← Book details Miftahuzzarbil Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
CHAPTER 3 OF 4

PART D ❤️❤️

Miftahuzzarbil Part 1 Complete Hausa Novel · about 60 min read

NA ABDUL'AZIZ SANI MADAKIN GINI 🤴
TYPING AHMAD MUNNIR ☺️
POSTING NAJIBULLAH MUHAMMAD ❤️

MARUBUCIN YACI GABA DA CEWA...
Cikin zafin nama Ashikatul Ashiriya ta yunqura ta zare wata qaramar wuqa daga qugunta ta kai masa sura a kirji.Haiman ya goce wuqar ta soki iska.Kafin ta sake wani yunqurin tuni ya kir6a mata tasa wuqar a kirji.Wuqar ta nutse a cikin kirjin nata ta fadi qasa jini na 6ul6ulowa tana kakarin mutuwa,har ynx bata saki wuqar dake hannun ta ba.Haiman ya sunkuya a kanta yace,"wannan shine sakamakon 'yar uwar data nemi hallaka dan uwanta saboda mulki da dukiya."
Kafin Haiman ya gama rufe bakinsa Ashikatul Ashiriya ta luma masa wuqar nan dake hannun ta a maqoshin sa,take ya fadi qasa matacce.A lokacin ne na qaraso wajen na fusge littafin nan daga hannun ta kuma na doki hannun ta mai ruqe da wuqa da qafata.Wuqar tayi can gefe guda.Ashikatul Ashiriya tayi dariyar qarshe tace,"yake 'ya ta kiyi sani cewa ban mutu raguwa ba,jaruma ce ni wadda na kashe daya daga cikin manyan jaruman duniya wato dan uwana Haiman.Kiyi sani cewa ga dukiyar nan bisa raquma da alfadarai duk taki ce ke kadai,amma ki sani kema ba zaki gama rayuwar ki ba ta duniya sai qunci da bakin ciki sun riske ki.Tuni na gama shirya hakan cikin sihirin tsafi.Da wannan kalma nake miki bankwana a ci duniya da tsinke lafiya."
Ashikatul Ashiriya na gama fadin haka idanun ta suka qafe komai nata ya daina motsi.A dai dai wannan lokaci ne jarumi Miqdad da sarki Shaubatul Azman suka gama karkashe sauran dakarun Ashikatul Ashiriya.Sannan suka taho gareni.Koda jarumi Miqdad yaga gawar Haiman kusa da gawar sarauniya saiya durqusa ya dago da gawar Haiman ya rungume ta.Sannan ya fashe da kuka yana mai cewa,
"Shi kenan na rasa abokina,na rasa aminina."
Nan dai muka yi ta rarrashin sa har ya daina kuka.Sannan muka tsaya saida duk raquman nan da alfadaran nan masu dauke da dukiya sama da dubu dari uku suka gama fita daga cikin kogon Baitul Husuk,sannan muma muka fita.A bakin kogon na tsaya na bude littafin nan zuwa shafin karshe na karanta wadansu kalmomin tsafi.Take kogon ya fara ruftawa cikin kasa.Kasa ta kama girgiza bisa dole muka ruga da gudu tare da raquman mu da alfadaran mu.Har muka yi nisa daga wajen kogon nan bai gama nutsewa ba a cikin kasa.
Daga inda muke muna iya hango nutsewar kogon.Anan ne na tsaya na dubi jarumi Miqdad da mahaifina Shaubatul Azman ina mai murmushi kawai saina rungume su muka kama tsalle gaba daya cikin matuqar farin ciki.Mu uku kacal muka tsira daga cikin miliyoyin mutanen da suka shiga cikin kogon Baitul Husuk.Ba tare da 6ata lokaci ba muka kada raquman mu da alfadaran mu muka yi ta tafiya har muka iso birnin mahaifina Shaubatul Azman.Anan ne aka daura aurena da jarumi Miqdad.
Bayan an daura aurene yayi sallama dani yace zai tafi kasar su in yaso na riske shi a can.Lokacin da Miqdad yaje birnin Shauqib inda dan uwansa ke mulki saiya iske ana yaki har an kashe dan uwan nasa.Nan take ya kai dauki ya kashe abokan gabar gaba daya.Bisa wannan dalili ne aka ba shi mulkin kasar.Saida ya kwana ashirin akan mulki sannan mahaifina Shaubatul Azman yasa aka shirya mini tafiya tare da dakaru dubu dari 'yan rakiya.Sannan ya bani dukkanin raquman nan da alfadaran nan masu dauke da dukiya muka tafi ga mijina sarki Miqdad.Bamu shigo nan birnin Shauqib ba sai la'asar sakaliya.Raqumana da alfadarai na kuwa sai da kwanaki bakwai suka shude suna shigowa cikin garin sannan suka qare saboda yawa.
Koda gimbiya suhaila tazo nan a labarin ta sai kuyanga suzaila tayi ajiyar xuciya tace,"ya shugabata a gaskiya kinyi butulci ga sarki Miqdad domin ba don shi ba da baki kawo iyanzu ba.Ya kamata ace kinso duk abinda ya ke so.Ki tuna baqar wahalar daya sha a yakin da yayi a cikin garin ku,duk saboda ke kuma ki tuna yadda ya saida rayuwar sa a cikin kogon Baitul Husuk.Ina mai shawartar ki kije ki nemi gafarar sa bisa qin bawa Mozur da kika yi tunda farko."
Koda zulaiya ta gama wannan jawabi sai Suhaila ta kama dariya tayi ta dariyar kamar ba zata daina ba.Al'amarin daya firgita Zulaiya kenan ta miqe tsaye zata gudu.Cikin zafin nama Suhaila ta cafkota ta shaqe mata wuya da hannu biyu.Tun Zulaiya na harba kafafunta da hannayenta harta kasa motsi harshenta ya zazzago waje.Suhaila tayi jifa da gawar Zulaiya tace,"wace ce ke da har za ki bani shawara akan abinda ya dace nayi?
Ke baiwa ce ya kamata ace kin tsaya iya matsayin ki."
Tana gama fadin hakan ne ta miqe tsaye ta shige cikin turakar ta.Nan da nan fadawa suka dauke gawar Zulaiya suka tafi da ita.Wannan shine abinda ya faru ga Suhaila matar sarki Miqdad bayan ta gama bada labarin yadda ta hadu da sarki Miqdad har ta zamo matarsa.
A can nahiyar kasashen baqaqen fata kuwa a cikin birnin Malhiya inda sarki Amzadu ke mulki anan ne bawa Mozur ke bauta a wani 6angare na gidan sarautar.Da yake Mozur ya kasance kakkarfa sai aka kaishi cikin wani wani dakin wata na'urar dutse wadda ake nuqa hatsi da ita.A kalla sai kato arba'in sun taru suke iya juya dutsen dake nuqa dawar,amma bawa Mozur shi kadai yake juya dutsen kuma saiya yini yana aikin da kato arba'in za suyi cikin kwana biyu.
***********
Tunda aka siyo bawa Mozur a birnin Shauqib aka kawo wannan daki na nuqan hatsi bai ta6a fita wajen dakin nan ba na tsawon wata tara.Kai bai qara ganin hasken rana ma ba.Ko yaushe yana cikin aiki.Da daddare ne kadai yake samun damar hutu,kuma sau daya ake ba shi abinci da ruwa.Wani lokacin idan bawa Mozur ya tuno da irin rayuwar sa ta da sa'adda yake can kasar Shauqib tare da sarki Miqdad saiya fashe da kuka domin ya san cewa ya rasa babban masoyi,wanda har abada ba zai sake samun kamar sa ba.Kuma rayuwar sa tazo karshe domin karfinsa gaba daya a cikin daki na nuqan hatsi zai kare.
Sarki Amzadu nada wata kyakkyawar 'ya budurwa 'yar shekara goma sha takwas wacce yake matuqar kauna,ana kiran ta da suna gimbiya Laslaiya.A iya rayuwar gimbiya Laslaiya babu abinda take so face kallon 'yan kokawa.Bisa wannan dalili ne take shirya wasan kokowa bayan kowane kwana talatin.Duk wanda yaci gasar sai ta kawo kyautar dukiya mai tsananin yawa ta ba shi.Jaruman dake wannan kokowa sukan zo ne daga kasa-kasa.
Akwai wani babban bafaden sarki Amzadu mai suna Azmandu wanda shine da alhakin kula da gidan nuqan hatsin sarki inda bawa Mozur ke aiki.Duk sa'ar da za'a yi wannan gasa ta kokawa ya kan tafi neman babban jarumi yazo da shi,domin idan jarumin yaci gasar ya sami dukiya mai yawa suyi kashe mu raba.Yanzu anyi gasar har sau uku amma duk jaruman da yake kawowa basa nasara.A ranar da ya rage saura kwana bakwai ayi gasa ta gaba sai hankalin Azmandu ya dugunzuma saboda jin cewa dukiyar da gimbiya Laslaiya zata bayar a wannan karon tafi ta duk wadda ta bayar a baya.Ba wani abu ne ya tayar da hankalin Azmandu ba face sanin an gama qureshi bashi da sauran wani jarumi wanda yake ganin zai iya cin gasar saboda an kawo zakwaquran jarumai fitattu wadanda suka yi shuhura a wasu 6angararo na duniya.
Gefen magriba ne Azmandu ya shigo cikin ɗakin nuƙan inda bawa Mozur ke kishingiɗe yana hutawa saboda gajiyar aikin da yayi.Azmandu ya kewaya cikin ɗakin yaga cewa Mozur ya niƙa buhun hatsi da yawa sama da yadda ya saba yi a kullum.Koda ganin haka sai yayi murna nan take yasa aka ƙarowa Mozur abinci da ruwan sha ishasshe.Sannan ya zauna kusa dashi yana tambayar sa yace,
"Ya kai Mozur ya akayi yau kayi aiki mai yawa fiye da yadda ka saba yi?"
Koda jin wannan tambaya sai Mozur yayi murmushi yace,"ya shugabana kayi sani cewa a duk sa'adda raina ya ɓaci ina iya yin abinda kowa zaiyi mamaki.Kayi sani cewa a yau na tuno da wani tsohon mai gidana ne wanda ke matuƙar ƙaunata fiye da komai a rayuwar sa amma saida matarsa ta rabamu.Sa'adda na tuno da irin makircin data ƙulla mini ne don ta kashe ni nayi ta aiki a ɗakin nan fiye da yadda na saba yi."
Koda jin wannan batu sai Azmandu yayi shiru yana tunani.Daga can ya dubi Mozur yace,"shin ka taɓa yin wasan kokowa kuwa a can garinku?"
Mozur yace,"eh na taɓa yi sau ɗaya harma na ci gasar."
Yayin da Azmandu yaji haka sai murna ta kamashi ya dubi Mozur yace,"ina son na shigar dakai cikin gasar kokawa wadda gimbiya Laslaiya ke shiryawa a kowanne kwana talatin,zaka iya?"
Cikin murna Mozur yace,"ƙwarai kuwa zan iya kuma zan baka mamaki."
Ba komai ne yasa Mozur yake son a shigar da shi wannan gasa ba sai don kawai ya sami damar fita daga cikin wannan ɗaki yaga hasken rana wanda rabonsa da shi yau wata tara kenan da ƴan kwanaki.
Tun daga wannan rana ya dinga ɗokin zuwan ranar gasa,saboda jin daɗin hakanne ya cigaba da hazaƙar aikinsa fiye da yadda ya saba.Azmandu kuwa yasa a rinƙa bashi abinci mai kyau kuma isasshe.Nan da nan jikin Mozur yayi kyau a cikin kwana bakwan ya zamana ya mayar da duk komaɗar jikinsa da ramarsa.Kyawunsa da kwarjinin sa suka ƙara bayyana ƙarara.
Da ranar gasa tazo tunda sassafe Azmandu yazo ya riski Mozur ya kawo masa abinci da abin sha na musamman tare da waɗansu kyawawan tufafi.Bayan Mozur yaci ya ƙoshi sai Azmandu ya bashi waɗannan tufafin gasa,sannan ya dube shi yace,"ya kai Mozur ka sani cewa kai bawa ne na sarki kuma a ƙa'ida bai kamata na ciyar da kai abinci mai kyau ba kuma isasshe,amma gashi tun daga ranar daka yi aikin nan mai yawa kawo iyanzu ban fasa ba.Idan har kana son na cigaba da kyautata maka dole kayi iya ƙoƙarinka kaci gasar wannan kokawa.Kai in dai kaci wannan gasa nayi maka alƙawari zaka rinƙa samun hutun kwana uku a sati,kuma duk sanda kake da muradin mace zansa a kawo maka ɗaya daga cikin bayi na."
Koda jin haka sai bawa Mozur yayi murmushi yace,"ni kuwa da izinin abin bautata mai girma Lazzatul sakaru saina sami nasara a cikin wannan gasa."
Haka dai Azmandu da bawa Mozur suka cigaba da tattaunawa har lokacin tafiya fada yayi inda za'a gabatar da wannan gasa ta kokawa.

MU HADU A PART E DON JIN CIGABAN WANNAN KAYATACCIYAR HIKAYAR.**MIFTAHUL-ZARBIL**
LITTAFI NA BIYU✍️✍️❤
PART E 👌✌
NA: ABDUL'AZIZ SANI MADAKIN GINI✍️✍️
TYPING: AHMAD MUNNIR.
POSTING:NAJIBULLAH MUHAMMAD 🙂❤👌

Tom jama'a kyan alkawari cikawa, kamar yadda na maku alkawarin kawo maku cigaban wannan littafin a yau din nan, to gashi na cika.
Allah ya Temake mu akan cika duk irin alkawarin da muka ɗauka.

MARUBUCIN YA CI GABA DA CEWA..

Koda jin haka sai bawa Mozur yayi murmushi yace,"ni kuwa da izinin abin bautata mai girma Lazzatul sakaru saina sami nasara a cikin wannan gasa."
Haka dai Azmandu da bawa Mozur suka cigaba da tattaunawa har lokacin tafiya fada yayi inda za'a gabatar da wannan gasa ta kokawa.
Lokacin da su Mozur suka isa ƙofar fada sun makara domin tuni an fara gasar kuma wasu jarumai biyu ne akan wani faffaɗan gini mai tudu suke kafsawa.Jama'a sun kewaye wannan tudu an cika maƙil sai shewa da ihu da tafi ake yi.Daga can ɓangaren gabas kuwa nesa kaɗan sarki Amzadu ne da ƴarsa gimbiya Laslaiya zaune bisa karagar mulki dakaru sun kewaye su suna kallon wannan kokowa.Kallo ɗaya mutum zai yiwa gimbiya Laslaiya ya san cewa yau tana cikin matuƙar nishaɗi domin fuskar ta cike take da murmushi da annuri.
Gimbiya Laslaiya ta kasance kyakkyawa ta kwatance domin Allah yayi mata kyakkyawar surar ƙirar kalangu.Tana da dogon gashi baƙi siɗik mai ƙyalƙyali wanda ya sauko har ƙasan cibiyarta,tana da dara daran idanuwa,ɗan ƙaramin baki da dogon hanci.Ƙirjinta cike yake taf,kuma tana da tsukakken ƙugu.Ƴan yatsun hannayenta dogaye ne zara zara gwanin ban sha'awa kuma tana da dogon wuya.Duk da kasancewar ta baƙar fata ba balarabiya ba,bata da duhu ta kasance wankan tarwaɗa.A zahirin gaskiya babu wani ɗa namiji da zaiga gimbiya Laslaiya bata ɗau hankalin sa ba.
Koda shigowar Azmandu da Mozur cikin wannan taro sai Azmandu ya kama hannun Mozur ya kaishi wajen alƙalan gasar ya gabatar dashi a matsayin sabon gwanin sa.Cikin mamaki alƙalin gasar wanda ake kira Daraz ya dubi Azmandu,sannan ya ƙarewa Mozur kallo ya bushe da dariya yace,"haba Azmandu ya zako zo mana da wani ƙaramin mutum haka kace shine gwanin ka?
Anya kuwa ka dubi jaruman bana da kyau?"
Azmandu ya waiga inda jaruman suke tsaye wajen su talatin.Gaba ɗayansu gabza gabzan ƙarti ne masu ƙwanji da murɗaɗɗen jiki,babu wanda girmansa bai ninka na bawa Mozur ba sau uku.Azmandu ya haɗiyi miyau gami da ajiyar xuciya yace,
"Ba komai ɗan hakin daka raina shi ke tsone maka ido,kai dai kawai ka shigar dashi cikin gasar."
Nan take Daraz ya ƙara bushewa da dariya yace,"lallai yau da rabon zaka ji kunya kenan amma tunda kace a shigar dashi zan shigar."
Daraz ya dubi Mozur a wulaƙance yace,"mene ne sunanka?"
"Suna na Mozur bin Miƙdad."Ya bashi amsa.
Daraz ya sake tambaya yace,"daga wace ƙasa?"
"Daga birnin Shauƙib."
Koda jin haka sai Daraz ya ƙurawa Mozur idanu cikin yanayin mamaki har saida Mozur ɗin yace da shi,"Ina zan tsaya?"
Sannan ya nuna masa inda jaruman gasa ke tsaitsaye suna kallon waɗanda ke kafsawa.Kai tsaye Mozur ya tafi inda jaruman suke ya shige cikin su ya tsaya.Jaruman kuwa suka rinƙa kallonsa cikin mamaki don basu san dalilin da yasa yayi wauta ba ya shigo cikin su.Tsayuwar Mozur keda wuya sai idanun sa suka kai inda sarki Amzadu da gimbiya Laslaiya ke zaune.Koda yayi arba da Laslaiya sai ya ƙura mata ido yana mai mamakin tsananin kyawunta.Nan take ya tuno da gimbiya suhaila ya kasa tantance wadda tafi kyawu tsakanin Laslaiya da Suhaila,amma sai yace a ransa,"ni dai inda zaɓi za'a bani dana zaɓi wannan baƙar fatar ƴar uwata,domin tafi burgeni akan suhaila."
Yana gama faɗin haka ne hankalin sa ya koma kan jaruman dake kafsawa a kan wannan gini mai tudu.A lokacin ne ɗaya daga cikin su mai suna Zarto ya ɗaga abokin gwamin nasa sama ya dunga hajijiya dashi har saida ya jigata shi sannan ya kwaɗa shi da ƙasa.Take jarumin ya sume fili ya cika da shewa aka yi ta yiwa Zarto tafi.
Zarto ya kasance ƙaton gaske domin duk cikin ƴan kokawar babu mai girmansa da kwarjinin sa.Lokacin da Mozur yaga Zarto saida zuciyar sa ta kama bugawa da ƙarfi domin yasan cewa ka ba'a gwada ba linzami yafi ƙarfin bakin kaza.Nan dai Zarto ya sauko daga kan tudun gumurzu ya koma cikin jarumai ya tsaya.Shi kuma waccan jarumi da suka kafsa da Zarto sai da aka yayyafa masa ruwa sannan ya farfaɗo.Alƙalin gasa ya ƙara kiran wani jarumi waishi Kambus.
Kambus ya hawo kan tudun kafsawa yana mai tafiyar taƙama,jin kai da hura hanci.Shima Kambus ƙato ne na gaske domin da kaɗan Zarto zai fishi,amma kuma yafi Zarto tsawo sosai.Ba zato ba tsammani sai Mozur yaji an kirawo sunan sa cewa ya hawo kan tudun kafsawa shine zai kara da Kambus.Nan fa hankalin Mozur ya dugunzuma,amma sai ya dake ya hau kan tudun cikin ƙarfin hali.Koda ya tsaya a gaban Kambus sai ya zamo kamar ɗan tsako a gaban shirwa domin tsawon sa ma iya cibiyar Kambus ya tsaya.
A wannan lokaci ne gimbiya Laslaiya ta ƙurawa Mozur idanu tana mai mamakin tsautsayin da ya shigo da shi cikin wannan gasa domin shine mafi ƙanƙanta a cikin jaruman.Kambus ya sunkuyo da kanshi ƙasa fuskar sa ta tsaya daf da Mozur yana muzurai yace,"kai ɗan tatsitsi mai tsautsayin wahala wane irin karambani ne ya shigo dakai cikin wannan gasa?"
Mozur yayi murmushi yace,"neman suna da neman arziki ne ya kawo ni kamar yadda ya kawo ka."
Kambus ya ƙyalƙyale da dariya kuma ya murtuke fuskar sa a lokaci guda yana mai cewa,"yaro kayi ganganci,yau zan koya maka darasi domin kasan cewa bakin rijiya ba wajen wasan ka bane."
Kafin Mozur yace wani abu tuni Kambus ya shaƙo wuyansa da hannu ɗaya saiga Mozur na wutsil wutsil da ƙafafu a sama kamar jelar ɓera a bakin kyanwa.Nan fa filin wajen ya cika da dariya,kowa sai ƙyaƙyatawa yake.Azmandu ne kaɗai sai kuma gimbiya Laslaiya wacce ta shiga cikin tashin hankali saboda tausayi.Shima Kambus sai yayi ta ƙyalƙyala dariya yana zagaya wa akan tudun kuma yaƙi sakin wuyan Mozur.
Nan da nan idanun Mozur suka yi ƙulu ƙulu suka yi jawur.Koda yaji numfashin sa na neman ɗaukewa saiya harzuƙa cikin tsananin zafin nama ya tattare ƙarfinsa gaba ɗaya yasa hannu biyu ya ɓanɓare hannun Kambus daga wuyansa kuma yayi wurgi da Kambus can gefe ɗaya.Saiga Kambus na katantanwa a ƙas.Al'amarin daya jefa kowa cikin mamaki kenan filin gaba ɗaya yayi tsit kuma sai da kowa ya miƙe tsaye aka zubawa Mozur idanu ana mai al'ajabinsa.Shi kuwa Azmandu saboda farin ciki bai san sa'adda ya kama wuyan alƙalin gasa ba yana tsalle da shewa.Kamar haɗin baki sai kowa ya kama yiwa Mozur tafi.Gimbiya Laslaiya kuwa saita miƙe tsaye daga kan karagar ta tana ta tafi da kallon jarumi Mozur tana murmushi.
Koda ganin haka sai sarki Amzadu ya kamo hannun ta ya zaunar da ita yana mai harararta.Laslaiya ta nutsu ta kau da kai gefe ɗaya.Dama ƙa'idar wannan gasa itace indai mutum ya faɗi ƙasa to an cinye shi.Koda Kambus yaga yaje ƙas sai idanun sa suka ciko da ƙwalla saboda tsabar takaicin cewa ƙanƙanin mutum kamr Mozur ya kayar da shi.Haka dai Kambus ya sauka daga kan tudun cikin jin kunya da baƙin ciki har yana kuka.Bai tsaya a filin ba gaba ɗaya ya bar wajen gasar.Nan dai aka cigaba da wannan gasa.Duk wanda Mozur ya kara da shi sai yayi nasara.Sai da takai ta kawo cewa gaba ɗayan jaruman nan na tsoron kafsawa da Mozur face mutum ɗaya wato Zarto,kuma ba'a haɗasu ba sai a zagayen ƙarshe na gasar.Koda ƴan kallo suka ga jarumi Mozur da jarumi Zarto tsaye a kan tudun kafsawa sai filin ya kaure da shewa da ihu kowa na zaɓin gwanin sa.Wasu suce Zarto ne zaiyi nasara a wannan gasa,wasu kuma suce Mozur ne.Nan fa ƴan caca suka fara fito da kuɗaɗe don neman sa'a.A wannan rana ƴan caca sun zuba dubunnan dirhami masu yawa akan wannan gasa.
Zarto da Mozur suka fara kallon kallo.Sannan suka hau zagaya filin kowannen su zuciyar sa ciki da saƙe saƙen hanyar da zaibi ya sami nasara.Cikin shammace Zarto ya kawowa Mozur cafka da niyar ya rungume shi ya matse shi.Mozur ya goce cikin zafin nama ya wuce ta tsakankanin ƙafafunsa.Takaici ya kama Zarto ya ciza yatsa domin a tarihin kokawarsa bai taɓa kaiwa wani wannan hari ba ba tare da ya sami sa'a da nasara ba.Zarto ya juya ya sake fuskantar Mozur ya sake kai masa irin wannan hari a karo na biyu.Ai kuwa sai Zarto ya sami nasarar damƙar Mozur ya zamana ya matse masa baya da hannu biyu.Mozur ya kwarara ihu saboda tsananin jin zafin ruƙon da yayi masa.
Al'amarin da ya razana kowa kenan a wajen.Gimbiya Laslaiya kuwa bata san sa'adda ta miƙe tsaye ba zumbur cikin alamun razani.Sarki Amzadu ya sake danƙwafar da ita zaune yayi mata raɗa a kunne yace,"idan kika sake miƙewa kin gama kallon gasar kenan."
Cikin fushi Laslaiya ta kau da kai ta cigaba da kallon abinda yake faruwa.Mozur yayi iya ƙoƙarinsa akan ya ɓamɓare hannayen Zarto daga bayansa amma ya kasa kawai sai ya yiwa Zarto karo da ka a fuska.Bisa dole Zarto ya saki Mozur ya dire ƙasa da ƙafafunsa.Fuskar Zarto ta cika da raɗaɗi har idanun sa suka rufe ya zamana yana ganin mutane dishi dishi,saida ya girgiza kanshi sannan ya watstsake.Zarto ya ruga kan Mozur yana ruri da nufin ya sunkuce shi.Saida ya rage saura taku ɗaya ya riskeshi Mozur yayi tsalle sama ya shallake Zarto ya dira a bayansa.Cikin zafin nama ya juya ya shaƙo wuyan Mozur da hannu biyu saiga Mozur yana wutsiltsila ƙafafu yana kakarin mutuwa.Zarto ya ƙara haɗa ƙarfinsa duka yana mai daɗa shaƙe Mozur.Tabbas niyarsa kawai ya kashe Mozur murus har lahira.
Nan da Mozur ya fara ƙoƙarin ɓanɓare hannun Zarto amma saiya kasa.Nan da nan idanun Mozur suka wurƙile suna nuna alamun suma.Laslaiya dai bata san sa'adda ta fara zubar da hawayen tausayi ba.Gashi a ƙa'idar wannan gasa ba'a raba faɗan face ɗaya daga cikin ƴan kokawar yaje ƙasa.A zahiri dai mutane suna iya ganin wutsil wutsil ɗin ƙafafun Mozur da motsin hannuwansa kamar ba suma yayi ba amma a baɗini ƙanin suma yayi,inda ya shiga tunanin irin haɗarurrukan da ya shiga a can birnin Shauƙib a lokutan da gimbiya Suhaila tasa aka yi masa dukan kawo wuƙa don a kashe shi da kuma lokacin data sa aka ɗaure shi a cikin buhu aka jefa shi cikin tsakiyar teku.Koda Mozur yazo nan a tunanin sa sai zuciyarsa ta kama tafarfasa ya watstsake.Take wani sabon ƙarfin na musamman ya shige shi,kawai sai aka ji ya kwarara uban ruri lokaci guda ya ɓanɓare hannuwan Zarto daga wuyansa kuma ya sunkuci Zarto cikin zafin nama yayi sama dashi ya dinga hajijiya da shi.
****************
A wannan lokaci ne gimbiya Laslaiya ta bushe da dariyar farin ciki tana yiwa Mozur tafi.Mozur yayi ta hajijiya da Zarto a sama saida ya fita daga haiyacinsa sannan ya kwaɗa shi da ƙasa.Gaba ɗaya filin ya ruɗe da shewa da tafi.Jama'a suka ruga kan tudun da ake gasa suka ɗaga jarumi Mozur sama suna cilla shi a cikin iska yana dawowa kan hannuwansu ana yi masa jinjina.A sannan ne Mozur da gimbiya Laslaiya suka ƙurawa juna ido yaga tana yi masa tafi fuskarta cike da annuri amma kuma ga hawaye na zuba a idanun nata.Al'amarin da yayi matuƙar jefa Mozur cikin tsananin mamaki da damuwa kenan.Nan take aka kira Azmandu yazo gaban gimbiya Laslaiya ya kwashi gaisuwa.Sannan ta sunkuya ta ɗauki ƙatuwar jaka cike da dirhami ta miƙa masa.Azmandu ya karɓi jaka ya fara tiƙar rawa cikin tsananin farin ciki.Sannan ya ruga inda jarumi Mozur ke tsaye ya rungume shi yana mai yi masa jinjina.Sarki Amzadu ya kama hannun gimbiya Laslaiya suka nufi cikin gidan sarauta dakaru na biye da su.Laslaiya tayi ta waigen jarumi Mozur suna kallon juna tana murmushi a gareshi har ta ƙule ya daina ganinta.
Lokacin da Mozur da Azmandu suka koma cikin gidan nan inda Mozur ke bauta sai suka zauna don su huta.Azmandu yasa aka kawo musu abinci iri iri da kayen shaye shaye kala kala,don suyi walimar wannan nasara da suka samu.Nan take Azmandu ya kama ciye ciye,shi kuwa Mozur saiya zubawa abincin idanu ya kasa ci,kuma ba komai yake gani ba a cikin abincin face fuskar gimbiya Laslaiya.Zuciyarsa cike da wasu wasi yana mai tambayar kansa cewa me yasa gimbiya ke yi mini murmushi haka?
Kuma mene ne dalilin zubar hawaye a idanunta?
Amsar da ya kasa samar da ita kenan a cikin ƙwaƙwalwarsa.Koda Azmandu ya lura da halin da Mozur ya shiga saiya dubeshi yace,
"Ya kai wannan jarumi tunanin me kake haka wanda ya hanaka cin abinci alhalin yau ranar farin ciki ce a gare mu ko kuwa wani abun kake da buƙata ka kasa sanar dani?"
Koda jin wannan tambaya sai jarumi Mozur yayi ajiyar zuciya yace,"ya shugabana kayi sani cewa bana buƙatar komai daga gareka kuma babu abinda nake tunani face yadda al'amuran rayuwa ta suka kasance a da da yanzu."
Da jin haka sai Azmandu ya bushe da dariya sannan yace,"ashe kuma bayi kukan shiga damuwa da tunani irin wannan?Ai inda ni bawa ne har abada bazan yarda na sa wani abu a raina ba,wanda zai dame ni,tunda nasan cewa a cikin bauta rayuwa ta zata ƙare."

MU HAƊU A PART F DON JIN CIGABAN WANNAN KAYATACCEN LABARIN.**MIFTAHUZZARBIL**
LITTAFI NA BIYU✍️✌
PART F ❤❤
NA ABDUL'AZIZ SANI MADAKIN GINI🧝‍♀️
TYPING AHMAD MUNNIR.
POSTING NAJIBULLAH MUHAMMAD.

MARUBUCIN YA CI GABA DA CEWA...

Ai inda ni bawa ne har abada bazan yarda na sa wani abu a raina ba,wanda zai dame ni,tunda nasan cewa a cikin bauta rayuwa ta zata ƙare."
Mozur yayi murmushi yace,"ya shugabana kayi sani cewa ita rayuwa bata da wani haƙiƙani akan kowa.Da mu daku duk ɗaya ne domin bawa na iya zama sarki,haka kuma sarki na iya zama bawa."
Koda jin wannan batu sai Azmandu ya furzar da abincin dake bakinsa cikin fushi yace,"wannan wace irin maganar banza kake yi?
A ina ka taɓa ganin sarki ya zama bawa?
Ai abinda ba zai taɓa yiwuwa bane,domin ko tarihin labarun da suka shuɗe ban taɓa jin haka ba."
Nan dai Azmandu ya rufe Mozur da faɗa yayi ta bambami har ya gaji.Sannan ya tashi ya fice cikin fushi ba tare da ya kammala cin abubuwan dake gabansu ba.Shi kuwa Mozur saiya kishingiɗa ya lumshe idanun sa ya cigaba da ganin hoton fuskar gimbiya Laslaiya a cikin zuciyarsa.
Kamar yadda jarumi Mozur ya kasance cikin sabon yanayi na tunani da rashin sukuni haka gimbiya Laslaiya ta kasance domin ita ma dai a wannan rana ko ruwa bata iya sha ba bare cin abinci.Idan ta kwanta sai taji kwanciyar ba daɗi don haka saita miƙe zaune.
Zaman ma saita ji ba daɗi kawai saita tayi ta kai komo a cikin harabar gidanta ta kasa zaune ko tsaye.
Duniyar gaba ɗaya ta yi mata zafi.
Tana cikin wannan hali ne mahaifiyarta Zalisha ta shigo ta risketa.
Kallo ɗaya Zalisha ta yi wa Laslaiya ta fuskanci cewa lallai tana cikin damuwa.
Nan take Zalisha ta kama hannun Laslaiya ta jata izuwa cikin ɗakinta ta zaunar da ita a gefen gado suka fuskanci juna.
Zalisha tace,"yake 'ya ta ki yi sani cewa babu abinda nake so a duniyar nan sama da ke,kuma duk abinda kike so shi nake so,haka kuma wanda kike ƙi dole na ƙi shi.
Yake 'ya ta haƙiƙa yau kina cikin damuwa don haka zuciya ta ta sosu ina umartarki da ki hanzarta sanar dani abinda ke damunki,domin na amince miki shi yanzu take."
Sa'adda Zalisha tazo nan a zancen ta sai Laslaiya tayi ajiyar zuciya.
Sannan tace,"yake ummina ki yi sani cewa babu abinda ke damuna face son ganin jarumin da yaci nasarar gasar kokawa a yau."
Koda jin haka sai mamaki ya kama Zalisha tace,"wane ne wannan jarumin?"
Haka kuma mene ne sunansa?"
Cikin yanayin damuwa Laslaiya tace,"ban san kowane ne shi ba,amma naji ana kiransa da suna Mozur,kuma sarkin gida Azmandu ne yazo da shi filin gasa."
Koda jin haka sai Zalisha tace,"ai kuwa kamar na taɓa jin sunansa a cikin gidan sarautar nan amma dai bari dai nasa a bincika...."
Nan take Zalisha ta kira wata baiwa Amaratu tace da ita ta ruga gidan sarkin gida Azmandu tace yazo yanzun.
Amaratu ta ruga da gudu don cika umarni.
Jim kaɗan sai ga ta ta dawo tare da Azmandu.
Azmandu ya ƙaraso da sauri izuwa gaban Zalisha ya faɗi ya kwashi gaisuwa cikin biyayya da sunkui da kai ƙas.
Zalisha ta dube shi tace,"ya kai Azmandu kayi sani cewa ban kira ka nan dan komai ba don sai ka yi mini cikakken bayani.
Ina son nasan wanene Mozur jarumin da yaci gasar kokawa a yau."
Azmandu ya ɗago kai ya dubi Zalisha yace,
"Ya shugaba ta Mozur ba kowa bane face bawanku wanda ke aikin niƙan hatsin gidan nan.
Kiyi sani cewa yau watansa tara cif a cikin ɗakin hatsi bai taɓa fita ba sai yau tun daga ranar da aka kawo shi daga birnin Shauƙib sa'adda aka siyo shi a matsayin sa na bawa."
Koda jin wannan batu sai mamaki ya kama Zalisha da Laslaiya, saboda daɗewar Mozur a cikin gidan sarautar tasu amma ko sau ɗaya basu taɓa ganin sa ba.
Zalisha tace,"yanzu yana ina?"
"Yana cikin ɗakin aikinsa."Azmandu ya amsa.
Koda jin haka sai Zalisha ta miƙe tsaye.Sannan ta kamo hannun Laslaiya ta tashe ta tsaye,kuma ta dubi Azmandu tace,
"Na umarce ka da ka kaimu wajen Mozur yanzu-yanzu."
Cikin biyayya Azmandu yace,"an gama ya shugaba ta."

*********************************

Nan take Azmandu ya wuce gaba Zalisha da Laslaiya suka bishi a baya suka yi ta tafiya cikin gidan sarautar suna ratsawa ta saƙo-saƙo,lungu-lungu.
Sai da suka yi 'yar tafiya mai tsawo.
Sannan suka iso gidan da bawa Mozur ke ciki.
Ko ina ka duba dakaru ne a tsaitsaye riƙe da makamai suna kula da ma'aikata.Kuma sai mutum ya wuce ƙofofi goma sha biyu.
Sannan zai isa ƙaton ɗakin da bawa Mozur ke ciki.
A bakin kowace ƙofa dakarun tsaro ne a tsaitsaye guda goma sha biyu.
Duk ƙofar da aka zo sai Azmandu ya ƙwanƙwasa yayi magana.
Sannan za'a leƙo ta wata 'yar ƙaramar taga a tabbatar da cewa shine ɗin sannan a buɗe.
Duk inda suka shiga aka ga Zalisha da Laslaiya sai ayi mamakin zuwan su kuma ai yi ta gaishe su cikin girmamawa.
Ba wani abu ne yasa ake mamakin ganin su a wannan waje domin tun da aka gina wajen tsawon shekaru arba'in baya ba su taɓa kawo ziyara ba sai yau.
Shi kansa sarki Amzadu bai taɓa shigowa wajen ba.
Mozur na kishingiɗe yana tsakiyar tunanin gimbiya Laslaiya sai yaji an buɗe ƙofa an shigo.
A firgice ya ɗago kai ya dubi bakin ƙofar, domin a saninsa kullum sau ɗaya tak ake buɗe ƙofar a miƙo masa abinci kuma saida yamma gefen magriba ba kamar yanzu ba da hantsi.
Kwatsam,sai ga gimbiya Laslaiya,Zulaisha da sarkin gida Azmandu sun shigo.
Ba tare da ɓata lokaci ba Azmandu ya gabatar da Zalisha a wajen Mozur.
Sannan yace,
"Wannan kuwa gimbiya Laslaiya ce wadda na san ka ganta a yau wajen gasar kokawa."
Mozur ya risina ya kwashi gaisuwa a gare su.
Zalisha ta ƙarewa Mozur kallo sai ta ji ya kwanta mata a zuciya.Cikin murmushi ta dube shi tace,
"Ya kai wannan jarumi ka yi sani cewa na rako 'ya ta ne Laslaiya domin ta gana da kai,don haka yanzu zamu baku dama ku zanta."
Tana gama faɗin haka ta juya ta yiwa Azmandu inkiyar su fita.
Bada gardama ba Azmandu ya wuce gaba ta bi bayansa.
Sai da suka je bakin ƙofar ɗakin.
Sannan Zalisha ta waigo tace da Laslaiya,
"Karki daɗe sosai, domin mahaifin ki zai iya neman ki."
Laslaiya tayi murmushi tace,"ba zan daɗe ba."
Bayan fitar Zalisha da Azmandu sai Laslaiya da Mozur suka dubi juna suna murmushi aka rasa wanda zai ce ƙala har kunya ta kama Laslaiya ta kau da kai ga barin kallon sa.
Sannan tace,
"Daman can kai ɗan kokawa ne?"
Mozur yace,"A'a,amma na taɓa shiga gasar kokawa sau ɗaya sa'adda nake can birnin Shauƙib a daular Larabawa."
"Ina ne asalin garin ku?"
Laslaiya ta sake tambaya.
Mozur yace,
"A gaskiya ban sani ba,ni dai kawai na taso na tsinci kaina a birnin Shauƙib a hannun wani attajiri wai shi Abulkhairi.
A lokacin ban fi shekara bakwai ba,tun a sannan nake yi masa aikin bauta.
Wata rana sai sarki Miƙdad ya kawo masa ziyarar bazato koda ya ganni sai yaji yana sona don haka sai ya siye ni da tsada,kimanin dirhami dubu ɗari uku ya tafi da ni gidansa.
Daga wannan rana ya cigaba da kula da ni ya zamana kullum ni ke kula da turakarsa na shareta na tsaftace ta har dai ya aminta dani nake dafa masa shayi.
Kai har ta kai cewa abinci ma ni ke dafa masa kuma ni kaɗai ne zan ba shi abu yaci ko ya sha.
Hatta matarsa gimbiya Suhaila bai sakar mata al'amuran sa ba kamar yadda ya sakar mini.
Sai da ta kai ta kawo cewa babu wani sirri na sa da ban sani ba.
Wannan shine iyakar labarin asali na wanda zan iya baki."
Laslaiya tace,
"To yaya aka yi kuma aka siyo ka a matsayin bawa har aka kawo ka wannan nahiyar tamu ta baƙaƙen fata alhalin tafiya ce mai tsawo?"
Koda jin wannan tambaya sai jarumi Mozur yayi ajiyar zuciya yace,
"Ya shugabata kiyi sani cewa amsar wannan tambaya taki daidai yake da na baki gaba ɗayan tarihin rayuwa ta.
Idan kuwa nace zan baki wannan labari sai mu kwana anan ban gama ba."
Laslaiya tayi murmushi tace,
"Ai kuwa ko ba yau ba sai naji wannan labari daga bakin ka.
Ya kai wannan jarumi kayi sani cewa a iya rayuwa ta ban taɓa ganin mutumin dana ji ya burgeni ba face kai.
Ka sani cewa tun rabuwa ta da kai ɗazu a filin gasa na kasa samun sukuni, domin zuciya ta ta cika maƙil da begen ka,idanu na kuwa suka cika maƙil da hawayen rashin ganin ka.
Gaba jikina ya kama karkarwa saboda rashin jinka a kusa.
Ina mai sanar da kai cewa a halin yanzu ina ji a cikin raina cewa ba zan iya yin rayuwa ba muddin babu kai.
Lallai kaine zaka zamo abokin rayuwa ta.
Shin zaka iya gaya mini yadda kake ji a zuciyar ka dangane da ni?"
Yayin da gimbiya Laslaiya tazo nan a zancenta sai mamaki ya ƙara turnuƙe jarumi Mozur kuma hankalin sa ya dugunzuma domin ya san cewa Laslaiya ta naɗa gammo don ɗaukar dutsen da yafi kowane dutse girma a duniya,haka kuma tana shirin jefa rayuwar sa ne a cikin bala'in da bai taɓa shiga ba,don sai ya gwammace mutuwa da rayuwar sa.
Cikin alamun karayar zuciya Mozur ya dubi gimbiya Laslaiya yace,
"Yake wannan 'yar sarki kiyi sani cewa wutsiyar raƙumi tayi nesa da ƙasa,don haka tafi ƙarfin taɓawar yaro.
Ina bawa ina 'yar sarki?
Haƙiƙa nima na kasance a cikin irin halin da kika tsinci kanki na yawan tunani da bege to amma fa dole ne mu haƙura da juna in ba haka ba kuwa zamu jefa kanmu cikin rayuwar ƙunci,wataƙila ma ta zama sanadin nadama ga ɗaya daga cikin mu."
Koda jin wannan batu sai hawaye ya zubowa gimbiya Laslaiya tace,
"Ya kai Mozur kayi sani cewa in dai a kanka ne ba zan taɓa yin nadama ba koda kuwa zan rasa rayuwa ta.
Kayi sani cewa daga yau na ɗaura ɗamarar yaƙi da duk wanda ke son rabani da kai.
Idan har kana sona da gaskiya kaima ka ɗora taka ɗamarar.
Na barka lafiya sai nazo ganin ka a karo na biyu."
Laslaiya na gama faɗin haka ta juya ta fita ta bar Mozur a tsaye ƙiƙam kawai sai ya bita da kallo cikin tsananin damuwa zuciyarsa cike da fargaba.
****************************

Sa'adda Zalisha da Laslaiya suka koma gida suna shiga cikin turakar Laslaiya suka tsaya cak a razane sakamakon ganin sarki Amzadu zaune a bisa gado ya ɗora ƙafarsa ɗaya akan ɗaya fuskarsa a murtuke babu alamar annuri.
Zalisha da Laslaiya suka yi ƙerere ido ya raina fata.
Sarki Amzadu ya dubi Zalisha yace,
"Amma dai kin bani kunya.
Ban taɓa zaton cewa tunani da hankalin uwa zai zo ɗaya dana 'ya ba.
Ya kamata ace kin fita basira da hango abin da ita ba zata iya hangowa ba.
Ya za'a yi ace a matsayina na sarki mai daraja da ɗaukaka 'ya ta tace tana son bawa.
Bawan ma baƙo,kuma maƙasƙanci mai aikin niƙan abincin mu.
Haba!!
Haba 'yata ki tuna cewa 'ya'yan sarakai kyawawa sun zo sun biɗi auren ki,amma duk kin ƙi su.
Saboda son da nake miki ne na ƙyale ki da zaɓin zuciyarki kuma yanzu saiki rasa wanda zaki zaɓa sai maƙasƙancin bawa.
Na rantse da darajar abin bauta babbar wuta saina datse wannan soyayya dake tsakaninki da bawa Mozur ta kowanne hali."
Koda sarki Amzadu yazo nan a zancen sa sai gimbiya Laslaiya ta fashe da kuka.
Ita kuwa Zalisha sai ta matsa gabansa cikin ɓacin rai ta dube shi tace,
"Ya kai mijina yanzu kenan ka zaɓi kare martabar Mulkin ka fiye da farin cikin 'yarka guda ɗaya kacal a duniya?"
Cikin fushi Amzadu ya miƙe tsaye yace,
"Ƙwarai kuwa,daga yau ku sani cewa ina kishin daraja da darajar mulkina fiye da yadda nake kishin ku."
Yana gama faɗin haka ya nufi ƙofar fita daga ɗakin.
Har yasa ƙafarsa ɗaya waje sai ya waigo ya dubi Laslaiya yace,
"Zan sa kyawawan matakan tsaro akan ki don kada kije inda Mozur yake idan kuwa kika matsa har kuka sadu saina kashe shi."
Amzadu ya juya ya fice daga ɗakin.
Yana fita Laslaiya ta ruga ga Zalisha ta rungume ta tana kuka,ita kuma ta shiga rarrashin ta.
A wannan rana dai yadda Laslaiya taga rana haka taga dare, domin kwana tayi tana kuka.
Sai da ya zamana kullum bata da aikin yi face zama da tunanin jarumi Mozur.
Abinci kuwa sai Zalisha tayi matuƙar takura mata sannan take cin ƙanƙani.
Koda ta sami kwana bakwai a cikin wannan hali sai ta rame ta fita hayyacin ta.
Al'amarin da ya dugunzuma hankalin Zalisha kenan ta kirawo sarki Amzadu don yaga halin da Laslaiya ta shiga.
Yayin da sarki Amzadu yaga yadda Laslaiya ta zamo wato a rame,kuma a firgice.
Sai ya ƙyaƙyale da dariya.
Sannan ya dubi Laslaiya yace,
"Yake 'yata kiyi sani cewa ko zaki zamo ƙwarangol ba zan amince kiyi soyayya da bawa Mozur ba bare har kuyi aure."
Sa'adda Laslaiya taji wannan batu sai tayi murmushi tace,
"Ya kai Abba na kayi sani cewa bana fatan ka tausaya mini bisa duk irin halin da zan shiga,amma ina da burin ka sanya ni cikin kabarina da hannun ka idan ciwon son Mozur ya zamo ajali na."
Koda jin wannan batu sai sarki Amzadu yayi shiru ya kasa cewa komai.
Cikin sanyin jiki ya nufi ƙofar fita daga ɗakin.
Zalisha ta ruga da gudu ta sha gabansa tana mai fashewa da kuka tace,
"Ya kai mijina kayi tunani mai kyau bisa wannan al'amari.
Ya kamata ka hanzarta ceto rayuwar wannan 'ya tamu guda ɗaya kacal a duniya tun gabanin lokacin nadama bai zo ba."
Maimakon sarki Amzadu yace wani abu sai ya hankaɗe Zalisha ta faɗi ƙasa.
Nan yasa ƙafa ya shallake ta ya tafi abinsa.
Zalisha da Laslaiya suka ƙara fashewa da kuka a tare lokaci ɗaya.
Daga wannan rana al'amura suka ƙara dagulewa har ta kai cewa Laslaiya ta kwanta cuta aka yi ta magani amma a banza.
Shi kuwa sarki Amzadu wannan al'amari na ta nuƙurƙusar zuciyarsa amma ya rasa hanyar da zaibi ya magance matsalar domin ko zai mutu ba zai iya bari Laslaiya ta auri bawa Mozur ba.
Al'amarin jarumi Mozur kuwa shima duk ya rame ya ƙara baƙi,kuma ya tara gashi a fuskar sa saboda baƙin cikin rashin ganin Laslaiya da kuma yawan tunanin ta.
A koda yaushe a cikin tunaninta yake dare da rana koda kuwa yana kan aiki ne.
Sau tari sai ayi tayi masa magana amma baya jin mai maganar face an taɓa jikinsa saboda tsananin tunani.
Duk wanda ya dubi jarumi Mozur a wannan lokaci dole ne yaji tausayinsa.
Babu abinda yake ƙara ɗaga masa hankali face jin labarin irin halin da gimbiya Laslaiya ke ciki na rashin lafiya duk saboda shi.
Ba wani ne ke kawo masa wannan labari ba face Zalisha da kanta.
Bisa wannan dalili ne Mozur ya fara tunanin hanyar da zaibi ya gudu daga cikin wannan gida inda aka tsare shi,amma sai yaga cewa babu dama domin akwai cikakken tsaro.
Babu yadda za'a yi ya wuce ta ƙofofin nan guda goma sha biyu waɗanda ke ɗauke da zaratan dakaru sha bibbiyu dukkanin su na riƙe da muggan makamai.
Haka dai Mozur ya cigaba da zama a cikin ƙunci har ya rage saura kwana goma ranar gasar kokawa ta kewayo.
Koda sarki ya fuskanci kusantowar ranar sai ya kira Azmandu yace da shi,
"Ya kai sarkin gida kayi sani cewa ba zan hana wannan taro ba na gasar kokawa kuma bazan hana ka zuwa da bawa Mozur ba, domin idan nayi hakan duniya zata zage ni bisa abinda aka saba yi na al'ada a ƙasa ta.
Na yarda ka fito da Mozur ranar wannan gasa,amma sai na zuba masa dakaru dubu arba'in masu tsaronsa don kada ya gudu.
Kuma a ɗaure za'a zo da shi cikin sarƙoƙi a hannayen sa da ƙafafuwan sa da kuma wuyansa.
Ba za'a kwance shi ba face zai kafsa da abokin gwaminsa.
Yana gama kafsawar sai a ɗaure shi.

MU HADU A PART G DON JIN CIGABAN WANNAN HIKAYAR TA MOZUR✍️✍️😁😁👌**MIFTAHUZZARBIL**
LITTAFI NA BIYU ✍️✍️
PART G ❤❤💯
NA ABDUL'AZIZ SANI MADAKIN GINI 🧝‍♀️🧝‍♀️
TYPING AHMAD MUNNIR..
POSTING NAJIBULLAH MUHAMMAD 🥰🙏

Marubucin ya CI GABA DA CEWA..

Kuma a ɗaure za'a zo da shi cikin sarƙoƙi a hannayen sa da ƙafafuwan sa da kuma wuyansa.
Ba za'a kwance shi ba face zai kafsa da abokin gwaminsa.
Yana gama kafsawar sai a ɗaure shi.
Ba za'a gushe ana yin hakan ba har sai an kammala wannan gasa.
Ka sani cewa wannan karon gimbiya bata da lafiya tana kwance,don haka nine zan wakilce ta wajen bayar da kyauta ga wanda yaci gasar."
Koda sarki Amzadu yazo nan a zancen sa sai Azmandu ya sunkui da kansa a ƙas yace,
"Ya shugabana kayi sani cewa duk yadda kake son a tsara wannan al'amari haka za'a yi."
Sarki Amzadu ya bushe da dariya harda doka ƙafa.
Sannan ya kira sarkin yaƙinsa sadauki Akurga yace da shi,
"Na umarce ka daka shirya dakaru dubu arba'in waɗanda za suyi wa Mozur rakiya daga cikin gidan nuƙan abinci zuwa filin gasa don kada ya sami ƙofar guduwa."
Akurga ya rusuna yace,
"An gama ya mai duniya."
Nan take sarki Amzadu ya miƙe ya shiga gida,fada ta watse kowa ya kama gabansa.
Da ranar gasa tazo sai filin fada ya cika maƙil da jama'a ko'ina ka duba kawunan mutane ne birjik ba adadi.
Wannan karon dai jaruman kokawar basu da yawa,ba sufi su ashirin ba kuma akwai jarumi Zarto a cikin su.
Ga wanda baisan Zarto ba in ya ganshi a wannan lokaci ba zai gane shi ba saboda ya ƙara girma fiye da wancan karo da aka yi gasar har jarumi Mozur ya cinye shi.
Akwai alamun cewa wannan karon Zarto ya dawo da cikakken shirin,don ya karɓi kambun gasar daga hannun Mozur.
Har sarki Amzadu ya fito daga cikin gida ya zauna akan karaga don kallon wannan gasa ba'a kawo jarumi Mozur ba.
Wannan tasa jikin mutane yayi sanyi ya zamana ba'a wata hayaniya a filin gasar da kambama jarumai domin kowa so yake kawai yaga hallarar jarumi Mozur musamman masu goyon bayan jarumi Zarto saboda sun ci burin cewa wannan karon suke da nasara.
Har an kirawo jaruman farko sun hau tudun faɗan za su fara kafsawa sai aka hango dakaru dubu arba'in sun sako jarumi Mozur a tsakiya yana tafe yana jan sarƙa wacce ta ɗaure hannayen sa da ƙafafuwan sa kuma ta zarge wuyansa.
Duk da cewar fuskar Mozur ta cika da gashi kuma ya rame sai da masoyansa suka shaida shi.
Nan da nan filin ya kaure da shewa aka rinƙa ambaton sunansa ana cewa,
"Mozur!
Mozur!!
Mozur!!!"
Sautin wannan kiran suna ne yabi iska ya riski dodon kunnen gimbiya Laslaiya wacce ke kwance akan gado magashiyan tana jinya a cikin gidan sarautar.
Rabonta da miqewa zaune kwana ashirin da bakwai kenan.
Koda taji ambaton wannan suna na masoyinta sai ta miƙe zumbur ta fara waige-waige domin a tsammanin ta yana kusa ne.
Laslaiya ta dubi gabas da yamma,kudu da arewa ba taga kowa ba a cikin ɗakin data ke wannan jinya ba face wata baiwa guda ɗaya wadda ke kula da ita.
Ita ma kuma ta kishingiɗa a jikin bango barci ya kwashe ta,wataƙila saboda gajiyar aiki ne.
Gaba ɗaya gidan sarautar yayi shiru kamar babu mutane.
Sautin nan na kiran sunan Mozur ya cigaba da yawo a kunnen Laslaiya.
Nan take ta tuno cewar ai yau ne ranar zagayowar gasar jarumai.
Kawai sai Laslaiya ta ruga da gudu ta nufi hanyar fita daga cikin gidan sarautar.
A wannan lokaci wata doguwar farar rigace kawai a jikin ta mai shara-shara wadda ke nuna duk ilahirin surar jikinta babu takalmi a ƙafarta kuma babu wani ado a tare da ita.
Tana gudu gashin kanta na tarwatsewa a cikin iska.
Haka dai tayi ta gudun tana wuce tsirarun bayi da dakarun gidan masu hidima, kuma duk suka kasa ganewa cewa gimbiya Laslaiya ce a cikin wannan hali, saboda an san cewa ita kwance take cikin matsananciyar rashin lafiya.
A can filin gasa kuwa koda sarki yaga an zo da jarumi Mozur sai yace a janye kafsawar waɗannan jarumai na farko da suka hau kan tudu don buɗe taron a fara da karon jarumi Zarto da jarumi Mozur.
Koda jin haka sai jama'a suka sake ruɗewa da ihu da shewa domin dama kowa ya ɗagu saboda yaga yadda za'a yi wannan mugun karo ya zo.
Ba tare da ɓata lokaci ba aka kwance jarumi Mozur daga cikin sarƙa aka rako shi har bakin wannan gini mai tudu na gasa.
Mozur ya taka matattakala ya hau kan tudun.
Sannan jarumi Zarto ya hawo suka fuskanci juna aka fara kallan-kallo.
Nan da jama'a suka ƙara kaurewa da shewa.
Ko shakka babu ya karaya da wannan karo da zai yi da jarumi Zarto domin yasan cewa akwai yunwa a jikin sa da kuma ƙarancin lafiya.
Sai dai duk da haka masoyansa na ɗan ƙara masa ƙwarin gwiwa, saboda ganin yadda suke masa jinjina.
Ba tare da ɓata wani lokaci ba aka buga gangar fara gasa.
Yin hakan ke da wuya Zarto ya juya ya dubi sarki Amzadu yayi sujjada a gare shi yana mai kwasar gaisuwa.
Sarki Amzadu ya duƙar da kansa ƙasa kaɗan alamar ya karɓi gaisuwar.
Sannan ya nuna masa inkiyar ya kashe jarumi Mozur murus har lahira ta hanyar nuna kaifin hannu a wuya.
Zarto ya jinjina kai gami da murmushi alamar cewa ya fahimci buƙatar sarki.
Cikin zafin nama ya ruga ga Mozur.
Kafin Mozur yayi wani yunƙuri tuni Zarto ya matse shi da hannu biyu a gadon bayansa.
Mozur ya fara ihu saboda tsananin zafi da zugi tamkar ƙasusuwan bayansa zasu kakkarye.
Nan fa Mozur ya cigaba da ƙoƙarin ya cire hannayen Zarto daga ruƙon da yayi masa amma ya kasa.
Mozur ya yiwa Zarto karo da ka a fuska har sau huɗu,amma a banza,baiji komai ba bare ya sake shi.
Nan fa Mozur ya cigaba da rusa ihu saboda azabar da yake ji a bayansa.
Shi kuwa Zarto sai ƙara taƙarƙarewa iya ƙarfin sa kuma yana bushewa da dariya.
Saida kusan rabin sa'a ta shuɗe a haka Mozur bai fasa ihu ba shi kuma Zarto yaƙi ya sake shi.
A wannan rana dai Mozur yaci baƙar wahala tamkar zai mutu.
Da ƙyar ya samu ya ware 'yan yatsun hannunsa ya luma su cikin ƙwayar idanun Zarto.
Zarto yayi ihu ya saki Mozur saboda raɗaɗin da yaji a cikin idanun nasa.
Mozur ya tafi taga taga zai faɗi amma sai ya daure ya tsaya da ƙafafunsa.
Koda ganin haka sai masoyansa suka kaure da shewa aka hau yi masa tafi.
A lokacin ne Zarto ya dawo cikin hayyacinsa idanunsa suka buɗe.
Cikin tsananin fusata da shammata ya sake rugawa ya shaƙo wuyan Mozur shaƙa bata wasa ba.
Nan take idanun Mozur suka zazzaro kamar zasu faɗo ƙasa ya fara wutsil-wutsil da ƙafafuwan sa da kuma hannayen sa.
Tun yana motsa su da ƙarfi ya fara ɗaga su da ƙyar wata irin kumfar wuya da majinar wahala suka fara dalala.
Nan take gana ɗaya jikin masoyan jarumi Mozur yayi sanyi,wasu ma suka fara kuka don gani suke tabbas mutuwa zai yi.

**************
Sarki Amzadu kuwa banda ƙyaƙyata dariya babu abinda yake yi.
A daidai wannan lokaci ne gimbiya Laslaiya ta iso filin gasar cikin matsiyacin gudu.
Koda tayi arba da jarumi Mozur a hannun Zarto taga halin da ya shiga sai ta kwarara ihu tana mai kiran sunan Mozur.
Cikin shiɗewa Mozur ya jiyo wannan kira kuma ya shaida muryar mai kiran.
Ba zato ba tsammani,sai aka ji Mozur ya kwarara uban ihu shima yana mai kiran sunan Laslaiya.
Nan take ya ɓanɓare hannayen jarumi Zarto daga wuyansa da ƙarfin tsiya.
Sannan ya ɗaga shi sama ya dinga wulwula shi kamar yana wasa da majajjawa.
Lokaci guda kuma ya damfara shi da ƙasa.
Bisa tsautsayi sai Zarto ya cake da ka.
Take wuyansa ya karye ya mutu,ko shurawa bai yi ba.
Faruwar hakan ke da wuya gimbiya Laslaiya ta ruga da gudu ta hau kan matattakala ta isa kan tudun da Mozur ke tsaye.
Da zuwa ta faɗa kan ƙirjinsa suka rungume juna cikin tsananin farin ciki.
Sarki Amzadu ya miƙe zumbur a fusace yana mai bawa dakaru umarnin su hallaka jarumi Mozur.
Kafin dakarun suyi wani yunƙuri sai aka hango ƙura ta turnuƙe gabas.
Nan fa kallo ya koma gabas ɗin kowa ya tsaya ƙyam.
Kawai sai aka ga ashe wasu dubunnan mayaƙa ne a sukwane bisa dawakai suka kawo farmakin sumame.
Nan fa gari ya ruɗe,waje ya hargitse akayi ta gujeguje da iface-iface.
Shi kansa sarki Amzadu da rarrafe ya samu ya ruga ya kama doki ya hau.
Sannan ya sukwani dokin a guje izuwa cikin gidan sarautar baima kula da batun 'yarsa ba, gimbiya Laslaiya.
Su kuwa dakarun nan guda dubu arba'in waɗanda aka sasu tsaron jarumi Mozur sai suka riga suka tari waɗannan baƙin mayaƙan sumame aka fara kafsa yaƙi.
Koda jarumi Mozur yaga yadda waje ya hargitse sai ya ɗauki gimbiya a hannunsa ya ruga da ita zuwa inda wani farin doki ke ɗaure.
Koda ya iske dokin sai ya ɗora gimbiya akai.
Sannan shima yayi tsalle ya haye kan dokin ya fincike igiyar aka.
Sannan shima yayi tsalle ya haye kan dokin ya fincike igiyar da ta ɗaure ƙafar dokin da ƙarfin tsiya har turken da aka ɗaure igiyar a jiki ya tumɓuko daga cikin ƙasa.
Mozur ya zunguri dokin da ƙafafunsa ya sukwane shi a guje.
Maimakon subi hanyar cikin gari sai suka kewaye ta bayan dakarun dake gabza yaƙi da mayaƙan sumame suka nausa cikin daji suka yi ta gudu ba ƙaƙƙautawa.
Al'amarin sarki Amzadu kuwa lokacin da suka isa fada shi da fadawansa cikin gudu sai suka tsaya aka fara shirye-shiryen yaƙi,don akwai waɗancan dakaru dubu arba'in na ɗaukin gaggawa, domin kuwa mayaƙan sumamen na da matuƙar yawa fiye da ƙima.
Nan da nan aka shirya dakaru masu yawa aka yi hawa har da shi kansa sarki Amzadu inda ya bayar da umarnin cewa lallai a nemo jarumi Mozur da gimbiya Laslaiya a duk inda suke kuma a ƙarar da waɗannan abokan gaba da suka kawo farmakin sumame.
Nan take sarkin yaƙi ya jagoranci dubunnan ɗaruruwan mayaƙan garin suka sukwani dawakai cikin matsanancin gudu suka nufi ƙofar filin fada inda ake yaƙi.
Idan mutum yaga wannan zuga a wannan lokaci sai yayi zaton mayaƙan duniya ne kaf suka fito yaƙi.
Ƙarar kofaton dawakai ma kaɗai ya isa ya firgita mutum bare kuma ihun mayaƙan da kuma ƙarajin su wanda ya cika garin gaba ɗaya ya firgita ƙananan yara da mata suka kama koke-koke.
Tsofaffi kuwa suka tsure da gudawa.😅😅
Lokacin da mayaƙan kawo ɗauki suka iso filin yaƙin sai suka iske an yiwa 'yan uwansu lugude an karkashe su saura ƙalilan.
Nan fa aka sake kaurewa da sabon yaƙi.
Karafkiyar ƙarafa ta yawaita.
Jini ya ringa fallatsa yana malala a ƙas.
Nan fa kasuwar ɗaukar rayuka ta kama ci.
Masu ƙarfi da jarumta suka rinƙa ciniki ba sassautawa.
Jarumi Mozur da gimbiya Laslaiya kuwa saida suka kwana suka yini suna tafiya akan dokin nan tana kwance akan ƙirjinsa basu tsaya ba saboda gudun kada a biyo bayansu a cim masu.
Saida suka iso wani ƙaramin gari dake cikin nahiyar ƙasar.
Sannan suka tsaya gaban wata rijiya suka sauka.
Anan ne suka sha ruwa,suka zauna suna kallon juna.
Koda suka ga yadda kowannensu ya rame sakamakon ƙuncin rashin ganin juna sai suka fashe da kuka.
Gimbiya Laslaiya ta rungume Mozur tace,
"Ya kai masoyi na haƙiƙa na san mun shiga cikin mugun ƙunci da azabar cutar bege.
Amma yanzu ina jin farin ciki tamkar ban taɓa shiga damuwa ba, saboda kasancewa tare da kai a yanzu.
Lallai kuwa ba zan sake yarda wani abu ya raba mu ba face mutuwa."
Jarumi Mozur ya janye jikinsa daga cikin nata suka fuskanci juna.
Sannan yace,
"Ya ke abar begena dare da rana kiyi sani cewa zuciya ta da raina sun kori komai daga cikin su.
Ba za su bar abin da ya kai ƙwayar zarra ba face ke.
Ina tabbatar miki da cewa ji da gani na , tafiya da kwanciya ta begenki ne ke musu jagora dare da rana.
Nayi miki alƙawari daga yau ko ruwa ko iska ko wuta ko guguwa,komai yawan bala'i da masifa ba zan yarda mu rabu ba face babu ruhin numfashi a cikin gangar jikina."
Koda jin wannan batu sai farin ciki da daɗi suka lulluɓe gimbiya Laslaiya ta sake rungume Mozur.
***
Koda sarki Muhucul yazo nan a labarin sa sai yayi shiru ya dubi su Ruziyal yace,
"To lokaci yayi halinsa,anan zan dakata sai gobe kuma idan muna raye ku dawo na cigaba da wannan labari."
Yana gama faɗin haka ya miƙe ya shiga gida,fada ta watse kowa ya kama gabansa aka bar su Ruziyal a zaune cikin matuƙar damuwar rashin jin ƙarshen wannan labari.
*******
Al'amarin su aljani Markahus sabus kuwa bayan sun sami nasarar ɗebo narkakken dutse daga cikin dutsen da yafi kowane dutse girma,sai aljani Durmazalu ya cigaba da tafiya da su a cikin sararin samaniya.
Sai da suka yi tafiyar sa'a bakwai cif.
Sannan suka sauko ƙasa suka dira akan wani ƙaramin tsuburi.
Saukar su ke da wuya aljani Durmazalu yayi gyaran murya yace,
"Ya ku abokan tafiya ina kira a gare ku da kowa ya shirya, domin yanzu ne zamu yi tafiya mai haɗarin gaske fiye da wadda kuka gani a baya.
Kuyi sani cewa yanzu ne zamu shiga cikin ƙarƙashin ƙasa don mu isa duniyar ƙarshe mu ɗebo dutsen wuta.
Ina sanar da ku cewa ita dai wannan duniya ta ƙarshe itace ta bakwai kuma kafin mu risketa sai mun ratsa ta cikin duniyoyi shida a cikin kowacce duniya akwai irin halittun da ke cikin ta,kuma duk sun kasance masu ƙarfin mulki da ƙarfin sihiri.
Bai zamo lallai ba mu wuce ta cikin waɗannan duniyoyi shida lafiya.
Babu mamaki wasun mu su hallaka ko kuma mu duka mu halaka.
Saboda bala'in dake tattare da waɗannan halittu na duniyoyin ƙassai.
Ina mai shawartar mu damu jajirce,musa a ranmu cewa muna tare da nasara in kuwa zuciyoyinmu suka karaya ba zamu taɓa samun dacewa ba."
Koda aljani Durmazalu yazo nan a zancen sa sai markahus sabus,boka jinshan,durfus,boka sulbaini da yarinyar nan ta birnin duwatsu wato salusa suka yi tsuru-tsuru da idanu,tsoro ya baibaye su kuma hankalin su ya dugunzuma don basu san irin bala'in da zasu riska ba a cikin duniyoyin ƙassai.
Ba tare da ɓata lokaci ba Durmazalu ya nutse cikin ƙarƙashin ƙasa ɗauke da su markahus sabus,yayi ta tafiya.
Saida suka yi tafiyar kwana uku.
Sannan suka iso duniya ta ɗaya wadda ake kira Madinatul Aslik.
Koda bayyanar su a cikin wannan duniya sai duk suka zama ƙauyawa suka kama kalle-kalle suna masu mamakin irin gine-ginen birnin da suka tsinci kansu a ciki da kuma irin halittun dake rayuwa a cikin sa.
Shi dai wannan birni na Madinatul Aslik an gina gidaje a cikin sa da zallan darma.
Ko ina ka duba a garin babu ƙasa saidai ka taka shimfiɗaɗɗiyar darma mai kama da tabarma, domin za'a iya naɗeta.
Babu wani wuri wanda za'a iya yin shuka bare tsuro ya fito.
Su kuwa halittun sun kasance 'yan wadanni dugul-dugul babu wanda tsawonsa ya wuce kamu ɗaya,kuma sun kasance'yan ƙanana sirara,shafal-shafal basu da nauyi.
Babu abin mamaki face yadda suke iya ɗaukan gunguma-gunguman ƙarafa.
Wani ƙarfen ma ko markahus sabus bai isa ya iya raba shi da ƙasa ba,bare su boka jinshan 'yan ƙananan alhaki.
Fuskokin waɗannan halittu irin na mutane ne haka ma hannayen su da ƙafafuwan su,amma kuma wani irin dogon baki ne da su,wanda daga ƙarshen sa yayi doro da tsini,kamar bakin aku,kuma ƙwari ne da shi kamar ƙarfe,duk abinda suka caka da shi take abin zai huje ya burma koda kuwa dutse ne.
Gaba ɗaya ƙarfin waɗannan halittu a jikin bakin na su yake, domin ƙarafan ma da suke ɗauka masu nauyi da bakin na su suke ɗauka.
Basu da abin hawa kamar dawakai,ko jakai,amma suna yawo ne akan wasu irin manyan jemagu masu siffar ban tsoro.
Koda ganin dirar aljani Durmazalu a cikin wannan birni ɗauke dasu markahus sabus sai mutanen garin suka tsaya cak suka daina komai suka zuba musu na mujiya.
Su kuwa sai suka cigaba da tafiya bisa ƙafafunsu.
Su shiga nan su fita can.
Su dai ba su yiwa kowa magana ba, kuma babu wanda yayi musu magana.
Duk ta inda suka ratsa sai a tsai da harkoki ayi ta kallon su.
Haƙiƙa su markahus sabus sun ga abubuwan al'ajabi a cikin wannan duniya fiye da sauran abubuwan da suka gani a baya tun farkon shigowar su cikin wannan aiki na nemo abubuwa uku don ƙera kubar MIFTAHUL ZARBIL.
Babu abinda yafi basu mamaki face wata siririyar kwalba wacce mutanen wannan birni suka ajiye ta a tsakiyar birnin.
Saboda tsananin tsawon kwalbar sai kaga kamar zata tokare da hadarin sama.
Idan kuwa mutum yace saiya kewaye kwalbar to tabbas sai ya kwana arba'in yana zagaya ta bai dawo kan inda ya fara ba.
Ita dai wannan kwalba a cike take da ruwa,kuma anyi wani famfo a jikin ta wanda ke zubar da ruwa.
Kowa saika ga yazo ya tari ruwan yayi gaba don amfanin kansa.
A lokaci guda sai mutum dubu su zo su ɗiba suyi gaba,amma ruwan baya ƙarewa duk da cewar girman kwalbar baikai na mutum ɗaya ba,kawai dai tsawo gareta.
Markahus sabus ya dubi kwalbar da kyau yace,
"Jau wanda bai yawo ba a duniya bai more kallo ba.
Kun ga inda labari aka bamu aka ce akwai wannan kwalbar ba zamu yarda ba,amma tunda da idanun mu muka gani dole mu gasgata."
Kafin wani daga cikin su boka jinshan yace wani abu sai suka ga anyi musu ƙwawanya.
Wasu mutanen garin ne cikin shigar mayaƙa kimanin su dubu bisa jemagun nan.
Ko sillan kara babu a hannunsu,amma kuma bakunan su sun fi na sauran mutanen garin tsawo da faɗi.
Kafin su aljani Durmazalu suyi wani yunƙuri tuni an cafkosu da bakuna ɗaiɗai an ɗora su akan jemagun an cilla da su da gudu a cikin sararin samaniya ba tare da ɗayansu ya iya ƙoƙarin gudu ba.
********************

Aljani Durmazalu ya dubi girman halittar jikinsa mai ɗauke da fukafukai miliyan ɗaya yaga cewa girman sa bai amfane shi da komai ba,tunda ga ƙananan halittu sun kama shi tamau a hannu ya kasa motsi.
Kawai sai ya fashe da kukan takaici.
Markahus sabus ya dube shi ya ƙyaƙyale da dariya yace,
"Yau fa ake yinta ga zaki a hannun kyanwa,harma kyanwar ta sashi kuka.
Ashe dai ba girma ne ƙarfi ba.
Daga yau kuma babu batun kuri ko cika baki, domin baba ma da babansa."😅😅😅
Durmazalu ya dubi markahus sabus ya daka masa harara.
Sannan yace,
"To ƙaramin mara kunya ai dama ni banyi kuri ba tunda farko, domin saida na gaya maku cewa komai zai iya faruwa ga dukkanin mu ban ware kaina ba nayi kuri."
Haka dai aka cigaba da tafiya da su har izuwa wani lokaci mai tsawo.
Sannan aka iso wani babban gida wanda babu mai girmansa a duk faɗin birnin.
Gidan ya kasance an gina shine da farar darma.
Duk iya yawon markahus sabus a duniya bai taɓa ganin gida mai girman wannan ba.
Koda aka shigar da su cikin gidan kuwa sai gashi ana ratsawa da su ta cikin waɗansu ƙayatattun fadoji na alfarma.

Mu HADU a part H DON JIN CIGABAN WANNAN KASAITACCEN LITTAFIN
NAJIBULLAH MUHAMMAD🥰**MIFTAHUZZARBIL**
LITTAFI NA BIYU 🤝😍
PART H 😊
NA ABDUL'AZIZ SANI MADAKIN GINI 😎
TYPING AHMAD MUNNIR🤝
POSTING NAJIBULLAH MUHAMMAD 💪

Note: kuyi hakuri akan rashin isasshen posting akan lokaci. Kuyi sani cewa hakan ya faru ne sakamakon yanayin rayuwar da ya, Wanda ku kanku kunsan halin da ake ciki.
Don haka ku rinka yi mana uzuri.
A koyaushe muna fatan Allah ya taimakemu tare da fatan Allah ya tattara mu a cikin gidan Aljannar Firdausi Nuzila🤝😍🩷🙏

MARUBUCIN YACI GABA DA CEWA...

Duk iya yawon markahus sabus a duniya bai taɓa ganin gida mai girman wannan ba.
Koda aka shigar da su cikin gidan kuwa sai gashi ana ratsawa da su ta cikin waɗansu ƙayatattun fadoji na alfarma.
Kowace fada guda ɗaya ta ninka fadar nan ta Baharzus sau uku a girma,kyau da ƙayatuwa.
Saida aka wuce fadoji shida sannan aka tsaya da su a ta bakwai.
Ita dai wannan fada ta bakwai ta kasance uwa ga sauran fadoji shida na baya,kuma duk abinda ke cikin ta fari ne sol babu baƙi ko wata kalar dabam.
Abubuwan al'ajabi kuwa gasunan birjik ba adadi, domin anan ne suka ga kifaye na yawo a fili ba a cikin ruwa ba,haka kuma suka ga mutum mai rabin jikin zaki.
Wato kansa da hannayen sa ne na mutum,amma daga cibiyar sa zuwa gangar jikinsa da ƙafafuwan sa duk na zaki ne,haka ma ƙirjinsa irin na zaki ne wanda ke cike da gashi.
Wannan mutum na kishingiɗe bisa wata doguwar kujera ta alfarma ya riƙe wani babban tambulan cike da ruwan inibi yana sha,kuma yana karkaɗa jelarsa alamar yana jin daɗin ɗanɗanon ruwan inibin a bakinsa.
Koda aka shigo dasu markahus sabus cikin wannan ƙasaitacciyar fada sai mutumin nan mai rabin jikin zaki ya washe fuskar sa da murmushi ya ajiye tambulan ɗin ruwan inibin akan ƙaramin tebur dake gabansa.
Sannan ya dubi su markahus sabus yace,
"Lale marhaban,ina mai yi muku barka da zuwa birnin Madinatul Aslik yaku hadiman boka Shamharu."
Cikin tsananin mamaki su markahus sabus suka dubi juna.
Sannan suka maida hankalinsu ga mutumin suka yi shiru.
Caraf sai markahus sabus yace,
"Ya kai wannan sarki mai karamci,ya akai ka san da zuwan mu nan kuma yanzu me kake nufin aiwatarwa da mu har da kasa aka kamo mu aka gurfanar damu a gabanka?"
Koda jin wannan tambaya sai mutumin ya bushe da dariya.
Sannan yace,
"Ya kai markahul sabus kayi sani cewa ni sunana Sarudul Makam kuma nine sarkin wannan duniya ta Madinatul Aslik.
Babu wani sarki a cikin duniyar sama ko ta ƙasa ko ta tsakiya wanda bansan da zamansa ba,kuma bansan da shirin sa ba,ko burin rayuwar sa.
Kuyi sani cewa duk abinda ya faru gareku naji kuma na gani a cikin madubin tsafina.
Yanzu haka kun fito ne daga birnin duwatsu inda kuka samo narkakken dutsen da yafi kowane dutse girma a duniyar ku.
Yanzu kuma kuna son ku wuce izuwa duniyar ƙarshe ta nan ƙasan bakwai,don ku ɗebo dutsen wuta.
Idan kuka sami nasara ne zaku je ku ɗebo rabin ruwan tekun duniyar ku.
Sannan ku kaiwa Shamharu waɗannan abubuwa uku,don ya ƙera kubar MIFTAHUL ZARBIL wacce da ita ne zai buɗe fadar Saukatul Askur ta sarki Azmul gallar,don ya ɗauko kundin tsatsubansa ya karance shi saboda ya sami sirrikan tsafinsa.
Ko ba haka bane?"
Markahus sabus yace,
"Zancen ka dutse ne."
Sarudul Makam ya sake bushewa da dariya yace,
"Kuyi sani cewa gaba ɗaya duniyoyin nan guda bakwai dake nan ƙarƙashin ƙasa na ƙarƙashin ikon mahaifiyata,kuma duk 'yan uwana ne ke mulki a sauran duniyoyi shida.
Rana guda aka haife mu mu bakwai,amma nine na fara fitowa daga cikin ta,sai kuma Saradul Hasal, Saradul Algaz, Saradul Hisnu, Saradul Badal da kuma Saradul Imzan,wanda shike sarautar duniyar ƙarshe.
Ina mai sanar daku cewa gaba ɗayan mu mu bakwan nan bama ga maciji kuma kowa na ƙoƙarin kashe kowa.
Ba komai ne ya haddasa haka ba face kishi akan mulki.
A da can kafin mutuwar mahaifiyar mu duniyoyin bakwai a ƙarƙashin wannan duniyar tawa suke,kuma mahaifiyar mu ke mulkin ta.
Amma da ta kwanta ciwon ajali sai ta raba mana duniyoyin ta baiwa kowa guda ya mulka,don gudun rigima a tsakanin mu.
A halin yanzu kowa daga cikin mu so yake ya haɗe duniyoyin bakwai ya mulka shi kaɗai.
Kun ga kenan dabarar da tayi ba tayi amfani ba tunda dai rigima ta karƙe a tsakanin mu.
Nayi bincike na gano cewa sai nayi wani aiki sannan zan iya mallakar waɗannan duniyoyi shida kuma aikin ba zai yiwu ba saida taimakon halittu irin ku.
Don haka ni yanzu zuwan ku nan rahama ce a gare ni,don tamkar cikar buri na ne.
Lallai bazan bari ku gusa daga nan ba face kun bani haɗin kai nayi wannan aiki tare da ku."
Koda sarki Sarudul Makam yazo nan a zancen sa sai markahus sabus yayi ajiyar numfashi yace,
"Ya kai wannan sarki ina son na nemi wata alfarma guda ɗaya a wajen ka kafin ka sanar damu wannan aiki da zamu tayaka."
Sarudul Makam yace,
"Faɗi abin da kake buƙata."
Markahus sabus yayi gyaran murya sannan yace,
"Ya kai wannan sarki kayi sani cewa a duniya babu abinda nake so kuma nake matuƙar son gani face gimbiya Sima.
Ina son ka sanar dani halin data shiga,tun daga lokacin dana rabu da ita.
Tunda kace ka san duk abinda ke faruwa a ko'ina a cikin kowacce duniya."
Koda jin haka sai sarki Sarudul Makam ya ƙyalƙyale da dariya sannan yace,
"Ai wannan aiki ne mai sauƙin gaske,kuma ina yima albishir da cewa bama gaya maka zanyi ba.
Zan nuna maka al'amarin ne a zahiri yanzu take kaga duk abinda ya faru gareta."
Nan take Sarudul Makam ya shafi wani jan allon tsafi,saiga hoton abubuwan da suka faru ga gimbiya Sima na zayyana daki-daki tun daga lokacin da markahus sabus ya tafi da ita gida wajen mahaifiyarsa Samaratu kawo izuwa lokacin da aka yi gagarumin yaƙin nan nasu aljani Abtarul Hudeis da su sarki Lu'umanu sa'adda Hubairu da gimbiya Sima za suje garin nan inda gidan kayan tarihi suke har kuma izuwa lokacin da aka ɗaura auren gimbiya Sima da jarumi Hubairu a birnin Laharim aka kafa tutar musulunci a garin.
Koda markahus sabus ya gama ganin waɗannan abubuwa,sai idanunsa suka ciko da ƙwalla ya fara zubar da hawaye,don yasan cewa shike nan ya rasa gimbiya Sima har abada.
Nan dai markahus sabus ya shiga tunani a zuciyarsa yana mai cewa yanzu mene ne amfanin rayuwar sa tunda dai duk gwagwarmayar da yake yi akan gimbiya Sima ne,kuma gashi ya rasa ta.
Markahul sabus ya tuno da wahalar da yasha a hannun sarki Lu'umanu kuma ya tuno da gwagwarmayar da yayi da dodo kiryanu sa'adda yaje ɗebo tsumi.
Haka kuma ya tuno da yadda rayuwar sa ta kasance a hannun matsafan duniya sai yawo ake da shi a kaishi can a wulla shi can ba shi da wani iko nasa.
Ya sake yin nazari akan hanyar da zaibi ya kuɓuta sai yaga ai a duniya babu waɗanda suka gagari matsafa face ma'abota addinin Musulunci, tunda yanzu ma gashi a zahiri yaga yadda su Abtarul Hudeis suka sami nasara akan su Lu'umanu.
Nan take markahul sabus yaji zuciyarsa ta aminta da addinin musulunci, kuma yaji yana son shiga cikin addinin sai dai kash bai san yadda zai shiga cikin addinin ba.
Sarki Sarudul Makam ya dakawa aljani Markahus sabus tsawa yace,
"Tunanin me kake yi?
Bani hankalin ka nan don kaji aikin da zamu yi yanzu.
Wannan aiki ba komai bane face zamu tafi tare daku izuwa waɗannan duniyoyi guda shida dake ƙasan wannan, domin mu yaƙe su ɗaya bayan ɗaya,mu kashe na kashewa mu kama na kamawa,har dasu 'yan uwan nawa kuwa.
Sannan ku shiga cikin baitul malinsu ku ɗauko mini wasu ƙahonni na zinare guda shida.
Ma'ana a cikin kowacce baitul mali akwai ƙahon zinare guda.
Idan aka haɗa jimila ne zai zama shida,idan na mallaki waɗannan ƙahonni guda shida zan soka sune anan cikin tsakiyar duniya ta.
Sai na yi hakan ne zan iya mulkar waɗannan duniyoyi guda shida.
Kuyi sani cewa waɗannan ƙahonni guda shida 'yan ƙanana ne mitsi-mitsi,amma mu ba zamu iya taɓa su ba da hannuwan mu.
In kuwa muka taɓa su take zamu narke mu zagwanye.
Ba komai bane ya haddasa hakan ba face cewar mu a jikin mu babu jini face ƙashi da tsoka zalla.
Kuma dole sai mai jini a jikine zai iya taɓa waɗannan ƙahonni."
Koda jin wannan batu sai mamaki ya kama su markahul sabus.
Boka Jinshan ya dubi sarki Sarudul Makam yace,
"Ya zaka ce babu jini a jikin ku?"
Sarudul Makam yayi murmushi yace,
"Ai dama nasan ba zaku amince ba,don haka yanzun nan zan nuna muku zahiri."
Nan take Sarudul Makam ya ɗauko wata zureriyar wuƙa ya feraye hannun sa saiga ƙaton nama ya zaftaro yana lilo,amma ko ɗigon jini babu face ƙasusuwa da jijiyoyi ba kyan gani.
Cikin sauri su markahul sabus suka kau da kansu ga barin kallon hannun.
Sarudul Makam ya ƙyalƙyale da dariya sannan ya kamo yankakkiyar tsokar dake reto a jikin hannunsa ya maida ita mazaunin sa.
Take wajen ya haɗe kuma ya shafe kamar ba a taɓa yanka ba.
Al'amarin daya ƙara baiwa su markahul sabus mamaki kenan.
Boka sulbaini ya dubi Sarudul Makam yace,
"Ya kai wannan sarki shin mutanen dake sauran duniyoyin ƙasa duk irin ku ne?"
Sarudul Makam yace,
"A'a ba irin mu bane.
Kuyi sani cewa duk mutumin daku ka gani anan ɗana ne ko kuma 'yata.
Ma'ana duk nine na haifi gaba ɗayan mutanen wannan duniyar tare da matata guda ɗaya.
Kuma ga matar nan tawa a tsaye a gaban ku."
Sarudul Makam yayi nuni izuwa ga wata wadar tsohuwa tukuf.
Launin jikinta gaba ɗaya ja ne jajur.
Kuma haka duk mutanen garin suke.
Sarudul Makam ya cigaba da cewa,
"Idan kuka je duniya ta biyu zaku iske cewa launin mutanen garin gaba ɗaya fari ne, saboda haka launin matar Sarudul Hasal take.
Matar Sarudul Algaz shuɗiya ce,matar Sarudul Hisnu baƙa ce,matar Sarudul Badal koriya ce,matar Sarudul Imzan kuwa ruwan ɗorawa ce.
A taƙaice dai kowacce jama'a yanayin mahaifiyar su ne."
Salusa ta tsoma baki cikin wannan zance tace,
"Ya kai wannan sarki na fahimci cewa makami baya tasiri a jikin ku,ta yaya zaka yaƙi sauran 'yan uwanka dake cikin duniyoyin shida?"
Sarudul Makam yayi dariya yace,
"Haƙiƙa babu wani ƙarfe da zai iya tasiri a jikin mu domin ko an daddatsa mu anyi gutsin gutsin da mu sai jikin mu ya haɗe ya manne,kamar yadda yake.
Bari na baku misali ku gani."
Nan take Sarudul Makam ya sake luma waƙunnan a cikin ramin idonsa guda ya ƙwaƙulo ƙwayar idon ya ajiye ta akan tebur.
Kogon ramin idon yayi zururu babu kyan gani.
Koda Sarudul Makam ya durƙuso da fuskarsa ƙasa daf da kan tebur ɗin sai ƙwayar idon nasa tayi tsalle ta koma cikin gurbin ramin idon da kanta.
Sarudul Makam ya bushe da dariya sannan ya murtuke fuskar sa a lokaci guda.
Kawai sai ya buɗe wata akwati ya ɗauko wata irin takobin haske.
Ita dai wannan takobi in ka taɓa ta da hannu sai kaji baka taɓa komai ba,amma a zahiri surarta ta haske ce.
Ƙotarta kawai ake iya taɓawa asan an taɓa ta.
Sarudul Makam yace,
"Kunga wannan takobin ta musamman ce nine na ƙirƙire ta daga cikin sirrikan tsafina.
Da wannan takobi ne kaɗai za'a iya kashe irin mutanen mu, domin duk wanda aka sara da ita take zai zagwanye ya narke.
A halin yanzu na ƙera irin wannan takobi guda miliyan dubu ɗaya da ƙwaya biyar.
Ina dakarun yaƙi guda miliyan dubu ɗaya cif kunga kenan akwai sauran takobi guda biyar,kuma ba ta kowa bace face taku ku biyar ɗin nan,dama na tanade su ne saboda ku don nasan cewa kuna tafe."
Cikin matuƙar tsoro boka sulbaini ya dubi sarki Sarudul Makam yace,
"Au kana nufin cewa muma zamu tayaku yaƙin ne?"
"Ƙwarai kuwa,idan ma baku jagoranci yaƙin ba ba za mu yi nasara ba.
Kunga shike nan muna gama yaƙin sai nasa a ɗebo muku duwatsun da kuka zo nema a can duniyar ƙarshe ku yi tafiyar ku salin alin cikin kwanciyar hankali."
Koda jin wannan batu sai markahus sabus yayi tsaki yace,
"Ina fa batun salin alin kace dai bayan mun sha muguwar wuya ko kuma bayan mun halaka?"
Sarudul Makam ya ƙyalƙyale da dariya yace,
"Koma mene ne ai ba kuda zaɓi dole ne kuyi yadda na tsara in ba haka ba kuwa yanxun nan na azabtar daku da irin azabar da baku taɓa ɗanɗana ta ba."
Salusa tace,
"Kai kuwa wace irin azaba ce wannan wadda bamu taɓa ɗanɗana irin ta ba?"
Sarudul Makam yayi murmushi yace,
"Karki damu yanzun nan zan jarraba miki ita."
Nan take sarki Sarudul Makam yasa aka zo da wata ƙatuwar kwalba wadda aka rufe ta da wani irin faifai na ice.
Kawai sai yasa aka kama Salusa da ƙarfin tsiya aka sata a cikin kwalbar aka rufe da wannan faifai.
Yin hakan ke da wuya sai jikin Salusa ya fara daddarewa yana sala sala kamar ana feraye ta da zabira.
Nan fa Salusa ta rinƙa ihu saboda tsananin azaba,saida ta suma.
Sannan ne sarki Sarudul Makam yasa aka fito da ita daga cikin kwalbar.
Salusa dai bata farfaɗo ba sai bayan sa'a guda.
###########
Sarudul Makam ya dubi su markahul sabus yace da su,
"Duk wanda yayi mini gardama daga cikin ku haka zan yi masa."
Ya sake nuna salusa da ɗan yatsa yace,
"Ke kuma idan baki gamsu ba da wannan azabar akwai wadda ta ninka ta sai a jarraba miki ita kiji nata ɗanɗanon."
Cikin tsoro da kuka salusa tace,
"Kayi mini rai haƙiƙa na gamsu da wannan ma."
Markahul sabus ya bushe da dariya sannan yace,
"Amma dai salusa kinyi wauta koda yake ban yi mamaki ba domin 'yar fari ce ke zaki iya yin abinda yafi haka,amma in banda wauta wa zai nema wa kansa wahala."
Gama faɗin haka ke da wuya sai Sarudul Makam yace,
"Yanzu za a kai ku masauƙin ku don ku huta,amma ku kwana da shiri domin gobe da safe zamu yi shiri mu tafi wannan yaƙi."
Nan take dakarun nan da suka zo da su suka sake surarsu suka ɗora su akan manyan jemagun nan.
Su kuwa jemagun sai suka buɗe fukafukansu suka yi sama.
Sannan suka cigaba da tsala gudu a sararin sama.
Saida akayi tafiyar daƙiƙa ɗari sannan aka sauke su markahul sabus a masaukensu.
Masaukin ya kasance wani tamfatsetsen gida mai tsananin girma da faɗi domin aljani Durmazalu bai isa ya ƙure ƙarshen sa ba a cikin sa'a uku duk da cewa kuwa yana da fukafukai miliyan ɗaya.
Shi dai wannan gida a cike yake da hadimai sai tafiyar da aikace-aikacen su kawai suke.
Bayan an kai su markahul sabus cikin wani babban ɗaki sai aka kawo musu abinci da abin sha kala biyu.
Kalar farko irin na mutane ne irin su boka jinshan.
Kala ta biyu irin na aljanu ne.
Nan take suka kama ci da sha aka bar salusa ita kaɗai a gefe guda tayi zugum da tagumi kamar zata fashe da kuka kuma dama ga raɗaɗin ciwon jikinta,ga yunwa ga ƙishirwa.
Nan fa tausayin ta ya kama markahul sabus yace,
"Yake salusa taso mana kizo muci abinci."
Salusa ta gyaɗa kai tace,
"Ai ni babu abinci na anan.
Ni kam ina ganin cewa sarkin nan fa baya ƙaunata kawai so yake ya halaka ni.
Ku dubi fa yadda jikina ya zama sala-sala."
Rufe bakinta keda wuya sai ga wani hadimi ya shigo ɗauke da wani ƙaton faranti.
Akan farantin dafaffiyar dalma ce ke fitar da tururi.
Kai tsaye hadimin ya ajiye farantin a gaban salusa.
Koda taga abinda ke cikin farantin sai tasa hannu biyu ta rinƙa ɗiba tana shanye wa.
Da yake jikinta na dutse ne sai ruwan darmar data sha ya rinƙa manne jikin nata.
Cikin 'yan daƙiƙu kaɗan duk ciwon jikin nata ya ɓace ɓat.
Kawai sai su markahul sabus suka ji tayi wata irin gyatsa mai kama da rurin giwa.
Tana gama gyatsar ta dubi jikinta taga ya warke sumul gaba ɗaya, kawai sai ta bushe da dariyar farin ciki.
Tayi ta ƙyalƙyala dariyar kamar ba zata daina ba.
Dariyar ce ta baiwa su markahul sabus dariya suma suka hau ƙyaƙyatawa.
Kashe gari da sassafe sarki Sarudul Makam yasa aka zo aka ɗauki su aljani Durmazalu aka tafi dasu izuwa can fadarsa.
Da zuwa suka iske dakaru miliyan dubu ɗaya a tsaitsaye a jere kan layi,sahu sahu kowannensu riƙe da takobin haske.
Sarki Sarudul Makam na tsaye a gaban su yana kallon yawansu da kuma daidaiton tsayuwar su.
Koda aka zo da su markahul sabus sai aka gurfanar dasu a gaban sa.
Nan take ya ɗauko takubban haske guda biyar ya rarraba musu.
Sannan ya umarce su dasu shiga cikin sahun mayaƙan.
Ba tare da fargabar komai ba suka bi umarni.
Kawai sai sarki Sarudul Makam ya fara bayani kamar haka:
"Yaku mayaƙana kuyi sani cewa a yau ne ranar da zamu jajirce iyakar jajurcewar mu.
Yau ne ranar da zamu zamo iyaye ga sauran duniyoyin dake ƙasanmu,kuma yau ne ranar ƙwatar ranmu da cikar burin mu.
Ina mai kira a gare mu gaba ɗaya damu sallama rayuwar mu don kare mutuncin mu.
A matsayina na mahaifin ku ina mai horonku da kada ɗayan ku yaji tsoro ya gudu daga filin daga.
Kuyi sani cewa kamar yadda muke wannan shiri na son mallakar sauran duniyoyin nan haka suma suke nasu shirin na son mallakar mu.
To amma sunyi sake ɗan zaki ya girma,kuma sun manta da cewa wanda ya riga ka kwana dole ne ya riga ka tashi.
Ya ku 'ya'yana kuma mayaƙana kuyi sani cewa ga baƙi nan su biyar a tare damu, waɗannan baƙi sune za suyi mana jagora a cikin wannan yaƙi kuma su kaɗai ne zasu iya shiga cikin baitul malin duniyoyin ƙasa su ɗauko mana ƙahonnin nan guda shida."
Lokacin da sarki Sarudul Makam ke wannan jawabi sai su boka jinshan suka nutsu suna sauraronsa.
Koda jin cewa sune zasu jagoranci wannan yaƙi sai markahul sabus ya matsa daidai kunnen boka jinshan yayi masa raɗa yace,
"Ya kai jinshan kayi sani cewa nifa ina ganin cewa mutanen nan fa sun raina mana hankali.
Ya za'a yi mu da bamu da ƙarfi da kuma taurin rai irin nasu,amma suce wai mune zamu jagoranci wannan yaƙi?"
Jinshan yayi ƙwafa yace,
"Kaidai bari kawai ai ni tun jiya na gama suƙewa inda nasan cewa nafi ƙarfin mutumin nan da tuni nayi wa shege dukan tsiya na koya masa hankali, gajeren banza me kamar a kife da kwando🤣🤣🤣🤣(kuji pah boka jinshan da ƙarfin hali🤣🤣shi ya manta cewa shima gajere ne kamar waziri kuddaru 🤣🤣)
To in banda ma rainin wayo ya mu da aka turo mu wani aikin kai kuma saika tsare mu kace sai munyi maka naka aikin.
Sannan zamu aiwatar da namu?"
Markahul sabus yace,
"Ai abin ma ya wuce rainin wayo saidai a kira shi fin ƙarfi da zalunci."
Suna cikin wannan magana ne sarki Sarudul Makam ya gama jawabi kuma ya bada umarnin a tafi izuwa duniya ta biyu.
Kawai sai aka ga wata wawakekiyar ƙofa ta buɗe saiga jemagu na ta tuttuɗowa daga cikin ta har saida guda miliyan dubu ɗaya suka shigo kuma dukkanninsu suka sauko ƙasa suka tsaitsaya cak a waje guda.
Nan da nan mayaƙan nan guda miliyan dubu ɗaya kowa ya hau kan nasa jemagen.

Mu hadu a part I don Jin cigban wannan Kasaitaccen labarin.**MIFTAHUZZARBIL**
LITTAFI NA BIYU 2❤️
Chapter 3 · 0% Book details