dodo Abulungu amma shiru ko alamar su babu.
*********************
A can kogon dutsen dasu dodo Abulungu ke ciki kuwa sai da Abulungu ya kwana tara a kwance yana jinyar fuskarsa da ƙafarsa.
Sannan ya warke,harma ya iya tashi ya taka sawayensa.
Koda Abulungu yaga ya samu lafiya sai ya zabura da nufin ya ɗau kayan yaƙin sa ya koma birnin Hasiyatul Lauras ya yaƙe su shi kaɗai.
Cikin sauri matarsa dodanniya Kurdisa ta ruƙo hannun sa tace,
"Haba mai gidana kayi sani cewa ba'a ramuwa ranar gaba.
Ai zuwa da shiri yafi zuwa da wuri.
Ina mai sanar da kai cewa tabbas waɗannan abokan gaba ba zasu zauna haka ba,sai sunyi mana mugun tanadi don haka ya zama wajibi muma muyi musu tanadin da basu taɓa zato ba,yadda muna riskar su zamu gama dasu a cikin ƙanƙanin lokaci."
Abulungu yayi ƙwafa yace,
"Ai ni babu abinda ke mini takaici face ganin cewa da 'ya'yan cikina muke wannan yaƙi."
Kurdisa ta bushe da dariya tace,
"Ai maganin mai kwaɗayi kenan.
Inda ka haƙura dani kaɗai muna haihuwar dodanni irin mu ai da haka bata faru ba.
Yanzu gashi kaje ka haiƙewa bil'adama ta haifo 'ya'yan dake neman zama sanadin ajalinka.
In ba don ina tsoron kada a cuci 'ya'ya na a mayar dasu marayu ba ai da ba zan yarda a cigaba da yaƙin nan ba.
To kai kaɗai ne babba namiji a garin nan kuma kaine uban kowa,kaine kuma mai basirar kare mu daga kowane irin haɗari."
Sa'adda Kurdisa tazo nan a zancen ta sai Abulungu yace,
"Haƙiƙa kinyi gaskiya kuma na samu darasi don haka daga yau ba zan sake yarda na haiƙewa wata mace ba,in ba ke ba."
Nan take Abulungu ya tara gaba ɗaya mutanen sa waɗanda suka kasance 'ya'yan sa ne kaf yayi musu bayani cewa kowa ya fara shiri nan da kwana goma za'a koma birnin Hasiyatul Lauras ɗin.
Koda jin haka sai aka ruɗe da shewa ana kururuwa da ruri ana murna.
A sannan ne ya zayyana musu duk irin sabbin dabarun da za'a yi da kuma irin makaman da za'a tanada don a samu nasara a wannan yaƙi.
Ba tare da ɓata lokaci ba aka shiga aikin ƙera sabbin makamai.
Saida aka kwana tara ana ta shirye shirye, sannan komai ya kammalu.
A daren kwana na goma ne dodo Abulungu da jama'arsa suka kai sumame birnin Hasiyatul Lauras.
Kuma da tsakar dare suka shiga don ma kada a ji motsin tahowarsu.
Sai suka fara tafiya a dudduƙe da laɓe-laɓe domin a tunaninsu su Jafar na barci a cikin wannan lokaci.
Abinda basu sani ba shine tun daga ranar da akayi wancan yaƙi aka daina barci a birnin.
Lokacin da su Abulungu suka shigo tsakiyar birnin suna duƙe-duƙe da laɓe-laɓe kawai sai suka ji an fara watso musu raga,ɗanyen mai da wuta.
Wannan karon harda manyan duwatsu aka jeho musu yana ragargazar su.
Kafin su ankara anyi musu muguwar ɓarna.
Nan take Abulungu ya bada umarnin a koma da baya da gudu.
Ai kuwa nan da nan suka juya basu tsaya a ko'ina ba sai inda suka baro manya-manyan dawakansu masu kama da giwaye.
Da zuwa suka haye dawakan suka sake zaburo su a sukwane suka durfafo birnin Hasiyatul Lauras.
Suna isowa yaƙi mummuna ya sake ɓarkewa.
A wannan rana anci kasuwar mutuwa domin dubunnan ɗaruruwan rayuka sun salwanta tsakanin jama'ar dodonni da jama'ar Hasiyatul Lauras.
A lokacin ne Jafar da Yalisa suka shiga mugun hali na tsakanin mutuwa da rayuwa, domin duk jikinsu raunuka ne jini na zuba.
Jiri na ɗibarsu,suna faɗuwa,amma a hakan suka cigaba da gumurzu.
Aljani Gulzum kuwa da dodo Abulungu dama yau sun fito ne da niyyar ko rai ko mutuwa,amma ba gudu ba ja da baya.
Sai daya zamana dukkanin su sunyi fata-fata da juna, kowannensu ya sami saɓawar kamanni.
Tun suna iya yin yaƙin a tsaye suka koma yi a durƙushe.
A ƙarshe ma suka zub da makamansu suka kama kokawa suna cizo da yakushin juna.
Abulungu ya cafki kunnen Gulzum na hagu ya ciza da haƙoransa.
Sannan ya fincike shi da ƙarfin tsiya.
Gulzum yayi kururuwa yayi tsalle sama ya faɗo ƙasa tim saboda tsananin zafin daya ji.
(Wannan ya tunanin da boka karluz 😅😅😅,bambancin da aka samu shine,boka karluz dodon ne yayi watanda da kunnensa😅😅)
Koda Abulungu yaga ya samu wannan nasara sai ya ƙara mirginowa ya kaiwa hannun Gulzum wawura da gatso gatson haƙoransa.
Cikin zafin nama Gulzum ya goce shima ya kaima Abulungu cizo a marainan sa.
Ai kuwa yayi sa'ar damƙar su.
Take Gulzum ya taune su suka farfashe, ihun da Abulungu yayi saida ƙasa ta kama girgiza.
Nan da nan idanun sa suka ƙafe jikinsa ya sandare,komai nasa ya daina motsi.
Koda Gulzum yaga ya samu nasarar kashe Abulungu sai ya miƙe tsaye wuf ya kwarara kururuwa cikin ƙarfin hali da ƙwarin zuciya ya sungumi kulakensa biyu ya cigaba da ragargazar dodonnin nan.
Suma su Jafar koda suka ga an kashe Abulungu sai ƙarfi yazo musu suka cigaba da kashe dodannin.
Su kuwa dodannin gaba ɗaya suka rasa kuzari tunda suka ga an kashe ubansu don haka sai suka fara ƙoƙarin guduwa,amma damar hakan bata samu ba,don kewaye su su Jafar suka yi suka yi ta ragargazar su.
Ana cikin haka ne aka ga dodanniya Kurdisa tayi wani sabon ayarin dodannin jagora bisa kan dawakai ba adadi sun kawowa su Abulungu ɗauki.
A sukwane suka durfafo inda ake wannan yaƙi.
Tun daga nesa Kurdisa ta hango gawar mijinta ai kuwa nan take ta haukace ta dunga ihu tana ƙarawa dokin ta ƙaimi,don ta riski su Gulzum.
Koda su Gulzum suka hango wannan gagarumin ayari sai suka yarda dukkanin makamansu suka saduda,don sun san cewa tabbas ajalinsu yazo.
Saida ya rage saura baifi zira'i ashirin ba tsakanin su Kurdisa dasu Jafar kawai sai aka ga ƙatuwar macijiyar nan ta sarki Azmul gallar ta bayyana a gaban su Kurdisa.
Cikin razani dawakan nasu suka rinƙa turjiya suna juyawa da baya a guje,amma sai macijiyar ta sauko da kawunan ta ta rinƙa haɗiyar su Kurdisa daga su har dawakansu tayi ta tsince su ɗaya bayan ɗaya sai data ƙarar dasu gaba ɗaya babu wanda ya tsira.
Bayan ta gama lanƙwame sune ta juyo da kanta guda ta ƙare wa su Hasiyatul Lauras kallo,koda taga Jafar, Yalisa da Gulzum saita haɗiye su.
Sannan ta ɓace ɓat.
*****************************
Su Jafar dai sai gani suka yi an watsar dasu a tsakiyar fadar sarki Azmul gallar yana tsaye a kan su.
Azmul gallar ya dubi su Jafar ya ƙyalƙyale da dariya, sannan ya murtuke fuska yace,
"Sannun ku da hanya."
Jafar ya miƙe tsaye yana mai riƙe ƙugunsa da hannu biyu ya dubi Azmul gallar cikin alamun raini yace,
"Ya kai wannan sarki mene ne yasa baka ceto rayuwar mu ba da wuri sai bayan da kaga munsha baƙar wahala kamar zamu mutu?"
Sa'adda sarki Azmul gallar yaji wannan tambaya sai ya bushe da dariya yace,
"Ai ba zan iya ceto ku ba,face bayan kunsha wuya ainun, domin haka ƙa'idar kundin tsatsuba take.
Idan kuwa nace zan cece ku da wuri nima hallaka zanyi, domin fadar nan tawa gaba ɗaya ma ragargajewa zata yi, komai na cikinta ya ƙone.
Ni yanzu burina kawai kuyi sauri ku kammala karatun wannan littafi, domin sirrin shamharu ya bayyana gareni kafin ya gama haɗa abubuwa uku da zai ƙera kubar MIFTAHUL ZARBIL, wacce da ita ne zai iya buɗe fada ta inda nawa kundin tsatsuban ke ajiye ya ɗauko ya karanta.
Kuyi sani cewa a halin yanzu Shamharu ya tura su aljani markahul sabus nemo abubuwa ukun kuma har sun samo guda biyu saura guda ɗaya rak,wanda shine rabin ruwan tekun duniyar ku.
Tabbas idan baku gama karanta kundi ba kafin su samo rabin ruwan tekun tawa ta ƙare.
Don haka dole ne na ƙara saurin tafiyar ku a cikin kundin tsatsuba domin ku kammala karatun da wuri.
Ku sani cewa tafiyar su markahul sabus ta sami matsala domin a halin yanzu markahul sabus ya zama ma'abocin addinin musulunci don haka aljani Durmazalu ya sumar dashi sun gudu sun barshi a can cikin wani jeji.
Abinda da Durmazalu bai sani ba shine wannan rabin ruwan tekun ba zai ɗebu ba sai sunyi da gaske,amma inda suna tare da markahul sabus zai iya taimaka musu su ɗebi ruwan a sauƙaƙe."
Sa'adda sarki Azmul gallar yazo nan a zancen sa sai Jafar ya dube shi yace,
"Ya kai wannan sarki kayi sani cewa mu yanzu mun shiga cikin kundin tsatsuban shamharu munga irin bala'in dake ciki,kai kuma naka kundin mai ya ƙunsa?"
Koda jin wannan batu sai sarki Azmul gallar ya ƙyaƙyale da dariya, sannan yace,
"Ni nawa kundin tsatsuban babu komai a cikin sa face labarun nan na da dana yanzu na abubuwan al'ajabi dana tausayi waɗanda suka faru a tsakanin bil'adama tun daga kan mutanen farko kawo izuwa na yanzu.
Kuyi sani cewa a cikin wannan kundi nawa akwai hikayoyi guda dubu a cikin sa,haka kuma a cikin kowace hikaya akwai labarai dubu.
Idan har kuna son kuji kaɗan daga cikin irin waɗannan hikayoyi masu daɗaɗan labarai,ku nemi wani littafi mai suna "HIKAYA DUBU."
Yanzu littafin HIKAYA DUBU na nan a cikin birnin Misra a cikin gidan tarihin su a ƙarƙashin wata akwatu wadda aka sa wani gunki mai suna SARUƘ.
Wannan littafi ba zai taɓa ganuwa ba a wajen kowa ba sai nan da shekaru arba'in masu zuwa,don haka bana tsammanin zaku kai wannan zamani saidai 'ya'yan ku.
Zaku iya bar musu wasiyya don suje su duba littafin su karanta daɗaɗan Hikayoyin dake cikin sa.
Da wannan jawabi nake muku sallama sai mun sake saduwa a karo na uku."
Sarki Azmul gallar na gama wannan jawabi ne macijiyar nan ta sake haɗiye su Jafar suka tsinci kansu a gaban kundin tsatsuba,kuma shafi na ɗari uku da ashirin da biyar ne a buɗe.
Take shafin ya karanto kansa,sannan ya zuƙe su suka faɗa cikin kundi.
Haka dai suka yi ta tafiya a cikin kundi suna haɗuwa da masifu kala-kala a wurare dabam dabam sai da suka shiga har cikin shafi na ɗari shida da hamsin.
Sannan aka sake watso su tasu duniyar ta cikin kundin tsatsuba.
Wannan shine abinda ya faru gasu Jafar bayan sun baro birnin Hasiyatul Lauras inda suka yi mugun artabu da dodo Abulungu a cikin kundin tsatsuba.
(Wanda yanzu kuma sun zo shafi na ɗari shida da hamsin).
*****************************************
Al'amarin bokanya Samaratu kuwa wato mahaifiyar markahus sabus lokacin data baro fadar shamharu sai tayi ta tafiya har ta iso duniyar ƙasa.
Sannan ta nufi garinsu.
Cikin ƙanƙanin lokaci ta sauka a tsakiyar farfajiyar gidanta.
#######################
To masu karatu,iya inda nawa littafin MIFTAHUL ZARBIL na biyu 2 ya tsaya kenan,sauran duk sun falle,wannan iya rabin littafin ne.
Amma bari nayi muku summarizing ɗin abinda ya faru a iya na littafi na biyu 2.
***************************
Bokanya Samaratu ta isa gidanta,sannan kuma tayi bincike akan ɗanta wato markahul sabus,taga duk abinda ya faru dashi tun daga lokacin da suka samo narkakken dutse,zuwa duniyar ƙasa wato inda suka samo duwatsun wuta ma'ana duniyar su Sarudul Makam da 'yan uwansa.
Har taga lokacin da yayi imani da ubangijin musulunci har kuma sa'ilin da aljani Durmazalu ya shammace shi ya sumar dashi da wannan shuɗin hayaƙi.
Wannan al'amari ya jefa bokanya Samaratu cikin tsananin baƙin ciki inda ta cika da tsananin fushi ta tafi neman markahul sabus don ta tilasta shi ya fita daga musulunci.
In baku manta ba,a cikin littafin matsatsubi na uku 3 boka shamharu ya kama su markahul sabus harda Samaratu inda ya tura su su samo abubuwa ukun da zai ƙera kubar MIFTAHUL ZARBIL dashi,amma ya riƙe Samaratu a wajensa yace saidai idan sun kammala aikin su sannan zai sake ta kowa ya kama gabansa.
Wannan kenan.
Toh da yake ban karanta miftahul Zarbil na ɗaya 1 ba,ni dai abinda na fahimta shine Shamharu ya tafi izuwa wata hallarar tsafin sa inda ya bar bokanya Samaratu anan fadar sa ta Bahar zus.
Inda bansan ya akayi ba Samaratu ta kuɓuta sannan ta samu wani gagarumin ƙarfi har siffar jikinta ta sauya har fuka fukanta suka zamo guda miliyan ɗaya,sannan kuma ta hallaka gaba ɗaya dakarun shamharu dake bahar zus.
Ban san ya shi kuma Lu'umanu ya kuɓuta ba.
Wannan kenan.
To Samaratu ta tafi neman markahul sabus don ta tilasta shi ya fita daga musulunci.
To shi al'amarin markahul sabus kuwa,bayan ya farfaɗo kawai sai ya duba yaga ba abokanan tafiyar sa,anan ne yayi tunanin tabbas yaudarar shi suka yi.
Kurum sai ya tsaya yana tunani,daga ya nufi birnin Teheran,wato birnin sarki Lu'umanu saboda yadda Lu'umanu ya kulle shi a kurkuku tsawon shekaru hamsin in ban manta ba.
Shi kuma Lu'umanu bayan ya baro fadar Bahar zus sai shima ya nufi birnin sa na Teheran,da ya isa sai ya iske har sun naɗa sabon Sarki.
Nan take Lu'umanu kuma ya bayyana,koda suka ganshi sai dukkanin su suka firgice,babu wanda yafi tsorata face wanda aka naɗa a matsayin sabon sarki.
Anan Lu'umanu ya tambaye shi akan wannan babban ganganci da yayi,sai sabon sarkin yake sanar dashi cewa ai rabon shi da birnin tsawon shekara shida kenan.
Abin ya baiwa Lu'umanu mamaki,yace raina masa hankali yake son yi,inda sabon sarkin ya gabatar da shaidar shi wato wani zaki wanda yake a cikin gidan sarautar.
Shi kuma Lu'umanu tabbas yasan zakin domin da hannun sa ya kamo shi tun yana ƙarami kuma gashi zakin yanzu ya girma sosai.
Anan Lu'umanu ya yarda amma da yake azzalumi ne sai ya dubi sabon sarkin yace,duk da haka hukuncin kisa ne a kansa tunda ya zauna akan karagar sa😂😂😂.
Harya ɗaga takobin sa zai sare kan sabon sarkin nan sar kurum ga markahul sabus ya diro, sannan ya nuna Lu'umanu da ɗan yatsa yace shine ya kulle shi a kurkuku a cikin akwatin ƙarfe shekaru masu tsawo,amma daga yanzu zaluncin ya ƙare,kuma muddin yana so ya ƙyale shine ya karɓi addinin musulunci, Lu'umanu yace bai san zance ba,shi da musulmai sai yaƙi.
Anan ne suka kaure da faɗa,su faɗa nan su faɗa can,a inda markahul sabus ya tumurmusa Lu'umanu ya shaƙe shi,har Lu'umanu ya fara kakarin mutuwa ne kurum sai markahul sabus yaji an sure shi anyi sama dashi.
Shi kuma Lu'umanu ya tsaya yana shafa wuyan sa.
Karku manta,ni dai ban san ya akayi Lu'umanu ya tsira ba harya dawo Teheran,amma dai wannan asalin Lu'umanu ne, ma'ana asalin ruhinsa ne a gangar jikin sa.
Shi kuma markahus sabus sai da akayi can sama dashi sannan ya ganshi a cikin kejin ƙarfe sannan yaga mahaifiyarsa.
Anan nake maku sallama da fatan Alheri, tare da fatan idan an samu MIFTAHUZZARBIL na uku to zaki GA mun ci gaba da yardar Allah.
Nagode.
Najibullahi Muhammad #legends