← Book details Me & My Lion Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
CHAPTER 1 OF 6

Chapter 1 & 2

Me & My Lion Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

"Zaune suke acikin wani tanganemen parlor dukkan sun kewaye kujerin dake zagaye da dining tebble. Mutum kusan 6 de akai dattijuwa wadda bazata wuce shekaru 57 ba a duniya se megidanta dakuma yaransu duka maza su huɗu, kyawawa dasu tamkar ƴaƴan Larabawa Masha Allah ...Abinci sukeci hankali kwance bawanda ke wani ƙwaƙwaran motsi acikinsu. Kallon matar tayi akarona ba adadi kafin ta sake murmushi cikin soyayyar yaran nata tace "fawan wai duk wannan shiru shirun na minene abu kamar masu zaman makoki? Kodan son nagarine duk kuke wannan abin? Kafin fawan yabata amsa, Sena gafenshi yayi saurin cewa"yo ba dole mutum Yakama kanshi ba mami, idan kuma bahakan ba yasha horon sojoji. Dariya mahaifinsu yayi yaname faɗar "ah'ah da maheer Banda sharri ba'aninda SHATTIMA zemuku Indai bawani laifin kukayi masaba, yaƙarasa zancen cikin barkwanci acikin ahalin nashi. Cikin sauri wanda yake duka ƙarami acikinsu masuna Fa'iz yace "Allah Dady doline mutum Yakama kanshi koda bemaka komaiba idan yazubawa mutum waƴannan idanuwan nashi doline afirgita.

Ɗagawa wanda inaga shine babba acikinsu yayi yana kallonsu fuskarshi ɗaukar da lallausan murmushi kafin yace "ga wanda aka tambaya ga masu bada amsa, kai fawan dukafa kai mami tayiwa tamba amma kowanne kamar jira yakeyi wurin bada amsa. Dariya duka iyayen nasu sukayi. Kana fawan yace "bazaka ganeba bane yaa Noor lamarin babban yayane Seda taka tsantsan. Aiko suka koma sakin dariyar sedai kafin wani yakomayin magana acikinsu sukaji sohirtaccen ƙamshi turarenshi namusu sallama yana sanar dasu zuwanshi. Aiko atake duk suka ƙara shan jinin jikinsu suna maida hankalinsu akan acin abinci dasukeyi.

Takowa yashigayi zuwa inda yahango ahalin nashi zaune, ƙaƙƙarfan mutun ne cikakken namiji mejini ajika ma'abuci kyau da tsari irinna zaratan maza, farine tass dogo ingarman namiji mecikar zati. Kyakkyawa ne ajin farko domin duk kyawun ƙanenshi idan kaganshi zakace su ɗin munana ne, yanada manya kuma rikitattun idanuwanshi masu bala'in kaifi da saka mutum ya shiga taitayinshi, yanada dogon hanci wanda yayi dede da zubin kyakkyawar fuskarshi, idan aka gun suma kuwa bance komaiba domin yanada suma wadda bazata misiltuba sabida shi ɗin gargasa ne.

namijin gaske ne kuma kwallon dan iska ne ga wanda ya shiga gonarshi, ba shida mutunci ko kaɗan agun miyagun mutane ko kuma ɓata gari, kana baya ɗaukar wargi agida ko awaje, tsayayyen mutun ne me martaba kima da bukatar ahalinshi, agaskiya duk yadda zan misilta muku wannan guy ɗin to yawuce nan, sedai ku wassafa kamanninshi dakansu, halayenshi kuwa aikinshine zenuna muku asalin wayarshi. Sanye yake cikin kayan aikinshi wato kakin soja green color sunyi bala'in zaunawa a mirɗaɗɗen jikinshi na ƙaƙƙarfan namiji, domin kamar danshi kawai akayisu, farin silver dake manne akan gaban aljihun rigarshi nayi, inda naga anrubuta *LIEUTENANT MUSAYYEER MAHABUB SHATTIMA* da manyan haruffa, Hakan yasa nagane kenan Sunanshi musayyeer ne, woww gaskiya guy ɗinnan nikaina yatafi da inana ba ƙarya 🫣

Ƙarasowa yayi dining ɗin cikin sassarfa yaduƙa dede fuskar maminshi yana manna mata kiss a goshi kuma adede lokacin ne ya motsi siraran lips ɗinshi yiwa dady shi barka da safiya acikin wani irin cool husky voice meshiga rai da ratsa zuciya....cike da so da birgewa Dady ke amsa mishi ta hanyar faɗar "yawwa barka dai babana, fatan katashi lpy? "Alhmdulillah Dady, yafaɗa yana me lumshe rikitattun idanuwanshi jin yadda mami keshafa sumar kanshi. "Good morning Yaa shattima, cewar fawan, maheer kuwa cewa yayi "barka da safiya yaa Sayyeer. Yayinda Fa'iz yace "good morning yayanmu, yaname riƙo hannun yayan nasu. Dukkansu amsa musu yayi fuska asake cike da son ƙanen nashi, kafin Noor yabashi hannu yana faɗar "good morning big bro. "Morning too bro, how is my baby's? "They are fine big bro, zasuzo ma anjima sukace. "Okay, kawai yace tare da fara shan coffee da mami ta ajiye mishi anutse, batareda fa'iz yasake mishi hannuba har ya gama shan coffee, kana yamiƙe yana yiwa iyayen nashi sallama yafice daga gidan riƙeda hannun Fa'iz

besakeshiba seda yakaishi har inda dandazon motocinshi suke, yaranshi naganin fitowarshi sukazo cikin sauri suna sara mishi cike da girmamawa, kafin ɗaya yabuɗe mai motar dake tsakiyar motocin farakal parado girar GLK, shiga yayi yana kallon fa'iz dake manna mishi kiss a hannu, kana suma duk suka shiga sauran motocin tare da tadasu, suka harba su akan kwalta cikin azababben gudu kamar yadda sukeyi akoyoshe.

Suma duka matasan dake cikin gidan miƙewa suka yi domin kowanne yanufi wurin aikinshi, Noor Dr ne, fawan kuma company Dadynsu yake aiki shida maheer, fa'iz kuwa yanzu yake school begama amma yace yayanshi zegada.

Wannan kenan.

Musayyeer shine babba suna kiranshida shattima kasan cewar yanada Sunan mahaifin dady kuma shine shattiman garinsu, Hakan yasa suke kiran musayyeer da Sunan.
Sekuma Nuraddeen wato Noor
Fawan shikebin Noor se fawan, dakuma maheer kafin autansu fa'iz. Dukkansu sunada aure amma Banda auta fa'iz dakuma babban yayansu. Noor yaranshi biyu mace da namiji, fawan kuwa ƴarshi ɗaya yayinda matar maheer takeda shigar ciki ayanzu.

Kowannesu shine yanemo matar aurenshi ya aura amma Banda fawan daya auri yarinyar abokin Dady su wanda kuma Dady ne dakanshi tanemi wannan alfarman.

Sunan matar Noor Marwanatu suna kiranta da Anty Marwa. Sunan matar fawan, safiyya, suna kiranta Anty sofi, sematar maheer ita kuwa sunanta jidda.

Anty Marwa mace ce me Son mutane da kawaici, kuma ta fito gidan mutunci da sanin darajar ɗan Adam, amma fa batada kunya ko kaɗan wurin nunawa mijinta da soyayya.

Anty sofi, mace ce me jiji dakai da isa, tana mugun son fawan amma shi kam auren biyayya yayi mata, sedai betaɓa bari tafahimci hakanba. Iyayenta basuda mutunci ko kaɗan watsatsune naƙashe kana basuda tarbiyya ma balle subawa ƴaƴansu, su uku suke agidansu akwai yayansu mubina wadda tagirmewa safiya sosai sekuma ƙanwar safiya wato zeemama domin Zainab ne sunanta amma zeemama suke kiranta.

Jidda maheer kuwa, muguwar raguwa ce takarshe sedai ahakan mijinta na mugun sonta kuma itama tana sonshi sedai ragwanta kawai dake damunta.

Masu karatu kubi komai ahankali yadda Zaku fahimta domin akwai abubuwan dasu iya bayyana agaba wanda bamu faɗesuba ayanzu.


Bayan wani lokaci.

Cikin isa da izza irinta ƙaƙƙarfan namiji kuma jami'in soja mejini ajika ya fito daga cikin tanganemen office ɗinshi tafiya yake yi cikin sassarfa yanufi dandazon motocinshi, kyakkyawan mutum ajikin farko domin fa baƙarya lieutenant musayyeer mahabub shattima handsome ne baƙarya. Cikin sauri yaranshi suka miƙe tare da sara mishi kafin suka buɗemai motar tsakiya ya shiga, kana su kuwa suka shiga cikin sauran helux ɗin dake zagaye da ita, kana suka harba kan kwalta cikin azababben gudu. Suna ɗaukar hanya yabuɗe baki tamkar wanda akayiwa dole yace "suleja zamu nufa Usman. "Okay Sir, cewar captain Usman kana suka ɗauki hanyar dazata sadasu da suleja.

Tsugunne take gefen hanya tana tsintsar yayan goribarta data watse, yarinya ce ƙarama wadda bazata wuce shekaru 16 ba aduniya kyakkyawar budurwa me matuƙar birgewa da ɗaukar hankali, black beauty ce domin ba fara bace, tanada suma metarin yawa kuma me ɗaukar hankali, nagano Hakan ne ta hanyar ƙananun gargar dake kwance akan gashinta kasan cewar sanye take da milk hijab wanda yahanamin ganinta da kyau. Tana cikin tsintsar goribarta tamiƙe arazane tana faɗar kan ubancan, saka makon ruwan da akayimata wanka dasu na damana dake kwance agefen hanya. Ganin tayi motocin sunwuce tamkar basu wanzu a wurin ba, balle susan ta'asar dasuka yimata, Hakan yasa ta kwashe sauran goribar dake hannunta takwasa aguje tabi bayan motocin tana jifarsu da ƴaƴan goribar da iya ƙarfinta kuma tana zaginsu, ta hanyar ɗura musu ashar.....!


Humm ME & MY LION yanzufa za'afara wasan 💃💃💃


Autar Alheri ✍️

*🌹🦁🌹ME & MY LION🌹*🦁🌹


Special and romantic love story 💋💓🫣

Writer by Autar Alheri ✍️


🦁🦁🦁🦁🦁🦁🦁🦁🦁
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
🦁🦁🦁🦁🦁🦁🦁
🌹🌹🌹🌹🌹🌹
🦁🦁🦁🦁🦁
🌹🌹🌹🌹
🦁🦁🦁
🌹🌹
🦁


Oh'oh'ohhhh 🤭🤭🤭
Wannan kabcen tabbas zegigita duniyar makaranta littafen Hausa ze hautsina brain ɗinsu, kana ze cika zukatasu da shauƙi tareda begen reality love❤️🫂 na haƙiƙa 💯


Book one
Chapter 1 · 0% Book details