Sashe 8
Mabaraciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Na farko dai ni banda 'dakin da zan ajiyeki , bawai kuma saboda babu dakin a gidan bane sam sedai baki can canci ki zauna ba ,na biyu dole 7:00 yayi miki a cikin gidannan ,saboda 8 Nake tashi nayi sallah to kafin nashiga bayi ina bukatar ki tsaftace shi, se abu na karshe ,gada kiyarda yunwar iyayenki yasaki tunanin,daukar abincin gidan nan kitafi dashi koda kuwa an rage ne ,idan kika kiyaye wanan shikenan kuskure musu kuwa ,hmmm takarashe tana lumshe ido ,cikeda rashin damuwa Meerah tace " indai zaki kiyaye biyana hakkina ai wanan ba matsala bane ,jin amsarta yasaka Rufee dagowa ta dubeta ,sosai take mamakin jinkai irin na yarinyar ,kiran Larai wacce ke mata aiki tayi ,cikeda ladabi tace " Hajia gani ,kallon mamaki Meerah tabi Larai da shi ,idan aure kauye tayi kusan tahaifi Rufaida,amma gashi tana kankantar da kanta gareta " Rabbi ka kara rufa mana asiri tafada cikin xuciyarta " ki nuna mata dakina ta gyara komai kafin nazo ,tun kafin Larai tayi magana Meerah ta tashi binta tayi ,seda suka fara taka steeps tukuna ta juyo cikin sa'a kuwa sukayi ido biyu da Fatima ,kashe mata ido tayi tare da jinjina mata hannu alamar godiya , murmushi kawai Fatima tayi mata ,daga haka ta dawo kan Rufaida
" Nikam Rufee wai yanzu wane irin horo kike tunanin zakiyiwa yarinyar nan ,saboda da alama tanada jin kai "hararar ta Rufee tayi tace, malama ina da zan dauki matakin kece kika hana " haba taya zan hana baki fahimceni ba kenan ,kinsan dalilin da yasa na sanyayar mata da jiki saboda kar ta tafi? Bata jira amsar Rufee ba tacigaba da magana "to saboda nayi miki alkawarin se kin wulakanta ta kamar dai yanda kikayi alwashi kuma kema nasan kinason haka ,matsalar da aka samu ,saurin fushi dakikayi da wannan nayi anfani na tabbata komai zakiyi mata bazata bar gidannan ba saboda tana kaunar iyayenta kuma tana tausayinsu ,idan tabar gidan nan shikenan duk wani Hop nasu ya lalace,kinga dole zatayi hakuri ko badan saboda itaba ,domin iyayenta
Lumshe ido kawai Rufee tayi "amma yanayin da take magana ne idan kin kula kamar ba na sauran yayan talakawa ba,ni se nake ganin kamar tanada jin kai " karki damu da wannan ,haka wasu yayan talakawa suke idan kika ga suna daukar kai seki zata sudin wasu ne ,ajiyar zuciya Rufaida ta sauke tace " shikenan Teeamah na gode bari na koma bacci nakeji ,kallon mamaki tabita da shi kamar ba daga baccin ta taso ba ,amma a zahiri murmushi tayi tare da fadin " shikenan nima bara na wuce Mamana tana jirana ,dan ya mutsa fuska Rufaida tayi kamar bataji dadin furucin Teema ba bata dai ce komai ba ta tashi sukayi sallama.
Cikin ƙanƙanin lokaci Meerah ta gayara duka rooms ɗin ,bakin wani da yake a rufe ta dawo ,tsaye tayi tana ƙare wa ɗakin kallo cikin zuciyarta take ayyana cewar shine ɗakin Hajia Saudah ,ɗan zagayawa tayi inda taga window,sedai a rufe windown take ,motsin da tajine kamar ana taka steps yasakata barin wurin da sauri ,kallon tuhuma Rufee tabita dashi ƙasa tayi da kanta tace " na kammala ,tsaki kawai tayi mata ta taɓa ta tayi shigewarta ,da kallo Meerah tabita ,tana nemamata shiriya ga Allah,dan Allah yayi ka mai kuɗi bayana nufin kafi kowa bane .
Rufaida na shiga ɗakinta taji wani sanyi da ƙanshi ya bugeta babu shiri tafaɗa kan gado tana lumshe ido a zuciyarta mamaki take ya'akayi wannan villager ta iya gyaran ɗaki har haka gashi bata wani ɓata lokaci ba tayi mata aikin da ko Larai da take babba bazata iya irinshi ba ,taɓa baki tayi tace " ko da yake dagani tasaba aikatau .
Meerah kam tana saukowa ,ta samu wuri a falon ta zauna ganin shiru shiru bata fitoba yasakata sha'awar zuwa haraban gidan ,tana tafe tana ƙare wa gidan kallo ,batayi aune ba taji tayi karo da mutum,cikeda tsoro ta ɗago don gudun kar kowaye yayi mata rashin mutumci tunda ta kula kamar halayyar ƴan gidan ne "ke? taji yafaɗa yana nuna ta ,itama zare ido tayi saboda ta ganeshi mutumin nan ne da tataɓa yaɗuwa dashi kasuwa " me kikeyi a gidanmu ? Tambayar da yayi mata kenan,murguɗa masa baki tayi zata taɓa shi ta wuce ,fixgota yayi yace " bakiji me nace ba ? Cike da jin haushi tace " aikatau ,shiru yayi yana kallonta ,bece komaiba ya saketa ,raɓashi tayi ta wuce fasa zuwa balcony ɗin tayi tadawo falon ta zauna da kallo yabita ,tabbas yasaka wasi-wasi akan yarinyar ,da fari tazo gidan amatsayin Mabaraciya ahaka yaganta ,se kuma ya ganta a hanya a matsayin cikakkiyar me gata ,a yau kuma ta dawo gidansu amatsayin ƴar aiki,anya kuwa yarinyar nan Mabaraciya ce kodai anturo ta ne leƙen asiri" i will find it out ,yafaɗa yana shiga falon shima
a falon ya ganta raɓe gefen kujera ,bece da ita komai ba ,Larai da yaga tafito ya kalla yace " ke kiramin Rufaida , kusan a tare suka sauko itada Rufaida ,tunda ta hangoshi ta washe baki,cikeda jin daɗin ganinsa tace " Welcome MM ,shima Murmushi ya mayar mata yace " tnz ,haka kike zaune a ɗaki ke kaɗai instead of ko ƴan aikinnan kizauna kuyi hira ai sa ragemiki kaɗaici ko? Wane irin kallo tabi Meerah da sam tanuna hankalin ta baya kansu " yanzu Yaya saboda banda hankali se na zauna cikin ƴan aikin da sukecin abinci a ƙarƙashina na sakasu aikin da duk na gadama ,kuma zan iya marinsu idan suka kuskurewa umurni na ,amma duk da haka kake cewa wai nayi hira dasu? God forbid,never dead my body ,girgiza kai kawai Mu'aiseen yayi cikin zuciyarshi yake faɗar " yuh won't ever change ,a zahiri kuma tashi yayi tsaye yace " to ni zantafi dama fita zanyi nace bara na leƙoƙi tunda ke kinfi ƙarfin zuwa inda mutane suke "afuwan yaya ,harzaka tafi ko lemu bakasha ba ,laluba cikinsa yayi yace " don't worry am ok " ok to mutafi na rakaka,haka suka jero suna tafe suna hira ,itadai Meerah mamaki yakasheta ashe dama tana dariya lallai tafaɗa tana ci gaba da kallon tv,tana nan har Rufee tazo ta wuce ta,kallon agogon falon tayi taga har lokacin sallah yayi,inda taga Larai ta shiga tun ɗazu nan tabi Sega ta cikin kithen,sannu da aiki tayiwa Larai kafin ta tambayeta inda zata samu ruwan alolah,da sakin fuska Larai ta nuna mata wani coridor tace " akwai bayima acan idan zaki zagaya,Murmushi itama tayi tace " Nagode tare da bin hanyar seda tashiga toilet tayi fitsari tukuna tayi alwala ,a ɗan gefen wurin ta shinfiɗa kallabinta ta tayarda Sallah,tana idarwa ta dawo ciki zaman jiran tsammani ,ganin har kusan ƙarfe 4 Rufaida bata sauko ba ga kuma yunwa da takeji se kawai ta yanke shawar tafiya gida tunda dai ta kammala ayyukan ta to bataga dalilin zamanta ba kuma,wurin Larai taje tayi mata sallama ,kafin ta fito ta kama hanya ,koda ta shiga gida ana kiraye-kirayen sallar la'asar,a matuƙar gajiye tashiga gidan Aunty da ke zaune tana jiran dawo warta ta tareta da sauri tanayi mata sannu Ruwa tafara kawo mata girgiza kai tayi tace " Aunty ai se cikina ya ƙulle me kika dafa mana yau? Narasa me zan dafa shine kawai na yimana ɗan wake ,washe baki Meerah tayi tace," kin kyau ta min kamar kinsan nayi marmarin sa bani naci cikina har kukan yunwa yakeyi ,tashi aunty tayi ta kawo mata ɗan waken aikuwa ta hau ci kamar Mayun waciya ,seda tazo ƙarshe Aunty tace " gaskiya Ameerah ki canja wata shawarar dan bazaki sake komawa aikin nan ba ,a firgice ta saki sauran ɗan waken da yake hannunta tace " haba Aunty kenan duk wahalata tatafi a banza kenan seda nafarajin ƙanshin nasara shine zakice na dena ,koda a ce Rufaida zata riƙa yanka nama na ne zan jure matuƙar zan haɗu da muguwar matar nan Hajia Saudah.......
#Real@Bazamfaria
*INTELLIGENT* *WRITER'S* *ASSOCIATION*
( *On* *word* *together* )
*MABARACIYA*
*Story* *and* *writing*
*By*
*FIDDAUSI* *SANI*
(damsel feedorh)
🅿️:1️⃣2️⃣
dafa kafaɗarta Aunty tayi cikin sanyin murya tace "Meerah bawai ina so na hanaki ɗaukar fansan abinda akayi Miki bane ,saboda addini ma yabamu wannan damar idan har aka cuceka kuma kaga bazaka iya yafewa ba to ka rama daidai da yadda akayi maka ,sedai kituna irin tanadin da Allah yayiwa masu yafiya musamman a inda sukeda halin ramawa, Meerah inajin tsoron faruwar wani abu gareki Hajia saudah da kike gani ba ƙaramar mace ba kuma mijinta ma babban mutum ne na tabbata koda za'a kamata da lefin fasa kauri da yara mata tofa babu wani hukunci da zata fuskanta ,domin su sukeda doka , Allah ne kawai xe iya hukunta su bawai dan'adam ba musamman ke mace karama me rauni ,karkiyi wasa da rayuwar ki bamuda kowa se Allah.
Shiru Meerah tayi tana sauraren Aunty har seda tayi shiru ,alamun ta gama maganarta,murmushi tayi harseda fararen haƙoranta suka bayyana ,cikin salon maganarta tace " Aunty naji daɗi da kika ce Allah ne ce iya hukunta ,ki fahimceni bawai inason yaƙar ta bane ko kuma burin fansa ne kawai a gabana ba , a'a inaso ne na nuɓutar da sauran yaran da take ƙoƙarin halakarwa na kuma bayyanar da ɓoyayyiyar fuskanta wacce take cin amanar addini ,mutane da yawa suna yabonta akan kirkin ta har takan ɗauke wasu daga cikin yaran marasa ƙarfi da sunan zata tallafi rayuwar su wanda babu wanda yasan me take sakasu sunayi ,kasuwanci takeyi dasu
Saboda haka temako ɗaya nikeso kiyimin Aunty shine kitayani da addu'a Allah yabani ikon cin nasara akanta"
tana gama faɗar haka bata jira cewar Aunty ba ,tayi shigewar ta ɗaki, girgiza kai kawai tayi saboda tasan halin Meerah da naci akan bu tunda har tayi niyya to babu wanda ya isa ya dakar da ita.