← Book details Kuncin Zuci Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
CHAPTER 2 OF 48

Chapter 01

Kuncin Zuci Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Oxford, England
Zaune take kan sofa cikin madaidaicin apartment din nasu,gabanta laptop ce da textbooks guda biyu wanda ta ajiye kan karamin tebur dake cikin falon nasu tana typing, agefenta kuma cookies ne acikin plate da coffee a ajiye, jifa jifa take kai hannu tana dauka tanaci.
Dukkan hankalinta tamaida kan abunda take typing a laptop din wanda hakan yasa bata juya ta kalli wadda ta fito daga daya daga dakin dake cikin falon ba.
A sannu Nafisa ta qaraso gurinta ta zube akan kujerar, batareda ta juyo ba ko kuma ta bar abunda takeyi ba tace "Good morning" cikin sanyin muryarta wanda yasa Nafisa juyowa tana duban abunda take typing tace
"Morning, what are you working on?"
Matashiyar tace "just some essay"
Nafee tace "shine yayi keeping dinki almost all night?,nafarka around 1 naga lights are still on"
Matashiyar ta sake amsawa da "Eh" Nafee ta tsaya kallonta kawai,can tace "Na'ima" tsayawa matashiyar tayi da rubutun da takeyin ta juyo tana kallon nafisan da manyan idanunta, cikin sanyin muryarta tace "I have deadline for this" Nafee tace "I know, but girl..give yourself a break mana" bata jira amsan Na'ima ba ta miqe ta wuce zuwa kitchen domin hado nata morning coffee din, na'ima batace komai ba ta maida hankalinta kan rubutun da takeyi while sipping her coffee, sanye takeh cikin kayan bacci peach color wanda ya haska farar fatarta, gashinta rufe yake cikin hulan bacci, sai ta ajiye coffee din akan table din tareda dan komawa baya ta manna bayanta da kujerar tana cigaba da cin cookies dinta idonta nakan rubutun nata tana nazarin each line.
Nafee ta fito daga cikin kitchen din hannunta riqe da mug itama ta zauna wajen da ta tashi dazun, a gefen na'ima ta ajiye coffee din saman table tace "kaii, i slept like a baby today" murmushi na'ima tayi tace " you always sleep like a baby ai" 'yar dariya nafee tayi tace "yau na daban neh" na'ima ta sake cewa " i hear you" nafee tace "whatever...zanje shopping anjima naga fast foods dinmu sunyi qasa sannan inason cin tuwo miyan ganye yau dinnan dan nagaji da noodles gaskiya" na'ima tace "dazu nima nayi tunanin nan but my plan was tomorrow don yau nakeson kammala essay dinnan" nafee tace "yaushe neh deadline?" ta amsa da "jibi" nafee tace "toh ai akwai gobe, in Allah ya kaimu sai ki qarasa, muje tare ajiman" sai na'ima ta juyo ta kalleta tace "nafee bansan me goben zatazo dashi ba,tunda I'm halfway through gwara in qarasa once and for all. Beside, saura kadan fa" nafee ta juya idonta dramatically tace "yeah,right" sannan ta dauki satchet na cookies din tana duba calories din jiki tace "wait....these much calories in one cookie?, have to keep my body in check,I have a reputation to protect" na'ima batasan lokacin da ta fara yar dariya ba tace "sannu miss world contestant" nafee ma tana dariya ta dauki throw pillow ta jefa mata suna dariyan tare.
Saida suka lafa da dariyan nafee tace "nayi waya da Mami dazu, ta kiraki kuwa?" na'ima tace "Eh nayi waya da ita jiya da dare, meya faru?" Nafee tace "bawani abu bane,munyi magana akan bikin anty salma ne zan koma next month shine takeson mu taho tare,so i thought ta kiraki" Duk wani annurin dake fuskan na'ima a takeh ya bace tana kallon nafisa. itama nafisan kallonta take tana nazarinta da kuma jiran me zata ce,can ta juya tana jawo laptop dinta tace "A'a bata kirani ba maybe tayi tunanin ban tashi ba amma zan kirata, Allah ya kaimu lokacin zanje..why not?" Nafee dai kallonta take still,ta riqo hannunta daya tace "you don't have to go indai ranki bayaso, nima baifi nayi one week bama in dawo,ni na cewa Mami zan fara tuntubanki da zancen tafiyan tukunna don nasan inta fada miki straight zakice Toh, but kinsan Mami,ban zata ma zata jira nayi miki maganan ba i thought harta kiraki" ta qarasa maganan tana dan dariya, na'ima ta juyo tana murmushi tace "zanje nafee i missed Mami" nafee tace "aikuwa dai ta qagu bikin nan yazo dan kije taganki, always asking ko kinacin abinci ko kuma kinyi qiba ko rama" dan dariya na'ima tayi idonta nadan cikowa da hawaye tace "Mami dai" squeezing hannunta nafee tayi tana reassuring dinta tace "She Cares, and i do too,I'm here always" jijjiga kanta na'ima tayi tana hana hawayen idonta zubowa, nafee ta rungumota kadan tana dan buga bayanta batareda tace komai ba sukayi shiru na wani dan lokaci sannan ta sake ta tace "coffee na yayi sanyi" na'ima tace "nawa yayi qanqara nima" miqewa nafee tayi "bari kiga na dafa mana ko noodles ne" na'ima ta amsa "da kuwa kin taimakeni,yunwa nakeji" wucewa tayi zuwa kitchen din tana cewa "A'a ki dai tsaya nan yin assignment yunwa ta illataki baruwana" murmushi na'ima tayi tana maida hankalinta kan laptop dinta,fara typing dinta keda wuya tunanin maganarsu akan komawarta Abuja ya fado mata rai, shiru tayi ta fada tunani abubuwa dayawa suna dawo mata kanta, The last time she left Abuja in za'a tambayeta biggest wish dinta na rayuwa shine "karta sake komawa Nigeria" Amma yazatayi...shi gida,gida neh ko bata koma domin Mami ta fada ba,tasan dole watarana saita waiwayi rayuwar da ta baro acan Nigeria, dole ne watarana saita koma gida, she's here to find solace amma babu ranar da bata tuna abunda ya sa ta baro gida Nigeria..Ganin tunanin babu inda zai kaita yasa ta rufe laptop din ta wuce nata dakin dake gefen na nafisa don tayi wanka.
Zuwa 11 na safe bayan sun kammala breakfast sun tsaftace gidan nafisa ta tusata a gaba ta chanja kaya suje shopping din tare,a cewarta tunda ta ajiye schoolwork din nata to bazata zauna ita kadai a gida ba..tana murmushi ta tambayi nafisan "ni ke ina naki school work din?" Dariya nafee tayi tana mata wani kallo tace "ni nawa bana hana bacci bane,ke nifah ko exam bazata hanani bacci da hutu ba,Ina dalili" na'ima tace "Eh nima shaida ce" tana tuna lokacin da suke Bayero University Kano nafee dai baza'a taba ganin ta maida hankali akan lectures bama balle sauran school activities, Kuma batacin grade mara kyau domin Allah ya bata ilimin daidai gwargwado,kawai ita haka Allah yayita irin mutanen nan ne marasa sawa aki damuwa bakowanne abu ne yake daga mata hankali har ta sashi arai ba balle lamarin makaranta, sai abun nata ya hadu da gata kuma kasancewarta ita kadai mace wajen iyayenta babu abunda ta rasa daga wajensu da kuma siblings nata maza.
Haka na'ima ta shirya cikin maroon abaya tayi rolling gyalen ta saka flat shoe ta fito zasu tafi tana kallon kayan jikin nafeesa wadda sanye take da white silk jersey short dress ta hada da blue jean trouser tayi rolling white gyale hannunta riqe da car key, farkon zuwan na'ima England nafisa ta sha convincing dinta ta fara dressing kaman nata but she always stand by NO
Abune wanda bata taso taga anayi ba a inda tayi rayuwa. Rayuwarta da ta nafisa kamar banbancin fari da baqi neh wanda tun daga nesa zaka iya hango banbancin su batareda ka matso kusa ba,Amma haka Allah ya hada jininsu suka zamo kawaye tun level 100 a BUK har ila yau da suke Msc tare a Oxford University England.
Haka suka tafi wajen siyayyan a motan da Abban nafisan ya siya musu domin uzurin makaranta da kuma na yau da kullum.
Sun siyo duk kayan buqatunsu harda personal essentials dinsu suka koma gida cikin walwala
Bayan sun huta sunyi sallah nafee ta tafi kitchen zata jera kayan ta bar na'ima nan falo zaune kan sallaya saiga kiran Anty Amnah, qanwar baban nafisa ceh da take aure a London da yaranta biyu twins maza, daukan kiran tayi suka gaisa anty Amnah tace "na'ima munata jiran zuwanku tun jiya i thought zakuzo weekend, Boys suna ta murnan zakuzo har sun gaji,hope kuna lfy" na'ima tana murmushi tace " lafiya anty ,we are sorry, muna research akan wasu essays ne shiyasa bamu samu zuwa ba" anty Amnah tace "No bakomai na'ima dama saida nayi tunanin school activities ne suka riqeku this week, nakira nafee ma no answer hope she's okay" ta amsa cikin sanyinta "Eh lafiyanta kalau anty tana kitchen ne...In Sha Allah next week zamuzo abawa boys hakuri" tace "it's Okay kuhuta gajiya" sukayi sallama ta kashe wayan batakai ga ajiyewa ba kiran Mami yashigo ta daga da sallama tana gaisheta ta daya can bangaren Mami ta amsa da "lafiya kalau Habibti yakuke, ya karatu?" Na'ima tace "Lafiya Mami,yasu yah faruk?"
"Lafiya na'ima,fatan babu matsala ko"
tace "Alhamdulillah Mami"
Mami tace "nafisa tace zakuje siyayya yau" "Eh har mun dawo"
"Ma Sha Allah, Habibti ki kwantar da hankalinki kiyi karatu kinji, sannan ki rinqa addu'a"
Muryar na'ima na dan rawa ta amsa da "in Sha Allah Mami"
Mami tace "it's alright Habibti, everything is going to be fine..in kinji bakyason zuwa bikin Salman ma kiyi zamanki in su amnah zasu dawo zan biyosu inzo na dubaki kinji" Na'ima tace "A'a Mami zanzo, zamu taho tare da nafisan"
Mami tace "Toh na'ima,Allah ya bada sa'an karatu kinji"
Hawaye na taruwa a idonta tace "Amin Mami nagode"
Da haka sukayi sallama tagama goge idonta nafisa tafito daga kitchen hannunta riqe da chocolates guda biyu ta qaraso ta miqa mata daya itama tana bare daya ta zauna kan kujera
tace "Anty Amnah ta kiraki?"
Na'ima ta amsa da "Eh bamu jima da yin waya ba, takiraki baki dauka ba"
Nafee tana gyara zamanta a kujera tace "Nakirata ai, wai tsaya... don't tell me anty amnah tana expecting mu rinqa driving for 2 hours to go to London every two weeks to spend weekend there" murmushi na'ima tayi ta miqe tana cire hijabin jikinta tana girgiza kai draman nafee nabata dariya.
KUNCIN ZUCI
Bintu Musa
Chapter 2 · 0% Book details