Sashe 3
Kwarto Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Sanda Maryam ta shiga SS 2 makaranta Suka bata Labour prefect ,habawa !! Tun a wajen assembly da headteacher ya kira Sunan Maryam Mohammed matsayin labour prefect dalibai suka fara ihun basa so.
Wani abu tada hankalin displine master harda yinma Maryam kirari , hannun sa riqe da sabon dorina tasha man kade da dan kwalin Maryam na prefect .
"Borkono kenan,baqi baqi maganin daqiqin yaro .....Gwarzuwan daliban da makarantan nan muke alfahari da hazakanta mai dauke da quality da nagarta da yawa,ita tafi cancanta mu bata shugaban yara wato headgirl saboda kokarinta amma kuma kash makarantan nan suna neman jajirtacciya wacce zata qaro ma daliban makarantan nan ladabi da son karatu ,a don haka ne hukumar makaranta ta tace ta zaɓe ta zaqalo Maryam Mohammed a matsayin daliba mai horar da dalibai .....don Allah ku tafawa Maryam Mohammed.....raf raf raf" aka dauki tafi wasu na qunqunai wai Maryam mai taurin bashi aka ba labour prefect,matar da zataci aya ko gullisuwa bashi amma taqi biyanka kudi in ka matsa da tambaya ,tace aje filin kaci uwaka kawai ayi dambe in yaji wuya ta biya.
To bare kuma yanzu da aka bata muqami ai sudai dalibai kashinsu ta bushe......
Aikuwa anji jiki a mulkin Maryam ,dalibai basa fashi basa makara dukan gardi take ma dalibai ,in sunzo da kayan saidawa sai ta samu abinda take so sai tace tayi seizing haka zata cinye dan tingin sauran ta raba ma dalibai.
In bata da kudin mashin din komawa gida ,sai an dawo break haka zataje aji aji da basawanta da dorinai su kwakwace takalman gida da huluna da kayan saidawa ,sai mutum yayi beli za'a basa ,haka zata tashi da kudin ta cassss.
Lokacin da Maryam takai SS3 dalibai da yawa har addu'a suke Allah yasa ta fadi jarabawan mock da dalibai sukeyi a SS2 wanda in kaci zai baka daman waec da neco ,saidai abun Allah ita tazo daliba mai makin da yafi na kowa ,don haka gomnatin jihar Kano ta biya mata Neco ,babanta kuma ta tattara kudin markaden da takeyi ta biya mata Jamb .Bayan An gama jarabawa Maryam ta dawo gida ta zauna ana jiran sakamako.lokacin kuma Maryam ta kai shekara 18 tana ganin qawayenta da samari amma ita ta rasa me yasa bata da farinjinin samari ,ita daukan ta baqar fatanta ne yake cutanta dukda ga body tun yanzu akwai shape caraf da ita kalan jikin model maqerin en mata ya fara zanata.
Takaici ne ya ishi Maryam don haka ta shiga kasuwar garinsu neman kurkur da lemun tsami duk da Naira 100 ,mai kurkur zai tsaya mata dogon farashi ,ta fara balbaleshi da masifa "Malam nifa kasada yasa zan ɓannatar da har ₦100 na in siya kurkur ,So nake in fara bilicin din gargajiya kafin kudi ya samu in fara na kanti ,wannan muni har ina! Ga baqin jini kamar nasha hatimin jaɓa....to wai ma tsaya kana da garantin in na dinga goge jikina da kurkur din nan zan fari? Don wallahi in banyi fari na samu saurayi ba sai ka biyani kudina"
"Aah masifa! Gaskiya jeki wani shagon zaki siya kayana da dan kudin nan kuma kina samun sharadi? Aah waya aike Ni bare yaji na dade🤔kasuwa da fadi jeki wajen wani"
Caɓe baki Maryam tayi "Kaji matsalar bahaushe ba ,sam be iya retaining costomer ba ,kai ka Cutu bani ba .Ni kaga tafiya ta"
Daga murya yayi "A sauka lafiya uwar kishiya ta sai kura ,ai in baki sani ba wannan tsiyan naki shi yake koran maki farinjini ,yo ko nine ai dole inji shayin tunkaranki,haka nan in Kwanto ma kaina kura"
"Kanka ake ji matsolo yaso gulma!"
Dalilin hakan yasa Maryam ta fasa siyan kurkur din ta dawo gida wai tayi zuciya ,bilicin din ma An fasa! Kuma mazan kunci uwaku ! Kar Allah yasa ku ganni kuce kuna sona ɗin.
***
Ana wannan ritsitsin sakamakon jarabawan su Maryam ya fito kuma ta fito da grades me kyau duk A ,A Jamb dinta kuwa aggregade nata 375 .
Tuni gomnatin Kano ta bata admission a jami'ar BUK ,suka dauki nauyin karatunta har ta gama kyauta .Zata karanci fannin Madicine .
Iyaye da en uwa sunyi murna sosai ,saidai ba anan gizo ke saqan ba,Baban Maryam Malam Mamman mai itace lokaci daya ya juye shi atafau fau bazata qetare Riruwai ta tafi cikin Kano da sunan wai karatun boko ba ,kalan ta ja masa zagi ,ai shi auren sadaka ma zaiyi da ita.
Anyi dauki ba dadi da su mai unguwa, kafin aka shawo kansa da qyar ya barta taje a matsayin gwaji ,in bayan shekara yaga tarbiyyanta yayi tangarda zai cireta a jami'an yayi mata aure.
Wannan kenan.
****
Tambayan da nasan mai karatu ya zaku yaji amsan shine ? Meye alakan Yazeed da Maryam har take ce masa Yaya? Kuma yaya akayi ta dawo gidansu yazeed da zama?
......Cikin nasara Maryam ta fara karatu a jami'a saidai cikin qanqanin lokaci tayi fice a hostel gata er qauye ba wayewa tayi duk kalan haukan kwalliyarta gashi ba sarki gagaren da ya isa ya gyara mata,to matan da takan anyi tambaya a aji ta mike ta bada amsa daidai anyi dariya amma da aka dawo hostel saida aka ci dambe ,wa ya isa ya mata gyara🤔Duk kalan kwalliyar da tayi haka zakaji Students Dr din nan suna kuzuzuta tayi kyau kiga baki rangandau da jam baki amma a haka duk inda ta gifta zakaji suna melanin ko kaji ana queen queen. Itakuwa in taji haka sai kaga tana washe baki cike da annushuwa .
Jami'a gidan kazo nazo ,duk tsiyan Maryam to su fa comedy suka mai dashi ,don haka ko a school canteen ne in tana fada akan canji tana mere baki tana duddulo ido haka dalibai za suyi ta mata vedio ,su daurata a social media ,kamar wasa attention din mutane ke dawowa akan fuskar melanin ,ana updating vedio enta kiga ruwan likes da views .ita duk abunda akeyi Maryam bata da labari ,har watarana yunwa ta ishi Maryam ta shiga Restaurant din nan dake gefen makaranta ,ta kinkima dauri ta daura farin labcoat dinta da tunda aka bata a makaranta bai taba ganin guga ba ,baki yasha jan baki radau fuskar nan ya cakude da jar hoda da zufa abun dai ba sauki .
Yarkace yarkace ta shiga wajen masu saida abincin da er #200 dinta ,tunda ta hango hotunan abincin harda tuwo tasan dari biyu zai siya mata dauri biyu .
Da qwarin qwuiwarta taje tace a bata tuwo kulli biyu ,ta samu kujera ta kame .
Aikuwa waiter ta kawo ma Maryam semo qulli biyu da miyan kubewa da stew da manyan kpomo guda hudu a cikin miyan ,sai ruwan wanke hannu
A makance Maryam ta saka hannu a roban wanke hannun ta wanke hannu ta fara danna loma zufa yana tsatsafo mata har ta saman hanci.
Duk abunda ke faruwa Dr Yazeed na gefe yana cin chips yana kallonta,sosai ya ganeta melanin da ake sakata ta tiktok .bai gama shan mamaki ba saida kiftawa da bismilla ta cinye tuwon nan ta miqe tana side hannu ta nufi fridge dinsu zata dauki ruwa . Da sauri waiters din suka tare ta saboda kar tayi masu staining manja.
Harara ta Banka masa "Ji wani iskanci meye kake wani hantarata ku haka ake haba hana da costomer?"
"Haba baiwar Allah ji fa yanda duk kika diga ma farin uniform ɗinki miya,kinzo kuma zaki bata mana fridge"
"Yoo kun bani ruwa ne? Ko haka ake kawo abinci a garinku ba ruwa?"
Bai ce komai ba ya dauki ruwa ya bata ,tako murde wuyan ruwan roba ta shiga tittila ma cikinta "Yauwa tunda naci nayi qat,sai duk burauban da za ayi ayi .don ₦200 tal gareni kudin tuwon ku .ruwa kuwa bani nace ka bani ba"
Sa hannu tayi a aljihu ta fiddo ₦200 dinta,ta isa wajen biyan kudi ta mika masu.
Wani mugun kallo mai amsan kudin ya biya dashi "ke meye wannan?"
Maryam a Hassale ta kalli kudin kana ta kalli mutumin "Kudinku mana ,ko sadaka kuke rabawa ne ban sani ba"
Dukan table din gabansa yayi cike da zafin rai wanda hakan yaja hankulan kaf mutanen wajen ,ya soma bude murya yana ma Maryam tijara shi kudinsa 4500₦ ne dukda ruwan da tasha ₦4800 dafe ciki tayi
"Eyyeh kace ₦4800🤔a ciki na ? Sai kace wacce ta cinye tukunyar gidan yawa ! To ko mu kudin cefanen gidanmu 2000₦ ne dan rainin wayau rayuka takwas ake mulla ma tuwo da dubu biyu ,zan siya malmala biyu ka wani ce ₦4800 tuwon naku ma da ko nuna baiyi ba abu duk tsantsi ko meye oho"
"Wallahi ko ki bani kudi na ko in daddalla maki mari er mahaukaciya"
"Nafika zama daqiqiya zoka mareni din,kaga bala'i nida nake siyan fada da kudina !! Zoka tabeni yanzu in yagalgala maka fuska da qumba ,kuma tuwon anci ba'a biya ta qarfi ne in kana da zarrah ka bigeni ka qwata ,shegu ɓarayi macuta wai malmalan tuwon ne ₦4500 halan fashi da makami kuka fara ? Tuni yazeed ya aika yaronsa ya biya kudin ,don haka Waiter din ya dan natsu ganin an miko masa rafan en dubu 1 .bude ido yayi don neman qarin bayani
Nuno masa sashen da Dr Yazeed yake yayi wato shine wanda ya biya kudin.
A tare suka waiga Maryam da waiter din don suga wanda ya biya kudin ,saidai abun haushin yasa hulan face cap ,wato qi-sallah ga kafcecen bakin glass ya kuma ɗan dukkad dakai hannunsa a kan kunnensa yana taɓen earpod din kunnensa bakinsa yana motsi kadan kadan da alamu dai waya yikeyi .