← Book details Me & My Lion Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
CHAPTER 2 OF 6

Chapter 3 & 4

Me & My Lion Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Amma ko alamar sunsanda zamanta Basu nunaba har suka ɓullewa ganinta, bata haƙura tabisu har cikin gidan gonar da suka nufa....dukkansu sojojin sun fito tare da ƙamewa wuri ɗaya, shi kuwa ogan nasu yaziro kafarshi ɗaya, ɗayar kuma na cikin mota, da waya maƙale a kunnenshi. Dagudu taƙaraso gidan gonar tare da nufar inda ta hangesu tsaye, babu abinda mugun yimata ɗaci arai irin yadda suka jiƙa mata milk ɗin hijab ɗinta na islamiya.

Waye ketuƙin wannan motar? Tafaɗa cikin wani irin sexy sound tana zuba musu lulu ayes ɗinta masu kama da na yar shaya. Dukkansu juyowa suka yi suna kallonta jin wannan sweet sound ɗin metafiya da imanin mutum, ganinta sukayi asatsaye tazuba musu ido tana ƙare musu kallo. Yarinyar kyakkyawa ce baƙarya Sedai black beauty ce amma tanada wani irin sohirtaccen kyau me ɗaukar hankalin me kallonta. Bawanda yace mata ƙaka sema ɗauke kansu dasukeyi daga kallonta. Cikin ƙufula tasaka hannu tare da dukan motar dake kusanta tana faɗar "wlh sekun fiddamin kowaye ke tuƙin wannan motar domin bazan yadda ba Hakan kawai yajiƙani dan rashin imani kuma kugudu kubarni dan rashin tausayi tunku gaku sojoji, Toni wlh baruwa dako suwayeku kawai kufitimin da wanda yajiƙani dan Sena rama.


Cikin hasa da mamakin ƙarfin halin yarinyar Captain Usman yajiyo yana faɗar "kee barnan kafin natashi kanki da bindigarnan, yafaɗa cikin tsawa yana nunata da bidigar dake hannunshi...wani kallon bakada hankali tayi masa babu ɗigon tsoro ko ɗar aranta, domin ko karkarwar da jikinta keyi na sanyine bawai natsoroba sabida bata ƙaunar sanyi ko kaɗan ajikinta. Cikin tsiwa da rashin tsoro tace "au badai Zaku nunaminba kenan, tayi maganar tanabin ƙafar wanda ke cikin motar tsakiya da kallo, a kuma Dede wannan lokaci lieutenant musayyeer ya fito gabaki ɗaya daga cikin mitar dawayarshi akunne yafara takawa zuwa cikin cikin parlor.....Shi kuwa Caspian ganin renin hankalin yarinyar yayi yawane yasa yayi kanta cikin tsawa yake faɗar "dan ubanki munyi miki kamada sa'arkine? Yana faɗar Hakan yana kaima mata harbi daƙafa. Aiko cikin zafin nama tagoce tare da daka wani uban tsalle kamar wata kwaɗo segata ɗare ɗare ajikin lieutenant musayyeer shattima daya kusan ƙarasawa kofar parlor. Wani irin runtse ido yayi daƙarfi jin mutun yafaɗo mishi ajiki ajikin tamkar wani soso domin ko kaɗan batada wani nauyi. Ido duk sojojin dake wurin suka zaro cikin mugun tashin hankali da mamakinta, wasuna dafe kai wasu buɗe baki tamkar za su tsaga bakin sabida tsabar ruɗewa...shikuwa wani irin sanyi yaji yadsuke bayanshi saka makon jikinta datake cuɗawa aduka bayanshi tana goge masa ruwan da suka watsa mata. Wani irin fisgota yayi da hannu ɗaya taredayin jifa da Ita aƙasa, kana yajiyo yazuba mata wannan rikitattun idanuwan nashi masu firgita yan maza.

Ganin Hakan yasasu Captain Usman dawowa cikin hayya cinsu cikin hanzari sukayo kanta domin suci ubanta kafin su aci nasu, domin wlh shattima kwallon ɗan iskane ze iya cin ubansu amadadin ita, Sedai kafin su ƙarasa sukaga yaɗagata cak da hannu ɗaya yayi cikin parlor da ita.."yayi kyau kinkai ƙarshen rashin kunya yau. Cewar wani soja. Cikin takaicinta ɗaya daga cikinsu yaƙara cewa "Allah yasa boss yayi raping ɗin shegiya taso jaza mana masifa koyanzu kuma nasan batsira mukayiba. Girgiza kai Captain Usman yayi kawai domin ya san abune me wahala lieutenant yayi raping ɗinta kamar yadda suke faɗa domin shi sam baya harkar mata, amma da yanayi shikanshi zeso ya ɓalla yar iska.

Shi kuwa shattima yana shiga parlor yayi wani irin wulgata tamkar ya jefa kiyashi. Aiko ta tsandara ƙarar da seda gidan ya ɗauke saka makon mugun buguwar da ƙugunta yayi ajikin kujerar parlor. Tsallaketa yayi yashige wani bedroom dake cikin parlor yana shiga toilet yawuce domin wani irin ƙyanƙyamin kayan yakeji dudda kasan cewarsu kaya mafi yosuwa da daraja agareshi, cire su yayi doka har Short ɗin pajamas daje jikinshi. Yayi saura dagashi se Fatar jikinshi. Ataoroce nayo baya domin nikam bazan iya jurar kallon wannan mirɗaɗɗen sojanba🫣 bayan minti biyar ya fito ahakan yadda yake, kana yabuɗe widrop ya fiddo wando 3 kwata da ƙaramar riga duka farare ƙall yasanya.

Acan parlor kuwa gabaki ɗaya wannan budurwar tafita hayya cinta sabida wani irin ƙugi da ƙugunta keyi kasusuwanta narabuwa da junansu sosai take kuka tana jan Allah ya isa domin ko motsin kirki takasayi.

Unguwa uku


Misali ƙarfe 7:30pm wata dattijuwar sohuwa ce ke tsaye abakin ƙofar gidanta se kuka take yi, gabaki ɗaya taɗagawa maƙotanta hankali, mlm Bello se haƙuri yake bata amma fir taƙi se ƙara tuburewa takeyi. Daga gefe ɗaya kuwa samarine kusan su shida ke tattauna yadda zasuje neman jikar tsohuwar domin sunsan yau tabbas idan ba'aga *FAILUSHA* ba sunsan babu sauran zama lafiya a unguwar...da ƙyar da siɗin goshi mlm Bello da matarshi suka lallaɓa Hajiya kaka ta shiga cikin gida da aƙawarin zasu Nemo mata failusha Aduk inda tashiga.
Hakan suka zauna da Ita har kusan 11:00pm amma babu failusha babu dalilinta, wannan dalilin ne yasa hankalin Hajiya kaka yaƙara tashi, takira yayar failusha dake aure anan cikin suleja ɗin tasanar mata ɓatan ƙanwar tata. Cikin tashin hankali Anty fa'iqa tagaizayo zuwa idan Hajiya kaka itada mijinta, anan mijin nata yaƙara baza motane yadda sanarwa da ja'an tsaro zancen neman failusha, abu kamar wasa cibi na neman kaisu dare. Cikin karaya Anty fa'iqa tacewa Hajiya kaka "kaka wai kinsanarwa dady ne? "Nasanar mishi a ina inazanganshi tund kinzo yanzu ai seki kirashi.


Gidan gona

Tun da ya shiga bedroom ɗinshi beƙara fitowa ta se wuraren 2:30am. Yafitowa yayi sanyeda sleeping dress riga da wando masu santsi, se wani irin sihirtaccen ƙamshi yake bazawa memugun shiga jiki, riƙe yakeda laptop ahannunshi yana tafe yana aiki hankalinshi kwance, ga dukkan alamu ma yamanta da wata halitta acikin parlor. Sedai yana zama ya fara jiyo shashekar kuka ƙasa ƙasa murya ko fita batayi, atake yatinada abinda yafaru ɗazu. Cije lips ɗinshi naƙasa yayi cikin wani irin ɓacin ran abinda ƙaramar yarinya tayi mishi tabbas kowaye yaturota baƙaramin shiri yake dashi akanshi ba, yajima yana tinani acikin ranshi kafin yamiƙe ya shiga tako cike da izza da kurazari tamkar bijimin Zaki. Yana zuwa wurinda take, betsaya komai ba ya falla mata wani gigitaccen marinda seda ta mulmula sau kusan huɗu kafin tatsaya sabida ƙafar senter tebble data tareta. Takawa yakarayi ya cimma ta kana yadoƙo da zimmar tambayar ta, domin shi baya fara tambayar mutum seya fara sauke mishi maruka. Ganinta dayayi asomene yasa yamiƙe azuciya ya ɗauko ruwan faro masu bala'in sanyi yaɓalle marufin kawai ya shiga bulbula matasu atsakiyar kanta suna sauka ajikinta. Wani irin nunfashi taja tare da ƙoƙarin buɗe lulu ayes ɗinta ataoroce Sedai takasa Hakan sakamon wani arnen sanyi dataji yana shiga cikin ƙofofin gashin jikinta wanda yasa nomfashinta fara kokawar barin jikinta, bata gama kokawa da nomfashinta tafara wani irin kakari idonta na neman kafewa saka makon wata muguwar shaƙa da shattima yayi mata tare da falla mata mari lokaci ɗaya, cikin wani cool voice me firgita tsagera yace "uban waye yaturoki gareni? Waye shi baze iya tunkarana ba harse yaturomin mace? Macen ma jinjira irinki. Zaki gayamin wanda yaturoki kosena kashe anan naɓatar da gawarki. Yaƙarasa zancen yana karayin jifa da ita again. Afirgice taƙara farkawa domin tun sheƙar da yayi mata taƙara somewa. Cikin wani irin tashin hankali da tsoron ganin mutuwa afilin Allah, tabuɗe bakinta dake rawa muryarta ko fita batayi sabida tsabar gala baita, tace "MY LION, zokaceceni ahannun wanna sojan zekasheni sekuma tasake rushewa da kukan nadamar zuwanta makasarta. Shi kuwa azuciye yayi kanta, sedai tana ganin yanofota tamkar wani Zaki yasa taƙarayin ɗib tasome akaro na uku. Wani mugun tsaki yaja taredayin Ball da ita kana ya ɗauki laptop ɗinshi yakoma bedroom domin tabbatar idan yabi ta zuciya to kasheta kawai zeyi.

Ashe gari

Misalin ƙarfe 9:00am ya fito cikin wasu ƙananun kaya wanda suka yi bala'in karɓar Fatar jikinshi blue gens and jar t-shirt kayan baƙaramin kyau suka yi mishiba, tako yake yi cike da jamunta ya fito daga cikin gidan kai tsaye motocinshi yanufa da da waya a kunnenshi yana magana cikin harshen Turanci tamkar ba ɗan Nigeria ba, magana yake yi da abokinshi kuma aminin shi mutallab. Cikin sauri duka yaranshi suka taso suna sara mishi cike da girmamawa kafin Caspian sahib yabuɗe masa kofa ya shiga kana yarufe suma duk suka shiga nasu motocin sukabar gidan gonar cikin azababben gudu tamkar zasu tada ƙwallar kamar yadda suka saba... Captain Usman da Captain sahib kuwa tunanin yarinyar dake cikin gidan sukeyi sunsan tunda sukabar gidan gonar bazasu dawoba kana kuma ga yar mutane aciki, kuma basuda halin tambaya ko tunatar dashi domin basuga fuskaba, wata zuciyar natabayarsu to wai koya kasheta ne? Wata kuma na gaya musu sam shattima baze iya kashe maceba macen ma ƙaramar yarinya kamar wannan dudda kuwa yakeda baƙar zuciya. Suna cikin wannan tunanin sukaji sansanyar muryarshi yana faɗar "muce unguwa uku kawai sauri nakeyi mu koma Abuja dawuri.."okay Sir cewar captain Usman kana suka ɗauki hanyar unguwa uku dudda cewar sunsan dama can ne inda zasu nufa a suleja ɗin.....!


🌹ME & MY LION 🦁

Kofa sanwa ba'a ɗoraba balle ayi zancen fara girki💃💃💃


Autar Alheri ✍️

*🌹🦁🌹ME & MY LION🌹*🦁🌹


Special and romantic love story 💋💓🫣

Writer by Autar Alheri ✍️


🦁🦁🦁🦁🦁🦁🦁🦁🦁
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
🦁🦁🦁🦁🦁🦁🦁
🌹🌹🌹🌹🌹🌹
🦁🦁🦁🦁🦁
🌹🌹🌹🌹
🦁🦁🦁
🌹🌹
🦁


Oh'oh'ohhhh 🤭🤭🤭
Wannan kabcen tabbas zegigita duniyar makaranta littafen Hausa ze hautsina brain ɗinsu, kana ze cika zukatasu da shauƙi tareda begen reality love❤️🫂 na haƙiƙa 💯


Book one
Chapter 2 · 0% Book details