← Book details Kauyen Yar Kadde Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 12

Sashe 4

Kauyen Yar Kadde Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Haka suka nufi gida ciki farin ciki ,,suna tafy husna tace my yanxu kam an fasa mun kishiya nasan yau daga hajiya taji zata soni zata bari mukuma sabon gidah,,,dariya umar yayi yace my husna bazamu gayawa hajiya kina da ciki ba sai mun tabbatar,take husna ta hada rai tace ay yanxoma mun tabbatar tonda Dr ya fada ,,yace hakane duk da haka dai muyi shuru tace to ,,,

Haka husna take ta rainun cikinta bana bata boyeshiba ,,kuwa ya ganshi,,, siyayyar kayan yaro kuwa abin baa magana ,,,

Haka har Allah yakawu ranar haihuwa ikon Allah kuma aka haifi mace,,,,

*cigaban labarin*

Ko biyuni

Ummu farhana 😘
*BRILLIANT WRITERS ASS*

👱🏼‍♀👱🏼‍♀👱🏼‍♀👱🏼‍♀👱🏼‍♀
*YA,YA, MATAH*
(Abin Alfahari ne)
👱🏼‍♀👱🏼‍♀👱🏼‍♀👱🏼‍♀👱🏼‍♀

*BY UMMU FARHANA*

*DEDICATE TO MY FANS*❤❤❤💋💋

*MASOYANA KU CIGABA DA HAKURI ,,NA JINA SHURU ABUBUWA NE SAI A HANKALI BA LKC SOSAI ,INA BAKU HAKURI ,RASHIN JINA KULLUM* ,,,

PAGE 8

Haka surayya ta kama hannu su leema suka wuce sashensu ,,lami kuwa aranta cewa tayi jarababbiya ay bansan kina nan ba,,

Husna sosai tasawa kanta damuwa ita kishiya ne bataso ,,,

Bayan umar yadawu a aiki ,,yadauki jinjira ya wucewa zuwa gurin hajiya bayan sun gaisa ,,yace hajiya nakawu jinjira naji baki fadi sunan da zaasa mata ba,,,cewa tayi bani da suna haba umar kai har wani son yarnan kake ace kai kullum a haihuwar mata ,,,baka marmarin da namiji ne nidai abin nan ya isheni ga haihuwa akai akai ga kuma *ya,,ya,, mata*,,

Sunkuyar da kai umar yayi yace kiyi hakuri hajiya Allah ne bai bani da namijin ba ,,,kuma ay da mace da namiji duk dayane ,,masu albarka muke nema,,,

Kul kar kayiwa Allah sharri husna dai Allah bai bataba amma kaikam ay baka so bane ,,,shuru umar yayi ,,ta kuma cewa yau basai gobeba zanje gidan kawata hajiya indo in tambayu maka mata,wallahi nan da karshen wata nakeso kayi aure, wata tara masu zuwa in samu jika namiji,,,sai sannan umar yace ay hajiya kinada jikuki maza dayawa gasunan,,naka nakeson gani umar ,,,yace to hajiya yadda kike so haka zaayi,,,

Yace hajiya baki fadi sunan yarinyar ma,,tayi shuru tace kaje uwarta ta zaba mata kuma ban yanda da suna ba ,,,bani guri, haka umar sim sim yafitah,,,

Yana shiga sashensu ,husna tana ganin shi rai abace ta.mike ta karbi beby tace hajiya tace kayi aure ko na shiga uku ni husna ,,,surayya ta dakamata tsawa tace wai ke akanki aka fara kishiya ne haba,,

Husna tace yanzu shikenan in taxo ta haifi namiji na ga ta kaina ,,,umar ne yace husna saurareni hajiya tace tabaki dama kisawa yarki suna da kike so,,,

Tace hammm tagaji da samu suna ko sheken ,,ni inason kayana ,,,nasamata maryam sunan ummana,kuma sai ta fashe da kuka tace Allah ban raina kyeutar kaba ya Allah ka samin hakuri cikin wannan jarrabawar,,,

Haka umar yayiwa yarinya huduba da suna maryam ,,,shuru har ana jibi suna ba zancen cefanen sunan,,husna tace my bakayi zance suna ba shuru ,yace hajiya tace babu suna kiyi hakuri ,shuru tayi tafito falo da gayawa surayya ,ay bata jira karshen zance ba tayi waje sai dakin haji ,,,

Da sallama tashiga ,,hajiya ce ke shirin fida,, aw hajiya fita zakiyi ne ,,tace eh surayya da wani Abu ne ,,tace eh batun suna nazu naji danki yace ba suna to wallahi ko sama da kasa zata hade sai anyi suna haba yar shegiyace ko me ,,,hajiya tace ba shegiya bace amma ay mace ce mace koma har wani daraja ne da ita,in zakuyiwa yarku suna ban hanakuba amma ba sisin umar ,Dan aure yasa agaba yanzuma naimar masa aure zanje,,,,

Surayya tace wanan damuwarki ce ki aura masa hudu in kin isa ba akan husna zasu zauna ba. ,,,kuma in keki ke bada haihuwa ki basu mazan,,,

Suna kuwa sai anyi kuma umar ne zaiyi tunda shine uban yar

Tana gama fada tayi waje hajiyama fitowa tayi tayi gidan kawarta naima wa umar mata,

Surayya bashiga sashen husna tace umar ,dasauri ya fito ,tace mgnr suna wallahi in bakayi suna ba abakacin aurnka da husna haba hakurin tayi yawa sbd ta haifi mace ,,,yace anty kiyi hakuri umarnin hajiyane ,,,tace ay bance doleba ga hannuna ko kudin suna ko takardar sakin husna in natafi da ita nayi sunan da dalili ,sai kuma tasa kuka umar sabda maraici kake mana haka ko,,rikicewa umar yayi yace to anty ki rubuta me kuke bukata yanzo ,,haka suka rubuta suka bashi yanufi kasuwa,daman shima yanason ayi to amma yana tsoron rigimar hajiya,,,

Gidan hajiya indo bayan an gaggaisa an taba hira hajiya ta kwalawa yarta hajar kira,ta fito ,tace kawuwa bakuwa ruwa,tana fita hajiya tace indo ina kika samu budurwa haka tace,kai hajiya har kin manta hajar ne auta tace ay dayake makarantar kwana take jiya ta dawu sun gama,,,

Hajiya umar tace shekenan faduwa tazo daidai da zama dama danki umar nazo naimawa matah ko a ya,ya, yanuwanki,Ashe akwai ma a gidah,,,

Indo tace to ina matarshi ,tanan nan kari zaiyi ,,indo tace amma dai lfy ko ,,hajiya tace inafa lfy bata da aiki sai haihuwr ya,ya, mata gasunan har biyar ras,,indo tace gaskiya kama mezaayi da tarin mata ,,,hajiya tace Allah yasa dai baki mata mijiba ,,tace ay ko anyi a fasa ga na gida, ba ayiba ki turushi yazu su dai daidaita,,,

Haka hajiya tayi godiya SBD ita gani take hajar tunda duk gidan su mazane ita kadaice mace to ba makawa itama maza zata haifa kuji fa,,

Yaune suna ya taci suna maryam kuma yau surayya zata kuma gidanta damaturu ,,haka tayi tayiwa husna nasiha sanan tace mata kuma tayi hakuri ta rage kishi,,, haka surayya ta tafi ,suna begen juna da yar uwarta,,,

Umar ne zaune suna hira da hajiya tace masa ,ka shirya kaje gidan kawata indo mun gama mgn da ita ,,zakaje Ku daidaita da yarta ,,,

Ra's gaban umar yafadi har wani gumi ya hada yace hajiya da wuri haka banfa gama gini nah bah ,kuma kinga,tace rufemin baki India nice uwarka aure da hajar ba fashi husnan kishi ya kasheta,,,,

Jiri ne yake dibansa haka ya karaso sashensu ,yama rasa ta ina zaifara gayawa husna,,,

Kubashi shawara makaranta taya zai fara😃.

Taku uwar farhana😘
*BRILLIANT WRITERS ASSO*

👱🏼‍♀👱🏼‍♀👱🏼‍♀👱🏼‍♀👱🏼‍♀
*YA,,YA,, MATA*
(Abin Alfaharine)
👱🏼‍♀👱🏼‍♀👱🏼‍♀👱🏼‍♀👱🏼‍♀

*DEDICATED TO ZARA,U A MAHMUD*

*BANA GAJIYA DAI NACE KUYI HAKURI*

PAGE 9

Husna tai mai sannu da zuwa ,,,ta kawushi abinci ,,shi dai yayi jugum dashi yama rasa ha zaiyi ,,husna tace my lfy naga kayi shuru ko da mastala ne kaci abinci mana,,,

Yace to haka dai yake chakolar abincin daga karshe dai yatashi ya shiga wanka ,,bayan yafito mah ya zauna shuru,,,

Matsuwa kusa dashi husna tayi tace darling menene wai ,,,kafin yayi magana sai ji sukayi ance eyye lalle mah kin hanashi fita ko wato kai umar nace kaje gidan indo gurin hajar shine kazo ka zauna ko,, to maza tashi ka tafi indai ni na haifeka wannan aure ba fashi sai anyi,yace to hajiya naji zantafi amma bari muyi mgn da husna dama yanzu nakeson gayamata sai in tafi,,,,

Sbd itace uwarka ko sai ka naimi izinnta ba ,,sai tasa kuka ,shikuma umar aduniya ba abin da ya tsanah kamar. Kukan hajiya ,ay baibi takan husna ba ya zari key yay waje,,hajiyama tabishi a baya,, har tafita ta dawu tace, bari kiji na naimawa dana mata wanda zata haifa mar yaya maza kekuma ki zauna ki yi ta haihuwar mata takaicine zai kasheki ,tajuya a fusace tai waje,,,

Husna dai duk masifar hajiya bai dametaba abin da ya dameta shine mgnr auren umar ita a rayuwarta kishiyace bataso ,,haka ta zauna zaman kusan awa ba kuka ba addua ,,,chan dai tace Allah humma lasahala har zuwa karshe,,atake taji wani sanyi ya ziyarceta kuma chan sai kuka sai da tayi mai isarta San nan tai shuru ,,,tafara tunani,,

Umar bayan fitarshi bai zame ko ina ba sai gidan abokin shi salim ,,awaya yakira salim yafito yace abokina ya akayi ne yau bazaka shigo bane ,,,umar yace barni anan kawai ,,,salim yace to ya na ganka haka a gigice ,,umar ya bashi lbrn yadda sukayi da hajiya ga kuma husna ,,,salim ma yaji ba dadi amma sai yace umar dolene kabi umarnin hajiya ita kuma husna kaje ka rarrashi abinka barin shiga in kinsta in zo in rakaka,,,

Bayan salim yafito sun shiga muta suna tafiya umar yace salim a rayuwata bani da raayin auren mace fiye da daya amma gashi hajiya ta matsamin kawai dai da uwace,,,salim yace hakane umar dama kana naka Allah na nasa,

Bayan sun isa yaro suka ayka ya kira musu hajar inji umar ,,,bayan mintina kadan sai gata tai musu iso dakin zaure ,,

Sannu da zuwa tai musu a yangace sannan tace wanne ne angon nawa salim da umar duka abin yabasu mamaki ,,salim nai yayi karfin hali ya nuna umar yace gashi nan ,,,dasauri ta kara kujerar da yake zaune ta kamu hannunsa tace ina ba barka da zuwa da fatan ka amince dani kamar yadda na amince da kai,,,shidai umar abin ma haushi yabashi ya warce hannun sa ,,daga kan da zaiyi sai yaga wayam salim bayanan,,shima sai ya mike yace to ni zantafi ,,,zaro ido hajar tayi tace haba daga zuwa kai ko mgn ma bakayiba ,ta fara dire kafa alamar shagwaba ,wai bazai tafi bah,,,

Sai sannan umar ya karemata kallo ba laifi bata da muni ko kadan ,,,yace kinga bani hanya sauri nake ya hada rai bashiri ta matsa,,,

Yana fita yacewa salim kai banza ne kawai zaka tafi ka barni,,, salim ya kwashe da dariya yace to ay gani nayi ba a bukatar gabatarwa kaga yarinya karama da rawar kai lalle hajiya ta hadaka da kwaila suka dada kwashewa da dariya umar yace in banda hajiya ina zan kai wan nan uwar rawar kan ay wataran sai in duketa dariya salim yayi yace sai kace a shirin film ,Kai dai Allah ya sanya Alheri kawai ,shuru umar yayi,,a haka ya sauke salim ya wuce gida ,,,
Chapter 4 · 0% Book details